A farko-farko, Allah ya halicci sama da ƙasa. To, ƙasa dai ba ta da siffa, babu kuma kome a cikinta, duhu ne kawai ya rufe ko’ina, Ruhun Allah kuwa yana yawo a kan ruwan. Sai Allah ya ce, “Bari haske yă kasance,” sai kuwa ga haske. Allah ya ga hasken yana da kyau, sai ya raba tsakanin hasken da duhu. Allah ya kira hasken “yini,” ya kuma kira duhun “dare.” Yamma ta kasance, safiya kuma ta kasance, kwana ta fari ke nan. Allah ya ce, “Bari sarari yă kasance tsakanin ruwaye domin yă raba ruwa da ruwa.” Saboda haka Allah ya yi sarari ya raba ruwan da yake ƙarƙashin sararin da ruwan da yake bisansa. Haka kuwa ya kasance. Allah ya kira sararin “sama.” Yamma ta kasance, safiya kuma ta kasance, kwana ta biyu ke nan. Allah ya ce, “Bari ruwan da yake ƙarƙashin sama yă tattaru wuri ɗaya, bari kuma busasshiyar ƙasa tă bayyana.” Haka kuwa ya kasance. Allah ya kira busasshiyar ƙasar “doron ƙasa,” ruwan da ya taru kuma, ya kira “tekuna.” Allah ya ga yana da kyau. Sa’an nan Allah ya ce, “Bari ƙasa tă fid da tsire-tsire, da shuke-shuke, da itatuwa a bisa ƙasa masu ba da amfani da ’ya’ya a cikinsu, bisa ga irinsu.” Haka kuwa ya kasance. Ƙasar ta fid da tsire-tsire, da shuke-shuke masu ba da ’ya’ya bisa ga irinsu, ta fid kuma da itatuwa masu ba da ’ya’ya da iri a cikinsu bisa ga irinsu. Allah ya ga yana da kyau. Yamma ta kasance, safiya kuma ta kasance, kwana ta uku ke nan. Allah kuma ya ce, “Bari haskoki su kasance a sararin sama domin su raba yini da dare, bari su zama alamu domin su nuna yanayi, da ranaku, da kuma shekaru, bari kuma haskokin su kasance a sararin sama domin su ba da haske a duniya.” Haka kuwa ya kasance. Allah ya yi manyan haskoki biyu, babban hasken yă mallaki yini, ƙaramin kuma yă mallaki dare. Ya kuma yi taurari. Allah ya sa su a sararin sama domin su ba da haske a duniya, su mallaki yini da kuma dare, su kuma raba haske da duhu. Allah kuwa ya ga yana da kyau. Yamma ta kasance, safiya kuma ta kasance, kwana ta huɗu ke nan. Allah ya ce, “Bari ruwa yă cika da halittu masu rai, bari tsuntsaye kuma su tashi sama a bisa duniya a sararin sama.” Allah ya halicci manyan halittun teku, da kowane mai rai da abin da yake motsi a ruwa, bisa ga irinsu, da kuma kowane tsuntsu mai fiffike bisa ga irinsa. Allah kuwa ya ga yana da kyau. Allah ya albarkace su ya ce, “Ku yi ta haihuwa ku kuma ƙaru da yawa, ku cika ruwan tekuna, bari kuma tsuntsaye su yi yawa a bisa duniya.” Yamma ta kasance, safiya kuma ta kasance, kwana ta biyar ke nan. Allah kuwa ya ce, “Bari ƙasa tă ba da halittu masu rai bisa ga irinsu; dabbobi da halittu masu rarrafe, da kuma namun jeji, kowane bisa ga irinsa.” Haka kuwa ya kasance. Allah ya halicci namun jeji bisa ga irinsu, dabbobi bisa ga irinsu, da kuma dukan halittu masu rarrafe a ƙasa bisa ga irinsu. Allah kuwa ya ga yana da kyau. Sa’an nan Allah ya ce, “Bari mu yi mutum cikin siffarmu, cikin kamanninmu, bari kuma su yi mulki a bisa kifin teku, tsuntsayen sama, da kuma dabbobi, su yi mulki a bisa dukan duniya, da kuma a bisa dukan halittu, da masu rarrafe a ƙasa.” Saboda haka Allah ya halicci mutum cikin siffarsa. Cikin kamannin Allah, Allah ya halicci mutum. Miji da mace ya halicce su. Allah ya albarkace su, ya kuma ce musu, “Ku yi ta haihuwa ku ƙaru da yawa, ku mamaye duniya, ku mallake ta. Ku yi mulki a bisa kifin teku, da tsuntsayen sararin sama, da kuma bisa kowace halitta mai rai wadda take rarrafe a ƙasa.” Sa’an nan Allah ya ce, “Ga shi, na ba ku kowane tsiro mai ba da ’ya’ya masu kwaya da suke a fāɗin duniya, da dukan itatuwa masu ba da ’ya’ya, don su zama abinci a gare ku. Na kuma ba da dukan dabbobin ƙasa, da dukan tsuntsayen sama, da dukan abin da yake rarrafe a ƙasa, da dai iyakar abin da yake numfashi; haka kuma na ba da ganyaye su zama abinci.” Haka kuwa ya kasance. Allah ya ga dukan abin da ya yi, yana da kyau ƙwarai. Yamma ta kasance, safiya kuma ta kasance, kwana ta shida ke nan. Ta haka aka gama yin sammai da duniya da dukan abubuwan da suke cikinsu. Kafin kwana ta bakwai, Allah ya gama aikin da yake yi, saboda haka a kwana ta bakwai, ya huta daga dukan aikinsa. Allah kuwa ya albarkaci kwana ta bakwai, ya kuma mai da ita mai tsarki, saboda a kanta ne ya huta daga dukan aikin halittar da ya yi. Wannan shi ne asalin tarihin sammai da duniya sa’ad da aka halicce su. Sa’ad da Ubangiji Allah ya yi duniya da sammai, babu tsiro a duniya kuma ganyaye ba su tsira a busasshiyar ƙasa ko ba, gama Ubangiji Allah bai aiko da ruwan sama a kan duniya ba tukuna, babu kuma wani mutumin da zai nome ƙasar, amma dai rafuffuka suna ɓullo da ruwa daga ƙasa suna jiƙe ko’ina a fāɗin ƙasa. Sa’an nan Ubangiji Allah ya yi mutum daga turɓayar ƙasa, ya kuma hura numfashin rai cikin hancinsa, mutumin kuwa ya zama rayayyen taliki. To, fa, Ubangiji Allah ya yi lambu a gabas, a Eden, a can kuwa ya sa mutumin da ya yi. Ubangiji Allah ya kuma sa kowane irin itace ya tsira daga ƙasa, itace mai kyan gani, mai amfani kuma don abinci. A tsakiyar lambun kuwa akwai itacen rai da kuma itacen sanin abin da yake da kyau da abin da yake mugu. Akwai wani kogi mai ba da ruwa ga lambun wanda ya gangaro daga Eden, daga nan ya rarrabu, ya zama koguna huɗu. Sunan kogi na fari, Fishon. Shi ne yake malala kewaye da dukan ƙasar Hawila, inda akwai zinariya. (Zinariyar wannan ƙasa kuwa tana da kyau, akwai kuma kayan ƙanshi da duwatsun da ake kira onis a can ma.) Sunan kogi na biyu, Gihon. Shi ne ya malala kewaye da ƙasar Kush. Sunan kogi na uku Tigris. Wannan ne ya malala ya bi ta gefen gabashin Asshur. Kogi na huɗu kuwa shi ne Yuferites. Ubangiji Allah ya ɗauko mutumin ya sa shi cikin Lambun Eden domin yă nome shi, yă kuma lura da shi. Ubangiji Allah ya umarci mutumin ya ce, “Kana da ’yanci ka ci daga kowane itace a cikin lambun, amma kada ka ci daga itacen sanin abin da yake mai kyau da abin da yake mugu, gama a ranar da ka ci shi, lalle za ka mutu.” Ubangiji Allah ya ce, “Bai yi kyau mutumin yă kasance shi kaɗai ba. Zan yi masa mataimakin da ya dace da shi.” To, Ubangiji Allah ya yi dukan namun jeji da dukan tsuntsayen sama daga ƙasa. Ya kawo su wurin mutumin don yă ga wanda suna zai kira su; kuma duk sunan da mutumin ya kira kowane mai rai, sunansa ke nan. Saboda haka mutumin ya sa wa dukan dabbobi, da tsuntsayen sama da dukan namun jeji sunaye. Amma ba a sami mataimakin da ya dace da Adamu ba. Saboda haka Ubangiji Allah ya sa mutumin ya yi barci mai nauyi; yayinda yake barci sai ya ɗauko ɗaya daga cikin haƙarƙarin mutumin, ya kuma rufe wurin da nama. Sa’an nan Ubangiji Allah ya yi mace daga haƙarƙarin da ya ɗauko daga mutumin, ya kuwa kawo ta wurin mutumin. Sai mutumin ya ce, “Yanzu kam wannan ƙashi ne na ƙasusuwana nama kuma na namana. Za a ce da ita ‘mace,’ gama an ciro ta daga namiji.” Wannan ne ya sa mutum yakan bar mahaifinsa da mahaifiyarsa, yă manne wa matarsa, su kuma zama jiki ɗaya. Mutumin da matarsa, dukansu biyu tsirara suke, ba su kuwa ji kunya ba. To, maciji dai ya fi kowane a cikin namun jejin da Ubangiji Allah ya yi wayo. Ya ce wa macen, “Tabbatacce ne Allah ya ce, ‘Kada ku ci daga kowane itace a lambu’?” Macen ta ce wa macijin, “Za mu iya ci daga ’ya’ya itatuwa a lambun, amma Allah ya ce, ‘Kada ku ci daga ’ya’yan itacen da yake tsakiyar lambu, kada kuma ku taɓa shi, in ba haka ba kuwa za ku mutu.’ ” Maciji ya ce wa macen, “Tabbatacce ba za ku mutu ba. Gama Allah ya san cewa sa’ad da kuka ci daga itacen idanunku za su buɗe, za ku kuma zama kamar Allah, ku san abin da yake mai kyau da abin da yake mugu.” Sa’ad da macen ta ga ’ya’yan itacen suna da kyau don abinci, abin sha’awa ga ido, abin marmari kuma don samun hikima, sai ta tsinka ta ci, ta kuma ba da waɗansu wa mijinta wanda yake tare da ita, shi ma ya ci. Sa’an nan idanun dukansu biyu suka buɗe, suka kuma gane tsirara suke; saboda haka suka ɗinɗinka ganyayen ɓaure suka yi wa kansu sutura. Da mutumin da matarsa suka ji motsin Ubangiji Allah yana takawa a lambun a sanyin yini, sai suka ɓuya daga Ubangiji Allah a cikin itatuwan lambu. Amma Ubangiji Allah ya kira mutumin ya ce, “Ina kake?” Ya ce, “Na ji ka a cikin lambu, na kuwa ji tsoro gama ina tsirara, saboda haka na ɓuya.” Sai ya ce, “Wa ya faɗa maka cewa kana tsirara? Ko dai ka ci daga itacen da na umarce ka kada ka ci ne?” Mutumin ya ce, “Macen da ka sa a nan tare da ni, ita ta ba ni waɗansu ’ya’ya daga itacen, na kuwa ci.” Sai Ubangiji Allah ya ce wa matar, “Me ke nan kika yi?” Matar ta ce, “Macijin ne ya ruɗe ni, na kuwa ci.” Saboda haka Ubangiji Allah ya ce wa macijin, “Saboda ka yi haka, “Na la’anta ka cikin dukan dabbobi da kuma cikin dukan namun jeji! Daga yanzu rubda ciki za ka yi tafiya turɓaya kuma za ka ci dukan kwanakin rayuwarka. Zan kuma sa ƙiyayya tsakaninka da macen, tsakanin zuriyarka da zuriyarta. Zai ragargaje kanka, kai kuma za ka sari ɗiɗɗigensa.” Sa’an nan ya ce wa macen, “Zan tsananta naƙudarki ainun, da azaba kuma za ki haifi ’ya’ya. Za ki riƙa yin marmarin mijinki zai kuwa yi mulki a kanki.” Ga Adamu kuwa ya ce, “Saboda ka saurari matarka, ka kuma ci daga itacen da na ce, ‘Kada ka ci,’ “Za a la’anta ƙasa saboda kai. Da wahala za ka ci daga cikinta dukan kwanakin rayuwarka. Za tă ba ka ƙayayyuwa da sarƙaƙƙiya za ka kuwa ci ganyayen gona. Da zuffan goshinka za ka ci abincinka har ka koma ga ƙasa, da yake daga cikinta aka yi ka. Gama kai turɓaya ne, kuma ga turɓaya za ka koma.” Mutumin ya sa wa matarsa suna, Hawwa’u, gama za tă zama mahaifiyar masu rai duka. Ubangiji Allah ya yi tufafin fata domin Adamu da Hawwa’u, ya kuma yi musu sutura. Ubangiji Allah ya kuma ce, “To, fa, mutum ya zama kamar ɗaya daga cikinmu, ya san abin da yake mai kyau da abin da yake mugu. Kada a yarda yă miƙa hannunsa yă ɗiba daga itacen rai yă ci, yă kuma rayu har abada.” Saboda haka Ubangiji Allah ya kore shi daga Lambun Eden domin yă nome ƙasa wadda aka yi shi. Bayan da ya kori mutumin, sai ya sa kerubobi da takobi mai harshen wuta yana jujjuyawa baya da gaba a gabashin Lambun Eden don yă tsare hanya zuwa itacen rai. Adamu ya kwana da matarsa Hawwa’u, ta kuwa yi ciki ta haifi Kayinu. Sai ta ce, “Da taimakon Ubangiji na sami ɗa namiji.” Daga baya ta haifi ɗan’uwansa, ta kuma ba shi suna Habila. Sa’ad da suka yi girma sai Habila ya zama makiyayin tumaki, Kayinu kuwa ya zama manomi. Ana nan sai Kayinu ya kawo waɗansu amfanin gona a matsayin hadaya ga Ubangiji. Amma Habila ya kawo mafi kyau daga ’ya’yan fari na garkensa. Ubangiji ya yi farin ciki da sadakar da Habila ya kawo, amma bai yi farin ciki da sadakar da Kayinu ya kawo ba. Saboda haka Kayinu ya ji fushi sosai, fuskarsa kuma ta ɓace. Sai Ubangiji ya ce wa Kayinu, “Don me kake fushi? Don me fuskarka ta ɓace? Da ka yi abin da yake daidai, ai, da ka sami karɓuwa. Amma tun da ba ka yi abin da ba daidai ba, zunubi zai yi fakonka don yă rinjaye ka kamar naman jeji. Yana so yă mallake ka, amma tilas ka rinjaye shi.” To, Kayinu ya ce wa ɗan’uwansa Habila, “Mu tafi gona.” Yayinda suke a gona, sai Kayinu ya tasar wa Habila ya buge shi ya kashe. Sai Ubangiji ya ce wa Kayinu, “Ina ɗan’uwanka Habila?” Sai Kayinu ya ce, “Ban sani ba, ni mai gadin ɗan’uwana ne?” Ubangiji ya ce, “Me ke nan ka yi? Saurara! Ga jinin ɗan’uwanka yana mini kuka daga ƙasa. Yanzu, kai la’ananne ne, an kuma kore ka daga ƙasa wadda ta buɗe bakinta ta shanye jinin ɗan’uwanka daga hannunka. In ka nome ƙasa, ba za tă ƙara ba ka hatsinta ba. Za ka kuma zama mai yawo barkatai a duniya.” Kayinu ya ce wa Ubangiji, “Horon nan ya sha ƙarfina. Ga shi, yau kana kori na daga ƙasar, zan zama a ɓoye daga fuskarka, zan kuma zama mai yawo barkatai, duk wanda ya same ni kuwa zai kashe ni.” Amma Ubangiji ya ce masa, “Ba haka ba ne! Duk wanda ya kashe Kayinu, za a ninƙa hukuncinsa har sau bakwai.” Sa’an nan Ubangiji ya sa wa Kayinu alama don duk wanda ya same shi kada yă kashe shi. Saboda haka Kayinu ya yi tafiyarsa ya rabu da Ubangiji, ya je ya zauna ƙasar Nod a gabashin Eden. Kayinu ya kwana da matarsa, ta kuwa yi ciki, ta haifi Enok. A lokacin Kayinu yana gina birni, sai ya sa wa birnin sunan ɗansa Enok. Aka haifa wa Enok Irad, Irad kuma ya haifi Mehujayel, Mehujayel kuma ya haifi Metushayel, Metushayel kuma ya haifin Lamek. Lamek ya auri mata biyu, ana ce da ɗaya Ada, ɗayan kuma Zilla. Ada ta haifi Yabal, shi ne mahaifi waɗanda suke zama a tentuna, suna kuma kiwon dabbobi. Sunan ɗan’uwansa Yubal, shi ne mahaifin dukan makaɗan garaya da masu hura sarewa. Zilla ma ta haifi ɗa, Tubal-Kayinu, shi ne wanda ya ƙera kowane iri kayan aiki daga tagulla da kuma ƙarfe. ’Yar’uwar Tubal-Kayinu ita ce Na’ama. Wata rana, Lamek ya ce wa matansa, Ada da Zilla, “Ku saurara, matan Lamek, ku ji maganata. Na kashe wani saboda ya yi mini rauni, na kashe wani saurayi saboda ya ji mini ciwo. Idan za a rama wa Kayinu har sau bakwai, lalle za a rama wa Lamek sau saba’in da bakwai ke nan.” Sai Adamu ya sāke kwana da matarsa, ta haifi ɗa, aka kuma ba shi suna Set, gama ta ce, “Allah ya ba ni wani yaro a madadin Habila, tun da yake Kayinu ya kashe shi.” Set ma ya haifi ɗa, ya kuma kira shi Enosh. A lokaci ne, mutane suka fara kira ga sunan Ubangiji. Wannan shi ne rubutaccen tarihin zuriyar Adamu. Sa’ad da Allah ya halicci mutum, ya yi shi cikin kamannin Allah. Ya halicce su namiji da ta mace, ya kuma albarkace su. Sa’ad da kuma aka halicce su, ya kira su “Mutum.” Sa’ad da Adamu ya yi shekaru 130, sai ya haifi ɗa wanda ya yi kama da shi, ya kuma kira shi Set. Bayan an haifi Set, Adamu ya yi shekaru 800, ya kuma haifi waɗansu ’ya’ya maza da mata. Gaba ɗaya dai, Adamu ya yi shekaru 930, sa’an nan ya mutu. Sa’ad da Set ya yi shekara 105, sai ya haifi Enosh. Bayan ya haifi Enosh, Set ya yi shekara 807, ya kuma haifi waɗansu ’ya’ya maza da mata. Gaba ɗaya dai, Set ya yi shekaru 912, sa’an nan ya mutu. Sa’ad da Enosh ya yi shekara 90, sai ya haifi Kenan. Bayan ya haifi Kenan, Enosh ya yi shekara 815, ya kuma haifi waɗansu ’ya’ya maza da mata. Gaba ɗaya dai, Enosh ya yi shekaru 905, sa’an nan ya mutu. Sa’ad da Kenan ya yi shekara 70, sai ya haifi Mahalalel. Bayan ya haifi Mahalalel, Kenan ya yi shekara 840, ya kuma haifi waɗansu ’ya’ya maza da mata Gaba ɗaya dai, Kenan ya yi shekara 910, sa’an nan ya mutu. Sa’ad da Mahalalel ya yi shekara 65, sai ya haifi Yared. Bayan ya haifi Yared, Mahalalel ya yi shekara 830, ya kuma haifi waɗansu ’ya’ya maza da mata Gaba ɗaya dai, Mahalalel ya yi shekara 895, sa’an nan ya mutu. Sa’ad da Yared ya yi shekara 162, sai ya haifi Enok. Bayan ya haifi Enok, Yared ya yi shekaru 800, ya kuma haifi waɗansu ’ya’ya maza da mata. Gaba ɗaya dai, Yared ya yi shekara 962, sa’an nan ya mutu. Sa’ad da Enok ya yi shekara 65, sai ya haifi Metusela. Bayan ya haifi Metusela, Enok ya kasance cikin zumunci da Allah shekaru 300, ya kuma haifi waɗansu ’ya’ya maza da mata. Gaba ɗaya dai, Enok ya yi shekaru 365. Enok ya kasance cikin zumunci da Allah, sa’an nan ba a ƙara ganinsa ba. Saboda Allah ya ɗauke shi. Sa’ad da Metusela ya yi shekara 187, sai ya haifi Lamek. Bayan ya haifi Lamek, Metusela ya yi shekaru 782, ya kuma haifi waɗansu ’ya’ya maza da mata. Gaba ɗaya dai, Metusela ya yi shekaru 969, sa’an nan ya mutu. Sa’ad da Lamek ya yi shekara 182, sai ya haifi ɗa. Ya ba shi suna Nuhu ya kuma ce, “Zai yi mana ta’aziyya a cikin aikinmu da wahalar hannuwanmu a ƙasar da Ubangiji ya la’anta.” Bayan an haifi Nuhu, Lamek ya yi shekara 595, yana kuma da ’ya’ya maza da mata. Gaba ɗaya dai, Lamek ya yi shekaru 777, sa’an nan ya mutu. Bayan Nuhu ya yi shekara 500, sai ya haifi Shem, Ham da Yafet. Sa’ad da mutane suka fara ƙaruwa a duniya, aka kuma hahhaifi musu ’ya’ya mata, sai ’ya’yan Allah maza suka ga cewa ’ya’yan mutane mata suna da bansha’awa, sai suka zaɓi waɗanda suke so, suka aura. Sa’an nan Ubangiji ya ce, “Ruhuna ba zai zauna a cikin mutum har abada ba, saboda shi mai mutuwa ne, kwanakinsa za su zama shekaru ɗari da arba’in ne.” Nefilimawa suna nan a duniya a waɗancan kwanaki, da kuma kwanakin da suka bi baya, a sa’ad da ’ya’yan Allah suka kwana da ’ya’yan mutane mata, suka kuma hahhaifi musu ’ya’ya. Ai, su ne jarumawan dā, mutanen da suka shahara. Ubangiji kuwa ya lura cewa muguntar mutum ta yi yawa a duniya, kuma kowane abin da yake tunani a zuciyarsa mugu ne kawai a kowanne lokaci. Ubangiji ya damu da ya yi mutum a duniya, abin ya zafe shi ƙwarai. Saboda haka Ubangiji ya ce, “Zan kawar da mutum, da dabbobi, da halittu masu rarrafe a ƙasa da kuma tsuntsayen sama waɗanda na halitta, daga doron ƙasa, saboda na damu da na yi su.” Amma Nuhu ya sami tagomashi a gaban Ubangiji. Ga tarihin Nuhu. Nuhu mutum ne mai adalci, marar abin zargi a cikin mutanen zamaninsa, ya kuma yi tafiya tare da Allah. Nuhu yana da ’ya’ya maza uku, Shem, Ham da Yafet. Duniya dai ta lalace sosai a gaban Allah, ta kuma cika da tashin hankali. Allah ya ga yadda duniya ta lalace, gama dukan mutane a duniya sun lalatar da rayuwarsu. Saboda haka, Allah ya ce wa Nuhu, “Zan kawo ƙarshen dukan mutane, gama saboda su duniya ta cika da tashin hankali. Lalle zan hallaka su da kuma duniya. Saboda haka ka yi wa kanka jirgi da katakon Saifires, ka yi ɗakuna a cikinsa, ka shafe shi da ƙaro ciki da waje. Ga yadda za ka gina shi; jirgin zai kasance mai tsawon ƙafa 45, fāɗinsa ƙafa 75, tsayinsa kuma ƙafa 45. Ka yi masa rufi, ka kuma ba da fili inci 18 tsakanin rufin a kowane gefen jirgin. Ka sa ƙofa a gefen jirgin. Ka yi shi hawa uku, ka yi ƙofa a gefe. Ga shi zan aiko da ambaliya ruwa a duniya, in hallaka dukan mai rai da yake a ƙarƙashin sama, kowace halittar da take numfashi a cikinta. Dukan abin da yake a duniya zai hallaka. Amma zan kafa alkawarina da kai, kai kuma za ka shiga jirgin, kai da ’ya’yanka maza da matarka da matan ’ya’yanka tare da kai. Za ka shigar da biyu na dukan halittu masu rai, namiji da ta mace a cikin jirgin, domin su rayu tare da kai. Biyu na kowane irin tsuntsu, kowace irin dabba da kuma kowace irin halitta mai rarrafe a ƙasa, za su zo wurinka domin a bar su da rai. Za ka ɗauki kowane irin abinci wanda za a ci, ka adana don yă zama abincinka da nasu.” Nuhu ya yi kome kamar yadda Allah ya umarce shi. Sa’an nan Ubangiji ya ce wa Nuhu. “Shiga jirgin, kai da dukan iyalinka, gama na ga kai mai adalci ne a wannan zamani. Ka ɗauki bakwai na kowace iri tsabtaccen dabba tare da kai, namiji da ta mace, da kuma biyu na kowace dabba marar tsabta, namiji da ta mace, da kuma bakwai na kowane iri tsuntsu, namiji da ta mace, domin a bar kowane irinsu da rai a dukan duniya. Kwana bakwai daga yanzu zan aiko da ruwa a duniya yini arba’in da dare arba’in, zan kuma kawar da kowace halitta mai rai da na yi daga doron ƙasa.” Nuhu ya aikata duk abin da Ubangiji ya umarce shi. Nuhu yana da shekaru 106 ne sa’ad da aka yi ambaliya ruwa a duniya. Nuhu da matarsa da ’ya’yansa da matansu, suka shiga jirgi domin su tsira daga ruwa ambaliya. Biyu-biyu daga dabbobi masu tsabta da marasa tsabta, da tsuntsaye da kuma dukan halittu masu rarrafe a ƙasa, namiji da ta mace, suka zo wurin Nuhu, suka shiga jirgi, kamar yadda Allah ya umarce Nuhu. Bayan kwana bakwai kuwa ambaliya ruwa ta sauko a bisa duniya. A ranar sha bakwai ga wata na biyu, na shekara ta ɗari shida na rayuwar Nuhu, a ran nan sai dukan maɓuɓɓugai na manyan zurfafa suka fashe, tagogin sammai suka buɗe. Ruwa yana ta kwararowa bisa duniya, yini arba’in da dare arba’in. A wannan rana Nuhu tare da matarsa da ’ya’yansa maza, Shem, Ham da Yafet da matansu uku suka shiga jirgi. Tare da su kuwa, akwai kowane naman jeji bisa ga irinsa, da dukan dabbobin gida bisa ga irinsu, da kowace halitta mai rarrafe a ƙasa bisa ga irinta, da kowane tsuntsun gida da na jeji bisa ga irinsa, da dukan abu mai fiffike. Biyu-biyu na dukan halittu masu numfashi suka zo wurin Nuhu, suka shiga jirgi. Dabbobi da kowane abu mai rai da suka shiga ciki, namiji ne da ta mace, yadda Allah ya umarci Nuhu. Sa’an nan Ubangiji ya kulle jirgin daga baya. Kwana arba’in ambaliya ta yi ta saukowa a duniya, sa’ad da ruwa ya yi ta ƙaruwa sai ya yi ta ɗaga jirgin sama, ya kuwa tashi can bisa duniya. Ruwa ya taso, ya ƙaru ƙwarai a duniya, jirgin kuma ya yi ta yawo a bisa ruwa. Ruwa ya ƙaru ƙwarai a duniya, ya kuma rufe dukan duwatsu masu tsawo a ƙarƙashin sammai. Ruwan ya taso ya rufe duwatsu, zurfin ruwa daga duwatsun zuwa inda jirgin yake ya fi ƙafa ashirin. Kowane abu mai rai da yake tafiya a duniya ya hallaka, tsuntsaye, dabbobin gida, namun jeji, da dukan masu rarrafe waɗanda suke rarrafe a duniya, da kuma dukan mutane. Kome a busasshiyar ƙasa da yake numfashi a hancinsa ya mutu. Aka kawar da kowane abu mai rai, mutane da dabbobi da halittu masu rarrafe a ƙasa, da tsuntsayen sama a doron ƙasa, duka aka kawar da su daga duniya. Nuhu kaɗai aka bari da waɗanda suke tare da shi a cikin jirgi. Ruwa ya mamaye duniya har kwana ɗari da hamsin. Amma Allah ya tuna da Nuhu da dukan namun jeji da dabbobin da suke tare da shi a cikin jirgi, ya kuma aika da wata iska ta hura dukan duniya, ruwan kuwa ya janye. Aka toshe maɓuɓɓugan zurfafa da ƙofofin ambaliyar sammai, ruwan sama kuma ya daina saukowa daga sarari. Ruwan ya janye a hankali daga ƙasa. A ƙarshen kwanaki ɗari da hamsin ɗin, ruwan ya ragu. A rana ta goma sha bakwai ga watan bakwai, jirgin ya sauka a duwatsun Ararat. Ruwan ya ci gaba da janyewa har watan goma. A rana ta fari ga watan goma kuwa ƙwanƙolin duwatsun suka bayyana. Bayan kwana arba’in, sai Nuhu ya buɗe tagar jirgin da ya yi, ya saki hankaka. Hankaka ya yi ta kai da kawowa har sai da ruwa ya shanye a duniya. Sai ya saki kurciya don yă ga in ruwan ya janye daga doron ƙasa. Amma kurciyar ba tă sami inda za tă sa ƙafafunta ba gama akwai ruwa a dukan doron ƙasa, saboda haka ta komo wurin Nuhu a jirgi. Ya miƙa hannunsa ya ɗauko kurciyar ya shigar da ita wurinsa a cikin jirgi. Ya ƙara jira kwana bakwai, sai ya sāke aiken kurciyar daga jirgi. Sa’ad da kurciya ta komo wurinsa da yamma, sai ga ɗanyen ganyen zaitun da ta tsinko a bakinta! Sa’an nan Nuhu ya san cewa ruwa ya janye daga duniya. Ya ƙara jira kwana bakwai, sai ya sāke aiken kurciyar, amma a wannan ƙaro ba tă komo wurinsa ba. A rana ta fari ga wata na fari wanda Nuhu ya cika shekaru 601, ruwa ya shanye a ƙasa. Sai Nuhu ya buɗe murfin jirgin, ya ga cewa doron ƙasa ya bushe. A ran ashirin da bakwai ga wata na biyu, ƙasa ta bushe ƙaƙaf. Sa’an nan Allah ya ce wa Nuhu, “Fito daga jirgin, kai da matarka da ’ya’yanka maza da matansu. Ka fitar da kowane iri halitta mai rai da take tare da kai waje, tsuntsaye, dabbobi, da dukan halittu masu rarrafe a ƙasa, don su yi ta haihuwa, su yi yawa, su ƙaru a duniya.” Sai Nuhu ya fito tare da matarsa da ’ya’yansa maza da matan ’ya’yansa, da kowace irin dabba, da kowane mai rarrafe, da kowane irin tsuntsu, da kowane irin abu da yake tafiya a bisa duniya, suka fito daga jirgi daki-daki bisa ga irinsu. Sai Nuhu ya gina bagaden hadaya ga Ubangiji, ya ɗiba waɗansu dabbobi da tsuntsaye masu tsabta, ya yi hadaya ta ƙonawa da su a kan bagaden. Da Ubangiji ya ji ƙanshi mai daɗi, sai ya ce a zuciyarsa, “Ba zan ƙara la’anta ƙasa saboda mutum ba, ko da yake dukan tunanin zuciyar mutum mugu ne tun yana ƙarami. Ba kuwa zan ƙara hallaka dukan halittu masu rai, kamar yadda na yi ba. “Muddin duniya tana nan, lokacin shuki da na girbi, lokacin sanyi da na zafi, lokacin damina da na rani, dare da rana ba za su daina ba.” Sa’an nan Allah ya sa wa Nuhu da ’ya’yansa maza albarka, yana ce musu, “Ku haifi ’ya’ya, ku ƙaru, ku kuma cika duniya. Dukan namun jeji da dukan tsuntsayen sama da kowace halitta mai rarrafe a ƙasa, da dukan kifayen teku, za su riƙa jin tsoronku, suna fargaba. An sa su a cikin hannuwanku. Kome da yake da rai wanda yake tafiya, zai zama abincinku. Kamar yadda na ba ku kowane irin ganye, haka na ba ku kome da kome. “Akwai abu ɗaya da ba za ku ci ba, wato, nama wanda jininsa yake cikinsa tukuna. Game da jinin ranka kuwa lalle zan bukaci lissafi. Zan bukaci lissafi daga kowane dabba. kuma daga kowane mutum, shi ma zan bukaci lissafi game da ran ɗan’uwansa. “Duk wanda ya zub da jinin mutum, ta hannun mutum za a zub da jininsa; gama a cikin siffar Allah ne, Allah ya yi mutum. Amma ku, ku yi ta haihuwa, ku ƙaru; ku yaɗu a duniya, ku yi yawa a bisanta.” Sai Allah ya ce wa Nuhu da ’ya’yansa, “Yanzu na kafa alkawarina da ku da zuriyarku a bayanku, da kowace halitta mai rai wadda ta kasance tare da kai; wato, tsuntsaye da dabbobin gida da kuma dukan namun jeji, duk dai iyakar abin da ya fita daga jirgin; wato, kowane mai rai na duniya. Na kafa alkawarina da ku, ba za a ƙara hallaka dukan rayuka da ambaliyar ruwa ba; ba za a ƙara yin ambaliya don a hallaka duniya ba.” Allah ya kuma ce, “Wannan ita ce alamar alkawarin da na yi tsakanina da ku, da kowace halitta tare da ku; alkawari na dukan zamanai masu zuwa. Na sa bakan gizona cikin gizagizai, shi ne kuwa zai zama alamar alkawari tsakanina da duniya. Duk sa’ad da na kawo gizagizai a bisa duniya, bakan gizo kuma ya bayyana a ciki gizagizan, zan tuna da alkawari tsakanina da ku da kuma dukan halittu masu rai na kowane iri. Ruwa ba zai sāke yin ambaliyar da za tă hallaka dukan masu rai ba. Duk sa’ad da bakan gizo ya bayyana cikin gizagizan, zan gan shi in kuma tuna da madawwamin alkawari tsakanin Allah da dukan halittu masu rai, na kowane iri a duniya.” Saboda haka Allah ya ce wa Nuhu, “Wannan ita ce alamar alkawarin da na kafa tsakanina da dukan masu rai a duniya.” ’Ya’yan Nuhu maza, waɗanda suka fito daga cikin jirgi, su ne, Shem, Ham da Yafet. (Ham shi ne mahaifin Kan’ana.) Waɗannan su ne ’ya’yan Nuhu maza uku, daga gare su ne kuma duniya za tă cika da mutane. Nuhu, mutumin ƙasa, shi ne farko da ya fara yin gonar inabi. Sa’ad da ya sha ruwan inabin ya kuwa bugu, sai ya kwanta tsirara cikin tentinsa. Ham, mahaifin Kan’ana ya ga tsiraici mahaifinsa, ya kuma faɗa wa ’yan’uwansa biyu a waje. Amma Shem da Yafet suka ɗauki mayafi, suka shimfiɗa a kafaɗarsu, sa’an nan suka shiga suna tafiya da baya har zuwa inda mahaifinsu yake kwance, suka rufe tsiraicinsa. Suka kau da fuskokinsu domin kada su ga tsiraicin mahaifinsu. Sa’ad da Nuhu ya farka daga buguwarsa ya kuma gane abin da ƙarami ɗansa ya yi, sai ya ce, “Kan’ana la’ananne ne, zai zama bawa mafi ƙanƙanta ga ’yan’uwansa.” Ya kuma ce, “Albarka ta tabbata ga Ubangiji Allah na Shem! Bari Kan’ana yă zama bawan Shem. Allah yă ƙara fāɗin ƙasar Yafet; bari Yafet yă zauna a tentunan Shem, bari kuma Kan’ana yă zama bawansa.” Bayan ambaliyar, Nuhu ya yi shekaru 350. Gaba ɗaya dai, Nuhu ya yi shekara 950, sa’an nan ya mutu. Wannan shi ne labarin Shem, Ham da Yafet, ’ya’yan Nuhu maza, waɗanda su ma sun haifi ’ya’ya maza bayan ambaliyar. ’Ya’yan Yafet maza su ne, Gomer, Magog, Madai da Yaban, Tubal, Meshek, da kuma Tiras. ’Ya’yan Gomer maza su ne, Ashkenaz, Rifat, da Togarma. ’Ya’yan maza Yaban su ne, Elisha, Tarshish, Kittim da Rodanim. (Daga waɗannan mutane ne masu zama a bakin teku suka bazu zuwa cikin ƙasashensu da kuma cikin al’ummansu, kowanne da yarensa.) ’Ya’yan Ham maza su ne, Kush, Masar, Fut, da Kan’ana. ’Ya’yan Kush maza su ne, Seba, Hawila, Sabta, Ra’ama da Sabteka. ’Ya’yan Ra’ama maza kuwa su ne, Sheba da Dedan. Kush shi ne mahaifin Nimrod wanda ya yi girma ya zama jarumin yaƙi a duniya. Shi babban maharbi ne a gaban Ubangiji. Shi ya sa akan ce, kamar Nimrod babban maharbi a gaban Ubangiji. Cibiyoyin mulkinsa na farko su ne Babilon, Erek, Akkad, da Kalne a cikin Shinar. Daga wannan ƙasa, sai ya tafi Assuriya, inda ya gina Ninebe, Rehobot Ir, Kala da Resen, wadda take tsakanin Ninebe da Kala; wanda yake babban birni. Mizrayim shi ne mahaifin Ludiyawa, Anamawa, Lehabiyawa, Naftuhiyawa, Fetrusiyawa, da Kasluhiyawa (inda Filistiyawa suka fito) da kuma Kaftorawa. Kan’ana shi ne mahaifin, Sidon ɗan farinsa, da na Hittiyawa, Yebusiyawa, Amoriyawa, Girgashiyawa, Hiwiyawa, Arkiyawa, Siniyawa, Arbadiyawa, Zemarawa, da Hamawa. Daga baya zuriyar Kan’aniyawa suka yaɗu har iyakar Kan’ana ta kai Sidon ta wajen Gerar har zuwa Gaza, sa’an nan ta milla zuwa Sodom, Gomorra, Adma da Zeboyim, har zuwa Lasha. Waɗannan su ne ’ya’yan Ham maza bisa ga zuriyarsu da yarurrukansu, cikin ƙasashensu da kuma al’ummominsu. Aka kuma haifa wa Shem, wan Yafet, ’ya’ya maza. Shem shi ne kakan ’ya’yan Eber duka. ’Ya’yan Shem maza su ne, Elam, Asshur, Arfakshad, Lud da Aram. ’Ya’yan Aram maza su ne, Uz, Hul, Geter da Mash. Arfakshad ne mahaifin Shela. Shela kuma shi ne mahaifin Eber. Aka haifa wa Eber ’ya’ya maza biyu. Aka ba wa ɗaya suna Feleg, gama a zamaninsa ne aka raba duniya; aka kuma sa wa ɗan’uwansa suna Yoktan. Yoktan shi ne mahaifin, Almodad, Shelef, Hazarmawet, Yera, Hadoram, Uzal, Dikla, Obal, Abimayel, Sheba, Ofir, Hawila da Yobab. Dukan waɗannan ’ya’yan Yoktan maza ne. Yankin da suka zauna ya miƙe daga Mesha zuwa wajen Sefar a gabashin ƙasar tudu. Waɗannan su ne ’ya’yan Shem maza bisa ga zuriyarsu da yarurrukansu, cikin ƙasashensu da kuma al’ummominsu. Waɗannan su ne zuriyar ’ya’yan Nuhu maza bisa ga jerin zuriyarsu cikin al’ummominsu. Daga waɗannan ne al’ummomi suka bazu ko’ina a duniya bayan ambaliya. To, a lokacin, yaren mutanen duniya ɗaya ne, maganarsu kuma ɗaya ce. Yayinda mutane suke ta yin ƙaura zuwa gabas, sai suka sami fili a Shinar, suka zauna a can. Suka ce wa juna, “Ku zo, mu yi tubula, mu gasa su sosai.” Suka yi amfani da tubula a maimakon duwatsu, kwalta kuma a maimakon laka. Sa’an nan suka ce, “Ku zo, mu gina wa kanmu birni da hasumiyar da za tă kai har sammai, domin mu yi wa kanmu suna, don kada mu warwatsu ko’ina a doron ƙasa.” Sai Ubangiji ya sauko don yă ga birni da kuma hasumiyar da mutanen suke gini. Ubangiji ya ce, “Ga su, su jama’a ɗaya ce, su duka kuwa harshensu guda ne. Wannan kuwa masomi ne kawai na abin da za su iya yi, babu kuma abin da suka yi shirya yi da ba za su iya yi ba. Zo, mu sauka, mu rikitar da harshensu don kada su fahimci juna.” Saboda haka Ubangiji ya watsar da su daga wurin zuwa ko’ina a doron ƙasa, suka kuwa daina gina birnin. Shi ya sa aka kira birnin Babel, domin a can ne Ubangiji ya rikitar da harshen dukan duniya. Daga can Ubangiji ya watsar da su ko’ina a doron ƙasa. Wannan shi ne labarin Shem. Shekara biyu bayan ambaliya, sa’ad da Shem ya yi shekara 100, sai ya haifi Arfakshad. Bayan ya haifi Arfakshad, Shem ya yi shekara 500, ya haifi waɗansu ’ya’ya maza da mata. Sa’ad da Arfakshad ya yi shekara 35, sai ya haifi Shela. Bayan ya haifi Shela kuwa, Arfakshad ya yi shekara 403, ya kuma haifi waɗansu ’ya’ya maza da mata. Sa’ad da Shela ya yi shekaru 30, sai ya haifi Eber. Bayan ya haifi Eber, Shela ya yi shekara 403, ya kuma haifi waɗansu ’ya’ya maza da mata. Sa’ad da Eber ya yi shekaru 34, sai ya haifi Feleg. Bayan ya haifi Feleg, Eber ya yi shekara 430, ya kuma haifi waɗansu ’ya’ya maza da mata. Sa’ad da Feleg ya yi shekaru 30, sai ya haifi Reyu. Bayan ya haifi Reyu, Feleg ya yi shekara 209, ya kuma haifi waɗansu ’ya’ya maza da mata. Sa’ad da Reyu ya yi shekaru 32, sai ya haifi Serug. Bayan ya haifi Serug, Reyu ya yi shekara 207, ya kuma haifi waɗansu ’ya’ya maza da mata. Sa’ad da Serug ya yi shekaru 30, sai ya haifi Nahor. Bayan ya haifi Nahor, Serug ya yi shekara 200, ya kuma haifi waɗansu ’ya’ya maza da mata. Sa’ad da Nahor ya yi shekaru 29, sai ya haifi Tera. Bayan ya haifi Tera, Nahor ya yi shekara 119, ya kuma haifi waɗansu ’ya’ya maza da mata. Bayan Tera ya yi shekaru 70, sai ya haifi Abram, Nahor da Haran. Wannan ita ce zuriyar Tera. Tera ya haifi Abram, Nahor da Haran. Haran kuma ya haifi Lot. Yayinda mahaifinsa Tera yana da rai, Haran ya rasu a Ur ta Kaldiyawa, a ƙasar haihuwarsa. Abram da Nahor suka yi aure. Sunan matar Abram, Saira ne, sunan matar Nahor kuwa Milka; ita ’yar Haran ce, mahaifin Milka da Iska. Saira kuwa bakararriya ce, ba ta da yara. Tera ya ɗauki ɗansa Abraham, jikansa Lot ɗan Haran, da surukarsa Saira, matar Abram, tare kuwa suka bar Ur ta Kaldiyawa, don su tafi Kan’ana. Amma sa’ad da suka zo Haran sai suka zauna a can. Tera yi shekaru 205, ya kuma mutu a Haran. Ubangiji ya ce wa Abram, “Tashi ka bar ƙasarka, da mutanenka, da iyalin mahaifinka, ka tafi ƙasar da zan nuna maka. “Zan mai da kai al’umma mai girma, zan kuma albarkace ka; zan sa sunanka yă zama mai girma, ka kuma zama sanadin albarka. Zan albarkaci duk wanda ya albarkace ka, in kuma la’anci duk wanda ya la’anta ka, dukan mutanen duniya za su sami albarka ta wurinka.” Saboda haka Abram ya tashi yadda Ubangiji ya faɗa masa; Lot ma ya tafi tare da shi. Abram yana da shekaru 75, sa’ad da ya tashi daga Haran. Abram ya ɗauki matarsa Saira da Lot ɗan ɗan’uwansa, da dukan mallakar da suka tattara, da kuma mutanen da suka samu a Haran, suka kama hanya zuwa ƙasar Kan’ana. Abram ya ratsa ƙasar har zuwa wurin babban itace na More a Shekem. A lokacin Kan’aniyawa suna a ƙasar. Ubangiji ya bayyana ga Abram ya ce, “Ga zuriyarka ne zan ba da wannan ƙasa.” Saboda haka Abram ya gina bagade a can ga Ubangiji, wanda ya bayyana gare shi. Daga can, ya ci gaba zuwa wajen tuddai a gabashin Betel ya kafa tentinsa, Betel yana yamma, Ai, kuma a gabas. A can ya gina bagade ga Ubangiji ya kuma kira bisa sunan Ubangiji. Sa’an nan Abram ya tashi ya ci gaba da tafiya zuwa wajen Negeb. To, a lokacin, an yi yunwa a ƙasar, sai Abram ya gangara zuwa Masar don yă zauna a can na ɗan lokaci, domin yunwa ta yi tsanani. Yayinda yana gab da shiga Masar, sai ya ce wa matarsa Saira, “Na sani ke kyakkyawar mace ce. Sa’ad da Masarawa suka ganki, za su ce, ‘Wannan matarsa ce.’ Za su kuwa kashe ni, su bar ki da rai. Saboda haka ki ce ke ’yar’uwata ce, domin ta dalilinki a mutunta ni, a kuma bar ni da rai.” Sa’ad da Abram ya isa Masar, Masarawa suka ga cewa Saira kyakkyawa mace ce ƙwarai. Sa’ad da fadawan Fir’auna suka gan ta kuwa, sai suka yabe ta wajen Fir’auna, aka kuwa kawo ta cikin fadarsa. Ya mutunta Abram sosai saboda ita, Abram kuwa ya mallaki tumaki da shanu, da jakuna maza da mata, da bayi maza da mata, da kuma raƙuma. Amma Ubangiji ya wahalar da Fir’auna da gidansa da cututtuka masu zafi saboda Saira, matar Abram. Saboda haka Fir’auna ya kira Abram ya ce, “Me ke nan ka yi mini? Me ya sa ba ka faɗa mini cewa ita matarka ce ba? Don me ka ruɗe ni cewa, ‘Ita ’yar’uwata ce,’ har na ɗauke ta tă zama matata? To, ga matarka. Ɗauke ta ka tafi.” Sa’an nan Fir’auna ya yi wa mutanensa umarni a kan Abram, suka kuwa sallame shi tare da matarsa da kuma dukan abin da yake da shi. Saboda haka Abram ya haura daga Masar zuwa Negeb tare da matarsa, da dukan abin da yake da shi tare da Lot. Abram ya azurta ƙwarai da dabbobi, da azurfa, da kuma zinariya. Daga Negeb, ya ci gaba da tafiyarsa a wurare dabam-dabam har ya kai tsakanin Betel da Ai, a inda dā ya kafa tentinsa na fari da kuma inda dā ya gina bagade. A can Abram ya kira bisa sunan Ubangiji. Lot wanda yake tafiya tare da Abram, shi ma yana da garken shanu da tumaki da kuma tentuna. Wannan ya sa har ƙasar ba tă ishe su yayinda suke zama tare ba, saboda mallakarsu ta yi yawa har ba za su iya zama tare ba. Rikici kuma ya tashi tsakanin masu kiwon dabbobin Abram da na Lot. Mazaunan ƙasar, a lokacin kuwa Kan’aniyawa da Ferizziyawa ne. Saboda haka Abram ya ce wa Lot, “Kada mu bar rikici yă shiga tsakaninmu, ko kuma tsakanin masu kiwon dabbobinka da nawa, gama mu ’yan’uwa ne. Ba ga dukan ƙasar tana gabanka ba? Bari mu rabu. In ka yi hagu sai ni in yi dama. In ka yi dama, sai ni in yi hagu.” Lot ya ɗaga idanunsa sama ya dubi kwarin Urdun, sai ya ga kwarin yana da ciyawa mai kyau ƙwarai sai ka ce lambun Ubangiji, kamar ƙasar Masar, wajajen Zowar. (Wannan fa kafin Ubangiji yă hallaka Sodom da Gomorra.) Saboda haka sai Lot ya zaɓar wa kansa dukan kwarin Urdun, ya tashi ya nufi wajen gabas. Haka fa suka rabu da juna. Abram ya zauna a ƙasar Kan’ana, yayinda Lot ya zauna cikin biranen kwari, ya kafa tentunansa kusa da Sodom. Mutanen Sodom kuwa mugaye ne, sun aikata zunubi ƙwarai ga Ubangiji. Bayan Lot ya rabu da Abram, sai Ubangiji ya ce wa Abram, “Ɗaga idanunka daga inda kake, ka dubi arewa da kudu, gabas da yamma. Dukan ƙasar da kake gani zan ba ka, kai da zuriyarka har abada. Zan sa zuriyarka tă yi yawa kamar ƙurar ƙasa, har in wani yana iya ƙidaya ƙurar, to, za a iya ƙidaya zuriyarka. Tafi, ka ratsa tsawo da fāɗin ƙasar, gama zan ba ka ita.” Saboda haka Abram ya cire tentunansa, ya zo ya zauna kusa da manyan itatuwan Mamre a Hebron, inda ya gina bagade ga Ubangiji. A zamanin Amrafel sarkin Shinar, shi da Ariyok sarkin Ellasar, Kedorlayomer sarkin Elam, da kuma Tidal sarkin Goyim suka tafi don su yaƙi Bera sarkin Sodom, Birsha sarkin Gomorra, Shinab sarkin Adma, Shemeber sarkin Zeboyim, da kuma sarkin Bela (wato, Zowar). Dukan waɗannan sarakuna na bayan nan suka haɗa kai a Kwarin Siddim (Teku Gishiri). Shekara goma sha biyu suna bauta wa Kedorlayomer, amma a shekara ta sha uku sai suka yi tawaye. A shekara ta goma sha huɗu, Kedorlayomer da sarakunan da suka haɗa kai da shi suka tafi suka cinye Refahiyawa a Ashterot Karnayim, Zuziyawa a Ham, Emawa a Shabe Kiriyatayim, da Horiyawa a ƙasar tudun Seyir har zuwa El Faran kusa da hamada. Sa’an nan suka juya suka tafi En Mishfat (wato, Kadesh), suka cinye dukan ƙasar Amalekawa, da kuma Amoriyawa waɗanda suke zaune a Hazazon Tamar. Sai sarkin Sodom, sarkin Gomorra, sarkin Adma, sarkin Zeboyim da sarkin Bela (wato, Zowar), suka fita suka ja dāgā a Kwarin Siddim gāba da Kedorlayomer sarkin Elam, Tidal sarkin Goyim, Amrafel sarkin Shinar da Ariyok sarkin Ellasar; sarakuna huɗu gāba da biyar. Kwarin Siddim kuwa ya cika da ramummukan kwalta, sa’ad da sarakunan Sodom da Gomorra suka gudu kuwa, waɗansu mutane suka fāɗa cikin ramummukan kwaltan, sauran kuwa suka gudu zuwa tuddai. Sarakunan nan huɗu suka washe dukan kayayyakin Sodom da Gomorra, da kuma dukan abincinsu, sa’an nan suka tafi. Suka kuma kama Lot ɗan ɗan’uwan Abram, wanda yake zaune a Sodom, da kayayyakinsa, suka yi tafiyarsu. Sai wani wanda ya tsira, ya zo ya faɗa wa Abram mutumin Ibraniyawa. Abram kuwa yana zama kusa da manyan itatuwan Mamre, Mamre mutumin Amoriyawa ne ɗan’uwan Eshkol da Aner, su kuwa abokan Abram ne. Da Abram ya ji cewa an kama danginsa, sai ya tara horarrun mutane 318, da aka haifa a gidansa, ya bi sawun sarakunan da suka tafi da Lot, har Dan. Da dad dare, Abram ya rarraba mutanensa don su fāɗa wa sarakunan nan, ya ɗibge su, ya kore su har zuwa Hoba, arewa da Damaskus. Ya washe su da kuma dukan kayayyakinsu, ya kuma dawo da Lot danginsa da mallakarsa, tare da mata da sauran mutane. Bayan Abram ya dawo daga cin Kedorlayomer da sarakunan da suka haɗa kai da shi a yaƙi, sai sarkin Sodom ya fito don yă tarye Abram a Kwarin Shabe (wato, Kwarin Sarki). Sai Melkizedek sarkin Salem ya kawo burodi da ruwan inabi. Shi firist ne na Allah Mafi Ɗaukaka, ya albarkaci Abram yana cewa, “Allah Mafi Ɗaukaka Mahaliccin sama da ƙasa yă albarkace Abram. Kuma albarka ta tabbata ga Allah Mafi Ɗaukaka wanda ya ba da maƙiyanka a hannunka.” Sa’an nan Abram ya ba shi kashi ɗaya bisa goma na kome. Sarkin Sodom ya ce wa Abram, “Ka ba ni mutanena da ka ƙwace daga hannun sarakunan nan kawai, ka riƙe kayayyakin don kanka.” Amma Abram ya ce, wa sarkin Sodom, “Na ɗaga hannu ga Ubangiji Allah Mafi Ɗaukaka, Mahaliccin sama da ƙasa, na riga na rantse cewa ba zan karɓi kome da yake naka ba, ko zare ko maɗaurin takalma, don kada ka ce, ‘Na azurta Abram.’ Ba zan karɓi kome ba, sai dai abin da mutanena suka ci da kuma rabon mutanen da suka tafi tare da ni, ga Aner, Eshkol, da Mamre. Bari su ɗauki rabonsu.” Bayan wannan, maganar Ubangiji ta zo wa Abram cikin mafarki cewa, “Kada ka ji tsoro, Abram. Ni ne garkuwarka, kuma ladanka zai zama mai girma.” Amma Abram ya ce, “Ya Ubangiji Mai Iko Duka, mene ne za ka ba ni, ganin cewa ba na haihuwa, wanda kuma zai gāji gādon gidana shi ne Eliyezer mutumin Damaskus?” Abram ya kuma ce, “Ga shi ba ka ba ni ɗa ba, don haka bawan da aka haifa a gidana ne zai zama magājina.” Sa’an nan maganar Ubangiji ta zo gare shi cewa, “Wannan mutum ba zai zama magājinka ba, ɗa da yake zuwa daga jikinka ne zai zama magājinka.” Sai Ubangiji ya fito da kai shi waje ya ce, “Ka dubi sammai ka kuma ƙirga taurari, in har za ka iya ƙirga su.” Sa’an nan ya ce masa, “Haka zuriyarka za tă zama.” Abram ya gaskata, Ubangiji kuma ya lasafta shi adalci ga Abram. Ubangiji ya kuma ce wa Abram, “Ni ne Ubangiji wanda ya fitar da kai daga Ur na Kaldiyawa, domin in ba ka wannan ƙasa ka mallake ta.” Amma Abram ya ce, “Ya Ubangiji Mai Iko Duka, yaya zan san cewa zan mallake ta?” Saboda haka Allah ya ce masa, “Kawo mini karsana, akuya, da kuma rago kowanne yă kasance shi shekara uku ne, da kurciya da kuma ɗan tattabara.” Abram ya kawo waɗannan duka a gaban Allah, ya raba kowannensu a tsakiya, ya ajiye su gab da juna, amma bai tsaga tsuntsayen a tsaka ba. Sai tsuntsaye masu cin nama suka sauko a kan gawawwakin, amma Abram ya kore su. Yayinda rana tana fāɗuwa, sai Abram ya yi barci mai zurfi, sai wani duhu mai kauri mai kuma bantsoro ya rufe shi. Sa’an nan Ubangiji ya ce wa Abram, “Ka sani tabbatacce cewa shekaru ɗari huɗu, zuriyarka za tă zama baƙi a ƙasar da ba tasu ba, za a mai da su bayi, a kuma wulaƙanta su. Amma zan hukunta al’ummar da suka yi bauta kamar bayi, daga baya kuma za su fita da mallaka mai yawa. Amma kai za ka koma wurin kakanninka cikin salama a kuma binne ka da kyakkyawan tsufa. A tsara ta huɗu zuriyarka za tă komo nan, saboda zunubin Amoriyawa bai riga ya cika ba.” Sa’ad da rana ta fāɗi, aka kuwa yi duhu, sai wata tukunya mai hayaƙi, mai harshen wuta mai ci, ta bayyana, ta kuma wuce tsakanin abubuwan nan da aka tsaga. A wannan rana, Ubangiji ya yi alkawari da Abram ya ce, “Ga zuriyarka na ba da wannan ƙasa, daga kogin Masar zuwa babban kogi, Yuferites ke nan, ƙasar Keniyawa, Kenizziyawa, Kadmoniyawa, Hittiyawa, Ferizziyawa, Refahiyawa, Amoriyawa, Kan’aniyawa, Girgashiyawa da kuma Yebusiyawa.” To, Saira, matar Abram, ba tă haifa masa ’ya’ya ba. Amma tana da wata baiwa mutuniyar Masar mai suna Hagar, saboda haka sai ta ce wa Abram, “ Ubangiji ya hana mini haihuwar ’ya’ya. Tafi ka kwana da baiwata; wataƙila in sami iyali ta wurinta.” Abram kuwa ya yarda da abin da Saira ta faɗa. Saboda haka bayan Abram ya yi zama a Kan’ana shekaru goma, Saira matarsa ta ɗauki Hagar baiwarta ta ba wa mijinta tă zama matarsa. Abram kuwa ya kwana da Hagar, ta kuma yi ciki. Sa’ad da Hagar ta gane tana da ciki, sai ta fara rena uwargijiyarta. Sai Saira ta ce wa Abram, “Kai ne da alhakin wahalan nan da nake sha. Na sa baiwata a hannunka, yanzu da ta sani tana da ciki, sai ta fara rena ni. Bari Ubangiji yă shari’anta tsakanina da kai.” Abram ya ce, “Baiwarki tana a hannunki? Ki yi da ita yadda kika ga ya fi kyau.” Sai Saira ta wulaƙanta Hagar; saboda haka ta gudu daga gare ta. Mala’ikan Ubangiji ya sami Hagar kusa da maɓulɓula a jeji, ita ce maɓulɓular da take gefen hanya zuwa Shur. Ya kuma ce mata, “Hagar, baiwar Saira, daga ina kika fito, kuma ina za ki?” Ta amsa ta ce, “Ina gudu ne daga wurin uwargijiyata Saira.” Sai mala’ikan Ubangiji ya ce mata, “Koma wurin uwargijiyarki Saira, ki yi mata biyayya.” Mala’ikan ya ƙara da cewa, “Zan ƙara zuriyarki har su yi yawan da ba wanda zai iya lasafta su.” Mala’ikan Ubangiji ya kuma ce mata, “Ga shi kina da ciki za ki kuwa haifi ɗa. Za ki ba shi suna Ishmayel, gama Ubangiji ya ga wahalarki. Zai zama mutum mai halin jakin jeji. Hannunsa zai yi gāba da kowa, hannun kowa kuma zai yi gāba da shi. Zai yi zama gāba ga dukan ’yan’uwansa.” Sai ta ba wa Ubangiji wanda ya yi magana da ita, wannan suna. “Kai Allah ne wanda yake ganina,” gama ta ce, “Yanzu na ga wanda yake ganina.” Shi ya sa ake kira rijiyar Beyer-Lahai-Royi tana nan har yanzu, tsakanin Kadesh da Bered. Haka fa Hagar ta haifa wa Abram ɗa, Abram kuwa ya ba da suna Ishmayel ga ɗan da ta haifa. Abram yana da shekaru 86 sa’ad da Hagar ta haifa masa Ishmayel. Sa’ad da Abram ya yi shekaru 99, sai Ubangiji ya bayyana a gare shi ya ce, ni “Ni ne Allah Maɗaukaki, ka yi tafiya a gabana ka kuma zama marar abin zargi. Zan tabbatar da alkawarina tsakanina da kai, zan kuma ƙara zuriyarka ta yi yawa.” Abram ya rusuna da fuskarsa har ƙasa, Allah kuma ya ce masa, “Gare ni kam, wannan shi ne alkawarina da kai, za ka zama mahaifin al’ummai masu yawa. Ba za a ƙara kiranka Abram ba; sunanka zai zama Ibrahim, gama na mai da kai uban al’ummai masu yawa. Zan sa ka azurta sosai, zan yi al’ummai daga cikinka, sarakuna kuma za su fito daga cikinka, zan kafa alkawarina kamar madawwamin alkawari tsakanina da kai da kuma zuriyarka bayanka har tsararraki masu zuwa, in zama Allahnka da kuma Allahn zuriyarka a bayanka. Dukan ƙasar Kan’ana inda kake baƙo a yanzu, zan ba da ita a matsayin madawwamiyar mallaka gare ka da kuma zuriyarka a bayanka, zan kuma zama Allahnsu.” Sa’an nan Allah ya ce wa Ibrahim. “Kai fa, sai ka kiyaye alkawarina, kai da zuriyarka bayanka, har tsararraki masu zuwa. Wannan shi ne alkawarina da kai da kuma zuriyarka a bayanka, alkawarin da za ka kiyaye ke nan. Kowane namiji a cikinku kuwa za a yi masa kaciya. Za ku yi kaciya, za tă kuma zama alamar alkawari tsakanina da kai. Daga yanzu duk namijin da aka haifa a cikinku za a yi masa kaciya a rana ta takwas har dukan zamananku, ko haifaffen gida ne, ko sayayye da kuɗi daga kowane baƙo wanda ba na zuriyarku ba. Ko haifaffe a gidanka ko an sayo da kuɗi, dole a yi musu kaciya. Alkawarina cikin jikinku zai kasance madawwamin alkawari. Kowane namijin da ba a yi masa kaciya a jiki ba, za a fid da shi daga cikin mutanensa; domin ya karya alkawarina.” Allah ya kuma ce wa Ibrahim, “Game da Saira matarka kuwa, ba za ka ƙara kiranta Saira ba, sunanta zai zama Saratu. Zan sa mata albarka, ban da haka ma, zan ba ka ɗa ta wurinta, zan sa mata albarka, za tă kuwa zama mahaifiyar al’ummai; sarakunan mutane za su fito daga gare ta.” Ibrahim ya rusuna da fuskarsa har ƙasa, ya yi dariya, ya ce wa kansa, “Za a haifi ɗa wa mutum mai shekaru ɗari? Saratu za tă haifi ɗa tana da shekaru tasa’in?” Ibrahim ya kuma ce wa Allah, “Me zai hana a dai bar Ishmayel kawai yă gāji alkawarin nan da ka yi mini.” Sai Allah ya ce, “Duk da haka dai, matarka Saratu za tă haifi maka ɗa; za ka kuma kira shi Ishaku. A kansa zan tabbatar da madawwamin alkawarina, da kuma ga zuriyarsa da za su zo bayansa. Game da Ishmayel kuwa, na ji ka. Tabbatacce zan albarkace shi, zan sa yă azurta, zai kuma ƙaru ƙwarai. Zai zama mahaifin masu mulki goma sha biyu, zan kuma maishe shi babban al’umma! Amma dai zan kafa alkawarina da Ishaku wanda Saratu za tă haifa maka war haka shekara mai zuwa.” Da ya gama magana da Ibrahim, sai Allah ya tashi daga gare shi. A wannan rana, Ibrahim ya ɗauki ɗansa Ishmayel da dukan waɗanda aka haifa cikin gidansa, da waɗanda aka sayo da kuɗinsa, ya kuwa yi wa kowane namiji a cikin gidansa kaciya kamar yadda Allah ya faɗa masa. Ibrahim yana da shekara tasa’in da tara sa’ad da aka yi masa kaciya, Ishmayel ɗansa kuma yana da shekara goma sha uku. Aka yi wa Ibrahim da ɗansa Ishmayel kaciya a rana ɗaya. Aka yi wa kowane namiji a gidan Ibrahim kaciya, da waɗanda aka haifa a gidansa, da waɗanda aka sayo da kuɗi daga baƙo. Ubangiji ya bayyana ga Ibrahim kusa da manyan itatuwan Mamre yayinda yake zaune a mashigin tentinsa da tsakar rana. Da Ibrahim ya ɗaga ido, sai ya ga mutum uku suna tsaye kusa da shi. Sa’ad da ya gan su, sai ya tashi nan da nan daga mashigin tentinsa, ya tarye su, ya rusuna har ƙasa. Ya ce, “Ranka yă daɗe, in na sami tagomashi daga gare ku kada ku wuce bawanku. Bari a kawo ruwa ku wanke ƙafafunku, ku huta a ƙarƙashin wannan itace. Bari in samo muku wani abu ku ci don ku wartsake, sa’an nan ku ci gaba da tafiyarku; da yake kun biyo wurin bawanku.” Suka ce, “To, sai ka yi abin da ka ce.” Saboda haka Ibrahim ya ruga zuwa wurin Saratu a cikin tenti ya ce, “Yi sauri, ki shirya mudu uku na gari mai laushi, ki cuɗa shi, ki yi burodi.” Sa’an nan Ibrahim ya yi gudu zuwa garkensa, ya zaɓi ɗan maraƙi ya ba wa bawansa, bawansa kuma ya yi sauri ya gyara shi. Sa’an nan Ibrahim ya ɗauko dambu da madara da naman ɗan maraƙin da aka gyara, ya kawo a gabansu. Yayinda suke ci, ya tsaya a gindin itace kusa da su. Sai suka ce masa, “Ina Saratu matarka?” Ibrahim ya ce, “Tana can cikin tenti.” Sa’an nan ɗayansu ya ce, “Lalle zan komo wurinka war haka shekara mai zuwa. Saratu matarka kuwa za tă haifi ɗa.” Saratu kuwa tana a bayansu tana ji daga mashigin tenti. Ibrahim da Saratu dai sun riga sun tsufa sosai. Saratu kuma ta wuce shekarun haihuwa. Saboda haka Saratu ta yi dariya da ta yi tunani a zuci tana cewa, “Bayan ƙarfina ya ƙare, maigidana kuma ya tsufa, yanzu zan sami wannan jin daɗi?” Sai Ubangiji ya ce wa Ibrahim, “Me ya ba Saratu dariya har da ta ce, ‘Har zan iya haifi ɗa duk ta tsufata yanzu?’ Akwai abin zai gagari Ubangiji? Zan komo wurinka a ƙayyadadden lokacin nan shekara mai zuwa kuma Saratu za tă haifi ɗa.” Saratu ta ji tsoro, don haka sai ta yi ƙarya ta ce, “Ban yi dariya ba.” Ya ce, “A’a, kin yi dariya.” Sai mutanen suka tashi suka nufi Sodom, Ibrahim kuwa ya yi musu rakiya, ya yi bankwana da su. Sai Ubangiji ya ce, “Zan ɓoye wa Ibrahim abin da nake shirin yi? Lalle Ibrahim zai zama al’umma mai girma da kuma mai iko, kuma ta wurinsa dukan al’umman duniya za su sami albarka. Saboda na zaɓe shi don yă umarci ’ya’yansa da iyalinsa a bayansa su kiyaye hanyoyin Ubangiji, ta wurin yin abin da yake daidai da kuma yin adalci, domin Ubangiji ya aikata abin da ya yi wa Ibrahim alkawari.” Sa’an nan Ubangiji ya ce, “Kuka a kan Sodom da Gomorra ta yi yawa, zunubinsu kuma ya yi muni sosai, zan gangara in ga ko abin da suka yi ya yi muni kamar yadda kukan ya zo gare ni, zan bincike.” Sai mutanen suka juya suka nufi wajen Sodom amma Ibrahim ya ci gaba da kasance a gaban Ubangiji. Sai Ibrahim ya matso wurinsa ya ce, “Za ka hallaka masu adalci tare da masu mugunta? Me zai faru in akwai mutum hamshin masu adalci a cikin birnin? Ashe, za ka hallaka shi, ba za ka cece wurin saboda mutane hamsin nan masu adalcin da suke a cikinsa ba? Tabbatacce ba za ka taɓa aikata irin wannan abu ba, ka kashe masu adalci tare da masu mugunta, ka ɗauka masu adalci da masu mugunta daidai? Tabbatacce ba za ka taɓa aikata irin wannan abu ba! Mai hukuncin dukan duniya ba zai aikata gaskiya ba?” Ubangiji ce, “In na sami mutum hamshin masu adalci a cikin birnin Sodom, zan bar dukan birnin saboda su.” Sai Ibrahim ya ƙara cewa, “Yanzu da na yi karambani har na yi magana da Ubangiji, ko da yake ni ba kome ba ne illa turɓaya da toka, in yawan masu adalci sun kāsa hamshin da mutum biyar fa? Za ka hallaka dukan birnin saboda rashin mutum biyar ɗin?” Ya ce, “In na sami mutum arba’in da biyar a wurin, ba zan hallaka shi ba.” Ya sāke cewa, “In mutum arba’in kaɗai aka samu a can fa?” Ya ce, “Saboda mutum arba’in ɗin, ba zan aikata ba.” Sai ya ce, “Kada Ubangiji ya yi fushi, amma bari in ƙara magana. A ce mutum talatin kaɗai aka samu a can fa?” Ya ce, “Ba zan aikata ba, in na sami mutum talatin a can.” Ibrahim ya ce, “Yanzu fa da na yi karambani har na yi magana da Ubangiji, in ashirin kaɗai aka samu a can fa?” Ya ce, “Saboda ashirin ɗin, ba zan hallaka shi ba.” Sa’an nan Ibrahim ya ce, “Kada Ubangiji yă yi fushi, amma bari in ƙara magana sau ɗaya tak. In aka sami mutum goma kaɗai a can fa?” Ubangiji ya ce, “Saboda goma nan, ba zan hallaka shi ba.” Sa’ad da Ubangiji ya gama magana da Ibrahim, ya tafi, Ibrahim kuma ya koma gida. Mala’ikun nan biyu suka iso Sodom da yamma. Lot kuwa yana zama a hanyar shiga birnin. Da ya gan su, sai ya tashi don yă tarye su, ya kuma rusuna da fuskarsa har ƙasa. Ya ce, “Ranku yă daɗe, ina roƙonku ku ratsa zuwa gidan bawanku. Ku wanke ƙafafunku, ku kwana, sa’an nan ku kama hanyarku da sassafe.” Suka ce, “A’a, za mu kwana a dandali.” Amma ya nace musu ƙwarai, sai suka tafi tare da shi, suka kuma shiga gidansa. Ya shirya musu abinci, ya gasa burodi marasa yisti, suka ci. Kafin suka shiga barci, sai ga dukan mutane, ƙanana da manya daga kowane ɓangare na birnin Sodom, suka kewaye gidan. Suka kira Lot, suka ce, “Ina mutanen da suka zo wurinka a daren nan? Fito mana da su waje domin mu kwana da su.” Lot ya fita daga cikin gida, ya rufe ƙofar a bayansa. Ya je wurin mutanen ya ce musu, “A’a, abokaina kada ku yi wannan mummunan abu. Duba, ina da ’ya’ya mata biyu waɗanda ba su taɓa sanin namiji ba, bari in kawo muku su ku yi kome da kuke so da su. Amma kada ku taɓa waɗannan mutane, gama su baƙina ne kuma dole in tsare su.” Sai mutanen birnin suka amsa, “Ba mu wuri! Wannan mutum ya zo nan kamar baƙo, ga shi yanzu yana so yă zama alƙali! Za mu wulaƙanta ka fiye da su.” Suka ci gaba da matsa wa Lot lamba, suka matsa kusa domin su fasa ƙofar. Amma mutanen da suke ciki suka miƙa hannunsu, suka ja Lot zuwa cikin gida, suka rufe ƙofar. Sai suka bugi mutanen da suke a bakin ƙofar gidan da makanta, ƙanana da manya duka, har suka gajiyar da kansu, suna lalluba inda ƙofar take. Mutanen nan biyun suka ce wa Lot, “Kana da wani a nan, ko surukai, ko ’ya’ya maza ko mata, ko kuwa wani dai a cikin birni wanda yake naka? Ka fitar da su daga nan, gama za mu hallaka wannan wuri. Kukan da aka yi ga Ubangiji game da mutanen birnin nan ya yi yawa sosai, ya sa har ya aiko mu domin mu hallaka birnin.” Saboda haka Lot ya tafi ya yi magana da surukansa waɗanda suka yi alkawari za su aure ’ya’yansa mata. Ya ce, “Ku yi sauri ku fita daga wannan wuri, gama Ubangiji yana gab da hallaka birnin.” Amma surukansa suka ɗauka wasa yake yi. Gari na wayewa, sai mala’ikun nan suka ƙarfafa Lot suna cewa, “Yi sauri! Ka ɗauki matarka da ’ya’yanka biyu mata waɗanda suke a nan, don kada a shafe ku sa’ad da ake hukunta birnin.” Da yana jan jiki, sai mutanen suka kama hannunsa da hannuwan matarsa da na ’ya’yansa biyu mata, suka kai su bayan birni, gama Ubangiji ya nuna musu jinƙai. Da suka fitar da su, sai ɗaya daga cikin mala’ikun ya ce, “Ku gudu domin ranku; kada ku duba baya, kada kuma ku tsaya ko’ina cikin kwarin! Ku gudu zuwa cikin duwatsu, don kada a hallaka ku!” Amma Lot ya ce musu, “A’a, ranka yă daɗe, ka yi haƙuri! Bawanku ya riga ya sami tagomashi daga gare ku, kun kuma nuna mini alheri mai yawa. Ba zan iya in gudu zuwa duwatsu ba, wannan masifa za tă same ni, zan kuma mutu. Ga ɗan gari can ya fi kusa inda zan gudu in fake. Bari in gudu zuwa can, in tsirar da raina.” Sai ya ce masa, “Na yarda da abin da ka ce, ba zan hallakar da garin da ka ambata ba. Gaggauta, ka gudu zuwa can, ba zan yi kome ba sai ka isa can.” (Domin haka ne ake kira garin Zowar.) A lokacin da Lot ya isa Zowar, rana ta hau. Sai Ubangiji ya yi ta zuba kibiritu a bisa Sodom da Gomorra daga sama. Haka ya hallakar da waɗannan birane da kuma kwarinsu gaba ɗaya, haɗe da dukan waɗanda suke zama a biranen, da kuma dukan shuke-shuke da suke cikin ƙasar. Amma matar Lot ta waiwaya baya, ta kuma zama ginshiƙin gishiri. Da sassafe kashegari, Ibrahim ya tashi ya koma wurin da dā ya tsaya a gaban Ubangiji. Ya duba ta wajen Sodom da Gomorra, da wajen dukan filayen ƙasar, sai ya ga hayaƙi baƙin ƙirin yana tashi daga ƙasar kamar hayaƙi daga matoya. Saboda haka sa’ad da Allah ya hallaka waɗannan biranen kwarin, ya tuna da Ibrahim, ya kuma fitar da Lot daga masifar da ta hallaka biranen da Lot ya zauna. Lot da ’ya’yansa biyu mata suka bar Zowar suka kuma zauna a cikin duwatsu, gama ya ji tsoro yă zauna a Zowar. Shi da ’ya’yansa biyu mata suka zauna a ciki wani kogo. Wata rana ’yarsa babba ta ce wa ƙanuwarta, “Mahaifinmu ya tsufa, kuma babu wani mutum kusa a nan da zai yi mana ciki mu haifi ’ya’ya; yadda al’ada take a ko’ina a duniya. Bari mu sa mahaifinmu yă sha ruwan inabi, sa’an nan sai mu kwana da shi, don kada zuriyar mahaifinmu ta ƙare.” A wannan dare, suka sa mahaifinsu ya sha ruwan inabi, ’yar farin ta shiga ta kwana da shi. Shi kuwa bai san sa’ad da ta kwanta ko sa’ad da ta tashi ba. Kashegari, ’yar farin ta ce wa ƙanuwar, “Jiya da dare na kwana da mahaifina. Bari mu sa yă sha ruwan inabi kuma yau da dare, ke ma ki shiga ki kwana da shi, domin kada zuriyar mahaifinmu ta ƙare.” Sai suka sa mahaifinsu ya sha ruwan inabi, a wannan dare ma, ƙanuwar ta shiga ta kwana da shi. Bai kuwa san sa’ad da ta kwanta ko sa’ad da ta tashi ba. Ta haka ’ya’yan Lot biyu mata duk suka yi ciki daga mahaifinsu. ’Yar farin ta haifi ɗa, ta kuma ba shi suna Mowab, shi ne mahaifin Mowabawa a yau. ’Yar ƙaramar ma ta haifi ɗa, ta kuwa ba shi suna Ben-Ammi, shi ne mahaifin Ammonawa a yau. Daga Mamre, Ibrahim ya kama hanya ya nufi wajajen Negeb, ya zauna a tsakanin Kadesh da Shur. Ya zauna a Gerar na ɗan lokaci, a can ne Ibrahim ya ce game da matarsa Saratu, “Ita ’yar’uwata ce.” Sai Abimelek sarkin Gerar ya aiko a kawo masa Saratu. Amma wata rana da dad dare Allah ya zo wa Abimelek a cikin mafarki ya ce masa, “Kai da matacce ɗaya kuke, saboda matar da ka ɗauka. Ita matar aure ce.” Abimelek dai bai riga ya kusace ta ba tukuna, saboda haka ya ce, “Ya Ubangiji za ka hallaka al’umma marar laifi? Ba shi ne ya ce mini, ‘Ita ’yar’uwata ba ce,’ ita ma ba tă ce, ‘Shi ɗan’uwana ba ne’? Na yi haka da kyakkyawan nufi da hannuwa masu tsabta.” Sai Allah ya ce masa a cikin mafarki “I, na san ka yi wannan da kyakkyawan nufi, saboda haka ne na kiyaye ka daga yin mini zunubi. Shi ya sa ban bar ka ka taɓa ta ba. Yanzu ka komar da matar mutumin, gama shi annabi ne, zai kuma yi maka addu’a, za ka kuwa rayu. In ba ka komar da ita ba fa, ka sani tabbatacce kai da dukan abin da yake naka za ku mutu.” Kashegari da sassafe, sai Abimelek ya tara dukan fadawansa, ya faɗa musu duk abin da ya faru, suka ji tsoro ƙwarai da gaske. Sa’an nan Abimelek ya kira Ibrahim ciki ya ce, “Me ke nan ka yi mana? Ta wace hanya ce na yi maka laifi har da ka kawo irin wannan babban laifi a kaina da kuma masarautata? Ka yi mini abubuwan da bai kamata a yi ba.” Abimelek ya kuma ce wa Ibrahim, “Me ya sa ka yi wannan?” Ibrahim ya ce, “Na ce a raina, ‘Tabbatacce babu tsoron Allah a wannan wuri, za su kuwa kashe ni saboda matata.’ Ban da haka, tabbatacce ita ’yar’uwata ce, ’yar mahaifina, ko da yake ba daga uwata ba, ta kuma zama matata. Sa’ad da Allah ya sa na tashi daga gidan mahaifina na ce mata, ‘Wannan shi ne yadda za ki nuna mini ƙaunarki. Duk inda muka tafi, ki ce game da ni, “Shi ɗan’uwana ne.” ’ ” Sai Abimelek ya kawo awaki da shanu da bayi maza da mata, ya ba wa Ibrahim, ya kuma komar da Saratu matarsa gare shi. Abimelek ya kuma ce, “Ƙasata tana gabanka, ka zauna a duk inda kake so.” Ga Saratu kuwa ya ce, “Ina ba wa ɗan’uwanki shekel dubu na azurfa, shaida ce ta tabbatarwa a idanun dukan waɗanda suke tare da ke, da kuma a gaban kowa cewa ba ki da laifi.” Sai Ibrahim ya yi addu’a ga Allah, Allah kuma ya warkar da Abimelek, da matarsa da bayinsa mata domin su haihu, gama Ubangiji ya rufe kowace mahaifa a gidan Abimelek saboda Saratu, matar Ibrahim. Ana nan sai Ubangiji ya nuna wa Saratu alheri kamar yadda ya ce, Ubangiji kuma ya yi wa Saratu abin da ya yi alkawari. Saratu ta yi ciki, ta kuma haifa wa Ibrahim ɗa a tsufansa; a daidai lokacin da Allah ya yi masa alkawari. Ibrahim ya sa wa ɗan da Saratu ta haifa masa suna Ishaku. Sa’ad da ɗansa Ishaku ya kai kwana takwas da haihuwa, sai Ibrahim ya yi masa kaciya, kamar yadda Allah ya umarce shi. Ibrahim yana da shekara ɗari, sa’ad da aka haifa masa ɗansa Ishaku. Saratu ta ce, “Allah ya sa na yi dariya, kuma duk wanda ya ji game da wannan, zai yi dariya tare da ni.” Ta kuma ƙara da cewa, “Dā, wa zai iya ce wa Ibrahim, Saratu za tă yi renon yara? Duk da haka na haifar masa ɗa cikin tsufansa.” Yaron ya yi girma, aka kuma yaye shi, a ranar da aka yaye shi kuwa, Ibrahim ya yi babban biki. Amma Saratu ta ga cewa yaron da Hagar, mutuniyar Masar ta haifa wa Ibrahim yana wa ɗanta Ishaku gori, sai ta ce wa Ibrahim, “Ka kori baiwan nan tare da ɗanta, saboda ɗan baiwan nan ba zai taɓa raba gādo da ɗana Ishaku ba.” Al’amarin ya ɓata wa Ibrahim rai sosai domin zancen ya shafi ɗansa. Amma Allah ya ce wa Ibrahim, “Kada hankalinka yă tashi game da yaron nan da kuma baiwarka. Ka saurari duk abin da Saratu ta faɗa maka, saboda ta wurin Ishaku ne za a lissafta zuriyarka. Zan ba ɗan baiwan nan al’umma shi ma, domin shi zuriyarka ne.” Kashegari da sassafe sai Ibrahim ya ɗauki abinci da salkar ruwa, ya ba wa Hagar. Ya ɗora su a kafaɗunta, sa’an nan ya sallame ta da yaron. Ta kama hanyarta ta kuma yi ta yawo a cikin jejin Beyersheba. Sa’ad da ruwan da yake cikin salkan ya ƙare, sai ta ajiye yaron a ƙarƙashin wani ƙaramin itace. Sai ta tafi, ta zauna ɗan nesa da yaron, misalin nisan harbin baka, gama ta yi tunani ta ce, “Ba zan iya kallon yaron yana mutuwa ba.” Da ta zauna nesa da yaron, sai ta fara kuka. Allah kuwa ya ji yaron yana kuka, sai mala’ikan Allah ya kira Hagar daga sama ya ce mata, “Mene ne damuwarki, Hagar? Kada ki ji tsoro, Allah ya ji yaron yana kuka yayinda yake kwance a can. Ki ɗaga yaron ki riƙe shi a hannu, gama zan mai da shi al’umma mai girma.” Sa’an nan Allah ya buɗe idanunta ta ga wata rijiyar ruwa. Don haka sai ta tafi ta cika salkan da ruwa, ta kuma ba wa yaron ruwa ya sha. Allah ya kasance da yaron, yayinda yake girma. Ya yi zama a jeji, ya kuma zama maharbi. Yayinda yake zama a Jejin Faran, sai mahaifiyarsa ta samo masa mata daga Masar. A lokacin nan Abimelek da Fikol, komandan rundunoninsa suka zo suka ce wa Ibrahim, “Allah yana tare da kai a ko mene ne kake yi. Yanzu ka rantse mini a nan a gaban Allah cewa, ba za ka yaudare ni ko ’ya’yana ko kuma zuriyata ba. Ka nuna mini alheri, kai da ƙasar da kake zama baƙunci kamar yadda na nuna maka.” Ibrahim ya ce, “Na rantse.” Sa’an nan Ibrahim ya kawo kuka ga Abimelek game da rijiyar ruwan da bayin Abimelek suka ƙwace. Sai Abimelek ya ce, “Ban san wanda ya yi wannan ba. Ba ka faɗa mini ba, ban kuwa taɓa ji ba, sai yau.” Sai Ibrahim ya kawo tumaki da shanu ya ba wa Abimelek, sai su biyun suka yi yarjejjeniya. Ibrahim ya ware ’yan raguna bakwai daga cikin garke, sai Abimelek ya ce wa Ibrahim, “Mene ne ma’anar ’yan raguna bakwai da ka keɓe?” Ibrahim ya amsa ya ce, “Ka karɓi waɗannan ’yan tumaki bakwai daga hannuna a matsayin shaida cewa ni ne na haƙa wannan rijiya.” Saboda haka aka kira wurin Beyersheba, domin a nan ne su biyun suka yi rantsuwa. Bayan da aka yi yarjejjeniya a Beyersheba, sai Abimelek da Fikol, komandan rundunoninsa suka koma ƙasar Filistiyawa. Sai Ibrahim ya shuka itacen tsamiya a Beyersheba, a can kuma ya kira bisa sunan Ubangiji, Allah Madawwami. Ibrahim kuwa ya zauna a ƙasar Filistiyawa na dogon lokaci. Bayan abubuwan nan suka faru, sai Allah ya gwada Ibrahim. Ya ce masa, “Ibrahim!” Ibrahim ya amsa ya ce, “Ga ni.” Sai Allah ya ce, “Ka ɗauki ɗanka, makaɗaicin ɗanka Ishaku, wanda kake ƙauna, ka tafi yankin Moriya, ka miƙa shi hadaya ta ƙonawa a can a kan ɗaya daga cikin duwatsun da zan nuna maka.” Kashegari da sassafe, Ibrahim ya tashi ya ɗaura wa jakinsa sirdi. Ya ɗauki bayinsa biyu, da ɗansa Ishaku. Bayan ya faskare isashen itace saboda hadaya ta ƙonawa sai ya kama hanya zuwa wurin da Allah ya faɗa masa. A rana ta uku Ibrahim ya ɗaga ido sai ya ga wurin daga nesa. Ibrahim ya ce wa bayinsa, “Ku tsaya a nan da jakin, ni da yaron kuwa mu haura can. Za mu yi sujada sa’an nan mu komo wurinku.” Ibrahim ya ɗauki itace saboda hadaya ta ƙonawa ya ɗora wa ɗansa Ishaku, shi kuwa ya riƙe wuƙa da wutar. Yayinda su biyun suke tafiya, sai Ishaku ya yi tambaya, ya ce wa mahaifinsa Ibrahim, “Baba?” Ibrahim ya ce masa, “Na’am ɗana!” Ishaku ya ce, “Ga dai wuta, ga kuma itace, amma ina ɗan ragon hadaya ta ƙonawa?” Ibrahim ya amsa ya ce, “Ɗana, Allah kansa zai tanada ɗan ragon hadayar ƙonawa.” Sai su biyu suka ci gaba da tafiya. Sa’ad da suka isa wurin da Allah ya faɗa masa, sai Ibrahim ya gina bagade a can, ya kuma shisshirya itacen a kai. Ya ɗaura ɗansa Ishaku, ya kwantar da shi a kan itacen, a bisa bagaden. Sa’an nan Ibrahim ya miƙa hannunsa ya ɗauki wuƙar don yă yanka ɗansa. Amma mala’ikan Ubangiji ya kira shi daga sama ya ce, “Ibrahim, Ibrahim!” Sai Ibrahim ya amsa ya ce, “Ga ni.” Mala’ikan ya ce, “Kada ka yi wa yaron nan rauni. Kada kuma ka ji masa ciwo. Yanzu na san cewa kana tsoron Allah, gama ba ka hana ni ɗanka, makaɗaicin ɗanka ba.” Ibrahim ya ɗaga ido, ya duba, sai ya ga rago da ƙahoninsa a kafe a wani ɗan kurmi. Sai Ibrahim ya tafi ya kamo ragon ya miƙa shi hadaya ta ƙonawa a maimakon ɗansa. Ibrahim kuwa ya ba wa wurin suna, Ubangiji Zai Tanada. Gama kamar yadda ake ce har yă zuwa yau, “A bisan dutsen Ubangiji, za a tanada.” Mala’ikan Ubangiji ya kira Ibrahim daga sama sau na biyu ya ce, “Na rantse da kaina, in ji Ubangiji, domin ka yi wannan, ba ka kuwa hana ni ɗanka, makaɗaicin ɗanka ba, tabbatacce zan albarkace ka, zan kuma sa zuriyarka su yi yawa kamar taurari a sararin sama, kamar kuma yashi a bakin teku. Zuriyarka za su mallaki biranen abokan gābansu, ta wurin zuriyarka kuma dukan al’umman duniya za su sami albarka, domin ka yi mini biyayya.” Sa’an nan Ibrahim ya koma wurin bayinsa, suka kuma kama hanya tare zuwa Beyersheba. Ibrahim kuwa ya yi zamansa a Beyersheba. Bayan wani ɗan lokaci, sai aka faɗa wa Ibrahim cewa, “Ga shi, Milka ita ma ta haifa wa Nahor ɗan’uwanka, ’ya’ya maza; ɗan fari shi ne Uz, ɗan’uwansa kuma Buz, Kemuwel (shi ne mahaifin Aram), Kesed, Hazo, Fildash; Yidlaf, da kuma Betuwel.” Betuwel ya haifi Rebeka. Milka ta haifa wa Nahor ɗan’uwan Ibrahim waɗannan ’ya’ya maza takwas. Ban da haka ma, ƙwarƙwararsa, mai suna Reyuma, ta haifa masa ’ya’ya maza, Teba, Gaham, Tahash da kuma Ma’aka. Saratu ta yi shekara ɗari da ashirin da bakwai a duniya. Ta rasu a Kiriyat Arba (wato, Hebron) a ƙasar Kan’ana, Ibrahim kuwa ya tafi ya yi makokin Saratu, yana kuka saboda ita. Sai Ibrahim ya tashi daga gefen matarsa da ta mutu, ya yi magana da Hittiyawa. Ya ce, “Ni baƙo ne, kuma baƙo a cikinku. Ku sayar mini da wani wuri yă zama wurin binnewa a nan, domin in binne mataccena.” Hittiyawa suka ce wa Ibrahim, “Ranka yă daɗe, ka saurare mu. Kai babban yerima ne a cikinmu. Ka binne mataccenka a kabari mafi kyau na kaburburanmu. Babu waninmu da zai hana ka kabarinsa don binne mataccenka.” Sai Ibrahim ya tashi ya rusuna a gaban mutanen ƙasar, wato, Hittiyawan. Ya ce musu, “In kuna so in binne mataccena, sai ku ji ni, ku roƙi Efron ɗan Zohar a madadina domin yă sayar mini da kogon Makfela, wanda yake nasa, wannan da yake a ƙarshen filinsa. Ku ce masa yă sayar mini a cikakken farashi, yă zama mallakata domin makabarta tsakaninku.” Efron mutumin Hitti yana zaune a cikin mutanensa, sai ya amsa wa Ibrahim a kunnuwan dukan Hittiyawa waɗanda suka zo ƙofar birni. Ya ce, “A’a, ranka yă daɗe, ka ji ni, na ba ka filin, na kuma ba ka kogon da yake cikinsa. Na ba ka shi a gaban mutanena. Ka binne mataccenka.” Ibrahim ya sāke rusuna a gaban mutanen ƙasar ya ce wa Efron a kunnuwansu, “Ka ji, in ka yarda. Zan biya farashin filin. Ka karɓa daga gare ni don in iya binne mataccena a can.” Efron ya ce wa Ibrahim, “Ka saurare ni, ranka yă daɗe; darajan filin ya kai shekel ɗari huɗu na azurfa, amma mene ne wannan a tsakanina da kai? Ka binne mataccenka.” Ibrahim ya yarda da sharuɗan Efron, sai ya auna masa farashin da ya faɗa a kunnuwan Hittiyawa, shekel ɗari huɗu na azurfa, bisa ga ma’aunin da ’yan kasuwa suke amfani da shi a lokacin. Ta haka filin Efron a Makfela kusa da Mamre, wato, filin da kogon a cikinsa, da kuma dukan itatuwan da suke cikin iyakoki filin, aka ba wa Ibrahim a matsayin mallakarsa a gaban dukan Hittiyawa waɗanda suka zo ƙofar birnin. Bayan wannan Ibrahim ya binne matarsa Saratu a kogon a filin Makfela kusa da Mamre (wanda yake a Hebron) a ƙasar Kan’ana. Da filin da kuma kogon da yake cikinsa, Hittiyawa suka tabbatar wa Ibrahim a matsayin makabarta. Yanzu fa Ibrahim ya tsufa, yana da shekaru masu yawa, Ubangiji kuma ya albarkace shi a kowace hanya. Sai Ibrahim ya ce wa babban bawan gidansa, wanda yake lura da duk abin da yake da shi, “Sa hannunka a ƙarƙashin cinyata. Ina so ka rantse da sunan Ubangiji Allah na sama da ƙasa, cewa ba za ka samo wa ɗana mata daga ’yan matan Kan’aniyawa, waɗanda nake zama cikinsu ba. Amma za ka tafi ƙasata da kuma cikin ’yan’uwana, ka samo mata saboda ɗana Ishaku.” Bawan ya ce masa, “Me zai faru in matar ba tă yarda tă zo tare da ni zuwa wannan ƙasa ba? In komar da ɗanka a ƙasar da ka fito ne ke nan?” Ibrahim ya ce, “Ka tabbata ba ka komar da ɗana can ba.” Ubangiji Allah na sama, wanda ya fitar da ni daga gidan mahaifina, da kuma ƙasar asalina wanda kuma ya yi magana da ni, ya yi mini alkawari da rantsuwa cewa, “Ga zuriyarka zan ba da wannan ƙasa, zai aika mala’ikansa yă sha gabanka domin ka samo wa ɗana mata daga can. In matar ba tă yarda tă zo tare da kai ba, za a kuɓutar da kai daga wannan rantsuwa. Sai dai kada ka kai ɗana a can.” Saboda haka bawan ya sa hannunsa a ƙarƙashin cinyar maigidansa Ibrahim, ya kuma rantse masa game da wannan al’amari. Sai bawan ya ɗibi raƙuma goma na maigidansa ya tafi, ɗauke da kowane irin abubuwa masu kyau daga wurin maigidansa. Ya fita don yă tafi Aram-Naharayim, ya kama hanyarsa zuwa garin Nahor. Ya sa raƙuman suka durƙusa kusa da rijiya a bayan gari; wajen yamma ne, lokacin da mata sukan fita ɗiban ruwa. Sai ya yi addu’a ya ce, “Ya Ubangiji Allah na maigidana Ibrahim, ka ba ni nasara yau, ka kuma nuna alheri ga maigidana Ibrahim. Duba, ina tsaye a bakin rijiyar ruwa, ’ya’ya matan mutanen gari kuma suna fitowa domin ɗiban ruwa. Bari yă zama sa’ad da na ce wa wata yarinya, ‘Ina roƙonki ki saukar da tulunki domin in sha,’ in ta ce, ‘Ka sha, zan kuma ba wa raƙumanka ma’; bari tă zama ita ce ka zaɓa wa bawanka Ishaku. Ta haka zan san cewa ka nuna wa maigidana alheri.” Kafin ya gama addu’a, sai Rebeka ta fito da tulu a kafaɗarta. Ita ’yar Betuwel ɗan Milka, matar Nahor, ɗan’uwan Ibrahim. Yarinyar kuwa kyakkyawa ce, budurwa, ba namijin da ya taɓa kwana da ita. Ta gangara zuwa rijiyar, ta cika tulunta ta kuma hauro. Bawan ya yi sauri ya same ta ya ce, “Ina roƙonki ki ba ni ɗan ruwa daga tulunki.” Ta ce, “Ka sha, ranka yă daɗe,” ta yi sauri ta saukar da tulun a hannuwanta, ta kuma ba shi, ya sha. Bayan ta ba shi ya sha, sai ta ce, “Zan ɗebo wa raƙumanka ruwa su ma, har sai sun gama sha.” Sai ta yi sauri ta juye ruwan da yake tulunta cikin kwami, ta koma zuwa rijiyar da gudu don ta ƙara ɗebo ruwa, ta kuma ɗebo isashe saboda dukan raƙumansa. Mutumin bai ce uffam ba, ya dai kalle ta sosai don yă san ko Ubangiji ya ba shi nasara a tafiyarsa ko babu. Sa’ad da raƙuman suka gama shan ruwa, mutumin ya fitar da zoben hanci na zinariya mai nauyin giram biyar da woroworo biyu na zinariya masu nauyin shekel goma, ya ba ta. Sa’an nan ya tambaye ta ya ce, “Ke ’yar wace ce? Ina roƙonki ki faɗa mini, akwai wuri a gidan mahaifinki da za mu kwana?” Sai ta ce masa, “Ni ’yar Betuwel ce ɗan da Milka ta haifa wa Nahor.” Ta ƙara da cewa, “Muna da isashen ciyawa da abincin dabbobi, da kuma wuri domin ku kwana.” Sa’an nan mutumin ya rusuna ya yi wa Ubangiji sujada, yana cewa, “Yabo ya tabbata ga Ubangiji Allah na maigidana Ibrahim, wanda bai daina nuna alheri da amincinsa ga maigidana ba. Ni kam, Ubangiji ya bishe ni a tafiyata zuwa gidan ’yan’uwan maigidana.” Yariyan ta gudu ta faɗa wa mutanen gidan mahaifiyarta game da abubuwan nan. Rebeka fa tana da wani ɗan’uwa mai suna Laban, sai ya yi hanzari ya fita zuwa wurin mutumin a rijiyar. Nan da nan da ya ga zoben hancin da woroworo a hannuwan ’yar’uwansa, ya kuma ji Rebeka ta faɗa abin da mutumin ya ce mata, sai ya fita zuwa wurin mutumin, ya same shi yana tsaye wajen raƙuma kusa da rijiyar. Sai ya ce, “Zo, ya kai mai albarka na Ubangiji, don me kake tsaye a waje? Gama na shirya gida da wuri domin raƙuma.” Don haka mutumin ya tafi gidan, aka kuma saukar da kaya kan raƙuman. Aka kawo wa raƙuman ciyawa da abincin dabbobi, aka kuma kawo ruwa dominsa da mutanensa su wanke ƙafafunsu. Sa’an nan aka ajiye abinci a gabansa, amma ya ce, “Ba zan ci ba, sai na faɗi abin da yake tafe da ni.” Sai Laban ya ce, “Faɗa mana.” Saboda haka ya ce, “Ni bawan Ibrahim ne. Ubangiji ya albarkaci maigidana sosai, ya kuma zama mai arziki. Ya ba shi tumaki, shanu, azurfa, zinariya, bayi maza da mata, raƙuma, da kuma jakuna. Saratu matar maigidana ta haifa masa ɗa a tsufanta, ya kuma ba shi duk mallakarsa. Maigidana ya sa na yi rantsuwa, ya kuma ce, ‘Kada ka ɗauko wa ɗana mata daga ’ya’ya matan Kan’aniyawa, waɗanda nake zama a ƙasarsu, amma ka tafi wajen gidan mahaifina da kuma dangina, ka ɗauko wa ɗana mata.’ “Sai na ce wa maigidana, ‘A ce matar ba tă yarda tă zo tare da ni ba fa?’ “Maigidana ya ce, ‘ Ubangiji wanda yake tare da ni zai aiki mala’ikansa tare da kai, yă kuma sa tafiyarka tă yi nasara, don ka samo wa ɗana mata daga dangina, daga kuma gidan mahaifina. Ta haka za ka kuɓuta daga rantsuwata sa’ad da ka tafi wurin dangina, ko ma sun ƙi su ba ka ita, za ka kuɓuta daga rantsuwata.’ “Sa’ad da na zo rijiya a yau, na ce, ‘Ya Ubangiji Allah na maigidana Ibrahim, ina roƙonka ka ba ni nasara a tafiyar da na yi. Duba, ina tsaye kusa da wannan rijiya; in wata yarinya ta fito domin tă ɗiba ruwa, wadda in na ce mata, “Ina roƙonki bari in ɗan sha ruwa daga tulunki,” in ta ce, “Ka sha, zan kuma ba wa raƙumanka ma,” bari tă zama wadda Ubangiji ya zaɓar wa ɗan maigidana.’ “Kafin in gama addu’ar, a zuciyata, sai ga Rebeka ta fito da tulunta a kafaɗarta. Ta gangara zuwa rijiyar ta ɗebo ruwa, na kuma ce mata, ‘Ina roƙonki ki ba ni ɗan ruwa daga tulunki.’ “Ta yi sauri ta saukar da tulun daga kafaɗarta ta ce, ‘Sha, zan kuma ba wa raƙumanka su ma.’ Sai na sha, ta kuma shayar da raƙumana su ma. “Na tambaye ta, ‘Ke ’yar wane ne?’ “Ta ce, ‘’Yar Betuwel ɗan Nahor, wanda Milka ta haifa masa.’ “Sai na sa mata zobe a hancinta, woroworo kuma a hannuwata, na kuma sunkuya na yi wa Ubangiji sujada. Na yabi Ubangiji Allah na maigidana Ibrahim wanda ya bi da ni a hanyar da take daidai, don in samo wa ɗan maigidana jikanyar ɗan’uwansa. Yanzu fa in za ku nuna wa maigidana alheri da aminci, ku faɗa mini, in kuma ba haka ba, ku faɗa mini, don in san hanyar da zan juya.” Laban da Betuwel suka ce, “Wannan daga wurin Ubangiji ne, ba abin da za mu ce I, ko a’a ba. Ga Rebeka, ɗauke ta ku tafi, bari tă zama matar ɗan maigidanka, yadda Ubangiji ya umarta.” Sa’ad da bawan Ibrahim ya ji abin da suka ce, sai ya rusuna har ƙasa a gaban Ubangiji. Sa’an nan bawan ya fito da kayan ado na zinariya da azurfa da kayayyaki na tufafi ya ba wa Rebeka; ya kuma ba wa ɗan’uwanta da mahaifiyarta kyautai masu tsada. Sa’an nan shi da mutanen da suke tare da shi suka ci, suka sha, suka kuma kwana a can. Kashegari da safe da suka tashi sai ya ce, “A sallame ni in koma wurin maigidana.” Amma ɗan’uwanta da mahaifiyarta suka ce, “Bari yarinyar ta ɗan zauna tare da mu kwana goma ko fiye, sa’an nan ka ta fi.” Amma ya ce musu, “Kada ku tsai da ni, tun da Ubangiji ya ba ni nasara a tafiyata. Ku sallame ni domin in tafi wurin maigidana.” Sa’an nan suka ce, “Bari mu kira yarinyar mu tambaye ta game da zancen.” Saboda haka suka kira Rebeka suka ce mata, “Za ki tafi tare da mutumin nan?” Sai ta ce, “Zan tafi.” Saboda haka suka sallame Rebeka, ’yar’uwarsu, duk da uwar goyonta da bawan Ibrahim da mutanensa. Suka kuma albarkaci Rebeka suka ce mata, “’Yar’uwarmu, bari ki zama mahaifiyar dubu dubbai, bari zuriyarki su mallaki ƙofofin abokan gābansu.” Sa’an nan Rebeka da bayinta mata suka shirya suka hau raƙumansu suka koma tare da mutumin. Da haka bawan ya ɗauki Rebeka ya tafi. Ishaku kuwa ya zo daga Beyer-Lahai-Royi, gama yana zama a Negeb. Wata rana da yamma ya fita zuwa fili domin yă yi tunani, sa’ad da ya ɗaga ido, sai ya ga raƙuma suna zuwa. Rebeka ma ta ɗaga ido sai ta ga Ishaku. Ta sauka daga raƙuminta da sauri, ta ce wa bawan, “Wane ne mutumin can a fili, da yake zuwa yă tarye mu?” Bawan ya ce, “Maigidana ne.” Saboda haka ta ɗauki mayafinta to rufe kanta. Sai bawan ya faɗa wa Ishaku duk abin da ya yi. Ishaku ya kawo ta cikin tentin mahaifiyarsa Saratu, ya kuma auri Rebeka. Ta haka ta zama matarsa, ya kuwa ƙaunace ta; Ishaku kuma ya ta’azantu bayan rasuwar mahaifiyarsa. Ibrahim ya auro wata mace, mai suna Ketura. Ta haifa masa Zimran, Yokshan, Medan, Midiyan, Ishbak da Shuwa. Yokshan shi ne mahaifin Sheba da Dedan. Zuriyar Dedan su ne mutanen Ashur, da mutanen Letush, da kuma mutanen Lewummin. ’Ya’yan Midiyan maza su ne, Efa, Efer, Hanok, Abida, da kuma Elda’a. Dukan waɗannan zuriyar Ketura ce. Ibrahim ya bar wa Ishaku kome da ya mallaka. Amma yayinda Ibrahim yake da rai, ya ba wa ’ya’yan ƙwarƙwaransa maza kyautai, ya kuma sallame su daga ɗansa Ishaku zuwa ƙasashen gabas. Duka-duka, Ibrahim ya yi shekara ɗari da saba’in da biyar. Sa’an nan Ibrahim ya ja numfashinsa na ƙarshe, ya kuma mutu da kyakkyawar tsufa, tsoho da kuma shekaru masu yawa; aka kuma tara shi ga mutanensa. ’Ya’yansa maza kuwa Ishaku da Ishmayel suka binne shi cikin kogon Makfela, kusa da Mamre, a cikin filin Efron ɗan Zohar mutumin Hitti, filin da Ibrahim ya saya daga Hittiyawa. A nan aka binne Ibrahim tare da matarsa Saratu. Bayan rasuwar Ibrahim, Allah ya albarkaci ɗansa Ishaku wanda a lokacin yana zama kusa da Beyer-Lahai-Royi. Waɗannan su ne zuriyar Ishmayel ɗan Ibrahim, wanda Hagar mutuniyar Masar, baranyar Saratu, ta haifa wa Ibrahim. Ga jerin sunayen ’ya’yan Ishmayel maza bisa ga haihuwarsu, Nebayiwot ɗan farin Ishmayel, Kedar, Adbeyel, Mibsam, Mishma, Duma, Massa, Hadad, Tema, Yetur, Nafish da Kedema. Waɗannan su ne ’ya’yan Ishmayel maza, waɗanda kuma suke sunayen kabilu goma sha biyu masu mulki bisa ga wuraren zamansu da sansaninsu. Duka-duka Ishmayel ya yi shekara ɗari da talatin da bakwai; sai ya ja numfashinsa na ƙarshe, ya kuma mutu, aka kuma tara shi ga mutanensa. Zuriyarsa sun zauna tsakanin Hawila ne da Shur, wanda yake kusa da gabashin iyakar Masar wajen Asshur. Sun yi zaman rikici da dukan sauran ’yan’uwansu. Waɗannan su ne zuriyar Ishaku ɗan Ibrahim. Ibrahim ya haifi Ishaku, Ishaku yana da shekara arba’in sa’ad da ya auri Rebeka ’yar Betuwel, mutumin Aram, daga Faddan Aram, ’yar’uwar Laban mutumin Aram. Ishaku ya yi addu’a ga Ubangiji a madadin matarsa, saboda ba ta haihuwa. Ubangiji ya amsa addu’arsa, matarsa Rebeka kuwa ta yi ciki. Jariran suka kama kokawa da juna a cikinta, sai ta ce, “Me ya sa wannan yake faruwa da ni?” Saboda haka ta tafi don ta nemi nufin Ubangiji. Ubangiji ya ce mata, “Al’ummai biyu suna a cikin mahaifarki mutum biyu da za ki haifa, za su rabu da juna, ɗayan zai fi ɗayan ƙarfi, babban kuma zai bauta wa ƙaramin.” Da lokaci ya yi da za tă haihu, sai ga ’yan biyu maza a mahaifarta. Wanda ya fara fita ja ne, dukan jikinsa kuwa kamar riga mai gashi. Don haka aka sa masa suna Isuwa. Bayan wannan, ɗan’uwansa ya fito, da hannunsa yana riƙe da ɗiɗɗigen Isuwa; don haka aka sa masa suna Yaƙub. Ishaku yana da shekara sittin, lokacin da Rebeka ta haife su. Yaran suka yi girma, Isuwa kuwa ya zama riƙaƙƙen maharbi, mutumin jeji, yayinda Yaƙub, shiru-shiru ne mai son zama a tentuna. Ishaku, mai son ci naman jeji, ya ƙaunaci Isuwa, amma Rebeka ta ƙaunaci Yaƙub. Wata rana sa’ad da Yaƙub yana dafa fate. Isuwa ya shigo daga jeji, da yunwa sosai. Ya ce wa Yaƙub, “Ina roƙonka, ka ɗan ɗiba mini faten nan! Ina fama da yunwa!” (Shi ya sa aka kira shi Edom.) Yaƙub ya amsa ya ce, “Ka fara sayar mini da matsayinka na ɗan fari tukuna.” Isuwa ya ce, “Duba, ina gab da mutuwa, me matsayina na ɗan fari zai yi mini?” Amma Yaƙub ya ce, “Ka rantse mini tukuna.” Don haka ya rantse masa, ya sayar da matsayinsa na ɗan fari ga Yaƙub. Sa’an nan Yaƙub ya ba wa Isuwa burodi da ɗan miyan lansir. Ya ci, ya sha, sa’an nan ya tashi ya tafi. Ta haka Isuwa ya yi banza da matsayinsa na ɗan fari. Aka yi yunwa a ƙasar; ban da yunwar da aka yi da fari a zamanin Ibrahim, sai Ishaku ya tafi wurin Abimelek sarkin Filistiyawa a Gerar. Ubangiji kuwa ya bayyana ga Ishaku ya ce, “Kada ka gangara zuwa Masar; ka yi zauna a ƙasar da zan faɗa maka. Ka zauna a wannan ƙasa na ɗan lokaci, zan kuwa kasance tare da kai, zan kuma albarkace ka. Gama zan ba da waɗannan ƙasashe gare ka da kuma zuriyarka. Zan kuma cika rantsuwar da na yi wa mahaifinka Ibrahim. Zan sa zuriyarka ta yi yawa kamar taurari a sararin sama zan kuwa ba su dukan waɗannan ƙasashe, ta wurin ’ya’yanka kuma za a albarkaci dukan al’umman duniya, domin Ibrahim ya yi mini biyayya ya kuma kiyaye umarnaina, ƙa’idodina da kuma dokokina.” Sai Ishaku ya zauna a Gerar. Sa’ad da mutanen wurin suka tambaye shi game da matarsa, sai ya ce, “’Yar’uwata ce,” gama yana tsoro yă ce, “Ita matata ce.” Ya yi tunani, “Mutane wannan wuri za su kashe ni ta dalili Rebeka, domin kyakkyawa ce.” Sa’ad da Ishaku ya daɗe a can, sai Abimelek sarkin Filistiyawa ya duba daga taga ya ga Ishaku yana rungumar matarsa Rebeka. Saboda haka Abimelek ya aika Ishaku yă je, sa’an nan ya ce, “Tabbatacce ita matarka ce! Me ya sa ka ce, ‘Ita ’yar’uwata ce?’ ” Ishaku ya amsa masa ya ce, “Don na yi tsammani zan rasa raina saboda ita.” Sa’an nan Abimelek ya ce, “Me ke nan ka yi mana? Da a ce wani daga mazanmu ya kwana da matarka, ai, da ka jawo laifi a kanmu.” Saboda haka Abimelek ya yi umarni ga dukan mutane. “Duk wanda ya fitine wannan mutum ko matarsa, tabbatacce za a kashe shi.” Ishaku ya shuka hatsi a wannan ƙasa, a shekaran nan ya yi girbi ninki ɗari, domin Ubangiji ya albarkace shi. Mutumin ya arzuta, arzikinsa ya yi ta haɓaka har ya zama attajiri. Ya kasance da garkunan tumaki da na shanu da bayi masu yawa, har Filistiyawa suka yi ƙyashinsa. Saboda haka dukan rijiyoyin da bayin mahaifinsa suka haƙa a kwanakin da mahaifinsa Ibrahim yake da rai, Filistiyawa sun toshe su, suka kuma ciccike su da ƙasa. Sai Abimelek ya ce wa Ishaku, “Fita daga cikinmu; ka fi ƙarfinmu.” Saboda haka Ishaku ya fita daga can, ya yi sansani a Kwarin Gerar, ya kuma zauna a can. Ishaku ya sāke tona rijiyoyi waɗanda dā aka haƙa a zamanin Ibrahim mahaifinsa, gama Filistiyawa suka tattoshe bayan mutuwar Ibrahim, ya kuma sa musu sunayen da mahaifinsa ya ba su. Barorin Ishaku suka haƙa cikin kwarin suka kuwa sami rijiya mai ruwa mai kyau a can. Amma makiyayan Gerar suka yi faɗa da na Ishaku suka ce, “Ruwan namu ne!” Saboda haka Ishaku ya ba wa rijiyar suna Esek, domin sun yi faɗa da shi. Sai suka haƙa wata rijiya, amma suka yi faɗa a kanta ita ma, saboda haka ya ce da ita Sitna. Sai Ishaku ya matsa daga can ya sāke haƙa wata rijiyar, babu wani kuma da yi faɗa a kanta. Sai ya ba ta suna Rehobot, yana cewa, “Yanzu Ubangiji ya ba mu wuri, za mu kuwa yi ta haihuwa a ƙasar.” Daga can ya haura zuwa Beyersheba. A wannan dare Ubangiji ya bayyana gare shi ya ce, “Ni ne Allah na mahaifinka Ibrahim. Kada ka ji tsoro, gama ina tare da kai, zan albarkace ka, zan kuma ƙara yawan zuriyarka saboda bawana Ibrahim.” Sai Ishaku ya gina bagade a can, ya kuma kira bisa sunan Ubangiji. A can ya kafa tentinsa, a can kuma bayinsa suka haƙa wata rijiya. Ana cikin haka, sai Abimelek ya zo wurinsa daga Gerar, tare da Ahuzzat mai ba shi shawara da Fikol shugaban mayaƙansa. Ishaku ya tambaye su, “Me ya kawo ku gare ni, da yake kun yi gāba da ni, kuka kuma kore ni?” Suka amsa, “Mun ga a zahiri cewa Ubangiji yana tare da kai; saboda haka muka ce, ‘Dole rantsuwa ta kasance tsakaninmu da kai.’ Bari mu yi yarjejjeniya da kai cewa ba za ka cuce mu ba, kamar yadda ba mu fitine ka ba, amma muka yi maka kirki, muka kuma sallame ka cikin salama. Yanzu kuwa kai albarkatacce ne na Ubangiji.” Sai Ishaku ya shirya musu liyafa, suka ci suka kuma sha. Kashegari da sassafe sai mutanen suka yi wa juna rantsuwa. Sa’an nan Ishaku ya sallame su, suka kuwa tafi cikin salama. A wannan rana bayin Ishaku suka zo suka faɗa masa game da rijiyar da suka haƙa. Suka ce, “Mun sami ruwa!” Sai ya kira ta Shiba, don haka har wa yau ana kira garin Beyersheba. Sa’ad da Yaƙub ya kai shekaru arba’in da haihuwa, sai ya auri Yudit ’yar Beyeri mutumin Hitti, da kuma Basemat ’yar Elon mutumin Hitti. Su ne suka zama sanadin baƙin ciki ga Ishaku da Rebeka. Sa’ad da Ishaku ya tsufa idanunsa suka raunana har ba ya iya gani, sai ya kira Isuwa babban ɗansa ya ce masa, “Ɗana.” Isuwa kuwa ya amsa, ya ce “Ga ni.” Ishaku ya ce, “Yanzu na tsufa kuma ban san ranar mutuwata ba. Saboda haka yanzu, ka ɗauki makamanka, kwari da bakanka, ka tafi jeji ka farauto mini nama. Ka shirya mini irin abinci mai daɗin da nake so, ka kawo mini in ci, domin in sa maka albarka kafin in mutu.” Ashe, Rebeka tana ji sa’ad da Ishaku ya yi wa ɗansa Isuwa magana. Da Isuwa ya tafi jeji don yă farauto nama yă kawo, sai Rebeka ta ce wa ɗanta Yaƙub, “Ka ji nan, na ji mahaifinka ya ce wa ɗan’uwanka Isuwa, ‘Kawo mini nama ka shirya mini abinci mai daɗi don in ci, in sa maka albarka a gaban Ubangiji kafin in mutu.’ Saboda haka ɗana, ka saurara da kyau ka kuma yi abin da na faɗa maka. Je garke ka kawo mini awaki biyu kyawawa, domin in shirya abinci mai daɗi wa mahaifinka, kamar yadda dai yake so. Sa’an nan ka kai wa mahaifinka yă ci, domin yă sa maka albarka kafin yă mutu.” Yaƙub ya ce wa mahaifiyarsa Rebeka, “Amma ɗan’uwana Isuwa mutum ne mai gashi a jiki, ni kuma jikina sumul yake. A ce baba ya tattaɓa ni fa? Zai zama kamar ina ruɗunsa ne, wannan fa zai jawo mini la’ana a maimakon albarka.” Mahaifiyarsa ta ce masa, “Ɗana, bari la’anar tă fāɗo a kaina. Kai dai yi abin da na faɗa, jeka ka kawo mini su.” Sai ya tafi ya kamo su, ya kawo wa mahaifiyarsa, ta kuwa shirya abinci mai daɗi, yadda mahaifinsa yake so. Sa’an nan Rebeka ta ɗauki riguna mafi kyau na Isuwa babban ɗanta, waɗanda take da su a gida ta sa wa ƙaramin ɗanta Yaƙub. Sai ta mamanne gashin awakin nan biyu a hannuwansa da bayan wuyarsa wanda ba gashi. Sa’an nan ta ba wa ɗanta Yaƙub abinci mai daɗi da kuma burodin da ta yi. Shi kuwa ya tafi wurin mahaifinsa ya ce, “Babana.” Shi kuma ya amsa “I, ɗana, wane ne?” Yaƙub ya ce wa mahaifinsa, “Ni ne Isuwa ɗan farinka. Na yi yadda ka faɗa mini. Ina roƙonka tashi ka zauna ka ci naman, domin ka sa mini albarkarka.” Ishaku ya tambayi ɗansa, “Yaya aka yi ka samo shi da sauri haka, ɗana?” Yaƙub ya amsa ya ce, “ Ubangiji Allahnka ne ya ba ni nasara.” Sai Ishaku ya ce wa Yaƙub, “Zo kusa don in taɓa ka, ɗana, domin in sani ko tabbatacce kai ne ɗana Isuwa ko babu.” Yaƙub kuwa ya matsa kusa da mahaifinsa Ishaku, wanda ya tattaɓa shi, sa’an nan ya ce, “Muryan nan dai, muryar Yaƙub ce, amma hannuwan, hannuwan Isuwa ne.” Bai gane shi ba, gama hannuwansa suna da gashi kamar na ɗan’uwansa Isuwa, saboda haka ya albarkace shi. Ya tambaya, “Tabbatacce kai ne ɗana Isuwa?” Ya amsa ya ce “Ni ne.” Sa’an nan ya ce, “Ɗana, kawo mini naman da ka farauto in ci, domin in sa maka albarka.” Yaƙub ya kawo masa ya kuwa ci; ya kuma kawo masa ruwan inabi ya kuma sha. Sa’an nan mahaifinsa Ishaku ya ce masa, “Zo nan, ɗana ka sumbace ni.” Saboda haka ya je gunsa ya sumbace shi. Sa’ad da Ishaku ya ji ƙanshin rigunansa, sai ya sa masa albarka ya ce, “Aha, ƙanshin ɗana yana kama da ƙanshin jejin da Ubangiji ya sa wa albarka ne. Allah yă ba ka daga raɓar sama da kuma yalwar ƙasa, yalwar hatsi da sabon ruwan inabi. Bari al’ummai su bauta maka mutane kuma su rusuna maka. Ka zama shugaba a kan ’yan’uwanka bari kuma ’ya’yan mahaifiyarka su rusuna maka. Bari waɗanda suka la’anta ka, su la’antu; waɗanda kuma suka sa maka albarka, su sami albarka.” Bayan Ishaku ya gama sa masa albarka, Yaƙub yana fita daga mahaifinsa ke nan, sai ga ɗan’uwansa Isuwa ya dawo daga farauta. Shi ma ya shirya abinci mai daɗi ya kawo wa mahaifinsa. Sa’an nan ya ce masa, “Babana, tashi ka zauna ka ci daga abin da na farauto, domin ka sa mini albarka.” Mahaifinsa Ishaku ya tambaye shi, “Wane ne kai?” Ya amsa, “Ni ne ɗanka, ɗan farinka, Isuwa.” Ishaku ya yi makyarkyata ƙwarai ya ce, “To, wane ne wannan da ya farauto nama ya kawo mini kafin ka zo, har na ci na kuma sa masa albarka? Tabbatacce zai zama mai albarka!” Sa’ad da Isuwa ya ji kalmomin mahaifinsa, sai ya fashe da kuka mai zafi kuma da ƙarfi, ya ce wa mahaifinsa, “Ka albarkace ni, ni ma, baba!” Amma ya ce, “Ɗan’uwanka ya zo da makirci ya karɓi albarkarka.” Isuwa ya ce, “Ba saboda haka ne aka raɗa masa suna Yaƙub ba? Ya yi mini ƙwace sau biyu ke nan; ya ƙwace mini matsayina na ɗan fari, ga shi yanzu kuma ya karɓi albarkata.” Sa’an nan ya yi tambaya, “Ba sauran albarkar da ka rage mini?” Ishaku ya amsa wa Isuwa, “Na mai da shi shugaba a kanka, na sa dukan dangoginsa su zama bayinsa, na kuma ba shi hatsi da sabon ruwan inabi. Saboda haka me kuma zan yi maka ɗana?” Isuwa ya ce wa mahaifinsa, “Iyakar albarkar da kake da ita ke nan, baba? Ka albarkace ni ni ma, baba!” Sai Isuwa ya ɗaga murya ya yi kuka. Mahaifinsa Ishaku ya amsa masa ya ce, “Ga shi, ni’imar ƙasar za tă nisanci mazauninka. Raɓar samaniya can ƙwanƙoli za tă nisance ka. Za ka rayu ta wurin takobi za ka kuwa bauta wa ɗan’uwanka. Amma sa’ad da ka ɓalle, za ka kakkarye karkiyarsa daga wuyanka.” Isuwa ya riƙe Yaƙub a zuciya saboda albarkar da mahaifinsa ya sa masa. Ya ce wa kansa, “Kwanakin mutuwar mahaifina sun yi kusa; sa’an nan zan kashe ɗan’uwana Yaƙub.” Sa’ad da aka faɗa wa Rebeka abin da babban ɗanta Isuwa ya faɗa, sai ta kira ɗanta Yaƙub ta ce masa, “Ɗan’uwanka Isuwa yana ta’azantar da kansa da tunanin kashe ka. To, fa, ɗana, yi abin da na ce; gudu nan take zuwa wurin ɗan’uwana Laban a Haran. Zauna tare da shi na ɗan lokaci sai ɗan’uwanka ya huce. Sa’ad da ɗan’uwanka ya daina fushi da kai, ya kuma manta da abin da ka yi masa, zan aika don ka dawo daga can. Don me zan rasa ku biyu a rana guda?” Sa’an nan Rebeka ta ce wa Ishaku, “Ni fa na gaji da matan Hittiyawan nan. In Yaƙub ya auri mata daga cikin matan ƙasan nan, wato, daga matan Hittiyawa irin waɗannan, rayuwata ba za tă daɗa mini kome ba.” Saboda haka Ishaku ya kira Yaƙub, ya kuma albarkace shi, sa’an nan ya umarce shi ya ce, “Kada ka auri mace daga Kan’ana. Tashi nan da nan ka tafi Faddan Aram, zuwa gidan mahaifin mahaifiyarka Betuwel. Ka ɗauko wa kanka mata a can daga cikin ’ya’ya matan Laban ɗan’uwan mahaifiyarka. Bari Allah Maɗaukaki yă albarkace ka, yă kuma sa ka yi ta haihuwa ka riɓaɓɓanya har ka zama ƙungiyar jama’o’i. Bari Allah yă ba ka da kuma zuriyarka albarkar da ya ba wa Ibrahim, don ka amshi ƙasar da kake baƙunci, ƙasar da Allah ya ba wa Ibrahim.” Sa’an nan Ishaku ya sallami Yaƙub, ya kuwa tafi Faddan Aram, zuwa wurin Laban ɗan Betuwel mutumin Aram. Laban ne ɗan’uwan Rebeka, wadda take mahaifiyar Yaƙub da Isuwa. Yanzu Isuwa ya san cewa Ishaku ya albarkaci Yaƙub ya kuma aike shi zuwa Faddan Aram don yă auri mata daga can, ya kuma san cewa sa’ad da ya albarkace shi, ya umarce shi cewa, “Kada ka auro wata mace daga cikin Kan’aniyawa,” ya kuma san cewa Yaƙub ya yi biyayya da mahaifinsa da kuma mahaifiyarsa, ya kuwa tafi Faddan Aram. Sai Isuwa ya gane cewa matan Kan’aniyawa ba su gamshi mahaifinsa Ishaku ba; saboda haka sai ya tafi wurin Ishmayel ya auri Mahalat, ’yar’uwar Nebayiwot da kuma ’yar Ishmayel ɗan Ibrahim, ban da matan da yake da su. Yaƙub ya bar Beyersheba ya kama hanyar Haran. Sa’ad da ya kai wani wuri, sai ya dakata domin yă kwana, gama rana ta riga ta fāɗi. Ya ɗauki dutse daga cikin duwatsun wurin, ya sa shi ya zama matashin kansa, sa’an nan ya kwanta don yă yi barci. Ya yi mafarki inda ya ga wata matakalar hawa, tsaye a ƙasa, kanta ta kai sama, mala’ikun Allah kuwa suna hawa, suna sauka a kanta. A can bisanta Ubangiji ya tsaya, ya kuma ce, “Ni ne Ubangiji Allah na mahaifinka Ibrahim da kuma Allah na Ishaku. Zan ba ka, kai da kuma zuriyarka, ƙasar da kake kwance a kai. Zuriyarka za tă zama kamar ƙurar ƙasa, za ka kuma bazu zuwa yamma da kuma gabas, zuwa arewa da kuma kudu. Dukan mutanen duniya za su sami albarka ta wurinka da kuma ta wurin ’ya’yanka. Ina tare da kai, zan lura da kai duk inda ka tafi, zan kuma dawo da kai zuwa wannan ƙasa. Ba zan rabu da kai ba sai na cika abin da na yi maka alkawari.” Sa’ad da Yaƙub ya farka daga barci, sai ya yi tunani ya ce, “Tabbatacce Ubangiji yana a wannan wuri, ban kuwa sani ba.” Ya ji tsoro, ya kuma ce, “Wane irin wuri ne mai banrazana haka! Lalle wannan gidan Allah ne, kuma nan ne ƙofar sama.” Kashegari da sassafe, sai Yaƙub ya ɗauki dutsen da ya yi matashin kai da shi, ya kafa shi al’amudi, ya kuma zuba mai a kansa. Ya kira wannan wuri Betel ko da yake dā ana kiran birnin Luz ne. Sa’an nan Yaƙub ya yi alkawari cewa, “In Allah zai kasance tare da ni yă kuma lura da ni a wannan tafiya, yă kuma ba ni abinci in ci da tufafi in sa, har in dawo lafiya zuwa gidan mahaifina, to, Ubangiji zai zama Allahna kuma wannan dutsen da na kafa al’amudi, zai zama gidan Allah, kuma dukan abin da ka ba ni zan ba ka kashi ɗaya bisa goma.” Sa’an nan Yaƙub ya ci gaba da tafiyarsa har ya kai ƙasar mutanen gabashi. A can ya ga rijiya a jeji da garkuna uku na tumaki kwance kusa da ita, gama a wannan rijiya ce ake shayar da garkuna. Dutsen da ake rufe bakin rijiyar mai girma ne. Sa’ad da dukan garkuna suka taru a can, sai makiyayan su gungurar da dutsen daga bakin rijiyar su shayar da tumaki. Sa’an nan su mai da dutsen a wurinsa a bakin rijiya. Yaƙub ya tambayi makiyayan ya ce, “’Yan’uwa, ina kuka fito?” Suka amsa, “Mu daga Haran ne.” Sai ya ce musu, “Kun san Laban, jikan Nahor?” Suka amsa, “I, mun san shi.” Sa’an nan Yaƙub ya tambaye su, “Yana nan lafiya?” Suka ce, “I, yana lafiya, ga ma ’yarsa Rahila tafe da tumaki.” Ya ce, “Duba har yanzu da sauran rana da yawa, lokaci bai kai na tara garkuna ba. Ku shayar da tumaki ku mai da su wurin kiwo.” Suka amsa suka ce, “Ba za mu iya ba, sai dukan garkunan sun taru, aka kuma gungurar da dutsen daga bakin rijiyar. Sa’an nan za mu shayar da tumakin.” Tun yana cikin magana da su, sai ga Rahila ta zo da tumakin mahaifinta, gama ita makiyayyiya ce. Sa’ad da Yaƙub ya ga Rahila ’yar Laban, ɗan’uwan mahaifiyarsa, da tumakin Laban, sai ya tafi ya gungurar da dutsen daga bakin rijiyar, ya kuma shayar da tumakin kawunsa. Sa’an nan Yaƙub ya sumbaci Rahila, ya kuma ɗaga murya ya yi kuka. Ya riga ya faɗa wa Rahila cewa shi dangin mahaifinta ne kuma ɗan Rebeka. Saboda haka ta ruga da gudu ta faɗa wa mahaifinta. Nan da nan, da Laban ya sami labari game da Yaƙub, ɗan ’yar’uwarsa, ya gaggauta yă sadu da shi. Sai ya rungume shi ya sumbace shi, ya kuma kawo shi gidansa, a can kuwa Yaƙub ya faɗa masa dukan waɗannan abubuwa. Sa’an nan Laban ya ce masa, “Kai nama da jinina ne.” Bayan Yaƙub ya zauna da shi na wata guda cif, sai Laban ya ce masa, “Don kawai kai dangina ne na kusa, sai kawai ka yi mini aiki a banza? Faɗa mini abin da albashinka zai zama.” Laban dai yana da ’ya’ya mata biyu; sunan babbar Liyatu, sunan ƙaramar kuwa Rahila. Liyatu tana da raunannun idanu, amma Rahila dai tsarinta yana da kyau kuma kyakkyawa ce. Yaƙub ya ƙaunaci Rahila, sai ya ce, “Zan yi maka aiki na shekaru bakwai domin ƙaramar ’yarka Rahila.” Laban ya ce, “Ya fi kyau in ba ka ita, da in ba wani mutum dabam. Zauna tare da ni.” Saboda haka Yaƙub ya yi bauta shekaru bakwai domin a ba shi Rahila, amma shekarun suka zama kamar ’yan kwanaki ne kawai gare shi saboda ƙaunar da yake mata. Sa’an nan Yaƙub ya ce wa Laban, “Ba ni matata. Lokacina ya cika, ina kuma so in kwana da ita.” Saboda haka Laban ya tara dukan mutanen wurin, ya yi biki. Amma da yamma ta yi, sai ya ɗauki ’yarsa Liyatu ya ba da ita ga Yaƙub, sai Yaƙub ya kwana da ita. Laban kuma ya ba da baranyarsa Zilfa wa ’yarsa tă zama mai hidimarta. Sa’ad da safiya ta yi, sai ga Liyatu! Saboda haka Yaƙub ya ce wa Laban, “Mene ne ke nan ka yi mini? Na yi maka bauta domin Rahila, ba haka na yi ba? Don me ka ruɗe ni?” Laban ya amsa, “Ba al’adarmu ba ce a nan a ba da ’ya ƙarama aure kafin ’yar fari. Ka gama makon amaryanci na ’yar nan; sa’an nan za mu ba ka ƙaramar ita ma, don ƙarin waɗansu shekaru bakwai na aiki.” Haka kuwa Yaƙub ya yi. Ya gama mako guda da Liyatu, sa’an nan Laban ya ba shi ’yarsa Rahila tă zama matarsa. Laban ya ba da baranyarsa Bilha wa ’yarsa Rahila ta zama mai hidimarta. Yaƙub ya kwana da Rahila ita ma, ya kuwa ƙaunaci Rahila fiye da Liyatu. Ya kuma yi wa Laban aiki na ƙarin waɗansu shekaru bakwai. Sa’ad da Ubangiji ya ga ba a ƙaunar Liyatu, sai ya buɗe mahaifarta, amma Rahila ta zama bakararriya. Sai Liyatu ta yi ciki ta haifi ɗa. Ta sa masa suna Ruben, gama ta ce, “Domin Ubangiji ya ga wahalata. Tabbatacce mijina zai ƙaunace ni yanzu.” Ta sāke yin ciki, sa’ad da kuma ta haifi ɗa sai ta ce, “Gama Ubangiji ya ji cewa ba a ƙaunata, ya ba ni wannan shi ma.” Saboda haka ta ba shi suna Simeyon. Har yanzu ta yi ciki, sa’ad da kuma ta haifi ɗa sai ta ce, “Yanzu, a ƙarshe mijina zai manne mini, gama na haifa masa ’ya’ya maza uku.” Saboda haka ta ba shi suna Lawi. Ta sāke yin ciki, sa’ad da ta haifi ɗa sai ta ce, “A wannan lokaci zan yabi Ubangiji.” Saboda haka ta ba shi suna Yahuda. Sa’an nan ta daina haihuwa. Sa’ad da Rahila ta ga cewa ba tă haifa wa Yaƙub ’ya’ya ba, sai ta fara kishin ’yar’uwarta. Saboda haka ta ce wa Yaƙub, “Ka ba ni ’ya’ya, ko kuwa in mutu!” Yaƙub ya fusata da ita ya ce, “Ina a matsayin Allah ne wanda ya hana ke samun ’ya’ya?” Sa’an nan ta ce, “Ga Bilha, mai baiwata, ka kwana da ita don tă haifa mini ’ya’ya, ta gare ta kuwa ni ma in gina iyali.” Saboda haka ta ba shi baranyarta Bilha tă zama matarsa. Yaƙub kuwa ya kwana da ita, ta kuwa yi ciki, ta kuma haifi ɗa. Sa’an nan Rahila ta ce, “Allah ya baratar da ni; ya saurari roƙona ya kuma ba ni ɗa.” Saboda wannan ta ba shi suna Dan. Baranyar Rahila ta sāke yin ciki ta kuma haifi wa Yaƙub ɗa na biyu. Sai Rahila ta ce, “Na yi kokawa sosai da ’yar’uwata, na kuwa yi nasara.” Saboda haka ta kira shi Naftali. Sa’ad da Liyatu ta ga cewa ta daina haihuwa, sai ta ɗauki mai hidimarta Zilfa ta ba da ita ga Yaƙub tă zama matarsa. Baranyar Liyatu, Zilfa ta haifa wa Yaƙub ɗa. Sai Liyatu ta ce, “Na yi sa’a!” Saboda haka ta ba shi suna Gad. Zilfa baranyar Liyatu ta haifa wa Yaƙub ɗa na biyu. Sai Liyatu ta ce, “Ni mai farin ciki ce! Mata za su ce da ni mai farin ciki.” Saboda haka ta sa masa suna Asher. A lokacin girbin alkama, sai Ruben ya je jeji ya ɗebo manta-uwa ya kawo wa mahaifiyarsa Liyatu. Sai Rahila ta ce wa Liyatu, “Ina roƙonki ki ɗan sam mini manta-uwa ɗanki.” Amma ta ce mata, “Bai ishe ki ba ne da kika ƙwace mijina? Yanzu kuma kina so ki ƙwace manta-uwa na yarona?” Sai Rahila ta ce “Shi ke nan, mijina zai iya kwana da ke yau saboda manta-uwa na ɗanki.” Saboda haka sa’ad da Yaƙub ya dawo daga jeji a wannan yamma sai Liyatu ta fito ta tarye shi. Ta ce, “Dole ka kwana da ni, na yi hayarka da manta-uwa na ɗana.” Saboda haka ya kwana da ita a wannan dare. Allah ya saurari Liyatu, ta kuwa yi ciki ta kuma haifa wa Yaƙub ɗa na biyar. Sai Liyatu ta ce, “Allah ya sāka mini saboda na ba da mai hidimata ga mijina.” Saboda haka ta ba shi suna Issakar. Liyatu ta sāke yin ciki ta kuma haifa wa Yaƙub ɗa na shida. Sai Liyatu ta ce, “Allah ya ba ni kyauta mai daraja. A wannan lokaci mijina zai darajarta ni, domin na haifa masa ’ya’ya maza shida.” Saboda haka ta ba shi suna Zebulun. Daga baya ta haifi ’ya ta kuwa ba ta suna Dina. Sai Allah ya tuna da Rahila; ya saurare ta ya kuma buɗe mahaifarta. Sai ta yi ciki ta kuma haifi ɗa ta ce, “Allah ya ɗauke mini kunyata.” Ta ba shi suna Yusuf, ta kuma ce, “Bari Ubangiji yă ƙara mini wani ɗa.” Bayan Rahila ta haifi Yusuf, sai Yaƙub ya ce wa Laban, “Ka sallame ni don in koma ƙasata. Ba ni matana da ’ya’yana, waɗanda na bauta maka dominsu, zan kuwa tafi. Ka dai san yadda na bauta maka.” Amma Laban ya ce masa, “In na sami tagomashi daga gare ka, ina roƙonka ka zauna. Na gane ta wurin duba cewa Ubangiji ya albarkace ni saboda kai.” Ya ƙara da cewa, “Faɗa albashinka, zan kuwa biya shi.” Yaƙub ya ce masa, “Ka dai san yadda na yi maka aiki da kuma yadda dabbobinka suka yi yawa a hannuna. Kaɗan da kake da shi kafin zuwata ya ƙaru sosai, kuma Ubangiji ya albarkace ka a duk inda na tafi. Amma yanzu, yaushe zan yi wani abu domin gidana ni ma?” Sai Laban ya yi tambaya, “Me zan ba ka?” Yaƙub ya amsa ya ce, “Kada ka ba ni wani abu. Amma in za ka yi mini abu guda ɗaya, zan ci gaba da kiwon garkunanka, ina kuma lura da su. Bari in ratsa cikin dukan garkunanka yau in fid da masu dabbare-dabbare da tumaki babare-babare, da kowane ɗan rago baƙi, da dabbare-dabbare da babare-babare na awaki daga ciki, waɗannan ne za su zama ladana. Gaskiyata kuwa za tă zama mini shaida nan gaba, duk sa’ad da ka bincika a kan albashin da ka biya ni. Duk akuyar da take tawa da ba dabbare-dabbare ko babare-babare, ko ɗan ragon da ba baƙi ba, zai kasance sata na yi.” Sai Laban ya ce, “Na yarda. Bari yă zama yadda ka faɗa.” A wannan rana ya ware dukan bunsurai da suke dabbare-dabbare da masu zāne-zāne, da dukan awakin da suke dabbare-dabbare (duka da suke da fari-fari a jikinsu), da dukan baƙaƙen tumaki, ya sa su a hannun ’ya’yansa maza. Sa’an nan ya sa nisan tafiya kwana uku tsakaninsa da Yaƙub, yayinda Yaƙub ya ci gaba da lura da sauran garkunan Laban Yaƙub. Yaƙub ya samo ɗanyen reshen itatuwan aduruku, da na katambiri, da na durumi, ya ɓare ya bar fararen cikin katakon rassan. Sa’an nan ya zuba ɓararre rassan cikin dukan kwamame na banruwa saboda su kasance a gaban garkunan sa’ad da suka zo shan ruwa. A sa’ad da garkunan suke barbara suka kuma zo shan ruwa, sai su yi barbara a gaban rassan. Sai kuwa su haifi ƙanana masu zāne dabbare-dabbare, ko babare-babare ko masu zāne-zāne. Sai Yaƙub yă ware ƙananan garken dabam, amma sai yă sa sauran su fuskanci dabbobin da suke dabbare-dabbare da kuma baƙaƙe da suke na Laban. Ta haka ya ware garkuna dabam domin kansa bai kuwa haɗa su da dabbobin Laban ba. A duk sa’ad da ƙarfafa dabbobi mata suke barbara, Yaƙub yakan zuba rassan a kwamame a gaban dabbobin saboda su yi barbara kusa da rassan, amma in dabbobin raunana ne, ba ya sa su a can. Saboda haka raunanan dabbobi suka zama na Laban, ƙarfafan kuma suka zama na Yaƙub. Ta haka mutumin ya zama riƙaƙƙe mai arziki, ya kasance mai manya-manyan garkuna, da bayi mata da maza, da raƙuma da kuma jakuna. Yaƙub ya ji cewa ’ya’ya Laban mazan suna cewa, “Yaƙub ya kwashe dukan abin da mahaifinmu yake da shi, ya kuma sami dukan wannan arziki daga abin da yake na mahaifinmu.” Yaƙub kuma ya lura cewa halin Laban gare shi ya canja ba kamar yadda yake a dā ba. Sai Ubangiji ya ce wa Yaƙub, “Koma ƙasar kakanninka da kuma danginka, zan kuwa kasance tare da kai.” Saboda haka Yaƙub ya aika a ce wa Rahila da Liyatu su zo jeji inda garkunan suke. Sai ya ce musu, “Na ga cewa halin mahaifinku gare ni ba kamar yadda dā yake ba, amma Allah na mahaifina yana tare da ni. Kun san cewa na yi aiki wa mahaifinku da dukan ƙarfina, duk da haka mahaifinku ya cuce ni ta wurin sauya albashina sau goma. Amma dai, Allah bai yardar masa yă yi mini lahani ba. In ya ce, ‘Dabbare-dabbare ne za su zama ladanka,’ sai dukan garkunan su haifi dabbare-dabbare, in kuma ya ce, ‘Masu zāne-zāne ne za su zama ladanka,’ sai dukan garkunan su haifi ƙananan masu zāne-zāne. Ta haka Allah ya kwashe dabbobin mahaifinku ya ba ni. “A lokacin ɗaukar cikin garken, na taɓa yin mafarki inda na ga bunsuran da suke barbara da garken, masu dabbare-dabbare, ko babare-babare, ko masu zāne-zāne ne. Sai mala’ikan Allah ya ce mini a mafarkin, ‘Yaƙub.’ Sai na amsa na ce, ‘Ga ni.’ Ya ce, ‘Ɗaga idanunka ka gani, dukan bunsuran da suke hawan garken, masu dabbare-dabbare, ko babare-babare, ko masu zāne-zāne ne, gama na ga dukan abin da Laban yake yin maka. Ni ne Allah na Betel, inda ka zuba wa al’amudi mai, da kuma inda ka yi mini alkawari. Yanzu ka bar wannan ƙasa nan take, ka koma ƙasarka ta ainihi.’ ” Sai Rahila da Liyatu suka amsa suka ce, “Muna da wani rabo a gādon kayan mahaifinmu ne? Ba kamar baƙi ne yake ɗaukarmu ba? Ba sayar da mu kaɗai ya yi ba, har ma ya yi amfani da abin da aka biya saboda mu. Tabbatacce dukan dukiyar da Allah ya kwashe daga mahaifinmu ya zama namu da ’ya’yanmu. Saboda haka ka yi duk abin da Allah ya faɗa maka.” Sa’an nan Yaƙub ya sa ’ya’yansa da matansa a kan raƙuma, ya kuma kora dukan dabbobinsa, suka ja gabansa, tare da dukan abubuwan da ya samu a Faddan Aram, don su tafi wurin mahaifinsa Ishaku a ƙasar Kan’ana. Sa’ad da Laban ya tafi don askin tumakinsa, sai Rahila ta sace gumakan gidan mahaifinta. Yaƙub kuwa ya ruɗe Laban mutumin Aram da bai sanar da shi zai gudu ba. Saboda haka ya gudu da dukan abin da ya mallaka, ya ƙetare Kogi, ya nufi yankin tuddan Gileyad. A rana ta uku, sai aka faɗa wa Laban cewa Yaƙub ya gudu. Sai Laban ya ɗauki danginsa tare da shi, ya bi bayan Yaƙub har kwana bakwai, ya kuma same shi a yankin tuddan Gileyad. Sai Allah ya bayyana ga Laban mutumin Aram a mafarki da dare, ya ce masa, “Ka yi hankali kada ka faɗa wa Yaƙub wani abu, ko mai kyau ko marar kyau.” Yaƙub ya riga ya kafa tentinsa a yankin tuddan Gileyad sa’ad da Laban ya same shi. Laban da danginsa suka kafa sansani a can su ma. Sai Laban ya ce wa Yaƙub, “Me ke nan ka yi? Ka ruɗe ni, ka kuma ɗauki ’ya’yana mata kamar kamammun yaƙi. Me ya sa ka gudu a ɓoye ka kuma ruɗe ni? Me ya sa ba ka faɗa mini don in sallame ka da farin ciki da waƙoƙi haɗe da kiɗin ganguna da garayu ba? Ba ka ma bari in sumbaci jikokina da ’ya’yana mata in yi musu bankwana ba. Ka yi wauta. Ina da iko in cuce ka; amma jiya da dare Allahn mahaifinka ya faɗa mini, ‘Ka yi hankali kada ka faɗa wa Yaƙub wani abu ko mai kyau ko marar kyau.’ Yanzu ka gudu domin kana marmari komawa gidan mahaifinka. Amma don me ka sace mini gumakana?” Yaƙub ya amsa wa Laban, “Na ji tsoro ne, domin na yi tsammani za ka ƙwace ’ya’yanka mata daga gare ni ƙarfi da yaji. Amma in ka sami wani wanda yake da gumakanka, ba zai rayu ba. Kai da kanka ka duba a gaban danginmu, ko akwai wani abin da yake naka a nan tare da ni; in ka gani, ka ɗauka.” Yaƙub dai bai san cewa Rahila ta sace gumakan ba. Saboda haka Laban ya shiga tentin Yaƙub, ya shiga tentin Liyatu da kuma tentuna matan nan biyu bayi, amma bai sami kome ba. Bayan ya fita daga tentin Liyatu, sai ya shiga tentin Rahila. Rahila fa ta kwashe gumakan gidan ta sa su cikin sirdin raƙumi, ta kuma zauna a kansu. Laban ya bincika cikin kowane abu a tentin amma bai sami kome ba. Sai Rahila ta ce wa mahaifinta, “Kada ka yi fushi, ranka yă daɗe da ban tashi tsaye a gabanka ba; gama ina al’adar mata ne.” Saboda haka ya bincika amma bai sami gumakan gidan ba. Yaƙub ya fusata, ya kuma yi wa Laban faɗa. Ya tambayi Laban, “Mene ne laifina? Wanda zunubi na yi da kake farautata? Yanzu da ka bincika dukan kayayyakina, me ka samu da yake na gidanka? Kawo shi nan a gaban danginka da kuma dangina, bari su zama alƙali tsakaninmu biyu. “Na kasance tare da kai shekaru ashirin. Tumakinka da awakinka ba su yi ɓarin ciki ba, ban kuwa ci raguna daga garkunanka ba. Ban kawo dabbobinka da namun jeji suka yayyaga; na kuma ɗauki hasarar ba? Ka nemi in biya dukan abin da aka sace da rana ko da dare. Yanayin da na kasance ke nan, da rana na sha zafin rana da dare kuma na sha sanyi, ga rashin barci. Haka ya kasance shekaru ashirin da na yi a gidanka. Na yi maka aiki shekaru goma sha huɗu domin ’ya’yanka mata biyu, na kuma yi shekaru shida domin garkunanka, ka kuma canja albashina sau goma. Da ba don Allah na mahaifina, Allah na Ibrahim da kuma Tsoron Ishaku ya kasance tare da ni ba, tabbatacce da ka sallame ni hannu wofi. Amma Allah ya ga wahalata da famar hannuwana, ya kuwa tsawata maka da dare jiya.” Laban ya amsa wa Yaƙub, “Matan, ’ya’yana ne, ’ya’yansu, ’ya’yana ne, garkunan kuma garkunana ne. Dukan abin da kake gani, nawa ne. Duk da haka me zan yi a rana ta yau ga waɗannan ’ya’yana mata, ko kuma ga ’ya’yan da suka haifa? Zo, bari mu ƙulla yarjejjeniya, da kai da ni, bari kuma ta kasance shaida a tsakaninmu.” Saboda haka Yaƙub ya ɗauki dutse ya kafa yă zama al’amudi. Ya ce wa danginsa. “Ku tattara waɗansu duwatsu.” Sai suka kwashe duwatsu suka tsiba, suka kuwa ci abinci a can kusa da tsibin. Laban ya sa masa suna Yegar Sahaduta, Yaƙub kuwa ya kira shi Galeyed. Laban ya ce, “Wannan tsibi, shi ne shaida tsakaninka da ni a yau.” Shi ya sa aka kira shi Galeyed. Aka kuma kira shi Mizfa, domin ya ce, “ Ubangiji yă sa ido tsakanin ni da kai sa’ad da muka rabu da juna. Laban ya ce in ka wulaƙanta ’ya’yana mata, ko ka auri waɗansu mata ban da ’ya’yana mata, ko da yake babu wani da yake tare da mu, ka tuna cewa Allah shi ne shaida tsakaninka da ni.” Laban ya kuma ce wa Yaƙub, “Ga wannan tsibi, ga kuma wannan al’amudin da na kafa tsakaninka da ni. Wannan tsibin shi ne shaida, wannan al’amudi kuma shaida ne, cewa ba zan tsallake wannan tsibi zuwa gefenka don in cuce ka ba, kai kuma ba za ka tsallake wannan tsibi da al’amudi zuwa gefena don ka cuce ni ba. Bari Allah na Ibrahim da Allah na Nahor, Allah na iyayensu, yă zama alƙali tsakaninmu.” Saboda haka Yaƙub ya yi rantsuwa da sunan Tsoron mahaifinsa Ishaku. Ya miƙa hadaya a can a ƙasar tudu, ya kuma gayyaci danginsa zuwa wurin cin abinci. Bayan suka ci, sai suka kwana a can. Da sassafe kashegari sai Laban ya sumbaci jikokinsa da ’ya’yansa mata, ya sa musu albarka. Sa’an nan ya yi bankwana da su, ya koma gida. Yaƙub shi ma ya kama hanyarsa, sai mala’ikun Allah suka sadu da shi. Sa’ad da Yaƙub ya gan su sai ya ce, “Wannan sansanin Allah ne!” Saboda haka ya kira wannan wuri Mahanayim. Sai Yaƙub ya aiki manzanni su sha gabansa zuwa wurin ɗan’uwansa Isuwa a ƙasar Seyir, a ƙauyen Edom. Ya umarce su, “Ga abin da za ku faɗa wa maigidana Isuwa, ‘Bawanka Yaƙub ya ce, na yi zama tare da Laban na kuwa kasance a can sai yanzu. Ina da shanu da jakuna, tumaki da awaki, bayi maza da mata. Yanzu ina aika da wannan saƙo zuwa ga ranka yă daɗe, don in sami tagomashi a idanunka.’ ” Sa’ad da manzannin suka komo wurin Yaƙub, suka ce, “Mun tafi wurin ɗan’uwanka Isuwa, yanzu kuwa yana zuwa ya sadu da kai, da kuma mutum ɗari huɗu tare da shi.” Da tsoro mai yawa da kuma damuwa, Yaƙub ya rarraba mutanen da suke tare da shi ƙungiyoyi biyu, haka ma garkunan tumaki da awaki, da garkunan shanu da raƙuma. Ya yi tunani, “In Isuwa ya zo ya fāɗa wa ƙungiya ɗaya, sai ƙungiya ɗayan da ta ragu ta tsira.” Sa’an nan Yaƙub ya yi addu’a, “Ya Allah na mahaifina Ibrahim, Allah na mahaifina Ishaku. Ya Ubangiji kai da ka ce mini, ‘Koma ƙasarka zuwa wurin danginka, zan kuma sa ka yi albarka.’ Ban cancanci dukan alheri da amincin da ka nuna wa bawanka ba. Da sanda kaɗai nake sa’ad da na ƙetare wannan Urdun, amma ga shi yanzu na zama ƙungiyoyi biyu. Ka cece ni, ina roƙonka daga hannun ɗan’uwana Isuwa, gama ina tsoro zai zo yă fāɗa mini, yă karkashe mu duka, ’ya’ya da iyaye. Amma ka riga ka faɗa, ‘Tabbatacce zan sa ka yi albarka. Zan kuma sa zuriyarka su zama kamar yashin teku da ba a iya ƙirgawa.’ ” Ya kwana a can, daga cikin abin da yake tare da shi kuwa, ya zaɓi kyauta domin ɗan’uwansa Isuwa, awaki ɗari biyu da bunsurai ashirin, tumaki ɗari biyu da raguna ashirin, raƙuma mata talatin tare da ƙananansu, shanu arba’in da bijimai goma, jakuna mata ashirin da kuma jakuna maza goma. Ya sa su a ƙarƙashin kulawar bayinsa, kowane kashin garke ya kasance a ware. Ya ce wa bayinsa, “Ku sha gabana, ku kuma ba da rata tsakanin garke da garke.” Ya umarci wanda yake jagorar ya ce, “Sa’ad da ɗan’uwana Isuwa ya sadu da ku ya kuma yi tambaya, ‘Ku na wane ne, ina za ku, kuma wane ne mai dukan dabbobin nan da suke gabanku?’ Sai ku ce, ‘Na bawanka Yaƙub ne. Kyauta ce wa maigidana Isuwa, yana kuma tafe a bayanmu.’ ” Yaƙub ya kuma umarci na biyu da na uku da kuma dukan waɗansu da suka bi garkunan, “Sai ku faɗa irin abu guda ga Isuwa sa’ad da kuka sadu da shi. Ku kuma tabbata kun ce, ‘Bawanka Yaƙub yana tafe a bayanmu.’ ” Gama Yaƙub ya yi tunani cewa, “Zan kwantar da ran Isuwa da waɗannan kyautai, kafin mu sadu fuska da fuska, wataƙila yă karɓe shi.” Saboda haka kyautai Yaƙub suka sha gabansa, amma shi kansa ya kwana a sansani. A wannan dare Yaƙub ya tashi ya ɗauki matansa biyu, da matan nan biyu masu hidima da ’ya’yansa goma sha ɗaya ya haye rafin Yabbok. Bayan ya sa suka haye rafin, haka ma ya tura dukan mallakarsa zuwa hayen. Saboda haka sai aka bar Yaƙub shi kaɗai. Sai ga wani mutum ya zo ya yi kokawa da shi har wayewar gari. Da mutumin ya ga cewa bai fi ƙarfin Yaƙub ba, sai ya bugi kwarin ƙashin cinyar Yaƙub, sai gaɓar ƙashin cinyarsa ya goce, a sa’ad da yake kokawa da mutumin. Sa’an nan mutumin ya ce, “Bar ni in tafi, gama gari ya waye.” Amma Yaƙub ya amsa ya ce, “Ba zan bar ka ka tafi ba, sai ka sa mini albarka.” Mutumin ya tambaye shi ya ce, “Mene ne sunanka?” Yaƙub ya amsa ya ce, “Yaƙub.” Sai mutumin ya ce, “Sunanka ba zai ƙara zama Yaƙub ba, amma Isra’ila, gama ka yi kokawa da Allah da mutane, ka kuwa yi rinjaye.” Yaƙub ya ce, “Ina roƙonka, faɗa mini sunanka.” Amma mutumin ya amsa ya ce, “Me ya sa kake tambayata sunana?” Sa’an nan ya albarkace shi. Saboda haka Yaƙub ya kira wurin Feniyel, yana cewa, “Domin na ga Allah fuska da fuska, duk da haka aka bar ni da rai.” Rana ta yi sama a sa’ad da ya wuce Fenuwel yana kuma ɗingishi saboda ƙashin cinyarsa. Wannan ya sa har wa yau Isra’ilawa ba sa cin jijiyar ƙashin cinya wadda take a kwarin ƙashin cinya, domin an taɓa kwarin ƙashin cinyar Yaƙub kusa da jijiyar. Yaƙub ya ɗaga ido ke nan, sai ga Isuwa yana zuwa tare da mutanensa ɗari huɗu; saboda haka sai ya rarraba ’ya’yan wa Liyatu, Rahila da kuma matan nan biyu masu hidima. Ya sa matan nan biyu masu hidima da ’ya’yansu a gaba, Liyatu da ’ya’yanta biye, sa’an nan Rahila da Yusuf a baya. Shi kansa ya sha gabansu, ya rusuna har ƙasa sau bakwai, kafin ya kai kusa da inda ɗan’uwansa Isuwa yake. Amma Isuwa ya ruga a guje ya sadu da Yaƙub ya rungume shi; ya faɗa a wuyansa ya sumbace shi. Suka kuma yi kuka. Sa’an nan Isuwa ya ɗaga ido ya ga mata da ’ya’ya. Ya yi tambaya, “Su wane ne waɗannan tare da kai?” Yaƙub ya amsa, “Su ne ’ya’yan da Allah cikin alheri ya ba bawanka.” Sai matan nan biyu masu hidima da ’ya’yansu suka matso kusa suka durƙusa. Biye da su, Liyatu da ’ya’yanta suka zo suka rusuna. A ƙarshe duka, sai Yusuf da Rahila suka zo, su ma suka rusuna. Isuwa ya yi tambaya, “Me kake nufi da dukan abubuwan nan da na sadu da su ana korarsu?” Sai Yaƙub ya ce, “Don in sami tagomashi a idanunka ne, ranka yă daɗe.” Amma Isuwa ya ce, “Na riga na sami abin da ya ishe ni, ɗan’uwana. Riƙe abin da kake da shi don kanka.” Sai Yaƙub ya ce, “A’a, ina roƙonka, in na sami tagomashi a idanunka, sai ka karɓi wannan kyautai daga gare ni. Gama ganin fuskarka kamar ganin fuskar Allah ne, yanzu da ka karɓe ni da farin ciki. Ina roƙonka ka karɓi kyautar da aka kawo maka, gama Allah ya yi mini alheri kuma ina da kome da nake bukata.” Ganin yadda Yaƙub ya nace, sai Isuwa ya karɓa. Sa’an nan Isuwa ya ce, “Bari mu tafi, zan yi maka rakiya.” Amma Yaƙub ya ce masa, “Ranka yă daɗe, ka san cewa ’ya’yan ƙanana ne, dole in lura da tumaki da shanun da suke shayar da jariransu. In aka kore su da gaggawa a rana guda kaɗai, dukan dabbobin za su mutu. Saboda haka bari ranka yă daɗe yă sha gaban bawansa, ni kuma in tafi a hankali bisa ga saurin abin da ake kora a gabana da kuma saurin ’ya’yan, sai na iso wurinka ranka yă daɗe, a Seyir.” Sai Isuwa ya ce, “To, bari in bar waɗansu mutanena tare da kai.” Yaƙub ya ce, “Amma me ya sa za ka yi haka? Bari dai in sami tagomashi a idanunka ranka yă daɗe.” Saboda haka a wannan rana Isuwa ya kama hanyar komawa zuwa Seyir. Yaƙub kuwa, ya tafi Sukkot, inda ya gina wuri domin kansa, ya kuma yi bukkoki domin dabbobinsa. Shi ya sa aka kira wurin Sukkot. Bayan Yaƙub ya zo daga Faddan Aram, ya iso lafiya a birnin Shekem a Kan’ana, ya kuma kafa sansani a ƙofar birni. Ya sayi fili daga ’ya’yan Hamor maza, mahaifin Shekem inda ya kafa tentinsa, a bakin azurfa ɗari. A can ya kafa bagade ya kuma kira shi El Elohe Isra’ila. To, Dina, ’yar da Liyatu ta haifa wa Yaƙub, ta je ta ziyarci matan ƙasar. Sa’ad da Shekem ɗan Hamor Bahiwiye mai mulkin wurin ya gan ta, sai ya kama ta, ya kwana da ita, ya ɓata ta. Zuciyarsa kuwa ta damu da son Dina ’yar Yaƙub, ya kuwa ƙaunaci yarinyar, ya yi mata magana a hankali. Sai Shekem ya ce wa mahaifinsa Hamor, “Ka auro mini wannan yarinya ta zama matata.” Sa’ad da Yaƙub ya ji cewa an ɓata ’yarsa Dina, sai ya yi shiru game da batun sai ’ya’yansa maza sun dawo gida, gama ’ya’yansa suna a jeji tare da dabbobinsa suna kiwo. Sai Hamor mahaifin Shekem ya je don yă yi magana da Yaƙub. Da ’ya’yan Yaƙub maza suka dawo daga jeji sai suka ji labarin. Abin kuwa ya zafe su ƙwarai, don Shekem ya jawo abin kunya wa jama’ar Isra’ila ta wurin kwana da ’yar Yaƙub, don bai kamata wannan abu yă faru ba. Amma Hamor ya ce musu, “Ɗana Shekem ya sa zuciyarsa a kan ’yarku. Ina roƙonku ku ba shi ita yă aura. Ku yi auratayya da mu; ku aurar mana da ’ya’yanku mata, ku kuma ku auro ’ya’yanmu mata wa kanku. Za ku iya zauna a cikinmu, ƙasar tana nan a buɗe dominku. Ku yi zama a cikinta, ku yi sana’a, ku kuma sami dukiya.” Sai Shekem ya ce wa mahaifin Dina da kuma ’yan’uwanta. “Bari in sami tagomashi a idanunku, zan kuwa ba ku duk abin da kuka tambaya. Ku faɗa mini nawa ne dukiyar aure da kuma sadakin da zan kawo bisa ga yadda kuke so, zan kuwa biya duk abin da kuka ce. Ku dai bar ni in aure yarinyar ta zama matata.” Domin an ɓata ’yar’uwansu Dina, sai ’ya’yan Yaƙub maza suka amsa a ha’ince yayinda suke wa Shekem da mahaifinsa Hamor magana. Suka ce musu, “Ba za mu iya yin wannan abu ba, ba za mu iya ba da ’yar’uwarmu ga mutumin da ba shi da kaciya ba. Wannan zai zama abin kunya ne a gare mu. Za mu yarda da wannan kaɗai ta wannan sharaɗi, cewa za ku zama kamar mu ta wurin yin wa dukan ’ya’yanku maza kaciya. Sa’an nan za mu ba da ’ya’yanmu mata aure gare ku, mu kuma mu aure ’ya’yanku mata wa kanmu. Za mu zauna a cikinku mu kuma zama mutane ɗaya da ku. Amma in ba za ku yarda a yi muku kaciya ba, za mu ɗauki ’yar’uwanmu mu tafi.” Sharuɗansu sun gamshi Hamor da ɗansa, Shekem. Saurayin wanda aka fi girmamawa a cikin dukan gidan mahaifinsa, bai ɓata lokaci a yin abin da suka ce ba, domin ya ji daɗin ’yar Yaƙub. Saboda haka Hamor da ɗansa Shekem suka tafi ƙofar birninsu don su yi magana da mutanen garinsu. Suka ce, “Waɗannan mutane ba su da damuwa, bari su zauna a cikin ƙasarmu, su kuma yi sana’a a ciki; ƙasar tana da isashen fili dominsu. Za mu iya auro ’ya’yansu mata, su kuma su auri namu. Amma mutanen za su yarda su zauna tare da mu kamar mutane ɗaya kawai bisa wannan sharaɗi, cewa a yi wa mazanmu kaciya, kamar yadda su kansu suke. Ashe, shanunsu, dukiyarsu da dukan sauran dabbobinsu, ba za su zama namu ba? Saboda haka mu yarda, za su kuwa zauna a cikinmu.” Dukan mazan da suka fito ƙofar birnin suka yarda da Hamor da kuma ɗansa Shekem, aka kuwa yi wa kowane namiji a birnin kaciya. Bayan kwana uku, yayinda dukansu suna cikin zafi mikin kaciya, sai biyu daga cikin ’ya’yan Yaƙub maza, Simeyon da Lawi, ’yan’uwan Dina, suka ɗauki takubansu suka fāɗa wa birnin ba labari, suka kashe kowane namiji. Suka kashe Hamor da ɗansa Shekem da takobi, suka ɗauko Dina daga gidan Shekem suka tafi. Sa’an nan ’ya’yan Yaƙub maza suka bi kan gawawwakin, suka washe arzikin birni saboda an ɓata ’yar’uwarsu. Suka kwashe garkunansu na shanu da jakuna, da kuma kome na mutanen a birnin da kuma cikin gonaki. Suka kwashe dukan dukiyarsu da dukan matansu da ’ya’yansu, suka kwashe kome da yake cikin gidaje. Sai Yaƙub ya ce wa Simeyon da Lawi, “Kun jawo mini wahala ta wurin sa in zama abin ƙi ga Kan’aniyawa da Ferizziyawa, mazaunan wannan ƙasa. Mu kima ne, in kuwa suka haɗa kai gāba da ni, suka fāɗa mini, za su hallaka ni da gidana.” Amma ’ya’yansa suka amsa, “To, ya dace ke nan da ya yi da ’yar’uwarmu kamar karuwa?” Sa’an nan Allah ya ce wa Yaƙub, “Haura zuwa Betel ka yi zama a can, ka kuma gina bagade a can wa Allah wanda ya bayyana gare ka sa’ad da kake gudu daga ɗan’uwanka Isuwa.” Saboda haka Yaƙub ya ce wa gidansa da kuma dukan waɗanda suke tare da shi, “Ku zubar da baƙin allolin da kuke da su, ku tsarkake kanku, ku kuma canja tufafinku. Sa’an nan ku zo, mu haura zuwa Betel, inda zan gina bagade wa Allah wanda ya amsa mini a ranar wahalata, wanda kuma ya kasance tare da ni a dukan inda na tafi.” Saboda haka suka ba Yaƙub dukan baƙin allolin da suke da su, da zoban da suke kunnuwansu, sai Yaƙub ya binne su a ƙarƙashin itacen oak a Shekem. Sa’an nan suka kama hanya, tsoron Allah kuwa ya kama dukan garuruwan da suke kewayensu har babu wanda ya iya bin su. Yaƙub da dukan mutanen da suke tare da shi suka zo Luz (wato, Betel) a ƙasar Kan’ana. A can ya gina bagade, ya kuma kira wurin El Betel, gama a can ne Allah ya bayyana kansa gare shi sa’ad da yake gudu daga ɗan’uwansa. To, Debora, ungozomar Rebeka ta rasu aka kuma binne ta a ƙarƙashin itacen oak, ƙasa da Betel. Saboda haka aka kira wurin Allon Bakut. Bayan Yaƙub ya komo daga Faddan Aram, sai Allah ya bayyana gare shi, ya kuma albarkace shi. Allah ya ce masa, “Sunanka Yaƙub ne, amma ba za a ƙara kira ka Yaƙub ba; sunanka zai zama Isra’ila.” Saboda haka ya ba shi suna Isra’ila. Sai Allah ya ce masa, “Ni ne Allah Maɗaukaki, ka yi ta haihuwa, ka kuma riɓaɓɓanya. Al’umma da tarin al’ummai za su fito daga gare ka, sarakuna kuma za su fito daga jikinka. Ƙasar da na ba wa Ibrahim da Ishaku, zan kuma ba ka, zan kuma ba da wannan ƙasa ga zuriyarka a bayanka.” Sa’an nan Allah ya tashi sama daga gare shi a wurin da ya yi magana da shi. Yaƙub kuwa ya kafa al’amudin dutse a inda Allah ya yi magana da shi, ya zuba hadaya ta sha a kansa; ya kuma zuba mai a kansa. Yaƙub ya kira inda Allah ya yi magana da shi, Betel. Sa’an nan suka tashi daga Betel. Yayinda suna da ɗan nisa da Efrat, sai Rahila ta fara naƙuda ta kuwa sha wahala sosai. Sa’ad da take cikin zafin haihuwa, sai macen da ta karɓi haihuwar ta ce mata, “Kada ki ji tsoro, gama yanzu kin sami wani ɗa.” Yayinda take jan numfashinta na ƙarshe, sai ta ba wa ɗanta suna Ben-Oni. Amma mahaifinsa ya kira shi Benyamin. Ta haka Rahila ta rasu, aka kuma binne ta a hanya zuwa Efrata (wato, Betlehem). Yaƙub ya kafa al’amudi bisa kabarinta, al’amudin kabarin Rahila ke nan, wanda yake can har wa yau. Isra’ila ya yi gaba, ya kafa tentinsa gaba da Migdal Eder. Yayinda Isra’ila yana zama a wancan yanki, Ruben ya shiga ya kwana da Bilha ƙwarƙwarar mahaifinsa, Isra’ila kuwa ya ji labari. Yaƙub ya haifi ’ya’ya maza goma sha biyu. ’Ya’yan Liyatu maza, Ruben shi ne ɗan fari na Yaƙub. Sauran su ne, Simeyon, Lawi, Yahuda, Issakar da Zebulun. ’Ya’yan Rahila maza su ne, Yusuf da Benyamin. ’Ya’yan Bilha maza, mai hidimar Rahila su ne, Dan da Naftali. ’Ya’yan Zilfa maza, mai hidimar Liyatu su ne, Gad da Asher. Waɗannan su ne ’ya’yan Yaƙub maza, waɗanda aka haifa masa a Faddan Aram. Yaƙub ya dawo gida wurin mahaifinsa Ishaku a Mamre, kusa da Kiriyat Arba (wato, Hebron), inda Ibrahim da Ishaku suka zauna. Ishaku ya rayu shekaru ɗari da tamanin, sa’an nan ya ja numfashinsa na ƙarshe, ya kuwa mutu, aka kuma tara shi ga mutanensa da kyakkyawan tsufa da kuma cikakken shekaru. ’Ya’yansa maza, Isuwa da Yaƙub suka binne shi. Waɗannan su ne zuriyar Isuwa (wato, Edom). Isuwa ya ɗauko matansa daga cikin matan Kan’ana, ya ɗauko Ada ’yar Elon mutumin Hitti, da Oholibama ’yar Ana wadda take jikanyar Zibeyon Bahiwiye ya kuma auri Basemat ’yar Ishmayel wadda take ’yar’uwar Nebayiwot. Ada ta haifi wa Isuwa, Elifaz. Basemat kuma ta haifa masa Reyuwel. Oholibama kuwa ta haifa masa Yewush, Yalam da Kora. Waɗannan su ne ’ya’yan Isuwa maza, waɗanda aka haifa masa a Kan’ana. Isuwa ya ɗauki matansa da ’ya’yansa maza da mata da kuma dukan membobin gidansa, ya kuma ɗauki shanunsa da dukan sauran dabbobinsa, da dukan dukiyarsa da ya samu a ƙasar Kan’ana zuwa wata ƙasa nesa da ɗan’uwansa Yaƙub. Mallakarsu ta yi yawa ƙwarai da ba za su iya zauna tare ba; gama ƙasar da suke zaune a ciki ba za tă ishe su su biyu ba saboda dabbobinsu. Saboda haka Isuwa (wato, Edom) ya zauna a ƙasar tuddai na Seyir. Wannan shi ne zuriyar Isuwa, kakan mutanen Edom, a ƙasar tuddai na Seyir. Waɗannan su ne sunayen ’ya’yan Isuwa maza, Elifaz, ɗan Ada matar Isuwa, da Reyuwel ɗan Basemat matar Isuwa. ’Ya’yan Elifaz maza su ne, Teman, Omar, Zefo, Gatam da Kenaz. Elifaz ɗan Isuwa kuma yana da ƙwarƙwara mai suna Timna, wadda ta haifa masa Amalek. Waɗannan su ne jikokin Ada matar Isuwa. ’Ya’yan Reyuwel maza su ne, Nahat, Zera, Shamma da Mizza. Waɗannan su ne jikokin Basemat matar Isuwa. ’Ya’yan Oholibama maza ’yar Ana wadda take jikanyar Zibeyon, matar Isuwa, waɗanda ta haifa wa Isuwa su ne, Yewush, Yalam da Kora. Waɗannan su ne manya a cikin zuriyar Isuwa, ’Ya’ya Elifaz maza ɗan farin Isuwa, Shugabannin su ne; Teman, Omar, Zefo, Kenaz, Kora, Gatam da kuma Amalek. Waɗannan ne manya da suka fito daga dangin Elifaz a Edom; su ne jikokin Ada. ’Ya’yan Reyuwel maza, Shugabannin su ne; Nahat, Zera, Shamma da Mizza. Waɗannan su ne manya da suka fito daga dangin Reyuwel a Edom; su ne jikokin Basemat matar Isuwa. ’Ya’yan Oholibama maza matar Isuwa, Shugabannin su ne; Yewush, Yalam da Kora. Waɗannan su ne manya da suka fito daga dangin Oholibama ’yar Ana matar Isuwa. Waɗannan su ne ’ya’yan Isuwa maza (wato, Edom), waɗannan ne manyansu. Waɗannan su ne ’ya’yan Seyir Bahore maza, waɗanda suke zaune a yankin, Lotan, Shobal, Zibeyon, Ana, Dishon, Ezer da Dishan. Waɗannan su ne manyan Horiyawa, ’ya’yan Seyir, maza, a ƙasar Edom. ’Ya’yan Lotan maza su ne, Hori da Homam. Timna ’yar’uwar Lotan ce. ’Ya’yan Shobal maza su ne, Alwan, Manahat, Ebal, Shefo da Onam. ’Ya’yan Zibeyon maza su ne, Aiya da Ana. Wannan shi ne Ana wanda ya sami maɓulɓulan ruwan zafi a hamada yayinda yake kiwon jakuna na mahaifinsa Zibeyon. ’Ya’yan Ana su ne, Dishon da Oholibama ’yar Ana. ’Ya’yan Dishon maza su ne, Hemdan, Eshban, Itran da Keran. ’Ya’yan Ezer maza su ne, Bilhan, Za’aban da Akan. ’Ya’yan Dishan maza su ne, Uz da Aran. Waɗannan su ne manyan Horiyawa, Lotan, Shobal, Zibeyon, Ana, Dishon, Ezer da Dishan. Waɗannan su ne manyan Horiyawa, bisa ga ɓangarorinsu, a ƙasar Seyir. Waɗannan su ne sarakunan da suka yi mulki a Edom kafin wani sarki mutumin Isra’ila yă yi mulki, Bela ɗan Beyor ya zama sarkin Edom. Sunan birninsa shi ne Dinhaba. Sa’ad da Bela ya rasu, Yobab ɗan Zera daga Bozra ya gāje shi. Sa’ad da Yobab ya rasu, Husham daga ƙasar Temaniyawa ya gāje shi. Sa’ad da Husham ya rasu, Hadad ɗan Bedad, wanda ya ci Midiyan da yaƙi a ƙasar Mowab, ya gāje shi. Sunan birninsa shi ne Awit. Sa’ad da Hadad ya rasu, Samla daga Masreka ya gāje shi. Sa’ad da Samla ya rasu, Sha’ul daga Rehobot na ta kogi ya gāje shi. Sa’ad da Sha’ul ya rasu, Ba’al-Hanan ɗan Akbor ya gāje shi. Sa’ad da Ba’al-Hanan ɗan Akbor ya rasu, Hadad ya gāje shi. Sunan birninsa shi ne Fau, kuma sunan matarsa Mehetabel ce ’yar Matired, jikanyar Me-Zahab. Waɗannan su ne manya da suka fito daga zuriyar Isuwa, bisa ga danginsu, bisa kuma ga kabilansu da yankunansu. Sunayensu su ne, Timna, Alwa, Yetet. Oholibama, Ela, Finon. Kenaz, Teman, Mibzar. Magdiyel da Iram. Waɗannan su ne manyan Edom bisa ga mazauninsu cikin ƙasar da suka zauna. Wannan shi ne zuriyar Isuwa, kakan mutanen Edom. Yaƙub ya zauna a ƙasar da mahaifinsa ya zauna, wato, ƙasar Kan’ana. Wannan shi ne labarin zuriyar Yaƙub. Yusuf, saurayi ne mai shekara goma sha bakwai. Shi da ’yan’uwansa, wato, ’ya’yan Bilha maza da kuma ’ya’yan Zilfa maza, matan mahaifinsa suna kiwon garkuna tare. Sai Yusuf ya kawo wa mahaifinsu rahoto marar kyau game da ’yan’uwansa. Isra’ila dai ya fi ƙaunar Yusuf fiye da kowanne a cikin sauran ’ya’yansa maza, gama an haifa masa shi a cikin tsufansa. Sai ya yi masa riga mai gwanin kyau. Sa’ad da ’yan’uwansa suka ga cewa mahaifinsu ya fi ƙaunarsa fiye da kowanne daga cikinsu, sai suka ƙi jininsa, ba sa kuma maganar alheri da shi. Sai Yusuf ya yi mafarki, sa’ad da ya faɗa wa ’yan’uwansa, suka ƙara ƙin jininsa. Ya ce musu, “Ku saurari wannan mafarkin da na yi. Muna daurin dammunan hatsi a gona, sai nan da nan damina ya tashi ya tsaya, yayinda dammunanku suka taru kewaye da nawa suka rusuna masa.” Sai ’yan’uwansa suka ce masa, “Kana nufin za ka yi mulki a kanmu ke nan? Ko kuwa za ka zama sarki, a bisanmu?” Suka ƙara ƙin jininsa saboda mafarkinsa da kuma abin da ya faɗa. Sai Yusuf ya sāke yin wani mafarki, ya faɗa wa ’yan’uwansa. Ya ce, “Ku saurara, na sāke yin wani mafarki, a wannan lokaci, na ga rana da wata da taurari goma sha ɗaya suna rusuna mini.” Sa’ad da ya faɗa wa mahaifinsa da kuma ’yan’uwansa, sai mahaifinsa ya kwaɓe shi ya ce, “Wanne irin mafarki ne haka da ka yi? Kana nufin ni da mahaifiyarka da ’yan’uwanka za mu zo gabanka mu rusuna maka?” ’Yan’uwansa suka yi kishinsa, amma mahaifinsa ya riƙe batun nan a zuciya. To, ’yan’uwansa suka tafi kiwon garkunan mahaifinsu kusa da Shekem. Sai Isra’ila ya ce wa Yusuf, “Kamar yadda ka sani, ’yan’uwanka suna kiwon garkuna kusa da Shekem. Zo, in aike ka gare su.” Ya ce, “To.” Saboda haka Isra’ila ya ce wa Yusuf, “Jeka ka ga ko kome lafiya yake da ’yan’uwanka da kuma garkunan, ka kawo mini labari.” Sa’an nan ya sallame shi daga Kwarin Hebron. Sa’ad da Yusuf ya kai Shekem, sai wani mutum ya same shi yana yawo a cikin jeji, sai mutumin ya tambaye shi ya ce, “Me kake nema?” Yusuf ya amsa ya ce, “Ina neman ’yan’uwana ne. Za ka iya faɗa mini inda suke kiwon garkunansu?” Mutumin ya amsa, “Sun yi gaba daga nan. Na ji su suna cewa, ‘Bari mu je Dotan.’ ” Saboda haka Yusuf ya bi bayan ’yan’uwansa, ya kuwa same su kusa da Dotan. Amma da suka gan shi daga nesa, kafin yă kai wurinsu, sai suka ƙulla su kashe shi. Suka ce wa juna, “Ga mai mafarkin nan can zuwa! Ku zo mu kashe shi mu kuma jefa shi a ɗaya daga cikin rijiyoyin nan, mu ce mugun naman jeji ya cinye shi. Mu ga yadda mafarkinsa zai cika.” Sa’ad da Ruben ya ji wannan, sai ya yi ƙoƙari yă cece shi daga hannuwansu. Ya ce, “Kada mu ɗauki ransa. Kada mu zub da wani jini. Mu dai jefa shi cikin wannan rijiya a nan cikin hamada, amma kada mu sa hannu a kansa.” Ruben ya faɗa wannan ne don yă cece shi daga gare su, yă kuma mai da shi ga mahaifinsa. Saboda haka sa’ad da Yusuf ya zo wurin ’yan’uwansa, sai suka tuɓe masa rigarsa, rigan nan mai gwanin kyau da ya sa, suka kuma ɗauke shi suka jefa a cikin rijiya. To, rijiyar wofi ce, babu ruwa a ciki. Da suka zauna don cin abinci, sai suka tā da idanu, suka ga ayarin mutanen Ishmayel suna zuwa daga Gileyad. An yi wa raƙumansu labtu da kayan yaji da na ƙanshi, suna kan hanyarsu za su Masar. Yahuda ya ce wa ’yan’uwansa, “Me zai amfane mu in muka kashe ɗan’uwanmu muka ɓoye jininsa? Ku zo, mu sayar da shi wa mutanen Ishmayelawan nan, kada mu sa hannuwanmu a kansa; ban da haka ma, shi ɗan’uwanmu ne, jiki da jininmu.” Sai ’yan’uwansa suka yarda. Saboda haka sa’ad da Fataken Midiyawa suka iso, sai ’yan’uwansa suka ja Yusuf daga rijiyar, suka sayar da shi a bakin shekel ashirin na azurfa wa mutanen Ishmayel, waɗanda suka ɗauke shi zuwa Masar. Sa’ad da Ruben ya dawo wurin rijiyar, sai ya tarar cewa Yusuf ba ya can, sai ya kyakkece tufafinsa. Ya koma wurin ’yan’uwansa ya ce, “Yaron ba ya can! Ina zan bi yanzu?” Sai suka ɗauki rigar Yusuf, suka yanka akuya suka tsoma rigar a cikin jinin. Suka ɗauki rigan nan mai gwanin kyau, suka kawo wa mahaifinsu suka ce, “Mun sami wannan. Ka bincika shi ka gani ko rigar ɗanka ne.” Ya gane shi, sai ya ce, “Rigar ɗana ne! Waɗansu mugayen namun jeji sun cinye shi. Tabbatacce an yayyaga Yusuf.” Sa’an nan Yaƙub ya kyakkece tufafinsa, ya sa tufafin makoki, ya kuma yi makoki domin ɗansa kwanaki masu yawa. Dukan ’ya’yansa maza da mata, suka zo don su ta’azantar da shi, amma ya ƙi yă ta’azantu. Ya ce, “A’a, cikin makoki zan gangara zuwa kabari wurin ɗana.” Saboda haka, mahaifin Yusuf ya yi kuka saboda shi. Ana cikin haka, Midiyawa suka sayar da Yusuf a Masar wa Fotifar, ɗaya daga cikin shugabannin ’yan gadin fadar Fir’auna. A wannan lokaci, Yahuda ya bar ’yan’uwansa ya gangara don yă zauna da mutumin Adullam, mai suna Hira. A can Yahuda ya sadu da ’yar wani Bakan’ane, mai suna Shuwa. Ya aure ta, ya kuma kwana da ita; ta yi ciki, ta kuma haifi ɗa, wanda aka kira Er. Ta sāke yin ciki, ta haifi wani ɗa, ta kira shi Onan. Ta kuma haifi wani ɗa har yanzu, aka kuwa ba shi suna Shela. A Kezib ne ta haife shi. Sai Yahuda ya auro wa Er mata, ɗansa na fari, sunanta Tamar. Amma Er, ɗan farin Yahuda mugu ne a fuskar Ubangiji, saboda haka Ubangiji ya kashe shi. Sa’an nan Yahuda ya ce wa Onan, “Ka kwana da matar ɗan’uwanka ka cika wajibinka gare ta a matsayin ɗan’uwan miji, don ka samar wa ɗan’uwanka ’ya’ya.” Amma Onan ya san cewa ’ya’yan ba za su zama nasa ba; saboda haka a duk sa’ad da ya kwana da matar ɗan’uwansa, sai yă zub da maniyyinsa a ƙasa don kada yă samar wa ɗan’uwansa ’ya’ya. Abin nan da ya yi mugunta ce a gaban Ubangiji, saboda haka Ubangiji ya kashe shi, shi ma. Sai Yahuda ya ce wa surukarsa Tamar, “Ki yi zama kamar gwauruwa a gidan mahaifinki sai ɗana Shela ya yi girma.” Gama ya yi tunani, “Shi ma zai mutu, kamar ’yan’uwansa.” Saboda haka Tamar ta je ta zauna a gidan mahaifinta. Bayan an daɗe sai matar Yahuda, ’yar Shuwa ta rasu. Sa’ad da Yahuda ya gama makoki, sai ya haura zuwa Timna, zuwa wurin mutanen da suke askin tumakinsa, abokinsa Hira mutumin Adullam kuwa ya tafi tare da shi. Sa’ad da aka faɗa wa Tamar cewa, “Surukinki yana kan hanyarsa zuwa Timna don askin tumakinsa,” sai ta tuɓe rigunan gwaurancinta ta rufe kanta da lulluɓi don ta ɓad da kamanninta, sa’an nan ta je ta zauna a ƙofar shigar Enayim, wadda take a hanyar zuwa Timna. Gama ta lura cewa ko da yake Shela yanzu ya yi girma, ba a ba da ita gare shi ta zama matarsa ba. Sa’ad da Yahuda ya gan ta, ya yi tsammani karuwa ce, gama ta lulluɓe fuskarta. Bai san cewa ita surukarsa ce ba, sai ya ratse zuwa wurinta a gefen hanya ya ce, “Zo mana, in kwana da ke.” Sai ta ce, “Me za ka ba ni in na kwana da kai?” Ya ce, “Zan aika miki da ɗan akuya daga garkena.” Sai ta ce, “Za ka ba ni wani abu jingina, kafin ka aika da shi?” Ya ce, “Wace jingina zan ba ki?” Sai ta amsa, “Hatiminka da ka rataye a wuya da kuma sandan da yake a hannunka.” Ya ba da su gare ta, ya kuma kwana da ita, sai ta yi ciki. Bayan ta tafi, sai ta tuɓe lulluɓin, ta sāke sa tufafin gwaurancinta. Ana cikin haka sai Yahuda ya aika da ɗan akuya ta hannun abokinsa mutumin Adullam don yă karɓo masa jinginar daga wurin macen, amma bai same ta a can ba. Ya tambayi mutanen da suke zama a can ya ce, “Ina karuwar haikalin da take a bakin hanya a Enayim?” Sai suka ce, “Ba a taɓa kasance da karuwar haikali a nan ba.” Saboda haka sai ya koma zuwa wurin Yahuda ya ce, “Ban same ta ba. Ban da haka ma, mutanen da suke zama a can, sun ce, ‘Ba a taɓa kasance da wata karuwar haikali a nan ba.’ ” Sa’an nan Yahuda ya ce, “Bari tă riƙe kayan kiɗa garin nema mu zama abin dariya. Ni kam, na aika da tunkiyar amma ba a same ta ba.” Bayan misalin wata uku sai aka faɗa wa Yahuda cewa, “Tamar, surukarka ta yi laifin karuwanci, a sakamakon haka yanzu ta yi ciki.” Yahuda ya ce, “A fid da ita, a ƙone!” Yayinda ake fitar da ita, sai ta aika saƙo zuwa wurin surukinta, ta ce, “Mutumin da yake da waɗannan kayan ne ya yi mini ciki.” Ta kuma ƙara da cewa, “Duba ko za ka gane da hatimin nan, da abin ɗamaran nan, da kuma sandan nan, ko na wane ne?” Yahuda ya gane su, sai ya ce, “Ai, ta fi ni gaskiya, da yake ban ba da ita ga ɗana Shela ba.” Bai kuwa ƙara kwana da ita ba. Sa’ad da lokaci ya yi da za tă haihu, ashe, tagwaye ’yan maza ne suke cikinta. Yayinda take haihuwa, ɗaya daga cikinsu ya fid da hannunsa; sai ungonzomar ta ɗauki jan zare ta ɗaura a hannun, ta ce, “Wannan ne ya fito da farko.” Amma sa’ad da ya janye hannunsa, sai ɗan’uwansa ya fito, sai ta ce, “Wato, haka ne ka keta ka fito!” Sai aka ba shi suna Ferez. Sa’an nan ɗan’uwansa wanda yake da jan zare a hannunsa ya fito, aka kuma ba shi suna Zera. To, aka kai Yusuf Masar, Fotifar wani mutumin Masar wanda yake ɗaya daga cikin hafsoshin Fir’auna, shugaban masu tsaro, ya saye shi daga mutanen Ishmayel waɗanda suka kai shi can. Ubangiji kuwa yana tare da Yusuf, Yusuf kuwa yi nasara, ya zauna a gidan mutumin Masar maigidansa. Sa’ad da maigidansa ya ga cewa Ubangiji yana tare da Yusuf, kuma cewa Ubangiji ya ba shi nasara a kome da ya yi, sai Yusuf ya sami tagomashi a idanunsa, ya kuma zama mai hidimarsa. Fotifar ya sa shi yă zama shugaba a gidansa, ya kuma danƙa masa kome da yake da shi. Daga lokacin da ya sa shi shugaban gidansa da kuma a kan dukan abin da yake da shi, sai Ubangiji ya albarkaci gidan mutumin Masar saboda Yusuf. Albarkar Ubangiji tana a kan kome da Fotifar yake da shi a gida da kuma a jeji. Saboda haka sai ya bar kome a ƙarƙashin kulawar Yusuf, bai dame kansa a wani abu ba sai dai abincin da yake ci. To, fa, Yusuf ƙaƙƙarfa ne, kyakkyawa kuma, bayan an ɗan jima sai matar maigidansa ta fara sha’awar Yusuf, sai ta ce, “Zo ka kwana da ni!” Amma ya ƙi. Ya ce mata, “Ga shi kome yana a ƙarƙashina, don haka ne ma maigidana bai dami kansa da wani abu a cikin gidan nan ba; kome da ya mallaka, ya danƙa ga kulawata. Babu wani da ya fi ni a wannan gida. Maigidana bai hana ni kome ba sai ke, saboda ke matarsa ce. Yaya fa, zan yi irin wannan mugun abu, in yi zunubi wa Allah?” Ko da yake ta yi ta yin wa Yusuf maganar kowace rana, amma ya ƙi yă kwana da ita, ko ma yă zauna da ita. Wata rana, ya shiga cikin gida don yă yi ayyukansa, ba wani daga cikin bayin gidan da yake ciki. Sai ta cafke shi a riga, ta ce, “Zo ka kwana da ni!” Amma ya bar rigarsa a hannunta, ya gudu ya fita daga gidan. Sa’ad da ta ga ya bar rigarsa a hannunta ya gudu ya fita daga gidan, sai ta kira bayin gidan ta ce musu, “Duba, an kawo mana wannan mutumin Ibraniyawa don yă ci mutuncinmu! Ya zo nan don yă kwana da ni, amma na yi ihu. Sa’ad da ya ji na yi ihu neman taimako, sai ya bar rigarsa kusa da ni, ya gudu ya fita daga gida.” Ta ajiye rigar kusa da ita sai da maigidansa ya dawo gida. Sa’an nan ta faɗa masa wannan labari, “Mutumin Ibraniyawan, bawan da ka kawo mana, ya zo wurina don yă ci mutuncina. Amma da zarar na yi ihu neman taimako, sai ya bar rigarsa kusa da ni, ya gudu ya fita daga gida.” Sa’ad da maigidansa ya ji labarin da matarsa ta faɗa masa cewa, “Ga yadda bawanka ya yi da ni,” sai ya husata. Maigidan Yusuf ya ɗauke shi ya sa a kurkuku, wurin da ake tsare ’yan kurkukun sarki. Amma yayinda Yusuf yake can a cikin kurkuku, Ubangiji ya kasance tare da shi; ya nuna masa alheri, ya kuma sa ya sami tagomashi a idanun mai gadin kurkukun. Saboda haka mai gadin ya sa Yusuf ya zama shugaban dukan waɗanda aka tsare a kurkukun, Yusuf ne kuma yake lura da dukan abin da ake yi a can. Mai gadin ba ya sa kansa game da kome da yake ƙarƙashin kulawar Yusuf, gama Ubangiji yana tare da Yusuf, ya kuma ba shi nasara a cikin dukan abin da ya yi. Bayan ɗan lokaci, sai mai riƙon kwaf da mai tuyan sarkin Masar suka yi wa maigidansu, sarkin Masar laifi. Fir’auna ya yi fushi da hafsoshin nan nasa guda biyu, shugaban masu shayarwa da shugaban masu tuya, ya kuma sa su a kurkuku a cikin gidan shugaban masu tsaro, a wannan kurkukun da aka sa Yusuf. Sai shugaban masu tsaro ya danƙa su a hannun Yusuf, ya kuwa yi musu hidima. Bayan sun jima cikin kurkuku, sai kowanne a cikin mutum biyun nan, mai riƙon kwaf da mai tuya na sarkin Masar, waɗanda aka sa a kurkuku, suka yi mafarki a dare ɗaya, kuma kowane mafarki ya kasance da fassara irin tasa. Sa’ad da Yusuf ya zo wurinsu kashegari, sai ya ga duk sun damu. Saboda haka ya tambayi hafsoshin Fir’auna, waɗanda suke a kurkuku tare da shi, a gidan maigidansa ya ce, “Me ya sa fuskokinku suke a ɓace haka?” Sai suka amsa, “Mu biyu, mun yi mafarki, amma babu wani da zai fassara mana su.” Sa’an nan Yusuf ya ce musu, “Fassara ba daga Allah take zuwa ba? Ku faɗa mini mafarkanku.” Sai shugaban masu shayarwa ya faɗa wa Yusuf mafarkinsa. Ya ce masa, “A cikin mafarkina, na ga kuringa a gabana, kuma a kuringar, akwai rassa uku. Nan da nan kuringar ta yi toho, ta huda, ta kuma yi nonna har suka nuna, suka zama inabi. Kwaf Fir’auna kuwa yana a hannuna, na kuma ɗiba inabin na matse su cikin kwaf Fir’auna, na kuma sa kwaf ɗin a hannunsa.” Yusuf ya ce masa, “Ga abin da mafarkin yake nufi, ‘Rassan nan uku, kwana uku ne. Cikin kwana uku, Fir’auna zai fitar da kai, yă maido da kai a matsayinka, za ka kuwa sa kwaf Fir’auna cikin hannunsa, kamar yadda ka saba yi sa’ad da kake mai riƙon kwaf nasa. Amma fa, sa’ad da kome ya zama maka da kyau, ka tuna da ni, ka kuma yi mini alheri, ka ambace ni wa Fir’auna, ka fid da ni daga wannan kurkuku. Gama da ƙarfi ne aka ɗauke ni daga ƙasar Ibraniyawa, ko a nan ma ban yi wani abin da ya cancanci a sa ni cikin kurkuku ba.’ ” Sa’ad da shugaban masu tuya ya ga cewa Yusuf ya ba da fassara mai gamsarwa, sai ya ce, wa Yusuf, “Ni ma na yi mafarki. A kaina, akwai kwanduna uku na burodi. A kwandon na bisa, akwai kayan iri-iri da aka toya, masu kyau domin Fir’auna, amma tsuntsaye suka ci su a kwandon da yake kaina.” Yusuf ya ce, “Ga abin da mafarkin yake nufi, ‘Kwanduna uku, kwanaki uku ne. Cikin kwana uku, Fir’auna zai fid da kai, yă rataye ka a kan itace. Tsuntsaye kuwa za su ci naman jikinka.’ ” To, a rana ta uku ne, ranar tunawa da haihuwar Fir’auna, ya kuwa yi biki wa dukan hafsoshinsa. Ya fid da shugaban masu shayarwa da kuma shugaban masu tuya a gaban hafsoshinsa. Ya mai da shugaban masu shayarwa a matsayinsa, saboda haka shugaban masu shayarwa ya sāke sa kwaf a hannun Fir’auna, amma ya rataye shugaban masu tuya, kamar dai yadda Yusuf ya faɗa musu a fassarar mafarkan da suka yi. Shugaban masu shayarwa fa, bai tuna da Yusuf ba; ya mance da shi. Bayan shekaru biyu cif, Fir’auna ya yi mafarki. A mafarkin, ya ga yana tsaye kusa da Nilu, sai ga shanu bakwai masu ƙiba mulmul, suka fito daga kogin, suna kiwo a cikin kyauro. Bayansu, sai ga waɗansu shanu bakwai, munana, ramammu, suka fito daga Nilu, suka tsaya kusa da waɗancan masu ƙiban, a bakin kogin. Shanun nan da suke munana ramammu, suka cinye shanu bakwai nan masu ƙiba mulmul. Sai Fir’auna ya farka. Ya sāke yin barci, sai ya yi mafarki na biyu; ya ga kawuna bakwai na dawa, ƙosassu masu kyau, suka yi girma a kara guda. Bayansu, sai ga waɗansu kawuna bakwai na dawa, suka fito sirara waɗanda iskar gabas ta sa suka yanƙwane. Siraran dawan suka haɗiye kawuna bakwai nan ƙosassu masu kyau. Sai Fir’auna ya farka, ashe, mafarki ne. Da safe sai hankalinsa ya tashi, saboda haka sai ya aika a kawo dukan masu duba da masu hikima na Masar. Fir’auna ya faɗa musu mafarkansa, amma babu wanda ya iya ba shi fassararsu. Sai shugaban masu shayarwa ya ce wa Fir’auna, “Yau an tuna mini da kāsawata. Sai ya ci gaba ya ce, Fir’auna ya taɓa husata da bayinsa, ya kuma jefa ni da shugaban masu tuya a cikin kurkuku a gidan shugaban masu tsaro. Kowannenmu ya yi mafarki a wani dare, kowane mafarki kuma ya kasance da ma’anarsa. To, wani saurayi, mutumin Ibraniyawa ya kasance a can tare da mu, bawan shugaban masu tsaro. Sai muka faɗa masa mafarkanmu, ya kuwa fassara mana su, yana ba wa kowane mutum fassarar mafarkinsa. Abubuwan kuwa suka kasance daidai yadda ya fassara su gare mu; aka mai da ni a matsayina, ɗaya mutumin kuwa aka rataye shi.” Sai Fir’auna ya aika a kawo Yusuf, aka kuwa kawo shi da sauri daga kurkuku. Sa’ad da ya yi aski, ya kuma canja tufafinsa, sai ya zo gaban Fir’auna. Fir’auna ya ce wa Yusuf, “Na yi mafarki, kuma babu wanda ya iya fassara shi. Amma na ji an ce sa’ad da ka ji mafarki, kana iya fassara shi.” Yusuf ya amsa wa Fir’auna ya ce, “Ba ni ne da iyawar ba, Allah zai iya ba wa Fir’auna amsar da yake nema.” Sa’an nan Fir’auna ya ce wa Yusuf, “A cikin mafarkina, na ga ina tsaye a bakin Nilu, sai ga shanu bakwai masu ƙiba mulmul, suka fito daga kogin, suna kiwo a cikin kyauro. Bayansu kuma, sai ga waɗansu shanu bakwai suka fito ƙanjamammu, munana, ramammu. Ban taɓa ganin irin munanan shanu haka a cikin dukan ƙasar Masar ba. Ramammun shanun nan munana, suka cinye shanun nan bakwai masu ƙiba da suka fito da fari. Amma ko bayan da suka cinye su, babu wanda zai iya faɗa cewa sun yi haka; suna nan dai munana kamar yadda suke a dā. Sai na farka. “Har yanzu kuma, a cikin mafarkina na ga kawuna bakwai na dawa ƙosassu masu kyau, suna girma a kara guda. Bayansu, sai ga waɗansu kawuna bakwai suka fito, yanƙwananne sirara waɗanda iskar gabas ta yanƙwane. Siraran kawunan dawan nan suka haɗiye kawuna bakwai nan masu kyau. Na faɗa wannan wa masu duba, amma ba wanda ya iya fassara mini shi.” Sai Yusuf ya ce wa Fir’auna, “Mafarkan Fir’auna, ɗaya ne. Allah ya bayyana wa Fir’auna abin da yake shirin yi. Shanu masu kyau nan, shekaru bakwai ne, kawunan dawa bakwai ƙosassun nan kuwa shekaru bakwai ne; mafarkan iri ɗaya ne. Shanun nan ramammu, munana, da suka zo daga baya, shekaru bakwai ne, haka ma kawuna dawan nan shanyayyu da iskar gabas ta yanƙwane. Shekaru ne bakwai na yunwa. “Haka yake kamar yadda na faɗa wa Fir’auna cewa Allah ya nuna wa Fir’auna abin da yake shirin yi. Shekaru bakwai na yalwar abinci suna zuwa a dukan ƙasar Masar, amma shekaru bakwai na yunwa za su biyo bayansu. Tsananin yunwar za tă sa a manta da dukan isashen abincin da aka samu a ƙasar Masar, yunwa kuwa za tă rufe dukan ƙasar. Ba za a tuna da isashen abincin da aka samu a ƙasar ba, domin yunwar da za tă biyo baya za tă zama da tsanani ƙwarai. Dalilin da aka ba wa Fir’auna mafarkan nan kashi biyu kuwa shi ne cewa Allah ya riga ya ƙaddara al’amarin. Allah zai aikata shi, ba da daɗewa ba. “Yanzu fa, bari Fir’auna yă nemi mutum mai basira da kuma hikima, yă sa shi yă shugabanci ƙasar Masar. Bari Fir’auna yă naɗa komishinoni a kan ƙasar don su karɓi kashi ɗaya bisa biyar na girbin Masar a lokacin shekaru bakwai na yalwar abinci. Ya kamata su tara dukan abincin waɗannan shekaru masu kyau da suke zuwa, su yi ajiyar hatsin a ƙarƙashin ikon Fir’auna, don a ajiye a birane don abinci. Ya kamata a adana abincin nan don ƙasar, kāriya shekaru bakwai na yunwa, domin a yi amfani da shi a lokacin shekarun yunwan da za su zo wa Masar, saboda kada ƙasar ta lalace da yunwa.” Shirin ya yi wa Fir’auna da kuma dukan hafsoshinsa kyau. Saboda haka Fir’auna ya tambaye su, “Za mu iya samun wani kamar wannan mutum, wannan wanda Ruhun Allah yake cikinsa?” Sai Fir’auna ya ce wa Yusuf, “Da yake Allah ya ba ka sanin dukan waɗannan, babu wani mai basira da kuma hikima kamar ka. Za ka shugabanci fadata, kuma dukan mutanena za su zama a ƙarƙashinka. Da sarauta kaɗai zan fi ka girma.” Saboda haka Fir’auna ya ce wa Yusuf, “Ga shi na sa ka zama shugaban dukan ƙasar Masar.” Sa’an nan Fir’auna ya zare zoben sarauta daga yatsarsa, ya sa shi a yatsan Yusuf. Ya sanya masa rigar lallausan lilin, ya kuma sa masa sarƙar zinariya a wuyansa. Ya sa shi ya hau keken yaƙi a matsayi mai binsa na biyu, mutane kuwa suka yi shela a gabansa suna cewa, “A ba da hanya!” Ta haka ya sa shi shugaba a kan dukan ƙasar Masar. Sa’an nan Fir’auna ya ce wa Yusuf, “Ni ne Fir’auna, amma in ba tare da umarninka ba, ba wanda zai ɗaga hannu ko ƙafa a cikin dukan Masar.” Fir’auna ya ba wa Yusuf suna Zafenat-Faneya, ya kuma ba shi Asenat ’yar Fotifera firist na On, ta zama matarsa. Yusuf kuwa ya zaga dukan ƙasar Masar. Yusuf yana zuwa shekara talatin sa’ad da ya shiga hidimar Fir’auna sarkin Masar. Yusuf kuwa ya fita daga gaban Fir’auna, ya zaga ko’ina a Masar. A shekaru bakwai na yalwa, ƙasar ta ba da amfani mai yawa. Yusuf ya tattara dukan abincin da aka samu a waɗannan shekaru bakwai na yalwa a Masar, ya kuma yi ajiyarsu a cikin birane. A kowane birni, ya sa abincin da aka nome a kewayensa. Sai Yusuf ya tara hatsi da yawan gaske, kamar yashi a bakin teku, har sai da ya kāsa iya auna shi, gama ba a iya aunawa. Kafin shekarun yunwa su zo, Asenat ’yar Fotifera, firist na On, ta haifa wa Yusuf ’ya’ya maza biyu. Yusuf ya ba wa ɗansa na fari suna Manasse ya ce, “Gama Allah ya sa na mance dukan wahalata da dukan gidan mahaifina.” Ya ba wa ɗansa na biyu suna Efraim ya ce, “Gama Allah ya wadata ni cikin wahalata.” Shekaru bakwai na yalwa a Masar suka zo ga ƙarshe, sai shekaru bakwai na yunwa suka soma shigowa, kamar yadda Yusuf ya faɗa. Aka yi yunwa ko’ina amma ban da ƙasar Masar. Don akwai abinci. Sa’ad da dukan Masar ta fara jin yunwa, sai mutane suka yi wa Fir’auna kuka don abinci. Sai Fir’auna ya ce wa dukan Masarawa, “Ku tafi wurin Yusuf, ku kuma yi abin da ya faɗa muku.” Sa’ad da yunwa ta bazu a dukan ƙasar, sai Yusuf ya buɗe gidajen ajiya, ya kuma sayar da hatsi ga Masarawa, gama yunwa ta yi tsanani a dukan Masar. Dukan ƙasashe kuwa suka zo Masar don saya hatsi daga Yusuf, gama yunwa ta yi tsanani a dukan duniya. Sa’ad da Yaƙub ya sami labari cewa akwai hatsi a Masar, sai ya ce wa ’ya’yansa maza, “Don me kuke duban juna kawai?” Ya ci gaba, “Na ji cewa akwai hatsi a Masar. Ku gangara can ku sayo mana, domin mu rayu kada mu mutu.” Sai goma daga cikin ’yan’uwan Yusuf suka gangara don su saya hatsi daga Masar. Amma Yaƙub bai aiki Benyamin, ɗan’uwan Yusuf tare da sauran ba, gama yana tsoro kada wani abu yă faru da shi. Sai ’ya’yan Yaƙub suka isa Masar tare da sauran mutanen don sayen abinci, gama yunwar ta kai yankin Kan’ana ma. To, Yusuf ne gwamnar ƙasar wanda yake sayar da hatsi ga dukan mutanenta. Saboda haka sa’ad da ’yan’uwan Yusuf suka isa, sai suka rusuna masa har ƙasa da fuskokinsu. Nan da nan da Yusuf ya ga ’yan’uwansa, sai ya gane su, amma ya yi kamar baƙo, ya kuma yi musu magana da tsawa. Ya tambaya, “Daga ina kuka fito?” Suka amsa, “Daga ƙasar Kan’ana, don mu saya abinci.” Ko da yake Yusuf ya gane ’yan’uwansa, su ba su gane shi ba. Sa’an nan ya tuna da mafarkansa game da su, ya kuma ce musu, “Ku ’yan leƙen asiri ne! Kun zo don ku leƙi asirin ƙasar ku ga inda ba ta da tsaro.” Suka amsa suka ce, “A’a, ranka yă daɗe, bayinka sun zo don saya abinci ne. Mu duka ’ya’yan mutum ɗaya maza ne. Bayinka mutane ne masu gaskiya, ba ’yan leƙen asiri ba ne.” Ya ce musu “Sam! Kun zo ne ku ga inda ƙasarmu babu tsaro.” Amma suka amsa suka ce, “Bayinka dā su goma sha biyu ne, ’yan’uwa, ’ya’yan mutum guda maza, wanda yake zama a ƙasar Kan’ana. Ƙaraminmu yanzu yana tare da mahaifinmu, ɗayan kuma ya rasu.” Yusuf ya ce musu, “Daidai ne yadda na faɗa muku. Ku ’yan leƙen asiri ne! Ga kuwa yadda za a gwada ku. Muddin Fir’auna yana a raye, ba za ku bar wannan wuri ba sai ƙaramin ɗan’uwanku ya zo nan. Ku aiki ɗaya daga cikinku yă kawo ɗan’uwanku; za a sa sauranku a kurkuku, saboda a gwada maganarku a ga ko gaskiya ce kuke faɗi. In ba haka ba, to, da ran Fir’auna, ku ’yan leƙen asiri ne!” Ya kuwa sa su duka a kurkuku na kwana uku. A rana ta uku, Yusuf ya ce musu, “Ku yi wannan za ku kuwa rayu, gama ina tsoron Allah. In ku mutane masu gaskiya ne, ku bar ɗaya daga cikin ’yan’uwanku yă zauna a kurkuku, yayinda sauranku su tafi, su kai hatsi don gidajenku da suke yunwa. Amma dole ku kawo ƙaramin ɗan’uwanku gare ni, saboda a tabbatar da maganarku har ba za ku mutu ba.” Suka kuwa yi haka. Sai suka ce wa juna, “Tabbatacce ana hukunta mu ne saboda ɗan’uwanmu. Mun ga yadda ya yi wahala sa’ad da ya roƙe mu saboda ransa, amma ba mu saurare shi ba, shi ya sa wannan wahala ta zo mana.” Ruben ya amsa, “Ban faɗa muku cewa kada ku ɗauki alhakin yaron nan ba, sai kuka ƙi ji, to, yau ga alhakin jininsa muke biya.” Ba su san cewa Yusuf yana jin su ba, da yake yana amfani da mai fassara ne. Sai ya juya daga gare su ya yi kuka, sa’an nan ya dawo ya yi musu magana kuma. Ya sa aka ɗauke Simeyon daga gare su, aka daure shi a idanunsu. Yusuf ya yi umarni a cika buhunansu da hatsi, a kuma sa azurfan kowane mutum a cikin buhunsa, a kuma ba su kalaci don tafiyarsu. Bayan aka yi musu wannan, suka jibga hatsinsu a kan jakuna, sai suka kama hanya. A wurin da suka tsaya don su kwana, ɗaya daga cikinsu ya buɗe buhunsa don yă ciyar da jakinsa, sai ya ga azurfansa a bakin buhunsa. Sai ya ce wa ’yan’uwansa, “An mayar mini da azurfata. Ga shi a cikin buhuna.” Zuciyarsu ta karai, suka dubi juna suna rawan jiki, suka ce, “Mene ne wannan da Allah ya yi mana?” Sa’ad da suka zo wurin mahaifinsu Yaƙub a ƙasar Kan’ana, suka faɗa masa dukan abin da ya faru da su. Suka ce, “Mutumin da yake shugaba a ƙasar ya yi mana matsananciyar magana, ya kuma ɗauke mu tamƙar ’yan leƙen asirin ƙasa. Amma muka ce masa, ‘Mu masu gaskiya ne; mu ba ’yan leƙen asiri ba ne. Dā mu ’yan’uwa ne goma sha biyu, ’ya’yan mahaifi guda maza. Ɗayanmu ya rasu, kuma ƙaramin yanzu yana tare da mahaifinmu a Kan’ana.’ “Sai mutumin wanda yake shugaba a kan ƙasar ya ce mana, ‘Ga yadda zan san ko ku mutane masu gaskiya ne. Ku bar ɗaya daga cikin ’yan’uwanku a nan tare da ni, ku ɗauki abinci domin gidajenku masu yunwa, ku tafi. Amma ku kawo mini ƙaramin ɗan’uwanku domin in san cewa ku ba ’yan leƙen asiri ba ne, amma mutane ne masu gaskiya. Sa’an nan zan mayar muku da ɗan’uwanku, ku kuma iya yin sana’a a ƙasar.’ ” Yayinda suke juyewa hatsi daga buhunansu, sai ga ƙunshin azurfan kowane mutum a buhunsa! Sa’ad da su da mahaifinsu suka ga ƙunshe-ƙunshen kuɗi, suka firgita. Yaƙub mahaifinsu, ya ce musu, “Kun sa ni rashin ’ya’yana. Yusuf ya rasu, Simeyon kuma ba ya nan, yanzu kuma kuna so ku ɗauki Benyamin. Kome yana gāba da ni!” Sai Ruben ya ce wa mahaifinsa, “Ka kashe dukan ’ya’yana maza, in ban dawo da shi gare ka ba. Ka sa shi ga kulawata, zan kuwa dawo da shi.” Amma Yaƙub ya ce, “Ɗana ba zai gangara zuwa can tare da ku ba, ɗan’uwansa ya rasu, shi ne kaɗai ya rage. In wani abu ya faru da shi a tafiyar da za ku yi, za ku sa furfurata ta gangara zuwa kabari cikin baƙin ciki.” A yanzu, yunwa ta yi tsanani a ƙasar. Saboda haka sa’ad da suka cinye dukan hatsin da suka kawo daga Masar, mahaifinsu ya ce musu, “Ku koma, ku sayo mana ƙarin abinci.” Amma Yahuda ya ce masa, “Mutumin ya gargaɗe mu sosai cewa, ‘Ba za ku sāke ganin fuskata ba sai in ɗan’uwanku yana tare da ku.’ In za ka aika da ɗan’uwanmu tare da mu, za mu gangara mu sayo maka abinci. Amma in ba za ka aika da shi ba, ba za mu gangara ba, gama mutumin ya ce mana, ‘Ba za ku sāke ganin fuskata ba sai ko in ɗan’uwanku yana tare da ku.’ ” Isra’ila ya yi tambaya, “Me ya sa kuka kawo wannan damuwa a kaina ta wurin faɗa wa mutumin cewa kuna da wani ɗan’uwa?” Suka amsa, “Mutumin ya yi mana tambaya sosai game da kanmu da iyalinmu. Ya tambaye mu, ‘Mahaifinku yana da rai har yanzu? Kuna da wani ɗan’uwa?’ Mu dai mun amsa tambayoyinsa ne. Ta yaya za mu sani zai ce, ‘Ku kawo ɗan’uwanku a nan’?” Sa’an nan Yahuda ya ce wa Isra’ila mahaifinsa, “Ka aika saurayin tare da ni za mu kuwa tafi nan da nan, saboda mu da ’ya’yanmu mu rayu, kada mu mutu. Ni kaina zan tabbatar da lafiyarsa; na ɗauki lamuninsa, a hannuna za ka neme shi. In ban dawo da shi gare ka, in sa shi nan a gabanka ba, zan ɗauki laifin a gabanka dukan kwanakina. Ai, da ba mun jinkirta ba, da mun komo har sau biyu.” Sa’an nan mahaifinsu Isra’ila ya ce musu, “In dole ne a yi haka, to, sai ku yi. Ku sa waɗansu amfani mafi kyau na ƙasar a buhunanku, ku ɗauka zuwa wurin mutumin a matsayin kyauta, da ɗan man ƙanshi na shafawa, da kuma ’yar zuma, da kayan yaji, da ƙaro, da tsabar citta da kuma almon. Ku ɗauki ninki biyu na yawan azurfa tare da ku, gama dole ku mayar da azurfan da aka sa a cikin bakunan buhunanku. Mai yiwuwa an yi haka a kuskure ne. Ku ɗauki ɗan’uwanku kuma ku koma wurin mutumin nan da nan. Bari Allah Maɗaukaki yă nuna muku alheri a gaban mutumin saboda yă bar ɗan’uwanku da Benyamin su dawo tare da ku. Ni kuwa, in na yi rashi, na yi rashi.” Saboda haka mutanen suka ɗauki kyautar, da kuma kuɗin da ya ninka na farko. Suka kuma ɗauki Benyamin, suka gaggauta suka gangara zuwa Masar suka kuma gabatar da kansu ga Yusuf. Sa’ad da Yusuf ya ga Benyamin tare da su, sai ya ce wa mai hidimar gidansa, “Ka shigar da mutanen cikin gida, ka yanka dabba ka shirya, gama mutanen za su ci abincin rana tare da ni.” Mutumin ya yi kamar yadda Yusuf ya faɗa masa, ya kuwa ɗauki mutanen zuwa gidan Yusuf. Mutanen dai suka firgita sa’ad da aka ɗauke su zuwa gidansa. Suka yi tunani, “An kawo mu nan ne saboda azurfan da aka sa a cikin buhunanmu da farko. Yana so yă fāɗa mana, yă kuma sha ƙarfinmu, yă ƙwace mu kamar bayi, yă kuma kwashe jakunanmu.” Saboda haka suka je wurin mai yin wa Yusuf hidima, suka yi masa magana a bakin ƙofar gida. Suka ce, “Ranka yă daɗe, mun zo nan ƙaro na farko don mu saya abinci, amma a inda muka tsaya don mu kwana, da muka buɗe buhunanmu sai kowannenmu ya sami azurfansa daidai a bakin buhunsa. Saboda haka ga kuɗin a hannunmu, mun sāke komowa da su. Mun kuma kawo ƙarin azurfa tare da mu don mu saya abinci. Ba mu san wa ya sa azurfanmu a cikin buhunanmu ba.” Sai mai hidimar ya ce, “Ba kome, kada ku ji tsoro. Allahnku, Allahn mahaifinku ne ya ba ku dukiyar a cikin buhunanku; ni dai, na karɓi azurfanku.” Sa’an nan ya fitar musu da Simeyon. Mai yin hidimar ya ɗauki mutane zuwa gidan Yusuf ya ba su ruwa su wanke ƙafafunsu, ya kuma tanada wa jakunansu abinci. Suka shirya kyautansu domin isowar Yusuf da rana, gama sun ji cewa zai ci abinci a nan. Sa’ad da Yusuf ya zo gida, sai suka ba shi kyautai da suka kawo, suka rusuna a gabansa har ƙasa. Ya tambaye su, yaya suke, sa’an nan ya ce, “Yaya tsohon nan mahaifinku da kuka faɗa mini? Yana da rai har yanzu?” Suka amsa, “Bawanka mahaifinmu yana da rai har yanzu da kuma ƙoshin lafiya.” Suka kuma rusuna suka yi mubaya’a. Da ya ɗaga idanu, sai ya ga ɗan’uwansa Benyamin, ɗan mahaifiyarsa, sai ya yi tambaya, “Wannan ne ƙaramin ɗan’uwanku, wanda kuka faɗa mini a kai?” Ya kuma ce, “Allah yă yi maka albarka, ɗana.” Saboda motsi mai zurfi da zuciyarsa ta yi da ganin ɗan’uwansa, sai Yusuf ya gaggauta ya fita, ya nemi wuri yă yi kuka. Ya shiga ɗakinsa ya yi kuka a can. Bayan ya wanke fuskarsa, sai ya fito ya daure, ya umarta, “A kawo abinci.” Sai aka raba musu abinci, nasa shi kaɗai su kuma su kaɗai, domin Masarawa ba sa cin abinci tare da Ibraniyawa, gama wannan abin ƙyama ne ga Masarawa. Aka zaunar da ’yan’uwan Yusuf a gabansa bisa ga shekarunsu, daga ɗan fari zuwa auta. ’Yan’uwan kuwa suka duddubi juna suna mamaki. Daga teburin da yake a gaban Yusuf aka riƙa ɗibar rabonsu ana kai musu, amma rabon Benyamin ya yi biyar ɗin na kowannensu. Suka kuwa sha, suka yi murna tare da shi. Yusuf kuwa ya ba wa mai yin masa hidima a gida, waɗannan umarnai cewa, “Cika buhunan mutanen nan da abinci iyakar yadda za su iya ɗauka, ka kuma sa kuɗin kowanne a bakin buhunsa. Sa’an nan ka sa kwaf nawa, wannan na azurfa a bakin buhun autan, tare da kuɗinsa na hatsi.” Sai mai hidimar ya yi kamar yadda Yusuf ya umarta. Da gari ya waye, sai aka sallami mutanen tare da jakunansu. Ba su yi nisa da birnin ba sa’ad da Yusuf ya ce wa mai yin masa hidima, “Tashi, ka bi waɗannan mutane nan da nan, in ka same su, ka ce musu, ‘Me ya sa kuka sāka alheri da mugunta? Ba da wannan kwaf ne maigidana yake sha daga ciki yana kuma yin amfani da shi don duba? Wannan mugun abu ne da kuka yi.’ ” Sa’ad da ya same su, sai ya maimaita waɗannan kalmomi gare su. Amma suka ce masa, “Me ya sa ranka yă daɗe yake faɗin irin waɗannan abubuwa? Allah yă sawwaƙe bayinka su yi irin wannan abu! Mun ma dawo maka da kuɗin da muka samu a cikin bakunan buhunanmu daga ƙasar Kan’ana. Saboda haka me zai sa mu saci azurfa ko zinariya daga gidan maigidanka? In aka sami wani daga cikin bayinka da shi, zai mutu; sai sauran su zama bayin mai girma.” Sai ya ce, “To, shi ke nan, bari yă zama yadda kuka faɗa. Duk wanda aka same shi da kwaf na azurfan zai zama bawana, sauran kuwa za su ’yantu daga zargin.” Da sauri kowannensu ya sauko da buhunsa ƙasa, ya buɗe. Sa’an nan mai hidimar ya fara bincike, farawa daga babba, ya ƙare a ƙaramin. Aka kuwa sami kwaf ɗin a buhun Benyamin. Ganin wannan sai suka kyakkece rigunansu. Sa’an nan suka jibga wa jakunansu kaya, suka koma birni. Yusuf yana nan har yanzu a gida sa’ad da Yahuda da ’yan’uwansa suka shiga, suka fāɗi rub da ciki a ƙasa a gabansa. Yusuf ya ce musu, “Mene ne wannan da kuka yi? Ba ku san cewa mutum kamar ni yana iya gane abubuwa ta wurin duba ba?” Yahuda ya amsa ya ce, “Me za mu ce wa ranka yă daɗe? Yaya kuma za mu wanke kanmu daga wannan zargi? Allah ya tona laifin bayinka. Ga mu, za mu zama bayinka, da mu da wanda aka sami kwaf ɗin a hannunsa.” Amma Yusuf ya ce, “Allah yă sawwaƙe in yi haka! Mutumin da aka sami kwaf ɗin a hannunsa ne kaɗai zai zama bawana. Sauranku, ku koma ga mahaifinku da salama.” Sai Yahuda ya haura zuwa wurinsa ya ce, “Ranka yă daɗe, roƙo nake, bari bawanka yă yi magana da ranka yă daɗe. Kada ka yi fushi da bawanka, ko da yake daidai kake da Fir’auna kansa. Ranka yă daɗe ya tambayi bayinka ya ce, ‘Kuna da mahaifi ko ɗan’uwa?’ Muka kuwa amsa, ‘Muna da mahaifi tsoho, akwai kuma ɗa matashi, wanda aka haifa masa cikin tsufarsa. Ɗan’uwansa ya rasu, shi ne kuwa ɗa kaɗai na mahaifiyarsa da ya rage, mahaifinsa kuwa yana ƙaunarsa.’ “Sai ka ce wa bayinka, ‘Ku kawo mini shi don in gan shi da kaina.’ Muka kuwa ce wa ranka yă daɗe, ‘Saurayin ba zai iya barin mahaifinsa ba, gama in ya bar shi, mahaifinsa zai mutu.’ Amma ka faɗa wa bayinka, ‘Sai kun kawo ƙaramin ɗan’uwanku tare da ku, in ba haka ba, ba za ku sāke ganin fuskata ba.’ Sa’ad da muka koma wurin bawanka mahaifinmu, sai muka faɗa masa abin da ranka yă daɗe ya ce. “Sai mahaifinmu ya ce, ‘Ku koma ku sayo ƙarin abinci.’ Amma muka ce, ‘Ba za mu iya gangarawa ba, sai in ƙaramin ɗan’uwanmu yana tare da mu. Ba za mu iya ganin fuskar mutumin ba, sai ƙaramin ɗan’uwanmu yana tare mu.’ “Bawanka mahaifinmu ya ce mana, ‘Kun san cewa matata ta haifa mini ’ya’ya biyu maza. Ɗayansu ya tafi daga gare ni, na kuwa ce, “Tabbatacce an yayyage shi kaca-kaca.” Ban kuwa gan shi ba tuntuni. In kun ɗauki wannan daga wurina shi ma wani abu ya same shi, za ku kawo furfura kaina zuwa kabari cikin baƙin ciki.’ “Saboda haka yanzu, in saurayin ba ya nan tare da mu sa’ad da na koma ga bawanka mahaifina, in kuma mahaifina, wanda ransa yana daure kurkusa da ran saurayin, ya ga cewa saurayin ba ya nan, zai mutu. Bayinka za su sa bawanka, mahaifinmu, yă mutu cikin baƙin ciki, da tsufansa. Gama ni baranka na ɗauki lamunin saurayin a wurin mahaifinsa da cewa, ‘In ban komo maka da shi ba, sai alhakinsa yă zauna a kaina a gaban mahaifina, dukan raina!’ “To, yanzu, ina roƙonka bari bawanka yă zauna a nan a matsayin bawanka, ranka yă daɗe a maimakon saurayin, a kuma bar saurayin yă koma da ’yan’uwansa. Yaya zan koma ga mahaifina, in saurayin ba ya tare da ni? A’a! Kada ka bari in ga baƙin cikin da zai auko wa mahaifina.” Yusuf bai ƙara iya daurewa a gaban dukan masu yi masa hidima ba, sai ya yi kuka da ƙarfi ya ce, “Kowa yă tashi daga gabana!” Saboda haka ba kowa a wurin sa’ad da Yusuf ya sanar da kansa ga ’yan’uwansa. Sai ya yi kuka da ƙarfi har Masarawa suka ji, har labarin ya kai gidan Fir’auna. Yusuf kuwa ya ce wa ’yan’uwansa, “Ni ne Yusuf! Mahaifina yana nan da rai har yanzu?” Amma ’yan’uwansa ba su iya amsa masa ba, gama sun firgita ƙwarai a gabansa. Sa’an nan Yusuf ya ce wa ’yan’uwansa, “Ku zo kusa da ni.” Da suka yi haka, sai ya ce, “Ni ne ɗan’uwanku Yusuf, wannan da kuka sayar zuwa Masar! Yanzu dai, kada ku damu, kada kuma ku yi fushi da kanku saboda kun sayar da ni a nan, gama Allah ya aiko ni gabanku ne don in ceci rayuka. Ga shi shekaru biyu ke nan ake yunwa a ƙasar, kuma da sauran shekara biyar masu zuwa da ba za a yi noma ko girbi ba. Amma Allah ya aiko ni gabanku ne don in adana muku raguwa a duniya, in kuma ceci rayukanku ta wurin ceto mai girma. “Saboda haka fa, ba ku ba ne kuka aiko ni nan, Allah ne. Ya mai da ni mahaifi ga Fir’auna, shugaban dukan gidansa da kuma mai mulkin dukan Masar. Yanzu sai ku gaggauta zuwa wurin mahaifina ku faɗa masa, ‘Abin da ɗanka Yusuf ya ce; Allah ya mai da ni shugaban dukan Masar. Gangaro wurina; kada ka jinkirta. Za ka yi zama a yankin Goshen, ka kasance kusa da ni. Kai, ’ya’yanka da kuma jikokinka, garkunanka da shanunka, da kuma dukan abin da kake da shi. Zan tanada maka a nan, domin akwai saura shekaru biyar na yunwa masu zuwa. In ba haka ba, kai da gidanka da dukan mallakarka za ku zama gajiyayyu.’ “Ku kanku kun gani, haka ma ɗan’uwana Benyamin, cewa tabbatacce ni ne nake magana da ku. Faɗa wa mahaifina game da dukan girman da aka ba ni a Masar, da kuma game da kome da kuka gani. Ku kuma kawo mahaifina a nan da sauri.” Sa’an nan ya rungume ɗan’uwansa Benyamin ya yi kuka, sai Benyamin ya rungume shi yana kuka. Ya sumbaci dukan ’yan’uwansa, ya kuma yi kuka a kansu. Bayan haka sai ’yan’uwansa suka yi masa magana. Sa’ad da labarin ya kai fadan Fir’auna cewa ’yan’uwan Yusuf sun zo, sai Fir’auna da dukan hafsoshin suka ji daɗi. Fir’auna ya ce wa Yusuf, “Faɗa wa ’yan’uwanka, ‘Yi wannan; ku jibge dabbobinku ku koma zuwa ƙasar Kan’ana, Ku kawo mahaifinku da iyalanku zuwa wurina. Zan ba ku mafi kyau na ƙasar Masar, za ku kuwa ci moriyar ƙasar.’ “An kuma umarce ka, ka faɗa musu, ‘Ku yi wannan, ku ɗauki wagonu daga Masar domin ’ya’yanku da matanku, ku ɗauki mahaifinku ku zo. Kada ku damu da mallakarku, gama mafi kyau na Masar za su zama naku.’ ” Sai ’ya’yan Isra’ila maza suka yi haka. Yusuf ya ba su wagonu kamar yadda Fir’auna ya umarta, ya kuma ba su guzuri don tafiyarsu. Ya ba da sababbin riguna ga kowannensu amma ga Benyamin ya ba shi shekel ɗari uku na azurfa da riguna kashi biyar. Ga kuma abin da ya aika wa mahaifinsa, jakuna goma da aka jibge da abubuwa mafi kyau na Masar, da jakuna mata guda goma ɗauke da hatsi da burodi da waɗansu tanade-tanade don tafiyarsa. Sa’an nan ya sallami ’yan’uwansa, yayinda suke barin wurin ya ce musu, “Kada ku yi faɗa a hanya!” Saboda haka suka haura, suka fita daga Masar, suka zo wurin maihaifinsu Yaƙub a ƙasar Kan’ana. Suka faɗa masa, “Yusuf yana da rai! Gaskiya, shi ne mai mulkin dukan Masar.” Gaban Yaƙub ya fāɗi, domin bai gaskata su ba. Amma sa’ad da suka faɗa masa kome da Yusuf ya faɗa musu, da kuma sa’ad da ya ga wagonun da Yusuf ya aika don a ɗauke shi a kai da shi can, sai ya farfaɗo, ya dawo cikin hankalinsa. Sai Yaƙub ya ce, “Na yarda! Ɗana Yusuf yana da rai har yanzu. Zan tafi in gan shi kafin in mutu.” Saboda haka Isra’ila ya kama hanya da dukan abin da yake nasa, sa’ad da ya kai Beyersheba, sai ya miƙa hadayu ga Allah na Ishaku, mahaifinsa. Allah kuwa ya yi magana ga Isra’ila a wahayi da dare ya ce, “Yaƙub! Yaƙub!” Yaƙub kuwa ya amsa ya ce, “Ga ni.” Sai Allah ya ce, “Ni ne Allah, Allah na mahaifinka. Kada ka ji tsoron zuwa Masar, gama zan mai da kai al’umma mai girma a can. Zan gangara zuwa Masar tare da kai, tabbatacce zan sāke dawo da kai. Kuma hannun Yusuf zai rufe idanunka.” Sa’an nan Yaƙub ya bar Beyersheba, ’ya’yan Isra’ila maza, suka ɗauki mahaifinsu Yaƙub da ’ya’yansu da matansu a cikin wagonun da Fir’auna ya aika don a kawo shi. Suka kuma ɗauki dabbobinsu da mallakarsu, da suka samu a Kan’ana, Yaƙub kuwa da dukan zuriyarsa suka tafi Masar. Ya ɗauki ’ya’yansa maza da jikokinsa da ’ya’yansa mata da jikokinsa mata, dukan zuriyarsa zuwa Masar. Waɗannan su ne sunayen ’ya’yan Isra’ila maza (Yaƙub da zuriyarsa) waɗanda suka tafi Masar, Ruben ɗan farin Yaƙub. ’Ya’yan Ruben maza su ne, Hanok, Fallu, Hezron da Karmi. ’Ya’yan Simeyon maza su ne, Yemuwel, Yamin, Ohad, Yakin, Zohar da Sha’ul ɗan mutuniyar Kan’ana. ’Ya’yan Lawi maza su ne, Gershon, Kohat da Merari. ’Ya’yan Yahuda maza su ne, Er, Onan, Shela, Ferez da Zera (amma Er da Onan sun mutu a ƙasar Kan’ana). ’Ya’yan Ferez maza su ne, Hezron da Hamul. ’Ya’yan Issakar maza su ne, Tola, Fuwa, Yoshub da Shimron. ’Ya’yan Zebulun maza su ne, Sered, Elon da Yaleyel. Waɗannan su ne ’ya’yan Liyatu maza da ta haifa wa Yaƙub a Faddan Aram, ban da ’yarsa Dina. ’Ya’yansa maza da mata duka, mutum talatin da uku ne. ’Ya’yan Gad maza su ne, Zafon, Haggi, Shuni, Ezbon, Eri, Arodi da Areli. ’Ya’yan Asher maza su ne, Imna, Ishba, Ishbi da Beriya. ’Yar’uwarsu ita ce Sera. ’Ya’yan Beriya maza su ne, Heber da Malkiyel. Waɗannan su ne ’ya’yan da Zilfa ta haifa wa Yaƙub, ita ce Laban ya ba wa ’yarsa Liyatu. ’Ya’yan duka, su sha shida ne. ’Ya’yan Yaƙub maza waɗanda Rahila ta haifa su ne, Yusuf da Benyamin. A Masar, Asenat ’yar Fotifera, firist na On ta haifi Manasse da Efraim wa Yusuf. ’Ya’yan Benyamin maza su ne, Bela, Beker, Ashbel, Gera, Na’aman, Ehi, Rosh, Muffim, Huffim da Ard. Waɗannan su ne ’ya’yan Rahila maza waɗanda ta haifa wa Yaƙub, dukansu mutum goma sha huɗu ne. Yaron Dan shi ne, Hushim. ’Ya’yan Naftali maza su ne, Yazeyel, Guni, Yezer da Shillem. Waɗannan su ne ’ya’ya mazan da Bilha ta haifa wa Yaƙub, ita ce Laban ya ba wa ’yarsa Rahila. ’Ya’yan suka su bakwai ne. Dukan waɗanda suka tafi Masar tare da Yaƙub, waɗanda suke zuriyarsa kai tsaye ban da matan ’ya’yansa maza, su mutum sittin da shida ne. In aka haɗa da ’ya’yan nan maza guda biyu waɗanda aka haifa wa Yusuf a Masar, membobin iyalin Yaƙub, waɗanda suka tafi Masar, duka su saba’in ne. To, Yaƙub ya aiki Yahuda yă yi gaba yă sadu da Yusuf, don yă nuna musu hanyar da za su bi zuwa yankin Goshen. Da suka isa yankin Goshen, sai Yusuf ya kintsa keken yaƙinsa ya haura zuwa Goshen don yă taryi mahaifinsa, Isra’ila. Nan da nan da isowar Yusuf a wurin mahaifinsa, sai ya rungumi mahaifinsa, ya yi kuka na dogon lokaci. Isra’ila ya ce wa Yusuf, “Yanzu ina a shirye in mutu, da yake na gani da kaina cewa har yanzu kana da rai.” Sa’an nan Yusuf ya ce wa ’yan’uwansa da gidan mahaifinsa, “Zan haura in yi magana da Fir’auna, zan kuwa ce masa, ‘’Yan’uwana da gidan mahaifina, waɗanda suke zaune a ƙasar Kan’ana, sun zo wurina. Mutanen fa, makiyaya ne; suna kiwon dabbobi, sun kuma zo tare da garkunansu da shanunsa da kuma kome da suka mallaka.’ Sa’ad da Fir’auna ya kira ku ciki, ya yi tambaya, ‘Mece ce sana’arku?’ Ku amsa, ‘Bayinka suna kiwon dabbobi ne, tun muna samari har zuwa yanzu, kamar yadda kakanninmu suka yi.’ Ta haka za a bar ku ku zauna a yankin Goshen, gama Masarawa suna ƙyamar makiyaya.” Yusuf ya tafi yă faɗa wa Fir’auna, “Mahaifina da ’yan’uwana, tare da garkunansu da shanunsu da kome da suke da shi, sun zo daga ƙasar Kan’ana, suna kuwa a Goshen yanzu.” Sai ya zaɓi mutum biyar daga cikin ’yan’uwansa, ya gabatar da su a gaban Fir’auna. Fir’auna ya tambayi ’yan’uwan, “Mece ce sana’arku?” Suka amsa wa Fir’auna suka ce, “Bayinka makiyaya ne, kamar yadda kakanninmu suke.” Suka kuma ce masa, “Mun zo, mu zauna a nan na ɗan lokaci, gama yunwa ta yi tsanani a Kan’ana, dabbobin bayinka kuma ba su da wurin kiwo. Saboda haka yanzu, muna roƙonka, bari bayinka su zauna a Goshen.” Fir’auna ya ce wa Yusuf, “Mahaifinka da ’yan’uwanka sun zo maka, ƙasar Masar kuma tana gabanka, ka zaunar da mahaifinka da ’yan’uwanka a sashe mafi kyau na ƙasar, bari su zauna a Goshen. Idan kuma ka ga waɗansu a cikinsu da suka fi dacewa, sai ka sa su lura mini da shanuna.” Sa’an nan Yusuf ya shigar da Yaƙub mahaifinsa, ya gabatar da shi a gaban Fir’auna. Bayan Yaƙub ya albarkaci Fir’auna, sai Fir’auna ya tambaye shi, “Shekarunka nawa da haihuwa?” Yaƙub kuwa ya ce wa Fir’auna, “Shekarun hijirata, shekaru ɗari da talatin ne. Shekaruna kaɗan ne cike da wahala, ba za a kuwa daidaita su da shekarun hijirar kakannina ba.” Sai Yaƙub ya albarkaci Fir’auna, ya yi masa bankwana, sa’an nan ya fita. Ta haka Yusuf ya zaunar da mahaifinsa da ’yan’uwansa a Masar, ya ba su mallaka a sashe mafi kyau na ƙasar, a yankin nan na Rameses, kamar yadda Fir’auna ya umarta. Yusuf ya kuma tanada wa mahaifinsa da kuma ’yan’uwansa da dukan gidan mahaifinsa, abinci bisa ga yawan ’ya’yansu. A yanzu, a cikin ƙasar duka, ba abinci, gama yunwa ta yi tsanani ƙwarai, har ƙasar Masar da ƙasar Kan’ana suka shiga matsananciyar wahala! Yusuf ya tattara dukan kuɗaɗen da suke a Masar da Kan’ana don biyan hatsin da suke saya, ya kuwa kawo su a fadan Fir’auna. Sa’ad da kuɗin mutanen Masar da Kan’ana suka ƙare, dukan Masar ta zo wurin Yusuf ta ce, “Ka ba mu abinci. Me zai sa mu mutu a idanunka? Kuɗinmu duk sun ƙare.” Yusuf ya ce, “To, ku kawo dabbobinku, zan sayar muku da abinci a madadin dabbobinku, tun da kuɗinku ya ƙare.” Saboda haka suka kawo dabbobinsu wa Yusuf, ya kuma ba su abinci a madadin dawakai, tumaki da awaki, shanu da jakunansu. Ya kuwa ba su abinci a madadin dabbobinsu, a wannan shekara. Sa’ad da wannan shekara ta ƙare, sai suka zo wurinsa a shekara ta biye suka ce, “Ba za mu ɓoye maka ba ranka yă daɗe, kuɗinmu sun ƙare, dabbobinmu kuma sun zama naka. Ranka yă daɗe, in ban da jikunanmu da gonakinmu, ba abin da ya rage mana. Kada ka bar mu mu mutu, ka yi wata dabara! Kada ka bari mu rasa gonakinmu. Ka musaye mu da abinci, mu da gonakinmu. Mu kuwa za mu zama bayin Fir’auna. Ka ba mu iri don mu rayu, kada mu mutu, don kuma kada gonakin ƙasarmu su zama kango.” Ta haka Yusuf ya saya wa Fir’auna ƙasar Masar duka, gama Masarawa duka sun sayar da gonakinsu, saboda yunwa ta tsananta musu. Ƙasar ta zama mallakar Fir’auna. Yusuf kuwa ya mai da mutanen bayi, daga wannan iyakar Masar zuwa wancan. Amma bai sayi gonakin firistoci ba, gama suna karɓa rabo daga Fir’auna ne, suna kuma da isashen abinci daga rabon da Fir’auna yake ba su. Dalilin ke nan da ba su sayar da gonakinsu ba. Yusuf ya ce wa mutane, “Yanzu da na saye ku da kuma gonakinku a yau wa Fir’auna, ga iri don ku shuka a gonaki. Amma sa’ad da hatsi suka nuna, za ku ba da kashi ɗaya bisa biyar ga Fir’auna. Sauran kashi huɗu bisa biyar kuma ku riƙe a matsayin iri don gonaki da kuma abinci wa kanku da gidajenku da kuma ’ya’yanku.” Suka ce, “Ka ceci rayukanmu, in ya gamshe ka, ranka yă daɗe, za mu zama bayin Fir’auna.” Ta haka Yusuf ya kafa wannan ya zama doka game da ƙasa a Masar, har yă zuwa yau cewa kashi ɗaya bisa biyar na amfani gona ya zama na Fir’auna. Gonakin firistoci ne kaɗai ba su zama na Fir’auna ba. To, Isra’ilawa suka zauna a Masar a yankin Goshen. Suka mallaki filaye a can, suka riɓaɓɓanya suka ƙaru ƙwarai. Yaƙub ya yi zama a Masar shekaru goma sha bakwai, yawan shekarunsa duka sun zama ɗari da arba’in da bakwai. Sa’ad da lokaci ya gabato da Isra’ila zai mutu, sai ya kira ɗansa Yusuf, ya ce masa, “Ka yi mini wannan alheri, ka sa hannunka ƙarƙashin cinyar ƙafata, ka yi mini alkawari saboda ina roƙonka kaɗa ka bizne ni a Masar, amma sa’ad da na huta da kakannina, ka ɗauke ni, ka fid da ni daga Masar, ka binne ni a inda aka binne su.” Yusuf ya ce, “Zan yi yadda ka faɗa.” Yaƙub ya ce, “Ka rantse mini.” Sai Yusuf ya rantse masa, Isra’ila kuwa ya yi godiya ga Allah yayinda ya jingina a kan sandansa. Bayan wani lokaci aka faɗa wa Yusuf, “Mahaifinka yana ciwo.” Sai ya ɗauki ’ya’yansa maza biyu, Manasse da Efraim suka tafi tare da shi. Sa’ad da aka faɗa wa Yaƙub, “Ɗanka Yusuf ya zo gare ka,” sai Isra’ila ya ƙoƙarta ya tashi ya zauna a kan gado. Yaƙub ya ce wa Yusuf, “Allah Maɗaukaki ya bayyana gare ni a Luz a ƙasar Kan’ana, a can ya albarkace ni ya kuma ce mini, ‘Zan sa ka yi ta haihuwa ka kuma riɓaɓɓanya, za ka ƙaru a yawa. Zan mai da kai al’ummar mutane, zan kuma ba ka wannan ƙasa tă zama madawwamiyar mallaka ga zuriyarka a bayanka.’ “To, yanzu, ’ya’ya mazanka biyu da aka haifa maka a Masar kafin in zo a nan za su zama nawa; Efraim da Manasse za su zama nawa, kamar yadda Ruben da Simeyon suke nawa. Duk waɗansu ’ya’yan da aka haifa maka bayansu za su zama naka; a yankin da suka gāda za a lissafa a ƙarƙashin sunayen ’yan’uwansu. Yayinda nake dawowa daga Faddan Aram, cikin baƙin cikina Rahila ta rasu a ƙasar Kan’ana yayinda muke kan hanya, ’yar rata daga Efrata. Saboda haka na binne ta a can kusa da hanya zuwa Efrata” (wato, Betlehem). Sa’ad da Isra’ila ya ga ’ya’yan Yusuf maza, sai ya yi tambaya, “Su wane ne waɗannan?” Yusuf ya ce wa mahaifinsa, “Su ne ’ya’yan da Allah ya ba ni a nan.” Sa’an nan Isra’ila ya ce, “Kawo mini su saboda in albarkace su.” Yanzu fa idanun Isra’ila sun fara rasa ƙarfi saboda tsufa, har ba ya iya gani sosai. Saboda haka Yusuf ya kawo ’ya’yansa maza kusa da shi, sai mahaifinsa ya sumbace su ya rungume su. Isra’ila ya ce wa Yusuf, “Ban yi tsammani zan ga fuskarka kuma ba, yanzu kuwa Allah ya bar ni in ga ’ya’yanka su ma.” Sa’an nan Yusuf ya ɗauke su daga gwiwoyin Isra’ila ya rusuna da fuskarsa har ƙasa. Yusuf ya ɗauke su biyu, Efraim a damansa zuwa hagun Isra’ila, Manasse kuma a hagunsa zuwa hannun daman Isra’ila, ya kuma kawo su kusa da shi. Amma Isra’ila ya miƙa hannun damansa ya sa shi a kan Efraim, ko da yake shi ne ƙaramin, ta wurin harɗewa hannuwansa, ya sa hannun hagunsa a kan Manasse, ko da yake Manasse ne ɗan farinsa. Sa’an nan ya albarkaci Yusuf ya ce, “Bari Allah a gaban wanda kakannina Ibrahim da Ishaku suka yi tafiya, Allahn da ya zama makiyayina dukan raina zuwa wannan rana, Mala’ikan da ya cece ni daga dukan cuta bari yă albarkaci samarin nan. Bari a kira su da sunana da sunayen kakannina Ibrahim da Ishaku bari kuma su ƙaru ƙwarai a bisa duniya.” Sa’ad da Yusuf ya ga mahaifinsa yana sa hannun damansa a kan Efraim bai ji daɗi ba; saboda haka ya ɗauke hannun mahaifinsa ya cire shi daga kan Efraim zuwa kan Manasse. Yusuf ya ce masa, “A’a, mahaifina, wannan shi ne ɗan farin; ka sa hannunka na dama a kansa.” Amma mahaifinsa ya ƙi ya ce, “Na sani, ɗana, na sani. Shi ma zai zama mutane, zai kuma zama mai girma. Duk da haka ɗan’uwansa zai zama mai girma fiye da shi, kuma zuriyarsa za tă zama ƙungiyar al’ummai.” Ya albarkace su a wannan rana ya ce, “A cikin sunanku Isra’ila zai sa wannan albarka ‘Bari Allah yă sa ku zama kamar Efraim da Manasse.’ ” Saboda haka ya sa Efraim gaban Manasse. Sa’an nan Isra’ila ya ce wa Yusuf, “Ina gab da mutuwa, amma Allah zai kasance tare da ku Kuma gare ka, a matsayi wanda yake kan ’yan’uwanka, na ba da gonar da na karɓe daga Amoriyawa da takobi da kuma bakana.” Sai Yaƙub ya kira ’ya’yansa maza ya ce, “Ku tattaru don in faɗa muku abin da zai faru gare ku, a kwanaki masu zuwa. “Ku tattaru, ku saurara, ’ya’yan Yaƙub maza; ku saurari mahaifinku, Isra’ila. “Ruben, kai ne ɗan farina, ƙarfina, alamar farko ta ƙarfina, mafi matsayi, kuma mafi iko. Mai tumbatsa kamar ruwa, amma ba za ka ƙara zama mai daraja ba, gama ka hau gadon mahaifinka ka hau kujerata, ka kuma ƙazantar da shi. “Simeyon da Lawi ’yan’uwa ne, takubansu makamai ne na tā da hankali. Ba zan shiga shawararsu ba, ba zan shiga taronsu ba, gama sun kashe maza cikin fushinsu cikin ganin dama suka kashe bijimai. La’ananne ne fushinsu, mai tsanani ne ƙwarai, hasalarsu kuwa, muguwa ce ƙwarai! Zan warwatsa su cikin Yaƙub in kuma daidaita su cikin Isra’ila. “Yahuda, ’yan’uwanka za su yabe ka; hannuwanka za su kasance a wuyan abokan gābanka, ’ya’yan mahaifinka maza za su rusuna maka. Kai ɗan zaki ne, ya Yahuda, ka dawo daga farauta, ɗana. Kamar zaki, yakan kwanta a miƙe, kamar zakanya, wa yake da ƙarfin halin tashe shi? Kursiyi ba zai tashi daga Yahuda ba, ba kuwa sandan mulki daga tsakani ƙafafunsa ba, sai ya zo ga wanda yake mai shi. Biyayyar al’umma kuwa tasa ce. Zai daure jakinsa a kuringa, aholakinsa a rassa mafi kyau; zai wanke tufafinsa cikin ruwan inabi rigunansa cikin inabi ja wur kamar jini. Idanunsa za su duhunce fiye da ruwan inabi, haƙorarsa farare kamar madara. “Zebulun zai zauna a bakin teku, yă zama tasar jiragen ruwa; iyakarsa za tă nausa zuwa Sidon. “Issakar doki mai ƙarfi, kwance tsakanin buhunan sirdi. Sa’ad da ya ga yadda wurin hutunsa yana da kyau da kuma daɗin da ƙasarsa take, zan tanƙware kafaɗarsa ga nauyi yă miƙa kai ga aikin dole. “Dan zai tanada adalci wa mutanensa kamar ɗaya cikin kabilan Isra’ila. Dan zai zama maciji a gefen hanya, kububuwa a bakin hanya, da take saran ɗiɗɗigen doki domin mahayinsa yă fāɗi da baya. “Ina zuba ido ga cetonka, ya Ubangiji. “Masu fashi za su fāɗa wa Gad, amma zai runtume su. “Abincin Asher zai zama a wadace, zai yi tanadin abinci iri-iri da suka dace don sarki. “Naftali sakakkiyar barewa ce da take haihuwar kyawawan ’ya’ya. “Yusuf kuringa ce mai ba da amfani. Kuringa mai ba da amfani kusa da rafi wadda rassanta na hawan bango. Da ɗaci rai mahara suka fāɗa masa; suka harbe shi babu tausayi. Amma bakansa yana nan daram hannuwansa masu ƙarfi ba sa jijjiguwa saboda hannun Maɗaukaki na Yaƙub, saboda Makiyayi, Dutsen Isra’ila, saboda Allah na mahaifinka, wanda ya taimake ka, saboda Maɗaukaki, wanda yake albarkace ka da albarkar sama da take bisa albarkun zurfafa da suke ƙarƙashin ƙasa albarkun mama da kuma mahaifa. Albarkun mahaifi suna da girma fiye da albarkun daɗaɗɗun duwatsu fiye da yalwar madawwaman tuddai. Bari dukan waɗannan su zauna a kan Yusuf, a goshin ɗan sarki a cikin ’yan’uwansa. “Benyamin kyarkeci ne mai kisa; da safe yakan cinye abin da ya farauto da yamma yakan raba ganima.” Dukan waɗannan su ne kabilu goma sha biyu na Isra’ila, kuma abin da mahaifinsu ya faɗa musu ke nan sa’ad da ya albarkace su, yana ba kowane albarkar da ta dace da shi. Sa’an nan ya ba su waɗannan umarnai ya ce, “Ina gab da a tara ni ga mutanena. Ku binne ni tare da kakannina a kogon da yake cikin filin Efron mutumin Hitti, kogon da yake cikin filin Makfela, kusa da Mamre a Kan’ana, wanda Ibrahim ya saya tare da filin, yă zama makabarta daga Efron mutumin Hitti. A can aka binne Ibrahim da matarsa Saratu, a can aka binne Ishaku da matarsa Rebeka, a can kuma na binne Liyatu. Filin tare da kogon da yake ciki, an saya daga Hittiyawa.” Sa’ad da Yaƙub ya gama ba da umarnan ga ’ya’yansa maza, sai ya ɗaga ƙafafunsa zuwa gado, ya ja numfashinsa na ƙarshe, aka kuwa tara shi ga mutanensa. Yusuf kuwa ya fāɗa a kan mahaifinsa, ya yi kuka a kansa, ya kuma sumbace shi. Sa’an nan Yusuf ya umarci masu maganin da suke yin masa hidima, su shafe mahaifinsa Isra’ila da maganin hana ruɓa. Saboda haka masu maganin suka shafe shi da maganin hana ruɓa. Suka ɗauki kwana arba’in cif suna yin wannan, gama kwanakin da ake bukata ke nan don shafewa da maganin hana ruɓa. Masarawa kuwa suka yi makoki dominsa kwana saba’in. Sa’ad da kwanakin makoki suka wuce, sai Yusuf ya ce wa iyalin gidan Fir’auna, “In na sami tagomashi a idanunku, ku yi magana da Fir’auna domina. Ku faɗa masa, ‘Mahaifina ya sa na yi rantsuwa, ya kuma ce, “Ina gab da mutuwa, ka binne ni a kabarin da na haƙa wa kaina a ƙasar Kan’ana.” Yanzu fa bari in haura in binne mahaifina, sa’an nan in dawo.’ ” Fir’auna ya ce, “Haura ka binne mahaifinka, kamar yadda ya sa ka rantse za ka yi.” Saboda haka Yusuf ya haura don yă binne mahaifinsa. Dukan hafsoshin Fir’auna suka yi masa rakiya tare da manyan mutanen gidan Fir’auna, da kuma dukan manyan mutanen Masar da kuma dukan membobin gidan Yusuf, da ’yan’uwansa da kuma waɗanda suke na gidan mahaifinsa. Yara kaɗai da garkunansu da kuma shanunsu ne aka bari a Goshen. Kekunan yaƙi da mahayan dawakai su ma suka haura tare da shi. Babbar ƙungiya jama’a ce ƙwarai. Sa’ad da suka kai masussukar Atad, kusa da Urdun, sai suka yi kuka da ƙarfi da kuma mai zafi, a can Yusuf ya yi makoki kwana bakwai saboda mahaifinsa. Sa’ad da Kan’aniyawa waɗanda suke zama a can suka ga makokin a masussukan Atad, sai suka ce, “Masarawa suna bikin makoki na musamman.” Shi ya sa ake kira wannan wurin da yake kusa da Urdun, Abel-Mizrayim. Haka fa ’ya’yan Yaƙub maza suka yi yadda ya umarce su. Suka ɗauke shi zuwa ƙasar Kan’ana suka kuma binne shi a kogon da yake cikin filin Makfela, kusa da Mamre, wanda Ibrahim ya saya tare da filin, ya zama makabarta daga Efron mutumin Hitti. Bayan ya binne mahaifinsa, sai Yusuf ya koma Masar, tare da ’yan’uwansa da kuma dukan waɗanda suka tafi tare da shi don binne mahaifinsa. Sa’ad da ’yan’uwan Yusuf suka ga cewa mahaifinsu ya mutu, sai suka ce, “Mai yiwuwa Yusuf yana riƙe da mu a zuciya, wataƙila zai rama dukan abubuwa marasa kyau da muka yi masa?” Saboda haka suka aika wa Yusuf suna cewa, “Mahaifinka ya bar waɗannan umarnai kafin yă rasu. Ga abin da za ku ce wa Yusuf, ‘Na roƙe ka, ka gafarta wa ’yan’uwanka zunubai da laifofin da suka aikata na abubuwa marasa kyau da suka yi maka.’ Yanzu muna roƙonka ka gafarta zunuban bayin Allah na mahaifinka.” Sa’ad da saƙonsu ya zo masa, sai Yusuf ya yi kuka. ’Yan’uwansa kuwa suka zo suka fāɗi a gabansa suka ce, “Mu bayinka ne.” Amma Yusuf ya ce musu, “Kada ku ji tsoro. Ni Allah ne? Kun yi niyya ku yi mini lahani, amma Allah ya nufe wannan ya zama alheri don yă cika abin da yanzu yake faruwa, ceton rayuka masu yawa. Saboda haka, kada ku ji tsoro. Zan tanada muku da kuma ’ya’yanku.” Ya sāke tabbatar musu, ya kuma yi musu magana ta alheri. Yusuf ya zauna a Masar tare da dukan iyalin mahaifinsa. Ya rayu shekara ɗari da goma. Ya kuma ga tsara ta uku ta ’ya’yan Efraim. Haka ma ’ya’yan Makir ɗan Manasse, an haife su aka sa a gwiwoyin Yusuf. Sai Yusuf ya ce wa ’yan’uwansa, “Ina gab da mutuwa. Amma tabbatacce Allah zai taimake ku, yă fid da ku daga wannan ƙasa zuwa ƙasar da ya alkawarta da rantsuwa wa Ibrahim, Ishaku da kuma Yaƙub.” Yusuf kuwa ya sa ’ya’yan Isra’ila maza suka yi rantsuwa, ya kuma ce, “Tabbatacce Allah zai taimake ku, ku kuma dole ku ɗauki ƙasusuwana, ku haura da su daga wannan wuri.” Yusuf kuwa ya rasu yana da shekara ɗari da goma. Bayan an shafe shi da maganin hana ruɓa, sai aka sa shi a akwatin gawa a Masar. Waɗannan su ne sunayen ’ya’yan Isra’ila maza, waɗanda suka tafi Masar tare da Yaƙub; kowanne da iyalinsa. Ruben, Simeyon, Lawi da Yahuda; Issakar, Zebulun da Benyamin; Dan da Naftali; Gad da Asher. Zuriyar Yaƙub duka sun kai mutum saba’in. Yusuf ya riga ya kasance a Masar. Yanzu Yusuf da dukan ’yan’uwansa da kuma dukan tsaran nan da suka tafi Masar, sun mutu, amma Isra’ilawa sun riɓaɓɓanya, suka kuma yi ta haihuwa sosai, suka yi yawan sosai, har ƙasar ta cika da su. Sai wani sabon sarki wanda bai san Yusuf ba, ya hau sarautar Masar. Ya ce wa mutanensa, “Duba Isra’ilawa sun yi yawa, sun fi ƙarfinmu. Ku zo, mu yi dabara a kansu, in ba haka ba za su ƙaru fiye da haka, in kuwa yaƙi ya tashi tsakaninmu da abokan gāba, za su iya haɗa kai da abokan gāba, su yaƙe mu, su bar ƙasar.” Saboda haka sai suka naɗa shugabannin gandu a kansu don su wahalshe su, su kuma bauta musu, suka sa su suka gina biranen Fitom da Rameses su zama biranen ajiya, domin Fir’auna. Amma duk da wannan ƙarin wulaƙancin da ake yi musu, su kuwa sai daɗa riɓaɓɓanya suke ta yi. Sai tsoron Isra’ilawa ya ƙaru a zuciyar Masarawa, ganin haka sai Masarawa suka ƙara musu wahala. Suka baƙanta wa Isra’ilawa rai da bauta mai wuya, ta wurin sa su yin tubali da yumɓu, da kuma kowace irin bauta a gonaki. A cikin dukan ayyukansu, Masarawa ba su ji tausayinsu ba ko kaɗan. Sai Sarkin Masar ya gaya wa ungozomomin matan Ibraniyawa, wato, su Shofra da Fuwa ya ce, “Sa’ad da kuke taimakon matan Ibraniyawa lokacin haihuwa, in jaririn namiji ne ku kashe shi, amma in ta mace ce, ku bar ta da rai.” Amma ungozomomin nan masu tsoron Allah ne, ba su kuwa aikata abin da sarkin Masar ya gaya musu ba; suka bar jarirai maza su rayu. Sai sarkin Masar ya kira ungozomomin, ya tambaye su ya ce, “Don me kuka yi haka? Don me kuka bar jarirai maza su rayu?” Ungozoman suka amsa wa Fir’auna suka ce, “Ai, matan Ibraniyawa ba kamar matan Masarawa ba ne, gwarzaye ne, sukan haihu kafin ungozomomin su kai wurinsu.” Saboda haka Allah ya nuna alheri wa ungozomomin, Isra’ilawa kuwa suka yi yawa fiye da dā. Saboda ungozomomin suna tsoron Allah, sai Allah ya ba su iyalan kansu. Sai Fir’auna ya ba da umarni wa mutanensa ya ce, “Duk yaron da yake namijin da haka haifa, dole ku jefa shi cikin kogi, amma ku bar yara mata su rayu.” Ana nan, sai wani Balawe ya auri wata Balawiya, ta kuwa yi ciki, ta haifi ɗa. Sa’ad da ta ga jaririn kyakkyawa ne, sai ta ɓoye shi har watanni uku. Amma da ba tă iya ɓoye shi kuma ba, sai ta yi kwandon kyauro ta shafa masa kwalta. Bayan haka sai ta sa jaririn a cikin kwandon, ta je ta ajiye kwandon tare da jaririn a cikin kyauro, a bakin kogin. ’Yar’uwarsa ta tsaya da ɗan rata tana lura da abin da zai faru da shi. Sai ’yar Fir’auna ta gangara zuwa kogi domin tă yi wanka, bayinta kuwa suna tafiya a bakin kogi. Sai ta ga kwandon a ciyawa, ta aiki ɗaya daga cikin masu hidimarta tă ɗauko mata. Da ta buɗe kwandon, sai ta ga yaro yana kuka, ta kuwa ji tausayinsa. Ta ce, “Wannan ɗaya daga cikin jariran Ibraniyawa ne.” Sai ’yar’uwarsa ta tambayi ’yar Fir’auna, ta ce, “In tafi in samo ɗaya daga cikin matan Ibraniyawa tă yi miki renon yaron?” Sai ta amsa ta ce, “I, tafi.” Sai yarinyar ta tafi ta kawo mahaifiyar yaron. Diyar Fir’auna ta ce mata, “Ɗauki jaririn, ki yi mini renonsa, zan kuwa biya ki.” Saboda haka ta ɗauki yaron, ta yi renonsa. Sa’ad da ya yi girma, sai ta kawo shi wajen ’yar Fir’auna, ya kuwa zama ɗanta, ta kuma ba shi suna Musa, tana cewa, “Na tsamo shi daga ruwa.” Wata rana, bayan Musa ya yi girma, sai ya haura, ya tafi inda mutanensa suke, ya kuma ga yadda suke shan wahala da aiki. Ya ga wani mutumin Masar yana dūkan mutumin Ibraniyawa, ɗaya daga cikin mutanensa. Da ya leƙa nan da can bai kuwa ga kowa ba, sai ya kashe mutumin Masar, ya ɓoye shi a yashi. Kashegari ya fita, sai ya ga Ibraniyawa biyu suna faɗa. Ya tambayi mai laifin ya ce, “Don me kake bugun ɗan’uwanka, mutumin Ibraniyawa?” Mutumin ya ce masa, “Wa ya mai da kai mai mulki da mai hukunci a kanmu? Kana so ne ka kashe ni kamar yadda ka kashe mutumin Masar nan?” Sai Musa ya tsorata, ya yi tunani ya ce, “To, fa, abin nan da na yi, ya zama sananne.” Da Fir’auna ya ji wannan, sai ya yi ƙoƙari yă kashe Musa, amma Musa ya gudu daga wajen Fir’auna, ya tafi ƙasar Midiyan inda ya zauna kusa da wata rijiya. To, fa, akwai wani firist na Midiyan, yana da ’ya’ya mata bakwai, suka zo su shayar da dabbobin mahaifinsu. Sai waɗansu makiyaya suka zo suka kore su, amma Musa ya tashi ya taimake su ya shayar da dabbobinsu. Da ’yan matan suka komo wurin Reyuwel mahaifinsu, sai ya tambaye su ya ce, “Yaya kuka dawo da wuri yau?” Suka amsa suka ce, “Wani mutumin Masar ne ya taimake mu daga hannun waɗansu makiyaya. Har ma ya ɗebo ruwa ya shayar da dabbobin.” Ya tambayi ’yan matansa, “To ina yake? Don me kuka bar shi a can? A gayyace shi, yă zo, yă ci wani abu.” Musa ya yarda yă zauna da mutumin wanda ya ba da ’yarsa Ziffora aure da Musa. Ziffora ta haifi wa Musa ɗa, ya kuma raɗa masa suna Gershom cewa, “Na zama baƙo a baƙuwar ƙasa.” Ana nan dai, a kwana a tashi, sai sarkin Masar ya mutu. Isra’ilawa suka yi kuka mai zafi saboda bautarsu mai wuya, sai kukar neman taimakonsu saboda bauta, ya kai wurin Allah. Allah kuwa ya ji kukansu sai ya tuna da alkawarinsa da Ibrahim da Ishaku da Yaƙub. Sai Allah ya dubi Isra’ilawa, ya kuma damu da su. Ana nan wata rana Musa yana kiwon tumakin Yetro surukinsa, firist na Midiyan, sai ya bi da tumaki zuwa gefe mai nisa a cikin hamada, har ya zo Horeb, dutsen Allah. A can mala’ikan Ubangiji ya bayyana a gare shi cikin harshen wuta, a ƙaramin itace. Musa ya lura cewa ko da yake wuta na ci ƙaramin itacen, amma bai ƙone ba. Sai Musa ya ce, “Wannan abin mamaki ne, don me wannan itace bai ƙone ba? Bari in matso kusa in gani.” Da Ubangiji ya ga Musa ya matso don yă duba, sai Allah ya yi kira daga cikin ƙaramin itacen ya ce, “Musa! Musa!” Sai Musa ya amsa ya ce, “Ga ni.” Allah ya ce, “Kada ka zo kusa, tuɓe takalmanka, gama inda kake tsaye, wuri ne mai tsarki.” Sai Allah ya ce, “Ni ne Allah na kakanninka, Allah na Ibrahim, Allah na Ishaku da kuma Allah na Yaƙub.” Da jin wannan, sai Musa ya ɓoye fuskarsa, domin ya ji tsoro yă dubi Allah. Ubangiji ya ce, “Tabbatacce na ga azabar mutanena a Masar. Na ji su suna kuka saboda matsin da shugabannin gandunsu suke musu, na kuma damu da wahalarsu. Saboda haka na sauko domin in cece su daga hannun Masarawa, in kuma fitar da su daga ƙasar Masar, in kai su ƙasa mai kyau mai fāɗi, ƙasa mai zub da madara da zuma, inda Kan’aniyawa, Hittiyawa, Amoriyawa, Ferizziyawa, Hiwiyawa da Yebusiyawa suke. Yanzu kukan Isra’ilawa ya kai gare ni, na kuma ga yadda Masarawa suke wulaƙanta su To, fa, sai ka tafi. Ina aikan ka wurin Fir’auna don ka fitar da mutanena Isra’ilawa daga Masar.” Amma Musa ya ce wa Allah, “Wane ni in tafi wurin Fir’auna, in kuma fitar da Isra’ilawa daga Masar?” Sai Allah ya ce, “Zan kasance da tare kai. Wannan kuwa za tă zama alama a gare ka cewa Ni na aike ka. Bayan ka fitar da mutanen daga Masar, za ku yi sujada ga Allah a kan dutsen nan.” Musa ya ce wa Allah, “A ce ma na tafi wurin Isra’ilawa na ce musu, ‘Allah na kakanninku ya aiko ni wurinku,’ in suka tambaye ni, ‘Mene ne sunansa?’ Me zan ce?” Allah ya ce wa Musa, “NI NE wanda NINE. Abin da za ka faɗa wa Isra’ilawa ke nan cewa, ‘NI NE, ya aiko ni wurinku.’ ” Allah ya kuma ce wa Musa, “Ka faɗa wa Isra’ilawa, ‘ Ubangiji, Allah na kakanninka, Allah na Ibrahim, Allah na Ishaku da kuma Allah na Yaƙub, ya aiko ni wurinku.’ Wannan shi ne sunana har abada, sunan da za a tuna da ni daga tsara zuwa tsara ke nan. “Tafi ka tattara dattawan Isra’ila, ka ce musu, ‘ Ubangiji, Allah na kakanninku, Allah na Ibrahim, Ishaku da Yaƙub, ya bayyana a gare ni ya ce, Na lura da ku, na kuma ga abubuwan da ake yi muku a Masar. Na kuma yi alkawari, zan fitar da ku daga azabarku a Masar zuwa ƙasar Kan’aniyawa, Hittiyawa, Amoriyawa, Ferizziyawa, Hiwiyawa da Yebusiyawa, ƙasa mai zub da madara da zuma.’ “Dattawan Isra’ila za su saurare ka. Sa’an nan da kai da dattawan Isra’ila, za ku tafi wurin sarkin Masar, ku ce masa, ‘ Ubangiji, Allah na Ibraniyawa, ya sadu da mu. Bari mu yi tafiyar kwana uku zuwa cikin hamada domin mu yi hadaya wa Ubangiji Allahnmu.’ Amma na san cewa sarkin Masar ba zai yarda ku tafi ba, sai hannu mai ƙarfi ya tilasta shi. Saboda haka zan miƙa hannuna in bugi Masarawa da duk al’ajaban da zan aikata a cikinsu. Bayan haka zai bar ku, ku tafi. “Zan kuma sa mutanen su sami tagomashi daga wurin Masarawa, saboda sa’ad da za ku fita, ba za ku fita hannu wofi ba. Kowace mace ta tambayi maƙwabciyarta, da kuma duk wata macen da take cikin gidanta, kayayyakin azurfa da na zinariya da kuma na riguna, waɗanda za ku sa wa ’ya’yanku maza da mata. Ta haka nan za ku washe Masarawa.” Musa ya amsa ya ce, “In ba su gaskata ni ba, suka kuma ce, ‘ Ubangiji bai bayyana gare ka ba fa’?” Sai Ubangiji ya ce, “Mene ne wannan a hannunka?” Musa ya amsa ya ce, “Sanda.” Sai Ubangiji ya ce, “Jefa shi ƙasa.” Musa ya jefa shi ƙasa, sai sandan ya zama maciji, Musa kuwa ya gudu daga gare shi. Sai Ubangiji ya ce masa, “Sa hannunka ka ɗauke shi ta wutsiya.” Sai Musa ya miƙa hannu, ya kama macijin, macijin kuwa ya dawo sanda a hannunsa. Ubangiji ya ce, “Wannan zai sa su ba da gaskiya cewa Ubangiji, Allah na kakanninsu, Allah na Ibrahim, Allah na Ishaku, da kuma Allah da Yaƙub, ya bayyana gare ka.” Sa’an nan Ubangiji ya ce, “Sa hannunka cikin rigarka.” Sai Musa ya sa hannunsa cikin rigarsa, sa’ad da ya fitar da shi, sai hannun ya a kuturce fari fat, kamar ƙanƙara. Sai Ubangiji ya ce, “Yanzu, mayar da hannunka a rigarka.” Sai Musa ya sa hannunsa cikin rigarsa, da ya fitar da shi, sai hannun ya koma kamar sauran jikinsa. Sa’an nan Ubangiji ya ce, “In ba su gaskata ba, ko kuma ba su kula da mu’ujiza ta fari ba, wataƙila su gaskata da ta biyun. Amma in ba su gaskata mu’ujizan nan biyu ba, ko kuwa ba su saurare ka ba, sai ka ɗibo ruwa daga Nilu, ka zuba a busasshiyar ƙasa. Ruwan da ka ɗebo daga kogin zai zama jini a ƙasar.” Musa ya ce wa Ubangiji, “Ya Ubangiji, ni ban mai iya magana ba ne, ban taɓa iya ba, ko a yanzu ma, bayan ka yi magana da ni, gama ni mai nauyin baki ne, mai nauyin harshe kuma.” Ubangiji ya ce masa, “Wa ya ba mutum bakinsa? Wa yake maishe shi kurma ko bebe? Wa yake ba shi gani ko yă makanta shi? Ashe ba Ni Ubangiji ba ne? Yanzu tafi, zan taimake ka ka yi magana, zan kuma koya maka abin da za ka faɗa.” Amma Musa ya ce, “Ya Ubangiji, ina roƙonka, ka nemi wani ka aika.” Sai Ubangiji ya yi fushi da Musa ya ce, “Ɗan’uwanka Haruna Balawe, ba ya nan ne? Na san ya iya magana. Ya riga ya kama hanya don yă sadu da kai, zai kuma yi farin ciki sa’ad da ya gan ka. Za ka yi masa magana. Ka kuma sa masa maganata a baki; zan kuma taimake ku magana, in koya muku abin da za ku yi. Zai yi magana da mutane a madadinka, zai zama kamar bakinka, kai kuwa kamar Allah a gare shi. Amma ka ɗauki wannan sanda a hannunka domin yă aikata mu’ujizan.” Sai Musa ya koma wurin Yetro surukinsa, ya ce masa, “Bari in koma wurin mutanena a Masar, in ga ko da mai rai a cikinsu.” Yetro ya ce, “Tafi, ka kuma sauka lafiya.” Ubangiji ya riga ya gaya wa Musa a Midiyan, “Koma Masar, domin dukan mutanen da suke neman su kashe ka sun mutu.” Sai Musa ya ɗauki matarsa da ’ya’yansa maza, ya sa su a kan jaki, suka kama hanya zuwa Masar. Ya kuma ɗauki sandan Allah a hannunsa. Ubangiji ya ce wa Musa, “Bayan ka koma Masar, ka tabbata ka aikata dukan mu’ujizan da na sa cikin ikonka a gaban Fir’auna. Amma zan taurare zuciyarsa domin kada yă bar mutanen su tafi. Sa’an nan ka gaya wa Fir’auna, ‘Ga abin da Ubangiji ya ce; Isra’ila shi ne ɗan farina, na gaya maka, “Ka bar ɗana yă tafi domin yă yi mini sujada.” Amma ka ƙi ka bari yă tafi, saboda haka zan kashe ɗan farinka.’ ” Ya zama kuwa sa’ad da Musa yake masauki a kan hanya sai Ubangiji ya gamu da shi, ya nema ya kashe shi. Amma Ziffora ta ɗauki dutsen ƙanƙara mai ci, ta yanke loɓar ɗanta ta taɓa ƙafafun Musa da shi. Ta ce, “Tabbatacce kai angon jini ne a gare ni.” Sai Ubangiji ya ƙyale shi. (A lokacin ta ce “angon jini,” tana nufin kaciya.) Ubangiji ya ce wa Haruna, “Tafi cikin hamada ka sadu da Musa.” Sai ya sadu da Musa a dutsen Allah, ya sumbace shi. Sai Musa ya gaya wa Haruna dukan abin da Ubangiji ya aike yă faɗa, da kuma dukan mu’ujizan da ya umarce shi yă aikata. Musa da Haruna suka tattara dukan dattawan Isra’ilawa, sai Haruna ya gaya musu dukan abin da Ubangiji ya ce wa Musa. Ya kuma aikata mu’ujizan a gaban mutanen, sai suka gaskata. Sa’ad da suka ji cewa Ubangiji ya damu da su, ya kuma ga azabarsu, sai suka durƙusa suka yi sujada. Daga bisani sai Musa da Haruna suka tafi wurin Fir’auna suka ce, “Ga abin da Ubangiji, Allah na Isra’ila ya ce, ‘Bari mutanena su tafi domin su yi mini biki a hamada.’ ” Fir’auna ya ce, “Wane ne Ubangiji da zan yi biyayya da shi, har in bar Isra’ila su tafi? Ban san Ubangiji ba, kuma ba zan bar Isra’ila su tafi ba.” Sai suka ce, “Allah na Ibraniyawa ya sadu da mu. Yanzu bari mu ɗauki tafiyar kwana uku cikin hamada domin mu miƙa hadaya ga Ubangiji Allahnmu, don kada yă buga mu da annoba ko takobi.” Amma sarkin Masar ya ce wa, “Musa da Haruna, don me kuke hana mutane yin aikinsu? Ku koma wurin aikinku!” Sa’an nan Fir’auna ya ce, “Ga shi mutane sun yi yawa a ƙasar Masar, ku kuma yanzu kuna so ku hana su yin aiki.” A wannan rana Fir’auna ya ba da wannan umarni wa shugabannin masu gandu, “Kada ku ƙara ba wa mutanen ciyawar tattaka domin su yi tubula, bari su tafi su tattara tattaka da kansu. Ku kuma bukace su su yi tubula daidai yawan tubalin da suka saba yi, kada ku rage. Ragwaye ne, shi ya sa suke kuka cewa, ‘Bari mu tafi mu yi hadaya ga Allahnmu.’ Ku sa waɗannan mutane su yi aiki mai tsanani sosai, don kada su sami zarafin kasa kunne ga maganganun ƙarya.” Sai shugabannin masu aikin gandu suka fita suka gaya wa mutanen Isra’ila, “Ga abin da Fir’auna ya ce, ‘Ba zan ƙara ba ku tattaka ba. Ku tafi ku nemo wa kanku tattaka duk inda za ku samu, amma ba za a rage aikinku ba ko kaɗan.’ ” Saboda haka mutane suka warwatsu ko’ina a Masar domin tattara bunnun da za su yi amfani da su, maimakon tattaka. Shugabannin gandu suka dinga matsa musu suna cewa, “Ku cika aikin da aka bukace ku na kowace rana kamar yadda kuke yi sa’ad da kuke da tattaka.” Manyan Isra’ilawa waɗanda shugabannin gandun Fir’auna suka naɗa, suka sha dūka, aka kuma yi musu tambayoyi ana cewa, “Don me ba ku cika yawan tubula na jiya da na yau kamar yadda kuka saba ba?” Sai manyan Isra’ila masu bi da aikin gandu suka tafi wurin Fir’auna suka yi roƙo suna cewa, “Don me kake yi wa bayinka haka? Ba a ba wa bayinka tattaka, duk da haka ana ce mana, ‘Ku yi tubula!’ Ana wa bayinka dūka, amma fa laifin na mutanenka ne.” Fir’auna ya ce, “Ku ragwaye ne! Shi ya sa kuke cewa, ‘Bari mu tafi mu yi hadaya wa Ubangiji.’ Ku ɓace yanzu daga nan, ku koma wurin aikinku. Ba za a ba ku tattaka ba, kuma dole ku fid da tubula kamar yadda kuka saba.” Manyan Isra’ilawa da suke bi da aikin gandu suka gane cewa sun shiga uku, sa’ad da aka gaya musu, “Ba za ku rage yawan tubulan da aka bukace ku ku yi na kowace rana ba.” Da suka bar Fir’auna, sai suka sadu da Musa da Haruna suna jira su sadu da su, sai suka ce, “Bari Ubangiji yă duba, yă kuma hukunta ku! Kun maishe mu abin ƙyama ga Fir’auna da bayinsa, kuka kuma sa musu takobi a hannunsu don su kashe mu.” Musa ya koma wurin Ubangiji ya ce, “Ya Ubangiji, don me ka kawo wahala a kan mutanen nan? Abin da ya sa ka aiko ni ke nan? Gama tun da na tafi wurin Fir’auna, na yi masa magana da sunanka, sai ya fara gasa wa mutanen nan azaba, ba ka kuma ceci mutanenka.” Sa’an nan Ubangiji ya ce wa Musa, “Yanzu za ka gan abin da zan yi da Fir’auna. Zan sa shi dole yă bar su su tafi, har ma yă iza ƙyeyarsu don su bar ƙasarsa!” Allah ya kuma ce wa Musa, “Ni ne Ubangiji. Na bayyana ga Ibrahim, ga Ishaku da kuma ga Yaƙub a matsayin Allah Maɗaukaki, amma sunan nan nawa Ubangiji, ban bayyana kaina a gare su ba. Na kuma kafa alkawari da su don in ba su ƙasar Kan’ana, inda suka yi zaman baƙunci. Ban da haka ma, na ji nishe-nishen Isra’ilawa, waɗanda Masarawa suka bautar, na kuma tuna da alkawarina. “Saboda haka, ka ce wa Isra’ilawa, ‘Ni ne Ubangiji, zan kuma fitar da ku daga bauta ta Masarawa. Zan ’yantar da ku daga zama bayinsu, da ƙarfina zan fanshe ku, in kawo hukunci mai zafi a kansu, don in cece ku. Zan ɗauke ku tamƙar mutanena, in kuma zama Allahnku. Sa’an nan za ku sani Ni ne Ubangiji Allahnku, wanda ya fitar da ku daga wahalar Masarawa. Zan kuwa kawo ku a ƙasar da na rantse da hannun da na ɗaga sama, cewa zan ba wa Ibrahim, wa Ishaku, da kuma wa Yaƙub. Zan ba da ita gare ku gādo. Ni ne Ubangiji.’ ” Musa ya faɗa wa Isra’ilawa wannan magana, amma ba su kasa kunne a gare shi ba, don ɓacin rai saboda tsananin aikin bauta. Sa’an nan Ubangiji ya ce wa Musa, “Koma ka ce wa Fir’auna sarkin Masar, yă bar Isra’ilawa su fita daga ƙasarsa.” Amma Musa ya ce wa Ubangiji, “In Isra’ilawa ba su ji ni ba, yaya Fir’auna zai ji ni, da yake ina magana da ƙyar?” Ubangiji ya yi magana da Musa da Haruna game da Isra’ilawa da Fir’auna sarkin Masar, ya umarce su su fitar da Isra’ilawa daga Masar. Waɗannan su ne shugabannin iyalansu. ’Ya’yan Ruben maza ɗan farin Isra’ila su ne, Hanok da Fallu, Hezron da Karmi. Waɗannan su ne dangin Ruben. ’Ya’yan Simeyon maza su ne, Yemuwel, Yamin, Ohad, Yakin, Zohar da Sha’ul ɗan mutuniyar Kan’ana. Waɗannan su ne dangin Simeyon. Waɗannan su ne sunayen ’ya’yan Lawi maza bisa ga abin da aka rubuta, Gershon, Kohat da Merari. Lawi ya yi shekara 137. ’Ya’yan Gershon maza, bisa ga dangi su ne, Libni da Shimeyi. ’Ya’yan Kohat maza, su ne, Amram, Izhar, Hebron da Uzziyel. Kohat ya yi shekara 133. ’Ya’yan Merari maza, su ne, Mali da Mushi. Waɗannan su ne dangin Lawi bisa ga abin da aka rubuta. Amram ya auri ’yar’uwar mahaifinsa Yokebed, wadda ta haifa masa Haruna da Musa. Amram ya yi shekara 137. ’Ya’yan Izhar maza, su ne, Kora, Nefeg da Zikri. ’Ya’yan Uzziyel maza, su ne, Mishayel, Elzafan da Sitri. Haruna ya auri Elisheba, ’yar Amminadab, ’yar’uwar Nashon, sai ta haifa masa Nadab da Abihu, Eleyazar da Itamar. ’Ya’yan Kora maza, su ne, Assir, Elkana da Abiyasaf. Waɗannan su ne dangin Kora. Eleyazar ɗan Haruna, ya auri ɗaya daga cikin ’yan matan Futiyel, sai ta haifa masa Finehas. Waɗannan su ne shugabannin iyalan Lawi, dangi, dangi. Wannan Haruna da Musa ne, waɗanda Ubangiji ya yi musu magana ya ce, “Ku fitar da Isra’ilawa daga Masar ɓangare-ɓangare.” Su ne suka yi magana da Fir’auna sarkin Masar game da fitar da Isra’ilawa daga Masar, wannan Musa da Haruna. Ana nan, sa’ad da Ubangiji ya yi magana da Musa a Masar, ya ce masa, “Ni ne Ubangiji. Sai ka faɗa wa Fir’auna sarkin Masar kome da na faɗa maka.” Amma Musa ya ce wa Ubangiji, “Ni mai nauyin baki ne, ina magana da ƙyar, ƙaƙa Fir’auna zai kasa kunne gare ni?” Sai Ubangiji ya ce wa Musa, “Duba, na maishe ka kamar Allah ga Fir’auna, ɗan’uwanka Haruna kuma zai zama annabinka. Za ka faɗi kome da na umarce ka, ɗan’uwanka Haruna kuwa zai faɗa wa Fir’auna, yă bar Isra’ilawa su fita daga ƙasarsa. Amma zan taurare zuciyar Fir’auna, kuma ko da na ninka mu’ujizai da kuma alamu a Masar, ba zai saurare ku ba. Don haka zan miƙa hannuna a kan Masar, in murƙushe ta da bala’i iri-iri, bayan haka zan fitar da taron mutanen Isra’ila daga ƙasar Masar ta wurin hukuntaina masu girma. Masarawa kuwa za su san cewa ni ne Ubangiji sa’ad da na miƙa hannuna a kan Masar, na kuma fitar da Isra’ilawa daga gare ta.” Musa da Haruna suka aikata yadda Ubangiji ya umarce su. Musa yana da shekara tamanin da haihuwa, Haruna kuma yana da shekara tamanin da uku, sa’ad da suka yi magana da Fir’auna. Ubangiji ya ce wa Musa da Haruna, “Sa’ad da Fir’auna ya ce muku, ‘Aikata wani al’ajabi,’ sai ka ce wa Haruna, ‘Ɗauki sandanka ka jefa shi a ƙasa, a gaban Fir’auna,’ zai kuwa zama maciji.” Sai Musa da Haruna suka tafi wurin Fir’auna, suka yi yadda Ubangiji ya umarce su. Haruna ya jefa sandansa ƙasa, a gaban Fir’auna da bayinsa, sai sandan ya zama maciji. Fir’auna kuwa ya kira masu hikima da masu sihiri, sai bokayen Masarawa ma suka yi irin abubuwan nan da bokancinsu. Kowannensu ya jefa sandansa ƙasa, ya kuwa zama maciji. Amma sandan Haruna ya haɗiye sandunansu. Duk da haka zuciyar Fir’auna ta taurare, bai kuwa saurare su ba, kamar dai yadda Ubangiji ya riga ya faɗa. Sa’an nan Ubangiji ya ce wa Musa, “Zuciyar Fir’auna taurariya ce, ya ƙi yă bar mutanen su tafi. Ka je wurin Fir’auna da safe, yayinda za shi kogi. Ka jira a bakin Nilu don ka sadu da shi, ka ɗauki sandan nan da ya canja zuwa maciji a hannunka. Sa’an nan ka ce masa, ‘ Ubangiji, Allah na Ibraniyawa, ya aiko ni in faɗa maka, Ka bar mutanena su tafi domin su yi mini sujada a hamada. Amma har yanzu ba ka yi biyayya ba. Ga abin da Ubangiji ya ce, da wannan za ka san cewa ni ne Ubangiji. Da sandan da yake hannuna zan bugi ruwan Nilu, zai kuma zama jini. Kifi a ciki Nilu za su mutu, ruwan kuma zai yi ɗoyi; Masarawa ba za su iya shan ruwansa ba.’ ” Ubangiji ya ce wa Musa, “Ka ce wa Haruna, ‘Ka ɗauki sandanka, ka miƙa hannunka kan ruwan Masar, kan kogunansu da rafuffukansu da kududdufansu da kuma dukan tafkunansu, za su zama jini.’ Jini zai kasance ko’ina a Masar, har ma a cikin abubuwan ajiyar ruwansu da aka yi da itace da kuma dutse.” Musa da Haruna suka yi yadda Ubangiji ya umarta. Ya ɗaga sandansa a gaban Fir’auna da bayinsa, ya bugi ruwan Nilu, dukan ruwan kuwa ya zama jini. Kifin da suke cikin Nilu suka mutu, kogin kuwa ya yi wari sosai yadda Masarawa ba su iya shan ruwan ba. Jini ya bazu ko’ina a Masar. Amma bokayen Masar ma suka yi abubuwan nan da sihirinsu, sai zuciyar Fir’auna ta taurare; bai saurari Musa da Haruna ba, kamar dai yadda Ubangiji ya riga ya faɗa. A maimakon yă saurara, sai ya juya ya koma fadarsa, bai ma damu da abin da aka yi ba. Sai dukan Masarawa suka yi ta tonon gefen Nilu don su sami ruwan sha, domin ba su iya shan ruwan kogin ba. Kwana bakwai suka wuce bayan da Ubangiji ya bugi kogin. Sa’an nan Ubangiji ya ce wa Musa, “Ka je wurin Fir’auna, ka ce masa, ‘Ga abin da Ubangiji yana cewa, ka bar mutanena su tafi domin su yi mini sujada. In ka ƙi barinsu, zan hore ka da annoban kwaɗi a dukan ƙasarka. Nilu zai cika da kwaɗi. Za su haura zuwa cikin fadanka da kan gadonka, cikin gidajen bayinka da kan mutanenka, cikin kwanonin toye-toyenka da na cin abincinka. Kwaɗin nan za su yi ta tsalle a kanka, da kan mutanenka, da kuma kan dukan bayinka.’ ” Sai Ubangiji ya ce wa Musa, “Ka ce wa Haruna, ‘Ka miƙa hannunka da sandanka bisa koguna da rafuffuka da kuma kududdufai, ka sa kwaɗi su fito su mamaye ƙasar Masar.’ ” Sai Haruna ya miƙa hannunsa bisa ruwan Masar, kwaɗi kuwa suka fito, suka mamaye ƙasar Masar. Amma bokaye ma suka yi abubuwan nan ta wurin sihirinsu; suka sa kwaɗi suka fito suka mamaye ƙasar Masar. Fir’auna ya kira Musa da Haruna ya ce, “Yi addu’a ga Ubangiji yă ɗauke kwaɗi daga gare ni da mutanena, zan kuwa bar mutanenku su tafi su yi hadaya ga Ubangiji.” Musa ya ce wa Fir’auna, “Na ba ka dama ka ba da lokacin da zan yi addu’a dominka da kuma bayinka da mutanenka, gidajenku kuwa za su rabu da kwaɗi, amma ban da waɗanda suke cikin Nilu.” Fir’auna ya ce, “Gobe.” Musa ya amsa, “Za a yi kamar yadda ka faɗa, domin ka sani babu wani kamar Ubangiji, Allahnmu. Kwaɗin za su bar ka da gidajenka, bayinka da mutanenka; za su kasance a Nilu ne kaɗai.” Bayan Musa da Haruna sun bar Fir’auna, Sai Musa ya yi kuka ga Ubangiji saboda kwaɗin da ya kawo a bisa Fir’auna. Sai Ubangiji ya yi abin da Musa ya nema. Kwaɗin suka mutu a gidaje, da filaye, da kuma gonaki. Aka jibga su tsibi-tsibi, ƙasar ta yi ɗoyi saboda su. Amma da Fir’auna ya ga an sami sauƙi, sai ya taurare, ya ƙi yă saurari Musa da Haruna kamar dai yadda Ubangiji ya riga ya faɗa. Sa’an nan Ubangiji ya ce wa Musa, “Ka ce wa Haruna, ‘Miƙa hannunka ka bugi ƙurar ƙasa,’ dukan ƙurar ƙasar Masar kuwa za tă zama ƙwari masu cizo.” Suka yi haka, da Haruna ya miƙa hannunsa da sandan, ya bugi ƙurar ƙasa, sai ƙwari masu cizo suka fito a kan mutane da dabbobi. Dukan ƙurar, ko’ina a ƙasar Masar ta zama cinnaku. Sa’ad da bokayen Fir’auna suka yi ƙoƙari yin sihiri iri na rufe ido domin su fito da kwari, sai suka kāsa. Ƙwari masu cizo kuwa suka rufe mutane da dabbobi. Sai bokaye suka ce wa Fir’auna, “Wannan fa da hannun Allah a ciki.” Amma zuciyar Fir’auna ta taurare, bai kuwa saurara ba, kamar dai yadda Ubangiji ya riga ya faɗa. Sai Ubangiji ya ce wa Musa, “Ka tashi da sassafe ka sadu da Fir’auna a lokacin da za shi kogi, ka ce masa, ‘Ga abin da Ubangiji yana cewa, bari mutanena su tafi, don su yi mini sujada. In ba ka bar mutanena suka tafi ba, zan turo da tarin ƙuda a kanka da bayinka, a kan mutanenka da cikin gidajenka. Gidajen Masarawa za su cika da ƙudaje, har ma da ƙasa inda za su taka. “ ‘Amma zan keɓe yankin Goshen, inda mutanena suke don kada ƙudaje su taɓa wurin, domin ka sani cewa Ni, Ubangiji, ina cikin wannan ƙasa. Zan sa iyaka tsakanin jama’ata da jama’arka. Gobe ne wannan mu’ujiza za tă auku.’ ” Ubangiji kuwa ya yi haka. Tarin ƙuda suka zubo a fadar Fir’auna da cikin gidajen bayinsa, da ko’ina a Masar, ƙasar kuwa ta lalace saboda ƙudaje. Sai Fir’auna ya kira Musa da Haruna ya ce, “Ku tafi, ku miƙa hadaya ga Allahnku, a nan a cikin ƙasar.” Amma Musa ya ce, “Wannan ba zai yiwu ba. Hadayun da mukan miƙa wa Ubangiji, Allahnmu haram ne ga Masarawa. In kuwa muka miƙa hadayun da suke haram a idanunsu, ba za su jajjefe mu ba? Dole mu yi tafiya kwana uku cikin hamada domin miƙa hadayu ga Ubangiji Allahnmu, yadda ya umarce mu.” Fir’auna ya ce, “Zan bar ku ku tafi, don ku miƙa hadayu ga Ubangiji Allahnku, a cikin hamada, amma ba za ku tafi da nisa ba. Yanzu ku yi mini addu’a.” Musa ya amsa, “Da zarar na bar ka, zan yi addu’a ga Ubangiji, gobe kuwa ƙudaje za su bar Fir’auna da fadawansa da kuma mutanensa. Sai dai a tabbata Fir’auna bai sāke yin ruɗi ta wurin ƙin barin mutane su tafi su miƙa hadayu ga Ubangiji ba.” Sa’an nan Musa ya rabu da Fir’auna, ya kuma yi addu’a ga Ubangiji, Ubangiji kuwa ya yi abin da Musa ya roƙa. Ƙudaje suka rabu da Fir’auna da fadawansa da kuma mutanensa; ba ƙudan da ya rage. Amma a wannan lokaci ma, Fir’auna ya taurare zuciyarsa, bai kuma bar mutanen suka tafi ba. Sai Ubangiji ya ce wa Musa, “Ka je wurin Fir’auna ka ce masa, ‘Ga abin da Ubangiji Allah na Ibraniyawa ya ce, “Ka bar mutanena su tafi, domin su yi mini sujada.” In ka ƙi ka bar su su tafi, kana ta riƙonsu, hannun Ubangiji zai kawo muguwar annoba a kan dabbobinka a gona, a kan dawakanka, da jakuna da raƙuma, da kuma a kan shanunka da tumaki da awaki. Amma Ubangiji zai raba tsakanin dabbobin Isra’ila da na Masar, saboda kada wata dabbar Isra’ilawa ta mutu.’ ” Sai Ubangiji ya sa lokaci ya ce, “Gobe Ubangiji zai yi wannan a ƙasar.” Kashegari Ubangiji ya yi haka. Dukan dabbobin Masarawa suka mutu, amma babu dabba guda ta Isra’ilawan da ta mutu. Fir’auna ya aiki mutane su bincika, sai suka tarar babu dabba guda ta Isra’ilawan da ta mutu. Duk da haka zuciyar Fir’auna ta taurare, bai kuwa bar mutanen su tafi ba. Sa’an nan Ubangiji ya ce wa Musa da Haruna, “Ɗibi tokar matoya cike da tafin hannuwanku, Musa kuwa zai watsa tokar sama a gaban Fir’auna. Za tă zama ƙura bisa dukan ƙasar Masar, sai marurai masu zafi su fiffito bisa mutane da dabbobi a dukan ƙasar.” Sai suka ɗibi tokar matoya, suka tsaya a gaban Fir’auna, Musa ya watsa ta a iska, sai marurai masu zafi suka fiffito bisa mutane da dabbobi. Bokaye suka kāsa tsayawa a gaban Musa saboda maruran da suke bisansu da a kan dukan Masarawa. Amma Ubangiji ya taurare zuciyar Fir’auna, bai kuwa saurare Musa da Haruna ba kamar yadda Ubangiji ya riga ya ce wa Musa. Sa’an nan Ubangiji ya ce wa Musa, “Tashi da sassafe, ka sadu da Fir’auna, ka ce masa, ‘Ga abin da Ubangiji, Allah na Ibraniyawa ya ce, Ka bar mutanena su tafi don su yi mini sujada, ko kuwa a wannan lokaci zan aika da cikakkiyar annoba mai ƙarfi a kanka da a kan fadawanka da mutanenka, domin ka san cewa ba kama da ni a dukan duniya. Gama da ni kaina na miƙa hannuna na buge ka da jama’arka da annoba, ai, da an hallaka ku a duniya ƙaƙaf. Amma na bar ka ka rayu domin in nuna maka ikona, domin kuma sunana yă zama abin darajantawa a dukan duniya. Har yanzu kana gāba da mutanena, ba ka kuma bar su su tafi ba. Saboda haka, gobe war haka, zan sa a yi ƙanƙara mai tsananin gaske, irin wadda Masar ba tă taɓa gani ba tun kahuwarta, har yă zuwa yanzu. Yanzu, ka ba da umarni a dawo da shanunku da kuma kome da kuke da shi wanda yake a gona zuwa gida, gama ƙanƙarar za tă kashe kowane mutum ko dabba wadda take a gona wadda ba a kawo cikin gida ba, sa’ad da ta fāɗo.’ ” Waɗansu daga cikin dattawan Fir’auna suka cika da tsoro saboda abin da Ubangiji ya faɗa, nan da nan suka shigo da dabbobinsu da bayinsu da sauri daga gona zuwa cikin gida. Amma waɗanda ba su kula da maganar Ubangiji ba, suka bar bayinsu da dabbobi a gona. Sa’an nan Ubangiji ya ce wa Musa, “Miƙa hannunka sama don a yi ƙanƙara a bisa dukan Masar, a bisa mutane da dabbobi, da bisa dukan abubuwan da suke girma a gonakin Masar.” Da Musa ya miƙa sandansa sama, sai Ubangiji ya aiko da tsawa da ƙanƙara, da walƙiya har ƙasa. Ta haka Ubangiji ya yi ruwan ƙanƙara a bisa ƙasar Masar; ƙanƙara ta fāɗo, walƙiya kuma tana ta wulƙawa. Wannan ce ƙanƙara mafi munin da aka taɓa yi, a dukan ƙasar Masar, tun tarihin kahuwarta na zaman al’umma. Ko’ina a Masar ƙanƙara ta bugi duk abin da yake a gonaki, mutane da dabbobi, ta bugi duk ganyaye da suke a gonaki, ta kuma ragargaza kowane itace. Wuri guda kaɗai da ba a yi ruwan ƙanƙara ba, shi ne yankin Goshen, inda Isra’ilawa suke. Sai Fir’auna ya aika a kira Musa da Haruna. Ya ce musu, “A wannan karo na yi zunubi. Ubangiji, shi ne da gaskiya, ni da mutane mu ke da kuskure. Ku roƙi Ubangiji, yă tsai da tsawar da ƙanƙarar. Ni kuwa na yi alkawari zan bar ku ku tafi, ba za ku ƙara tsayawa a nan ba.” Musa ya amsa, “To, da kyau, da zarar na fita daga birnin, zan yi addu’a ga Ubangiji, tsawar za tă tsaya, ƙanƙarar kuma za tă daina, don ku sani cewa duniya ta Ubangiji ce. Amma na san cewa kai da fadawanka, har wa yau ba ku ji tsoron Ubangiji Allah ba tukuna.” (Rama da sha’ir suka lalace, gama sha’ir ya riga ya nuna, rama kuwa tana fid da kai. Alkama da gero kam, ba a hallaka su ba, gama lokacin nunansu bai yi ba tukuna.) Sai Musa ya tashi daga gaban Fir’auna, ya fita daga birni. Da ya miƙa hannuwansa ta wajen Ubangiji, sai tsawa da ƙanƙara suka tsaya, kwararowar ruwa kuma ta ɗauke. Da Fir’auna ya ga cewa ruwa da ƙanƙara da tsawa sun daina, sai ya sāke yin zunubi. Shi da fadawansa, suka taurare zukatansu. Ta haka zuciyar Fir’auna ta taurare, bai kuwa bar Isra’ilawa suka tafi ba, kamar yadda Ubangiji ya riga ya faɗa ta wurin Musa. Sai Ubangiji ya ce wa Musa, “Je wurin Fir’auna, gama na riga na taurare zuciyarsa da kuma zukatan fadawansa domin in aikata waɗannan mu’ujizai nawa a tsakiyarsu, don kuma ku gaya wa ’ya’yanku da jikokinku yadda na tsananta wa Masarawa, da kuma yadda na aikata mu’ujizai a cikinsu, don ku sani ni ne Ubangiji.” Sai Musa da Haruna suka tafi wurin Fir’auna suka ce masa, “Ga abin da Ubangiji, Allah na Ibraniyawa ya ce, ‘Har yaushe za ka ƙi ƙasƙantar da kanka a gabana? Ka bar mutanena su tafi domin su yi mini sujada. In ka ƙi ka bari su tafi, gobe zan aiko da fāra a ƙasarka. Za su rufe fuskar ƙasar, har da ba za a iya ganin ƙasa ba. Za su cinye ɗan sauran abin da ya rage muku daga ɓarnar ƙanƙara, za su cinye dukan itatuwan da suke girma a gonakinku. Za su cika gidajenka, da na fadawanka, da na dukan Masarawa, abin da iyayenka da kakanninka ba su taɓa gani ba, tun daga ranar da suka sami kansu a duniya, har yă zuwa yau.’ ” Sa’an nan Musa ya juya, ya rabu da Fir’auna. Fadawan Fir’auna suka ce masa, “Har yaushe mutumin nan zai zama mana tarko? Ka bar mutanen su tafi domin su yi wa Ubangiji Allahnsu sujada. Har yanzu ba ka san cewa Masar ta lalace ba?” Sa’an nan aka dawo da Musa da Haruna wurin Fir’auna. Sai ya ce, “Ku tafi, ku yi wa Ubangiji Allahnku sujada. Amma wa da wa za su tafi?” Musa ya amsa, “Za mu tafi tare da ƙanananmu, da tsofaffinmu, da ’ya’yanmu maza da mata, da kuma garkunanmu na shanu da tumaki, gama dole ne mu yi bikin ga Ubangiji.” Fir’auna ya ce, “ Ubangiji ya taimaka bisa ga niyyarku, amma matanku da ƙanananku ba za su tafi ba! A fili yake kuna da niyyar mugunta. Sam! Wannan ba zai taɓa yiwu ba, sai ko maza kaɗai su tafi su yi wa Ubangiji sujada, gama abin da kuke so ke nan.” Sa’an nan aka kori Musa da Haruna daga gaban Fir’auna. Sai Ubangiji ya ce wa Musa, “Miƙa hannunka a bisa Masar domin fāra su sauko bisa ƙasar, su ci duk abin da yake girma a gonaki, duk abin da ƙanƙara ta rage.” Saboda haka Musa ya miƙa sandansa bisa Masar, Ubangiji kuwa ya sa iskar gabas ta hura a kan ƙasar dukan dare da kuma dukan yini. Da safe kuwa iskar ta kawo fāra; suka mamaye ƙasar duka, suka sauka a ko’ina a ƙasar. Ba a taɓa ganin annobar fāra haka ba, ba kuwa za a ƙara ganin fāra kamar haka ba. Suka rufe ƙasar har ta zama baƙi. Suka cinye abin da ƙanƙara ta rage, kowane tsiron da yake girma a gonaki, da dukan ’ya’yan itatuwa. Babu ɗanyen abin da ya ragu a kan itatuwa ko tsire-tsire a dukan ƙasar Masar. Fir’auna ya kira Musa da Haruna da gaggawa ya ce, “Na yi wa Ubangiji Allahnku zunubi, na kuma yi muku. Yanzu ku gafarta mini zunubina a wannan karo, ku kuma yi addu’a ga Ubangiji Allahnku yă ɗauke wannan muguwar annoba daga gare ni.” Sai Musa ya bar Fir’auna ya kuma yi addu’a ga Ubangiji. Sai Ubangiji ya canja iska zuwa iska mai ƙarfi ta yamma wadda ta ɗibi fārar zuwa Jan Teku. Babu fāran da suka rage a wani wuri a Masar. Amma Ubangiji ya taurare zuciyar Fir’auna, bai kuwa bar Isra’ilawa suka tafi ba. Sa’an nan Ubangiji ya ce wa Musa, “Miƙa hannunka sama domin a yi duhu a bisa Masar, duhun da za a iya taɓawa.” Sai Musa ya miƙa hannunsa sama, aka kuma yi duhu baƙi ƙirin bisa dukan ƙasar Masar na kwana uku. Ba wanda ya iya gani wani ko yă bar wurinsa na kwana uku. Amma dukan Isra’ilawa sun kasance da haske a inda suke zama. Sai Fir’auna ya aika aka kira Musa, ya kuma ce, “Ku tafi, ku yi wa Ubangiji sujada. Matanku da yaranku ma za su iya tafiya tare da ku; sai dai ku bar garkunanku na shanu da tumaki.” Amma Musa ya ce, “Dole ka bari mu kasance da hadayu, da kuma hadayu na ƙonawa waɗanda za mu miƙa wa Ubangiji Allahnmu. Dole dabbobinmu ma su tafi tare da mu; ko kofato ma, ba za a bari a baya ba. A cikinsu ne za mu ɗibi abin da za mu yi wa Ubangiji Allahnmu sujada. Ba mu kuma san irin abin da za mu miƙa wa Ubangiji ba, sai mun kai can.” Amma Ubangiji ya taurare zuciyar Fir’auna, har bai yarda yă sake su ba. Fir’auna ya ce wa Musa, “Fita, ka ba ni wuri! Ka mai da hankali, kada ka ƙara bayyana a gabana, gama ran da ka sāke ganin fuskata, a ran nan za ka mutu.” Musa ya amsa, “Madalla, kamar yadda ka faɗa, ba zan ƙara bayyana a gabanka ba.” To, fa, sai Ubangiji ya ce wa Musa, “Zan ƙara kawo annoba guda a kan Fir’auna da kan Masar. Bayan haka, zai bar ku, ku fita daga nan. Sa’ad da ya yi haka kuwa, zai kore ku gaba ɗaya. Ka faɗa wa mutane cewa dukan maza da mata, su roƙi maƙwabtansu kayan azurfa da na zinariya.” ( Ubangiji ya sa mutane suka sami tagomashi a idon Masarawa, Musa kuwa ya sami girma sosai a cikin ƙasar Masar a gaban fadawan Fir’auna da kuma a gaban jama’ar.) Saboda haka Musa ya ce, “Ga abin da Ubangiji ya ce, ‘Wajen tsakar dare, zan ratsa dukan Masar. Kowane ɗan fari, namiji, a Masar zai mutu, daga kan ɗan fari na Fir’auna wanda zai ci gadon sarauta, har zuwa kan ɗan fari na baiwa, wadda take niƙa, da kuma dukan ’yan farin shanu. Za a yi kuka mai zafi ko’ina a Masar, irin wadda ba a taɓa yi ba, ba kuwa za a ƙara yi ba. Amma a cikin Isra’ilawa, ba karen da zai yi haushi wa mutum ko dabba.’ Ta haka za ku sani Ubangiji zai bambanta tsakanin Masar da Isra’ila. Dukan fadawan nan naka za su zo wurina, suna fāɗi a gabana suna cewa, ‘Ka fita, kai da dukan jama’arka!’ Sa’an nan zan fita.” Daga nan sai Musa ya fita daga gaban Fir’auna a husace. Ubangiji ya ce wa Musa, “Fir’auna zai ƙi kasa kunne gare ka, sai na ƙara aikata waɗansu mu’ujizai cikin Masar.” Musa da Haruna suka aikata dukan waɗannan mu’ujizai a gaban Fir’auna, amma Ubangiji ya taurare zuciyar Fir’auna, bai kuwa bar Isra’ilawa su fita daga ƙasarsa ba. Ubangiji ya ce wa Musa da Haruna a Masar, “Wannan wata za tă zama a gare ku wata na farko, wata na fari na shekararku. Ka faɗa wa dukan jama’ar Isra’ila cewa a rana ta goma ga wannan wata, kowane mutum zai ɗauki ɗan rago domin iyalinsa, ɗaya domin kowane gida. In akwai wani gidan da ba za su iya cinye rago guda ɗungum ba, saboda iyalin kima ne, to, sai su haɗa kai da maƙwabtansu, su ɗauki rago guda gwargwadon yawansu, bisa ga abin da mutum guda zai ci. Dabbobin da za ku zaɓa, dole su zama bana ɗaya, namiji marar tabo, za ku kuma kamo su daga cikin tumaki ko awaki. Za ku turke dabbar har rana ta goma sha huɗu ga wata, wato, sa’ad da dukan taron jama’ar Isra’ila za su yanka ragunansu da yamma. Sa’an nan za su ɗauki jinin, su shafa a gefen da yake saman dogaran ƙofa na gidajen da suke cin naman dabbobin. A wannan dare, za su gasa naman, su ci da ganyaye masu ɗaci, da kuma burodi marar yisti. Kada ku ci nama ɗanye, ko kuma dafaffe, amma a gasa shi, da kan, da ƙafafun, da kuma kayan cikin. Kada ku bar kome yă kai gobe, abin da ya kai gobe kuwa, sai ku ƙone shi. Ga yadda za ku ci shi, ku yi ɗamara, takalma kuwa a ƙafafunku, kuna riƙe da sandunan tafiya a hannunku. Ku ci shi da gaggawa; Bikin Ƙetarewa ne na Ubangiji. “A wannan dare, zan ratsa Masar, in bugi kowane ɗan fari, na mutum da na dabba, zan kuma hukunta dukan gumakan Masar. Ni ne Ubangiji. Jinin zai zama alama a gare ku, a gidajen da kuke; sa’ad da kuwa na ga jinin, zan ƙetare ku. Ba wata annoba mai hallakarwa da za tă taɓa ku yayinda na bugi Masar. “Wannan rana za tă zama muku abin tunawa dukan zamananku masu zuwa, za ku kiyaye ta kamar biki ga Ubangiji, dawwammamiyar farilla ce har abada. Kwana bakwai za ku ci burodi marar yisti. A rana ta fari, za ku fid da yisti daga gidajenku gama duk wanda ya ci abu mai yisti daga rana ta fari har zuwa rana ta bakwai, za a fid da shi daga Isra’ila. A rana ta fari, za ku yi taro mai tsarki, haka kuma za ku sāke yi a rana ta bakwai. Kada ku yi aiki a waɗannan ranaku, sai dai ku shirya abinci domin kowa, abin da za ku yi ke nan kawai. “Ku yi Bikin Burodi Marar Yisti domin a wannan rana ce na fitar da ku ɓangare-ɓangare daga Masar. Ku kiyaye wannan rana ta zama muku dawwammamiyar farilla wa tsara masu zuwa. A wata na fari, za ku ci burodi marar yisti daga yammancin ranar goma sha huɗu har zuwa yammancin ranar ashirin da ɗaya. Kada a sami yisti a gidajenku har kwana bakwai. Kuma duk wanda ya ci wani abu mai yisti, za a fid da shi daga taron jama’ar Isra’ila, ko baƙo ne, ko haifaffen ɗan ƙasa. Kada ku ci wani abincin da aka yi da yisti. Ko’ina kuka zauna, dole ku ci burodi marar yisti.” Sa’an nan Musa ya kira dukan dattawan Isra’ila ya ce musu, “Ku je da sauri ku zaɓi dabbobin iyalanku, ku yanka ragon Bikin Ƙetarewa. Ku ɗauki ƙunshin itacen hizzob, ku tsoma cikin jinin da yake a kwano, ku yayyafa wa dogaran ƙofa duka biyu, da bisa kan ƙofar. Kada wani daga cikinku yă fita daga ƙofar gidansa sai da safe. Sa’ad da Ubangiji yake ratsa ƙasar don yă bugi Masarawa, zai ga jinin a bisa da kuma gefen madogaran ƙofa, zai ƙetare ƙofar, ba zai bar mai hallakawa yă shiga gidajenku, yă buge ku ba. “Ku kiyaye waɗannan dokokin a matsayin dawwammamiyar farilla, da ku da ’ya’yanku har abada. Sa’ad da kuka shiga ƙasar da Ubangiji zai ba ku yadda ya alkawarta, ku kiyaye wannan biki. Sa’ad da kuma ’ya’yanku suka tambaye ku, ‘Mece ce manufar wannan biki?’ Sai ku faɗa musu, ‘Hadaya ce ta Bikin Ƙetarewa ga Ubangiji, domin ya tsallake gidajen Isra’ilawa a Masar, lokacin da ya kashe Masarawa, amma bai taɓa gidajenmu ba.’ ” Sai mutane suka rusuna, suka yi sujada. Isra’ilawa suka tafi suka yi yadda Ubangiji ya umarci Musa da Haruna. Da tsakar dare, sai Ubangiji ya karkashe dukan ’ya’yan fari a ƙasar Masar, tun daga ɗan farin Fir’auna, wato, magājinsa, har zuwa ɗan fari na ɗan sarƙa da yake kurkuku, har da ’ya’yan fari na dabbobi. Fir’auna da dukan fadawansa da kuma dukan Masarawa, suka tashi a cikin daren da kuka mai zafi, aka kuma ji kukan a ko’ina a cikin ƙasar Masar, gama ba gidan da ba a yi mutuwa ba. A cikin daren, Fir’auna ya aika a kira Musa da Haruna ya ce, “Ku tashi, ku da jama’arku, ku fita daga cikin jama’ata. Ku tafi, ku bauta wa Ubangiji yadda kuka ce. Ku kwashi garkunanku na tumaki da na awaki, da na shanu, ku yi tafiyarku kamar yadda kuka ce, amma ku sa mini albarka.” Masarawa suka matsa wa Isra’ilawa su fita daga ƙasarsu da sauri. Gama mutanen Masar sun ce, “Ai, za mu mutu duka, in ba su tafi ba!” Sai mutanen suka ɗauki garin da sun kwaɓa ba yisti a ciki, tare da ƙwaryansu na aikin kwaɓan, suka nannaɗe su a mayafansu, suka rataye a kafaɗunsu. Isra’ilawa kuwa suka yi yadda Musa ya umarce su, suka roƙi Masarawa kayan adonsu na azurfa da na zinariya, da kuma tufafi. Ubangiji kuwa ya sa Isra’ilawa suka yi farin jini a wurin Masarawa, Masarawa kuma suka saki hannu wa mutanen, suka ba su duk abin da suka roƙa; ta haka Isra’ilawa suka washe Masarawa. Isra’ilawa suka kama tafiya daga Rameses zuwa Sukkot. Akwai maza dubu ɗari shida da suke tafiya da ƙafa, ban da mata da yara. Waɗansu mutane da yawa da ba Isra’ilawa ba, suka haura tare da su, da garkunan shanu, da na tumaki da awaki. Suka toya burodi marar yisti da garin da aka kwaɓa wanda suka kawo daga Masar. Garin da aka kwaɓan ba shi da yisti, domin an kore su daga Masar, ba su kuwa sami damar shirya wa kansu abinci ba. Zaman da Isra’ilawa suka yi a Masar, ya kai shekara 430. A ranar da shekara 430 ɗin nan suka cika, a ran nan ne dukan ɓangare-ɓangare na mutanen Ubangiji suka bar Masar. Gama Ubangiji ya yi tsaro a wannan dare, domin yă fitar da su daga Masar, a wannan dare, dole dukan Isra’ilawa su yi tsaro, don su girmama Ubangiji, cikin dukan tsararraki masu zuwa. Ubangiji ya ce wa Musa da Haruna, “Waɗannan ne ƙa’idodin Bikin Ƙetarewa. “Ba baƙon da zai ci shi. Duk bawan da kuka sayo, yana iya ci, in dai an yi masa kaciya, amma wanda ba ya zama tare da ku na ɗinɗinɗin, da kuma wanda aka ɗauki hayansa, ba zai ci ba. “Dole a ci shi a cikin gida ɗaya; kada a kai naman waje. Kada a karya wani daga ƙasusuwansa. Dole dukan taron jama’ar Isra’ila su yi bikin. “Baƙon da yake zama tare da ku da yake so yă yi Bikin Ƙetarewar Ubangiji, dole yă yi wa dukan mazan da suke cikin gidansa kaciya; sa’an nan ne zai iya yin abubuwa kamar haifaffen ɗan ƙasa. Wannan za tă zama dawwammamiyar farilla ta shafi ɗan ƙasa da kuma baƙon da yake zama a tsakaninku.” Dukan Isra’ilawa suka yi na’am da shi, suka yi yadda Ubangiji ya umarci Musa da Haruna. A wannan rana, Ubangiji ya fito da Isra’ilawa ɓangare-ɓangare daga Masar. Ubangiji ya ce wa Musa, “Keɓe mini kowane ɗan fari. Ɗan fari wanda ya fara buɗe mahaifa a cikin Isra’ilawa nawa ne, ko na mutum ko na dabba.” Sai Musa ya ce wa mutane, “Ku tuna da wannan rana, ranar da kuka fito daga Masar, daga ƙasar bauta, gama Ubangiji ya fito da ku da hannu mai iko. Kada ku ci wani abin da yake da yisti. A wannan rana kuka fita, wato, a watan Abib. Sa’ad da Ubangiji ya kawo ku cikin ƙasar Kan’aniyawa, Hittiyawa, Amoriyawa, Hiwiyawa da Yebusiyawa, ƙasar da ya rantse wa kakanninku cewa zai ba ku, ƙasar da take zub da madara da zuma, za ku kiyaye wannan biki a wannan wata. Kwana bakwai za ku ci burodi marar yisti, a kan rana ta bakwai kuma za ku yi biki ga Ubangiji. Ku ci burodi marar yisti cikin kwana bakwai; kada a sami wani abu mai yisti a cikinku, ko a sami yisti a ko’ina a wurinku. A ranan nan kowa zai faɗa wa ɗanka, ‘Ina yin haka saboda abin da Ubangiji ya yi mini, sa’ad da na fita daga Masar.’ Wannan abin tunawa zai zama muku alama a hannunku, da kuma a goshinku cewa dokar Ubangiji tana a bakinku. Gama Ubangiji ya fitar da ku daga Masar da hannu mai iko. Dole ku kiyaye wannan farilla kowace shekara a lokacinta. “Bayan Ubangiji ya kawo ku cikin ƙasar Kan’aniyawa, ya kuma ba da ita yadda ya alkawarta muku da rantsuwa, ku da kakanninku, sai ku miƙa kowane ɗan fari ga Ubangiji. Duk ɗan farin dabbobinku na Ubangiji ne. Amma a fanshi kowane ɗan farin jakinku da ɗan rago. In kuwa ba za ku fanshe shi ba, sai ku karye wuyansa. Sai ku fanshe kowane ɗan farin daga cikin ’ya’yanku. “A kwanaki masu zuwa, in ɗanka ya tambaye ka, ‘Mene ne manufar wannan?’ Ka faɗa masa cewa, ‘Da hannu mai iko Ubangiji ya fito da mu daga Masar, daga ƙasar bauta. Sa’ad da Fir’auna ya taurare zuciyarsa, bai yarda ya sallame mu ba, sai Ubangiji ya kashe dukan ’ya’yan farin ƙasar Masar, na mutum da na dabba, gaba ɗaya. Domin haka nake yin hadaya ga Ubangiji da ’ya’yan fari, maza, da suka fara buɗe mahaifa, amma nakan fanshi dukan ’ya’yan farina maza.’ Za tă kuma zama alama a hannunku da kuma shaida a goshinku cewa Ubangiji ya fito da mu daga Masar da hannunsa mai iko.” Sa’ad da Fir’auna ya bar mutane su tafi, Allah bai bi da su a hanyar da ta bi ta iyakar Filistiyawa ba, ko da yake wannan hanya ce ta fi kusa. Gama Allah ya ce, “In suka fuskanci yaƙi, wataƙila su canja ra’ayinsu su koma Masar.” Saboda haka Allah ya kewaye da mutanen ta hamada zuwa Jan Teku. Isra’ilawa kuwa suka fita daga Masar da shirin yaƙi. Musa ya ɗauki ƙasusuwan Yusuf tare da shi, gama Yusuf ya sa Isra’ilawa su rantse masa. Ya ce, “Tabbatacce Allah zai taimake ku, sai ku ɗibi ƙasusuwana tare da ku daga wannan wuri.” Bayan sun bar Sukkot sai suka kafa sansani a Etam a bakin hamada. Da rana Ubangiji yakan ja gabansu a cikin al’amudin girgije domin yă bishe su a kan hanyarsu, da dare kuma a cikin al’amudin wuta domin yă ba su haske, domin su iya tafiya dare da rana. Al’amudan nan biyu, na girgije da na wuta, ba su daina yi wa jama’a jagora ba. Sa’an nan Ubangiji ya ce wa Musa, “Ka faɗa wa Isra’ilawa, su juya su kafa sansani a Fi Hahirot, a tsakanin Migdol da teku. Za su kafa sansanin kai tsaye kusa da teku, wanda ya fuskanci Ba’al-Zafon. Fir’auna zai yi tsammani, ‘Aha, Isra’ilawa sun rikice cikin ƙasar, hamada kuwa ta yimƙe su.’ Zan kuma taurare zuciyar Fir’auna, zai kuwa bi su. Na shirya wannan domin in nuna ɗaukakata a bisa Fir’auna da ƙungiyar sojansa. Bayan wannan, mutanen Masar za su sani ni ne Ubangiji.” Sai Isra’ilawa suka yi haka. Sa’ad da aka faɗa wa Fir’auna cewa Isra’ilawa sun gudu, sai Fir’auna da bayinsa suka canja ra’ayinsu game da su, suka ce, “Me muka yi? Mun bar Isra’ilawa suka tafi, mun kuwa rasa hidimarsu!” Sai shi da keken yaƙinsa suka shirya, ya kuma ɗauki sojojinsa tare da shi. Ya ɗauki kekunan yaƙi ɗari shida mafi kyau duka, tare da duk sauran keken yaƙin Masar, da shugabanni kuma a kan dukansu. Ubangiji ya taurare zuciyar Fir’auna sarkin Masar, domin yă bi Isra’ilawa waɗanda suke tafiya ba tsoro. Masarawa, dukan dawakan Fir’auna da kekunan yaƙi da mahaya da sojoji, suka bi Isra’ilawa suka cin musu yayinda suke a sansani kusa da teku kurkusa da Fi Hahirot, wanda ya fuskanci Ba’al-Zafon. Da Fir’auna ya yi kusa, Isra’ilawa suka ɗaga idanu sai suka hange Masarawa daga nesa suna tā da ƙura suna zuwa. Sai suka tsorata ƙwarai, suka kuwa yi kuka ga Ubangiji. Suka ce wa Musa, “Don babu makabarta a Masar ne, ka kawo mu a hamada mu mutu? Me ka yi mana ke nan da ka fitar da mu daga Masar? Ba mu faɗa maka a Masar ba, cewa ‘Ka bar mu mu bauta wa Masarawa’? Ai, da ya fi mana mu bauta wa Masarawa, da a ce mu mutu a hamada!” Musa ya amsa wa mutane ya ce, “Kada ku ji tsoro. Ku tsaya dai ku ga ceton da Ubangiji zai kawo muku yau. Masarawan da kuke gani yau, ba za ku ƙara ganinsu ba. Ubangiji zai yi yaƙi dominku, ku dai tsaya kurum.” Sa’an nan Ubangiji ya ce wa Musa, “Don me kake mini kuka? Ka faɗa wa Isra’ilawa su ci gaba da tafiya. Ka ɗaga sandanka, ka miƙa shi bisa teku don ruwa yă rabu domin Isra’ilawa su wuce cikin teku a kan busasshiyar ƙasa. Zan taurare zukatan Masarawa su shiga don su bi su. Ta haka zan ci nasara bisa Fir’auna da rundunansa, da keken yaƙinsa, da mahayan dawakansa. Masarawa za su sani ni ne Ubangiji sa’ad da na sami nasara bisa kan Fir’auna, da keken yaƙinsa, da mahayan dawakansa.” Sai mala’ikan Allah wanda yake tafiya a gaban sojojin Isra’ila, ya janye, ya koma bayansu. Al’amudin girgije shi ma ya koma, ya tsaya a bayansu, ya dawo tsakanin sojojin Masar da na Isra’ila. Duk dare, girgijen ya jawo duhu ga gefe ɗaya, haske kuma ga ɗaya gefen; saboda haka ba wanda ya kusaci wani duk dare. Da Musa ya miƙa hannunsa a bisa teku, sai Ubangiji ya tura teku baya da iskar gabas mai ƙarfi duk dare, ya maishe shi busasshiyar ƙasa. Ruwa ya rabu, sai Isra’ilawa suka wuce cikin teku a kan busasshiyar ƙasa, ruwan ya zama musu katanga dama da hagu. Masarawa suka bi su da dukan dawakan Fir’auna, da kekunan yaƙi, da mahayan, suka bi su cikin teku. Da asubahin fāri, sai Ubangiji ya dubi ƙasa a kan sojojin Masarawa daga al’amudin wuta da kuma girgije, sai ya sa suka ruɗe. Ya sa ƙafafun keken yaƙinsu suka fita don su kāsa tuƙi. Sai Masarawa suka ce, “Bari mu gudu daga Isra’ilawa gama Ubangiji yana yaƙi dominsu gāba da Masar.” Sa’an nan Ubangiji ya ce wa Musa, “Miƙa hannunka bisa teku don ruwa yă koma kan Masarawa, da keken yaƙinsu, da kuma mahayansu.” Musa ya miƙa hannunsa a bisa tekun, da wayewar gari kuwa teku ya koma wurinsa na dā. Masarawa suka yi ƙoƙari su gudu, sai Ubangiji ya tura su cikin teku. Ruwan ya komo ya rufe keken yaƙin da mahayan, dukan sojojin Fir’aunan da suka bi bayan Isra’ilawa cikin teku, ba ko ɗaya da ya tsira. Amma Isra’ilawa suka wuce cikin teku a busasshiyar ƙasa, ruwa kuwa ya yi musu katanga dama da hagu. A rana nan Ubangiji ya cece Isra’ila daga hannuwan Masarawa, Isra’ilawa kuwa suka ga gawawwakin Masarawa a bakin teku. Sa’ad da Isra’ilawa suka ga iko mai girma da Ubangiji ya yi gāba da Masarawa, sai mutanen suka ji tsoron Ubangiji, suka amince da shi, da kuma bawansa Musa. Sa’an nan Musa da Isra’ilawa suka rera wannan waƙa ga Ubangiji suka ce, “Zan rera waƙa ga Ubangiji gama an ɗaukaka shi ƙwarai. Doki da mahayinsa ya jefa su cikin teku. “ Ubangiji ne ƙarfina da mafakata, ya zama cetona. Shi Allahna ne, zan yabe shi. Allah na kakana, zan ɗaukaka shi. Ubangiji mai yaƙi ne Ubangiji ne sunansa. Karusan Fir’auna da sojojinsa ya jefa cikin teku. Zaɓaɓɓun jarumawansa ya nutsar da su cikin Bahar Maliya. Zurfafan ruwaye sun rufe su; suka nutse cikin zurfi kamar dutse. Hannun damanka, ya Ubangiji, Mai kwarjini ne da iko, hannun damanka, ya Ubangiji, ya farfashe magabci. “A cikin girman kwarjininka ka kā da waɗanda sun yi gāba da kai. Ka aiki fushinka mai zafi ya cinye su kamar tattaka. Da hucin numfashin hancinka ruwaye suka tattaru. Ruwaye masu kwararowa, suka tsaya kamar bango; ruwaye na zurfafa suka daskare a tsakiyar teku. Magabci ya yi fahariya, cewa ‘Zan fafare su, in ci musu. Zan raba ganima; abin da na so ya samu. Zan ja takobina hannuna kuwa zai hallaka su.’ Amma ka hura numfashinka sai teku ya rufe su. Suka nutse kamar darma cikin manyan ruwaye. Wane ne cikin alloli, ya yi kamar ka, ya Ubangiji? Wane ne kamar ka, mai ɗaukaka cikin tsarki, mai banrazana cikin ɗaukaka, mai aikata al’ajabai? “Ka miƙa hannunka na dama, ƙasa ta haɗiye abokan gābanka. A cikin ƙaunarka marar iyaka, za ka bishe mutanen da ka fansa. A cikin ƙarfinka, za ka bishe su zuwa mazauninka mai tsarki. Al’ummai za su ji, su yi rawar jiki tsoro zai kama mutanen Filistiya. Sarakunan Edom za su tsorata, shugabannin Mowab za su yi rawar jiki, mutanen Kan’ana za su narke. Razana da tsoro za su fāɗo a kansu. Da ikon hannunka za su tsaya cik kamar dutse, har sai mutanen da ka kawo sun wuce, ya Ubangiji. Za ka kawo su, ka dasa su a kan dutsen nan naka inda, ya Ubangiji, ka shirya domin mazauninka, wuri mai tsarkin da hannuwanka suka kafa, ya Ubangiji. “ Ubangiji zai yi mulki har abada abadin.” Sa’ad da dawakai, kekunan yaƙi da mahayan dawakan Fir’auna suka shiga cikin teku, Ubangiji ya mayar da ruwan teku a kansu, amma Isra’ilawa suka wuce a cikin teku a busasshiyar ƙasa. Sa’an nan Miriyam annabiya, ’yar’uwar Haruna ta ɗauki ganga a hannunta, dukan mata kuwa suka bi ta, da ganguna suna rawa. Miriyam ta yi musu waƙa. “Ku rera ga Ubangiji gama ya ci gawurtacciyar nasara. Doki da mahayi, ya jefa cikin teku.” Sai Musa ya jagoranci Isra’ila daga jan teku zuwa hamadar Shur. Kwana uku suka yi tafiya cikin hamada ba su sami ruwa ba. Da suka zo Mara, ba su iya shan ruwan ba saboda yana da ɗaci (shi ya sa ake kira wurin Mara). Sai mutanen suka yi gunaguni a kan Musa, suna cewa, “Me za mu sha?” Sai Musa ya yi kuka ga Ubangiji, Ubangiji kuwa ya nuna masa wani itace. Sai ya jefa shi cikin ruwan, sai ruwan ya zama mai daɗi. A can Ubangiji ya yi musu doka da farilla, a can kuma ya gwada su. Ya ce, “In kun kasa kunne ga muryar Ubangiji Allahnku kuka yi abin da yake daidai a idanunsa, in kun mai da hankali ga umarnansa, kuka kiyaye dukan farillansa, ba zan kawo muku wani ciwon da na kawo a kan Masarawa ba, gama ni ne Ubangiji da nake warkar da ku.” Sai suka zo Elim inda akwai maɓulɓulan ruwa goma sha biyu da itatuwan dabino saba’in, suka sauka a can, kusa da ruwa. Dukan taron Isra’ila suka tashi daga Elim suka zo hamadar Sin, wadda take tsakanin Elim da Sinai, a rana ta goma sha biyar ga wata biyu, bayan sun fito daga Masar. A hamadan, dukan taro suka yi gunaguni a kan Musa da Haruna. Isra’ilawa suka ce musu, “Da ma a hannun Ubangiji ne muka mutu a Masar, inda muka zauna kewaye da tukwanen nama, muna cin duk abincin da muke so, amma kun kawo mu cikin wannan hamada don ku kashe dukan wannan taro da yunwa.” Sai Ubangiji ya ce wa Musa, “Zan zubo muku burodi kamar ruwa daga sama. Mutanen za su fita kowace rana su tattara abin da zai ishe su na ranan. Ta haka zan gwada su in ga ko za su bi umarnaina. A rana ta shida za su shirya abin da suka kwaso, wannan kuwa zai zama ninki biyu na abin da sukan tattara na sauran ranaku.” Saboda haka Musa da Haruna suka ce wa dukan Isra’ila, “Da yamma za ku sani Ubangiji ne ya fitar da ku daga Masar. Da safe za ku ga ɗaukakar Ubangiji, saboda ya ji gunaguninku a kansa. Wane mu, da za ku yi gunaguni a kanmu?” Musa ya kuma ce, “Za ku san cewa shi ne Ubangiji, sa’ad da ya ba ku nama ku ci da yamma, da kuma duk burodin da kuke so da safe, saboda ya ji gunagunin da kuka yi a kansa. Namu a wane? Ai, gunaguninku ba a kanmu ba, amma a kan Ubangiji ne.” Sai Musa ya ce wa Haruna, “Ka faɗa wa dukan taron Isra’ila, ‘Ku zo gaban Ubangiji, gama ya ji gunaguninku.’ ” Yayinda Haruna yake magana da dukan taron Isra’ila, sai suka duba wajen hamada, sai ga ɗaukakar Ubangiji tana bayyana a girgije. Ubangiji ya ce wa Musa, “Na ji gunagunin Isra’ilawa. Ka faɗa musu, ‘A tsakanin fāɗuwar rana da almuru, za ku ci nama, da safe kuma za ku ƙoshi da burodi. Sa’an nan za ku sani ni ne Ubangiji Allahnku.’ ” Da yamman wannan rana, sai makware suka rufe dukan sansani, da safe kuma sai ga raɓa ta kewaye sansani. Lokacin da raɓar ta watse, sai ga wani abu kamar tsaki, falle-falle kuma da laushi, fari, kamar hazo, a ƙasa. Sa’ad da Isra’ilawa suka ga wannan, sai suka ce wa junansu, “Mene ne wannan?” Gama ba su san ko mene ne ba. Musa ya ce musu, “Wannan shi ne burodin da Ubangiji ya ba ku ku ci. Wannan shi ne abin da Ubangiji ya umarta, ‘Kowane mutum zai tattara bisa ga bukatarsa. Ku tara rabin gallon don mutum guda da yake cikin tentinku.’ ” Isra’ilawa suka yi kamar yadda aka faɗa musu, waɗansu suka tattara da yawa, waɗansu kuma kaɗan. Da suka gwada a mudu, wanda ya tattara da yawa bai sami mafi yawa ba, wanda kuma ya tattara kaɗan bai sami ƙanƙani ba. Kowane mutum ya tattara daidai bukatarsa. Sa’an nan Musa ya ce musu, “Kada wani yă bar saura har safe.” Duk da haka waɗansu ba su kula da umarnin Musa ba, suka bar saura har safe, kashegari kuwa ta yi tsutsotsi, ta ruɓe, sai Musa ya yi fushi da su. Kowace safiya, kowanne mutum yakan tattara daidai bukatarsa, lokacin da rana ta yi zafi, sai ta narke. A rana ta shida, suka tattara ninki biyu, mudu biyu ga mutum guda, sai shugabannin taron suka zo suka kawo ƙara wurin Musa. Shi kuma ya ce musu, “Wannan shi ne umarnin Ubangiji, ‘Gobe za tă zama ranar hutu, Asabbaci mai tsarki ga Ubangiji. Domin haka sai ku toya abin da kuke so ku toya, ku kuma dafa abin da kuke so ku dafa. Abin da ya rage ku ajiye har safe.’ ” Sai suka bar saura har safe, kamar yadda Musa ya umarta, bai kuwa yi wari ko yă yi tsutsa ba. Musa ya ce, “Ku ci shi yau, saboda yau Asabbaci ne na Ubangiji. Ba za ku same shi a ƙasa a yau ba. Kwana shida za ku tattara shi, amma a rana ta bakwai, Asabbaci, ba za a same shi ba.” Duk da haka waɗansu mutane suka fita a ranar Asabbaci don su tattara, amma ba su sami kome ba. Sai Ubangiji ya ce wa Musa, “Har yaushe za ku ƙi bin dokokina da umarnaina? Ku lura fa, ai, Ubangiji ne ya ba ku Asabbaci; shi ya sa a kan ba ku burodi na kwana biyu, a rana ta shida. Kowa ya kamata yă kasance inda yake a rana ta bakwai; kada kowa yă fita.” Sai mutanen suka huta a rana ta bakwai. Mutanen Isra’ila suka kira burodin Manna. Manna yana nan fari kamar farin riɗi, ɗanɗanonsa kuma yana kama da masa da aka yi da zuma. Musa ya ce, “Wannan shi ne abin da Ubangiji ya umarta, ‘Ku auna mudu guda na Manna, a adana ta dukan zamananku, domin kowane zamani yă ga irin abincin da na ba ku ku ci a hamada, yayinda na fitar da ku daga Masar.’ ” Saboda haka Musa ya ce wa Haruna, “Ka ɗauki tulu, ka sa mudu guda na Manna a ciki. Sa’an nan ka sa shi a gaban Ubangiji, don a adana don tsararraki masu zuwa.” Sai Haruna ya ajiye Mannar a gaban Akwatin Alkawari, don a adana ta kamar yadda Ubangiji ya umarci Musa. Isra’ilawa suka yi shekaru arba’in suna cin Manna, har sai da suka shiga cikin ƙasar da take da mutane, suka ci Manna har zuwa kan iyakar ƙasar Kan’ana. (Omer guda, daidai ne da kashi ɗaya bisa goma na Efa.) Dukan taron Isra’ilawa suka kama tafiya daga Hamadar Sin, suka yi ta tafiya suna sauka a wurare dabam-dabam bisa ga umarnin Ubangiji. A ƙarshe suka sauka a Refidim, suka zauna a can, amma ba ruwan da jama’a za su sha. Saboda haka suka yi wa Musa maganganun banza suka ce, “Ba mu ruwa mu sha.” Musa ya amsa ya ce, “Don me kuke mini maganganun banza? Don me kuke gwada Ubangiji?” Amma mutanen suka yi fama da ƙishirwa a can, suka yi gunaguni a kan Musa. Suka ce, “Don me ka fitar da mu daga Masar, ka sa mu da ’ya’yanmu da dabbobinmu, mu mutu da ƙishirwa?” Sai Musa ya yi kuka ga Ubangiji ya ce, “Me zan yi da wannan jama’a? Suna shiri su jajjefe ni da duwatsu.” Ubangiji amsa wa Musa, “Ka ɗauki sandan da ka bugi ruwan Nilu da shi. Ka kira waɗansu shugabannin Isra’ila, ku wuce a gaban jama’ar. Zan tsaya a can a gabanka, kusa da dutsen Horeb. Ka bugi dutsen, ruwa kuwa zai fito daga gare shi domin mutane su sha.” Sai Musa ya yi haka a idon dattawan Isra’ila. Sai suka ba wa wurin suna, Massa da Meriba, saboda Isra’ilawa sun yi jayayya, suka kuma gwada Ubangiji cewa, “ Ubangiji yana tsakaninmu ko babu?” Amalekawa suka zo, suka yaƙi Isra’ilawa a Refidim. Musa ya ce wa Yoshuwa, “Zaɓi waɗansu mazanmu, ka je ka yaƙi Amalekawa. Gobe zan tsaya a bisa tudu, da sandan Allah a hannuwana.” Sai Yoshuwa ya yaƙi Amalekawa kamar yadda Musa ya umarta, Musa, Haruna da Hur kuwa suka tafi bisa tudu. Muddin hannun Musa yana a miƙe, sai Isra’ilawa su yi ta cin nasara, amma da zarar hannunsa ya sauka, sai Amalekawa su yi ta cin nasara. Sa’ad da hannuwan Musa suka gaji, sai Haruna da Hur suka ɗauki dutse suka sa ya zauna a kai. Sa’an nan su kuma suka tsaya gefe da gefe, suna riƙe da hannuwansa har fāɗuwar rana. Sai Yoshuwa kuwa ya ci nasara a kan Amalekawa da takobi. Sa’an nan Ubangiji ya ce wa Musa, “Ka rubuta wannan a cikin littafi, yă zama abin tuni, ka kuma faɗa wa Yoshuwa zan hallaka Amalekawa ƙaƙaf daga duniya.” Musa ya gina bagade, sai ya kira shi Ubangiji shi ne Tutata. Ya ce, “Gama an ɗaga hannuwa sama zuwa kursiyin Ubangiji, Ubangiji zai yaƙi Amalekawa daga tsara zuwa tsara.” Ana nan sai Yetro firist na Midiyan, kuma surukin Musa, ya ji duk abin da Allah ya yi wa Musa da mutanensa Isra’ila, da kuma yadda Ubangiji ya fitar da Isra’ila daga Masar. Bayan da Musa ya tura matarsa Ziffora gida, sai surukinsa Yetro ya karɓe ta da ’ya’yanta biyu maza. Ana kira ɗaya Gershom, domin Musa ya ce, “Na zama baƙo a baƙuwar ƙasa”; ɗayan kuma Eliyezer, domin ya ce, “Allah mahaifina ya taimake ni ya cece ni daga takobin Fir’auna.” Yetro surukin Musa tare da ’ya’yan Musa da matarsa suka zo wurin Musa a hamada, inda suka kafa sansani kusa da dutsen Allah Yetro ya riga ya aika wa Musa cewa, “Ni surukinka Yetro, ina zuwa wurinka tare da matarka da ’ya’yanka maza biyu.” Sai Musa ya tafi yă taryi surukinsa, ya sunkuya ya yi masa sumba. Suka gai da juna, sa’an nan suka shiga tenti. Musa kuwa ya faɗa wa surukinsa duk abubuwan da Ubangiji ya yi wa Fir’auna da Masarawa domin Isra’ila, da batun wahalolin da suka sha a hanya, da yadda Ubangiji ya cece su. Yetro ya yi murna da jin duk abubuwa masu kyau da Ubangiji ya yi wa Isra’ila, wajen cetonsu daga hannun Masarawa. “Yabo ga Ubangiji wanda ya cece ku daga hannun Masarawa da na Fir’auna, wanda kuma ya cece mutanensa daga hannun Masarawa. Yanzu na san cewa Ubangiji ya fi kowane allah, gama ya yi wannan ga masu girman kai da kuma waɗanda suka wulaƙanta Isra’ila.” Sa’an nan Yetro surukin Musa, ya kawo hadaya ta ƙonawa da waɗansu hadayu wa Allah, Haruna ya zo tare da dukan dattawan Isra’ila, suka ci abinci tare da surukin Musa a gaban Allah. Kashegari, Musa ya zauna domin yă yi wa mutane shari’a, sai suka tsaya kewaye da shi daga safe har yamma. Sa’ad da surukinsa ya lura da duk abin da Musa yake yi saboda mutane, sai ya ce, “Mene ne wannan da kake yi wa mutane? Don me kai kaɗai kake zama kana yin shari’a wa mutane, yayinda mutanen nan suke tsaya kewaye da kai daga safe har yamma?” Musa ya amsa ya ce, “Saboda mutanen suna zuwa wurina, don su nemi nufin Allah. Duk lokacin da suke da gardama, akan kawo su a wurina, ni kuma sai in raba tsakaninsu, in kuma koya musu dokokin Allah da farillansa.” Surukin Musa ya amsa ya ce, “Abin da kake yi ba daidai ba ne. Kai da dukan mutanen da suke zuwa wurinka za ku gajiyar da kanku. Aikin ya fi ƙarfinka; ba za ka iya yinsa kai kaɗai ba. Ka kasa kunne gare ni yanzu, zan ba ka shawara, Allah kuma yă kasance tare da kai. Kai za ka zama wakilin mutane a gaban Allah, ka kuma kawo gardamansu gare shi. Ka koya musu dokokinsa da farillarsa, ka kuma nuna musu hanyar rayuwa da ayyukan da za su yi. Amma ka zaɓi mutane masu iyawa daga dukan mutane, maza masu tsoron Allah, amintattu, masu ƙin rashawa, ka sanya su shugabanni na dubbai, ɗari-ɗari, hamsin-hamsin da goma-goma. Bari waɗannan mutane su sassanta mutane a kan ƙananan matsaloli, amma kowace babban matsala, ko bukata ta musamman, sai su kawo wurinka, ƙananan matsaloli kuma sai su yanke hukuncin da kansu. Ta haka ne za su taimaka wajen ɗaukan nauyin jama’a, don su sa aikin yă zama maka da sauƙi. In ka yi haka, Allah ya umarta za ka iya jimre gajiyar, kuma dukan mutanen nan za su koma gida da murna.” Musa ya kasa kunne ga surukinsa, ya kuma aikata duk abin da ya faɗa. Ya zaɓi mutane masu iyawa daga cikin dukan Isra’ila, ya naɗa su shugabannin mutane, shugabanni a kan dubbai, ɗari-ɗari, hamsin-hamsin da goma-goma. Suka yi hidimar alƙalanci na mutane a dukan lokaci. Gardandamin da suke da wuya, suka kawo wurin Musa, amma ƙananan batuttuwa, suka shari’anta a tsakaninsu. Sa’an nan Musa ya sallame surukinsa Yetro, ya kuwa koma ƙasarsa. A rana ta farko a cikin watan uku bayan da Isra’ilawa suka bar Masar, a wannan rana, suka iso Hamadar Sinai. Bayan da suka tashi daga Refidim, suka shiga Hamadar Sinai, sai Isra’ilawa suka yi sansani a gaban dutsen. Sai Musa ya hau kan dutsen don yă sadu da Allah, Ubangiji kuwa ya kira shi daga dutsen ya ce, “Wannan shi ne abin da za ka faɗa wa gidan Yaƙub, da kuma abin da za ka faɗa wa mutanen Isra’ila. ‘Ku da kanku kun ga abin da na yi wa Masar, da yadda na ɗauko ku a kan fikafikan gaggafa na kawo ku wurina. Yanzu, in kuka yi mini cikakken biyayya, kuka kuma kiyaye yarjejjeniyata, to, za ku zama keɓeɓɓiyar taska a gare ni a cikin dukan al’ummai. Ko da yake duk duniya tawa ce, za ku zama firistoci masu tsarki da kuma al’umma keɓaɓɓiya a gare ni.’ Waɗannan su ne kalmomin da za ka faɗa wa Isra’ilawa.” Sai Musa ya koma ya aika a kira dukan dattawan mutane, ya bayyana dukan kalmomin da Ubangiji ya umarta, ya faɗa. Dukan mutane suka amsa gaba ɗaya suka ce, “Za mu yi duk abin da Ubangiji ya faɗa.” Sai Musa ya mayar wa Ubangiji amsar da mutane suka bayar. Ubangiji kuwa ya ce wa Musa, “Ina zuwa wurinka a cikin baƙin hadari, domin mutane su ji ni ina maganar da kai, domin su amince da kai koyaushe.” Sa’an nan Musa ya faɗa wa Ubangiji abin da mutane suka ce. Sai Ubangiji ya ce wa Musa, “Tafi wurin mutanen, ka tsarkake su yau da gobe, ka sa su wanke tufafinsu. Su zama da shiri a rana ta uku, gama a ranar ce Ubangiji zai sauko a kan Dutsen Sinai a idon dukan mutane. Sai ka yi wa jama’a iyaka kewaye da dutsen, ka kuma faɗa musu cewa, ‘Ku mai da hankali, kada ku hau dutsen ko ku taɓa gefensa. Duk wanda ya taɓa dutsen, lalle za a kashe shi. Za a jajjefe shi da duwatsu, ko a harbe shi da kibiyoyi, ba hannun da zai taɓa shi. Mutum ko dabbar da ya taɓa, ba za a bar shi da rai ba.’ Lokacin da aka ji muryar ƙaho ne kawai za su iya taru a gindin dutsen.” Bayan da Musa ya gangara wurin mutane, ya tsarkake su, sai suka wanke tufafinsu. Sa’an nan ya ce wa mutane, “Ku shirya kanku domin rana ta uku. Ku ƙame kanku daga yin jima’i.” A safiyar rana ta uku, aka yi tsawa, da walƙiyoyi, sai ga girgije mai duhu a bisa dutsen, aka tsananta busar ƙaho, sai dukan jama’ar da suke cikin sansani suka yi rawar jiki. Sa’an nan Musa ya jagoranci mutane daga sansani domin su sadu da Allah, sai suka tsaya a gefen dutsen. Dutsen Sinai kuwa ya tunnuƙe duka da hayaƙi, gama Ubangiji ya sauko a bisan dutsen cikin wuta. Hayaƙin ya hau kamar hayaƙin da yake fitowa daga matoya, duk dutsen ya yi rawa da ƙarfi, sai karar ƙaho ya yi ta ƙaruwa. Sa’an nan Musa ya yi magana, murya Allah kuwa ta amsa masa. Ubangiji ya sauko a kan ƙwanƙolin Dutsen Sinai, ya kira Musa zuwa ƙwanƙolin dutsen. Musa kuwa ya haura sai Ubangiji ya ce masa, “Ka sauka ka faɗa wa jama’a, kada su kuskura su ƙetare layin iyakan nan, garin son zuwa don ganin Ubangiji, gama duk waɗanda suka yi haka za su mutu. Ko firistocin da za su kusato Ubangiji sai su tsarkake kansu, don kada in hallaka su.” Musa ya ce wa Ubangiji, “Mutanen ba za su hau Dutsen Sinai ba, gama kai da kanka ka gargaɗe mu, ‘Ku sa iyaka kewaye da dutsen ku kuma tsarkake shi.’ ” Ubangiji ya amsa, “Sauka ka kawo Haruna tare da kai. Amma kada firistoci da mutane su zarce iyakan nan, a kan za su zo wurin Ubangiji, don kada in hallaka su.” Saboda haka Musa ya sauka wurin mutane ya kuma faɗa musu. Sai Allah ya faɗi waɗannan kalmomi ya ce, “Ni ne Ubangiji Allahnka, wanda ya fitar da ku daga Masar, daga ƙasar bauta. “Ba za ka yi wa kanka waɗansu alloli ba sai ni. Ba za ka yi wa kanka waɗansu alloli a siffar wani abu a sama a bisa, ko a ƙarƙashin ƙasa, ko a ƙarƙashin ruwa ba. Ba za ka durƙusa gare su, ko ka yi musu sujada ba. Gama ni, Ubangiji Allahnka mai kishi ne, nakan hukunta ’ya’ya har tsara ta uku da ta huɗu na waɗanda suke ƙina, amma ina nuna ƙauna ga tsara dubbai na waɗanda suke ƙaunata, suke kuma kiyaye umarnaina. Ba za ka yi amfani da sunan Ubangiji Allahnka a banza ba, gama Ubangiji zai hukunta duk wanda ya mai da sunansa banza. Ka tuna da ranar Asabbaci domin ka kiyaye ta da tsarki. Kwana shida za ka yi dukan aikinka, amma rana ta bakwai Asabbaci ne ga Ubangiji, Allahnka. A ranar ba za ka yi wani aiki ba, ko kai, ko ɗanka, ko ’yarka, ko bawa, ko baiwa, ko dabbarka, ko baƙon da yake zama tare da kai. Gama kwana shida Ubangiji ya halicci sama da ƙasa, da teku, da duk abin da yake cikinsu, amma ya huta a rana ta bakwai. Saboda haka Ubangiji ya albarkaci ranar Asabbaci, ya kuma mai da ita mai tsarki. Ka girmama mahaifinka da mahaifiyarka, domin ka yi tsawon rai a ƙasar da Ubangiji Allahnka yake ba ka. Ba za ka yi kisankai ba. Ba za ka yi zina ba. Ba za ka yi sata ba. Ba za ka ba da shaidar ƙarya a kan maƙwabcinka ba. Ba za ka yi ƙyashin gidan maƙwabcinka ba. Ba za ka yi ƙyashin matar maƙwabcinka ba, ko bawansa, ko baiwarsa, ko sansa, ko jakinsa, ko duk abin da yake na maƙwabcinka ba.” Da mutane suka ga tsawa da walƙiya, suka ji karar ƙaho, suka kuma ga dutsen yana hayaƙi, sai suka yi rawar jiki don tsoro. Suka tsaya da nisa suka ce wa Musa, “Ka yi magana da mu da kanka, za mu kasa kunne. Amma kada Allah ya yi mana magana, don kada mu mutu.” Musa ya ce wa mutane, “Kada ku ji tsoro, gama Allah ya zo don yă gwada ku, don ku riƙa girmama shi, don kuma kada ku yi zunubi.” Sa’ad da mutane suka tsattsaya da nesa, sai Musa ya matsa kusa da girgije mai duhu, inda Allah yake. Sa’an nan Ubangiji ya ce wa Musa, “Ka faɗa wa Isra’ilawa wannan. ‘Kun gani da kanku cewa na yi magana da ku daga sama. Kada ku yi waɗansu alloli in ban da ni, kada ku yi wa kanku allolin azurfa ko na zinariya. “ ‘Ku yi mini bagaden ƙasa, ku kuma miƙa mini hadaya ta ƙonawa da hadaya ta salama, za ku hadayar da tumakinku da awakinku da shanu. Duk inda na sa a girmama sunana, zan zo wurinku, in sa muku albarka. In kuka yi mini bagade dutse, kada ku gina shi da sassaƙaƙƙun duwatsu, gama inda guduma ta taɓa duwatsun, sun haramtu ke nan. Kada ku gina wa bagadena matakala, domin kada yayinda wani yana hawa, mutane su ga tsiraicinsa.’ “Waɗannan su ne dokokin da za ka sa a gabansu. “In ka sayi mutumin Ibraniyawa a matsayin bawa, zai bauta maka shekara shida. Amma a shekara ta bakwai, za ka ’yantar da shi, yă tafi ’yantacce, ba tare da ya biya kome ba. In ya zo shi kaɗai, zai tafi ’yantacce shi kaɗai; amma in yana da mata a lokacin da ya zo, za tă tafi tare da shi. In maigidansa ya yi masa aure, ta kuwa haifa masa ’ya’ya maza ko mata, matan da ’ya’yan, za su zama na maigidan, sai mutumin kaɗai zai tafi ’yantacce. “Amma in bawan ya furta ya ce, ‘Ina ƙaunar maigidana, da matata, da ’ya’yana, ba na so kuma in ’yantu,’ dole maigidansa yă kai shi gaban alƙalai. Zai kai shi ƙofa ko madogarar ƙofa, yă huda kunnensa da basilla, sa’an nan zai zama bawansa duk tsawon kwanakinsa a duniya. “In mutum ya sayar da ’yarsa a matsayin baiwa, ba za a ’yantar da ita kamar bawa ba. In ba tă gamshi maigida wanda ya zaɓe ta domin kansa ba, dole yă bari a fanshe ta. Ba shi da dama yă sayar da ita ga baƙi, tun da yake bai kyauta mata ba. In ya zaɓe ta domin ɗansa, dole yă ba ta duk damar da ’ya ta mace take da shi. In ya auri wata mace, ba zai hana wa baiwar abinci da sutura ba, ba kuma zai ƙi kwana da ita ba. In bai tanada mata waɗannan abubuwa uku ba, sai tă tafi ’yantacciya, babu biyan kome. “Duk wanda ya bugi mutum har ya kashe shi, lalle a kashe shi. Amma in ba da nufin yă kashe shi ba, sai dai in Allah ne ya nufa haka, to, sai mutumin yă tsere zuwa inda zan nuna muku. Amma in mutumin ya yi dabara har ya kashe wani mutum da gangan, sai a ɗauke shi daga bagadena a kashe shi. “Duk wanda ya bugi mahaifinsa ko mahaifiyarsa, dole a kashe shi. “Duk wanda ya saci mutum ya sayar da shi, ko kuwa aka iske shi a hannunsa, lalle kashe shi za a yi. “Duk wanda ya la’anta mahaifinsa ko mahaifiyarsa, dole a kashe shi. “Idan mutane suka yi faɗa, ɗayan ya jefa ɗayan da dutse, ko ya naushe shi amma bai mutu ba, sai dai ya yi ta jiyya, idan mutumin ya sāke tashi ya yi tafiya ko da yana dogarawa da sanda ne, wanda ya buge shi zai kuɓuta, sai dai zai biya diyyar lokacin da ya ɓata masa, yă kuma lura da shi, har yă warke sarai. “In mutum ya dūke bawansa ko baiwarsa da sanda, sai bawan ko baiwar ta mutu saboda dūkan, dole a hukunta shi, amma ba za a hukunta shi ba, in bawan ko baiwar ta tashi, bayan kwana ɗaya ko biyu, tun da bawan ko baiwar mallakarsa ne. “Idan mutum biyu suna faɗa, har suka yi wa mace mai ciki rauni, har ya sa ta yi ɓari, amma wani lahani bai same ta ba, za a ci wa wanda ya yi mata raunin tara bisa ga yadda mijinta ya yanka za a biya, in dai abin da ya yanka ya yi daidai da abin da alƙalai suka tsara. Amma in akwai rauni mai tsanani, sai a ɗauki rai a maimakon rai, ido don ido, haƙori don haƙori, hannu don hannu, ƙafa don ƙafa, ƙuna don ƙuna, rauni don rauni, ƙujewa don ƙujewa. “In mutum ya bugi bawa ko baiwa a ido, har idon ya lalace, dole yă ’yantar da shi ko ita, maimakon ido. In kuma ya fangare haƙorin bawa ko baiwa, dole yă ’yantar da bawan ko baiwar, a maimakon haƙorin. “In bijimi ya kashe namiji ko ta mace, dole a jajjefe bijimin har yă mutu, ba za a kuma ci namansa ba. Amma mai bijimin ba shi da laifi. In, har an san bijimin da wannan hali, an kuma yi wa mai shi gargaɗi, amma bai ɗaura shi ba, har ya kashe namiji ko ta mace, za a jajjefe bijimin tare da mai shi, har su mutu. Amma fa, in an bukace shi yă biya, zai biya don yă fanshi ransa ta wurin biyan abin da aka aza masa. Wannan doka ta shafi batun bijimin da ya kashe ɗa ko ’ya. In bijimin ya kashe bawa ko baiwa, mai shi zai biya shekel talatin na azurfa wa maigidan bawan, a kuma a jajjefe bijimin. “In mutum ya bar rami a buɗe, ko ya haƙa rami bai kuma rufe ba, sai saniya ko jaki ya fāɗi a ciki, Mai ramin zai biya rashin da aka yi wa mai shi, matacciyar saniyan ko jakin, zai zama na mai ramin. “In bijimin mutum ya raunana bijimin wani, har ya mutu, sai mutanen biyu su sayar da mai ran, su raba kuɗin daidai, haka ma su yi da mai ran. Amma fa, in tun can, an san bijimin yana da wannan halin faɗa, duk da haka mai shi bai ɗaura shi ba, dole mai shi yă biya, dabba domin dabba, matacciyar dabbar kuwa tă zama nasa. “In mutum ya saci saniya ko tunkiya ya yanka, ko ya sayar, zai biya shanu biyar, a maimakon saniyar da ya sata, ko kuma tumaki huɗu, maimakon tunkiyar da ya sata. “In aka iske ɓarawo yana cikin ƙoƙarin shiga yă yi sata, aka buge shi har ya mutu, to, ba za a nemi alhakin jininsa daga wurin kowa ba; amma in ya faru bayan wayewar gari, to, za a nemi alhakin jinin ɓarawon a hannun wanda ya bugi ɓarawon. “Ɓarawon da aka kama da abin da ya sata, dole yă yi cikakkiyar ramuwa, amma in ba shi da kome, dole a sayar da shi a biya abin da ya sata. In an sami dabbar, ko saniya, ko jaki, ko tunkiya da ya sata da rai a hannunsa, dole ɓarawon yă biya taran da za a ci shi, sau biyu na kowane ɗaya. “In mutum ya sa dabbobinsa su yi kiwo a fili ko a gonar inabi, ya kuma bar dabbobinsa suka yi ɓarna a cikin gonar wani, sai a sa mai dabbar yă biya tara daga amfanin gonarsa mafi kyau duka. “In gobara ta tashi, ta kuma bazu cikin ƙayayyuwa, har ta cinye tarin hatsi, ko hatsin da ke tsaye, ko dukan gonar, dole wanda ya sa wutar, yă biya taran da aka yanka masa saboda ɓarnan da wutar ta yi. “In mutum ya ba maƙwabcinsa azurfa, ko kaya ajiya, aka kuma sace su daga gidan maƙwabcin, in an kama ɓarawon, sai ɓarawon yă biya abin da ya sata har sau biyu. Amma in ba a sami ɓarawon ba, sai wanda aka yi ajiyar a gidansa, yă bayyana a gaban alƙalai a bincika ko yana da hannu a kan kayan maƙwabcinsa. A kowane rikicin cin amana da zai shiga tsakanin mutum biyu, ko a kan bijimi, ko jaki, ko tunkiya, ko riga, kai, ko a kan kowane irin abin da ya ɓata, da ma abin da aka samu a hannun wani, in akwai jayayya, za a kawo mutumin a gaban alƙalai. Wanda alƙali ya ce shi ne mai laifi, sai yă biya ɗayan taran da za a yanka, har sau biyu. “In mutum ya ba da jaki, ko saniya, ko tunkiya, ko kowace dabba wa maƙwabcinsa ajiya, sai abin ya mutu, ko ya ji rauni, ko an ɗauke shi, in ba shaida, rantsuwa ce za tă raba tsakaninsu a gaban Ubangiji cewa babu hannunsa a dukiyar maƙwabcinsa. Mai dukiyar kuwa zai yarda da rantsuwar, ba za a bukaci wanda aka bai wa amanar yă biya ba. Amma idan satan dabbar ce aka yi, dole wanda aka bai wa ajiyar yă biya mai dabbar taran da aka ci masa. In naman jeji ne ya kashe ta, zai nuna gawar don shaida, ba za a kuwa sa maƙwabcin yă biya abin da naman jeji ya kashe ba. “In mutum ya yi aron dabba daga wurin maƙwabcinsa, sai dabbar ta ji rauni ko ta mutu, yayinda mai shi ba ya nan, dole wanda ya yi aron dabbar yă biya. Amma idan mai dabbar yana a wurin, wanda ya karɓa aron, ba zai biya kome ba. In an yi hayar dabbar ce, to, kuɗin da aka biya na hayar zai zama a madadin rashin. “Idan mutum ya ruɗe budurwa, wadda ba wanda yake nemanta, ya kuma kwanta da ita, dole yă biya kuɗin aurenta, za tă kuma zama matarsa. In mahaifinta ya ƙi yă ba da ita ga mutumin, dole mutumin yă biya dukiya daidai da abin da akan biya domin budurwai. “Kada ku bar maiya da rai. “Duk mutumin da ya yi jima’i da dabba dole a kashe shi. “Duk wanda ya yi hadaya ga wani allah ban da Ubangiji, dole a hallaka shi. “Kada a wulaƙanta, ko a zalunci baƙo, domin dā ku baƙi ne a ƙasar Masar. “Kada ku ci zalin gwauruwa, ko maraya. In kuka yi haka, idan kuma suka yi kuka gare ni, zan ji kukansu. Zan husata, in kuma kashe ku da takobi; matanku kuma, su ma su zama gwauraye, ’ya’yanku kuwa su zama marayu. “In kun ba wa jama’ata matalauta da suke tsakaninku bashin kuɗi, kada ku zama kamar masu ba da rance; kada ku sa yă biya da ruwa. In kun ɗauki mayafi maƙwabcinku a matsayin jingina, ku mayar masa kafin fāɗuwar rana, domin mayafin ne abin da yake da shi na rufe jikinsa. To, da me zai rufu yă yi barci? Sa’ad da ya yi mini kuka, zan ji, gama ni mai tausayi ne. “Kada ku yi maganar saɓo ga Allah, ko ku la’anta mai mulkin mutanenku. “Kada ku jinkirta fitar da zakarku daga rumbunanku, ko harajin kayan da kuka saya. “Dole ku ba ni ’ya’yan farinku maza. Ku yi haka da shanunku da tumakinku. Bari su kasance da iyayensu mata, har kwana bakwai, amma ku ba ni su a rana ta takwas. “Za ku kasance mutanena masu tsarki. Saboda kada ku ci naman da namun jeji suka kashe; ku jefa wa karnuka. “Kada ku baza rahoton ƙarya. Kada kuma ku haɗa baki da mugayen mutane har da ku zama munafukai ta wurin ba da shaidar ƙarya. “Kada ku yi abin da ba daidai ba, don galibin mutane suna yin haka. Sa’ad da kuke ba da shaida a gaban shari’a, kada ku ba da shaidar ƙarya a kauce wa gaskiya don ku faranta wa taron jama’a rai. Kada ku yi wa matalauci sonkai a gaban shari’a. “In ka ga saniyar abokin gābanka, ko jakinsa ya ɓace, ka yi ƙoƙari ka mai da shi wurinsa. In ka ga jakin wani maƙiyinka ya fāɗi a ƙarƙashin kayan da ya ɗauka, kada ka bar shi can, ka yi ƙoƙari ka taimake shi. “Kada ku kāsa yin adalci ga matalauci a wurin shari’a. Ku yi nesa da ƙage. Kada ku kashe marar laifi tare da mai adalci, gama ba zan bar mugun yă tafi haka kawai ba. “Kada ka karɓi cin hanci, gama cin hanci yakan makanta waɗanda suke gani, yakan kuma karkatar da maganar masu adalci. “Kada ka zalunci baƙo, ku kanku kun san halin baƙunci, gama dā ku baƙi ne a Masar. “Shekara shida za ku nome gonakinku ku girbe amfanin gonar, amma a shekara ta bakwai za ku bar ƙasa tă huta. Sa’an nan matalautan da suke cikinku za su sami abinci daga cikinta, namun jeji kuma za su ci abin da aka bari. Ku yi haka da gonakinku na inabi, da na itatuwan zaitun. “Kwana shida za ku yi aikinku, amma a rana ta bakwai, kada ku yi aiki, saboda saniyarku da jakinku su huta, haka kuma bawan da aka haifa a gidanku, da kuma baƙon da yake a cikinku yă wartsake. “Ku mai da hankali, ku yi biyayya da duk abin da na faɗa muku. Kada ku kira sunaye waɗansu alloli; kada a ji su a bakinku. “Sau uku a shekara za ku yi mini biki. “Ku yi Bikin Burodi Marar Yisti, kwana bakwai za ku ci burodi marar yisti, kamar yadda na umarce ku. Ku yi wannan a lokacin da aka ayana a watan Abib, gama a watan ne kuka fito daga Masar. “Kada wani yă zo a gabana hannu wofi. “Ku yi Bikin Girbi da nunan fari na amfanin shuke-shuken gonarku. “Ku yi Bikin Tattarawa a ƙarshen shekara, sa’ad da kuka tattara amfani daga gonarku. “Sau uku a shekara, maza duka za su bayyana a gaban Ubangiji Mai Iko Duka. “Kada ku miƙa mini hadayar jini tare da wani abu mai yisti. “Ba za a bar kitsen bikin hadayata yă kwana ba. “Dole ne ku kawo mafi kyau daga nunan fari na gonakinku a gidan Ubangiji Allahnku. “Kada ku dafa ɗan akuya a cikin madarar mahaifiyarsa. “Ga shi, zan aika mala’ika a gabanku, yă tsare ku a tafiyarku, yă kuma kawo ku wurin da na shirya. Ku saurare shi, ku kuma kasa kunne ga abin da yake faɗa. Kada ku yi masa tawaye; ba zai gafarta tawayenku ba, gama shi wakilina ne. In kun kasa kunne sosai ga abin da yake faɗi, kuka kuma yi abin da na faɗa, zan zama magabci ga abokan gābanku, zan kuma yi hamayya da abokan hamayyanku. Mala’ikana zai sha gabanku, yă kawo ku cikin ƙasar Amoriyawa, da Hittiyawa, da Ferizziyawa, da Kan’aniyawa, da Hiwiyawa, da kuma Yebusiyawa, zan kuma kawar da su. Kada ku durƙusa wa allolinsu, ko ku yi musu sujada, ko kuma ku bi al’adunsu. Za ku hallaka dukan allolinsu, ku kuma farfasa keɓaɓɓun duwatsunsu. Ku bauta wa Ubangiji Allahnku, albarkansa kuwa za tă kasance a kan abincinku da ruwan shanku. Zan ɗauke cuta daga cikinku. A ƙasarku, mace ba za tă yi ɓari ba, ba kuma za a sami marar haihuwa ba. Zan ba ku tsawon rai. “Zan aiki razanata a gabanku, in kuma sa ruɗami a cikin kowace al’ummar da za ku sadu da ita. Zan sa duk abokan gābanku su juye da baya, su gudu. Zan aiki rina a gabanku, su kori Hiwiyawa, Kan’aniyawa da kuma Hittiyawa. Amma ba a shekara guda zan kore muku su ba, don kada ƙasar tă zama kufai har namun jeji su fi ƙarfinku. Da kaɗan da kaɗan zan kore muku su, har yawanku yă kai yadda za ku mallaki ƙasar. “Zan kafa iyakokinku daga Jan Teku zuwa Bahar Rum, daga hamada kuma zuwa Kogi. Zan ba da mazaunan ƙasar a hannunku, za ku kuwa kore su daga gabanku. Kada ku ƙulla yarjejjeniya da su, ko da allolinsu. Kada ku bari su zauna a cikin ƙasarku, in har kuka bar su, za su ɓata ku da zunubinsu na bautar allolinsu, har zai yă zama muku tarko.” Ana nan sai Ubangiji ya ce wa Musa, “Ku hauro zuwa wurina, kai da Haruna, Nadab da Abihu, da kuma dattawa saba’in a cikin Isra’ila. Za ku yi sujada da ɗan nisa, sai Musa kaɗai zai kusaci Ubangiji. Amma sauran kada su zo kusa, kada kuma jama’a su hau tare da shi.” Sa’ad da Musa ya tafi ya faɗa wa mutanen duk kalmomin Ubangiji da dokokinsa, sai suka amsa da murya ɗaya suna cewa, “Duk abin da Ubangiji ya faɗa, za mu yi.” Sai Musa ya rubuta duk abin da Ubangiji ya faɗa. Ya tashi kashegari da sassafe ya gina bagade kusa da dutsen, ya aza al’amudai goma sha biyu bisa ga kabilu goma sha biyu na Isra’ila. Sai ya aiki samarin Isra’ilawa, suka miƙa hadaya ta ƙonawa, suka kuma miƙa ƙananan bijimai don hadaya ta salama ga Ubangiji. Musa ya ɗauki rabin jinin ya zuba a cikin kwanoni, rabin kuma ya yayyafa a kan bagaden. Sa’an nan ya ɗauki Littafin Alkawari ya karanta wa mutane. Suka amsa suka ce, “Za mu yi duk abin da Ubangiji ya faɗa; za mu yi biyayya.” Musa ya kuma ɗauki jinin, ya yayyafa a kan mutanen ya ce, “Wannan shi ne jinin alkawarin da Ubangiji ya yi da ku, bisa ga dukan waɗannan kalmomi.” Musa da Haruna, Nadab da Abihu, da dattawa saba’in, Allah na Isra’ila suka haura suka kuma ga Allah na Isra’ila. A ƙarƙashin ƙafafunsa akwai wani abu wanda aka yi da saffaya, mai haske kuma kamar sararin sama kansa. Amma Allah bai yi wa shugabannin Isra’ila wani abu ba; suka ga Allah, suka ci suka kuma sha. Ubangiji ya ce wa Musa, “Hauro wurina a kan dutse, ka tsaya a nan, zan ba ka allunan dutsen, da doka da umarnan da na rubuta don koyonsu.” Sa’an nan Musa ya fita tare da Yoshuwa mataimakinsa, ya kuwa hau kan dutsen Allah. Ya ce wa dattawan, “Ku jira mu a nan, sai mun dawo wurinku. Haruna da Hur suna tare da ku, in wani yana da wata damuwa, sai yă je wurinsu.” Da Musa ya hau dutsen, sai girgije ya rufe dutsen, sai ɗaukakar Ubangiji ta sauka a kan Dutsen Sinai, kwana shida girgije ya rufe dutsen, a rana ta bakwai, sai Ubangiji ya kira Musa daga cikin girgijen. Ga Isra’ilawa dai, ɗaukakar Ubangiji ta yi kamar wuta mai ci a kan dutse. Sa’an nan Musa ya shiga girgijen ya hau kan dutsen. Ya zauna a kan dutsen yini arba’in da dare arba’in. Ubangiji ya ce wa Musa, “Ka faɗa wa Isra’ilawa su kawo mini hadaya. Za ka karɓi hadaya daga hannun kowane mutum wanda zuciyarsa ta yarda yă bayar. “Ga iri jerin kayan da za ka karɓo daga hannunsu, “zinariya, da azurfa, tagulla, shuɗi, shunayya da jan zare, lallausan lilin, da gashin akuya, fatun ragunan da aka wanke, fatun awaki masu kyau, itacen akashiya, mai domin fitila, kayan yaji domin man keɓewa da kuma turare mai ƙanshi, da duwatsun Onis, da duwatsun da za a mammanne a efod da ƙyallen maƙalawa a ƙirji. “Sa’an nan ka sa su yi mini wuri mai tsarki, domin in zauna a cikinsu. Ka ƙera wannan tabanakul da duk kayan da suke ciki da waje, daidai yadda zan nuna maka. “Ka sa a yi akwatin alkawarin da itacen ƙirya, tsawonsa kamu biyu da rabi, fāɗinsa kamu ɗaya da rabi, tsayinsa kuma kamu ɗaya da rabi. Ka dalaye shi da zinariya zalla ciki da waje, za ka yi wa gefe-gefensa ado da gurun zinariya. Ka kewaye akwatin da zoban zinariya huɗu ka kuma haɗa su da ƙafafunsa huɗu, zobai biyu a kowane gefe. Sa’an nan ka yi sanduna da itacen ƙirya, ka dalaye su da zinariya. Ka sa sandunan a cikin zoban, a gefen akwatin domin ɗaukansa. Sanduna za su kasance a cikin waɗannan zoban akwatin alkawarin; ba za a cire su ba. Sa’an nan ka sa Shaidar da zan ba ka, a cikin akwatin. “Ka yi murfin kafara da zinariya zalla, tsawonsa kamu biyu da rabi, fāɗinsa kuma kamu ɗaya da rabi. Ka kuma yi kerubobi biyu da zinariyar da aka ƙera, ka sa a gefen nan biyu na murfin. Ka yi kerubobi biyu, ɗaya a wannan gefe, ɗaya kuma a ɗayan gefen; za ka manne su a kan murfin, su zama abu ɗaya. Kerubobin su kasance da fikafikansu a buɗe, domin su inuwantar da murfin, za su fuskanci juna, suna duba murfin. Ka sa murfin a bisa akwatin ka kuma sa allunan dokokin alkawarin da zan ba ka a ciki. Can, a bisa murfin da yake tsakanin kerubobi biyu da suke bisa akwatin alkawari na Shaida, zan sadu da kai, in kuma ba ka dukan umarnai domin Isra’ilawa. “Ka yi tebur da itacen ƙirya, tsawonsa kamu biyu, fāɗinsa kamu ɗaya, tsayinsa kuma kamu ɗaya da rabi. Ka dalaye shi da zinariya zalla ka kuma yi masa ado kewaye da gurun zinariya. Ka yi dajiya mai fāɗin tafin hannu, ka kuma yi wa dajiyar ado da gurun zinariya. Ka yi zoban zinariya huɗu domin teburin, ka daure su a kusurwoyi huɗu, inda ƙafafu huɗun suke. Zoban za su kasance kusa da dajiyar don riƙe sandunan da za a yi amfani don ɗaukar teburin. Ka yi sandunan da itacen ƙirya, ka dalaye su da zinariya, da sandunan ne za ku riƙa ɗaukan teburin. Da zinariya zalla kuma za ka yi farantansa, da kwanoninsa na tuya, da butocinsa, da kwanoninsa domin zuban hadayu. Ka sa burodin Kasancewa a kan wannan tebur, yă kasance a gabana kullum. “Ka yi wurin ajiye fitilar da zinariya zalla, ka kuma yi gindinsa tare da gorar jikinsa da ƙerarriyar zinariya; kwafunansa da suka yi kamar furanni, tohonsa da furanninsa su yi yadda za su zama ɗaya da shi. Wurin ajiye fitilar yă kasance da rassa shida, rassan nan za su miƙe daga kowane gefe na wurin ajiye fitilan, uku a gefe guda, uku kuma a ɗaya gefen. Kwafuna uku masu siffar furanni almon, da toho, da kuma furannin za su kasance a rashe guda, uku a kan rashe na biye, haka kuma a kan saura rassan shida da suka miƙe daga wurin ajiye fitilan. A bisa wurin ajiye fitilan kuwa za a kasance da kwafuna huɗu masu siffar furannin almon, da toho, da furanni. Toho ɗaya zai kasance a ƙarƙashin rassa biyu na farkon da suka miƙe daga wurin ajiye fitilan, toho na biyu a ƙarƙashin rassa biyu na biye, toho na uku a ƙarƙashin rassa na uku, rassa shida ke nan duka. Tohon da kuma rassan za su kasance ɗaya da wurin ajiye fitilan da aka yi da ƙerarriyar zinariya. “Sa’an nan ka yi fitilu bakwai, ka sa su a bisa wurin ajiye fitilan ta yadda za su haskaka wajen da suka fuskanta. Za a yi lagwaninsa da manyan farantansa da ƙerarriyar zinariya. Da zinariya zalla na talenti ɗaya za ka yi wurin ajiye fitilan da waɗannan abubuwa duka. Sai ka lura ka yi su daidai bisa ga fasalin da aka nuna maka a kan dutse. “Ka yi tabanakul da labule goma na lilin mai laushi a naɗe shi biyu, a saƙa labulen da ulu mai ruwan shuɗi, da ulu mai ruwan shunayya, da kuma ulu mai ruwan ja. Waɗannan labule za a yi musu zānen siffofin kerubobi, aikin gwani. Dukan labulen, girmansu zai zama kamu ashirin da takwas, fāɗinsu kuwa kamu huɗu. Labulen su zama daidai wa daida. Ka haɗa labule biyar tare, ka yi haka kuma da suran biyar ɗin. Ka sa wa labulen rammuka da ulu mai ruwan shuɗin a gefen ƙarshe na labule ɗaya, a kuma yi haka a ƙarshen gefe na ɗaya kuma. Ka yi wa labulen rammuka hamsin a ɗayan labule, ka kuma yi haka a ƙarshe ɗayan labulen, rammukan su fuskanci juna. Sa’an nan ka yi maɗauri hamsin na zinariya don amfanin ɗaura labulen a haɗe, domin tabanakul yă zama ɗaya. “Ka yi labule goma sha ɗaya na gashin akuya da za ka rufe tabanakul. Tsawon kowanne yă zama kamu talatin, fāɗinsa kuma yă zama kamu huɗu. Labulen za su zama daidai wa daida. Ka haɗa labule biyar ka ɗinka. Haka kuma za ka yi da sauran shidan. Ka naɗe shida ɗin biyu, ka yi labulen ƙofar tentin da shi. Ka yi rammuka hamsin a ƙarshen gefen kashi ɗaya na labulen, haka kuma a ƙarshen kashi ɗayan. Sai ka kuma yi maɗauri hamsin da tagulla, ka ɗaura su a haɗe da tentin su zama ɗaya. Ragowar rabin labulen da yake a bisa tenti kuma sai a bar shi yana lilo a bayan tabanakul. Tsawon labulen tenti zai zama kamu ɗaya a kowane gefe, abin da ya rage kuma sai a bar shi ya yi ta lilo a kowane gefe don yă rufe tabanakul. Ka yi abin rufe tentin da fatun raguna da aka rina ja, a kansa kuma ka rufe shi da fatun shanun teku. “Ka yi tabanakul da katakon itacen ƙiryar da aka kakkafa a tsaye. Tsawon kowane katako zai zama kamu goma, fāɗinsa kuma kamu ɗaya da rabi, ka kafa katakan suna duban juna. Ka yi da dukan katakan tabanakul haka. Ka shirya katakai ashirin a gefen kudu na tabanakul, ka kuma yi rammuka arba’in da azurfar da za a sa wa katakan nan ashirin. Za a sa kawunan katakan da aka fiƙe a cikin rammukan. Game da ɗayan gefen, gefen arewa na tabanakul, za ka kafa katakai ashirin, da rammukan azurfa arba’in, biyu a ƙarƙashin kowane katako. Ka kafa katakai shida don can ƙarshen katakan, wato, a wajen yamma na ƙarshen tabanakul, ka kuma kafa katakai biyu a kusurwoyi can ƙarshe. Za a haɗa katakan nan a kusurwa daga ƙasa zuwa sama a daure su. Haka za a yi da katakan kusurwa na biyu. Ta haka za a sami katakai takwas da rammukansu na azurfa guda goma sha shida, kowane katako yana da rammuka biyu. “Ka kuma yi sanduna da itacen ƙirya. Sanduna biyar domin katakai na gefe ɗaya na tabanakul, biyar domin katakai wancan gefe, biyar kuma domin na gefe wajen yamma, can ƙarshen tabanakul. Sandan da yake tsakiyar katakan, zai bi daga wannan gefe zuwa ƙarshen wancan gefe. Ka dalaye dukan katakan da zinariya, ka kuma yi zoban zinariya don su riƙe sandunan. Ka kuma dalaye sandunan da zinariya. “Ka yi tabanakul bisa ga fasalin da aka nuna maka a bisa dutsen. “Ka yi labule mai ruwan shuɗi, shunayya da jan zare da kuma lallausan lilin da aka tuƙa, da zānen kerubobin da mai fasaha ya yi. Ka rataye shi a bisa dogayen sanduna huɗun nan na itacen ƙirya, waɗanda aka dalaye da zinariya, waɗanda suke tsaya a rammuka huɗu na azurfa. Ka rataye labule daga maɗauri, ka sa akwatin alkawari a bayan labulen. Labulen zai raba Wurin Mai Tsarki da Wurin Mafi Tsarki. Ka sa murfin kafara a bisa akwatin alkawari a Wuri Mafi Tsarki. Ka sa tebur a gaba labulen, a gefen arewa na tabanakul, ka kuma sa wurin ajiye fitilan ɗaura da shi, a wajen kudu. “Game da ƙofar shigar tenti kuwa, ka yi labule mai ruwan shuɗi, shunayya da jan zare na lallausan lilin da aka tuƙa, aikin gwani. Ka yi ƙugiyoyin zinariya domin wannan labule da katakai itacen ƙirya biyar, waɗanda aka dalaye da zinariya. Ka kuma yi zubi na tagulla biyar dominsu. “Ka gina bagade da itacen ƙirya, mai tsawo kamu uku, zai zama murabba’i, mai tsawo kamu biyar, fāɗi kuma kamu biyar. Ka yi masa ƙaho a kowace kusurwan nan huɗu, domin bagade da ƙahoni duk su zama ɗaya, ka dalaye bagade da tagulla. Ka yi duk kayan aikinsa da tagulla, tukwanensa na ɗiban toka, da manyan cokula, da kwanonin yayyafawa, da cokula masu yatsotsi don nama da kuma farantai domin wuta. Ka yi raga na tagulla dominsa, ka kuma yi zoben tagulla a kowace kusurwan nan huɗu na bagaden. Ka sa ragar a ƙarƙashin bagade domin tă kai tsakiyar bagade. Ka yi wa bagaden sanduna da itacen ƙirya, ka dalaye su da tagulla. Za a zura sandunan a cikin zoban saboda su kasance a gefe biyu na bagade a lokacin da ake ɗaukarsa. Ka yi bagaden da katakai, sa’an nan ka robe cikinsa. Ka yi shi bisa ga fasalin da aka nuna maka a bisa dutsen. “Ka yi fili domin tabanakul. Tsawon gefen kudu zai zama kamu ɗari da labulen da aka yi da zaren lili mai kyau, da katakai ashirin da rammukan tagulla ashirin da ƙugiyoyin azurfa da kuma rammuka a kan katakai. A wajen arewa shi ma, tsawon yă zama ƙafa ɗari. Ka kama labulen da ƙugiyoyin da aka yi da azurfa waɗanda aka manna a kan ƙarfen da aka dalaye da azurfa. “Faɗin ƙarshen filin a yamma zai zama kamu hamsin. A kuma sa labule tare da rammuka goma da kuma katakai goma. A wajen gabas can ƙarshe, wajen fitowar rana, fāɗin filin zai zama kamu hamsin. Tsayin labulen ƙofa na gefe ɗaya zai zama kamu goma sha biyar, da katakai uku tare da rammukansu uku, haka kuma tsayin labule na wancan gefen, zai zama kamu goma sha biyar, da katakai uku tare da rammukansu uku. “Domin ƙofar tentin, a saƙa labule mai tsayin kamu ashirin da lallausan zaren lilin mai ruwan shuɗi, da shunayya, da jan zare, mai aikin gwani, da katakai huɗu tare da rammukansu huɗu. Duk katakan da suke kewaye da filin, za a yi musu maɗaurai na azurfa da kuma ƙugiyoyi, da rammukan tagulla. Tsayin filin zai zama kamu ɗari, fāɗinsa kuma kamu hamsin, tsayin labulensa na lallausan zaren lilin zai zama kamu biyar, a kuma yi rammukansa da tagulla. Dukan sauran kayan da aka yi amfani da su a aikin wannan tabanakul, ko da wanda irin aiki ne za a yi da su, har da dukan dogayen turakunsa da na filin, za a yi su da tagulla ne. “Ka umarci Isra’ilawa su kawo tsabtataccen mai, tatacce daga zaitun domin fitilu, saboda fitilun su yi ta ci a koyaushe. A cikin Tentin Sujada, a waje da labulen da yake a gaban Akwatin Alkawari, Haruna da ’ya’yansa za su sa fitilu su yi ta ci a gaban Ubangiji, daga yamma har safiya. Wannan za tă zama dawwammamiyar farilla a cikin Isra’ila har tsararraki masu zuwa. “Ka sa a kawo maka Haruna ɗan’uwanka, tare da ’ya’yansa Nadab da Abihu, Eleyazar da Itamar daga cikin Isra’ilawa, domin su yi mini hidima a matsayin firistoci. Ka yi tufafi masu tsarki domin ɗan’uwanka Haruna, domin a girmama, a kuma ɗaukaka shi. Ka faɗa wa dukan gwanayen da na ba su hikima a irin abubuwan nan, cewa su yi tufafi saboda Haruna, don a tsarkakewarsa, domin yă yi mini hidima a matsayin firist. Waɗannan su ne tufafin da za su ɗinka, ƙyallen maƙalawa a ƙirji, da efod, da taguwa, da doguwar riga, da rawani, da abin ɗamara. Za su yi wa ɗan’uwanka, Haruna da ’ya’yansa, waɗannan tsarkaka tufafi, don su zama firistoci masu yi mini hidima. Ka sa su yi amfani da zinariya, da zare mai ruwan shuɗi da shunayya da ja, da kuma lallausan lilin. “Ka yi efod da zinariya, da shuɗi, da shunayya, da jan zare, da kuma lallausan lilin, aikin gwani mai sana’a. Za a yi fele biyu, gaba da baya, sa’an nan a haɗa, a ɗinka a mahaɗinsu a kafaɗa. Za a yi mata abin ɗamara da irin kayan da aka yi efod da shi, wato, da zinariya, da shuɗi, da shunayya, da mulufi, da lallausan zaren lilin. “Ka ɗauki duwatsu biyu masu daraja, ka rubuta sunayen ’ya’yan Isra’ila a kai bisa ga haihuwarsu, sunaye shida a kan dutse ɗaya, saura shida kuma a kan ɗaya dutsen. A rubuta sunayen ’ya’yan Isra’ila a kan duwatsu biyun, yadda mai yin aiki da dutse mai daraja yakan zāna hatimi. Sa’an nan a sa kowane dutse a cikin tsaiko na zinariya a ɗaura su a kan ƙyallen kafaɗa efod a matsayin duwatsun tuni ga ’ya’yan Isra’ila. Haruna ne zai ɗauki sunayen a kafaɗarsa don tuni a gaban Ubangiji. Ka yi tsaiko na zinariya da tuƙaƙƙun sarƙoƙi biyu kamar igiya, na zinariya zalla, ka kuma ɗaura wa tsaikunan nan biyu tuƙaƙƙun sarƙoƙi. “Ka shirya ƙyallen da za a manna a ƙirji don neman nufin Allah. Sai a saƙa shi da gwaninta kamar yadda aka saƙa efod ɗin. A saƙa shi da zinariya, da shuɗi, da shunayya, da mulufi, da lallausan zaren lilin. Zai zama murabba’i, tsawonsa kamu ɗaya, fāɗinsa kuma kamu ɗaya, a naɗe shi biyu. Sa’an nan ka yi jeri huɗu na duwatsu masu daraja a kansa. A jeri na fari, a sa yakutu, da tofaz, da zumurrudu. A jeri na biyu, a sa turkuwoyis, da saffaya, da emeral. A jeri na uku, a sa yakin, da idon mage da ametis. A jeri na huɗu, a sa kirisolit, da onis, da yasfa. Ka sa su a tsaiko na zinariya. A bisa duwatsun nan goma sha biyu, sai a zāna sunayen ’ya’yan Isra’ila bisa ga kabilansu goma sha biyu. Za a zāna sunayen kamar hatimi. “Ka yi wa ƙyallen maƙalawa a ƙirjin tuƙaƙƙun sarƙoƙin zinariya zalla. Ka yi zobe biyu na zinariya saboda ƙyallen maƙalawa a ƙirjin, ka kuma ɗaura su a kusurwoyin ƙyallen maƙalawa a ƙirji. Ka ɗaura sarƙoƙin zinariyan nan biyu a zoban a kusurwan ƙyallen maƙalawa a ƙirji. Ka kuma sa sauran bakunan sarƙoƙin nan biyu a kan tsaikon nan biyu, kana haɗa su da ƙyallen kafaɗa na efod a gaba. Ka yi zobai biyu na zinariya ka ɗaura su ga sauran kusurwoyi ƙyallen maƙalawa a ƙirji, a gefen ciki kusa da efod. Ka ƙara zobai biyu, ka kuma ɗaura su a bakin ƙyallen da ya sauka daga kafaɗa ta gaban efod, kusa da mahaɗin ƙyallaye biyu a bisa ɗamara na efod. Za a ɗaura zoban ƙyallen maƙalawa a ƙirji a zoban efod da shuɗiyar igiya, domin ƙyallen maƙalawa a ƙirji yă zauna a bisa abin ɗamarar efod, don kada yă kunce. “Duk sa’ad da Haruna zai shiga Wuri Mai Tsarki, zai shiga riƙe da sunayen ’ya’yan Isra’ila a zuciyarsa a kan ƙyallen maƙalawa a ƙirji na neman nufin Allah, domin yă zama abin tunawa a gaban Ubangiji. Ka kuma sa Urim da Tummim a ƙyallen maƙalawa a ƙirji, don su kasance a zuciyar Haruna, a duk sa’ad da zai shiga gaban Ubangiji. Haka kuwa kullum Haruna zai riƙa kai koke-koken Isra’ilawa a gaban Ubangiji. “Ka yi taguwar efod da shuɗi duka, ka yanke wuya a tsakiyarta don sawa. A kuma naɗe wuyan rigar yă yi kauri domin kada yă yage. Za a yi wa bakin rigar ado da fasalin ’ya’yan rumman masu launin shuɗi, da shunayya, da mulufi. A sa ƙararrawa ta zinariya a tsakankaninsu. Za ka jera su bi da bi, wato, ’ya’yan rumman na biye da ƙararrawar zinariya kewaye da bakin rigar. Dole Haruna yă sa shi sa’ad da yake hidima. Za a ji ƙarar ƙararrawar sa’ad da zai shiga Wuri Mai Tsarki a gaban Ubangiji, da sa’ad da ya fita, don kada yă mutu. “Ka yi allo na zinariya zalla, ka kuma yi rubutu a kansa kamar na hatimi, haka, Mai tsarki ga Ubangiji. Ka ɗaura shi da igiyar ruwa bula domin a haɗa shi da rawani; zai kasance a gaban rawanin. Zai kasance a goshin Haruna, ta haka zai ɗauki kurakuran da ya yiwu Isra’ilawa sun yi cikin miƙa baye-bayensu masu tsarki. Zai kasance a goshin Haruna kullayaumin, domin su zama abin karɓa ga Ubangiji. “Ka saƙa doguwar riga da lallausan lilin ka kuma yi hula da lallausan zaren lilin, ka kuma saƙa abin ɗamara mai ado. “Ka saƙa doguwar riga, abin ɗamara da kuma huluna domin ’ya’yan Haruna, don yă ba su girma da ɗaukaka. Bayan ka sa waɗannan riguna wa ɗan’uwanka Haruna da ’ya’yansa, ka shafe su da mai, ka kuma naɗa su. Ka keɓe su domin su yi mini hidima a matsayin firistoci. “Ka yi ’yan wandunan ciki na lilin don su rufe tsiraicinsu, tsayinsu zai kama daga kwankwaso zuwa cinya. Dole Haruna da ’ya’yansa su sa su sa’ad da za su shiga Tentin Sujada, ko sa’ad da suka kusace bagade domin hidima a Wuri Mai Tsarki, don kada su yi laifi, su kuma mutu. “Wannan za tă zama dawwammamiyar farilla wa Haruna da zuriyarsa har abada. “Ga abin da za ka yi don ka keɓe su, don su yi mini hidima a matsayin firistoci. Ka ɗauki ɗan bijimi da raguna biyu marasa lahani. Daga garin alkama mai laushi marar yisti kuwa, ka yi burodi, da wainan da aka kwaɓa da mai, da ƙosai waɗanda an barbaɗa mai a kai. Ka sa waɗannan a cikin kwando. Sa’an nan ka miƙa su tare da ɗan bijimin da ragunan nan biyu. Bayan haka sai ka kawo Haruna da ’ya’yansa a ƙofar Tentin Sujada ka yi musu wanka. Ka ɗauki rigar ka sa wa Haruna, ka sa masa doguwar rigar, da rigar efod, da efod kanta, da ƙyallen maƙalawa a ƙirji. Ka ɗaura masa efod da ɗamarar da aka yi mata ado. Ka naɗa masa rawani a kai, ka kuma sa kambi mai tsarki a bisa rawanin. Ka ɗauki man shafewa ka shafe shi, ta wurin zuba man a kansa. Ka kawo ’ya’yansa, ka sa musu taguwoyi, ka kuma sa musu huluna a kansu. Sa’an nan ka ɗaura wa Haruna da ’ya’yansa abin ɗamara. Su kuwa da zuriyarsu, aikin firist kuwa zai zama nasu ta wurin dawwammamiyar farilla. “Ta haka za ka keɓe Haruna da ’ya’yansa maza. “Ka kuma kawo bijimin a gaban Tentin Sujada, sai Haruna da ’ya’yansa su ɗora hannuwansu a kansa. Ka yanka shi a gaban Ubangiji a ƙofar Tentin Sujada. Ka ɗibi jinin bijimin ka zuba a kan ƙahoni na bagade da yatsanka, sauran jinin kuwa ka zuba a gindin bagaden. Sa’an nan ka ɗauki dukan kitsen da ya rufe kayan ciki, da kitsen da yake manne da hanta, da ƙoda biyu da kuma kintsen da yake a kansu, ka ƙone su a kan bagade. Amma ka ƙone naman bijimin, da fatarsa, da kayan cikin, a bayan sansani. Hadaya ce ta zunubi. “Ka ɗauki ɗaya daga cikin ragunan, Haruna kuwa da ’ya’yan maza za su ɗora hannuwansa a kansa. Ka yanka ragon, ka ɗibi jinin, ka yayyafa shi kewaye da gefen bagaden. Ka yayyanka rago gunduwa-gunduwa, ka wanke kayan cikin, da ƙafafun, da kan, ka haɗa su da gunduwoyin. Sa’an nan ka ƙone ragon ɗungum a kan bagade. Hadaya ta ƙonawa ce ga Ubangiji, mai daɗin ƙanshi, wato, hadaya ce da aka ƙone da wuta ga Ubangiji. “Ka ɗauki ɗayan ragon, sai Haruna da ’ya’yansa maza su ɗora hannuwansu a kansa. Ka yanka ragon, ka ɗibi jinin, ka shafa a bisa leɓen kunnen Haruna na dama, da bisa leɓen kunnuwan ’ya’yansa maza na dama, da kan manyan yatsotsin hannuwansu na dama, da kuma a kan manyan yatsotsin ƙafafunsu na dama. Sauran jinin kuwa, sai ka yayyafa shi kewaye da gefen bagaden. Ka ɗibi jinin da yake a kan bagade, da man shafewa, ka yafa a kan Haruna da rigunansa, da kuma a kan ’ya’yansa maza da rigunansu. Sa’an nan shi da ’ya’yansa maza da rigunansu za su tsarkake. “Ka ɗebi kitse daga wannan rago, ka yanke wutsiyarsa mai kitse, ka kuma ɗebi kitsen da ya rufe kayan ciki, da kitsen da yake bisa hanta, da ƙoda biyu da kitsen da yake kansu, da cinyar dama. (Gama rago ne don naɗi.) Daga kwandon burodi marar yisti, wanda yake gaban Ubangiji, ka ɗauki dunƙule ɗaya, da waina da aka yi da mai, da kuma ƙosai. Ka sa dukan waɗannan a hannun Haruna da ’ya’yansa maza, su kaɗa su a gaban Ubangiji a matsayin hadaya ta kaɗawa. Sa’an nan ka karɓe su daga hannuwansu, ka ƙone su a kan bagade tare da hadaya ta ƙonawa, domin ƙanshi mai daɗi ga Ubangiji, wato, hadaya ce da aka ƙone da wuta ga Ubangiji. Bayan haka, ka ɗauki ƙirjin ragon domin naɗin Haruna, ka kaɗa shi a gaban Ubangiji kamar hadaya ta kaɗawa. Wannan ƙirji zai zama rabonka. “Ka tsarkake ƙirji na hadaya ta kaɗawa, da cinya ta hadaya ta ɗagawa, waɗanda za a kaɗa a kuma ɗaga na ragon naɗin, wanda yake na Haruna da kuma na ’ya’yansa maza. Wannan zai zama rabon Haruna da ’ya’yansa maza daga Isra’ilawa. Gama wannan hadaya ta ɗagawa ce daga cikin hadayu na salama da Isra’ilawa za su miƙa wa Ubangiji. “Keɓaɓɓun tufafin nan na Haruna za su zama na zuriyarsa bayan mutuwarsa. Da tufafin nan ne za a zuba musu mai, a keɓe su. Ɗan da ya gāje shi a matsayin firist, shi ne zai sa su har kwana bakwai, lokacin da ya shiga Tentin Sujada, don yă yi aiki a Wuri Mai Tsarki. “Ka ɗauki ragon naɗi, ka dafa naman a tsattsarkan wuri. A ƙofar Tentin Sujada, Haruna da ’ya’yansa maza za su ci wannan rago da burodin da yake cikin kwandon. Za su ci abubuwan nan da aka yi kafara da su a lokacin tsarkakewarsu da keɓewarsu. Ba wanda zai ci, sai su kaɗai, gama abubuwan nan tsarkaka ne. In naman ragon naɗi ko wani burodin ya ragu har safiya, a ƙone shi, kada a ci gama tsarkake ne. “Ka yi wa Haruna da ’ya’yansa maza duk abin da na umarce ka, ka ɗauki kwana bakwai don naɗinsu. Ka miƙa bijimi ɗaya kowace rana domin hadaya don zunubi ta yin kafara. Ka tsarkake bagade ta wuri yin kafara dominsa, ka shafe shi da mai don ka tsarkake shi. Kwana bakwai za ka yi kafara saboda bagaden, ka kuma tsarkake shi. Sa’an nan bagaden zai zama mafi tsarki, kuma duk abin da ya taɓa bagaden zai tsarkaka. “Ga abin da za ka miƙa a bisa bagaden kowace rana. ’Yan raguna biyu masu shekara ɗaya-ɗaya. Ka miƙa ɗaya da safe, ɗaya kuma da yamma. Haɗe da ɗan rago na farkon, ka miƙa mudun gari mai laushi wanda an gauraye da kwalaba ɗaya na tataccen mai zaitun, da kwalaba ɗaya na ruwan inabi don hadaya ta sha. Ka miƙa ɗaya ragon da yamma, tare da hadaya ta gari da hadaya ta sha kamar aka yi ta safe, mai daɗin ƙanshi, wato, hadaya ce da aka ƙone da wuta ga Ubangiji. “Wannan za tă zama hadaya ta ƙonawar da za a dinga yi kowace rana, daga tsara zuwa tsara. Za a yi ta miƙa hadayar a ƙofar Tentin Sujada a gaban Ubangiji. A can zan sadu da kai, in yi magana da kai; a can kuma zan sadu da Isra’ilawa, in kuma tsarkake wurin da ɗaukakata. “Ta haka zan tsarkake Tentin Sujada da bagaden, in kuma tsarkake Haruna da ’ya’yansa maza su yi mini hidima a matsayin firistoci. Sa’an nan zan zauna a cikin Isra’ilawa, in kuma zama Allahnsu. Za su san cewa ni ne Ubangiji Allahnsu, wanda ya fitar da su daga Masar saboda in zauna a cikinsu. Ni ne Ubangiji Allahnsu. “Ka yi bagade da itacen ƙirya don ƙona turare. Zai zama murabba’i, tsawon zai zama kamu ɗaya, fāɗi kuma kamu ɗaya, amma tsayin yă zama kamu biyu, ƙahoninsa kuma su zama ɗaya da shi. Ka dalaye bisansa da kuma dukan gefe-gefensa da kuma ƙahoninsa da zinariya zalla, ka kuma yi zubi na zinariya kewaye da shi. Ka yi zobai biyu na zinariya domin bagade a ƙarƙashin zubin, biyu a gefe da gefe su fuskanci juna, don su riƙe sandunan da ake amfani da su don ɗaukarsa. Ka yi sandunan nan da itacen ƙirya, ka dalaye su da zinariya. Ka sa bagaden a gaban labulen da yake gaban akwatin alkawari, a gaba murfin kafara wanda yake bisa akwatin alkawari, inda zan sadu da kai. “Haruna zai ƙone turare a bisa bagaden kowace safiya, sa’ad da yake shirya fitilu. Dole Haruna yă ƙone turare sa’ad da ya ƙuna fitilu da yamma, ta haka za a riƙa ƙona turare a gaban Ubangiji, daga tsara zuwa tsara. Ba za a ƙona wani irin turare dabam a bisa wannan bagade ba, ba kuma za a miƙa hadaya ta ƙonawa, ko ta hatsi, ko ta sha a bisansa ba. Sau ɗaya a shekara, Haruna zai yi kafara a bisa ƙahoninsa. Dole a yi wannan kafara ta shekara-shekara da jinin kafara ta hadaya don zunubi daga tsara zuwa tsara. Gama bagaden mafi tsarki ne ga Ubangiji.” Sa’an nan Ubangiji ya ce wa Musa, “Sa’ad da za ku ƙidaya Isra’ilawa, dole kowanne yă biya domin yă fanshe kansa ga Ubangiji a lokacin da aka ƙidaya shi. Ta haka babu wata annobar da za tă buge su sa’ad da kuke ƙidaya su. Kowannen da ya ƙetare zuwa wurin waɗanda aka riga aka ƙidaya, dole yă ba da rabin shekel, bisa ga ma’aunin shekel na tsattsarkan wuri, wanda nauyinsa garwa ashirin ne. Wannan rabin shekel hadaya ce ga Ubangiji. Duk waɗanda suka ƙetare, waɗanda shekarunsu ya kai ashirin ko fiye, za su ba da hadaya ga Ubangiji. Masu arziki ba za su bayar fiye da rabin shekel ba, talakawa kuma ba za su bayar ƙasa da haka ba, sa’ad da za ku yi hadaya ga Ubangiji don kafara rayukanku. Ku karɓi kuɗin kafara daga hannun Isra’ilawa, ku yi amfani da shi domin hidimar Tentin Sujada. Zai zama abin tunawa ga Isra’ilawa a gaban Ubangiji, don su yi kafarar rayukansu.” Sa’an nan Ubangiji ya ce wa Musa, “Ka yi daro na tagulla, ka yi masa ƙafafun da za a ajiye shi da tagulla don wanki. Ka ajiye shi tsakanin Tentin Sujada da bagade, ka zuba ruwa a ciki. Haruna da ’ya’yansa maza za su wanke hannuwansu da ƙafafunsu da ruwan da yake cikinsa. Duk lokacin da suka shiga Tentin Sujada, za su yi wanka, don kada su mutu. Duk lokacin da suka yi kusa da bagade don hidima ta miƙa hadayar da aka yi wa Ubangiji da wuta, za su wanke hannuwansu da ƙafafunsu, don kada su mutu. Wannan za tă zama dawwammamiyar farilla domin Haruna da zuriyarsa daga tsara zuwa tsara.” Sa’an nan Ubangiji ya ce wa Musa, “Ka ɗauki waɗannan kayan yaji masu kyau, shekel 500 na ruwan mur, rabin turaren sinnamon mai daɗin ƙanshi shekel 250, shekel 250 na turaren wuta mai ƙanshi, shekel 500 na kashiya, duk bisa ga ma’aunin shekel na tsattsarkan wuri, da moɗa na man zaitun. Da waɗannan za ka yi man shafewa mai tsarki, yadda mai yin turare yake yi. Zai zama man shafewa mai tsarki. Sa’an nan ka yi amfani da shi don shafa wa Tentin Sujada, da akwatin alkawari, da tebur da kuma dukan kayansa, da wurin ajiye fitila da dukan kayansa, da bagaden ƙona turare, bagaden hadaya ta ƙonawa da dukan kayansa, da daro da mazauninsa. Za ka tsarkake su don su zama mafi tsarki, kuma duk abin da ya taɓa su, zai zama mai tsarki. “Ka shafe Haruna da ’ya’yansa maza, ka kuma tsarkake su don su yi mini hidima a matsayin firistoci. Ka faɗa wa Isra’ilawa, ‘Wannan mai, zai zama mai tsarki ne a gare ni don shafewa, daga tsara zuwa tsara. Kada a zuba a jikunan mutane, kada kuma a yi wani mai irinsa. Wannan mai, mai tsarki ne, za ku kuma ɗauke shi a matsayi mai tsarki. Duk wanda ya yi irin wannan mai, duk wanda kuma ya shafa shi a kan wani wanda yake ba firist ba, za a ware shi daga mutanensa.’ ” Sa’an nan Ubangiji ya ce wa Musa, “Ka ɗauki kayan yaji mai ƙanshi, resin na gum, da onika, da galbanum, da kuma zallan lubban, duk nauyinsu yă zama daidai. Ka yi turare mai ƙanshi yadda mai yin turare yake yi. A sa masa gishiri, yă zama tsabtatacce, tsarkakakke. Ka ɗiba kaɗan daga ciki, ka niƙa, ka ajiye a gaban akwatin alkawari a cikin Tentin Sujada, inda zan sadu da kai. Zai zama mafi tsarki a gare ku. Kada ku yi wani turare irinsa wa kanku; ku ɗauke shi a matsayi mai tsarki ga Ubangiji. Duk wanda ya yi irinsa don jin daɗin ƙanshinsa, dole a ware shi daga mutanensa.” Sai Ubangiji ya ce wa Musa, “Duba, na zaɓi Bezalel ɗan Uri, ɗan Hur, na kabilar Yahuda, na kuma cika shi da Ruhun Allah, fasaha, azanci, da kuma sani cikin kowace irin sana’a, don yin zāne-zāne na aikin zinariya, azurfa da tagulla, don yanka da shirya duwatsu, yin aikin katako, da kuma yin kowane irin aikin sana’ar hannu. Ban da haka, na zaɓi Oholiyab ɗan Ahisamak, na kabilar Dan, don yă taimake shi. Na kuma ba da fasaha ga dukan masu aikin sana’ar hannu, don yin duk abin da na umarce ka. Tentin Sujada, akwatin Alkawari tare da murfin kafara a bisansa, da dukan kayan aiki na tentin, tebur da kayansa, wurin ajiye fitila na zinariya zalla, da dukan kayansa, bagaden ƙona turare, bagaden hadaya ta ƙonawa da dukan kayansa, daro tare da mazauninsa, da kuma saƙaƙƙun riguna, tsarkakan riguna don Haruna firist da rigunan ’ya’yansa maza, sa’ad da suke hidima a matsayin firistoci, da man shafewa, da turare mai ƙanshi don Wuri Mai Tsarki. Za a yi su kamar yadda na umarce ka.” Sa’an nan Ubangiji ya ce wa Musa, “Ka faɗa wa Isra’ilawa, ‘Dole ku kiyaye Asabbataina. Wannan zai zama alama tsakanina da ku daga tsara zuwa tsara, saboda ku sani ni ne Ubangiji, wanda ya mai da ku masu tsarki. “ ‘Ku kiyaye Asabbaci, domin yă zama mai tsarki a gare ku. Duk wanda ya ƙazantar da shi, za a kashe shi; duk wanda ya yi wani aiki a ranar, za a ware shi daga mutane. Kwana shida, za a yi aiki, amma a rana ta bakwai, Asabbaci ne na hutu, mai tsarki ga Ubangiji. Duk wanda ya yi wani aiki a Asabbaci, za a kashe shi. Isra’ilawa za su kiyaye Asabbaci, suna bikinsa daga tsara zuwa tsara a matsayin madawwamin alkawari. Zai zama alama tsakanina da Isra’ilawa har abada, gama cikin kwana shida Ubangiji ya yi sama da ƙasa, a rana ta bakwai kuma ya daina aiki, ya kuma huta.’ ” Sa’ad da Ubangiji ya gama yin wa Musa magana a kan Dutsen Sinai, sai ya ba shi alluna biyu na Alkawari, allunan duwatsu rubutattu da yatsan Allah. Sa’ad da mutane suka ga Musa ya daɗe bai sauko daga dutse ba, sai suka taru kewaye da Haruna suka ce, “Zo, ka yi mana alloli waɗanda za su yi mana jagora. Game da wannan Musa wanda ya fitar da mu daga Masar dai, ba mu san abin da ya faru da shi ba.” Haruna ya amsa musu ya ce, “Ku tuttuɓe zoban zinariya waɗanda suke kunnuwan matanku, da na ’ya’yanku maza da mata, ku kawo mini.” Saboda haka dukan mutane suka tuttuɓe ’yan kunnensu suka kawo wa Haruna. Sai ya karɓi abubuwan da suka ba shi, ya yi gunki na siffar ɗan maraƙi, ya sassaƙa shi da kayan aiki. Sa’ad da mutane suka gani, sai suka tā da murya suka ce, “Waɗannan su ne allolinku, ya Isra’ila, waɗanda suka fitar da ku daga Masar.” Da Haruna ya ga haka, sai ya gina bagade a gaban ɗan maraƙi, ya yi shela ya ce, “Gobe akwai biki ga Ubangiji.” Saboda haka kashegari, mutane suka tashi da sassafe suka miƙa hadaya ta ƙonawa, da hadaya ta salama. Bayan haka suka zauna suka ci, suka sha, suka kuma tashi suka yi rawa. Sai Ubangiji ya ce wa Musa, “Sauka, gama mutanenka, waɗanda ka fitar da su daga Masar sun ƙazantu. Sun yi saurin juyawa daga abin da na umarce su, sun kuma yi wa kansu gunki na siffar ɗan maraƙi. Sun yi sujada ga ɗan maraƙi, suka yi hadaya gare shi, suka kuma ce, waɗannan su ne allolinka ya Isra’ila, waɗanda suka fito da kai daga Masar.” Ubangiji ya ce wa Musa, “Na ga waɗannan mutane, mutane ne masu taurinkai.” Yanzu ka bar ni kurum fushina yă yi ƙuna a kansu, in hallaka su. Sa’an nan in maishe ka al’umma mai girma. Amma Musa ya nemi tagomashin Ubangiji, Allahnsa ya ce, “Ya Ubangiji don me fushinka zai yi ƙuna a kan mutanenka, waɗanda ka fisshe su daga Masar da ikon hannunka mai girma? Don me za ka sa Masarawa su ce, ‘Ai, da mugun nufi ne ya fito da su don yă shafe su daga fuskar duniya’? Ka juya daga fushinka mai zafi, ka ji tausayi, kada ka kawo masifa a kan mutanenka. Ka tuna da bayinka Ibrahim, Ishaku da Isra’ila, waɗanda ka rantse da kanka cewa, ‘Zan mai da zuriyarka kamar taurarin sama kuma zan ba wa zuriyarka wannan ƙasa wadda na yi musu alkawari, za tă kuma zama abin gādonsu har abada.’ ” Sai Ubangiji ya yi juyayi, bai kuwa kawo wa mutanensa bala’in da ya yi niyya ba. Musa ya juya, ya sauka daga kan dutsen da alluna biyu na Alkawari a hannuwansa. An yi rubutun a kowane gefe, gaba da baya. Allunan aikin Allah ne; rubutun kuma rubutun Allah ne, da ya zāna a kan alluna. Sa’ad da Yoshuwa ya ji surutun mutane suna ihu, sai ya ce wa Musa, “Kamar akwai ƙarar yaƙi a sansani.” Musa ya amsa ya ce, “Ba ƙarar nasara ba ce, ba ƙarar wanda yaƙi ya ci ba ne; ƙarar waƙa ce nake ji.” Da Musa ya kusato sansanin, sai ya ga ɗan maraƙin da kuma mutane suna rawa. Sai fushinsa ya yi ƙuna, ya kuwa jefar da allunan da suke hannuwansa, allunan kuwa suka farfashe a gindin dutsen. Sai ya ɗauki ɗan maraƙin da suka yi, ya ƙone a wuta; sa’an nan ya niƙa shi ya zama gari, ya barbaɗa garin a ruwa, ya sa Isra’ilawa suka sha. Ya ce wa Haruna, “Mene ne waɗannan mutane suka yi maka da ka kai su ga wannan zunubi mai girma?” Haruna ya amsa ya ce, “Kada ka yi fushi da ni ranka yă daɗe, ka san yadda mutanen nan suke da saurin yin mugunta. Sun ce mini, ‘Ka yi mana alloli waɗanda za su yi mana jagora, game da wannan Musa dai, wanda ya fito da mu daga Masar, ba mu san abin da ya faru da shi ba.’ Sai na gaya musu, ‘Duk wanda yana da kayan ado na zinariya, ya cire?’ Sa’an nan suka ba ni zinariya, sai na jefa cikin wuta, wannan ɗan maraƙi ya fito.” Musa ya duba ya ga mutane sun kauce gaba ɗaya domin Haruna ya sa suka kauce, har suka zama abin dariya ga abokan gābansu. Saboda haka sai ya tsaya a ƙofar sansani ya ce, “Duk wanda yake na Ubangiji yă zo wurina.” Sai dukan Lawiyawa suka taru wurinsa. Sa’an nan ya ce musu, “Ga abin da Ubangiji, Allah na Isra’ila ya ce, ‘Kowane mutum yă rataya takobinsa, yă kai yă kawo daga wannan gefe zuwa wancan cikin sansani, kowa yă kashe ɗan’uwansa, da abokinsa, da kuma maƙwabcinsa.’ ” Lawiyawa suka yi yadda Musa ya umarta, a ranar, mutane wajen dubu uku suka mutu. Sa’an nan Musa ya ce, “An keɓe ku ga Ubangiji a yau, gama kun yi gāba da ’ya’yanku da ’yan’uwanku, ya kuma albarkace ku a wannan rana.” Kashegari Musa ya ce wa mutane, “Kun yi zunubi mai girma. Amma yanzu zan hau wurin Ubangiji; wataƙila zan iya yin kafara domin zunubinku.” Don haka Musa ya koma wurin Ubangiji ya ce, “Kaito, mutanen nan sun yi zunubi mai girma! Sun yi wa kansu allolin zinariya. Amma yanzu, ina roƙonka ka gafarta zunubinsu, in ba haka ba, to, ka shafe ni daga littafin da ka rubuta.” Ubangiji ya amsa wa Musa, “Duk wanda ya yi mini zunubi, shi zan shafe daga littafina. Yanzu tafi, ka jagoranci mutanen zuwa inda na yi zance, mala’ikana kuma zai sha gabanku. Duk da haka sa’ad da lokaci ya yi da zan yi horo, zan hore su domin zunubinsu.” Ubangiji kuwa ya bugi mutanen da annoba, saboda abin da suka yi da ɗan maraƙin da Haruna ya yi. Sa’an nan Ubangiji ya ce wa Musa, “Ka bar wannan wuri, kai da mutanen da ka fito da su daga Masar, ka haura zuwa ƙasar da na alkawarta da rantsuwa wa Ibrahim, Ishaku da Yaƙub cewa, ‘Zan ba zuriyarka.’ Zan aika da mala’ika a gabanka in kuma kori Kan’aniyawa, Amoriyawa, Hittiyawa, Ferizziyawa, Hiwiyawa da Yebusiyawa. Ka haura zuwa ƙasar da take zub da madara da zuma. Amma ba zan tafi tare da ku ba, saboda ku mutane ne masu taurinkai domin mai yiwuwa in hallaka ku a hanya.” Da mutane suka ji wannan mugun magana, sai suka fara makoki. Ba kuma wanda ya sa kayan ado. Gama Ubangiji ya riga ya ce wa Musa, “Ka faɗa wa Isra’ilawa, ‘Ku mutane ne masu taurinkai. In na yi tafiya da ku ko na ɗan lokaci, mai yiwuwa in hallaka ku. Yanzu sai ku tuɓe kayan adonku, zan kuwa yanke shawara a kan abin da zan yi da ku.’ ” Saboda haka Isra’ilawa suka tuttuɓe kayan adonsu a Dutsen Horeb. Musa fa ya saba ɗaukan tenti yă kafa shi a bayan sansani da ɗan nisa, yana kiransa “Tentin Sujada.” Duk wanda yake neman wani abu daga wurin Ubangiji sai yă tafi Tentin Sujada a bayan sansani. A sa’ad da kuma Musa ya fita zuwa Tentin, dukan mutanen sukan tashi su tsaya a ƙofofin tentinsu, suna kallon Musa, sai ya shiga tentin. Yayinda Musa ya shiga cikin tentin, sai al’amudin girgije yă sauko, yă tsaya a ƙofar yayinda Ubangiji yana magana da Musa. Lokacin da mutane suka ga al’amudin girgije a tsaye a ƙofar tentin, sai duk su miƙe tsaye su yi sujada, kowa a ƙofar tentinsa. Ubangiji yakan yi magana da Musa fuska da fuska, kamar yadda mutum yake magana da abokinsa. Sa’an nan Musa yă koma sansani, amma saurayin nan Yoshuwa ɗan Nun mai taimakonsa ba ya barin tentin. Musa ya ce wa Ubangiji, “Kana ta faɗa mini cewa, ‘Ka jagoranci mutane nan,’ amma ba ka faɗa mini wanda zai tafi tare da ni ba. Ga shi ka ƙara ce mini, ‘Na san ka, na san sunanka, ka kuma sami tagomashi a wurina.’ In ka ji daɗina, ka koya mini hanyarka don in san ka, in kuma ci gaba da samun tagomashi daga gare ka. Ka tuna cewa wannan al’umma mutanenka ne.” Ubangiji ya amsa ya ce, “Zan tafi tare da kai, zan kuma rage maka nauyin kaya.” Musa kuwa ya ce masa, “In ba za tă tafi tare da mu ba, to, kada ka ɗaga mu daga nan. Yaya wani zai sani ko ka ji daɗina da kuma mutanenka, in ba ka tafi tare da mu ba? Mene ne kuma zai bambanta ni da mutanenka daga sauran jama’ar da suke a duniya?” Sai Ubangiji ya ce wa Musa, “Zan yi yadda ka faɗa, gama ka sami tagomashi a wurina, na san ka, na kuma san sunanka.” Musa kuwa ya ce, “To, ka nuna mini ɗaukakarka.” Sai Ubangiji ya ce, “Zan wuce a gabanka, Ni Ubangiji zan yi shelar sunana a gabanka. Zan yi alheri ga duk wanda na so in yi masa alheri, zan nuna jinƙai ga duk wanda na so in yi masa jinƙai. Amma ya ce, ba za ka ga fuskata ba, don ba mutumin da zai gan ni yă rayu.” Sa’an nan Ubangiji ya ce, “Ga wani wuri kusa da ni inda za ka tsaya bisa dutsen. A sa’ad da ɗaukakata tana wucewa, zan sa ka a cikin tsaguwar dutsen, in rufe ka da hannuna har sai na wuce. Sa’an nan zan ɗauke hannuna, ka kuwa ga bayana; amma fuskata, ba za ka gani ba.” Ubangiji ya ce wa Musa “Sassaƙa alluna biyu kamar na farko, ni kuwa in rubuta kalmomin da suke cikin alluna na farko da ka farfasa. Ka shirya da safe, ka hauro kan Dutsen Sinai. Ka gabatar da kanka a gare ni a can kan dutse. Ba wani da zai zo tare da kai, ko a gan shi ko’ina a kan dutsen, kada garkunan tumaki ko na shanu su yi kiwo kusa da dutsen.” Saboda haka Musa ya sassaƙa alluna biyu na dutse kamar na fari, sai ya hau Dutsen Sinai da sassafe, kamar yadda Ubangiji ya umarce shi, yana kuma ɗauke da alluna biyu na dutse a hannuwansa. Sa’an nan Ubangiji ya sauko a cikin girgije ya tsaya can tare da shi, ya kuma yi shelar sunansa. Sai Ubangiji ya wuce a gaban Musa, ya yi shela ya ce, “Ni ne Ubangiji Allah mai tausayi, mai alheri, mai jinkirin fushi, cike da ƙauna da aminci, nakan nuna ƙauna wa dubbai, nakan kuma gafarta mugunta, tawaye da zunubi. Amma ba na barin mai laifi, ba tare da na hore shi ba; nakan hukunta ’ya’ya da jikoki har tsara ta uku da ta huɗu saboda laifin iyaye.” Musa ya yi sauri ya rusuna har ƙasa, ya yi sujada. Ya ce, “Ya Ubangiji, in na sami tagomashi a idanunka, bari Ubangiji yă tafi tare da mu. Ko da yake wannan mutane masu taurinkai ne, ka gafarta muguntanmu da zunubanmu, ka kuma sāke sa mu zama abin gādonka.” Sai Ubangiji ya ce, “Ga shi na yi alkawari da kai. A gaban dukan mutanenka zan yi abubuwan banmamakin da ba a taɓa yinsa a cikin wata al’umma a duniya ba. Mutanen da kuke zaune cikinsu za su ga aikin bantsoro, da Ni Ubangiji zan yi muku. Ku yi biyayya da umarnin da na ba ka yau. Zan kora muku Amoriyawa, Kan’aniyawa, Hittiyawa, Ferizziyawa, Hiwiyawa da Yebusiyawa. Ku kula, kada ku yi yarjejjeniya da waɗanda suke zaune a ƙasar da za ku tafi, in ba haka ba, za su zama muku tarko. Ku rurrushe bagadansu, ku farfashe keɓaɓɓun duwatsunsu, ku sassare ginshiƙan Asheransu. Kada ku bauta wa wani allah, gama Ubangiji, wanda sunansa Kishi, Allah ne mai kishi. “Ku kula, kada ku yi yarjejjeniya da mazaunan wannan ƙasa, don kada sa’ad da suke yi wa allolinsu sujada, suna miƙa musu hadaya, su gayyace ku, ku ci hadayar da suka miƙa wa allolinsu. Kada ku auro wa ’ya’yanku maza ’yan matansu, waɗanda suke yi wa alloli sujada, har su sa ’ya’yanku su bi allolinsu. “Kada ku yi alloli na zubi. “Sai ku yi Bikin Burodi Marar Yisti. Ku kuma ci burodi marar yisti har kwana bakwai, kamar yadda na umarce ku. Ku yi wannan a ƙayyadadden lokacinsa a watan Abib, gama a cikin watan ne kuka fita daga Masar. “Ɗan fari na kowane mutum zai zama nawa, har da ɗan farin na dabbobi, ko na garken shanu ko na tumaki. Ku fanshi ɗan farin jaki da na tunkiya, amma in ba ku fanshe shi ba, ku karya wuyansa. Ku fanshi duk ’ya’yan farinku maza. “Kada wani yă zo gabana hannu wofi. “Kwana shida za ku yi aiki, amma a rana ta bakwai za ku huta; ko da lokacin noma ne, ko lokacin girbi, sai ku huta. “Ku kiyaye Bikin Makoni wato, bikin girbin nunan fari na alkama, da Bikin Gama Tattara amfanin gonaki, a ƙarshen shekara. Sau uku a shekara, dukan mazanku za su bayyana a gaban Ubangiji Mai Iko Duka, Allah na Isra’ila. Zan kore al’umma daga gabanku, in fadada kan iyakarku, babu wanda zai yi ƙyashin ƙasarku a lokutan nan uku na shekara da kuka haura don ku bayyana a gaban Ubangiji, Allahnku. “Kada ku miƙa mini jinin hadaya tare da wani abin da yana da yisti, kada kuma ku bar kowace hadaya ta Bikin Ƙetarewa ta kwana. “Ku kawo nunan farin amfanin gonarku mafi kyau a gidan Ubangiji, Allahnku. “Kada ku dafa ɗan akuya a cikin madarar mahaifiyarsa.” Sa’an nan Ubangiji ya ce wa Musa, “Ka rubuta waɗannan kalmomi, gama bisa ga kalmomin nan, na yi alkawari da kai da kuma Isra’ila.” Musa ya kasance tare da Ubangiji kwana arba’in da dare arba’in, bai ci ba, bai sha ba. Ya kuma rubuta kalmomin alkawari a kan alluna, wato, dokoki goma. Sa’ad da Musa ya sauko daga kan Dutsen Sinai tare da alluna biyu na Alkawari a hannuwansa, bai san cewa fuskarsa tana ƙyalli ba saboda zaman da ya yi a gaban Ubangiji. Da Haruna da dukan Isra’ila suka ga Musa, fuskarsa kuma tana ƙyalli, sai suka ji tsoron zuwa kusa da shi. Amma Musa ya kira su, sai Haruna da dukan shugabannin jama’ar suka zo wurinsa, ya kuwa yi musu magana. Daga baya sai dukan Isra’ilawa suka zo kusa da shi, ya kuma ba su dukan dokokin da Ubangiji ya ba shi a Dutsen Sinai. Da Musa ya gama magana da su, sai ya lulluɓe fuskarsa. Amma duk sa’ad da ya je gaban Ubangiji don yă yi magana da shi, sai yă tuɓe lulluɓin har sai ya fito. Kuma duk sa’ad da ya fito yă faɗa wa Isra’ilawa abin da aka umarce shi, sai su ga fuskarsa tana ƙyalli. Sa’an nan Musa yă sāke lulluɓe fuskarsa, har sai ya shiga don yă yi magana da Ubangiji. Musa ya tara dukan jama’ar Isra’ilawa ya ce musu, “Waɗannan su ne abubuwan da Ubangiji ya umarce ku, ku yi. Kwana shida za ku yi aiki, amma rana ta bakwai za tă zama rana mai tsarki, Asabbaci ne na hutu ga Ubangiji. Duk wanda ya yi aiki a wannan rana dole a kashe shi. Kada ku hura wuta a cikin duk mazauninku a ranar Asabbaci.” Musa ya ce wa dukan jama’ar Isra’ilawa, “Ga abin da Ubangiji ya umarta. Daga cikin abin da kuke da shi, ku ɗauki kyauta domin Ubangiji, duk wanda yana niyya, sai yă kawo wa Ubangiji kyauta ta, “zinariya, azurfa da tagulla; shuɗi, shunayya da jan zare, lallausan lilin, da gashin akuya; fatun rago da aka rina ja, da fatun shanun teku; da itacen ƙirya da man zaitun don fitila; da kayan yaji don man shafewa, da kuma turare mai ƙanshi; duwatsun onis, da sauran duwatsu masu daraja waɗanda za a mammanne a efod da ƙyallen maƙalawa a ƙirji. “Duk waɗanda suke da fasaha a cikinku, su zo su yi dukan abin da Ubangiji ya umarta, “wato, aikin tabanakul da tentinsa tare da murfinsa, maɗauransa, katakansa, sandunansa da tussansa; akwatin alkawari da sandunansa, murfin kafara da labulen da ya rufe shi; tebur da sandunansa, da dukan kayansa da kuma burodin kasancewa; wurin ajiye fitila da yake don fitilu da kayayyakinsa, fitilu da mai don fitila; bagaden turare da sandunansa, man shafewa da turare mai ƙanshi; da labulen ƙofar shiga tabanakul; bagaden hadaya ta ƙonawa da rigarsa ta tagulla da sandunansa da duk kayayyakinsa, daron tagulla da wurin ajiye shi. Labulen filin tenti da sandunansa da tussansa, da kuma labulen ƙofar shiga fili; turakun tenti don tabanakul da kuma don filin, da igiyoyinsu; saƙaƙƙun riguna na sawa don hidima cikin wuri mai tsarki da tsarkakakkun riguna na Haruna firist, da riguna don ’ya’yansa maza lokacin da suke aiki a matsayin firistoci.” Sai dukan jama’ar Isra’ilawa suka janye daga fuskar Musa, duk waɗanda suke da niyya, waɗanda kuma zukatansu suka motsa su, suka kawo kyautai wa Ubangiji, don aikin Tentin Sujada, don duk aikinsa, da don tsarkakakkun riguna. Duk waɗanda suke da niyya, maza da mata, gaba ɗaya, suka kawo kayan ado na zinariya na kowane iri. ’Yan kunne, da ƙawane, da mundaye, da kayayyakin zinariya iri-iri. Dukansu suka miƙa zinariyarsu a matsayin hadaya ga Ubangiji. Kowane mutumin da yake da shuɗi, shunayya ko jan zare, ko lallausan lilin, ko gashin akuya, ko fatun rago da aka rina ja, ko fatun shanun teku, suka kawo. Masu miƙa kyautar azurfa, ko tagulla suka kawo su a matsayin kyautai ga Ubangiji, kuma kowane mutumin da yake da itacen ƙirya don kowane sashin aikin, ya kawo. Kowace mace mai fasaha ta kaɗa zare da hannuwanta, ta kuma kawo abin da ta kaɗa na shuɗi, shunayya, ko jan zare, ko lallausan lilin. Kuma dukan matan da suke da niyya, suke kuma da fasaha, suka kaɗa gashin akuya. Shugabannin suka kawo duwatsun Onis. Da duwatsu masu daraja don a jera a kan efod da ƙyallen maƙalawa a ƙirji. Suka kawo kayan yaji da man zaitun don fitila da don man shafewa da kuma don turare mai ƙanshi. Dukan mazan Isra’ilawa da matan da suke da niyya suka kawo wa Ubangiji kyautai na yardar rai, domin dukan aikin da Ubangiji ya umarce su ta bakin Musa. Sa’an nan ya ce wa Isra’ilawa, “Duba Ubangiji ya zaɓi Bezalel ɗan Uri, ɗan Hur, daga kabilar Yahuda, ya kuma cika shi da Ruhun Allah, da fasaha, azanci da kuma sani cikin dukan sana’ar hannu, don yă ƙirƙiro zāne-zāne na gwaninta waɗanda za yi da zinariya, da azurfa da kuma tagulla. Haka kuma wajen sassaƙar duwatsu na jerawa, da sassaƙar itace, da kowane irin aiki na gwaninta. Ya kuma ba Bezalel da Oholiyab ɗan Ahisamak, daga kabilar Dan, iyawa don koya wa waɗansu. Ya cika su da fasaha don yin kowane irin aikin sana’a, zāne-zāne, ɗinke-ɗinke shuɗi, shunayya da jan zare, da lallausan lilin, da kuma masu yin saƙa, sun gwaninta ƙwarai cikin kowane irin aikin hannu da kuma zāne-zāne. Saboda haka Bezalel, Oholiyab da kowane mutumin da Ubangiji ya ba shi basira da iyawa, na sanin yadda za a yi duk aikin shirya wuri mai tsarki, za su yi aiki yadda Ubangiji ya umarta.” Sa’an nan Musa ya kira Bezalel da Oholiyab da kowane mutumin da Ubangiji ya ba shi iyawa da kuma wanda ya yi niyya yă yi aiki. Suka karɓa daga wurin Musa dukan kyautai da Isra’ilawa suka kawo don su yi aikin shirya wuri mai tsarki. Mutane suka ci gaba da kawo kyautai yardar rai kowace safiya. Sai dukan masu fasaha waɗanda suke aikin wuri mai tsarki suka ɗan dakata suka ce wa Musa, “Mutane suna kawo fiye da abin da ake bukata domin aikin da Ubangiji ya umarta a yi.” Sai Musa ya ba da umarni, suka aika ko’ina a cikin sansani cewa, “Kada namiji ko ta mace yă sāke kawo kyauta don wuri mai tsarki.” Ta haka mutane suka daina kawowa. Saboda abin da suke da shi ya fi abin da ake bukata domin aikin. Dukan maza masu fasaha a cikin sauran masu aikin suka yi tabanakul da labule goma na tuƙaƙƙun lallausan lilin na shuɗi, da shunayya, da jan zare, aka yi wa labulen zānen kerubobi na gwaninta. Tsawon kowane labule, kamu ashirin da takwas ne, fāɗinsa kuma kamu huɗu. Dukan labulen, girmansu ɗaya ne. Suka ɗinɗinke labule biyar a harhaɗe, suka kuma yi haka da sauran labule biyar ɗin. Suka yi rami a gefe-gefen labulen da zaren ruwan bula, haka kuma suka yi da ɗayan gefen na biyu ɗin. Suka kakkafa rammuka hamsin a daidai bakin labulen, haka kuma suka yi a kan labule na biyun. Haka aka ɗaɗɗaura rammukan nan da junansu yă zama kamar abu guda. Sa’an nan suka yi maɗaurai hamsin na zinariya, suka yi amfani da su don daurin kashi biyu na labulen saboda tabanakul yă zama ɗaya. Suka yi labule da gashi akuya goma sha ɗaya don tenti a bisa tabanakul. Dukan labule goma sha ɗayan girmansu ɗaya ne, tsawonsa kamu talatin, fāɗinsa kuma kamu huɗu ne. Suka harhaɗa labule biyar wuri ɗaya, suka kuma harhaɗa shida wuri ɗaya. Sa’an nan suka yi rammuka hamsin a gefen labule na kashe na farko, haka kuma a gefen labule na ƙarshen na kashi biyar. Suka yi maɗaurin tagulla hamsin don su ɗaura tenti yă zama ɗaya. Sai suka yi wa tentin murfi da fatun rago da aka rina ja, a bisa wannan kuwa akwai murfin fatun shanun teku. Suka yi katakan tabanakul da itacen ƙirya. Tsawon kowane katako kamu goma ne, kaurinsa kuma kamu ɗaya da rabi, tare da katakai a fiƙe ɗaura da juna. Haka suka yi da dukan katakan tabanakul. Suka yi katakai ashirin don gefen kudu na tabanakul suka kuma yi rammukan azurfa arba’in don katakan su shiga ƙarƙashinsu, rammuka biyu domin kowane katako, ɗaya ƙarƙashin kowanne da aka fiƙe. A ɗaya gefen, gefen arewa na tabanakul, suka yi katakai ashirin da rammuka arba’in na azurfa, biyu-biyu don kowane katako. Suka yi katako shida don iyaka ta ƙarshe, wato, gefen yamma na tabanakul, aka kuma yi katakai biyu domin kusurwoyi tabanakul a iyaka ta ƙarshe. A waɗannan kusurwoyi biyu, an ninka katakan sau biyu daga ƙasa har sama, aka kuma sa su cikin zobe guda; dukansu biyu an yi su daidai. Ta haka aka sami katakai takwas da rammukan azurfa goma sha shida, biyu-biyu a ƙarƙashin kowane katako. Suka kuma yi sanduna na itace ƙirya, biyar domin katakan da suke a gefe guda na tabanakul, biyar domin waɗanda suke ɗayan gefen da kuma biyar domin katakan da suke gefen yamma na iyaka ta ƙarshen tabanakul. Suka sa sandan da yake a tsakiya yă wuce daga wannan gefe zuwa wancan. Sai suka dalaye katakan da zinariya, suka yi zoban zinariya don su riƙe sandunan. Suka kuma dalaye sandunan da zinariya. Suka kuma yi labule da shuɗi, shunayya, jan zare, da kuma lallausan lilin, suka kuma yi wa labulen zānen kerubobi na gwaninta. Suka yi dogayen sanduna huɗu na itacen ƙirya dominsa, suka dalaye su da zinariya. Suka yi ƙugiya na zinariya dominsa, suka yi rammuka huɗu da azurfa. Suka yi wa ƙofar tenti labulen shuɗi, shunayya, jan zare, da kuma lallausan lilin, aikin gwaninta; suka kuma yi dogayen sanduna biyar da ƙugiya dominsu. Suka dalaye saman dogayen sandunan da abin daurinsu da zinariya, suka kuma yi rammukansu guda biyar da tagulla. Bezalel ya yi akwatin alkawari da itacen ƙirya, tsawonsa kamu biyu da rabi, fāɗinsa kamu ɗaya da rabi, tsayinsa kamu ɗaya da rabi. Ya dalaye shi da zinariya zalla, ciki da waje, ya kuma yi zubin zinariya kewaye da shi. Ya yi masa zubi huɗu na zoban zinariya, ya kuma ɗaura su a ƙafafunsa huɗu, zobai biyu a wannan gefe da kuma biyu a wancan. Sa’an nan ya yi sanduna na itacen ƙirya, ya dalaye shi da zinariya. Sai ya sa sandunan a cikin rammukan da suke gefen Akwatin don ɗaukarsa. Ya yi murfin jinƙai da zinariya zalla, wato, tsawonsa ƙafa biyu, fāɗinsa kuma ƙafa ɗaya da rabi. Sa’an nan ya yi kerubobi biyu da ƙeraren zinariya a ƙarshen murfin jinƙan. Ya yi kerub a iyakar gefe ɗaya, ya yi ɗayan kuma a wancan gefe; a iyakan nan biyu, ya yi su a haɗe da murfin. Kerubobin suka buɗe fikafikansu sama, suka inuwatar da murfin da fikafikansu. Kerubobin suna fuskantar juna, suna kuma kallon murfin. Suka yi tebur da itacen ƙirya, tsawonsa ƙafa biyu, fāɗinsa ƙafa ɗaya, tsayinsa kuma ƙafa ɗaya da rabi. Sa’an nan suka dalaye shi da zinariya zalla, suka kuma yi zubi na zinariya kewaye da shi. Suka kuma yi masa baki mai fāɗin tafi hannu, suka yi zubin zinariya a bisa bakin. Suka yi zubin zobai huɗu na zinariya don tebur ɗin, sai suka ɗaura su a kusurwoyi huɗu inda ƙafafu huɗun suke. Sa’an nan aka sa zoban kurkusa da bakin don riƙe sandunan da ake amfani da su wurin ɗaukan teburin. An yi sandunan da ake ɗaukan tebur da itacen ƙirya, aka kuma dalaye su da zinariya. Suka kuma yi duk kayayyakin teburin da zinariya zalla, farantansa, kwanonin tuya, kwanoninsa, da kuma butoci domin hadaya ta sha. Suka yi wurin ajiye fitila da zinariya zalla, suka yi gindinsa da kuma gorar jikinsa, da ƙerarriyar zinariya. Kwaf wurin ajiye fitila da mahaɗansa, da furanninsa, a haɗe aka yi su da wurin ajiye fitilan. Akwai rassa guda shida da suka miƙe daga gefe wurin ajiyar fitilar, uku a wannan gefe, uku kuma a wancan. A reshe guda na wurin ajiye fitilan, akwai kwaf uku masu kama da tohon almon, akwai kuma uku a reshe na biye, haka kuma suke a dukan rassa shida da suke daga wurin ajiye fitilan. A bisa wurin ajiye fitilan kuma akwai kwaf huɗu da aka yi su kamar furannin almon da toho da kuma mahaɗai. Toho ɗaya yana a ƙarƙashin rassa biyu waɗanda suke daga wurin ajiye fitilan, toho na biyu yana a ƙarƙashin rassa biyu na biye, toho na uku kuma yana a ƙarƙashin rassa biyu na uku, duka-duka rassa shida ne. An ƙera mahaɗai da rassa wurin ajiye fitila a haɗe. Da ƙerarriyar zinariya aka yi wurin ajiye fitilar da dukan komensa a haɗe. Da zinariya zalla suka yi fitilu bakwai, da hantsuka da farantansa. Daga talenti ɗaya na zinariya zalla suka yi wurin ajiye fitila da dukan kayayyakinsa. Suka yi bagaden ƙona turare da itacen ƙirya. Shi bagaden, murabba’i ne, tsawonsa kamu ɗaya, fāɗinsa kamu ɗaya, tsayinsa kuma kamu biyu, ƙahoninsa kuwa a haɗe suke da shi. Suka dalaye saman da dukan gefe-gefen da kuma ƙahonin da zinariya zalla, suka kuma yi zubin zinariya kewaye da shi. Suka yi zobai biyu na zinariya a ƙarƙashin zubin, biyu-biyu ɗaura da juna, don su riƙe sandunan da za a ɗauka shi. Suka yi sandunan da itacen ƙirya, suka kuma dalaye su da zinariya. Suka kuma yi tsattsarkan mai na shafewa da kuma zalla turare mai ƙanshi, yadda mai yin turare yakan yi. Suka gina bagaden ƙona hadaya da itacen ƙirya, tsawonsa kamu biyar, fāɗinsa kamu biyar, murabba’i ke nan, tsayinsa kuwa kamu uku. Suka yi ƙahoni a kusurwansa huɗu, ƙahonin da bagade a haɗe suke, suka kuma dalaye bagaden da tagulla. Da tagulla kuma ya yi duk kayayyakin bagaden, da kwanoni, da babban cokali, da daruna, da cokula masu yatsotsi, da farantan wuta. Suka yi wa bagaden raga, tagulla kuma don yă sa shi a tsakiya. Suka yi zubin zoban tagulla don riƙe sanduna a kusurwoyi huɗu na ragar tagullar. Suka yi sanduna da itacen ƙirya, suka kuma dalaye su da tagulla. Suka sa sandunan a cikin zoban saboda su kasance a gefen bagade don ɗaukarsa, suka yi rami cikinsa. Suka yi daro da gammonsa da tagulla daga madubai na mata masu yin aiki a ƙofar Tentin Sujada. Suka kuma yi filin Tentin Sujada. Suka yi labulanta na gefen kudu da lallausan lilin, tsawonsu kamu ɗari, da sanduna ashirin da rammukan sandunan tagulla ashirin, da kuma ƙugiyoyin azurfa da maɗauri a kan sandunan. Tsawon labule na wajen gefen arewa kamu ɗari ne, yana kuma da sanduna guda ashirin da rammuka ashirin na tagulla, da ƙugiyoyin azurfa da maɗaurai a kan sandunan. Labule na gefen yamma kamu hamsin, da sanduna guda goma, da rammuka guda goma, da ƙugiyoyin azurfa da maɗaurai a kan sandunan. A ƙarshen gefen gabas, wajen fitowar rana, shi ma fāɗinsa kamu hamsin ne. Labule na gefe ɗaya na ƙofar, kamu goma sha biyar ne, da sanduna guda uku da rammukansu, akwai labule mai kamu goma sha biyar a ɗayan gefen ƙofar shiga zuwa filin Tentin Sujada, da sanduna uku da rammuka uku. An yi dukan labulan da suke kewaye da filin Tentin Sujada da lallausan zaren lilin. An yi rammukan sandunan da tagulla. An dalaye ƙugiyoyi da maɗauran da suke kan sandunan da azurfa; saboda haka dukan sandunan filin Tentin Sujada suna da maɗaurai na azurfa. Aka yi wa labulen ƙofar filin Tentin Sujada ado na ɗinki da na shuɗi, da na shunayya, da na jan zare, da na lallausan lilin, aikin gwaninta. Tsawonsa kamu ashirin, kuma kamar yadda labulen filin Tentin Sujada suke, tsayinsa kamu biyar ne, da sanduna guda huɗu da rammuka guda huɗu na tagulla. Ƙugiyoyinsu da maɗauransu na azurfa ne, aka kuma dalaye bisansu da azurfa. Aka yi dukan ƙarafan kafa tabanakul da kuma na kewayen filin Tentin Sujada da tagulla ne. Waɗannan su ne kayayyakin da aka yi amfani da su domin aikin tabanakul, da tabanakul na Shaida, waɗanda aka rubuta bisa ga umarnin Musa ta wurin Lawiyawa, a ƙarƙashin jagorancin Itamar ɗan Haruna, firist. (Bezalel ɗan Uri, ɗan Hur, na kabilar Yahuda, ya yi dukan abin da Ubangiji ya umarci Musa; tare da shi akwai Oholiyab ɗan Ahisamak, na kabilar Dan, shi gwani ne cikin aikin zāne-zāne, da ɗinki na shuɗi, da na shunayya, da na jan zare, da na lallausan lilin.) Jimillar zinariya daga hadaya ta kaɗawar da aka yi amfani da su domin aikin wuri mai tsarki ta kai talenti 29 da shekel 730, bisa ga ma’aunin shekel na tsattsarkan wuri. Azurfar da aka samu daga ƙidayar taron jama’a, talenti 100 ne, da shekel 1,775, bisa ga ma’aunin shekel na tsattsarkan wuri. Duk mutumin da ya shiga ƙirge daga mai shekaru ashirin zuwa gaba, ya ba da rabin shekel. Mazan da suka shiga ƙirge sun kai mutum 603,550. An yi amfani da azurfa talenti 100 don yin rammuka na wuri mai tsarki, da kuma rammukan labule, rammuka 100 daga talenti 100, talenti ɗaya don rami ɗaya. Suka yi amfani da shekel 1,775 don yin ƙugiyoyi saboda sanduna, suka dalaye bisan sandunan da maɗauransu. Tagullar da aka bayar daga hadaya ta kaɗawa ya kai talenti 70 da shekel 2,400. Suka yi amfani da shi don yin rammukan ƙofar Tentin Sujada, da bagaden tagulla tare da ragar tagulla da dukan kayayyakinsa, da rammukan sanduna don kewaye filin, da waɗanda suke ƙofarsa, da dukan ƙarafan kafa tenti don tabanakul, da kuma don kewaye filin. Daga zare mai ruwan shuɗi, da shuɗayya da kuma jan zare suka yi tsarkaken rigunan domin hidima a wuri mai tsarki. Suka kuma yi tsarkaken riguna don Haruna, yadda Ubangiji ya umarci Musa. Suka yi efod na zinariya, da shuɗi, da shunayya, da jan zare, da kuma lallausan lilin. Suka bubbuga zinariya ta zama falle, suka yayyanka ta zare-zare don su yi saƙa da ita, tare da zane na shuɗi, da na shunayya, da na jan zare, da na lallausan lilin, aikin gwani mai fasaha. Suka yi wa efod kafaɗu, sa’an nan suka haɗa su a gefenta biyu na sama, don a iya ɗaurawa. Gwanin mai saƙa ya saƙa abin ɗamarar efod. Da irin kayan da aka saƙa efod ne aka saƙa abin ɗamarar, wato, da zinariya, da shuɗi, da shunayya, da jan zare, da zaren lallausan lilin, yadda Ubangiji ya umarci Musa. Suka shimfiɗa duwatsun onis, suka jera su cikin tsaiko na zinariya, suka kuma zāna sunayen ’ya’yan Isra’ila a kan duwatsun kamar yadda akan yi hatimi. Sa’an nan suka ɗaura su a ƙyallen kafaɗun efod a matsayin duwatsun tuni wa ’ya’yan Isra’ila, yadda Ubangiji ya umarci Musa. Suka yi ƙyallen maƙalawa a ƙirji, aikin gwani. Suka yi shi kamar efod, na zinariya, da na shuɗi, da na shunayya, da na jan zare, da kuma na lallausan lilin. Ƙyallen maƙalawa a ƙirjin murabba’i ne, aka ninka shi biyu, tsawonsa da fāɗinsa kamu ɗaya-ɗaya ne. Sa’an nan suka sa jeri huɗu na duwatsu masu daraja a bisansa. A jeri na farko akwai yakutu, da tofaz, da zumurrudu; a jeri na biyu akwai turkuwoyis, da saffaya, da daimon; a jeri na uku akwai yakinta, da idon mage, da ametis; a jeri na huɗu akwai beril, da onis, da yasfa. Aka sa su cikin tsaiko na zinariya. Aka zāna duwatsu goma sha biyu, ɗaya don kowane sunan ’ya’yan Isra’ila goma sha biyu, kamar yadda akan yi hatimi. Sai suka yi tuƙaƙƙun sarƙoƙi na zinariya zalla a kan ƙyallen maƙalawa a ƙirji. Suka yi tsaiko biyu na zinariya da zoban zinariya biyu, suka kuma ɗaura zoban a kusurwoyi biyu na ƙyallen maƙalawa a ƙirji. Suka ɗaura sarƙoƙi biyu na zinariya da kusurwoyi na ƙyallen maƙalawa a ƙirji. Suka maƙala waɗancan bakin sarƙoƙin zinariya a tsaikon nan biyu, sa’an nan suka rataya su a kafaɗun efod daga gaba. Suka yi zobai biyu na zinariya suka haɗa, suka sa su a gefe biyu na ƙyallen maƙalawa a ƙirji daga ciki kusa da efod. Sa’an nan suka yi waɗansu ƙarin zobai biyu na zinariya, suka maƙale su daga ƙasa a gaban kafaɗu biyu na efod kusa da mahaɗin a bisa abin ɗamarar efod. Suka ɗaura zoban ƙyallen maƙalawa a ƙirjin a zoban efod da shuɗiyar igiya don ƙyallen maƙalawa a ƙirji, ya kwanta lif a bisa kan abin ɗamarar efod don kada yă kunce daga efod, sun yi yadda Ubangiji ya umarci Musa. Suka kuma saƙa taguwa ta efod da shuɗi duka, aikin gwani mai saƙa, an yi wa taguwar wuyan wundi a tsakiya kamar sulke, aka daje wuyan don kada yă kece. Suka yi fasalin ’ya’yan rumman da shuɗi, da shunayya, da jan zare, da lallausan lilin kewaye da gefe-gefen taguwar. Suka yi ƙararrawa da zinariya zalla, suka sa su a tsakanin fasalin ’ya’yan rumman kewaye da gefe-gefen taguwa. Aka jera ƙararrawan da ’ya’yan rumman bi da bi. Haka aka jera su kewaye da gefe-gefen taguwar aiki, yadda Ubangiji ya umarci Musa. Suka saƙa doguwar riga da lallausan lilin don Haruna da ’ya’yansa, aikin gwani mai saƙa, suka yi rawanin da lallausan lilin, da hulan lilin da rigunan ciki na lallausan lilin. Suka yi abin ɗamara da lallausan lilin da shuɗi, shunayya da jan zare, aikin gwanin mai ɗinki, yadda Ubangiji ya umarci Musa. Suka yi allo tsattsarka da zinariya tsantsa, suka zāna rubutu irin na hatimi a kansa haka, Mai tsarki ga Ubangiji. Sa’an nan suka ɗaura shi da shuɗiyar igiya a gaban rawanin, yadda Ubangiji ya umarci Musa. Ta haka aka gama dukan aikin tabanakul da Tentin Sujada. Isra’ilawa suka yi kome yadda Ubangiji ya umarci Musa. Sa’an nan suka kawo wa Musa tabanakul, tentin da dukan kayayyakinsa, ƙugiyoyinsa, katakansa, da sandunansa, da dogayen sandunansa da rammukansa; murfi na fatun rago wanda aka rina ja, da murfi na fatun shanun teku; da kuma laɓulen akwatin Alkawari da sandunansa da murfin kafara; tebur da dukan kayayyakinsa, da burodin Kasancewa; wurin ajiye fitilu na zinariya zalla, da jerin fitilunsa da dukan kayayyakinsa, da man fitila, bagade na zinariya, da man shafewa, da turare mai ƙanshi, da labulen ƙofar shiga tenti, bagade na tagulla na raga, da sandunansa da kayan aikinsa; da daro da wurin ajiyarsa, labulen filin, sandunansa da rammukansa, labulen ƙofar shiga filin; igiyoyi da ƙarafan kafa filin; dukan kayan aikin tabanakul da Tentin Sujada; da kuma saƙaƙƙun rigunan da ake sawa don hidima a wuri mai tsarki, duk da tsarkakan riguna na Haruna firist da rigunan ’ya’yansa maza, sa’ad da suke hidima a matsayin firistoci. Isra’ilawa suka yi dukan aikin nan yadda Ubangiji ya umarci Musa. Musa ya duba aikin, sai ya ga cewa sun yi shi daidai yadda Ubangiji ya umarta. Sai Musa ya sa musu albarka. Sa’an nan Ubangiji ya ce wa Musa, “Ka kafa tabanakul, da Tentin Sujada, a kan rana ta fari ga watan fari. Ka sa akwatin Alkawari a cikinsa, sa’an nan ka rufe shi da labule. Ka shigar da teburin ka shirya kayayyakin a kansa. Sa’an nan ka shigar da wurin ajiye fitilan ka kuma sa fitilunsa. Ka sa bagaden zinariya na ƙona turare a gaban akwatin Alkawari, ka kuma sa labule a ƙofar shiga tabanakul. “Ka ajiye bagade na yin hadaya ta ƙonawa a gaban ƙofar tabanakul, da Tentin Sujada; ka ajiye daron tsakanin Tentin Sujada da bagaden, ka kuma zuba ruwa a cikinsa. Ka yi fili kewaye da shi, ka kuma sa labule a ƙofar shiga filin. “Ka ɗauki man shafewa ka shafe tabanakul da duka abin da yake cikinsa; ka keɓe shi da dukan kayayyakinsa, zai zama tsarkake. Sa’an nan ka shafe bagaden hadaya ta ƙonawa da kayansa; ka keɓe bagaden, zai zama mai tsarki. Ka shafe daron da wurin ajiyarsa, ka kuma keɓe su. “Ka kawo Haruna da ’ya’yansa a ƙofar Tentin Sujada ka wanke su da ruwa. Sa’an nan ka sa wa Haruna tsarkakun riguna, ka shafe shi, ka kuma keɓe shi don yă yi mini hidima a matsayin firist. Ka kawo ’ya’yansa maza ka sa musu taguwoyi. Ka shafe su yadda ka shafe mahaifinsu, don su yi mini hidima a matsayin firistoci. Shafe musu man, zai sa su zama firistoci na ɗinɗinɗin, dukan zamanansu.” Musa ya aikata dukan kome yadda Ubangiji ya umarce shi. Da haka aka kafa tabanakul, a rana ta fari ga wata na fari a shekara ta biyu. Sa’ad da Musa ya kafa tabanakul, ya sa rammuka a wurinsu, ya sa katakan, ya kuma sa sandunan, ya kakkafa dogayen sandunan. Sa’an nan ya shimfiɗa tentin a bisa tabanakul, ya kuma sa murfi a bisa tentin, yadda Ubangiji ya umarce shi. Ya ɗauki dokokin Alkawari ya sa a cikin akwatin, ya kuma zura sandunan a zoban akwatin, sa’an nan ya sa murfin kafara a bisansa. Sai ya kawo akwatin a cikin tabanakul, ya kuma rataye labulen rufewa ya tsare akwatin Alkawarin, yadda Ubangiji ya umarce shi. Musa ya sa teburin a Tentin Sujada, a gefen arewa na tabanakul waje da labulen. Ya shirya burodin a kai a gaban Ubangiji, yadda Ubangiji ya umarce shi. Ya sa wurin ajiye fitilan a Tentin Sujada ɗaura da teburin a gefen kudu na tabanakul ya kuma shirya fitilun a gaban Ubangiji, yadda Ubangiji ya umarce shi. Musa ya sa bagaden zinariya a cikin Tentin Sujada a gaban labulen ya ƙone turare mai ƙanshi a kai, yadda Ubangiji ya umarce shi. Sa’an nan ya sa labule a ƙofar shiga na tabanakul. Ya sa bagaden hadaya ta ƙonawa kusa da ƙofar tabanakul, Tentin Sujada, sa’an nan ya miƙa hadaya ta ƙonawa da hadaya ta gari a kansa, yadda Ubangiji ya umarce shi. Ya sa daro tsakanin Tentin Sujada da bagade, ya kuma zuba ruwa a cikinsa don wanki, a cikin kuwa Musa da Haruna da ’ya’yansa maza sukan wanke hannunsa da ƙafafunsu. Sukan yi wanka a duk sa’ad da suka shiga Tentin Sujada, ko in suka kusaci bagade, yadda Ubangiji ya umarci Musa. Sa’an nan Musa ya yi fili kewaye da tabanakul da kuma bagaden, ya rataye labule a ƙofar shiga filin. Da haka Musa ya gama aikin. Sa’an nan girgije ya rufe Tentin Sujada sai ɗaukakar Ubangiji ta cika tabanakul. Musa bai iya shiga Tentin Sujada ba domin girgije ya riga ya sauka a kansa, ɗaukakar Ubangiji kuwa ta cika tabanakul. Cikin tafiyar Isra’ilawa duka, sukan kama tafiyarsu ne a duk sa’ad da girgijen ya tashi daga kan tabanakul. Idan girgijen bai tashi ba, ba za su tashi ba, sai a ranar da ya tashi. Gama a cikin tafiyarsu duka, girgijen Ubangiji yana kan tabanakul da rana, da dare kuwa wuta yake cikinsa domin dukan Isra’ilawa su gani. Ubangiji ya kira Musa ya yi masa magana daga cikin Tentin Sujada ya ce, “Yi magana da Isra’ilawa ka ce musu, ‘Duk sa’ad da waninku ya kawo hadaya ga Ubangiji, ku kawo hadayarku ta dabba daga garkenku ta shanu ko kuwa daga tumakinku. “ ‘In hadaya ta ƙonawar daga shanu ne, sai yă miƙa namiji marar lahani. Dole yă kawo shi a ƙofar Tentin Sujada don yă zama yardajje ga Ubangiji. Zai ɗibiya hannunsa a kan hadaya ta ƙonawar, za a kuwa karɓa a madadinsa don a yi kafara dominsa. Zai yanka ɗan bijimin a gaban Ubangiji, Haruna kuwa da ’ya’yansa maza firist, za su kawo jinin su kuma yafa shi a kan bagaden a kowane gefe a mashigin Tentin Sujada. Zai feɗe hadaya ta ƙonawar, yă yayyanka shi gunduwa-gunduwa. ’Ya’yan Haruna maza waɗanda suke firistoci za su hura wuta a bagade, su kuma shirya itace a kan wutar. Sa’an nan ’ya’yan Haruna maza waɗanda suke firistoci za su shirya gunduwa-gunduwar haɗe da kan da kuma kitsen a kan itace mai cin wuta wanda yake a kan bagaden. Zai wanke kayan cikin da kuma ƙafafun da ruwa, firist ɗin kuwa zai ƙone dukan waɗannan a kan bagade. Hadaya ce ta ƙonawa, hadaya ce kuma wadda aka yi da wuta, mai daɗin ƙanshi ga Ubangiji. “ ‘In hadaya ta ƙonawar daga garke ne, ko na tumaki, ko na awaki, zai miƙa namiji ne marar lahani. Zai yanka shi a gefen arewa na bagaden a gaban Ubangiji, ’ya’yan Haruna firistoci kuwa za su yayyafa jinin dabbar a bagaden a kowane gefe. Zai yanka shi gunduwa-gunduwa, firist kuwa zai shirya su haɗe da kan, da kuma kitsen a kan itace mai cin wutar da yake a kan bagade. Zai wanke kayan cikin da kuma ƙafafun da ruwa, firist ɗin kuwa zai ƙone dukan waɗannan a kan bagade. Hadaya ce ta ƙonawa, hadaya ce kuma wadda aka yi da wuta, mai daɗin ƙanshi ga Ubangiji. “ ‘In hadaya ga Ubangiji ɗin, hadaya ta ƙonawa ta tsuntsaye ce, zai miƙa kurciya ko ’yar tattabara. Firist zai kawo ta bagade, yă murɗe wuyan tsuntsun yă ƙone shi a kan bagade; zai tsiyaye jininsa tsuntsun a gefen bagaden. Amma zai ɗauki kayan cikin tsuntsun da gashin yă zubar da su a gefen bagaden a wajen gabas a wurin zuba toka. Zai tsaga shi biyu a tsaka, amma ba zai raba shi ba. Firist ɗin zai ɗibiya shi a bisa itacen da yake bisa bagaden, yă ƙone shi. Hadaya ce ta ƙonawa, hadaya ce kuma wadda aka yi da wuta, mai daɗin ƙanshi ga Ubangiji. “ ‘Sa’ad da wani ya kawo hadaya ta gari ga Ubangiji, hadayarsa za tă zama gari mai laushi ne. Zai zuba mai a kai, yă sa turare a kansa yă kai wa ’ya’yan Haruna maza waɗanda suke firistoci. Firist zai ɗiba gari mai laushin a tafin hannu da kuma man, tare da dukan turaren, yă ƙone wannan a sashen tunawa a kan bagade, hadaya ce da aka yi da wuta, mai daɗin ƙanshi ga Ubangiji. Sauran hadaya ta garin zai zama na Haruna da ’ya’yansa; sashe mafi tsarki ne na hadayar da aka yi ga Ubangiji ta wuta. “ ‘In kuka kawo toyayyen hadayar gari da aka yi daga matoya, zai ƙunshi gari mai laushi, toyayye ba tare da yisti ba, gauraye kuma da mai, ko kuwa ƙosai da aka yi ba tare da yisti ba, aka kuma kwaɓa da mai. In an toya hadaya ta garinku a kasko, sai a yi shi da gari mai laushi haɗe da mai, ba kuwa da yisti ba. A gutsuttsura shi, a zuba mai a kansa, hadaya ce ta hatsi. In hadayarku ta hatsin da aka dafa ne a tukunya, sai a yi shi da gari mai laushi da kuma mai. A kawo hatsin da aka yi da waɗannan abubuwa ga Ubangiji; a ba wa firist wanda zai ɗauka yă kai bagade. Zai fid da sashen tunawa daga hadaya ta gari, yă ƙone shi a kan bagade kamar hadayar da ka yi da wuta, mai daɗin ƙanshi ga Ubangiji. Sauran hadaya ta garin za tă zama ta Haruna da ’ya’yansa; sashe mafi tsarki ne na hadayun da aka yi ga Ubangiji ta wuta. “ ‘Kowace hadaya ta garin da kuka kawo ga Ubangiji, dole a yi shi ba tare da yisti ba, gama ba za ku ƙone wani yisti, ko zuma a cikin hadayar da aka yi ga Ubangiji ta wuta ba. Za ku iya kawo su ga Ubangiji kamar hadaya ta ’ya’yan fari, amma ba za a miƙa su a bagade kamar turare mai ƙanshi ba. A sa gishiri a dukan hadayunku na hatsi. Kada a rasa sa gishirin alkawari na Allahnku a hadayunku na hatsi, a sa gishiri a dukan hadayunku. “ ‘In kuka kawo hadaya ta gari na ’ya’yan fari ga Ubangiji, sai ku miƙa ɓarzajjen kawunan sabon hatsin da aka gasa a wuta. A sa mai da turare a kansa, hadaya ce ta hatsi. Firist zai ƙone sashe na ɓarzajjen hatsin da kuma mai, tare da turare don tunawa, gama hadaya ce da aka ƙone da wuta ga Ubangiji. “ ‘In hadayar wani mutum, hadaya ta salama ce, ya kuma miƙa ’yar dabba daga garke, ko namiji ko ta mace ce, sai yă miƙa dabbar da ba ta da lahani a gaban Ubangiji. Yă kuma ɗibiya hannunsa bisa kan hadayarsa, yă yanka ta a mashigin Tentin Sujada. Sa’an nan ’ya’yan Haruna waɗanda suke firistoci za su yayyafa jinin a kan bagade a kowane gefe. Daga hadaya ta zumuncin da zai kawo, sai a miƙa waɗannan hadayu na ƙonawa ga Ubangiji a wuta; wato, dukan kitsen da ya rufe kayan ciki ko kuwa da sun shafe su, da ƙodoji biyu tare da kitsen da yake kansu kusa da kwiɓi, da kuma murfin hanta waɗanda zai cire tare da ƙodoji. ’Ya’yan Haruna za su ƙone shi a kan bagade a bisa hadaya ta ƙonawa wadda take a kan itacen da yake cin wuta, kamar hadayar da ka yi da wuta, mai daɗin ƙanshi ga Ubangiji. “ ‘In ya miƙa dabba ce daga garke a matsayin hadaya ta salama ga Ubangiji, zai miƙa namiji ko ta mace marar lahani. In ya miƙa ɗan rago ne, zai kawo shi a gaban Ubangiji. Zai ɗibiya hannu a kan hadayarsa, yă yanka shi a gaban Tentin Sujada. Sa’an nan ’ya’yan Haruna maza za su yayyafa jinin dabbar a kowane gefe na bagade. Daga hadaya ta zumuncin zai kawo, sai a miƙa waɗannan hadayu na ƙonawa ga Ubangiji a wuta, wato, kitsen, ƙibabbiya wutsiyar gaba ɗaya da ya yanka gab da ƙashin gadon baya, dukan kitsen da ya rufe kayan ciki, ko kuwa da suka shafe su, da ƙodoji biyu tare da kitsen da yake kansu kusa da kwiɓi, da kuma murfin hanta waɗanda zai cire tare da ƙodoji. Firist zai ƙone su a kan bagade kamar hadayar abinci, wato, hadaya ce da aka ƙone da wuta ga Ubangiji. “ ‘In yana miƙa akuya ce, zai kawo ta a gaban Ubangiji. Zai ɗibiya hannunsa a kanta yă kuma yanka ta a gaban Tentin Sujada. Sa’an nan ’ya’yan Haruna maza za su yayyafa jininta a kowane gefe na bagade. Daga abin da zai miƙa sai a miƙa waɗannan hadayu na ƙonawa ga Ubangiji a wuta, wato, dukan kitsen da ya rufe kayan cikin, ko kuwa da suka shafe su, da ƙodoji biyu tare da kitsen da yake kansu kusa da kwiɓi, da kuma murfin hanta waɗanda zai cire tare da ƙodoji. Firist zai ƙone su a kan bagade kamar abinci, hadaya ce da aka yi da wuta, mai daɗin ƙanshi. Dukan kitsen na Ubangiji ne. “ ‘Wannan dawwammamiyar farilla ce ga tsararraki masu zuwa, a inda za ku zauna. Ba za ku ci wani kitse ko wani jini ba.’ ” Ubangiji ya ce wa Musa, “Faɗa wa Isra’ilawa cewa, ‘Sa’ad da wani ya yi zunubi ba da gangan ba, har ya karya ɗaya daga cikin dokokin Ubangiji, “ ‘In shafaffen firist ya yi zunubi, ya jawo wa jama’a laifi, dole yă kawo wa Ubangiji ɗan bijimi marar lahani a matsayin hadaya don zunubi saboda zunubin da ya yi. Zai kawo bijimin a ƙofar Tentin Sujada a gaban Ubangiji. Zai ɗibiya hannunsa a kan bijimin, yă kuma yanka shi a gaban Ubangiji. Sa’an nan shafaffen firist zai ɗiba jinin bijimin yă kai cikin Tentin Sujada. Yă tsoma yatsarsa a cikin jinin, yă kuma yafa sau bakwai a gaban Ubangiji, a gaban labulen wuri mai tsarki. Sa’an nan firist ɗin zai zuba jinin a ƙahonin bagaden turare masu ƙanshi da suke a gaban Ubangiji a Tentin Sujada. Sauran jinin bijimin zai zuba a gindin bagaden hadaya ta ƙonawa a ƙofar zuwa Tentin Sujada. Zai cire dukan kitsen daga bijimin hadaya don zunubi, kitsen da ya rufe kayan cikin, ko kuwa da suka shafe su, da ƙodoji biyu tare da kitsen da yake kansu kusa da kwiɓi, da kuma murfin hanta, waɗanda zai cire tare da ƙodoji. Zai cire su daidai kamar yadda akan cire na bijimin hadaya ta salama. Sai firist ɗin yă ƙone su a kan bagaden ƙona hadaya. Amma fatar ɗan bijimin, da namansa, da kansa, da ƙafafunsa, da kayan cikinsa, da hanjinsa, wato, dukan sauran bijimi, dole yă ɗauke su zuwa waje da sansani zuwa wani wuri mai tsabta inda ake zub da toka, yă ƙone shi a itacen da yake cin wuta a tarin toka. “ ‘In dukan jama’ar Isra’ilawa suka yi zunubi ba da gangan ba, har suka aikata ɗaya daga cikin abubuwan da Ubangiji ya umarta kada a yi, ko da yake jama’ar ba su san batun ba, duk da haka sun yi laifi. Sa’ad da suka gane da zunubin da suka aikata, dole taron su kawo ɗan bijimi a matsayin hadaya don zunubi, su kawo shi a gaban Tentin Sujada. Dattawan jama’a za su ɗibiya hannuwansu a kan bijimin a gaban Ubangiji, sai a yanka bijimin a gaban Ubangiji. Sa’an nan shafaffen firist zai ɗibi jinin bijimi zuwa cikin Tentin Sujada. Zai tsoma yatsarsa cikin jini yă kuma yayyafa shi a gaban Ubangiji sau bakwai a gaban labule. Zai zuba jinin a ƙahonin bagaden da suke gaban Ubangiji a cikin Tentin Sujada. Zai zuba sauran jinin a gindin bagaden hadaya ta ƙonawa a ƙofar zuwa Tentin Sujada. Zai cire dukan kitsen daga gare shi yă ƙone a kan bagade, yă kuma yi da wannan bijimi kamar yadda ya yi da bijimi na hadaya don zunubi. Ta haka firist zai yi kafara dominsu, za a kuwa gafarta musu. Sa’an nan zai ɗauki bijimin waje da sansani yă ƙone shi kamar yadda ya ƙone bijimi na fari. Wannan ita ce hadaya don zunubi domin jama’a. “ ‘Sa’ad da shugaba ya yi zunubi ba da gangan ba, har ya aikata ɗaya daga cikin abubuwan da Ubangiji Allahnsa ya umarta, to, ya yi laifi. Sa’ad da aka sanar da shi game da zunubin da ya yi, dole yă kawo bunsuru marar lahani a matsayin hadayarsa. Zai ɗibiya hannunsa a kan bunsurun yă kuma yanka shi a inda ake yankan hadayar ƙonawa a gaban Ubangiji. Hadaya ce ta zunubi. Sa’an nan firist zai ɗibi jinin hadaya don zunubi da yatsarsa yă sa a ƙahonin bagaden hadayar ƙonawa, yă kuma zuba sauran jinin a gindin bagade. Zai ƙone dukan kitse a kan bagade kamar yadda ya ƙone kitsen hadaya ta salama. Ta haka firist zai yi kafara saboda zunubin mutumin, za a kuwa gafarta masa. “ ‘In wani memba a cikin jama’a ya yi zunubi ba da gangan ba, ya aikata ɗaya daga cikin abubuwan da Ubangiji ya umarta kada a yi, to, ya yi laifi. Sa’ad da aka sanar da shi game da zunubin da ya yi, dole yă kawo akuya marar lahani a matsayin hadayarsa domin zunubin da ya yi. Zai ɗibiya hannunsa a kan hadaya don zunubin yă kuma yanka ta a inda ake hadaya ta ƙonawa. Sa’an nan firist zai ɗibi jinin da yatsarsa yă zuba a ƙahoni a bagaden hadaya ta ƙonawa, yă kuma zuba sauran jinin a ƙasan bagade. Za a ɗebe kitsenta duka kamar yadda akan ɗebe kitsen hadaya ta salama. Firist zai ƙona shi a kan bagaden don ƙanshi mai daɗi ga Ubangiji. Ta haka firist zai yi kafara dominsa, za a kuwa gafarta masa. “ ‘Idan kuwa daga cikin ’yan tumaki zai ba da hadayarsa, sai ya kawo ’yar tunkiya marar lahani. Zai ɗibiya hannunsa a kanta yă kuma yanka ta hadaya don zunubi a inda ake yankan hadayar ƙonawa. Sa’an nan firist zai ɗibi jinin hadaya don zunubin da yatsarsa yă zuba a ƙahonin bagaden hadayar ƙonawa, yă kuma zuba sauran jinin a gindin bagade. Zai kuma ɗebe kitsenta duka kamar yadda a kan ɗebe na ragon hadaya ta salama. Firist zai ƙone shi a bisa bagaden a bisa hadaya ta ƙonawa ga Ubangiji. Ta haka firist ɗin zai yi kafara dominsa saboda zunubin da ya yi, za a kuwa gafarta masa. “ ‘Mutum zai yi zunubi in bai yi magana ba sa’ad da ya ji ana shelar neman shaida game da wani abin da ya gani ko kuwa ya ji, alhakin zai zauna a wuyansa. “ ‘Ko kuwa in mutum ya taɓa wani abin da yake mai ƙazanta, ko gawar naman jeji marar tsabta, ko na shanu marar tsabta, ko na halittu marasa tsabtan da suke motsi a ƙasa; ko da yake bai sani ba, ya ƙazantu ke nan, kuma ya yi laifi. Ko kuwa in ya taɓa rashin tsabta na mutane, wani abin da zai sa shi rashin tsabta; ko da yake bai sani ba, sa’ad da ya gane, zai zama mai laifi. Ko kuwa in mutum bai yi tunani ba, ya yi rantsuwar yin wani abu, ko mai kyau ko marar kyau; ko da yake bai sani ba, duk da haka sa’ad da ya gane zai zama mai laifi. Sa’ad da wani yana da laifi a kowanne cikin waɗannan hanyoyi, dole yă furta a hanyar da ya yi zunubin kuma don zunubin da ya yi, dole yă kawo wa Ubangiji tunkiya ko akuya daga garke kamar hadaya don zunubi; firist kuwa zai yi kafara dominsa da kuma domin zunubinsa. “ ‘In ba zai iya kawo tunkiyar ba, sai yă kawo kurciyoyi biyu ko tattabarai biyu ga Ubangiji a matsayin hakki don zunubinsa, ɗaya domin hadaya don zunubi ɗayan kuma domin hadaya ta ƙonawa. Zai kawo su wa firist, wanda da fari zai miƙa ɗaya domin hadaya don zunubi. Zai murɗe kan daga wuyanta, ba tare da tsinke kan gaba ɗaya ba, zai kuma yayyafa jinin hadaya don zunubin a gefen bagade; a tsiyaye sauran jinin kuma a gindin bagade. Hadaya ce ta zunubi. Firist zai miƙa ɗayan matsayin hadaya ta ƙonawa bisa ga yadda aka tsara, yă kuma yi kafara dominsa saboda zunubin da ya yi, za a kuwa gafarta masa. “ ‘In ba zai iya kawo kurciyoyi biyu ko tattabarai biyu ba, sai yă kawo humushin garwan gari mai laushi domin hadaya don zunubi. Ba lalle ba ne yă sa mai ko turare a kansa, saboda wannan hadaya ce ta zunubi. Zai kawo wa firist, firist kuwa zai ɗiba da hannu don yă kasance abin tunawa, sai yă ƙone a bisan bagaden kamar hadayar da ake ƙona da wuta ga Ubangiji. Hadaya ce ta zunubi. Ta haka firist zai yi kafara dominsa saboda dukan waɗannan zunuban da ya yi, za a kuwa gafarta masa. Sauran hadayar za tă zama ta firist, kamar yadda yake bisa ga hadaya ta gari.’ ” Ubangiji ya ce wa Musa, “Sa’ad da mutum ya ci amana, ya kuma yi zunubi ba da gangan ba dangane da wani cikin abubuwa masu tsarki na Ubangiji, zai kawo ga Ubangiji rago daga garke wanda ba shi da lahani saboda yin hadaya don laifinsa. Za a kimata kuɗinsa bisa ga ma’aunin shekel na tsattsarkan wuri. Hadaya ce ta laifi. Dole yă biya abin da ya kāsa yi dangane da abubuwa masu tsarki, yă ƙara kashi ɗaya bisa biyar na darajar abin a kan wannan sa’an nan yă ba wa firist. Firist kuwa zai yi kafara dominsa da ragon hadaya don laifi. Za a kuwa gafarta masa. “In mutum ya yi zunubi, ya aikata ɗaya daga cikin abubuwan da Ubangiji ya umarta kada a yi, ko da yake bai sani ba, shi mai laifi ne. Za a kuwa nemi hakki daga gare shi. Zai kawo wa firist rago daga garke, marar lahani. Za a kimanta tamanin rago daidai da tamanin hadaya don laifi. Firist kuwa zai yi kafara don kuskuren da mutumin ya yi ba da saninsa ba, za a gafarta masa. Hadaya ce ta laifi, ya yi laifi na abin da ya yi marar kyau ga Ubangiji.” Ubangiji ya ce wa Musa, “In wani ya yi zunubi bai kuma yi aminci ga Ubangiji ba, wato, ta wurin yin wa abokin zamansa karya game da ajiyar da abokin ya ba shi amana, ko a kan wani alkawarin da suka yi wa juna, ko kuwa a kan yă cuci abokin, ko kuma idan ya sami abin da ya ɓace amma ya yi ƙarya cewa bai samu ba. Ko ya yi rantsuwar ƙarya a kan duk irin abubuwan da akan aikata na laifi, sa’ad da mutum ya yi irin laifin nan, ya kuwa tabbata mai laifi ne, to, sai yă komar da abin da ya ƙwace, ko abin da ya samu ta hanyar zalunci, ko abin da aka ba shi ajiya, ko abin da ya tsinta. Zai mai da abin da ya yi rantsuwar ƙarya a kai. Zai mayar wa mai abin da abinsa a yadda yake, har yă ƙara kashi ashirin bisa ɗari na abin. A ranar da zai yi hadaya don laifinsa, a ranar ce zai mayar wa mai abin da abinsa. A matsayin hakki kuwa, dole yă kawo wa firist, wato, ga Ubangiji, hadaya rago marar lahani kuma wanda aka kimanta tamaninsa daga garke don laifinsa. Ta haka firist zai yi kafara dominsa a gaban Ubangiji, za a kuwa gafarta masa irin laifin da ya yi.” Ubangiji ya ce wa Musa, “Ka ba Haruna da ’ya’yansa maza wannan umarni, ‘Waɗannan su ne ƙa’idodi don hadaya ta ƙonawa. Hadaya ta ƙonawa za tă kasance a bagade dukan dare, sai da safe, kuma dole a bar wutar tă yi ta ci a bisa bagaden. Sa’an nan firist zai sa rigunarsa ta lilin da kuma rigar lilin da ake sa a ciki, sa’an nan yă kwashe tokan hadaya ta ƙonawa da wuta da ta ci a kan bagaden, yă sa kusa da bagaden. Sa’an nan yă tuɓe waɗannan rigunan yă sa waɗansu, sa’an nan yă ɗauki tokar yă kai waje da sansani zuwa inda yake da tsabta. Dole a bar wutar da take bisa bagaden tă yi ta ci; kada tă mutu. Kowace safiya firist zai ƙara itacen wuta, yă shirya hadaya ta ƙonawa a bisa wutar yă kuma ƙone kitsen hadaya ta salama a kansa. Dole a bar wutar tă ci gaba da ci a bisa bagade; kada tă mutu. “ ‘Waɗannan su ne ƙa’idodi domin hadaya ta gari. ’Ya’yan Haruna za su kawo ta a gaban Ubangiji, a gaban bagaden. Firist zai ɗiba garin hadayar mai laushin wanda aka zuba masa mai da kuma turare cike da tafin hannu. Zai ƙona wannan a bisa bagaden, hadaya ce mai daɗin ƙanshi ga Ubangiji don tunawa. Haruna da ’ya’yansa maza za su ci sauran, amma za a ci shi ba tare da yisti ba a tsattsarkan wuri; za su ci shi a harabar Tentin Sujada. Ba za a toya shi da yisti ba; na ba su yă zama rabonsu daga cikin hadayun da ake ƙonawa da wuta, abu ne mafi tsarki, kamar hadaya don zunubi da laifi. Kowane ɗa namiji cikin zuriyar Haruna zai iya cinsa. Wannan rabonsa ne na kullum na hadayar da aka yi ga Ubangiji da wuta. Wannan madawwamiyar doka ce cikin zamananku duka. Duk abin da ya taɓa hadayun zai tsarkaka.’ ” Ubangiji ya kuma ce wa Musa, “Wannan ne hadayar da Haruna da ’ya’yansa maza za su kawo ga Ubangiji a ranar da za a naɗa su firistoci, humushin garwan gari mai laushi a matsayin hadaya ta gari na kullum, rabinsa da safe, rabinsa kuma da yamma. A shirya shi da mai a kwanon tuya, a kawo shi kwaɓaɓɓe sosai, a miƙa shi hadaya ta gari dunƙule-dunƙule don ƙanshi mai daɗi ga Ubangiji. Duk wanda aka naɗa daga ’ya’yan Haruna yă zama firist a madadinsa, shi ne zai miƙa wannan hadayar ga Ubangiji. Zai ƙone hadayar ƙurmus. Wannan za tă zama dawwammamiyar farilla ce har abada. Kowace hadaya ta gari ta firist, za a ƙone ta ƙurmus, ba za a ci ba.” Ubangiji ya ce wa Musa, “Faɗa wa Haruna da ’ya’yansa maza, ‘Waɗannan su ne ƙa’idodi domin hadaya don zunubi. Za a yanka hadaya don zunubi a gaban Ubangiji a inda ake yankan hadaya ta ƙonawa; dole tă kasance mai tsarki. Firist da ya miƙa ta zai ci, za a ci ta a tsattsarkan wuri, a harabar Tentin Sujada. Duk abin da ya taɓa wani sashe na naman, zai zama da tsarki, kuma in wani jini ya ɗiga a riga, dole ka wanke shi a tsattsarkan wuri. Dole a farfashe tukunyar lakar da aka dafa naman a ciki; amma in an dafa a tukunyar tagulla, sai a kankare tukunyar, a kuma ɗauraye da ruwa. Kowane namiji a iyalin firistoci zai iya ci; gama abu ne mafi tsarki. Amma duk wata hadaya don zunubi wadda aka kawo jininta cikin Tentin Sujada don a yi kafara a Wuri Mai Tsarki, ba za a ci ba. A maimako haka za a ƙone ta ɗungum. “ ‘Waɗannan su ne ƙa’idodi na hadaya don laifi, hadaya ce tsattsarka. Za a yanka hadaya don laifi a inda ake yanka hadaya ta ƙonawa, za a kuma yayyafa jinin a kowane gefe na bagade. Za a miƙa kitsen abin hadaya duka, da wutsiya mai kitse, da kitsen da yake rufe da kayan ciki, da ƙodoji biyu da kitsen da yake a bisansu kusa da kwiɓi, da kuma rufin hanta, wanda za a cire tare da ƙodoji. Firist zai ƙone su a kan bagade, hadaya ce da aka ƙone da wuta ga Ubangiji. Hadaya ce don laifi. Kowane da namiji cikin iyalin firistoci zai iya ci. Sai a tsattsarkan wuri ne za a ci; gama abu mafi tsarki ne. “ ‘Hadaya don laifi kamar hadaya don zunubi take, saboda haka ƙa’ida hanyar yinsu iri ɗaya ce. Su ɗin na firist da ya yi kafara da su ne. Firist da ya miƙa hadaya ta ƙonawa domin wani, zai iya ajiye fatar wa kansa. Kowace hadaya ta garin da aka toya a tanda, ko aka dafa a tukunya ko a kan kaskon tuya, na firist da ya miƙa ta ne, kuma kowace hadaya ta gari wadda aka kwaɓa da mai, ko wadda ba a kwaɓa ba, ita ma, ta dukan ’ya’ya Haruna ne maza. “ ‘Waɗannan su ne ƙa’idodin hadaya don zumuncin da mutum zai iya miƙa ga Ubangiji. “ ‘In ya miƙa hadayar a matsayin hadaya ta godiya ce, to, zai miƙa ta tare da burodi mai kauri marar yisti, wanda aka kwaɓa da mai, da burodi marar kauri, wanda aka shafa wa mai, da kuma burodi mai kauri da aka yi da gari mai laushi wanda aka kwaɓa sosai da mai. Tare da hadayarsa don zumunci ta godiya, zai miƙa dunƙulen burodin da aka yi da yisti. Zai kuma kawo ɗaya daga kowace a matsayin hadaya, baiko ne ga Ubangiji. Wannan zai zama na firist da ya yafa jinin hadaya ta salama ne. Za a ci wannan nama na hadaya don zumunci ta godiya a ranar da aka miƙa ta, kada yă bar wani abu daga naman yă kwana. “ ‘In hadayarsa cika wa’adin rantsuwa ce ko kuwa ta yardar rai ce, sai a ci hadayar a ranar da ya miƙa ta, amma za a iya cin duk abin da ya rage kashegari. Duk naman hadayar da ya rage har kwana uku, dole a ƙone shi. Idan aka ci naman hadayarsa ta salama a rana ta uku, ba za a karɓi wanda ya ba da hadayar har ya sami albarkar hadayar ba, naman zai zama abin ƙyama, duk wanda ya ci kuwa ya yi laifi. “ ‘Ba za a ci naman da ya taɓa wani abu marar tsarki ba; dole a ƙone shi. Game da sauran nama, kowa da yake mai tsarki zai iya ci. Amma in wani wanda ba shi da tsarki ya ci naman hadaya ta salama ga Ubangiji, za a fid da mutumin daga cikin mutanensa. Idan wani mutum ya taɓa abu marar tsarki, ko mutum ne, ko dabba ce, ko wani abu na banƙyama, ya kuma ci naman hadaya ta salama ga Ubangiji, za a fid da mutumin daga cikin mutanensa.’ ” Ubangiji ya ce wa Musa, “Ka faɗa wa Isra’ilawa, ‘Kada ku ci wani kitsen shanu, ko na tumaki, ko kuwa na awaki. Za a iya yin wani amfani da kitsen dabbar da ta mutu mushe, ko kitsen dabbar da namun jeji su yayyaga, amma kada a kuskura a ci. Duk wanda ya ci kitsen dabbar da aka miƙa ta wuta ga Ubangiji, za a fid da shi daga mutanensa. Kuma duk inda kuke zama, ba za ku ci jinin wani tsuntsu ko na dabba ba. Duk wanda ya ci jini, za a fid da mutumin daga mutanensa.’ ” Ubangiji ya ce wa Musa, “Faɗa wa Isra’ilawa, ‘Duk wanda ya kawo hadaya ta salama ga Ubangiji, sai ya kawo hadayarsa ga Ubangiji daga cikin hadayu na salama. Da hannuwansa zai kawo hadayar da za a ƙona ga Ubangiji; zai kawo kitsen tare da ƙirjin, yă kuma kaɗa ƙirjin a gaban Ubangiji a matsayin hadaya ta kaɗawa. Firist zai ƙone kitsen a bisa bagade, amma ƙirjin zai zama na Haruna da ’ya’yansa maza. Za ku ba da cinya ta dama ta hadaya don zumuncinku ga firist a matsayin baiko. Ɗan Haruna da ya miƙa jini da kitsen hadaya ta salama, zai ɗauki cinyar tă zama rabonsa. Daga hadaya ta salama ta Isra’ilawa, na ɗauki ƙirjin da aka kaɗa da kuma cinyar da aka miƙa, na ba da su ga Haruna firist da kuma ’ya’yansa maza a matsayin rabonsu na kullum daga Isra’ilawa.’ ” Wannan shi ne sashen hadayar da aka ba wa Haruna da ’ya’yansa maza, hadayar da aka yi ga Ubangiji da wuta, tun ranar da aka gabatar da su don su yi wa Ubangiji hidima a matsayin firist. A ranar da aka keɓe su, Ubangiji ya umarta cewa Isra’ilawa su ba da wannan a gare su a matsayin rabonsu na kullum, a dukan tsararraki masu zuwa. Waɗannan su ne ƙa’idodi don hadaya ta ƙonawa, hadaya ta gari, hadaya don zunubi, hadaya don laifi, hadaya ta naɗi da kuma hadaya ta salama, waɗanda Ubangiji ya ba wa Musa a Dutsen Sinai, a Hamadar Sinai, a ranar da ya umarci Isra’ilawa su kawo hadayunsu ga Ubangiji. Ubangiji ya ce wa Musa, “Kawo Haruna da ’ya’yansa maza, ka ɗauki rigunansu, man keɓewa, bijimi domin hadaya don zunubi, ’yan raguna biyu da kuma kwandon da yake da burodi marar yisti, ka kuma tara dukan jama’a a ƙofar Tentin Sujada.” Sai Musa ya yi yadda Ubangiji ya umarce shi, jama’a kuwa suka taru a ƙofar Tentin Sujada. Sai Musa ya ce wa jama’ar, “Ga abin da Ubangiji ya umarta a yi.” Sa’an nan Musa ya kawo Haruna da ’ya’yansa maza gaba, ya kuma wanke su da ruwa. Ya sa wa Haruna taguwa, ya ɗaura igiya kewaye da shi, ya sa masa riga, ya sa masa efod. Ya kuma ɗaura masa efod wanda aka yi masa saƙar gwaninta. Ya sa masa ƙyallen maƙalawa a ƙirji, ya kuma sa Urim da Tummim a ƙyallen maƙalawa a ƙirjin. Sai ya naɗa masa rawani, daga gaban rawanin ya sa allon zinariya, wato, kambi tsattsarka, kamar yadda Ubangiji ya umarce shi. Sa’an nan Musa ya ɗauki man keɓewa ya keɓe tabanakul da kuma kowane abin da yake cikinsa, ta haka ya tsarkake su. Ya yayyafa mai a kan bagade sau bakwai, yana keɓe bagade da dukan kayayyaki, da daro, da abin da yake tsaya a kai, don yă tsarkake su. Ya zuba man keɓewa a kan Haruna, ya kuma keɓe shi don yă tsarkake shi. Sa’an nan ya kawo ’ya’yan Haruna maza, ya sa musu taguwoyi, ya ɗaɗɗaura igiyoyi kewaye da su, ya kuma sa musu huluna yadda Ubangiji ya umarce shi. Sa’an nan ya miƙa bijimi domin hadaya don zunubi, sai Haruna da ’ya’yansa suka ɗibiya hannuwansu a bijimin. Musa ya yanka bijimin ya ɗauki jinin, ya sa yatsarsa ya zuba a dukan ƙahonin bagade don yă tsarkake bagaden. Ya zuba sauran jinin a gindin bagade. Ta haka ya tsarkake shi don yă yi kafara dominsa. Musa ya ɗebo dukan kitsen da yake kewaye da kayan ciki, da kuma wanda ya rufe hanta, da ƙodojin, da kuma kitsensu, ya kuma ƙone su a kan bagade. Amma bijimin da fatarsa da namansa da kuma ƙashinsa ya ƙone su a bayan sansani, yadda Ubangiji ya umarce shi. Sa’an nan ya miƙa ɗan rago domin hadaya ta ƙonawa, sai Haruna da ’ya’yansa maza suka ɗibiya hannuwansu a kan ɗan rago. Sa’an nan Musa ya yanka ɗan ragon, ya kuma yayyafa jinin a kowane gefe na bagaden. Ya yanka ragon gunduwa-gunduwa ya ƙone kan, ya kuma ƙone gunduwa-gunduwan da kitsen. Ya wanke kayan cikin da ƙafafun a ruwa, ya kuma ƙone dukan ragon a bisa bagade kamar hadaya ta ƙonawa, mai daɗin ƙanshi, hadaya ce da aka ƙone da wuta ga Ubangiji, yadda Ubangiji ya umarce shi. Sai ya miƙa ɗayan ɗan ragon, ɗan ragon naɗin, sai Haruna da ’ya’yansa maza suka ɗibiya hannuwansu a kan ɗan ragon. Musa kuwa ya yanka ɗan ragon ya ɗibi jinin ya sa leɓatun kunnen dama na Haruna, ya kuma sa a babbar yatsarsa ta hannun dama da kuma a babbar yatsar ƙafarsa ta dama. Musa ya kuma kawo ’ya’yan Haruna gaba, ya sa jini a leɓatun kunnuwansu na dama, ya kuma sa a manyan yatsotsinsu na hannun dama da kuma a manyan yatsotsinsu na ƙafafunsu na dama. Sa’an nan ya yayyafa jinin a kowane gefen bagade. Ya ɗibi kitsen, da wutsiya mai kitse, da kuma dukan kitsen da ke kewaye da kayan ciki, da wanda ya rufe hanta, ƙodoji biyu da kitsensu da kuma cinya ta dama. Sa’an nan daga cikin kwandon burodi marar yisti wanda yake a gaban Ubangiji, ya ɗauko dunƙulen burodi, da kuma guda da aka yi da mai, da kuma ƙosai; ya sa waɗannan a sassan kitsen, da kuma a cinya ta dama. Ya sa waɗannan a hannuwan Haruna da ’ya’yansa, suka kuma kaɗa su a gaban Ubangiji a matsayin hadaya ta kaɗawa. Sa’an nan Musa ya karɓe su daga hannuwansu ya ƙone a bagade a bisa hadaya ta ƙonawa a matsayin hadaya ta naɗi, mai daɗin ƙanshi, hadaya ce da aka ƙone da wuta ga Ubangiji. Ya kuma ɗauki ƙirjin; rabon Musa na ɗan ragon naɗi, ya kaɗa shi a gaban Ubangiji, a matsayin hadaya ta kaɗawa, yadda Ubangiji ya umarce shi. Sai Musa ya ɗibi man keɓewa da jini daga bagade, ya yayyafa su a kan Haruna da rigunansa, da kuma a kan ’ya’yansa da rigunansu, don yă tsarkake Haruna da rigunansa da kuma ’ya’yansa da rigunansu. Sai Musa ya ce wa Haruna da ’ya’yansa maza, “Ku dafa naman a ƙofar Tentin Sujada, ku kuma ci shi a can tare da burodi daga kwandon naɗi, yadda na umarta, cewa, ‘Haruna da ’ya’yansa maza za su ci shi.’ Sa’an nan ku ƙone sauran naman da kuma burodin. Kada ku bar ƙofar Tentin Sujada har kwana bakwai, sai ranakun naɗi suka cika, gama naɗinku zai ɗauki kwana bakwai. Abin da aka yi a yau umarni ne daga Ubangiji don yin kafara saboda ku. Dole ku kasance a ƙofar Tentin Sujada dare da rana har kwana bakwai, ku kuma yi abin da Ubangiji yake bukata, don kada ku mutu; gama abin da aka umarce ni ke nan.” Saboda haka Haruna da ’ya’yansa maza suka yi kome da Ubangiji ya umarta ta wurin Musa. A rana ta takwas, Musa ya kira Haruna da ’ya’yansa maza da kuma dattawan Isra’ila. Ya ce wa Haruna, “Ka ɗauki ɗan maraƙi domin hadayarka don zunubi da kuma ɗan rago domin hadaya ta ƙonawa, dukan biyu su kasance marar lahani, ka miƙa su a gaban Ubangiji. Sa’an nan ka ce wa Isra’ilawa, ‘Ku ɗauki bunsuru na yin hadaya don zunubi, da ɗan maraƙi bana ɗaya, da ɗan rago bana ɗaya marasa lahani, don hadaya ta ƙonawa, da bijimi da rago don hadayun salama, a yi hadaya da su ga Ubangiji, da hadaya ta gari da aka kwaɓa da mai, gama yau Ubangiji zai bayyana a gare ku.’ ” Suka ɗauki abubuwan da Musa ya umarta zuwa gaban Tentin Sujada, sai dukan jama’a suka zo kusa suka tsaya a gaban Ubangiji. Sa’an nan Musa ya ce, “Ga abin da Ubangiji ya umarce ku ku yi, domin ɗaukakar Ubangiji za tă bayyana gare ku.” Musa ya ce wa Haruna, “Matsa kusa da bagaden, ka miƙa hadayarka don zunubi, da hadayarka ta ƙonawa, ka yi kafara don kanka da kuma don jama’a. Ka kuma kawo hadayar jama’a, ka yi kafara dominsu kamar yadda Ubangiji ya umarta.” Sai Haruna ya matsa kusa da bagaden, ya yanka ɗan maraƙi na yin hadaya don zunubi saboda kansa. ’Ya’yan Haruna maza suka kawo masa jinin, ya kuma tsoma yatsarsa a cikin jinin ya zuba cikin ƙahonin bagade; sauran jinin kuwa ya zuba a gindin bagaden. A kan bagaden, ya ƙone kitsen, ƙodojin, da abin da ya rufe hanta, daga hadaya don zunubi, yadda Ubangiji ya umarci Musa. Naman da fatar kuwa ya ƙone waje da sansanin. Sa’an nan ya yanka hadaya ta ƙonawa. ’Ya’yan Haruna maza suka miƙa masa jinin, ya kuwa yayyafa shi a kowane gefe na bagaden. Suka miƙa masa hadaya ta ƙonawa gunduwa-gunduwa, haɗe da kan, ya kuwa ƙone su a bisa bagaden. Sai ya wanke kayan ciki da ƙafafun, ya kuwa ƙone su tare da hadaya ta ƙonawa a kan bagade. Sa’an nan Haruna ya kawo hadayar da take domin mutane. Ya ɗauki akuya ta hadaya don zunubin mutane, ya yanka shi, ya miƙa shi domin hadaya don zunubi kamar yadda ya yi da na farko. Ya kawo hadaya ta ƙonawa ya kuma miƙa ta yadda aka tsara. Ya kuma kawo hadaya ta gari, ya ɗiba a tafi hannu ya ƙone a kan bagade tare da hadaya ta ƙonawa ta safe. Haruna ya yanka maraƙin da ragon a matsayin hadaya ta salama domin mutane. ’Ya’yansa maza suka miƙa masa jinin, ya kuwa yayyafa shi a kowane gefe na bagade. Amma sashen kitsen maraƙin da na ragon, da wutsiya mai kitse, da kitsen da yake rufe da kayan ciki, da ƙodoji da kuma kitsen da ya rufe hanta, suka shimfiɗa waɗannan a kan ƙirjin, sa’an nan Haruna ya ƙone kitsen a kan bagade. Sai Haruna ya kaɗa ƙirjin da kuma cinyar dama a gaban Ubangiji a matsayin hadaya ta kaɗawa, kamar yadda Musa ya umarta. Sa’an nan Haruna ya ɗaga hannuwansa wajen mutane ya sa musu albarka. Da yake ya miƙa hadaya don zunubi, hadaya ta ƙonawa da kuma hadaya ta salama, sai ya sauka. Sai Musa da Haruna suka shiga cikin Tentin Sujada. Da suka fita, sai suka sa wa mutane albarka; sai ɗaukakar Ubangiji ta bayyana ga dukan mutane. Sai wuta ta fito daga gaban Ubangiji ta cinye hadaya ta ƙonawa da sassan kitsen a kan bagaden. Sa’ad da dukan mutane suka ga haka, sai suka yi ihu suna farin ciki, suka fāɗi rubda ciki, suka yi sujada. ’Ya’yan Haruna maza, Nadab da Abihu suka ɗauki farantansu, suka sa wuta a ciki, suka zuba turare a kai; suka kuma miƙa haramtacciyar wuta a gaban Ubangiji, ba irin wadda Ubangiji ya umarta ba. Sai wuta ta fito daga Ubangiji ta cinye su, suka kuma mutu a gaban Ubangiji. Sai Musa ya ce Haruna, “Ga abin da Ubangiji yake nufi sa’ad da ya ce, “ ‘A cikin waɗanda suka kusace ni za a tabbata ni mai tsarki ne; a fuskar dukan mutane za a kuwa girmama ni.’ ” Haruna ya yi shiru. Sai Musa ya kira Mishayel da Elzafan, ’ya’yan Uzziyel kawun Haruna, ya ce musu, “Ku zo nan; ku ɗauki ’yan’uwanku waje da sansani, daga gaban wuri mai tsarki.” Sai suka zo suka ɗauke su, suna nan cikin taguwoyinsu, zuwa waje da sansani yadda Musa ya umarta. Sa’an nan Musa ya ce wa Haruna da Eleyazar da Itamar ’ya’yansa maza, “Kada ku bar gashin kanku barkatai, kada kuma ku yage tufafinku, don kada ku mutu. Yin haka zai jawo fushin Ubangiji a kan dukan jama’a. Amma dangoginku, wato, dukan Isra’ilawa, suna iya kuka saboda waɗanda Ubangiji ya hallaka da wuta. Kada ku bar ƙofar Tentin Sujada ko kuwa ku mutu, domin man Shafan Ubangiji yana kanku.” Saboda haka suka yi kamar yadda Musa ya faɗa. Sa’an nan Ubangiji ya yi magana da Haruna ya ce, “Kai da ’ya’yanka maza, ba za ku sha ruwan inabi ko wani abu mai sa jiri ba a duk sa’ad da za ku shiga cikin Tentin Sujada, in ba haka ba za ku mutu. Wannan dawwammamiyar farilla ce wa tsararraki masu zuwa. Dole ku bambanta tsakanin mai tsarki da marar tsarki, tsakanin marar tsabta da mai tsabta, za ku kuma koyar da Isra’ilawa dukan farillan da Ubangiji ya ba su ta wurin Musa.” Musa ya ce wa Haruna da Eleyazar da Itamar ’ya’yansa maza da suka ragu, “Ku ɗauki ragowar hadaya ta gari wadda aka yi hadaya ta ƙonawa da ita ga Ubangiji ku ci ba tare da yisti ba, a gefen bagaden, gama tsattsarka ne. Ku ci shi a tsattsarkan wuri, gama rabonka ne da na ’ya’yanka daga cikin hadayun da akan ƙone da wuta ga Ubangiji; gama haka aka umarce ni. Amma kai da ’ya’yanka maza da mata za su iya ci ƙirjin da aka kaɗa, da kuma cinyar da aka miƙa. Ku ci su a wuri mai tsabta; an ba da su gare ku da kuma ’ya’yanku a matsayin rabo daga hadaya ta salama ta Isra’ilawa. Cinyar da aka miƙa da kuma ƙirjin da aka kaɗa, dole a kawo su tare da ɓangarori kitsen hadayun da aka yi ta wuri wuta, don a kaɗa a gaban Ubangiji a matsayin hadaya ta kaɗawa. Wannan zai zama na kullayaumi gare ka da ’ya’yanka, yadda Ubangiji ya umarta.” Sa’ad da Musa ya nemi sani game da akuyar hadaya don zunubi, ya kuwa gane cewa an ƙone shi, sai ya yi fushi da Eleyazar da kuma Itamar, ’ya’yan Haruna maza da suka ragu, ya kuma yi tambaya, “Me ya sa ba ku ci hadaya don zunubi a cikin wuri mai tsarki ba? Mafi tsaki ne; an ba ku ne don a ɗauke laifin jama’a ta wurin yin kafara saboda su a gaban Ubangiji. Da yake ba a kai jininsa cikin wuri mai tsarki ba, ya kamata ku ci akuyar a wuri mai tsarki, kamar yadda na umarta.” Sai Haruna ya amsa wa Musa, “Yau sun miƙa hadayarsu don zunubi da kuma hadayarsu ta ƙonawa a gaban Ubangiji, ga kuma irin waɗannan abubuwa da suka same ni, da a ce na ci hadaya don zunubi yau, da zai yi kyau ke nan a gaban Ubangiji?” Da Musa ya ji haka, sai ya gamsu. Ubangiji ya ce wa Musa da Haruna, “Ku ce wa Isra’ilawa, ‘Cikin dabbobin da suke a doron ƙasa, waɗannan ne za ku ci. Za ku iya cin dabbobin da suke da rababben kofato, waɗanda suke kuma tuƙa. “ ‘Akwai waɗanda suke tuƙa ko kuwa suna da rababben kofato kawai, duk da haka ba za ku ci su ba. Waɗannan kuwa su ne, raƙumi, ko da yake yana tuƙa, amma ba shi da rababben kofato; saboda haka cin namansa haram ne gare ku. Rema, ko da yake tana tuƙa, duk da haka ba ta da rababben kofato; saboda haka namanta haram ne gare ku. Zomo, ko da yake yana tuƙa, duk da haka ba shi da rababben kofato; saboda haka namansa haram ne gare ku. Alade, ko da yake yana da rababben kofato, amma ba ya tuƙa, saboda haka namansa haram ne gare ku. Ba za ku ci namansu ba, ko ku taɓa gawawwakinsu, gama haram ne gare ku. “ ‘Cikin dukan halittu masu rai da suke a cikin ruwan tekuna da rafuffuka, za ku iya cin kowane da yake da ƙege da kamɓori. Amma kowace halittar da take cikin tekuna da koguna da ba ta da ƙege da kamɓori, ko cikin dukan abubuwa masu rai a ruwa ko kuma sauran halittu a cikin ruwa za ku ɗauka su marasa tsaki ne gare ku. Da yake abubuwan ƙyama ne a gare ku, ba za ku ci namansu ba, kuma dole ku yi ƙyamar gawawwakinsu. Duk abin da yake a ruwa amma ba shi da ƙege ko kamɓori, za ku yi ƙyamarsa. “ ‘Waɗannan su ne tsuntsayen da za ku yi ƙyamarsu, ba za ku ci su ba domin sun zama abin ƙyama. Tsuntsayen kuwa su ne, gaggafa, ungulu, baƙin ungulu, shirwa, da duk wani irin baƙin shirwa, kowane irin hankaka, mujiya mai ƙaho, jimina, shaho, da kowane irin shaho, ƙaramin ƙururu, babba da jaka, zalɓe, kazar ruwa, kwasakwasa, da ungulu, shamuwa, kowane irin jinjimi, katutu da kuma jamage. “ ‘Dukan ƙwarin da suke da fikafikai masu tafiya da ƙafafu huɗu abin ƙyama ne gare ku. Sai dai akwai ƙwarin da suke da fikafikai masu tafiya da ƙafafu huɗu da za ku ci; waɗanda suke da cinyoyin da suke sa su iya tsalle. Za ku iya cin kowane irin fāra, gyare, ƙwanso da danginsu. Amma sauran ƙananan ƙwari duka masu fikafikai, suna kuma jan ciki, abin ƙyama ne a gare ku. “ ‘Duk wanda ya taɓa mushen waɗannan dabbobi, zai ƙazantu har fāɗuwar rana. Duk wanda ya ɗauki ɗaya daga cikin gawawwakinsu dole yă wanke rigunansa, zai kuma ƙazantu har zuwa yamma. “ ‘Kowace dabbar da ba ta da rababben kofato ko ba ta tuƙa, haram ce gare ku; duk wanda ya taɓa gawarsu zai ƙazantu. Duk abin da yake tafiya a kan dāginsa cikin dabbobin da suke da ƙafa huɗu, haram ne a gare ku. Duk wanda ya taɓa mushensu zai ƙazantu har zuwa yamma. Duk wanda ya ɗauki gawawwakinsu dole yă wanke rigunansa, zai kuma ƙazantu har yamma. Waɗannan dabbobi za su zama marasa tsabta a gare ku. “ ‘Waɗannan ƙananan dabbobi da suke rarrafe a ƙasa, haram ne a gare ku, wato, murɗiya, da ɓera, da gafiya da irinsa, da tsaka, da hawainiya, da ƙadangare, da guza, da damo. Dukan waɗanda suke rarrafe, za su zama marasa tsarki gare ku. Duk wanda ya taɓa su sa’ad da suka mutu, zai zama ƙazantacce har zuwa yamma. Duk abin da mushensu ya fāɗa a kai, zai ƙazantu. Ko a kan itace ne, ko a bisa tufafi, ko a fata, ko a buhu, ko cikin kowane irin abu da ake amfani da shi, to, tilas a sa shi cikin ruwa, zai zama ƙazantacce har zuwa yamma, sa’an nan zai tsarkaka. In waninsu ya fāɗi a cikin tukunyar laka, kome da yake a tukunyar zai ƙazantu, kuma dole a fashe tukunyar. Duk abincin da aka yarda a ci, wanda ya taɓa ruwa daga irin tukunyan nan zai zama marar tsabta, kuma duk ruwan da za a sha daga irin tukunyan nan ƙazantacce ne. Kowane irin abu da mushensu ya fāɗa a kai ya ƙazantu ke nan; ko a kan murhu, ko a tukunyar dahuwa, dole a farfashe su. Su haramtattu ne kuma dole ku ɗauke su haramtattu. Maɓuɓɓuga ko tafki na tarin ruwa zai ci gaba da zauna mai tsabta, amma duk wanda ya taɓa ɗaya daga cikin waɗannan gawawwakin ya haramtu. In gawa ta fāɗi a irin da za a shuka, irin zai ci gaba da zama mai tsabta. Amma in an sa ruwa a irin sai kuma gawar ta fāɗi a kai, to, irin ya zama haram gare ku. “ ‘In dabbar aka yarda a ci ta mutu, duk wanda ya taɓa gawarta zai ƙazantu har yamma. Duk wanda ya ci wani sashe na gawar dole yă wanke rigunansa, kuma zai ƙazantu har yamma. Duk wanda ya ɗauki gawar dole yă wanke rigunansa, zai kuwa ƙazantu har yamma. “ ‘Duk dabba mai rarrafe a ƙasa abin ƙyama ne; ba kuwa za a ci shi ba. Ba za ku ci wani halittar da take rarrafe a ƙasa, ko tana jan ciki, ko tana tafiya a kan ƙafafu huɗu, ko a kan ƙafafu da yawa ba; abin ƙyama ne. Kada ku ƙazantar da kanku ta wurin wani daga waɗannan halittu. Kada ku ƙazantar da kanku ta dalilinsu, ko a mai da ku haramtattu ta wurinsu. Ni ne Ubangiji Allahnku; ku tsarkake kanku ku kuma zama da tsarki, domin Ni mai tsarki ne. Kada ku ƙazantar da kanku ta wurin wani halittar da take rarrafe a ƙasa. Ni ne Ubangiji wanda ya fitar da ku daga Masar don in zama Allahnku; saboda haka ku zama da tsarki, domin Ni mai tsarki ne. “ ‘Waɗannan ne ƙa’idodi game da dabbobi, tsuntsaye, da kowane abu mai rai da yake motsi a cikin ruwa, da kowace halitta mai rarrafe a ƙasa. Dole ku bambanta tsakanin haramtacce da halaltacce, tsakanin halittu masu ran da za a iya ci da waɗanda ba za a iya ci ba.’ ” Ubangiji ya ce wa Musa, “Faɗa wa Isra’ilawa, ‘Macen da ta yi ciki ta kuma haihu ɗa namiji za tă ƙazantu kwana bakwai, kamar yadda takan ƙazantu a lokacin al’adarta. A rana ta takwas, za a yi wa yaron kaciya. Sa’an nan dole macen ta jira kwana talatin don a tsabtacce ta daga zub da jini. Ba za tă taɓa wani abu mai tsarki, ko ta je wuri mai tsarki ba sai kwanakin tsabtaccewarta sun cika. In ta haifi ’ya ta mace ce, makoni biyu macen za tă ƙazantu kamar yadda takan kasance a lokacin al’adarta. Sa’an nan dole tă jira kwana sittin don a tsabtacce ta daga zub da jininta. “ ‘Sa’ad da kwanakin tsabtaccewarta don ɗa namiji ko ’ya ta mace suka cika, sai ta kawo ɗan rago bana ɗaya wa firist a bakin ƙofar Tentin Sujada don hadaya ta ƙonawa da tattabara ko kurciya na hadaya don zunubi. Firist zai miƙa su a gaban Ubangiji don yă yi kafara dominta, sa’an nan tă tsabtacce daga zub da jininta. “ ‘Waɗannan su ne ƙa’idodi domin macen da ta haifi ɗa namiji ko ’ya ta mace. In ba za tă iya kawo ɗan rago ba, sai ta kawo kurciyoyi biyu ko tattabarai biyu, ɗaya domin hadaya ta ƙonawa ɗayan kuma domin hadaya don zunubi. Ta haka firist zai yi kafara dominta, za tă kuwa zama tsabtacciya.’ ” Ubangiji ya ce wa Musa da Haruna, “Sa’ad da wani yana da kumburi, ko ɓamɓaroki, ko tabo a fatar jikinsa da zai iya zama cutar fatar jiki, dole a kawo shi ga Haruna firist, ko kuwa ga ɗaya a cikin ’ya’yansa maza wanda yake firist. Firist zai bincika mikin da yake a fatar mai cutar, in gashin a mikin ya juya ya zama fari, mikin kuma ya zama kamar ya fi zurfin fatar jiki, wannan cutar kuturta ce. Sa’ad da firist ya bincike shi, zai furta shi marar tsarki. In tabon a fata jikinsa fari ne amma bai zama ya fi zurfin fatar jikin ba, gashin a cikinsa kuma bai juya ya zama fari ba, firist ɗin zai kaɗaice mai cutar na kwana bakwai. A rana ta bakwai firist zai bincike shi, in kuwa ya ga cewa mikin bai canja ba, bai kuwa yaɗu a fatar jikin ba, zai kaɗaice shi na waɗansu ƙarin kwana bakwai. A rana ta bakwai ɗin firist zai sāke bincike shi, in kuwa mikin ya bushe bai kuwa yaɗu a fatar jikin ba, firist ɗin zai furta shi mai tsarki; ƙurji ne kawai. Dole mutumin yă wanke rigunansa, zai kuma tsarkaka. Amma in ƙurjin ya yaɗu a fatar jikinsa bayan ya nuna kansa ga firist don a furta shi tsarkake, dole yă sāke bayyana a gaban firist. Firist ɗin zai bincike shi, in ƙurjin ya yaɗu a fatar jikinsa, zai furta shi marar tsarki; cuta ce mai yaɗuwa. “Sa’ad da wani yana da cutar fatar jiki, dole a kawo shi ga firist. Firist zai bincike shi, in kuwa farin kumburi a fatar jikin ya juyar da gashin fari in kuma akwai sabon miki a kumburi, to, cutar fatar jikin ne mai ƙarfi kuma firist zai furta shi marar tsarki. Ba zai kaɗaice shi ba, domin ya riga ya zama marar tsarki. “In cutar ta fashe ko’ina a fatar jiki, har iyakar ganin firist, ta rufe dukan fatar jikin mai fama da cutar, daga kai har zuwa ƙafa, firist zai bincike shi, in cutar ta riga ta rufe dukan jikinsa, zai furta wannan mutum tsarkakakke ne. Da yake ya juya fari fat, tsarkakakke ne. Amma sa’ad da sabon miki ya bayyana a jikinsa, zai furta shi marar tsarki. Sa’ad da firist ɗin ya ga sabon miki, zai furta shi marar tsarki. Sabon mikin marar tsarki, yana da cuta mai yaɗuwa. A ce sabon mikin ya canja ya juya fari, dole yă je wurin firist. Firist zai bincike shi, in kuma mikin ya juya ya zama fari, firist zai furta mai cutar tsarkakakke; to, zai zama tsarkakakke. “Sa’ad da wani yana da kumburi a fatar jikinsa ya kuma warke, kuma a inda ƙurjin yake, wani farin kumburi ko tabo ja-ja, fari-fari ya bayyana, dole yă gabatar da kansa ga firist. Firist zai bincike shi, in kuma ya zama ya fi fatar jiki zurfi kuma gashinsa ya juya ya zama fari, firist ɗin zai furta shi marar tsarki. Cuta ce mai yaɗuwa da ta fasu a inda ƙurjin yake. Amma in sa’ad da firist ya bincike shi, ya tarar babu farin gashi a ciki, kuma bai yi zurfi fiye da fatar jikin ba, ya kuma bushe, sai firist ɗin ya kaɗaice shi har kwana bakwai. In yana yaɗuwa a cikin fatar jikin, firist zai furta shi marar tsarki; cuta mai yaɗuwa ce. Amma in tabon bai canja ba, bai kuma yaɗu ba, tabo ne kawai daga ƙurji, kuma firist zai furta shi tsarkakakke. “Sa’ad da wani yana da ƙuna a fatar jikinsa, wurin kuwa ya yi ja-ja, ko fari-fari, ko kuwa farin tabo ya bayyana a sabon miki na ƙunan, firist zai bincike tabon, idan kuma gashin a cikinsa ya juya ya zama fari, kuma ya yi zurfi fiye da fatar jikin, cuta ce mai yaɗuwa da ta fasu daga ƙunan. Firist zai furta shi marar tsarki; cuta ce mai yaɗuwa. Amma in firist ɗin ya bincike shi bai kuwa ga wani farin gashi a wurin ba, in kuma bai yi zurfi fiye da fatar jikin ba, ya kuma bushe, to, firist ɗin zai kaɗaice shi na kwana bakwai. A rana ta bakwai ɗin firist zai bincike shi, in kuma cutar tana yaɗuwa a cikin fatar jikin, firist ɗin zai furta shi marar tsarki, cutar fatar jiki ce mai yaɗuwa. In kuma wurin bai canja ba, bai kuma yaɗu cikin fatar jikin ba amma ya bushe, kumburi ne daga ƙuna, firist ɗin kuwa zai furta shi tsarkakakke; tabo ne kawai daga ƙuna. “In namiji ko ta mace tana da miki a kai ko kuwa a gemu, firist zai bincike mikin, in ya yi zurfi fiye da fatar jiki, gashin ya zama rawaya, ya kuma zama siriri, firist zai furta wannan mutum marar tsarki; ƙaiƙayi ne, cuta mai yaɗuwa ce na kai ko na gemu. Amma in, sa’ad da firist ya bincika wannan irin mikin, bai yi zurfi fiye da fatar jiki ba kuma babu baƙin gashi a cikinsa, firist ɗin zai kaɗaice mutum mai fama da cutar, kwana bakwai. A rana ta bakwai ɗin firist zai bincika mikin in kuwa ƙaiƙayin bai bazu ba, ba rawayan gashi kuma a ciki, babu zurfin da yake fiye da fatar jiki, dole a yi masa aski, sai dai ba zai aske wurin cutar ba, kuma firist zai kaɗaice shi kwana bakwai. A rana ta bakwai firist zai bincike ƙaiƙayin, idan bai bazu a fatar jikin ba, bai kuma yi zurfin fiye da fatar jikin ba, firist ɗin zai furta shi tsarkakakke. Dole kuma yă wanke rigunansa, zai kuwa zama tsarkakakke. Amma in ƙaiƙayin ya yaɗu a cikin fatar jikin bayan aka furta shi tsarkakakke, firist ɗin zai bincike shi, in kuma ƙaiƙayin ya yaɗu a fatar jikin, firist ɗin ba ya bukatar neman ganin rawayan gashi; mutumin marar tsarki ne. In fa a ganinsa bai canja ba kuma baƙin gashi ya fito a cikinsa, ƙaiƙayin ya warke ke nan. Mutumin tsarkakakke ne, firist ɗin kuwa zai furta shi tsarkakakke. “Sa’ad da namiji ko ta mace tana da farare wurare a fatar jiki, firist ya bincika su, in kuma wuraren toka-toka ne, to, ƙurji marar lahani ne ya faso a fatar jikin; wannan mutum tsarkakakke. “Mutumin da ya rasa gashi kansa ya zama mai sanƙo ke nan, duk da haka mutumin tsattsarka ne. In ya rasa gashin goshinsa yana kuma da sanƙo a goshinsa, shi tsarkakakke ne. Amma in yana da miki ja-ja da ya yi fari a sanƙonsa ko a goshinsa, cuta mai yaɗuwa ce take fasuwa a kai ko a goshin. Sai firist ya bincike shi, in kuma kumburarren miki a kansa ko goshinsa ja-ja da fari-fari kamar cutar fatar jiki mai yaɗuwa ne, mutumin ya kamu da cutar kuma marar tsarki ne. Firist ɗin zai furta mutumin marar tsarki saboda mikin da yake a kansa. “Mutum mai wannan cuta mai yaɗuwa dole yă sa yagaggun riguna, yă kuma bar gashin kansa ba gyara, yă rufe sashe ƙasa na fuskarsa, sa’an nan yă riga cewa, ‘Marar tsarki! Marar tsarki!’ Muddin yana da cutar zai ci gaba da kasance marar tsarki. Dole yă yi zama shi kaɗai; dole yă yi zama waje da sansani. “In akwai cutar fatar jiki a riguna, duk wani rigar ulu ko na lilin, duk wani kayan zare, ko saƙa na lilin, ko ulu, duk wani kayan fata, ko wanda aka yi da fata, in kuma cutar a cikin rigar, ko fatar, ko kayan saƙan kore-kore ne, ko ja-ja, to, cutar fatar jiki da ake samu a riguna ce mai yaɗuwa, kuma dole a nuna wa firist. Firist ɗin zai bincike cutar fatar jikin da take a rigar, yă kuma kaɗaice kayan da abin ya shafe shi kwana bakwai. A rana ta bakwai ɗin zai bincike shi, in cutar rigar ta yaɗu, ko a tariyar zaren, ko a wadarin, ko a fatar, ko kuwa a duk abin da ake amfani da shi, to wannan muguwar cutar riga ce; kayan marar tsarki ne. Dole yă ƙone rigar, ko tariyar zaren, ko kayan da aka saƙa na ulu ko lilin, ko kuwa na kaya da aka yi da fatar, wanda cutar ta fāɗa wa, domin cutar rigar muguwa ce, dole a ƙone kayan. “Amma in sa’ad da firist ya bincike shi, cutar rigar ba ta yaɗu a rigar, ko a tariyar zare, ko a kayan da aka saƙa, ko a kayan da aka yi da fata ba, zai umarta cewa a wanke kayan da cutar ta shafa. Sa’an nan zai kaɗaice shi na waɗansu kwana bakwai. Bayan an wanke kayan da cutar ta shafa, firist zai bincike shi, in kuwa cutar rigar ba tă canja yadda take ba, ko da yake ba tă yaɗu ba, marar tsarki ce. In sa’ad da firist ya bincike shi, cutar rigar ta bushe bayan da aka wanke kayan, sai yă yage sashen da cutar ta shafa na rigar, ko fatar, ko tariyar zaren, ko kuwa na kayan da aka saƙa. Amma in ya sāke bayyana a rigar, ko a tariyar zaren, ko a kayan da aka saƙa, ko a kayan da aka yi da fatar, to, yana yaɗuwa ke nan, kuma dole a ƙone duk abin da yake da cutar rigar da wuta. Rigar, ko tariyar zare, ko kayan da aka saƙa, ko kuwa duk kayan da aka yi da fatar da aka wanke, aka kuma fid da cutar rigar, dole a sāke wanke shi, zai kuwa zama tsarkakakke.” Waɗannan su ne ƙa’idodi game da cutar fatar jiki na rigar ulu, ko rigar lilin, tariyar zare, ko kayan da aka saƙa, ko kuwa duk wani abin da aka yi da fata, don furta su tsarkakakke, ko kuwa marar tsarki. Ubangiji ya ce wa Musa, “Waɗannan su ne ƙa’idodi domin mutumin da yake da cuta a lokacin tsabtaccewarsa, sa’ad da aka kawo shi ga firist. Firist zai fita waje da sansani ya bincike shi. In mutumin ya warke daga cutar fatar jiki mai yaɗuwa, firist zai umarta a kawo tsuntsaye biyu masu rai, masu tsabta da itacen al’ul, jan ƙyalle da kuma hizzob saboda mutumin da za a tsabtacce. Sa’an nan firist zai umarta a kashe ɗaya daga cikin tsuntsayen a bisa ruwa mai kyau a tukunyar laka. Zai ɗauki tsuntsu mai rai ya tsoma shi tare da itacen al’ul, jan ƙyalle da kuma hizzob cikin jinin tsuntsun da aka yanka a bisa ruwa mai kyau. Sau bakwai zai yayyafa wa mutumin da za a tsabtacce daga cutar mai yaɗuwa ya kuma furta shi tsarkakakke. Sa’an nan ya saki tsuntsu mai rai ɗin ya tafi. “Dole mutumin da aka tsabtaccen ya wanke rigunansa, ya aske dukan gashinsa ya kuma yi wanka; sa’an nan zai tsabtacce. Bayan wannan zai iya zo cikin sansani, amma dole yă tsaya waje da tentinsa kwana bakwai. A rana ta bakwai ɗin dole yă aske dukan gashinsa; dole yă aske kansa, gemunsa, gashin girarsa da sauran gashinsa. Dole yă wanke rigunansa ya kuma yi wanka, zai kuwa tsabtacce. “A rana ta takwas dole yă kawo ɗan rago da ’yar tunkiya bana ɗaya, kowane marar lahani, tare da rabin garwan gari mai laushi haɗe da mai domin hadaya ta gari, da kuma moɗa ɗaya na mai. Firist da ya furta shi tsarkakakke zai miƙa da wanda za a tsabtaccen da kuma hadayunsa a gaban Ubangiji a ƙofar Tentin Sujada. “Sa’ad da firist zai ɗauki ɗaya daga cikin ragunan ya kuma miƙa shi kamar hadaya don laifi, tare da moɗan mai; zai kaɗa su a gaban Ubangiji kamar hadaya kaɗawa. Zai yanka ɗan ragon a tsattsarkan wuri inda ake yanka hadaya don zunubi da hadaya ta ƙonawa. Gama yadda hadaya ta zunubi ta firist ne, haka hadaya domin laifi ma, hadaya ce mafi tsarki. Firist ɗin zai ɗiba jinin hadaya don laifin ya zuba a leɓatun kunnen dama na wanda za a tsabtacce, a babbar yatsar hannunsa na dama a kuma a babbar yatsar ƙafa damansa. Firist ɗin zai ɗiba daga moɗan mai ɗin ya zuba a tafin hannunsa na hagu, ya tsoma yatsarsa ta dama cikin man da yake a tafin hannunsa, kuma da yatsar zai yayyafa man a gaban Ubangiji sau bakwai. Firist zai sa sauran mai da yake cikin tafinsa a leɓatun kunnen dama na wanda za a tsabtacce, a babbar yatsarsa na dama da kuma a babbar yatsar ƙafarsa ta dama, a bisa jinin hadaya don laifin. Sauran man a tafin hannunsa firist zai sa a kan wanda za a tsabtaccen ya kuma yi kafara dominsa a gaban Ubangiji. “Sa’an nan firist ɗin zai miƙa hadaya don zunubi ya kuma yi kafara saboda wannan da za a tsabtacce daga rashin tsarkinsa. Bayan haka, firist zai yanka hadaya ta ƙonawa ya miƙa ta a bagade, tare da hadaya ta gari, ya kuma yi kafara dominsa, zai kuwa tsabtacce. “In kuwa mutumin matalauci ne ba zai iya samu waɗannan ba, to, dole yă ɗauki ɗan rago guda kamar hadaya don laifi a kaɗa don a yi kafara dominsa, tare da humushin garwa gari mai laushi haɗe da mai don hadaya ta gari, da moɗa na mai, da kurciyoyi biyu ko tattabarai biyu, wanda zai iya samu, ɗaya domin hadaya don zunubi ɗayan kuma domin hadaya ta ƙonawa. “A rana ta takwas dole yă kawo su domin tsabtaccewarsa ga firist a ƙofar Tentin Sujada, a gaban Ubangiji. Firist zai ɗauki ɗan rago na hadaya don laifi tare da moɗa na mai, ya kaɗa su a gaban Ubangiji kamar hadaya ta kaɗawa. Zai yanka ɗan rago domin hadaya don laifi ya kuma ɗibi jinin ya sa a leɓatun kunnen dama na wanda za a tsabtaccen, a babban yatsar hannun damansa da kuma a babban yatsar ƙafarsa na dama. Firist zai zuba man a tafin hannunsa na hagu, da yatsarsa na dama zai yayyafa man daga tafinsa sau bakwai a gaban Ubangiji. Daga cikin man da yake a tafinsa zai zuba a wuri da ya zuba jinin hadaya don laifi, a leɓatun kunnen dama na wanda za a tsabtaccen, a babban yatsar hannun damansa da kuma a babban yatsar ƙafa damansa. Sauran man da yake cikin tafinsa firist ɗin zai zuba a kan wannan da za a tsabtaccen don a yi kafara dominsa a gaban Ubangiji. Sa’an nan zai miƙa kurciyoyi ko tattabarai, waɗanda mutumin zai iya, ɗaya kamar hadaya don zunubi ɗayan kuma kamar hadaya ta ƙonawa, tare da hadaya ta gari. Ta haka firist zai yi kafara a gaban Ubangiji a madadin wanda za a tsabtacce.” Waɗannan su ne ƙa’idodi domin mutumin da yake da cutar fatar jiki wanda kuma ba zai iya samun abubuwan hadaya ta kullum domin tsabtaccewarsa ba. Ubangiji ya ce wa Musa da Haruna, “Sa’ad da kuka shiga ƙasar Kan’ana, wadda nake ba ku kamar gādonku, na kuma sa yaɗuwa cutar fatar jiki a riga a cikin gida a wannan ƙasa, dole maigidan ya tafi ya faɗa wa firist ya ce, ‘Na ga wani abu da ya yi kamar cutar fatar jikin da take a riga a cikin gidana.’ Firist zai umarci a fitar da kome a gidan kafin ya shiga ya bincike cutar fatar jiki da take a rigar, saboda babu abin da yake gidan da za a furta marar tsarki ne. Bayan haka firist zai shiga ya dudduba gidan. Zai bincike cutar fatar jiki da take a riga a bangaye, in kuma yana da tabon kore-kore ko ja-ja da suka bayyana da suka yi zurfi fiye da saman bangon, firist ɗin zai fita a bakin ƙofar gidan ya rufe ta na kwana bakwai. A rana ta bakwai ɗin firist zai dawo don yă dudduba gidan. In cutar fatar jiki da take a riga ta yaɗu a bangayen, zai umarta a ciccire duwatsun da suke da cutar a zubar a wuri marar tsarki waje da birnin. Dole yă sa a kankare duka shafen bangon cikin gidan a kuma zuba kayan da aka kankare a wurin marar tsarki waje da birnin. Sai su ɗebi waɗansu duwatsu su sa a wuraren da suka ciccire waɗancan, su kuma ɗiba sabon laka su yi shafen gidan. “In cutar fatar jiki da take ta rigar ta sāke bayyana a gidan bayan an ciccire duwatsu aka kankare gidan aka kuma yi shafe, firist zai je ya bincika shi, in kuwa cutar ta bazu a gidan, to, muguwar cuta ce; gidan marar tsarki ne. Dole a rushe gidan, a fid da duwatsun, katakai da kuma dukan shafen daga birnin zuwa wuri marar tsarki. “Duk wanda ya shiga gidan yayinda aka rufe shi zai ƙazantu har yamma. Duk wanda ya kwana ko ya ci abinci a gidan dole yă wanke rigunansa. “Amma in firist ya zo ya bincika gidan kuma cutar fatar jiki da take ta rigar ba tă bazu ba bayan an yi wa gidan shafe, zai furta gidan tsarkakakke, domin cutar ta tafi. Don a tsabtacce gidan, zai ɗauki tsuntsaye biyu da itacen al’ul, jan ƙyalle da hizzob. Zai yanka ɗaya daga cikin tsuntsayen a bisa ruwa mai kyau a cikin tukunyar laka. Sa’an nan zai ɗauki itacen al’ul, hizzob, jan ƙyalle da kuma tsuntsu mai ran ya tsoma su cikin jinin tsuntsun da aka yanka da kuma cikin ruwa mai kyau, ya yayyafa wa gida sau bakwai. Zai tsabtacce gidan da jinin tsuntsun, ruwa mai kyau, tsuntsu mai ran, itacen al’ul, hizzob da kuma jan ƙyalle. Sa’an nan zai saki tsuntsu mai rai ɗin a fili waje da birnin ya tafi. Ta haka zai yi kafara saboda gidan, gidan kuwa zai zama tsarkakakke.” Waɗannan su ne ƙa’idodi saboda duk wani cuta mai yaɗuwa, don ƙaiƙayi, don cutar fatar jiki da take a riga ko a cikin gida, da kuma don kumburi, ɓamɓaroki ko tabo, don a tabbatar sa’ad da wani abu mai tsarki da marar tsarki. Waɗannan su ne ƙa’idodi domin cutar fatar jiki mai yaɗuwa da cutar fatar jikin da take a riga. Ubangiji ya ce wa Musa da Haruna, “Yi wa Isra’ilawa magana, ku ce musu, ‘Duk sa’ad da wani namiji yake ɗiga daga azzakarinsa, wannan ɗiga marar tsarki ne. Ko ɗigar ta ci gaba da fitowa daga azzakarinsa ko an tsere ta, za tă sa mutumin yă zama marar tsarki. Ga yadda ɗigarsa za tă kawo ƙazantuwa, “ ‘Duk gadon da mutumin mai ɗigar ya kwanta a kai, zai zama marar tsarki, kuma duk abin da ya zauna a kai, zai zama marar tsarki. Duk wanda ya taɓa gadonsa dole yă wanke rigunansa, yă kuma yi wanka, zai kuwa ƙazantu har yamma. Duk wanda ya zauna a inda wannan mai ɗiga ya zauna a kai, dole yă wanke rigunansa yă kuma yi wanka, zai kuwa ƙazantu har yamma. “ ‘Duk wanda ya taɓa jikin mai ɗiga, dole yă wanke rigunansa, yă kuma yi wanka, zai kuma ƙazantu har yamma. “ ‘In mai ɗiga ya tofa miyau a kan wani wanda yake tsarkakakke, dole tsarkakakken nan yă wanke rigunansa, yă kuma yi wanka, zai kuma ƙazantu har yamma. “ ‘Kowane sirdi da mai ɗigar ya zauna a kai zai ƙazantu, kuma duk wanda ya taɓa wani abu cikin abubuwan da suke a ƙarƙashin sirdin zai ƙazantu har yamma; duk wanda ya ɗauki abubuwan nan dole yă wanke rigunansa, yă kuma yi wanka, zai kuwa ƙazantu har yamma. “ ‘Duk wanda mai ɗiga ya taɓa ba tare da ya wanke hannuwansa da ruwa ba, dole yă wanke rigunansa yă kuma yi wanka, zai kuma ƙazantu har yamma. “ ‘Dole a farfashe tukunya lakar da mutumin ya taɓa, kuma dole a ɗauraye duk wani abin da aka yi da katako wanda ya taɓa da ruwa. “ ‘Sa’ad da aka tsabtacce mai ɗigar, zai ɗauki kwana bakwai don tsabtaccewarsa; dole yă wanke rigunansa, yă kuma yi wanka mai tsabta, zai kuwa zama tsarkakakke. A rana ta takwas dole yă ɗauki kurciyoyi biyu ko tattabarai biyu, yă zo gaban Ubangiji a ƙofar Tentin Sujada, yă ba da su ga firist. Firist ɗin zai miƙa su, ɗaya domin hadaya don zunubi, ɗayan kuma domin hadaya ta ƙonawa. Ta haka zai yi kafara a gaban Ubangiji saboda mai ɗigar. “ ‘Sa’ad da namiji ya ɗigar maniyyi, dole yă wanke jikinsa gaba ɗaya da ruwa, zai kuma ƙazantu har yamma. Dole a wanke duk riga ko fatar da yake da maniyyin a kansa da ruwa, zai kuma ƙazantu har yamma. Sa’ad da namiji ya kwana da mace ya kuwa zub da maniyyi, dole dukansu biyu su yi wanka, za su kuma ƙazantu har yamma. “ ‘Sa’ad mace take al’adarta ta ƙa’ida, rashin tsabtarta ta al’adar zai ɗauki kwana bakwai, kuma duk wanda ya taɓa ta, zai ƙazantu har yamma. “ ‘Duk abin da ta kwanta a kai a lokacin al’adarta zai ƙazantu, kuma duk abin da ta zauna a kai zai ƙazantu. Duk wanda ya taɓa gadonta dole yă wanke rigunansa yă kuma yi wanka, zai kuma ƙazantu har yamma. Duk wanda ya taɓa wani abin da ta zauna a kai, dole yă wanke rigunansa yă kuma yi wanka, zai kuma ƙazantu har yamma. Ko gado ne, ko kuwa wani abin da ta zauna a kai, sa’ad da wani ya taɓa shi, zai ƙazantu har yamma. “ ‘In namiji ya kwana da ita, al’adarta kuwa ta taɓa shi, zai ƙazantu na kwana bakwai; duk kuma gadon da ya kwanta a kai, zai ƙazantu. “ ‘Idan mace tana ɗigar jini na tsawon kwanaki, ban da kwanakin ganin al’adarta, ko kuwa idan al’adarta ya wuce yawan kwanakin da ya kamata, to, za tă ƙazantu daidai kamar na kwanakin al’adar da ta saba yi. Wato, muddin tana cikin ɗiga, ta zama mai ƙazanta. Duk gadon da ta kwanta yayinda ta ci gaba da ɗiga zai zama marar tsarki, kamar yadda gadonta yake a lokacin al’adarta, kuma duk abin da ta zauna a kai zai zama marar tsarki, kamar yadda yake a lokacin al’adarta. Duk wanda ta taɓa su zai zama marar tsarki; dole yă wanke rigunansa yă kuma yi wanka, zai kuma ƙazantu har yamma. “ ‘Sa’ad da aka tsabtacce ta daga ɗigarta, dole tă ɗauki kwana bakwai, bayan haka za tă zama mai tsarki. A rana ta takwas, dole tă ɗauki kurciyoyi biyu ko tattabari biyu ta kawo su ga firist a bakin ƙofar Tentin Sujada. Firist zai miƙa ɗaya saboda hadaya don zunubi, ɗayan kuma don hadaya ta ƙonawa. Ta haka zai yi kafara dominta a gaban Ubangiji saboda ƙazantar ɗigarta. “ ‘Ta haka za ka tsarkake Isra’ilawa daga rashin tsarkinsu, domin kada su mutu saboda rashin tsarkinsu ta wurin ƙazantar da wurin zamana wanda yake tsakiyarsu.’ ” Waɗannan su ne ƙa’idodi a kan wanda yake ɗiga, da wanda yake zubar da maniyyi, ƙa’idodi ne kuma ga mace wadda take al’ada, ga namiji ko macen da take ɗiga, ga kuma namijin da ya kwana da mace marar tsarki. Ubangiji ya yi magana da Musa bayan mutuwar ’ya’yan Haruna biyu maza waɗanda suka mutu sa’ad da suka kusaci Ubangiji. Ubangiji ya ce wa Musa, “Faɗa wa ɗan’uwanka Haruna, kada yă riƙa shiga Wuri Mafi Tsarki bayan labule koyaushe, wato, a gaban murfi wanda yake bisa akwatin alkawari, domin kada yă mutu, gama zan bayyana a cikin girgije a kan murfin. “Ga yadda Haruna zai shiga wuri mai tsarki, zai zo da ɗan bijimi domin hadaya don zunubi da kuma rago domin hadaya ta ƙonawa. Zai sa toguwar lilin mai tsarki, tare da ɗan ciki na lilin; zai yi ɗamara da igiya kewaye da shi, yă kuma sa hular lilin. Waɗannan su ne riguna masu tsarki; saboda haka dole yă yi wanka kafin yă sa su. Zai ɗauki bunsurai biyu daga jama’ar Isra’ilawa na hadaya don zunubi da ɗan rago don hadaya ta ƙonawa. “Haruna zai miƙa bijimi hadaya don zunubinsa yă kuma yi kafara don kansa da gidansa. Sa’an nan zai ɗauki bunsurai biyu yă miƙa su a gaban Ubangiji a ƙofar Tentin Sujada. Haruna zai jefa ƙuri’a don awaki biyun ɗin, ƙuri’a ɗaya domin Ubangiji, ɗayan kuma don azazel Haruna zai kawo akuyar da ƙuri’a ta fāɗi a kai wa Ubangiji yă miƙa ta na hadaya don zunubi. Amma za a miƙa akuyar da aka zaɓa ta wurin ƙuri’a a matsayi ta azazel da rai a gaban Ubangiji don a yi amfani da ita don kafara ta wurin korinta zuwa cikin jeji kamar azazel. “Haruna zai kawo bijimi domin hadayarsa ta zunubi don yă yi kafara wa kansa da kuma domin gidansa, zai kuma yanka bijimin domin nasa hadaya don zunubi. Zai ɗauki faranti cike da garwashin wuta daga bagade a gaban Ubangiji, yă kuma cika hannunsa biyu da turare mai ƙanshin da aka niƙa yă kai su bayan labule. Zai sa turaren a wuta a gaban Ubangiji, hayaƙin turaren kuwa zai rufe murfin kafarar a bisa Akwatin Alkawari, don kada yă mutu. Zai ɗibi jinin bijimin da yatsarsa yă yayyafa a gaban murfin kafarar; sa’an nan yă yayyafa jinin da yatsarsa sau bakwai a gaban murfin kafarar. “Sa’an nan zai yanka akuya na hadaya don zunubi saboda mutane, yă kai jinin bayan labule, yă yi da shi yadda ya yi da jinin bijimin. Zai yayyafa shi a kan murfin kafarar da kuma a gabansa. Ta haka zai yi kafara domin Wuri Mafi Tsarki saboda ƙazantar tawayen Isra’ilawa, da laifofinsu, da dukan zunubansu. Haka zai yi saboda Tentin Sujada wanda yake a cikinsu a tsakiyar ƙazantarsu. Kada kowa yă kasance a Tentin Sujada daga lokacin da Haruna ya shiga don yă yi kafara a Wuri Mafi Tsarki har sai ya fita, bayan ya yi kafara domin kansa, gidansa da kuma dukan jama’ar Isra’ila. “Sa’an nan zai fita zuwa bagade da yake a gaban Ubangiji, yă yi kafara dominsa. Zai ɗibi jinin bijimi da na akuya yă zuba a ƙahonin bagade. Zai yayyafa jinin a kan bagade da yatsarsa sau bakwai, yă tsabtacce shi yă kuma tsarkake shi daga ƙazantar Isra’ilawa. “Sa’ad da Haruna ya gama yin kafara domin Wuri Mafi Tsarki, Tentin Sujada da kuma bagade, sai yă kawo akuya mai rai. Haruna zai ɗibiya hannuwansa a kan akuya mai ran, yă furta a kansa dukan mugunta da tawayen Isra’ilawa, dukan zunubansu, yă kuma sa su a kan akuyan. Zai kori akuyan zuwa cikin jeji a hannun mutumin da aka ba shi aikin yin haka. Akuyan zai ɗauka a kansa dukan zunubansu zuwa kaɗaitaccen wuri, a can mutumin zai sake shi a jeji. “Sa’an nan Haruna zai shiga Tentin Sujada yă tuɓe rigunansa na lilin da ya sa, kafin yă shiga Wuri Mafi Tsarki, zai kuma bar su a can. Zai yi wanka a tsattsarkan wuri yă sa rigunarsa na kullum. Sa’an nan zai fita yă miƙa hadaya ta ƙonawa domin kansa da hadaya ta ƙonawa domin mutane, don yă yi kafara domin kansa da kuma domin mutane. Zai kuma ƙone kitsen hadaya don zunubi a kan bagade. “Dole mutumin da ya saki akuya na azazel yă wanke rigunansa yă kuma yi wanka; bayan haka zai iya shiga sansani. Dole a ɗauki jini, fata, nama da kuma ƙashin bijimi da akuyan hadaya don zunubi, waɗanda aka kawo jininsu cikin Wuri Mafi Tsarki don kafara, a kai waje da sansani a ƙone. Dole mutumin da ya ƙone su yă wanke rigunansa yă kuma yi wanka, bayan haka zai iya shiga sansani. “Wannan za tă zama dawwammamiyar farilla a gare ku. A rana ta goma ga wata na bakwai, dole ku yi mūsu kanku, ba kuwa za ku yi wani aiki ba, ko da mutum baƙo ne a cikinku ko kuwa ɗan ƙasa, gama a wannan rana za a yi kafara dominku, don a tsarkake ku. Sa’an nan a gaban Ubangiji, za a tsarkake ku daga dukan zunubanku. Asabbaci ne don hutawa, kuma dole ku yi mūsun kanku; wannan dawwammamiyar farilla ce. Firist da aka keɓe aka kuma naɗa don yă gāji mahaifinsa a matsayin babban firist ne zai yi kafara. Zai sa rigunan lilin masu tsarki yă yi kafara domin Wuri Mafi Tsarki, Tentin Sujada da bagade, da kuma saboda firistoci da kuma dukan jama’ar Isra’ila. “Wannan za tă zama dawwammamiyar farilla ce gare ku. Za a riƙa yin kafara sau ɗaya a shekara saboda dukan zunuban Isra’ilawa.” Aka kuma yi haka, yadda Ubangiji ya umarci Musa. Ubangiji ya ce wa Musa, “Yi magana da Haruna da ’ya’yansa maza da kuma dukan Isra’ilawa, ka ce musu, ‘Ga abin da Ubangiji ya umarta. Duk mutumin Isra’ilan da ya yanka sa, ɗan rago ko akuya a sansani ko waje da shi a maimakon kawo shi a matsayin hadaya ga Ubangiji a gaban tabanakul na Ubangiji, za a ɗauki wannan mutum a matsayi mai laifin zub da jini, ya zub da jini, kuma dole a raba shi da mutanensa. Wannan ya zama haka saboda Isra’ilawa su kawo wa Ubangiji hadayun da suke yi a filaye. Dole su kawo su ga firist, wato, ga Ubangiji, a ƙofar Tentin Sujada, su miƙa su a matsayin hadayun salama. Firist zai yayyafa jinin a bagaden Ubangiji, a ƙofar Tentin Sujada, yă kuma ƙone kitsen kamar ƙanshi mai daɗi ga Ubangiji. Kada kuma su ƙara yin hadayunsu ga gumaka masu siffar bunsurai waɗanda suka bauta wa. Wannan za tă zama dawwammamiyar farilla a gare su wa tsararraki masu zuwa.’ “Faɗa musu, ‘Duk wani mutumin Isra’ila ko wani baƙon da yake zama a cikinsu wanda ya miƙa hadaya ta ƙonawa ko sadaka kuma bai kawo shi a ƙofar Tentin Sujada don yă miƙa shi ga Ubangiji ba, dole a raba wannan mutum da mutanensa. “ ‘Duk mutumin Isra’ila ko baƙon da yake zama a cikinsu wanda ya ci wani jini, zan yi gāba da wannan mutum wanda ya ci jinin, za a kuma raba shi da mutanensa. Gama ran halitta yana a cikin jinin, kuma na ba da shi gare ku don kafara a kan bagade, jini ne yake kafara saboda ran mutum. Saboda haka na ce wa Isra’ilawa, “Babu waninku da zai ci jini, babu wani baƙon da yake zama a cikinku da zai ci jini.” “ ‘Duk wani mutumin Isra’ila ko baƙon da yake zama a cikinku wanda ya ji wa wani dabba ko tsuntsu wanda ake ci ciwo, dole yă tsiyaye jinin yă rufe shi da ƙasa, domin ran kowace halitta yana cikin jini. Shi ya sa na ce wa Isra’ilawa, “Kada ku ci jinin wani halitta, domin ran kowace halitta yana cikin jinin; duk wanda ya ci shi dole a fid da shi.” “ ‘Kowa, ko haifaffe ɗan ƙasa ko baƙo, da ya ci wani abin da aka sami a mace, ko naman jeji ya yayyage, dole yă wanke rigunansa, yă kuma yi wanka, zai kuma ƙazantu har yamma; sa’an nan zai tsarkake. Amma in bai wanke rigunansa ya kuma yi wanka ba, alhaki zai kasance a kansa.’ ” Ubangiji ya ce wa Musa, “Yi wa Isra’ilawa magana ka kuma faɗa musu cewa, ‘Ni ne Ubangiji Allahnku. Kada ku yi yadda suke yi a Masar inda da kuke zama, kuma ba a ku yi kamar yadda suke yi a ƙasar Kan’ana inda nake kawo ku ba. Kada ku yi yadda suke yin abubuwa. Dole ku kiyaye dokokina kuma ku lura ku bi farillaina. Ni ne Ubangiji Allahnku. Ku kiyaye farillaina da dokokina, gama mutumin da ya aikata waɗannan abubuwa zai rayu ta wurinsu. Ni ne Ubangiji. “ ‘Kada wani ya kusaci wani dangi na kusa don yă yi jima’i. Ni ne Ubangiji. “ ‘Kada ka ƙasƙantar da mahaifinka ta wurin kwana da mahaifiyarka. Ita mahaifiyarka ce; kada ka yi jima’i da ita. “ ‘Kada ka yi jima’i da matar mahaifinka, wannan zai ƙasƙantar da mahaifinka. “ ‘Kada ka yi jima’i da ’yar’uwarka, ko ’yar mahaifinka ko ’yar mahaifiyarka, ko an haife ta a gida ɗaya da kai ko kuwa a wani wuri dabam. “ ‘Kada ka yi jima’i da ’yar ɗanka ko ’yar ’yarka, wannan zai ƙasƙantar da kai. “ ‘Kada ka yi jima’i da ’yar matar mahaifinka wadda aka haifa wa mahaifinka; ita ’yar’uwarka ce. “ ‘Kada ka yi jima’i da ’yar’uwar mahaifinka, ita dangin mahaifinka ne na kusa. “ ‘Kada ka yi jima’i da ’yar’uwar mahaifiyarka, domin ita dangin mahaifiyarka ce na kusa. “ ‘Kada ka ƙasƙantar da ɗan’uwan mahaifinka ta wurin kusaci matarsa don ka yi jima’i da ita, ita bābarka ce. “ ‘Kada ka yi jima’i da matar ɗanka. Ita matar ɗanka ne; kada ka yi jima’i da ita. “ ‘Kada ka yi jima’i da matar ɗan’uwanka; wannan zai ƙasƙanta ɗan’uwanka. “ ‘Kada ka yi jima’i da mace da kuma ’yarta. Kada ka yi jima’i da ’yar ɗanta ko ’yar ’yarta; su danginta ne na kusa. Wannan mugun abu ne. “ ‘Kada ka auri ’yar’uwar matarka ta zama kishiyar matarka ka kuma yi jima’i da ita yayinda matarka tana da rai. “ ‘Kada ka kusaci mace don ka yi jima’i da ita a lokacin ƙazantar al’adarta. “ ‘Kada ka yi jima’i da matar maƙwabcinka ka ƙazantar da kanka tare da ita. “ ‘Kada ku ba da wani daga cikin ’ya’yanku don a yi hadaya wa Molek, gama ba za ku ƙasƙantar da sunan Allahnku ba. Ni ne Ubangiji. “ ‘Kada ka kwana da namiji kamar yadda namiji yakan kwana da ta mace, wannan abin ƙyama ne. “ ‘Kada ka yi jima’i da dabba ka ƙazantar da kanka. Mace ba za tă ba da kanta ga dabba don yă yi jima’i da ita ba; wannan abin ƙyama ne. “ ‘Kada ku ƙazantar da kanku da wani daga cikin waɗannan, domin haka al’umman da zan kora a gabanku suka ƙazantu. Har ƙasar ma ta ƙazantu, saboda haka na hukunta ta saboda zunubinta, ƙasar kuwa ta amayar da mazaunanta. Amma dole ku kiyaye farillaina da kuma dokokina. Kada haifaffe ɗan ƙasa da baƙin da suke zama a cikinku yă yi wani daga cikin waɗannan abubuwa banƙyama, gama mutanen da suka zauna a wannan ƙasa kafin ku sun aikata dukan waɗannan abubuwa, suka kuma ƙazantu. Kuma in kuka ƙazantar da ƙasar, za tă amayar da ku kamar yadda ta amayar da al’umman da suka riga ku. “ ‘Duk wanda ya yi wani daga cikin waɗannan abubuwa banƙyama, dole a fid da mutumin daga cikin mutanensa. Ku kiyaye umarnaina kuma kada yi ku wata al’ada mai banƙyamar da aka yi kafin ku zo kuma kada ku ƙazantar da kanku da su. Ni ne Ubangiji Allahnku.’ ” Ubangiji ya ce wa Musa, “Yi wa taron jama’ar Isra’ila gaba ɗaya magana, ka ce musu, ‘Ku zama masu tsarki, domin Ni, Ubangiji Allahnku, mai tsarki ne. “ ‘Dole kowannenku yă girmama mahaifiyarsa da mahaifinsa, dole kuma ku kiyaye Asabbacina. Ni ne Ubangiji Allahnku. “ ‘Kada ku juyo ga gumaka, ko ku yi wa kanku allolin da aka yi zubi da ƙarfe. Ni ne Ubangiji Allahnku. “ ‘Sa’ad da kuka miƙa hadaya ta salama ga Ubangiji, ku miƙa ta yadda za tă karɓu a madadinku. Za a ci ta a ranar da kuka miƙa ta, ko kuwa a kashegarin; duk abin da ya rage har kwana ta uku dole a ƙone shi. In aka ci ta a rana ta uku, marar tsabta ce, ba kuma za a karɓe ta ba. Duk wanda ya ci ta zai zama da laifi domin ya ƙazantar da abin da yake da tsarki ga Ubangiji, dole a raba mutumin nan da mutanensa. “ ‘Sa’ad da kuka yi girbin amfanin gonarku, kada ku girbe har zuwa gefen gonar, ko ku yi kalan girbinku. Kada ku koma gonar inabinku kuna kala, ko ku tattara ’ya’yan inabin da suka fāffāɗi. Ku bar su domin matalauta da kuma baƙi. Ni ne Ubangiji Allahnku. “ ‘Kada ku yi sata. “ ‘Kada ku yi ƙarya. “ ‘Kada ku ruɗe juna. “ ‘Kada ku rantse bisa ƙarya da sunana, ta haka har ku ƙasƙantar da sunan Allahnku. Ni ne Ubangiji. “ ‘Kada ku zalunci maƙwabcinku, ko ku yi masa ƙwace. “ ‘Kada ku riƙe albashin ma’aikaci yă kwana. “ ‘Kada ku zagi kurma, ko ku sa abin tuntuɓe a gaban makaho, amma ku ji tsoron Allahnku. Ni ne Ubangiji. “ ‘Kada ku yi rashin adalci cikin shari’a; kada ku nuna sonkai ga matalauci, ko ku goyi bayan mai arziki, amma ku shari’anta maƙwabci cikin gaskiya. “ ‘Kada ku yi ta yawo kuna yaɗa ƙarya a cikin mutanenku. “ ‘Kada ku yi wani abin da zai sa ran maƙwabcinku cikin hatsari. Ni ne Ubangiji. “ ‘Kada ka yi ƙiyayyar ɗan’uwanka a zuciya. Ka tsawata wa maƙwabcinka da gaske don kada ka sami rabo cikin laifinsa. “ ‘Kada ka nemi yin ramuwa, ko ka riƙe wani cikin mutanenka a zuciya, amma ka ƙaunaci maƙwabcinka kamar kanka. Ni ne Ubangiji. “ ‘Ku kiyaye farillaina. “ ‘Kada ku sa dabbobin da ba iri ɗaya ba su yi barbara. “ ‘Kada ku yi shuki iri biyu a gonarku. “ ‘Kada ku sa rigar da aka saƙa da yadi iri biyu. “ ‘In wani ya kwana da mace wadda take baiwa, wadda aka yi wa wani alkawari amma bai fanshe ta ba, ko kuwa ba a ’yantar da ita ba, dole a yi hukuncin da ya dace. Duk da haka ba za a kashe su ba, domin ba a ’yantar da ita ba. Dole mutumin da ya kwana da ita yă kawo rago a ƙofar Tentin Sujada domin hadaya don laifi ga Ubangiji. Da ragon hadaya don laifin ne firist zai yi kafara saboda mutumin a gaban Ubangiji saboda zunubin da ya yi, za a kuwa gafarta zunubinsa. “ ‘Sa’ad da kuka shiga ƙasar kuka kuma shuka kowane irin itace mai ’ya’ya na ci, ku ɗauki ’ya’yan itatuwan nan a matsayi an hana ku ci. Shekara uku za ku ɗauka a matsayi an hana ku, ba za ku ci su ba. A shekara ta huɗu, dukan ’ya’yansu za su zama tsarkakakku, hadaya ta yabo ga Ubangiji. Amma a shekara ta biyar, za ku iya cin ’ya’yan itatuwan. Ta haka girbinku zai ƙaru. Ni ne Ubangiji Allahnku. “ ‘Kada ku ci wani abinci tare da jini a cikinsa. “ ‘Kada ku yi duba ko sihiri. “ ‘Ba za ka aske gefe-gefe na gashin kanka ba, ko ku aske gemunku. “ ‘Kada ku tsattsaga jikunanku saboda matattu, ba kuwa za ku yi wa kanku zāne-zāne a jiki ba. Ni ne Ubangiji. “ ‘Kada ka ƙasƙantar da ’yarka ta wurin mai da ita karuwa, in ba haka ba ƙasar za tă juya ga karuwanci tă kuma cika da mugunta. “ ‘Ku kiyaye Asabbacina, ku kuma girmama wuri mai tsarkina. Ni ne Ubangiji. “ ‘Kada ku juya ga masu duba, ko ku nemi shawarar bokaye, gama za ku ƙazantu ta wurinsu. Ni ne Ubangiji Allahnku. “ ‘Ku miƙe tsaye a gaban tsofaffi, ku nuna bangirma ga waɗanda suka tsufa, ku kuma girmama Allahnku. Ni ne Ubangiji. “ ‘Sa’ad da baƙo yana zama tare da ku a ƙasarku, kada ku wulaƙanta shi. Dole ku ɗauki baƙon da yake zama tare da ku kamar haifaffe ɗan ƙasa. Ku ƙaunace shi kamar kanku, gama dā ku ma baƙi ne a Masar. Ni ne Ubangiji Allahnku. “ ‘Kada ku yi amfani da mudun ƙarya sa’ad da kuke awon tsawo, nauyi, ko yawan abu. Ku yi amfani da ma’auni na gaskiya da mudu na gaskiya, da kuma magwaji na gaskiya. Ni ne Ubangiji Allahnku, wanda ya fitar da ku daga Masar. “ ‘Ku kiyaye dukan farillaina da kuma dukan dokokina, ku kuma bi su. Ni ne Ubangiji.’ ” Ubangiji ya ce wa Musa, “Faɗa wa Isra’ilawa cewa, ‘Duk wani mutumin Isra’ila ko baƙon da yake zama a cikin Isra’ila da ya miƙa wani daga cikin ’ya’yansa wa Molek, dole sa kashe shi. Mutanen ƙasar za su jajjefe shi. Zan yi gāba da wannan mutum, zan kuma raba shi da mutanensa; gama ta wurin miƙa ’ya’yansa ga Molek, ya ƙazantar da wuri mai tsarkina, ya kuma ƙazantar da sunana mai tsarki. In mutanen ƙasar suka kau da idanunsu sa’ad da wannan mutum ya miƙa ’ya’yansa ga Molek, suka kāsa kashe shi, zan yi gāba da wannan mutum da iyalinsa, zan raba shi da kuma duk waɗanda suka bi shi cikin karuwanci ga Molek daga mutanensu. “ ‘Zan yi gāba da mutumin da ya juyo ga masu duba da bokaye, don yă yi karuwanci ta wurin bin su, zan kuma raba shi daga mutanensa. “ ‘Ku tsarkake kanku, ku kuma zama da tsarki, gama Ni ne Ubangiji Allahnku. Ku kiyaye farillaina, ku kuma bi su. Ni ne Ubangiji, wanda ya mai da ku masu tsarki. “ ‘In wani ya zagi mahaifinsa ko mahaifiyarsa, dole a kashe shi. Domin ya zagi mahaifinsa ko mahaifiyarsa, alhakin jininsa zai zauna a kansa. “ ‘In mutum ya yi zina da matar wani, da matar maƙwabcinsa, dole a kashe su biyu da suka yi zinan. “ ‘In mutum ya kwana da matar mahaifinsa, ya ƙasƙantar da mahaifinsa. Dole a kashe shi da macen, alhakin jininsu zai zauna a kansu. “ ‘In mutum ya kwana da matar ɗansa, dole a kashe su biyun. Abin da suka yi haram ne; alhakin jininsu zai zauna a kansu. “ ‘In mutum ya kwana da mutum kamar yadda ake kwana da mace, su biyun sun yi abin ƙyama. Dole a kashe su, alhakin jininsu zai zauna a kansu. “ ‘In mutum ya auri ’ya da mahaifiyarta, mugun abu ne. Da shi da su, dole a ƙone su da wuta, saboda kada mugun abu yă kasance a cikinku. “ ‘In mutum ya yi jima’i da dabba, dole a kashe shi, dole kuma ku kashe dabbar. “ ‘In mace ta kusaci dabba don tă yi jima’i da ita, ku kashe macen da dabbar. Dole a kashe su; alhakin jininsu zai zauna a kansu. “ ‘In mutum ya auri ’yar’uwarsa, ko ’yar mahaifinsa, ko kuwa ta mahaifiyarsa, suka kuma yi jima’i, abin kunya ne. Dole a raba su a idanun mutanensu. Ya ƙasƙantar da ’yar’uwarsa kuma za a nemi hakki daga gare shi. “ ‘In mutum ya kwana da mace a lokacin al’adarta, duka biyunsu za a kore su daga cikin jama’arsu, gama sun karya ƙa’idodi a kan rashi tsarki. “ ‘Kada ka yi jima’i da ’yar’uwar mahaifiyarka, ko ta mahaifinka, gama wannan zai ƙasƙantar da dangi na kurkusa, dukanku za ku ɗauki laifin. “ ‘In mutum ya kwana da bābarsa, ya ƙasƙantar da kawunsa ke nan. Hakkin zai kasance a kansu, za su mutu babu ’ya’ya. “ ‘In mutum ya auri matar ɗan’uwansa, aikin rashin tsabta ne, ya ƙasƙantar da ɗan’uwansa ke nan. Za su mutu babu ’ya’ya. “ ‘Ku kiyaye dukan farillaina da dokokina duka, don kada ƙasar da nake kai ku ta amayar da ku. Kada ku yi zama bisa ga al’adun al’umman da zan kora a gabanku. Domin sun aikata dukan waɗannan abubuwa, na yi ƙyamarsu. Amma na faɗa muku, “Za ku mallaki ƙasarsu, zan ba ku ita gādo, ƙasa mai zub da madara da zuma.” Ni ne Ubangiji Allahnku, wanda ya keɓe ku daga al’ummai. “ ‘Saboda haka sai ku bambanta tsakanin dabbobi masu tsarki da marasa tsarki, da kuma tsakanin tsuntsaye masu tsarki da marasa tsarki. Kada ku ƙazantar da kanku ta wurin wata dabba, ko tsuntsu, ko wani abin da yake rarrafe a ƙasa, waɗanda na keɓe a matsayi marasa tsarki a gare ku. Ku zama tsarkakakke gare ni, gama Ni Ubangiji, mai tsarki ne, na kuma keɓe ku daga al’ummai don ku zama nawa. “ ‘Namiji, ko ta macen da yake mai duba, ko maita a cikinku dole a kashe. Za ku jajjefe su da duwatsu; alhakin jininsu zai zauna a kansu.’ ” Ubangiji ya ce wa Musa, “Yi magana da firistoci, ’ya’yan Haruna maza, ka ce musu, ‘Kada firist yă ƙazantar da kansa saboda wani cikin mutanensa da suka mutu, sai dai na danginsa na kusa, kamar mahaifiyarsa ko mahaifinsa, ɗansa ko ’yarsa, ɗan’uwansa, ko ’yar’uwarsa da ba tă riga ta yi aure ba, wadda take dogara gare shi, da yake ba ta da miji, saboda ita zai iya ƙazantar da kansa. Kada yă ƙazantar da kansa saboda mutanen da suke da dangantakar da shi ta wurin aure, ta yin haka zai ƙazantar da kansa. “ ‘Kada firistoci su aske kansu ƙwal ko su kwakkwafe gemunsu, ko su tsattsage jikunansu. Dole su kasance masu tsarki ga Allahnsu, kada kuma su ɓata sunan Allahnsu. Domin sukan miƙa hadayun da aka kawo wa Ubangiji da wuta, abincin Allahnsu, saboda haka sai su kasance da tsarki. “ ‘Ba za su auri matan da karuwanci ya ɓata su, ko waɗanda mazansu suka sake su ba, gama firistoci masu tsarki ne ga Allahnsu. An ɗauke su da tsarki, domin suna miƙa abincin Allahnku. An ɗauka su masu tsarki gama Ni Ubangiji, mai tsarki ne, Ni wanda ya mai da ku masu tsarki. “ ‘In ’yar firist ta ɓata kanta ta wurin zama karuwa, ta kunyatar da mahaifinta ke nan; dole a ƙone ta da wuta. “ ‘Babban firist, wanda yake ɗaya cikin ’yan’uwansa wanda aka shafe da mai a kansa, wanda kuma aka naɗa don yă sa rigunan firistoci, kada yă bar gashin kansa buzu-buzu, ko ya kyakketa rigunansa. Ba zai shiga inda akwai gawa ba. Kada yă ƙazantar da kansa, ko ma ta mahaifinsa ce ko ta mahaifiyarsa. An keɓe shi domina, kada yă ƙazantar da kansa, kada kuwa yă ɓata Tentin Sujada ta wurin shiga gidan da gawa take, ko ta mahaifinsa, ko ta mahaifiyarsa ce. Ni ne Ubangiji. “ ‘Dole macen da zai aura ta kasance budurwa. Ba zai auri matan da mijinta ya mutu, ko macen da mijinta ya rabu da ita, ko macen da ta ɓata kanta ta wurin karuwanci ba, sai dai yă auri budurwa daga cikin mutanensa, don kada yă ƙazantar da ’ya’yansa a cikin mutanensa. Ni ne Ubangiji, wanda ya mai da shi mai tsarki.’ ” Ubangiji ya ce wa Musa, “Faɗa wa Haruna cewa, ‘Don tsararraki masu zuwa, kada ko ɗaya daga cikin zuriyarka, da yake da lahani yă zo kusa domin yă miƙa hadaya ta ci gare ni. Duk mai lahani, ko makaho, ko gurgu, ko mai naƙasa, ko mai wani lahani a jiki; ko mai karyayyen ƙafa, ko mai karyayyen hannu, ko mai ƙusumbi, ko wada, ko wanda yake da lahani a ido, ko mai cuta mai sa ƙaiƙayi, ko mai kirci, ko wanda aka daƙe, ba zai yi kusa domin yă miƙa hadaya ba. Ba zuriyar Haruna firist, mai lahanin da zai zo kusa don yă miƙa hadayun da aka yi ga Ubangiji da wuta. Da yake yana da lahani, ba zai zo kusa don yă miƙa abincin Allahnsa ba. Zai iya cin abinci mafi tsarki na Allahnsa, haka ma abinci mai tsarki; duk da haka saboda lahaninsa, ba zai yi kusa da labule, ko yă yi kusa da bagade don kada yă ƙazantar da wuri mai tsarkina. Ni ne Ubangiji wanda yake mai da su masu tsarki.’ ” Sai Musa ya faɗa wannan wa Haruna da ’ya’yansa maza da kuma dukan Isra’ilawa. Ubangiji ya ce wa Musa, “Faɗa wa Haruna da ’ya’yansa maza, su lura da tsarkakakkun abubuwan da Isra’ilawa suka keɓe gare ni da bangirma, saboda ba za su ƙazantar da sunana mai tsarki ba. Ni ne Ubangiji. “Faɗa musu cewa, ‘Don tsararraki masu zuwa, in wani zuriyarku ya ƙazantu, duk da haka ya kusaci tsarkakakku hadayun da Isra’ilawa suka keɓe ga Ubangiji, dole a raba wannan mutum daga gabana. Ni ne Ubangiji. “ ‘In zuriyar Haruna yana da kuturu, ko mai ɗiga, ba zai ci daga cikin tsarkakakkun abubuwa ba, sai lokacin da ya tsarkaka. Duk wanda ya taɓa wani abu marar tsarki na mamaci, ko wanda maniyyinsa yake ɗiga, da duk kuma wanda ya taɓa wani abu mai rarrafe wanda yake ƙazantarwa, ko kuwa wani mutum mai ƙazanta, duk mutumin da ya taɓa kowane irin abu haka, zai ƙazantu har yamma, ba kuwa zai ci daga cikin tsarkakakkun abubuwan nan ba, sai ya yi wanka tukuna. Sa’ad da rana ta fāɗi, zai zama tsarkakakke, bayan wannan kuwa zai iya cin tsarkakakkun hadayu, gama abincinsa ne. Kada yă ci wani abin da ya mutu mushe, ko wanda namun jeji suka yayyaga, don kada yă ƙazantar da kansa. Ni ne Ubangiji. “ ‘Firistoci za su kiyaye umarnaina don kada su yi laifi su mutu saboda sun rena su. Ni ne Ubangiji, wanda ya mai da su masu tsarki. “ ‘Duk wanda ba daga cikin iyalin firistoci ba, ko da yake yana zama tare da su, ko kuwa an ɗauke shi yana yin musu aiki, ba zai ci daga cikin tsarkakakkun hadayun ba. Amma in firist ya sayi bawa da kuɗi, ko kuwa in an haifi bawan a gidansa, wannan bawan zai iya cin tsattsarkan abincin. In ’yar firist ta auri wani da ba firist ba, ba za tă ci wani tsarkakakkun sadaka ba. Amma idan ’yar firist ta zama gwauruwa ko sakakkiya, ba ta da ’ya’ya, ta kuwa dawo don tă zauna a gidan mahaifinta kamar matashiya, za tă iya cin abincin. “ ‘In wani ya ci tsarkakakken abinci cikin kuskure, dole yă maido wa firist hadayar, yă kuma ƙara kashi ɗaya bisa biyar na tamanin abin. Firist ɗin ba zai ƙasƙantar da tsarkakakkun hadayun da Isra’ilawa suka kawo ga Ubangiji ta wurin barinsu su ci tsarkakakkun hadayu, ta yin haka su jawo wa kansu laifin da zai bukaci biya ba. Ni ne Ubangiji, wanda ya mai da ku masu tsarki.’ ” Ubangiji ya ce wa Musa, “Yi wa Haruna da ’ya’yansa maza da kuma dukan Isra’ilawa magana ka ce musu, ‘In waninku, ko mutumin Isra’ila, ko baƙon da yake zama a Isra’ila, ya kawo kyauta don hadaya ta ƙonawa ga Ubangiji, ko don yă cika alkawari, ko kuwa a matsayin hadaya ta yardar rai, dole ku miƙa dabba namiji marar lahani, daga shanu, tumaki, ko awaki, domin yă zama yardajje a madadinku. Kada ku kawo wani abu mai lahani, domin ba zai zama yardajje ba a madadinku. Sa’ad da wani ya kawo hadaya ta salama daga garken shanu, ko na tumaki, ga Ubangiji don yă cika wani alkawari na musamman, ko hadaya ta yardar rai, dole yă zama marar lahani, ko tabo, don yă zama yardajje. Kada ku miƙa wa Ubangiji dabbobi makafi, ko naƙasassu, ko masu gundumi, ko masu ɗiga, ko masu susa, ko masu kirci. Kada ku sa wani daga cikin waɗannan a bisa bagade a matsayin hadaya, gama hadaya ce da aka ƙone da wuta ga Ubangiji. Za ku iya miƙa hadaya ta yardar rai da maraƙi, ko tunkiya mai naƙasa, ko marar cikakken lafiya, amma ba za tă zama yardajje don cika alkawarin da aka yi ba. Ba za ku miƙa wa Ubangiji dabbar da lunsayinta yake da ƙujewa, ko dandaƙewa, ko yagewa, ko yankewa ba. Ba za ku kuma karɓi irin waɗannan dabbobi daga hannun baƙi ku miƙa su a matsayin abinci ga Allahnku ba. Ba za su zama yardajje a madadinku ba, domin sun naƙasa, suna kuma da lahani.’ ” Ubangiji ya ce wa Musa, “Sa’ad da aka haifi ɗan maraƙi, tunkiya, ko akuya, sai yă kasance da mahaifiyarsa kwana bakwai. Daga rana ta takwas zuwa gaba, zai zama yardajje hadaya, hadaya ce da aka ƙone da wuta ga Ubangiji. Kada a yanka saniya, ko tunkiya da ɗanta rana ɗaya. “Sa’ad da kuka miƙa hadaya ta godiya ga Ubangiji, ku miƙa ta a yadda za tă zama yardajje a madadinku. Dole a ci hadayar a ranar; kada a bar saura sai da safe. Ni ne Ubangiji. “Ku kiyaye dokokina, ku kuma bi su. Ni ne Ubangiji. Kada ku ƙasƙantar da sunana mai tsarki. Dole Isra’ilawa su gane Ni mai tsarki ne. Ni ne Ubangiji, wanda ya keɓe ku a matsayin tsarkaka da kuma wanda ya fitar da ku daga Masar don in zama Allahnku. Ni ne Ubangiji.” Ubangiji ya ce wa Musa, “Yi magana da Isra’ilawa, ka ce musu, ‘Ga ƙayyadaddun bukukkuwa, ƙayyadaddun bukukkuwan Ubangiji, da za ku sanar wa mutane su riƙa kiyayewa, su zama lokutan tarurruka masu tsarki. “ ‘Akwai kwanaki shida da za ku iya yin aiki, amma rana ta bakwai, Asabbaci ne na hutu, rana mai tsarki ga jama’a. Kada ku yi wani aiki a ko’ina kuke da zama, Asabbaci ne ga Ubangiji. “ ‘Waɗannan su ne bukukkuwan da Ubangiji ya kafa da tsarkakakkun taron jama’a za su yi a ƙayyadaddun lokuta. Bikin Ƙetarewar Ubangiji, zai fara da yamma a ranar goma sha huɗu na wata na fari. A rana ta goma sha biyar na wannan wata, za a fara Bikin Burodi Marar Yisti na Ubangiji. Za ku yi kwana bakwai kuna cin burodi marar yisti. A rana ta fari, ku yi taro mai tsarki, ba kuwa za ku yi aiki na kullum ba. Kwana bakwai za ku miƙa hadaya ga Ubangiji da wuta. A rana ta bakwai ɗin ku yi taro mai tsarki, ba za ku kuwa yi aiki na kullum ba.’ ” Ubangiji ya ce wa Musa, “Yi magana da Isra’ilawa, ka ce musu, ‘Sa’ad da kuka shiga ƙasar da zan ba ku, kuka kuma girbe amfanin gonarta, sai ku kawo wa firist damin hatsi na farko da kuka girbe. Zai kaɗa damin a gaban Ubangiji domin yă zama yardajje a madadinku; firist ɗin zai kaɗa shi a kashegarin Asabbaci. A ranar da kuka kaɗa damin, dole ku miƙa hadaya ta ƙonawa na ɗan rago bana ɗaya, marar lahani ga Ubangiji, tare da hadaya ta gari mai laushi, humushi biyu haɗe da mai, wato, hadaya ce da aka ƙone da wuta ga Ubangiji, mai daɗin ƙanshi, da kuma abin sha kwalaba ɗaya na ruwan inabi. Ba za ku ci wani burodi, ko gasasshen hatsi, ko sabon hatsi ba, sai ran nan da kuka kawo wannan hadaya ga Allahnku. Wannan za tă zama dawwammamiyar farilla wa tsararraki masu zuwa, a duk inda kuke zama. “ ‘Daga kashegarin Asabbaci, ranar da kuka kawo dami don hadaya ta kaɗawa, ku ƙirga cikakku makoni bakwai. Ku ƙirga kwana hamsin har zuwa kashegarin Asabbaci na bakwai, sa’an nan ku miƙa hadaya ta sabon hatsi ga Ubangiji. Daga ko’ina kuke da zama, ku kawo dunƙule biyu na humushin gari mai laushi da aka tuya da yisti, a matsayin hadaya ta kaɗawa ta ’ya’yan fari na itatuwa ga Ubangiji. Tare da wannan, ku miƙa ’yan raguna bakwai, kowanne bana ɗaya-ɗaya marar lahani, bijimi da kuma raguna biyu. Za su zama hadaya ta ƙonawa ga Ubangiji, tare da hadayunsu na hatsi, da hadayunsu na sha, hadaya da aka yi da wuta, mai daɗin ƙanshi ga Ubangiji. Sa’an nan ku miƙa bunsuru ɗaya na hadaya don zunubi, da ’yan raguna biyu, kowanne bana ɗaya-ɗaya, don hadaya ta salama. Firist zai kaɗa ’yan raguna biyun a gaban Ubangiji, a matsayin hadaya ta kaɗawa, tare da burodin sababbin ’ya’yan fari na itatuwan. Tsarkaken hadaya ce ga Ubangiji ga firist. A wannan rana za ku yi taro mai tsarki, ba kuwa za ku yi aiki na kullum ba. Wannan za tă zama dawwammamiyar farilla wa tsararraki masu zuwa, a ko’ina kuke da zama. “ ‘Sa’ad da kuka yi girbin gonarku, kada ku girbe har ƙarshen gefen gonar, ko ku yi kalar girbinku. Ku bar su wa matalauta da baƙi. Ni ne Ubangiji Allahnku.’ ” Ubangiji ya ce wa Musa, “Faɗa wa Isra’ilawa cewa, ‘A ranar farko ga wata na bakwai, za tă zama ranar hutu, rana ce ta tuni da yin taro mai tsarki na sujada da za a fara busar ƙaho. Kada ku yi aiki na kullum, amma ku miƙa hadaya ta ƙonawa ga Ubangiji.’ ” Ubangiji ya ce wa Musa, “Rana ta goma ta wata bakwai, za tă zama Ranar Kafara. Sai ku yi taro mai tsarki don ku yi mūsun kanku ku kuma miƙa hadayar da aka yi da wuta ga Ubangiji. Kada ku yi aiki a ranar, gama Ranar Kafara ce, sa’ad da za a yi kafara saboda ku a gaban Ubangiji Allahnku. Duk wanda bai yi mūsun kansa a wannan rana ba, dole a raba shi daga mutanensa. Zan hallaka duk wani da ya yi aiki a wannan rana daga mutanensa. Sam ba za ku yi wani aiki ba. Wannan za tă zama dawwammamiyar farilla ce, wa tsararraki masu zuwa, a ko’ina kuke da zama. Asabbaci ne na hutu dominku, kuma dole ku yi mūsun kanku. Daga yamman rana ta tara ga wata, har zuwa yamma na biye, za ku kiyaye Asabbacinku.” Ubangiji ya ce wa Musa, “Faɗa wa Isra’ilawa cewa, ‘A ranar goma sha biyar ga wata na bakwai, za a fara Bikin Tabanakul na Ubangiji, zai kuma ɗauki kwana bakwai. A ranar farko za tă zama ta taro mai tsarki, kada ku yi aiki na kullum. Kwana bakwai za ku miƙa hadayun da aka yi da wuta ga Ubangiji, a rana ta takwas, ku yi taro mai tsarki, ku kuma miƙa hadayar da aka yi da wuta ga Ubangiji. Wannan ranar rufewar taro ce; kada ku yi aiki na kullum. (“ ‘Waɗannan su ne bukukkuwan da Ubangiji ya kafa, waɗanda za ku yi a matsayin tsarkakakkun taro, don kawo hadayun da aka yi da wuta ga Ubangiji, hadayu na ƙonawa da hadayu na hatsi, sadaka da kuma hadayu na sha, da ake bukata kowace rana. Waɗannan hadayu, ƙari ne a kan waɗannan na Asabbatan Ubangiji, haɗe kuma da kyautanku, da kome da kuka yi alkawari, da kuma hadayu yardar ran da za ku ba wa Ubangiji.) “ ‘Saboda haka, farawa daga ranar goma sha biyar ga watan bakwai, bayan kun tara hatsin gona, ku yi bikin Ubangiji kwana bakwai; rana ta fari, rana hutu ce, rana ta takwas kuma rana hutu ce. A rana ta fari, za ku ɗebi zaɓaɓɓun ’ya’yan itatuwa daga itatuwa, da rassan dabino, rassa masu ganye, da kuma ganyayen itacen wardi na rafi, ku yi farin ciki a gaban Ubangiji Allahnku, kwana bakwai. Za ku kiyaye bikin nan har kwana bakwai a kowace shekara ga Ubangiji. Wannan za tă zama dawwammamiyar farilla wa tsarraraki masu zuwa, ku kiyaye ta a wata na bakwai. Ku zauna a bukkoki kwana bakwai. Dukan ’yan ƙasa haifaffun Isra’ilawa, za su zauna a bukkoki don zuriyarku tă san cewa na sa Isra’ilawa suka zauna a bukkoki sa’ad da na fitar da su daga Masar. Ni ne Ubangiji Allahnku.’ ” Saboda haka Musa ya sanar wa Isra’ilawa ƙayyadaddun bukukkuwan Ubangiji. Ubangiji ya ce wa Musa, “Ka umarci Isra’ilawa su kawo tsabtataccen mai na zaitun da aka matse, don ƙuna fitilun yadda harshen wutar ba zai taɓa mutuwa ba. Za a ajiye su waje da labulen Wuri Mafi Tsarki a Tentin Sujada, Haruna zai riƙa kula da fitilun a gaban Ubangiji, daga yamma zuwa safiya. Wannan za tă zama dawwammamiyar farilla wa tsararraki masu zuwa. Dole a ci gaba da shirya fitilu a kan wurin ajiye fitila na zinariya, a gaban Ubangiji. “Ɗauki gari mai laushi a gasa dunƙulen burodi goma sha biyu, a yi amfani da humushi biyu na garwan gari don kowace burodi. A shirya su jeri biyu, guda shida a kowane jeri a kan teburin da aka yi da zinariya zalla, a gaban Ubangiji. Za a zuba turare a kowane layin dunƙulen burodin don yă kasance abin tunawa a bisa burodin. Turaren zai ƙone a madadin burodin don yă zama kamar hadayar da aka miƙa da wuta ga Ubangiji. Za a shirya wannan gurasa a gaban Ubangiji kowane Asabbaci, a madadin Isra’ilawa a matsayin madawwamin alkawari. Wannan burodin zai zama na Haruna da ’ya’yansa maza, waɗanda za su ci a tsattsarkan wuri, gama sashe ne mafi tsarki na rabonsu na kullum na hadayar da aka yi da wuta ga Ubangiji.” To, ɗan wata mutuniyar Isra’ila wanda mahaifinsa mutumin Masar ne, ya je cikin Isra’ilawa, sai faɗa ta tashi tsakaninsa da wani mutumin Isra’ila a cikin sansani. Ɗan mutuniyar Isra’ila ya saɓi Sunan Ubangiji, ya kuma la’ana shi, saboda haka aka kawo shi wa Musa. (Sunan mahaifiyarsa Shelomit ne, ’yar Dibri na kabilar Dan.) Suka sa shi a gidan tsaro sai lokacin da nufin Ubangiji ya nuna musu abin da za su yi da shi. Sai Ubangiji ya ce wa Musa, “Ka kai mai saɓon nan waje da sansani. Duk waɗanda suka ji maganar da mai saɓon nan ya yi su ɗibiya hannuwansu a kansa, taron jama’a kuwa gaba ɗaya su jajjefe shi da duwatsu. Faɗa wa Isra’ilawa cewa, ‘Duk wanda ya zagi Allahnsa, alhakin zai rataya a wuyansa, duk wanda ya saɓi sunan Ubangiji, dole a kashe shi. Dole jama’a gaba ɗaya su jajjefe shi da duwatsu. Ko baƙo, ko haifaffen ɗan ƙasa, sa’ad da ya saɓi Sunan Ubangiji, dole a kashe shi. “ ‘Duk wanda ya kashe mutum, dole a kashe shi. Duk wanda ya kashe dabbar wani, dole yă biya, rai domin rai. Duk wanda ya yi wa maƙwabcinsa rauni, sai a yi masa abin da ya yi; karaya don karaya, ido don ido, haƙori don haƙori. Kamar yadda ya yi wa wani rauni, shi ma a yi masa. Duk wanda ya kashe dabba, dole yă biya, amma duk wanda ya kashe mutum, dole a kashe shi. Za ku kasance da doka iri ɗaya wa baƙo da kuma wa haifaffen ɗan ƙasa. Ni ne Ubangiji Allahnku.’ ” Sai Musa ya yi wa Isra’ilawa magana, suka kuwa kai mai saɓon waje da sansani, suka jajjefi shi da duwatsu. Isra’ilawa suka yi yadda Ubangiji ya umarci Musa. Ubangiji ya yi magana da Musa a kan Dutsen Sinai ya ce, “Yi wa Isra’ilawa magana, ka ce musu, ‘Sa’ad da kuka shiga ƙasar da zan ba ku, dole ƙasar kanta ta kiyaye Asabbaci ga Ubangiji. Shekara shida, za ku yi shuki, shekara shida kuma za ku aske gonakin inabinku, ku kuma tattara hatsinsu. Amma a shekara ta bakwai, ƙasar za tă sami hutun Asabbaci, Asabbaci ga Ubangiji. Kada ku yi shuki a gonakinku, ko kuwa ku aske gonakinku na inabi. Kada ku girbe abin da ya yi girma ba tare da ku kuka shuka ba, ko ku girbe inabin da ba ku aske ba. Ƙasar za tă kasance da shekarar hutu. Duk abin da gonar ta ba da amfani a shekara ta Asabbaci, zai zama abinci gare ku, wa kanku, bayinku maza da mata, da ma’aikatan da kuka ɗauka aiki, da kuma waɗanda ba zama ɗinɗinɗin suke yi tare da ku ba, haka ma zai zama abinci domin dabbobinku, da kuma namun jeji a ƙasarku. Duk abin da ƙasar ta bayar za a ci. “ ‘Ku ƙirga asabbatai bakwai na shekaru bakwai, sau bakwai. Gama asabbatai bakwai na shekaru bakwai za su yi daidai da shekaru arba’in da tara. Sa’an nan a busa ƙaho a ko’ina, a rana ta goma ga wata na bakwai; a Ranar Kafara, a busa ƙaho a dukan ƙasarku. Ku keɓe shekara ta hamsin ku kuma yi shelar ’yanci a dukan ƙasar ga mazaunanta. Za tă zama shekarar murna gare ku; kowannenku zai koma ga mallakar iyalinsa, kuma kowa ga danginsa. Shekara ta hamsin za tă zama ta murna a gare ku; kada ku yi shuki, kada kuma ku yi girbi abin da ya yi girma da kansa, ko ku girbe inabin da ba ku lura da shi ba. Gama shekara ce ta murna, za tă kuma zama mai tsarki a gare ku, ku dai ci abin da aka ɗauka kai tsaye daga gonaki. “ ‘A wannan Shekara ta Murna, kowa zai koma ga mallakarsa. “ ‘In ka sayar da gona wa wani daga mutanen ƙasarka, ko ka saya wata gona daga gare shi, kada ku cuci juna. Sa’ad da mutum ya sayi fili daga abokin zamansa, kuɗin zai kasance bisa ga yawan shekara hamsin ta murna da suka wuce, da kuma bisa ga yawan shekarun noma da suka rage kafin wata shekara hamsin ta murna. Idan shekarun suna da yawa, sai ku kara kuɗin filin, idan kuma shekarun ba su da yawa, sai ku rage kuɗin filin, gama ainihin abin da ake sayar maka shi ne yawan hatsin. Kada ku cuci juna, amma ku ji tsoron Allahnku. Ni ne Ubangiji Allahnku. “ ‘Ku bi farillaina, ku kuma yi hankali ga kiyaye dokokina, za ku kuwa zauna lafiya a ƙasar. Sa’an nan ƙasar za tă ba da amfaninta, za ku kuwa ci ku ƙoshi, ku kuma zauna lafiya. Mai yiwuwa ku ce, “Me za mu ci a shekara ta bakwai in ba mu yi shuki ko girbin hatsinmu ba?” Zan aika muku da irin albarka a shekara ta shida har da ƙasar za tă ba da amfani isashe na shekara uku. Yayinda kuke shuki a shekara ta takwas, za ku kasance da raguwa hatsi na shekarar da ta wuce, za ku kuma ci gaba da ci daga gare shi har girbin shekara ta tara yă shigo. “ ‘Kada a sayar da gona ɗinɗinɗin, gama ƙasar tawa ce, ku kuwa baƙi ne kawai, kuma ’yan haya nawa. Ko’ina a ƙasar da kuke da mallaka, dole ku tanadar da dama fansar ƙasar. “ ‘In ɗaya daga cikin mutanen ƙasarku ya talauta, ya kuma sayar da mallakarsa, sai danginsa na kusa yă je yă fanshi abin da mutumin ƙasarsa ya sayar. In mutumin ba shi da wanda zai fansa masa ita, shi kansa kuwa ya wadace, ya kuma sami isashen halin fansarta, sai yă lasafta yawan shekarun da aka yi tun da an sayar da filin. Kuɗin filin zai dangana ga yawan shekarun da suka rage kafin shekara hamsin ta murna da za tă zo; sa’an nan zai iya koma ga mallakarsa. Amma in bai sami halin sāke biyansa ba, abin nan da ya sayar zai ci gaba da zama mallakar mai sayan, sai Shekara ta Murna. Za a maido masa da ita a Shekara ta Murna, sa’an nan zai iya koma ga mallakarsa. “ ‘In mutum ya sayar da gida a birni mai katanga, yana da izini yă fanshe shi a ƙarshen shekara guda, bayan ya sayar da shi. In ba a fanshe shi a ƙarshen shekara ba, gidan da yake a birni mai katanga, zai zama mallakar na ɗinɗinɗin na mai sayan da kuma zuriyarsa. Ba za a mai da shi a Shekara ta Murna ba. Amma za a ɗauki gidaje a ƙauyuka marasa katanga kewaye da su daidai da gonaki. Za a iya fanshe su, a kuma mayar da su a Shekara ta Murna. “ ‘Kullum, Lawiyawa suna da izini su fanshi gidajensu a biranen Lawiyawa waɗanda suka mallaka. Saboda haka ana iya fansa mallakar Lawiyawa, wato, gidan da aka sayar a duk birnin da yake nasu, za a kuma mayar a Shekara ta Murna, gama gidaje a biranen Lawiyawa, mallakar Isra’ilawa ne. Amma kada a sayar da filayen kiwo na waɗannan birane; mallakarsu ce, ta ɗinɗinɗin. “ ‘In ɗaya daga ciki mutanen ƙasarku ya talauta, ba ya kuma iya tallafa wa kansa a cikinku, sai ku taimake shi kamar yadda za ku yi da baƙo a cikinku. Kada ku karɓi riba ta kowace iri daga gare shi, amma ku ji tsoron Allahnku, saboda mutumin ƙasarku yă ci gaba da zama a cikinku. Kada ku ba shi rancen kuɗi da ruwa, ko ku sayar masa abinci don samun riba. Ni ne Ubangiji Allahnku, wanda ya fitar da ku daga Masar, don in ba ku ƙasar Kan’ana in kuma zama Allahnku. “ ‘In ɗaya daga cikin mutanen ƙasarku ya talauta a cikinku, ya kuma sayar da kansa gare ku, kada ku sa yă yi kamar bawa. Amma a ɗauke shi a matsayin ma’aikacin da aka ɗauka aiki, ko mazaunan da ba na ɗinɗinɗin ba a cikinku, sai yă yi muku aiki sai Shekara ta Murna. Sa’an nan a sake shi da ’ya’yansa, yă kuma koma ga danginsa da mallakar kakanninsa. Gama Isra’ilawa bayina ne, waɗanda na saya daga Masar, kada a sayar da su a matsayin bayi. Kada ku gwada musu azaba, amma ku ji tsoron Allahnku. “ ‘Bayinku maza da mata, za su zo daga al’ummai da suke kewaye da ku, daga gare su za ku iya saya bayi. Za ku iya saya waɗansu mutanen da ba sa zama ɗinɗinɗin a cikinku, da kuma membobin danginsu da aka haifa a ƙasarku. Za ku iya ba da su ga ’ya’yanku a matsayin kayan gādo, za ku kuma iya mai da su bayi dukan rayuwarsu, amma kada ku yi mulki a bisa ’yan’uwanku Isra’ilawa da tsanani. “ ‘In baƙo, ko wani da yake zama ba na ɗinɗinɗin ba a cikinku, ya wadace, ɗaya daga cikin mutanen ƙasarku kuwa ya talauta, ya kuma sayar da kansa ga baƙon da yake zama a cikinku, ko memba na dangin baƙon, yana da izini samun fansa, bayan ya sayar da kansa. Ɗaya daga cikin danginsa zai iya fansarsa. Kawu ko yaron ɗan’uwan mahaifin wannan mutum, ko kuwa wani dangi a cikin zuriyarsa, zai iya fanshe shi. Ko kuma in ya azurta, zai iya fansar kansa. Da shi da mai sayansa, za su ƙirga lokaci daga shekarar da ya sayar da kansa har zuwa Shekara ta Murna. Farashin sakinsa zai dangana a kuɗin da ake biyan ma’aikacin da aka ɗauka aiki, na yawan shekarun ne. In shekaru sun ragu, dole yă biya don fansarsa da kuɗi mai yawa fiye da wanda aka saye shi. In shekarun sun rage kaɗan ne kafin Shekara ta Murna, sai yă yi lissafin wannan, yă kuma biya fansarsa daidai wa daida. Sai a yi da shi kamar ma’aikacin da aka ɗauka aiki, daga shekara zuwa shekara; dole ku tabbata mai shi bai mallake shi da tsanani ba. “ ‘Ko ma ba a fanshe shi a ɗaya daga cikin waɗannan hanyoyi ba, sai a sake shi da ’ya’yansa a Shekara ta Murna, gama Isra’ilawa nawa ne a matsayin bayi. Su bayina ne waɗanda na saya daga Masar. Ni ne Ubangiji Allahnku. “ ‘Kada ku yi gumaka, ko ku kafa siffa, ko al’amudi wa kanku, kada kuma ku sa sassaƙaƙƙun duwatsu a ƙasarku don ku rusuna musu. Ni ne Ubangiji Allahnku. “ ‘Ku kiyaye Asabbataina, ku kuma ba wa wuri mai tsarkina girma. Ni ne Ubangiji. “ ‘In kuka kiyaye farillaina, kuka yi biyayya da umarnaina, zan aika da ruwan sama a lokacinsa, ƙasa kuma za tă ba da hatsi, itatuwa kuma za su haihu ’ya’yansu. Masussukanku za su ci gaba har lokacin girbin inabi, girbin inabi kuma zai ci gaba har lokacin shuki, za ku kuma ci duk abincin da kuke so cikin salama a ƙasarku. “ ‘Zan ba ku salama a ƙasar, za ku kuwa kwanta, kuma babu wani da zai tsorata ku. Zan kori mugayen namun jeji daga ƙasar, takobi kuma ba zai ratsa cikin ƙasarku ba. Za ku kori abokan gābanku, za su kuwa fāɗi a kaifin takobi a gabanku. Mutanenku biyar za su kori mutum ɗari, mutanenku ɗari kuma za su kori mutane dubu goma, abokan gābanku kuma za su fāɗi a kaifin takobi a gabanku. “ ‘Zan dube ku da idon rahama, in kuma sa ku riɓaɓɓanya ku kuma ƙaru, zan kiyaye alkawarina da ku. Za ku ci gaba da cin girbin bara, har ku fitar da shi don ku sami wurin saboda sabo. Zan kafa wurin zamana a cikinku, ba zan kuma yi ƙyamarku ba. Zan yi tafiya a cikinki in kuma zama Allahnku, za ku kuwa zama mutanena. Ni ne Ubangiji Allahnku, wanda ya fitar da ku daga Masar don kada ku ƙara zama bayi ga Masarawa; na karya sandunan wahalarku, na kuma bar ku ku yi tafiya a sake. “ ‘Amma in za ku kasa kunne gare ni, ku kuma aikata dukan waɗannan umarnai, in kuka kuma ƙi farillaina, kuka yi ƙyamar dokokina, kuka kuma kāsa kiyaye umarnaina, har kuka karya alkawarina, to, zan yi muku wannan. Zan kawo muku abin bantsoro, cututtuka da zazzaɓin da zai lalatar da idonku, yă kuma sa ranku a wahala. Za ku shuka iri a banza, domin abokan gābanku ne za su ci. Zan yi gāba da ku har abokan gābanku su ci ku a yaƙi, su waɗanda suke ƙinku za su yi mulki a kanku, za ku gudu ba tare da wani yana korinku ba. “ ‘In bayan dukan wannan, ba ku saurare ni ba, zan hukunta ku saboda zunubanku har sau bakwai. Zan karya ikonku wanda kuke fariya da shi, in hana ruwan sama, ƙasa kuma tă zama kamar tagulla. Ƙarfinku zai ƙare a banza domin ƙasarku ba za tă ba da hatsi ba, balle itatuwan ƙasar su ba da ’ya’ya. “ ‘In kuka ci gaba da tayar mini, kuka ƙi ku saurare ni, zan ninka wahalolinku sau bakwai, yadda ya dace da zunubanku. Zan aika da mugayen namun jeji a kanku, za su kuwa kashe ’ya’yanku, su hallaka shanunku, su rage yawanku, ku zama kaɗan. Wannan zai sa a rasa mutane a kan hanyoyinku. “ ‘In duk da waɗannan abubuwa, ba ku yarda da gyaran da nake yi muku ba, kuka ci gaba da yin adawa da ni, zan yi adawa da ku, zan kuma aukar muku saboda zunubanku har sau bakwai. Zan kawo takobi a kanku don in yi ramuwa saboda karya alkawarin da kuka yi. Sa’ad da kuka janye zuwa cikin biranenku, zan aika da annoba a cikinku, za a kuwa ba da ku ga hannun abokan gāba. Sa’ad da na yanke abincinku, mata goma za su dafa abinci a murhu ɗaya, za su kuma rarraba abincin a ma’auni. Za ku ci amma ba za ku ƙoshi ba. “ ‘In duk da haka kuka ci gaba da ƙin saurare ni, kuka ci gaba da yin adawa da ni, cikin fushina, sai in yi adawa da ku, in kuma hukunta ku saboda zunubanku har sau bakwai. Za ku ci naman ’ya’yanku maza da na ’ya’yanku mata. Zan rurrushe dukan masujadanku, in yanke bagadanku na turare, in yi tarin gawawwakinku a kan gumakanku, zan kuma yi ƙyamarku. Zan mai da biranenku kango, in lalace wuraren tsarkinku, ba zan kuma shaƙi ƙanshi hadayunku ba. Zan mai da ƙasarku kango har abokan gābanku da suke zama a wurin su yi mamaki. Zan watsar da ku cikin al’ummai, in kuma ja takobina in kore ku. Ƙasarku za tă zama kufai, biranenku kuma su zama kango. Sa’an nan ƙasar za tă ji daɗin hutun shekarun Asabbacinta, a dukan lokutan da take kango, ku kuwa kuna a ƙasar abokan gābanku, sa’an nan ƙasar za tă huta ta ji daɗin asabbatanta. A dukan lokutan da take kango, ƙasar za tă sami hutun da ba tă samu a lokutan asabbatan da kuke zama a cikinta ba. “ ‘Ga waɗanda za su ragu kuwa, zan cika zukatansu da tsoro a ƙasashen abokan gābansu har motsin ganyen da iska ta hura zai sa su ruga da gudu. Za su yi gudu kamar suna gudu daga takobi ne, za su kuma fāɗi, ko da yake babu wanda yake korinsu. Za su yi karo da juna kamar waɗanda suke tsere wa takobi, ko da yake babu wanda yake korinsu. Ta haka ba za ku iya tsaya a gaban abokan gābanku ba. Za ku mutu a cikin al’ummai, ƙasar abokan gābanku za tă cinye ku. Sauranku da suka ragu za su lalace a ƙasashen abokan gābansu saboda zunubansu; da kuma saboda zunuban kakanninsu. “ ‘Amma in suka tuba daga zunubansu da zunuban kakanninsu, da cin amanar da suka yi mini, da kuma adawar da suka yi da ni, waɗanda suka sa na yi adawa da su har da na aika da su ƙasar abokan gābansu, sa’ad da suka ƙasƙantar da zukatansu marasa kaciya, suka kuma biya hukuncin zunubansu, zan tuna da alkawarina da Yaƙub, da alkawarina da Ishaku, da kuma alkawarina da Ibrahim, zan tuna da ƙasar. Gama za su gudu su bar ƙasar, ƙasar kuwa ta ji daɗin asabbatanta yayinda take kango muddin ba su ciki. Za su biya hukuncin zunubansu domin sun ƙi dokokina, suka kuma yi ƙyamar farillaina. Duk da haka, sa’ad da suke a ƙasar abokan gābansu, ba zan ƙi su, ko in yi ƙyamarsu, in hallaka su ƙaƙaf, har in karya alkawarina da su ba. Ni ne Ubangiji Allahnsu. Amma saboda su, zan tuna da alkawarin da na yi da kakanninsu, waɗanda na fitar da su daga Masar a idon al’ummai, don in zama Allahnsu. Ni ne Ubangiji.’ ” Waɗannan su ne farillai, da dokoki, da kuma ƙa’idodin da Ubangiji ya kafa a Dutsen Sinai, tsakaninsa da Isra’ilawa ta wurin Musa. Ubangiji ya ce wa Musa, “Ka yi magana da Isra’ilawa, ka ce musu, ‘Duk sa’ad da mutum ya yi rantsuwa ta musamman zai keɓe wani ga Ubangiji, ta wurin biyan kuɗaɗen fansa, ga yadda ma’aunin biyan zai kasance, mutum mai shekara tsakanin ashirin da sittin, za a biya azurfa hamsin. Mace kuma za a biya azurfa talatin. Saurayi mai shekara tsakanin biyar da ashirin, za a biya azurfa ashirin, yarinya kuma azurfa goma. Yaro mai shekara tsakanin wata ɗaya da shekara biyar, za a biya azurfa biyar, ’yar yarinya kuma azurfa uku. Namijin da ya fi shekara sittin, za a biya azurfa goma sha biyar, mace kuma azurfa goma. In mai alkawarin matalauci ne da ba zai iya biyan ƙayyadadden abin da aka tsara ba, sai yă tafi wurin firist, shi firist kuma yă duba yadda mutumin da ya yi alkawarin zai iya biya. Sa’an nan mutumin zai biya abin da firist ya faɗa. “ ‘In abin da ya yi alkawarin yardajje ne a matsayin hadaya ga Ubangiji, wannan dabbar da aka bayar ga Ubangiji, za tă zama mai tsarki. Kada yă yi musayarta ko yă yi musaya mai kyau da marar kyau, ko marar kyau da mai kyau; in lalle ne yă yi musayar dabbar da wata, to, duk wannan da kuma wanda zai yi musayar da ita za su zama masu tsarki. In abin da ya yi alkawari dabba ce marar tsarki, wadda ba yardajje ba ce, a matsayin hadaya ga Ubangiji, dole a kai dabbar wa firist, wanda zai yanke hukunci dacewarta, ko mai kyau ce, ko marar kyau. Duk darajar da firist ya kimanta, haka za tă zama. In mai shi yana so yă fanshi dabbar, dole yă ƙara kashi ɗaya bisa biyar na darajarta. “ ‘In mutum ya miƙa gidansa a matsayin wani abu mai tsarki ga Ubangiji, firist zai daidaita dacewar ko mai kyau ne, ko marar kyau. Duk darajar da firist ya kimanta, haka za tă zama. In mutumin da ya keɓe gidansa ya fanshe shi, dole yă ƙara kashi ɗaya bisa biyar na darajar, gidan kuma zai zama nasa. “ ‘In wani ya keɓe wa Ubangiji wani sashe daga cikin gonarsa ta gādo, sai yă kimanta kuɗin gonar daidai da yawan irin da za a iya shuka a gonar. Za a kimanta kuɗin a kan shekel hamsin na irin sha’ir. In ya keɓe gonarsa a Shekara ta Murna, darajar da aka kimanta za tă zauna. Amma in ya keɓe gonar bayan Shekara ta Murnan, firist zai kimanta darajar bisa ga yawan shekarun da suka rage har zuwa Shekara ta Murna mai zuwa, sai a rage darajar da aka kimanta a kanta. In mutumin da ya keɓe gonar, yana so yă fanshe ta, to, dole yă ƙara kashi ɗaya bisa biyar na darajarta, gonar kuwa tă zama nasa. In kuma bai fanshe gonar ba, ko kuwa in ya sayar wa wani dabam, ba za a taɓa fanshe ta ba. Sa’ad da aka saki gonar a Shekara ta Murna, za tă zama mai tsarki, a matsayin gonar da aka miƙa ga Ubangiji, za tă zama mallakar firistoci. “ ‘In mutum ya keɓe gonar da ya saya, wadda take ba sashe na gonar iyali ba, ga Ubangiji, firist zai kimanta darajarta har Shekara ta Murna, dole kuma mutumin yă biya darajarta a ranar, a matsayin wani abu mai tsarki ga Ubangiji. A Shekara ta Murna ɗin, gonar za tă dawo ga mutumin da aka saye ta daga wurinsa, wanda yake mai gonar. A kimanta kowace daraja bisa ga ma’aunin shekel na tsattsarkan wuri, gera ashirin ga shekel. “ ‘Ba wani da zai iya keɓe ɗan farin dabba, da yake ɗan fari ya riga ya zama na Ubangiji, ko na saniya, ko na tunkiya, na Ubangiji ne. In tana cikin dabbobin da suke marasa tsarki, zai iya saye ta a darajar da aka kimanta, yă ƙara da kashi ɗaya bisa biyar na darajarta. In bai fanshe ta ba, sai a sayar da ita a darajar da aka kimanta. “ ‘Amma babu abin da mutum ya mallaka, ya kuma keɓe ga Ubangiji, ko mutum ne, ko dabba, ko ganar iyali da za a sayar, ko a fansa; kome da aka keɓe a wannan hanya, mafi tsarki ne ga Ubangiji. “ ‘Babu wani da aka keɓe don hallaka da za a fansa; dole a kashe shi. “ ‘Ushirin kome daga gona, ko hatsi daga ƙasa, ko ’ya’yan itatuwa daga itatuwa, na Ubangiji ne, mai tsarki ne ga Ubangiji. In mutum ya fanshi wani zakansa, dole yă ƙara kashi ɗaya bisa biyar na darajar. Ushirin gaba ɗaya na garken shanu, da na tumaki, kowane kashi ɗaya bisa goma na dabbar da ta wuce ƙarƙashin sandan mai kiwo, za tă zama mai tsarki ga Ubangiji. Kada kuwa ya zaɓa mai kyau daga marar kyau, ko yă yi musaya. In ya yi musaya kuwa, dabbar da wadda ya musayar, za su zama masu tsarki, ba kuma za a fanshe su ba.’ ” Waɗannan su ne dokokin da Ubangiji ya ba wa Musa a Dutsen Sinai saboda Isra’ilawa. Ubangiji ya yi magana da Musa a Tentin Sujada a cikin Hamadar Sinai, a rana ta fari na watan biyu a shekara ta biyu, bayan Isra’ilawa suka fito Masar ya ce, “Ka yi ƙidayan dukan al’umman Isra’ilawa bisa ga iyalansu da kabilarsu, ka rubuta kowa da sunansa bi da bi. Da kai da Haruna za ku lissafta dukan mazan Isra’ila bisa ga sashensu, waɗanda suka kai shekaru ashirin ko fiye, da za su iya shiga soja. Mutum ɗaya daga kowace kabila wanda yake shugaban danginsa, zai taimake ku. “Ga sunayen da za su taimake ku. “Daga kabilar Ruben, Elizur ɗan Shedeyur; daga kabilar Simeyon, Shelumiyel ɗan Zurishaddai; daga kabilar Yahuda, Nashon ɗan Amminadab; daga kabilar Issakar, Netanel ɗan Zuwar; daga kabilar Zebulun, Eliyab ɗan Helon; daga kabilar ’ya’yan Yusuf, daga Efraim, Elishama ɗan Ammihud; daga Manasse, Gamaliyel ɗan Fedazur; daga kabilar Benyamin, Abidan ɗan Gideyoni; daga kabilar Dan, Ahiyezer ɗan Ammishaddai; daga kabilar Asher, Fagiyel ɗan Okran; daga kabilar Gad, Eliyasaf ɗan Deyuwel; daga kabilar Naftali, Ahira ɗan Enan.” Waɗannan su ne mutanen da aka naɗa daga cikin jama’a, shugabannin asalin kabilu. Su ne kuma shugabannin dangogin Isra’ila. Sai Musa da Haruna suka ɗauki sunayen mutanen nan da aka ba su, suka kira dukan al’umma wuri ɗaya a rana ta fari ga wata na biyu. Aka kuwa rubuta mutanen bisa ga asalin kabilansu da iyalansu. Aka kuma rubuta sunayen maza ɗaya-ɗaya da suka kai shekaru ashirin ko fiye, yadda Ubangiji ya umarci Musa. Da haka ya ƙidaya su a Hamadar Sinai. Daga zuriyar Ruben ɗan fari na Isra’ila. Aka rubuta sunayen dukan maza ɗaya-ɗaya da suka kai shekara ashirin ko fiye da suka isa shiga soja, bisa ga iyalansu da kabilarsu da take a rubuce. Jimillar maza daga mutanen Ruben 46,500 ne. Daga zuriyar Simeyon. Aka rubuta sunayen dukan maza ɗaya-ɗaya da suka kai shekara ashirin ko fiye da suka isa shiga soja, bisa ga iyalansu da kabilarsu da take a rubuce. Jimillar maza daga mutanen Simeyon 59,300 ne. Daga zuriyar Gad. Aka rubuta sunayen dukan maza ɗaya-ɗaya da suka kai shekara ashirin ko fiye da suka isa shiga soja, bisa ga iyalansu da kabilarsu da take a rubuce. Jimillar maza daga mutanen Gad 45,650 ne. Daga zuriyar Yahuda. Aka rubuta sunayen dukan maza ɗaya-ɗaya da suka kai shekara ashirin ko fiye da suka isa shiga soja, bisa ga iyalansu da kabilarsu da take a rubuce. Jimillar maza daga mutanen Yahuda 74,600 ne. Daga zuriyar Issakar. Aka rubuta sunayen dukan maza ɗaya-ɗaya da suka kai shekara ashirin ko fiye da suka isa shiga soja, bisa ga iyalansu da kabilarsu da take a rubuce. Jimillar maza daga mutanen Issakar 54,400 ne. Daga zuriyar Zebulun. Aka rubuta sunayen dukan maza ɗaya-ɗaya da suka kai shekara ashirin ko fiye da suka isa shiga soja, bisa ga iyalansu da kabilarsu da take a rubuce. Jimillar maza daga mutanen Zebulun 57,400 ne. Daga ’ya’yan Yusuf. Daga zuriyar Efraim. Aka rubuta sunayen dukan maza ɗaya-ɗaya da suka kai shekara ashirin ko fiye da suka isa shiga soja, bisa ga iyalansu da kabilarsu da take a rubuce. Jimillar maza daga mutanen Efraim 40,500 ne. Daga zuriyar Manasse. Aka rubuta sunayen dukan maza ɗaya-ɗaya da suka kai shekara ashirin ko fiye da suka isa shiga soja, bisa ga iyalansu da kabilarsu da take a rubuce. Jimillar maza daga mutanen Manasse 32,200 ne. Daga zuriyar Benyamin. Aka rubuta sunayen dukan maza ɗaya-ɗaya da suka kai shekara ashirin ko fiye da suka isa shiga soja, bisa ga iyalansu da kabilarsu da take a rubuce. Jimillar maza daga mutanen Benyamin 35,400 ne. Daga zuriyar Dan. Aka rubuta sunayen dukan maza ɗaya-ɗaya da suka kai shekara ashirin ko fiye da suka isa shiga soja, bisa ga iyalansu da kabilarsu da take a rubuce. Jimillar maza daga mutanen Dan 62,700 ne. Daga zuriyar Asher. Aka rubuta sunayen dukan maza ɗaya-ɗaya da suka kai shekara ashirin ko fiye da suka isa shiga soja, bisa ga iyalansu da kabilarsu da take a rubuce. Jimillar maza daga mutanen Asher 41,500 ne. Daga zuriyar Naftali. Aka rubuta sunayen dukan maza ɗaya-ɗaya da suka kai shekara ashirin ko fiye da suka isa shiga soja, bisa ga iyalansu da kabilarsu da take a rubuce. Jimillar maza daga mutanen Naftali kuwa 53,400 ne. Waɗannan su ne mazan da Musa da Haruna, tare da shugabanni goma sha biyun nan na Isra’ila suka ƙidaya, kowa a madadin iyalinsa. Dukan Isra’ilawan da suka kai shekara ashirin ko fiye da suka isa shiga soja, an ƙidaya su bisa ga iyalansu. Jimillar kuwa ita ce mutum 603,550. Ba a dai ƙidaya zuriyar Lawi tare da saura kabilan ba. Ubangiji ya riga ya gaya wa Musa cewa, “Ka tabbatar ba ka ƙidaya mutanen Lawi ko kuma ka haɗe su tare a ƙidayan sauran Isra’ilawa ba. A maimakon haka sai ka naɗa Lawiyawa su lura da tabanakul Shaida, wato, kan dukan kayayyaki da kuma kome da yake na wuri mai tsarki. Za su ɗauko tabanakul da dukan kayayyakinsa; za su lura da shi, su kasance kewaye da shi. Duk sa’ad da za a gusar da tabanakul, Lawiyawa ne za su saukar da shi; kuma duk sa’ad da za a kafa shi, Lawiyawa ne za su yi haka. Duk wani dabam da ya je kusa da shi za a kashe shi. Sauran Isra’ilawa za su zauna ƙungiya-ƙungiya, kowane mutum a ƙungiyarsa daidai bisa ga ƙa’idarsa. Amma Lawiyawa za su kafa sansaninsu kewaye da tabanakul na Shaida. Don kada fushi yă fāɗo a kan al’ummar Isra’ilawa. Hakkin Lawiyawa ne su kula da tabanakul na Shaida.” Isra’ilawa suka yi duk waɗannan kamar dai yadda Ubangiji ya umarci Musa. Ubangiji ya ce wa Musa da Haruna, “Duk sa’ad da Isra’ilawa suka yi sansani, kowane mutum zai sauka a inda tutar ƙungiyar kabilarsa take. Sansanin zai kasance a kewaye da Tentin Sujada.” Kabilar Yahuda za su yi sansani bisa ga ƙa’idarsu a gabas, wajen fitowar rana. Shugaban mutanen Yahuda kuwa shi ne Nashon ɗan Amminadab. Yawan mutanen sashensa 74,600 ne. Kabilar Issakar za su yi sansani biye da su. Shugabansu shi ne Netanel ɗan Zuwar. Yawan mutanen sashensa 54,400 ne. Kabilar Zebulun za su yi sansani biye da su. Shugabansu shi ne Eliyab ɗan Helon. Yawan mutanen sashensa 57,400 ne. Dukan mazan da aka ba su aiki a sansanin Yahuda bisa ga sashensu sun kai 186,400. Su ne za su ja gaba. A kudu, a nan ne sashe sansanin mutanen Ruben a ƙarƙashin ƙa’idarsu, za su yi sansani. Shugaban mutanen Ruben shi ne Elizur ɗan Shedeyur. Yawan mutanen sashensa 46,500 ne. Kabilar Simeyon za su yi sansani biye da su. Shugaban mutanensa shi ne Shelumiyel ɗan Zurishaddai. Yawan mutanen sashensa 59,300 ne. Kabilar Gad za su zama na biye. Shugaban mutanensa shi ne Eliyasaf ɗan Reyuwel. Yawan mutanen sashensa 45,650 ne. Dukan mazan da aka ba su aiki a sansanin Ruben, bisa ga sashensu sun kai 151,450. Su ne za su zama na biyu in za a tashi. Sa’an nan Lawiyawa ɗauke da Tentin Sujada za su kasance a tsakiyar sansani sa’ad da aka tashi tafiya. Za su kama hanya kamar yadda aka dokace su su zauna a sansani, kowa a wurinsa a ƙarƙashin ƙa’idarsu. Ta wajen yamma kuma sashen Efraim za su yi sansani a ƙarƙashin ƙa’idarsu. Shugaban mutanensa, shi ne Elishama ɗan Ammihud. Yawan mutanen sashensa 40,500 ne. Kabilar Manasse ce za tă zama ta biye. Shugabansu shi ne Gamaliyel ɗan Fedazur. Yawan mutanen sashensa 32,200 ne. Na biye da su su ne mutanen Benyamin. Shugaban mutanensu kuwa Abidan ɗan Gideyoni. Yawan mutanen sashensa 35,400 ne. Dukan mazan da aka ba su aiki a sansanin Efraim, bisa ga sashensu su kai 108,100 ne. Su ne za su zama na uku sa’ad da za a tashi. A arewa za a sami sashen sansanin Dan, a ƙarƙashin ƙa’idarsu. Shugabansu shi ne Ahiyezer ɗan Ammishaddai. Yawan mutanen sashensa 62,700 ne. Kabilar Asher ce za tă zama ta biye. Shugabansu shi ne Fagiyel ɗan Okran. Yawan mutanen sashensa 41,500 ne. Kabilar Naftali za su zama na biye da su. Shugaban mutanen kuwa shi ne Ahira ɗan Enan. Yawan mutanen sashensa 53,400 ne Dukan mazan da aka ba su aiki a sansanin Efraim, bisa ga sashensu su kai 157,600. Su ne za su zama na ƙarshe, ƙarƙashin ƙa’idarsu. Waɗannan su ne Isra’ilawan da aka a ƙidaya bisa ga iyalansu. Dukansu da suke a sansani, mutane 603,550 ne. Ba a dai ƙidaya Lawiyawa tare da sauran Isra’ilawa ba yadda Ubangiji ya umarci Musa. Saboda haka Isra’ilawa suka yi duk ko mene ne da Ubangiji ya umarci Musa. Ta haka ne suka yi sansani a ƙarƙashin ƙa’idarsu kowanne tare da kabilarsa da danginsa. Waɗannan su ne zuriyar Haruna da Musa a lokacin da Ubangiji ya yi magana da Musa a kan Dutsen Sinai. Sunayen ’ya’yan Haruna su ne, Nadab ɗan fari, da Abihu, da Eleyazar da Itamar. Waɗannan su ne sunayen ’ya’yan Haruna, shafaffun firistocin da aka naɗa domin su yi aiki firist. Amma Nadab da Abihu suka fāɗi suka mutu a gaban Ubangiji a Hamadar Sinai a sa’ad da suka ƙona turare da haramtacciyar wuta a gabansa. Ba su kuwa da ’ya’ya; saboda haka Eleyazar da Itamar kaɗai suka yi aiki firist a zamanin mahaifinsu Haruna. Ubangiji ya ce wa Musa, “Ka kawo mutanen Lawi, ka kuma gabatar da su ga Haruna firist, don su taya shi aiki. Za su yi wa Haruna da dukan al’umma aikace-aikace a Tentin Sujada, ta wurin yin aikin tabanakul. Za su lura da dukan kayayyakin Tentin Sujada, suna cika hakkin Isra’ilawa ta wurin yin aiki a tabanakul. Ka ba da Lawiyawa ga Haruna da ’ya’yansa; su ne za su zama Isra’ilawan da za a ba da su ɗungum gare shi. Ka naɗa Haruna da ’ya’yansa su yi aiki firistoci; duk wanda ya yi shisshigi a wuri mai tsarki kuwa dole a kashe shi.” Ubangiji ya kuma ce wa Musa, “Ga shi na ɗauki Lawiyawa daga cikin Isra’ilawa a maimakon ɗan fari na kowace mace a Isra’ila. Lawiyawa nawa ne, gama duk ’ya’yan fari nawa ne. Lokacin da karkashe duk ’ya’yan fari a Masar, na keɓe wa kaina kowane ɗan fari a Isra’ila, ko mutum, ko dabba. Za su zama nawa. Ni ne Ubangiji.” Ubangiji ya yi magana da Musa a Hamadar Sinai ya ce, “Ka ƙidaya Lawiyawa bisa ga iyalansu da kabilarsu. Ka ƙidaya kowane ɗan jinjiri mai wata ɗaya ko fiye.” Saboda haka Musa ya ƙidaya su duka, kamar yadda maganar Ubangiji ta umarta. Ga sunayen ’ya’yan Lawi, Gershon, Kohat da Merari. Ga sunayen mutanen Gershon, Libni, da Shimeyi Sunayen mutanen Kohat kuwa su ne, Amram, Izhar, Hebron da Uzziyel. Dangin Merari su ne. Mali da Mushi. Ga kabilan Lawiyawa bisa ga iyalansu. A wajen Gershonawa, kabilarsa su ne Libniyawa, da Shimeyiyawa; waɗannan su ne mutanen Gershom. Jimillar dukan jarirai maza daga wata ɗaya zuwa gaba da haihuwa su kai 7,500. Kabilar Gershonawa za su yi sansani ta fuskar yamma, a bayan tabanakul. Eliyasaf ɗan Layel shi ne shugaban iyalan Gershonawa. A Tentin Sujada, Gershonawa su ne za su lura da mazauni da tabanakul da kuma tentin, abubuwan rufensa, labule a ƙofar Tentin Sujada, da labulen filin da yake kewaye da tabanakul da kuma bagade, da igiyoyi, da kuma kowane abin da ya danganci aikinsu. Kabilar Kohat su ne, Amramawa da Izharawa da Hebronawa da Uzziyelawa; waɗannan su ne kabilar Kohatawa. Jimillar dukan jarirai maza daga wata ɗaya ko fiye, 8,600 ne. Kohatawa ne suke lura da wuri mai tsarki. Kohatawa za su yi sansani a kudu da tabanakul. Shugaban kabilar Kohatawa shi ne Elizafan ɗan Uzziyel. Su ne da hakkin kula da akwatin alkawari, tebur, wurin ajiye fitila, bagade, kayayyakin wuri mai tsarki da ake amfani da su a sujada, labule, da kuma kome da ya danganci aikinsu. Babban shugaban Lawiyawa shi ne Eleyazar ɗan Haruna, firist. An naɗa shi a kan waɗanda suke kula da wuri mai tsarki. Kabilar Merari su ne Maliyawa da Mushiyawa; waɗannan su ne kabilar Merari. Jimillar dukan jarirai maza daga wata ɗaya ko fiye, 6,200 ne. Shugaban iyalan Merari shi ne Zuriyel ɗan Abihayil. Za su yi sansani arewa da tabanakul. Kabilar Merari ne aka sa su lura da katakan tabanakul, sandunanta, dogayen sandunanta, tarukanta, dukan kayan aiki da kowane abin da ya danganci aikinsu, da ginshiƙai kewaye da filin tare da rammuka da turaku da igiyoyinsu. Musa da Haruna da ’ya’yansu za su yi sansani gabas da tabanakul, wajen fitowar rana; a gaban Tentin Sujada. Su ne da hakkin lura da wuri mai tsarki a madadin Isra’ilawa. Duk wani wanda ba ya wannan aiki, ya kuma kusaci wuri mai tsarki, za a kashe shi. Jimillar Lawiyawan da Musa da Haruna suka ƙidaya bisa ga umarnin Ubangiji bisa ga danginsu, haɗe da kowane jariri daga wata ɗaya ko fiye, 22,000 ne. Sai Ubangiji ya ce wa Musa, “Ƙidaya dukan ’ya’yan fari na Isra’ilawa maza daga wata ɗaya da kuma fiye ka kuma rubuta sunayensu. Ka ɗauko mini Lawiyawa a maimakon dukan ’ya’yan fari na Isra’ilawa, haka ma na dabbobi na Lawiyawa, a maimakon ’ya’yan fari na dabbobin Isra’ilawa. Ni ne Ubangiji.” Haka Musa ya ƙidaya ’ya’yan fari na Isra’ilawa, yadda Ubangiji ya umarce shi. Jimillar ’ya’yan fari maza daga wata ɗaya da kuma fiye, da aka rubuta bisa ga sunayensu, 22,273 ne. Sai Ubangiji ya kuma yi magana da Musa ya ce, “Ka ɗauki Lawiyawa a maimakon dukan ’ya’yan fari na Isra’ila, dabbobin Lawiyawa kuma a maimakon dabbobinsu. Lawiyawa za su zama nawa. Ni ne Ubangiji. Don a fanshi ’ya’yan fari 273 na Isra’ilawa da suka fi Lawiyawa yawa, ka karɓi shekel biyar domin kowannensu, bisa ga ma’aunin shekel na tsattsarkan wuri, wanda yake da nauyin gera ashirin. Ka ba wa Haruna da ’ya’yansa kuɗin fansar da ya haura kai na ’ya’yan farin Isra’ilawa.” Haka, Musa ya karɓi kuɗin fansar waɗanda suka haura yawan Lawiyawa. Daga ’ya’yan fari na Isra’ilawa, ya karɓi azurfa masu nauyin shekel 1,365, bisa ga ma’aunin shekel na tsattsarkan wuri. Sa’an nan Musa ya ba da kuɗin fansar ga Haruna da ’ya’yansa, yadda maganar Ubangiji ta umarce shi. Ubangiji ya ce wa Musa da Haruna, “Ku yi ƙidaya Kohatawa daga Lawiyawa, bisa ga kabilarsu da iyalansu. Ku ƙidaya dukan maza daga shekara talatin zuwa hamsin da suka zo domin aiki a Tentin Sujada. “Ga aikin Kohatawa a Tentin Sujada, kulawa da kayayyaki mafi tsarki. Lokacin da za a tashi daga sansani, Haruna da ’ya’yansa za su shiga ciki su kunce labulen kāriya, su rufe Akwatin Alkawari da shi. Sa’an nan su rufe shi da fatun shanun teku, su shimfiɗa zane mai ruwan shuɗi a bisansa, su sa masa sandunansa. “A bisa teburin Burodin Ajiyewa, za su shimfiɗa zane mai ruwan shuɗi, a kansa kuma su sa farantai, kwanoni da manyan kwanoni, da tuluna don hadayun sha; da burodin da zai ci gaba da kasancewa a kansa. A bisa waɗannan za su shimfiɗa jan zane, su rufe su da fatun shanun teku, su kuma zura masa sandunansa. “Za su ɗauki zane mai ruwan shuɗi su rufe wurin ajiye fitilan da yake don fitilu, tare da fitilunsa, lagwaninsa da farantansa, da dukan tulunansa don man amfaninsu. Sa’an nan su naɗe shi da kuma dukan kayayyakinsa a cikin fatar shanun teku, su sa shi a kan sandan ɗaukarsa. “A kan bagaden zinariya, za su shimfiɗa zane mai ruwan shuɗi, su kuma rufe shi da fatar shanun teku, sai a zura masa sandunansa. “Za su ɗauki dukan kayayyakin da ake amfani da su a wuri mai tsarki, su nannaɗe su da zane mai ruwan shuɗi, su rufe shi da fatar shanun teku, sa’an nan a sa su a kan sandan ɗaukarsa. “Za su kwashe tokar da take a bagaden tagulla, su shimfiɗa zane mai ruwan shuɗi a bisansa. Sa’an nan su sa a kansa dukan kayayyakin da aka yi amfani da su a bagaden, haɗe da farantai don wuta, cokula masu yatsu don nama, manyan cokula, da darunan yayyafawa. A kansa za su shimfiɗa murfi na fatun shanun teku, su zura sandunan ɗaukarsa. “Bayan Haruna da ’ya’yansa suka gama rufe kayayyaki masu tsarki da dukan abubuwa masu tsarki, sa’ad da kuma aka shirya tashi daga sansani, sai Kohatawa su zo gaba, su ɗauka. Amma kada su taɓa abubuwa masu tsarki, don kada su mutu. Kohatawa za su ɗauki abubuwan da suke cikin Tentin Sujada. “Eleyazar ɗan Haruna firist zai lura da man fitila da turare da hadaya ta gari na kullum da kuma keɓaɓɓen mai. Shi ne zai lura da dukan tabanakul da duk abin da yake cikinsa da kuma kayayyaki da abubuwan masu tsarki.” Ubangiji ya ce wa Musa da Haruna, “Ku tabbata cewa ba a kawar da zuriyar Kohatawa daga Lawiyawa ba. Saboda su rayu, kada su mutu sa’ad da suka zo kusa da abubuwa mafi tsarki, a yi musu wannan, wato, Haruna da ’ya’yansa za su shiga wuri mai tsarki su ba wa kowane mutum aikinsa da kuma abin da zai ɗauka. Amma kada Kohatawa su shiga don su dubi abubuwa masu tsarki, ko na ɗan ƙanƙanin lokaci, in ba haka ba za su mutu.” Ubangiji ya ce wa Musa, “Ka ƙidaya mutanen Gershon bisa ga iyalansu da kabilarsu. Ka ƙidaya maza masu shekara talatin zuwa hamsin waɗanda sukan zo hidimar aiki a Tentin Sujada. “Ga aikin kabilar Gershonawa yayinda suke aiki, suke kuma ɗaukar kaya. Za su ɗauki labulen tabanakul, Tentin Sujada, kayan da za a rufe shi, da kuma kayan da za a rufe shi daga waje na fatun rufuwa na shanun teku, labulen ƙofar Tentin Sujada, labulen filin da yake kewaye da tabanakul da bagade, labulen ƙofa, igiyoyi da kuma dukan abubuwan da ake amfani da su wajen hidima. Geshonawa za su yi dukan abin da ya kamata a yi da waɗannan abubuwa. Dukan hidimominsu, ko na ɗauko, ko kuma na yin wani aiki, za a yi su ne bisa ga umarnin Haruna da ’ya’yansa. Za ka ba su dukan kayan da za su ɗauka a matsayin hakkinsu. Wannan shi ne hidimar da kabilar Gershonawa za su yi a Tentin Sujada. Ayyukansu za su kasance bisa ga umarnin Itamar ɗan Haruna firist. “Ka ƙidaya kabilar Merari bisa ga kabilarsu da iyalansu. Ka ƙidaya maza daga masu shekara talatin zuwa hamsin waɗanda sukan zo hidimar aiki a Tentin Sujada. Ga aikinsu sa’ad da suke hidima a Tentin Sujada, za su ɗauki katakan tabanakul, sandunansa da dogayen sandunansa, da rammukansa, har ma da dogayen sandunan kewayen filin da rammukansu, turakun tenti, igiyoyi, da dukan kayayyaki, da kuma dukan abubuwan da suke dangane da amfaninsu. Ka ba wa kowane mutum ayyuka na musamman da zai yi. Wannan ce hidimar da mutanen Merari za su yi a aikin Tentin Sujada, a ƙarƙashin jagorancin Itamar ɗan Haruna, firist.” Musa, Haruna da kuma shugabannin jama’a, suka ƙidaya Kohatawa ta kabilarsu da kuma iyalansu. Dukan maza daga shekara talatin zuwa hamsin waɗanda sukan zo hidimar aiki a Tentin Sujada, da aka ƙidaya, kabila-kabila, su 2,750 ne. Jimillar dukan waɗanda suke na kabilan Kohatawa, waɗanda suka yi hidimar aiki a Tentin Sujada ke nan. Musa da Haruna sun ƙidaya su bisa ga umarnin Ubangiji. Aka ƙidaya mazan Gershonawa ta kabilansu da kuma iyalansu. Dukan maza daga shekara talatin zuwa hamsin waɗanda sukan zo hidimar aiki a Tentin Sujada, da aka ƙidaya kabila-kabila da kuma iyali-iyali, su 2,630 ne. Jimillar waɗanda suke na kabilar Gershonawa ke nan, waɗanda suka yi hidimar aiki a Tentin Sujada. Musa da Haruna sun ƙidaya su bisa ga umarnin Ubangiji. Aka ƙidaya mazan Merari ta kabilarsu da kuma iyalansu. Dukan maza daga shekara talatin zuwa hamsin waɗanda sukan zo hidimar aiki a Tentin Sujada, da aka ƙidaya kabila-kabila, su 3,200 ne. Jimillar waɗanda suke na kabilar Merari ke nan. Musa da Haruna suka ƙidaya su bisa ga umarnin Ubangiji. Saboda haka, Musa, Haruna da shugabannin Isra’ila, suka ƙidaya dukan Lawiyawa kabila-kabila da kuma iyali-iyali. Dukan maza daga shekara talatin zuwa hamsin waɗanda sukan zo hidimar aiki da kuma ɗaukar Tentin Sujada jimillarsu ta kai 8,580. Bisa ga umarnin Ubangiji ta wurin Musa, aka ba kowa aikinsa, aka kuma faɗa musu abin da za su ɗauka. Ta haka aka ƙidaya su, yadda Ubangiji ya umarci Musa. Ubangiji ya ce wa Musa, “Ka umarci Isra’ilawa su kori duk wanda yake da ciwon fatan jiki, ko mai ɗiga na kowane iri, ko wanda ya ƙazantu ta wurin taɓa gawa, daga cikin sansani. Ka kori maza da mata ma; ka kai su bayan sansani domin kada su ƙazantar da sansani inda nake zama a cikinsu.” Isra’ilawa suka yi haka; suka kore su daga sansanin. Suka aikata yadda dai Ubangiji ya umarci Musa. Ubangiji ya ce wa Musa, “Gaya wa Isra’ilawa, ‘Sa’ad da namiji ko mace ya yi wa ɗan’uwansa laifi ta kowace hanya, ta yin haka, ya yi rashin aminci ga Ubangiji, mutumin kuwa ya yi laifi ke nan kuma dole yă furta zunubin da ya yi. Dole yă yi biya cikakkiyar diyya saboda laifinsa, yă ƙara kashi ɗaya bisa biyar a kai, yă kuma bayar da shi duka ga wanda ya yi wa laifin. Amma in mutumin da aka yi wa laifin ba shi da ɗan’uwa na kusa da za a biya diyya saboda laifin, sai diyyar tă zama ta Ubangiji, dole kuma a ba wa firist, haɗe da ragon da za a yi kafara da shi. Dukan tsarkakakkun abubuwan da Isra’ilawa suka kawo wa firist za su zama nasa. Kowace tsarkakakkiyar kyauta da mutum ya kawo nasa ne, sai dai abin da ya ba wa firist, zai zama na firist.’ ” Sai Ubangiji ya ce wa Musa, “Yi magana da Isra’ilawa, ka ce musu, ‘In matar wani ta kauce, ta kuma yi rashin aminci gare shi ta wurin kwana da wani dabam, wannan kuwa ya kasance a ɓoye ga mijinta, rashin tsarkinta kuwa bai tonu ba (da yake babu shaida, ba a kuma kama ta tana yi ba), in kuma kishi ya sha kan mijinta kuma tana da ƙazanta, ko kuwa idan yana kishi yana kuma zatonta ko ma ba ta da ƙazanta mijin zai kai matansa a gaban firist, yă kuma kawo hadayar abubuwan da ake bukata; abubuwa kamar, garin sha’ir garwa ɗaya, amma kada yă zuba mai a kan garin sha’ir, kada kuma yă sa turaren wuta a kansa, domin hadaya ce ta miji mai tuhumar matarsa da aka kawo domin gaskiya tă fito fili. “ ‘Firist zai kawo ta, yă sa tă tsaya a gaban Ubangiji. Sa’an nan zai ɗebi ruwa mai tsarki a tulun laka, yă zuba ƙurar da ya ɗebo daga daɓen tabanakul a cikin ruwan. Bayan da firist ya sa matan ta tsaya a gaban Ubangiji, sai yă kunce gashin kanta, yă kuma sa hadaya ta gari don tunawa a hannuwanta, hadayar gari ce ta kishi, yayinda shi kansa zai riƙe ruwa mai ɗaci, mai jawo la’ana. Sa’an nan firist zai sa tă yi rantsuwa, yă kuma ce mata, “In ba wani mutumin da ya kwana da ke kuma ba ki kauce kin ƙazantar da kanki yayinda kike auren mijinki ba, kada wannan ruwa mai ɗaci, mai jawo la’ana, yă cuce ki. Amma in kin kauce yayinda kike auren mijinki, kika kuma ƙazantar da kanki ta wurin kwana da wani dabam da ba mijinki ba,” (a nan firist zai sa macen a ƙarƙashin la’anar rantsuwa cewa) “bari Ubangiji yă sa mutanenki su la’ance ki, su kuma yi Allah wadai da ke, sa’ad da Ubangiji ya sa cinyarki ta shanye, cikinki kuma ya kumbura. Bari wannan ruwa mai jawo la’ana, yă shiga jikinki saboda cikinki yă kumbura, cinyarki kuma yă shanye.” “ ‘Sai macen tă ce, “Amin. Bari yă zama haka.” “ ‘Firist zai rubuta waɗannan la’anoni a littafi, sa’an nan yă wanke su cikin ruwa mai ɗaci. Sai yă sa macen tă sha ruwa mai ɗaci, mai jawo la’ana, wannan ruwa kuwa zai shiga cikinta yă kawo mata wahala mai zafi. Firist zai karɓi hadaya ta gari don kishi daga hannuwanta, yă kaɗa shi a gaban Ubangiji sa’an nan yă kawo a bagade. Sa’an nan firist zai ɗiba hatsi na hadaya cike da hannunsa don hadayar tunawa, yă kuma ƙone a bagade; bayan haka sai yă sa macen tă sha ruwan. In ta ƙazantar da kanta ta kuma ci amanar mijinta, to, yayinda aka sa tă sha ruwa mai jawo la’ana, ruwan zai shiga cikinta, yă jawo mata wahala mai zafi; cikinta zai kumbura, cinyarta kuma yă shanye, tă kuwa zama la’ananniya a cikin mutanenta. Amma fa, in macen ba tă ƙazantar da kanta ba, ba tă kuma da ƙazanta, za a kuɓutar da ita daga laifin, za tă kuma iya haihuwa. “ ‘Wannan dai, ita ce dokar kishi sa’ad da mace ta kauce, ta kuma ƙazantar da kanta yayinda take aure da mijinta, ko kuma sa’ad da mijin yana kishi domin yana shakkar matarsa. Firist zai sa tă tsaya a gaban Ubangiji, yă kuma yi amfani da wannan doka gaba ɗaya a kanta. Mijin zai zama marar laifi daga kowane laifi, amma matar za tă ɗauki muguntarta, idan ta yi laifin.’ ” Ubangiji ya ce wa Musa, “Yi magana da Isra’ilawa, ka ce musu, ‘In mace, ko namiji yana so yă yi alkawari na musamman, alkawarin zaman keɓaɓɓe ga Ubangiji, a matsayin Banazare, dole yă keɓe kansa daga ruwan inabi, ko daga waɗansu abubuwa sha masu sa maye, kada kuma yă sha ruwan tsamin da aka yi daga ruwan inabi, ko daga waɗansu abubuwa sha masu sa maye. Ba zai sha ruwan ’ya’yan inabi, ko yă ci ’ya’yan inabi ɗanye ko busasshe ba. Muddin yana Banazare, ba zai ci wani abin da ya fito daga ’ya’yan inabi ba, ko ƙwayar inabi, ko ɓawonsa ma. “ ‘A dukan lokacin da yake a kan alkawarin keɓewarsa, reza ba zai taɓa kansa. Dole yă kasance da tsarki har ƙarshen keɓewarsa ga Ubangiji; tilas yă bar gashin kansa yă yi tsawo. A dukan kwanakin keɓewarsa ga Ubangiji, Banazarin ba zai yi kusa da gawa ba. Ko da ma gawar ta mahaifinsa ce, ko ta mahaifiyarsa, ko ta ɗan mahaifiyarsa, ko kuma ta ’yar’uwarsa ce, ba zai ƙazantar da kansa saboda su ba, domin alamar keɓewarsa ga Allah tana kansa. A dukan kwanakin keɓewarsa, an tsarkake shi ga Ubangiji. “ ‘In farat ɗaya wani ya mutu kusa da shi, to, keɓewarsa ta ƙazantu, dole yă aske kansa a ranar tsarkakewarsa, a rana ta bakwai. Sa’an nan a rana ta takwas, tilas yă kawo wa firist ’yan kurciyoyi biyu, ko kuma ’yan tattabarai biyu a bakin ƙofar Tentin Sujada. Firist kuwa zai miƙa ɗaya don hadaya ta zunubi, ɗayan kuma don hadaya ta ƙonawa, yă yi kafara dominsa, gama ya yi zunubi ta dalilin gawar. A wannan rana zai sāke keɓe kansa. Dole yă keɓe kansa ga Ubangiji, har kwanakin keɓewarsa, kuma dole yă kawo ɗan rago bana ɗaya a matsayin hadayar laifi. Kwanakin baya ba sa cikin lissafi, domin ya ƙazantu a lokacin keɓewarsa. “ ‘To, ga doka saboda Banazare sa’ad da kwanakin keɓewarsa suka gama. Za a kawo shi a bakin ƙofar Tentin Sujada. A can zai miƙa hadayunsa ga Ubangiji. Hadayun kuwa su ne, ɗan rago, bana ɗaya marar lahani don hadaya ta ƙonawa, ’yar tunkiya, bana ɗaya marar lahani na hadaya don zunubi, rago marar lahani don hadaya ta salama, tare da hadayu na hatsi da hadayu na sha, da kuma kwando burodi marar yisti, ƙosai da aka yi da lallausan gari kwaɓaɓɓe da mai, da kuma wainan da aka barbaɗa da mai. “ ‘Firist zai kawo su a gaban Ubangiji, yă miƙa hadaya don zunubi da hadaya ta ƙonawa. Zai miƙa kwandon burodi marar yisti, yă kuma miƙa ɗan ragon hadaya ta salama tare da hadaya ta gari, da hadaya ta sha ga Ubangiji. “ ‘Sa’an nan a ƙofar Tentin Sujada, dole Banazaren yă aske gashin da ya alamta keɓewarsa, yă kwashe gashin, yă zuba a cikin wutar da take ƙarƙashin hadaya ta salama. “ ‘Bayan Banazaren ya aske gashinsa da ya alamta keɓewa, firist zai ɗauki dafaffiyar kafaɗar rago, da ƙosai da kuma waina daga cikin kwando waɗanda duka biyu marar yisti ne, yă sa su a tafin hannun keɓaɓɓen. Firist zai kaɗa su a gaban Ubangiji, hadaya ce ta kaɗawa; mai tsarki ne kuma, zai zama na firist, tare da ƙirjin da aka kaɗa da kuma cinyar da aka kawo. Bayan haka, Banazaren zai iya shan ruwan inabi. “ ‘Wannan ita ce dokar Banazare wanda ya yi alkawari ga Ubangiji bisa ga keɓewarsa, tare da duk abin da zai iya bayarwa. Tilas yă cika alkawarin da ya yi bisa ga dokar zaman Banazare.’ ” Ubangiji ya ce wa Musa, “Gaya wa Haruna da ’ya’yansa, ‘Ga yadda za ku albarkaci Isra’ilawa. Za ku ce musu, “ ‘ “ Ubangiji yă albarkace ku, yă kuma kiyaye ku; Ubangiji yă sa fuskarsa ta haskaka a kanku, yă kuma yi muku alheri; Ubangiji yă dube ku da idon rahama, yă kuma ba ku salama.” ’ “Da haka za su sa sunana a kan Isra’ilawa, ni kuma zan albarkace su.” Sa’ad da Musa ya gama kafa tabanakul, sai ya shafe shi da mai, ya tsarkake shi tare da dukan kayayyakinsa, ya kuma shafe bagaden da mai, ya tsarkake shi da dukan kayayyakinsa. Sa’an nan shugabannin Isra’ila, wato, shugabannin iyalai waɗanda suke shugabancin kabilan da aka ƙidaya, suka miƙa hadayu. Suka kawo kyautansu a gaban Ubangiji. Kyautayin kuwa su ne, kekunan yaƙi shida da aka rufe, da shanu goma sha biyu, saniya guda daga kowane shugaba, da kuma keken yaƙi guda daga shugabanni biyu. Suka miƙa waɗannan a gaban tabanakul. Ubangiji ya ce wa Musa, “Ka karɓi abubuwan nan daga gare su, domin a yi amfani da su a aikin Tentin Sujada. Ka ba da su ga Lawiyawa, a ba kowane mutum bisa ga aikinsa.” Haka fa Musa ya ɗauki kekunan yaƙi da shanun ya ba wa Lawiyawa. Ya ba wa Gershonawa, kekunan yaƙi biyu da shanu huɗu bisa ga aikinsu, ya kuma ya ba wa kabilar Merari kekunan yaƙi huɗu da shanu takwas bisa ga aikinsu. Aka ba da su duka a ƙarƙashin ikon Itamar ɗan Haruna, firist. Amma Musa bai ba wa Kohatawa kome ba, gama aikinsu shi ne lura da kayayyaki masu tsarki waɗanda ake ɗauka a kafaɗa. Sa’ad da aka shafe bagaden da mai, sai shugabannin suka kawo hadayunsu saboda keɓewarsa, suka miƙa su a bagaden. Gama Ubangiji ya riga ya gaya wa Musa cewa, “Kowace rana, shugaba guda zai kawo hadayarsa saboda keɓewar bagade.” Wanda ya kawo hadayarsa a rana ta farko shi ne Nashon ɗan Amminadab, shugaban mutanen Yahuda. Hadayar da ya kawo ita ce, faranti guda ɗaya na azurfa, nauyinsa shekel ɗari ɗaya da talatin, da kuma daro na yayyafawa na azurfa, nauyinsa shekel saba’in, dukan biyu, an auna su bisa ga ma’aunin shekel na tsattsarkan wuri ne, kowannensu cike da lallausan gari, haɗe da mai kamar hadaya ta gari; ya kawo kwanon zinariya ɗaya, mai nauyin shekel goma, cike da turaren hayaƙi; da ƙaramin bijimi guda ɗaya, tunkiya ɗaya, da rago, dukansu bana ɗaya-ɗaya domin hadaya ta ƙonawa; ya kuma kawo bunsuru ɗaya domin hadaya don zunubi; da shanu biyu, raguna biyar, bunsurai biyar da kuma ’yan raguna biyar dukansu bana ɗaya-ɗaya, a miƙa su hadaya ta salama. Wannan ita ce hadayar Nashon ɗan Amminadab. A rana ta biyu, Netanel ɗan Zuwar, shugaban mutanen Issakar, ya kawo hadayarsa. Hadayar da ya kawo ita ce, faranti guda ɗaya na azurfa, nauyinsa shekel ɗari ɗaya da talatin, da kuma daro na yayyafawa na azurfa, nauyinsa shekel saba’in, dukan biyu, an auna su bisa ga ma’aunin shekel na tsattsarkan wuri, kowannensu cike da lallausan gari, haɗe da mai kamar hadaya ta gari; ya kuma kawo kwanon zinariya ɗaya mai nauyin shekel, goma cike da turaren hayaƙi; da ƙaramin bijimi guda ɗaya, tunkiya ɗaya da rago, dukansu bana ɗaya-ɗaya domin hadaya ta ƙonawa; ya kuma kawo bunsuru ɗaya domin hadaya don zunubi; da shanu biyu, raguna biyar, bunsurai biyar da kuma ’yan raguna biyar dukansu bana ɗaya-ɗaya, a miƙa su hadaya ta salama. Wannan ita ce hadayar Netanel ɗan Zuwar. A rana ta uku, Eliyab ɗan Helon, shugaban mutanen Zebulun, ya kawo hadayarsa. Hadayar da ya kawo ita ce, faranti guda ɗaya na azurfa, nauyinsa shekel ɗari ɗaya da talatin, da kuma daro na yayyafawa na azurfa, nauyinsa shekel saba’in, dukan biyu, an auna su bisa ga ma’aunin shekel na tsattsarkan wuri, kowannensu cike da lallausan gari, haɗe da mai kamar hadaya ta gari; ya kuma kawo kwanon zinariya ɗaya, mai nauyin shekel goma, cike da turaren hayaƙi; da ƙaramin bijimi guda ɗaya, tunkiya ɗaya, da rago, dukansu bana ɗaya-ɗaya domin hadaya ta ƙonawa; ya kuma kawo bunsuru ɗaya domin hadaya don zunubi; da shanu biyu, raguna biyar, bunsurai biyar da kuma ’yan raguna biyar, dukansu bana ɗaya-ɗaya, a miƙa su hadaya ta salama. Wannan ita ce hadayar Eliyab ɗan Helon. A ranan ta huɗu, Elizur ɗan Shedeyur, shugaban mutanen Ruben, ya kawo hadayarsa. Hadayar da ya kawo ita ce, faranti guda ɗaya na azurfa, nauyinsa shekel ɗari ɗaya da talatin, da kuma daro na yayyafawa na azurfa, nauyinsa shekel saba’in, dukan biyu, an auna su bisa ga ma’aunin shekel na tsattsarkan wuri, kowannensu cike da lallausan gari, haɗe da mai kamar hadaya ta gari; ya kuma kawo kwanon zinariya ɗaya mai nauyin shekel goma, cike da turaren hayaƙi; da ƙaramin bijimi guda ɗaya, tunkiya ɗaya, da rago, dukansu bana ɗaya-ɗaya domin hadaya ta ƙonawa; ya kuma kawo bunsuru ɗaya domin hadaya don zunubi; da shanu biyu, raguna biyar, bunsurai biyar da kuma ’yan raguna biyar, dukansu bana ɗaya-ɗaya, a miƙa su hadaya ta salama. Wannan ita ce hadayar Elizur ɗan Shedeyur. A rana ta biyar, Shelumiyel ɗan Zurishaddai, shugaban mutanen Simeyon, ya kawo hadayarsa. Hadayar da ya kawo ita ce, faranti guda ɗaya na azurfa, nauyinsa shekel ɗari ɗaya da talatin, da kuma daro na yayyafawa na azurfa, nauyinsa shekel saba’in, dukan biyu, an auna su bisa ga ma’aunin shekel na tsattsarkan wuri, kowannensu cike da lallausan gari, haɗe da mai kamar hadaya ta gari; ya kuma kawo kwanon zinariya ɗaya mai nauyin shekel goma, cike da turaren hayaƙi; da ƙaramin bijimi guda ɗaya, tunkiya ɗaya, da rago, dukansu bana ɗaya-ɗaya domin hadaya ta ƙonawa; ya kuma kawo bunsuru ɗaya domin hadaya don zunubi; da shanu biyu, raguna biyar, bunsurai biyar da kuma ’yan raguna biyar, dukansu bana ɗaya-ɗaya, a miƙa su hadaya ta salama. Wannan ita ce hadayar Shelumiyel ɗan Zurishaddai. A rana ta shida, Eliyasaf ɗan Deyuwel, shugaban mutanen Gad, ya kawo hadayarsa. Hadayar da ya kawo ita ce, faranti guda ɗaya na azurfa, nauyinsa shekel ɗari ɗaya da talatin, da kuma daro na yayyafawa na azurfa, nauyinsa shekel saba’in, dukan biyu, an auna su bisa ga ma’aunin shekel na tsattsarkan wuri, kowannensu cike da lallausan gari, haɗe da mai kamar hadaya ta gari; ya kuma kawo kwanon zinariya ɗaya mai nauyin shekel goma, cike da turaren hayaƙi; da ƙaramin bijimi guda ɗaya, tunkiya ɗaya, da rago, dukansu bana ɗaya-ɗaya domin hadaya ta ƙonawa; ya kuma kawo bunsuru ɗaya domin hadaya don zunubi; da shanu biyu, raguna biyar, bunsurai biyar da kuma ’yan raguna biyar, dukansu bana ɗaya-ɗaya, a miƙa su hadaya ta salama. Wannan ita ce hadayar Eliyasaf ɗan Deyuwel. A rana ta bakwai, Elishama ɗan Ammihud, shugaban mutanen Efraim, ya kawo hadayarsa. Hadayar da ya kawo ita ce, faranti guda ɗaya na azurfa, nauyinsa shekel ɗari ɗaya da talatin, da kuma daro na yayyafawa na azurfa, nauyinsa shekel saba’in, dukan biyu, an auna su bisa ga ma’aunin shekel na tsattsarkan wuri, kowannensu cike da lallausan gari, haɗe da mai kamar hadaya ta gari; kwanon zinariya ɗaya mai nauyin shekel goma, cike da turaren hayaƙi; da ƙaramin bijimi guda ɗaya, tunkiya ɗaya, da rago, dukansu bana ɗaya-ɗaya domin hadaya ta ƙonawa; ya kuma kawo bunsuru ɗaya domin hadaya don zunubi; da shanu biyu, raguna biyar, bunsurai biyar da kuma ’yan raguna biyar, dukansu bana ɗaya-ɗaya, a miƙa su hadaya ta salama. Wannan ita ce hadayar Elishama ɗan Ammihud. A rana ta takwas, Gamaliyel ɗan Fedazur, shugaban mutanen Manasse, ya kawo hadayarsa. Hadayar da ya kawo ita ce, faranti guda ɗaya na azurfa, nauyinsa shekel ɗari ɗaya da talatin, da kuma daro na yayyafawa na azurfa, nauyinsa shekel saba’in, dukan biyu, an auna su bisa ga ma’aunin shekel na tsattsarkan wuri, kowannensu cike da lallausan gari, haɗe da mai kamar hadaya ta gari; kwanon zinariya ɗaya mai nauyin shekel goma, cike da turaren hayaƙi; da ƙaramin bijimi guda ɗaya, tunkiya ɗaya, da rago, dukansu bana ɗaya-ɗaya domin hadaya ta ƙonawa; ya kuma kawo bunsuru ɗaya domin hadaya don zunubi; da shanu biyu, raguna biyar, bunsurai biyar da kuma ’yan raguna biyar, dukansu bana ɗaya-ɗaya, a miƙa su hadaya ta salama. Wannan ita ce hadayar Gamaliyel ɗan Fedazur. A rana ta tara, Abidan ɗan Gideyoni, shugaban mutanen Benyamin, ya kawo hadayarsa. Hadayar da ya kawo ita ce, faranti guda ɗaya na azurfa, nauyinsa shekel ɗari ɗaya da talatin, da kuma daro na yayyafawa na azurfa, nauyinsa shekel saba’in, dukan biyu, an auna su bisa ga ma’aunin shekel na tsattsarkan wuri, kowannensu cike da lallausan gari, haɗe da mai kamar hadaya ta gari; kwanon zinariya ɗaya mai nauyin shekel goma, cike da turaren hayaƙi; da ƙaramin bijimi guda ɗaya, tunkiya ɗaya, da rago, dukansu bana ɗaya-ɗaya domin hadaya ta ƙonawa; ya kuma kawo bunsuru ɗaya domin hadaya don zunubi; da shanu biyu, raguna biyar, bunsurai biyar da kuma ’yan raguna biyar, dukansu bana ɗaya-ɗaya, a miƙa su hadaya ta salama. Wannan ita ce hadayar Abidan ɗan Gideyoni. A rana ta goma, Ahiyezer ɗan Ammishaddai, shugaban mutanen Dan, ya kawo hadayarsa. Hadayar da ya kawo ita ce, faranti guda ɗaya na azurfa, nauyinsa shekel ɗari ɗaya da talatin, da kuma daro na yayyafawa na azurfa, nauyinsa shekel saba’in, dukan biyu, an auna su bisa ga ma’aunin shekel na tsattsarkan wuri, kowannensu cike da lallausan gari, haɗe da mai kamar hadaya ta gari; kwanon zinariya ɗaya mai nauyin shekel goma, cike da turaren hayaƙi; da ƙaramin bijimi guda ɗaya, tunkiya ɗaya, da rago, dukansu bana ɗaya-ɗaya domin hadaya ta ƙonawa; ya kuma kawo bunsuru ɗaya domin hadaya don zunubi; da shanu biyu, raguna biyar, bunsurai biyar da kuma ’yan raguna biyar, dukansu bana ɗaya-ɗaya, a miƙa su hadaya ta salama. Wannan ita ce hadayar Ahiyezer ɗan Ammishaddai. A rana ta goma sha ɗaya, Fagiyel ɗan Okran, shugaban mutanen Asher, ya kawo hadayarsa. Hadayar da ya kawo ita ce, faranti guda ɗaya na azurfa, nauyinsa shekel ɗari ɗaya da talatin, da kuma daro na yayyafawa na azurfa, nauyinsa shekel saba’in, dukan biyu, an auna su bisa ga ma’aunin shekel na tsattsarkan wuri, kowannensu cike da lallausan gari, haɗe da mai kamar hadaya ta gari; kwanon zinariya ɗaya mai nauyin shekel goma, cike da turaren hayaƙi; da ƙaramin bijimi guda ɗaya, tunkiya ɗaya, da rago, dukansu bana ɗaya-ɗaya domin hadaya ta ƙonawa; ya kuma kawo bunsuru ɗaya domin hadaya don zunubi; da shanu biyu, raguna biyar, bunsurai biyar da kuma ’yan raguna biyar, dukansu bana ɗaya-ɗaya, a miƙa su hadaya ta salama. Wannan ita ce hadayar Fagiyel ɗan Okran. A rana ta goma sha biyu, Ahira ɗan Enan, shugaban mutanen Naftali, ya kawo hadayarsa. Hadayar da ya kawo ita ce, faranti guda ɗaya na azurfa, nauyinsa shekel ɗari ɗaya da talatin, da kuma daro na yayyafawa na azurfa, nauyinsa shekel saba’in, dukan biyu, an auna su bisa ga ma’aunin shekel na tsattsarkan wuri, kowannensu cike da lallausan gari, haɗe da mai kamar hadaya ta gari; kwanon zinariya ɗaya mai nauyin shekel goma, cike da turaren hayaƙi; da ƙaramin bijimi guda ɗaya, tunkiya ɗaya, da rago, dukansu bana ɗaya-ɗaya domin hadaya ta ƙonawa; ya kuma kawo bunsuru ɗaya domin hadaya don zunubi; da shanu biyu, raguna biyar, bunsurai biyar da kuma ’yan raguna biyar, dukansu bana ɗaya-ɗaya, a miƙa su hadaya ta salama. Wannan ita ce hadayar Ahira ɗan Enan. Waɗannan su ne hadayun shugabannin Isra’ilawa saboda keɓewar bagade sa’ad da aka shafe shi, an kawo faranta goma sha biyu na azurfa, darunan goma sha biyu na azurfa don yayyafawa, da kuma kwanonin zinariya goma sha biyu. Kowane faranti na azurfa yana da nauyin shekel ɗari da talatin, kuma kowane daro na azurfa don yayyafawa yana da nauyin shekel saba’in. Duka-duka dai, nauyin kwanonin azurfa, shekel dubu biyu ne da ɗari huɗu, bisa ga ma’aunin shekel na tsattsarkan wuri. Kwanonin zinariya goma sha biyu da aka cika da turaren hayaƙi kuwa, nauyinsu shekel goma ne kowanne, bisa ga ma’aunin shekel na tsattsarkan wuri. Duka-duka dai, nauyin kwanonin zinariya, shekel ɗari ɗaya ne da ashirin. Jimillar dabbobi don hadaya ta ƙonawa, ta kai ƙanana bijimai goma sha biyu, raguna goma sha biyu da ’yan raguna goma sha biyu, dukansu bana ɗaya-ɗaya, tare da hadayarsu ta hatsi. Aka yi amfani da bunsurai goma sha biyu domin hadaya don zunubi. Jimillar dabbobi don hadaya ta salama, ta kai shanu ashirin huɗu, raguna sittin, bunsurai sittin da kuma ’yan raguna sittin, dukansu bana ɗaya-ɗaya. Waɗannan su ne hadayu saboda keɓewar bagade, bayan an shafe shi. Sa’ad da Musa ya shiga Tentin Sujada don yă yi magana da Ubangiji, sai ya ji murya tana magana da shi daga tsakanin kerubobi biyu a bisa murfin akwatin Alkawari. A ta haka Ubangiji ya yi masa magana. Ubangiji ya ce wa Musa, “Yi magana da Haruna, ka ce masa, ‘Sa’ad da za ka shisshirya fitilun nan bakwai, ka shirya su yadda za su fuskanci gaba domin haskensu yă haskaka ta gaba.’ ” Haka kuwa Haruna ya yi; ya shisshirya fitilun yadda za su fuskanci gaba a kan wurin ajiye fitilan, kamar dai yadda Ubangiji ya umarci Musa. Ga yadda aka yi wurin ajiye fitilan. An ƙera shi da zinariya daga gindinsa har zuwa sama inda ya buɗu. Aka ƙera wurin ajiye fitilan yadda Ubangiji ya nuna wa Musa. Ubangiji ya ce wa Musa, “Keɓe Lawiyawa daga sauran Isra’ilawa, ka tsarkake su. Ga yadda za ka tsarkake su, ka yayyafa musu ruwan tsarkakewa; ka sa su aske jikunansu duka su kuma wanke tufafinsu, ta haka za su tsarkake kansu. Ka sa su ɗauki ɗan bijimi tare da lallausan garin hadaya, kwaɓaɓɓe da mai; sa’an nan, kai kuma ka ɗauki ɗan bijimi na biyu na hadaya don zunubi. Ka kawo Lawiyawa a gaban Tentin Sujada, ka kuma kira taron Isra’ilawa duka. Za ka kawo Lawiyawa a gaban Ubangiji, Isra’ilawa kuma za su ɗibiya musu hannuwansu. Haruna zai miƙa Lawiyawa a gaban Ubangiji a matsayin hadaya ta kaɗawa daga Isra’ilawa, saboda a shirya su domin aikin Ubangiji. “Bayan Lawiyawa sun ɗibiya hannuwansu a kan bijiman, sai ka yi amfani da ɗaya a matsayin hadaya don zunubi ga Ubangiji, ɗayan kuma domin hadaya ta ƙonawa, don yin kafara saboda Lawiyawa. Ka kuma sa Lawiyawa su tsaya a gaban Haruna da ’ya’yansa, sai ka miƙa su kamar hadaya ta kaɗawa ga Ubangiji. Da haka za ka keɓe Lawiyawa daga sauran Isra’ilawa, Lawiyawa za su zama nawa. “Bayan ka tsarkake Lawiyawa, ka kuma miƙa su kamar hadaya ta kaɗawa, sai su zo su yi aikinsu a Tentin Sujada. Gama dukansu an ba ni su daga cikin Isra’ilawa a maimakon dukan waɗanda suka fara buɗe mahaifa, wato, dukan ’ya’yan farin Isra’ilawa. Na karɓi Lawiyawa su zama nawa. Kowane ɗan farin haihuwa, ko mutum, ko dabba a Isra’ila, nawa ne. Sa’ad da na kashe ’ya’yan fari a Masar, na keɓe ’ya’yan fari na Isra’ilawa wa kaina. Na kuma ɗauki Lawiyawa a maimakon dukan ’ya’yan fari maza a Isra’ila. Cikin dukan Isra’ilawa, na ba da Lawiyawa kyauta ga Haruna da ’ya’yansa, su yi hidima a Tentin Sujada a madadin Isra’ilawa, su kuma yi kafara dominsu saboda kada annoba ta bugi Isra’ilawa sa’ad da suka je kusa da wuri mai tsarki.” Musa, Haruna da kuma dukan taron Isra’ilawa, suka yi da Lawiyawa yadda Ubangiji ya umarci Musa. Lawiyawa suka tsarkake kansu, suka kuma wanke tufafinsu. Sai Haruna ya miƙa su kamar hadaya ta kaɗawa a gaban Ubangiji, ya kuma yi kafara saboda su don yă tsarkake su. Bayan haka, sai Lawiyawa suka zo don su yi aikinsu a Tentin Sujada, a ƙarƙashin Haruna da ’ya’yansa. Suka yi da Lawiyawa kamar dai yadda Ubangiji ya umarci Musa. Ubangiji ya ce wa Musa, “Wannan ya shafi Lawiyawa ne, wato, mazan da suka kai shekara ashirin da biyar, ko fiye, za su zo su yi aiki a Tentin Sujada, amma in suka kai shekaru hamsin da haihuwa, dole su huta daga wannan aiki na yau da kullum, su kuma daina aiki. Za su iya taimakon ’yan’uwansu cikin tafiyar da ayyuka a Tentin Sujada, amma su kansu ba za su yi aikin ba. Haka fa za ka ba wa Lawiyawa aikinsu.” Ubangiji ya yi magana da Musa a Hamadar Sinai, a watan farko na shekara ta biyu bayan fitarsu daga ƙasar Masar. Ya ce, “Ka sa Isra’ilawa su yi Bikin Ƙetarewa a ƙayyadadden lokaci. A yi wannan bikin ƙayyadadden lokaci da yamma, a rana ta goma sha huɗu ga wannan wata, a yi shi bisa ga dokokinsa da ƙa’idodinsa.” Saboda haka sai Musa ya gaya wa Isra’ilawa su yi Bikin Ƙetarewa, suka kuwa yi haka a Hamadar Sinai da yamma, a rana ta sha huɗu ga watan farko. Isra’ilawa suka yi dukan abubuwa yadda Ubangiji ya umarci Musa. Amma waɗansunsu ba su iya yin Bikin Ƙetarewa a ranar ba gama sun ƙazantu ta wurin taɓa gawa. Saboda haka suka zo wurin Musa da Haruna a wannan rana suka ce wa Musa, “Mun ƙazantu saboda mun taɓa gawa, don me aka hana mu mu ba da hadaya ga Ubangiji tare da sauran Isra’ilawa a ƙayyadadden lokaci?” Musa ya amsa musu ya ce, “Ku dakata sai na sami umarni daga wurin Ubangiji game da ku.” Sai Ubangiji ya ce wa Musa, “Gaya wa Isra’ilawa cewa, ‘Sa’ad da waninku ko zuriyarku ya ƙazantu ta wurin taɓa gawa, ko kuwa ya yi tafiya mai nisa, duk da haka zai kiyaye Bikin Ƙetarewa ta Ubangiji. Za su yi bikin da yamma, a rana ta sha huɗu ga wata na biyu. Za su ci naman tunkiya, tare da burodi marar yisti, da ganyaye masu ɗaci. Kada su bar kome daga cikinsa yă kai safe, ko a karye ƙashinsa. Sa’ad da suke Bikin Ƙetarewa, dole su kiyaye dukan ƙa’idodinsa. Amma in mutumin da yake da tsarki bai kuma yi tafiya ba, ya kuwa ƙi yă yi Bikin Ƙetarewar, dole a ware wannan mutum daga mutanensa, domin bai miƙa hadaya ga Ubangiji a ƙayyadadden lokaci ba. Wannan mutum zai ɗauki alhakin zunubinsa. “ ‘Baƙon da yake zaune a cikinku wanda yake so yă yi Bikin Ƙetarewar Ubangiji, dole yă yi shi bisa ga dokokinsa da ƙa’idodinsa. Dole ku kasance da ƙa’ida ɗaya ga baƙo da kuma ɗan ƙasa.’ ” A ranar da aka kafa Tenti na Alkawari, sai girgije ya rufe shi. Daga yamma har safe, girgijen da yake bisa tabanakul ya yi kama da wuta. Haka ya ci gaba da kasancewa; girgijen ya rufe shi, da dare kuma sai ya yi kamar wuta. Duk sa’ad da aka ɗaga girgijen daga Tentin, sai Isra’ilawa su kama hanya; duk inda girgijen ya tsaya, a nan Isra’ilawa za su yi sansani. Da umarnin Ubangiji, Isra’ilawa suke tashi. Da umarninsa kuma suke sauka. Muddin girgijen yana tsaye a bisa tabanakul, sukan yi ta zamansu a sansanoni. Sa’ad da girgijen ya ci gaba da kasancewa a bisan tabanakul na dogon lokaci, Isra’ilawa sukan bi umarnin Ubangiji, ba kuwa za su tashi ba. Wani lokaci girgijen yakan yi ’yan kwanaki ne kawai a bisa tabanakul; da umarnin Ubangiji sukan kafa sansani da umarninsa kuma su tashi. Wani lokaci girgijen yakan zauna daga yamma har safiya ne kawai, sa’ad da kuma aka ɗaga shi da safe, sai su kama hanya. Ko da rana, ko da dare, duk sa’ad da aka ɗaga girgijen, sai su ma su tashi. Ko girgijen ya yi kwana biyu a bisa tabanakul, ko wata guda, ko shekara, Isra’ilawa za su zauna a sansani ba kuwa za su tashi ba; amma sa’ad da aka ɗaga shi, sai su kuma su tashi. Da umarnin Ubangiji sukan kafa sansani, da umarninsa kuma sukan tashi. Sukan bi umarnin Ubangiji, bisa ga umarninsa ta wurin Musa. Ubangiji ya ce wa Musa, “Ka ƙera kakaki guda biyu na azurfa, ka kuma yi amfani da su don kira taron jama’a wuri ɗaya, don kuma ka riƙa sanar da su lokacin tashi daga sansani. Sa’ad da aka busa su biyu, dukan jama’a za su taru a gabanka a ƙofar Tentin Sujada. In ɗaya ne kaɗai aka busa, sai shugabannin kabilan Isra’ila, su taru a gabanka. Sa’ad da aka ji karar busar kakaki, sai sansanin da yake a gabashi, su kama hanya. A kara ta biyu, sansanin da yake a kudanci, su kama hanya. Busan kakaki zai zama alama ta kama hanya. In don a tara jama’a ne, sai a busa kakaki, amma ba da irin alama ɗaya ba. “’Ya’yan Haruna, firistoci ne, za su busa kakaki. Wannan za tă zama dawwammamiyar farilla gare ku da kuma tsararraki masu zuwa. Duk lokacin da za ku tafi yaƙi a ƙasarku, in akwai waɗansu da suke matsa muku, za ku yi amfani da waɗannan kakaki ta wurin hura su, alama ce, cewa za a je yaƙi. Sa’an nan Ubangiji Allahnku zai tuna da ku, yă cece ku daga maƙiyanku. Haka ma in kuna cikin jin daɗinku, musamman lokacin da kuke bukukkuwanku, kamar Bikin Sabon Wata da dai kowane Bikinku, za ku hura waɗannan kakaki lokacin da kuke miƙa hadayunku na ƙonawa, da hadayunku na salama, za su kuma zama muku abin tunawa a gaban Allahnku. Ni ne Ubangiji Allahnku.” A rana ta ashirin ga wata na biyu, a shekara ta biyu, sai girgijen ya tashi daga tabanakul na Shaida. Sai Isra’ilawa suka tashi daki-daki daga Hamadar Sinai, suna tafiya daga wuri zuwa wuri, har sai da girgijen ya tsaya a Hamadar Faran. Suka kama hanya, a wannan lokaci, bisa umarnin Ubangiji, ta wurin Musa. Ɓangarorin sansanin Yahuda suka fara tashi, bisa ga ƙa’idar da aka yi, aka kuma umarta. Nashon ɗan Amminadab ne shugaba. Netanel ɗan Zuwar ne shugaban ɓangaren kabilar Issakar, Eliyab ɗan Helon kuma shi ne shugaban ɓangaren kabilar Zebulun. Sa’an nan aka saukar da tabanakul ƙasa, Gershonawa da mutanen Merari da suke ɗauke da shi suka kama hanya. Sai ɓangarori sansanin Ruben suka biyo, bisa ga ƙa’idar da aka yi, aka kuma umarta. Elizur ɗan Shedeyur ne shugaba. Shelumiyel ɗan Zurishaddai ne shugaban ɓangaren kabilar Simeyon, Eliyasaf ɗan Deyuwel kuma shi ne shugaban ɓangaren kabilar Gad. Sai Kohatawa suka kama hanya, ɗauke da kayayyaki masu tsarki, domin kafin su kai wurin da za a kafa sansani, a riga an kafa tabanakul. Biye da waɗannan kuma sai ɓangaren sansanin kabilar Efraim suka biyo bisa ga ƙa’ida da aka yi, aka kuma umarta. Elishama ɗan Ammihud ne shugaba. Gamaliyel ɗan Fedazur ne shugaban ɓangaren kabilar Manasse, Abidan ɗan Gideyoni kuma shi ne shugaban ɓangaren kabilar Benyamin. A ƙarshe, a matsayi masu gadin bayan dukan ɓangarori, sai ɓangaren sansanin Dan suka tashi bisa ga ƙa’idar da aka yi, aka kuma umarta. Ahiyezer ɗan Ammishaddai ne shugaba. Fagiyel ɗan Okran ne shugaban ɓangaren kabilan Asher, Ahira ɗan Enan kuma shi ne shugaban kabilar Naftali. Wannan shi ne tsarin tafiyar ɓangarorin Isra’ilawa, sa’ad da sukan kama hanya. Sai Musa ya ce wa Hobab ɗan Reyuwel Bamidiyane surukinsa, “Yanzu fa, muna shirin tashi ne daga nan, domin mu tafi inda Ubangiji ya ce, ‘Zan ba ku.’ Ka zo tare da mu, za mu kuwa yi maka alheri, gama Ubangiji ya yi wa Isra’ilawa alkawari abubuwa masu kyau.” Ya amsa, ya ce “A’a, ba zan tafi ba; zan koma ƙasata da kuma wurin mutanena.” Amma Musa ya ce, “Ina roƙonka kada ka rabu da mu. Ka san inda ya kamata mu kafa sansani a hamada, za ka kuma zama idanunmu. In ka zo tare da mu, za mu raba duk abin alherin Ubangiji ya ba mu tare da kai.” Saboda haka suka kama hanya daga dutsen Ubangiji, suka yi tafiya kwana uku. Akwatin alkawarin Ubangiji ya ja gabansu a waɗannan kwanaki uku, don yă samo musu masauƙi. A duk lokacin da suka tashi daga sansani, girgijen Ubangiji ya inuwantar da su da rana. Duk kuma sa’ad da akwatin ya kama hanya, sai Musa ya ce, “Ka tashi, ya Ubangiji! Ka sa maƙiyanka su warwatse; masu ƙinka kuma su gudu a gabanka.” Duk sa’ad da akwatin ya sauka kuma, sai Musa ya ce, “Ka komo, ya Ubangiji, a wurin dubban da ba a iya ƙidayawa na iyalan Isra’ila.” Da Ubangiji ya ji gunagunin da mutanen suke yi saboda wahalarsu, sai ya husata ƙwarai. Sai wuta daga Ubangiji ta yi ta ci a cikinsu har ta ƙone waɗansu wurare na sansanin. Da jama’ar suka yi wa Musa kuka, sai ya yi addu’a ga Ubangiji, wutar kuwa ta mutu. Saboda haka aka kira wannan wuri Tabera, gama a wurin ne wuta daga Ubangiji ta ƙuna a cikinsu. Wata rana, baƙin da suke cikinsu, suka fara kwaɗayin waɗansu abinci, har suka sa Isra’ilawa suka fara kuka, suna cewa, “Da mun sami nama mun ci mana! Mun tuna da kifin da muka ci kyauta a Masar, haka ma kayan lambu irin su kukumba, guna, safa, albasa da kuma tafarnuwa. Amma ga shi yanzu ba mu da wani abin marmari; in ba wannan Manna ba!” Manna kuwa kamar tsabar riɗi take, kamanninta kuma kamar ƙaro ne. Mutane sukan fita su tattara ta, su niƙa a dutsen niƙa, ko kuwa su daka a turmi. Su dafa, ko su yi waina da ita. Ɗanɗanonta yakan yi kamar abin da aka yi da man zaitun. Sa’ad da raɓa tana saukowa da dad dare a kan sansani, Manna ma takan sauko. Musa ya ji mutanen suna ta gunaguni ko’ina a cikin iyalansu, kowane mutum a ƙofar tentinsa. Ubangiji kuwa ya husata ƙwarai, sai Musa ya damu. Sai ya ce wa Ubangiji, “Me ya sa ka kawo wannan damuwar a kan bawanka? Me na yi da ya ɓata maka rai har ka ɗora dukan nauyin mutanen nan a kaina? Ni ne na yi cikin dukan mutanen nan? Ni ne na haife su? To, me ya sa ka ce in ɗauke su a ƙirjina kamar yadda mai reno yake rungume jariri, zuwa ƙasa wadda ka yi alkawari da rantsuwa za ka ba wa kakanninsu? Ina ne zan sami nama in waɗannan mutane? Sun dinga yin mini kuka suna cewa ‘Ka ba mu nama mu ci!’ Ba zan iya ɗaukan dukan mutanen nan ni kaɗai ba, nauyin ya yi mini yawa. In haka za ka yi da ni, ka kashe ni yanzu, in na sami tagomashi daga gare ka, kada ka bar ni in rayu in ga wannan baƙin ciki.” Sai Ubangiji ya ce wa Musa, “Ka tattaro mini dattawa saba’in daga cikin mutanen Isra’ila, waɗanda aka sani su ne dattawa da kuma shugabanni a cikin jama’a. Ka sa su zo Tentin Sujada, su tsaya a can tare da kai. Zan sauko in yi magana da kai a can, zan kuma ɗauki Ruhun da yake kanka in mai da shi wajensu. Za su taimake ka ɗaukan nauyin mutane, don yă zama ba kai kaɗai ba ne mai ɗaukan kaya. “Ka gaya wa mutane, ‘Ku tsarkake kanku don gobe, za ku ci nama. Ubangiji ya ji ku sa’ad da kuka yi kuka cewa, “Da mun sami nama mun ci mana! Ai, da ba mu da damuwa, gama lokacin da muke zama cikin Masar ba mu da damuwa!” Yanzu Ubangiji zai ba ku nama, za ku kuma ci. Ba za ku ci shi na kwana ɗaya, ko biyu, ko biyar, ko goma, ko kuma kwana ashirin kaɗai ba, amma za ku ci har na wata guda cur, sai ya gundure ku a hanci har ku yi ƙyamarsa, domin kun ƙi Ubangiji wanda yake cikinku, kuka yi kuka a gabansa, kuna cewa, “Don me ma muka bar ƙasar Masar?” ’ ” Amma Musa ya ce, “Ga ni a cikin mutane dubu ɗari shida tafe tare da ni, kana kuma cewa, ‘Zan ba su nama su ci har wata guda cur!’ Za su ma sami isashe in har aka yanka musu garkuna tumaki da na shanu? Za su sami isashe in aka kama musu dukan kifin teku?” Ubangiji ya ce wa Musa, “Akwai abin da ya fi ƙarfina ne? Bari ka gani ko abin da na ce zan yi, zai faru ko babu.” Saboda haka Musa ya fita ya gaya wa jama’a abin da Ubangiji ya faɗa. Ya tattaro dattawansu saba’in, ya sa suka tsaya kewaye da Tentin Sujada. Sa’an nan Ubangiji ya sauko daga girgije, ya yi magana da shi, ya kuma ɗauke Ruhun da yake kan Musa ya ɗora shi a kan dattawa saba’in nan. Sa’ad da Ruhun ya zauna a kansu, sai suka yi annabci, amma daga wannan ba su ƙara yin haka kuma ba. To, fa, akwai dattawa biyu da suka kasance a sansani, wato, Eldad da Medad. Su ma an lasafta su cikin dattawan, amma ba su fita zuwa Tentin Sujada ba. Duk da haka Ruhun ya sauka a kansu, suka kuma yi annabci a cikin sansanin. Wani saurayi ya sheƙa a guje zuwa wajen Musa ya ce, “Eldad da Medad suna can suna annabci a sansani.” Sai Yoshuwa ɗan Nun, wanda yake mataimakin Musa tun yana saurayi, ya amsa ya ce, “Ranka yă daɗe, Musa, ka hana su!” Amma Musa ya amsa ya ce, “Kana kishi domina ne? Da ma a ce dukan mutanen Ubangiji annabawa ne, da ma a kuma ce Ubangiji ya sa Ruhunsa a kansu mana!” Sai Musa da dattawan Isra’ila suka koma sansani. Ana nan, sai Ubangiji ya kawo wata iska mai tsanani ta koro makware daga teku. Ta bar su birjik kewaye da sansani, tsayinsu daga ƙasa ya kai kamu biyu, misalin tafiyar nisan yini guda ta kowace fuska. Dukan yini da dukan dare da kuma kashegari, mutane suka fito suka tattara makware. Ba wanda ya kāsa tara ƙasa da garwa goma. Sai suka shanya abinsu kewaye da sansanin. Amma da suna cikin cin naman, tun ba su ma haɗiye ba, sai Ubangiji ya husata sosai a kan jama’ar, ya buge su da annoba mai zafi. Saboda haka aka kira wannan wuri Kibrot Hatta’awa, gama a can ne aka binne mutanen nan makwaɗaita. Daga Kibrot Hatta’awa, mutane suka yi tafiya zuwa Hazerot, a can suka sauka. Miriyam da Haruna suka fara zargin Musa saboda matarsa ’yar ƙasar Kush da ya aura. Suka ce, “ Ubangiji ya yi magana ta wurin Musa ne kaɗai? Ashe, bai yi magana ta wurinmu mu ma ba?” Ubangiji kuwa ya ji wannan. (Musa kuwa mutum ne mai tawali’u ƙwarai, mafi tawali’u fiye da kowane mutum a duniya.) Nan da nan Ubangiji ya ce wa Musa, da Haruna da kuma Miriyam, “Ku fita ku tafi Tentin Sujada, dukanku uku.” Sai dukansu uku suka tafi. Sai Ubangiji ya sauko a cikin ginshiƙin girgije; ya tsaya a bakin ƙofar Tenti, ya kira Haruna da Miriyam. Sa’ad da su biyu suka gusa gaba, sai ya ce, “Ku ji abin da zan faɗa, “Duk lokacin da akwai annabin Ubangiji a cikinku, nakan bayyana kaina gare shi cikin wahayi, in yi magana da shi cikin mafarkai. Amma ba haka nake magana da Musa bawana ba; na sa shi yă lura da dukan jama’ata Isra’ila. Da shi nake magana fuska da fuska, a fili kuma, ba a kacici-kacici ba; yakan ga siffar Ubangiji. To, me ya sa ba ku ji tsoro ku yi magana a kan bawana Musa ba?” Sai fushin Ubangiji ya yi ƙuna a kansu, ya kuma rabu da su. Da girgijen ya tashi daga bisa Tentin, sai ga Miriyam tsaye, kuturwa, fari fat. Haruna kuwa ya juya wajenta ya ga ta kuturce; sai Haruna ya ce wa Musa, “Ranka yă daɗe, ina roƙonka kada ka hukunta mu, gama zunubin da muka yi, mun yi ne cikin wauta. Kada ka sa ta zama kamar haifaffen mataccen jariri daga cikin mahaifiya wanda rabin jikin ruɓaɓɓe ne.” Saboda haka sai Musa ya yi kuka ga Ubangiji ya ce, “Ya Allah, ina roƙonka ka warkar da ita!” Sai Ubangiji ya ce wa Musa, “Da a ce mahaifinta ne ya tofa mata miyau a fuskarta, ashe, ba za tă ji kunya har kwana bakwai ba? A fitar da ita bayan sansani kwana bakwai; bayan haka za a iya dawo da ita.” Haka aka fitar da Miriyam bayan sansani kwana bakwai, mutane kuwa ba su ci gaba da tafiya ba sai da aka dawo da ita. Bayan haka sai mutane suka bar Hazerot suka sauka a Hamadan Faran. Ubangiji ya ce wa Musa, “Ka aiki waɗansu mutane zuwa ƙasar Kan’ana, wadda nake ba Isra’ilawa. Daga kowace kabila, ka aiki ɗaya daga cikin shugabanninta.” Saboda haka bisa ga umarnin Ubangiji, Musa ya aike su daga Hamadan Faran. Dukansu kuwa shugabanni ne na Isra’ilawa. Shugabannin kuwa su ne, Shammuwa ɗan Zakkur, daga kabilar Ruben; Shafat ɗan Hori, daga kabilar Simeyon; Kaleb ɗan Yefunne, daga kabilar Yahuda; Igal ɗan Yusuf, daga kabilar Issakar; Hosheya ɗan Nun, daga kabilar Efraim; daga kabilar Benyamin, Falti ɗan Rafu; Gaddiyel ɗan Sodi, daga kabilar Zebulun; Gaddi ɗan Susi, daga kabilar Manasse (wata kabilar Yusuf); Ammiyel ɗan Gemalli, daga kabilar Dan; Setur ɗan Mika’ilu, daga kabilar Asher; Nabi ɗan Bofsi, daga kabilar Naftali; Geyuwel ɗan Maki, daga kabilar Gad. Waɗannan su ne sunayen mutanen da Musa ya aika su binciki ƙasar. (Sai Musa ya ba Hosheya ɗan Nun, suna Yoshuwa.) Sa’ad da Musa ya aike su domin su binciki Kan’ana ya ce, “Ku haura, ku ratsa ta Negeb har zuwa ƙasar tudu. Ku ga yadda ƙasar take, ku ga ko mutanen da suke zama a can ƙarfafa ne, ko raunannu, ko su kima ne, ko kuma suna da yawa. Wace irin ƙasa ce suke zama a ciki, Mai kyau ce, ko mummuna? Waɗanne irin birane ne suke zama a ciki? Suna da katanga, ko babu? Yaya ƙasar take? Tana da wadata, ko babu? Akwai itatuwa, ko babu? Ku yi iya ƙoƙarinku ku ɗebo daga cikin albarkar ƙasar ku kawo.” (Lokacin farkon nunan inabi ne.) Saboda haka suka haura, suka binciki ƙasar daga Hamadan Zin har zuwa Rehob, wajen Lebo Hamat. Suka kuma haura ta Negeb, suka iso Hebron, inda Ahiman, da Sheshai, da Talmai, zuriyar Anak, suke zama. (An gina Hebron da shekara bakwai kafin a gina Zowan a Masar.) Da suka iso Kwarin Eshkol, sai suka yanko reshe guda na nonon inabi tare da ’ya’yansa cunkus. Mutum biyu suka ɗauka shi rataye a sanda a kafaɗarsu, suka haɗa tare da rumman da kuma ɓaure. Sai aka kira wurin Kwarin Eshkol saboda nonon inabin da suka yi cunkus, wanda Isra’ilawa suka yanko a wurin. A ƙarshen kwana arba’in sai suka komo daga bincikensu. Suka dawo wurin Musa, da Haruna, da dukan jama’ar Isra’ilawa, a Kadesh, a Hamadan Faran. A can suka ba da rahoton ga dukan taron da yake wurin, suka kuma nuna musu amfanin ƙasar. Suka ce wa Musa, “Mun je ƙasar da ka aike mu, ƙasar tana zub da madara da zuma! Ga kuma amfaninta. Amma fa mazaunan can ɗin ƙarfafa ne, an kuma kewaye biranen da manya-manyan katanga. Mun kuma ga zuriyar Anak a can. Amalekawa suna zama a Negeb; Hittiyawa, Yebusiyawa da kuma Amoriyawa, suna zama ne a ƙasar tudu. Kan’aniyawa kuma suna zama kusa da teku da kuma a bakin Urdun.” Sai Kaleb ya sa mutane suka yi shiru a gaban Musa, sai ya ce, “Ya kamata mu tafi mu mallaki ƙasar, gama lalle za mu iya cinta.” Amma sauran mutanen da suka je tare da shi, suka ce, “Ba za mu iya kara da mutanen nan ba; sun fi mu ƙarfi.” Sai suka yaɗa labari marar kyau ga Isra’ilawa game da ƙasar da suka binciko. Suka ce, “Ƙasar da muka ratsa cikinta domin mu leƙi asirinta, tana cinye waɗanda suke zama a cikinta. Dukan mutanen da muka gani a wurin, ƙatti ne. Mun ga Nefilimawa a can (zuriyar Anak sun fito ne daga Nefilim). Sai muka ga kanmu kamar fāra ne kawai, haka kuwa muke a gare su.” A daren nan, sai dukan jama’ar suka tā da murya, suka yi kuka da ƙarfi. Dukan Isra’ilawa suka yi gunaguni a kan Musa da Haruna, dukan taron kuwa suka ce musu, “Da ma mun mutu a Masar! Ko kuma a wannan hamada ma! Don me Ubangiji yana kawo mu wannan ƙasa yă bar mu kawai mu mutu da takobi? A kuma kwashe matanmu da ’ya’yanmu ganima. Ashe, bai fi mana mu koma Masar ba?” Sai suka ce wa junansu, “Mu naɗa wa kanmu shugaba, mu koma Masar.” Sai Musa da Haruna suka fāɗi rubda ciki a gaban jama’ar Isra’ilawa da suka taru a can. Yoshuwa ɗan Nun da Kaleb ɗan Yefunne waɗanda suke tare da masu leƙo asirin ƙasar, suka yayyage tufafinsu suka ce wa dukan taron Isra’ilawa, “Ƙasar da muka ratsa, muka kuma leƙi asirinta, tana da kyau sosai. In Ubangiji ya ji daɗinmu, zai kai mu ƙasan nan, ƙasar da take zub da madara da zuma, yă kuwa ba mu ita. Sai dai kada ku tayar wa Ubangiji. Kada kuma ku ji tsoron mutane ƙasar, domin za mu gama da su. Kāriyarsu ta gama, amma Ubangiji yana nan tare da mu. Kada ku ji tsoronsu.” Amma taron jama’a suka ce za su jajjefe su da duwatsu. Sai ɗaukakar Ubangiji ta bayyana a Tentin Sujada ga dukan Isra’ilawa. Ubangiji ya ce wa Musa, “Har yaushe mutanen nan za su rena ni? Har yaushe za su ƙi gaskata da ni, duk da yawan mu’ujizan da nake yi a cikinsu? Zan buge su duka da annoba, in hallaka su, amma zan mai da kai al’umma mai girma, da kuma ƙarfi fiye da su.” Sai Musa ya ce wa Ubangiji, “Ai, Masarawa za su ji game da wannan! Da ikonka ka fitar da mutanen nan daga cikinsu. Za su kuwa gaya wa mutanen wannan ƙasa. Sun riga sun ji cewa kai, ya Ubangiji, kana tare da waɗannan mutane, kuma cewa kai, ya Ubangiji, an gan ka fuska da fuska, cewa girgijenka ya tsaya bisansu, cewa kana tafiya a gabansu cikin ginshiƙin girgije da rana, da ginshiƙin wuta kuma da dare. In ka kashe dukan mutanen nan gaba ɗaya, al’ummai da suka ji wannan labari game da kai za su ce, ‘ Ubangiji ya kāsa kai waɗannan mutane a ƙasar da ya yi alkawari da rantsuwa ne, shi ya sa ya kashe su a hamada.’ “Yanzu bari Ubangiji yă nuna ikonsa, kamar dai yadda ka furta. ‘ Ubangiji mai jinkiri fushi ne, mai yawan ƙauna, mai gafarta zunubi da tawaye. Duk da haka ba ya ƙyale mai laifi, babu horo. Yana horin ’ya’ya saboda zunubin iyayensu har tsara ta uku, da ta huɗu.’ Bisa ga ƙaunarka mai girma, ka gafarta zunubin mutanen nan, kamar dai yadda ka gafarta musu daga lokacin da suka bar Masar har zuwa yanzu.” Ubangiji ya amsa ya ce, “Na gafarta musu, yadda ka roƙa. Duk da haka, muddin ina raye, kuma muddin ɗaukakar Ubangiji ta cika dukan duniya, ko ɗaya daga cikinsu da suka ga ɗaukakata da mu’ujizai da na yi a Masar, da kuma a cikin hamada, da suka ƙi yin mini biyayya, suka kuma gwada ni har sau goma, ba ko ɗayansu da zai gan ƙasar da na yi alkawari da rantsuwa zan ba wa kakanninsu. Ba ko ɗaya da ya rena ni, da zai taɓa ganinta. Amma domin Kaleb bawana ya kasance da ruhu dabam, ya kuma bi ni da zuciya ɗaya, zan kai shi cikin ƙasar da ya je, zuriyarsa kuwa za su gāje ta. Da yake Amalekawa da Kan’aniyawa suna zama a kwarin, gobe sai ka koma baya, ka nufi wajen hamada ta hanyar Jan Teku.” Ubangiji ya ce wa Musa da Haruna, “Har yaushe wannan muguwar al’umma za tă yi gunaguni a kaina? Na ji koke-koken waɗannan Isra’ilawa masu gunaguni. Saboda haka ka gaya musu cewa, ‘Muddin ina raye, in ji Ubangiji, zan yi muku daidai da abin da na ji kuke faɗa. A cikin wannan hamadan, jikunanku za su fāɗi, kowanne a cikinku mai shekara ashirin ko fiye, wanda aka ƙirga shi cikin ƙidaya, wanda kuma ya yi gunaguni a kaina, da zai shiga wannan ƙasa. Ba ko ɗaya daga cikinku da zai shiga ƙasar da na ɗaga hannu na rantse, za tă zama gidanku, sai dai Kaleb ɗan Yefunne da Yoshuwa ɗan Nun. Amma game da ’ya’yanku da kuka ce za a kwashe ganima, zan kawo su cikin ƙasar, su ji daɗin ƙasar wadda kuka ƙi. Amma ku, jikunanku za su fāɗi a wannan hamada. ’Ya’yanku za su zama makiyaya a nan, shekaru arba’in suna shan wahala domin rashin amincinku, har sai mutum na ƙarshe a cikinku ya kwanta a hamada. Shekaru arba’in, shekara ɗaya a madadi kwana ɗaya cikin kwanakin arba’in da kuka ɗauka kuka leƙi asirin ƙasa, za ku sha wahala saboda zunubanku, ku kuma san abin da ake nufi da sa ni in yi gāba da ku.’ Ni, Ubangiji na faɗa, zan kuwa aikata waɗannan abubuwa a kan dukan muguwar jama’an nan da suka haɗa kai, suka tayar mini. Za su sadu da ƙarshensu a wannan hamada; a nan za su mutu.” Saboda haka mutanen da Musa ya aika, su leƙo asirin ƙasar, waɗanda suka komo, suka sa taron jama’a su yi gunaguni a kansa saboda sun kawo rahoto mai banrazana a kan ƙasar, waɗannan mutanen da suka kawo rahoto mai banrazana a kan ƙasar, annoba ta buge su, suka kuwa mutu a gaban Ubangiji. Daga cikin mutanen da suka leƙo asirin ƙasar, Yoshuwa ɗan Nun, da Kaleb ɗan Yefunne ne, kaɗai suka rayu. Da Musa ya gaya wa dukan Isra’ilawa wannan labari, sai suka yi baƙin ciki ƙwarai. Kashegari da sassafe suka haura ta wajen ƙasa mai tudu suka ce, “Mun yi zunubi, za mu tafi inda Ubangiji ya yi alkawari.” Amma Musa ya ce, “Don me kuke rashin biyayya da umarnin Ubangiji? Wannan ba zai yiwu ba! Kada ku haura, domin Ubangiji, ba ya tare da ku. Magabtanku za su ci nasara a kanku, gama Amalekawa da Kan’aniyawa za su kara da ku a can. Domin kun juya daga Ubangiji, ba zai kasance da ku ba, za a kuma karkashe ku da takobi.” Duk da haka, suka yi tsammani ba zai zama haka ba, sai suka haura ta wajen ƙasa mai tudu, Musa da akwatin alkawarin Ubangiji dai ba su gusa daga sansanin ba. Sai Amalekawa da Kan’aniyawa mazaunan ƙasar tudu, suka gangaro suka auka musu, suka bubbuge su suka kokkore su har Horma. Ubangiji ya ce wa Musa, “Ka yi magana da Isra’ilawa, ka ce musu, ‘Bayan kun shiga ƙasar da nake ba ku a matsayin gida, kuka yi hadayar da akan yi da wuta ga Ubangiji, daga cikin shanu, ko tumaki, abin ƙanshi mai daɗi ga Ubangiji, ko hadaya ta ƙonawa, ko hadayu don alkawura na musamman, ko hadayar yardar rai, ko kuma hadaya ta biki, sai shi wanda ya kawo hadayar yă miƙa wa Ubangiji hadaya ta gari mai laushi mai kyau, kashi ɗaya bisa goma na efa wanda aka kwaɓa da kwalaba ɗaya na mai. Da kowane ɗan rago don hadaya ta ƙonawa, a shirya kwalaba ɗaya na ruwan inabi, a matsayin hadaya ta sha. “ ‘In da rago ne za a miƙa, to, sai a shirya hadaya ta gari mai laushi, garin yă zama kashi biyu bisa goma na efa. A kwaɓa shi da kashi ɗaya bisa uku na garwan mai, da kashi ɗaya bisa uku na garwan ruwan inabi, a matsayin hadaya ta sha. A miƙa ta abin ƙanshi mai daɗi ga Ubangiji. “ ‘Sa’ad da kuka shirya rago don hadaya ta ƙonawa saboda alkawari na musamman, ko hadaya ta salama ga Ubangiji, sai ku kawo hadaya ta gari tare da bijimi, kashi ɗaya bisa uku na gari mai laushi kwaɓaɓɓe da rabin garwan mai. A kuma kawo rabin garwan ruwan inabi na hadaya ta sha. Za tă zama hadayar da aka yi da wuta mai daɗin ƙanshi ga Ubangiji. Haka za a yi da kowane bijimi, ko rago, ko ɗan rago, ko bunsuru. Haka za a yi da kowannensu bisa ga abin da aka shirya. “ ‘Duk wanda yake ɗan ƙasa, ta haka ne dole zai aikata waɗannan abubuwa sa’ad da ya kawo hadaya da akan yi da wuta mai daɗin ƙanshi ga Ubangiji. Idan baƙon da yake baƙunci a cikinku, ko kowane ne da yake tare da ku a dukan zamananku, yana so yă ba da hadayar da akan yi da wuta don a yi ƙanshi mai daɗi ga Ubangiji, dole yă yi kamar yadda kuke yi. Ƙa’ida ɗaya ce ga jama’a da kuma baƙin da suke zama a cikinku, wannan za tă zama dawwammamiyar farilla a dukan tsararraki masu zuwa. Da ku, da baƙi, za ku zama ɗaya a gaban Ubangiji. Doka ɗaya da ƙa’ida ɗaya za a yi aiki da ita a kan ku da kuma baƙin da suke zama a cikinku.’ ” Ubangiji ya ce wa Musa, “Ka yi magana da Isra’ilawa, ka ce musu, ‘Sa’ad da kuka shiga ƙasar da ina kai ku, kuka ci abincin ƙasar, ku miƙa wani sashe na amfanin ƙasar a matsayin hadaya ga Ubangiji. Ku kawo waina daga nunan fari na ɓarzajjen hatsinku, ku kuma miƙa shi a matsayin hadaya daga masussuka. A duk tsararraki masu zuwa, za ku miƙa wannan hadaya daga nunan fari na ɓarzajjen hatsinku ga Ubangiji. “ ‘To, in ku a matsayin jama’a, da gangan kuka ƙi kiyaye waɗannan ƙa’idodi da Ubangiji ya ba wa Musa ba, ko wani daga cikin umarnan da Ubangiji ya ba ku ta wurinsa, daga ranar da Ubangiji ya ba da su, har zuwa tsararraki masu zuwa, in kuwa aka yi haka ba da gangan ba, kuma da rashin sani, sai duk jama’a su miƙa ɗan bijimi don hadaya ta ƙonawa mai daɗin ƙanshi ga Ubangiji, tare da ƙayyadadden hadaya ta gari, da hadaya ta sha, da kuma bunsuru na hadaya don zunubi. Firist kuwa zai yi kafara domin dukan jama’ar Isra’ilawa, za a kuma gafarta musu, gama ba da gangan ba ne suka aikata, kuma sun kawo wa Ubangiji hadayar da akan yi da wuta da kuma hadaya don zunubi saboda laifinsu. Za a gafarta wa dukan jama’ar Isra’ilawa, da baƙin da suke zama a cikinsu, gama duk laifin da aka yi da rashin sani, yakan shafi dukan mutane. “ ‘Amma in mutum ɗaya ne kaɗai ya yi laifi ba da gangan ba, dole yă kawo akuya domin hadaya don zunubi. Firist zai yi kafara a gaban Ubangiji saboda mutumin nan da ya aikata laifi ba da gangan ba, in kuwa an yi kafara saboda shi, za a gafarta masa. Ƙa’ida dai za tă zama ɗaya ga duk wanda ya yi laifi ba da gangan ba, ko shi ɗan ƙasa ne, ko kuma baƙon da yake zama a cikinku. “ ‘Amma duk wanda ya yi zunubi da gangan, ko shi ɗan ƙasa ne, ko baƙo, ya saɓi Ubangiji, dole a ware wannan mutum daga mutanensa, gama ya rena maganar Ubangiji, ya kuma karya umarninsa. Tabbatacce za a kashe wannan mutum, alhakinsa laifinsa kuwa yana wuyansa.’ ” Yayinda Isra’ilawa suke ciki hamada, sai aka sami wani mutum yana tattara itace a ranar Asabbaci. Waɗanda suka gan shi, suka kawo shi wurin Musa da Haruna da dukan taro, sai suka sa shi a gidan waƙafi don ba su riga sun san abin da za a yi da shi ba tukuna. Sai Ubangiji ya ce wa Musa, “Dole mutumin yă mutu. Dole dukan taron su jajjefe shi a bayan sansani.” Saboda haka taron suka ɗauke shi zuwa bayan sansani, suka kuma jajjefe shi har ya mutu, yadda Ubangiji ya umarci Musa. Ubangiji ya ce wa Musa, “Ka yi magana da Isra’ilawa, ka ce musu, ‘A dukan tsararraki masu zuwa, za ku sa tuntaye a gefen rigunarku, su sa zare mai ruwan shuɗi a bisan kowane tuntu. Tuntayen za su zama muku abin dubawa don ku riƙa tunawa da dukan umarnan Ubangiji, don kada ku bi son zuciyarku, da sha’awar idanunku yadda kuka taɓa yi. Sa’an nan za ku riƙa tuna, ku kuma aikata dukan umarnaina ku zama tsarkaka ga Allahnku. Ni ne Ubangiji Allahnku, da ya fitar da ku daga Masar, don in zama Allahnku. Ni ne Ubangiji Allahnku.’ ” Kora ɗan Izhar, wanda yake Balawe ne daga dangin Kohatawa, wata rana ya nemi Datan da Abiram ’ya’yan Eliyab, da On ɗan Felet dukansu daga kabilar Ruben, suka haɗa kai suka tayar wa Musa. Sai suka nemi goyon bayan sanannun shugabannin Isra’ilawa da aka naɗa a majalisa su guda 250, tare kuwa suka zo wurin Musa da Haruna, suka ce musu, “Kun wuce gona da iri! Dukan jama’an nan masu tsarki ne, kowannensu, Ubangiji kuma yana tare da su. Me ya sa kuke ɗaukan kanku fiye da taron jama’ar Ubangiji?” Da Musa ya ji haka, sai ya fāɗi rubda ciki ya yi addu’a Sai ya ce wa Kora da dukan waɗannan da suke tare shi, “Da safe, Ubangiji zai nuna wane ne yake nasa, da kuma wane ne yake da tsarki. Zai kuma sa mutumin yă zo kusa da shi. Mutumin da ya zaɓa kuwa zai sa yă zo kusa da shi. Kai Kora da ƙungiyarka, gobe, za ku ɗauki farantai, ku zuba wuta a ciki, ku kuma zuba musu turaren wuta a gaban Ubangiji. Sa’an nan wanda Ubangiji ya zaɓa a tsakaninmu sh ne mai tsarki. Ku Lawiyawa ku ne kuka wuce gona da iri!” Musa ya kuma ce wa Kora, “Yanzu ku saurara, ku Lawiyawa! Ashe, bai ishe ku ba, cewa Allah na Isra’ila, ya keɓe ku daga sauran jama’ar Isra’ilawa, ya kuma kawo ku kusa da shi don ku yi aiki a tabanakul na Ubangiji, ku kuma tsaya a gaba jama’a don ku yi musu aiki? Ya kawo ku da kuma dukan ’yan’uwanku Lawiyawa kusa da shi, amma yanzu kuna ƙoƙari ku karɓi aikin firist. Kai da ƙungiyarka kun haɗa kai kuna yi wa Haruna gunaguni, amma wane ne Haruna? A zahiri tawaye ne kuke wa Ubangiji.” Sai Musa ya aika a kira Datan da Abiram, ’ya’yan Eliyab maza, amma suka ce, “Ba za mu zo ba! Bai isa ba ne da ka fitar da mu daga ƙasar mai zub da madara da zuma, ka kawo mu nan hamada don ka kashe mu? Yanzu kuma so kake ka mai da kanka sarki a bisanmu? Ban da haka ma, ai, ba ka riga ka kai mu ƙasar mai zub da madara da zuma ba, ba ka ba mu gādon filaye da gonakin annabi ba, yanzu kuma kana so ka ruɗe mu. Mun ƙi, ba za mun zo ba!” Sai Musa ya husata ƙwarai, ya ce wa Ubangiji, “Kada ka karɓi hadayarsu. Ban ƙwace wani jakinsu ba, ban kuwa cuce waninsu ba.” Musa ya ce wa Kora, “Da kai da kuma dukan ƙungiyarka za ku bayyana a gaban Ubangiji gobe, kai da su. Haruna ma zai kasance a can. Kowannenku zai ɗauki faranti yă zuba turare a ciki. Wato, farantai 250 ke nan, a kuma miƙa su a gaban Ubangiji. Kai da Haruna za ku miƙa farantanku, ku ma.” Sai kowane mutum ya ɗauki farantinsa, ya sa wuta da kuma turare a ciki, suka tsaya da Musa da Haruna a ƙofar Tentin Sujada. Sa’ad da Kora ya tara mabiyansa don su yi hamayya da Musa da Haruna a ƙofar Tentin Sujada, sai ɗaukakar Ubangiji ta bayyana ga dukan taron. Ubangiji ya ce wa Musa da Haruna, “Ku ware kanku daga taron nan don in gama da su nan take.” Amma Musa da Haruna suka fāɗi rubda ciki suka tā da murya suka ce, “Ya Allah, Allahn ruhohin dukan ’yan adam, za ka husata da dukan taron ne, bayan mutum ɗaya ne ya yi zunubi?” Sai Ubangiji ya ce wa Musa, “Faɗa wa taron cewa, ‘Ku nisanci tentin Kora, da na Datan, da na Abiram.’ ” Musa ya tashi ya tafi wurin Datan da Abiram, dattawan Isra’ilawa kuwa suka bi shi. Ya gargaɗe taron ya ce, “Ku ƙaurace wa tentin waɗannan mugayen mutane! Kada ku taɓa kome da yake nasu, domin kada a shafe ku saboda zunubansu.” Sai suka tashi daga inda tentin Kora, da Datan, da Abiram suke. Datan da Abiram kuwa suka fita suna tsaye tare da matansu da ’ya’yansu da ’yan ƙananansu a ƙofar tentinsu. Sai Musa ya ce musu, “Da haka za ku san cewa Ubangiji ne ya aiko ni, in yi dukan waɗannan abubuwa, ba da nufin kaina na yi su ba. In waɗannan mutane sun mutu kamar yadda mutane suke mutuwa, in abin da yakan sami kowa shi ne ya same su, to, ba Ubangiji ne ya aiko ni ba. Amma in Ubangiji ya kawo wani abu sabo, ya sa ƙasa ta buɗe bakinta, ta haɗiye su da dukan abin da suke da shi, suka gangara cikin kabari a raye, ta haka za ku sani mutanen nan sun rena Ubangiji.” Nan da nan da ya gama faɗi wannan, sai ƙasa ta tsage inda Datan da Abiram suke tsaye, ta kuma buɗe bakinta, ta haɗiye su tare da mutanen gidansu da dukan mutanen Kora da dukan abin da yake mallakarsu. Suka gangara cikin kabari da rai, tare dukan mallakarsu; ƙasa ta rufe su, suka hallaka, suka rabu da jama’ar. Da jin kukansu, dukan Isra’ilawa da suke kewaye da su suka gudu, suna ihu, “Ƙasa za tă haɗiye mu, mu ma!” Sai wuta ta fito daga wurin Ubangiji ta cinye mutane 250 da suke miƙa hadaya da turare. Ubangiji ya ce wa Musa, “Ka gaya wa Eleyazar ɗan Haruna, firist, yă kawar da farantan ƙona turare daga wurin da wutar ta cinye, yă watsar da gawayin a wani wuri, gama farantan tsarkakakku ne, gama an yi amfani da farantan don miƙa mini turare. Sai ka ɗauki farantan mutanen da suka yi zunubin da ya jawo musu mutuwa ka ƙera farantan, ka yi murfin bagade da su, gama an miƙa su a gaban Ubangiji, suka zama tsarkakakku. Bari su zama alama ga Isra’ilawa.” Haka Eleyazar, firist, ya tattara farantan tagulla waɗanda mutanen da aka hallaka suka kawo, ya ƙera murfin bagade da su, yadda Ubangiji ya umarce shi, ta wurin Musa. Wannan ya zama abin tuni ga Isra’ilawa domin kada wani da ba firist ba, bai kuwa fito a cikin zuriyar Haruna ba, yă zo don yă ƙona turare a gaban Ubangiji, domin kada yă zama kamar Kora da mabiyansa. Kashegari dukan taron Isra’ilawa suka yi gunaguni a kan Musa da Haruna suka ce, “Kun kashe mutanen Ubangiji.” Bayan haka, sai dukan jama’a suka taru domin su nuna rashin yardansu da abin da suke zato Musa da Haruna ne suka aikata. Da suka fuskanci Tentin Sujada, nan take sai girgije ya rufe shi, ɗaukaka Ubangiji kuwa ta bayyana. Sai Musa da Haruna suka je gaban Tentin Sujada, Ubangiji kuma ya ce wa Musa, “Ku nisanci wannan taro, gama yanzu nan zan hallaka su.” Sai Musa da Haruna suka fāɗi rubda ciki. Sai Musa ya ce wa Haruna, “Ka ɗauki farantinka ka sa turare a ciki, da wuta daga bagade, ka yi maza ka tafi wajen taron, ka yi kafara dominsu. Gama fushin Ubangiji ya riga ya sauko; an kuma fara annoba.” Saboda haka Haruna ya yi kamar yadda Musa ya faɗa, ya ruga a guje zuwa tsakiyar taron. An riga an fara annobar a cikin mutane, amma Haruna ya miƙa turaren ya kuma yi kafara dominsu. Ya tsaya tsakanin matattu da masu rai, annobar kuwa ta tsaya. Amma mutane 14,700 ne suka mutu a annobar, ban da waɗanda suka mutu a sanadin Kora. Sai Haruna ya komo wurin Musa a ƙofar Tentin Sujada, gama annobar ta ƙare. Ubangiji ya ce wa Musa, “Ka yi magana da Isra’ilawa, ka kuma karɓi sanduna goma sha biyu daga wurinsu, sanda guda daga kowane shugaban gidan kakanninsu. Ka rubuta sunan kowa a sandansa. A kan sandan Lawi kuwa ka rubuta sunan Haruna, gama dole a sami sanda ɗaya saboda shugaban gidan kakanninsu. Ka ajiye su a Tentin Sujada, a gaba akwatin Alkawari, inda zan sadu da kai. Sandan mutumin da na zaɓa zai yi toho, da haka zan raba kaina da gunagunin da Isra’ilawa suke yi.” Saboda haka Musa ya yi magana da Isra’ilawa, sai shugabanninsu suka ba shi sanduna goma sha biyu, sanda ɗaya don shugaba, bisa ga gidajen kakanninsu, sandan Haruna kuma yana a cikinsu. Sai Musa ya ajiye sandunan a gaban Ubangiji a cikin Tentin Sujada. Kashegari da Musa ya shiga cikin Tentin Sujada sai ga sandan Haruna na gidan Lawiyawa ya yi toho, ya yi furanni, ya kuma yi ’ya’yan almon. Sai Musa ya fitar wa dukan Isra’ilawa dukan sandunan da suke daga gaban Ubangiji. Suka duba, kowa kuma ya ɗauki sandansa. Ubangiji ya ce wa Musa, “Ka mayar da sandan Haruna a akwatin Alkawari, don a ajiye shi alama ga masu tawaye. Wannan zai kawo ƙarshen gunaguninsu a kaina, domin kada su mutu.” Musa kuwa ya aikata kamar dai yadda Ubangiji ya umarce shi. Sai Isra’ilawa suka ce wa Musa, “To, ai in haka ne, mun ƙare ke nan! Idan an ce duk wanda ya zo kusa da tabanakul na Ubangiji zai mutu, ai rayuwarmu kamar mun mutu ke nan.” Ubangiji ya ce wa Haruna, “Kai da ’ya’yanka, da kuma iyalin mahaifinka za ku ɗauki hakkin abin da ya shafi Tentin Sujada, kai da ’ya’yanka kaɗai za ku ɗauki hakkin aikinku wanda ya shafi firistoci. Ka kawo ’yan’uwanka Lawiyawa daga kabilar kakanka tare da kai, don su taimake ka sa’ad da kai da ’ya’yanka kuke hidima a gaban Tentin Sujada. Za su kasance a ƙarƙashinka, su ne kuma za su yi dukan hidima ta Tenti, amma kada su je kusa da kayayyakin wuri mai tsarki, ko bagade, in ba haka ba, da kai da su, za ku mutu. Za su haɗa hannu tare da kai su ɗauki nauyin lura da Tentin Sujada, dukan ayyuka a Tenti, ba kuma wanda zai zo kusa da inda kake. “Kai ne za ka ɗauki nauyin lura da wuri mai tsarki da bagade, domin kada fushi yă sāke fāɗa a kan Isra’ilawa. Ni da kaina na zaɓo ’yan’uwanka Lawiyawa daga cikin Isra’ilawa a matsayin kyauta a gare ku, keɓaɓɓu don Ubangiji, domin su yi hidima a Tentin Sujada. Amma kai ne kaɗai da ’ya’yanka za ku yi aiki a matsayin firistoci game da kowane abu a Tentin Sujada da kuma bayan labule. Ina ba ka aikin firist, yă zama naka. Duk wani kuma da ya zo kusa da wuri mai tsarki, dole a kashe shi.” Sai Ubangiji ya ce wa Haruna, “Na ba ka aikin lura da hadayun da za a miƙa mini, dukan tsarkakan hadayun da Isra’ilawa suka ba ni, na ba ka su su zama rabonka da na ’ya’yanka har abada. Kai za ka riƙe sashe mafi tsarki na hadayun da suka ragu daga wuta. Daga dukan kyautai mafi tsarki na hadayun da suka miƙa mini, ko ta gari, ko don zunubi, ko kuma don laifi, wannan kashi naka ne da ’ya’yanka. Ku ci shi a matsayin abu mafi tsarki; kowane namiji zai ci. Dole ku ɗauke shi da tsarki. “Har yanzu kuma duk abin da aka keɓe daga kyautai na dukan hadayun kaɗawa na Isra’ilawa naka ne. Na ba da wannan gare ka da ’ya’yanka maza da mata, a kowane lokaci. Kowa da yake da tsarki a gidanka zai iya ci. “Na ba ka duk man zaitun mafi kyau, da ruwan inabi mafi kyau duka, da hatsi mafi kyau duka na nunan farinsu da suke bayarwa ga Ubangiji. Dukan nunan fari na ƙasar da suke kawo wa Ubangiji, zai zama naka. Kowa da yake da tsarki a gidanka zai iya ci. “Kome a Isra’ila da aka keɓe wa Ubangiji, zai zama naka. Kowane haihuwar fari, ta mutum, ko ta dabba da suka miƙa wa Ubangiji, naka ne. Amma ka fanshi kowace haihuwar fari ta mutum, ko ta dabbar da take haram. Sa’ad da suke wata ɗaya da haihuwa, dole a fanshe su a bakin shekel biyar-biyar, bisa ga ma’aunin shekel na tsattsarkan wuri da ake amfani da shi, wanda nauyinsa ya kai gera ashirin. “Amma kada ka fanshe ɗan fari na saniya, tunkiya, ko akuya; gama suna da tsarki. Ka yayyafa jininsu a bisan bagade, ka kuma ƙone kitsensu kamar hadayar da ka yi da wuta, mai daɗin ƙanshi ga Ubangiji. Namansu zai zama naka, haka ma ƙirji na kaɗawa da cinyar dama za su zama naka. Kome da aka keɓe daga tsarkakakku hadayun da Isra’ilawa suka miƙa wa Ubangiji, na ba ka, da kai da ’ya’yanka maza da mata a matsayin zaunannen rabo. Wannan madawwamin alkawarin gishiri ne a gaban Ubangiji dominka da zuriyarka.” Ubangiji ya ce wa Haruna, “Ba ka da gādo a ƙasarsu, ba kuwa za ka sami rabo daga cikinsu ba; ni ne rabonka da gādonka a cikin Isra’ilawa. “Na ba wa Lawiyawa dukan zakka na Isra’ilawa a matsayin gādonsu, saboda aikin da suke yi yayinda suke hidima a Tentin Sujada. Daga yanzu zuwa gaba, kada Isra’ilawa su yi kusa da Tentin Sujada, in ba haka ba kuwa su sha hukuncin zunubinsu, su kuma mutu. Lawiyawa ne za su yi aikin Tentin Sujada, su kuma ɗauki nauyin kowane laifin da aka aikata a wurin. Wannan za tă zama dawwammamiyar farilla ce daga yanzu har tsararraki masu zuwa. Ba za su sami gādo a cikin Isra’ilawa ba. A maimako haka, na ba wa Lawiyawa zakka da Isra’ilawa suka kawo domin hadaya ga Ubangiji, a matsayin gādonsu. Shi ya sa na ce game da su, ‘Ba su da gādo a cikin Isra’ilawa.’ ” Ubangiji ya ce wa Musa, “Ka yi wa Lawiyawa magana, ka ce musu, ‘Sa’ad da kuka karɓi zakka daga Isra’ila da na ba ku gādo, dole ku miƙa kashi ɗaya bisa goma na wannan zakka a matsayin hadaya ga Ubangiji. Za a lissafta hadayarku kamar hatsin da aka sussuka daga masussuka, ko ruwan inabi daga wurin matsewar inabi. Ta haka za ku miƙa hadaya ga Ubangiji daga cikin dukan zakkar da kuka karɓa daga wurin Isra’ilawa. Daga waɗannan zakka kuwa dole ku ba Haruna firist rabon Ubangiji. Dole ku miƙa wa Ubangiji rabo mafi kyau da kuma sashi mafi tsarki na kowane abin da aka ba ku.’ “Ka faɗa wa Lawiyawa cewa, ‘Sa’ad da kuka miƙa sashi mafi kyau, za a lissafta shi a matsayin abin da ya fito daga masussuka, ko wurin matsewar ruwan inabi ne. Da kai da gidanka, za ku iya cin abin da ya rage a ko’ina, gama ladan aikinku ne a Tentin Sujada. Ta wurin miƙa masa sashi mafi kyau, ba za ku zama masu laifi a wannan batu ba; ta haka ba za ku ƙazantar da tsarkakakkun hadayu na Isra’ilawa ba, ba kuwa za ku mutu ba.’ ” Ubangiji ya ce wa Musa da Haruna, “Wannan ita ce ƙa’ida wadda Ubangiji ya umarta. Faɗa wa Isra’ilawa su kawo maka jan karsana marar lahani, ko marar aibi wadda ba a taɓa sa ta tă yi noma ba. Ka ba wa Eleyazar firist; a kuma kai ta bayan sansani, a yanka a gaban Eleyazar. Sa’an nan Eleyazar firist zai ɗiba jininta a yatsarsa, yă yayyafa sau bakwai wajen gaban Tentin Sujada. Sa’an nan a ƙone dukan karsanar, haɗe da fatarta, naman, jinin da kayan cikin, yayinda Eleyazar yake kallo. Firist zai ɗauki itacen al’ul, da hizzob, da jan ulu, yă jefa su a kan karsanar da ake ƙonewa. Bayan haka, dole firist yă wanke rigunarsa, yă kuma yi wanka. Sa’an nan zai iya shiga cikin sansani, amma zai kasance da ƙazanta har yamma. Dole mutumin da ya ƙone ta yă wanke rigunarsa, yă kuma yi wanka, shi ma zai kasance da ƙazanta har yamma. “Mutumin da yake da tsarki, zai tara tokar karsanar, yă sa ta a wurin da yake da tsabta a bayan sansani. Jama’ar Isra’ilawa ne za su adana shi don amfani a ruwan tsabtaccewa; wannan domin tsarkakewa ne daga zunubi. Dole mutumin da ya tara tokar karsanar yă wanke rigunarsa, zai kuwa kasance da ƙazanta har yamma. Wannan za tă zama dawwammamiyar farilla ta har abada ga Isra’ilawa, da kuma baƙin da suke zama a cikinsu. “Duk wanda ya taɓa gawa, zai kasance da ƙazanta har kwana bakwai. Dole yă tsarkake kansa da ruwa a rana ta uku, da kuma a rana ta bakwai; sa’an nan zai zama da tsarki. Amma in bai tsarkake kansa a rana ta uku da kuma a rana ta bakwai ba, ba zai kasance da tsarki ba. Duk wanda ya taɓa gawar wani, bai kuma tsarkake kansa ba, ya ƙazantar da tabanakul na Ubangiji ke nan. Dole a ware wannan mutum daga cikin Isra’ilawa. Gama ba a yayyafa ruwan tsabtaccewa a kansa ba; ya ƙazantu, ya kasance da ƙazanta ke nan. “Ga ƙa’idar da za a bi in mutum ya mutu a cikin tenti. Duk wanda ya shiga tentin, kuma duk wanda yake cikinsa, za su zama da ƙazanta har kwana bakwai, kuma kowane abin da ake zuba kaya, wanda ba shi da murfi a kansa, zai zama da ƙazanta. “Wanda duk yake a fili, ya kuma taɓa gawa wanda aka kashe da takobi, ko wanda ya mutu mutuwar Allah, ko ƙashin mutum, ko kabari, zai ƙazantu har bakwai. “Ga wanda ya ƙazantu kuwa, a ɗiba toka daga hadaya ta ƙonawa ta tsarkakewa, a zuba a cikin tulu, sa’an nan a zuba ruwa mai gudu a kansu. Sa’an nan wanda yake tsarkakakke, zai ɗauki hizzob yă tsoma a ruwa, yă yayyafa a tentin da dukan kayayyakinsa, da kuma a kan mutanen da suke wurin. Dole kuma yă yayyafa ruwan a kan duk wanda ya taɓa ƙashin mutu, ko kabari, ko kuma wanda aka kashe, ko wanda ya yi mutuwa ta Allah. A rana ta uku, da ta bakwai kuma mai tsarkakewa zai yayyafa wa marar tsarkin ruwa, a rana ta bakwai kuma yă tsarkake shi. Wanda aka tsarkaken kuwa, dole yă wanke rigunarsa, yă kuma yi wanka da yamma, zai kuma tsarkaka. Amma in wanda yake da ƙazanta bai tsarkake kansa ba, dole a ware shi daga cikin jama’a, domin ya ƙazantar da wuri mai tsarki na Ubangiji. Ba a yayyafa masa ruwa na tsarkakewa ba, ya zama da ƙazanta. Wannan za tă zama musu dawwammamiyar farilla. “Mutumin da ya yayyafa ruwa na tsarkakewa, shi ma dole yă wanke rigarsa. Duk wanda kuma ya taɓa ruwan tsarkakewa, zai kasance da ƙazanta har yamma. Duk abin da mai ƙazanta ya taɓa, ya ƙazantu, kowa kuma ya taɓa wannan abu, ya ƙazantu ke nan, har yamma.” A watan fari, dukan jama’ar Isra’ilawa suka iso Hamadan Zin. Suka sauka a Kadesh. A nan ne Miriyam ta mutu, aka kuma bizne ta. Sai aka rasa ruwa da jama’a za su sha, mutane suka taru, suka tayar wa Musa da Haruna. Suka yi gunaguni wa Musa suka ce, “Da ma mun mutu sa’ad da ’yan’uwanmu suka mutu a gaban Ubangiji! Don me ka kawo jama’ar Ubangiji a wannan hamada, don mu da dabbobinmu mu mutu a nan ke nan? Don me ka fitar da mu daga Masar zuwa wannan banzan wuri, inda babu hatsi ko ɓaure, inabi ko rumman. Kuma babu ruwan da za a sha?” Sai Musa da Haruna suka tashi daga taron, suka tafi ƙofar Tentin Sujada, suka fāɗi rubda ciki, sai ɗaukakar Ubangiji ta bayyana musu. Ubangiji ya ce wa Musa, “Ka ɗauki sandanka, kai da Haruna, ɗan’uwanka, ku tara jama’a, ku yi magana da dutsen a gabansu ya ba da ruwan da yake cikinsa. Za ka sa ruwa ya ɓuɓɓugo musu daga dutsen. Ta haka za ka ba taron jama’a da garkunansu ruwan sha.” Sai Musa ya je ya ɗauki sandan kamar yadda Ubangiji ya umarce shi. Shi da Haruna, suka tara jama’a a gaban dutsen, Musa ya ce musu, “Ku saurara, ku ’yan tawaye, dole mu kawo muku ruwa daga wannan dutse?” Sai Musa ya ɗaga hannu, ya bugi dutsen sau biyu da sandansa. Ruwa kuwa ya yi ta kwararowa, jama’a da dabbobinsu suka sha. Amma Ubangiji ya ce wa Musa da Haruna. “Tun da yake ba ku gaskata ni ba, ba ku kuwa ɗaukaka ni a idon Isra’ilawa ba, to, ba za ku kai taron jama’an nan a ƙasar da na ba su ba.” Waɗannan su ne ruwan Meriba, inda Isra’ilawa suka yi wa Ubangiji gunaguni, inda kuma ya nuna kansa mai tsarki a cikinsu. Musa ya aiki manzanni daga Kadesh zuwa wurin sarkin Edom cewa, “Ga abin da ɗan’uwanka Isra’ila ya ce ka san duk irin wahalolin da ya same mu. Kakanninmu sun gangaro zuwa Masar, muka zauna can shekaru da yawa. Masarawa suka wulaƙanta mu, da kuma kakanninmu, amma da muka yi kuka a gaban Ubangiji, ya kuwa ji mu, sai ya aiko mala’ika, ya fitar da mu daga Masar. “Yanzu ga mu a Kadesh, garin da yake kan iyakar yankinka. Muna roƙonka, ka yarda mana mu bi ta ƙasarka. Ba za mu bi ta wani fili, ko gonar inabi ba, ko mu sha ruwa daga wata rijiya ba. Za mu bi ta babban hanyar sarki, ba kuwa za mu kauce dama, ko hagu ba, har mu wuce yankinka.” Amma Edom ya amsa ya ce, “Ba za ku bi ta nan ba; in kuka kuskura, za mu fito, mu yaƙe ku da takobi.” Sai Isra’ilawa suka amsa, suka ce, “Za mu bi ta babbar hanya, in mu, ko dabbobinmu suka sha ruwanku, za mu biya. Mu dai muna so mu wuce ne kawai.” Sai mutanen Edom suka sāke amsa suka ce, “Ba za ku bi nan ba dai.” Sai Edom ya fito da runduna mai ƙarfi da yawa gaske a kan Isra’ila. Da yake Edom suka ƙi su bar su su ratsa yankinsu, sai Isra’ila suka juya suka janye daga gare su. Dukan Jama’ar Isra’ilawa suka tashi daga Kadesh, suka zo Dutsen Hor. A Dutsen Hor, kusa da iyakar Edom, Ubangiji ya ce wa Musa da Haruna, “Haruna zai rasu. Ba zai shiga ƙasar da na ba Isra’ilawa ba, domin ku biyu, kun ƙi ku bi umarnina a ruwan Meriba. Ka kawo Haruna da ɗansa Eleyazar, ka kai su a bisan Dutsen Hor. Ka tuɓe taguwar Haruna ka sa wa ɗansa Eleyazar, gama Haruna zai rasu a can.” Musa ya yi yadda Ubangiji ya umarta. Suka hau Dutsen Hor a idon dukan jama’a. Musa ya tuɓe taguwar Haruna, ya kuma sa wa Eleyazar ɗan Haruna. Nan kuwa Haruna ya mutu a bisa dutsen. Sa’an nan Musa da Eleyazar suka sauka daga dutsen, sa’ad da dukan jama’a kuwa suka ji cewa Haruna ya mutu, sai dukan gidan Isra’ila suka yi makoki dominsa har kwana talatin. Sa’ad da sarkin Arad, mutumin Kan’ana, wanda yake zaune a Negeb, da ya ji cewa Isra’ila yana zuwa ta hanyar Atarim, sai ya fito, yă yaƙi Isra’ilawa, yă kuma kama waɗansunsu. Sai Isra’ila suka yi alkawari wa Ubangiji suka ce, “In ka ba da waɗannan mutane a hannunmu, za mu hallaka dukan garuruwansu ƙaf.” Ubangiji kuwa ya saurari kukan Isra’ila, ya kuma ba da Kan’aniyawa a gare su. Suka hallaka su da biranensu ƙaf; saboda haka aka sa wa wurin suna Horma. Suka kama hanya daga Dutsen Hor ta hanya zuwa Jan Teku, don su kauce wa Edom. Amma mutane suka rasa haƙuri a hanya; suka yi wa Allah da Musa gunaguni, suka ce, “Me ya sa kuka fitar da mu daga Masar, kuka kawo mu mu mutu a wannan hamada? Babu abinci! Babu ruwa! Mu dai mun gaji da wannan abinci marar amfani!” Sai Ubangiji ya aiko da macizai masu dafin a cikinsu, suka sassari mutane, Isra’ilawa masu yawa kuwa suka mutu. Mutanen suka zo wurin Musa, suka ce, “Mun yi zunubi, da muka yi wa Ubangiji da kai gunaguni. Ka yi addu’a don Ubangiji yă ɗauke mana macizan nan.” Saboda haka Musa ya yi addu’a domin mutane. Ubangiji ya ce wa Musa, “Ka ƙera siffar maciji ka rataye shi a bisa doguwar sanda; kowa da maciji ya sare shi, idan ya dubi macijin nan da ka rataye, zai rayu.” Saboda haka Musa ya ƙera macijin tagulla, ya kuma rataye shi bisa doguwar sanda. Sa’an nan duk wanda maciji ya sare shi, ya kuma dubi macijin tagullar, zai warke. Isra’ilawa suka kama hanya, suka yi sansani a Obot. Sai suka tashi daga Obot, suka yi sansani a Iye Abarim a hamadar da take fuskantar Mowab, wajen fitowar rana. Daga nan kuma suka ci gaba, suka yi sansani a Kwarin Zered. Suka tashi daga nan, suka sauka kusa da Arnon wanda yake a hamadar da ta miƙe zuwa iyakar Amoriyawa. Arnon shi ne iyakar Mowab, wanda yake tsakanin Mowab da Amoriyawa. Shi ya sa Littafin Yaƙoƙin Ubangiji ya ce, “Waheb ta cikin yankin Sufa, da kwaruruka na tuddan Arnon, da gangaren kwaruruka, wanda ya nausa zuwa garin Ar, ya kuma dangana da kan iyakar Mowab.” Daga can, suka gangara zuwa Beyer, wato, rijiyar da Ubangiji ya ce wa Musa, “Ka tattara mutane duka, zan kuwa ba su ruwa.” Sai Isra’ilawa suka rera wannan waƙa, “Ki ɓuɓɓugo da ruwa, Ke rijiya! Rera waƙa game da ita, game da rijiyar da ’ya’yan sarki suka haƙa, rijiyar da manyan mutane masu sandunan sarauta suka nuna da sandunansu.” Sa’an nan suka tashi daga hamadar, suka tafi Mattana, daga Mattana, suka tafi Nahaliyel, daga Nahaliyel, suka tafi Bamot, daga Bamot kuma suka tafi kwarin da yake cikin Mowab inda ƙwanƙolin Fisga yake fuskantar hamada. Isra’ila suka aiki manzanni wurin Sihon sarkin Amoriyawa su ce, “Ka bari mu ratsa ta ƙasarka. Ba za mu shiga wata gona ba, ba za mu kuma shiga gonar inabi, ko mu sha ruwa daga wata rijiya ba. Za mu bi ta babbar hanyar sarki, har mu fita ƙasarka.” Amma Sihon bai bar Isra’ila su ratsa ta yankinsa ba. Sai ya tara dukan sojojinsa, suka fita zuwa cikin hamada, su yaƙi Isra’ila. Da ya kai Yahaz, sai ya yaƙi Isra’ila. Isra’ila fa suka kashe shi da takobi, suka ƙwace ƙasarsa, tun daga kogin Arnon har zuwa kogin Yabbok, zuwa kan iyakar Ammonawa kawai, gama sun yi wa iyakansu katanga. Isra’ila suka ci dukan biranen Amoriyawa, suka kuma zauna a cikinsu, haɗe da babban birnin Heshbon da dukan ƙauyukanta. Sihon sarkin Amoriyawa ya yi mulkin Heshbon, bayan ya ci sarkin Mowab na dā da yaƙi, ya kuma ƙwace dukan ƙasarsa har zuwa arewancin kogin Arnon. Shi ya sa Amoriyawa suka rubuta wannan waƙa game da Heshbon suka ce, “Ku zo mu sāke gina Heshbon, birnin Sihon. “Mayaƙansa sun fito kamar harshen wuta suka ƙone birnin Ar na Mowab suna hallaka ’yan ƙasar tuddan Arnon. Kaitonki, Mowab! Gunkinki Kemosh ya yashe mutanenki; aka kuma kama su, aka kai su bauta wajen Sihon sarkin Amoriyawa. “Amma mun tumɓuke su, mun hallaka garuruwan Heshbon har zuwa Dibon. Mun ragargaza su har zuwa Nofa wanda ya miƙe zuwa Medeba.” Ta haka Isra’ila suka zauna a ƙasar Amoriyawa. Sai Musa ya aika ’yan leƙen asiri zuwa Yazer. Daga baya, sai Isra’ilawa suka ci ƙauyukan da suke kewaye, suka kuma kori Amoriyawa da suke zaune a can. Sai suka juya suka haura kan hanya ta zuwa Bashan, inda Og yake sarauta, ya kuwa fito tare da dukan sojojinsa suka yi yaƙi da Isra’ila a Edireyi. Ubangiji ya ce wa Musa, “Kada ka ji tsoronsa, gama na ba da shi a gare ka, da dukan sojojinsa da kuma ƙasarsa. Ka yi da shi yadda ka yi da Sihon sarkin Amoriyawa, wanda ya yi mulki a Heshbon.” Ta haka suka kashe shi, tare da ’ya’yansa maza da kuma dukan sojojinsa, ba wanda ya ragu. Suka kuma mamaye ƙasarsa. Sai Isra’ilawa suka kama hanya, suka tafi filayen Mowab, a wajen Urdun, a ƙetare Yeriko, suka yi sansani a can. To, fa, Balak ɗan Ziffor ya ga duk abin da Isra’ila suka yi da Amoriyawa. Sai Mowab ya firgita ƙwarai saboda yawan mutanen. Tsoron Isra’ilawa ya kama su. Sai Mowabawa suka ce wa dattawan Midiyawa, “Wannan taron zai lashe duk abin da ya kewaye mu kamar yadda saniya takan lashe ciyawa a fili.” Saboda haka Balak ɗan Ziffor, wanda yake sarkin Mowab a lokacin, ya aika manzanni su zo da Bala’am ɗan Beyor, wanda yake a Fetor, kusa da Kogi, a ƙasar haihuwarsa. Balak ya ce, “Ga mutane sun fito daga Masar; sun mamaye ƙasar, suka kuma yi sansani kusa da ni. Ka zo yanzu ka la’anta waɗannan mutane, domin sun fi ƙarfina. Wataƙila zan iya cin nasara a kansu, in kuma kore su daga ƙasar. Gama na sani duk waɗanda ka sa musu albarka, sun zama masu albarka ke nan, waɗanda kuma ka la’anta, sun la’antu ke nan.” Sai dattawan Mowab da na Midiyawa suka tashi, suka ɗauki kuɗi don duba. Da suka zo wurin Bala’am sai suka faɗa masa abin da Balak ya ce. Bala’am ya ce musu, “Ku kwana a nan, ni kuwa zan faɗa muku abin da Ubangiji ya faɗa mini.” Saboda haka dattawan sarkin Mowab suka zauna da shi. Sai Allah ya zo wurin Bala’am ya ce, “Su wane ne waɗannan tare da kai?” Bala’am ya ce wa Allah, “Balak ɗan Ziffor, sarkin Mowab ne, ya aiko mini wannan saƙo cewa, ‘Ga mutane sun fito daga Masar sun mamaye ƙasar. Ka zo yanzu ka la’anta mini su. Wataƙila ta haka zan yi nasara a kansu, in kuma kore su.’ ” Amma Allah ya ce wa Bala’am, “Kada ka tafi tare da su. Kada ka la’anta mutanen nan, gama su masu albarka ne.” Kashegari Bala’am ya tashi ya ce wa dattawan Balak, “Ku koma ƙasarku, domin Ubangiji ya hana ni in tafi tare da ku.” Saboda haka dattawan Mowab suka koma wurin Balak suka ce, “Bala’am ya ƙi yă zo tare da mu.” Sai Balak ya aika waɗansu dattawa masu yawa, masu daraja kuma fiye da na dā. Suka zo wurin Bala’am suka ce, “Ga abin da Balak ɗan Ziffor ya ce, Kada ka bar wani abu yă hana ka zuwa wurina, gama zan ba ka lada mai yawa in kuma yi duk abin da ka ce. Ka zo ka la’anta mini waɗannan mutane.” Amma Bala’am ya amsa musu ya ce, “Ko da a ce Balak zai ba ni gidansa cike da azurfa da zinariya, ba zan yi wani abu ko kaɗan saɓanin umarnin Ubangiji Allahna ba. To, fa, sai ku kwana a nan kamar yadda waɗancan suka yi, ni kuma in roƙi Ubangiji, in ji, wace magana zai ce mini.” A wannan dare, Allah ya zo wurin Bala’am ya ce, “Da yake waɗannan mutane sun zo su tafi da kai, to, ka tafi tare da su, sai dai ka yi abin da na ce ka yi ne kaɗai.” Bala’am ya tashi da safe, ya ɗaura wa jakarsa sirdi, ya tafi tare da dattawan Mowab. Amma Allah ya husata sa’ad da ya tafi, mala’ikan Ubangiji kuwa ya tsaya a hanya don yă hana shi. Bala’am kuwa yana kan jakarsa tare da bayinsa biyu. Da jakar ta hangi mala’ikan Ubangiji tsaye a hanya da takobi a hannunsa, sai ta kauce daga hanya, ta shiga jeji. Bala’am kuwa ya buge ta don tă koma hanya. Sai mala’ikan Ubangiji ya tsaya a wata matsattsiyar hanya tsakanin gonaki inabi biyu, da bango a kowane gefe. Sa’ad da jakar ta ga mala’ikan Ubangiji, sai ta matse a jikin bango, ta goge ƙafar Bala’am da bangon. Saboda haka sai Bala’am ya sāke bugunta. Sai mala’ikan Ubangiji ya sha gabansa, ya tsaya a ƙunƙuntaccen wuri inda ba wurin juyawa dama ko hagu. Da jakar ta ga mala’ikan Ubangiji, sai ta kwanta a ƙasa, Bala’am kuwa ya husata, sai ya buge ta da sandansa. Ubangiji ya buɗe bakin jakar, sai jakar ta ce wa Bala’am, “Me na yi maka da ka buge ni har sau uku?” Bala’am ya ce wa jakar “Domin kin wulaƙanta ni! Da a ce ina da takobi a hannuna da zan kashe ki nan take.” Jakar ta ce wa Bala’am, “Ni ba jakarka ba ce wadda kake hawa kullum, har yă zuwa yau? Na taɓa yin maka haka?” Bala’am ya ce, “A’a.” Sa’an nan Ubangiji ya buɗe idanun Bala’am, ya kuwa ga mala’ikan Ubangiji tsaye a hanya da takobi a zāre. Sai ya sunkuyar da kansa, ya fāɗi rubda ciki. Sa’an nan mala’ikan Ubangiji ya tambaye shi, “Don me ka buge jakarka har sau uku? Na fito ne don in hana ka, gama hanyarka ba daidai ba ce a gabana. Jakar ta gan ni, ta kauce mini har sau uku. Da a ce ba tă kauce ba, lalle da na kashe ka, in kuwa bar ta da rai.” Bala’am ya ce wa mala’ikan Ubangiji, “Na yi zunubi. Ban san ka tsaya a hanya don ka hana ni ba. Yanzu in ba ka ji daɗin tafiyata, sai in koma.” Mala’ikan Ubangiji ya ce wa Bala’am, “Ka tafi tare da mutanen, amma abin da na faɗa maka ne kaɗai za ka faɗa.” Saboda haka Bala’am ya tafi tare da dattawan Balak. Da Balak ya ji cewa Bala’am yana zuwa, sai ya fito, ya tarye shi a garin Mowabawa da suke a iyakar Arnon, a ƙarshen yankinsa. Balak ya ce wa Bala’am, “Ban aika maka saƙo cikin gagawa ba? Me ya sa ba ka zo ba? Ko ban isa in sāka maka ba ne?” Bala’am ya amsa ya ce, “To, ai, ga shi, na zo yanzu. Ina da wani ikon yin wata magana ne? Dole in faɗa abin da Allah ya ce in faɗa ne kawai.” Sa’an nan Bala’am ya tafi tare da Balak zuwa Kiriyat-Huzot, a can ya yi hadaya da shanu da tumaki, ya kuwa aika wa Bala’am da dattawan da suke tare da shi. Kashegari, Balak ya ɗauki Bala’am ya kai shi kan Bamot Ba’al, daga can ya iya ganin sassan sansanin Isra’ilawa. Bala’am ya ce, “Ka gina mini bagadai bakwai a nan, ka shirya mini bijimai bakwai da raguna bakwai.” Balak ya yi yadda Bala’am ya faɗa, sai su biyu suka miƙa bijimi da rago a kan kowane bagade. Sa’an nan Bala’am ya ce wa Balak, “Tsaya nan kusa da hadayarka, ni kuwa in koma wani wurin da yake a kaɗaice. Wataƙila Ubangiji zai sadu da ni. Duk abin da ya bayyana mini, zan faɗa maka.” Sai ya haura kan wani wurin da yake a kaɗaice a tudun. Allah kuwa ya sadu da Bala’am. Bala’am ya ce, “Na shirya bagadai bakwai, na kuma miƙa bijimi guda da rago guda, a kan kowane bagade.” Ubangiji ya ba wa Bala’am saƙo ya ce, “Ka koma wurin Balak, ka faɗa masa wannan saƙo.” Saboda haka, sai Bala’am ya koma wurin Balak ya same shi tsaye a kusa da hadayarsa, tare da dukan dattawan Mowab. Sai Bala’am ya furta abin da Allah ya faɗa masa ya ce, “Balak ya kawo ni daga Aram, sarkin Mowab ya kawo ni daga gabashin duwatsu. Ya ce, ‘Zo, ka la’anta mini Yaƙub; zo, ka tsine Isra’ila.’ Yaya zan iya la’anta waɗanda Allah bai la’anta ba? Yaya zan tsine waɗanda Ubangiji bai tsine ba? Daga kan duwatsu na gan su, daga bisa kan tuddai na hange su. Na ga mutane da suke zaune su kaɗai ba sa ɗauki kansu ɗaya da al’ummai ba. Wa zai iya ƙidaya ƙurar Yaƙub ko yă ƙidaya kashi ɗaya bisa huɗu na Isra’ila? Bari in mutu, mutuwar adali ƙarshena kuma yă zama kamar nasu!” Balak ya ce wa Bala’am, “Me ke nan ka yi mini? Na kawo ka, ka la’anta abokan gābana, sai ga shi albarka kake sa musu!” Bala’am ya ce, “Ba dole in faɗa abin da Ubangiji ya sa a bakina ba?” Sa’an nan Balak ya ce masa, “Zo, mu tafi wani wuri inda za ka gan su; a nan kana ganin sashe ne kawai, ba dukansu ba. Daga can kuwa, ka la’anta mini su.” Saboda haka ya ɗauke shi zuwa filin Zofim a ƙwanƙolin Fisga, a can ya gina bagadai bakwai, ya kuma miƙa bijimi da rago a kan kowane bagade. Bala’am ya ce wa Balak, “Tsaya nan kusa da hadayarka, ni kuwa in je in sadu da Ubangiji a can.” Ubangiji ya sadu da Bala’am, ya kuma ba shi saƙo ya ce, “Koma wurin Balak ka ba shi wannan saƙo.” Saboda haka ya tafi ya same Balak tsaye a kusa da hadayarsa, tare da dattawan Mowab. Balak ya tambaye Bala’am ya ce, “Mene ne Ubangiji ya ce?” Sai Bala’am ya furta saƙon da aka ba shi ya ce, “Tashi, Balak, ka saurara; ka kasa kunne gare ni, ɗan Ziffor. Allah ba mutum ba ne, da zai yi ƙarya, shi ba ɗan mutum ba ne, da zai canja tunaninsa. Yana maganar abin da ba zai iya aikata ba ne? Yakan kuma yi alkawarin da ba zai iya cikawa ba? Na karɓi umarni in sa albarka; na kuwa sa albarka, ba zan iya janye ta ba. “Bai ga mugunta a cikin Yaƙub ba, bai kuma ga wahala a Isra’ila ba. Ubangiji Allahnsu yana tare da su; sowar Sarki yana cikinsu. Allah ya fitar da su daga Masar; suna da ƙarfi iri na kutunkun ɓauna. Ba wata maitar da za tă ci Yaƙub, ba sihiri da zai cuci Isra’ila. Yanzu za a ce game da Yaƙub da Isra’ila, ‘Duba abin da Allah ya yi!’ Mutane sun tashi kamar ƙaƙƙarfar zakanya; sun tā da kansu kamar zaki wanda ba ya hutawa sai ya cinye naman abin da ya kama ya kuma sha jinin abin da ya kama.” Sai Balak ya ce wa Bala’am, “Kada ka la’anta su, kada kuma ka sa musu albarka!” Bala’am amsa ya ce, “Ban faɗa maka zan yi kaɗai abin da Ubangiji ya ce ba?” Sai Balak ya ce wa Bala’am, “Zo in kai ka wani wuri. Wataƙila zai gamshi Allah, yă bari ka la’anta mini su daga can.” Balak kuwa ya ɗauki Bala’am zuwa ƙwanƙolin Feyor, wanda yake fuskantar hamada. Bala’am ya ce, “Ka gina mini bagadai bakwai a nan, ka kuma shirya mini bijimai bakwai da raguna bakwai.” Balak ya yi yadda Bala’am ya ce, ya kuwa miƙa bijimi da rago a kan kowane bagade. To, da Bala’am ya ga cewa Ubangiji yana jin daɗin sa wa Isra’ila albarka, bai koma wajen sihiri kamar dā ba, amma ya juya fuskarsa wajen hamada. Da Bala’am ya duba sai ya ga Isra’ila sun yi sansani kabila, kabila, Ruhun Allah kuwa ya sauko masa, sai ya yi annabcinsa ya ce, “Maganar Bala’am ɗan Beyor, saƙon mutumin da idanunsa ke gani sarai, maganar mutumin da ya saurari maganar Allah, maganar wanda yake ganin wahayi daga Maɗaukaki, mutumin da ya fāɗi rubda ciki, wanda kuma idanunsa suna a buɗe. “Ina misalin kyan tentunanka, ya Yaƙub, wuraren zamanka, ya Isra’ila! “Kamar kwaruruka suke a shimfiɗe, kamar lambu kusa da rafi, kamar itatuwan aloyes da Ubangiji ya dasa, kamar itatuwa al’ul kusa da ruwaye. Ruwa zai kwararo daga bokitinsu; irinsu za su sami ruwa a yalwace. “Sarkinsu zai fi sarkin Agag; mulkinsu zai ɗaukaka. “Allah ya fitar da su daga Masar; suna da ƙarfin kutunkun ɓauna. Sun cinye abokan gāban, suka kakkarya ƙasusuwansu; da kibiyoyinsu suka sossoke su. Kamar zaki sun laɓe sun kwanta, kamar zakanya, wa zai yi ƙarfin hali yă tashe su? “Bari waɗanda suka albarkace ka, su sami albarka waɗanda kuma suka la’anta ka, su la’antu!” Fushin Balak ya ƙuna a kan Bala’am. Ya tafa hannunsa, ya ce masa, “Na kira ka don ka la’anta abokan gābana, amma sai ga shi ka sa musu albarka har sau uku. Yanzu ka bar nan ka tafi gida! Na ce zan sāka maka da lada mai kyau, amma Ubangiji ya hana ka samun ladan.” Bala’am ya ce wa Balak, “Ban faɗa wa ’yan aikan da ka aiko wurina ba cewa, ‘Ko da a ce Balak zai ba ni gidansa cike da azurfa da zinariya, ba zan yi wani abu ko kaɗan saɓanin umarnin Ubangiji Allahna ba, kuma dole in faɗa abin da Ubangiji ya ce ne kawai’? Yanzu zan koma wajen mutanena, amma bari in gargaɗe ka game da abin da mutanen nan za su yi wa mutanenka cikin kwanaki masu zuwa.” Sa’an nan ya furta saƙonsa. “Maganar Bala’am ɗan Beyor, saƙon mutumin da idanunsa ke gani sarai, maganar mutumin da ya saurari maganar Allah, wanda yake da sani daga Mafi Ɗaukaka, wanda yake ganin wahayi daga Maɗaukaki, wanda ya fāɗi rubda ciki, wanda kuma idanunsa suna a buɗe. “Na gan shi, amma ba yanzu ba; na hange shi, amma ba kusa ba. Tauraro zai fito daga Yaƙub; sandan mulki zai fito daga Isra’ila. Zai ragargaje goshin Mowab, kawunan dukan ’ya’yan Set. Za a ci Edom da yaƙi; za a ci Seyir, abokiyar gābanta, amma Isra’ila zai ƙara ƙarfi. Mai mulki zai fito daga Yaƙub yă hallaka waɗanda suka ragu a birnin.” Sai Bala’am ya ga Amalek, ya kuma furta maganarsa. “Amalek yana cikin al’ummai na fari, amma zai zama na ƙarshen da za a hallaka.” Sai ya ga Keniyawa, ya kuma furta maganarsa. “Wurin zamanku lafiya yake, an kuma sa sheƙarku a cikin duwatsu; duk da haka, za a hallaka ku Keniyawa sa’ad da Asshur ya kame ku.” Sai ya furta maganarsa ya ce, “Wayyo, wa zai rayu sa’ad da Allah ya yi haka? Jiragen ruwa za su zo daga Kittim; za su murƙushe Asshur da Eber, amma su ma za a hallaka su.” Sa’an nan Bala’am ya tashi ya koma gidan, Balak kuma ya yi tafiyarsa. Lokacin da Isra’ila suke a sansani a Shittim, sai maza suka fara yin lalata da matan Mowabawa, waɗanda suka gayyace su zuwa wajen hadayu na allolinsu. Mutane suka ci suka kuma yi wa waɗannan alloli sujada. Ta haka Isra’ila suka sa kai a bautar gumaka Ba’al-Feyor. Ubangiji kuwa ya husata da su. Ubangiji ya ce wa Musa, “Ka kama dukan shugabannin mutanen nan, ka kashe su, ka kuma bar su a tsakar rana a gaban Ubangiji, don Ubangiji yă huce daga fushin da nake yi da Isra’ila.” Saboda haka Musa ya ce wa alƙalan Isra’ila, “Dole kowannenku yă kashe mutanen nan da suka haɗa kai cikin bautar Ba’al-Feyor.” Sa’an nan wani mutumin Isra’ila ya kawo wata Bamidiyana a iyalinsa a idon Musa da dukan taron jama’ar Isra’ila, yayinda suke kuka a ƙofar Tentin Sujada. Da Finehas ɗan Eleyazar, ɗan Haruna, firist, ya ga haka, sai ya bar taron, ya ɗauki māshi ya bi mutumin Isra’ilan nan cikin tenti, ya soke dukansu biyu, māshin ya ratsa jikin mutumin Isra’ilan har zuwa jikin macen. Sa’an nan aka tsai da annoban nan a kan Isra’ilawa. Waɗanda suka mutu a wannan annoba, sun kai mutum 24,000. Ubangiji ya ce wa Musa, “Finehas ɗan Eleyazar, ɗan Haruna, firist, ya kawar da fushina daga Isra’ilawa; saboda ya yi kishi irin nawa a gabansu, don haka saboda ɗaukakata ban kawo ƙarshensu ba. Saboda haka ka faɗa masa cewa zan yi alkawarin salama da shi. Shi da zuriyarsa za su kasance da alkawari na zama firist har abada, saboda kishinsa domin ɗaukakar Allahnsa, ya kuma yi kafara domin Isra’ilawa.” Sunan mutumin Isra’ilan da aka kashe tare da macen nan Bamidiyana kuwa Zimri ne, ɗan Salu, shugaban mutanen Simeyon. Sunan macen nan Bamidiyana da aka kashe kuwa Kozbi ne, ’yar Zur, wani basaraken iyalin Midiyawa. Ubangiji ya ce wa Musa, “Ka ɗauki Midiyawa a matsayin abokan gāba, ka kuma kashe su, gama sun ɗauke ku a matsayin abokan gāba, sa’ad da suka ruɗe ku a kan al’amuran Feyor da ’yar’uwarsu Kozbi ’yar shugaban Midiyawa, macen da aka kashe a annoba ta dalili Feyor.” Bayan annobar, sai Ubangiji ya yi magana da Musa da Eleyazar ɗan Haruna, firist ya ce, “Ku ƙidaya dukan jama’ar Isra’ila daga mai shekaru ashirin zuwa gaba da za su iya aikin sojan Isra’ila.” Musa da Eleyazar firist suka yi musu magana a filayen Mowab kusa da Urdun daga ƙetaren Yeriko, suka ce, “Ku ƙidaya maza daga mai shekara ashirin zuwa gaba yadda Ubangiji ya umarci Musa.” Waɗannan su ne Isra’ilawan da suka fito daga Masar. Zuriyar Ruben ɗan fari na Isra’ila, daga Hanok; kabilar Hanokawa; daga Fallu; kabilar Falluyawa; daga Hezron, kabilar Hezronawa; daga Karmi, kabilar Karmiyawa. Waɗannan su ne kabilan Ruben; jimillarsu ta kai 43,730. Ɗan Fallu kuwa shi ne Eliyab, ’ya’yan Eliyab maza kuwa su ne, Nemuwel, Datan da Abiram. Datan da Abiram nan, su ne shugabannin mutanen da suka tayar wa Musa da Haruna, suna kuma cikin waɗanda suka bi Kora sa’ad da ya tayar wa Ubangiji. Ƙasa kuwa ta buɗe ta haɗiye su tare da Kora, wanda ƙungiyarsa ta mutu sa’ad da wuta ta cinye mutum 250. Wannan kuwa ya zama alamar faɗakarwa. Amma fa, zuriyar Kora ba tă mutu ba. Zuriyar Simeyon bisa ga kabilansu, daga Nemuwel, kabilar Nemuwelawa; daga Yamin, kabilar Yaminawa; daga Yakin, kabilar Yakinawa; daga Zera, kabilar Zerawa; daga Sha’ul, kabilar Sha’ul. Waɗannan su ne kabilan Simeyon; jimillarsu ta kai 22,200. Zuriyar Gad bisa ga kabilansu, daga Zafon, kabilar Zafonawa; daga Haggi, kabilar Haggiwa; daga Shuni, kabilar Shunawa; daga Ozni, kabilar Ozniyawa daga Eri, kabilar Eriyawa; daga Arod, kabilar Arodiyawa; daga Areli, kabilar Areliyawa. Waɗannan su ne kabilan Gad, jimillarsu ta kai 40,500. Er da Onan, ’ya’yan Yahuda ne, amma sun mutu a Kan’ana. Zuriyar Yahuda bisa ga kabilansu, daga Shela, kabilar Shelayawa daga Ferez, kabilar Ferezawa; daga Zera, kabilar Zerawa; Zuriyar Ferez kuwa, daga Hezron, kabilar Hezronawa; daga Hamul; kabilar Hamulawa. Waɗannan su ne kabilan Yahuda; jimillarsu ta kai 76,500. Zuriyar Issakar bisa ga kabilansu, daga Tola, kabilar Tolatawa; daga Fuwa, kabilar Fuwayawa; daga Yashub, kabilar Yashubawa; daga Shimron, kabilar Shimronawa. Waɗannan su ne kabilan Issakar; jimillarsu ta kai 64,300. Zuriyar Zebulun bisa ga kabilansu, daga Sered, kabilar Seredawa; daga Elon kabilar Elonawa; daga Yaleyel; kabilar Yaleyewa. Waɗannan su ne kabilan Zebulun, jimillarsu ta kai 60,500. Zuriyar Yusuf bisa ga kabilansu ta wurin Manasse da Efraim. Zuriyar Manasse, daga Makir, kabilar Makiriyawa (Makir shi ne mahaifin Gileyad); daga Gileyad, kabilar Gileyadawa. Waɗannan su ne zuriya Gileyad, daga Iyezer, kabilar Iyezerawa; daga Helek, kabilar Helekawa; daga Asriyel, kabilar Asriyelawa; daga Shekem, kabilar Shekem; daga Shemida, kabilar Shemadawa; daga Hefer, kabilar Heferawa. (Zelofehad ɗan Hefer, ba shi da ’ya’ya maza; ’yan mata ne kaɗai ya haifa, sunayensu kuwa su ne Mala, Nowa, Hogla, Milka da Tirza.) Waɗannan su ne kabilan Manasse, jimillarsu ta kai 52,700. Waɗannan su ne kabilan Efraim bisa ga kabilansu, daga Shutela, kabilar Shutelawa; daga Beker, kabilar Bekerawa; daga Tahan, kabilar Tahanawa. Waɗannan su ne kabilan Shutelawa, daga Eran, kabilar Eranawa. Waɗannan su ne kabilan Efraim; jimillarsu ta kai 32,500. Waɗannan su ne kabilan Yusuf ta wurin kabilansu. Zuriyar Benyamin bisa ga kabilansu, daga Bela, kabilar Belawa; daga Ashbel, kabilar Ashbelawa; daga Ahiram, kabilar Ahiramawa; daga Shufam, kabilar Shufamawa; daga Hufam, kabilar Hufamawa. Zuriyar Bela daga Ard da Na’aman, daga Ard, kabilar Ardawa; daga Na’aman, kabilar Na’amawa; Waɗannan su ne kabilan Benyamin, jimillarsu ta kai 45,600. Waɗannan su ne kabilan Dan bisa ga kabilarsu, daga Shuham, kabilar Shuhamawa. Waɗannan su ne kabilan Dan. Dukansu kabilan Shuhamawa ne, jimillarsu ta kai 64,400. Zuriyar Asher bisa ga kabilansu, daga Imna, kabilar Imnawa daga Ishbi, kabilar Ishbiyawa; daga Beriya, kabilar Beriyawa; daga zuriyar Beriya kuwa, daga Heber, kabilar Heberawa; daga Malkiyel, kabilar Malkiyelawa. (Asher yana da ’ya mace da ake kira Sera.) Waɗannan su ne kabilan Asher; jimillarsu ta kai 53,400. Zuriyar Naftali bisa ga kabilansu, daga Yazeyel, kabilar Yazeyelawa; daga Guni, kabilar Guniyawa; daga Yezer, kabilar Yezerawa; daga Shillem, kabilar Shillemawa. Waɗannan su ne kabilan Naftali, jimillarsu ta kai 45,400. Dukan jimillar mazan Isra’ila ta kai 601,730. Ubangiji ya ce wa Musa, “Ka rarraba musu ƙasar a matsayin gādo, bisa ga yawan kabila. Ga ƙungiya mafi girma, ka ba ta rabo mafi girma; ga ƙaramar ƙungiya kuwa, ka ba ta ƙarami rabo; kowane zai karɓa rabonsa ga yawan mutanen da aka rubuta. Ka tabbatar an rarraba ƙasar ta wurin rabo. Abin da kowace ƙungiya ta gāda zai zama bisa ga sunayen kabilar kakanninta. Za a raba kowane gādo bisa ga rabo tsakanin manyan da ƙanana ƙungiyoyi.” Waɗannan su ne Lawiyawa da a ƙidaya bisa ga kabilansu, daga Gershom, kabilar Gershonawa; daga Kohat, kabilar Kohatawa; daga Merari, kabilar Merari. Waɗannan kuma su ne kabilan Lawiyawa, kabilar Libniyawa, kabilar Hebronawa, kabilar Maliyawa, kabilar Mushiyawa, kabilar Korayawa (Kohat shi ne kakan Amram; sunan matan Amram shi ne Yokebed, ita zuriyar Lawi ce, wadda aka haifa wa Lawiyawa a Masar. A wajen Amram kuwa ta haifi Haruna, Musa da kuma ’yar’uwarsu Miriyam. Haruna shi ne mahaifin Nadab, Abihu, Eleyazar da kuma Itamar. Amma Nadab da Abihu sun mutu sa’ad da suka miƙa hadaya da haramtacciyar wuta a gaban Ubangiji. ) Dukan ’ya’yan Lawiyawa maza daga wata ɗaya zuwa gaba, jimillarsu ta kai 23,000. Ba a ƙidaya su tare da sauran Isra’ilawa ba, domin ba a ba su gādo tare da su ba. Waɗannan su ne waɗanda Musa da Eleyazar firist, suka ƙidaya sa’ad da suka ƙidaya Isra’ilawa a filaye Mowab kusa da Urdun a hayen Yeriko. Ba ko ɗayansu da yake cikin waɗanda Musa da Haruna firist, suka ƙidaya sa’ad da suka ƙidaya Isra’ilawa a Hamadar Sinai. Gama Ubangiji ya riga ya gaya wa waɗancan Isra’ilawa cewa lalle za su mutu a hamada, kuma ba ko ɗayansu da ya rage, sai Kaleb ɗan Yefunne da Yoshuwa ɗan Nun. ’Ya’yan nan mata na Zelofehad, ɗan Hefer, ɗan Gileyad, ɗan Makir, ɗan Manasse, suna cikin kabilan Manasse ɗan Yusuf, suka tafi ƙofar shiga Tentin Sujada. Sunayensu kuwa su ne Mala, Nowa, Hogla, Milka da kuma Tirza. Da suka tafi ƙofar shiga Tentin Sujada, sai suka tsaya a gaban Musa, Eleyazar firist, shugabannin da sauran taro, suka ce, “Mahaifinmu ya mutu a hamada. Ba ya cikin mabiyan Kora waɗanda suka taru suka tayar wa Ubangiji, amma ya mutu ne saboda zunubinsa, bai kuma bar ’ya’ya maza ba. Me ya sa sunan mahaifinmu zai ɓace a kabilarsa don kawai ba shi da ɗa? Ka ba mu gādo cikin ’yan’uwan mahaifinmu.” Saboda haka Musa ya kawo maganarsu a gaban Ubangiji. Ubangiji kuwa ya ce wa masa, “Abin da ’ya’yan nan mata na Zelofehad suke faɗi gaskiya ne. Dole ka ba su mallaka a matsayin gādo cikin ’yan’uwan mahaifinsu, ka kuma mayar musu da gādon mahaifinsu. “Ka faɗa wa Isra’ilawa cewa, ‘In wani ya mutu ba shi da ɗa, a ba da gādonsa ga ’yarsa. In ba shi da diya, sai a ba wa ’yan’uwansa gādonsa. In ba shi da ’yan’uwa, a ba da gādonsa ga ’yan’uwan mahaifinsa. In mahaifinsa ba shi da ’yan’uwa, a ba da gādonsa ga danginsa na kusa, a kabilarsa don yă mallaka. Wannan ya zama ƙa’ida wa Isra’ilawa, yadda Ubangiji ya umarci Musa.’ ” Sa’an nan Ubangiji ya ce wa Musa, “Hau bisa wannan dutse a Abarim. Ka ga ƙasar da na ba wa Isra’ilawa. Bayan ka gani, kai ma za ka bi ƙafafun mutanenka, kamar yadda ɗan’uwanka Haruna ya yi, gama sa’ad da jama’a suka yi tayarwa saboda rashin ruwa a Hamadan Zin, ku biyu, ba ku kiyaye umarnina don ku ɗaukaka ni matsayin mai tsarki, a gabansu ba.” (Waɗannan su ne ruwaye na Meriba da Kadesh, a Hamadan Zin.) Musa ya ce wa Ubangiji, “Bari Ubangiji, Allah na ruhohin ’yan adam, yă naɗa wani a kan wannan jama’a yă shiga, yă kuma fita a gabansu, wanda zai bishe su zuwa waje, yă kuma dawo da su ciki, don kada mutanen Ubangiji su zama kamar tumakin da ba su da makiyayi.” Sai Ubangiji ya ce wa Musa, “Ka ɗauki Yoshuwa ɗan Nun, mutumin da ruhun shugabanci yake a cikinsa, ka ɗibiya masa hannunka. Ka sa yă tsaya a gaban Eleyazar firist, da gaban dukan jama’a, sa’an nan ka keɓe shi a gabansu. Ka danƙa masa ikonka don dukan jama’a Isra’ilawa su yi masa biyayya. Zai tsaya a gaban Eleyazar firist, wanda zai nemi masa shawara ta wurin Urim a gaban Ubangiji. Da umarninsa, da shi da dukan jama’ar Isra’ilawa za su fita, da umarninsa kuma za su shiga.” Musa ya yi yadda Ubangiji ya umarce shi. Ya ɗauki Yoshuwa, ya sa ya tsaya a gaban Eleyazar firist, da kuma gaban dukan jama’a. Sai ya ɗibiya masa hannuwansa, ya keɓe shi, yadda Ubangiji ya umarta ta wurin Musa. Sai Ubangiji ya ce wa Musa, “Ka umarci Isra’ilawa cewa, ‘Ku tabbatar kun miƙa mini hadaya ta abinci ta wuta mai daɗin ƙanshi a gare ni, a daidai lokaci.’ Ka gaya musu, ‘Ga hadaya ta ƙonawa ta kowace rana, da za ku miƙa wa Ubangiji, raguna biyu, bana ɗaya-ɗaya, marasa lahani. A miƙa rago ɗaya da safe, ɗaya kuma da yamma, tare da hadaya ta lallausan gari kashi ɗaya bisa goma na efan, kwaɓaɓɓe da kwalaba ɗaya na man zaitun mafi kyau. Wannan ita ce hadaya ta ƙonawa ta kullum wadda aka kafa a Dutsen Sinai, don daɗin ƙanshi, wato, hadaya ce da aka ƙone da wuta ga Ubangiji. Hadaya ta sha, za tă zama kwalaba ɗaya na ruwan inabi, da ɗan rago guda. Za a kwarara hadaya ta sha ga Ubangiji a wuri mai tsarki. Ɗayan ɗan ragon kuma za a miƙa shi da yamma, tare irin hadaya ta lallausan gari, da hadaya ta sha da ka yi da safe. Wannan hadaya ce ta ƙonawa mai daɗin ƙanshi ga Ubangiji. “ ‘A ranar Asabbaci, za a miƙa ’yan raguna biyu, bana ɗaya-ɗaya marasa lahani, tare da hadaya ta sha, da hadaya ta lallausan gari kashi biyu bisa goma na efa, kwaɓaɓɓe da mai. Wannan ita ce hadaya ta ƙonawa ta kowace Asabbaci, ban da hadaya ta ƙonawa ta kullum, tare da ta hadaya ta sha. “ ‘A rana ta fari ga kowane wata, za a miƙa wa Ubangiji hadayun ’yan bijimai biyu, rago ɗaya, da ’yan tumaki bakwai, bana ɗaya-ɗaya, dukansu kuma marasa lahani. Da kowane bijimi, a kasance da hadaya ta lallausan garin da aka kwaɓa da mai na kashi uku bisa goma na efa; da ɗan rago kuwa, a kasance da hadaya ta lallausan garin da aka kwaɓa da mai na kashi biyu bisa goma na efa; da kowane tunkiya kuma, a kasance da hadaya ta lallausan garin da aka kwaɓa da mai, na kashi ɗaya bisa goma na efa. Wannan hadaya ce da aka ƙone da wuta ga Ubangiji. Da kowane bijimi, za a kasance da hadaya ta sha, na rabin kwalabar ruwan inabi; da rago kuwa, a kasance da kashi ɗaya bisa uku; da kowace tunkiya kuma, a kasance da kashi ɗaya bisa huɗu. Wannan ita ce hadaya ta ƙonawa don tsayawar kowane sabon wata na shekara. Ban da hadaya ta ƙonawa ta kullum tare da hadaya ta sha, za a miƙa bunsuru ɗaya ga Ubangiji, hadaya ce don zunubi. “ ‘Za a yi Bikin Ƙetarewa ga Ubangiji a rana ta goma sha huɗu ga wata na fari. A rana ta goma sha biyar ga wannan wata, za a yi biki; kwana bakwai za a ci burodi marar yisti. A rana ta farko, za ku yi tsattsarkan taro, ba kuwa za a yi aikin da aka saba yi na kullum ba. Za a miƙa hadaya ta ƙonawa da bijimai biyu, rago ɗaya, da ’yan raguna bakwai, bana ɗaya-ɗaya; dukansu kuma marasa lahani ga Ubangiji. Da kowane bijimi, a shirya kashi ɗaya bisa uku na efan lallausan gari, kwaɓaɓɓe da mai; da rago guda kuwa, a shirya kashi biyu bisa goma na efan lallausan gari, kwaɓaɓɓe da mai; da kowane ’yan raguna bakwai, kashi ɗaya bisa goma. A haɗa da bunsuru guda, a matsayin hadaya don zunubi, don yin muku kafara. Ku shirya wannan tare da hadaya ta ƙonawa ta kowace safiya. Ta haka za a shirya abinci don hadayar da aka yi da wuta, kowace rana, har kwana bakwai don daɗin ƙanshi ga Ubangiji; a shirya shi haɗe da hadaya ta ƙonawa ta kullum, da kuma hadaya ta sha. A rana ta bakwai, za ku yi tsattsarkan taro, amma ba za a yi aikin da aka saba yi kullum ba. “ ‘A ranar nunan fari, sa’ad da za ku miƙa wa Ubangiji hadayar sabon hatsi, a lokacin Bikin Makoni, za a yi tsattsarkan taro, ba kuwa za a yi aikin da aka saba yi ba. A miƙa hadaya ta ƙonawa da ’yan bijimai biyu, rago ɗaya da ’yan raguna bakwai, bana ɗaya-ɗaya don daɗin ƙanshi ga Ubangiji. Da kowane bijimi a kasance da hadaya ta lallausan gari kashi uku bisa goma na efa, kwaɓaɓɓe da mai; da rago kuwa, a kasance da hadaya ta lallausan gari kashi biyu bisa goma na efa, kwaɓaɓɓe da mai; da kowane ’yan raguna bakwai, kashi ɗaya bisa goma. A haɗa da bunsuru guda don yin muku kafara. A miƙa waɗannan tare da hadayarsu ta sha, haɗe da hadaya ta ƙonawa ta kullum, da kuma hadayarta ta sha. A tabbata dabbobin nan marasa lahani ne. “ ‘A rana ta farko ga wata na bakwai, a yi tsattsarkan taro, kada kuma a yi aikin da aka saba na kullum. Rana ce don busa ƙahoni. Za a miƙa hadaya ta ƙonawa da bijimi guda, rago guda, ’yan raguna bakwai, bana ɗaya-ɗaya don daɗin ƙanshi ga Ubangiji, duka su kasance marasa lahani. Tare da bijimin za a kuma miƙa hadaya ta gari na kashi ɗaya bisa goma na efa na lallausan gari, kwaɓaɓɓe da mai; da rago guda, kashi biyu bisa goma na efa na lallausan gari, kwaɓaɓɓe da mai; kowane ’yan raguna bakwai, kashi ɗaya bisa goma. A haɗa da bunsuru guda a matsayin hadaya don zunubi, don yin muku kafara. Waɗannan ƙari ne ga hadayun ƙonawa na wata-wata da na kullayaumi, tare da hadayun garinsu da hadayun sha yadda aka tsara. Hadayu ne da aka miƙa wa Ubangiji ta wuta don daɗin ƙanshi. “ ‘A rana ta goma ga wannan watan bakwai, za a yi tsattsarkan taro. Ba za ku ci abinci ba, ba kuma za ku yi aiki ba. Za a miƙa hadaya ta ƙonawa da bijimi guda, rago guda, da kuma ’yan raguna bakwai, ’yan bana ɗaya-ɗaya, dukansu marasa lahani don daɗin ƙanshi ga Ubangiji. Tare da bijimin a miƙa hadaya ta gari na kashi ɗaya bisa goma na efa, na lallausan gari kwaɓaɓɓe, da mai; da rago guda, kashi biyu bisa goma na efa, na lallausan gari kwaɓaɓɓe, da mai; kowane ’yan raguna bakwai, kashi ɗaya bisa goma. A haɗa da bunsuru guda a matsayin hadaya don zunubi, don yin muku kafara da kuma hadaya ta ƙonawa ta kullum; tare da hadaya ta garinta, da kuma hadayu na shansu. “ ‘A rana ta goma sha biyar ga wata na bakwai, za a yi tsattsarkan taro, ba kuwa za a yi aikin da aka saba yi ba. Ku yi biki ga Ubangiji har kwana bakwai. A miƙa hadayar da aka yi da wuta, mai daɗin ƙanshi ga Ubangiji, hadaya ta ƙonawa ta bijimai guda sha uku, raguna biyu, da ’yan raguna goma sha huɗu, bana ɗaya-ɗaya, dukansu marasa lahani. Da kowane bijimai goma sha uku nan, a miƙa hadaya ta gari, kashi uku bisa goma na efa, kwaɓaɓɓe da mai; da ragunan biyu ɗin, a miƙa hadaya ta gari kashi biyu bisa goma na efa, kwaɓaɓɓe da mai; tare kuma da kowane ’yan raguna goma sha huɗu, kashi ɗaya bisa goma. A haɗa da bunsuru guda, a matsayin hadaya don zunubi, ban da hadaya ta ƙonawa na kullum tare da hadayarta, ta gari da kuma hadaya ta sha. “ ‘A rana ta biyu, a miƙa bijimai goma sha biyu, raguna biyu, da ’yan raguna goma sha huɗu, bana ɗaya-ɗaya, dukansu marasa lahani. Tare da bijiman, ragunan da ’yan ragunan a miƙa hadayarsu da gari da hadaya ta sha, bisa ga adadin da aka ƙayyade. A haɗa da bunsuru guda a matsayin hadaya, don zunubi, ban da hadaya ta ƙonawa ta kullum, tare da hadayarta ta gari da hadayunsu ta sha. “ ‘A rana ta uku za a miƙa bijimai goma sha ɗaya, raguna biyu, da kuma ’yan raguna goma sha huɗu, bana ɗaya-ɗaya, dukansu marasa lahani. Tare da bijiman, ragunan da ’yan raguna, a miƙa hadayun gari da hadayun sha, bisa ga adadin da aka ƙayyade. A haɗa da bunsuru guda a matsayin hadaya don zunubi, ban da hadaya ta ƙonawa ta kullum, tare da hadayarta ta gari da hadaya ta sha. “ ‘A rana ta huɗu a miƙa bijimai goma, raguna biyu, da ’yan raguna goma sha huɗu, bana ɗaya-ɗaya, dukansu marasa lahani. Tare da bijiman, ragunan da kuma ’yan raguna, a miƙa hadayunsu na gari da hadayu na sha bisa ga adadin da aka ƙayyade. A haɗa da bunsuru guda, a matsayin hadaya don zunubi, ban da hadaya ta ƙonawa ta kullum, tare da hadayarta ta gari da hadaya ta sha. “ ‘A rana ta biyar a miƙa bijimai tara, raguna biyu, da ’yan raguna goma sha huɗu, bana ɗaya-ɗaya, dukansu marasa lahani. Tare da bijiman, ragunan da kuma ’yan ragunan, a miƙa hadayu na gari, da hadayu na sha bisa ga adadin da aka ƙayyade. A haɗa da bunsuru guda a matsayin hadaya don zunubi, ban da hadaya ta ƙonawa ta kullum, tare da hadayarta ta gari da hadaya ta sha. “ ‘A rana ta shida a miƙa bijimai takwas, raguna biyu, da ’yan raguna goma sha huɗu, bana ɗaya-ɗaya, dukansu marasa lahani. Tare da bijiman, ragunan da kuma ’yan raguna, a miƙa hadayunsu ta gari da hadayu na sha bisa adadin da a ƙayyade. A haɗa da bunsuru guda a matsayin hadaya don zunubi, ban da hadaya ta ƙonawa ta kullum tare da hadayarta ta hatsi da hadaya ta sha. “ ‘A rana ta bakwai a miƙa bijimai bakwai, raguna biyu da ’yan raguna goma sha huɗu, bana ɗaya-ɗaya, dukansu marasa lahani. Tare da bijiman, ragunan da kuma ’yan raguna, a miƙa hadayunsu na gari, da hadayun sha bisa ga adadin da a ƙayyade. A haɗa da bunsuru guda a matsayin hadaya don zunubi, ban da hadaya ta ƙonawa ta kullum tare da hadayarta ta hatsi da hadayarta ta sha. “ ‘A rana ta takwas kuwa za a yi tsattsarkan taro, ban da aikin da aka saba. A miƙa hadayar da aka yi da wuta mai daɗin ƙanshi ga Ubangiji, a yi hadaya ta ƙonawa da bijimi guda, rago guda, da ’yan raguna bakwai, bana ɗaya-ɗaya, dukansu marasa lahani. Tare da bijimin, ragon da kuma ’yan ragunan, a miƙa hadayunsu na gari da hadayu na sha bisa ga adadin da aka ƙayyade. A haɗa da bunsuru guda a matsayin hadaya don zunubi, ban da hadaya ta ƙonawa ta kullum, tare da hadayarta ta hatsi da hadayarta ta sha. “ ‘Ban da abin da kuka yi alkawari, da kuma sadakokinku na yardar rai, a miƙa waɗannan ga Ubangiji a lokacin bukukkuwanku, hadayunku na ƙonawa, hadayu na gari, hadayu na sha da hadayu na salama.’ ” Musa ya faɗa wa Isra’ilawa dukan abin da Ubangiji ya umarce shi. Musa ya ce wa shugabannin kabilan Isra’ila, “Ga abin da Ubangiji ya umarta. Sa’ad da mutum ya yi wa Ubangiji alkawari, ko kuwa ya rantse zai yi wani abu, kada yă ƙi cika maganarsa, amma yă cika kome da ya faɗa. “Sa’ad da yarinya, wadda har yanzu tana a gidan mahaifinta ta yi wa Ubangiji alkawari, ko ta rantse za tă yi wani abu, mahaifinta kuwa ya ji alkawarin da ta yi, bai kuma ce mata kome ba, to, sai alkawarin da ta yi da wa’adinta su tabbata. Amma in mahaifinta ya hana ta, sa’ad da ya ji game da shi, to, ba wani daga cikin alkawari ko rantsuwar da ta yi zai tabbata; Ubangiji kuwa zai gafarta mata domin maihaifinta ya hana ta. “In ta yi aure, sai daga baya ta yi alkawari ko kuwa leɓunanta sun furta alkawari da garaje, cewa za tă yi wani abu, mijinta kuwa ya ji game da wannan, amma bai ce mata kome ba, to, alkawarin da ta yi da kuma rantsuwar da ta yi, su tabbata. Amma in mijin ya hana ta sa’ad da ya ji, zai warware alkawari da kuma rantsuwar da ta yi da garaje, Ubangiji kuwa zai gafarce ta. “Duk wani alkawari ko rantsuwar da gwauruwa, ko macen da aurenta ya mutu, ta yi, zai tabbata a kanta. “In macen aure ta yi alkawari, ko ta rantse za tă yi wani abu, mijinta kuwa ya ji game da wannan, amma bai ce mata kome ba, bai kuma hana ta ba, to, dukan alkawari da kuma rantsuwar da ta yi su tabbata a kanta. Amma in mijin ya warware su sa’ad da ya ji, to, ba wani alkawari ko rantsuwar da ya fito daga leɓunanta da zai tabbata. Mijinta ya warware su, Ubangiji kuma zai gafarce ta. Mijinta yana iya tabbatar, ko yă rushe duk wani alkawari ko rantsuwar da ta ɗauka. Amma in mijinta bai ce mata kome ba, to, ya tabbatar da dukan alkawarinta da kuma rantsuwarta ke nan. Ya tabbatar da su ta wurin yin shiru sa’ad da ya ji ta. Amma in ya ji, sa’an nan daga baya ya hana ta, to, zai sha hukuncin laifinta.” Waɗannan su ne ƙa’idodin da Ubangiji ya ba wa Musa game da dangantakar miji da matarsa, da kuma tsakanin mahaifi da ’yarsa wadda har yanzu tana a gidansa. Ubangiji ya ce wa Musa, “Ka ɗaukar wa Isra’ilawa fansa, a kan Midiyawa. Bayan wannan za ka mutu, a kuwa tara ka ga mutanenka.” Saboda haka Musa ya ce wa mutane, “Ku shirya waɗansu daga cikin mazanku, su tafi su yi yaƙi da Midiyawa don su ɗaukar wa Ubangiji fansa a kansu.” Ku aiki maza dubu ɗaya daga kowace kabilar Isra’ila. Saboda haka aka samo mayaƙa dubu goma sha biyu shiryayyu don yaƙi, maza dubu ɗaya daga kowace kabilar Isra’ila. Musa ya aike su zuwa yaƙi, dubu ɗaya daga kowace kabila, tare da Finehas ɗan Eleyazar, firist, wanda ya ɗauki kayayyaki daga wuri mai tsarki da ƙahoni don kiran yaƙi. Suka yi yaƙi da Midiyawa, suka kashe kowane mutum yadda Ubangiji ya umarci Musa. A cikin waɗanda aka kashe kuwa akwai Ewi, Rekem, Zur, Hur da Reba; sarakuna biyar na Mediyawa. Suka kuma kashe Bala’am ɗan Beyor da takobi. Isra’ilawa suka kwashe mata da yaran Midiyawa, a matsayin bayi. Suka kwashe shanunsu da tumakinsu da kuma dukan dukiyarsu, a matsayin ganima. Suka ƙone dukan garuruwan da Midiyawa suke zama, da dukan sansaninsu. Suka kwashe dukan ganima haɗe da mutane da dabbobi, suka kawo bayi da ganiman nan, wurin Musa da Eleyazar firist, da kuma jama’ar Isra’ilawa, a sansaninsu a filayen Mowab kusa da Urdun daga ƙetaren Yeriko. Musa, da Eleyazar firist da dukan shugabannin jama’a, suka fito suka tarye su a bayan sansani. Musa kuwa ya husata da shugabannin sojojin da suke shugabannin dubbai da shugabannin ɗari-ɗarin da suka dawo daga yaƙi. Ya tambaye su ya ce, “Kun bar dukan mata da rai? Su ne waɗanda suka bi shawarar Bala’am suka kuma zama sanadin sa Isra’ilawa suka juya wa Ubangiji baya, har ya kawo abin da ya faru da Feyor, har annoba ya kashe dukan mutanen Ubangiji. Yanzu ku kashe dukan yara maza, ku kuma kashe kowace macen da ta yi lalata da namiji, amma ku bar kowace yarinyar da ba tă taɓa yin lalata da namiji ba. “Dukanku da kuka kashe mutum, ko kuka taɓa wani da aka kashe, dole ku kasance a bayan sansani har kwana bakwai. A rana ta uku da rana ta bakwai dole ku tsabtacce kanku da kuma bayinku. Ku tsarkake kowace taguwa da kuma kome da aka yi da fata, da gashin akuya, ko kuwa itace.” Sa’an nan Eleyazar firist, ya ce wa sojojin da suka je yaƙi, “Wannan ita ce ƙa’idar da Ubangiji ya ba wa Musa. Zinariya, azurfa, tagulla, baƙin ƙarfe, kuza, darma da dukan abin da wuta ba ta iya ci, dole yă shiga wuta sa’an nan zai zama da tsabta. Amma dole a kuma tsarkake ta da ruwan tsarkakewa. Duk abin da wuta za tă iya ci, dole a shigar da ita a ruwan tsarkakewa. A rana ta bakwai za ku wanke tufafinku, sa’an nan za ku tsarkaka, bayan haka ku shigo sansani.” Ubangiji ya yi magana da Musa ya ce, “Da kai da Eleyazar firist, da shugabannin jama’a, ku ƙidaya dukan mutane da dabbobin da aka ci da yaƙi. Ku kasa ganimar kashi biyu, ku ba sojojin da suka tafi yaƙi kashi ɗaya, kashi ɗaya kuma ku ba wa jama’a. Daga sojojin da suka je yaƙin kuwa, ka ware ganima wa Ubangiji, ka ɗauki ɗaya daga cikin mutum ɗari biyar, da shanu ɗari biyar, da jakuna ɗari biyar, da tumaki ɗari biyar. Ka ɗauki wannan sashe daga rabin rabonsu ka ba wa Eleyazar firist, a matsayin sashe na Ubangiji. Daga cikin rabin rabon Isra’ilawa, ka zaɓi ɗaya daga kowane hamsin na mutane, shanu, jakuna, tumaki, awaki ko kuma sauran dabbobi. Ka ba wa Lawiyawan da suke lura da tabanakul na Ubangiji.” Saboda haka Musa da Eleyazar suka aikata yadda Ubangiji ya umarci Musa. Yawan ganimar da sojoji suka kawo ita ce tumaki 675,000 shanu 72,000 da jakuna 61,000. Akwai kuma mata 32,000 da ba su yi lalata ba da namiji ba. Kashin da aka ba sojoji waɗanda suka tafi yaƙi shi ne, tumaki 337,500, tumakin da aka ware wa Ubangiji kuwa 657 ne; shanu 36,000, shanun da aka ware wa Ubangiji kuwa 72 ne; jakuna 30,500, jakunan da aka ware wa Ubangiji kuwa 61 ne; mutane 16,000, mutanen da aka ware wa Ubangiji kuwa 32 ne. Musa ya ba wa Eleyazar abin da aka ware wa Ubangiji, kamar yadda Ubangiji ya umarci Musa. Kashin da aka ba wa Isra’ilawa, wanda Musa ya ware daga cikin na waɗanda suka tafi yaƙi, kashin da aka ba wa jama’a kuwa tumaki 337,500 ne, shanu 36,000, jakuna 30,500 da mutane 16,000. Daga rabin kashi na Isra’ilawa, Musa ya ɗauki ɗaya daga cikin hamsin na mutane da na dabbobi, yadda Ubangiji ya umarce shi, ya ba wa Lawiyawan da suke lura da tabanakul na Ubangiji. Sai shugabannin da suka shugabancin rundunar yaƙin, shugabanni na dubu-dubu da shugabanni na ɗari-ɗari, suka zo wurin Musa suka ce masa, “Barorinka sun ƙidaya mayaƙan da suke ƙarƙashinmu, babu ko ɗayan ya ɓace. Saboda haka mun kawo wa Ubangiji hadaya na kayan zinariya da kowannenmu ya samu, mundaye, ƙawane, ’yan kunne da duwatsun wuya, don yin wa kanmu kafara a gaban Ubangiji.” Musa da Eleyazar firist, suka karɓi zinariya da kayan adon duka daga gare su. Dukan zinariya da shugabannin dubu-dubu da shugabannin ɗari-ɗari, waɗanda Musa da Eleyazar suka karɓa, suka kuma miƙa hadaya ga Ubangiji, nauyinta ta kai shekel 16,750. Kowane soja, ya kwashi ganima wa kansa. Musa da Eleyazar firist, suka karɓi zinariya daga shugabannin dubu-dubu da shugabannin ɗari-ɗari, suka kawo cikin Tentin Sujada, don su zama abin tuni ga Isra’ilawa a gaban Ubangiji. Mutanen Ruben da mutanen Gad, da suke da garken shanu da kuma garke tumaki masu yawa, suka ga cewa ƙasashen Yazer da Gileyad wurare ne masu kyau don kiwon shanu da tumaki. Saboda haka suka zo wurin Musa da Eleyazar da kuma shugabannin jama’a, suka ce, “Atarot, Dibon, Yazer, Nimra, Heshbon, Eleyale, Sebam, Nebo da Beyon, ƙasar da Ubangiji ya ci da yaƙi a gaban mutane Isra’ila, suna da kyau don dabbobi, bayinku kuma suna da dabbobi.” Suka ce, “In mun sami tagomashi daga gare ka bari a ba da wannan ƙasa ga bayinka, tă zama mallakanmu. Kada ka sa mu haye Urdun.” Musa ya ce wa mutanen Gad da mutanen Ruben, “Wato, sai ’yan’uwanku su yi ta yaƙi ku kuwa ku zauna nan? Don me za ku karya zuciya Isra’ilawa daga hayewa zuwa ƙasar da Ubangiji ya ba su? Haka iyayenku suka yi sa’ad da na aike su daga Kadesh Barneya don su dubo ƙasar. Gama bayan suka haura Kwarin Eshkol suka hangi ƙasar, sai suka karya zuciyar Isra’ilawa daga shigar ƙasar da Ubangiji ya ba su. A ranar kuwa Ubangiji ya husata har ya yi wannan rantsuwa cewa, ‘Tabbatacce ba wani daga cikin mutanen da suka fito daga Masar, tun daga mai shekara ashirin zuwa gaba, da zai ga ƙasar da na rantse zan ba Ibrahim, da Ishaku, da Yaƙub, domin ba su bi ni sosai ba, ba ko ɗaya sai dai Kaleb ɗan Yefunne Bakenizze da Yoshuwa ɗan Nun, don su ne kaɗai suka bi Ubangiji da zuciya ɗaya.’ Ubangiji ya husata da Isra’ila har ya sa suka yi ta yawo a hamada shekara arba’in, sai da dukan tsaran da suka aikata wannan mugunta a gabansa, suka mutu. “Ga shi ku kuma, tarin masu zunubi, kuna tsaya a matsayin kakanninku, kuna sa Ubangiji yă sāke husata da Isra’ila. In kun juye daga binsa, zai sāke barin dukan wannan mutane a hamada, ku ne kuwa za ku zama sanadin hallakarsu.” Sai suka zo wurin Musa, suka ce, “Muna so mu gina katangar dutse don dabbobinmu, da kuma birane don matanmu da ’ya’yanmu a nan. Matanmu da ’ya’yanmu za su zauna a biranen da suke da katanga, don kāriya daga mazaunan ƙasar, amma mu, za mu ɗauki makamai mu tafi tare da sauran Isra’ilawa, har mu kai su wuraren zamansu. Ba za mu koma gidajenmu ba sai kowane mutumin Isra’ila ya sami gādonsa. Ba za mu ci gādo tare da su a wancan hayin Urdun ba, domin mun sami gādonmu a wannan hayin gabashin Urdun.” Sai Musa ya ce musu, “In za ku yi haka, in za ku sha ɗamara da makamai a gaban Ubangiji, ku tafi yaƙi, in kuma dukanku za ku yi ɗamara, ku ɗauki makaman yaƙi a hayin Urdun a gaban Ubangiji har lokacin da ya kori abokan gābansa daga gabansa, to, sa’ad da aka ci ƙasar a gaban Ubangiji, kwa kuɓuta daga alhakinku ga Ubangiji da kuma Isra’ila. Ƙasan nan kuwa za tă zama mallakarku a gaban Ubangiji. “Amma in ba ku yi haka ba, kun yi zunubi ke nan ga Ubangiji; kuma ku san cewa zunubinku zai tone ku. Ku gina birane domin matanku da ’ya’yanku, ku gina katanga kuma domin dabbobinku, amma fa ku cika abin da kuka yi alkawari.” Mutanen Gad da mutanen Ruben, suka ce wa Musa, “Mu bayinka za mu yi yadda ranka yă daɗe ya umarta. ’Ya’yanmu da matanmu, garkunan shanunmu da na tumakinmu, za su kasance a nan biranen Gileyad. Amma bayinka, kowane mutum a cikinmu zai haye a gaban Ubangiji, zuwa yaƙi kamar yadda ranka yă daɗe ya faɗa.” Sai Musa ya yi wa Eleyazar firist, da Yoshuwa ɗan Nun, da shugabannin gidajen kakannin kabilan mutanen Isra’ila kashedi a kansu, ya ce, “In kowane sojan mutanen Gad da na mutanen Ruben, ya ɗauki makaman yaƙi, ya haye Urdun tare da ku a gaban Ubangiji, to, sa’ad da a ci ƙasar a gabanku, ku ba da ƙasar Gileyad tă zama mallakarsu. Amma in ba su haye tare da ku da shirin yaƙi ba, to, sai ku ba su gādo a wancan haye kamar sauran kabilun a Kan’ana.” Mutanen Gad da mutanen Ruben suka amsa, suka ce, “Barorinka za su yi abin da Ubangiji ya faɗa. Za mu haye a gaban Ubangiji zuwa Kan’ana, amma mallakarmu ta gādo, za tă kasance a wannan hayi na Urdun.” Sai Musa ya ba wa mutanen Gad, mutanen Ruben, da rabin mutanen Manasse ɗan Yusuf, masarautar Sihon, sarkin Amoriyawa, da masarautar Og na Bashan, dukan ƙasar, tare da biranenta da kuma yankunan da suke kewaye. Mutanen Gad suka gina Dibon, Atarot, Arower, Atrot Shofan, Yazer, Yogbeha, Bet-Nimra, da Bet-Haran a matsayin birane masu katanga, suka kuma gina katanga don dabbobinsu. Mutanen Ruben suka sāke gina Heshbon, Eleyale, da Kiriyatayim, haka kuma suka gina Nebo da Ba’al-Meyon (an canja waɗannan sunaye) suka kuma gina Sibma. Suka ba wa biranen da suka sāke ginawa sunaye. Zuriyar Makir ɗan Manasse suka tafi Gileyad, suka ci ta da yaƙi, suka kori mutanen Amoriyawa da suke can. Saboda haka Musa ya ba da Gileyad ga mutanen Makir, zuriyar Manasse, suka kuma zauna a can. Yayir, wani ɗan Manasse, ya ci ƙauyukansu da yaƙi, ya kuma ba su sunan Hawwot Yayir. Noba kuma ya ci Kenat da ƙauyukanta da yaƙi, ya kuma ba ta suna Noba, bisa ga sunansa. Ga wuraren da Isra’ilawa suka yi sansani sa’ad da suka fito runduna-runduna a ƙarƙashin Musa da Haruna daga Masar. Bisa ga umarnin Ubangiji, Musa ya rubuta wuraren tafiye-tafiyensu da sansaninsu. Ga yadda tafiye-tafiyen suka kasance. Isra’ilawa sun tashi daga Rameses a rana ta goma sha biyar, ga watan fari, kashegarin Bikin Ƙetarewa. Suka fita gabagadi a gaban dukan Masarawa, waɗanda suke binne gawawwakin ’ya’yan farinsu da Ubangiji ya karkashe; gama Ubangiji ya hukunta allolinsu. Isra’ilawa suka tashi daga Rameses, suka yi sansani a Sukkot. Suka tashi daga Sukkot, suka yi sansani a Etam, a gefen hamada. Suka tashi daga Etam, suka koma baya zuwa Fi Hahirot, wajen gabashin Ba’al-Zafon, suka yi sansani kusa da Migdol. Suka tashi daga Fi Hahirot, suka ratsa cikin teku zuwa hamada, bayan sun yi tafiya kwana uku a cikin Hamadan Etam, sai suka yi sansani a Mara. Suka tashi daga Mara, suka tafi Elim, inda akwai maɓulɓulan ruwa goma sha biyu, da itatuwan dabino guda saba’in, suka yi sansani a can. Suka tashi daga Elim, suka yi sansani kusa da Jan Teku. Suka tashi daga Jan Teku, suka yi sansani a Hamadan Sin. Suka tashi daga Hamadan Sin, suka yi sansani a Dofka. Suka tashi daga Dofka, suka yi sansani a Alush. Suka tashi daga Alush, suka yi sansani a Refidim, inda babu ruwan da mutane za su sha. Suka tashi daga Refidim, suka yi sansani a Hamadan Sinai. Suka tashi daga Hamadan Sinai, suka yi sansani a Kibrot Hatta’awa. Suka tashi daga Kibrot Hatta’awa, suka yi sansani a Hazerot. Suka tashi daga Hazerot, suka yi sansani a Ritma. Suka tashi daga Ritma, suka yi sansani a Rimmon Ferez. Suka tashi daga Rimmon Ferez, suka yi sansani a Libna. Suka tashi daga Libna, suka yi sansani a Rissa. Suka tashi daga Rissa, suka yi sansani a Kehelata. Suka tashi daga Kehelata, suka yi sansani a Dutsen Shefer. Suka tashi daga Dutsen Shefer, suka yi sansani a Harada. Suka tashi daga Harada, suka yi sansani a Makhelot. Suka tashi daga Makhelot, suka yi sansani a Tahat. Suka tashi daga Tahat, suka yi sansani a Tera. Suka tashi daga Tera, suka yi sansani a Mitka. Suka tashi daga Mitka, suka yi sansani a Hashmona. Suka tashi daga Hashmona, suka yi sansani a Moserot. Suka tashi daga Moserot, suka yi sansani a Bene Ya’akan. Suka tashi daga Bene Ya’akan, suka yi sansani a Hor Haggidgad. Suka tashi daga Hor Haggidgad, suka yi sansani a Yotbata. Suka tashi daga Yotbata, suka yi sansani a Abrona. Suka tashi daga Abrona, suka yi sansani a Eziyon Geber. Suka tashi daga Eziyon Geber, suka yi sansani a Kadesh, cikin Hamadan Zin. Suka tashi daga Kadesh, suka yi sansani a Dutsen Hor, a iyakar Edom. Bisa ga umarni Ubangiji, Haruna firist, ya hau Dutsen Hor, inda ya mutu a rana ta fari ga watan biyar, a shekara ta arba’in, bayan Isra’ilawa suka fito daga Masar. Haruna yana da shekara ɗari da ashirin da uku, sa’ad da ya mutu a Dutsen Hor. Sarki Arad Bakan’ane, wanda yake zaune a Negeb na Kan’ana, ya ji labari cewa Isra’ilawa suna zuwa. Suka tashi daga Dutsen Hor, suka yi sansani a Zalmona. Suka tashi daga Zalmona, suka yi sansani a Funon. Suka tashi daga Funon, suka yi sansani a Obot. Suka tashi daga Obot, suka yi sansani a Iye Abarim, a iyakar Mowab. Suka tashi daga Iyim, suka yi sansani a Dibon Gad. Suka tashi daga Dibon Gad, suka yi sansani a Almon Dibilatayim. Suka tashi daga Almon Dibilatayim, suka yi sansani a duwatsun Abarim, kusa da Nebo. Suka tashi daga duwatsun Abarim, suka yi sansani a filayen Mowab kusa da Urdun, ɗaura da Yeriko. A can filayen Mowab, suka yi sansani kusa da Urdun ɗaura da Bet-Yeshimot har zuwa Abel-Shittim. A filayen Mowab kusa da Urdun ɗaura da Yeriko ne Ubangiji ya ce wa Musa, “Ka gaya wa Isra’ilawa cewa, ‘Sa’ad da kuka haye Urdun zuwa Kan’ana, ku kori dukan mazaunan ƙasar a gabanku. Ku rurrushe sassaƙaƙƙun duwatsu, da siffofinsu na zubi, ku kuma rurrushe dukan masujadansu na kan tudu. Ku mallaki ƙasar, ku kuma zauna a ciki, gama na ba ku ƙasar, ku mallake ta. Ku rarraba ƙasar ta wurin jefan ƙuri’a, bisa ga kabilanku. Kabilar da take babba, a ba ta babban gādo, ƙarami kabila kuwa, a ba ta ƙaramin gādo. Duk abin da ƙuri’a ta ba su, shi zai zama nasu. Ku rarraba wannan bisa zuriyar kakanninku. “ ‘Amma in ba ku kori mazaunan ƙasar ba, waɗanda kuka bari su ci gaba da zama, za su zama muku hakki a idanunku, da kuma ƙayayyuwa a bayanku. Za su ba ku wahala a ƙasar da kuke zama. Sa’an nan kuwa zan yi muku abin da na shirya yin musu.’ ” Ubangiji ya ce wa Musa, “Ka umarci Isra’ilawa, ka ce musu, ‘Sa’ad da kuka shiga Kan’ana, ƙasar da aka ba ku gādo za tă kasance da waɗannan iyakoki. “ ‘Gefenku na kudu zai haɗa da wani sashin Hamadan Zin ta iyakar Edom. A gabas, iyakarku ta kudu za tă fara daga ƙarshen Tekun Gishiri, tă ƙetare Mashigin Kunama a kudu, tă ci gaba zuwa Zin, sa’an nan tă nufi kudu da Kadesh Barneya. Sa’an nan za tă zarce zuwa Hazar Addar, tă nausa zuwa Azmon, inda za tă juya tă haɗu da Rafin Masar, tă kuma ƙarasa a Bahar Rum. “ ‘Iyakarku a yammanci, za tă kasance bakin Bahar Rum. Wannan ce za tă zama iyakarku a yamma. “ ‘Iyakarku a arewanci kuwa za tă tashi daga Bahar Rum zuwa Dutsen Hor, za tă kuma tashi daga Dutsen Hor, zuwa Lebo Hamat. Sa’an nan tă miƙe zuwa Zedad, tă ci gaba zuwa Zifron, sa’an nan tă ƙarasa a Hazar-Enan. Wannan ce za tă zama iyakarku a arewa. “ ‘Iyakarku a gabashi, za tă tashi daga Hazar-Enan zuwa Shefam. Iyakar za tă gangara daga Shefam zuwa Ribla a gefen gabashin Ayin, sa’an nan tă ci gaba a gangaren gabashin Tekun Kinneret. Sa’an nan tă gangara ta Urdun, tă ƙarasa a Tekun Gishiri. “ ‘Wannan za tă zama ƙasarku, tare da iyakokinta a kowane gefe.’ ” Sai Musa ya umarci Isra’ilawa ya ce, “Ku raba wannan ƙasa da za ku gāda ta hanyar jefa ƙuri’a. Ubangiji ya umarta cewa a ba da ita ga kabilu tara da rabi, saboda iyalan kabilar Ruben, kabilar Gad da rabin kabilar Manasse sun riga sun sami gādonsu. Waɗannan kabilu biyu da rabi, sun sami gādonsu a wancan hayin Urdun a gabashin Yeriko wajen fitowar rana.” Ubangiji ya ce wa Musa, “Waɗannan su ne sunayen mutanen da za su raba muku ƙasar gādo. Eleyazar firist, da Yoshuwa ɗan Nun. Ka kuma naɗa shugaba guda ɗaya daga kowace kabila domin yă taimaka a rabon ƙasar. “Ga sunayensu. “Kaleb ɗan Yefunne, daga kabilar Yahuda; Shemuyel ɗan Ammihud, daga kabilar Simeyon Elidad ɗan Kislon, daga kabilar Benyamin; Bukki ɗan Yogli, shugaba daga kabilar Dan; Hanniyel ɗan Efod, shugaba daga kabilar Manasse ɗan Yusuf; Kemuwel ɗan Shiftan, shugaba daga kabilar Efraim ɗan Yusuf; Elizafan ɗan Farnak, shugaba daga kabilar Zebulun; Faltiyel ɗan Azzan, shugaba daga kabilar Issakar; Ahihud ɗan Shelomi, shugaba daga kabilar Asher; Fedahel ɗan Ammihud, shugaba daga kabilar Naftali.” Waɗannan su ne mutanen da Ubangiji ya umarta su raba gādo ga Isra’ilawa a ƙasar Kan’ana. A filayen Mowab, wajen Urdun, ɗaura da Yeriko, Ubangiji ya yi magana da Musa ya ce, “Ka umarci Isra’ilawa su ba wa Lawiyawa garuruwan da za su zauna a ciki daga cikin gādon da Isra’ilawa za su mallaka. A kuma ba su wurin kiwo kewaye da garuruwan. Sa’an nan za su kasance da garuruwan da za su zauna, su sami fili, da kuma za su yi kiwon garkensu na shanu da tumaki da kuma sauran dabbobinsu. “Wuraren kiwo a kewayen garuruwan da za a ba wa Lawiyawa, girmansu zai zama mai fāɗin kamu dubu ɗaya daga katangar garin. A bayan garin, ka auna kamu dubu biyu a wajen gabas, kamu dubu biyu a wajen yamma, kamu dubu biyu wajen kudu, da kuma kamu dubu uku wajen arewa, a bar garin a tsakiya. Za su kasance da wannan a matsayin wurin kiwo na garuruwan. “A cikin biranen da za a ba Lawiyawa, shida daga cikin garuruwan za su zama biranen mafaka, inda wanda ya kashe mutum zai gudu yă je. Ban da wannan, a ba su waɗansu garuruwa arba’in da biyu. Duka-duka dai a ba Lawiyawa garuruwa arba’in da takwas, tare da wuraren kiwonsu. Garuruwan da za ku ba wa Lawiyawa daga ƙasar da Isra’ilawa suka mallaka, za a ba da su bisa girman gādon kowace kabila. Ka karɓi garuruwa masu yawa daga kabilar da take da garuruwa masu yawa, amma kaɗan daga kabilar da ba ta da garuruwa masu yawa.” Sa’an nan Ubangiji ya ce wa Musa, “Ka yi magana da Isra’ilawa, ka ce musu, ‘Sa’ad da kuka haye Urdun zuwa Kan’ana, ku zaɓi waɗansu garuruwan da za su zama biranen mafakarku, inda wanda ya kashe mutum cikin kuskure zai iya gudu zuwa. Za su zama wuraren mafaka daga hannun mai bin hakki, don kada a kashe mai kisankai, tun ba a kai shi gaban shari’a, a gaban taron jama’a ba. Waɗannan garuruwa shida da aka bayar za su zama biranen mafakarku. A ba da uku a wannan gefe na Urdun, a kuma ba da uku a Kan’ana, su zama biranen mafaka. Waɗannan garuruwa shida za su zama wurin mafaka wa Isra’ilawa, baƙi da duk sauran mutanen da suke zama a cikinsu, saboda duk wanda ya kashe mutum cikin kuskure yă iya gudu zuwa. “ ‘In wani ya bugi wani da makami na ƙarfe har ya mutu, to, shi mai kisankai ne; sai a kashe mai kisankan nan. Ko kuwa in wani yana riƙe da dutsen da ya isa yă kashe mutum a hannunsa, ya kuma harbi wani da dutsen har ya mutu, to, shi mai kisankai ne, sai a kashe mai kisankan nan. Ko kuwa wani yana da makami na itace a hannunsa da ya isa yă kashe mutum, ya kuma bugi wani da shi har ya mutu, shi ma mai kisankai ne, sai a kashe mai kisankan nan. Sai mai bin hakkin jinin yă kashe mai kisankan, sa’ad da ya sadu da mai kisankan, sai yă kashe shi. In saboda ƙiyayya, mutum ya laɓe, ya soke wani, ko ya jefe shi da wani abu da gangan har ya mutu, ko kuwa saboda ƙiyayya ya naushe shi har ya mutu, sai a kashe wannan mutumin da ya yi haka; shi mai kisankai ne. Sai mai bin hakkin jini yă kashe mai kisankan in ya same shi. “ ‘Amma in cikin tsautsayi ne ya soke shi, ba don ƙiyayya ba, ko kuma ya jefe shi, ba da gangan ba, ko kuwa bai gan shi ba, ya jefa dutsen da zai kashe shi a kansa, ya kuwa mutu, to, da yake shi ba abokin gābansa ba ne, bai kuma yi nufi yă ji masa ba, dole taro su yi hukunci tsakanin mai laifin, da mai bin hakkin jini bisa waɗannan ƙa’idodi. Dole taro su kāre wanda ake zargi da kisa, daga mai bin hakkin jini. Su mai da shi birnin mafaka inda ya gudu ya tafi. Dole yă kasance a can sai mutuwar babban firist, wanda aka shafe da mai mai tsarki. “ ‘Amma in wanda ake zargin ya kuskura ya fita, ya kai iyakar birnin mafaka wadda ya gudu ya je, idan mai bin hakkin jinin ya same shi a bayan gari, mai bin hakkin jinin zai iya kashe mai kisankai ɗin ba tare da wani laifi ba. Dole wanda ake zargin, yă kasance a birninsa na mafaka sai bayan mutuwa babban firist; sai bayan mutuwar babban firist ne kawai zai iya komo ga mallakarsa. “ ‘Waɗannan su ne za su zama ƙa’idodin da za ku kasance da su, a dukan tsararraki masu zuwa. “ ‘Kowa da ya kashe wani, za a kashe shi a matsayin mai kisankai, bisa ga shaidar shaidu. Amma kada a kashe wani bisa ga shaidar mutum ɗaya. “ ‘Kada a karɓi fansa don ran wanda ya yi kisankai, wanda ya cancanci mutuwa. Lalle ne a kashe shi. “ ‘Kada a karɓi fansa saboda wanda ya tsere zuwa birnin mafaka don yă koma yă zauna gidansa tun babban firist bai rasu ba. “ ‘Kada ku ƙazantar da ƙasar da kuke zama a ciki. Zub da jini yakan ƙazantar da ƙasa, ba a kuma iya yin kafara saboda wannan ƙasa da aka zub da jini, sai dai ta wurin jinin mutumin da ya zub da jinin. Kada ku ƙazantar da ƙasar da kuke zama, wadda ni kuma nake zama a ciki, gama Ni Ubangiji, ina zama a cikin Isra’ilawa.’ ” Sai shugabannin gidajen iyalan Gileyad ɗan Makir, ɗan Manasse, waɗanda suka fito daga kabilar zuriyar Yusuf, suka zo, suka yi magana a gaban Musa da shugabanni, shugabannin iyalan Isra’ilawa. Suka ce, “Sa’ad da Ubangiji ya umarce ranka yă daɗe, yă raba ƙasar gādo ga Isra’ilawa ta wurin ƙuri’a, ya umarce ka, ka ba wa ’ya’ya matan nan na Zelofehad ɗan’uwanmu gādonsa. To, a ce sun auri mutane daga waɗansu kabilan Isra’ilawa fa; ka ga, za a ɗebe gādonsu daga gādon kakanninmu a ƙara wa gādon kabilan mutanen da suka aura ke nan. Ta haka za a ɗebe sashe daga gādon da aka ba mu ke nan. Sa’ad da Shekara ta Murnar Isra’ilawa ta kewayo, za a haɗa gādonsu da na kabilan mutanen da suka aura, a kuma ba su mallakar gādon da aka ɗebe daga kabilar kakanninmu.” Ta wurin umarnin Ubangiji, Musa ya ba Isra’ilawa wannan umarni, “Abin da kabilar zuriyar Yusuf suke faɗi, daidai ne. Ga abin da Ubangiji ya umarta saboda ’ya’ya matan nan na Zelofehad. Za su iya auri duk wanda suka ga dama, muddin sun yi aure a cikin kabilar kakanninsu. Ba gādon Isra’ilan da za a ba wa wata kabila daga wata kabila, gama kowane mutumin Isra’ila zai riƙe gādonsa na kabilar da ya gāda daga kakanninsa. Kowace ’ya wadda ta ci gādon ƙasa, a kowace kabilar Isra’ilawa, dole tă auri wani cikin kabilar kakanninta, saboda kowane mutumin Isra’ila yă mallaki gādon kakanninsa. Ba gādon da za a ba wa wata kabila daga wata kabila, gama kowace kabilar Isra’ilawa za tă riƙe mallaka da ta gāda.” Saboda haka ’ya’yan Zelofehad mata suka yi yadda Ubangiji ya umarci Musa. ’Ya’yan Zelofehad mata, Mala, Tirza, Hogla, Milka da Nowa, suka auri ’ya’yan ’yan’uwa na gefen mahaifinsu. Suka yi aure cikin kabilar zuriyar Manasse ɗan Yusuf, gādonsu kuwa ya kasance a cikin iyali da kuma kabilar mahaifinsu. Waɗannan su ne umarnai da ƙa’idodin da Ubangiji ya ba wa Isra’ilawa ta wurin Musa, a filayen Mowab kusa da Urdun, ɗaura da Yeriko. Waɗannan su ne kalmomin da Musa ya yi wa dukan Isra’ila, a hamada gabas da Urdun, wato, Araba, ɗaura da Suf, tsakanin Faran da Tofel, Laban, Hazerot da Dizahab. (Yakan ɗauki kwana goma sha ɗaya daga Horeb zuwa Kadesh Barneya ta hanyar Dutsen Seyir.) A shekara ta arba’in, a rana ta fari ga wata na goma sha ɗaya, Musa ya yi shela ga Isra’ilawa game da dukan abin da Ubangiji ya umarta shi game da su. Wannan ya faru bayan ya ci Sihon sarkin Amoriyawa wanda ya yi mulki a Heshbon da yaƙi. A Edireyi kuma ya ci Og sarkin Bashan wanda ya yi mulki a Ashtarot da yaƙi. Gabas da iyakar Mowab, Musa ya fara bayyana wannan doka, yana cewa, Ubangiji Allahnmu ya faɗa mana a Horeb cewa, “Daɗewarku a wannan dutse ya isa haka. Ku tashi, ku ci gaba zuwa ƙasar tudun Amoriyawa; ku tafi wurin dukan maƙwabta a cikin Araba, a cikin duwatsu, a gindin yammancin tuddai, a Negeb da kuma a ta kwaruruka, da ƙasar Kan’aniyawa da kuma zuwa Lebanon, har zuwa babban kogi, wato, Yuferites. Duba na riga na ba ku wannan ƙasa. Ku shiga ku mallaki ƙasar da Ubangiji ya rantse zai ba wa kakanninku, ga Ibrahim, Ishaku da kuma Yaƙub, da kuma ga zuriyarsu bayansu.” A wancan lokaci na faɗa muku cewa, “Ku kaya ne masu nauyi da ni kaɗai ba zan iya ɗauka ba. Ubangiji Allahnku ya ƙara yawanku har yau kuka zama da yawa kamar taurari a sarari. Bari Ubangiji, Allahn kakanninku yă ƙara yawanku sau dubu, yă kuma albarkace ku yadda ya yi alkawari! Amma yaya zan ɗauka dukan damuwoyinku da nawayarku da kuma faɗace-faɗacenku duka ni kaɗai? Ku zaɓi waɗansu masu hikima, masu ganewa, da kuma mutanen da ake girmama daga kowace kabilarku, zan kuma sa su a kanku.” Kuka amsa mini, kuka ce, “Abin da ka ce za ka yi, yana da kyau.” Saboda haka na ɗauko shugabannin kabilanku masu hikima, waɗanda suka saba da ma’amala da jama’a, na sa su shugabanni a gabanku, waɗansu suka zama shugabanni a kan dubu-dubu, waɗansu a kan ɗari-ɗari, waɗansu a kan hamsin-hamsin, waɗansu kuma a kan goma-goma. Na sa su zama shugabanni a kabilanku. Na kuma umarci alƙalanku a wancan lokaci, na ce, “Ku yi adalci cikin shari’a tsakanin ’yan’uwanku, ko damuwar tana tsakanin ’yan’uwa Isra’ilawa ne, ko kuwa tsakanin Isra’ilawa da baƙin da suke zaune a cikinku. Kada ku nuna sonkai a cikin hukuncinku, ku saurari kowane ɓangare, babba da ƙarami, kada ku ji tsoron wani, gama hukunci na Allah ne. Ku kawo kowane batun da ya sha ƙarfinku, zan kuwa saurare shi.” A wancan lokacin kuwa na faɗa muku dukan abin da ya kamata ku yi. Sa’an nan, muka kama hanya daga Horeb muka ratsa wajen ƙasar tudun Amoriyawa ta dukan hamadarta mai fāɗi, da kuma mai bantsoron da kuka gani, muka kuma kai Kadesh Barneya yadda Ubangiji, Allahnmu ya umarce mu. Sai na ce muku, “Kun iso ƙasar tudun Amoriyawa, wadda Ubangiji, Allahnmu yake ba mu. Duba, Ubangiji Allahnku ya ba ku ƙasar. Ku haura ku mallake ta yadda Ubangiji Allahn kakanninku ya faɗa muku. Kada ku ji tsoro, kada ku fid da zuciya.” Sai dukanku kuka zo wurina kuka ce, “Bari mu aiki mutane su yi gaba su leƙi mana asirin ƙasar, su kuma kawo mana labari game da hanyar da za mu bi, da kuma biranen da za mu shiga.” Ra’ayin nan naku ya yi mini kyau, saboda haka na zaɓe ku goma sha biyu, mutum guda daga kowace kabila. Suka tafi, suka haura zuwa ƙasar tudu, suka kai Kwarin Eshkol, suka leƙo asirin ƙasar. Suka ɗebi ’ya’yan itatuwan ƙasar, suka sauko mana da su, suka kuma ba da labari cewa, “Ƙasar da Ubangiji Allahnmu yake ba mu, kyakkyawa ce.” Amma ba ku yi niyya ku haura ba, kuka yi tawaye gāba da umarnin Ubangiji Allahnku. Kuka yi gunaguni a cikin tentunanku, kuna cewa, “ Ubangiji ya ƙi mu; shi ya sa ya fitar da mu daga Masar don yă ba da mu ga hannuwan Amoriyawa su hallaka mu. Ina za mu? ’Yan’uwanmu suka sa muka fid da zuciya. Suka ce, ‘Mutanen sun fi mu ƙarfi, sun kuma fi mu tsayi; biranen manya ne, da katanga har sama. Mun ma ga Anakawa a can.’ ” Sai na ce muku, “Kada ku firgita; kada ku ji tsoronsu. Ubangiji Allahnku yana a gabanku, zai yi yaƙi saboda ku, kamar yadda ya yi a kan idanunku a Masar, da kuma a cikin hamada. A can ma kun ga yadda Ubangiji Allahnku ya riƙe ku ko’ina da kuka tafi, kamar yadda mahaifi yakan riƙe ɗansa, sai da kuka kai wannan wuri.” Duk da haka, ba ku amince da Ubangiji Allahnku ba, shi da ya sha gabanku a tafiyarku, cikin wuta da dad dare da kuma girgije da rana, don yă nemi wurare domin ku kafa sansani, don kuma yă nuna muku hanyar da za ku bi. Da Ubangiji ya ji abin da kuka faɗa, sai ya husata, ya kuma yi rantsuwa ya ce, “Babu wani a cikin wannan muguwar tsara da zai ga ƙasa mai kyau da na rantse zan ba wa kakanninku, sai dai Kaleb ɗan Yefunne. Zai gan ta, zan ba shi duk ƙasar da tafin ƙafarsa ta taka, shi da zuriyarsa, gama ya bi Ubangiji da zuciya ɗaya.” Saboda ku Ubangiji ya husata da ni, ya kuma ce, “Kai ma, ba za ka shiga ƙasar ba. Amma mataimakinka, Yoshuwa ɗan Nun, zai shiga. Ka ƙarfafa shi gama shi ne zai jagoranci Isra’ila su gāje ta. Amma ’ya’yanku ƙanana waɗanda ba su san mugunta ko nagarta ba, waɗanda kuke tsammani za a kwashe su ganima, su za su shiga ƙasar. Zan ba da ita gare su, za su kuwa mallake ta. Amma ku kam, sai ku juya, ku koma cikin hamada ta hanyar Jan Teku.” Sai kuka amsa, kuka ce, “Mun yi zunubi ga Ubangiji. Za mu haura mu yi yaƙi yadda Ubangiji Allahnmu ya umarce mu.” Saboda haka kowannenku ya yi ɗamara da kayan yaƙinsa, kuka yi tsammani zai zama muku da sauƙi ku ci ƙasar tuddai da yaƙi. Amma Ubangiji ya ce mini, “In faɗa muku, ‘Kada ku fāɗa musu da yaƙi, gama ba zai kasance tare da ku ba. Idan kuka kuskura, abokan gābanku za su murƙushe ku.’ ” Sai na faɗa muku, amma ba ku saurara ba. Kuka yi tawaye ga umarnin Ubangiji, a cikin jahilcinku kuwa kuka taka, kuka haura cikin ƙasar tudu. Amoriyawan da suke zama a waɗannan tuddai, suka fito kamar tarin ƙudan zuma gāba da ku, suka kore ku, suka fatattake ku daga Seyir har zuwa Horma. Kuka dawo, kuka yi kuka a gaban Ubangiji, amma bai kula da ku ba, balle yă saurare ku. Haka kuwa kuka zauna a Kadesh kwanaki masu yawa, kuka ci lokaci a can. Sai muka juya muka kama hanya, muka nufi hamada, ta hanyar Jan Teku yadda Ubangiji ya umarce ni. Da daɗewa muka yi ta yawo kewaye da ƙasar tudun Seyir. Sai Ubangiji ya ce mini, “Kun yi ta yawo kewaye da ƙasar tudun nan da daɗewa; yanzu ku juya, ku nufi arewa. Ka ba wa mutane waɗannan umarnai, ka ce, ‘Kuna gab da wucewa cikin yankin ’yan’uwanku, zuriyar Isuwa, wanda yake zama a Seyir. Za su ji tsoronku, amma ku yi hankali kada ku tsokane su da yaƙi, gama ba zan ba ku wata ƙasa daga cikinsu ba, ba ma wadda za tă iya isa ku sa ƙafarku a kai. Na ba wa Isuwa ƙasar tudu ta Seyir, ta zama tasa. Duk abincin za ku ci, da ruwan da za ku sha, za ku biya su.’ ” Ubangiji Allahnku ya albarkace ku cikin dukan aikin hannuwanku. Ya kiyaye ku cikin tafiyarku a duk fāɗin hamada. Waɗannan shekaru arba’in Ubangiji Allahnku ya kasance tare da ku, ba kuwa kun rasa wani abu ba. Saboda haka muka ci gaba, muka wuce ’yan’uwanmu, zuriyar Isuwa, wanda yake zama a Seyir. Muka bar hanyar Araba, wadda ta haura daga Elat da Eziyon Geber, muka nufi wajen hamadar Mowab. Sai Ubangiji ya ce mini, “Kada ku dami Mowabawa, ko ku tsokane su da yaƙi, gama ba zan ba ku wani sashe na ƙasarsu ba. Na ba da Ar ga zuriyar Lot, ta zama mallakarsu.” (Emawa, mutane ne masu ƙarfi da kuma yawa, suna kuma da tsayi kamar Anakawa, dā sun zauna a can. Kamar Anakawa, su ma an ɗauka su Refahiyawa ne, amma Mowab suna kiransu Emawa. Haka ma Horiyawa, a dā sun zauna a Seyir, amma zuriya Isuwa suka kore su. Suka hallaka Horiyawa da suke kafinsu, suka kuma zauna a wurinsu, kamar dai yadda Isra’ila ta yi a ƙasar da Ubangiji ya ba su a matsayin mallaka.) Ubangiji kuwa ya ce, “Yanzu ku tashi ku ƙetare Kwarin Zered.” Sai muka ƙetare kwarin. Dukan shekarun da muka yi a tafiyarmu daga Kadesh Barneya zuwa lokacin da muka ƙetare Kwarin Zered, sun kai shekaru talatin da takwas. A lokacin, wannan tsara gaba ɗaya ta mutanen da suka isa yaƙi sun mutu daga sansani, yadda Ubangiji ya rantse musu. Hannun Ubangiji ya yi gāba da su sai da ya hallaka su ƙaƙaf daga sansani. To, sa’ad da na ƙarshe cikin waɗannan mayaƙa a cikin mutanen ya rasu, sai Ubangiji ya ce mini, “Yau za ku wuce ta yankin Mowab a Ar. Sa’ad da kuka iso kusa da Ammonawa, kada ku dame su, ko ku tsokane su da yaƙi, gama ba zan ba ku mallakar wata ƙasar da take ta Ammonawa ba. Na riga na ba da ita mallaka ga zuriyar Lot.” (Wannan ita ma a ɗauka ta a matsayin ƙasar Refahiyawa waɗanda dā sun zauna a can ne; amma Ammonawa suna ce da su Zamzummawa. Mutane ne masu ƙarfi da kuma yawa, suna kuma da tsayi kamar Anakawa. Ubangiji ya hallaka su daga gaban Ammonawa, waɗanda suka kore su, suka kuma zauna a wurinsu. Ubangiji ya yi daidai yadda ya yi wa zuriyar Isuwa waɗanda suka zauna a ƙasar Seyir, sa’ad da ya hallaka Horiyawa a gabansu. Su kuma suka kore su, suka zauna a wurinsu. Har wa yau, zuriyar Isuwa ne suke zama a can. Kusan abu ɗaya ya faru, sa’ad da Kaftorawa daga ƙasar Kaftor suka hallaka Awwiyawa, waɗanda dā suke zaune a yankin ƙauyukan da suke kewaye da Gaza. Suka zauna a wurinsu.) “Ku fito yanzu ku ƙetare Kwarin Arnon. Duba, na ba da Sihon mutumin Amoriyawa a hannunku, na kuma ba da sarkin Heshbon da ƙasarsa. Ku fara mallake ta, ku kuma yi yaƙi da shi. A wannan rana zan fara sa tsoro da fargabanku a kan dukan al’ummai, a ƙarƙashin sama. Za su ji labarinku, za su yi rawan jiki, su kuma damu saboda ku.” Daga hamadar Kedemot, na aiki ’yan saƙo zuwa wurin Sihon sarkin Heshbon, a kan ina neman zaman lafiya, ina cewa, “Bari mu wuce cikin ƙasarka. Za mu bi ta kan hanya ne kaɗai; ba za mu ratse dama ko hagu ba. Ka sayar mana da abincin da za mu ci, da kuma ruwan da za mu sha a farashinsu na azurfa. Ka dai bar mu mu wuce ta ƙasarka kawai, kamar yadda zuriyar Isuwa, waɗanda suke zaune a Seyir, da Mowabawa, waɗanda suke zaune a Ar, suka yardar mana, gama muna so mu ƙetare Urdun zuwa ƙasa wadda Ubangiji, Allahnmu yake ba mu.” Amma Sihon sarkin Heshbon ya ƙi yă bar mu mu wuce a ciki. Gama Ubangiji Allahnku ya sa ruhunsa ya taurare don yă ba da shi a hannuwanku kamar yadda ya yi yanzu. Ubangiji ya ce mini, “Duba, na fara ba da Sihon da ƙasarsa gare ku. Yanzu ku fara cinta, ku kuma mallake ƙasarsa.” Sa’ad da Sihon da dukan sojojinsa suka fito don su sadu da mu, a yaƙi, a Yahaz, sai Ubangiji Allahnmu ya ba da shi gare mu, muka kuwa buga shi tare da ’ya’yansa maza da kuma dukan sojojinsa. A wannan lokaci mun ci dukan biranensa, muka kuma hallaka su, maza, mata da kuma yara. Ba mu bar wani da rai ba. Amma muka washe, muka kuma kwasa shanu da kuma ganima daga biranen wa kanmu. Ubangiji Allahnmu ya taimake mu muka ci Arower wadda take a gefen Kwarin Arnon, da garin da yake a cikin kwarin, har zuwa Gileyad. Babu garin da ya gaggare mu. Amma bisa ga umarnin Ubangiji Allahnmu, ba ku yi kusa da wata ƙasar Ammonawa, ko ƙasar da take gefen kwarin kogin Yabbok, ko kuwa wadda take kewaye da birane cikin tuddai ba. Biye da wannan muka juya muka haura ta hanyar wajen Bashan, inda Og, sarkin Bashan tare da dukan mayaƙansa suka fito don su sadu da mu a yaƙi, a Edireyi. Ubangiji ya ce mini, “Kada ka ji tsoronsa, gama na riga na miƙa shi da dukan mayaƙansa da kuma ƙasarsa gare ka. Yi masa abin da ka yi wa Sihon sarkin Amoriyawa, wanda ya yi mulkin Heshbon.” Saboda haka Ubangiji Allahnmu ya ba da Og, sarkin Bashan da dukan mayaƙansa a hannuwanmu. Muka karkashe su, ba mu bar wani da rai ba. A wannan lokaci muka kwashe dukan biranensa. Babu ɗaya daga birane sittin da ba mu ɗauke daga gare su ba, dukan yankin Argob, masarautar Og a Bashan. Dukan biranen nan masu katanga da suke da tsayi masu ƙofofi da ƙyamare, akwai kuma manya ƙauyukan da ba su da katanga. Muka hallaka su ƙaƙaf, kamar yadda muka yi wa Sihon sarkin Heshbon, muka hallaka kowace birni, maza, mata da yara. Amma dukan dabbobin da kuma ganimar daga biranensu muka kwaso wa kanmu. A lokacin ne muka ƙwace wannan ƙasa daga hannun sarakunan nan biyu na Amoriyawa, wato, ƙasa wadda take a hayin Urdun, daga Kwarin Arnon zuwa Dutsen Hermon. (Hermon ne Sidoniyawa suke kira Siriyon, Amoriyawa kuwa suna kira shi Senir.) Muka kama dukan biranen da suke kan tudu, da dukan Gileyad, da dukan Bashan, har zuwa Saleka da Edireyi, biranen masarautar Og a Bashan. (Og sarkin Bashan, ne kaɗai ya ragu cikin Refahiyawa. An yi gadonsa da ƙarfe, tsawon gadon ya fi ƙafa goma sha uku, fāɗinsa kuwa ƙafa shida ne. Yana nan a Rabba ta Ammonawa har yanzu.) Cikin ƙasar da muka kwasa a lokacin, na ba wa mutanen Ruben da mutanen Gad yankin arewa na Arower ta Kwarin Arnon, haɗe da rabin ƙasar tudu ta Gileyad, tare da biranenta. Sai kuma na ba wa rabin kabilar Manasse sauran rabin ƙasar tudu ta Gileyad da kuma dukan Bashan, masarautar Og (Wato, dukan yankin ƙasan nan na Argob a Bashan da dā ake kira ƙasar Refahiyawa. Yayir na zuriyar Manasse ya karɓi dukan yankin ƙasar Argob a Bashan har zuwa iyakar Geshurawa da Ma’akatiyawa. Sai ya kira ƙauyukan wurin da sunansa, Hawwot Yayir.) Na kuma ba da Gileyad ga Makir. Amma ga mutanen Ruben da mutanen Gad, na ba da yankin da ya tashi daga Gileyad, ya gangara zuwa Kwarin Arnon (tsakiyar kwarin kuwa shi ne iyaka) ya fita zuwa Kogin Yabbok, wanda yake shi ne iyakar Ammonawa. Iyakarsa daga yamma kuwa shi ne Urdun a Araba, daga Kinneret zuwa Tekun Araba (wato, Tekun Gishiri) a gangaren gindin Dutsen Fisga wajen gabas. Na umarce ku a lokacin na ce, “ Ubangiji Allahnku ya ba ku wannan ƙasa ku mallake ta. Dukan mayaƙanku za su haye da shirin yaƙi a gaban ’yan’uwanku, Isra’ilawa. Amma matanku, yaranku da dabbobinku (na sani kuna da dabbobi masu yawa), su ne za ku bari a garuruwan da na ba ku, sai Ubangiji ya ba da hutu ga sauran ’yan’uwanku, yadda ya yi da ku, su ma suka sami ƙasar da Ubangiji Allahnku yake ba su, a ƙetaren Urdun, sa’an nan kowannenku zai komo ga mallakar da na ba ku.” A lokacin nan na umarci Yoshuwa na ce, “Da idanunka ka ga dukan abin da Ubangiji Allahnku ya yi da waɗannan sarakuna biyu. Haka Ubangiji zai yi da dukan masarautai a can, inda za ku. Kada ku ji tsoronsu, gama Ubangiji Allahnku zai yi yaƙi dominku.” A lokacin, na roƙi Ubangiji na ce, “Ya Ubangiji Mai Iko Duka, ka fara nuna wa bawanka ɗaukakarka da ikonka. Akwai wani allah a sama ko a duniya, wanda zai aikata waɗannan manyan ayyukan kamar ka? Ina roƙonka, bari in ƙetare in ga ƙasa mai kyau ɗin nan a ƙetaren Urdun, wannan ƙasar mai kyau ta tuddai, da kuma Lebanon.” Amma saboda ku, Ubangiji ya yi fushi da ni, bai kuwa saurare ni ba. Sai Ubangiji ya ce, “Ya isa haka, kada ka ƙara yin magana da ni game da wannan batu. Haura zuwa ƙwanƙolin Fisga, ka dubi ƙasar da idanunka daga kowane gefe, yamma, da arewa, da kudu, da kuma gabas, gama ba za ka ƙetare wannan Urdun ba. Amma ka umarci Yoshuwa, ka ƙarfafa shi, ka kuma ba shi ƙarfin gwiwa, gama shi ne zai jagoranci wannan mutane su haye, yă kuma ba su gādon ƙasar da za ka gani.” Sai muka zauna a kwari kusa da Bet-Feyor. To, ku ji, ya Isra’ila, ku kasa kunne ga ƙa’idodi da dokokin da nake shirin koya muku. Ku bi su domin ku yi tsawon rai, ku kuma shiga ku mallaki ƙasar da Ubangiji, Allahn kakanninku yake ba ku. Kada ku ƙara, kada ku rage daga cikin abin da nake umarce ku. Amma ku kiyaye umarnan nan na Ubangiji Allahnku, da na ba ku. Da idanunku, kun ga abin da Ubangiji ya yi a Ba’al-Feyor. Yadda Ubangiji Allahnku ya hallaka waɗansu daga cikinku waɗanda suka yi wa Ba’al-Feyor sujada, Amma ku da kuka manne ga Ubangiji Allahnku, kuna da rai har wa yau. Ga shi, na koya muku ƙa’idodi da dokoki, yadda Ubangiji Allahna ya umarce ni, don ku bi su a ƙasar da za ku shiga ku mallaki. Ku kiyaye su, ku aikata su, gama yin haka zai tabbatar wa sauran al’ummai, kuna da hikima da ganewa. Sa’ad da al’ummai za su ji waɗannan dokoki, za su ce, “Ba shakka, wannan babbar al’umma tana da hikima da ganewa.” Wace al’umma ce mai girma haka wadda allolinta take kusa da su yadda Ubangiji Allahnmu yake kusa da mu a duk sa’ad da muka yi addu’a gare shi? Wace al’umma ce mai girma haka wadda take da ƙa’idodi da dokoki masu adalci kamar waɗannan ƙunshin dokokin da nake sa a gabanku a yau? Ku kula, ku kuma lura da kanku sosai, don kada ku manta da abubuwan da idanunku suka gani, ko kuwa ku bari su fita daga zuciyarku muddin ranku. Ku koyar da su ga ’ya’yanku, da ’ya’yan ’ya’yanku. Ku tuna da ranar da kuka tsaya a gaban Ubangiji Allahnku a Horeb, sa’ad da ya ce mini, “Ka tara mutane a gabana, don su ji maganata, su koya yin mini bangirma muddin ransu a ƙasar, su kuma iya koyar da su ga ’ya’yansu.” Sai kuka matso kusa, kuka tsaya a gindin dutse yayinda yana cin wuta har zuwa sararin sama, ga kuma baƙin gizagizai da kuma baƙin duhu. Sai Ubangiji ya yi magana daga wutar. Kuka ji furcin kalmomin, amma ba ku ga siffar kome ba, sai dai murya kaɗai kuka ji. Ya furta alkawarinsa gare ku, Dokoki Goma, waɗanda ya umarce ku ku bi, ya kuma rubuta su a alluna biyu. Sa’an nan Ubangiji ya umarce ni a wannan lokaci, in koya muku ƙa’idodi da dokokin da za ku bi a ƙasar da kuke hayewa Urdun don mallake. Ba ku ga wata siffa a ranar da Ubangiji ya yi magana da ku a Horeb daga wuta ba. Saboda haka ku lura da kanku sosai, don kada ku lalace, ku kuma yi wa kanku gunki, siffa ta wani kama, ko a kamannin namiji, ko kuwa ta mace, ko a kamannin wata dabba a duniya, ko na wani tsuntsun da yake tashi a sama, ko kuwa a kamannin wata halittar da take rarrafe a ƙasa, ko na wani kifi a cikin ruwaye a ƙarƙashi. Sa’ad da kuka ɗaga ido kuka kali sama, kuka ga rana da wata, da taurari, da dukan halittun sama, sai ku kula fa, kada ku jarrabtu, ku ce za ku yi musu sujada, ko ku bauta musu; abubuwan nan Ubangiji Allahnku ne ya rarraba wa dukan al’umman da suke ko’ina a ƙarƙashin sararin sama. Amma ku, Ubangiji ya ɗauke ku, ya fid da ku daga matuya mai narken ƙarfe, wato, daga Masar, domin ku zama jama’arsa ta musamman kamar yadda kuke a yau. Ubangiji ya yi fushi da ni saboda ku, ya kuma yi rantsuwa cewa ba zan haye Urdun, in shiga ƙasan nan mai kyau da Ubangiji Allahnku yake ba ku gādo ba. Zan mutu a wannan ƙasa; ba zan haye Urdun ba; amma kuna gab da ƙetarewa, ku mallaki wannan ƙasa mai kyau. Ku yi hankali kada ku manta da alkawarin da Ubangiji Allahnku ya yi da ku; kada fa ku yi wa kanku gunki a kamannin wani abin da Ubangiji Allahnku ya hana. Gama Ubangiji Allahnku wuta ne mai ƙuna, Allah ne mai kishi. Bayan kun haifi ’ya’ya da jikoki, kuka kuma zauna na dogon lokaci a ƙasar, in har kuka lalace, kuka kuma yi wani irin gunki, kuna aikata mugunta a gaban Ubangiji Allahnku, kuna kuma sa shi fushi. Yau, na kira sama da duniya, su zama shaidata a kanku. Idan kuka yi rashin biyayya, lalle za ku hallaka nan da nan daga ƙasar da kuke ƙetare Urdun ku gāda. Ba za ku daɗe a cikinta ba, amma za a kawar da ku ƙaƙaf. Ubangiji zai watsar da ku a cikin mutane, ɗan kaɗan ne kaɗai za su ragu a cikin al’umman da Ubangiji zai kai ku. A can za ku bauta wa allolin da mutum ya yi, na itace da dutse da ba sa gani, ba sa ji, ba sa ci, ba kuma iya sansanawa. Amma daga can in kuka nemi Ubangiji Allahnku, da dukan zuciyarku da kuma dukan ranku, za ku same shi. Sa’ad da kuke cikin wahala saboda waɗannan abubuwan da suka same ku nan gaba, to, sai ku juyo ga Ubangiji Allahnku, ku kuma yi masa biyayya. Gama Ubangiji Allahnku, Allah ne mai jinƙai; ba zai yashe ku ko yă hallaka, ko kuma yă manta da alkawarin da ya yi da kakanninku, wanda ya tabbatar da su da rantsuwa ba. Ku bincika dukan tarihi mana, tun daga lokacin da Allah ya halicci mutane a cikin duniya har yă zuwa yanzu; ku tantambaya daga wannan kusurwa ta samaniya zuwa waccan, ko wani babban abu irin wannan ya taɓa faruwa, ko kuma an taɓa jin labarin irinsa? Akwai waɗansu mutanen da suka taɓa jin muryar Allah yana magana daga wuta, kamar yadda kuka ji har suka rayu? Akwai wani allahn da ya taɓa yin ƙoƙari yă ɗauko wa kansa wata al’umma daga wata al’umma, ta wurin gwaje-gwaje, ta wurin alamu masu banmamaki da al’ajabai, ta wurin yaƙi, ta wurin hannu mai iko, da kuma hannu mai ƙarfi, ko kuwa ta wurin ayyuka masu bangirma da na banmamaki, kamar dukan abubuwan da Ubangiji Allahnku ya yi saboda ku a Masar, a kan idanunku? An nuna muku dukan waɗannan abubuwa saboda ku san cewa Ubangiji, shi ne Allah; ban da shi, babu wani. Daga sama ya sa kuka ji muryarsa, don yă hore ku. A duniya ya nuna muku wutarsa mai girma, kuka kuma ji kalmominsa daga wuta. Domin ya ƙaunaci kakanninku, ya kuma zaɓi zuriyarsu a bayansu, ya fitar da ku daga Masar ta wurin kasancewarsa da kuma ƙarfinsa mai girma, don yă fitar da ku a gaban al’ummai da suka fi ku girma da kuma ƙarfi, ya kawo ku cikin ƙasarsu, don yă ba ku ita ta zama gādonku, kamar yadda yake a yau. Ku sani, ku kuma riƙe a zuciya a wannan rana, cewa Ubangiji shi ne Allah a sama da kuma a ƙasa. Babu wani kuma. Ku kiyaye ƙa’idodi da umarnai, waɗanda nake ba ku a yau, domin zaman lafiyarku da kuma na zuriyarku bayan ba ku, domin kuma ku yi tsawon rai a ƙasa wadda Ubangiji Allahnku yake ba ku har abada. Sa’an nan Musa ya keɓe birane uku gabas da Urdun, waɗanda duk wanda ya yi kisankai, in ba da gangan ba ne ya kashe maƙwabcinsa, wanda babu ƙiyayya tsakaninsu a dā, zai iya gudu zuwa. Zai iya gudu zuwa cikin ɗaya daga waɗannan birane, yă tsira da ransa. Biranen kuwa su ne, Bezer a dutsen hamada, don mutanen Ruben; Ramot Gileyad, don mutanen Gad; da kuma Golan a Bashan, don mutanen Manasse. Wannan ita ce dokar da Musa ya sa a gaban Isra’ilawa. Waɗannan su ne farillai, ƙa’idodi da kuma dokokin da Musa ya ba su, sa’ad da suka fito daga Masar. Sa’ad da suke a kwari kusa da Bet-Feyor, gabas da Urdun, a ƙasar Sihon sarkin Amoriyawa, wanda ya yi mulki a Heshbon, da Musa da Isra’ilawa suka ci da yaƙi sa’ad da suka fito daga Masar. Suka mallaki ƙasarsa da kuma ƙasar Og sarkin Bashan, sarakuna biyu na Amoriyawa, gabas da Urdun. Wannan ƙasa ta tashi daga Arower a kewayen Kwarin Arnon zuwa Dutsen Siyon (wato, Hermon), ya kuma haɗa da dukan Araba gabas da Urdun, har zuwa tekun Araba a gindin gangaren Fisga. Musa ya tattara dukan Isra’ila ya ce, Ku ji, ya Isra’ila, ƙa’idodi da dokokin da na furta a kunnuwanku a yau. Ku koye su, ku kuma tabbata kun bi su. Ubangiji Allahnmu ya yi alkawari da mu a Horeb. Ba da kakanninmu ba ne Ubangiji ya yi wannan alkawari, amma da mu ne, da dukanmu waɗanda muke da rai a yau. Ubangiji ya yi magana fuska da fuska da ku daga wuta a kan dutse. (A wannan lokaci na tsaya tsakanin Ubangiji da ku, don in furta muku maganar Ubangiji, domin kun ji tsoron wutar, ba ku kuwa hau dutsen ba.) Ya ce, “Ni ne Ubangiji Allahnka, wanda ya fitar da ku daga Masar, daga ƙasar bauta. “Ba za ka kasance da waɗansu alloli a gabana ba. Ba za ka yi wa kanka gunki, ko wata siffar abin da take a sama a bisa, ko siffar abin da yake a duniya a ƙasa, ko siffar abin da yake a cikin ruwa a ƙarƙashin ƙasa ba. Ba za ka rusuna musu, ko ka yi musu sujada ba. Gama Ni, Ubangiji Allahnka, Allah ne mai kishi, nakan hukunta ’ya’ya saboda zunuban iyaye har tsara ta uku da ta huɗu na waɗanda suka ƙi ni. Amma nakan nuna ƙauna ga dubban tsararraki na waɗanda suke ƙaunata, suke kuma kiyaye dokokina. Ba za ka yi amfani da sunan Ubangiji Allahnka a banza ba, gama Ubangiji zai ba wa duk mai yin amfani da sunansa a banza laifi. Ka kiyaye ranar Asabbaci ta wurin kiyaye ta da tsarki, yadda Ubangiji Allahnka ya umarce ka. Kwanaki shida za ka yi aiki, ka kuma yi dukan aikinka, amma rana ta bakwai, Asabbaci ne ga Ubangiji Allahnka. A kanta ba za ka yi wani aiki ba, ko kai, ko ɗanka, ko ’yarka, ko bawanka, ko baiwarka, ko saniyarka, ko jakinka, ko wani daga dabbobinka, ko baƙo a ƙofofinka, don bayinka maza da mata su ma su huta, kamar ka. Ka tuna fa, dā kai bawa ne a ƙasar Masar amma Ubangiji Allahnka ya fitar da kai daga can da iko da kuma ƙarfi. Saboda haka Ubangiji Allahnka ya umarce ka ka kiyaye ranar Asabbaci. Ka ba da girma ga mahaifinka da mahaifiyarka, yadda Ubangiji Allahnka ya umarce ka, don ka yi tsawon rai, ka kuma sami zaman lafiya a ƙasar da Ubangiji Allahnka yake ba ka. Kada ka yi kisankai. Kada ka yi zina. Kada ka yi sata. Kada ka ba da shaidar ƙarya a kan maƙwabcinka. Kada ka yi ƙyashin matar maƙwabcinka. Kada kuma ka yi sha’awar gidan maƙwabcinka, ko gonarsa, ko bayinsa maza da mata, ko saniyarka, ko jakinsa, ko dai wani abin da yake na maƙwabtanka.” Waɗannan su ne dokokin da Ubangiji ya furta da babbar murya ga taronku gaba ɗaya, a can dutse ta tsakiyar wuta, girgije da kuma baƙin duhu; bai kuma ƙara kome ba. Sa’an nan ya rubuta su a kan alluna biyu na dutse, ya kuma ba ni su. Sa’ad da kuka ji muryar daga duhu, yayinda dutsen yana cin wuta, dukan manyan kabilanku da dattawanku suka zo wurina. Kuka kuma ce, “ Ubangiji Allahnmu ya nuna mana ɗaukakarsa da zatinsa, mun kuma ji muryarsa a tsakiyar wutar. A yau mun ga cewa mutum zai iya rayu idan ma Allah ya yi magana da shi. Amma yanzu, don me za mu mutu? Wannan wuta mai girma za tă cinye mu, za mu kuwa mutu in muka ci gaba da jin muryar Ubangiji Allahnmu. Gama wanda ɗan adam ne ya taɓa jin muryar Allah mai rai yana magana daga wuta, kamar yadda muka ji, ya kuma tsira? Kai, ka matsa kusa, ka saurara ga dukan abin da Ubangiji Allahnmu ya faɗa. Sa’an nan ka faɗa mana dukan abin da Ubangiji Allahnmu ya faɗa maka. Za mu saurara, mu kuma yi biyayya.” Ubangiji ya ji ku, sa’ad da kuka yi magana da ni, sai Ubangiji ya ce mini, “Na ji abin da wannan mutane suka faɗa maka. Abin da suka faɗa daidai ne. Kash, da a ce zukatansu za su zama masu tsorona, su kuma kiyaye dukan dokokina kullum mana, saboda kome yă zama da lafiya gare su, da kuma ’ya’yansu har abada! “Je, ka faɗa musu su koma tentunansu. Kai kuwa ka tsaya a nan tare da ni saboda in ba ka umarnai, ƙa’idodi da kuma dokoki duka, da za ka koya musu don su bi a ƙasar da nake ba su, su mallaka.” Sai ku yi hankali don ku yi abin da Ubangiji Allahnku ya umarce ku; kada ku juya dama ko hagu. Ku yi tafiya cikin dukan hanyar da Ubangiji Allahnku ya umarce ku, saboda ku zauna, ku yi nasara, ku kuma yi tsawon rai a ƙasar da za ku mallaka. Waɗannan su ne umarnai, ƙa’idodi da kuma dokokin da Ubangiji Allahnku ya umarce ni in koya muku don ku kiyaye a ƙasar da kuke haye Urdun don mallaka, saboda ku, ’ya’yanku, da kuma ’ya’yansu bayansu za su ji tsoron Ubangiji Allahnku muddin kuna rayuwa ta wurin kiyaye dukan ƙa’idodinsa da umarnan da na ba ku, da kuma don ku yi tsawon rai. Ku ji, ya Isra’ila, ku kuma kula, ku kiyaye su don yă zama muku da lafiya, ku kuma ƙaru sosai a ƙasa mai zub da madara da zuma, kamar dai yadda Ubangiji, Allahn kakanninku ya yi muku alkawari. Ku ji, ya Isra’ila, Ubangiji Allahnmu, Ubangiji ɗaya ne. Ku ƙaunaci Ubangiji Allahnku da dukan zuciyarku, da dukan ranku, da kuma dukan ƙarfinku. Waɗannan umarnai da nake ba ku a yau, za su kasance a zukatanku. Ku koya wa ’ya’yanku su da himma. Yi musu magana game da su sa’ad da kuke zaune a gida, da sa’ad da kuke tafiya a hanya, sa’ad da kuke kwance, da sa’ad da kuka tashi. Ku ɗaura su su zama alamu a hannuwanku, ku kuma ɗaura su a goshinku. Ku rubuta su a dogaran ƙofofin gidajenku, da ƙofofinku. Sa’ad da Ubangiji Allahnku ya kawo ku cikin ƙasar da ya rantse ga kakanninku, ga Ibrahim, Ishaku da Yaƙub, yă ba ku, ƙasa mai girma, mai manyan biranen da ba ku kuka gina ba, gidaje cike da kowane irin abubuwa masu kyau, da ba ku kuka tanadar ba, rijiyoyin da ba ku kuka haƙa ba, da gonakin inabi da itatuwan zaitun da ba ku kuka shuka ba, sa’ad da kuwa kuka ci, kuka kuma ƙoshi, ku yi hankali cewa ba ku manta da Ubangiji wanda ya fitar da ku daga Masar, da gidan bauta ba. Ku ji tsoron Ubangiji Allahnku, ku bauta masa shi kaɗai, ku kuma yi alkawaranku da sunansa. Kada ku bi waɗansu alloli, allolin mutanen da suke kewaye da ku; gama Ubangiji Allahnku, wanda yake cikinku, Allah ne mai kishi, fushinsa kuma zai yi ƙuna gāba da ku, zai kuma hallaka ku daga fuskar ƙasar. Kada ku gwada Ubangiji Allahnku kamar yadda kuka yi a Massa. Ku tabbata kun kiyaye umarnan Ubangiji Allahnku, da farillansa da kuma ƙa’idodinsa da ya ba ku. Ku aikata abin da yake daidai da kuma mai kyau a idon Ubangiji, don yă zama muka da lafiya, ku kuwa shiga ku mallaki ƙasa mai kyau da Ubangiji ya yi alkawari da rantsuwa ga kakanninku. Zai kuwa korin dukan abokan gābanku da suke gabanku, yadda Ubangiji ya faɗa. Nan gaba, sa’ad da ’ya’yanku suka tambaye ku, “Mene ne ma’anar farillai, ƙa’idodi da kuma dokokin da Ubangiji Allahnmu ya umarce ku?” Sai ku gaya musu, “Dā mu bayin Fir’auna ne a Masar, amma Ubangiji ya fitar da mu daga Masar da hannu masu ƙarfi. A idanunmu Ubangiji ya aikata manyan alamu masu banmamaki, da al’ajabai gāba da Masarawa, da Fir’auna, da kuma dukan gidansa. Amma ya fitar da mu daga can domin yă kawo mu cikin ƙasar da ya yi wa kakanninmu alkawari tare da rantsuwa zai ba mu. Ubangiji ya umarce mu mu yi biyayya da dukan waɗannan ƙa’idodi, mu kuma ji tsoron Ubangiji Allahnmu, saboda kullum mu ci gaba, a kuma bar mu da rai, kamar yadda yake a yau. In kuma muka kula, muka kiyaye dukan dokokin nan a gaban Ubangiji Allahnmu, kamar yadda ya umarce mu, wannan zai zama adalci a gare mu.” Sa’ad da Ubangiji Allahnku ya kawo ku ƙasar da kuke shiga don ku mallaka, ya kuma kori al’ummai masu yawa a gabanku; wato, Hittiyawa, Girgashiyawa, Amoriyawa, Kan’aniyawa, Ferizziyawa, Hiwiyawa da Yebusiyawa, al’ummai bakwai masu girma da ƙarfi fiye da ku. Sa’ad da kuma Ubangiji Allahnku ya ba da su gare ku, kuka kuma ci su da yaƙi, sai ku hallaka su ƙaƙaf. Kada ku yi yarjejjeniya da su, kada kuma ku nuna musu jinƙai. Kada ku yi auratayya da su. Kada ku ba da ’ya’yanku mata wa ’ya’yansu maza, ko ku ɗauko ’ya’yansu mata wa ’ya’yanku maza. Gama za su juye ’ya’yanku maza daga bina, su bauta waɗansu alloli, fushin Ubangiji kuma zai ƙuna a kanku da sauri, zai kuma hallaka ku. Ga abin da za ku yi da su, za ku rurrushe bagadansu, ku ragargaza keɓaɓɓun duwatsunsu, ku farfashe ginshiƙan Asheransu, ku kuma ƙona gumakansu da wuta. Gama ku mutane masu tsarki ne ga Ubangiji Allahnku. Ubangiji Allahnku ya zaɓe ku daga dukan mutane a fuskar duniya, don ku zama mutanensa, kayan gādonsa. Ba don kun fi sauran al’ummai yawa ne ya sa Ubangiji ya ƙaunace ku, ya kuma zaɓe ku ba, gama ku ne mafi ƙanƙanta cikin dukan al’ummai. Amma ya zama haka domin Ubangiji ya ƙaunace ku, ya kuma kiyaye rantsuwar da ya yi wa kakanninku da ya fitar da ku da hannu mai ƙarfi, ya kuma cece ku daga ƙasar bauta, daga ikon Fir’auna sarkin Masar. Saboda haka, ku sani cewa Ubangiji Allahnku, shi ne Allah; shi Allah ne mai aminci, yana kiyaye alkawarinsa na ƙauna ga tsararraki dubu na waɗanda suke ƙaunarsa suke kuma kiyaye umarnansa. Amma waɗanda suke ƙinsa, a fili yakan sāka musu da hallaka; ba zai yi jinkiri yin ramuwa a kan maƙiyinsa ba, zai yi ramuwar a fili. Saboda haka, sai ku lura, ku bi umarnai, ƙa’idodi, da dokokin nan da nake ba ku a yau. In kuka mai da hankali ga waɗannan dokoki, kuka kuma yi hankali ga bin su, to, Ubangiji Allahnku zai kiyaye alkawarinsa na ƙauna gare ku, kamar yadda ya rantse wa kakanninku. Zai ƙaunace ku, yă albarkace ku, yă kuma ƙara yawanku. Zai albarkaci ’ya’yanku, amfanin gonarku; hatsinku, sabon ruwan inabinku da kuma mai, ƙanana shanunku, da ’yan tumaki na tumakinku, a ƙasar da ya rantse wa kakanninku cewa zai ba ku. Za a albarkace ku fiye da waɗansu mutane; babu wani cikin maza ko matanku da zai kasance babu haihuwa, ba kuwa wata dabbarku da za tă kasance babu haihuwa. Ubangiji zai kiyaye ku daga kowace cuta. Ba zai wahalshe ku da mugayen cututtukan da kuka sani a Masar ba, amma zai aukar wa dukan maƙiyanku. Dole ku hallaka dukan mutanen da Ubangiji Allahnku ya bashe su gare ku. Kada ku ji tausayinsu, kada kuma ku bauta wa allolinsu, gama wannan zai zama tarko gare ku. Wataƙila ku ce wa kanku, “Waɗannan al’ummai sun fi mu ƙarfi. Yaya za mu kore su?” Amma kada ku ji tsoronsu; ku tuna da kyau abin da Ubangiji Allahnku ya yi wa Fir’auna da kuma dukan Masar. Kun ga da idanunku, manyan gwaje-gwaje, alamu masu banmamaki da al’ajabai, hannu mai ƙarfi da kuma mai ikon da Ubangiji Allahnku ya fitar da ku. Ubangiji Allahnku zai yi haka ga dukan mutanen da yanzu kuke tsoro. Ban da haka ma, Ubangiji Allahnku zai aika da rina a cikinsu, har sai sun hallaka sauran mutanen da suka ragu, waɗanda suka ɓuya daga gare ku. Kada ku tsorata saboda su, gama Ubangiji Allahnku, wanda yake a cikinku, Allah ne mai girma da kuma mai banrazana. Da kaɗan da kaɗan Ubangiji Allahnku zai kore waɗannan al’ummai a gabanku. Ba a bari ku hallaka su duka gaba ɗaya ba, in ba haka namun jeji za su yaɗu kewaye da ku. Amma Ubangiji Allahnku zai ba da su gare ku, yana jefa su cikin rikicewa mai girma, har sai an hallaka su. Zai ba da sarakunsu a hannunku, za ku kuwa shafe sunayensu daga duniya. Babu wani da zai yi tsayayya da ku, za ku hallaka su. Ku ƙone siffar allolinsu da wuta. Kada ku yi ƙyashin azurfa ko zinariyar da aka rufe allolin da ita, Kada ku kwashe su, don kada su zamar muku tarko, gama abin ƙyama ne ga Ubangiji Allahnku. Kada ku kawo abin ƙyama cikin gidajenku, domin kada ku zama kamar su. Gaba ɗaya ku yi ƙyamarsu, ku ƙi su, gama an ware su, sun zama domin a hallaka. Ku hankali, ku bi kowane umarnin da nake ba ku a yau, saboda ku rayu, ku ƙaru, ku kuma shiga, ku mallaki ƙasar da Ubangiji ya alkawarta da rantsuwa ga kakanninku. Ku tuna yadda Ubangiji Allahnku ya bishe ku a dukan hanya, a cikin hamada waɗannan shekaru arba’in, don yă ƙasƙantar da ku, yă kuma gwada ku don yă san abin da yake a zuciyarku, ko za ku kiyaye umarnansa, ko babu. Ya ƙasƙantar da ku, ya bar ku da yunwa, sa’an nan ya ciyar da ku da Manna, wadda ku, ko kakanninku, ba su sani ba, ta haka ne ya sa kuka sani cewa, ba da abinci kaɗai mutum zai rayu ba, amma ta wurin kowace kalmar da ta fito daga bakin Ubangiji. Tufafinku ba su yayyage ba, ƙafafunku kuma ba su kumbura ba a waɗannan shekaru arba’in. Sai ku sani fa a cikin zuciyarku cewa kamar yadda mutum kan horar da ɗansa, haka Ubangiji Allahnku ke horar da ku. Ku kiyaye umarnan Ubangiji Allahnku, kuna tafiya cikin hanyoyinsa, kuna kuma girmama shi. Gama Ubangiji Allahnku yana fitar da ku zuwa cikin ƙasa mai kyau, ƙasa mai rafuffuka da tafkunan ruwa, tare da maɓulɓulai masu gudu a kwari da tuddai; ƙasa mai alkama da sha’ir, inabi da ɓaure, rumman, man zaitun da zuma; ƙasa inda abinci ba zai yi ƙaranci ba, ba kuma za ku rasa kome ba; ƙasa ce inda ƙarfe ne duwatsunta, ana kuma haƙar tagulla a tuddanta. Sa’ad da kuka ci, kuka ƙoshi, sai ku yabi Ubangiji Allahnku saboda ƙasa mai kyau da ya ba ku. Ku yi hankali cewa ba ku manta da Ubangiji Allahnku, har ku kāsa kiyaye umarnansa, dokokinsa da ƙa’idodinsa da nake ba ku a wannan rana ba. To, sa’ad da kuka ci, kuka ƙoshi, sa’ad da kuka gina gidaje masu kyau, kuka zauna, sa’ad da kuma garkunanku na shanu da na tumaki suka ƙaru, azurfanku da zinariyarku kuma suka ƙaru, sa’an nan dukan abin da kuke da shi ya haɓaka, to, sai ku lura, kada ku ɗaukaka kanku, har ku manta da Ubangiji Allahnku, wanda ya fitar da ku daga Masar, daga ƙasar bauta kuma. Ya bishe ku cikin hamada mai fāɗi, mai bantsoro, wannan busasshiyar ƙasa wadda ba ta da ruwa, ga macizai masu dafi da kuma kunamai. Ya ba ku ruwa daga dutsen ƙanƙara. Ya ba ku Manna don ku ci a cikin hamada, wani abin da kakanninku ba su taɓa sani ba, don yă ƙasƙantar yă kuma gwada ku, saboda yă yi muku alheri daga baya. Wataƙila ku ce wa kanku, “Ikona da ƙarfin hannuwana ne suka ba ni da wannan arziki.” Amma ku tuna da Ubangiji Allahnku, gama shi ne wanda yake ba ku azanci na yin arziki, ta haka kuwa ya tabbatar da alkawarinsa, wanda ya rantse wa kakanninku, kamar yadda yake a yau. In kuka manta da Ubangiji Allahnku, kuka kuma bi waɗansu alloli, kuka yi musu sujada, kuka kuma rusuna musu, to, a yau ina gargaɗe ku cewa tabbatacce za a hallaka ku. Kamar al’ummai da Ubangiji ya hallakar kafin ku, haka zai hallaka ku, domin ba ku yi biyayya da muryar Ubangiji Allahnku ba. Ku ji, ya Isra’ila. Kuna gab da haye Urdun, ku shiga, ku kuma kori al’ummai da suka fi ku yawa, suka kuma fi ku ƙarfi, masu manyan biranen da suke da katangar da suka yi tsaye zuwa sama. Mutane ne masu ƙarfi, kuma dogaye, zuriyar Anakawa! Ai, kun ji akan ce, “Wa zai iya tsayayya da Anakawa?” Amma ku zauna da sani a yau, cewa Ubangiji Allahnku, shi ne wanda ya ƙetare ya sha gabanku kamar wuta mai cinyewa. Zai hallaka su, zai rinjaye su a gabanku. Za ku kore su, ku kuma hallaka su nan da nan, yadda Ubangiji ya yi muku alkawari. Bayan Ubangiji Allahnku ya kore su a gabanku, kada ku faɗa a zuciyarku, “Ubangiji ya kawo mu a nan, mu mallaki wannan ƙasa saboda adalcinmu ne.” A’a, saboda muguntar waɗannan al’umma ne ya sa Ubangiji ya kore su a gabanku. Ba domin adalci ko mutuncinku ba ne ya sa za ku mallaki ƙasarsu; sai dai saboda muguntar al’umman nan ne ya sa Ubangiji Allahnku yana korinsu a gabanku don yă cika abin da ya rantse wa kakanninku, wato, Ibrahim, Ishaku da Yaƙub. Ku gane wannan, cewa ba domin adalcinku ba ne ya sa Ubangiji Allahnku yana ba ku wannan ƙasa mai kyau, ku mallaki, gama ku mutane masu taurinkai ne. Ku tuna da wannan, kada kuma ku manta yadda kuka tsokane Ubangiji Allahnku, har ya yi fushi a hamada. Daga ranar da kuka bar Masar har sai da kuka isa nan, kuna ta tawaye wa Ubangiji. A Horeb, kun tayar wa Ubangiji har ya yi fushin da ya isa yă hallaka ku. Sa’ad da na hau kan dutse don in karɓi allunan dutse, allunan alkawarin da Ubangiji ya yi da ku, na zauna a kan dutse yini arba’in da dare arba’in; ban ci abinci ba, ban sha ruwa ba. Ubangiji ya ba ni alluna biyu wanda shi kansa ya yi rubutu da yatsarsa. A kansu akwai dukan umarnan Ubangiji da an furta muku a kan dutse a tsakiyar wuta, a ranar taron jama’a. A ƙarshen yini arba’in da dare arba’in ɗin, Ubangiji ya ba ni alluna biyu na dutse, allunan alkawari. Sa’an nan Ubangiji ya faɗa mini, “Sauka daga nan da sauri, domin mutanenka waɗanda ka fitar da su daga Masar sun lalace. Sun juye da sauri daga abin da na umarce su, suka kuma yi zubin gunki wa kansu.” Sai Ubangiji ya ce mini, “Na ga mutanen nan, su masu taurinkai ne sosai! Bar ni kawai, in hallaka su, in kuma shafe sunansu daga ƙarƙashin sama. Zan kuwa yi maka wata al’umma mafi ƙarfi da kuma masu yawa fiye da su.” Saboda haka na juya, na sauko daga dutsen yayinda yake cin wuta. Allunan biyu na alkawarin kuma suna a hannuwana. Sa’ad da na duba, sai na ga cewa kun yi zunubi wa Ubangiji Allahnku; kun yi wa kanku gunkin da kuka yi zubi a siffar ɗan maraƙi. Kun kauce da sauri daga hanyar da Ubangiji ya umarce ku. Saboda haka na ɗauko alluna biyun na jefar da su daga hannuwana, na farfashe su a idanunku. Sai nan da nan kuma na fāɗi rubda ciki a gaban Ubangiji, yini arba’in da dare arba’in; ban ci ba, ban sha ba, kamar yadda dā na yi, duka saboda zunubin da kuka aikata a gaban Ubangiji. Ta haka kuka tsokane shi don yă yi fushi. Na ji tsoron fushi da hasalar Ubangiji, gama ya yi fushin da ku da ya isa yă hallaka ku. Amma na yi roƙo a lokacin, Ubangiji kuwa ya saurare ni. Ubangiji ya yi fushi sosai da Haruna, har ya yi niyya yă hallaka shi, amma a wannan lokaci, na yi addu’a saboda Haruna shi ma. Sa’an nan na ɗauki kayan zunubin da kuka yi, wato, gunkin ɗan bijimi, na ƙone shi da wuta, na farfashe shi, na niƙa shi liɓis, sai da ya zama kamar ƙura mai laushi, na zubar da ƙurar a cikin ruwan rafin da yake gangarowa daga dutse. Kun kuma sa Ubangiji ya yi fushi a Tabera, a Massa da kuma a Kibrot Hatta’awa. Sa’ad da Ubangiji ya aike ku daga Kadesh Barneya ya ce, “Ku haura ku mallaki ƙasar da na ba ku.” Amma kuka yi tawaye ga umarnin Ubangiji Allahnku. Ba ku amince da shi, ko ku yi masa biyayya ba. Kun yi ta tawaye wa Ubangiji tun ran da na san ku. Na kwanta rubda ciki a gaban Ubangiji waɗannan yini arba’in da dare arba’in domin Ubangiji ya ce zai hallaka ku. Na yi addu’a ga Ubangiji na ce, “Ya Ubangiji Mai Iko Duka, kada ka hallaka mutanenka, gādon kanka, da ka fansa ta wurin ikonka mai girma, ka kuma fitar da su daga Masar da hannu mai ƙarfi. Ka tuna da bayinka Ibrahim, Ishaku da Yaƙub. Kada ka kula da taurinkan, mugunta da kuma zunubin wannan mutane. In ba haka ba, ƙasar da ka fitar da mu, za tă ce, ‘Domin Ubangiji bai iya kai su cikin ƙasar da ya yi musu alkawari ba ne, kuma domin ya ƙi su, shi ya sa ya fitar da su ya kashe su a hamada.’ Amma su mutanenka ne, gādonka da ka fitar ta wurin ikonka mai girma, da kuma hannunka mai ƙarfi.” A lokacin Ubangiji ya ce mini, “Ka sassaƙa alluna biyu na dutse kamar na farko, ka haura wurina a kan dutse. Ka kuma yi akwatin katako. Ni kuwa zan yi rubutu a kan allunan nan biyu, kalmomin da suke a alluna na farko, waɗanda ka farfashe. Za a ajiye su a cikin akwatin.” Sai na yi akwatin da itacen ƙirya, na kuma sassaƙa alluna biyu na dutse kamar na farko, sai na haura dutse da alluna biyun a hannuwana. Ubangiji kuwa ya sāke yin rubutu a waɗannan alluna abin da ya rubuta a allunan farko, wato, Dokoki Goma da ya furta a kan dutse a tsakiyar wuta, a ranar da mutane suka taru. Sai Ubangiji ya ba ni su. Sa’an nan na sauko daga dutsen, na kuma ajiye allunan a cikin akwatin da na yi, yadda Ubangiji ya umarce ni, kuma suna can a yanzu. (Isra’ilawa suka kama hanya daga rijiyoyin Beyerot Bene Ya’akan zuwa Mosera. A can Haruna ya rasu, aka kuma binne shi. Sai Eleyazar ɗansa ya gāje shi a matsayin firist. Daga can suka tashi zuwa Gudgoda, daga Gudgoda kuma suka tafi Yotbata, ƙasa mai rafuffukan ruwa. A lokacin Ubangiji ya keɓe kabilar Lawi don su riƙa ɗaukar akwatin alkawarin Ubangiji, su tsaya a gaban Ubangiji, su riƙa yin masa hidima, su kuma sa albarka a cikin sunansa, yadda suke yi har wa yau. Shi ya sa Lawiyawa ba su da rabo, ko gādo a cikin ’yan’uwansu; Ubangiji ne gādonsu yadda Ubangiji Allahnku ya faɗa musu.) To, na kasance a kan dutse yini arba’in da dare arba’in kamar yadda dā na yi da farko. Ubangiji kuwa ya saurare ni a wannan lokaci kuma. Ba nufinsa ba ne yă hallaka ku. Ubangiji ya ce mini, “Ka sauka, ka jagoranci mutanen a hanyarsu, domin su shiga, su kuma mallaki ƙasar da na rantse wa kakanninsu, zan ba su.” Yanzu fa, ya Isra’ila, mene ne Ubangiji Allahnku yake so a gare ku, in ba ku ji tsoron Ubangiji Allahnku, ku yi tafiya cikin hanyoyinsa, ku ƙaunace shi, ku bauta wa Ubangiji Allahnku da dukan zuciyarku da kuma dukan ranku, ku kuma kiyaye umarnan Ubangiji da kuma ƙa’idodinsa da nake ba ku a yau don amfaninku ba? Sammai, har da sama sammai, da duniya, da kome da yake cikinta na Ubangiji Allahnku ne. Duk da haka Ubangiji ya ƙaunaci kakanninku, ya kuma zaɓe ku, ku zuriyarsu, a bisa dukan al’ummai, yadda yake a yau. Saboda haka sai ku kame zukatanku, kada ku ƙara yin taurinkai. Gama Ubangiji Allahnku ne Allahn alloli da Ubangijin iyayengiji, Allah mai girma, mai ƙarfi da kuma mai banrazana, wanda ba ya sonkai, ba ya cin hanci. Yakan tsare marayu da gwauraye, yana ƙaunar baƙon da yake zama a cikinku, yana ba su abinci da tufafi. Sai ku ƙaunaci baƙi, gama dā ku ma baƙi ne a ƙasar Masar. Ku ji tsoron Ubangiji Allahnku, ku kuma bauta masa. Ku manne masa, ku kuma yi rantsuwarku da sunansa. Shi ne abin yabonku; shi ne Allahnku, wanda ya aikata muku waɗancan manya abubuwa banmamaki masu banrazanar da kuka gani da idanunku. Kakanninku da suka gangara zuwa Masar, su saba’in ne, yanzu kuwa Ubangiji Allahnku ya sa kuka ƙaru, kuka zama kamar taurari a sama. To, sai ku ƙaunaci Ubangiji Allahnku, kullum ku kuma kiyaye abubuwan da yake bukata, ku kiyaye ƙa’idodinsa, dokokinsa da kuma umarnansu. Ku tuna a yau, cewa ’ya’yanku ba su ne suka gani suka kuma ɗanɗana horon Ubangiji Allahnku ba; ba su suka gani girmansa, hannunsa mai ƙarfi, hannunsa mai iko; alamun da ya aikata da abubuwan da ya yi a cikin Masar, ga Fir’auna sarkin Masar da kuma ga dukan ƙasarsa ba; ba su suka gani abin da ya yi wa mayaƙan Masar, da dawakansu da keken yaƙinsu, yadda ya sha kansu da ruwan Jan Teku yayinda suke bin ku, da yadda Ubangiji ya hallaka su ƙaƙaf ba. Ba ’ya’yanku ba ne suka gani abin da ya yi dominku a hamada har sai da kuka kai wannan wuri ba, ba su ba ne suka gani abin da ya yi ga Datan da Abiram, ’ya’yan Eliyab mutumin Ruben, sa’ad da ƙasa ta buɗe bakinta a tsakiyar dukan Isra’ila ta haɗiye su tare da gidajensu, tentunansu da kowane abu mai rai da yake nasu ba. Amma idanunku ne suka ga dukan waɗannan manyan abubuwan da Ubangiji ya yi. Saboda haka sai ku kiyaye dukan umarnan da nake ba ku a yau, don ku sami ƙarfin da za ku shiga, ku kuma karɓi ƙasar da kuke haye Urdun ku mallaka, domin kuma ku yi tsawon rai a ƙasar da Ubangiji ya rantse wa kakanninku zai ba su da zuriyarsu, ƙasa mai zub da madara da zuma. Ƙasar da kuke shiga, ku karɓa, ba kamar ƙasar Masar ba ce, inda kuka fito, inda kuka shuka iri, ku yi ta zuwa kuna banruwa kamar lambu. Amma ƙasar da kuke haye Urdun ku mallaki, ƙasa ce ta duwatsu da kwaruruka wadda ruwan sama ne yake jiƙe ta. Ƙasa ce da Ubangiji Allahnku yake lura da ita; idanun Ubangiji Allahnku yana a kai daga farkon shekara har zuwa ƙarshenta. Saboda haka in kun yi biyayya ga umarnan da nake ba ku a yau cikin aminci, kuna ƙaunaci Ubangiji Allahnku, kuna kuma bauta masa da dukan zuciyarku da kuma dukan ranku, sai in aika da ruwan sama a ƙasarku a lokacinsa, ruwan saman bazara da kuma na kaka, don ku tattara hatsinku, sabon inabinku da kuma manku. Zan tanadar da ciyawa a filaye don shanunku, za ku ci, ku kuma ƙoshi. Ku yi hankali, kada a ruɗe ku har ku bauta wa alloli, ku kuma yi musu sujada, don kada fushin Ubangiji yă ƙuna a kanku, yă rufe sammai, ku rasa ruwa, ƙasa kuma ta kāsa ba da amfaninta, da haka za ku murmutu nan da nan a kyakkyawar ƙasar da Ubangiji yake ba ku. Saboda haka, sai ku riƙe waɗannan kalmomina gam a zukatanku da ranku; ku ɗaura su kamar alama a hannuwanku, da goshinku. Ku koyar da su ga ’ya’yanku, ku yi ta haddace su, sa’ad da kuke zaune a gida, da sa’ad da kuke tafiya, sa’ad da kuke kwance, da sa’ad da kuka tashi. Ku rubuta su a kan madogaran ƙofofin gidajenku, da a kan ƙofofinku, saboda kwanakinku da kwanakin ’ya’yanku su yi tsawo a ƙasar da Ubangiji ya rantse zai ba wa kakanninku, muddin sama tana bisa duniya. In kuka lura, kuka kuma kiyaye dukan umarnai da nake ba ku, ku ƙaunaci Ubangiji Allahnku, ku yi tafiya a hanyoyinsa, ku kuma riƙe shi gam, Ubangiji zai kori dukan waɗannan al’ummai a gabanku, za ku kuma kore al’umman da suka fi ku yawa da ƙarfi. Duk inda tafin ƙafanku ya taka, zai zama naku; iyakarku zai kama daga hamadan Lebanon da kuma daga Kogin Yuferites zuwa Bahar Rum. Babu mutumin da zai iya tsayayya da ku. Ubangiji Allahnku, zai sa razana da tsoronku a dukan ƙasar, a duk inda kuka tafi, kamar yadda ya alkawarta muku. Ga shi, a yau, ina sa a gabanku albarka da kuma la’ana, albarka in kun yi biyayya da umarnan Ubangiji Allahnku, da nake ba ku; la’ana in ba ku yi biyayya da umarnan Ubangiji Allahnku, kuka kuma juya daga hanyar da na umarce ku, ta wurin bin waɗansu alloli, waɗanda ba ku sani ba. Sa’ad da Ubangiji Allahnku ya kawo ku cikin ƙasar da za ku shiga ku ci gādonta, sai ku yi shelar albarkun nan a dutsen Gerizim, ku kuma yi na la’ana a dutsen Ebal. Waɗannan duwatsu biyu suna a hayin Urdun, yamma da hanya a ƙasar Kan’aniyawa mazaunan Araba, kusa da Gilgal wajajen manyan itatuwan More. Kuna gab da ƙetare Urdun fa, ku shiga, ku kuma mallaki ƙasar da Ubangiji Allahnku yake ba ku. Sa’ad da kuka karɓe ta, kuka kuma zauna a can, ku tabbata kun yi biyayya da dukan ƙa’idodi, da kuma dokokin da nake sawa a gabanku a yau. Waɗannan su ne ƙa’idodi da kuma dokokin da za ku lura, ku kuma kiyaye a ƙasar da Ubangiji, Allahn kakanninku, yake ba ku don ku ci gādonta, muddin kuna zama a ƙasar. Ku hallaka dukan wuraren da al’umman da kuke kora suke yi wa allolinsu sujada, a kan duwatsu masu tsawo, da a kan tuddai, da kuma ƙarƙashin kowane itace gaba ɗaya. Ku rurrushe bagadansu, ku farfashe keɓaɓɓun duwatsunsu, ku kuma ƙone ginshiƙan Asheransu da wuta; ku yayyanka gumakan allolinsu, ku kuma shafe sunayensu daga waɗannan wurare. Ba za ku yi wa Ubangiji Allahnku sujada a hanyar da suke yi ba. Amma sai ku nemi wurin da Ubangiji Allahnku zai zaɓa daga cikin dukan kabilanku, inda zai sa Sunansa, yă mai wurin mazauninsa. A wannan wuri ne za ku tafi; a can ne kuma za ku kawo hadayun ƙonawa da sadakoki, zakkarku da kyautai na musamman, da abin da kuka yi alkawari za ku bayar, da hadayunku na yardar rai, da kuma ’ya’yan farin garkunanku na shanu da na tumaki. A can, a gaban Ubangiji Allahnku, ku da iyalanku za su ci, su kuma yi farin ciki a kome da kuka sa hannunku a kai, domin Ubangiji Allahnku zai albarkace ku. Kada ku yi kamar yadda muke yi a nan yau, yadda kowa yake yin abin da ya ga dama. Gama ba ku kai wurin hutawa wanda Ubangiji Allahnku zai ba ku gādo ba tukuna. Amma sa’ad da kuka haye Urdun, kuka zauna a ƙasar da Ubangiji Allahnku yake ba ku ita gādo, zai kuwa ba ku hutu daga dukan abokan gābanku da suke kewaye da ku, kuka sami zaman lafiya, sai ku kai dukan abin da na umarce ku ku kai, wato, hadayu na ƙonawa, da sadakokinku, da zakkarku, da hadayunku na ɗagawa, da hadayunku na alkawarin da kuka yi wa Ubangiji a wurin da Ubangiji Allahnku ya zaɓa yă sa sunansa. A can kuma za ku yi farin ciki a gaban Ubangiji Allahnku, ku da ’ya’yanku maza da mata, da bayinku maza da mata, da kuma Lawiyawa daga biranenku, waɗanda ba a ba su rabo ba, ba su kuma da gādo na kansu. Ku kula fa kada ku miƙa hadayun ƙonawa a wani wurin da kuka ga dama. Ku miƙa su kawai a wurin da Ubangiji zai zaɓa a cikin ɗaya daga kabilanku, a can za ku yi kowane abin da na umarce ku. Amma kwa iya yanka nama ku ci a garuruwanku, a duk lokacin da ranku yake so, kamar yadda ake yi da gada ko barewa, bisa ga albarkar da Ubangiji Allahnku yake sa muku. Marar tsarki da mai tsarki, duka za ku iya ci. Amma kada ku ci jini, ku zubar da shi a ƙasa kamar ruwa. Kada ku ci zakkar hatsi, da na sabon inabi, da kuma na mai a biranenku, ko kuwa na ’ya’yan fari na garkunanku na shanu da na tumaki, ko kuwa duk wani abin da kuka yi alkawari za ku bayar, ko hadayunku na yardar rai, ko kyautai na musamman. A maimakon haka, sai ku ci su a gaban Ubangiji Allahnku a wurin da Ubangiji Allahnku ya zaɓa, da ku da ’ya’yanku maza da mata, da bayinku maza da mata, da kuma Lawiyawa daga biranenku, ku kuwa yi farin ciki a gaban Ubangiji Allahnku a kowane abin da kuka sa hannunku. Ku yi hankali, kada ku manta da Lawiyawa, muddin kuna zaune a ƙasarku. Sa’ad da Ubangiji Allahnku ya fadada iyakarku kamar yadda ya yi muku alkawari, kuka kuma ji marmarin nama, kuka kuma ce, “Muna so mu ci nama,” to, za ku iya cin yadda kuke so. In wurin da Ubangiji Allahnku ya zaɓa don yă sa Sunansa yana da nisa sosai daga inda kuke, za ku iya yankan dabbobi daga garkunanku na shanu da na tumakin da Ubangiji ya ba ku, kamar yadda na umarce ku, a cikin biranenku kuma za ku iya ci, yadda kuke so. Ku ci su yadda akan ci barewa ko mariri. Marar tsarki da mai tsarki, za ku iya ci. Amma ku tabbata ba ku ci jinin ba, domin jini ne rai, ba kuwa za ku ci rai cikin naman ba. Ba za ku ci jini ba, ku zubar da shi a ƙasa kamar ruwa. Kada ku ci shi, don ku zauna lafiya, da ku da ’ya’yanku bayanku, gama za ku riƙa aikata abin da yake daidai a gaban Ubangiji. Amma ku ɗauki abubuwa masu tsarki, da kuma duk abin da kuka yi alkawari za ku bayar, ku tafi inda Ubangiji ya zaɓa. Ku miƙa hadayunku na ƙonawa a bagaden Ubangiji Allahnku, da naman da kuma jinin. Dole a zub da jinin hadayunku a gindin bagaden Ubangiji Allahnku, amma za ku iya cin naman. Ku yi hankali, ku yi biyayya da dukan waɗannan umarnan da nake ba ku, da kuma ’ya’yanku, don ku zauna lafiya, da ku da ’ya’yanku a bayanku, gama za ku riƙa aikata abin da yake daidai da kuma yake mai kyau a gaban Ubangiji Allahnku. Ubangiji Allahnku zai kawar muku da al’umman nan da kuke niyyar shiga cikin ƙasarsu don ku kore su, bayan kuka kore su, kuka kuma zauna a ƙasarsu, to, sai ku lura, kada ku jarrabtu ku kwaikwaye su bayan da an riga an shafe su daga gabanku, kada ku tambayi kome game da allolinsu, kuna cewa, “Yaya waɗannan al’ummai suke bauta wa allolinsu? Mu ma za mu yi kamar yadda suka yi.” Ba za ku yi wa Ubangiji Allahnku sujada a hanyar da suke yi ba, gama a cikin yin sujada wa allolinsu, sun yi dukan abubuwan banƙyaman da Ubangiji yake ƙi. Har ma sukan ƙone ’ya’yansu maza da mata a wuta a matsayin hadayu. Ku lura, ku aikata dukan abin da na umarce ku; kada ku ƙara, kada ku rage daga cikin. In wani annabi ko mai mafarkai, ya bayyana a cikinku, ya kuma yi muku shelar wata alama mai banmamaki ko al’ajabi, in kuwa alamar, ko al’ajabin da annabin ya yi faɗin ya faru, ya kuma ce, “Bari mu bi waɗansu alloli (allolin da ba ku sani ba) mu kuma yi musu sujada,” kada ku saurari kalmomin wannan annabi ko mai mafarki. Ubangiji Allahnku yana gwada ku ne don yă sani ko kuna ƙaunarsa da dukan zuciyarku da kuma dukan ranku. Ubangiji Allahnku ne za ku bi, shi ne kuma za ku girmama. Ku kiyaye umarnansa, ku kuma yi masa biyayya; ku bauta masa, ku kuma manne masa. Dole a kashe wannan annabi ko mai mafarki, domin ya yi wa’azin tawaye ga Ubangiji Allahnku, wanda ya fitar da ku daga Masar, ya fanshe ku daga ƙasar bauta; gama annabin nan ya yi ƙoƙari yă juye daga hanyar da Ubangiji Allahnku ya umarce ku, ku bi. Dole ku fid da mugu daga cikinku. In ɗan’uwanka, ko ɗanka, ko ’yarka, ko matar da kake ƙauna, ko abokinka na kusa, a ɓoye ya ruɗe ka, yana cewa, “Mu je mu yi wa waɗansu alloli sujada” (allolin da ko kai, ko kakanninka ba su sani ba, allolin mutanen kewayenku, ko na kusa, ko na nisa, daga wannan ƙarshen ƙasar zuwa wancan), kada ka yarda da shi, kada ma ka saurare shi. Kada ka ji tausayinsa. Kada ka haƙura da shi, ko ka tsare shi. Dole ka kashe shi. Dole hannunka yă zama na farko a kisansa, sa’an nan hannuwan sauran dukan mutane. Ku jajjefe shi da duwatsu har sai ya mutu, domin ya yi ƙoƙari yă juye ku daga Ubangiji Allahnku, wanda ya fitar da ku daga Masar, daga ƙasar bauta kuma. Sa’an nan dukan Isra’ila za su ji su kuma tsorata, babu kuma wani a cikinku da zai ƙara yin irin wannan mugun abu. In kuka ji an yi magana a kan wani daga cikin biranen da Ubangiji Allahnku yake ba ku ku zauna a ciki cewa mugaye sun taso a cikinku, suna rikitar da mutane a birni, suna cewa, “Mu je mu yi wa waɗansu alloli sujada” (allolin da ba ku sani ba), to, sai ku bincike labarin sosai a hankali. In kuwa gaskiya ne, an kuma tabbatar wannan abin ƙyama ya faru a cikinku, dole a karkashe dukan waɗanda suke zama a wannan birni da takobi. Ku hallaka su ƙaƙaf, ku karkashe mutanen birnin da kuma dabbobinsa. Ku tattara dukan ganimar birnin a tsakiyar gari, ku ƙone birnin da kuma ganimar ƙurmus a matsayin hadaya ta ƙonawa ga Ubangiji Allahnku. Birnin zai kasance kufai har abada, kada a sāke gina shi. Ba za a iske wani daga cikin abubuwan nan da aka haramta a hannuwanku ba, saboda Ubangiji yă juya daga fushinsa mai ƙuna, yă nuna jinƙai, yă ji tausayinku, yă kuma ƙara yawanku, kamar yadda ya alkawarta da rantsuwa ga kakanninku, domin kun yi biyayya da Ubangiji Allahnku, kuna kiyaye dukan umarnan da nake ba ku a yau, kuna kuma aikata abin da yake daidai a idanunsa. Ku ’ya’yan Ubangiji Allahnku ne. Kada ku yi wa kanku zāne, ko ku yi wa kanku aski irin da akan bar sanƙo, saboda wanda ya mutu, gama ku jama’a ce mai tsarki ga Ubangiji Allahnku. Daga dukan mutane a fuskar duniya, Ubangiji ya zaɓe ku, ku zama abin mallakarsa. Kada ku ci wani haramtaccen abu. Waɗannan su ne dabbobin da za ku iya ci, saniya, tunkiya, akuya, mariri, barewa, mariya, makwarna, mazo, gada da kuma tunkiyar dutse. Za ku iya cin duk dabbar da take da rababben kofato, wadda kuma take sāke tona abin da suka riga suka haɗiye. Amma, cikin waɗanda suke sāke tona abin da suka riga suka haɗiye ɗin, ko suke da rababben kofato, ba za ku ci raƙumi, zomo ko rema ba. Ko da yake suna sāke tona abin da suka riga suka haɗiye, suna kuma da rababben kofato, su ɗin marar tsarki ne gare ku. Alade ma marar tsarki ne; ko da yake yana da rababben kofato, shi ba ya sāke tona abin da ya riga ya haɗiye. Ba za ku ci namansu ko ku taɓa gawarsu ba. Cikin dukan halittun da suke cikin ruwa, za ku iya cin duk wani da yake da ƙege da ɓamɓaroki. Amma duk wani abin da ba shi da ƙege da ɓamɓaroki, ba za ku ci ba; gama marar tsarki ne gare ku. Za ku iya cin kowane tsuntsu mai tsabta. Amma waɗannan ba za ku ci ba, gaggafa, ungulu, ungulun kwakwa, duki, buga zaɓi, kowace irin shirwa, kowane irin hankaka, jimina, ƙururu, bubuƙuwa, kowane irin shaho, da mujiya, da babbar mujiya, ɗuskwi, kwasakwasa, ungulu, da babba da jaka, zalɓe, kowane irin jinjimi, katutu, da kuma jamage. Dukan ’yan ƙwari masu fikafikai masu rarrafe, haram ne a gare ku, kada ku ci su. Amma duk wata halitta mai fikafikai mai tsabta ce, za ku iya ci. Kada ku ci abin da kun samu ya riga ya mutu. Za ku iya ba wa baren da yake zama a cikin wani daga biranenku, zai kuwa iya cinsa, ko kuwa za ku iya sayar da shi wa baƙo. Amma ku jama’a ce mai tsarki ga Ubangiji Allahnku. Kada ku dafa ɗan akuya a cikin madara mamansa. Ku tabbata kun keɓe kashi ɗaya bisa goma na amfanin gonakinku kowace shekara. Ku ci zakkar hatsinku, da na sabon ruwan inabinku, da na manku, da kuma na ’ya’yan fari na garkunanku na shanu da na tumaki a gaban Ubangiji Allahnku, a wurin da ya zaɓa a matsayin mazauni don Sunansa, don ku koyi girmama Ubangiji Allahnku kullum. Amma in wurin nan yana da nisa sosai, Ubangiji Allahnku kuma ya albarkace ku, ba za ku kuwa iya riƙe zakkarku ba (Saboda wurin da Ubangiji ya zaɓa yă sa Sunansa ya yi nisa sosai), to, sai ku sayar da zakkar, ku tafi da kuɗin wurin da Ubangiji Allahnku ya zaɓa. Yi amfani da kuɗin ku saya duk abin da kuke so, ko shanu, ko tumaki, ko ruwan inabi, ko dai wani abin shan da ya yi tsami, ko kuwa duk abin da kuke so. Sai ku da gidanku, ku ci a can, a gaban Ubangiji Allahnku, ku kuma yi farin ciki. Kada dai ku manta da Lawiyawan da suke zama a biranenku, gama ba su da rabo, ko gādo na kansu. A ƙarshen kowace shekara uku, ku kawo dukan zakkarku na amfanin gona na wannan shekara, ku ajiye su a cikin birane, saboda Lawiyawa (waɗanda ba su da rabo ko gādo na kansu) da baƙo, da marayu, da kuma gwauraye, waɗanda suke zama a biranenku, su zo su ci su ƙoshi, ta haka Ubangiji Allahnku zai albarkace ku cikin dukan ayyukan hannuwanku. A ƙarshen kowace shekara ta bakwai, dole ku yafe basusuwan da kuke bi. Ga yadda za ku yafe basusuwan, kowane mai bin bashi, yă yafe bashin da yake bin ɗan’uwansa mutumin Isra’ila. Ba zai bukaci mutumin Isra’ila wanda yake ɗan’uwa yă biya shi bashi ba, gama an yi shelar lokacin da Ubangiji ya ajiye na yafe bashi. Za ku iya nemi baƙo yă biya ku bashin da kuke binsa, amma dole ku yafe duk wani bashin da kuke bin ɗan’uwa. Amma bai kamata a sami matalauci a cikinku ba, gama Ubangiji Allahnku zai albarkace ku a ƙasar da yake ba ku, ku mallaka a matsayin gādo, in dai kun yi cikakken biyayya ga Ubangiji Allahnku, kuka kuma lura, kuna kiyaye dukan waɗannan umarnan da nake ba ku yau. Gama Ubangiji Allahnku zai albarkace ku kamar yadda ya yi alkawari, za ku kuma ba al’ummai masu yawa bashi, amma ba za ku karɓa bashi daga wurin wani ba. Za ku yi mulkin al’ummai masu yawa, babu wata kuwa da za tă yi mulkinku. In akwai matalauci a cikin ’yan’uwanku, a duk wani daga cikin biranen da Ubangiji Allahnku yake ba ku, kada ku taurara zuciya, ko ku ƙi saki hannu ga ɗan’uwanku matalauci. A maimakon haka ku bayar hannu sake, ku kuma ba shi bashi gwargwadon abin da yake bukata a sauƙaƙe. Ku yi hankali kada ku riƙe wannan mugun tunani cewa, “Shekara ta bakwai, shekarar yafewar basusuwa, ta yi kusa,” har ku nuna mugun nufi ga ɗan’uwa mabukaci, ku ƙi ba shi wani abu. Zai yi kuka ga Ubangiji a kanku, abin kuwa zai zama laifi a kanku. Ku bayar hannu sake gare shi, ku kuma yi haka ba tare da gunaguni ba; saboda wannan fa Ubangiji Allahnku zai albarkace ku a cikin dukan aikinku, da kuma kome da kuka sa hannunku a kai. Kullum za ku kasance da matalauta a ƙasar. Saboda haka na umarce ku ku bayar hannu sake ga ’yan’uwa da kuma matalauta, da masu bukata a ƙasarku. In ɗan’uwa mutumin Ibraniyawa, namiji ko ta mace, ya sayar da kansa gare ka, ya kuma bauta maka shekaru shida, a shekara ta bakwai dole ka ’yantar da shi. Sa’ad da kuka sake shi, kada ku bar shi yă tafi hannu wofi. Ku ba shi kyautai hannu sake daga tumakinku, daga masussukarku, da kuma daga wurin matsewar inabinku. Ku ba shi yadda Ubangiji Allahnku ya albarkace ku. Ku tuna, dā ku bayi ne a Masar, Ubangiji Allahnku kuma ya fisshe ku. Shi ya sa nake ba ku wannan umarni a yau. Amma in bawanka ya ce maka, “Ba na so in bar ka,” saboda yana ƙaunarka da iyalinka, ya kuma fiye masa yă zauna da kai, sai ka ɗauki basilla ka huda kunnensa a bakin ƙofa, zai kuwa zama bawanka dukan rayuwarsa. Ka yi haka ma wa baiwarka. Sa’ad da kuka ’yantar da shi kada ku damu, gama shekara shida ya yi muku bauta wadda ta ninka ta ɗan ƙodago. Ubangiji Allahnku kuwa zai albarkace ku a kome da kuke yi. Ku keɓe wa Ubangiji Allahnku kowane ɗan fari na garkenku na shanu, da na tumaki. Kada ku sa ɗan fari na shanunku aiki, kada kuma ku aske gashin ɗan fari na tumakinku. Kowace shekara, kai da iyalinka za ku ci su a gaban Ubangiji Allahnku, a wurin da ya zaɓa. In dabbar tana da lahani, gurguntaka ko makantaka, ko kuwa tana da wani mugun lahani, kada ku miƙa ta ga Ubangiji Allahnku. Sai ku ci a cikin biranenku. Mutum marar tsabta da mai tsabta zai iya ci kamar yadda ake yi da barewa ko mariri. Amma kada fa ku ci jinin, ku zubar da shi a ƙasa kamar ruwa. Ku kiyaye watan Abib, ku kuma yi shagalin Bikin Ƙetarewar Ubangiji Allahnku, domin a watan Abib ne ya fitar da ku daga Masar da dad dare. Ku miƙa ’yar dabba daga cikin garkenku na tumaki, ko na shanu a matsayin Bikin Ƙetarewa ga Ubangiji Allahnku a wurin da Ubangiji zai zaɓa a matsayin mazauni don Sunansa. Kada ku ci shi da burodin da aka yi da yisti, kwana bakwai za ku ci burodi marar yisti, burodi ne na wahala, gama kun bar Masar da gaggawa, saboda haka dukan kwanakin rayuwarku za ku tuna da lokacin da kuka fita daga Masar. Kada a iske yisti a cikin mallakarku a dukan ƙasarku har kwana bakwai. Kada ku bar wani nama na hadayar da kuka yi a yammancin ranar farko, yă kwana har safe. Kada ku miƙa hadayar Bikin Ƙetarewa a wani garin da Ubangiji Allahnku yake ba ku, sai dai a wurin da ya zaɓa yă zama mazauni don Sunansa. A can za ku miƙa hadayar Bikin Ƙetarewa da yamma, sa’ad da rana tana fāɗuwa, a ranar tunawa da fitowarku daga Masar. Ku gasa shi, ku kuma ci a wurin da Ubangiji Allahnku ya zaɓa. Sa’an nan da safe, ku dawo cikin tentunanku. Kwana shida za ku ci burodi marar yisti, a rana ta bakwai kuma sai ku yi taro ga Ubangiji Allahnku, a cikin wannan rana ba za ku yi kowane irin aiki ba. Ku ƙirga makoni bakwai, wato, ku fara ƙirga mako bakwai ɗin daga lokacin da kuka sa lauje don ku yanke hatsinku da suke tsaye. Sa’an nan ku yi shagalin Bikin Makoni ga Ubangiji Allahnku, ta wurin ba da hadaya ta yardar rai daidai da albarkun da Ubangiji Allahnku ya yi muku. Ku kuma yi farin ciki a gaban Ubangiji Allahnku a wurin da ya zaɓa a matsayin mazauni don Sunansa, da ku da ’ya’yanku maza da mata, da bayinku maza da mata, da Lawiyawan cikin biranenku, har ma da baƙi, da marayu, da kuma gwaurayen da suke zama a cikinku. Ku tuna fa, dā ku bayi ne a Masar, sai ku lura, ku bi waɗannan ƙa’idodi. Ku yi shagalin Bikin Tabanakul har kwana bakwai, bayan kuka gama tattara amfanin gona daga masussukarku da kuma daga wuraren matsin inabinku. Ku yi farin ciki a Bikinku, da ku da ’ya’yanku maza da mata, da bayinku maza da mata, da Lawiyawa, da baƙi, da marayu, da kuma gwaurayen da suke zama a cikin biranenku. Kwana bakwai za ku yi shagalin Bikin ga Ubangiji Allahnku a wurin da ya zaɓa. Gama Ubangiji Allahnku zai albarkace ku a cikin dukan girbinku da kuma cikin dukan aikin hannuwanku, farin cikinku kuwa zai cika. Sau uku a shekara dukan maza su bayyana a gaban Ubangiji Allahnku a wurin da ya zaɓa; a Bikin Burodi Marar Yisti, da a Bikin Makoni, da kuma a Bikin Tabanakul. Babu wani da zai bayyana a gaban Ubangiji hannu wofi. Dole kowannenku yă kawo kyauta daidai yadda Ubangiji Allahnku ya albarkace shi. Ku naɗa alƙalai da shugabanni don kowace kabila, a kowane birnin da Ubangiji Allahnku yake ba ku, za su kuma shari’anta mutane ba nuna bambanci. Kada ku ɓata shari’a, ko ku nuna bambanci. Kada ku karɓi cin hanci, gama cin hanci yakan makanta idanu mai hikima, yă murɗe maganar mai gaskiya. Gaskiya ce kaɗai za ku bi don ku rayu, ku kuma mallaki ƙasar da Ubangiji Allahnku yake ba ku. Kada ku kafa wani ginshiƙin itacen Ashera kusa da bagaden da kuka gina wa Ubangiji Allahnku, kada kuma ku tayar da dutse mai tsarki, gama waɗannan ne Ubangiji Allahnku yana ƙi. Kada ku miƙa wa Ubangiji Allahnku, saniya ko tunkiyar da take da wani lahani, ko naƙasa a cikinta, gama wannan zai zama abar ƙyama gare shi. In an sami wani namiji ko ta mace mai zama a cikinku, a ɗaya daga biranen da Ubangiji ya ba ku yana aikata abin da yake mugu a gaban Ubangiji Allahnku ta wurin karya alkawarinsa, wanda ya saba wa umarnina, har ya yi sujada ga waɗansu alloli, yana rusuna musu, ko ga rana, ko ga wata, ko kuwa ga taurarin sama, in kuwa aka faɗa muku wannan, to, dole a bincika sosai. In kuwa gaskiya ne, aka kuma tabbatar cewa wannan abin ƙyama ya faru a cikin Isra’ila, sai a ɗauki namijin, ko ta mace wanda ya aikata wannan mugun abu zuwa ƙofar birni, a jajjefe wannan mutum sai ya mutu. Bisa ga shaidar mutum biyu ko uku, za a iya kashe mutum, amma ba za a iya kashe mutum bisa ga shaida mutum guda ba. Hannuwan shaidun ne za su zama na farko a kisan wanda ake zargin, sa’an nan hannuwan dukan mutane. Dole ku fid da mugu daga cikinku. In aka kawo ƙarar da yake da wuya sosai ga alƙali a kotunanku, ko wadda aka zub da jini ne, ko ta faɗa ce, ko kuwa ta wadda aka ci mutunci ce, ku kai su wurin da Ubangiji Allahnku zai zaɓa. Ku je wurin firistoci, waɗanda suke Lawiyawa, ga kuma alƙalin wanda yake mulki a lokacin. Ku bincika daga gare su, za su kuwa ba da hukunci. Dole ku aikata hukuncin da suka yi a wurin da Ubangiji zai zaɓa. Ku lura fa, ku aikata kome da suka faɗa muku. Ku yi bisa ga dokar da suka koyar muku da kuma hukuncin da suka yi muku. Kada ku juya daga abin da suka faɗa muku, ko zuwa dama, ko zuwa hagu. Duk mutumin da ya yi rashin hankali wa alƙali, ko ga firist wanda yake aiki a nan wa Ubangiji Allahnku, dole a kashe shi. Dole ku fid da mugu daga Isra’ila. Dukan mutane kuwa za su ji, su kuma ji tsoro, ba kuwa za su ƙara yin rashin hankali kuma ba. Sa’ad da kuka shiga ƙasar da Ubangiji Allahnku yake ba ku, kuka mallake ta, kuka kuma zauna a cikinta, sai kuka ce, “Bari mu naɗa sarki a kanmu kamar sauran al’umman da suke kewaye da mu,” ku tabbata kun naɗa sarki a kanku wanda Ubangiji Allahnku ya zaɓa ne. Dole yă zama daga cikin ’yan’uwanku. Kada ku sa baƙo a kanku, wanda ba mutumin Isra’ila ɗan’uwanku ba. Sarkin, ba zai nemi dawakai da yawa wa kansa ba, ko yă sa mutane su koma Masar don su sami ƙarin dawakai ba, gama Ubangiji ya faɗa muku, “Ba za ku ƙara koma wancan hanya kuma ba.” Sarkin ba zai auri mata masu yawa ba, in ba haka ba zuciyarsa za tă karkata. Ba zai tara azurfa da zinariya da yawa ba. Sa’ad da ya hau kursiyin mulkinsa, sai yă rubuta wa kansa a littafin kofin wannan doka da aka ɗauka daga na firistoci, waɗanda suke Lawiyawa. Zai kasance tare da shi, zai kuma karanta shi dukan kwanakin ransa, saboda yă koyi girmama Ubangiji Allahnsa, yă kuma bi dukan kalmomin wannan doka da kuma waɗannan ƙa’idodi a hankali don kada yă ɗauki kansa ya fi ’yan’uwansa, yă kuma juya daga dokar zuwa dama, ko zuwa hagu. Sa’an nan shi da kuma zuriyarsa za su daɗe suna mulki a Isra’ila. Firistocin da suke Lawiyawa, tabbatacce dukan kabilar Lawi, ba za su sami rabo ko gādo tare da Isra’ila ba. Za su yi rayuwa a kan hadayun da aka kawo wa Ubangiji da wuta ne, gama wannan ne gādonsu. Ba za su sami gādo a cikin ’yan’uwansu ba; Ubangiji ne gādonsu, kamar yadda ya yi musu alkawari. To, ga rabon da jama’a za su ba firistoci daga hadayun da suka miƙa ta bijimi ne, ko ta tunkiya ce; sai su ba firistoci kafaɗar, kumatun, da kuma kayan cikin. Za ku ba su nunan fari na hatsinku, da sabon ruwan inabinku, da manku, da kuma gashi na fari daga askin da kuka yi na tumakinku. Gama Ubangiji Allahnku ya zaɓe su da zuriyarsu daga cikin dukan kabilanku don su tsaya su yi hidima a cikin sunan Ubangiji har abada. Idan Balawe ya tashi daga wani garinku, wurin da yake da zama a Isra’ila, ya tafi a wurin da Ubangiji ya zaɓa, zai iya dawo a duk lokacin da ya ga dama. Zai iya yin hidima a cikin sunan Ubangiji Allahnsa kamar dukan sauran ’yan’uwansa Lawiyawa waɗanda suke hidima a can, a gaban Ubangiji. Zai sami rabo daidai da sauran, ko da yake ya karɓi kuɗin mallaka na iyali da ya sayar. Sa’ad da kuka shiga ƙasar da Ubangiji Allahnku yake ba ku, kada ku kwaikwayi hanyoyin banƙyama na al’ummai da suke can. Kada a sami wani a cikinku da ya miƙa ɗansa, ko ’yarsa a wuta, ko a sami mai duba, ko mai maita, ko mai fassara gaibi, ko mai sihiri, ko boka, ko mabiya, ko maye, ko mai sha’ani da matattu. Duk wanda yake yin waɗannan abubuwa, shi abin ƙyama ne ga Ubangiji, saboda waɗannan abubuwa banƙyama ne kuwa Ubangiji Allahnku ya kori waɗancan al’ummai kafin ku. Dole ku zama marasa zargi a gaban Ubangiji Allahnku. Al’ummai da za ku kora sukan saurari waɗannan masu maita, ko masu duba. Amma ku, Ubangiji Allahnku bai yarda muku ku yi haka ba. Ubangiji Allahnku zai tayar muku da wani annabi kamar ni daga cikin ’yan’uwanku. Dole ku saurare shi. Gama abin da kuka nema daga Ubangiji Allahnku ke nan a Horeb, a ranar taro, sa’ad da kuka ce, “Kada ka bari mu ji muryar Ubangiji Allahnmu, ko mu ƙara ganin wuta mai girma, in ba haka ba, za mu mutu.” Sai Ubangiji ya ce mini, “Abin da suka faɗa yana da kyau. Zan tayar musu da wani annabi kamar ka daga cikin ’yan’uwansu; zan sa kalmomina a cikin bakinsa, zai kuma faɗa musu kome da na umarce shi. Duk wanda bai saurari kalmomina da annabin nan yake magana da sunana ba, ni kaina zan nemi hakki a kan mutumin. Amma duk annabin da ya ɗauka cewa yana magana da sunana a kan wani abin da ban umarce shi ya faɗa ba, ko kuwa wani annabin da ya yi magana da sunan waɗansu alloli, dole a kashe shi.” Mai yiwuwa ku ce wa kanku, “Yaya za mu san cewa wannan saƙo ba Ubangiji ne ya faɗa ba?” In abin da annabin ya furta da sunan Ubangiji bai faru ba, ko bai zama gaskiya ba, saƙo ne da Ubangiji bai faɗa ba ke nan. Wannan annabi ya yi rashin hankali ne kawai. Kada ku ji tsoronsa. Sa’ad da Ubangiji Allahnku ya hallakar da al’ummai waɗanda yake ba ku ƙasarsu, sa’ad da kuka kore su, kuka kuma zauna a birane da gidajensu, sai ku keɓe wa kanku birane uku waɗanda suke a tsakiyar ƙasar da Ubangiji Allahnku yake ba ku ku mallaka. Ku gina hanyoyi zuwa cikinsu, ku kuma raba ƙasar da Ubangiji Allahnku yake ba ku gādo kashi uku, saboda duk wani da ya yi kisankai yă iya gudu zuwa can. Ga doka game da mutumin da ya kashe wani, ya kuma gudu don yă cece ransa, wani wanda ya kashe maƙwabcinsa ba da gangan ba, ba kuwa da wata ƙiyayya a tsakaninsu a dā ba. Misali, in mutum ya je jeji da maƙwabcinsa domin yankan itace, sai ruwan gatarinsa ya kwaɓe daga ƙotar yayinda yake saran itacen, ya sari maƙwabcin har ya mutu. Mutumin nan zai iya gudu zuwa ɗaya daga cikin waɗannan birane don yă ceci ransa. In ba haka ba mai neman ɗaukan fansa jini, zai iya binsa cikin fushi, yă cim masa, saboda nisan hanyar, har ya kashe shi, ko da yake bai cancanci mutuwa ba, tun da yake ba ƙiyayya tsakaninsa da abokinsa a dā. Wannan ne ya sa na umarce ku ku keɓe wa kanku birane uku. In Ubangiji Allahnku ya fadada yankinku, kamar yadda ya alkawarta da rantsuwa wa kakanninku, ya kuma ba ku ƙasar gaba ɗaya kamar yadda ya yi musu alkawari, idan dai kun lura, kuka kiyaye umarnin da nake ba ku a yau, wato, ta wurin ƙaunar Ubangiji Allahnku, kuka kuma yi tafiya kullum cikin hanyoyinsa, to, sai ku keɓe ƙarin birane uku. Ku yi haka don kada a zub da jinin marar laifi a ƙasar da Ubangiji Allahnku yake ba ku gādo, don kada ku kuma zama masu laifin zub da jini. Amma idan wani mutum yana ƙin maƙwabcinsa, ya kuma yi kwanto yana fakonsa, ya yi masa rauni, har ya kashe shi, sa’an nan ya gudu zuwa ɗaya daga cikin waɗannan birane, dattawan garinsa za su aika a kawo shi, a dawo da shi daga birnin, a miƙa shi ga mai neman fansar jini don yă kashe shi. Kada ku ji tausayinsa. Dole ku fid da laifin zub da jinin marar laifi daga Isra’ila, don ku sami zaman lafiya. Kada ka gusar da dutsen nuna shaidar iyakar maƙwabcinka wanda kakanni suka sa, a gādon da ka samu a ƙasar da Ubangiji Allahnka yake ba ka mallaka. Shaidar mutum guda ba tă isa a tabbatar cewa mutum yana da laifi game da laifin da ake tuhumarsa ba, ko kuwa a kan wani laifin da ake zaginsa da aikata ba. Dole a tabbata da batun ta bakin shaidu biyu, ko uku. In wani ɗan sharri ya tashi ya yi wa wani sharri, don a sami wani da laifi, dole mutanen nan biyu da suke rikici su tsaya a gaban Ubangiji, a gaban firistoci da alƙalai waɗanda suke aiki a lokacin. Dole alƙalan su yi bincike sosai, in kuma aka tabbatar mai ba da shaida maƙaryaci ne, yana ba da shaidar zur a kan ɗan’uwansa ne, to, sai a yi da shi yadda ya yi niyya yă yi da ɗan’uwansa. Dole ku fid da mugu daga cikinku. Sauran mutane za su ji wannan su kuma ji tsoro, ba kuwa za a ƙara yin irin wannan mugun abu a cikinku ba. Kada ku ji tausayi, rai yă zama a maimakon rai, ido a maimakon ido, haƙori a maimakon haƙori, hannu a maimakon hannu, ƙafa a maimakon ƙafa. Sa’ad da kuka tafi yaƙi da abokan gābanku, kuka ga dawakai da kekunan yaƙi da kuma mayaƙan da suka fi ku yawa, kada ku ji tsoronsu, domin Ubangiji Allahnku, wanda ya fitar da ku daga Masar zai kasance tare da ku. Sa’ad da kuke gab da kama yaƙi, sai firist yă zo gaba yă yi wa mayaƙan jawabi. Zai ce, “Ku ji, ya Isra’ila, yau kuna gab da kama da abokan gābanku. Kada ku karai, ko ku ji tsoro; kada ku firgita, ko ku yi rawar jiki a gabansu. Gama Ubangiji Allahnku, yana tafe tare da ku, zai yaƙi abokan gābanku dominku, yă ba ku nasara.” Hafsoshi za su ce wa mayaƙa, “Ko akwai wanda ya gina sabon gida bai kuma buɗe shi ba? Bari yă tafi gida, kada yă mutu a yaƙi, wani dabam yă buɗe shi. Ko akwai wani da ya shuka inabi, bai kuwa fara jin daɗinsa ba? Bari yă tafi gida, kada yă mutu a yaƙi, wani dabam yă ji daɗinsa. Ko akwai wani da aka yi masa alkawarin mata, bai kuwa aure ta ko ba? Bari yă tafi gida, kada yă mutu a yaƙi, wani dabam yă aure ta.” Sa’an nan hafsoshin za su ƙara da cewa, “Ko akwai wani da yake tsoro, ko ya karai? Bari yă tafi gida don kada ’yan’uwansa su karai su ma.” Sa’ad da hafsoshin suka gama magana da mayaƙan, sai su naɗa komandodi a kansu. Sa’ad da kuka haura don ku fāɗa wa birni, sai ku fara neman garin da salama. In sun yarda da salamar, suka buɗe ƙofofin garinsu, to, sai dukan mutanen da suke cikinsa su yi muku aikin gandu, su kuma yi muku aiki. In kuwa suka ƙi salamar, suka fāɗa muku da yaƙi, sai ku yi wa wannan birni ƙawanya. Sa’ad da Ubangiji Allahnku ya ba da shi cikin hannunku, sai ku kashe dukan mazan da suke cikinsa da takobi. Game da mata, yara, dabbobi da kuma sauran abubuwan da suke cikin birnin, za ku iya kwasa waɗannan a matsayin ganima wa kanku. Za ku kuma yi amfani da ganimar da Ubangiji Allahnku ya ba ku daga abokan gābanku. Haka za ku yi da dukan biranen da suke nesa da ku, waɗanda kuma ba na al’ummai da suke kusa ba. Amma fa, a cikin biranen al’ummai da Ubangiji Allahnku yake ba ku gādo, kada ku bar wani abu mai numfashi da rai. Ku hallaka su ƙaƙaf, wato, Hittiyawa, Amoriyawa, Kan’aniyawa, Ferizziyawa, Hiwiyawa da kuma Yebusiyawa, yadda Ubangiji Allahnku ya umarce ku. In ba haka ba, za su koya muku ku bi dukan abubuwan banƙyaman da suke yi, ta yin sujada wa allolinsu, ta haka kuwa ku yi wa Ubangiji Allahnku zunubi. Sa’ad da kuka yi wa birni ƙawanya kuka daɗe, kuka yi ta yaƙi don ku ci shi, kada ku sassare itatuwansa da gatari, domin za ku ci ’ya’yansu. Kada ku sassare su. Gama itatuwan da suke cikin gonaki, ba mutane ne da za ku yi musu ƙawanya? Amma fa, za ku iya sassare itatuwan da kuka sani ba sa ba da ’ya’ya, ku kuma yi amfani da su don ayyukan gina ƙawanyar, sai an ci birnin da yaƙi. In aka sami an kashe mutum kwance a fili, a ƙasar da Ubangiji Allahnku yake ba ku ku mallaka, ba a kuma san wanda ya kashe shi ba, sai dattawanku da alƙalanku su je su gwada nisan wurin da gawar take zuwa garuruwan da suke maƙwabtaka. Sai dattawan garin da suke kurkusa da gawar su ɗauki karsanar da ba a taɓa yin aiki da ita ba, ba a kuma taɓa sa mata karkiya ba, a gangara da ita kwarin da ba a taɓa nome, ko shuki a ciki ba, inda kuma akwai rafi mai gudu, a can cikin kwarin za su karye wuyanta. Firistoci, ’ya’yan Lawi maza, za su fito, gama Ubangiji Allahnku ya zaɓe su su yi masa hidima, su kuma furta albarku a cikin sunan Ubangiji, za su kuma daidaita duk rigimar cin mutunci. Sa’an nan dukan dattawan garin da yake kurkusa da gawar za su wanke hannuwansu a bisa karsanan da aka karye wuyar a kwarin, za su kuma furta, “Hannuwanmu ba su zub da wannan jini ba, idanunmu kuma ba su ga an yi haka ba. Karɓi wannan kafara saboda mutanenka Isra’ila, wanda ka fansar, ya Ubangiji, kada kuma ka ɗaura wa mutanenka alhakin jinin mutumin nan marar laifi.” Za a kuwa yi kafarar zub da jinin da aka yi. Ta haka za ku fid da laifin zub da jinin marar laifi daga cikinku, da yake kun yi abin da yake daidai a gaban Ubangiji. Sa’ad da kuka tafi yaƙi da abokan gābanku, sai Ubangiji Allahnku ya bashe su a hannuwanku kuka kuma kama su a matsayin bayi, in ka ga wata kyakkyawar mace wadda ta ɗauki hankalinka a cikin bayin, za ka iya aure ta tă zama matarka. Ka kawo ta gidanka ka sa tă aske kanta, tă yanka kumbanta tă kuma tuɓe tufafin da ta sa sa’ad da aka kama ta. Bayan ta zauna a gidanka ta kuma yi makokin mahaifinta da mahaifiyarta wata ɗaya cif, sai ka shiga wurinta ka zama mijinta, za tă kuwa zama matarka. In ba ka jin daɗinta, ka bar tă tafi inda take so. Ba za ka sayar da ita ko ka yi da ita kamar baiwa ba, da yake ka ƙasƙantar da ita. In mutum yana da mata biyu, yana kuwa ƙaunar ɗaya, ba ya kuma ƙaunar ɗayan, su biyun kuwa suka haifi masa ’ya’ya maza, sai ya zamana cewa ɗan farin ya kasance na wadda ba ya ƙauna, to, a ranar da zai yi faɗa wane ne a cikin ’ya’yansa zai riƙe gādon da zai bar musu, kada yă sa ɗan matar da yake ƙauna yă zama kamar shi ne ɗan fari, a maimakon ɗan matar da ba ya ƙauna, wanda shi ne ɗan farin. Dole yă yarda cewa ɗan matar da ba ya ƙaunar ne ɗan fari, ta wurin ba shi rabo kashi biyu na dukan abin da yake da shi, gama shi ne mafarin ƙarfinsa, yana da hakkin ɗan fari. In mutum yana da gagararren ɗa mai tawaye, wanda ba ya biyayya ga mahaifinsa da mahaifiyarsa, ba ya kuma jin su sa’ad da suke horonsa, mahaifinsa da mahaifiyarsa za su kama shi su kawo shi ga dattawa a ƙofar garinsu. Za su ce wa dattawan, “Wannan ɗanmu gagararre ne, mai tawaye. Ba ya mana biyayya. Mai zari ne, kuma mashayi.” Sa’an nan dukan mazan garinsa za su jajjefe shi har yă mutu. Dole ku fid da mugu daga cikinku. Dukan Isra’ila kuwa za su ji wannan su kuma ji tsoro. In mutum ya yi laifin da ya isa kisa, aka kuwa rataye shi a itace, kada ku bar jikinsa a kan itacen yă kwana. Ku tabbata kun binne shi a ranar, domin duk wanda aka rataye a kan itace la’ananne ne ga Allah. Kada ku ƙazantar da ƙasar da Ubangiji Allahnku yake ba ku gādo. In kun ga saniya ko tunkiyar ɗan’uwanku wadda ta ɓace, kada ku ƙyale ta, amma ku tabbata kun komar da ita gare shi. In ɗan’uwan ba ya zama kusa da ku, ko kuwa ba ku san shi ba, sai ku kai ta gida ku ajiye ta sai ya zo nemanta. Sa’an nan ku ba shi ita. Ku yi haka in kun sami jakin ɗan’uwanku, ko rigarsa, ko kowane abin da ya ɓace. Kada ku ƙyale shi. In kuka ga jakin ɗan’uwanku, ko saniyarsa ya fāɗi a kan hanya, kada ku ƙyale shi. Ku taimaka, ku tā da shi. Kada mace ta sa suturar maza, kada kuma namiji ya sa suturar mata, gama Ubangiji Allahnku yana ƙyamar duk mai yin haka. In kuka ga gidan tsuntsu kusa da hanya, ko a kan itace, ko kuma a ƙasa, mahaifiyar tsuntsun kuwa tana kwance a kan ’ya’yanta, ko kuwa a kan ƙwanta, kada ku kama mahaifiyar duk da ’ya’yan. Za ku iya kwashe ’ya’yan, amma ku tabbata kun bar mahaifiyar tă tafi. Yin haka zai sa ku sami zaman lafiya da tsawon rai. Sa’ad da kuka gina sabon gida, ku ja masa dakali kewaye da rufinku don kada ku jawo laifin zub da jini a kan gidanku in wani ya fāɗi daga kan rufin. Kada ku shuka iri biyu a gonar inabinku; in kuka yi haka, ba abin da kuka shuka ne kaɗai zai ƙazantu ba, amma har da inabinku ma. Kada ku haɗa bijimi da jaki su yi noma tare. Kada ku sa rigar ulu da aka gauraye da lilin aka saƙa. Ku yi tuntu a kusurwan huɗu na rigar da kuke sa. In mutum ya auri mace, bayan ya kwana da ita, sa’an nan ya ƙi ta ya kuma zarge ta, ya ba ta mummunan suna, yana cewa, “Na auri wannan mata, amma sa’ad da na kusace ta, ban sami tabbaci cewa ita budurwa ba ce,” sai mahaifin yarinyar da mahaifiyarta su kawo shaida cewa ita budurwa ce wa dattawan gari a ƙofar garin. Mahaifin yarinyar zai ce wa dattawa, “Na ba da ’yata aure ga wannan mutum, amma ya ƙi ta. Yanzu ya zage ta cewa, ‘Ban sami ’yarku budurwa ba.’ Amma ga shaidar budurcin ’yata.” Sa’an nan iyayenta za su shimfiɗa zanen a gaban dattawan garin, dattawan kuwa za su ɗauki mutumin su hukunta shi. Za su ci masa tara shekel azurfa ɗari, su ba mahaifin yarinyar, domin wannan mutum ya ba wa budurwa mutuniyar Isra’ila mummunan suna. Za tă ci gaba da zama matarsa; ba kuwa zai sake ta ba muddin ransa. Amma fa in zarge gaskiya ne, ba a kuwa sami shaidar budurcin yarinyar ba, sai a kawo ta a ƙofar gidan mahaifinta, a can mazan gari za su jajjefe ta da dutse har tă mutu. Ta yi abin kunya a Isra’ila ta wurin lalaci a yayinda take a gidan mahaifinta. Dole ku fid da mugu daga cikinku. In aka kama wani yana kwance da matar wani, dole a kashe dukansu biyu, wato, mutumin da ya kwana da matar da kuma matar. Dole a fid da mugu daga Isra’ila. In mutum ya sadu da budurwa a gari wadda aka yi alkawarin aure, ya kuma kwana da ita sai ku ɗauki su biyu zuwa ƙofar wannan gari, ku jajjefe su da dutse har su mutum, za a kashe yarinyar domin tana a cikin gari ba ta kuwa yi ihu neman taimako ba, za a kashe mutumin domin ya yi lalata da matar wani. Dole ku fi da mugu daga cikinku. Amma in a bayan gari ne mutumin ya sadu da yarinyar da aka yi alkawari aure, ya kuma yi mata fyaɗe, mutumin da ya yi wannan ne kaɗai zai mutu. Kada ku yi wa yarinyar kome, ba tă yi zunubin da ya cancanci mutuwa ba. Wannan batu ya yi kamar da na mutumin da ya fāɗa wa maƙwabcinsa ya kuma kashe shi. Tun da ya same ta a jeji ne, wataƙila yarinyar ta yi kukan neman taimako, amma babu wani da zai cece ta. In mutum ya sadu da yarinyar da ba a yi alkawarin aurenta ba, ya kuma yi mata fyaɗe, aka kuma kama su, sai yă biya mahaifin yarinyar shekel hamsin na azurfa. Dole yă auri yarinyar, gama ya yi lalata da ita. Ba zai taɓa sake ta ba muddin ransa. Kada mutum yă auri matar mahaifinsa, kada yă ƙasƙantar gādon mahaifinsa. Duk wanda aka daƙe, ko yanke gabansa, ba zai shiga taron jama’ar Ubangiji ba. Duk wanda aka haifa ta wurin cikin shege, har tsara ta goma, zuriyarsa ba za su shiga taron jama’ar Ubangiji ba, har zuwa tsara ta goma. Ba mutumin Ammon, ko mutumin Mowab, ko kuwa wani zuriyarsu da zai shiga taron jama’ar Ubangiji, har tsara ta goma. Gama ba su zo sun tarye ku da burodi da ruwa a hanyarku, sa’ad da kuka fito daga Masar ba, sai ma suka yi haya Bala’am ɗan Beyor daga Fetor a Aram-Naharayim yă furta la’ana a kanku. Amma Ubangiji Allahnku bai saurari Bala’am ba, sai ya mai da la’anar ta koma albarka gare ku, domin Ubangiji Allahnku yana ƙaunarku. Kada ku yi yarjejjeniyar abuta da su, muddin kuna da rai. Kada ku yi ƙyamar mutumin Edom, gama mutumin Edom ɗan’uwanku ne. Kada ku yi ƙyamar mutumin Masar, domin kun yi zama baƙunta a ƙasarsa. ’Ya’yan da aka haifa musu na tsara ta uku za su iya shiga taron jama’ar Ubangiji. Sa’ad da kuka yi sansani don ku yi yaƙi da abokan gābanku, ku kiyaye kanku daga duk wani abu marar tsabta. In ɗaya daga cikin mazanku ya ƙazantu saboda zubar da maniyyi, sai yă fita daga sansani yă zauna waje da sansani. Amma yayinda yamma ke gabatowa sai yă wanke kansa, da fāɗuwar rana kuwa sai yă koma cikin sansani. Ku keɓe wuri waje da sansani inda za ku iya zuwa don yin bayan gari. Sai ku ɗauki wani abin tona ƙasa, sa’ad da kuka yi bayan gari, sai ku tona rami, ku rufe bayan garinku. Gama Ubangiji Allahnku yana zagawa a cikin sansaninku don yă tsare ku, yă kuma bashe abokan gābanku gare ku. Dole sansaninku yă kasance da tsarki, saboda kada yă ga wani abu marar kyau a cikinku, har yă juya daga gare ku. In bawa ya tsere zuwa wurinku don mafaka, kada ku miƙa shi ga ubangidansa. Ku bar shi yă zauna a cikinku a duk inda yake so, da kuma a kowane garin da ya zaɓa. Kada ku tsananta masa. Kada mutumin Isra’ila ko mutuniyar Isra’ila yă zama karuwar haikali. Kada ku kawo kuɗin a cikin gida Ubangiji Allahnku da aka samu ta wurin karuwanci wanda mace ko namiji ya yi don biyan wani alkawari, domin Ubangiji Allahnku yana ƙyamar su duka. Kada ku nemi ɗan’uwanku yă biya bashin da kuka ba shi da ruwa, ko kuɗi, ko abinci, ko kowane irin abin da yana iya ba da ruwa. Za ku iya nemi ruwa a bashin da kuka ba baƙo, amma ba ɗan’uwanku mutumin Isra’ila ba, domin Ubangiji Allahnku yă sa muku albarka a kowane abin da kuka sa hannunku a kai, a ƙasar da kuke shiga ku ci gādonta. In fa kuka yi alkawari ga Ubangiji Allahnku, to, kada ku yi jinkirin cikawa, gama tabbatacce Ubangiji Allahnku zai neme shi daga gare ku, za ku kuma zama masu laifin zunubi. Amma in ba ku yi alkawari ba, ba kuwa zai zama muku zunubi ba. Duk abin da ya fita daga bakinku, sai ku lura ku cika shi, kamar yadda kuka yarda da kanku, kuka yi alkawarin ga Ubangiji Allahnku da bakinku. In kun shiga gonar inabin maƙwabcinku, za ku iya cin inabin da kuke so, amma kada ku sa wani a kwandonku. In kun shiga gonar hatsin maƙwabcinku, za ku iya murmure tsabar da hannuwanku, amma kada ku sa lauje ku yanka hatsinsa da yake tsaye. Idan mutum ya auri mata, daga baya ba tă gamshe shi ba domin ya gano wani abu marar kyau game da ita, ya ba ta takardar saki, ya kuma kore ta daga gidansa, in bayan ta bar gidansa ta zama matar wani dabam, sai mijinta na biyu ya ƙi ta, ya ba ta takardan saki, ya kore ta daga gidansa, ko kuwa ya mutu, to, kada mijinta na farko, wanda ya sake ta yă sāke aurenta, tun da yake ta ƙazantu. Wannan zai zama abin ƙyama a gaban Ubangiji. Kada ku kawo zunubi a ƙasar da Ubangiji Allahnku yake ba ku gādo. In mutum bai daɗe da aure ba, kada a sa yă je yaƙi, ko yă yi wani aiki. Gama zai huta shekara guda a gida, yă faranta wa matar da ya aura rai. Kada ku karɓi jinginar dutsen niƙa tare da ɗan dutsen niƙan, domin yin haka zai zama karɓar jinginar rai ne. Idan aka kama wani yana satar ɗan’uwansa mutumin Isra’ila domin yă sa ya zama bawansa, ko yă sayar da shi, sai a kashe ɓarawon nan. Haka za ku kawar da mugunta daga cikinku. Game da cututtukan kuturta, sai ku lura, ku yi yadda firistocin da suke Lawiyawa suka umarce ku. Dole ku lura ku bi abin da na umarce su. Ku tuna da abin da Ubangiji Allahnku ya yi wa Miriyam a hanya, bayan kun fito Masar. Sa’ad da kuka ba da rance na kowane iri ga maƙwabcinku, kada ku shiga gidansa don karɓar wani abu a matsayin jingina. Ku tsaya a waje ku bar mutumin da yake karɓan rancen yă kawo muku abin da zai bayar a matsayin jingina. In matalauci ne, kada ku kwana da abin da zai bayar a matsayin jingina a wurinku. Ku mayar da rigarsa a fāɗuwar rana saboda yă sami abin rufuwa. Yin haka zai sa yă gode muku, za a kuma ɗauka wannan a matsayin aikin adalci da kuka yi a gaban Ubangiji Allahnku. Kada ku zalunci ɗan ƙodago matalauci da mabukaci, ko da shi ɗan’uwanku ne mutumin Isra’ila, ko baƙon da yake zama a cikin garuruwanku. Ku biya kuɗin aikinsa kowace rana kafin fāɗuwar rana, domin shi matalauci ne, yana kuma sa rai a kan wannan hakkin ne, don kada ya yi wa Ubangiji kuka a kanku, har yă zama laifi a gare ku. Ba za a kashe iyaye a maimakon ’ya’yansu ba, ba kuwa za a kashe ’ya’ya a maimakon iyayensu ba; kowa ya yi zunubi, shi za a kashe. Ba za ku danne hakkin baƙon da yake zama a cikinku ko na marayu ba, ba za ku ɗauki rigar matar da mijinta ya mutu a matsayin jingina ba. Ku tuna dā ku bayi ne a Masar, Ubangiji Allahnku kuwa ya fisshe daga can. Shi ya sa na umarce ku ku yi wannan. Sa’ad da kuke girbi a gonarku, sai kuka manta da dami, kada ku koma don ku ɗauka. Ku bar shi don baƙo, maraya da kuma gwauruwa, saboda Ubangiji Allahnku yă albarkace ku a cikin dukan aikin hannuwanku. Sa’ad da kuka kakkaɓe ’ya’yan zaitun daga itatuwanku, kada ku yi kalan abin da ya rage. Ku bar shi don baƙo, maraya da kuma gwauruwa. Sa’ad da kuka yi girbin inabi a gonar inabinku, kada ku yi kalan abin da ya rage. Ku bar shi don baƙo, maraya da kuma gwauruwa. Ku tuna dā ku bayi ne Masar. Shi ya sa na umarce ku ku yi wannan. Idan mūsu ya tashi tsakanin mutum biyu har abin ya kai su kotu, alƙalai kuwa suka yanke hukunci a kan batun, suka kuɓutar da marar laifi sa’an nan suka hukunta mai laifi, in mai laifin ya cancanci bulala, alƙali zai sa yă kwanta a yi masa bulala a gabansa da yawan bulalan da ya dace da laifin, amma kada yă yi masa bulala fiye da arba’in. In ya yi masa fiye da haka, za a ƙasƙantar da ɗan’uwanku, zai kuma zama rainanne a idonku. Kada ku yi wa saniya takunkumi sa’ad da take tattaka hatsi. In ’yan’uwa suna zama tare, in ɗayansu ya mutu babu ɗa, kada gwauruwar tă yi aure waje da iyalin. Ɗan’uwan mijinta zai ɗauke ta, yă aure ta, yă kuma cika abin da yă kamaci ɗan’uwan miji yă yi. Ɗan farin da ta haifa zai ɗauki sunan ɗan’uwan da ya rasu saboda kada sunansa yă ɓace daga Isra’ila. Amma fa, in mutum ba ya so yă auri matar ɗan’uwansa, sai tă tafi wurin dattawa a ƙofar gari tă ce, “Ɗan’uwan mijina ya ƙi yă wanzar da sunan ɗan’uwansa a Isra’ila. Ya ƙi yă cika abin da ya kamaci ɗan’uwan miji yă yi gare ni.” Sai dattawan garinsa su kira shi, su kuma yi masa magana. In ya nace yana cewa, “Ba na so in aure ta,” sai gwauruwan nan, matar ɗan’uwansa tă haura wurinsa a gaban dattawa, tă tuɓe takalminsa guda, ta tofa masa miyau a fuska, tă ce, “Haka za a yi ga mutumin da zai ƙi kafa gidan ɗan’uwansa.” Za a kira zuriyarsa a Isra’ila Iyalin da aka tuɓe masa takalmi. In mutane biyu suna faɗa, sai matar mutum ɗaya daga cikinsu ta zo don tă kuɓutar da mijinta daga abokin faɗarsa, ta kuma miƙa hannu ta kama marainan wancan, sai ku yanke hannunta. Kada ku ji tausayinta. Kada ku kasance da ma’auni iri biyu a jakarku, ɗaya babba, ɗaya ƙarami. Kada ku kasance da mudu iri biyu a jakarku, ɗaya babba, ɗaya ƙarami. Dole ku kasance da ma’aunin da kuma mudun da yake daidai, kuma na gaskiya, saboda ku yi tsawon rai a ƙasar da Ubangiji Allahnku yake ba ku. Gama Ubangiji Allahnku yana ƙyamar duk mai yi waɗannan abubuwa, da kuma mai rashin gaskiya. Ku tuna da abin da Amalekawa suka yi muku a hanya, sa’ad da kuka fito Masar. Yadda suka yi muku kwanto a hanya, suka fāɗa muku ta baya, suka karkashe waɗanda suka gaji tiɓis. Ba su ko ji tsoron Allah ba. Sa’ad da Ubangiji Allahnku ya ba ku hutu daga dukan abokan gābanku kewaye da ku, a ƙasar da yake ba ku ku mallaka a matsayin gādo, sai ku shafe Amalekawa daga duniya, don kada a ƙara tunawa da su. Kada fa ku manta! Sa’ad da kuka shiga ƙasar da Ubangiji Allahnku yake ba ku gādo, kuka mallake ta, kuka kuma zauna a cikinta, sai ku ɗauki ’ya’yan fari na dukan amfanin gonar ƙasar da Ubangiji Allahnku yake ba ku, ku zuba a kwando. Sa’an nan ku je wurin da Ubangiji Allahnku ya zaɓa yă zama mazauni don Sunansa, ku faɗa wa firist da yake aiki a lokacin, “Na sakankance yau ga Ubangiji Allahnka, cewa na zo ƙasar da Ubangiji ya rantse zai ba wa kakanninmu.” Firist ɗin zai karɓi kwandon daga hannuwanku yă sa shi a ƙasa a gaban bagaden Ubangiji Allahnku. Sa’an nan za ku furta a gaban Ubangiji Allahnku cewa, “Mahaifina mutumin Aram ne mai yawo, ya gangara zuwa Masar da mutane kaɗan, ya zauna a can, ya kuma zama babban al’umma, mai iko da kuma mai yawa. Amma Masarawa suka wulaƙanta mu suka sa muka sha wahala, suna sa mu aikin dole. Sai muka yi kuka ga Ubangiji Allahn kakanninmu, Ubangiji kuwa ya ji kukanmu, ya kuma azabar da muke sha, da wahalar da muke sha, da danniyar da suke yin mana. Sai Ubangiji ya fitar da mu daga Masar da hannu mai ƙarfi da kuma iko, da razana mai girma da kuma alamu banmamaki da al’ajabai. Ya kawo mu wannan wuri, ya kuma ba mu wannan ƙasa, ƙasa mai zub da madara da kuma zuma; yanzu kuwa na kawo ’ya’yan fari na gonar da kai, ya Ubangiji ka ba ni.” Sai ku sa kwandon a gaban Ubangiji Allahnku, sa’an nan ku rusuna a gabansa. Ku da Lawiyawa da baƙin da suke a cikinku, za ku yi murna cikin dukan abubuwa masu kyau da Ubangiji Allahnku ya ba ku tare da gidanku. Sa’ad da kuka gama fitar da kashi ɗaya bisa goma na dukan amfanin gona a shekara ta uku, shekarar zakka, za ku ba da su ga Balawe, baƙo, maraya da kuma gwauruwa, don su ci a cikin garuruwanku su ƙoshi. Sa’an nan ku faɗa wa Ubangiji Allahnku, “Na cire tsattsarkan rabo daga gidana na kuma ba wa Balawe, baƙo, maraya da gwauruwa, bisa ga dukan abin da ka umarta. Ban ja gefe daga umarnanka ko in manta da wani a cikinsu ba. Ban ci wani daga cikin tsattsarkan rabo yayinda nake makoki, ko in cire wani rabo mai tsarki yayinda nake marar tsarki, ko in miƙa wani sashensa ga matattu ba. Na yi biyayya ga Ubangiji Allahna, na aikata kome da ka umarce ni. Ka duba ƙasa daga sama, mazauninka mai tsarki, ka albarkace mutanenka Isra’ila da kuma ƙasar da ka ba mu kamar yadda ka yi wa kakanninmu alkawari da rantsuwa, ƙasa mai zub da madara da zuma.” Yau Ubangiji Allahnku ya umarce ku ku bi waɗannan ƙa’idodi da kuma dokoki, cikin natsuwa ku kiyaye su da dukan zuciyarku da kuma dukan ranku. Kun furta a wannan rana cewa Ubangiji shi ne Allahnku, cewa za ku kuma yi tafiya a hanyoyinsa, cewa za ku kiyaye ƙa’idodinsa, umarnansa da kuma dokokinsa, kuka kuma ce za ku yi masa biyayya. Ubangiji kuwa ya furta a wannan rana cewa ku mutanensa ne, mallakarsa kamar yadda ya yi alkawari, da kuma cewa za ku kiyaye dukan umarnansa. Ya furta cewa zai sa ku zama masu yabo, masu suna, masu daraja, fiye da dukan al’umman da ya yi. Za ku zama jama’a tsattsarka ta Ubangiji Allahnku, kamar yadda ya yi alkawari. Musa tare da dattawan Isra’ila suka umarci mutane suka ce, “Ku kiyaye dukan umarnai da na ba ku a yau. Sa’ad da kuka haye Urdun zuwa cikin ƙasar da Ubangiji Allahnku yake ba ku, ku kakkafa waɗansu manyan duwatsu, ku yi musu shafe da farar ƙasa. Ku rubuta dukan waɗannan kalmomin doka a kansu, sa’ad da kuka haye kuka shiga ƙasar da Ubangiji Allahnku yake ba ku, ƙasa mai zub da madara da zuma, kamar dai yadda Ubangiji Allah na kakanninku, ya yi muku alkawari. Sa’ad da kuma kuka haye Urdun, ku kakkafa waɗannan duwatsu a bisa Dutsen Ebal, kamar yadda na umarce a yau, ku yi musu shafe da farar ƙasa. Ku gina bagade wa Ubangiji Allahnku, bagaden dutse. Kada ku yi amfani da wani kayan aiki na ƙarfe a kansu. Ku gina bagaden Ubangiji Allahnku da duwatsun fili, ku kuma miƙa hadaya ta ƙonawa a kansa ga Ubangiji Allahnku. Ku miƙa hadayun salama a can, kuna ci, kuna farin ciki a gaban Ubangiji Allahnku. Za ku kuma rubuta a fayyace dukan kalmomin wannan doka a kan waɗannan duwatsun da kuka kakkafa.” Sai Musa da firistoci waɗanda suke Lawiyawa suka ce wa dukan Isra’ila, “Ku yi shiru, ya Isra’ila, ku saurara! Yanzu kun zama mutanen Ubangiji Allahnku. Ku yi biyayya ga Ubangiji Allahnku, ku bi umarnansa da ƙa’idodin da nake ba ku a yau.” A wannan rana Musa ya umarce mutane, Sa’ad da kuka haye Urdun, sai waɗannan kabilai su tsaya a bisa Dutsen Gerizim su sa wa jama’a albarka, wato, kabilar Simeyon, Lawi, Yahuda, Issakar, Yusuf da Benyamin. Waɗannan kabilai kuma za su tsaya a bisa Dutsen Ebal su furta la’ana, wato, kabilar Ruben, Gad, Asher, Zebulun, Dan da Naftali. Lawiyawa za su karanta wa dukan mutanen Isra’ila da babbar murya su ce, “La’ananne ne mutumin da ya sassaƙa siffa, ko ya yi zubin gunki, abar ƙyama ce ga Ubangiji, aikin hannu mai sana’a da aka kafa a ɓoye.” Sai dukan mutane su ce, “Amin!” “La’ananne ne mutumin da ya ƙasƙantar da mahaifinsa ko mahaifiyarsa.” Sai dukan mutane su ce, “Amin!” “La’ananne ne mutumin da ya gusar da dutsen da aka kafa don nuna shaidar iyaka.” Sai dukan mutane su ce, “Amin!” “La’ananne ne mutumin da ya karkatar da makaho daga hanya.” Sai dukan mutane su ce, “Amin!” “La’ananne ne mutumin da ya yi rashin adalci ga baƙo, maraya ko gwauruwa.” Sai dukan mutane su ce, “Amin!” “La’ananne ne mutumin da ya kwana da matar mahaifinsa, gama ya ƙasƙantar da gadon mahaifinsa ke nan.” Sai dukan mutane su ce, “Amin!” “La’ananne ne mutumin da ya yi jima’i da dabba.” Sai dukan mutane su ce, “Amin!” “La’ananne ne mutumin da ya kwana da ’yar’uwarsa, ’yar mahaifinsa ko ’yar mahaifiyarsa.” Sai dukan mutane su ce, “Amin!” “La’ananne ne mutumin da ya kwana da mahaifiyar matarsa.” Sai dukan mutane su ce, “Amin!” “La’ananne ne mutumin da ya kashe maƙwabcinsa a ɓoye.” Sai dukan mutane su ce, “Amin!” “La’ananne ne mutumin da ya karɓi cin hanci don yă kashe marar laifi.” Sai dukan mutane su ce, “Amin!” “La’ananne ne mutumin da bai yi na’am da kalmomin wannan doka ta wurin aikata su ba.” Sai dukan mutane su ce, “Amin!” In kun yi biyayya da maganar Ubangiji Allahnku, kuka kuma lura, kuka bi dukan umarnan da na ba ku a yau, Ubangiji Allahnku zai sa ku bisa dukan al’ummai a duniya. Dukan waɗannan albarku za su sauko muku, su zama naku, in kuka yi biyayya ga Ubangiji Allahnku. Za ku zama masu albarka a cikin birni, za ku kuma zama masu albarka har a ƙauye. ’Ya’yanku za su zama masu albarka, haka ma hatsin gonakinku da kuma ’ya’yan dabbobinku, wato, ’ya’yan shanu da ’yan tumakinku. Za a albarkaci kwandonku da kwanon kwaɓan kullunku. Za ku zama masu albarka sa’ad da kuka shiga, za ku kuma zama masu albarka sa’ad da kuka fita. A gabanku, Ubangiji zai sa ku fatattaki abokan gāban da za su taso suna gāba da ku. Ta hanya guda za su auka muku, amma ta hanyoyi bakwai za su gudu daga gabanku. Ubangiji zai aika da albarka a rumbunanku da kuma a bisa kome da kuka sa hannunku a kai. Ubangiji Allahnku zai albarkace ku a ƙasar da yake ba ku. Ubangiji zai kafa ku kamar mutanensa masu tsarki, kamar yadda ya yi alkawari da rantsuwa, in kun kiyaye umarnan Ubangiji Allahnku, kuka kuma yi tafiya a hanyoyinsa. Sa’an nan dukan mutane a duniya za su ga cewa ana kiranku da sunan Ubangiji, za su kuwa ji tsoronku. Ubangiji zai azurta ku sosai, a ’ya’yan cikinku, a ’ya’yan dabbobinku da kuma a hatsin gonarku, a cikin ƙasar da ya rantse wa kakanninku zai ba ku. Ubangiji zai buɗe sammai, wurin ajiyarsa mai yalwa, don yă aika da ruwan sama a gonarku a lokacinsa, yă kuma albarkaci dukan aikin hannuwanku. Za ku ba wa al’ummai masu yawa rance, amma ba za ku karɓa bashi daga wurin wani ba. Ubangiji zai sa ku zama kai, ba wutsiya ba. In kun mai da hankali ga umarnan Ubangiji Allahnku da nake ba ku a wannan rana, kuka kuma lura, kuka bi su, kullum za ku kasance a bisa, ba a ƙasa ba. Kada ku kauce zuwa dama ko zuwa hagu daga umarnan da na ba ku a yau, har ku bi waɗansu alloli kuna yin musu sujada. Amma fa, in ba ku yi biyayya ga Ubangiji Allahnku ba, ba ku kuma lura kun bi dukan umarnansa da ƙa’idodin da nake ba ku a yau ba, dukan la’anan nan za su zo a bisanku, su kuma same ku. Za ku zama la’anannu a birni da kuma a ƙauye. Za a la’anta kwandonku da kwanon kwaɓan kullunku. Za a la’anta ’ya’yan cikinku, haka ma hatsin gonarku, da ’ya’yan shanunku da ’yan tumakinku. Za a la’anta ku sa’ad da kuka shiga da sa’ad da kuka fita. Ubangiji zai aiko muku da la’ana, da ruɗewa, da damuwa cikin dukan abin da za ku yi, har ya hallaka ku, ku lalace da sauri saboda mugayen ayyukanku, domin kuma kuka rabu da ni. Ubangiji zai aiko muku da annoba wadda za tă manne muku, tă cinye ku cikin ƙasar da za ku shiga, ku mallake ta. Ubangiji zai buga ku da cuta mai lalacewa, da zazzaɓi, da ƙuna, da zafin rana, da fāri, da burtuntuna, da fumfuna, waɗanda za su azabtar da ku sai kun hallaka. Girgijen da yake bisanku zai zama tagulla, ƙasar da take ƙarƙashinku za tă zama ƙarfe. Ubangiji zai juye ruwan saman ƙasarku yă zama ƙura da gari; zai sauko daga gizagizai har sai kun hallaka. Ubangiji zai sa a rinjaye ku a gaban abokan gābanku. Ta hanya guda za ku auka musu, amma ta hanyoyi bakwai za ku gudu daga gabansu. Za ku zama abin ƙi ga dukan mulkokin duniya. Gawawwakinku za su zama abincin dukan tsuntsayen sarari da namun duniya, ba kuwa wanda zai kore su. Ubangiji zai buge ku da maruran Masar, da ƙazuwa, da kuma ƙaiƙayi waɗanda ba za su warke ba Ubangiji zai buge ku da hauka, makanta, da rikicewar hankali. Da tsakar rana za ku riƙa lallubawa kamar makaho. Za ku zama marasa nasara a cikin kome da kuka yi; kowace rana za a zalunce ku, a kuma yi muku ƙwace, ba tare da wani ya cece ku ba. Za ku yi tashin yarinya, amma wani ne zai ɗauke ta yă kwana da ita. Za ku gina gida amma wani ne zai zauna a ciki. Za ku shuka inabi, amma ba za ku ma fara jin daɗin ’ya’yansa ba. Za a yanka sanku a idanunku, amma ba za ko ci wani abu a cikinsa ba. Za a ƙwace jakinku ƙiri-ƙiri, amma ba za a mayar muku da shi ba. Za a ba da tumakinku ga abokan gābanku, kuma ba kowa da zai cece su. Za a ba da ’ya’yanku maza da mata ga wata al’umma, za ku kuma yi ta zuba idanunku kuna neman su kullayaumi, amma a banza, domin ba ku da ikon yin kome. Mutanen da ba ku sani ba za su ci kayan gonarku da amfanin wahalarku, za a yi ta cucinku, ana kuma danne ku kullum. Abubuwan da za ku gani za su sa ku yi hauka. Ubangiji zai buge gwiwoyinku da ƙafafunku da marurai masu zafi da ba za a iya warkar da su ba, za su yaɗu daga tafin ƙafafu zuwa bisa kanku. Ubangiji zai kore ku, ku da sarkin da kuka naɗa a bisanku zuwa al’ummar da ku, ko kakanninku ba su sani ba. A can za ku yi wa waɗansu alloli sujada, allolin itace da na dutse. Za ku zama abin ƙi, abin dariya, da kuma abin habaici ga dukan al’ummai inda Ubangiji zai kore ku zuwa. Za ku shuka iri da yawa a gona, amma za ku girbe kaɗan, domin fāra za su cinye su. Za ku shuka inabi ku kuma yi musu banƙasa, amma ba za ku sha ruwan inabin ba, domin tsutsotsi za su cinye su. Za ku kasance da itatuwan zaitun ko’ina a ƙasarku, amma ba za ku yi amfani da mansu ba, domin ’ya’yan zaitun za su kakkaɓe. Za ku haifi ’ya’ya maza da mata, amma za su zama naku ba, domin za a kai su bauta. Tarin fāra za su mamaye dukan itatuwanku da kuma hatsin gonarku. Baƙin da suke tare da ku, za su yi ta ƙaruwa, ku kuwa za ku yi ta komawa baya-baya. Za su ba ku bashi, amma ba za ku ba su bashi ba. Za su zama kai, ku kuwa za ku zama wutsiya. Dukan waɗannan la’anoni za su sauko a kanku. Za su bi ku, su same ku, sai an hallaka ku, domin ba ku yi biyayya ga Ubangiji Allahnku, kuka kuma kiyaye umarnai da ƙa’idodin da ya ba ku ba. Za su zama alamu da al’ajabi gare ku da kuma zuriyarku har abada. Gama ba ku bauta wa Ubangiji Allahnku da farin ciki da kuma murna a lokacin wadata ba, saboda haka a cikin yunwa da ƙishirwa, cikin tsiraici da mugun talauci, za ku bauta wa abokan gāban da Ubangiji ya aiko muku. Zai sa karkiyar ƙarfe a wuyanku har sai ya hallaka ku ƙaf. Ubangiji zai kawo al’umma daga nesa, daga iyakar duniya, ta sauko a kanku kamar gaggafa, al’ummar da ba ku san yarenta ba, al’umma mai zafin hali wadda ba ta ba wa tsofaffi girma, kuma ba ta tausayin yara. Za su cinye ’ya’yan dabbobinku da hatsin gonarku sai an hallaka ku. Ba za su rage ko ƙwayar hatsi, ko sabon ruwan inabi, ko mai ba, ba kuwa za a bar ’yan tumakinku ba, sai an lalatar da ku. Za su kuwa kewaye ku a dukan garuruwanku, har sai katangarku masu tsayi wadda kuke dogara gare su, sun fāɗi ko’ina a ƙasar da Ubangiji Allahnku yake ba ku. Saboda wahalar da abokan gābanku za su gasa muku a lokacin kwanto, za ku ci ’ya’yan cikinku, naman ’ya’yanku maza da mata waɗanda Ubangiji Allahnku ya ba ku. Kai, har da mutumin da ya fi hankali da kuma kirki a cikinku, ba zai ji tausayi ɗan’uwansa, ko matar da yake ƙauna, ko ’ya’yansa da suka ragu ba, ba kuwa zai ba waninsu wani naman ’ya’yansa da yake ci ba. Gama dukan abin da ya rage masa ke nan saboda wahalar da abokan gābanku za su gasa muku a lokacin da ake kwanton wa dukan biranenku. Mace mafi hankali da kuma kirki a cikinku, kai, mafi hankali da kirki da ba ta ma karambanin taɓa ƙasa da tafin ƙafarta, za tă hana wa mijinta da take ƙauna, da kuma ɗanta, ko ’yarta abinci. A ɓoye za tă ci mahaifar da take biyo bayan ta haihu, da ’ya’yan da za tă haifa, saboda ba ta da wani abinci lokacin da abokan gābanku za su kewaye garuruwanku da yaƙi mai tsanani. In ba ku lura kuka bi dukan kalmomi wannan doka, waɗanda an rubuta a wannan littafi ba, ba ku kuma girmama wannan suna mai ɗaukaka da kuma mai banrazana na Ubangiji Allahnku ba, Ubangiji zai aika da annoba masu zafi a kanku da zuriyarku, masifu masu zafi waɗanda za su daɗe, da mugayen cututtuka waɗanda ba sa kawuwa. Zai kawo muku dukan cututtukan Masar da kuke tsoro, za su kuwa manne muku. Ubangiji kuma zai kawo muku kowane irin ciwo da masifar da ba a rubuta a cikin wannan Littafin Doka ba, har sai an hallaka ku. Ku da kuke da yawa kamar taurari a sarari za ku ragu ku zama kaɗan, domin ba ku yi biyayya ga Ubangiji Allahnku ba. Kamar yadda ya gamshi Ubangiji ya sa kuka yi arziki kuka kuma ƙaru, haka zai gamshe shi yă lalatar yă kuma hallaka ku. Za a tumɓuke ku daga ƙasar da kuke shiga ku mallaka. Sa’an nan Ubangiji zai watsar da ku cikin dukan al’ummai, daga wannan bangon duniya zuwa wancan. A can za ku bauta waɗansu alloli, allolin itace da na dutse, waɗanda ko ku, ko kakanninku, ba ku sani ba. A cikin waɗancan al’ummai ba za ku sami hutu ba, ba wurin hutu wa tafin ƙafanku. A can Ubangiji zai sa fargaba a zuciyarku, yă sa idanunku su lalace, ranku zai yi suwu. Za ku yi zama cikin damuwa kullum, cike da tsoro, dare da rana, ba tabbacin abin da zai faru da ranku. Da safe za ku ce, “Da ma yamma ne!” Da yamma kuma ku ce, “Da ma safiya ce!” Saboda tsoron da ya cika zukatanku da kuma abubuwan da idanunku za su gani. Ubangiji zai komar da ku cikin jiragen ruwa zuwa Masar, tafiyar da na ce kada ku ƙara yi. A can za ku ba da kanku don sayarwa ga abokan gābanku a matsayin bayi maza da mata, amma ba wanda zai saye ku. Waɗannan su ne sharuɗan alkawarin da Ubangiji ya umarci Musa yă yi da Isra’ilawa a Mowab, wato, ban da alkawarin da ya yi da su a Dutsen Horeb. Sai Musa ya tara dukan Isra’ila, ya ce musu, Idanunku sun ga dukan abin da Ubangiji ya yi a Masar ga Fir’auna, ga kuma dukan shugabanninsa da kuma ga dukan ƙasarsa. Da idanunku kun ga waɗannan gwaje-gwaje, waɗannan alamu masu banmamaki, da al’ajabai masu girma. Duk da haka har wa yau Ubangiji bai ba ku hankalin ganewa, ko idanun da za su gani, ko kunnuwan da za su ji ba. Shekaru arba’in da na jagorance ku cikin hamada, tufafinku ba su yage ba, haka kuwa takalman da suke a ƙafafunku. Ba ku ci burodi ba, ba ku kuwa sha ruwan inabi, ko wani abu mai sa jiri ba. Ya yi haka don ku san cewa shi ne Ubangiji Allahnku. Sa’ad da kuka kai wannan wuri, Sihon sarkin Heshbon, da Og sarkin Bashan, suka fito don su yi yaƙi da mu, amma muka ci su da yaƙi. Muka ƙwace ƙasarsu, muka ba da ita gādo ga mutanen Ruben, mutanen Gad, da kuma rabin mutanen Manasse. Saboda haka sai ku kiyaye, ku bi sharuɗan wannan alkawari, don ku yi nasara a cikin kome da kuke yi. Yau, ga ku nan tsaye, dukanku a gaban Ubangiji Allahnku, shugabanninku da manyan mutanenku, dattawanku da hafsoshinku, da kuma dukan sauran mutanen Isra’ila, tare da ’ya’yanku da matanku, da baƙin da suke zama sansanoninku, har ma da waɗanda suke muku faskare, da waɗanda suke ɗiba muku ruwa. Kuna tsaye a nan don ku yi alkawari da Ubangiji Allahnku, alkawarin da Ubangiji yake yi ta wurin rantsuwa da ku a wannan rana, don yă mai da ku jama’arsa yau, shi kuwa yă zama Allahnku kamar yadda ya yi muku alkawari, da yadda kuma ya rantse wa kakanninku, Ibrahim, Ishaku da kuma Yaƙub. Ina yin wannan alkawari da rantsuwar, ba da ku kaɗai da kuke tsattsaye a nan tare da mu a yau a gaban Ubangiji Allahnmu ba, amma har da waɗanda ba sa nan yau. Ku kanku kun san yadda muka yi zama a Masar, da yadda muka yi ta ratsawa ta tsakiyar al’ummai muka wuce. A cikinsu, kun ga siffofi masu banƙyama da gumaka na itace da dutse, na azurfa da zinariya. Kada zuciyar wani mutum, ko ta wata mata ko na wani iyali, ko wata kabila cikinku yau, ta bar bin Ubangiji Allahnku, tă koma ga bauta wa gumakan waɗannan al’ummai. Kada a sami wani tushe mai ba da ’ya’ya masu dafi, masu ɗaci a cikinku. Idan kuma wani mutum ya ji kalmomi na wannan rantsuwa, ya kuma sa wa kansa albarka yana tunani cewa, “Ba abin da zai same ni, ko da na nace a taurinkaina.” Wannan zai jawo lalacewar dukan Isra’ila tare da kai. Ubangiji ba zai gafarce shi ba, fushinsa da kishinsa za su ƙuna a kan wannan mutum. Dukan la’anonin da aka rubuta a wannan littafi za su fāɗo a kansa, Ubangiji kuwa zai shafe sunansa daga ƙarƙashin sama. Ubangiji zai ware shi daga dukan kabilan Isra’ila don yă hukunta shi bisa ga dukan la’anonin alkawarin da aka rubuta a wannan Littafin Doka. Tsararraki masu zuwa nan gaba, wato, ’ya’yan da za su gāje ku, da baƙon da ya zo daga ƙasa mai nisa, za su ga annobar ƙasar, da cuce-cucen da Ubangiji ya buge ta da su. Ƙasar gaba ɗaya za tă zama gishiri mai ƙuna marar amfani da kuma kibiritu, babu shuki, babu abin da yake tsirowa, babu itatuwan da suke girma a cikinta. Za tă zama kamar yadda aka hallaka Sodom da Gomorra, Adma da Zeboyim, waɗanda Ubangiji ya hallaka cikin zafin fushinsa. Dukan al’ummai za su yi tambaya su ce, “Me ya sa Ubangiji ya yi haka da wannan ƙasa? Me ya jawo wannan fushi mai tsanani haka?” Amsar kuwa za tă zama, “Wannan ya zama haka domin wannan mutane, sun yi watsi da alkawarin Ubangiji Allah na kakanninsu, alkawarin da ya yi da su sa’ad da ya fitar da su daga Masar. Sun juya, suka bauta wa waɗansu alloli, suka rusuna musu, allolin da ba su sani ba, allolin da Ubangiji bai ba su ba. Saboda haka fushin Ubangiji ya yi ƙuna a kan wannan ƙasa, har ya kawo dukan la’anoni da aka rubuta a wannan littafi a kanta. Cikin zafin fushi da babbar hasala Ubangiji ya tumɓuke su daga ƙasarsu, ya watsar da su cikin wata ƙasa dabam, kamar yadda suke a yau.” Ubangiji Allahnmu bai bayyana abubuwa na yanzu da na nan gaba ba, amma ya umarce mu mu kiyaye kalmomin dokar da ya ba mu, mu da kuma ’ya’yanmu har abada. Sa’ad da dukan albarku da la’anonin nan da na sa a gabanku suka zo muku, kuka kuma sa su a zuciya, a duk inda Ubangiji Allahnku ya watsar da ku a cikin al’ummai, sa’ad da kuma ku da ’ya’yanku kuka komo ga Ubangiji Allahnku, kuka kuma yi biyayya da dukan zuciyarku da kuma dukan ranku, bisa ga kome da na umarce ku a yau, a sa’an nan ne Ubangiji Allahnku zai yi muku jinƙai, yă ji tausayinku, yă kuma sāke tattara ku daga dukan al’ummai inda ya warwatsa ku. Ko da ma an kore ku zuwa ƙasa mafi nisa a ƙarƙashin sammai, daga can Ubangiji Allahnku zai tattara ku, yă dawo da ku. Zai dawo da ku zuwa ƙasar da take ta kakanninku, za ku kuwa mallake ta. Zai sa ku yi arziki, ku kuma yi yawa fiye da kakanninku. Ubangiji Allahnku zai yi wa zukatanku kaciya da kuma zukatan zuriyarku, saboda ku ƙaunace shi da dukan zuciyarku da kuma dukan ranku, ku kuma rayu. Ubangiji Allahnku zai sa dukan waɗannan la’anoni a kan abokan gābanku waɗanda suke ƙinku, suke kuma tsananta muku. Za ku sāke yi wa Ubangiji biyayya, ku kuma bi dukan umarnan da nake ba ku a yau. Sa’an nan Ubangiji Allahnku zai mayar da ku masu arziki ƙwarai a cikin dukan aiki hannuwanku, da kuma cikin ’ya’yanku, da ’ya’yan shanunku, da kuma hatsin gonarku. Ubangiji zai sāke jin daɗinku yă sa ku yi arziki, kamar dai yadda ya ji daɗin kakanninku. In dai kuka yi biyayya ga Ubangiji Allahnku, kuka kuma kiyaye umarnansa da ƙa’idodin da aka rubuta a wannan Littafin Doka, kuka juyo ga Ubangiji Allahnku da dukan zuciyarku da kuma dukan ranku. To, abin da nake umartanku a yau, ba mai wuya ba ne gare ku, ba kuma abin da ya fi ƙarfinku ba ne. Ba ya can sama, balle ku ce, “Wa zai hau sama yă kawo mana, yă kuma furta mana, don mu yi biyayya?” Ba kuwa yana gaba da teku ba, da za ku ce, “Wa zai haye tekun don yă kawo mana, yă kuma furta mana, don mu yi biyayya?” A’a, kalmar tana nan dab da ku, tana cikin bakinku da cikin zuciyarku, don ku yi biyayya. Ku duba, na sa a gabanku a yau, rai da wadata, mutuwa da kuma hallaka. Gama na umarce ku a yau, ku ƙaunaci Ubangiji Allahnku, don ku yi tafiya a hanyoyinsa, ku kuma kiyaye umarnansa, ƙa’idodinsa da kuma dokokinsa, sa’an nan za ku rayu, ku kuma ƙaru, Ubangiji Allahnku kuwa zai albarkace ku a ƙasar da kuke shiga don ci gādonta. Amma in zukatanku suka kangare, ba su kuwa yi biyayya ba, in kuma aka rinjaye ku don ku rusuna ga waɗansu alloli ku yi musu bauta, na furta muku yau cewa tabbatacce za a hallaka ku. Ba za ku zauna a ƙasar da kuke hayewa Urdun don ku shiga ku ci gādonta ba. A wannan rana na kira bisa sama da ƙasa a matsayin shaidu a kanku, cewa na sa a gabanku rai da mutuwa, albarku da la’anoni. Yanzu sai ku zaɓi rai, saboda ku da ’ya’yanku ku rayu don kuma ku ƙaunaci Ubangiji Allahnku, ku saurari muryarsa, ku kuma manne masa. Gama Ubangiji shi ranku, zai kuwa ba ku shekaru masu yawa a ƙasar da ya rantse zai ba wa kakanninku, Ibrahim, Ishaku da Yaƙub. Sai Musa ya fita ya kuma faɗa waɗannan kalmomi ga dukan Isra’ila cewa, “Yanzu shekaruna ɗari da ashirin ne, ba na iya kaiwa da komowa. Ubangiji ya ce mini, ‘Ba za ka haye Urdun ba.’ Ubangiji Allahnku kansa zai haye a gabanku. Zai hallaka waɗannan al’ummai da suke gabanku, za ku kuwa mallaki ƙasarsu. Yoshuwa shi ma zai haye a gabanku, yadda Ubangiji ya faɗa. Ubangiji zai yi da su, yadda ya yi da Sihon da Og, sarakunan Amoriyawa, waɗanda ya hallaka tare da ƙasarsu. Ubangiji zai bashe su gare ku, dole kuma ku yi musu dukan abin da na umarce ku. Ku ƙarfafa, ku yi ƙarfin hali. Kada ku ji tsoro, ko ku firgita saboda su, gama Ubangiji Allahnku yana tafe tare da ku, ba zai taɓa barinku ko yă yashe ku ba.” Sai Musa ya kira Yoshuwa, ya ce masa a gaban dukan Isra’ila, “Ka ƙarfafa, ka kuma yi ƙarfin hali, gama dole ka tafi tare da mutanen nan zuwa cikin ƙasar da Ubangiji ya rantse cewa za ba wa kakanninku, dole kuma ka raba ta gare su ta zama gādonsu. Ubangiji kansa yana tafe a gabanka, zai kuma kasance tare da kai, ba zai taɓa barinka ko yă yashe ka ba. Kada ka ji tsoro; kada kuma ka karai.” Sai Musa ya rubuta wannan doka ya kuma ba da ita ga firistoci, ’ya’yan Lawi maza, waɗanda sukan ɗauka akwatin alkawarin Ubangiji, da kuma dukan dattawan Isra’ila. Sa’an nan Musa ya umarce su ya ce, “A ƙarshen kowace shekara bakwai, a shekara ta yafe basusuwa, a lokacin Bikin Tabanakul, sa’ad da dukan Isra’ila suka zo, don su bayyana a gaban Ubangiji Allahnku, a wurin da zai zaɓa, za ku karanta wannan doka a gabansu, a kunnuwansu. Ku tattara mutane, maza, mata da kuma yara, da baƙin da suke zama a cikin garuruwanku, saboda su saurara, su kuma koyi tsoron Ubangiji Allahnku, su lura, su bi dukan kalmomin wannan doka. ’Ya’yansu, waɗanda ba su san wannan doka ba, dole su ji ta, su kuma koyi tsoron Ubangiji Allahnku muddin ranku a ƙasar da kuke haye Urdun ku ci gādonta.” Sai Ubangiji ya ce wa Musa, “Yanzu ranar mutuwarka ta yi kusa. Ka kira Yoshuwa, ku shigo Tentin Sujada, inda zan ba shi ragamar aiki.” Saboda haka Musa da Yoshuwa suka zo, suka kuma shiga Tentin Sujada. Ubangiji kuwa ya bayyana a Tentin Sujada a cikin ginshiƙin girgije, sai girgijen ya tsaya a ƙofar Tentin Sujada. Sai Ubangiji ya ce wa Musa, “Za ka huta tare da kakanninka, waɗannan mutane kuwa ba da daɗewa ba za su yi karuwanci ga baƙin alloli na ƙasar da za su shiga. Za su yashe ni su kuma karya alkawarin da na yi da su. A wannan rana zan yi fushi da su, in kuma yashe su; zan ɓoye fuskata daga gare su, za a kuwa hallaka su. Masifu masu yawa da wahaloli masu yawa za su auka musu, a wannan rana kuwa za su ce, ‘Masifun nan sun same mu domin Allahnmu ba ya tare da mu’ Tabbatacce kuwa, zan ɓoye musu fuskata saboda muguntar da suka aikata, suka kuma bi gumaka. “To, sai ka rubuta wannan waƙa domin kanka, ka koya wa Isra’ilawa, ka kuma sa su rera ta, don tă zama shaida a kansu. Sa’ad da na kawo su cikin ƙasa mai zub da madara da zuma, ƙasar da na yi alkawari da rantsuwa ga kakanninsu, sa’ad da kuma suka ci suka ƙoshi, suka kuma yi ƙiba, za su juya ga waɗansu alloli su bauta musu, su ƙi ni, su kuma karya alkawarina. Sa’ad da kuma masifu masu yawa da wahaloli masu yawa suka auko musu, wannan waƙa za tă zama shaida a kansu, domin zuriyarsu ba za tă manta da ita ba. Na san abin da za su iya yi, kafin ma in kawo su cikin ƙasar da na yi musu alkawari da rantsuwa.” Sai Musa ya rubuta wannan waƙa a wannan rana, ya kuma koya wa Isra’ilawa. Ubangiji ya ba wa Yoshuwa ɗan Nun wannan umarni, “Ka ƙarfafa, ka kuma yi ƙarfin hali, gama za ka kawo Isra’ilawa cikin ƙasar da na yi musu alkawari da rantsuwa, ni kaina kuwa zan kasance tare da kai.” Bayan Musa ya gama rubuta kalmomin dokan nan a littafi daga farko zuwa ƙarshe, sai ya ba wa Lawiyawa, waɗanda suke ɗaukar akwatin alkawarin Ubangiji wannan umarni, “Ku ɗauki wannan Littafin Doka ku sa shi kusa da akwatin alkawarin Ubangiji Allahnku. A can zai kasance a matsayin shaida a kanku. Gama na sani yadda kuke ’yan tawaye da masu taurinkai. In kuna yin tawaye ga Ubangiji tun ina da rai tare da ku, yaya tawayen da za ku yi masa bayan na rasu! Ku tattara dukan dattawan kabilanku, da kuma dukan hafsoshinku a gabana, saboda in faɗa waɗannan kalmomi a kunnuwansu, in kuma kira ga sama da ƙasa su zama shaida a kansu. Gama na san cewa bayan rasuwata, tabbatacce za ku lalace gaba ɗaya, ku juye daga hanyar da na umarce ku. A kwanaki masu zuwa, masifa za tă auka muku saboda za ku aikata mugunta a gaban Ubangiji, ku tsokane shi har yă yi fushi ta wurin abin da hannuwanku suka yi.” Sai Musa ya karanta kalmomin waƙar daga farko zuwa ƙarshe a kunnuwan dukan taron jama’ar Isra’ila. Ku saurara, ya ku sammai, zan yi magana; bari duniya ta ji maganar bakina. Bari koyarwata tă zubo kamar ruwan sama kalmomina kuma su sauko kamar raɓa, kamar yayyafi a kan sabuwar ciyawa, kamar ruwan sama mai yawa a kan tsirai marasa ƙarfi. Zan yi shelar sunan Ubangiji. Ku yabi girman Allahnmu! Shi Dutse ne, ayyukansa cikakku ne, dukan hanyoyinsa kuwa masu adalci ne. Allah mai aminci, wanda ba ya yin rashi gaskiya, shi mai adalci ne, nagari ne kuma. Sun aikata mugunta a gabansa; saboda abin kunyarsu, su ba ’ya’yansa ba ne, amma wata muguwar tsara ce, karkatacciya. Haka za ku biya Ubangiji, Ya ku wawaye da kuma mutane marasa hikima? Shi ba Ubanku ba ne, Mahaliccinku, wanda ya yi ku, ya kuma siffanta ku? Ku tuna da kwanakin dā, ku tuna da tsararrakin da suka wuce tun tuni, Ku tambayi iyayenku, za su faɗa muku, dattawanku, za su kuma bayyana muku. Sa’ad da Mafi Ɗaukaka ya ba da al’ummai gādonsu, sa’ad da ya raba dukan ’yan adam, ya kafa iyakoki wa mutane bisa ga yawan ’ya’yan Isra’ila maza. Gama rabon Ubangiji shi ne mutanensa, Yaƙub shi ne rabon gādonsa. A cikin hamada ya same shi, a jeji marar amfani, inda namomi suke kuka. Ya tsare shi, ya kuma lura da shi; ya bi da shi kamar ƙwayar idonsa, kamar gaggafar da take yawo a kan sheƙarta tana rufe ’ya’yanta, ta buɗe fikafikanta don tă kwashe su tă ɗauke su a kafaɗunta. Ubangiji kaɗai ya jagorance shi; babu wani baƙon gunkin da yake tare da shi. Ya sa shi ya hau ƙwanƙolin dutse ya ciyar da shi da amfanin gona. Ya shayar da shi da zuma daga dutse, da kuma mai daga dutsen ƙanƙara, da kindirmo da madara daga shanu da tumaki da ƙibabbun tumaki da awaki, da zaɓaɓɓun ragunan Bashan da kuma ƙwayoyin alkama mafi kyau. Ka sha ruwan inabi ja wur mai kumfa. Yeshurun ya yi ƙiba, ya yi kauri; cike da abinci, ya zama da nauyi, ya kuma zama sumul. Ya yashe Allahn da ya yi shi, ya ƙi Dutse Cetonsa. Suka sa shi kishi saboda baƙin allolinsu, suka husata shi da gumakan banƙyamarsu. Suka yi hadaya ga aljanu, waɗanda ba Allah ba, ga allolin da ba su sani ba, ga allolin da aka shigo da su daga baya, allolin da kakanninku ba su ji tsoronsu ba. Kuka rabu da Dutsen da ya zama mahaifi gare ku; kuka manta da Allahn da ya haife ku. Ubangiji ya ga wannan ya kuma ƙi su, domin ’ya’yansa maza da mata sun husata shi. Ya ce, “Zan ɓoye fuskata daga gare su, in ga ƙarshensu; gama su muguwar tsara ce, ’ya’ya ne marasa aminci. Sun sa ni kishi ta wurin abin da ba allah ba, suka kuma husata ni da gumakansu na wofi. Zan sa su yi kishi ta wurin waɗanda ba mutane ba; zan sa su yi fushi ta wurin al’ummar da ba ta da sani. Gama fushina ya kama wuta, tana ci har ƙurewar zurfin lahira. Za tă cinye duniya da girbinta, tă kuma sa wuta a tussan duwatsu. “Zan tula masifu a kansu in kuma gama kibiyoyina a kansu. Zan aika da yunwa mai tsanani a kansu, zazzaɓi mai zafi da muguwar annoba; zan aika da haƙoran namun jeji a kansu, da dafin mesa masu ja da ciki. Waɗanda suke a waje, takobi zai kashe su, a cikin gidajensu kuma tsoro zai mamaye su. ’Yan maza da ’yan mata za su hallaka, haka ma jarirai da maza masu furfura. Na ce zan watsar da su in sa a manta da su a tunanin ’yan adam. Amma ina tsoron tsokanar abokin gāba, don kada abokan gāba su kāsa ganewa har su ce, ‘Hannunmu ne ya yi nasara; ba Ubangiji ne ya aikata dukan wannan ba.’ ” Al’ummai ne marasa azanci, babu ganewa a cikinsu. A ce su masu hikima ne har su gane wannan su gane abin da ƙarshensu zai zama! Yaya mutum guda zai kore dubu, mutum biyu su sa dubu goma su gudu, sai ko Dutsensu ya sayar da su, sai ko Ubangiji ya bashe su. Gama dutsensu ba kamar Dutsenmu ba ne, abokan gābanmu sun san da haka. Kuringarsu ta fito daga kuringar Sodom ne, daga gonakin Gomorra kuma. ’Ya’yan inabinsu dafi ne, nonnansu masu ɗaci ne. Ruwan inabinsu dafin macizai ne, mugun dafin gamshaƙa ne. “Ban jibge wannan a ma’ajiya na kuma yimƙe shi a taskokina ba? Sakayya nawa ne, zan kuwa ɗau fansa. A cikin lokaci, ƙafarsu za tă yi santsi; ranar masifarsu ta yi kusa hallakarsu kuma tana gaggautawa a kansu.” Ubangiji zai shari’anta mutanensa yă kuma ji tausayin bayinsa sa’ad da ya ga ƙarfinsu ya ƙare babu kowa kuma da ya rage, bawa ko ’yantacce. Zai ce, “To, ina allolinsu, dutsen da suka yi mafaka a ciki, allolin da suka ci kitsen hadayunsu suka kuma sha ruwan inabin hadayunsu? Ku sa su tashi su taimake ku mana! Bari su ba ku mafaka! “Ku duba yanzu cewa ni ne Shi! Ba wani allah in ban da ni. Nakan kashe in kuma rayar, nakan sa rauni in kuma warkar, ba wanda yake da iko yă cece wani daga hannuna. Na ɗaga hannu sama na kuma furta. Muddin ina raye har abada, sa’ad da na wasa takobi mai walƙiya hannuna kuwa ya cafke shi don yin hukunci, zan ɗau fansa a kan abokan gābana in sāka wa waɗanda suke ƙina. Zan sa kibiyoyina su bugu da jini, yayinda takobina yana cin nama, jinin kisassu da na kamammu, kawunan shugabannin abokan gāba.” Ku yi farin ciki, ya ku al’ummai, tare da mutanensa, gama zai rama ɗau fansar jinin bayinsa; zai ɗau fansa a kan abokan gābansa yă kuma yi kafara domin ƙasarsa da mutanensa. Sai Musa ya zo da Yoshuwa ɗan Nun suka faɗa dukan waɗannan kalmomi wannan waƙa a kunnen mutane. Sa’ad da Musa ya gama karanta waɗannan kalmomi ga dukan Isra’ila, ya ce musu, “Ku riƙe dukan kalmomin da na furta muku a yau, don ku umarce ’ya’yanku su lura, su yi biyayya da dukan kalmomin wannan doka. Ba kalmomi kurum ba ne dominku, amma har ranku ma. Ta wurinsu za ku yi tsawon rai a ƙasar da kuke haye Urdun ku ci gādonta.” A wannan rana Ubangiji ya ce wa Musa, “Ka hau Duwatsun Abarim zuwa Dutsen Nebo a Mowab, tsallake daga Yeriko, ka hangi Kan’ana, ƙasar da nake ba wa Isra’ilawa gādo. A can kan dutsen da ka hau za ka mutu a kuma tara ka ga mutanenka, kamar yadda ɗan’uwanka Haruna ya mutu a Dutsen Hor aka kuma tara shi ga mutanensa. Wannan kuwa domin ku biyu kun fid da aminci gare ni a gaban Isra’ilawa a ruwan Meriba ta Kadesh, a Hamadar Zin kuma saboda ba ku riƙe tsarkina a cikin Isra’ilawa ba. Saboda haka, za ka ga ƙasar daga nesa kawai; ba za ka shiga ƙasar da nake ba wa mutanen Isra’ila ba.” Wannan ita ce albarkar da Musa mutumin Allah ya furta a kan Isra’ilawa, kafin yă rasu. Ya ce, “ Ubangiji ya zo daga Sinai ya haskaka a bisansu daga Seyir; ya haskaka daga Dutsen Faran. Ya zo tare da dubban tsarkakansa daga kudu, daga gangara dutsensa. Tabbatacce kai ne wanda yake ƙaunar mutane; dukan tsarkaka suna a hannunka. A ƙafafunka, duk suka rusuna, daga wurinka kuma suka karɓi umarni, dokar Musa ta ba mu dokoki, mallakar taron Yaƙub. Shi ne sarki a bisa Yeshurun sa’ad da shugabannin mutane suka taru, tare da kabilan Isra’ila. “Bari Ruben yă rayu, kada yă mutu, kada mutanensa su zama kaɗan.” Ya kuma faɗa wannan game da Yahuda, “Ka ji, ya Ubangiji, kukan Yahuda; ka kawo shi wurin mutanensa. Da hannuwansa ya kāre kansa. Ka taimake shi a kan maƙiyansa!” Game da Lawi ya ce, “Tummim da Urim na mutumin da ka nuna masa tagomashi ne. Ka gwada shi a Massa; ka yi faɗa da shi a ruwan Meriba. Ya yi zancen mahaifinsa da mahaifiyarsa ya ce, ‘Ban kula da su ba.’ Bai gane da ’yan’uwansa ba, ko yă yarda da ’ya’yansa, amma ya kiyaye maganarka ya tsare alkawarinka. Ya koyar da farillanka ga Yaƙub, dokarka kuma ga Isra’ila. Ya miƙa turare a gabanka da kuma hadaya ta ƙonawa ɗungum a kan bagadenka. Ka albarkaci ɗaukan dabarunsa, ya Ubangiji, ka kuma ji daɗin aikin hannuwansa. Ka murƙushe kwankwaso waɗanda suka tayar masa; ka bugi abokan gābansa har sai ba su ƙara tashi ba.” Game da Benyamin ya ce, “Bari ƙaunataccen Ubangiji yă zauna lafiya kusa da shi, gama yana tsare shi dukan yini, wanda kuma Ubangiji yake ƙauna yana zama a tsakanin kafaɗunsa.” Game da Yusuf ya ce, “Bari Ubangiji yă albarkaci ƙasarsa da raɓa mai daraja daga sama a bisa da kuma zurfin ruwan da suke kwance a ƙarƙashi; da abubuwa masu kyau da rana take kawo, da kuma abubuwa mafi kyau da wata zai iya haifar; da zaɓaɓɓun kyautai na daɗaɗɗun duwatsu, da kyawawan amfani na madawwaman tuddai. Tare da kyautai mafi kyau na duniya da cikarta, da tagomashi na wanda yake zama a ƙaramin itace mai ƙonewa. Bari duk waɗannan su zauna a kan Yusuf, a goshin sarki a cikin ’yan’uwansa. Cikin daraja yana yi kamar ɗan fari na bijimi; ƙahoninsa ƙahonin ɓauna ne. Tare da su zai tukwiyi al’ummai, har ma da waɗanda suke ƙarshen duniya. Haka dubu dubban Efraim suke; haka dubban Manasse suke.” Game da Zebulun ya ce, “Ka yi farin ciki, Zebulun, a fitowarka, kai kuma Issakar, a cikin tentunanka. Za su kira mutane zuwa dutse, a can za su miƙa hadayun adalci; za su yi biki a yalwan tekuna, a dukiyoyin da aka ɓoye a cikin yashi.” Game da Gad ya ce, “Mai albarka ne wanda ya fadada mazaunin Gad! Gad yana zama a can kamar zaki, yana yayyage a hannu da kai. Ya zaɓi ƙasa mafi kyau wa kansa; aka ajiye masa rabon shugaba. Sa’ad da shugabannin mutane suka taru, ya aikata adalcin Ubangiji da kuma hukuncinsa game da Isra’ila.” Game da Dan ya ce, “Dan ɗan zaki ne, yana tsalle daga Bashan.” Game da Naftali ya ce, “Naftali ƙosasshe ne da tagomashin Ubangiji, ya kuma cika albarkarsa; zai gāji gefen kudu zuwa tafki.” Game da Asher ya ce, “Mafi albarka na ’ya’yan, shi ne Asher; bari yă sami tagomashi daga ’yan’uwansa, bari kuma yă wanke ƙafafunsa a cikin mai. Madogaran ƙofofinka za su zama ƙarfe da tagulla, ƙarfinka kuma zai zama daidai da kwanakinka. “Babu wani kamar Allah na Yeshurun, wanda yake hawa a bisa sammai don yă taimake ka a kan gizagizai kuma a cikin darajarsa. Allah madawwami shi ne mafakarka, a ƙarƙashina kuma madawwamin hannuwa ne. Zai kore abokin gābanka a gabanka, yana cewa, ‘Ka hallaka shi!’ Haka Isra’ila zai zauna lafiya shi kaɗai; zuriyar Yaƙub a tsare a ƙasar hatsi da sabon ruwan inabi, inda sammai za su zuba raɓa. Kai mai albarka ne, ya Isra’ila! Wane ne yake kamar ka, mutanen da Ubangiji ya ceta? Shi ne mafakarka da mai taimakonka da kuma takobinka mai ɗaukaka. Abokan gābanka za su zo neman jinƙai a gabanka, za ka kuwa tattake masujadansu.” Sai Musa ya hau Dutsen Nebo daga filayen Mowab, zuwa ƙwanƙolin Fisga, wanda yake ƙetare Yeriko. A can Ubangiji ya nuna masa dukan ƙasar, daga Gileyad zuwa Dan, da ta dukan Naftali, da yankin Efraim da na Manasse, dukan ƙasar Yahuda har zuwa Bahar Rum, da Negeb da dukan yankin Kwarin Yeriko, Birnin Dabino, har zuwa Zowar. Sa’an nan Ubangiji ya ce masa, “Wannan ce ƙasar da na yi alkawari da rantsuwa wa Ibrahim, Ishaku da Yaƙub, sa’ad da na ce, ‘Zan ba da ita ga zuriyarku.’ Na bar ka ka gani da idanunka, amma ba za ka haye zuwa cikinta ba.” Nan fa, a ƙasar Mowab Musa bawan Ubangiji ya mutu, yadda Ubangiji ya faɗa. Aka binne shi a Mowab, a kwarin kusa da Bet-Feyor, amma har wa yau babu wanda ya san inda kabarinsa yake. Musa yana da shekara ɗari da ashirin sa’ad da ya mutu, duk da haka idanunsa ba su dushe ba, ƙarfinsa kuwa bai ragu ba. Isra’ilawa suka yi makoki domin Musa a filayen Mowab kwana talatin, sai da lokacin kuka, da na makoki suka ƙare. To, Yoshuwa ɗan Nun ya cika da ruhun hikima, gama Musa ya ɗibiya hannuwansa a kansa. Saboda haka Isra’ilawa suka saurare shi, suka kuma aikata abin da Ubangiji ya umarci Musa. Tun daga nan ba a sāke yin wani annabi a Isra’ila kamar Musa ba, wanda Ubangiji ya san shi fuska da fuska, wanda kuma ya yi dukan waɗannan alamu banmamaki da al’ajaban da Ubangiji ya aike shi yă yi a Masar, da a kan Fir’auna, da a kan dukan shugabanninsa, da kuma a kan dukan ƙasarsa. Gama babu wani wanda ya taɓa nuna iko mai ƙarfi, ko yă aikata ayyukan banrazana waɗanda Musa ya yi a gaban dukan Isra’ila. Bayan mutuwar Musa bawan Ubangiji, sai Ubangiji ya ce wa Yoshuwa ɗan Nun, mataimakin Musa, “Bawana Musa ya mutu. Yanzu sai ka tashi tare da mutanen nan duka, ku yi shirin ƙetare kogin Urdun zuwa cikin ƙasar da zan ba su Isra’ilawa. Zan ba ku duk ƙasar da za ku taka, kamar yadda na yi wa Musa alkawari. Ƙasar da ta kama daga hamada zuwa Lebanon, zuwa babban Kogin, wato, Kogin Yuferites, da dukan ƙasar Hittiyawa zuwa Bahar Rum, wajen yamma. Ba wanda zai yi tsayayya da kai dukan kwanakin ranka. Yadda na kasance tare da Musa, haka zan kasance tare da kai; ba zan taɓa rabuwa da kai ba; ba zan yashe ka ba. “Ka yi ƙarfin hali ka kuma kasance da rashin tsoro, gama kai za ka bi da mutanen nan har su karɓi ƙasar da na yi wa kakanninsu alkawari zan ba su. Ka yi ƙarfin hali ka kuma kasance da rashin tsoro, ka yi lura fa, ka yi biyayya da dokokin da bawana Musa ya ba ka; kada ka kauce ga bin dokokin ko hagu ko dama, domin ka yi nasara a duk, inda za ka je. Kada ka bar Littafin Dokokin nan yă rabu da bakinka, sai dai ka yi ta tunani game da shi dare da rana, don ka lura, ka yi duk abin da aka rubuta a ciki, ta haka ne za ka yi nasara cikin duk abin da za ka yi. Ba ni na umarce ka ba? Ka yi ƙarfin hali ka kuma kasance da rashin tsoro. Kada ka ji tsoro; kada ka karaya, gama Ubangiji Allahnka zai kasance tare da kai duk inda za ka je.” Saboda haka sai Yoshuwa ya umarci shugabannin mutane, “Ku ratsa cikin sansani, ku gaya wa mutane, ‘Ku shirya guzurinku. Nan da kwana uku za ku ƙetare Urdun a nan, don ku je ka mallaki ƙasar da Ubangiji Allahnku yake ba ku ta zama taku.’ ” Amma Yoshuwa ya ce wa mutanen Ruben, mutanen Gad da kuma rabin mutanen kabilar Manasse, “Ku tuna da umarnin da Musa bawan Ubangiji ya yi muku. ‘ Ubangiji Allahnku ya ba ku hutawa, ya kuma ba ku wannan ƙasa.’ Matanku, da yaranku, da kuma dabbobinku za su kasance a ƙasar da Musa ya ba ku a gabashin Urdun, amma dole mayaƙanku, su yi shirin yaƙi su haye, su yi gaba tare da ’yan’uwanku, za ku taimaki ’yan’uwanku har sai lokacin da Ubangiji ya ba su hutawa, kamar yadda ya yi muku, kuma har sai su ma sun ƙwace ƙasar da Ubangiji Allahnku ya yi alkawari zai ba su. Bayan haka ne za ku koma ku mallaki ƙasarku, wadda Musa bawan Ubangiji ya ba ku a gabashin Urdun.” Sai suka amsa wa Yoshuwa suka ce, “Duk abin da ka ce mu yi, za mu yi. Duk inda kuma ka aike mu, za mu je. Kamar yadda muka yi wa Musa biyayya, haka za mu yi maka biyayya. Ubangiji Allahnka ya kasance tare da Musa. Duk wanda ya yi wa maganarka tawaye, ya ƙi yă yi biyayya da maganarka, ko da umarnin da ka ba shi, za a kashe shi. Ka dai ƙarfafa ka kuma yi ƙarfi hali!” Sai Yoshuwa ɗan Nun ya aika ’yan leƙen asiri guda biyu a ɓoye daga Shittim ya ce, “Ku je ku duba, ku ga yadda wurin yake, musamman Yeriko.” Sai suka je suka shiga gidan wata karuwa mai suna Rahab, suka sauka a can. Aka gaya wa sarkin Yeriko cewa, “Ji fa, waɗansu Isra’ilawa sun shigo nan da dare don su leƙi asirin ƙasar.” Saboda haka sai sarki ya aika wannan saƙo zuwa ga Rahab, “Ki fito da mutanen da suka zo suka sauka a gidanki, gama sun zo su leƙi asirin ƙasar ne gaba ɗaya.” Amma matar ta ɓoye mutanen nan biyu. Ta ce, “I, mutanen sun zo wurina, amma ban san daga ina suka zo ba, da yamma kuwa, kafin a rufe ƙofar gari sai mutanen suka tafi. Ban san hanyar da suka bi ba, ku yi sauri ku bi su. Mai yiwuwa ku same su.” (Amma ta kai su saman rufin ɗaki ta ɓoye su a ƙarƙashin karan rama da ta baza a rufin ɗaki.) Sai mutanen garin suka kama hanyar Urdun don su nemi ’yan leƙen asirin, daga fitar su sai aka rufe ƙofar garin. Kafin ’yan leƙen asirin su kwanta, sai ta tafi wurinsu a bisa rufin ɗakin ta ce musu, “Na sani Ubangiji ya riga ya ba ku ƙasan nan, tsoronku kuma ya kama mu har zukatan mazaunan ƙasar duka sun narke saboda ku. Mun ji yadda Ubangiji ya busar da ruwan Jan Teku domin ku lokacin da kuka fito daga ƙasar Masar, da kuma abin da kuka yi wa Sihon da Og, sarakunan nan biyu na Amoriyawa gabas da Urdun, waɗanda kuka hallaka su sarai. Da muka ji labarin, duk sai zuciyar kowa ta narke, kowa ya karaya saboda ku, gama Ubangiji Allahnku shi ne Allah na sama da ƙasa. Yanzu ina roƙonku ku rantse mini da Ubangiji cewa za ku yi wa iyalina alheri kamar yadda na yi muku alheri. Ku ba ni ƙwaƙƙwarar shaida cewa za ku ceci rayukan mahaifina da mahaifiyata, da ’yan’uwana maza da mata, da duk waɗanda suke nasu, za ku cece mu daga mutuwa.” Mutanen suka tabbatar mata suka ce, “Ranmu a bakin ranki! In ba ki faɗa wa kowa abin da ya kawo mu ba, za mu yi miki alheri da aminci lokacin da Ubangiji ya ba mu ƙasar.” Sai ta zura igiya ta taga suka bi, domin gidan da take yana haɗe da katangar birnin. Ta ce musu, “Ku tafi cikin tuddan ƙasar don kada mutanen sarki su same ku. Ku ɓuya a can na kwana uku, har sai masu nemanku su komo, sa’an nan ku kama hanyarku.” Mutanen suka ce mata, “Rantsuwar da kika sa muka yi, ba za tă yi amfani ba sai in kin ɗaura jan ƙyalle a tagar da kika zura mu, kuma sai in kin kawo mahaifinki da mahaifiyarki, da ’yan’uwanki, da dukan iyalinki cikin gidanki. In wani ya fita kan hanya, alhakin jininsa yă kasance a kansa; ba ruwanmu. Amma in aka taɓa wani da yake cikin gidanki tare da ke, alhakin jininsa yana kanmu. In kika tone mana asiri, za mu karya alkawarin da kika sa muka yi.” Ta ce, “Na yarda! Bari yă zama yadda kuka ce.” Sai ta sallame su suka tafi. Ta kuwa ɗaura jan ƙyalle a tagar. Sai suka tafi, suka shiga cikin tuddai, suka yi zamansu a can kwana uku har masu nemansu suka koma, gama masu nemansu suka yi ta nema ko’ina a hanyar, amma ba su sami kowa ba. Sa’an nan mutanen nan biyu, ’yan leƙen asiri suka sauka daga tuddai suka haye kogi zuwa wurin Yoshuwa ɗan Nun, suka gaya masa duk abin da ya faru da su. Suka ce wa Yoshuwa, “Ba shakka Ubangiji ya ba mu ƙasan nan duka, tana hannunmu, mutane can duk sun narke da tsoro saboda mu.” Kashegari Yoshuwa da dukan Isra’ilawa suka tashi daga Shittim suka nufi Urdun inda suka sauka kafin su haye. Bayan kwana uku sai shugabannin suka zazzaga sansani, suna ba da umarni ga mutane, suna cewa, “Lokacin da kuka ga akwatin alkawari na Ubangiji Allahnku, da firistoci waɗanda su ne Lawiyawa, suna ɗauke da shi, sai ku tashi daga inda kuke, ku bi shi. A ta haka za ku san inda za ku bi, gama ba ku taɓa bin hanyar ba. Sai dai ku ɗan ba da rata wajen yadi ɗari tara tsakaninku da akwatin alkawari, kada ku kusace shi.” Yoshuwa ya ce wa mutane, “Ku tsarkake kanku, gama gobe Ubangiji zai yi abubuwan al’ajabi a cikinku.” Yoshuwa ya ce wa firistoci, “Ku ɗauki akwatin alkawari ku sha gaba.” Sai suka ɗauki akwatin alkawari suka wuce gaban sauran jama’a. Ubangiji kuwa ya ce wa Yoshuwa, “Yau, zan fara ɗaukaka ka a gaban Isra’ilawa duka don su sani cewa ina tare da kai kamar yadda na kasance tare da Musa. Ka ce wa firistoci waɗanda suke ɗauke da akwatin alkawari, ‘Sa’ad da kuka kai bakin Urdun, ku shiga cikin ruwan ku tsaya.’ ” Yoshuwa ya ce wa Isra’ilawa, “Ku zo nan ku ji maganar Ubangiji Allahnku. Ta haka ne za ku san cewa Allah mai rai yana tare da ku, kuma ba shakka a gabanku za ku gani zai kore Kan’aniyawa, Hittiyawa, Hiwiyawa, Ferizziyawa, Girgashiyawa, Amoriyawa da Yebusiyawa. Ku duba, akwatin alkawarin Ubangiji na dukan duniya zai yi gaba cikin Urdun kafin ku. Yanzu sai ku zaɓi mutum goma sha biyu daga kabilan Isra’ila, ɗaya daga kowace kabila. Kuma da firistoci waɗanda suke ɗauke da akwatin alkawarin Ubangiji, Ubangiji dukan duniya, sun sa ƙafa cikin ruwan kogin Urdun, ruwan da yake gudu a rafin zai tsaya cik yă taru a wuri ɗaya.” Saboda haka sa’ad da mutanen suka tashi don su ƙetare Urdun, firistocin da suke ɗauke da akwatin alkawarin suka sha gaba. Da kaka Urdun yakan cika makil da ruwa. Duk da haka da zarar firistoci masu ɗauke da akwatin alkawari suka tsoma ƙafafunsu a gefen ruwa, sai ruwan da yake gangarowa ya tsaya, ya tattaru a wuri ɗaya ya yi tudu daga nan har zuwa wani garin da ake kira Adam kusa da Zaretan, ruwan da yake gangarowa zuwa Tekun Araba (Tekun Gishiri) kuma ya yanke gaba ɗaya. Sai mutane suka ƙetare kusa da Yeriko. Firistocin kuwa da suke ɗauke da akwatin alkawarin Ubangiji suka tsaya daram a kan busasshiyar ƙasa a tsakiyar Urdun a lokacin da Isra’ilawa suka ƙetarewa, har sai da dukan mutane suka gama ƙetarewa. Da al’umma gaba ɗaya suka ƙetare Urdun, Ubangiji ya ce wa Yoshuwa, “Ka zaɓi mutum goma sha biyu daga cikin mutane, ɗaya daga kowace kabila, ka ce musu kowa yă ɗauki dutse ɗaya daga tsakiyar Urdun daidai inda firistoci suka tsaya, ku kai su, ku ajiye a inda za ku sauka yau.” Sai Yoshuwa ya kira mutum goma sha biyu da ya zaɓa daga cikin Isra’ilawa, ɗaya daga kowace kabila ya ce musu, “Ku je tsakiyar Urdun inda akwatin alkawari na Ubangiji Allahnku yake. Kowannenku yă ɗauki dutse ɗaya a kafaɗarsa, bisa ga yawan kabilan Isra’ila, yă zama muku alama. Nan gaba in yaranku suka tambaye ku suka ce, ‘Mece ce ma’anar kasancewar duwatsun nan a nan?’ Sai ku ce musu, ruwan Urdun ya yanke a gaban akwatin alkawari na Ubangiji, a lokacin da akwatin alkawarin ya ƙetare Urdun. Waɗannan duwatsu za su zama abin tuni ga Isra’ilawa har abada.” Isra’ilawa kuwa suka yi yadda Yoshuwa ya umarce su. Suka ɗauki duwatsu guda goma sha biyu bisa ga yawan kabilan Isra’ila, yadda Ubangiji ya gaya wa Yoshuwa; suka tafi da su masauƙinsu, a can suka ajiye su. Yoshuwa ya ɗora duwatsu goma sha biyun a tsakiyar Urdun daidai inda firistoci waɗanda suke ɗauke da akwatin alkawarin Ubangiji suka tsaya. Suna nan a can har wa yau. Firistocin da suke ɗauke da akwatin alkawari suka tsaya a tsakiyar Urdun, har aka gama dukan abin da Ubangiji ya umarci Yoshuwa yă gaya wa mutane, kamar yadda Musa ya ce Yoshuwa yă yi. Mutanen suka wuce da sauri. Sai da dukan mutanen suka wuce sa’an nan akwatin alkawari da firistoci suka sha gaba. Mutanen Ruben, Gad da rabin kabilar Manasse suka ƙetare da shirin yaƙi, suka wuce gaban Isra’ila kamar yadda Musa ya ce su yi. Wajen mutum dubu arba’in shirye domin yaƙi, suka wuce a gaban Ubangiji zuwa filayen Yeriko. A ranan nan Ubangiji ya ɗaukaka Yoshuwa a gaban Isra’ilawa; suka kuma ba shi girma dukan kwanakin ransa, kamar yadda suka girmama Musa. Sa’an nan Ubangiji ya ce wa Yoshuwa, “Ka umarci firistocin da suke ɗauke da akwatin Shaida su fito daga cikin Urdun.” Sai Yoshuwa ya umarci firistoci ya ce, “Ku fito daga cikin Urdun.” Firistocin kuwa suka fito daga kogin ɗauke da akwatin alkawarin Ubangiji. Nan da nan da ƙafafunsu suka taɓa busasshiyar ƙasa, sai ruwan Urdun ya gangaro ya cika kogin kamar yadda yake a dā. A rana ta goma ga wata na farko, mutane suka haura daga Urdun suka sauka a Gilgal a gabashin iyakar Yeriko. Sai Yoshuwa ya kafa duwatsu goma sha biyun nan da suka ɗauko daga Urdun. Ya ce wa Isra’ilawa, “Nan gaba in yaranku suka tambayi iyayensu suka ce, ‘Mece ce ma’anar waɗannan duwatsun?’ Ku ce musu, ‘Isra’ilawa sun ƙetare kogin Urdun a kan busasshiyar ƙasa.’ Gama Ubangiji Allahnku ya sa ruwan Urdun ya yanke a gabanku, har sai da kuka gama wucewa, kamar yadda ya yi a Jan Teku, a lokacin da ya busar da shi a gabanmu har sai da muka gama wucewa. Ya yi wannan ne domin dukan mutanen duniya su san cewa Ubangiji mai iko ne, domin kuma ku zama masu tsoron Ubangiji Allahnku.” To, da dukan sarakunan Amoriyawa na yammancin Urdun, da dukan sarakunan Kan’aniyawan da suke bakin teku suka ji yadda Ubangiji ya busar da kogin Urdun a gaban Isra’ilawa, har sai da dukansu suka ƙetare, zuciyarsu ta narke, suka karaya sosai har ma suka rasa samun ƙarfin hali su fuskanci Isra’ilawa. A lokacin nan Ubangiji ya ce wa Yoshuwa, “Ka yi wuƙaƙe na duwatsu ka yi wa Isra’ilawa kaciya.” Sai Yoshuwa ya yi wuƙaƙe na duwatsu, ya yi wa Isra’ilawa kaciya a Gibeyat-Ha’aralot. Dalilin da ya sa ya yi haka shi ne, dukan waɗanda suka fito daga Masar, dukan mazan da suka kai shekarun shiga soja, sun mutu a cikin jeji a hanya bayan sun bar Masar. Dukan mutanen da suka fito daga Masar an yi musu kaciya, amma duk waɗanda aka haifa a jeji a tafiya daga Masar, ba a yi musu ba. Isra’ilawa sun yi tafiya a jeji shekaru arba’in, har sai da dukan mazan da suka kai shekarun shiga soja da suka bar Masar suka mutu, domin ba su yi wa Ubangiji biyayya ba. Gama Ubangiji ya rantse cewa ba zai bar su su ga ƙasar da ya yi wa iyayensu alkawari da rantsuwa cewa zai ba su ba, ƙasar da zuma da madara suke kwarara, ƙasar da take cike da albarka. Sai ya sa yaransu ne suka taso a maimakonsu, su ne waɗanda Yoshuwa ya yi wa kaciya. Sun kasance ba kaciya gama ba a yi musu ba a hanya. Kuma bayan da aka yi wa al’ummar kaciya dukansu, sai suka dakata a nan, sai da suka warke. Sai Ubangiji ya ce wa Yoshuwa, “Yau na kawar muku da zargin Masar.” Saboda haka ake kiran sunan wurin Gilgal har wa yau. Da yamman rana ta goma sha huɗu ga wata, lokacin da suke a Gilgal a filin Yeriko, Isra’ilawa suka yi Bikin Ƙetarewa. A kashegarin Bikin, a wannan rana, sai suka ci daga cikin amfanin ƙasar, burodi marar yisti da hatsin da aka gasa. Kashegari bayan da suka ci amfanin ƙasar kuwa, Manna ta yanke, mutanen Isra’ila kuma ba su ƙara samunta ba. A wannan shekara suka fara cin amfanin ƙasar Kan’ana. To, da Yoshuwa ya yi kusa da Yeriko, ya tā da idanunsa ya duba, sai ya ga wani mutum tsaye a gabansa riƙe da takobi, sai Yoshuwa ya je wurinsa ya ce masa, “Kai namu ne ko na abokan gābanmu?” Mutumin ya ce, “Babu ko ɗaya, na dai zo ne a matsayin shugaban rundunar sojojin Ubangiji.” Sai Yoshuwa ya kwanta da fuskarsa har ƙasa, ya girmama shi, ya ce masa, “Ranka yă daɗe, wane saƙo kake da shi domin bawanka?” Shugaban rundunar sojojin Ubangiji ya amsa ya ce, “Ka cire takalmanka, gama wurin da kake tsaye, mai tsarki ne.” Sai Yoshuwa ya cire takalmansa. Ƙofofin Yeriko kuwa a kulle suke ciki da waje saboda Isra’ilawa, ba mai fita babu kuma mai shiga. Sai Ubangiji ya ce wa Yoshuwa, “Duba, na ba ka nasara a kan Yeriko, duk da sarkinta da mayaƙanta. Da kai da dukan sojoji, ku zaga birnin sau ɗaya kullum. Ku yi haka har kwana shida. Ka sa firistoci guda bakwai su riƙe ƙahoni raguna su kasance a gaban akwatin alkawari. A rana ta bakwai sai ku zaga birnin sau bakwai, firistocin suna busa ƙahoni. Sa’ad da kuka ji sun ɗauki dogon lokaci suna busa ƙaho, sai mutane gaba ɗaya su tā da murya su yi ihu da ƙarfi; katangar birnin kuwa za tă rushe, sai sojoji su haura, ko wanne yă nufi inda ya fuskanta kai tsaye.” Yoshuwa ɗan Nun kuwa ya kira firistoci ya ce musu, “Ku ɗauki akwatin alkawari, ku sa firistoci guda bakwai su riƙe ƙahoni su kasance a gabansa.” Sai ya umarci jama’a ya ce, “Mu je zuwa! Ku zaga birnin, masu tsaro da makamai su shiga gaban akwatin alkawarin Ubangiji.” Da Yoshuwa ya gama yin wa mutane magana, sai firistoci guda bakwai waɗanda suke riƙe da ƙahoni guda bakwai a gaban Ubangiji suka sha gaba suna busa ƙahoninsu, akwatin alkawari kuwa yana biye da su. Masu tsaro da makamai kuma suna gaban firistoci waɗanda suke busa ƙahoni, masu tsaro daga baya kuma suna bin akwatin alkawari, ana ta busa ƙahoni. Amma Yoshuwa ya umarci mutane ya ce, “Kada ku yi kururuwar yaƙi, kada ku tā da murya, kada ku ce kome, sai ranar da na ce ku yi ihu, a sa’an nan ne sai ku yi ihu!” Sai ya sa aka ɗauki akwatin alkawarin Ubangiji aka kewaye birnin da shi sau ɗaya, sa’an nan mutane suka dawo masauƙinsu suka kwana a can. Kashegari, Yoshuwa ya tashi da sassafe, firistoci kuma suka ɗauki akwatin alkawarin Ubangiji. Firistoci guda bakwai waɗanda suke riƙe da ƙahoni guda bakwai suka shiga gaba, suna takawa a gaban akwatin alkawarin Ubangiji suna kuma busa ƙahoni, masu tsaro ɗauke da makamai suna gabansu, sai masu tsaro da suke baya suna biye da akwatin alkawarin Ubangiji. A rana ta biyu suka sāke zaga birnin sau ɗaya, suka kuma koma masauƙinsu. Haka suka yi har kwana shida. A rana ta bakwai, suka tashi da sassafe suka zaga birnin sau bakwai yadda suka saba. A wannan rana kaɗai ne suka zaga birnin sau bakwai. A zagawa ta bakwai, da firistoci suka busa ƙahoni, sai Yoshuwa ya ba sojojin umarni ya ce, “Ku yi ihu, gama Ubangiji ya ba ku birnin! Birnin da dukan abin da yake cikinta za a miƙa su ga Ubangiji. Rahab karuwan nan kaɗai ce, da dukan waɗanda suke tare da ita a gidanta za a bari da rai domin ta ɓoye ’yan leƙen asirin ƙasa da muka aika. Amma, ba za ku ɗauki wani abin da za a hallaka ba, idan kuka yi haka, za ku jawo masifa da hallaka a kan mutanen Isra’ila a inda kuka sauka. Dukan azurfa da zinariya, da kwanonin tagulla da na ƙarfe, keɓaɓɓu ne ga Ubangiji, dole a sa su cikin ma’ajin Ubangiji.” Da aka busa ƙahoni, sojoji suka yi ihu, da jin ƙarar ƙahoni, mutane suka kuma yi ihu, sai katangar ta rushe; dukan mutanen kuwa suka shiga birnin kai tsaye, suka yi nasara a kanta. Suka miƙa wa Ubangiji birnin, suka hallaka kowane abu mai ran da yake cikin birnin da takobi, maza da mata, yara da tsofaffi, shanu, tumaki da jakuna. Yoshuwa ya ce wa mutanen nan biyu waɗanda suka je leƙen asirin ƙasar, “Ku shiga gidan karuwan nan ku fitar da ita da duk waɗanda suke nata bisa ga alkawarin da kuka yi mata.” Sai samarin waɗanda suka je leƙen asirin suka shiga suka fitar da Rahab, mahaifinta da mahaifiyarta, da ’yan’uwanta da duk abin da yake nata. Suka fitar da iyalinta gaba ɗaya suka sa su a wani wuri, ba a cikin masauƙin Isra’ilawa ba. Sa’an nan suka ƙona birnin tare da dukan abin da yake ciki tatas, amma suka sa azurfa da zinariya da kayan tagulla da na ƙarfe a cikin ma’aji na haikalin Ubangiji. Amma Yoshuwa ya bar Rahab karuwan nan bai kashe ta ba, ita da iyalinta da duk abin da yake nata, domin ita ta ɓoye mutanen da Yoshuwa ya aika Yeriko don su leƙo asirin ƙasar kuma ta zauna tare da Isra’ilawa har wa yau. A lokacin nan Yoshuwa ya yi wannan alkawari cewa, “ Ubangiji zai tsine wa mutumin da zai yi ƙoƙarin sāke gina birnin nan, Yeriko. “A bakin ran ɗan farinsa zai kafa harsashin birnin; a bakin ran ɗan autansa kuma zai sa ƙofofin birnin.” Ubangiji ya kasance tare da Yoshuwa, aka kuma san da shi a duk fāɗin ƙasar. Amma Isra’ilawa ba su yi aminci game da kayan da aka hallaka ba; Akan ɗan Karmi, ɗan Zabdi, ɗan Zera, na kabilan Yahuda ya kwashi waɗansu abubuwa, saboda haka fushin Ubangiji ya sauka a kan Isra’ilawa. Sai Yoshuwa ya aika mutane daga Yeriko zuwa Ai kusa da Bet-Awen gabas da Betel, ya ce musu, “Ku je ku leƙo ku ga yadda yankin yake.” Sai mutanen suka je suka leƙo asirin ƙasar Ai. Da suka dawo wurin Yoshuwa suka ce, “Ba lalle dukan jama’a su je yaƙi da Ai ba, ka aika mutum dubu biyu ko dubu uku su je su ciwo ƙasar da yaƙi, ba sai ka dami mutane duka ba, gama mutanen wurin kaɗan ne.” Saboda haka sai kimanin mutum duba uku suka haura; amma mutanen Ai suka fatattake su, suka kashe Isra’ilawa wajen mutum talatin da shida, suka fafari Isra’ilawa tun daga bakin ƙofar birnin har zuwa wurin da ake fasa duwatsu. Suka karkashe su a gangare. Wannan ya sa zuciyar Isra’ilawa ta narke suka zama kamar ruwa. Sai Yoshuwa ya yaga tufafinsa ya fāɗi rubda ciki a gaban akwatin alkawarin Ubangiji, yana can har yamma. Dattawan Isra’ila ma suka yi haka, suka zuba toka a kawunansu. Yoshuwa kuma ya ce, “Ya Ubangiji Mai Iko Duka, me ya sa ka sa mutanen nan suka ƙetare Urdun don ka bari mu shiga hannun Amoriyawa su hallaka mu? Kila da mun haƙura mun zauna a ɗaya gefen Urdun da ya fi mana! Ya Ubangiji me zan ce, yanzu da abokan gāban Isra’ilawa suka ci ƙarfinsu? Yanzu Kan’aniyawa da sauran jama’a za su ji, za su zo su kewaye mu su share sunanmu daga duniya. To, yanzu me za ka yi don girman sunanka?” Ubangiji ya ce wa Yoshuwa, “Ka tashi! Me kake yi kwance rubda ciki? Isra’ilawa sun yi zunubi, sun karya sharaɗin da na yi musu. Sun ɗauki waɗansu abubuwan da aka keɓe; sun yi sata, sun yi ƙarya, sun ɓoye su cikin kayansu. Shi ne ya sa Isra’ilawa suka kāsa yin tsayayya da abokan gābansu; suka juya suka gudu domin za a hallaka su. Ba zan sāke kasancewa tare da ku ba sai in kun hallaka duk abin da aka keɓe don hallaka. “Tashi, ka je ka tsarkake mutane. Ka ce musu su tsarkake kansu, su yi shiri domin gobe; gama ga abin da Ubangiji, Allah na Isra’ila ya ce, a cikinku akwai abubuwan da aka keɓe, ya Isra’ilawa. Ba za ku iya yin tsayayya da abokan gābanku ba sai in kun rabu da abubuwan nan da aka haramta. “ ‘Da safe ku zo kabila-kabila. Kabilar da Ubangiji ya ware, za tă zo gaba gida-gida; gidan da Ubangiji ya ware, za su zo gaba iyali-iyali. Iyalin kuma da Ubangiji ya ware, za su zo gaba mutum bayan mutum. Mutumin da aka same shi da haramtattun abubuwan kuwa za a ƙone shi, duk da mallakarsa domin ya karya sharaɗin da Ubangiji ya yi muku, ya yi abin kunya a Isra’ila!’ ” Kashegari da sassafe Yoshuwa ya sa Isra’ilawa suka fito kabila-kabila, aka ware kabilar Yahuda. Gidan Yahuda suka zo gaba, sai aka ware gidan Zera, aka sa suka fito iyali-iyali, sai aka ware Zabdi. Yoshuwa kuwa ya sa iyalin Zabdi suka fito mutum-mutum, sai kuwa aka ware Akan ɗan Karmi, ɗan Zimri, ɗan Zera na kabilar Yahuda. Sai Yoshuwa ya ce wa Akan, “Ɗana, sai ka ba Ubangiji, Allah na Isra’ila ɗaukaka, ka yi masa yabo. Ka gaya mini abin da ka yi; kada ka ɓoye mini.” Akan kuwa ya amsa ya ce, “Gaskiya ne! Na yi wa Ubangiji, Allah na Isra’ila zunubi. Ga abin da na yi. A cikin ganimar, na ga doguwar riga mai kyau irin ta Babilon, da shekel ɗari biyu na azurfa, da kuma sandan zinariya mai nauyin shekel hamsin, sai raina ya so su, na kuwa kwashe su. Na tona rami a cikin ƙasa a tentina; na ɓoye.” Sai Yoshuwa ya aiki ’yan aika suka tafi da gudu zuwa tenti ɗin, haka kuwa suka same su a ɓoye a tentinsa, da azurfa a ƙarƙashi. Suka kwashe kayan daga tenti ɗin suka kawo wa Yoshuwa da sauran Isra’ilawa, suka baza su a gaban Ubangiji. Sai Yoshuwa da dukan Isra’ilawa suka ɗauki Akan ɗan Zera, da azurfar, doguwar rigar, sandan zinariya, ’ya’yansa maza da mata, shanunsa, jakuna da tumaki, tentinsa da duk abin da yake da shi, suka kai su Kwarin Akor. Yoshuwa ya ce, “Me ya sa ka jawo mana wahala haka? Ubangiji zai kawo maka wahala kai ma a yau.” Sai dukan Isra’ilawa suka jajjefe shi, bayan da suka gama jifarsa sai suka ƙone sauran. Suka tara manyan duwatsu a kan Akan, tarin duwatsun na nan a can har wa yau. Sa’an nan Ubangiji ya huce daga fushinsa mai zafi. Saboda haka ake kiran wurin Kwarin Akor. Sai Ubangiji ya ce wa Yoshuwa, “Kada ka ji tsoro; kada ka karaya. Ka ɗauki dukan sojojin ku kai wa Ai hari, gama na ba ka nasara a kan sarkin Ai, mutanensa, birninsa da kuma ƙasarsa. Za ku yi wa Ai yadda kuka yi wa Yeriko da sarkinta, sai dai za ku kwashe ganima da dabbobinta su zama naku. Ku yi kwanto a bayan birnin.” Yoshuwa da dukan sojojin suka fita su kai wa Ai hari. Sai ya zaɓi sojojinsa waɗanda suka fi saura duka iya yaƙi guda dubu talatin, ya tura su da dad dare ya ba su umarni ya ce, “Ku ji da kyau, za ku yi kwanto a bayan birnin, kada ku yi nisa da birnin. Kowannenku yă kasance a faɗake. Ni da waɗanda suke tare da ni za mu nufi birnin, a lokacin da mutanen suka taso mana yadda suka yi dā, sai mu guje musu. Za su bi mu har su yi nisa da birnin, gama za su ce, ‘Suna gudu kamar yadda suka yi dā.’ Saboda haka lokacin da muka guje musu, sai ku tashi daga inda kuka yi kwanto, ku ci birnin da yaƙi, Ubangiji Allahnku zai ba da shi a hannunku. Lokacin da kuka ƙwace birnin, sai ku sa masa wuta. Ku yi abin da Ubangiji ya umarta. Ku tabbata kun yi abubuwan da na ce.” Sai Yoshuwa ya sallame su, suka kuma tafi wurin da za su yi kwanto, suka kwanta suna fako tsakanin Betel da Ai, yamma da Ai, amma Yoshuwa ya kwana tare da mutanen. Kashegari da sassafe Yoshuwa ya tattara mutanensa, sai shi da shugabannin Isra’ilawa suka sha gaba suka taka zuwa Ai. Dukan sojojin da suke tare da shi suka nufi birnin, da suka kai kuwa sai suka kafa sansaninsu a arewancin Ai. Tsakaninsu da Ai akwai kwari. Yoshuwa ya sa mutum dubu biyar suka yi kwanto tsakanin Betel da Ai, a yammancin birnin. Mutanen suka kafa sansaninsu arewa da birnin, sansani na ’yan kwanto kuwa yana yamma da birnin, amma Yoshuwa ya kwana a kwarin. Sa’ad da sarkin Ai ya ga haka, shi da duk mutanen birnin suka hanzarta da sassafe don su gamu da Isra’ilawa, su yi yaƙi da su a wani wurin da yake fuskantar Araba. Amma bai san cewa an yi masa kwanto a bayan birnin ba. Yoshuwa da duk Isra’ilawa suka bari aka fafare su, sai suka gudu zuwa cikin jeji. Aka kira duk mazan Ai su fafare su, suka kuwa fafari Yoshuwa, aka yaudare su suka yi nisa da birnin. Ba namijin da ya rage a Ai ko Betel da bai fita don yă fafari Isra’ilawa ba. Suka bar birnin a buɗe, suka tafi fafarar Isra’ilawa. Sai Ubangiji ya ce wa Yoshuwa, “Ka riƙe māshin da yake hannunka ka nuna wajen Ai, gama zan ba da birnin a hannunka.” Yoshuwa kuwa ya miƙa māshin ta wajen Ai. Da yin haka kuwa sai mutanen da suka yi kwanto suka tashi nan da nan daga inda suke, suka nufi birnin a guje, suka shiga suka ci birnin da yaƙi, suka kuma cinna mata wuta da sauri. Mutanen Ai suka juya suka ga hayaƙin birninsu yana tashi sama, amma ba yadda za su iya tsira ta ko’ina, gama Isra’ilawan da suke gudu zuwa cikin jeji suka juya suka fara fafarar waɗanda suke fafararsu. Lokacin da Yoshuwa da dukan Isra’ilawa suka ga waɗanda suka yi kwanto sun ci birnin da yaƙi, hayaƙi kuwa ya cika birnin, sai suka juya suka kai wa mutanen Ai hari. Mutanen da suka yi kwanto su ma suka fito daga birnin suka tasar musu, ya zama an kama su a tsakiya, ga Isra’ilawa daga kowane gefe. Isra’ilawa kuwa suka karkashe su duka ba su bar wani da rai ba, ba kuma wanda ya tsere. Amma suka tafi da sarkin Ai da rai suka kawo shi wurin Yoshuwa. Da Isra’ilawa suka gama kashe duk mutanen Ai a filaye da kuma a cikin jeji inda suka fafare su, kuma da aka karkashe kowane mutumin Ai da takobi sai dukan Isra’ilawa suka koma Ai suka karkashe duk waɗanda suke cikinsa. A ranan nan, dukan mutanen Ai da aka kashe, mutum dubu goma sha biyu ne maza da mata. Gama Yoshuwa bai janye hannunsa da yake riƙe da māshinsa ba har sai da ya hallaka dukan mazaunan Ai. Amma Isra’ilawa suka kwashe ganima da dabbobin birnin nan yadda Ubangiji ya umarci Yoshuwa. Yoshuwa kuwa ya ƙone Ai, ya mai da ita tarin ƙasa, ta zama kufai har wa yau. Ya rataye sarkin Ai a kan itace, ya bar shi a can har yamma. Da rana ta fāɗi, Yoshuwa ya umarta a ɗauke gawar sarkin a jefa a gaban ƙofar birnin. Suka kuma tara manyan duwatsu a kan gawar, tsibin na nan har wa yau. Yoshuwa kuwa ya yi wa Ubangiji, Allah na Isra’ila bagade a Dutsen Ebal, kamar yadda Musa bawan Ubangiji ya umarci Isra’ilawa. Ya gina bisa ga abin da yake a rubuce a cikin Littafin Dokoki na Musa, bagade na duwatsun da ba a sassaƙa su ba, waɗanda ba wani ƙarfen da ya taɓa su. Suka miƙa wa Ubangiji hadayu na ƙonawa da hadayu na salama a kai. A can, a gaban Isra’ilawa, Yoshuwa ya rubuta dokokin Musa a kan duwatsun. Sai Isra’ilawa duka, da baƙi, da haifaffun gida, da dattawansu, da shugabanninsu, da alƙalansu, suka tsaya a gefe-gefen akwatin alkawarin Ubangiji, suna fuskantar waɗanda suke ɗauke da shi, wato, firistoci waɗanda su ne Lawiyawa. Rabin mutanen suka tsaya a gaban Dutsen Gerizim, rabinsu kuma suka tsaya a gaban Dutsen Ebal, kamar yadda Musa bawan Ubangiji ya riga ya umarta, cewa su sa wa mutanen Isra’ilawa albarka. Bayan haka, Yoshuwa ya karanta duk abin da yake a cikin Dokoki, albarku da la’anoni, kamar yadda suke a rubuce a cikin Littafin Dokoki. Babu wata kalmar da Musa ya umarta da Yoshuwa bai karanta wa dukan taron Isra’ilawa ba, haɗe da mata, da yara, da baƙin da suke zama tare da su. To, sa’ad da dukan sarakunan yammancin Urdun suka ji waɗannan abubuwa, sai waɗanda suke kan tudu, da na cikin kwari a yammanci, da dukan waɗanda suke gefen Bahar Rum har zuwa Lebanon (sarakunan Hittiyawa, Amoriyawa, Kan’aniyawa, Ferizziyawa, Hiwiyawa da Yebusiyawa) suka haɗa kansu don su yaƙi Yoshuwa da Isra’ila. Amma da mutanen Gibeyon suka ji abin da Yoshuwa ya yi wa Yeriko da Ai, sai suka shirya wata dabara ta ruɗu, suka shirya ɗan abinci don tafiya, suka ɗauki tsofaffin buhuna a kan jakunansu da tsofaffin salkuna na ruwan inabi, yagaggu da suka sha ɗinki. Suka sa tsofaffin takalman da suka sha gyara, suka sa tsofaffin tufafi. Dukan abincinsu na tafiya ya bushe ya yi fumfuna. Sai suka je wurin Yoshuwa a sansanin Gilgal suka ce masa da mutanen Isra’ila, “Daga ƙasa mai nisa muka fito, yanzu fa, sai ku yi alkawari da mu.” Mutanen Isra’ila kuwa suka ce wa Hiwiyawa, “Wataƙila kuna kusa da mu, ta yaya za mu yi alkawari da ku?” Suka ce wa Yoshuwa, “Mu bayinku ne.” Amma Yoshuwa ya tambaye su ya ce, “Ku wane ne, kuma daga ina kuka zo?” Suka amsa suka ce, “Bayinka sun zo ne daga ƙasa mai nisa gama Ubangiji Allahnka ya yi suna sosai. Gama mun ji labarin abubuwan da ya yi. Dukan abubuwan da ya yi a Masar da kuma duk abubuwan da ya yi wa sarakuna biyu na Amoriyawa gabas da Urdun, Sihon sarkin Heshbon, da Og sarkin Bashan wanda ya yi mulki a Ashtarot. Dattawanmu da duk mazaunan ƙasar, suka ce mana, ‘Ku ɗauki abincin tafiyar da za ku riƙe; ku je ku same su ku ce musu, “Mu bayinku ne, ku yi alkawari da mu.” ’ Abincin tafiyan nan namu yana da ɗumi lokacin da muka kintsa tashi daga gida a ranar da za mu kama hanya zuwa wurinku. Amma yanzu duba yadda ya bushe, ya yi fumfuna. Waɗannan salkuna kuma da muka cika ruwan inabi, sababbi ne amma duba yadda suka yayyage. Tufafinmu da takalmanmu duk sun yayyage don doguwar tafiya.” Mutanen Isra’ila suka ɗiba daga cikin abincin tafiyar amma ba su nemi nufin Ubangiji ba. Sa’an nan Yoshuwa ya yi alkawari zaman salama da su, cewa ba zai kashe su ba, sai shugabannin mutanen Isra’ila kuwa suka tabbatar musu da haka ta wurin yin rantsuwa. Kwana uku bayan sun yi alkawari da Gibeyonawa, sai Isra’ilawa suka ji cewa Gibeyonawa maƙwabtansu ne, waɗanda suke zaune kurkusa da su. Saboda haka Isra’ilawa suka tashi a rana ta uku suke je biranen mutanen, wato, Gibeyon, Kefira, Beyerot da Kiriyat Yeyarim. Amma Isra’ilawa ba su kai musu hari ba domin shugabanninsu sun rantse musu da sunan Ubangiji, Allah na Isra’ila. Mutane Isra’ila duka kuwa suka yi gunaguni a kan shugabannin. Amma shugabanni suka amsa musu suka ce, “Mun rantse musu da sunan Ubangiji, Allah na Isra’ila, saboda haka ba za mu taɓa su ba yanzu. Ga abin da za mu yi musu, za mu bar su da rai don kada fushin Allah yă sauka a kanmu gama mun riga mun rantse musu.” Suka ƙara da cewa, “Mu bar su da rai, amma bari su zama masu yankan itace da masu ɗibo mana ruwa.” Haka shugabannin suka cika alkawarinsu. Yoshuwa kuwa ya aika aka kira Gibeyonawa ya ce musu, “Don me kuka ruɗe mu kuka ce, ‘Mun zo ne daga wuri mai nisa,’ bayan kuwa kuna nan kurkusa da mu? Yanzu ku la’anannu ne. Ba za ku daina zama mana masu yankan itace da kuma masu ɗebo ruwa domin haikalin Allahnmu ba.” Suka amsa wa Yoshuwa suka ce, “An gaya wa bayinka dalla-dalla yadda Ubangiji Allahnka ya umarci bawansa Musa yă ba ka ƙasar duka, ka kuma kashe duk masu zama a cikinta, muka ji tsoro cewa za ka kashe mu shi ya sa muka yi haka. Yanzu, a hannunka muke, ka yi duk abin da ka ga ya yi maka kyau.” Yoshuwa kuwa ya cece su daga hannun Isra’ilawa, har ba su kashe su ba. A ranar Yoshuwa ya sa Gibeyonawa suka zama masu yankan itace da ɗebo ruwa wa jama’ar Isra’ila da kuma domin haikalin Ubangiji a inda Ubangiji zai zaɓa. Abin da suke ke nan har wa yau. Adoni-Zedek sarkin Urushalima ya ji cewa Yoshuwa ya ci Ai da yaƙi ya kuma hallaka ta sarai, ya yi wa Ai da sarkinta abin da ya yi wa Yeriko da sarkinta, mutanen Gibeyon kuwa sun yi yarjejjeniya ta salama da Isra’ilawa, suna kuma zama kusa da su. Shi da mutanensa suka ji tsoron wannan sosai, gama Gibeyon muhimmiyar birni ce, har ma kamar ɗaya daga cikin biranen sarauta, ya ma fi Ai girma, mazanta duka kuwa mayaƙa ne na ƙwarai. Saboda haka sai Adoni-Zedek sarkin Urushalima ya roƙi Hoham sarkin Hebron, Firam sarkin Yarmut, Yafiya sarkin Lakish da Debir sarki Eglon ya ce, “Ku zo ku taimake ni in kai wa Gibeyon hari. Domin sun yi yarjejjeniya ta salama da Yoshuwa da Isra’ilawa.” Sai sarakunan nan biyar na Amoriyawa, sarakunan Urushalima, Hebron, Yarmut, Lakish da Eglon suka haɗa sojojinsu. Suka je dukansu suka yi shirin kai wa Gibeyon hari. Sai mutanen Gibeyon suka aika zuwa wurin Yoshuwa a sansani a Gilgal, “Kada ka juya wa bayinka baya, ka zo da sauri ka cece mu! Ka taimake mu domin sarakunan Amoriyawa duka daga kan tudu sun haɗa ƙarfinsu tare za su tasar mana.” Saboda haka Yoshuwa ya tashi da rundunarsa duka, tare da dukan jarumawansa. Ubangiji ya ce wa Yoshuwa, “Kada ka ji tsoronsu; na ba ka su a hannunka. Ba waninsu da zai iya tsayayya da kai.” Bayan sun yi tafiya dukan dare daga Gilgal, Yoshuwa ya auko musu ba labari. Ubangiji ya sa suka ruɗe a gaban Isra’ilawa, Isra’ilawa kuwa suka yi babbar nasara a kansu a Gibeyon. Isra’ilawa suka fafare su a kan hanyar zuwa Bet-Horon suka karkashe su duka har zuwa Azeka da Makkeda. Suna guje wa Isra’ilawa suna gangarawa a kan hanyar Bet-Horon har zuwa Azeka, sai Ubangiji ya turo manyan duwatsu daga sararin sama suka karkashe su, waɗanda manyan duwatsun suka kashe sun fi waɗanda Isra’ilawa suka kashe da takobi. A ranar da Ubangiji ya ba da Amoriyawa a hannun Isra’ilawa, Yoshuwa ya ce wa Ubangiji a gaban Isra’ilawa, “Ke rana, ki tsaya cik a Gibeyon Kai wata, ka je Kwarin Aiyalon.” Sai rana ta tsaya cik, wata kuma ya tsaya, har sai da al’ummar ta ɗauki fansa a kan abokan gābanta, kamar yadda aka rubuta a cikin littafin Yashar. Rana ta tsaya a sararin sama, ba tă fāɗi ba har kusan yini guda. Ba a taɓa ganin abu haka ba ko dā can, ranar da Ubangiji ya saurari mutum. Ba shakka Ubangiji yana yaƙi domin Isra’ilawa. Sai Yoshuwa ya koma sansanin Gilgal tare da dukan Isra’ilawa. Sarakunan guda biyar suka gudu, suka ɓuya a cikin kogo a Makkeda. Lokacin da aka gaya wa Yoshuwa cewa an sami sarakunan nan biyar a ɓoye a cikin kogo a Makkeda. Sai ya ce, “Ku mirgina manyan duwatsu ku rufe bakin kogon, sai ku sa waɗannan mutane su yi tsaron kogon. Amma kada ku tsaya a can! Ku fafari abokan gābanku, ku kai musu hari ta baya, kada ku bari su kai biranensu, gama Ubangiji Allahnku ya ba da su a hannunku.” Saboda haka Yoshuwa da Isra’ilawa suka hallaka su da yawa ƙwarai, amma ’yan kaɗan ɗin da suka rage suka tsere zuwa cikin biranensu masu kāriya. Dukan rundunar kuma suka dawo sansanin Makkeda tare da Yoshuwa, ba abin da ya same su. Ba wanda ya sāke tsokanar Isra’ilawa. Yoshuwa ya ce, “Ku buɗe bakin kogon ku kawo mini sarakunan nan guda biyar.” Sai suka kawo sarakunan biyar daga cikin kogo; sarakunan Urushalima, Hebron, Yarmut, Lakish da Eglon. Sa’ad da aka kawo sarakunan nan wurin Yoshuwa, ya kira dukan Isra’ilawa ya ce wa shugabannin rundunoni waɗanda suke tare da shi, “Ku zo nan ku taka wuyan sarakunan nan.” Sai suka zo suka taka wuyansu. Yoshuwa ya ce musu, “Kada ku ji tsoro, ko kuwa ku razana, amma ku ƙarfafa, ku yi ƙarfin hali. Haka Ubangiji zai yi da duk abokan gāban da za ku yi yaƙi da su.” Sai Yoshuwa ya karkashe waɗannan sarakuna guda biyar, ya kuma rataye kowannensu a bisa itace inda jikunansu suka kasance har yamma. Da yamma Yoshuwa ya ba da umarni a sauko da su daga itatuwan a jefa su cikin kogon da suka ɓuya. Aka sa manyan duwatsu aka rufe bakin kogon, suna a can har wa yau. A ranan nan Yoshuwa ya ci Makkeda da yaƙi. Ya karkashe mutanen tare da sarkinta. Bai bar wani da rai ba. Ya yi wa sarkin Makkeda yadda ya yi wa sarkin Yeriko. Sai Yoshuwa da dukan Isra’ilawa suka tashi daga Makkeda zuwa Libna, suka kai mata hari. Ubangiji kuma ya ba da ƙasar da sarkinta a hannun Yoshuwa. Yoshuwa ya karkashe kowa ya hallaka birnin, bai bar wani da rai ba. Ya kuma yi wa sarkin yadda ya yi wa sarkin Yeriko. Sai Yoshuwa da dukan Isra’ilawa suka tashi daga Libna zuwa Lakish; suka yi shiri suka kai mata hari. Ubangiji ya ba da Lakish a hannun Isra’ilawa, a rana ta biyu kuwa Yoshuwa ya ci nasara a kansu. Ya karkashe duk mutanen birnin ya kuma hallaka birnin, kamar yadda ya yi a Libna. Horam sarkin Gezer kuwa ya zo don yă taimaki Lakish, amma Yoshuwa ya haɗa duk da shi da rundunarsa ya ci su da yaƙi, har bai bar waninsu da rai ba. Yoshuwa kuwa da dukan Isra’ilawa suka tashi daga Lakish zuwa Eglon; suka yi shiri suka kai mata hari. A ranan nan suka ci ƙasar da yaƙi, suka buge ta, suka karkashe kowa da takobi kamar dai yadda suka yi a Lakish. Sai Yoshuwa da dukan Isra’ilawa suka tashi daga Eglon zuwa Hebron suka kai hari a can. Suka ci birnin da yaƙi, suka karkashe mazaunanta, da sarkin, har da ƙauyukan, ba wanda ya tsira kamar yadda ya yi wa Eglon. Ya hallakar da ita sarai duk da kowane mutum da yake cikinta. Yoshuwa da Isra’ilawa duka suka juya suka kai wa Debir hari, suka hallaka birnin, da sarkinta da ƙauyukanta, suka karkashe dukan mazaunan wurin, ba su bar wani da rai ba. Suka yi wa Debir da sarkinta yadda suka yi wa Libna da sarkinta da kuma Hebron. Yoshuwa ya cinye yankin duka da yaƙi, haɗe da na kan tudu, da Negeb, da kwarin yamma, da filayen cikin duwatsu tare da sarakunansu duka. Bai bar wani da rai ba, ya kashe duk wani mai numfashi, yadda Ubangiji, Allah na Isra’ilawa ya umarta. Yoshuwa ya ci su da yaƙi daga Kadesh Barneya zuwa Gaza, da kuma daga dukan yankin Goshen zuwa Gibeyon. Yoshuwa kuwa ya cinye sarakunan nan duka da ƙasashensu gaba ɗaya gama Ubangiji, Allah na Isra’ila ne ya yi yaƙi domin Isra’ilawa. Yoshuwa kuwa ya dawo da dukan Isra’ilawa zuwa sansani a Gilgal. Sa’ad da Yabin sarkin Hazor ya ji wannan, sai ya aika saƙo zuwa wurin Yobab sarkin Madon, da sarkin Shimron, da Akshaf, ya kuma aika zuwa ga sarakunan arewa waɗanda suke kan tuddai da kuma waɗanda suke cikin Araba a kudancin Kinneret da cikin filayen kwari, da cikin Nafot Dor a yamma; ya kuma aika zuwa ga Kan’aniyawa a gabas da yamma; da kuma zuwa ga Amoriyawa, Hittiyawa da Ferizziyawa, da Yebusiyawa da suke kan tuddai; da kuma Hiwiyawa masu zama a gindin dutsen Hermon a yankin Mizfa. Suka fito da dukan rundunansu da keken yaƙi masu yawan gaske, babbar runduna, yawansu ya yi kamar yashin bakin teku. Duk sarakunan nan suka haɗa mayaƙansu tare, suka kafa sansani a bakin Ruwayen Meron don su yi yaƙi da Isra’ilawa. Ubangiji ya ce wa Yoshuwa, “Kada ka ji tsoronsu, domin war haka gobe zan ba da dukansu a hannun Isra’ilawa, za su kuwa karkashe su. Za ku gurgunta dawakansu, ku kuma ƙone keken yaƙinsu.” Sai Yoshuwa da dukan mayaƙan suka auka musu a bakin Ruwayen Meron. Ubangiji kuwa ya ba Isra’ilawa nasara a kan su, suka ci su da yaƙi, suka fafare su har zuwa Sidon Babba, zuwa Misrefot Mayim, har zuwa Kwarin Mizfa a gabas, ba wanda suka bari da rai. Yoshuwa ya yi musu yadda Ubangiji ya umarta, ya gurgunta dawakansu, ya kuma ƙone keken yaƙinsu. A lokacin nan Yoshuwa ya koma da baya ya ci Hazor da yaƙi, ya kuma kashe sarkinta da takobi. (Hazor ce babbar masarautan ƙasashen nan.) Suka karkashe duk mazaunan ƙasar da takobi, ba su bar wani mai numfashi ba, suka kuma ƙona Hazor. Yoshuwa ya ƙwace masarautun nan duka ya kuma kashe sarakunansu da takobi, ya hallakar da su ƙaƙaf kamar yadda Musa bawan Ubangiji ya umarta. Duk da haka Isra’ilawa ba su ƙone biranen da suke kan tuddai ba, sai Hazor kaɗai Yoshuwa ya ƙone. Isra’ilawa suka kwashi ganima da dabbobi na waɗannan birane, amma suka karkashe mutanen duka da takobi, ba su bar wani mai numfashi ba. Yadda Ubangiji ya umarci bawansa Musa, haka Musa ya umarci Yoshuwa, shi kuwa ya yi duk abin da Ubangiji ya umarci Musa. Saboda haka Yoshuwa ya cinye ƙasar duka da yaƙi, dukan Negeb, duka yankin Goshen, filayen kwari na yamma, Araba da tuddai na Isra’ila da kwarinta. Daga Dutsen Halak wanda ya miƙe zuwa wajajen Seyir, zuwa Ba’al-Gad a Kwarin Lebanon ƙasa da Dutsen Hermon. Ya kama sarakunansu ya karkashe su. Yoshuwa ya daɗe yana yaƙi da dukan waɗannan sarakuna. Sai Hiwiyawa kaɗai waɗanda suke zama a Gibeyon, sauran ba ko birni ɗaya da ta yi yarjejjeniya ta salama da Isra’ilawa, Isra’ilawa kuwa suka ci dukansu da yaƙi. Gama Ubangiji ne ya taurare zukatansu waɗannan sarakuna suka yi yaƙi da Isra’ilawa don yă hallaka su gaba ɗaya, yă gamar da su ba jinƙai, yadda Ubangiji ya umarci Musa. A lokacin nan Yoshuwa ya je ya hallaka Anakawa daga ƙasar tudu. Daga Hebron, Debir da Anab. Daga dukan ƙasar tuddai na Yahuda, da kuma dukan ƙasar tudu ta Isra’ila, Yoshuwa ya hallaka su duka da garuruwansu. Ba a bar waɗansu Anakawa a harabar Isra’ila ba; sai dai a Gaza, Gat da Ashdod ne aka samu waɗanda suka ragu da rai. Yoshuwa kuwa ya ƙwace dukan ƙasar yadda Ubangiji ya umarci Musa, ya ba da ita ta zama ƙasar gādo ga Isra’ilawa, kabila-kabila. Ta haka ƙasar ta huta daga yaƙi. Waɗannan su ne sarakunan ƙasashen da Isra’ilawa suka ci da yaƙi, suka kuma mallaki ƙasarsu a gabashin Urdun, daga kwarin Arnon zuwa Dutsen Hermon haɗe da dukan gefen gabas na Araba. Sihon sarkin Amoriyawa, wanda ya yi mulki a Heshbon. Ya yi mulki daga Arower wadda take iyakar kwarin Arnon, daga tsakiyar kwarin har zuwa, Kogin Yabbok, wanda yake iyakar Ammonawa. Wannan ya haɗa da rabin Gileyad. Ya kuma yi mulki a kan gabashin Araba daga tekun Kinneret zuwa Tekun Araba (wato, Tekun Gishiri), zuwa Bet-Yeshimot da kuma kudu zuwa gangaren dutsen Fisga. Haka ma suka ci sashen Og sarkin Bashan, ɗaya daga cikin Refahiyawa na ƙarshe da ya yi mulki a Ashtarot da Edireyi. Mulkinsa ya taso daga Dutsen Hermon, da Saleka, da dukan Bashan har zuwa iyakar Geshurawa da Ma’akatiyawa haɗe da rabin Gileyad, zuwa kan iyakar Heshbon ta sarki Sihon. Sai Musa, bawan Ubangiji da Isra’ilawa suka ci Sihon da Og da yaƙi. Musa bawan Ubangiji kuwa ya ba da ƙasarsu ga mutanen Ruben, mutanen Gad da kuma rabin mutanen kabilar Manasse. Waɗannan su ne sarakuna da kuma ƙasashen da Yoshuwa da Isra’ilawa suka ci da yaƙi a yammancin Urdun, daga Ba’al-Gad a Kwarin Lebanon zuwa Dutsen Halak wanda ya miƙe zuwa Seyir. Yoshuwa ya raba ƙasarsu ta zama gādo ga Isra’ilawa bisa ga yadda aka raba su kabila-kabila. Ƙasar ta haɗa da ƙasar kan tudu, filayen arewanci, Araba, gangaren Dutse, da jejin, da kuma Negeb, wato, ƙasashen Hittiyawa, Amoriyawa, Kan’aniyawa, Ferizziyawa, Hiwiyawa, da Yebusiyawa. Sarkin Yeriko, ɗaya sarkin Ai (kusa da Betel), ɗaya sarkin Urushalima, ɗaya sarkin Hebron, ɗaya sarkin Yarmut, ɗaya sarkin Lakish, ɗaya sarkin Eglon, ɗaya sarkin Gezer, ɗaya sarkin Debir, ɗaya sarkin Bet-Gader, ɗaya sarkin Horma, ɗaya sarkin Arad, ɗaya sarkin Libna, ɗaya sarkin Adullam, ɗaya sarkin Makkeda, ɗaya sarkin Betel, ɗaya sarkin Taffuwa, ɗaya sarkin Hefer, ɗaya sarkin Afek, ɗaya sarkin Sharon, ɗaya sarkin Madon, ɗaya sarkin Hazor, ɗaya sarkin Shimron Meron, ɗaya sarkin Akshaf, ɗaya sarkin Ta’anak, ɗaya sarkin Megiddo, ɗaya sarkin Kedesh, ɗaya sarkin Yokneyam a Karmel, ɗaya sarkin Dor (A Nafot Dor), ɗaya sarkin Goyim a Gilgal, ɗaya sarki Tirza, ɗaya. Duka-duka dai sarakuna talatin da ɗaya ne. Sa’ad da Yoshuwa ya tsufa, Ubangiji ya ce masa, “Ka tsufa ƙwarai, ga shi kuma akwai sauran ƙasa mai fāɗi da ba ku riga kun mallaka ba. “Ga ƙasar da ta rage, “dukan yankunan Filistiyawa da na Geshurawa. Daga Kogin Shihor a gabashin Masar zuwa sashen Ekron a arewa, dukan wannan ƙasa ana lissafta ta a cikin ƙasar Kan’aniyawa, ko da yake tana a sashen da sarakuna biyar na Filistiyawa na Gaza, Ashdod, Ashkeloniyawa, Gat da Ekron; na Awwiyawa. Daga wajen kudu kuma, dukan ƙasar Kan’aniyawa ce. Iyakarta a arewa ta fara daga Ara ta Sidoniyawa har zuwa Afek, ta zarce har zuwa iyakar Amoriyawa; da ƙasar Gebaliyawa; da dukan Lebanon wajen gabas daga Ba’al-Gad a gindin Dutsen Hermon zuwa Lebo Hamat. “Dukan mazauna kan yankunan tuddai daga Lebanon zuwa Misrefot Mayim, wato, dukan Sidoniyawa, ni da kaina zan kore su a gaban Isra’ilawa. Ka tabbata ka raba wa Isra’ilawa ƙasar ta zama gādonsu kamar yadda na umarce ka, ka raba ta tă zama gādo wa kabilu tara da kuma rabin kabilar Manasse.” Rabin kabilar Manasse, mutanen Ruben da mutanen Gad suka karɓi rabonsu na gādo wanda Musa ya ba su a gabashin Urdun. Abin da Musa bawan Ubangiji ya ba su ke nan. Wannan ya tashi daga Arower a gefen kwarin Arnon, da kuma daga garin da yake tsakiyar kwarin, ya kuma haɗa da ƙasar da take tudun Medeba har zuwa Dibon, da dukan garuruwan Sihon sarkin Amoriyawa, wanda ya yi mulkin Heshbon, har zuwa iyakar Ammonawa. Haɗe da Gileyad, inda mutanen Geshur da Ma’aka suke. Dukan Dutsen Hermon, da dukan Bashan har zuwa Saleka, wato, dukan masarautar Og a Bashan, wanda ya yi mulkin Ashtarot da Edireyi, yana cikin waɗanda suke na ƙarshe da ba a kashe ba a cikin Refahiyawa. Musa ya ci su da yaƙi, ya ƙwace ƙasarsu. Amma Isra’ilawa ba su kori mutanen Geshur da Ma’aka ba, saboda haka suka ci gaba da zama cikin Isra’ilawa har wa yau. Kabilar Lawiyawa ne kaɗai Musa bai ba ta gādo ba, gama hadayun ƙonawa da ake miƙa wa Ubangiji, Allah na Isra’ila ne gādonsu, kamar yadda ya yi musu alkawari. Ga abin da Musa ya ba kabilar Ruben bisa ga iyalansu. Abin da ya kama daga Arower a gefen kwarin Arnon, da kuma daga garin da yake tsakiyar kwarin, da dukan ƙasar tudu kusa da Medeba zuwa Heshbon, da dukan garuruwan kan tudu, haɗe da Dibon, Bamot Ba’al, Bet-Ba’al-Meyon, Yahza, Kedemot, Mefa’at, Kiriyatayim, Sibma, Zeret Shahar kan tudu cikin kwari, Bet-Feyor, gangaren Fisga da Bet-Yeshimot, dukan garuruwan da suke kan tudu da dukan masarautar Sihon sarkin Amoriyawa, wanda ya yi mulki a Heshbon. Musa ya yi nasara da shi, da shugabannin Midiyawa, wato, Ewi, Rekem, Zur, Hur, da Reba, sarakunan Sihon, waɗanda suka zauna a ƙasar. Ƙari a kan waɗanda aka kashe a yaƙi, Isra’ilawa suka kashe Bala’am ɗan Beyor da takobi don yana duba. Gefen Urdun shi ne iyakar mutanen Ruben. Waɗannan garuruwa da ƙauyukansu su ne gādon mutanen Ruben, bisa ga iyalansu. Ga abin da Musa ya ba kabilar Gad, bisa ga iyalansu. Yankin ƙasarsu ya ƙunshi Yazer, da dukan garuruwan Gileyad, da rabin ƙasar Ammonawa har zuwa Arower kusa da Rabba, da kuma daga Heshbon zuwa Ramat Mizfa da Betonim, da kuma daga Mahanayim zuwa sashen Debir, kuma a cikin kwari, Bet-Haram, Bet-Nimra, Sukkot da Zafon da kuma sauran masarautar Sihon sarkin Heshbon (gabashin Urdun, abin da ya kama har zuwa ƙarshen Tekun Kinneret). Waɗannan garuruwan da ƙauyukansu duka, gādon mutanen Gad ne, bisa ga iyalansu. Ga abin da Musa ya ba rabin kabilar Manasse, wato, wa rabin zuriyar Manasse, bisa ga iyalansu. Abin da ya miƙe daga Mahanayim haɗe da dukan Bashan, da gefen masarautar Og sarkin Bashan, da dukan garuruwan Yayir guda sittin da suke a Bashan, da rabin Gileyad, da Ashtarot, Edireyi (biranen sarki Og a Bashan). Wannan shi ne rabon da zuriyar Makir ɗan Manasse suka samu, domin rabin ’ya’yan Makir maza, bisa ga iyalansu. Waɗannan su ne rabon gādon da Musa ya yi lokacin da suke cikin filayen Mowab a hayin gabashin Urdun kusa da Yeriko. Amma Musa bai ba kabilar Lawiyawa gādo ba; Ubangiji, Allah na Isra’ila, shi ne gādonsu kamar yadda ya yi musu alkawari. Ga wuraren da Isra’ilawa suka sami gādo a ƙasar Kan’ana waɗanda Eleyazar firist, Yoshuwa ɗan Nun da kuma shugabannin iyalai kabila-kabila na Isra’ila suka raba musu. Ta wurin yin ƙuri’a aka raba wa kabilan nan tara da rabi, yadda Ubangiji ya umarta ta wurin Musa. Musa ya ba wa kabilan biyu da rabin nan gādonsu gabashin Urdun, amma bai ba wa Lawiyawa gādo a cikin sauran ba, gama ’ya’yan Yusuf sun zama kabilu biyu, Manasse da Efraim. Ba a ba Lawiyawa gādon ba sai dai garuruwan da aka ba su su zauna a ciki, da wurin kiwo mai kyau domin dabbobinsu. Haka Isra’ilawa suka raba ƙasar, yadda Ubangiji ya umarci Musa. Mutanen Yahuda kuma suka je wurin Yoshuwa a Gilgal, sai Kaleb ɗan Yefunne Bakenizze ya ce wa Yoshuwa, “Ka san abin da Ubangiji ya gaya wa Musa, mutumin Allah a Kadesh Barneya game da kai da ni. Ina da shekara arba’in lokacin da Musa bawan Ubangiji ya aike ni zuwa Kadesh Barneya in leƙi asirin ƙasar. Na kuwa kawo masa rahoto daidai yadda na ga ƙasar, amma ’yan’uwana waɗanda muka je tare su suka ba da rahoton da ya sa zukatan mutane suka narke don tsoro. Ni kam na bi Ubangiji Allah da dukan zuciyata. Saboda haka a ranan nan Musa ya rantse mini cewa, ‘Ƙasar da ka taka za tă zama ƙasarka ta gādo kai da ’ya’yanka har abada, domin ka bi Ubangiji Allahna da dukan zuciyarka.’ “Ga shi, kamar yadda Ubangiji ya yi alkawari, ya bar ni da rai har na ƙara shekaru arba’in da biyar tun daga lokacin da ya gaya wa Musa wannan, a lokacin da Isra’ilawa suke yawo a cikin jeji. Ga ni nan yau shekaruna tamanin da biyar! Ina nan da ƙarfina kamar yadda nake da ƙarfi a lokacin da Musa ya aike ni; zan iya fita zuwa yaƙi da ƙwazo yanzu kamar yadda nake zuwa a dā. Yanzu sai ka ba ni wannan ƙasar da take kan tudu wadda Ubangiji ya yi alkawari zai ba ni a ranan nan. Kai ma ka ji a lokacin, yadda Anakawa suke a can, biranensu manya ne kuma sun kewaye su sosai, amma na sani Ubangiji zai taimake ni, zan kore su kamar yadda ya faɗa.” Sai Yoshuwa ya sa wa Kaleb ɗan Yefunne albarka, ya ba shi Hebron. Saboda haka Hebron ta zama ƙasar Kaleb ɗan Yefunne Bakenizze tun daga lokacin nan, domin ya bi Ubangiji, Allah na Isra’ila da dukan zuciyarsa. (Dā a kan kira wannan Hebron, Kiriyat Arba. Wannan Arba kuwa shi ne wani katon mutum a cikin Anakawa.) Sa’an nan ƙasar ta huta daga yaƙi. An raba wa kabilar Yahuda gādonsu ta wurin yin ƙuri’a, bisa ga iyalansu, rabon ya kai har zuwa sashen Edom, zuwa Jejin Zin can kurewar kudu. Iyakarsu a kudanci ta tashi tun daga kurewar kudu na Tekun Gishiri, zuwa kudancin Hanyar Kunama, ta ci gaba har zuwa Zin, zuwa kudancin Kadesh Barneya. Sa’an nan ta kurɗa zuwa Hezron har zuwa Addar, ta kuma karkata zuwa Karka. Sai ta wuce zuwa Azmon ta haɗu da Rafin Masar, ta ƙarasa a Bahar Rum. Wannan shi ne iyakarsu ta kudu. Iyakarsu ta gabas kuwa ita ce Tekun Gishiri wadda ta zarce har zuwa gaɓar Urdun. Iyakarsu ta arewa ta fara ne daga Tekun Gishiri a bakin Urdun, wajen Bet-Hogla ta wuce har zuwa arewancin Bet-Araba, zuwa Dutsen Bohan ɗan Ruben. Sai iyakar ta haura zuwa Debir daga Kwarin Akor ta juya arewa da Gilgal, wadda take fuskantar hawan Adummim a kudancin kwari, ta ci gaba zuwa ruwan En Shemesh, ta ɓullo ta En Rogel. Sai kuma ta gangara zuwa Kwarin Ben Hinnom a gangaren kudancin birnin Yebusiyawa (wato, Urushalima). Daga can ta haura zuwa kan tudun a yammancin Kwarin Hinnom, a arewancin ƙarshen Kwarin Refayim. Daga kan tudun, iyakar ta nufi maɓulɓular ruwa na Neftowa, ta ɓullo a garuruwan da suke a Dutsen Efron, ta gangara zuwa Ba’ala (wato, Kiriyat Yeyarim). Sa’an nan ta karkata yamma daga Ba’ala zuwa Dutsen Seyir, ta wuce ta gangaren Dutsen Yeyarim (wato, Kesalon), ta ci gaba zuwa Bet-Shemesh, ta bi zuwa Timna. Ta wuce zuwa gangaren arewancin Ekron, ta juya zuwa Shikkeron, ta wuce zuwa Dutsen Ba’ala, ta kai Yabneyel, iyakarta ta ƙare a teku. Bakin Bahar Rum nan ne iyakar yammanci. Wannan ita ce iyakar da ta kewaye jama’ar Yahuda bisa ga iyalansu. Yoshuwa ya ba Kaleb ɗan Yefunne wuri a Yahuda, Kiriyat Arba, wato, Hebron, bisa ga umarnin Ubangiji. (Arba shi ne mahaifin Anak.) Daga can sai Kaleb ya kori ’ya’yan Anak, maza su uku daga Hebron, wato, Sheshai, Ahiman da Talmai. Daga can ya nufi Debir ya yi yaƙi da mutanen da suke zama a can (Dā sunan Debir, Kiriyat Sefer ne). Kaleb ya ce, “Zan ba da ’yata Aksa aure ga wanda zai ci Kiriyat Sefer da yaƙi.” Otniyel ɗan Kenaz, ɗan’uwan Kaleb, ya ci Kiriyat Sefer da yaƙi; saboda haka Kaleb ya ba wa Aksa ’yarsa, ya kuwa aure ta. Wata rana da ta zo wurin Otniyel, sai ya zuga ta ta roƙi mahaifinta fili. Da ta sauka daga kan jakinta sai Kaleb ya tambaye ta ya ce, “Me kike so in yi miki?” Ta amsa ta ce, “Ka yi mini alheri na musamman, tun da ka ba ni wuri a Negeb, ina roƙonka, ka ba ni maɓulɓulan ruwa.” Kaleb kuwa ya ba ta maɓulɓulan ruwa na tuddai da na kwari. Wannan shi ne gādon kabilar Yahuda bisa ga iyalansu. Garuruwan kabilar Yahuda da suke kudu cikin Negeb zuwa iyakar Edom su ne. Kabzeyel, Eder, Yagur, Kina, Dimona, Adada, Kedesh, Hazor, Itnan, Zif, Telem, Beyalot, Hazor-Hadatta, Keriyot Hezron (wato, Hazor), Amam, Shema, Molada, Hazar Gadda, Heshmon, Bet-Felet, Hazar Shuwal, Beyersheba, Biziyotiya, Ba’ala, Iyim, Ezem, Eltolad, Kesil, Horma, Ziklag, Madmanna, Sansanna, Lebayot, Shilhim, Ayin, Rimmon, jimillarsu, garuruwa da ƙauyukansu duka ashirin da tara ne. Biranen da suke a filayen kwari su ne, Eshtawol, Zora; Ashna, Zanowa, En Gannim, Taffuwa, Enam, Yarmut, Adullam, Soko, Azeka, Sha’arayim, Aditayim, Gedera (Gederotayim ke nan). Garuruwa goma sha huɗu ke nan da ƙauyukansu. Zenan, Hadasha, Migdal Gad, Dileyan, Mizfa, Yokteyel, Lakish, Bozkat, Eglon, Kabbon, Lahman, Kitlish, Gederot, Bet-Dagon, Na’ama, Makkeda, garuruwa goma sha shida ke nan da ƙauyukansu. Libna, Eter, Ashan, Yefta, Ashna, Nezib, Keyila, Akzib, Maresha, garuruwa tara ke nan da ƙauyukansu. Ekron da ƙauyukan da suke kewaye da ita; yammancin Ekron da dukan garuruwa da ƙauyukan da suke kusa da Ashdod. Ashdod da garuruwa da kuma ƙauyukan da suke kewaye da ita, Gaza da garuruwanta da ƙauyukanta har zuwa Rafin Masar da kuma Bahar Rum. Birane na cikin ƙasar tuddai kuwa, su ne, Shamir, Yattir, Soko, Danna, Kiriyat Sanna (wato, Debir), Anab, Eshtemo, Anim, Goshen, Holon, Gilo, garuruwa goma sha ɗaya ke nan da ƙauyukansu. Arab, Duma, Eshan, Yanum, Bet-Taffuwa, Afeka, Humta, Kiriyat Arba (wato, Hebron) da Ziyor, garuruwa tara ke nan da ƙauyukansu. Mawon, Karmel, Zif, Yutta Yezireyel, Yokdeyam, Zanowa, Kayin, Gibeya, Timna, garuruwa goma ke nan da ƙauyukansu. Halhul, Bet-Zur, Gedor, Ma’arat, Bet-Anot, Eltekon, garuruwa shida ke nan da ƙauyukansu. Kiriyat Ba’al (wato, Kiriyat Yeyarim) da Rabba, garuruwa biyu ke nan da ƙauyukansu. Biranen da suke a jeji kuwa su ne, Bet-Araba, Middin, Sekaka, Nibshan, Birnin gishiri da En Gedi, garuruwa shida ke nan da ƙauyukansu. Kabilar Yahuda kuwa ba su iya korar Yebusiyawa waɗanda suke zama cikin Urushalima ba; har wa yau Yebusiyawa suna nan zaune tare da mutanen Yahuda. Rabon da aka ba wa Yusuf ya fara tun daga Urdun kusa da Yeriko, gabas da ruwan Yeriko, sai ya miƙe zuwa jeji, ya haura har zuwa cikin ƙasar tudu na Betel. Ya ci gaba daga Betel (wato, Luz), ya zarce zuwa sashen Arkitawa na Atarot, ya sauka zuwa yammancin bakin iyakar Yalfetiyawa har zuwa yankin Bet-Horon wanda yake cikin kwari. Ya zarce kuma zuwa Gezer, ya gangara ya yi ƙarshe a Bahar Rum. Wannan ne yankin da aka ba wa Manasse da Efraim zuriyar Yusuf gādonsu. Yankin Efraim ke nan bisa ga iyalansu. Iyakar ƙasarsu ta gādo ta kama daga Atarot Addar a gabas zuwa Bet-Horon, ta wuce zuwa Bahar Rum. Daga Mikmetat a arewa kuwa iyakar ta karkata gabas zuwa Ta’anat Shilo, ta wuce zuwa Yanowa a gabas. Sai ta gangara daga Yanowa zuwa Atarot da Na’ara, ta bi ta Yeriko, ta kuma fito ta Urdun. Daga Taffuwa kuma iyakar ta bi yamma zuwa kwazazzaban Kana, ta ƙarasa a Bahar Rum. Wannan shi ne gādon mutanen Efraim bisa ga iyalansu. Gādon ya kuma haɗa da dukan garuruwa da ƙauyuka waɗanda aka keɓe wa mutanen Efraim daga cikin gādon mutanen Manasse. Ba su kori Kan’aniyawan da suke zama a Gezer ba, don haka Kan’aniyawa suna zama tare da mutanen Efraim har wa yau; amma Kan’aniyawa suka zama masu yin aikin dole. Wannan shi ne gādon da aka ba wa kabilar Manasse, a matsayin ɗan farin Yusuf. Manasse yana da ɗan farin mai suna Makir. Makir shi ne mahaifin mutanen Gileyad, aka ba shi Gileyad da Bashan gama Makiriyawa jarumai ne ƙwarai. Aka kuma raba wa sauran mutanen kabilar Manasse rabon gādonsu bisa ga iyalansu, wato, Abiyezer, Helek, Asriyel, Shekem, Hefer da Shemida. Waɗannan su ne ’ya’yan Manasse, maza, ɗan Yusuf bisa ga iyalansu. Zelofehad kuwa ɗan Hefer, ɗan Gileyad, ɗan Makir, ɗan Manasse ba shi da ’ya’ya maza, sai dai mata. Ga sunayensu, Mala, Nowa, Hogla, Milka da Tirza. Suka je wurin Eleyazar firist, da Yoshuwa ɗan Nun, da kuma shugabannin, suka ce musu, “ Ubangiji ya umarci Musa cewa yă ba mu gādonmu tare da ’yan’uwanmu maza.” Saboda haka Yoshuwa ya ba su gādo tare da ’yan’uwan mahaifinsu maza bisa ga umarnin Ubangiji. Dalilin ke nan Manasse ya sami kashi goma ban da ƙasar Gileyad da Bashan a gabashin Urdun, domin ’ya’ya mata na kabilar Manasse sun sami gādo tare da ’ya’ya maza. Aka ba wa sauran mutanen kabilar Manasse ƙasar Gileyad. Iyakar ƙasar Manasse ta tashi daga Asher zuwa Mikmetat a gabashin Shekem. Iyakar kuma ta miƙe har zuwa kudu wadda ta ƙunshi mutanen da suke zaune a En Taffuwa. (Manasse ne yake da ƙasar Taffuwa, amma garin Taffuwa kansa, a kan iyakar Manasse ta mutanen Efraim ce.) Sa’an nan iyakar ta ci gaba ta yi kudu zuwa Rafin Kana. Akwai garuruwan da suke kudancin rafin, waɗanda suke Efraim, ko da yake suna cikin yankin Manasse. Iyakar Manasse ta miƙe zuwa arewa ta bi gefen rafin ta kuma ƙarasa a Bahar Rum. Ƙasar a wajen kudu ta Efraim ce, ta wajen arewa kuma ta Manasse ce. Bahar Rum ita ce iyakarsu. Asher yana wajen arewa, Issakar kuma a wajen gabas. A yanki tsakanin Issakar da Asher, Manasse yana da waɗannan wurare, Bet-Sheyan, Ibileyam da ƙauyukanta, da mazaunan Dor da ƙauyukanta, da mazaunan En Dor da ƙauyukanta, da mazaunan Ta’anak da ƙauyukanta, da mazaunan Megiddo da ƙauyukanta (Na uku cikin jerin shi ne Nafot). Duk da haka mutanen Manasse ba su iya mallakar garuruwan nan ba, domin Kan’aniyawa sun nace da zama a wannan yanki. Da Isra’ilawa suka yi ƙarfi, sai suka sa Kan’aniyawa suka zama masu yin musu aiki, amma ba su iya korarsu duka ba. Mutanen Yusuf kuwa suka ce wa Yoshuwa, “Me ya sa ka ba mu rabon gādo ɗaya kawai? Ga shi muna da yawa kuma Ubangiji ya albarkace mu sosai.” Yoshuwa ya ce musu, “In kuna da yawa sosai, in kuma ƙasar kan tudu ta Efraim ba ta ishe ku ba, sai ku je cikin jeji, ku nema wa kanku ƙasa a ƙasar Ferizziyawa da Refahiyawa.” Mutanen Yusuf suka amsa suka ce, “Ƙasar kan tudu ba ta ishe mu ba, ga kuma Kan’aniyawan da suke zama a filin, da waɗanda suke Bet-Sheyan da ƙauyukanta, da waɗanda suke Kwarin Yezireyel, duk suna da keken yaƙin ƙarfe.” Amma Yoshuwa ya ce wa mutanen Yusuf, wa Efraim da Manasse, “Kuna da yawa, kuna kuma da ƙarfi sosai. Ba wuri ɗaya kaɗai za ku samu gādo ba, amma har da ƙasar kan tudu ma, ko da yake jeji ne, ku je ku gyara shi, duk yă zama naku. Ko da yake Kan’aniyawa suna da kekunan yaƙi na ƙarfe, suna kuma da ƙarfi, duk da haka za ku kore su.” Isra’ilawa duka suka taru a Shilo suka kafa tenti inda za su dinga taruwa. Yanzu ƙasar tana ƙarƙashin mulkinsu, amma akwai sauran kabilu bakwai na Isra’ila waɗanda ba su samu rabon gādonsu ba tukuna. Saboda haka Yoshuwa ya ce wa Isra’ilawa, “Har yaushe za ku yi jinkirin shiga, ku mallaki ƙasar da Ubangiji Allah na iyayenku ya ba ku? Ku ba da mutum uku daga kowace kabila, ni kuwa in aike su, su zagaya dukan ƙasar su rubuta bayani game da ita, bisa ga yadda za a raba ta gādo ga kowace kabila, sa’an nan su dawo wurina. Za ku raba ƙasar kashi bakwai. Mutanen Yahuda za su ci gaba da kasancewa a wurin da suke a kudu, sai kuma mutanen Yusuf a wurin da suke a arewa. Bayan kun auna ƙasar, ku raba ta kashi bakwai, sai ku kawo mini taswirar ƙasar. Ni kuma in yi muku ƙuri’a a gaban Ubangiji Allahnmu. Lawiyawa ba su da rabo a cikinku, domin aikin firistocin da suke yi wa Ubangiji shi ne gādonsu. Gad, Ruben da rabin kabilar Manasse kuwa sun riga sun samu gādonsu a gabashin gefen Urdun, Musa bawan Ubangiji ya ba su.” Da mutanen za su kama hanya su je su zāna yadda ƙasar take, Yoshuwa ya umarce su cewa, “Ku je ku ga yadda ƙasar take. Sa’an nan ku dawo wurina, zan yi muku ƙuri’a a nan Shilo a gaban Ubangiji.” Mutanen kuwa suka tafi suka bi ta cikin ƙasar, suka bayyana yadda take a rubuce, gari-gari, kashi bakwai, suka koma wurin Yoshuwa a Shilo. Sai Yoshuwa ya yi musu ƙuri’a a gaban Ubangiji, a nan ne ya raba wa Isra’ilawa ƙasar bisa ga yadda aka raba su kabila-kabila. Ƙuri’ar kabilar Benyamin bisa ga iyalansu. Rabonsu ya kama daga ƙasar da take tsakanin kabilar Yahuda da ta Yusuf. Daga gefen arewa, iyakarsu ta kama ne daga Urdun, ta wuce arewa a gangaren Yeriko, ta nufi yamma cikin ƙasar kan tudu, ta fito a jejin Bet-Awen. Daga can ta ƙetare zuwa gangaren Luz a kudu (wato, Betel), ta wuce zuwa Atarot Adda a tudun arewa na kwarin Bet-Horon. Daga tudun da yake fuskantar Bet-Horon a kudu, iyakar ta juya kudu ta gefen yamma ta ɓullo a Kiriyat Ba’al (wato, Kiriyat Yeyarim), birnin Yahuda. Wannan ita ce iyakar a wajen yamma. A gefen kudu kuwa, iyakar ta fara daga ƙauyukan Kiriyat Yeyarim wajen yamma sai ta miƙe zuwa maɓuɓɓugar ruwan Neftowa. Iyakar ta gangara zuwa gefen dutsen da yake fuskantar Kwarin Ben Hinnom, wanda yake arewa da Kwarin Refayim. Ta ci gaba ta gangara ta Kwarin Hinnom ta yi kudu kusa da birnin Yebusiyawa har zuwa En Rogel. Sai ta nausa ta yi wajen arewa, zuwa En Shemesh, ta ci gaba zuwa Gelilot, wanda yake fuskantar hawan Adummim. Daga can ta gangara zuwa Dutsen Bohan, ɗan Ruben. Sai ta wuce ta yi arewancin gangaren Bet-Araba, ta wuce har zuwa cikin Araba. Sa’an nan ta wuce zuwa arewancin gangaren Bet-Hogla ta kuma ɓulla a arewancin gaɓar Tekun Gishiri, a bakin Urdun a kudu. Wannan ita ce iyakar a wajen kudu. Urdun shi ne iyaka a wajen gabas. Waɗannan su ne iyakokin yankin ƙasar da iyalan kabilar Benyamin suka gāda. Waɗannan su ne garuruwan da kabilar Benyamin suke da su na gādo. Yeriko, Bet-Hogla, Emek Keziz, Bet-Araba, Zemarayim, Betel, Awwim, Fara, Ofra, Kefar Ammoni, Ofni da Geba, garuruwa goma sha biyu ke nan da ƙauyukansu. Akwai kuma Gibeyon, Rama, Beyerot, Mizfa Kefira, Moza, Rekem, Irfeyel, Tarala, Zela, Hayelef, birnin Yebusiyawa (wato, Urushalima), Gibeya da Kiriyat, garuruwa goma sha huɗu ke nan da ƙauyukansu. Wannan shi ne rabon gādon kabilar Benyamin bisa ga iyalansu. Ƙuri’a ta biyu ta fāɗa a kan kabilar Simeyon, bisa ga iyalansu. Ƙasarsu ta gādo tana cikin yankin Yahuda. Waɗannan su ne wuraren da suka gāda. Beyersheba (ko Sheba), Molada, Hazar Shuwal, Bilha, Ezem, Eltolad, Betul, Horma, Ziklag, Bet-Markabot, Hazar-Susa, Bet-Lebayot da Sharuhen, garuruwa goma sha uku ke nan da ƙauyukansu. Akwai kuma Ayin, Rimmon, Eter da Ashan, garuruwa huɗu ke nan da ƙauyukansu, da kuma dukan ƙauyukan da suke kewaye da garuruwan nan har zuwa Rama na Negeb (wato, Ba’alat-Beyer). Wannan shi ne gādon kabilar Simeyon bisa ga iyalansu. Daga cikin gādon mutanen Yahuda ne aka fitar da gādon kabilar Simeyon, bisa ga iyalansu, domin rabon da kabilar Yahuda suka samu ya fi ƙarfin abin da suke bukata. Saboda haka kabilar gādon Simeyon yana cikin harabar Yahuda. Ƙuri’a ta uku ta fāɗa a kan Zebulun bisa ga iyalansu. Iyakar ƙasarsu ta gādo ta kai har Sarid. Ta nufi yamma zuwa Marala, ta taɓa Dabbeshet, ta wuce zuwa rafin da yake kusa da Yokneyam. Daga Sarid, ta juya gabas zuwa harabar Kislot Tabor, ta kuma wuce zuwa Daberat har zuwa Yafiya. Sa’an nan ta ci gaba, ta yi gabas zuwa Gat-Hefer da Et Kazin; ta ɓulla a Rimmon, ta juya zuwa Neya. A can ne iyakar ta kewaya zuwa Hannaton, sa’an nan ta ƙarasa a Kwarin Ifta El. Zebulun ta ƙunshi garuruwa goma sha biyu da ƙauyukansu. Garuruwan sun haɗa da Kattat, Nahalal, Shimron, Idala da Betlehem. Garuruwan nan da ƙauyukansu su ne gādon da kabilar Zebulun ta samu, bisa ga iyalansu. Ƙuri’a ta huɗu ta fāɗa a kan kabilar Issakar, bisa ga iyalansu. Ƙasarsu gādonsu ta haɗa da, Yezireyel, Kessulot, Shunem, Hafarayim, Anaharat, Rabbat, Kishiyon, Ebez, Remet, En Gannim, En Hadda da Bet-Fazez. Iyakar ta taɓa Tabor Shahazuma da Bet-Shemesh ta kuma ƙarasa a Urdun. Duka-duka garuruwa goma sha shida ke nan da ƙauyukansu. Waɗannan garuruwa da ƙauyukansu su ne rabon da kabilar Issakar ta samu, bisa ga iyalansu. Ƙuri’a ta biyar ta fāɗa a kan kabilar Asher, bisa ga iyalansu. Ƙasarsu gādonsu ta haɗa da, Helkat, Hali, Beten, Akshaf, Allammelek, Amad da Mishal. A arewanci kuma iyakar ta taɓa Karmel da Shihor Libnat. Sai ta yi gabas zuwa Bet-Dagon, ta taɓa Zebulun da kuma Kwarin Ifta El, ta wuce arewa zuwa Bet-Emek da Neyiyel, ta wuce Kabul a hagu, ta kai Abdon, Rehob, Hammon da Kana, har zuwa Sidon Babba. Daga nan iyakar ta juya baya zuwa Rama, ta bi ta birnin nan mai katanga na Taya, ta juya ta nufi Hosa, sa’an nan ta ɓulla ta Bahar Rum cikin yankin Akzib, Umma, Afek da Rehob. Garuruwa ashirin da biyu ke nan da ƙauyukansu. Garuruwan nan da ƙauyukansu su ne gādon da kabilar Asher ta samu bisa ga iyalansu. Ƙuri’a ta shida ta fāɗa a kan kabilar Naftali, bisa ga iyalansu. Iyakarsu ta kama daga Helef, daga babban itacen Mamre nan da yake a Za’anannim, ta wuce Adami Nekeb da Yabneyel zuwa Lakkum, ta kuma ƙarasa a Urdun. Iyakar kuma ta juya yamma ta cikin Aznot-Tabo ta ɓulla a Hukkok. Ta taɓa Zebulun a kudu, Asher a yamma, da kuma Urdun a gabas. Biranen da suke da katanga su ne Ziddim, Zer, Hammat, Rakkat, Kinneret, Adama, Rama, Hazor, Kedesh, Edireyi, En Hazor, Yiron, Migdal El, Horem, Bet-Anat da Bet-Shemesh. Garuruwa goma sha tara ke nan da ƙauyukansu. Waɗannan garuruwa da ƙauyukansu su ne rabon da kabilar Naftali ta samu, bisa ga iyalansu. Ƙuri’a ta bakwai ta fāɗa a kan kabilar Dan, bisa ga iyalansu. Ƙasarsu ta gādo ta haɗa da, Zora, Eshtawol, Ir Shemesh, Shalim, Aiyalon, Itla, Elon, Timna, Ekron, Elteke, Gibbeton, Ba’alat, Yehud, Bene-Berak, Gat-Rimmon, Me Yarkon da Rakkon tare da sashen da yake fuskantar Yaffa. (Amma ya zama wa mutanen kabilar Dan da wahala su mallaki ƙasar da aka ba su gādo, saboda haka sai suka nufi Leshem suka ci su da yaƙi, suka karkashe mutanen wurin, suka mallake ta, suka zauna a ciki. Suka kuma sa wa Leshem, sunan kakansu, wato, Dan.) Waɗannan garuruwa da ƙauyukansu su ne gādon kabilar Dan, bisa ga iyalansu. Sa’ad da aka gama raba gādon ƙasar bisa ga ƙuri’a. Sai Isra’ilawa suka ba Yoshuwa ɗan Nun nasa rabo a cikinsu, yadda Ubangiji ya umarta, suka ba shi garin da ya ce a ba shi, Timnat Serad a ƙasar tudu ta Efraim. Ya kuma gina garin ya zauna a can. Waɗannan su ne rabe-raben gādon da Eleyazar firist, Yoshuwa ɗan Nun, da kuma shugabannin kabilan iyalan Isra’ila suka rarraba ta hanyar jefa ƙuri’a a Shilo a gaban Ubangiji a ƙofar Tentin Sujada. Da haka suka yi suka gama rarraba ƙasar. Sai Ubangiji ya ce wa Yoshuwa, “Ka gaya wa Isra’ilawa su keɓe waɗansu birane su zama biranen mafaka kamar yadda na umarce ku ta wurin Musa, domin idan wani ya kashe wani bisa kuskure ba da niyyar yin kisankai ba, mutumin zai iya gudu zuwa can yă fake don kada a kashe shi. Lokacin da ya gudu zuwa ɗaya daga cikin biranen nan, sai yă tsaya a ƙofar birnin yă gaya wa dattawan wannan birni damuwarsa. Sa’an nan su karɓe shi su ba shi wurin zama a cikin birninsu. In mai neman yă kashe shi don ramako ya bi shi zuwa can, ba za su miƙa shi ba domin ba da niyya ya kashe wani ba, kuma ba fushi ne ya sa ya yi kisan ba. Zai zauna a wannan birni har sai taron jama’a sun yi masa shari’a, kuma har sai lokacin da babban firist wanda yake aiki a lokacin ya mutu, sa’an nan zai iya koma garinsa na dā.” Saboda haka suka keɓe Kedesh a Galili a ƙasar kan tudu ta Naftali, Shekem a ƙasar kan tudu ta Efraim, da Kiriyat Arba (wato, Hebron) a ƙasar kan tudu ta Yahuda. A hayin Urdun, gabas da Yeriko, suka keɓe Bezer ta jeji a kan tudu a cikin yankin kabilar Ruben, Ramot cikin Gileyad a kabilar Gad, da Golan cikin Bashan a kabilar Manasse. In wani mutumin Isra’ila ko kuma wani baƙon da yake zama a cikinsu, ya yi kisankai cikin kuskure, zai iya gudu zuwa biranen da aka keɓe, ba za a bari mai neman ramako yă kashe shi kafin jama’a su yi masa shari’a ba. To, a lokacin, sai shugabannin iyalan Lawiyawa suka je wurin Eleyazar firist, Yoshuwa ɗan Nun da kuma shugabannin sauran iyalan kabilu na Isra’ila a Shilo cikin Kan’ana, suka ce musu, “ Ubangiji ya yi umarni ta wurin Musa cewa a ba mu garuruwan da za mu zauna a ciki, da wurin kiwo mai kyau don dabbobinmu.” Saboda haka kamar yadda Ubangiji ya umarta, sai Isra’ilawa suka ba wa Lawiyawa waɗannan garuruwa da wuraren kiwo daga cikin gādonsu. Ƙuri’a ta farko ta fāɗa a kan Kohatawa bisa ga iyalansu. Sai aka ba wa Lawiyawa waɗanda suke ’yan zuriyar Haruna, firist, garuruwa goma sha uku daga kabilan Yahuda, Simeyon da Benyamin. Sauran Kohatawan kuma aka ba su garuruwa goma daga iyalan kabilar Efraim, Dan da kuma rabi kabilar Manasse. Aka kuma ba wa zuriyar Gershon garuruwa goma sha uku daga iyalan kabilan Issakar, Asher, Naftali, da kuma rabin kabilar Manasse a Bashan. Aka ba wa zuriyar Merari bisa ga iyalansu, garuruwa goma sha biyu daga kabilan Ruben, Gad da Zebulun. Haka Isra’ilawa suka ba wa Lawiyawa waɗannan garuruwa da wuraren kiwo masu kyau, yadda Ubangiji ya umarta ta wurin Musa. Daga kabilan Yahuda da Simeyon ne aka ba su waɗannan garuruwan da aka ambata, (ga garuruwan da aka ba wa zuriyar Haruna waɗanda suke daga iyalan Kohatawa na Lawiyawa, domin ƙuri’a ta farko ta fāɗa a kansu), an ba su, Kiriyat Arba (wato, Hebron), da wurin kiwon da yake kewaye da ƙasar kan tudu ta Yahuda. (Arba shi ne kakan Anak.) Amma sai aka ba Kaleb ɗan Yefunne filayen da kuma ƙauyukan da suke kewaye da birnin, su zama nasa. Sai aka ba zuriyar Haruna firist, ƙasar Hebron (garin masu neman mafaka don sun yi kisa), da Libna, da Yattir, da Eshtemowa, da Holon, da Debir, da Ayin, da Yutta, da kuma Bet-Shemesh, tare da wuraren kiwonsu, garuruwa tara ke nan daga kabilun nan biyu, Yahuda da Simeyon. Daga kabilar Benyamin kuwa aka ba su, Gibeyon, Geba, Anatot da Almon, tare da wuraren kiwonsu, garuruwa huɗu ke nan. Duka-duka garuruwan firistoci, zuriyar Haruna, su goma sha uku ne tare da wuraren kiwonsu. Aka kuma ba wa sauran Kohatawa, iyalan Lawiyawa, garuruwa daga kabilar Efraim. A ƙasar kan tudu ta Efraim, aka ba su, Shekem (garin masu neman mafaka don sun yi kisa) da Gezer, Kibzayim da Bet-Horon, tare da wuraren kiwonsu, garuruwa huɗu ke nan. Haka kuma daga kabilar Dan, aka ba su, Elteke, Gibbeton, Aiyalon da Gat-Rimmon, tare da wuraren kiwonsu, garuruwa huɗu ke nan. Daga rabin kabilar Manasse kuwa aka ba su, Ta’anak da Gat-Rimmon, tare da wuraren kiwonsu, garuruwa biyu ke nan. Dukan garuruwan nan goma tare da wuraren kiwonsu ne aka ba sauran iyalan Kohatawa. Aka ba wa zuriyar Gershon, waɗanda suke Lawiyawa, rabo. Daga rabin kabilar Manasse, Golan a cikin Bashan (garin masu neman mafaka don sun yi kisa), da Be’eshtera, tare da wuraren kiwonsu, garuruwa biyu ke nan; daga kabilar Issakar kuma aka ba su Kishiyon, Daberat, Yarmut da En Gannim, tare da wuraren kiwonsu, garuruwa huɗu ke nan; daga kabilar Asher kuwa aka ba su, Mishal, Abdon, Helkat da Rehob, tare da wuraren kiwonsu, garuruwa huɗu ke nan; daga kabilar Naftali kuma aka ba su, Kedesh a cikin Galili (garin masu neman mafaka don sun yi kisa), Hammon-Dor da kuma Kartan, tare da wuraren kiwonsu, garuruwa uku ke nan. Duka-duka, garuruwan iyalan Gershonawa goma sha uku ne, tare da wuraren kiwonsu. Aka ba wa iyalan Merari (sauran Lawiyawa) garuruwa, daga kabilar Zebulun, wato, Yokneyam, Karta, Dimna da kuma Nahalal, tare da wuraren kiwonsu, garuruwa huɗu ke nan; daga kabilar Ruben kuma aka ba su, Bezer, Yahza, Kedemot da kuma Mefa’at, tare da wuraren kiwonsu, garuruwa huɗu ke nan; daga kabilar Gad kuwa aka ba su, Ramot Gileyad (garin masu neman mafaka don sun yi kisa), Mahanayim, Heshbon da kuma Yazer, tare da wuraren kiwonsu, garuruwa huɗu ke nan. Duka-duka garuruwan da aka ba iyalan mutanen Merari, waɗanda su ne sauran Lawiyawa, garuruwa goma sha biyu ne. Jimillar birane da wurarensu na kiwon da aka ba Lawiyawa daga cikin mallakar jama’ar Isra’ila guda arba’in da takwas ne. Dukan garuruwan nan kowannensu yana kewaye da wurin kiwo. Ubangiji kuwa ya ba Isra’ilawa dukan ƙasar da ya yi wa kakanninsu alkawari, suka kuwa mallake ta, suka zauna a cikinta. Ubangiji ya ba su hutawa a kowane gefe kamar yadda ya yi wa kakanninsu alkawari, ba ko ɗaya daga cikin abokan gābansu da ya iya cinsu da yaƙi. Ubangiji kuwa ya cika kowane alkawarin alherin da ya yi wa mutanen Isra’ila. Yoshuwa ya kira mutanen Ruben, mutanen Gad, da rabin kabilar Manasse ya ce musu, “Kun yi duk abin da Musa bawan Ubangiji ya umarta, kun kuma yi mini biyayya cikin dukan umarnan da na ba ku. Dukan waɗannan yawan kwanaki, har zuwa yau, ba ku yashe ’yan’uwanku Isra’ilawa ba, amma kuka kiyaye umarnin da Ubangiji Allahnku ya ba ku. Yanzu da Ubangiji Allahnku ya ba ’yan’uwanku hutu kamar yadda ya yi alkawari, sai ku koma gidajenku a ƙasar da Musa bawan Ubangiji ya ba ku a Urdun. Amma ku yi hankali, ku kiyaye umarnai da kuma dokokin da Musa bawan Ubangiji ya ba ku. Ku ƙaunaci Ubangiji Allahnku, ku yi tafiya kan hanyarsa, ku yi biyayya da umarnansa, ku riƙe shi sosai, ku bauta masa da dukan zuciyarku da kuma dukan ranku.” Sai Yoshuwa ya sa musu albarka, ya sallame su, suka kuwa tafi gidajensu. (Musa ya riga ya ba rabin kabilar Manasse gādo a Bashan; sauran rabin kabilar kuma Yoshuwa ya ba su gādo tare ’yan’uwansu a yammacin hayin Urdun.) Sa’ad da Yoshuwa ya sallame su su tafi gida, ya sa musu albarka, ya ce, “Ku koma gidajenku tare da dukiya mai yawa, babban garken dabbobi, azurfa da zinariya, tagulla da ƙarfe, da tufafi masu yawa sosai, sai ku raba ganimar da kuka samu daga abokan gābanku, da ’yan’uwanku.” Saboda haka sai mutanen Ruben, mutanen Gad da kuma rabin mutanen kabilar Manasse, suka bar Isra’ilawa a Shilo cikin Kan’ana don su koma Gileyad, ƙasarsu, wadda suka samu bisa ga umarnin Ubangiji ta wurin Musa. Da suka kai Gelilot kusa da Urdun cikin ƙasar Kan’ana, sai mutanen Ruben, mutanen Gad da kuma rabin mutanen kabilar Manasse suka gina bagade a can, a Urdun. Sa’ad da Isra’ilawa suka ji cewa sun gina bagade a iyakar Kan’ana, a Gelilot kusa da Urdun wajen gefensu na Isra’ilawa, sai dukan Isra’ilawa suka taru a Shilo don su je su yaƙe su. Saboda haka sai Isra’ilawa suka aiki Finehas ɗan Eleyazar, firist, zuwa ƙasar Gileyad, wurin mutanen Ruben, mutanen Gad da kuma rabin mutanen kabilar Manasse. Suka aiki shugabanni guda goma su tafi tare da shi, ɗaya daga kowace kabilar Isra’ila, kowannensu shugaba ne a iyalansa. Sa’ad da suka je Gileyad, wurin mutanen Ruben, mutanen Gad da kuma rabin mutanen kabilar Manasse, sai suka ce musu, “Dukan jama’ar Ubangiji sun ce yaya za ku juya wa Allah na Isra’ila baya haka? Yaya za ku daina bin Ubangiji ku gina wa kanku bagade, ku yi masa tawaye yanzu? Zunubin da Feyor ya yi bai ishe mu ba ne? Ga shi, har yanzu ba mu gama tsarkakewa daga wannan zunubi ba, ko da yake annoba ta auko wa mutanen Ubangiji! Yanzu za ku daina bin Ubangiji ne? “In kuka yi wa Ubangiji tawaye yau, gobe zai yi fushi da dukan mutanen Isra’ila. Idan ƙasar mallakarku ƙazantacciya ce, sai ku haye zuwa ƙasar Ubangiji, inda tabanakul yake, mu zauna tare. Amma kada ku yi wa Ubangiji, ko kuma ku yi mana tawaye ta wurin gina wa kanku bagade wanda ba na Ubangiji Allahnmu ba. Lokacin da Akan ɗan Zera ya yi rashin aminci game da kayan da aka keɓe, fushinsa Ubangiji bai auko a kan mutanen Isra’ila duka ba? Ai, ba shi kaɗai ya mutu don zunubinsa ba.” Sai mutanen Ruben, mutanen Gad da kuma rabin mutanen kabilar Manasse suka amsa wa shugabannin iyalan Isra’ila suka ce, “Maɗaukaki, Allah, Ubangiji! Maɗaukaki, Allah, Ubangiji ya sani! In mun yi wannan cikin tawaye ko rashin biyayya ga Ubangiji ne, kada ku bar mu da rai yau. Idan mun bar bin Ubangiji, muka gina wa kanmu bagade don mu miƙa hadayun ƙonawa, ko kuwa hadayun gari, ko kuwa hadayun salama, to, bari Ubangiji kansa ya sāka mana. “A’a! Mun yi haka ne don tsoro, kada nan gaba ’ya’yanku su ce wa ’ya’yanmu, ‘Me ya haɗa ku da Ubangiji, Allah na Isra’ila? Ubangiji ya sa Urdun ya zama iyaka tsakaninmu da ku, ku mutanen Ruben da mutanen Gad! Ba ku da rabo cikin Ubangiji.’ ’Ya’yanku za su iya sa ’ya’yanmu su daina tsoron Ubangiji. “Shi ya sa muka ce, ‘Bari mu yi shiri mu gina bagade, amma ba na ƙona hadayu ko na sadaka ba.’ Sai dai yă zama shaida tsakaninmu da ku, da kuma waɗanda za su zo a baya, cewa za mu yi wa Ubangiji sujada a wurinsa mai tsarki, za mu miƙa hadayunmu na ƙonawa, hadayu na zumunta. Sa’an nan, nan gaba ’ya’yanku ba za su ce wa ’ya’yanmu, ‘Ba ku da rabo a cikin Ubangiji ba.’ “Muka kuma ce, ‘In har suka ce mana, ko ’ya’yanmu haka, sai mu amsa mu ce ku dubi bagaden da yake daidai da na Ubangiji wanda iyayenmu suka gina, ba don ƙona hadayu da kuma yin sadaka ba, sai dai don yă zama shaida tsakaninmu da ku.’ “Allah ya sawwaƙa mana mu tayar wa Ubangiji mu bar binsa, har mu gina bagade don miƙa hadayu na ƙonawa, da na gari, da na sadaka, ban da bagaden Ubangiji Allahnmu wanda yake tsaye a gaban tabanakul.” Da Finehas firist, da shugabannin mutanen, shugabannin iyalan Isra’ila, suka ji abin da mutanen Ruben, mutanen Gad da kuma rabin mutanen kabilar Manasse suka ce, sai suka ji daɗi. Sai Finehas ɗan Eleyazar, firist, ya ce wa mutanen Ruben, mutanen Gad da kuma rabin mutanen kabilar Manasse, “Yau mun san Ubangiji yana tare da mu, domin ba ku yi wa Ubangiji rashin aminci cikin wannan abu ba. Yanzu kun kuɓutar da Isra’ilawa daga hannun Ubangiji.” Sai Finehas ɗan Eleyazar, firist, da shugabannin suka koma Kan’ana daga saduwa da mutanen Ruben da mutanen Gad a Gileyad, suka kai wa Isra’ilawa rahoto. Isra’ilawa suka ji daɗin rahoton da suka ji, suka kuma yi wa Allah yabo. Ba su sāke yin maganar zuwa yaƙi don su rushe ƙasar da mutanen Ruben da mutanen Gad suke ciki ba. Sai mutanen Ruben da mutanen Gad suka ba wa wannan bagaden sunan, Shaida Tsakaninmu, cewa Ubangiji Allah ne. An daɗe bayan da Ubangiji ya ba Isra’ilawa hutu daga dukan abokan gāban da suke kewaye da su. Yoshuwa kuwa ya tsufa, shekarunsa sun yi yawa, sai ya aika a kira Isra’ilawa duka, dattawansu, shugabanninsu, alƙalansu, da manyan ma’aikatansu, ya ce musu, “Na tsufa, shekaruna kuwa sun yi yawa, ku kanku kun ga dukan abubuwan da Ubangiji Allahnku ya yi da idanunku wa dukan ƙasashen nan, Ubangiji Allahnku shi ne wanda ya yi yaƙi dominku. Ku tuna yadda na rarraba wa kabilanku ƙasashen nan su zama naku na gādo, dukan ƙasashen da suka rage, ƙasashen da na ci da yaƙi, tsakanin Urdun da Bahar Rum a yamma. Ubangiji Allahnku kansa zai kore su a madadinku. Zai fafare su a gabanku, za ku kuwa mallaki ƙasarsu, yadda Ubangiji Allah ya yi muku alkawari. “Ku yi ƙarfin hali, ku yi hankali, ku yi biyayya da dukan abin da aka rubuta a cikin Littafin Dokoki na Musa, ba tare da kun juya hagu ko dama ba. Kada ku haɗa kai da mutanen nan da suke zama cikinku; ba ruwanku da sunayen allolinsu, kada ku rantse da su. Kada kuwa ku bauta musu ko kuwa ku rusuna musu. Sai dai ku riƙe Ubangiji Allahnku da kyau, yadda kuka yi har zuwa yanzu. “ Ubangiji ya kori manyan ƙasashe masu ƙarfi; har wa yau ba wanda ya iya cin ku da yaƙi. Mutum ɗaya a cikinku ya isa yă sa mutane dubu nasu su gudu, domin Ubangiji Allahnku yana yaƙi dominku, kamar yadda ya yi alkawari. Saboda haka sai ku kula da kanku sosai, ku ƙaunaci Ubangiji Allahnku. “Amma in kuka juya baya kuka zama abokai ga waɗanda suka ragu suke zama a cikinku a ƙasashen nan, har kuka yi auratayya da su, kuka haɗa kai da su, ku tabbata cewa Ubangiji Allahnku ba zai kore muku mutanen ƙasashen nan ba, sai ma su zama muku dutsen tuntuɓe da tarko, za su zama bulala a bayanku, ƙayayyuwa a idanunku, har sai kun hallaka daga wannan ƙasa mai kyau wadda Ubangiji Allahnku ya ba ku. “Yanzu na kusa barin fuskar duniyan nan. Kun sani da dukan zuciyarku, da dukan ranku cewa, Ba ko ɗaya daga cikin alkawuran da Ubangiji Allahnku ya yi, da bai cika ba. Kowane alkawari ya cika; ba ko ɗaya da bai cika ba. Kamar yadda Ubangiji Allahnku kuwa ya cika kowane alkawari mai kyau, haka ma ba zai fasa kawo muku bala’in da ya faɗi ba, sai ya hallaka ku daga wannan ƙasa mai kyau da ya ba ku. In kuka karya alkawarin Ubangiji Allahnku wanda ya umarce ku, in kuka je kuka bauta wa waɗansu alloli, kuka rusuna musu, fushin Ubangiji zai sauko a kanku, za ku kuwa hallaka da sauri daga ƙasan nan mai kyau da ya ba ku.” Yoshuwa ya tattara dukan kabilan Isra’ila a Shekem. Ya aika a kira dattawa, shugabanni, alƙalai da manyan ma’aikatan Isra’ila, suka kai kansu gaban Allah. Yoshuwa ya ce wa dukan mutanen, “Ga abin da Ubangiji, Allah na Isra’ila ya ce, ‘Dā can, kakanninku, Tera mahaifin Ibrahim, da Nahor sun zauna a hayin Kogin Yuferites suka yi wa waɗansu alloli sujada. Amma na ɗauki mahaifinku Ibrahim, daga ƙasar da take can a hayin Kogin Yuferites, na kawo shi ƙasar Kan’ana, na kuma ba shi ’ya’ya masu yawa. Na ba shi Ishaku, ga Ishaku kuwa na ba shi Yaƙub da Isuwa. Na ba Isuwa ƙasar kan tudu ta Seyir, amma Yaƙub da ’ya’yansa maza suka gangara zuwa Masar. “ ‘Sai na aiki Musa da Haruna, na aukar wa Masarawa annobai, ta wurin abin da na yi ne na fitar da ku. Lokacin da na fitar da iyayenku daga Masar, suka zo teku, sai Masarawa suka fafare su da kekunan yaƙi da dawakai har zuwa Jan Teku. Amma suka yi kuka ga Ubangiji don taimako, ya kuwa sa duhu ya raba tsakaninsu da Masarawa; ya sa teku ya rufe Masarawa. Kun gani da idanunku abin da na yi wa Masarawa, sa’an nan kuka zauna a jeji na tsawon lokaci. “ ‘Na kawo ku ƙasar Amoriyawa waɗanda suke gabas da Urdun. Suka yi yaƙi da ku, amma na ba da su a hannunku, na hallaka su a gabanku, kuka kuma mallaki ƙasarsu. Lokacin da Balak ɗan Ziffor, sarkin Mowab, ya yi shiri yă yaƙi Isra’ila, ya aiki Bala’am ɗan Beyor don yă la’anta ku. Amma ban saurari Bala’am ba, saboda haka sai ya ma sa muku albarka, na kuɓutar da ku daga hannunsa. “ ‘Sai kuka ƙetare Urdun kuka isa Yeriko. Mutanen Yeriko suka yi faɗa da ku, kamar yadda Amoriyawa, Ferizziyawa, Kan’aniyawa, Hittiyawa, Girgashiyawa, Hiwiyawa, da Yebusiyawa suka yi, amma na ba da su a hannunku. Na aika rina ta kore su a idonku, haka kuma sarakunan Amoriyawan nan. Ba da takobinku ko bakanku ne kuka yi haka ba. Na ba ku ƙasar da ba ku yi wata wahala kafin ku samu ba, na ba ku kuma biranen da ba ku gina ba; kuka kuma zauna a cikinsu, kuka ci daga ’ya’yan itacensu da ’ya’yan zaitun da ba ku ne kuka shuka ba.’ “Yanzu, sai ku ji tsoron Ubangiji, ku bauta masa da dukan aminci. Ku zubar da allolin da kakanninku suka yi musu sujada a hayin Kogin Yuferites da kuma a Masar, ku bauta wa Ubangiji. Amma in kuka ga ba za ku iya bauta wa Ubangiji ba, sai ku zaɓa yau wanda za ku bauta masa, ko allolin da kakanninku suka bauta musu a hayin Kogin Yuferites, ko kuma allolin Amoriyawa, waɗanda kuke zama a cikin ƙasarsu. Amma da ni da gidana, Ubangiji ne za mu bauta wa.” Sai mutanen suka amsa suka ce, “Allah ya kiyashe mu da rabuwa da Ubangiji Allahnmu, har a ce mu bauta wa waɗansu alloli! Ubangiji Allahnmu ne da kansa ya fitar da iyayenmu daga Masar, daga ƙasar bauta, ya yi manyan abubuwan al’ajabi, a idanunmu. Ya kiyaye mu cikin dukan hanyar da muka bi, da cikin ƙasashen da muka ratsa; Ubangiji kuwa ya kore mana dukan Amoriyawa, waɗanda suke zaune a ƙasar. Don haka mu ma za mu bauta wa Ubangiji, gama shi ne Allahnmu.” Yoshuwa ya ce wa mutanen, “Ba za ku iya bauta wa Ubangiji ba gama shi Allah mai tsarki ne; mai kishi kuma. Ba zai gafarta muku zunubin tawaye ba. In kuka juya wa Ubangiji baya, kuka bauta wa waɗansu alloli, zai juya yă kawo muku bala’i, yă hallaka ku, yă kawo ƙarshenku.” Amma mutanen suka ce wa Yoshuwa, “Mu dai! Za mu bauta wa Ubangiji.” Yoshuwa kuwa ya ce musu, “Ku ne shaidun kanku cewa kun zaɓi ku bauta wa Ubangiji.” Suka amsa suka ce, “I, mu ne shaidun kanmu.” Yoshuwa ya ce musu, “Yanzu sai ku zubar da allolin da suke cikinku, ku miƙa wa Ubangiji, Allah na Isra’ila zuciyarku.” Mutanen kuma suka ce, “Za mu bauta wa Ubangiji Allahnmu, mu kuma yi masa biyayya.” A wannan rana Yoshuwa ya yi alkawari saboda mutanen, kuma a can Shekem ya tsara musu ƙa’idodi da dokoki. Yoshuwa kuwa ya rubuta abubuwan nan a cikin Littafin Dokoki na Allah. Sa’an nan ya ɗauki babban dutse ya ajiye a ƙarƙashin itacen oak kusa da tsattsarkan wuri na Ubangiji. Ya ce wa duka mutanen, “Ku gani! Wannan dutse zai zama mana shaida, ya ji duk maganar da Ubangiji ya yi mana, zai zama muku shaida in ba ku yi wa Allahnku gaskiya ba.” Sai Yoshuwa ya sallami mutane, kowa ya tafi ƙasar da aka ba shi gādo. Bayan waɗannan abubuwa, Yoshuwa ɗan Nun, bawan Ubangiji, ya mutu yana da shekaru ɗari da goma. Suka kuma binne shi a ƙasarsa ta gādo, a Timnat Sera a ƙasar kan tudu ta Efraim, arewa da Dutsen Ga’ash. Isra’ilawa kuwa sun bauta wa Ubangiji dukan kwanakin Yoshuwa, da kuma kwanakin dattawan da ya bari, da waɗanda suka ga duk abin da Ubangiji ya yi wa Isra’ila. Aka kuma binne ƙasusuwan Yusuf da aka kawo daga Masar, a Shekem a wurin da Yaƙub ya saya da azurfa ɗari daga ’ya’yan Hamor, babban Shekem. Wurin ya zama gādon zuriyar Yusuf. Eleyazar ɗan Haruna, ya mutu aka binne shi a Gibeya, wurin da aka ba ɗansa Finehas a ƙasar kan tudu ta Efraim. Bayan da Yoshuwa ya rasu, Isra’ilawa suka tambayi Ubangiji suka ce, “Wane ne zai fara tafiya don yă yaƙi Kan’aniyawa dominmu?” Sai Ubangiji ya ce, “Yahuda zai tafi. Na riga na ba da ƙasar a hannunsu.” Sa’an nan mutane Yahuda suka ce wa mutanen Simeyon “Ku zo tare da mu a yankin da aka ba mu rabon mu don mu yaƙi Kan’aniyawa. Mu ma mu bi ku wurin naku.” Saboda haka mutanen Simeyon suka tafi tare da su. Sa’ad da Yahuda ya fāɗa musu, Ubangiji kuwa ya ba da Kan’aniyawa da Ferizziyawa a hannunsu, suka kuwa kashe mutum dubu goma a Bezek. A can suka iske Adoni-Bezek, suka yaƙe shi, suka fatattaki Kan’aniyawa da Ferizziyawa. Sai Adoni-Bezek ya gudu, amma suka bi shi suka kama shi, suka yayyanka manyan yatsotsinsa na hannu da na ƙafa. Sa’an nan Adoni-Bezek ya ce, “Sarakuna saba’in waɗanda aka yayyanka manyan yatsotsinsu na hannu da na ƙafa, sun yi kalan abinci a ƙarƙashin teburina. Ga shi yanzu Allah ya rama abin da na yi musu.” Suka zo da shi Urushalima, a can kuwa ya mutu. Mutanen Yahuda suka yaƙi Urushalima ita ma suka ci ta. Suka karkashe mutanen birnin suka cinna mata wuta. Bayan wannan, mutanen Yahuda suka gangara suka yaƙi Kan’aniyawan da suke zaune a ƙasar tudu, Negeb, da gindin tuddai a yammanci. Suka ci gaba suka yaƙi Kan’aniyawan da suke zaune a Hebron (wadda dā ake kira Kiriyat Arba) suka kuma ci Sheshai, Ahiman da Talmai da yaƙi. Daga nan kuma suka ci gaba suka yaƙi mutanen da suke zaune a Debir (da ake kira a dā Kiriyat Sefer). Sai Kaleb ya ce, “Duk wanda ya fāɗa wa Kiriyat Sefer ya kuma ci ta da yaƙi, zan ba shi ’yata Aksa yă aura.” Sai Otniyel ɗan Kenaz, ƙanen Kaleb ya ci birnin, saboda haka Kaleb ya ba shi ’yarsa Aksa ya aura. Wata rana da ta zo wurin Otniyel, sai ta zuga shi yă roƙi mahaifinta fili. Sa’ad da ta sauko daga jakinta, sai Kaleb ya ce mata, “Me zan yi miki?” Sai ta ce, “Ka yi mini alheri na musamman. Da yake ka ba ni ƙasa a Negeb, to, sai ka ba ni maɓulɓulan ruwa kuma.” Sai Kaleb ya ba ta maɓulɓulan bisa da kuma na ƙasa. Zuriyar surukin Musa, Keniyawa, suka haura daga Birnin dabino tare da mutanen Yahuda don su zauna cikin mutanen Hamadan Yahuda a cikin Negeb kusa da Arad. Sa’an nan mutanen Yahuda suka tafi tare da ’yan’uwansu mutanen Simeyon suka fāɗa wa Kan’aniyawan da suke zaune cikin Zefat, suka kuwa hallaka birnin gaba ɗaya. Saboda haka aka kira wurin Horma. Mutanen Yahuda kuma suka ci Gaza, Ashkelon, da Ekron, kowace birni tare da yankinsa. Ubangiji kuwa yana tare da mutane Yahuda. Suka mallaki ƙasar tudu, amma ba su iya suka kori mutanen daga filaye ba, domin suna da keken yaƙin ƙarfe. Yadda Musa ya yi alkawari, sai aka ba Kaleb Hebron, wanda ya kori daga cikinta ’ya’ya maza uku na Anak. Ko da yake mutanen Benyamin sun kāsa su kori Yebusiyawa, waɗanda suke zaune a Urushalima; har yă zuwa yau, Yebusiyawa suna zaune a can tare da mutanen Benyamin. To, gidan Yusuf suka auka wa Betel, Ubangiji kuwa yana tare da su. Sa’ad da suka aike mutane don su leƙi asirin Betel (da dā ake kira Luz), ’yan leƙen asirin suka ga wani ya fito daga birnin sai suka ce masa, “Ka nuna mana yadda za mu shiga birnin, mu kuwa za mu yi maka alheri.” Saboda haka ya nuna musu, suka kuwa hallaka birnin, suka bar mutumin da dukan iyalinsa da rai. Sa’an nan ya tafi ƙasar Hittiyawa, inda ya gina birni ya kuma kira shi Luz, haka ake kira birnin har wa yau. Amma Manasse ba su kori mutane Bet-Sheyan ko Ta’anak ko Dor ko Ibileyam ko Megiddo tare da ƙauyukansu ba, gama Kan’aniyawa sun dāge su zauna a wannan ƙasa. Sa’ad da Isra’ila ta yi ƙarfi, sai suka tilasta Kan’aniyawa yin aikin gandu amma ba su kore su gaba ɗaya ba. Haka Efraim ma bai kori Kan’aniyawa da suke zaune a Gezer ba, amma Kan’aniyawa suka ci gaba da zama tare da su. Haka kuma Zebulun bai kori Kan’aniyawa da suke zaune a Kitron da Nahalol, waɗanda suka rage a cikinsu ba; sai dai sun sa su aikin gandu. Haka Asher ma bai kori waɗanda suke zama a Akko ko Sidon ko Ahlab ko Akzib ko Helba ko Afik ko kuma Rehob ba, kuma saboda wannan ne mutanen Asher suke zaune cikin mazaunan ƙasar Kan’aniyawa. Haka kuma Naftali bai kori waɗanda suke zaune a Bet-Shemesh ko Bet-Anat; amma mutanen Naftali su ma suna zama a ciki Kan’aniyawa mazaunan ƙasar, waɗanda suke zaune a Bet-Shemesh da Bet-Anat kuwa suka zama masu yi musu aikin gandu. Amoriyawa suka matsa wa mutanen Dan a ƙasar tudu, ba su yarda musu su gangaro zuwa filaye ba. Su Amoriyawa kuma suka dāge su zauna a Dutsen-Heres, Aiyalon, da Sha’albim. Amma yayinda mutanen Yusuf suka ƙara ƙarfi, sai suka su yin musu aikin gandu. Iyakar Amoriyawa kuwa daga Mashigin Kunama zuwa Sela da kuma zuwa gaba. Mala’ikan Ubangiji ya haura daga Gilgal zuwa Bokim ya ce, “Na hauro da ku daga Masar zuwa ƙasar da na rantse zan ba wa kakanninku. Na ce, ‘Ba zan taɓa tā da yarjejjeniyata da ku ba, ku kuma kada ku shiga wata yarjejjeniya da mazaunan ƙasan nan, sai dai za ku rurrushe bagadansu.’ Duk da haka ba ku yi biyayya mini ba. Me ya sa kuka yi haka? Saboda haka ina gaya muku cewa ba zan kore su a gabanku ba; za su zama muku ƙaya, gumakansu kuma za su zama muku tarko.” Da mala’ikan Ubangiji ya faɗa wa dukan Isra’ilawa waɗannan abubuwa, sai mutane suka yi kuka mai zafi, sai suka sa wa wannan wuri suna, Bokim. A nan suka miƙa hadaya a gaban Ubangiji. Bayan Yoshuwa ya sallami Isra’ilawa, sai suka tafi don su mallaki ƙasar, kowa da nasa gādon. Mutane suka bauta wa Ubangiji duk tsawon kwanakin Yoshuwa da na dattawan da suka rayu bayansa waɗanda suka ga manyan abubuwan da Ubangiji ya yi wa Isra’ila. Yoshuwa ɗan Nun, bawan Ubangiji, ya mutu yana da shekara ɗari da goma. Aka binne shi a ƙasar gādonsa, a Timnat Heres a ƙasar tudu ta Efraim, arewa da Dutsen Ga’ash. Bayan tsaran nan duka suka rasu, sai wata tsara ta taso wadda ba tă san Ubangiji ko abin da ya yi wa Isra’ila ba. Sai Isra’ilawa suka yi mugaye abubuwa a gaban Ubangiji suka kuma bauta Ba’al. Suka yashe Ubangiji Allah na kakanninsu, wanda ya fitar da su daga Masar. Suka bi suka kuma bauta alloli dabam-dabam na mutanen da suke kewaye da su. Suka tsokani Ubangiji ya yi fushi domin sun bar shi suka bauta wa Ba’al da Ashtarot. Cikin fushinsa a kan Isra’ila Ubangiji ya ba da su ga hannun waɗanda suka kawo musu hari suka washe su. Ya sayar da su ga abokan gābansu da suke kewaye da su, waɗanda ba za su iya yin tsayayya da su ba. Duk sa’ad da Isra’ila suka fita yaƙi, Ubangiji yakan yi gāba da su don a ci su a yaƙi, kamar dai yadda ya rantse musu. Suka kuwa shiga wahala ƙwarai. Sa’an nan Ubangiji ya naɗa mahukunta, waɗanda suka cece su daga hannun waɗannan musu hari. Duk da haka ba su saurari mahukuntansu ba amma sai suka shiga ha’inci da waɗansu alloli suka kuma bauta musu. Ba kamar kakanninsu ba, nan da nan suka kauce daga hanyar da kakanninsu suka bi, hanyar biyayya ga umarnan Ubangiji. Duk sa’ad da Ubangiji ya naɗa musu mahukunci, yakan kasance tare da mahukuncin, yă kuma cece su daga hannun abokan gāba, muddin mahukuncin yana a raye; gama Ubangiji yakan ji tausayinsu yayinda suke gunaguni ƙarƙashin waɗanda suka danne su suke kuma gasa musu azaba. Amma sa’ad da mahukuncin ya mutu, mutanen suka koma hanyar da ta fi ta kakanninsu muni, sukan bi waɗansu alloli suna bauta musu. Suka ƙi barin mugun ayyukansu da taurin zuciyarsu. Saboda haka sai Ubangiji ya fusata da Isra’ila ya ce, “Domin wannan al’umma ta tā da yarjejjeniyar da na yi da kakanninsu ba su kuwa saurare ni ba, ba zan ƙara kori wata al’ummar da Yoshuwa ya bari sa’ad da ya rasu ba. Zan yi amfani da su in gwada Isra’ila in ga ko za su bi hanyar Ubangiji su kuma yi tafiya a cikinta kamar yadda kakanninsu suka yi.” Ubangiji ya bar waɗannan al’ummai su kasance; bai kore su nan take ta wurin ba da su a hannun Yoshuwa ba. Waɗannan su ne al’umman da Ubangiji ya bari don yă gwada duk waɗannan Isra’ilawan da ba su san yaƙi a Kan’ana ba (ya yi haka ne domin yă koya wa zuriyar Isra’ilawa waɗanda ba su taɓa yin yaƙi a dā ba), sarakuna biyar na Filistiyawa, dukan Kan’aniyawa, Sidoniyawa, da kuma Hiwiyawan da suke zaune a duwatsun Lebanon daga Dutsen Ba’al-Hermon zuwa Lebo Hamat. An bar su domin su gwada Isra’ilawa a ga ko za su yi biyayya da umarnin Ubangiji, wanda ya ba wa kakanninsu ta wurin Musa. Isra’ilawa suka zauna tare da Kan’aniyawa da Hittiyawa, Amoriyawa, Ferizziyawa, Hiwiyawa da kuma Yebusiyawa. Suka auri ’ya’yansu mata, su ma suka bar ’ya’yansu maza suka auri ’ya’yansu mata, suka kuma yi wa gumakansu sujada. Isra’ilawa suka aikata mugunta a gaban Ubangiji; suka manta da Ubangiji Allahnsu suka kuma bauta wa Ba’al da Ashera. Fushin Ubangiji kuwa ya yi ƙuna a kan Isra’ila har ya sayar da su ga Kushan-Rishatayim sarkin Aram-Naharayim, a wurinsa ne Isra’ilawa suka zama bayi shekara takwas. Amma da suka yi kuka ga Ubangiji, sai ya tad musu da mai ceto, Otniyel ɗan Kenaz, ƙanen Kaleb wanda ya cece su. Ruhun Ubangiji ya sauko masa, domin yă zama mahukuncin Isra’ila yă kuma je yaƙi. Ubangiji ya bayar da Kushan-Rishatayim sarkin Aram a hannun Otniyel, ya kuwa sha ƙarfinsa. Saboda haka ƙasar ta zauna da lafiya shekara arba’in har sai da Otniyel ɗan Kenaz ya rasu. Isra’ilawa suka sāke aikata mugayen ayyuka a gaban Ubangiji, saboda sun aikata wannan mugunta sai Ubangiji ya ba wa Eglon sarkin Mowab ƙarfi a kan Isra’ila. Da ya sami Ammonawa da Amalekawa suka haɗa hannu tare, sai Eglon ya tafi ya auka wa Isra’ila, suka ƙwace Birnin Dabino. Isra’ilawa suka zama bayin Eglon sarkin Mowab shekara goma sha takwas. Isra’ilawa suka sāke yin kuka ga Ubangiji, ya kuwa ba su mai ceto, Ehud, wani bahago, ɗan Gera daga kabilar Benyamin. Isra’ilawa suka aike shi da haraji wurin Eglon sarkin Mowab. To, Ehud ya riga ya ƙera takobi mai kaifi biyu mai tsawo wajen kamu ɗaya da rabi, wanda ya yi ɗamara da shi a cinyarsa ta dama ƙarƙashin rigarsa. Ya kai wa Eglon sarkin Mowab harajin, wanda yake mai ƙiba ne. Bayan Ehud ya ba da harajin, sai ya sallame mutanen da suka ɗauko harajin. A wajen gumaka kusa da Gilgal, shi kansa ya juya ya koma ya ce, “Ranka yă daɗe, ina da saƙo na asiri dominka.” Sarkin ya ce, “Ku ba mu wuri!” Sai dukan fadawansa suka fita. Sai Ehud ya matso yayinda shi kuwa yake zaune shi kaɗai a ɗakin sama mai sanyi a fadansa ya ce, “Ina da saƙo daga wurin Allah dominka.” Sarki ya tashi daga kujerarsa, Ehud ya kai hannun hagunsa, ya zaro takobi daga cinyar ƙafar damansa ya soki sarki a ciki. Har ƙotar ma ta shige ciki, takobin kuma ya fito ta bayansa. Ehud bai zare takobin ba, kitse kuwa ya rufe shi. Sa’an nan Ehud ya fita daga shirayin; ya rufe ƙofar ɗakin saman, ya kuma kulle su. Bayan da ya tafi, bayin sarki suka zo suka tarar duk ƙofofin ɗakin sama suna kulle, suka ce, “Wataƙila yana bayan gari ne a ɗakin ciki.” Suka yi ta jira har suka gaji. Da suka ga dai bai buɗe ƙofar ba, sai suka ɗauki mabuɗi, suka buɗe. Sai ga shugabansu a ƙasa matacce. Yayinda suke fama jira, Ehud ya riga ya yi gaba. Ya bi ta wajen gumaka zuwa Seyira. Da ya iso can, sai ya busa ƙaho a ƙasar tudu ta Efraim, Isra’ilawa kuma suka gangaro tare da shi daga tuddai, shi kuwa yana jagorarsu. Ya umarce su ya ce, “Ku bi ni, gama Ubangiji ya ba Mowab abokin gābanku a hannunku.” Haka suka gangaro tare da shi suna mallaki mashigin Urdun da ta shiga zuwa Mowab, ba su yarda wani ya haye ba. A lokacin sun kashe mutanen Mowab dubu goma, dukansu jarumawa da masu ji da ƙarfi; ba ko ɗaya da ya tsira. A wannan rana aka mai da Mowab bayin Isra’ila, ƙasar kuwa ta sami zaman lafiya shekara takwas. Bayan Ehud, sai Shamgar ɗan Anat, wanda ya karkashe Filistiyawa ɗari shida da sandar korar shanun noma, shi ma ya ceci Isra’ila. Bayan rasuwar Ehud, Isra’ilawa suka sāke aikata mugayen ayyuka a gaban Ubangiji. Saboda haka Ubangiji ya sayar da su ga Yabin sarkin Kan’ana wanda yake mulki a Hazor. Shugaban mayaƙansa shi ne Sisera, wanda yake zaune a Haroshet Haggoyim. Domin Yabin sarkin Kan’ana yana da kekunan yaƙin ƙarfe ɗari tara, ya ji wa Isra’ilawa ƙwarai har shekara ashirin, sai suka yi kuka ga Ubangiji, don taimako. A lokacin Debora annabiya, matar Laffidot ce take bi da Isra’ila. Takan yi zaman shari’a a ƙarƙashin Dabinon Debora tsakanin Rama da Betel, a ƙasar tudu ta Efraim, Isra’ilawa kuwa sukan zo wurinta don tă yi musu shari’a. Sai ta aika a kira mata Barak ɗan Abinowam daga Kedesh a Naftali, ta ce masa, “ Ubangiji, Allah na Isra’ila ya umarce ka, ‘Je ka, ka ɗauki mutane Naftali da na Zebulun dubu goma tare da kai, ka yi jagoransu zuwa Dutse Tabor. Zan jawo Sisera, shugaban mayaƙan Yabin, da keken yaƙinsa da mayaƙansa zuwa Kogin Kishon in ba da su a hannunku.’ ” Barak ya ce, “In kika tafi tare da ni, zan tafi; amma in ba ki zo tare da ni ba, ba zan tafi ba.” Debora ta ce, “To, shi ke nan, zan tafi tare da kai. Amma saboda yadda ka ɗauki wannan batun, darajar ba za tă zama taka ba, gama Ubangiji zai ba da Sisera a hannun mace.” Saboda haka Debora ta tafi tare da Barak zuwa Kedesh, a can Barak ya kira Zebulun da Naftali. Mutum dubu goma suka kuma bi shi, Debora kuma tana tare da shi. To, Heber Bakene ya riga ya bar Keniyawa, zuriyar Hobab, ɗan’uwan matar Musa, ya kafa tentinsa wajen babban itace a Za’anannim kusa da Kedesh. Sa’ad da aka gaya wa Sisera cewa Barak ɗan Abinowam ya haura zuwa dutsen Tabor, sai Sisera ya tattara keken yaƙinsa na ƙarfe ɗari tara wuri ɗaya da dukan mutanen da suke tare da shi daga Haroshet Haggoyim zuwa Kogin Kishon. Sa’an nan Debora ta ce wa Barak, “Je ka! Wannan ita ce ranar da Ubangiji ya ba da Sisera a hannunka. Ba Ubangiji ya riga ya sha gabanka?” Saboda haka Barak ya gangara zuwa Dutsen Tabor, da mutum dubu goma biye da shi. Da matsowar Barak, Ubangiji ya murƙushe Sisera da dukan sarakunansa da mayaƙansa da takobi, Sisera kuwa ya gudu da ƙafa ya bar keken yaƙinsa. Amma Barak ya bi keken yaƙin da mayaƙan har Haroshet Haggoyim. Aka karkashe dukan mayaƙan Sisera ba ko ɗayan da ya tsira. Amma Sisera, ya tsere da ƙafa zuwa tentin Yayel, matar Heber Bakene, domin suna da abokantaka da Yabin sarkin Hazor da kuma kabilar Heber Bakene. Yayel ta fito ta taryi Sisera ta ce masa, “Ranka yă daɗe, ka shigo, ka shigo ciki. Kada ka ji tsoro.” Saboda haka ya shiga cikin tentinta, sai ta rufe shi da bargo. Sai ya ce, “Ina roƙonki, ki ba ni ruwa in sha, ina jin ƙishirwa.” Sai ta buɗe salkar madara, ta ba shi ya sha, sai ta kuma rufe shi. Ya ce mata, “Ki tsaya a ƙofar tenti, in wani ya zo ya tambaye ki, ‘Akwai wani a nan?’ Ki ce masa ‘a’a.’ ” Amma Yayel, matar Heber, ta ɗauki turken tenti da guduma ta tafi wurinsa da sauri sa’ad da yake barci saboda gajiya. Ta kafa masa turken a gindin kunnensa ta haɗa shi da ƙasa, har ya mutu. Sai ga Barak mai bin sawun Sisera, Yayel kuwa ta fito don marabtarsa, ta ce, “Shigo, zan nuna maka mutumin da kake nema.” Saboda haka ya shiga ciki tare da ita, sai ga Sisera kwance da turken a gindin kunnensa, matacce. A ranar Allah ya yi kaca-kaca da Yabin, sarkin Kan’ana a gaban Isra’ila. Isra’ilawa kuwa suka ƙara ƙarfi gāba da Yabin, sarkin Kan’aniyawa, har suka hallaka shi. A wannan rana ce Debora da Barak ɗan Abinowam suka rera wannan waƙa. “Sa’ad da ’ya’yan sarki a Isra’ila suka yi jagora, sa’ad da mutane suka niyya su ba da kansu, suna yabon Ubangiji! “Ya sarakuna, ku ji! Ku saurara, ku masu mulki! Zan yi waƙa ga Ubangiji, zan yi waƙa; zan yi kaɗe-kaɗe ga Ubangiji, Allah na Isra’ila. “Ya Ubangiji, sa’ad da ka bar Seyir, sa’ad da ka yi tafiya daga ƙasar Edom, ƙasa ta girgiza, sammai suka zubo, gizagizai sun zubo da ruwa. Duwatsu suka girgizu a gaban Ubangiji, Wannan na Sinai, a gaban Ubangiji, Allah na Isra’ila. “A zamanin Shamgar ɗan Anat, a zamanin Yayel, an yashe dukan hanyoyi; matafiye suka bi hanyoyin da suka yi kona-kona. Rayuwar ƙauye a Isra’ila ta daina, ta daina sai da ni, Debora, na taso, na taso mahaifiya a Isra’ila. Sa’ad da suka zaɓi sababbin alloli, sai ga yaƙi a ƙofofin birnin, ba a kuwa ga garkuwa ko māshi a cikin mutum dubu arba’in a Isra’ila ba. Zuciyata tana tare da ’ya’yan sarakunan Isra’ila, tare da masu niyyar ba da kansu da yardan rai cikin mutane. Yabo ya tabbata ga Ubangiji! “Ku da kuke hawan fararen jakuna, kuna zama a sirdin barguna, da ku da kuke tafiya a kan hanya, ku kula da muryoyin mawaƙa a wuraren ruwaye. Suna faɗi ayyukan adalcin Ubangiji, ayyukan adalcin mayaƙansa a Isra’ila. “Sa’an nan mutanen Ubangiji suka gangara zuwa ƙofofin birni. ‘Ki farka, ki farka, Debora! Ki farka, ki farka, ki tā da waƙa! Ka farka, ya Barak! Ka ta sa kamammunka gaba, ya ɗan Abinowam.’ “Sa’an nan waɗanda aka bari suka sauko zuwa wajen shugabanni; mutane na Ubangiji suka zo wurina tare da masu ƙarfi. Waɗansu suka zo daga Efraim, waɗanda ainihinsu daga Amalek ne; Benyamin yana tare da mutanen da suka bi ka. Daga Makir, shugabannin sojoji suka gangaro, daga Zebulun waɗanda suke riƙe da sandan komanda suka fito. ’Ya’yan sarautar Issakar suna tare da Debora; I, Issakar yana tare da Barak, yana binsa a guje zuwa kwari. A yankunan Ruben aka kuma bincike zuciya sosai. Don me kuka tsaya a wutar sansani don ku ji makiyaya suna kiran garkuna? A yankunan Ruben aka yi bincike zuciya sosai. Gileyad ya tsaya gaban Urdun. Kai kuma Dan, don me ka ka yi ta zama a wajen jiragen ruwa? Asher ya ci gaba da kasance a bakin teku ya kasance a wuraren zamansa. Mutanen Zebulun sun kasai da rayukansu; haka ma Naftali a bakin dāgā. “Sarakuna suka zo, suka yi yaƙi; sarakunan Kan’ana sun yi yaƙi a Ta’anak a gefen ruwan Megiddo, amma ba su ɗauki azurfa, ko ganima ba. Daga sama taurari suka yi faɗa, daga bakin tekuna suka yi yaƙi da Sisera. Kogin Kishon ya kwashe su, tsohon kogi, kogin Kishon. Ci gaba raina; ka ƙarfafa! Sa’an nan kofatan dawakai suka ƙwaƙula, suna sukuwa, haka dawakansa masu ƙarfi suke tafiya. Mala’ikan Ubangiji ya ce, ‘Ka la’anci Meroz.’ ‘Ka la’anci mutanensa sosai, domin ba su kawo wa Ubangiji taimako ba, su kawo wa Ubangiji taimako a kan masu ƙarfi ba.’ “Mafi albarka a ciki mata ta zama Yayel matar Heber Bakene, mafi albarka na mata masu zama a alfarma. Ya nemi ruwa, ta kuwa ta ba shi madara; a ƙwaryar da ta dace da sarakuna ta kawo masa kindirmo. Hannunta ya ɗauki turken tenti, da hannunta na dama ta ɗauko guduma. Ta bugi Sisera, ta ragargaza kansa, ta ragargaza ta huda kunnensa. A ƙafafunta ya fāɗi, ya fāɗi; a can ya kwanta. A ƙafafunta ya fāɗi, ya fāɗi; a can ya fāɗi, matacce. “Ta taga mahaifiyar Sisera ta leƙa; a bayan madogarar ƙofa ta yi ta ihu, ‘Me ya sa keken yaƙinsa ta daɗe ba tă dawo ba? Me ya sa dawakan keken yaƙinsa ba su dawo da wuri ba?’ Mafi hikima cikin ’yan matanta suka amsa mata, tabbatacce, ta ci gaba ta ce wa kanta, ‘Ba nema suke su raba ganima ba, yarinya guda ko biyu wa kowane mutum, riguna masu launi a matsayin ganima don Sisera, riguna masu ado, riguna masu ado sosai don wuyata, dukan wannan a matsayin ganima?’ “Ta haka bari dukan abokan gābanka su hallaka, ya Ubangiji! Amma bari waɗanda suke ƙaunarka su zama kamar rana sa’ad da ta fito da ƙarfinta.” Sa’an nan ƙasar ta sami zaman lafiya shekara arba’in. Isra’ilawa suka sāke yin mugayen ayyuka a gaban Ubangiji, sai ya ba da su ga Midiyawa shekara bakwai. Da Midiyawa suka matsa musu sosai, sai Isra’ilawa suka yi wa kansu mafakai a rammukan duwatsu, kogona da kuma mafaka. Duk lokacin da Isra’ilawa suka yi shuka sai Midiyawa da Amalekawa da waɗansu mutane daga gabashi sukan kai musu hari. Sukan yi sansani a ƙasar sun lalatar da hatsi har zuwa Gaza kuma ba sa barin wani abu mai rai wa Isra’ila, ko tumaki ko shanu ko jakuna. Sukan zo da dabbobinsu da tentinsu kamar tarin fāri. Yana da wuya a ƙidaya yawan mutanen da kuma raƙumansu; sukan mamaye ƙasar don su lalatar da ita. Midiyawa suka talauce Isra’ilawa ƙwarai, har ya sa suka yi kuka ga Ubangiji don taimako. Sa’ad da Isra’ilawa suka yi kuka ga Ubangiji saboda Midiyawa, sai ya aika musu da annabi, wanda ya ce, “Ga abin da Ubangiji, Allah na Isra’ila ya ce na fitar da ku daga Masar, daga ƙasar bauta. Na ƙwace ku daga ikon Masarawa da kuma daga dukan hannuwan masu danniya. Na kore su a gabanku na kuma ba ku ƙasarsu. Na ce muku, ‘Ni ne Ubangiji Allahnku; kada ku bauta allolin Amoriyawa, waɗanda kuke zama a ƙasarsu.’ Amma ba ku saurare ni ba.” Sai mala’ikan Ubangiji ya zo ya zauna a ƙarƙashin itacen oak a Ofra na Yowash mutumin Abiyezer, inda ɗansa Gideyon yake sussukar alkama a wurin matsin inabi don yă ɓoye daga Midiyawa. Sa’ad da mala’ikan Ubangiji ya bayyana wa Gideyon, sai ya ce masa, “ Ubangiji yana tare da kai, jarumi.” Gideyon ya ce, “Ranka yă daɗe, in Ubangiji yana tare da mu, me ya sa waɗannan abubuwa suka faru da mu? Ina dukan abubuwan al’ajabinsa waɗanda kakanninmu suka gaya mana game su sa’ad da suka ce, ‘Ashe, ba Ubangiji ne ya fitar da mu daga Masar ba?’ Amma yanzu Ubangiji ya rabu da mu ya kuma sa mu hannun Midiyawa.” Sai Ubangiji ya juya wajensa ya ce, “Ka je da ƙarfin da kake da shi ka ceci Isra’ila daga hannun Midiyawa. Ba Ni ne nake aikan ka ba?” Gideyon ya ce, “Amma Ubangiji, yaya zan iya ceci Isra’ila? Kabilata ce marar ƙarfi duka a Manasse, kuma ni ne ƙarami a iyalina.” Ubangiji ya ce, “Zan kasance tare da kai, za ka kuwa fatattake dukan Midiyawa gaba ɗaya.” Gideyon ya ce, “In lalle na sami tagomashi a gabanka, to, ka ba ni wata alamar da ta nuna lalle kai kake magana da ni. Ina roƙonka ka dakata har in komo in kawo maka hadayata in ajiye a gabanka.” Sai Ubangiji ya ce, “Zan jira har ka dawo.” Sai Gideyon ya shiga ciki, ya gyara ’yar akuya ya dafa, da garin efa ya yi burodi marar yisti. Da ya sa naman a kwando, romon kuma a tukunya, sai ya fito da su waje ya miƙa masa su a ƙarƙashin itacen oak. Mala’ikan Allah ya ce masa, “Ka ɗauko naman da burodi marar yisti ka sa su a kan wannan dutse, ka zuba romon a kai.” Gideyon kuwa ya yi haka. Da kan sandan da yake a hannunsa, mala’ikan Ubangiji ya taɓa naman da burodi marar yistin. Sai wuta ta fito daga dutsen ta cinye naman da burodin. Mala’ikan kuwa ya ɓace. Sa’ad da Gideyon ya gane mala’ikan Ubangiji ne, sai ya ce, “Ya Ubangiji Mai Iko Duka! Na ga mala’ikan Ubangiji ido da ido.” Amma Ubangiji ya ce masa, “Salama! Kada ka ji tsoro, ba za ka mutu ba.” Saboda haka Gideyon ya gina wa Ubangiji bagade a can, ya kuma kira shi, Ubangiji Salama ne. Har wa yau bagaden yana a Ofra ta mutanen Abiyezer. A wannan dare Ubangiji ya ce masa, “Ka ɗauki bijimi na biyu daga garken mahaifinka, wannan mai shekara bakwai. Ka rushe bagaden mahaifinka na Ba’al ka sare ginshiƙin Ashera kusa da ita. Sa’an nan ka gina bagade irin da ya dace wa Ubangiji Allahnka a kan wannan tudu. Ka yi amfani da itacen katakon ginshiƙin Ashera da ka sare, ka miƙa bijiman nan biyu hadaya ta ƙonawa.” Saboda haka Gideyon ya ɗebi bayinsa bakwai ya yi yadda Ubangiji ya ce masa. Amma saboda yana tsoron iyalinsa da mutanen gari, ya yi haka da dare a maimako da rana. Da safe sa’ad da mutanen garin suka tashi, sai suka tarar an rushe bagaden Ba’al, tare da ginshiƙin Ashera da yake kusa da shi, duk an sare, bijimi na biyu kuma aka miƙa hadaya a kan sabon bagaden! Sai suka tambayi junansu, “Wa ya yi wannan?” Sa’ad da suka bincika a hankali, sai aka faɗa musu, “Gideyon ɗan Yowash ne ya yi haka.” Mutanen garin suka ce wa Yowash, “Ka kawo mana ɗanka. Dole yă mutu, domin ya rushe bagaden Ba’al, ya sare ginshiƙin Asheran da yake tsaye kusa da shi.” Amma Yowash ya ce wa taron da suka tayar masa, “Za ku yi hamayya domin Ba’al ne? Kuna ƙoƙari ku cece shi ne? Duk wanda ya yi faɗa saboda shi za a kashe shi kafin safe. In lalle Ba’al allah ne, zai kāre kansa sa’ad da wani ya rushe bagadensa.” Saboda haka a ranar suka kira Gideyon, “Yerub-Ba’al,” suna cewa, “Bari Ba’al ya yi hamayya da shi,” domin ya rushe bagaden Ba’al. To, dukan Midiyawa, Amalekawa da sauran mutanen gabashi suka haɗa ƙarfi suka ƙetare Urdun suka kafa sansani a Kwarin Yezireyel. Sa’an nan Ruhun Ubangiji ya sauko wa Gideyon, ya kuma busa ƙaho, ya kira mutanen Abiyezer su bi shi. Ya aika manzanni ko’ina a Manasse, yana kiransu su kintsa, haka ma Asher, Zebulun da Naftali, ta haka su ma suka haura su sadu da su. Gideyon ya cewa Allah, “In za ka ceci Isra’ila ta hannuna yadda ka yi alkawari, to, zan shimfiɗa ulu a masussuka, inda safe akwai raɓa a kan ulun kaɗai, ƙasa kuwa a bushe, to, zan san cewa za ka ceci Isra’ila ta hannuna, yadda ka ce.” Abin da faru ke nan. Gideyon ya tashi da sassafe kashegari, ya matse ulun ya kakkaɓe raɓar, ruwan ya cika ƙwarya. Sa’an nan Gideyon ya ce wa Allah, “Kada ka yi fushi da ni. Bari in ƙara yin wani gwaji kuma da ulun. A wannan lokaci ka sa ulun yă bushe, ƙasar kuma ta rufu da raɓa.” A wannan dare Allah ya yi haka. Ulun ne kaɗai yake a bushe, amma dukan ƙasar ta jiƙe da raɓa. Kashegari da sassafe, Yerub-Ba’al (wato, Gideyon) da dukan mutanensa suka kafa sansani a maɓulɓulan Harod. Sansanin Midiyawa kuma yana arewa da su a kwari kusa da tudu na More. Sai Ubangiji ya ce wa Gideyon, “Mutanen da kake da su sun yi mini yawa da zan ba da Midiyawa a hannunsu. Don kada Isra’ila tă yi mini fahariya cewa ƙarfinta ne ya cece su, ka yi shela ga mutane yanzu cewa, ‘Duk wanda ya yi rawan jiki don tsoro, sai yă juya yă bar Dutsen Gileyad.’ ” Saboda haka mutum dubu ashirin da biyu suka koma, sai mutum dubu goma suka rage. Amma Ubangiji ya ce wa Gideyon, “Har yanzu mutanen sun yi yawa. Ka kai cikin ruwa, in kuma tankaɗe maka su a can. In na ce, ‘Wannan zai tafi da kai,’ to, zai tafi; amma in na ce, ‘Wannan ba zai tafi da kai ba,’ to, ba zai tafi ba.” Saboda haka Gideyon ya kai mutanen cikin ruwa. A can Ubangiji ya ce masa, “Ka ware waɗanda suka tanɗi ruwa kamar kare daga waɗanda suka durƙusa suka sha ruwan.” Mutum ɗari uku sun tanɗi ruwa, dukan sauran kuwa suka durƙusa suka sha ruwan. Sai Ubangiji ya ce wa Gideyon, “Da mutum ɗari uku ɗin nan da suka tanɗi ruwa, zan cece ka in kuma ba da Midiyawa a hannuwanku. Ka bar sauran mutane su tafi kowa zuwa wurinsa.” Saboda haka Gideyon ya mai da sauran Isra’ilawa zuwa tentinsu amma ya riƙe mutum ɗari uku waɗanda suka karɓi guzuri da ƙahonin sauran. To, sansanin Midiyawa yana ƙasa da su a kwarin. A daren nan Ubangiji ya ce wa Gideyon, “Tashi ka tafi sansaninsu domin zan ba da su a hannuwanka. In kana tsoron fāɗa musu, sai ka tafi da bawanka Fura ka kuma saurari abin da suke faɗi. Bayan haka za ka sami ƙarfin hali ka auka musu.” Saboda haka sai ya tafi tare da Fura bawansa zuwa sansanin. Midiyawa, Amalekawa da dukan sauran mutane gabashi suka yi sansani a kwari, kamar fāra. Raƙumansu kuma kamar yashi a bakin teku don sun wuce ƙirge. Gideyon ya iso daidai wani yana faɗa wa wani aboki mafarkinsa, yana cewa, “Na yi mafarki, na ga dunƙule burodin sha’ir ya fāɗo a tsakiyar sansanin Midiyawa. Ya bugi tentin da ƙarfin da ya sa tenti ta kife a ƙasa.” Abokinsa ya ce, “Ai wannan ba wani abu ba ne fiye da takobin Gideyon ɗan Yowash, mutumin Isra’ila. Allah ya ba da Midiyawa da dukan sansani a hannuwansa.” Da Gideyon ya ji mafarkin da fassararsa, sai ya yi wa Allah sujada. Ya koma sansanin Isra’ila ya yi kira da ƙarfi ya ce, “Ku tashi! Ubangiji ya ba da sansanin Midiyawa a hannuwanku.” Ya raba mutum ɗari uku ɗin kashi uku, ya ba kowannensu ƙaho da tulu da acibalbal a ciki. Ya ce musu, “Ku dube ni, ku bi abin da na yi. Sa’ad da na kai sansanin, ku yi daidai abin da na yi. Sa’ad da ni da dukan waɗanda suke tare da ni muka busa ƙahoninmu, to, ko’ina a kewayen sansanin sai ku busa naku ku kuma yi ihu, ku ce, ‘Don Ubangiji da kuma domin Gideyon.’ ” Gideyon da mutum ɗari da suke tare da shi suka kai sansanin da tsakar dare bayan an sauya matsara. Suka busa ƙahoninsu, suka farfashe tulunansu da suke hannuwansu. Ƙungiyoyi uku ɗin nan suka busa ƙahonin, suka fasa tuluna. Suka ɗauki acibalbal a hannuwansu na hagu da ƙahonin busawa a hannuwansu na dama, sai suka yi ihu, “Takobi don Ubangiji da kuma don Gideyon!” Yayinda kowannensu ya tsaya a inda yake kewaye da sansanin, dukan Midiyawa suka fito da gudu, suna kuka yayinda suke gudu. Sa’ad da aka busa ƙahonin nan ɗari uku sai Ubangiji ya sa Midiyawa suka yi ta saran juna. Mayaƙan suka gudu zuwa Bet-Shitta wajen Zerera har zuwa yankin Abel-Mehola kusa da Tabbat. Aka kira dukan Isra’ilawa daga Naftali, Asher da dukan Manasse, suka kuwa fatattaki Midiyawa. Gideyon ya aiki manzanni zuwa dukan ƙasar tudu ta Efraim cewa, “Ku gangaro ku yaƙi Midiyawa ku ƙwace ruwan Urdun gaba da su har zuwa Bet-Bara.” Saboda haka aka kira dukan mutanen Efraim suka ƙwace ruwan Urdun har zuwa Bet-Bara. Suka kuma kama shugabannin biyu na Midiyawa, Oreb da Zeyib suka kashe Oreb a dutsen Oreb, Zeyib kuma a wurin matsin ruwa inabin Zeyib. Suka fatattaki Midiyawa suka kawo kawunan Oreb da Zeba wurin Gideyon, wanda yake kusa da Urdun. To, mutanen Efraim suka ce wa Gideyon, “Me ya sa ka yi mana haka? Me ya sa ba ka kira mu lokacin da ka tafi yaƙi da Midiyawa ba?” Suka zarge shi sosai. Amma ya ce musu, “Me na yi da za a iya kwatanta da abin da kuka yi? Ashe, kalar inabin da Efraim ta yi bai fi dukan girbin inabin da Abiyezer suka yi ba? Allah ya ba da Oreb da Zeyib, shugabannin Midiyawa a hannuwanku. Me na yi da ya fi naku? Da ya faɗi haka sai hankalinsu ya kwanta.” Gideyon da mutanensa ɗari uku, sun gaji, duk da haka suka yi ta fafarar, suka zo Urdun suka haye shi. Ya ce wa mutanen Sukkot, “Ku ba wa mutanena burodi; sun gaji, har yanzu ina fafarar Zeba da Zalmunna, sarakunan Midiyawa.” Amma shugabannin Sukkot suka ce, “Ka kama Zeba da Zalmunna ko ne? Don me za mu ba wa mayaƙanka burodi?” Sai Gideyon ya ce, “Haka ko? To, sa’ad da Ubangiji ya ba da Zeba da Zalmunna a hannuna, zan tsattsaga jikinku da ƙayayyuwan jeji.” Daga nan ya wuce zuwa Fenuwel ya yi irin roƙon nan, amma suka amsa yadda mutanen Sukkot suka yi. Saboda haka sai ya ce wa mutanen Fenuwel, “Sa’ad da na dawo da nasara zan rushe wannan hasumiya.” To, Zeba da Zalmunna suna a Karkor da mayaƙa wajen dubu goma sha biyar, abin da ya rage ke nan na mayaƙan gabashi; mayaƙa masu takobi dubu ɗari da ashirin ne suka mutu. Gideyon ya haura ta hanyar makiyaya, gabas da Noba, da kuma Yogbeha, ya fāɗa wa mayaƙan ta yadda ba su zata ba. Zeba da Zalmunna, sarakunan biyu na Midiyawa suka tsere, amma ya bi su ya kama, ya fatattaki dukan mayaƙansu. Sa’an nan Gideyon ɗan Yowash ya komo daga yaƙi ta Hanyar Heres. Ya kama wani saurayin Sukkot ya tambaye shi, saurayin kuwa ya rubuta masa dukan sunayen shugabanni saba’in da bakwai na Sukkot, da dattawan garin. Sa’an nan Gideyon ya zo ya ce wa mutanen Sukkot, “To, ga Zeba da Zalmunna, waɗanda kuka yi mini ba’a kuna cewa, ‘Ka kama Zeba da Zalmunna ko ne? Me zai sa mu ba mutanenka da suka gaji burodi?’ ” Ya kwashe dattawan garin ya koya wa mutanen Sukkot hankali ta wurin hukunta su da ƙayayyuwan hamada. Ya rushe hasumiyar Fenuwel ya kuma karkashe mutanen garin. Sa’an nan ya ce wa Zeba da Zalmunna, “Waɗanne irin mutane ne kuka karkashe a Tabor.” Suka ce, “Mutane kamar ka ne kowane kamar ɗan sarki.” Gideyon ya ce, “Waɗannan ’yan’uwana ne, ’ya’yan mahaifiyata. Muddin Ubangiji yana a raye, da a ce kun bar su da rai, da ba zan kashe ku ba.” Da ya juya wajen Yeter, ɗan farinsa, sai ya ce, “Ka kashe su!” Amma Yeter bai zāre takobinsa ba, domin shi yaro ne kawai kuma yana tsoro. Zeba da Zalmunna suka ce masa, “Zo, ka yi da kanka. ‘Yadda mutum yake haka ƙarfinsa.’ ” Ta haka Gideyon ya matso gaba ya kashe su, ya ɗauki kayan ado daga wuyar raƙumansu. Isra’ilawa suka ce wa Gideyon, “Ka yi mulkinmu, kai, ɗanka da jikanka, domin ka cece mu daga hannun Midiyawa.” Amma Gideyon ya ce musu, “Ni, ko ɗana, ba za mu yi mulkinku ba. Ubangiji ne zai yi mulkinku.” Kuma ya ce, “Ina da roƙo guda ɗaya, cewa kowannenku ya ba ni ’yan kunne daga rabon ganima.” (Al’adar mutanen Ishmayel ce su sa ’yan kunnen zinariya.) Suka ce, “Za mu yi farin cikin ba ka su.” Saboda haka suka shimfiɗa mayafi, kowanne ya sa ɗan kunne ɗaya daga ganimar. Nauyin ’yan kunnen zinariyar ya kai shekel ɗari goma sha bakwai, ban da kayan ado, abin wuya da tufafin shunayya waɗanda sarakuna Midiyawa suke sawa ko sarƙoƙin da suke wuyar raƙumansu. Gideyon ya efod da zinariyar, wanda ya ajiye a Ofra, garinsa. Dukan Isra’ila suka shiga yin karuwanci ta wurin yin sujada a can, ya kuwa zama wa Gideyon da dukan iyalinsa tarko. Da haka Isra’ilawa suka mallaki Midiyawa ba su kuma sāke tā da kai ba. A zamanin Gideyon ƙasar ta sami zaman lafiya har shekara arba’in. Yerub-Ba’al ɗan Yowash ya koma gida don yă zauna. Yana da ’ya’ya saba’in maza da ya haifa, gama yana da mata da yawa. Yana kuma da ƙwarƙwara wadda take Shekem, ita ma ta haifa masa ɗa wanda ya ba shi suna Abimelek. Gideyon ɗan Yowash ya rasu da kyakkyawan tsufa aka kuma binne shi a kabarin Yowash mahaifinsa a Ofra na mutanen Abiyezer. Ba a daɗe da rasuwar Gideyon ba, sai Isra’ila ta sāke shiga karuwanci suna bauta wa Ba’al. Suka kafa Ba’al-Berit yă zama musu allahnsu ba kuma tuna da Ubangiji Allahnsu, wanda ya cece su daga hannuwan abokan gābansu a kowane gefe ba. Suka kāsa nuna alheri ga gidan Yerub-Ba’al (wato, Gideyon) saboda abubuwa masu alherin da ya yi musu. Abimelek ɗan Yerub-Ba’al ya tafi Shekem wurin ’yan’uwan mahaifiyarsa, ya ce musu da kuma dukan dangin mahaifiyarsa, “Ku tambayi ’yan ƙasar Shekem, ‘Wanne ya fi muku, a sa dukan ’ya’yan Yerub-Ba’al saba’in maza su yi mulkinku, ko dai mutum guda kawai yă yi mulkinku?’ Ku tuna, ni jininku ne.” Sa’ad da ’yan’uwan suka mayar wa ’yan ƙasar Shekem wannan, sai suka goyi bayan Abimelek, gama sun ce, “Shi ɗan’uwanmu ne.” Suka ba shi shekel saba’in na azurfa daga haikalin Ba’al-Berit, Abimelek kuwa ya yi amfani da shi ya yi hayar ’yan tauri waɗanda suka zama masu binsa. Sai ya tafi gidan mahaifinsa a Ofra kuma a dutse guda ya kashe ’yan’uwansa, ’ya’yan Yerub-Ba’al. Amma Yotam, autan ɗan Yerub-Ba’al ya tsira ta wurin ɓuya. Sa’an nan duka ’yan ƙasar Shekem da Bet Millo suka taru kusa da babban itacen wajen ginshiƙi a Shekem don a naɗa Abimelek sarki. Sa’ad da aka gaya wa Yotam wannan, sai ya hau Dutsen Gerizim ya yi kira da ƙarfi ya ce, “Ku saurare ni, ’yan ƙasar Shekem, don Allah yă saurare ku. Wata rana itatuwa suka fita don su naɗa wa kansu sarki. Suka ce wa itacen zaitun, ‘Ka zama sarkinmu.’ “Amma itacen zaitun ya ce, ‘In bar mai nawa, wanda da shi ake girmama alloli da mutane, don in zo in yi ta fama da itatuwa?’ “Biye da wannan, sai itatuwan suka ce wa itacen ɓaure, ‘Zo ka zama sarkinmu.’ “Amma itacen ɓauren ya ce, ‘In bar kyawawan ’ya’yana da zaƙinsu, in zo in yi ta fama da itatuwa?’ “Sa’an nan itatuwan suka ce wa kuringar inabi, ‘Ki zo ki zama sarkinmu.’ “Amma kuringar ta ce, ‘In bar ruwan inabina, wanda yake faranta zuciyar alloli da mutane, in zo in yi fama da itatuwa?’ “A ƙarshe sai dukan itatuwa suka ce wa itacen ƙaya, ‘Ka zo ka zama sarkinmu.’ “Itacen ƙaya ya ce wa itatuwan, ‘In da gaske ne kuke so ku naɗa ni sarkinku, ku zo ku sha inuwana; in ba haka ba, bari wuta ta fito daga itacen ƙaya ta cinye itacen al’ul na Lebanon!’ “To, da a ce kun yi abin bangirma da aniya mai kyau sa’ad da kuka naɗa Abimelek sarki, da kun nuna wa Yerub-Ba’al da iyalinsa ladabi, da kuma kun yi masa abin da ya cancanci shi, a yi tunani cewa mahaifina ya yi yaƙi saboda ku, ya yi kasai da ransa don yă cece ku daga hannun Midiyawa (amma ga shi yau kun tayar wa iyalin mahaifina, kuka kashe ’ya’yansa saba’in a dutse guda, kuka kuma naɗa Abimelek, ɗan baiwa, sarki a kan ’yan ƙasar Shekem domin shi ɗan’uwanku ne) in har kun aikata wannan cikin bangirma da kuma aminci wajen Yerub-Ba’al da iyalinsa a yau, bari Abimelek yă zama farin cikinku, ku kuma nasa! Amma in ba haka ba, bari wuta ta fito daga Abimelek ya cinye ku, ’yan ƙasar Shekem da Bet Millo, bari wuta kuma daga wurinku ’yan ƙasar Shekem da Bet Millo ta cinye Abimelek!” Sa’an nan Yotam ya gudu, ya tsere zuwa Beyer ya zauna a can gama yana tsoron ɗan’uwansa Abimelek. Bayan Abimelek ya yi shekara uku yana mulki a Isra’ila, sai Allah ya aiko da mugun ruhu tsakanin Abimelek da ’yan ƙasar Shekem, waɗanda suka ci amanar Abimelek. Allah ya yi haka saboda kisan ’ya’ya saba’in na Yerub-Ba’al, don a ɗauki fansar jininsu a kan Abimelek ɗan’uwansu da kuma ’yan ƙasar Shekem, waɗanda suka taimake shi kisan ’yan’uwansa. Cikin hamayya da shi waɗannan ’yan ƙasar Shekem suka sa mutane a kan tuddai don su yi kwanton ɓauna a kan su yi fashi ga duk wanda ya wuce a can, wannan fa ya kai kunnen Abimelek. To, Ga’al ɗan Ebed ya tafi tare da ’yan’uwansa zuwa Shekem, ’yan ƙasarta kuwa suka dogara da shi. Bayan sun tafi gonaki suka tattara inabi suka matse su, sai suka yi biki a haikalin allahnsu. Yayinda suke ci da sha, sai suka la’anci Abimelek. Sa’an nan Ga’al ɗan Ebed ya ce, “Wane ne Abimelek, kuma wane ne Shekem, da za mu bauta masa? Shi ba ɗan Yerub-Ba’al ba ne, kuma ba Zebul ne mataimakinsa ba? Ku bauta wa mutanen Hamor, mahaifin Shekem! Me ya sa za mu bauta wa Abimelek? Da a ce waɗannan mutane suna a ƙarƙashina mana! Da zan hamɓarar da shi. In ce wa Abimelek, ‘Ka tara dukan mayaƙanka!’ ” Sa’ad da Zebul gwamnar birnin ya ji abin da Ga’al ɗan Ebed ya ce, sai ya fusata. Asirce sai ya aiki manzanni wajen Abimelek, yana cewa, “Ga’al ɗan Ebed da ’yan’uwansa sun zo Shekem suna kuma zuga birnin sun tayar maka. To, in dare ya yi, sai ka zo da mutanenka ku yi kwanto a filaye. Kashegari da safe, sai ku tashi ku fāɗa wa birnin. Sa’ad da Ga’al da mutanensa suka faɗa maka, sai ka yi abin da ka iya yi da su.” Saboda haka Abimelek da dukan mutanensa suka tashi da dare suka ɓuya kusa da Shekem a ƙungiyoyi huɗu. To, Ga’al ɗan Ebed ya riga ya fita waje yana tsaye a ƙofar birni daidai Abimelek da mayaƙansa suka fito daga inda suka ɓuya. Sa’ad da Ga’al ya gan su, sai ya ce wa Zebul, “Duba, ga mutane suna gangarowa daga kan duwatsu!” Zebul ya ce, “Kana ɗaukan inuwan duwatsu kana ce mutane.” Amma Ga’al ya sāke magana ya ce, “Duba, mutane suna gangarowa daga tsakiyar filaye, kuma wata ƙungiya tana zuwa daga wajen itacen masu duba.” Sa’an nan Zebul ya ce masa, “Ina bakin da ka yi ɗin, kai da ka ce, ‘Wane ne Abimelek da za mu bauta masa.’ Ba mutanen ne ka yi musu ba’a ba? Fita, ka yaƙe su mana!” Saboda haka Ga’al ya fito da ’yan ƙasar Shekem suka yaƙi Abimelek. Abimelek ya kore shi, mutane da yawa suka ji ciwo a yaƙin, har zuwa ƙofar birnin. Abimelek ya zauna a Aruma, Zebul kuwa ya kori Ga’al da ’yan’uwansa daga Shekem. Kashegari mutanen Shekem suka tafi gonaki, aka kuwa gaya wa Abimelek. Saboda haka ya ɗauki mutanensa, ya raba su ƙungiya uku, sa’an nan ya yi kwanto a gonakin. Sa’ad da ya ga mutanen suna fitowa daga birni, sai ya yi wuf ya fāɗa musu. Abimelek da ƙungiyoyin da suke tare da shi suka yi maza suka yi tsaya a ƙofar birnin. Sa’an nan ƙungiyoyi biyu suka ruga suka fāɗa wa waɗanda suke a gonaki suka karkashe su. Dukan yinin, Abimelek ya matsa yaƙi da birnin sai da ya cinye ta ya kuma kashe mutanenta. Sa’an nan ya hallaka birnin ya barbaza gishiri a kanta. Da jin haka, sai ’yan ƙasa a hasumiyar Shekem suka shiga wurin mafaka a hankalin El-Berit. Da Abimelek ya ji dukan mutanen hasumiyar Shekem sun taru a can, sai Abimelek da dukan mutanensa suka haura zuwa Dutsen Zalmon. Sai ya ɗauki gatari ya sassare waɗansu rassa, waɗanda ya sa a kafaɗunsa. Ya umarci mutanen da suke tare da shi ya ce, “Sauri, ku yi abin da kuka ga na yi!” Saboda haka mutanen suka sassare rassan itatuwa suka bi Abimelek. Suka tattara su a jikin mafakar suka kuma cinna mata wuta a kan mutanen da suke a ciki. Ta haka dukan mutanen da suke cikin hasumiyar Shekem, wajen maza da mata dubu ɗaya suka mutu. Biye da wannan Abimelek ya tafi Tebez, ya kewaye ta ya kuma cinye ta da yaƙi. A cikin birnin, akwai wata hasumiya mai ƙarfi, inda dukan maza da mata, dukan mutanen birnin, suka ɓuya. Suka kulle kansu, suka kuma hau rufin hasumiyar. Abimelek ya je wajen hasumiya ya kuma auka mata. Amma da ya yi kusa da ƙofar hasumiyar don yă cinna mata wuta, sai wata mata ta saki ɗan dutsen niƙa a kan Abimelek ta fasa ƙoƙon kansa. Da sauri ya kira mai riƙon masa makami ya ce, “Zaro takobinka ka kashe ni, don kada a ce ‘Mace ce ta kashe shi.’ ” Saboda haka bawansa ya soke shi, ya mutu. Sa’ad da Isra’ilawa suka ga Abimelek ya mutu, sai suka tafi gida. Ta haka Allah ya sāka muguntar da Abimelek da ya yi wa mahaifinsa ta wurin kisan ’yan’uwansa saba’in. Allah kuma ya sa muguntar mutanen Shekem suka koma kansu. La’anar Yotam ɗan Yerub-Ba’al kuma ta kama su. Bayan zamanin Abimelek, sai Tola ɗan Fuwa ɗan Dodo daga Issakar ya tashi don yă ceci Isra’ila. Yana zama a Shamir a ƙasar tudu ta Efraim. Ya shugabanci Isra’ila shekara ashirin da uku sa’an nan ya mutu, aka kuma binne shi a Shamir. Bayansa kuma sai Yayir daga Gileyad, wanda ya shugabanci Isra’ila shekara ashirin da biyu. Yana ’ya’ya talatin, waɗanda suke hawan jakuna talatin. Sun shugabanci birane talatin a Gileyad, har wa yau ana ce da biranen Hawwot Yayir. Sa’ad da Yayir ya mutu, sai aka binne shi a Kamon. Isra’ilawa suka sāke yin mugayen ayyuka a gaban Ubangiji. Suka shiga bautar Ba’al da Ashtarot, da kuma allolin Aram, allolin Sidon, allolin Mowab, Ammonawa da kuma allolin Filistiyawa. Kuma domin Isra’ilawa sun bar Ubangiji ba su ƙara bauta masa ba, sai ya fusata da su. Ya sayar da su ga hannun Filistiyawa da Ammonawa, waɗanda suka fatattake su a shekarar suka kuma ragargaza su. Shekara goma sha takwas suka yi ta danne dukan Isra’ilawan da suke gabashin Urdun a Gileyad, ƙasar Amoriyawa. Ammonawa su ma suka haye Urdun domin su yi yaƙi da Yahuda, Benyamin da kuma gidan Efraim; Isra’ila kuwa suka kasance cikin wahala ƙwarai da gaske. Sa’an nan Isra’ilawa suka yi kuka ga Ubangiji, suka ce, “Mun yi maka zunubi, mun bar Allahnmu muka shiga bautar Ba’al.” Ubangiji ya ce, “Sa’ad da Masarawa, Amoriyawa, Ammonawa, Filistiyawa, Sidoniyawa, Amalekawa da kuma mutanen Mawon suka wulaƙanta ku kuka kuwa yi mini kuka, ban cece ku daga hannunsu ba? Amma kuka bar ni kuka bauta wa waɗansu alloli, saboda haka ni ma ba zan ƙara cece ku ba. Ku tafi ku yi wa allolin da kuka zaɓa. Bari su cece ku sa’ad da kuke cikin wahala!” Amma Isra’ilawa suka ce wa Ubangiji, “Mu dai mun yi zunubi. Ka yi da mu abin da ka ga dama, amma muna roƙonka ka cece mu a yanzu.” Sa’an nan suka zubar da allolin nan daga cikinsu suka bauta wa Ubangiji. Ubangiji kuwa bai ƙara daure da azabar da Isra’ila suke sha ba. Sa’ad da aka kira Ammonawa su yi ɗamarar yaƙi, sai su kuma kafa sansani a Gileyad, Isra’ilawa kuwa suka tattaru suka kafa sansani Mizfa. Shugabannin mutanen Gileyad suka cewa juna, “Duk wanda zai fara fāɗa wa Ammonawa shi zai zama shugaban duk waɗanda suke zama a Gileyad.” Yefta mutumin Gileyad, jarumi ne ƙwarai. Mahaifinsa ne Gileyad; mahaifiyar kuwa karuwa ce. Matar Gileyad ta haifa masa ’ya’ya maza, kuma sa’ad da suka yi girma, sai suka kore Yefta, suka ce “Ba ka da gādo a cikin iyalinmu, domin kai ɗan wata mace ce.” Saboda haka Yefta ya tsere daga ’yan’uwansa ya zauna a ƙasar Tob, inda waɗansu ’yan iska suka kewaye shi suka bi shi. Ana nan, sa’ad da Ammonawa suka kai wa Isra’ilawa hari, dattawan Gileyad suka je suka nemo Yefta daga ƙasar Tob. Suka ce masa, “Ka zo ka zama mana shugaba, don mu yaƙi Ammonawa.” Yefta ya ce musu, “Ba kun ƙi ni kuka kuma kore ni daga gidan mahaifina ba? Me ya sa kuke zuwa wurina yanzu sa’ad da kuke cikin wahala?” Mutanen Gileyad suka ce masa, “Duk da haka, muna juyo wajenka yanzu, ka zo tare da mu mu yaƙi Ammonawa, za ka kuma zama shugaban duk wanda yake zama a Gileyad.” Yefta ya ce, “A ce kun dawo da ni in yaƙi Ammonawa, Ubangiji kuwa ya ba da su a hannuna, zan zama shugabanku?” Dattawan Gileyad suka ce, “ Ubangiji ne shaidanmu; za mu yi duk abin da ka ce.” Saboda haka Yefta ya tafi tare da dattawan Gileyad, mutanen kuwa suka naɗa shi shugabansu da kuma sarkinsu. Ya kuwa maimaita dukan maganarsa a gaban Ubangiji a Mizfa. Sa’an nan Yefta ya aiki jakadu zuwa wurin sarkin Ammonawa su tambaya, “Me ya haɗa ka da ni, da ka kawo wa ƙasata yaƙi?” Sarkin Ammonawa ya ce wa jakadu, “Sa’ad da Isra’ilawa suka fito daga Masar, sun ƙwace mini ƙasa tun daga Arnon zuwa Yabbok, har zuwa Urdun. Yanzu ka mayar mini ita cikin salama.” Yefta ya sāke aikan jakadu wurin sarki, yana cewa, “Ga abin da Yefta yake faɗi, Isra’ila ba tă ƙwace ƙasar Mowab ko ta Ammonawa ba. Amma sa’ad da suka bar Masar, Isra’ila ta bi ta hamada zuwa Jan Teku har suka zo Kadesh. Sa’an nan Isra’ila ta aiki jakadu zuwa ga sarkin Edom cewa, ‘Ka ba mu izini mu ratsa ƙasarka,’ amma sarkin Edom bai saurara ba. Suka kuma aika wa sarkin Mowab, shi ma ya ƙi. Saboda haka Isra’ila ta zauna a Kadesh. “Daga can suka ci gaba ta hamada, suka zaga ƙasashen Edom da Mowab, suka wuce ta gabashin ƙasar Mowab, sa’an nan suka yi sansani a ɗaya gefen Arnon. Ba su shiga yankin Mowab ba, gama Arnon ce iyakarta. “Sa’an nan Isra’ila ta aiki jakadu zuwa ga Sihon sarkin Amoriyawa, wanda yake mulki a Heshbon, ta ce masa, ‘Ka bar mu mu ratsa ƙasarka mu wuce zuwa wurinmu.’ Sihon dai, bai amince da Isra’ila su ratsa ƙasarsa ba. Ya tattara dukan mutanensa suka yi sansani a Yahza suka kuwa yaƙi Isra’ila. “Sa’an nan Ubangiji, Allah na Isra’ila, ya ba da Sihon da dukan mutanensa a hannun Isra’ila, suka kuwa ci nasara a kansu. Isra’ila ta ƙwace dukan ƙasar Amoriyawa da suke zaune a ƙasar, suka ƙwace dukan yankin Amoriyawa tun daga ƙasar Arnon zuwa Yabbok, daga hamada har zuwa Urdun. “To, da yake Ubangiji, Allah na Isra’ila, ya kori Amoriyawa a gaban mutanensa Isra’ila, wane ’yanci kake da shi da za ka karɓe ta? Ba za ka karɓi abin da allahnka Kemosh ya ba ka ba? Haka mu ma, duk abin da Ubangiji Allahnmu ya riga ya ba mu, za mu mallake shi. Ka fi Balak ɗan Ziffor, sarkin Mowab ne? Ka taɓa ji ya yi hamayya da Isra’ila ko yă yi yaƙi da su? Shekara ɗari uku Isra’ilawa suka yi zamansu a Heshbon, Arower da ƙauyukan kewayenta da dukan biranen da suke gefen Arnon. Me ya sa ba ka karɓe su a lokacin ba? Ban yi maka laifi ba, amma kana musguna mini ta wurin kawo mini hari. Bari Ubangiji yă zama Alƙali, yă yanke hukunci tsakani Isra’ilawa da Ammonawa.” Duk da haka sarkin Ammonawa bai kula da saƙon da Yefta ya aika ba. Sa’an nan Ruhun Ubangiji ya sauko wa Yefta. Sai ya haye Gileyad da Manasse, ya ratsa ta Mizfa zuwa Gileyad, daga can kuma ya kai wa Ammonawa hari. Yefta kuwa ya yi wa’adi da Ubangiji ya ce, “In ka ba da Ammonawa a hannuwana, duk abin da ya fara fitowa daga ƙofar gidana don yă tarye ni, sa’ad da na komo daga yaƙi da Ammonawa, zai zama na Ubangiji, zan miƙa shi hadaya ta ƙonawa.” Sa’an nan Yefta ya haye zuwa wajen Ammonawa don yaƙi da su. Ubangiji kuwa ya ba da su a hannuwansa. Ya hallaka birane ashirin tun daga Arower zuwa yankin Minnit, har zuwa Abel-Keramim. Haka Isra’ila ta cinye Ammonawa ƙaf. Sa’ad da Yefta ya komo gida a Mizfa, wa ya fito yă tarye shi, ’yarsa tilo, tana rawa kiɗin ganguna! Ita ce kaɗai ’yarsa. Ban da ita ba shi da ɗa ko ’ya. Da ya gan ta, sai ya yayyage tufafinsa ya yi kuka ya ce, “Kaito! ’Yata! Kin karya mini gwiwa, kuma na lalace, domin na yi wa’adi ga Ubangiji da ba zan iya in karya ba.” Ta ce, “Mahaifina, idan ka riga ka yi wa Ubangiji magana, sai ka yi da ni yadda ka yi alkawari, da yake Ubangiji ya ɗau maka fansa a kan Ammonawa.” Sai ta kuma ce, “Sai dai, ka biya mini wannan bukata guda. Ka ba ni wata biyu in yi ta yawo da ni da ƙawayena a kan duwatsu mu yi makoki, domin ba zan yi aure ba.” Ya ce mata, “Ki tafi,” Ya bar ta tă tafi har wata biyu. Ita da ’yan matan suka tafi a kan duwatsu suka yi ta makoki domin ba za tă taɓa aure ba. Bayan watanni biyu ɗin sai ta komo wurin mahaifinta ya kuwa yi da ita yadda ya yi wa’adi. Ita kuwa ba tă taɓa san namiji ba. Wannan ya zama al’ada a Isra’ila, cewa kowace shekara ’yan mata sukan fita kwana huɗu don yin bikin tunawa da ’yar Yefta mutumin Gileyad. Mutanen Efraim suka tattaro mayaƙansu, suka haye zuwa Zafon suka cewa Yefta, “Don me ka tafi ka yaƙi Ammonawa ba ka gayyace mu ba? Za mu ƙone gidanka a kanka.” Yefta ya ce, “Ni da mutanena mun yi ta jayayya sosai da Ammonawa, ko da yake na kira ku, amma ba ku cece ni daga hannuwansu ba. Da na ga ba za ku taimake ni ba, sai na yi kasai da raina na kuwa haye don in yaƙi Ammonawa, Ubangiji kuwa ya ba ni nasara a kansu. To, don me kuka zo yau don ku yaƙe ni?” Sa’an nan Yefta ya tara mutanen Gileyad wuri guda ya kuma yaƙi Efraim. Mutanen Gileyad suka fatattake su domin mutanen Efraim sun ce, “Ku Mutanen Gileyad masu neman mafaka ne cikin Efraim da Manasse.” Mutanen Gileyad suka ƙwace mashigan Urdun masu zuwa Efraim, duk sa’ad da wani daga Efraim da ya tsira ya ce, “Bari in haye,” sai mutane Gileyad su ce “Kai mutumin Efraim ne?” In ya ce, “A’a,” sai su ce, “To, ka ce, ‘Shibbolet.’ ” In ya ce, “Sibbolet,” saboda ba sa iya faɗin kalmar daidai, sai su kama shi su kashe a mashigan Urdun. Aka kashe mutanen Efraim dubu arba’in da biyu a ta haka. Yefta ya shugabanci Isra’ila shekara shida. Sa’an nan Yefta mutumin Gileyad ya mutu, aka kuwa binne shi wani gari a Gileyad. Bayansa, Ibzan mutumin Betlehem, ya shugabanci Isra’ila. Yana ’ya’ya maza talatin da ’ya’ya mata talatin. Ya ba da auren ’ya’yansa mata ga waɗanda ba daga dangi ba, ga ’ya’yansa maza kuwa ya kawo ’yan mata talatin su zama matansu waje da danginsa. Ibzan ya shugabanci Isra’ila shekara bakwai. Sa’an nan Ibzan ya mutu, aka kuwa binne shi Betlehem. Bayansa, Elon mutumin Zebulun, ya shugabanci Isra’ila shekara goma. Sa’an nan Elon ya mutu, aka kuwa binne shi a Aiyalon a ƙasar Zebulun. Bayansa, Abdon ɗan Hillel, daga Firaton, ya shugabanci Isra’ila. Yana da ’ya’ya maza arba’in da ’yan taɓa kunne talatin, waɗanda suka hau jakuna saba’in. Ya shugabanci Isra’ila shekara takwas. Sa’an nan Abdon ɗan Hillel ya mutu, aka kuwa binne shi a Firaton a Efraim, a ƙasar tudu ta Amalekawa. Isra’ilawa suka sāke yin mugayen ayyuka a gaban Ubangiji, saboda haka ya ba da su a hannun Filistiyawa shekara arba’in. Akwai wani mutumin Zora, mai suna Manowa, daga kabilar Dan, matarsa kuwa bakararriya ce, ba ta haihuwa. Mala’ikan Ubangiji ya bayyana gare ta ya ce, “Ga shi ke bakararriya ce ba kya haihuwa, amma za ki yi ciki ki kuma haifi ɗa. To, sai ki lura kada ki sha ruwan inabi ko wani abu mai sa maye, kada kuma ki ci wani abu marar tsarki, gama za ki yi ciki, ki haifi ɗa. Aska ba za tă taɓa kansa ba, domin yaron zai zama Banazare, keɓaɓɓe ga Allah tun daga haihuwa, shi ne kuwa zai soma ceton Isra’ilawa daga hannuwan Filistiyawa.” Sa’an nan matar ta tafi wajen mijinta ta faɗa masa cewa, “Wani mutumin Allah ya zo wurina. Ya yi kama da mala’ikan Allah, yana da bantsoro ƙwarai. Ban tambaye shi inda ya fito ba, kuma bai gaya mini sunansa ba. Sai dai ya ce mini, ‘Za ki yi ciki, ki kuma haifi ɗa. To, fa, kada ki sha ruwan inabi ko abu mai sa maye kada kuma ki ci abin da yake marar tsarki, gama ɗan zai zama Banazare na Allah tun daga haihuwa har ranar mutuwarsa.’ ” Sai Manowa ya yi addu’a ga Ubangiji ya ce, “Ya Ubangiji, ina roƙonka, bari mutumin Allahn da ka aiko mana yă sāke zuwa don yă koya mana yadda za mu goyi yaron da za a haifa.” Allah ya ji Manowa, sai mala’ikan Allah ya sāke zuwa wurin matar yayinda take gona; amma Manowa mijinta ba ya tare da ita. Sai matar ta ruga don ta faɗa wa mijinta, ta ce, “Ga shi ya zo! Mutumin da ya bayyana mini ran nan!” Manowa ya tashi ya bi matarsa. Da ya zo wurin mutumin, sai ya ce, “Kai ne wanda ka yi magana da matata?” Ya ce, “Ni ne.” Saboda haka Manowa ya tambaye shi ya ce, “Sa’ad da maganarka ta cika, me za tă zama dokar rayuwar yaron da kuma aikinsa?” Mala’ikan Ubangiji ya ce, “Dole matarka ta kiyaye duk abin da na riga na gaya mata. Kada tă ci kowane iri abin da ya fito daga inabi, ba kuwa za tă sha ruwan inabi, ko abu mai sa maye ko ta ci abu marar tsarki ba. Dole tă kiyaye duk abin da na umarce mata.” Manowa ya ce wa mala’ikan Ubangiji, “Muna roƙonka ka jira mu yanka maka ɗan akuya.” Mala’ikan Ubangiji ya ce, “Ko kun sa na tsaya, ba zan ci abincinku ba. Amma in kun shirya hadaya ta ƙonawa, ku miƙa wa Ubangiji.” (Manowa bai gane cewa mala’ikan Ubangiji ne ba.) Sa’an nan Manowa ya sāke tambayi mala’ikan Ubangiji ya ce, “Mene ne sunanka, don mu girmama ka sa’ad da maganarka ta tabbata.” Ya ce, “Me ya sa kake tambaya sunana? Ai, ya wuce fahimta.” Sa’an nan Manowa ya ɗauki ɗan akuya, tare da hadaya ta hatsi ya miƙa wa Ubangiji a kan dutse. Ubangiji kuwa ya yi abin mamaki yayinda Manowa da matarsa suke kallo. Yayinda harshen wuta ya yi sama daga bagaden, sai mala’ikan Ubangiji ya haura cikin harshen wutar. Da ganin wannan Manowa da matarsa suka fāɗi da fuskokinsu har ƙasa. Da mala’ikan Ubangiji bai ƙara bayyana kansa ga Manowa da matarsa ba, sai Manowa ya gane cewa mala’ikan Ubangiji ne. Ya ce wa matar, “Ba shakka za mu mutu, gama mun ga Allah!” Amma matar ta ce, “Da Ubangiji yana nufin kashe mu ne, da ba zai karɓi hadaya ta ƙonawa da hadaya ta hatsi daga hannunmu, ko yă nuna mana dukan waɗannan abubuwa ko abin da ya gaya mana ba.” Matar kuwa ta haifi ɗa, aka sa masa suna Samson. Ya yi girma Ubangiji kuma ya albarkace shi, Ruhun Ubangiji kuwa ya fara iza shi yayinda yake a Mahane Dan, tsakanin Zora da Eshtawol. Samson ya gangara zuwa Timna a can ya ga wata daga cikin ’yan mata Filistiyawa. Da ya komo, sai ya gaya wa mahaifinsa da mahaifiyarsa ya ce, “Na ga wata mace a Timna; ku auro mini ita ta zama matata.” Mahaifinsa da mahaifiyarsa suka ce, “Babu wata karɓaɓɓiyar yarinya a cikin zuriyarku ko cikin dukan mutanenmu ne? Dole ne ka tafi wajen Filistiyawa marasa kaciya ka nemi aure?” Amma Samson ya ce wa mahaifinsa, “A auro mini ita dai. Ita ta dace da ni.” (Iyayensa ba su san cewa wannan daga wurin Ubangiji ne ba, wanda yake neman hanyar da za a kai wa Filistiyawa hari; gama a lokacin suna mulkin Isra’ila.) Sai Samson ya gangara zuwa Timna tare da mahaifinsa da kuma mahaifiyarsa. Da suka yi kusa da gonar inabin Timna, nan da nan sai ga ɗan zaki ya taso ya nufe shi yana ruri. Ruhun Ubangiji kuwa ya sauko masa da ƙarfi, ya sa ya yaga zakin kashi biyu da hannu kamar yadda akan yayyage ɗan akuya. Sai dai bai gaya wa iyayensa abin da ya yi ba. Sa’an nan ya gangara ya yi magana da yarinyar, yana kuwa sonsa. Daga baya, da ya koma don yă aure ta, sai ya ratse don yă ga gawar zakin. Sai ga taron ƙudan zuma da zuma a ciki, wanda ya sa hannu ya ɗebo yana tafiya yana sha. Sa’ad da ya iso wurin iyayensa, ya ba su zuman, su ma suka sha. Sai dai bai gaya musu cewa ya ɗebo zuman daga gawar zaki ba. To, mahaifinsa ya gangara don yă ga yarinyar. Samson kuwa ya shirya wata liyafa a can, yadda yake bisa ga al’adar angwaye. Sa’ad da ya bayyana, sai aka haɗa shi abokai talatin. Sai Samson ya ce, “Bari in yi muku kacici-kacici, in kun ba ni amsa cikin kwana bakwai na wannan biki, zan ba ku riguna lilin talatin da kuma tufafi talatin. In kuma ba ku iya ba ni amsar ba, dole ku ba ni rigunan lilin talatin da tufafi talatin.” Suka ce, “Ka gaya mana kacici-kacicin.” Sai ya ce, “Daga mai ci, abinci ya fito; daga mai ƙarfi, abu mai zaki ya fito.” Har kwana uku ba su iya ba da amsa ba. A rana ta huɗu suka ce wa matar Samson “Ki rarrashi mijinki yă bayyana mana kacici-kacicin, ko kuwa mu ƙone ki da gidan mahaifinki duka da wuta. Kun kira mu domin ku yi mana fashi ne?” Sa’an nan matar Samson ta kwanta masa a jiki tana kuka tana cewa, “Kai maƙiyina ne, lalle ba ka ƙaunata, ka yi wa mutanena kacici-kacici, amma ba ka gaya mini amsar ba.” Ya amsa ya ce, “Ban ma bayyana wa mahaifina ko mahaifiyata ba, to, don me zan bayyana miki?” Ta yi ta kuka har kwana bakwai na bikin. Saboda haka a rana ta bakwai sai ya gaya mata, don ta dame shi. Ita kuwa ta bayyana kacici-kacicin wa mutanenta. Kafin rana ta fāɗi a rana ta bakwai mutane garin suka ce masa, “Me ya fi zuma zaki? Me ya fi zaki ƙarfi?” Samson ya ce musu, “Da ba don kun haɗa baki da matata ba, da ba za ku san amsar kacici-kacici ba.” Sa’an nan Ruhun Ubangiji ya sauko masa da iko. Sai ya fita ya gangara zuwa Ashkelon, ya kashe mutanensu talatin, ya kwashe kayansu ya kuma ba da rigunarsu ga waɗanda suka bayyana kacici-kacicin. Cike da fushi, ya haura zuwa gidan mahaifinsa. Aka kuma ɗauki matar Samson aka ba wa ɗaya daga cikin waɗanda suka yi masa hidima a bikin. Daga baya, a lokacin girbin alkama, Samson ya ɗauki ɗan akuya ya tafi yă ziyarci matarsa. Sai ya ce, “Zan in shiga ɗakin matata.” Amma mahaifinta ya hana shi shiga. Ya ce wa, “Na tabbata ba ka sonta sam-sam, don haka na ba da ita ga abokinka. Ba ƙanuwarta ta fi kyau ba? Ka ɗauke ta a maimako.” Samson kuwa ya ce musu, “A wannan lokaci ina da iko in rama a kan Filistiyawa; tabbatacce zan ji musu.” Saboda haka ya tafi ya kama yanyawa ɗari uku ya ɗaura wutsiyoyinsu wutsiya da wutsiya. Sa’an nan ya daure acibalbal a tsakanin ko waɗanne wutsiya biyu, sai ya sa wa acibalbal wuta, ya saki yanyawan suka shiga gonakin Filistiyawa. Suka ƙone dammunan hatsi da hatsin da yake tsaye, tare da gonakin inabi da na zaitun. Filistiyawa suka yi tambaya suka ce, “Wane ne ya yi wannan abu?” Sai aka ce musu, “Ai, Samson ne surukin mutumin Timna, domin an ba wa abokinsa matarsa.” Saboda haka Filistiyawa suka haura suka je suka ƙone ta da mahaifinta ƙurmus da wuta. Samson ya ce musu, “Tun da kun aikata wannan, ba zan bari ba har sai na ɗau fansa a kanku.” Ya kuwa fāɗa musu ya kuma karkashe su da yawa. Sa’an nan ya gangara ya zauna a kogo a dutsen Etam. Filistiyawa suka haura suka yi sansani a Yahuda, suka bazu kusa da Lehi. Mutanen Yahuda suka ce, “Me ya sa kuka zo mana da yaƙi?” Sai suka ce, “Mun zo ne mu kama Samson, a matsayin fursunan yaƙi, mu yi masa kamar yadda ya yi mana.” Sa’an nan mutane dubu uku daga Yahuda suka gangara wajen Samson a kogo a dutsen Etam. Suka ce masa, “Ba ka san cewa Filistiyawa ne suke mulkinmu ba? Me ke nan ka yi mana?” Ya ce musu, “Na ɗan yi musu abin da suka yi mini ne.” Suka ce masa, “To, mun zo ne mu daure ka mu kai wa Filistiyawa.” Samson ya ce, “Ku rantse mini ba za ku kashe ni da kanku ba.” Suka ce, “Mun yarda, za mu dai daure ka mu ba da kai gare su. Ba za mu kashe ka ba.” Saboda haka suka daure shi da sababbin igiyoyi biyu, suka saukar da shi daga dutsen. Yayinda ya zo gab da Lehi, sai Filistiyawa suka sheƙo a guje da ihu suka nufo shi. Ruhun Ubangiji kuwa ya sauko da iko a kansa. Igiyoyin da suke daure a hannuwansa kuwa suka zama kamar abin da wuta ta babbaka, suka tsintsinke suka zuba daga hannuwansa. Da ya samo muƙamuƙin jaki, ya ɗauka, sai ya karkashe mutane dubu ɗaya. Sa’an nan Samson ya ce, “Da muƙamuƙin jaki na mai da su jakuna. Da muƙamuƙin jaki na kashe mutum dubu.” Da ya gama magana, sai ya jefar da muƙamuƙin; aka ba wa wannan wuri suna Ramat Lehi. Saboda ƙishirwa ta kama shi ƙwarai, sai ya ce wa Ubangiji, “Ka ba bawanka wannan babbar nasara. To, sai in mutu da ƙishirwa, har in shiga a hannun marasa kaciyan nan su kashe ni?” Sa’an nan Allah ya buɗe wani rami a Lehi, ruwa kuwa ya fito daga ciki. Da Samson ya sha, sai ƙarfinsa ya dawo, ya kuma wartsake. Aka sa wa wannan maɓulɓula suna En Hakkore, yana nan a Lehi har wa yau. Samson kuwa ya shugabanci Isra’ila shekara ashirin a zamanin Filistiyawa. Wata rana Samson ya tafi Gaza, inda ya ga wata karuwa. Ya shiga wurinta ya kwana. Aka gaya wa mutanen Gaza, “Ai, Samson yana a nan!” Saboda haka suka zo suka kewaye wurin suka yi kwanto dukan dare a bakin ƙofar birni. A daren nan ba su motsa nan da can ba, suna cewa, “Gari yana wayewa za mu kashe shi.” Amma Samson ya yi kwanciyarsa har tsakiyar dare. Sa’an nan ya tashi ya kama ƙofofin birnin, tare da madogarai biyunsu, ya tumɓuke, ya aza su a kafaɗarsa, ya kai su kan dutsen da yake a fuskantar Hebron. Bayan ɗan lokaci, sai ya shiga ƙaunar wata mace, mai suna Delila a Kwarin Sorek. Sai shugabannin Filistiyawa suka tafi wurinta suka ce, “Ki yi ƙoƙari ki ga ko za ki rarrashe shi yă nuna miki asirin ƙarfinsa da yadda za mu iya shan ƙarfinsa don mu ɗaura shi mu yi nasara a kansa. Kowannenmu zai ba ki shekel dubu ɗari ɗaya na azurfa.” Saboda haka Delila ta ce wa Samson, “Ka faɗa miki asirin ƙarfinka da yadda za a ɗaura ka a yi nasara a kanka.” Samson ya ce mata, “In wani ya ɗaura ni da sababbin igiyoyin da ba su bushe ba, zan zama marar ƙarfi kamar kowa.” Sa’an nan shugabannin Filistiyawa suka kawo mata sababbin igiyoyi guda bakwai da ba su bushe ba, sai ta daure shi da su. Da mutane a ɓoye a cikin ɗaki tare da ita, sai ta yi ihu ta ce, “Samson ga Filistiyawa sun zo su kama ka!” Da jin haka sai ya tsintsinke igiyoyin kamar zaren da ya yi kusa da harshen wuta. Saboda haka asirin ƙarfinsa bai tonu ba. Sa’an nan Delila ta ce wa Samson, “Ka mai da ni wawiya; ka ruɗe ni. Yanzu, ka gaya mini yadda za a daure ka.” Ya ce, “In wani ya ɗaura ni sosai da sababbin igiyoyin da ba a taɓa amfani da su ba, zan zama marar ƙarfi kamar kowa.” Saboda haka Delila ta ɗauki sababbin igiyoyi ta ɗaura shi da su. Sa’an nan, tare da mutane a ɓoye a ɗakin, ta yi ihu ta ce, “Samson ga Filistiyawa sun zo su kama ka!” Amma sai ya tsintsinke su kamar zare. Sa’an nan Delila ta ce, “Har yanzu, ka mai da shashasha, kana mai da ni wawiya kana kuma yin mini ƙarya. Ka gaya mini yadda za a daure ka mana.” Ya ce mata, “In kin yi kitson gashin kaina guda bakwai kika ɗaura su da zare kika buga su da akwasha, zan rasa ƙarfi in zama kamar kowa.” Saboda haka yayinda yake barci, sai Delila ta yi kitson gashin kansa guda bakwai ta ɗinka su da zare, ta kuma ɗaura su da akwasha. Ta sāke yin ihu ta ce, “Samson ga Filistiyawa sun zo su kama ka.” Ya tashi daga barcinsa ya tumɓuke akwashan tare da zaren da aka ɗaura gashin kansa da su. Sa’an nan ta ce masa, “Yaya kake cewa kana sona alhali ba ka yarda da ni ba? Wannan shi ne sau na uku kana mai da ni wawiya kuma ba ka nuna mini asirin ƙarfinka ba.” Da irin wannan fitina ta tsokane shi kwana da kwanaki har sai da ya gaji kamar zai mutu. Saboda haka sai ya faɗa mata kome ya ce, “Ba a taɓa sa reza a kaina ba, domin ni Naziri ne keɓaɓɓe ga Allah tun haihuwa. In kuwa an aske kaina, ƙarfina zai rabu da ni, sai in zama kamar kowa.” Da Delila ta gane ya gaya mata kome yanzu, sai ta aika saƙo zuwa ga shugabannin Filistiyawa ta ce, “Ku ƙara zuwa sau ɗayan nan, ai, ya gaya mini kome.” Saboda haka shugabannin Filistiyawa suka dawo tare da azurfa a hannuwansu. Bayan ta sa shi ya yi barci a cinyarta, sai ta kira wani ya zo ya aske kitso guda bakwai nan a kansa, aka fara rinjayensa. Ƙarfinsa kuwa ya rabu da shi. Sa’an nan ta yi ihu ta ce, “Samson ga Filistiyawa sun zo su kama ka!” Sai ya farka daga barci yana tsammani cewa, “Zan fita kamar dā in miƙe jikina.” Amma bai san cewa Ubangiji ya rabu da shi ba. Sa’an nan Filistiyawa suka fizge shi, suka ƙwaƙule idanunsa suka gangara da shi zuwa Gaza. Da suka daure shi da sarƙoƙin tagulla, sai aka sa shi yana niƙa a kurkuku. Amma gashi kansa ya fara tohuwa kuma bayan an aske shi. To, sai Filistiyawa suka taru don su miƙa hadaya ga Dagon allahnsu su kuma yi biki cewa, “Allahnmu ya bashe abokin gābanmu Samson a hannuwanmu.” Sa’ad da mutane suka gan shi, sai suka yabi allahnsu, suna cewa, “Allahnmu ya bashe abokin gābanmu a hannunmu, wanda ya lalace ƙasarmu ya kuma raɓanya kisan mutanenmu.” Yayinda suke cikin farin ciki, sai suka yi ihu, suka ce, “Fito mana da Samson yă yi mana wasa.” Saboda haka aka zo da Samson daga kurkuku, shi kuwa ya yi wasa a gabansu. Sa’ad da suka tsai da shi a tsakanin ginshiƙai, sai Samson ya ce wa bawan da ya riƙe hannunsa, “Ka kai ni inda zan taɓa ginshiƙan da suke ɗauke da wannan haikali, don in jingina a kai.” To, haikalin ya cika da mutane maza da mata; dukan shugabannin Filistiyawa kuwa suna a can, a bisan rufin kuwa akwai mutum wajen dubu uku maza da mata suna kallon Samson yana wasa. Sa’an nan Samson ya yi addu’a ga Ubangiji ya ce, “Ya Ubangiji Mai Iko Duka, ya Allah ka tuna da ni, ka ƙarfafa ni sau ɗaya nan kaɗai, ka bar ni da bugu ɗaya kawai in ɗauki fansa a kan Filistiyawa domin idanuna.” Sa’an nan Samson ya kai hannuwansa ga ginshiƙan waɗanda haikalin yake a kai, ya jingina jikinsa, hannunsa dama yana a ɗaya, hannun hagu kuma na ɗayan, Samson ya ce, “Bari in mutu tare da Filistiyawa!” Sa’an nan da dukan ƙarfinsa ya tura haikali ya fāɗa a kan shugabanni da dukan mutanen da suke ciki. Ta haka ya kashe mutane da yawa fiye da yayinda yake da rai. Sa’an nan ’yan’uwansa da dukan dangin mahaifinsa suka gangaro don su ɗauke shi. Suka kawo shi suka binne tsakanin Zora da Eshtawol a kabarin Manowa mahaifinsa. Ya yi mulkin Isra’ila shekara ashirin. To, wani mutum mai suna Mika daga ƙasar tudu ta Efraim ya ce wa mahaifiyarsa, “Shekel dubu ɗaya da ɗari ɗaya na azurfa da aka ɗauka daga gare ki wanda kuma ji kin furta la’ana a kai, azurfan yana wurina; ni ne na ɗauka.” Sa’an nan mahaifiyarsa ta ce, “ Ubangiji yă albarkace ka ɗana!” Sa’ad da ya mayar da azurfa dubu ɗaya da ɗari ɗaya na shekel wa mahaifiyarsa, sai ta ce, “Na ba da azurfata ga Ubangiji don ɗana yă sassaƙa sura yă kuma yi zubin gunki. Zan mayar maka.” Saboda haka ya mayar da azurfan wa mahaifiyarsa, ita kuwa ta ɗauki azurfa ɗari biyu na shekel ta ba wa maƙeri, wanda ya mai da su sura da kuma gunki. Aka kuwa sa su a gidan Mika. To, wannan mutum Mika yana da ɗakin gumaka, ya yi efod da waɗansu gumaka, ya kuma naɗa ɗaya daga cikin ’ya’yansa firist nasa. A kwanakin Isra’ila ba ta da sarki; kowa yana yin abin da ya ga dama. Wani saurayi Balawe daga Betlehem a Yahuda, wanda yake zama cikin zuriyar Yahuda, ya bar garin ya tafi neman inda zai zauna. A hanyarsa ya zo gidan Mika a ƙasar tudu ta Efraim. Mika ya ce masa, “Daga ina kake?” Ya ce, “Ni Balawe ne daga Betlehem a Yahuda, ina kuwa neman wurin zauna ne.” Sa’an nan Mika ya ce masa, “Ka zauna tare da ni ka zama mini mahaifi da firist, zan kuwa ba ka azurfa goma na shekel a shekara, tufafinka da kuma abincinka.” Sai Balawen ya tafi. Saboda haka Balawen ya yarda ya zauna tare da shi, ɗan saurayin kuwa ya zama kamar ɗaya daga cikin ’ya’yansa. Sa’an nan Mika ya naɗa Balawen, saurayin kuwa ya zama masa firist ya kuma zauna a gidansa. Mika ya ce, “Yanzu na san cewa Ubangiji zai yi mini alheri, da yake Balawen nan ya zama firist nawa.” To, a kwanakin nan Isra’ila ba ta da sarki. A kwanakin kuwa zuriyar Dan tana neman wurinsu na zama, gama ba su riga sun sami gādo tare da kabilan Isra’ila ba. Saboda haka mutanen Dan suka aika jarumawa guda biyar daga Zora da Eshtawol don su leƙi asirin ƙasar su kuma bincike ta. Waɗannan mutanen sun wakilci dukan kabilar. Suka ce musu, “Ku je, ku bincike ƙasar.” Mutanen suka shiga ƙasar tudu ta Efraim suka zo gidan Mika, inda suka kwana. Sa’ad da suka yi kusa da gidan Mika, sai suka gane muryar saurayin nan Balawe; saboda haka suka shiga wurin suka tambaye shi, “Wa ya kawo ka nan? Me kake yi a nan? Me ya sa kake a nan?” Ya gaya musu abin da Mika ya faɗa masa ya ce, “Ya ɗauke ni aiki ya kuma sa in zama masa firist.” Sa’an nan suka ce masa, “Muna roƙonka ka nemi mana nufin Allah don mu sani ko tafiyarmu tana da nasara.” Firist ya amsa ya ce, “Ku sauka lafiya, gama tafiyarku tana da yardan Ubangiji.” Saboda haka mutum biyar ɗin suka tashi suka iso Layish, inda suka ga mutane suna zamansu a huce, kamar Sidoniyawa, ba sa zato ga tsaro. Kuma da yake ƙasarsu ba ta bukata kome, suna da wadata. Suna kuma nesa da Sidoniyawa, ba sa kuma hulɗa da kowa. Da suka komo Zora da Eshtawol, ’yan’uwansu suka tambaye su, “Me kuka gano?” Suka ce, “Ku zo mu yaƙe su! Mun ga ƙasar tana da kyau sosai. Ba za ku yi wani abu ba? Kada ku yi wata-wata, ku je kun mallaki ƙasar. Sa’ad da kun kai can, za ku iske mutanen suna zama a sake, ƙasar kuwa mai faɗi ce wadda Allah ya sa a hannuwanku, ƙasar da ba tă rasa kome ba.” Sai mutane ɗari shida daga kabilar Dan suka yi ɗamarar yaƙi, suka tashi daga Zora da Eshtawol. A kan hanyarsu suka kafa sansani kusa da Kiriyat Yeyarim a Yahuda. Shi ya sa a ana kira wurin nan yamma da Kiriyat Yeyarim Mahane Dan har wa yau. Daga can suka tafi ƙasar tudu ta Efraim suka zo gidan Mika. Sa’an nan mutum biyar ɗin nan da suka leƙi asirin ƙasar Layish suka ce wa ’yan’uwansu, “Kun san cewa ɗaya daga cikin gidajen nan yana da efod, waɗansu allolin iyali, siffar da aka sassaƙa da kuma gunki na zubi? To, kun san abin da za ku yi.” Saboda haka suka juya a wurin suka shiga gidan saurayin nan Balawe a wajen Mika suka gaishe shi. Mutanen Dan ɗari shida da suka sha ɗamarar yaƙi suka tsaya a bakin ƙofa. Sai mutum biyar da suka leƙi asirin ƙasar suka shiga ciki suka ɗauke gunkin da aka sassaƙa, efod, sauran allolin gida da kuma gunki na zubi yayinda firist ɗin tare da mutane ɗari shida da suka yi ɗamarar yaƙi suna tsaye a bakin ƙofa. Sa’ad da waɗannan mutane suka shiga gidan Mika suka ɗauke gunkin da aka sassaƙa, efod, sauran allolin gida da kuma gunki na zubi, sai firist ya ce musu, “Me kuke yi?” Suka ce, “Ka yi shiru! Kada ka ce wani abu. Zo tare da mu, ka zama mahaifinmu da kuma firist. Bai fi maka ka yi wa kabila da kuma zuriya a Isra’ila aikin firist ba, da ka bauta wa iyali guda kawai?” Sai firist ya yi farin ciki. Ya ɗauki efod, sauran allolin gida da siffar da aka sassaƙa ya tafi tare da mutanen. Suka sa ’ya’yansu ƙanana a gaba, dabbobinsu da mallakansu a gabansu, suka juya suka tafi. Sa’ad da suka yi ɗan nisa daga gidan Mika, sai aka kira mutanen da suke maƙwabtakar da Mika suka taru suka bi mutanen Dan suka cim musu. Da suna ihu suna binsu, sai mutanen Dan suka waiga suka cewa Mika, “Mece ce damuwarka da ka kira mutanenka su zo su fāɗa mana?” Ya amsa ya ce, “Kun kwashe allolin da na yi, da kuma firist nawa, kuka tafi. Me kuma nake da shi? Yaya za ku ce, ‘Mece ce damuwata?’ ” Mutanen Dan suka ce, “Kada ka kuskura ka ce kome, in ba haka ba mutanen nan za su harzuƙa, da kai da iyalinka duka ku rasa rayukanku.” Saboda haka mutanen Dan suka kama hanyarsu, Mika kuwa da ya ga an fi ƙarfinsa, sai ya juya ya koma gida. Sa’an nan suka ɗauko abin da Mika ya yi, da firist nasa, suka tafi Layish, suka fāɗa wa mutanen da suke zaman lafiya, ransu kuma a kwance. Suka fāɗa musu suka kuma ƙone birninsu. Ba wanda zai cece su domin suna nesa da Bet-Sidon kuma ba sa hulɗa da kowa. Birnin yana a kwari kusa da Bet-Rekob. Mutanen Dan suka sāke gina birnin suka zauna a can. Suka sa wa birnin suna Dan, wato, sunan kakansu Dan, wanda aka haifa wa Isra’ila, ko da yake a dā ana kira birnin Layish. A can mutanen Dan suka kafa wa kansu gumaka, Yonatan ɗan Gershom, ɗan Musa, da ’ya’yansa maza firistoci ne na kabilar Dan har lokacin da aka kwashe mutane zuwa bauta. Suka ci gaba da amfani da gumakan da Mika ya yi, a duk wannan lokacin gidan Allah yana a Shilo. A kwanakin nan Isra’ila ba su da sarki. To, wani Balawe wanda yake zama a wani lungu na ƙasar tudu ta Efraim ya ɗauko wa kansa ƙwarƙwara daga Betlehem cikin Yahuda. Amma ba tă yi aminci ba. Ta bar shi ta komo gidan mahaifiyarta a Betlehem, a Yahuda. Bayan ta zauna a can wajen wata huɗu, sai mijinta ya je wajenta biko don yă rarashe ta komo. Ya tafi tare bawansa da kuma jakuna biyu. Sai ta shigar da shi gidan mahaifinta, sa’ad da mahaifinta ya gan shi, ya marabce shi da murna. Surukinsa, mahaifin yarinyar, ya sha kansa, yă dakata; saboda haka ya dakata tare da shi har kwana uku, yana ci yana sha, yana kuma kwanciya a can. A rana ta huɗu suka tashi da sassafe ya kuma yi shiri yă tafi, amma mahaifinta yarinyar ya ce wa surukinsa, “Ka ɗan ci wani abu don ka sami ƙarfi; sa’an nan ka tafi.” Saboda haka suka zauna su biyu suka ci suka sha tare. Bayan haka sai mahaifin yarinyar ya ce, “Don Allah ka kwana ka ji wa kanka daɗi.” Sa’ad da mutumin ya tashi zai tafi, sai surukinsa ya roƙe shi, saboda haka ya kwana a wannan dare. Da sassafen kashegari rana ta biyar, ya tashi zai tafi, sai mahaifin yarinyar ya ce, “Ka ɗan zauna ka shaƙata sai rana ta yi sanyi mana!” Saboda haka su biyu suka zauna suka ci abinci tare. Sa’ad da mutumin da ƙwarƙwaransa da bawansa, suka tashi don su tafi, surukinsa, mahaifin yarinyar ya ce, “Duba, rana ta kusan fāɗuwa, yamma ta riga ta yi, ka kwana a nan. Ka sāke kwana ka ji wa ranka daɗi. Kashegari da sassafe za ka iya tashi ka kama hanyarka zuwa gida.” Amma bai so ya sāke kwana a can ba, mutumin ya tashi ya tafi ya bi ta Yebus (wato, Urushalima), tare da jakunansa biyu da aka yi musu shimfiɗa da kuma ƙwarƙwaransa. Sa’ad da suka yi kusa da Yebus dare kuma ya riga ya yi, bawan ya ce wa maigidansa, “Mu dakata a birnin nan na Yebusiyawa mu kwana.” Maigidansa ya ce, “A’a. Ba za mu shiga birnin baƙi waɗanda mutanensu ba Isra’ilawa ba. Za mu ci gaba zuwa Gibeya.” Ya kuma ce, “Zo, mu yi ƙoƙari mu kai Gibeya ko Rama mu kwana a ɗaya cikinsu.” Saboda haka suka ci gaba, rana tana fāɗuwa sa’ad da suka yi kusa da Gibeya a Benyamin. A can suka dakata don su kwana, suka tafi suka zauna a dandali birnin, amma wani ya shigar da su gidansa da daren. A wannan yamma sai ga wani tsoho daga ƙasar tudu ta Efraim, wanda yake zama a Gibeya (mutane wurin kuwa mutanen Benyamin ne), ya shigo daga wurin aiki a gonaki. Sa’ad da ya duba ya ga matafiyin a dandalin birnin, sai tsohon ya yi tambaya ya ce, “Ina za ku? Ina kuka fito?” Balawen ya ce, “Muna fito daga Betlehem a Yahuda za mu wani lungu a ƙasar tudu ta Efraim inda nake da zama. Na tafi Betlehem a Yahuda, ga shi kuwa yanzu za ni gidan Ubangiji. Ba wanda ya shigar da ni gidansa. Muna da ƙara da abinci don jakunanmu, muna kuma da burodi da ruwan inabi dominmu da bayinka, ni, baiwarka da kuma saurayin nan tare da mu. Ba ma bukatar kome.” Tsohon ya ce, “Na marabce ku a gidana. Bari ni ba ku duk abin da kuke bukata. Kada ku dai kwana a dandali.” Saboda haka sai kai shi zuwa gidansa ya ciyar da jakunansa. Bayan sun wanke ƙafafunsu, sai aka ba su abinci da abin sha. Yayinda suke jin wa kansu daɗi, sai waɗansu ’yan iska daga birnin suka kewaye gidan. Suna bubbuga ƙofar, suna kira tsohon da yake da gidan suna cewa, “Ka fito mana da mutumin nan a gidanka domin mu yi jima’i da shi.” Maigidan ya fita waje ya ce musu, “A’a, abokaina, kada ku yi abin kunyan nan. Da yake mutumin nan baƙona ne, kada ku yi rashin kunyan nan. Duba, ga ’yata da ba tă taɓa sanin namiji ba da kuma ƙwarƙwaransa. Zan fito muku da su a waje yanzu, za ku kuwa iya yin ko mene ne da kuke so da su. Amma wannan mutum, kada ku yi abin kunya.” Amma mutanen ba su saurare shi ba. Saboda haka mutumin ya ba da ƙwarƙwaransa, suka yi mata fyaɗe suka yi lalata da ita dukan dare, gari yana wayewa sai suka bar ta. Da safe matar ta koma gidan da maigidanta yake, ta fāɗi a ƙofa ta kwanta a can har rana ta yi. Sa’ad da maigidanta ya tashi da safe ya buɗe ƙofar gidan don yă fita ya ci gaba da tafiyarsa, sai ga ƙwarƙwararsa, ta fāɗi a bakin ƙofar gidan da hannuwanta a madogarar ƙofar. Ya ce mata, “Tashi; mu tafi.” Amma ba amsa. Sai ya sa ta a kan jakinsa ya kama hanyar gida. Da ya kai gida, sai ya ɗauki wuƙa ya yayyanka ƙwarƙwaransa gunduwa-gunduwa, kashi goma sha biyu ya aika da su a ko’ina a Isra’ila. Duk wanda ya gani, sai ya ce, “Ba a taɓa gani ko yin irin wannan abu ba, tun lokacin da Isra’ilawa suka fito daga Masar. Ku yi tunani wannan! Ku kuma yi la’akari! Ku gaya mana abin da za mu yi!” Sa’an nan dukan Isra’ilawa daga Dan zuwa Beyersheba kuma daga ƙasar Gileyad mutane kamar mutum guda suka fito suka taru a gaban Ubangiji a Mizfa. Shugabanni dukan kabilan mutane na kabilan Isra’ila suka zazzauna a wurarensu a taron jama’ar Allah, mayaƙa dubu ɗari huɗu masu ɗamara da takuba. (Mutanen Benyamin suka ji cewa Isra’ilawa sun haura zuwa Mizfa.) Sa’an nan Isra’ilawa suka ce, “Gaya mana yadda wannan mugun abu ya faru.” Sai Balawen, mijin matar da aka kashe ya ce, “Ni da ƙwarƙwarata mun zo Gibeya a Benyamin don mu kwana. Da dad dare mutanen Gibeya suka bi ni suka kewaye gidan da niyya su kashe ni. Suka yi wa ƙwarƙwarata fyaɗe, har ta mutu. Na ɗauki ƙwarƙwarata na yayyanka gunduwa-gunduwa na aika da shi ga kowane yankin gādon Isra’ila, domin sun aikata mugu abu da abin kunya a Isra’ila. To, dukanku Isra’ilawa, sai ku yi magana ku kuma yanke hukuncinku.” Dukan mutane suka tashi kamar mutum ɗaya, suna cewa “Ba waninmu da zai tafi gida. Sam, babu ko ɗayanmu da zai koma gidansa. Amma yanzu ga abin da za mu yi wa Gibeya. Za mu haura mu fāɗa yadda ƙuri’a ta nunar. Za mu ɗauko mutum goma a kowane mutum ɗari daga dukan kabilan Isra’ila, da ɗari a dubu, da kuma dubu a dubu goma, domin a tanada wa mayaƙan. Sa’an nan, sa’ad da mayaƙan suka iso Geba a Benyamin, za su yi da su daidai bisa ga muguntar da suka yi a Isra’ila.” Saboda haka dukan mutane Isra’ilawa suka taru suka kuma haɗu kamar mutum guda don su fāɗa wa birnin da yaƙi. Kabilan Isra’ila suka aika jakadu a ko’ina a cikin kabilar Benyamin cewa, “Wace irin mugunta ce wannan da kuka aikata? Yanzu fa sai ku fitar da waɗannan ’yan iskan da suka aikata wannan abu na Gibeya don mu kashe su mu kawar da mugunta daga Isra’ila!” Amma mutanen Benyamin ba su saurari ’yan’uwansu Isra’ilawa ba. Daga biranensu suka tattaru a Gibeya don su yaƙi Isra’ilawa. Nan da nan mutanen Benyamin suka tattara mayaƙa dubu ashirin da shida masu takuba daga biranensu, ban da mayaƙa ɗari bakwai da aka zaɓa daga mazauna a Gibeya. Cikin dukan mayaƙan nan akwai zaɓaɓɓu mutane ɗari bakwai waɗanda su bahagwai ne, kowanne yana iya harbin gashin guda na kai da majajjawa ba kuskure. Isra’ila kuwa, ban da Benyamin, sun tara mayaƙa masu takobi dubu ɗari huɗu, dukansu gwanayen yaƙi ne. Sai Isra’ilawa suka haura zuwa Betel suka nemi nufin Allah, suka ce, “Wane ne a cikinmu zai fara fāɗa wa mutanen Benyamin?” Ubangiji ya ce, “Yahuda ce za tă fara.” Kashegari sai Isra’ilawa suka tashi suka kafa sansani kusa da Gibeya. Mutanen Isra’ila suka fita yaƙi da mutane Benyamin suka kuma ja dāgār yaƙi a Gibeya. Mutanen Benyamin suka fito daga Gibeya suka kashe mutum dubu ashirin da biyu na Isra’ilawa a dāgār yaƙi a ranar. Amma mutanen Isra’ila suka ƙarfafa juna, suka sāke koma inda suka ja dāgā a rana ta farko. Isra’ilawa suka haura suka yi kuka a gaban Ubangiji, har yamma, suka nemi nufin Ubangiji. Suka ce, “Mu sāke koma yaƙi da mutanen Benyamin, ’yan’uwanmu?” Ubangiji ya ce, “Ku haura ku fāɗa musu.” Sai Isra’ilawa suka matsa kusa da Benyamin a rana ta biyu. A wannan lokaci, da mutanen Benyamin suka fito daga Gibeya don su yaƙe su, sai suka sāke kashe Isra’ilawa dubu goma sha takwas, dukansu ɗauke da takuba. Sa’an nan Isra’ilawa, dukan mutane, suka haura zuwa Betel, a can suka zauna suna kuka a gaban Ubangiji. Suka yi azumi a wannan rana har yamma suka miƙa hadayun ƙonawa da hadayun salama ga Ubangiji. Isra’ilawa suka nemi nufin Ubangiji (A kwanakin nan akwatin alkawarin Allah yana can, Finehas ɗan Eleyazar, ɗan Haruna, kuwa yana hidima a gabansa.) Suka ce, “Mu sāke haura mu yi yaƙi da mutanen Benyamin ’yan’uwanmu, ko a’a?” Ubangiji ya ce, “Ku je, gama gobe zan ba da su a hannuwanku.” Sa’an nan Isra’ila ta yi kwanto kewaya da Gibeya. Suka haura su kara da mutanen Benyamin a rana ta uku suka ja dāgā a Gibeya kamar dā. Mutanen Benyamin suka fito su same su aka kuma jawo su nesa da birnin. Suka fara karkashe Isra’ilawa kamar dā, har aka kashe wajen mutum talatin a filaye da kuma a hanyoyi, wadda take zuwa Betel da kuma wadda take zuwa Gibeya. Yayinda mutanen Benyamin suna cewa, “Muna cin nasara a kansu kamar dā,” Isra’ilawa kuwa suna cewa, “Mu yi ta jan da baya mu janye su daga birni zuwa kan hanyoyi.” Dukan mutanen Isra’ila suka taso daga wurarensu suka ja dāgā a Ba’al-Tamar, Isra’ilawan da suka yi kwanto a yammancin Geba kuwa suka fito. Sa’an nan jarumai Isra’ila dubu goma suka yi gaba suka kai wa Gibeya hari. Yaƙi kuwa ya yi zafi har mutane Benyamin ba su san masifa tana dab da su ba. Ubangiji kuwa ya fatattake mutanen Benyamin a gaban Isra’ila; a ranar kuwa Isra’ilawa sun kashe mutum 25,100 na mutanen Benyamin, dukansu ɗauke da takuba. Sa’an nan Benyamin suka ga an ci su. To, mutanen Isra’ila sun yi ta ja da baya daga mutanen Benyamin domin suna dogara ga waɗanda sa su yi kwanto kusa da Gibeya ne. Mutanen da suke kwanto suka yi wuf suka ruga cikin Gibeya, suka bazu suka kuma karkashe dukan waɗanda suke a birnin. Mutanen Isra’ila sun riga sun shirya da ’yan kwanton cewa su murtuke hayaƙi daga birnin, a sa’an nan ne mutanen Isra’ila za su juya su fāɗa wa mutane Benyamin da yaƙi. Mutanen Benyamin sun fara karkashe mutum talatin na Isra’ila, sai suka ce, “Muna cin nasara a kansu kamar dā.” Amma da alamar hayaƙi ya fara murtukewa daga birnin, sai mutanen Benyamin suka juya suka ga hayaƙi yana murtukewa ko’ina a cikin birnin zuwa sararin sama. Sa’an nan mutanen Isra’ila suka juyo musu, mutanen Benyamin kuwa suka tsorata domin sun gane masifa ta zo musu. Saboda haka suka tsere a gaban Isra’ila zuwa wajen hamada, amma ba su iya tsere wa yaƙin ba. Mutanen Isra’ila da suka fito daga cikin birnin suka karkashe su a can. Suka kewaye mutanen Benyamin, suka kore su, suka fatattake su a wajajen Gibeya a gabashi. Mutum dubu goma sha takwas na mutanen Benyamin suka mutu dukansu kuwa jarumai ne. Da suka juya suka juya suka tsere zuwa wajajen hamada zuwa dutsen Rimmon, Isra’ilawa suka kashe mutum dubu biyar a kan hanyoyi. Suka yi ta matsa wa mutanen Benyamin har zuwa Gidom suka kashe mutum dubu biyu kuma. A ranar kuwa mutanen Benyamin dubu ashirin da biyar ne aka kashe, dukansu jarumai. Amma mutane ɗari shida suka juya suka tsere wajajen hamada zuwa dutsen Rimmon, inda suka zauna wata huɗu. Mutanen Isra’ila suka koma wurin mutanen Benyamin suka kashe dukan waɗanda suke a birnin, tare da dabbobi da kome da suka samu. Dukan garuruwan da suka samu sun ƙone su ƙaf. Mutanen Isra’ila sun riga sun yi rantsuwa a Mizfa cewa, “Ba ɗayanmu da zai ba da ’yarsa aure ga mutumin Benyamin.” Sai mutanen suka tafi Betel, inda suka zauna a gaban Allah har yamma, suna tā da muryoyinsu suna kuka mai zafi. Suka ce, ya Ubangiji, Allah na Isra’ila, “Me ya sa wannan abu ya faru da Isra’ila? Don me kabila ɗaya daga Isra’ila za tă ɓace a yau?” Kashegari da sassafe mutane suka gina bagade suka miƙa hadaya ta ƙonawa da hadaya ta salama. Sa’an nan Isra’ilawa suka ce, “Wace kabila ce cikin kabilan Isra’ila ba tă zo taro a gaban Ubangiji ba?” Gama an yi rantsuwa cewa duk wanda ya kāsa zuwa taro a gaban Ubangiji a Mizfa lalle a kashe shi. To, Isra’ilawa suka yi juyayin ’yan’uwansu, mutanen Benyamin. “Yau an hallaka kabila daga cikin Isra’ila. Yaya za mu ba wa waɗanda suka rage mata, da yake mun riga mun yi rantsuwa a gaban Ubangiji, ba za mu ba su ɗaya daga ’ya’yanmu su aura ba?” Sa’an nan suka ce, “Wace kabila ce cikin kabilan Isra’ila ba tă zo taro a gaban Ubangiji a Mizfa ba?” Sai su gane cewa babu wani daga Yabesh Gileyad da ya zo sansani don taron. Gama da aka yi ƙidaya mutane, sai aka gane cewa babu wani daga mutanen Yabesh Gileyad da yake a can. Saboda haka sai taron ya umarci jarumai dubu goma sha biyu su je Yabesh Gileyad su karkashe waɗanda suke zaune a can, duk da mata da yara. Suka ce musu, “Ga abin da za ku yi. Ku karkashe duk namiji da kowace macen da ta riga ta san namiji.” Suka samu a cikin mutanen da suke zaune a Yabesh Gileyad mata ɗari huɗu da ba su taɓa kwana da namiji ba, suka kwashe su zuwa sansani a Shilo a Kan’ana. Sa’an nan dukan taro suka aika wa mutanen Benyamin da suke a Dutsen Rimmon cewa yaƙi ya ƙare, yanzu sai salama. Saboda haka mutanen Benyamin suka komo a lokacin aka kuma ba su matan Yabesh Gileyad nan da aka bari da rai. Amma matan ba su ishe su duka ba. Mutanen kuwa suka yi juyayi saboda mutanen Benyamin, domin Ubangiji ya yi gibi a cikin kabilan Isra’ila. Shugabannin taron suka ce, “Da matan Benyamin da aka hallaka, yaya za mu yi da mazan da suka ragu da ba su sami mata ba?” Suka ce, “Dole mutanen Benyamin da suka ragu su sami gādo, domin kada wata kabila a Isra’ila ta ɓace. Ba za mu iya ba su ’yan matanmu su zama matansu ba, da yake mu Isra’ilawa mun riga mun yi wannan rantsuwa cewa, ‘La’ananne ne wanda ya ba da ’yarsa aure ga mutum Benyamin.’ Sai suka tuna, akwai bikin Ubangiji da sukan yi shekara-shekara a Shilo ya yi kusa. Shilo yana arewancin Betel, kudu da Lebona, gabas da hanyar da take tsakanin Betel da Shekem.” Saboda haka suka cewa mutanen Benyamin, “Ku je ku ɓuya a gonakin inabi ku lura. Sa’ad da ’yan matan Shilo suka fito waje don su yi rawa, ku fito a guje daga gonakin inabi, kowannenku yă kama wa kansa mata daga cikin ’yan matan Shilo, ku tafi ƙasar Benyamin. Sa’ad da iyayensu maza ko ’yan’uwansu suka kawo mana ƙara, za mu ce musu, ‘Ku yi mana alheri ku bar su, domin ba mu samo musu mata ba lokacin yaƙi, ku kuma marasa laifi ne, tun da yake ba ku ba da ’ya’yan matanku gare su ba.’ ” Haka mutanen Benyamin suka yi. Yayinda ’yan matan suke rawa, kowane mutum ya kama ɗaya ya yi gaba da ita ta zama matarsa. Sa’an nan suka komo ƙasar gādonsu suka sāke giggina garuruwan suka kuwa zauna a cikinsu. A lokacin, Isra’ilawa sun bar wurin suka tafi gida zuwa ga kabilansu da zuriyoyinsu, kowane zuwa gādonsa. A kwanakin Isra’ila ba ta da sarki; kowa ya yi abin da ya ga dama. A kwanakin da mahukunta suke mulki an yi yunwa a ƙasar, sai wani mutum daga Betlehem a Yahuda tare da matarsa da ’ya’yansu maza biyu, suka tafi su yi zama na ɗan lokaci a ƙasar Mowab. Sunan mutumin, Elimelek ne, sunan matarsa Na’omi; sunayen ’ya’yan nan nasu biyu, su ne Malon da Kiliyon. Su Efratawa ne daga Betlehem ta Yahuda. Suka kuwa tafi Mowab suka zauna a can. To, Elimelek mijin Na’omi ya rasu, aka bar ta da ’ya’yanta maza biyu. Suka auri mata Mowabawa, sunan ɗaya Orfa ɗayan kuma Rut. Bayan sun zauna a can kamar shekara goma, sai Malon da Kiliyon suka mutu su ma, aka kuma bar Na’omi babu ’ya’yanta maza biyu da kuma mijinta. Sa’ad da ta ji a Mowab cewa Ubangiji ya zo don yă taimaki mutanensa ta wurin tanada musu da abinci, sai Na’omi tare da surukanta suka shirya su koma gida daga can. Tare da surukanta biyu suka bar inda suka zauna suka kuma kama hanya da za tă komar da su zuwa ƙasar Yahuda. Sai Na’omi ta ce wa surukanta biyu, “Ku koma, kowannenku, zuwa gidan mahaifiyarta. Bari Ubangiji yă nuna muku alheri yadda kuka nuna wa matattun nan da kuma gare ni. Bari Ubangiji yă sa kowannenku ta sami hutu a gidan wani miji.” Sa’an nan ta sumbace su suka kuma yi kuka da ƙarfi suka ce mata, “Za mu tafi tare da ke zuwa ga mutanenki.” Amma Na’omi ta ce, “Ku koma gida, ’ya’yana mata. Don me za ku tafi tare da ni? Zan ƙara samun waɗansu ’ya’ya maza da za su zama mazanku ne? Ku koma gida ’ya’yana mata; na tsufa ainun da zan sāke samun wani miji. Ko ma na yi tsammani har yanzu ina da bege, ko ma na sami miji a wannan dare na kuma haifi ’ya’ya maza, za ku jira sai sun yi girma? Za ku ci gaba da kasance babu aure saboda su? A’a, ’ya’yana mata. Ina da baƙin ciki ƙwarai fiye da ku, domin hannun Ubangiji ya yi gāba da ni!” A kan wannan suka sāke ɓarke da kuka. Sa’an nan Orfa ta sumbaci surukarta ta yi bankwana, amma Rut ta manne mata. Sai Na’omi ta ce, “Duba, ’yar’uwanki ta koma zuwa ga mutanenta da kuma allolinta. Ki koma tare da ita.” Rut Amma Rut ta amsa, “Kada ki roƙe ni in bar ki ko in koma daga gare ki. Inda za ki, zan tafi, kuma inda za ki zauna, zan zauna. Mutanenki, za su zama mutanena kuma Allahnki, zai zama Allahna. Inda za ki mutu zan mutu, zan mutu a can kuma za a binne ni. Bari Ubangiji ya hukunta ni da tsanani sosai, in wani abu in ba mutuwa ce ta raba ke da ni ba.” Sa’ad da Na’omi ta gane cewa Rut ta ƙudura tă tafi tare da ita, sai ta daina nema tă koma. Saboda haka matan biyu suka ci gaba da tafiya sai da suka isa Betlehem. Da suka isa Betlehem, sai dukan garin ya ruɗe saboda su, matan kuwa suka ce, “Na’omi ce wannan kuwa?” Ta ce musu, “Kada ku kira ni Na’omi. Ku kira ni Mara gama Maɗaukaki ya sa raina ya yi ɗaci sosai. In tafi cikakke, amma Ubangiji ya dawo da ni ba kome. Don me kuke kirana Na’omi? Ubangiji ya wahalshe ni, Maɗaukaki ya kawo mini masifa.” Na’omi fa ta koma daga Mowab tare da Rut mutuniyar Mowab, surukarta, suka kai Betlehem a lokacin da ake fara girbin sha’ir. To, fa, Na’omi tana da dangi a gefen mijinta da iyalin Elimelek, mutum mai martaba, mai suna Bowaz. Sai Rut mutuniyar Mowab ta ce wa Na’omi, “Bari in tafi gonaki in yi kala raguwar hatsi a bayan duk wanda na sami tagomashi daga gare shi.” Na’omi ta ce mata, “Ki je, ’yata.” Saboda haka ta tafi ta fara kala a gonaki a bayan masu girbi. Sai ya zamana, ta sami kanta tana aiki a gonar da take ta Bowaz, wanda yake daga dangin Elimelek. Sai ga Bowaz ya iso daga Betlehem ya gai da masu girbi, “ Ubangiji yă kasance tare da ku!” Sai suka amsa, “ Ubangiji yă albarkace ka!” Sai Bowaz ya tambayi shugaban masu girbinsa, “Wace yarinya ce wannan?” Shugaban ya amsa, “Ita ce mutuniyar Mowab da ta zo daga Mowab tare da Na’omi. Ta ce, ‘Ina roƙo a bar ni in bi bayan masu girbin in yi kala.’ Haka ta shiga cikin gonar ta kuwa yi aiki tun da safe har zuwa yanzu, sai ɗan hutun da ta yi kaɗan.” Saboda haka Bowaz ya ce wa Rut, “’Yata, ki saurare ni. Kada ki tafi ki yi kala a wani gona, kada kuma ki tafi daga nan. Ki tsaya nan tare da ’yan matana bayi. Ki lura da gonar da mutanena suke girbi, ki bi su tare da ’yan matana. Na riga na faɗa wa mazan kada su taɓa ke. Kuma duk sa’ad da kika ji ƙishirwa, ki tafi ki ɗebo ruwa daga tulunan da mazan suka cika.” Jin haka, sai ta rusuna da fuskata har ƙasa ta ce, “Me ya sa na sami irin wannan tagomashi a idanunka da har ka lura da ni, ni da nake baƙuwa?” Bowaz ya amsa, “An faɗa mini duka game da abin kika yi domin surukarki tun mutuwar mijinki, yadda kika bar mahaifinki da mahaifiyarki da kuma ƙasarki kika zo ki yi zama da mutanen da ba ki taɓa sani ba. Bari Ubangiji yă sāka maka saboda abin da ka yi. Bari Ubangiji, Allah na Isra’ila yă sāka maka a yalwace, a ƙarƙashin fikafikan da ka sami mafaka.” Ta ce, “Bari in ci gaba da samun tagomashi a idanunka ranka yă daɗe. Ka ta’azantar da ni ka kuma yi wa baranyarka magana mai alheri ko da yake ban kai matsayi ɗaya daga cikin bayinka ’yan mata ba.” A lokacin cin abinci Bowaz ya ce mata, “Zo nan. Ki ɗebo burodi ki tsoma cikin ruwan inabi.” Da ta zauna tare da masu girbin, sai ya ba ta gasasshe hatsi. Ta ci duk abin da take so har ta bar ragowa. Da ta tashi don tă yi kala, sai Bowaz ya yi umarni wa samarinsa cewa, “Ko ta tara daga cikin dammuna, kada ku wulaƙanta ta. Ku kuma riƙa zarar mata waɗansu daga dammunan don ta ɗauka, kada ku kwaɓe ta.” Saboda haka Rut ta yi kala a gonar har yamma. Sa’an nan ta sussuka hatsin sha’ir da ta kalata ta sami kamar efa. Ta ɗauka ta koma gari sai surukarta ta ga yawan abin da ta kalato. Rut kuma ta fitar da ragowar abin da ta ci bayan ta ƙoshi ta ba ta. Surukarta ta tambaye ta, “Ina kika yi kala a yau? Ina kika yi aiki? Albarka ta tabbata ga mutumin nan ta ya lura da ke!” Sai Rut ta faɗa wa surukarta game da wurin wanda ta yi ta aiki. Ta ce, “Sunan mutumin da na yi aiki da shi a yau Bowaz ne.” Sai Na’omi ta ce wa surukarta, “ Ubangiji yă yi masa albarka! Bai daina nuna alheri ga masu rai da matattu ba.” Ta ƙara da cewa, “Wannan mutum danginmu ne na kusa; shi ɗaya daga cikin danginmu mai fansa.” Sa’an nan Rut mutuniyar Mowab ta ce, “Ya ma ce mini, ‘Ki riƙa bin ma’aikatana sai sun ƙare yin girbin dukan hatsina.’ ” Na’omi ta ce wa Rut surukarta, “Zai fi miki kyau, ’yata ki riƙa tafiya da ’yan matansa, domin a gonar wani dabam mai yiwuwa a yi miki lahani.” Saboda haka Rut ta tsaya kusa da bayi mata na Bowaz don tă yi kala sai da girbin sha’ir da na alkama suka ƙare. Ta kuwa zauna tare da surukarta. Wata rana Na’omi surukar Rut ta ce mata, “’Yata, bai kamata in nema miki gida, inda za a tanada miki da kyau? Bowaz wanda kike aiki da bayinsa ’yan mata ba danginmu ne na kusa ba? Da daren yau zai sussuka sha’ir nasa a masussuka. Ki yi wanka ki fesa turare, ki kuma sa tufafinki mafi kyau. Sa’an nan ki gangara zuwa masussuka, amma kada ki bari yă san cewa kina a can sai ya gama ci da sha. Sa’ad da ya kwanta, ki lura da inda yake kwance. Sa’an nan ki tafi ki buɗe ƙafafunsa ki kwanta. Zai faɗa miki abin da za ki yi.” Rut ta amsa ta ce “Zan yi abin da kika faɗa.” Saboda haka ta gangara zuwa masussuka ta kuma yi dukan abin da surukarta ta ce ta yi. Sa’ad da Bowaz ya gama ci da sha yana kuma cikin farin ciki, sai ya tafi ya kwanta a ƙarshen tarin hatsi. Rut kuwa ta sulalle ta je ta buɗe ƙafafunsa ta kwanta. Da tsakar dare sai wani abu ya firgitar da mutumin, ya kuwa juya sai ya tarar da mace kwance a ƙafafunsa. Sai ya yi tambaya ya ce, “Ke wace ce?” Ta amsa ta ce, “Ni ce baranyarka Rut, ka rufe ni ta mayafinka da yake kai dangi, mai fansa ne na kusa.” Sai ya amsa ya ce, “ Ubangiji yă albarkace ki ’yata. Wannan alheri ya fi wannan da kika nuna da farko. Ba ki gudu kin bi saurayi, mai arziki ko matalauci ba. Yanzu kuwa ’yata kada ki ji tsoro. Zan yi miki dukan abin da kika roƙa. Dukan ’yan’uwana na gari sun san cewa ke mace ce mai halin kirki. Ko da yake gaskiya ne ni dangi ne na kusa, amma akwai dangi mai fansa mafi kusa fiye da ni. Ki kwana a nan, da safe kuwa in yana so yă fansa, to, da kyau, sai yă fansa. Amma in ba ya niyya, tabbatacce, na rantse da Ubangiji mai rai zan yi. Ki kwanta a nan sai da safe.” Saboda haka ta kwanta a ƙafafunsa sai da safe, amma ta tashi kafin a gane wani, sai ya ce, “Kada ki bar wani yă san cewa mace ta zo masussuka.” Ya kuma ce, “Ki kawo gyalenki da kika yafa ki shimfiɗa shi a nan.” Sa’ad da ta yi haka, sai ya zuba mudu shida na sha’ir ya sa mata a kai. Sa’an nan ya koma gari. Sa’ad da Rut ta koma wurin surukarta Na’omi ta tambaye ta “Yaya aka yi ’yata?” Sai ta faɗa mata dukan abin da Bowaz ya yi mata ta kuma ƙara da cewa, “Ya ba ni waɗannan mudu shida na sha’ir, yana cewa, ‘Kada ki koma wurin surukarki hannu wofi.’ ” Sai Na’omi ta ce, “Ki jira, ’yata, sai kin ga abin da zai faru. Gama mutumin ba zai huta ba sai an warware batun a yau.” Ana cikin haka Bowaz ya haura zuwa ƙofar gari ya tafi ya zauna a can. Sa’ad da dangi mai fansan da ya yi zance ya iso, Bowaz ya ce, “Zo nan abokina ka zauna.” Saboda haka ya ratso ya zauna. Bowaz kuwa ya kira dattawa guda goma na garin ya ce, “Ku zauna a nan,” suka kuwa zauna. Sa’an nan ya ce wa dangin nan mai fansa, “Na’omi, wadda ta dawo daga Mowab, tana so ta sayar da filin da yake na ɗan’uwanmu Elimelek. Na ga ya kamata in jawo hankalinka ga batun in kuma ba da shawara ka saye shi a gaban waɗannan da suke zazzaune a nan da kuma a gaban dattawan jama’a. In kana so ka fanshe shi, to, sai ka yi. Amma in ba za ka yi ba, sai ka faɗa mini, don in sani. Gama babu wani mai izinin yin haka sai kai, ni ne kuwa na biye.” Sai ya ce, “Zan fansa.” Sa’an nan Bowaz ya ce, “A ranar da ka saya filin daga Na’omi da kuma daga Rut mutuniyar Mowab, ka sayi gwauruwar marigayin nan, domin ka riƙe sunan marigayin da kuma kayansa.” Da jin haka, sai dangin nan mai fansa ya ce, “To, ba zan iya fanshe shi ba don kada in yi wa nawa mallakar rauni. Za ka iya fanshe shi wa kanka. Ni dai ba zan iya ba.” (To, a kwanakin can a Isra’ila, domin a tabbatar da fansa da kuma musayar da mallaka, mutum zai cire takalminsa ya ba wa ɗayan. Wannan ita ce hanyar tabbatar da al’amarin a hukumance a cikin Isra’ila.) Saboda haka dangin nan mai fansa ya ce wa Bowaz, “Saye shi wa kanka.” Sai ya cire takalminsa. Sa’an nan Bowaz ya yi shela wa dattawa da kuma dukan mutane, “A yau ku ne shaidu cewa na saya daga Na’omi dukan mallakar Elimelek, Kiliyon da kuma Malon. Na kuma ɗauki Rut mutuniyar Mowab, gwauruwar Malon a matsayin matata domin sunan mamaci da kuma mallakarsa yă ci gaba, domin kada sunansa yă ɓace daga cikin iyali ko daga tarihin gari. A yau ku ne shaidu!” Sai dattawan da kuma dukan waɗanda suke a ƙofar suka ce, “Mu shaidu ne. Bari Ubangiji yă sa macen da take zuwa cikin gidanka ta zama kamar Rahila da Liyatu, waɗanda tare suka gina gidan Isra’ila. Bari ka sami martaba a cikin Efrata ka kuma zama sananne cikin Betlehem. Ta wurin ’ya’yan da Ubangiji zai ba ka ta wurin wannan mace, bari iyalinka yă zama kamar na Ferez, wanda Tamar ta haifa wa Yahuda.” Sai Bowaz ya ɗauki Rut ta kuwa zama matarsa. Sa’an nan ya kwana da ita, Ubangiji kuma ya sa ta yi ciki, ta haifi ɗa. Mata suka ce wa Na’omi, “Yabo ya tabbata ga Ubangiji, wanda a wannan rana bai bar ki ba tare da dangi mai fansa ba. Allah yă sa yă zama sananne a dukan Isra’ila! Zai sabunta rayuwarki yă adana ki a tsufanki. Gama surukarki wadda take ƙaunarki wadda kuma take mafi kyau gare ki fiye da ’ya’ya maza bakwai, ta haife shi.” Sai Na’omi ta ɗauki yaron, ta kwantar da shi a cinyarta ta kuma kula da shi. Matan da suke zama a wurin suka ce, “Na’omi ta sami yaro.” Suka kuwa ba shi suna Obed. Shi ne ya haifi Yesse, mahaifin Dawuda. Ga asalin zuriyar Ferez. Ferez shi ne mahaifin Hezron, Hezron ya haifi Ram, Ram ya haifi Amminadab, Amminadab ya haifi Nashon, Nashon ya haifi Salmon, Salmon ya haifi Bowaz, Bowaz ya haifi Obed, Obed ya haifi Yesse, Yesse kuwa ya haifi Dawuda. Akwai wani mutum daga Ramatayim, mutumin Zuf daga ƙasar tuddan Efraim, sunansa Elkana, ɗan Yeroham, shi jikan Elihu ɗan Tohu, tattaɓa kunnen Zuf, mutumin Efraim. Yana da mata biyu, ɗaya sunanta Hannatu, ɗayan kuwa ana kiranta Feninna. Ita Feninna tana da ’ya’ya, amma Hannatu ba ta da ’ya’ya. Shekara-shekara wannan mutum yakan haura daga garinsa zuwa Shilo domin yin sujada da miƙa hadayu ga Ubangiji Maɗaukaki. A can kuwa ’ya’yan Eli maza biyu, Hofni da Finehas su ne firistoci na Ubangiji. Duk sa’ad da rana ta kewayo don Elkana yă miƙa hadaya, yakan ba da kashin nama ga matarsa Feninna da dukan ’ya’yanta maza da mata. Amma Hannatu kuwa sai yă ba ta babban rabo gama yana ƙaunarta ko da yake Ubangiji ya kulle mahaifarta. Saboda Ubangiji ya kulle mahaifarta, sai kishiyarta ta dinga tsokanarta don tă ba ta haushi. Wannan ya ci gaba shekara da shekaru. Duk lokacin da Hannatu ta haura zuwa haikalin Ubangiji, sai kishiyarta tă tsokane ta har tă yi ta kuka tă kuma ƙi cin abinci. Elkana mijinta kuwa yakan ce mata, “Hannatu don me kike kuka? Me ya sa ba za ki ci abinci ba? Don me kika karaya? Ashe, ban fi ’ya’ya goma a gare ki ba?” Wata rana sa’ad da suka gama ci da sha a Shilo, Hannatu ta miƙe tsaye. Eli firist kuwa yana zaune a kujera a bakin ƙofar haikalin Ubangiji. A cikin baƙin ciki, Hannatu ta yi kuka mai zafi ta yi addu’a ga Ubangiji. Ta yi ta cewa, “Ya Ubangiji Maɗaukaki. In har ka dubi baƙin cikin baiwarka, ka tuna da ni, ba ka kuma manta da baiwarka ba, amma ka ba ta ɗa, ni ma zan miƙa shi ga Ubangiji dukan rayuwarsa, aska kuwa ba za tă taɓa kansa ba.” Yayinda take addu’a ga Ubangiji, Eli ya lura da bakinta. Hannatu tana addu’a a zuci, ba a jin muryarta, sai leɓunanta ne kawai suna motsi. Eli kuwa ya yi tsammani ta bugu ne. Sai ya ce mata, “Har yaushe za ki ci gaba da maye? Ki daina shan ruwan inabi.” Hannatu ta ce, “Ba haka ba ne, ranka yă daɗe, ni mace ce da take cikin matsala ƙwarai da gaske. Ban sha ruwan inabi ba, ko wani abu mai sa maye, ina dai faɗa wa Ubangiji abin da yake damuna ne. Kada ka yi zato baiwarka ’yar iska ce. Ina addu’a a nan saboda yawan azaba da baƙin cikin da nake ciki.” Eli ya ce, “In haka ne, to, ki sauka lafiya, Allah na Isra’ila kuma yă ba ki abin da kika roƙa daga gare shi.” Ta ce, bari baiwarka tă sami tagomashi a idonka. Sai ta yi tafiyarta ta je ta ci wani abu, fuskarta kuwa ba tă ƙara kasance da baƙin ciki ba. Kashegari da sassafe suka tashi suka yi sujada a gaban Ubangiji, sai suka koma garinsu a Rama. Elkana kuwa ya kwana da matarsa Hannatu, Ubangiji kuma ya tuna da ita. Ana nan sai Hannatu ta yi ciki, ta kuma haifi ɗa. Ta ba shi suna Sama’ila; tana cewa, “Domin na roƙe shi daga wurin Ubangiji.” Da shekara ta kewayo, sai Elkana da iyalinsa suka sāke tafi Shilo domin su yi hadaya ga Ubangiji, yă kuma cika alkawarin da ya yi. Hannatu kuwa ba tă bi su ba. Ta gaya wa mijinta cewa, “Sai bayan na yaye yaron, zan kai shi in miƙa shi a gaban Ubangiji, yă kuma kasance a wurin koyaushe.” Elkana mijinta ya ce mata, “Ki yi abin da kika ga ya fi miki kyau. Ki jira har sai bayan kin yaye shi. Ubangiji dai ya cika maganarsa.” Saboda haka matar ta tsaya a gida, ta yi ta renon ɗanta har ta yaye shi. Bayan ta yaye shi, sai ta ɗauki yaron tare da bijimi bana uku, da mudun gari, da salkan ruwan inabi, ta kawo su a gidan Ubangiji a Shilo. Bayan an yanka bijimin, sai suka kawo yaron wurin Eli. Sai ta ce masa, “Ranka yă daɗe, ba ka gane ni ba? Ai, ni ce matar da ta taɓa tsayawa a gabanka, tana addu’a ga Ubangiji. Wannan yaron ne na roƙa daga wurin Ubangiji, ya kuwa ba ni abin da na roƙa daga gare shi. Saboda haka, na ba da shi ga Ubangiji muddin ransa, zai zama na Ubangiji.” A can kuwa ya yi wa Ubangiji sujada. Sai Hannatu ta yi addu’a ta ce, “Zuciyata tana farin ciki a cikin Ubangiji; a cikin Ubangiji an sa ina jin daɗi ƙwarai. Na buɗe bakina na yi wa abokan gābana dariya. Kai! Ina murna domin ka cece ni! “Babu wani mai tsarki kamar Ubangiji babu wani, in ban da kai; babu wani dutse kamar Allahnmu. “Ka daina maganganu na girman kai ka kuma daina faɗin kalmomin ɗaga kai; gama Ubangiji Allah ne masani daga gare shi kuma ana auna ayyuka. “An kakkarya bakkuna masu yaƙi, amma su da ka raunana an ba su makaman ƙarfi. Waɗanda a dā suna da abinci sosai; yanzu suna ƙodago saboda abinci, masu fama da yunwa kuwa sun daina jin yunwa. Ita da take bakararriya, ta haifi ’ya’ya bakwai amma ita da tana da ’ya’ya da yawa, ta zama mai baƙin ciki. “Ubangiji ne ke kawo mutuwa, yă kuma rayar yana kai ga kabari, yă kuma tā da. Ubangiji ne yakan aika da talauci da kuma dukiya; yakan ƙasƙantar yă kuma ɗaukaka. Yakan tā da matalauci daga ƙura, yă kuma ɗaga mai bukata daga tarin toka; yă zaunar da su tare da ’ya’yan sarki; yă kuma sa su gāji mulki na ɗaukaka. “Harsashin duniya na Ubangiji ne; a bisansu ne ya kafa duniya. Zai kiyaye ƙafafun masu tsarki, amma mugaye za su lalace cikin duhu. “Ba bisa ga ƙarfi mutum ba ne mutum ke nasara; waɗanda suke gāba da Ubangiji za su hallaka. Zai yi musu tsawa daga sama, Ubangiji zai hukunta dukan duniya. “Zai ba wa sarkinsa ƙarfi, yă kuma ɗaukaka shafaffensa.” Sa’an nan, Elkana ya koma gida a Rama amma yaron ya yi hidima a gaban Ubangiji a ƙarƙashin Eli firist. ’Ya’yan Eli firist, mutane ne masu mugunta. Ba su ɗauki Ubangiji a bakin kome ba. Al’ada ce ga firistoci da mutane cewa in wani ya miƙa hadaya, yayinda nama yake kan wuta, bawan firist zai zo da babban cokali mai yatsu, zai soka cokali mai yatsun a tukunyar, ko butar da ake dafan naman. Duk abin da cokali mai yatsun ya cako daga tukunyar, ya zama na firist. Haka aka yi ta yi wa Isra’ilawan da suka zo miƙa hadaya a Shilo. Tun ma kafin a ƙona kitse, bawan firist yakan zo yă ce wa mutumin da yake miƙa hadaya, “Ka ba wa firist nama domin yă gasa, ba zai karɓi dafaffen nama daga wurinka ba, sai ɗanye.” In kuwa mutumin ya ce masa, “Bari kitse yă ƙone tukuna, sa’an nan ka ɗiba duk abin da kake so.” Sai bawan yă ce masa, “A’a, ka ba ni yanzu, in ka ƙi kuwa zan ɗiba ƙarfi da yaji.” Wannan zunubin samarin ya yi muni ƙwarai a gaban Ubangiji, domin sun wulaƙanta hadayar Ubangiji, ƙwarai da gaske. Amma yaron nan Sama’ila, yana hidima a gaban Ubangiji yana sanye da efod na lilin. Kowace shekara mahaifiyarsa takan ɗinka ’yar taguwa ta kai masa sa’ad da ita da mijinta suka je miƙa hadaya ta shekara. Eli yakan sa wa Elkana da matarsa albarka, yă ce, Ubangiji yă ba ka waɗansu ’ya’ya ta wurin matan nan, maimakon wanda ta roƙa daga Ubangiji, ta kuma ba da shi ga Ubangiji. Bayan haka sai su koma gida. Hannatu kuwa ta sami alfarma daga Ubangiji. Ta yi ciki. Ana cikin haka Sama’ila kuwa sai girma yake ta yi a gaban Ubangiji. To, Eli kuwa ya tsufa ƙwarai, yana kuma jin labari duk abin da ’ya’yansa suke yi wa dukan Isra’ila, da yadda suke lalata da matan da suke hidima a bakin ƙofar Tentin Sujada. Saboda haka ya ce musu, “Don me kuke yin waɗannan abubuwa? Na sami labari daga wurin mutane a kan duk ayyukan muguntanku. A’a, ’ya’yana ba labari mai kyau nake ji cikin mutanen Ubangiji ba. In mutum ya yi wa wani laifi Allah yakan kāre shi; amma in mutum ya yi wa Ubangiji zunubi wa zai kāre shi?” Duk da haka, ’ya’yansa ba su kula da gargaɗin mahaifinsu ba, domin nufin Ubangiji ne yă hallaka su. Yaron nan Sama’ila ya dinga girma cikin kwarjini da cikin tagomashi a gaba Ubangiji da mutane. Wani mutum ya zo wurin Eli ya ce masa, “Ga abin da Ubangiji ya ce, ‘Ashe ban bayana kaina sosai ga mahaifinka lokacin da yake a Masar a ƙarƙashin Fir’auna ba? Na zaɓi mahaifinka daga cikin dukan kabilar Isra’ila yă zama firist nawa don yă yi hidima a bagade, don yă ƙona turare mai ƙanshi, don kuma yă sanya doguwar riga a gabana. Na kuma ba wa iyalin mahaifinka dukan hadaya ta ƙonawa da Isra’ila suka miƙa. Don me kuke rena hadayata da sadakokina da na ƙayyade domin mazaunina? Don me kake girmama ’ya’yanka fiye da ni ta wurin cinye sashe mafi kyau na kowane hadayar da mutanena Isra’ila suka miƙa?’ “Saboda haka Ubangiji Allah na Isra’ila ya ce, ‘Na yi alkawari cewa gidanka da gidan mahaifinka za su yi mini hidima a gabana har abada.’ Amma, yanzu Allah ya ce, ba zai yiwu ba; waɗanda suke girmama ni; Ni ma zan girmama su. Amma waɗanda suke ƙasƙantar da ni, haka za a ƙasƙantar da su. Lokaci yana zuwa sa’ad da zan rage ƙarfinka da ƙarfin iyalin gidan mahaifinka. Domin kada a sāke samun tsohon mutum a zuriyarka. Za ka zama da ɓacin rai a mazaunina ko da yake za a yi wa Isra’ila alheri. A zuriyarka ba za a taɓa samun tsohon mutum ba. Kowannenku da ban kashe daga hidima a bagadena ba, za a bar shi don yă cika idanunka da hawaye da kuma baƙin ciki, dukan sauran zuriyarka kuwa za su mutu a ƙuruciyarsu. “ ‘Abin da kuma ya faru da ’ya’yanka biyu Hofni da Finehas zai zama alama a gare ka; saboda mutuwarsu za tă zama a rana ɗaya. Zan tayar wa kaina amintaccen firist wanda zai aikata abin da nake so yă yi, zan kuwa ba shi zuriya da koyaushe za su yi aiki a gaban zaɓaɓɓen sarkina. Sa’an nan duk wanda ya rage a zuriyarka zai zo yă durƙusa a gabansa yă roƙi kuɗi da abinci, zai kuma roƙa a yardar masa yă taimaki firistoci da aiki domin yă sami abin da zai ci.’ ” Yaron nan Sama’ila ya yi hidima a gaban Ubangiji a ƙarƙashin Eli. A waɗannan kwanaki kuwa jin magana daga wurin Ubangiji ba safai ba, babu kuma wahayi da yawa. Wata rana da dare Eli da idanunsa sun kusa makancewa har ba ya iya gani sosai yana kwance a inda ya saba. Fitilar Allah kuwa tana ci, ba tă mutu ba tukuna, Sama’ila kuma na kwance a haikali na Ubangiji inda akwai akwatin Allah. Sai Ubangiji ya kira Sama’ila. Sama’ila ya amsa ya ce, “Ga ni.” Sai ya ruga wajen Eli ya ce, “Ga ni, gama ka kira ni.” Eli ya ce, “Ɗana ban kira ba, je ka kwanta”. Saboda haka ya tafi ya kwanta. Ubangiji ya sāke kiransa ya ce, “Sama’ila!” Sama’ila ya tashi kuma ya je wurin Eli ya ce, “Ga ni, gama ka kira ni.” Amma Eli ya ce, “Ban kira ka ba, ɗana koma ka kwanta.” Sama’ila dai bai riga ya san Ubangiji ba tukuna. Ba a kuma taɓa bayyana maganar Ubangiji a gare shi ba tukuna ba. Ubangiji ya kira Sama’ila sau na uku, Sama’ila kuma ya tashi ya tafi wurin Eli, “Ga ni, gama ka kira ni.” Sai Eli ya gane cewa Ubangiji ne ke kira yaron. Saboda haka, Eli ya gaya wa Sama’ila cewa, “Je ka kwanta, in kuma ya kira ka, ka ce masa, ‘Ya Ubangiji ka yi magana gama bawanka yana saurara.’ ” Sama’ila ya koma ya kwanta a wurin kwanciyarsa. Ubangiji kuma ya zo ya tsaya a wurin, yana kira ya ce, “Sama’ila, Sama’ila!” Kamar yadda ya kira a lokutan baya. Sai Sama’ila ya ce, “Yi magana gama bawanka yana saurara.” Ubangiji ya ce wa Sama’ila, “Duba ina dab da yin wani abu a Isra’ila da zai sa kunne kowa da yake ji, yă ji tsoro. A ranar zan cika dukan maganar da na yi game da Eli da iyalinsa, daga farko har ƙarshe. Gama na gaya masa zan hukunta gidansa har abada saboda zunubin da yake sane da shi; ’ya’yansa sun wulaƙantar da kansu, shi kuma bai tsawata musu ba. Saboda haka na rantse a kan gidan Eli, ‘Ba za a taɓa shafe laifin gidan Eli da hadaya ko baiko ba.’ ” Sama’ila kuwa ya kwanta har safe, sa’an nan ya buɗe ƙofofin gidan Ubangiji. Ya ji tsoro yă gaya wa Eli wahayin, amma Eli ya kira shi ya ce, “Sama’ila, ɗana.” Sama’ila ya ce, “Ga ni.” Eli ya ce, mene ne ya ce maka? Kada ka ɓoye mini. Allah ya yi da kai har ma fiye in ka ɓoye mini kome da ya ce maka. Don haka sai Sama’ila ya gaya masa kome bai ɓoye masa kome ba. Sa’an nan Eli ya ce, “Shi ne Ubangiji bari yă yi abin da ya yi kyau a gare shi.” Ubangiji kuwa yana tare da Sama’ila har girmansa bai kuma bar ko ɗaya daga maganarsa ta kāsa cika ba. Dukan Isra’ila daga Dan har Beyersheba suka shaida amincin Sama’ila annabi ne na Ubangiji. Ubangiji kuwa ya dinga bayyana a Shilo, a nan ya bayyana kansa ga Sama’ila ta wurin maganarsa. Duk sa’ad da Sama’ila ya yi magana dukan Isra’ila sukan saurare shi. Isra’ilawa suka fita yaƙi da Filistiyawa. Isra’ilawa suka kafa sansani a Ebenezer, Filistiyawa kuma a Afek. Filistiyawa suka tunƙuro mayaƙansu domin su sadu da Isra’ilawa, yaƙi kuwa ya yi tsanani har Isra’ilawa suka sha kashi a hannun Filistiyawa. Filistiyawa suka kashe Isra’ilawa kusan mutum dubu huɗu a bakin dāgā. Lokacin da mayaƙan suka komo sansani, dattawan Isra’ilawa suka yi tambaya suka ce, “Me ya sa Ubangiji ya sa muka sha ɗibga a hannun Filistiyawa? Bari mu kawo akwatin alkawarin Ubangiji daga Shilo. Domin yă tafi tare da mu yă ba mu nasara kan abokan gābanmu.” Saboda haka mutanen suka aika waɗansu maza zuwa Shilo, suka kuwa tafi suka kawo akwatin alkawarin Ubangiji Maɗaukaki wanda yake zaune tsakanin Kerubobi. ’Ya’yan Eli biyun nan Hofni da Finehas suna wurin tare da akwatin alkawarin Ubangiji. Da aka shigo da akwatin alkawarin Ubangiji a cikin sansani, sai Isra’ilawa suka tā da babbar murya har ƙasa ta jijjiga. Da jin wannan, Filistiyawa suka yi tambaya suka ce, “Me ke kawo wannan ihu mai ƙarfi haka a sansanin Isra’ilawa?” Da suka gane cewa akwatin alkawarin Ubangiji ne ya shiga sansanin, sai Filistiyawa suka ji tsoro, suka ce, “Wani allah ya shiga cikin sansanin. Mun shiga uku! Ba a taɓa yin wani abu haka ba. Kaiton mu! Wa zai kuɓutar da mu daga hannun waɗannan manyan alloli? Su ne allolin da suka buga Masarawa da irin annoba masu yawa a jeji. Ku yi ƙarfin hali, ku yi mazantaka, ku Filistiyawa, domin kada ku zama bayin Ibraniyawa kamar yadda suke a gare ku. Ku yi mazantaka, ku yi yaƙi.” Saboda haka Filistiyawa suka yi yaƙi, Isra’ilawa kuwa suka sha ɗibga, kowane mutum kuwa ya gudu zuwa tentinsa. Kisan kuwa ya yi muni ƙwarai. Isra’ilawa sun rasa mayaƙa dubu talatin. Aka ƙwace akwatin alkawarin Ubangiji. Aka kuma kashe ’ya’yan Eli biyu, Hofni da Finehas. A wannan rana wani mutumin Benyamin ya ruga da bakin dāgā ya shigo Shilo, taguwarsa a yage, kansa kuma a rufe da ƙasa. Da ya iso sai ga Eli zaune a kujera kusa da hanya yana kallo, domin tsoron da yake da shi saboda akwatin alkawarin Allah. Da mutumin ya shigo a garin ya ba da labarin abin da ya faru sai dukan gari ya ruɗe da ihu. Eli ya ji ihun ya yi tambaya ya ce, mene ne dalilin wannan ihu? Mutumin ya rugo wurin Eli, wanda yake da shekaru tasa’in da takwas da haihuwa, idanunsa kuma ƙarfi ya ƙare, baya iya gani. Mutumin ya gaya wa Eli cewa, “Shigowata ke nan daga bakin dāgā. Na kuɓuce daga can yau ɗin nan.” Eli ya ce, “Me ya faru da ’ya’yana?” Mutumin da ya kawo labarin ya ce, “Isra’ilawa sun gudu a gaban Filistiyawa, mayaƙan kuma sun sha mummunar ɗibga. ’Ya’yanka Hofni da Finehas su ma sun mutu. Aka kuma ƙwace akwatin alkawarin Allah.” Da ya ambaci akwatin alkawarin Allah, sai Eli ya fāɗi da baya daga kujeransa kusa da ƙofa, wuyarsa ta karye, ya kuma mutu domin ya tsufa ƙwarai. Ya yi shugabancin Isra’ila shekaru arba’in. Matar Finehas, ɗansa tana da ciki a lokacin ta kuma kusa haihuwa. Sa’ad da ta ji labari cewa an ƙwace akwatin alkawarin Allah, ta kuma labarin surukinta da mijinta sun mutu, sai ta shiga naƙuda, ta kuma haihu. Amma naƙuda ta sha ƙarfinta. Da tana mutuwa, matan da suke lura da ita suka ce, “Kada ki karaya kin haifi ɗa namiji.” Amma ba tă ba da amsa ko tă kula ba. Ta ba wa yaron suna Ikabod, ma’ana “Ɗaukaka ta rabu da Isra’ila”, domin an ƙwace akwatin alkawarin Allah, domin kuma mutuwar surukinta da na mijinta. Ta ce, “Ɗaukaka ta rabu da Isra’ila, gama an ƙwace akwatin alkawarin Allah.” Bayan Filistiyawa sun ƙwace akwatin alkawarin Allah, sai suka ɗauke shi daga Ebenezer suka kai shi Ashdod. Sa’an nan suka ɗauki akwatin alkawarin suka kai shi cikin haikalin gunkinsu Dagon, suka ajiye kusa da Dagon. Kashegari da safe da mutanen Ashdod suka farka sai ga Dagon ya fāɗi a gaban akwatin alkawarin Ubangiji. Sai suka ɗauki Dagon suka ajiye a wurin zamansa. Amma kashegari kuma da safe suka farka sai ga Dagon ya fāɗi a ƙasa a gaban akwatin alkawarin Ubangiji! Kansa ya fashe, hannuwansa kuma sun kakkarye sun zube a madogarar ƙofa; jikinsa ne kaɗai ya rage. Saboda haka firistocin Dagon da waɗanda suke sujada a haikalin Dagon ba sa taka bakin ƙofar Dagon a Ashdod har wa yau. Hannun Ubangiji kuwa ya yi nauyi a bisa Ashdod da kewayenta. Ya kawo hallaka ga dukansu, ya kuma buga su da marurai. Da mutanen Ashdod suka ga abin da yake faruwa, sai suka ce, “Lalle Akwatin Alkawarin Allah na Isra’ila ba zai kasance da mu ba, domin hannunsa yana da nauyi a kanmu da bisan Dagon allahnmu.” Saboda haka suka kira duka shugabannin Filistiyawa suka tambaye su, suka ce, “Me za mu da akwatin alkawarin Allahn Isra’ila?” Sai suka amsa suka ce, “A ɗauki akwatin alkawarin Allah na Isra’ila a kai shi Gat.” Sai suka ɗauki akwatin alkawarin Allah na Isra’ila. Amma bayan sun kai shi can, sai hannun Ubangiji ya yi gāba da birnin, aka jefa shi cikin wani mawuyacin hali. Ya buga mutanen birnin da marurai, babba da yaro. Sai suka aika da akwatin alkawarin Allah zuwa Ekron. Yayinda akwatin alkawarin Allah yana shiga cikin Ekron, mutanen Ekron suka yi ihu, suka ce, “An kawo mana akwatin alkawarin Allah na Isra’ila domin yă kashe mu da mutanenmu.” Saboda haka suka kira ga dukan shugabannin Filistiyawa suka ce, “Ku komar da akwatin alkawarin Allah na Isra’ila inda ya fito; in ba haka ba zai kashe mu da mutanenmu.” Gama mutuwa ta cika garin da tsoro. Hannun Allah ya yi nauyi a kansa. Waɗanda ba su mutu ba kuwa, sun kamu da marurai. Kukan birnin kuwa ta hau har zuwa sama. Lokacin da akwatin alkawarin Ubangiji ya kai wata bakwai a ƙasar Filistiyawa. Filistiyawa suka kira firistoci da bokaye suka ce, “Me za mu yi da akwatin alkawarin Ubangiji? Ku gaya mana yadda za mu komar da shi inda ya fito.” Suka ce, in za ku komar da akwatin alkawarin Allah na Isra’ila kada ku komar da shi hannu wofi; amma ku tabbata kun aika da hadaya don laifi zuwa wurinsa. Sa’an nan za ku warke ku kuma san dalilin da ya sa bai cire hannunsa a kanku ba. Filistiyawa suka ce, “Wace irin hadaya don laifi za mu aika masa?” Suka ce, “Marurai biyar na zinariya da ɓeraye biyar na zinariya bisa ga yawan sarakunan Filistiyawa. Saboda annoba iri ɗaya ce ta buga ku da shugabanninku. Ku yi siffofin marurai da na ɓeraye da suke hallaka gari, ku ba da girma ga Allah na Isra’ila. Wataƙila zai ɗauke hukuncinsa daga gare ku da allolinku da kuma ƙasarku. Me ya sa kun taurare kanku kamar yadda Masarawa da Fir’auna suka yi? Da ya ba su matsanancin wahala, ba su bar Isra’ilawa suka tafi hanyarsu ba? “Yanzu fa ku shirya sabon keken shanu da shanu biyu masu ba wa ’ya’yansu nono, waɗanda ba a taɓa sa musu karkiya ba. Ku daure keken shanu wa shanun, amma ku tsare ’yan maruƙansu a gida. Ku ɗauki wani akwati ku sa siffofin zinariyan nan a ciki, waɗanda za su zama kyautai na shafen laifi, ku ajiye kusa da Akwati na UBANGIJI. Bayan haka sai ku sa keken shanun da akwatin a hanya, ku bar shi yă tafi. Amma ku zuba ido ku ga in ya haura zuwa yankinsa, zuwa Bet-Shemesh, to, Ubangiji ne ya kawo mana babban masifar a kanmu. Amma in bai bi ta nan ba, za mu san cewa ba shi ne ya buge mu ba, tsautsayi ne kawai.” Suka yi haka. Suka ɗauki shanun tatsa guda biyu suka ɗaura musu keken shanu, suka tsare ’yan maruƙansu a gida. Suka aza akwatin alkawarin Ubangiji a bisa keken shanun tare da akwatin siffofin ɓerayen zinariya da siffofin maruran. Sai shanun suka miƙe zuwa Bet-Shemesh. Suka bi hanya daidai, ba su juya dama ko hagu ba. Shugabannin Filistiyawa suka bi har zuwa iyakar ƙasar Bet-Shemesh. A lokacin kuwa mutanen Bet-Shemesh suna girbin alkamansu a kwari da suka ɗaga ido suka hangi akwatin alkawarin Ubangiji, sai suka yi farin ciki ganinsa. Keken shanun ya zo filin Yoshuwa a Bet-Shemesh ya tsaya a gefen wani babban dutse. Mutanen suka faskare keken shanun suka miƙa shanun hadaya ta ƙonawa ga Ubangiji. Lawiyawa suka saukar da akwatin alkawarin Ubangiji tare da babban akwati mai siffofin zinariya na ɓeraye da marurai suka ajiye su a kan ƙaton dutse. A wannan rana mutanen Bet-Shemesh suka miƙa hadaya ta ƙonawa da waɗansu hadayu ga Ubangiji. Shugabanni biyar na Filistiyawan nan suka ga duk abin da ya faru, suka koma zuwa Ekron a ranar. Waɗannan su ne siffofi marurai na zinariya waɗanda Filistiyawa suka aika domin miƙa hadaya don laifi ga Ubangiji, ɗaya domin Ashdod, ɗaya domin Gaza, ɗaya domin Ashkelon, ɗaya domin Gat, ɗaya kuma domin Ekron. Filistiyawa kuma suka aika da siffofin ɓeraye biyar na zinariya. Yawan ɓerayen sun yi daidai da yawan garuruwan sarakunan nan biyar na Filistiyawa. Garuruwan sun ƙunshi waɗanda aka gina katangar birni kewaye da su, da kuma ƙauyukansu. Babban dutsen da suka ajiye akwatin alkawarin Ubangiji, ya zama shaida har wa yau a filin Yoshuwa a Bet-Shemesh. Amma Allah ya kashe waɗansu mutum saba’in na mutanen Bet-Shemesh domin sun leƙa cikin akwatin alkawarin Ubangiji. Mutane kuwa suka yi makoki domin Ubangiji ya hallaka mutane da yawa. Mutanen Bet-Shemesh suka yi tambaya suka ce, wa zai iya tsaya a gaban Ubangiji Allah Mai Tsarki? Wurin wa akwatin alkawari zai je daga nan? Sai suka aiki manzanni zuwa Kiriyat Yeyarim suka ce, “Filistiyawa sun komo da akwatin alkawarin Ubangiji, ku zo ku ɗauka ku kai wajenku.” Mutanen Kiriyat Yeyarim suka ɗauki akwatin alkawarin Ubangiji. Suka kai a gidan Abinadab da ke kan tudu, suka keɓe Eleyazar ɗansa yă lura da akwatin alkawarin Ubangiji. Akwatin Alkawarin ya daɗe a Kiriyat Yeyarim ya kai shekara ashirin cif. Sai dukan mutanen Isra’ila suka yi makoki suka nemi Ubangiji. Saboda haka Sama’ila ya yi magana da dukan gidan Isra’ila ya ce, in har da zuciya ɗaya kuke juyowa ga Ubangiji sai ku raba kanku da baƙin alloli da gunkin nan Ashtarot, ku ba da kanku ga Ubangiji. Ku yi masa bauta shi kaɗai, zai kuɓutar da ku daga hannun Filistiyawa. Sai Isra’ilawa suka rabu da gumakan Ba’al da Ashtarot suka bauta wa Ubangiji kaɗai. Sama’ila ya ce, “Ku tattara dukan Isra’ila a Mizfa, ni kuwa zan yi addu’a ga Ubangiji dominku.” Sa’ad da suka taru a Mizfa, suka kawo ruwa suka zuba a gaban Ubangiji. A wannan rana suka yi azumi suka tuba, suka ce, “Mun yi wa Ubangiji zunubi!” Sama’ila kuwa ya zauna a Mizfa ya yi mulkin Isra’ilawa. Da Filistiyawa suka ji cewa Isra’ila sun taru a Mizfa, sai shugabanninsu suka zo don su yaƙe Isra’ila. Da Isra’ilawa suka ji labarin, sai suka tsorata saboda Filistiyawa. Suka ce wa Sama’ila, “Kada ka fasa kai kukanmu ga Ubangiji Allahnmu saboda mu, don yă cece mu daga hannun Filistiyawa.” Sama’ila ya kama ɗan rago ya miƙa shi ɗungum hadaya ta ƙonawa ga Ubangiji. Ya yi roƙo ga Ubangiji a madadin Isra’ila, Ubangiji kuwa ya amsa addu’arsa. Lokacin da Sama’ila yana miƙa hadaya ta ƙonawa, Filistiyawa suka matso kusa don su yi yaƙi da Isra’ila. A ranar Ubangiji ya sa babban tsawa ya ruɗar da Filistiyawa har suka gudu a gaban Isra’ilawa. Isra’ilawa suka fito a guje daga Mizfa suka fafari Filistiyawa suka yi ta karkashe su a hanya har kwarin Bet-Kar. Sa’an nan Sama’ila ya ɗauki dutse ya kafa tsakanin Mizfa da Shen, ya sa masa suna, Ebenezer ma’ana, “Har zuwa wannan lokaci Ubangiji ya taimake mu.” Ta haka Isra’ilawa suka ci Filistiyawa. Daga ranan Filistiyawa ba su ƙara yin nasara a kan Isra’ila ba. Ubangiji ya yi gāba da Filistiyawa har ƙarshen zamanin Sama’ila. Filistiyawa suka mayar wa Isra’ila da garuruwan da suka ƙwato, wato, daga Ekron zuwa Gat, dukan yankin ƙasarsu da yake ƙarƙashin ikon Filistiyawa. Aka kuma sami zaman lafiya tsakanin Isra’ilawa da Amoriyawa. Sama’ila kuwa ya ci gaba da mulkin Isra’ila dukan rayuwarsa. Shekara-shekara Sama’ila yakan fita rangadi zuwa Betel, da Gilgal da Mizfa inda yakan yi musu shari’a. Amma yakan komo Rama inda gidansa yake, a nan yakan yi wa Isra’ila shari’a. A nan ne kuma ya gina wa Ubangiji bagade. Da Sama’ila ya tsufa, sai ya naɗa ’ya’yansa maza su zama alƙalan Isra’ila. Sunan ɗansa na fari Yowel, na biyu kuwa Abiya. Suka yi alƙalanci a Beyersheba. Amma ’ya’yansa ba su bi hanyar mahaifinsu ba. Suka mai da hankalinsu ga neman kuɗi da cin hanci, suna kuma danne gaskiya. Sai dukan shugabannin Isra’ila suka taru suka zo wurin Sama’ila a Rama. Suka ce masa, “Ka tsufa, ’ya’yanka kuma ba sa bin hanyarka, saboda haka sai ka naɗa sarkin da zai bi da mu kamar yadda sauran ƙasashe suke da su.” Amma Sama’ila bai ji daɗi sa’ad da suka ce, “Ka ba mu sarki da zai bi da mu.” Sai ya yi addu’a ga Ubangiji. Ubangiji kuwa ya ce masa, “Ka saurari dukan maganganun da mutanen suke gaya maka. Ai, ba kai ba ne suka ƙi, ni ne suka ƙi in zama sarkinsu. Haka suka yi daga tun daga ranar da na fitar da su daga Masar har zuwa yau, suka ƙi ni, suka bauta wa waɗansu alloli, haka ma suke yi maka. Yanzu ka saurare su amma ka yi musu kashedi sosai, ka sa su san abin da sarkin da zai bi da su zai yi.” Sama’ila kuwa ya ce wa mutanen da suke roƙo yă naɗa musu sarki dukan abin da Ubangiji ya faɗa. Ya ce musu, “Ga abin da sarkin da zai yi mulkinku zai yi. Zai kwashe ’ya’yanku yă sa su yi aiki da kekunan yaƙi da dawakansa, waɗansu za su riƙa gudu a gaban keken yaƙinsa. Zai sa waɗansu su zama shugabannin mutum dubu-dubu da kuma na hamsin-hamsin. Waɗansu za su yi masa noma da girbi. Waɗansu za su ƙera masa makaman yaƙi da kayayyaki don keken yaƙinsa. Zai sa ’ya’yanku mata yin aikin turare da dafe-dafe da kuma toye-toye. Zai karɓi gonakinku mafi kyau da gonakin inabinku da gonakin zaitunku yă ba wa ma’aikatansa. Zai kuma karɓi zakan hatsinku da na inabinku yă ba shugabannin fadarsa da sauran masu hidimarsa. Zai ƙwace bayinku maza da mata, da shanunku, da jakunanku mafi kyau domin su yi masa aiki. Zai karɓi zakan dabbobinku, ku kanku za ku zama bayinsa. Sa’ad da ranar ta zo, za ku yi kuka ku nemi a fishe ku daga sarkin da kuka zaɓa, Ubangiji kuwa ba zai ji ku ba.” Amma mutanen suka ƙi jin Sama’ila, sai suka ce, “A’a, mu dai, muna son sarki yă bi da mu.” Ta haka za mu zama kamar sauran ƙasashe, mu kasance da sarkin da zai bi da mu, yă tafi tare da mu zuwa yaƙe-yaƙe. Da Sama’ila ya ji duk maganganun da mutanen suka faɗa, sai ya mayar wa Ubangiji. Ubangiji kuwa ya ce, “Ka saurare su, ka naɗa masu sarki.” Sa’an nan Sama’ila ya ce wa mutanen Isra’ila, “Kowa yă koma garinsa.” An yi wani mutum, attajiri daga kabilar Benyamin, sunansa Kish, ɗan Abiyel, jikan Zeror na iyalin Bekorat daga dangin Afiya. Yana da ɗa mai suna Shawulu, wani kyakkyawan saurayi. A cikin mutanen Isra’ila ba wanda ya fi shi kyau, ya kuma fi kowa tsaye. To, ana nan sai jakunan Kish mahaifin Shawulu suka ɓace. Kish ya ce wa ɗansa, “Tashi ka tafi tare da wani daga cikin bayi, ku nemo jakunan.” Suka bi ta ƙasar tudu ta Efraim, suka ratsa ta ƙasar Shalisha amma ba su same su ba. Suka bi ta ƙasar Shalim, a can ma ba su same su ba sai suka bi ta ƙasar Benyamin, a can ma ba su same su ba. Da suka iso gunduman Zuf, sai Shawulu ya ce wa bawan da yake tare da shi, “Zo mu koma kada mahaifina yă bar damuwa a kan jakuna, yă shiga damuwa game da mu.” Amma bawan ya amsa ya ce, “Duba, a wannan gari akwai wani mutumin Allah, ana ganin girmansa ƙwarai kuma duk abin da ya faɗa yakan zama gaskiya. Mu tafi can wurinsa wataƙila zai gaya mana hanyar da za mu bi.” Shawulu ya ce wa bawan, “Idan muka isa can, me za mu ba wa mutumin? Ga shi abinci guzurinmu duk ya ƙare, ba mu da wani abin da za mu kai wa mutumin Allahn nan. Me muke da shi?” Bawan ya sāke ce masa, “Duba ina da kwatar azurfar da zan ba wa mutumin Allah don yă gaya mana wace hanya ce za mu bi.” (A dā a Isra’ila, in wani yana so yă nemi nufin Allah, mutumin yakan ce, “Zo mu tafi wajen mai duba.” Gama wanda ake ce da shi annabi a yanzu, a dā ana kiransa mai duba ne.) Shawulu ya ce wa bawansa, “Madalla, zo mu tafi.” Sai suka kama hanya suka nufi birnin da mutumin Allah yake. Sa’ad da suke haura tudun zuwa birnin, sai suka sadu da waɗansu ’yan mata sun fito za su ɗiban ruwa. Sai suka tambaye su, suka ce, “Mai duba yana nan?” ’Yan matan suka ce, “I, yana nan, ai, ga shi ma a gabanku, ku hanzarta. Shigowarsa ke nan a garin, domin yau mutane za su ba da sadaka a bagade a kan tudu. Da zarar kun shiga garin, za ku same shi kafin yă tafi cin abinci a wurin yin sadakar, can kan tudu. Gama jama’a ba za su ci ba, sai ya kai can ya sa albarka a sadakar, sa’an nan waɗanda aka gayyata su ci. Ku haura da sauri, za ku same.” Suka haura zuwa birnin, da shigarsu sai ga Sama’ila ya nufo su a hanyarsa ta zuwa kan tudu. Kafin zuwa Shawulu, Ubangiji ya riga ya bayyana wa Sama’ila ya ce, “Gobe war haka zan aiko maka da wani mutum daga ƙasar Benyamin. Ka keɓe shi shugaban mutanena Isra’ila. Shi zai cece mutanena daga hannun Filistiyawa. Na ga azabar mutanena gama kukansu ya hauro wurina.” Da Sama’ila ya hangi Shawulu, Ubangiji ya ce masa, “Ga mutumin da na yi maka magana, shi ne zai bi da mutanena.” Shawulu ya sami Sama’ila a hanyar shiga gari, sai ya tambaye shi ya ce, “Ina roƙonka ka nuna mini gidan mai duba?” Sama’ila ya ce, “Ni ne mai duban, ka yi gaba zuwa ka tudu, gama yau za ka ci tare da ni, da safe kuma in sallame ka, in gaya muku duk abin da yake a zuciyarku. Game da jakunan da suka ɓace kwana uku kuwa, kada ka damu, an same su. Ga wane ne Isra’ila ta sa dukan zuciya, in ba ga kai da kuma dukan iyalin mahaifinka ba?” Shawulu ya ce, “Ashe, ni ba mutumin Benyamin ba ne daga ƙaramar kabila ta Isra’ila? Dangina kuma ba shi ba ne mafi kakanni a cikin kabilar Benyamin ba? Yaya za ka faɗa mini irin wannan magana.” Sa’an nan Sama’ila ya shiga da Shawulu da baransa ya zaunar da su a gaban waɗanda aka gayyata, mutanen sun kai wajen mutum talatin. Sama’ila ya ce wa mai dahuwa, “Kawo naman da na ba ka, wannan da na ce ka ajiye dabam.” Sai mai dahuwan ya ɗauko cinya da abin da yake bisanta ya kawo ya ajiye a gaban Shawulu. Sama’ila ya ce, “Ga abin da aka ajiye dominka. Ka ci, gama an keɓe shi dominka saboda wannan hidima daga lokacin da na ce, ‘Na gayyaci baƙi.’ ” Shawulu kuwa ya ci tare da Sama’ila a ranan nan. Bayan suka gangaro daga tudu zuwa cikin gari, Sai Sama’ila ya yi magana da Shawulu a ɗakin samansa. Da asuba sai suka tashi, Sama’ila ya kira Shawulu daga ɗakin sama ya ce, “Ka shirya, zan sallame ka.” Da Shawulu ya shirya, sai Sama’ila da Shawulu suka fita waje tare. Suna dab da ƙarshen gari, sai Sama’ila ya ce wa Shawulu, “Ka ce wa bawanka yă yi gaba, kai ka ɗan dakata a nan tukuna, domin in ba ka saƙo daga Allah.” Sai Sama’ila ya ɗauki ’yar kwalabar mai, ya zuba man ɗin wa Shawulu a kansa, ya yi masa sumba yana cewa, “ Ubangiji ya keɓe ka shugaba bisa gādonsa. Sa’ad da ka rabu da ni yau, za ka sadu da mutum biyu kusa da kabarin Rahila a Zelza, a yankin Benyamin. Za su ce maka, ‘An sami jakunan da ka fita nema, yanzu haka mahaifinka ya bar damuwa kan jakunan ya koma damuwa a kanka, yana cewa, yaya zan gan ɗana?’ “Sa’an nan za ka ci gaba daga nan sai ka kai wajen babban itace na Tabor. Waɗansu mutum uku za su sadu da kai a hanyarsu zuwa wurin yin wa Allah sujada a Betel. Ɗaya yana ɗauke da ’yan awaki uku, ɗaya yana ɗauke da burodi uku, ɗayan kuma yana ɗauke da salkar ruwan inabi. Za su gaishe ka, su ba ka burodi biyu, kai kuwa sai ka karɓa. “Bayan wannan, za ka tafi Gebiya ta Allah, inda sansanin Filistiyawa yake. Kana shiga garin, za ka sadu da jerin gwanon annabawa suna gangarowa daga tudu, ana kaɗa garaya, ana bugan ganguna, ana hura sarewa, ana kuma bugan molo, a gabansu, su kuma za su yi ta annabci. Ruhun Ubangiji zai sauko a kanka da iko, za ka kuma yi annabci tare da su. Za a canja ka ka zama dabam. Da zarar waɗannan alamu sun cika, sai ka aikata duk abin da kana iya yi gama Allah yana tare da kai. “Ka sha gabana zuwa Gilgal. Lalle zan gangara wurinka domin in miƙa hadaya ta ƙonawa da hadayu na salama. Sai ka jira ni kwana bakwai sai na zo wurinka na kuma gaya maka abin da za ka yi.” Da Shawulu ya juya zai bar Sama’ila, sai Allah ya canja wa Shawulu zuciya, alamun nan kuwa suka cika a ranar. Da suka iso Gibeya, jerin gwanon annabawa suka sadu da shi Ruhun Allah kuma ya sauko a kansa da iko, sai ya shiga yin annabci tare da su. Sa’ad da dukan waɗanda suka san shi a dā suka gan shi yana annabci tare da annabawa, sai suka tambayi juna, suka ce, “Me ya faru da ɗan Kish? Shawulu ma yana cikin annabawa ne?” Wani mutumin da yake zama a can ya ce, “Wane ne kuma mahaifinsu?” Ta haka sai wannan ya zama karin magana cewa, “Shawulu ma yana cikin annabawa?” Bayan da Shawulu ya gama annabci sai ya haura ya tafi tudu. Sai ɗan’uwan mahaifin Shawulu ya tambaye shi da baransa ya ce, “Ina kuka je?” Shawulu ya ce, “Mun tafi neman jakuna, amma da ba mu same su ba sai muka tafi wurin Sama’ila.” Ɗan’uwan mahaifin Shawulu ya ce, “Faɗa mini abin da Sama’ila ya ce maka.” Shawulu ya ce, “Ya tabbatar mana cewa an riga an sami jakuna.” Amma bai gaya wa ɗan’uwan mahaifinsa abin da Sama’ila ya ce game da sarauta ba. Sama’ila ta tattara mutanen Isra’ila a gaban Ubangiji a Mizfa ya ce musu, “Ga abin da Ubangiji, Allah na Isra’ila ya ce, ‘Na fito da Isra’ila daga Masar, na kuma cece ku daga hannun Masarawa da dukan mulkokin da suka wahalshe ku.’ Amma yanzu kun ƙi Allahnku wanda ya cece ku daga dukan masifu da wahaloli. Kuka ce, ‘Sam, a naɗa mana sarki.’ Saboda haka yanzu sai ku zo gaban Ubangiji kabila-kabila da iyali-iyali.” Sa’ad da Sama’ila ya kawo dukan Isra’ila gaba, kabila-kabila, sai aka zaɓi kabilar Benyamin ta wurin jefa ƙuri’a. Sai ya kawo kabilar Benyamin gaba, iyali-iyali, aka zaɓi iyalin Matri. A ƙarshe aka zaɓi Shawulu ɗan Kish. Amma da aka neme shi sai ba a same shi ba. Suka ƙara nemi bayani daga Ubangiji suka ce, “Mutumin ya zo nan kuwa?” Ubangiji ya ce, “I, ga shi can, ya ɓuya cikin kayayyaki.” Suka ruga suka kawo shi. Da ya tsaya cikin mutane, sai ya fi kowa tsayi. Sama’ila ya ce wa dukan mutane, “Kun ga wanda Ubangiji ya zaɓa ko? Ba wani kamar sa a cikin dukan mutane.” Sai mutane suka tā da murya suka ce, “Ran sarki yă daɗe.” Sama’ila kuwa ya bayyana wa mutane ƙa’idodin sarauta. Ya rubuta su cikin littafi ya ajiye a gaban Ubangiji. Sa’an nan ya sallame mutane, kowa ya koma gidansa. Shawulu ma ya tafi gidansa a Gibeya tare da waɗansu jarumawan da Allah ya taɓa zuciyarsu. Amma waɗansu ’yan iska suka ce, “Yaya wannan mutum zai iya cetonmu?” Suka rena shi suka ƙi su kawo masa kyautai. Amma Shawulu bai ce uffam ba. Nahash mutumin Ammon ya haura ya kewaye Yabesh Gileyad da yaƙi. Dukan mutanen Yabesh suka ce masa, “Ka ƙulla amana da mu, mu kuwa za mu bauta maka.” Amma Nahash ya ce, “Zan ƙulla amana da ku kawai a kan sharaɗin cewa zan ƙwaƙulo idon dama na kowannenku, ta haka za a kunyata Isra’ila.” Dattawan Yabesh suka ce masa, “Ka ba mu kwana bakwai don mu aika manzanni a dukan ƙasar Isra’ila idan ba mu sami wanda zai cece mu ba, za mu ba da kanmu gare ka.” Da manzannin suka zo Gibeya garin Shawulu, suka gaya wa mutane wannan sharaɗin, suka yi kuka mai zafi. A daidai wannan lokacin kuwa Shawulu yana dawowa daga gona tare da shanunsa na noma, sai ya ce, “Me ya faru, mutane suna kuka haka?” Sai suka faɗa masa abin da mutanen Yabesh suka faɗa musu. Da Shawulu ya ji, sa Ruhun Allah ya sauko a kansa da iko, ya husata ƙwarai. Ya ɗauki shanu biyu, ya yayyanka su gunduwa-gunduwa, ya aika da su ko’ina a ƙasar Isra’ila ta wurin manzanni cewa, “Duk wanda bai fita ya bi Shawulu da Sama’ila ba, haka za a yi da shanunsa.” Mutanen suka ji tsoron Ubangiji suka fita gaba ɗaya kamar mutum guda. Mutanen Isra’ila sun kai dubu ɗari uku. Mutanen Yahuda kuma dubu talatin, sa’ad da Shawulu ya tara su a Bezek. Suka ce wa ’yan aikan da suka zo, “Ku faɗa wa mutanen Yabesh Gileyad, ‘Gobe, kafin rana tă yi zafi, za ku sami ceto.’ ” Sa’ad da ’yan aikan suka tafi, suka ba da saƙon nan ga mutanen Yabesh, sai suka farin ciki. Suka ce wa Ammonawa, “Gobe za mu miƙa wuya gare ku, ku kuma yi duk abin da kuka ga dama.” Gari yana wayewa, sai Shawulu ya raba mutane kashi uku, a sa’a ta ƙarshe na daren sai suka fāɗa wa sansanin Ammonawa, suka kuma karkashe su har lokacin da rana ta yi zafi. Waɗanda suka kuɓuce kuwa suka warwatsu, har babu biyunsu da aka bari tare. Sai mutane suka ce wa Sama’ila, “Su wa suka ce, ‘Shawulu zai yi mulkinmu?’ A kawo mana su mu kashe.” Shawulu ya ce, “Ba wanda zai mutu yau, gama Ubangiji ya kuɓutar da Isra’ila a wannan rana.” Sai Sama’ila ya ce wa mutane, “Ku zo mu tafi Gilgal, a can za a yi wankan sarauta.” Don haka dukan mutane suka tafi Gilgal, suka tabbatar da Shawulu sarki a gaban Ubangiji. A can suka miƙa hadaya ta salama a gaban Ubangiji, Shawulu kuwa da dukan Isra’ila suka yi babban liyafa. Sama’ila ya ce wa Isra’ilawa duka, “Na saurari abubuwan da kuka faɗa mini, na kuma naɗa muku sarki. Yanzu kuna da sarki a matsayin shugaba, ni kuwa na tsufa har da furfura, yarana maza kuma suna tare da ku. Na yi shugabancinku tun ina yaro. Ga ni a gabanku. Idan na yi wani abin da ba daidai ba sai ku faɗa a gaban Ubangiji, da gaban sarkin da ya keɓe. Ko na taɓa ƙwace saniya ko jakin wani? Ko na taɓa cuce wani, ko in danne hakkinsa? Ko na taɓa cin hanci daga hannun ɗayanku? Idan na taɓa yi ɗaya daga cikin waɗannan, sai ku faɗa mini, zan kuwa mayar masa.” Suka ce, “Ba ka cuci ko danne hakkin kowa ba, ba ka ƙwace kome daga hannun kowa ba.” Sama’ila ya ce musu, “ Ubangiji yă zama shaida a kanku, shafaffensa kuma yă zama shaida a wannan rana cewa ba ku same ni da wani laifin kome ba.” Suka ce, “I, shi ne shaida.” Sa’an nan Sama’ila ya ce wa mutane, Ubangiji ne ya naɗa Musa da Haruna suka fitar da kakanninku daga Masar. Yanzu ku tsaya nan zan yi fito-na-fito da ku da shaida a gaban Ubangiji kan dukan ayyuka masu alherin da Ubangiji ya aikata saboda ku da kakanninku. Bayan da Yaƙub da ’ya’yansa suka shiga Masar suka yi kukan neman taimako daga Ubangiji, Ubangiji kuwa ya aika musu da Musa da Haruna. Su ne suka kawo kakanni-kakanninku daga Masar suka zauna a nan. Amma suka manta da Ubangiji Allahnsu, shi kuma ya bashe su a hannun Sisera shugaban rundunar Hazor da kuma hannun Filistiyawa da sarkin Mowab wanda suka yi yaƙi da su. Suka yi kuka a gaban Ubangiji suka ce, “Mun yi zunubi mun bar Ubangiji, muka bauta wa Ba’al da Ashtarot. Amma ka cece mu yanzu daga hannun abokan gābanmu, mu kuwa za mu bauta maka.” Sai Ubangiji ya aiki Yerub-Ba’al da Bedan da Yefta da Sama’ila, ya cece ku daga hannun abokan gābanku a kowane gefe domin ku sami cikakken zaman lafiya. Amma da kuka ga Nahash sarkin Ammonawa yana matsowa yă yaƙe, sai kuka ce mini, “Sam, muna so sarki yă shugabance mu.” Ko da yake Ubangiji Allahnku ne yake mulkinku. Yanzu ga sarkinku da kuka zaɓa wanda kuka nema, ga shi Ubangiji ya naɗa muku sarki. In kuka ji tsoron Ubangiji, kuka bauta masa, kuka yi masa biyayya, ba ku kuwa ƙi bin umarninsa ba, in kuma ku da sarkin da yake mulkinku kun bi Ubangiji Allahnku, to, za ku zauna lafiya. Amma in ba ku yi biyayya ga Ubangiji ba, in kuma kuka ƙi bin umarnansa, fushinsa zai zauna a kanku. Yanzu ku tsaya tsit ku ga abin da Ubangiji ke dab da yi a gabanku. Ba lokacin yankan alkama ke nan ba? Zan roƙi Ubangiji yă aiko da tsawa da ruwan sama, za ku kuwa gane wace irin mugunta kuka yi a gaban Ubangiji sa’ad da kuka roƙa a ba ku sarki. Sai Sama’ila ya roƙi Ubangiji, a ranar kuwa Ubangiji ya aiko da tsawa da ruwan sama. Dukan mutane suka ji tsoron Ubangiji da kuma Sama’ila. Dukan mutane suka ce wa Sama’ila, “Ka yi addu’a ga Ubangiji Allahnka saboda bayinka, domin kada mu mutu, gama mun ƙara wa kanmu zunubi da muka roƙa a yi mana sarki.” Sama’ila ya ce, “Kada ku ji tsoro.” Kun yi waɗannan mugunta duk da haka kada ku bar bin Ubangiji, amma ku bauta wa Ubangiji da dukan zuciyarku. Kada ku bi alloli marasa amfani. Ba za su iya yi muku kome nagari ba, ba kuwa za su iya cece ku ba, gama ba su da amfani. Saboda suna mai girma da Ubangiji yake da shi, ba zai taɓa ƙin mutanensa ba. Gama Ubangiji ya ji daɗi da ya yi ku mutanensa. Ni kam ba zai taɓa yiwu in yi wa Ubangiji zunubi ta wurin ƙin yin addu’a dominku ba. Zan koya muku hanyar da tana da kyau da ta kuma cancanta. Amma ku amince za ku ji tsoron Ubangiji, ku bauta masa da aniya da dukan zuciyarku, kuna da manyan abubuwan da ya yi muku. Amma in kuka duƙufa cikin aikin mugunta da ku da sarkinku za a hallaka ku. Shawulu yana da shekara talatin sa’ad da ya zama sarki, ya kuma yi sarautar Isra’ila shekara arba’in da biyu. Sai ya zaɓi sojoji dubu uku daga jama’ar Isra’ila. Ya keɓe dubu biyu su kasance tare da shi a Mikmash da kuma a tuddan yankin Betel. Ya kuma bar dubu ɗaya tare da ɗansa Yonatan a Gibeya a yankin zuriyar Benyamin. Sauran sojojin kuwa Shawulu ya sallame su su koma gidajensu. Yonatan ya kai wa Filistiyawa hari a Geba, sai Filistiyawa suka sami labarin. Sai Shawulu ya sa aka busa ƙaho ko’ina a ƙasar ya ce, “Bari Ibraniyawa su ji!” Haka kuwa dukan Isra’ila suka ji labari cewa, “Shawulu ya kai hari a ƙasar Filistiyawa, yanzu Isra’ila ta zama abin ƙi ga Filistiyawa.” Aka kira mutane su haɗu da Shawulu a Gilgal. Sai Filistiyawa suka taru don su yi yaƙi da Isra’ilawa. Suka fito da kekunan-dawakan yaƙi dubu talatin, da masu hawan dawakai dubu shida, da sojoji masu yawa kamar yashi a bakin teku. Suka tafi Mikmash a gabashin Bet-Awen, suka kafa sansani a can. Sa’ad da Filistiyawa suka fāɗa wa Isra’ilawa da yaƙi mai tsanani, suka sa su cikin wani hali mai wuya, sai Isra’ilawa suka ɓuya a kogwanni, da ciyayi, da duwatsu, da ramummuka, da rijiyoyi. Waɗansunsu ma suka haye Urdun zuwa ƙasar Gad da Gileyad. Shawulu ya zauna Gilgal, dukan ƙungiyoyi sojojin da suke tare da shi suka yi rawan jiki don tsoro. Ya jira har kwana bakwai bisa ga lokacin da Sama’ila ya bayar. Amma Sama’ila bai zo Gilgal ba, mutanen Shawulu suka fara watsewa. Sai ya ce, “Ku kawo mini hadaya ta ƙonawa da hadaya ta salama.” Sai Shawulu ya miƙa hadaya ta ƙonawa. Daidai yana gama miƙa hadaya ke nan sai Sama’ila ya iso. Shawulu kuma ya fito domin yă yi masa maraba. Sama’ila ya ce, “Me ke nan ka yi?” Shawulu ya ce, “Sa’ad da na ga mutane suna watsewa, kai kuwa ba ka zo cikin lokaci ba, ga Filistiyawa kuma suna taruwa a Mikmash, sai na yi tunani cewa, ‘Yanzu Filistiyawa za su gangaro su fāɗa mini a Gilgal, ga ni kuma ban riga na nemi nufin Ubangiji ba.’ Shi ya sa ya zama mini tilas in miƙa hadaya ta ƙonawa.” Sama’ila ya ce, “Ka yi wauta da ba ka bi umarnin da Ubangiji Allahnka ya ba ka ba. Da ka yi haka da Ubangiji ya tabbatar maka da sarautar Isra’ila har abada. Amma yanzu, masarautarka ba za tă dawwama ba, Ubangiji ya riga ya sami wani wanda zuciyarsa ke ƙauna, ya naɗa shi shugaban mutanensa gama ba ka bi umarnin Ubangiji ba.” Sama’ila ya tashi daga Gilgal ya tafi Gibeya a ƙasar Benyamin. Shawulu kuma ya ƙidaya mutanen da suke tare da shi, yawansu ya kai wajen mutum ɗari shida. Shawulu da ɗansa Yonatan da mutanen da suke tare da shi suka zauna a Geba ta Benyamin. Sa’an nan Filistiyawa suka yi sansani a Mikmash. Rundunar mayaƙa uku suka fito daga sansani Filistiyawa. Ɗaya ta nufi Ofra, zuwa ƙasar Shuwal. Runduna guda kuma ta nufi Bet-Horon, ɗayan kuwa ta nufi iyakar da take fuskantar Kwarin Ziboyim wajen jeji. Ba a sami maƙeri ɗaya a dukan ƙasar Isra’ila ba domin Filistiyawa sun ce, “In ba haka ba Ibraniyawa za su ƙera wa kansu takuba ko māsu.” Saboda haka dukan Isra’ila sukan gangara zuwa wajen Filistiyawa domin su gyara bakin garemaninsu, da fartanansu, da gaturansu, da kuma laujunansu. Duk lokacin da za su gyara bakin garmansu da fartanyarsu sai sun biya tsabar azurfa biyu. Haka ma idan za su gyara gatari ko bakunan abin korar shanun noma sai sun biya tsabar azurfa ɗaya. A ranar da yaƙi ya tashi, ba a sami wanda yake da takobi ko māshi ba a cikin mutanen da suke tare da Shawulu da Yonatan. Sai dai Shawulu da ɗansa Yonatan kaɗai. Ana nan sai sojojin Filistiyawa suka fita zuwa mashigin Mikmash. Wata rana Yonatan ɗan Shawulu ya ce wa saurayin da yake ɗaukar masa makamai, “Zo mu tafi wajen sansanin Filistiyawa a wancan hayi.” Amma bai gaya wa mahaifinsa ba. Shawulu kuwa na zaune a gindin itacen rumman a bayan garin Gibeya a Migron. Tare da shi akwai mutum wajen ɗari shida. A cikinsu akwai Ahiya sanye da efod. Shi yaron Ikabod ɗan’uwan Ahitub ne, ɗan Finehas, ɗan Eli, firist na Ubangiji a Shilo. Ba wanda ya san cewa Yonatan ya tafi wani wuri. A kowane gefe na mashigin da Yonatan ya so yă bi zuwa wurin Filistiyawa, akwai hawa mai tsawo, ana kira ɗaya Bozez, ɗayan kuma ana kira Senet. Hawan da yake arewa yana fuskantar Mikmash, wanda yake kudu kuma yana fuskantar Geba. Yonatan ya ce wa saurayin mai ɗaukan makamai, “Zo mu haye zuwa mashigin mutane marasa kaciyan nan, wataƙila Ubangiji zai yi aiki a madadinmu. Ba abin da zai iya hana Ubangiji yin aikin ceto ta wurin mutane masu yawa, ko ta wurin mutane kaɗan.” Mai ɗaukan makaman ya ce, “Ka yi duk abin da yake zuciyarka. Ci gaba, ina tare da kai gaba da baya.” Yonatan ya ce, “To, zo mu haye zuwa wajen mutanen, mu sa su gan mu. In suka ce mana, ‘Ku tsaya nan har mu zo wurinku,’ za mu dakata inda muke, ba za mu haura wajensu ba. Amma in suka ce mana, ‘Ku haura wurinmu,’ to, sai mu haura, wannan zai zama mana alama cewa Ubangiji ya bashe su a hannunmu.” Sai suka nuna kansu a sansanin Filistiyawa. Sai Filistiyawa suka ce, “Ku duba ga Ibraniyawa suna fitowa daga cikin ramummuka inda suka ɓuya.” Mutanen da suke sansanin suka kira Yonatan da mai ɗaukan makamansa da babbar murya suka ce, “Ku hauro wajenmu, mu kuwa za mu koya muku hankali.” Sai Yonatan ya ce wa mai ɗaukan makamansa, “Biyo ni, gama Ubangiji ya bashe su a hannun Isra’ila.” Sai Yonatan ya hau dutsen da rarrafe, mai ɗaukan makamansa kuwa yana biye. Yonatan ya yi ta fyaɗa Filistiyawa da ƙasa, mai ɗaukan makamansa kuma ya yi ta karkashe su. A wannan karo na farko Yonatan da mai ɗaukan makamansa suka kashe mutum wajen ashirin a wani fili mai fāɗi rabin kadada. Sai tsoro ya kama dukan sojojin Filistiyawa, waɗanda suke cikin sansanin da waɗanda suke fili, har da waɗanda suke waje, da kuma waɗanda suke kai hari, ƙasa ta girgiza. Allah ne ya kawo wannan rikicewa. Masu gadin Shawulu a Gebiya da take a Benyamin suka duba sai ga rundunar Filistiyawa a warwatsewa ko’ina. Sai Shawulu ya ce wa mutanen da suke tare da shi, “Ku ƙidaya mayaƙa ku ga wane ne ba ya nan.” Da suka ƙirga sai suka tarar Yonatan da mai ɗaukan makamansa ba sa nan. Shawulu ya ce wa Ahiya, “Kawo akwatin alkawarin Allah.” (A lokacin akwatin alkawarin yana tare da Isra’ilawa.) Yayinda Shawulu yake magana da firist kuwa, harguwa ya yi ta ƙaruwa a sansanin Filistiyawa. Sai Shawulu ya ce wa firist, “Janye hannunka.” Sa’an nan Shawulu da dukan mutanensa suka taru suka tafi yaƙi. Suka tarar Filistiyawa sun ruɗe suna yaƙi da juna da takubansu. Ibraniyawan da suke tare da Filistiyawa a dā, waɗanda suka bi Filistiyawan zuwa sansanin yaƙinsu, suka juya, suka goyi bayan Shawulu da Yonatan sa’ad da yaƙin ya taso. Sa’ad da dukan Isra’ilawan da suka ɓuya a duwatsu a ƙasar Efraim suka ji labari cewa Filistiyawa suna gudu, sai suka fito suka fafare su. Haka Ubangiji ya kuɓutar da Isra’ila a wannan rana. Yaƙin kuwa ya ci gaba har gaba da Bet-Awen. A wannan rana, Isra’ilawa suka sha wahala ƙwarai domin Shawulu ya sa mutane suka yi rantsuwa cewa, “La’ananne ne mutumin da ya ci abinci kafin fāɗuwar rana, kafin in ɗauki fansa a kan abokan gābana.” Don haka ba mutumin da ya ɗanɗana abinci. Dukan rundunar ta shiga kurmi, sai ga zuma a ƙasa. Da suka shiga ciki kurmin, suka ga zuma tana zubowa, duk da haka ba wanda ya sa yatsansa ya lasa saboda tsoron rantsuwar da suka yi. Yonatan bai san cewa mahaifinsa ya sa mutane suka yi rantsuwa ba. Sai ya sa gindin sandan da yake hannunsa a saƙar zuma, ya kai bakinsa. Nan da nan sai ya ji ƙarfin jiki ya zo masa. Sai wani soja ya gaya masa cewa, “Mahaifinka ya sa kowa ya yi rantsuwa cewa, ‘La’ananne ne mutumin da ya ci abinci kafin fāɗuwar rana!’ Shi ya sa duk sojojin ba su da ƙarfi.” Yonatan ya ce, “Mahaifina ya jefa ƙasar cikin matsala. Duba yadda na ji ƙarfin jiki sa’ad da na ɗanɗana wannan ’yar zuma mana. Da yaya zai kasance ke nan da a ce an bar sojoji suka ci abincin da suka ƙwace daga abokan gābansu? Ai, da gawawwakin Filistiyawan da aka kashe sun fi haka.” A ranan nan Isra’ilawa suka yi ta kashe Filistiyawa daga Mikmash har zuwa Aiyalon. Bayan haka gajiya ta kama su sosai saboda yunwa. Sai suka yi warwason ganima, suka kwashe tumaki, da shanu, da maruƙa, suka yayyanka su, suka ci naman ɗanye. Sai wani mutum ya ce wa Shawulu, “Duba, ga mutane suna zunubi ga Ubangiji, suna cin nama da jini.” Shawulu ya ce, “Kun ci amana. Ku mirgino babban dutse zuwa wurina nan da nan.” Sa’an nan ya ce, “Ku tafi ku faɗa wa jama’a duka, su kawo shanu da tumaki a nan, su yayyanka, su ci a nan, don kada su yi wa Ubangiji zunubi da cin nama ɗanye.” Haka nan kowa ya kawo saniyarsa a daren, ya yanka a can. Sa’an nan Shawulu ya gina wa Ubangiji bagade. Wannan ne bagade na farkon da ya gina. Shawulu ya ce, “Mu bi gangara mu fafare Filistiyawa da dare mu washe su har gari yă waye, mu kuma karkashe kowannensu, kada mu bar wani da rai.” Suka ce, “Ka yi duk abin da ka ga ya fi maka kyau.” Amma firist ya ce, “Bari mu nemi nufin Allah tukuna.” Saboda haka Shawulu ya tambayi Allah ya ce, “Mu bi bayan Filistiyawa? Za ka bashe su a hannun Isra’ila?” Amma Allah bai ba shi amsa a ranar ba. Saboda haka Shawulu ya ce, “Ku zo nan dukanku shugabannin rundunoni, mu bincika mu san zunubin da ya kawo rashin amsan nan yau. Muddin Ubangiji wanda ya ceci Isra’ila yana raye, ko da ɗana Yonatan ne ya yi zunubin, dole yă mutu.” Amma ba ko ɗaya daga cikinsu da ya ce uffam. Sai Shawulu ya ce wa dukan Isra’ilawa, “Ku tsaya a can, ni kuma da Yonatan ɗana mu tsaya a nan.” Mutanen suka ce, “Ka yi abin da ya fi maka kyau.” Sa’an nan Shawulu ya yi addu’a ga Ubangiji, Allah na Isra’ila ya ce, “Me ya sa ba ka amsa mini addu’ata a yau ba? Idan wannan laifina ne, ko kuwa na ɗana, Yonatan, ka nuna mana ta wurin Urim, amma idan laifin mutanen ne ka amsa ta wurin Tummim.” Ba a sami mutane da laifi ba, amma ƙuri’a ta fāɗa a kan Yonatan da Shawulu. Shawulu ya ce, “Ku jefa ƙuri’a tsakanina da ɗana Yonatan.” Sai ƙuri’ar ta fāɗa a kan Yonatan. Sai Shawulu ya ce wa Yonatan, “Gaya mini mene ne ka yi.” Yonatan ya ce masa, “Na ɗanɗana zuma kaɗan daga gindin sandanta. Yanzu kuwa dole in mutu!” Shawulu ya ce, “Bari hukunci mai tsanani na Allah yă kasance a kaina, in ba ka mutu ba, Yonatan.” Amma mutane suka ce wa Shawulu, “A ce Yonatan yă mutu bayan shi ya kawo babban nasara a Isra’ila? Faufau, muddin Ubangiji yana raye, ko gashin kansa ɗaya ba zai fāɗi a ƙasa ba, gama abin da ya yi yau, Allah ne yana tare da shi.” Ta haka mutane suka ceci Yonatan daga mutuwa. Sai Shawulu ya daina bin Filistiyawa, suka koma ƙasarsu. Bayan Shawulu ya hau karagar mulkin Isra’ila, ya yi yaƙi da abokan gābansu ta kowane gefe. Mowabawa, Ammonawa, mutanen Edom, sarakunan Zoba, da kuma Filistiyawa. Duk wurin da ya juya, ya hore su. Ya yi jaruntaka sosai, ya ci Amalekawa da yaƙi, ya kuma ceci Isra’ila daga hannuwan waɗanda suka ƙwace musu kaya. ’Ya’yan Shawulu maza su ne, Yonatan, Ishbi, da Malki-Shuwa. Sunan babban ’yarsa ita ce Merab, ƙaramar kuma Mikal. Sunan matarsa kuwa Ahinowam, ’yar Ahimawaz. Sunan shugaban ƙungiyar sojan Shawulu kuwa Abner ne ɗan Ner, shi Ner kuwa ɗan’uwan mahaifin Shawulu ne. Mahaifin Shawulu, Kish da kuma Ner mahaifin Abner, ’ya’yan Abiyel ne. Dukan kwanakin Shawulu sun kasance na yaƙe-yaƙe da Filistiyawa ne. Duk lokacin da Shawulu ya ga ƙaƙƙarfan mutum ko jarumi, sai yă ɗauke shi aikin sojansa. Sama’ila ya ce wa Shawulu, “Ni ne wanda Ubangiji ya aika in shafe ka ka zama sarki bisa mutanensa Isra’ila. Saurara yanzu ka ji saƙo daga wurin Ubangiji. Ga abin da Ubangiji Maɗaukaki ya ce, ‘Zan hori Amalekawa saboda abin da suka yi wa Isra’ila sa’ad da suka ba su wahala yayinda suka fito daga Masar. Yanzu ka tafi ka yaƙi Amalekawa, ka hallaka kome da yake nasu, kada ka bar su da rai, ka kashe maza, da mata, da yara, da jarirai, da dabbobi, da tumaki, da raƙuma, da kuma jakuna.’ ” Sai Shawulu ya tattara sojoji, ya ƙidaya su a Telayim, ya sami su dubu ɗari biyu da dubu goma daga Yahuda. Shawulu ya tafi birnin Amalek ya yi kwanto a kwari. Sai Shawulu ya ce wa Keniyawa, “Ku tashi ku bar Amalekawa don kada in hallaka ku tare da su, saboda kun yi wa dukan Isra’ilawa kirki, lokacin da suka fito daga Masar.” Saboda haka Keniyawa suka tashi suka bar Amalekawa. Sa’an nan Shawulu ya ci Amalekawa da yaƙi tun daga Hawila har zuwa Shur, a gabashin iyakar Masar. Ya kama Agag sarkin Amalekawa da rai. Ya kuma hallaka dukan mutanensa da takobi. Amma Shawulu da sojojinsa suka bar Agag, da tumaki, da shanu, da ’yan maruƙa masu ƙiba da kuma duk abin da yake mai kyau da rai. Waɗannan ba su so su hallaka su gaba ɗaya ba, amma duk abin da ba a so da kuma marar amfani suka hallaka. Sai Ubangiji ya yi magana da Sama’ila ya ce, “Na damu da na naɗa Shawulu sarki, domin ya juya mini baya, bai kuma bi umarnina ba.” Sama’ila ya damu ƙwarai, ya yi kuka ga Ubangiji dukan dare. Kashegari da sassafe sai Sama’ila ya tashi ya tafi domin yă sadu da Shawulu, amma aka gaya masa cewa Shawulu ya tafi Karmel. A can ya yi wa kansa abin tunawa don yă girmama kansa, daga can kuma ya juya ya gangara zuwa Gilgal. Da Sama’ila ya kai wurinsa, sai Shawulu ya ce, “ Ubangiji yă albarkace ka, na aikata umarnin Ubangiji.” Amma Sama’ila ya ce, “Ashe, waɗannan ba kukan tumaki ke nan nake ji a kunnena ba? Wane kuka shanu ke nan nake ji?” Shawulu ya amsa ya ce, “Sojoji ne suka kawo su daga Amalekawa. Sun bar tumaki da shanu masu kyau da rai don su yi wa Ubangiji Allahnka hadaya, amma sauran mun hallaka duka.” Sama’ila ya ce, “Dakata, bari in faɗa maka abin da Ubangiji ya ce mini jiya da dare.” Shawulu ya ce, “Gaya mini.” Sama’ila ya ce, “Ko da yake kana ganin kanka kai ba wani abu ne ba, ashe, ba kai ne yanzu shugaban kabilan Isra’ila ba? Ubangiji ya shafe ka ka zama sarkin Isra’ila. Shi kuma ya aika, ya umarce ka cewa, ‘Tafi ka hallaka Amalekawa mugayen mutanen nan duka, ka yaƙe su sai ka share su ƙaf.’ Me ya sa ba ka bi umarnin Ubangiji ba? Me ya sa ka sa hannu a ganima, ka kuma yi mugun abu a gaban Ubangiji?” Shawulu ya ce, “Amma na bi umarnin Ubangiji. Na bi saƙon da Ubangiji ya ba ni. Na hallaka Amalekawa, na kuma kamo Agag sarkinsu. Sojoji suka kawo tumaki da shanu mafi kyau daga cikin ganimar domin a miƙa hadaya ga Ubangiji Allahnka a Gilgal.” Amma Sama’ila ya ce, “ Ubangiji yana murna da sadaka da hadaya fiye da biyayya ga maganar Ubangiji? Yin biyayya ta fi hadaya a kula kuma ta fi ƙibabbun raguna. Gama tawaye yana kama da zunubi na duba, girman kai kuma yana kama da bautar gumaka. Saboda ka ƙi maganar Ubangiji, shi ma ya ƙi ka da zaman sarki.” Sai Shawulu ya ce wa Sama’ila, “Na yi zunubi, na ƙi bin umarnin Ubangiji, na kuma ƙi bin maganarka. Na ji tsoron mutane ne shi ya sa na bi maganarsu. Yanzu fa, ina roƙonka ka yafe mini zunubina, ka koma tare da ni, domin in yi wa Ubangiji sujada.” Amma Sama’ila ya ce, “Ba zan koma tare da kai ba. Ka ƙi maganar Ubangiji, Ubangiji kuma ya ƙi ka da zama sarki a bisa Isra’ila.” Da Sama’ila ya juya zai tafi, sai Shawulu ya kama bakin rigarsa, sai rigar ta yage. Sama’ila ya ce masa, “ Ubangiji ya yage masarautar Isra’ila daga gare ka yau, ya ba wa wani daga cikin maƙwabtanka wanda ya fi ka. Shi wanda yake Ɗaukakar Isra’ila ba ya ƙarya ko yă canja zuciyarsa, gama shi ba mutum ba ne da zai canja zuciyarsa.” Shawulu ya ce, “Na yi zunubi. Amma ina roƙonka ka ba ni girma a gaban dattawan mutanena da kuma a gaban Isra’ila, ka koma tare da ni domin in yi wa Ubangiji Allahnka sujada.” Saboda haka sai Sama’ila ya koma tare da Shawulu, Shawulu kuwa ya yi wa Ubangiji sujada. Sa’an nan Sama’ila ya ce, “Kawo mini Agag sarkin Amalekawa.” Agag kuwa ya zo wurinsa daure da sarƙa, yana tunani cewa, “Tabbatacce zancen mutuwa dai ya wuce.” Amma Sama’ila ya ce, “Yadda takobinka ya sa mata suka rasa ’ya’ya, haka mahaifiyarka za tă zama marar ’ya’ya a cikin mata.” Sama’ila kuwa ya kashe Agag a Gilgal a gaban Ubangiji. Sai Sama’ila ya tafi Rama, amma Shawulu ya haura zuwa gidansa a Gibeya na Shawulu. Daga wannan rana Sama’ila bai ƙara saduwa da sarki Shawulu ba, har rasuwar Sama’ila, amma ya yi baƙin ciki sosai a kan Shawulu. Ubangiji kuwa ya damu da ya sa Shawulu ya zama Sarkin Isra’ila ba. Ubangiji ya ce wa Sama’ila, “Har yaushe za ka yi ta makoki saboda Shawulu? Na riga na ƙi shi da zaman sarkin Isra’ila. Ka cika ƙahonka da mai, zan aike ka zuwa wurin Yesse na Betlehem. Na zaɓi ɗaya daga cikin ’ya’yansa maza yă zama sarki.” Amma Sama’ila ya ce, “Yaya zan yi haka? Ai, in Shawulu ya ji labari, zai kashe ni.” Ubangiji ya ce, “To, sai ka tafi tare da ’yar karsana ka ce, ‘Na zo don in yi wa Ubangiji hadaya.’ Ka gayyato Yesse a wurin hadayar, ni kuma zan gaya maka abin da za ka yi. Za ka shafe mini wanda na nuna maka.” Sama’ila kuwa ya yi abin da Ubangiji ya umarce shi. Da ya isa Betlehem, sai dattawan garin suka tarye shi da rawar jiki, suka ce masa, “Mai duba, wannan ziyara lafiya dai ko?” Sama’ila ya ce, “I, lafiya ƙalau. Na zo ne domin in yi wa Ubangiji hadaya. Ku tsarkake kanku sa’an nan ku zo mu tafi wurin yin hadaya tare.” Ya kuma sa Yesse da ’ya’yansa maza su tsarkake kansu, su je wurin hadayar. Da isarsu, Sama’ila ya ga Eliyab sai ya yi tsammani shi ne, sai ya ce, “Lalle ga shafaffe na Ubangiji tsaye a gaban Ubangiji.” Amma Ubangiji ya ce wa Sama’ila, “Kada ka dubi kyan tsarinsa ko tsayinsa, domin ba shi nake so ba, gama yadda Ubangiji yake gani, ba haka mutum yake gani ba. Mutum yakan dubi kyan tsari ne kawai daga waje, amma Ubangiji yakan dubi zuciya.” Sai Yesse ya kira Abinadab yă zo gaban Sama’ila. Amma Sama’ila ya ce, “Ko wannan ma Ubangiji bai zaɓe shi ba.” Sai Yesse ya sa Shamma yă zo gaban Sama’ila, amma Sama’ila ya ce, “ Ubangiji bai zaɓi wannan ma ba.” Yesse ya sa ’ya’yansa maza bakwai suka wuce gaban Sama’ila, amma Sama’ila ya ce masa, “ Ubangiji bai zaɓi waɗannan ba.” Don haka ya tambayi Yesse ya ce, “Su ke nan ’ya’yan maza da kake da su?” Yesse ya ce, “Har yanzu akwai ɗan autan, amma yana kiwon tumaki.” Sama’ila ya ce, “Ka aika yă zo, ba za mu zauna ba sai ya iso.” Sai ya aika aka kawo shi. Ga shi kuwa kyakkyawan saurayi ne mai kyan gani. Ubangiji ya ce, “Tashi ka shafe shi, shi ne wannan.” Saboda haka Sama’ila ya ɗauko ƙahon nan da yake da mai ya shafe Dawuda a gaban ’yan’uwansa. Daga wannan rana kuwa ruhun Ubangiji ya sauko wa Dawuda da iko. Sai Sama’ila ya koma Rama. To, fa, Ruhun Ubangiji ya riga ya rabu da Shawulu, sai mugun ruhu daga Ubangiji ya soma ba shi wahala. Ma’aikatan Shawulu suka ce masa, “Duba, ga mugun ruhu daga Allah yana ba ka wahala. Ranka yă daɗe, muna so ka ba mu izini mu tafi, mu nemo wanda ya iya kiɗan molo, domin duk sa’ad da mugun ruhun nan daga Allah ya tashi, sai yă kaɗa molon don hankalinka yă kwanta.” Saboda haka Shawulu ya ce wa ma’aikatansa, “Ku nemo wanda ya iya kiɗan molo sosai ku kawo mini.” Ɗaya daga cikin bayin ya ce, “Na san wani yaro, ɗan Yesse na Betlehem, ya iya kiɗan molo, yana da hikima, shi kuma ya iya yaƙi. Ya iya magana, ga shi kuma kyakkyawa, Ubangiji kuwa yana tare da shi.” Sai Shawulu ya aiki manzanni zuwa wurin Yesse ya ce, “Ka aiko mini da ɗanka Dawuda wanda yake kiwon tumaki.” Saboda haka Yesse ya ɗauki jaki tare da burodi da ruwan inabi da ɗan ƙarami bunsuru ya ba wa ɗansa Dawuda yă kai wa Shawulu. Dawuda ya isa wurin Shawulu ya shiga hidimarsa. Shawulu kuwa ya so shi ƙwarai da gaske. Dawuda ya zama ɗaya daga cikin masu sanya sulke. Sa’an nan Shawulu ya aika saƙo wurin Yesse cewa, “Ka bar Dawuda yă yi mini hidima domin ina jin daɗinsa ƙwarai.” Duk lokacin da ruhun nan daga Allah ya sauko a kan Shawulu, sai Dawuda yă ɗauki molonsa yă kaɗa. Sa’an nan sauƙi yă zo wa Shawulu, mugun ruhu kuma yă rabu da shi. To, fa, Filistiyawa suka tattara mayaƙansu suka haɗu a Soko cikin Yahuda domin yaƙi. Suka yi sansani a Efes-Dammim, tsakanin Soko da Azeka. Shawulu da Isra’ilawa suka taru suka yi sansani a Kwarin Ela suka ja dāgā don su yi yaƙi da Filistiyawa. Filistiyawa suka zauna a tudu guda, Isra’ilawa kuma suka zauna a ɗaya tudun. Kwari yana a tsakaninsu. Wani jarumin da ake kira Goliyat wanda ya fito daga Gat, ya fita daga sansanin Filistiyawa. Tsawonsa ya fi ƙafa tara. Ya sa hular kwanon da aka yi da tagulla, da rigar ƙarfe mai sulke, nauyin rigar ya kai shekel dubu biyar. A ƙafafunsa kuwa ya sa ƙarafar tagulla, rataye a bayansa kuma māshi ne na tagulla. Ƙotar kibiyarsa kuwa kamar sandar saƙar igiya take, ƙarfen kibiyar kuma nauyinsa ya kai shekel ɗari shida. Mai riƙe masa garkuwa yana tafe a gabansa. Goliyat ya tsaya ya tā da murya wa hafsoshin Isra’ila ya ce, “Me ya sa kuka fito kuna layi don yaƙi? Ni ba Bafilistin ba ne? Ku kuma ba bayin Shawulu ba ne? Ku zaɓi waninku yă zo nan. In zai iya yin faɗa har yă kashe ni, to, za mu zama bayinku. Amma in na fi ƙarfinsa na kashe shi, to, sai ku zama bayinmu, ku kuma yi mana bauta.” Sai Bafilistin ya ce, “A wannan rana, na kalubalanci sojojin Isra’ila, ku ba ni mutum ɗaya mu yi faɗa.” Da jin maganganun Bafilistin, sai Shawulu da dukan Isra’ila suka damu suka kuma ji tsoro. To, Dawuda dai ɗan wani mutumin Efratawa ne mai suna Yesse, shi mutumin Betlehem ne a cikin Yahudiya. Yesse yana da yara maza takwas, a zamanin Shawulu kuwa, Yesse ya riga ya tsufa. Manyan ’ya’yansa maza uku, sun bi Shawulu wajen yaƙi. Ɗansa na fari shi ne Eliyab, na biyu shi ne Abinadab, na uku kuwa shi ne Shamma. Dawuda shi ne ɗan autansu. Manyan ’yan mazan nan uku suka bi Shawulu. Amma Dawuda yakan tafi sansanin Shawulu lokaci-lokaci yă kuma koma Betlehem don yă yi kiwon tumakin mahaifinsa. Kwana arba’in cif, Bafilistin nan ya yi ta fitowa kowane safe da kuma kowace yamma. Yesse ya ce wa ɗansa Dawuda, “Ka ɗauki wannan gasasshen hatsi da waɗannan curin burodi goma, ka kai wa ’yan’uwanka a sansani da sauri. Ka haɗa da waɗannan cuku guda goma, ka kai wa komandan rundunarsu. Ka ga lafiyar ’yan’uwanka, ka kawo mini labari daga wurinsu. Suna tare da Shawulu da kuma dukan mutanen Isra’ila a Kwarin Ela, suna can suna yaƙi da Filistiyawa.” Kashegari da sassafe, Dawuda ya tashi ya bar tumakinsa wa wani yă lura da su, sai ya ɗauki kayansa, ya kama hanya kamar yadda Yesse ya umarce shi. Ya isa sansanin daidai sa’ad da rundunar tana fitowa zuwa bakin dāgā, suna kirarin yaƙi. Isra’ila da Filistiyawa suka ja dāgā suna fuskantar junansu. Dawuda ya bar kayansa a wajen wani mai lura da kaya, sai ya ruga zuwa bakin dāgā yă gai da ’yan’uwansa. Da yana magana da su sai Goliyat, jarumin nan Bafilistin daga Gat ya fito daga rundunar Filistiyawa, ya tā da murya kamar yadda ya saba. Dawuda kuwa ya ji shi. Da Isra’ilawa suka ga mutumin, sai dukansu suka gudu saboda tsananin tsoro. Isra’ilawa suka yi ta cewa, “Kun ga yadda wannan mutum yana ta fitowa? Yana fitowa ne don yă kalubalanci Isra’ila. Sarki zai sāka wa mutumin da ya kashe wannan da dukiya mai yawa. Zai kuma ba shi ’yarsa yă aura, yă cire suna mahaifinsa daga biyan kuɗin haraji cikin Isra’ila.” Dawuda ya tambayi mutanen da suke tsaye kusa da shi ya ce, “Me za a yi wa wanda ya kashe Bafilistin nan, ya kuma cire wannan kunya daga Isra’ila? Wane ne wannan bafilistin marar kaciya da yake kalubalantar rundunar yaƙi na Allah mai rai?” Sai suka sāke gaya masa abin da suka faɗa cewa, “Ga abin da zai faru da wanda ya kashe shi.” Da wansa Eliyab, ya ji yana magana da mutanen, sai ransa ya ɓace ƙwarai saboda fushi, sai ya ce wa Dawuda, “Me ka zo yi a nan? Wa kuma ka bar wa ’yan tumakin a jeji? Na san ka da taurinkai, da kuma mugun hali. Ka zo nan ne don ka yi kallon yaƙi kawai.” Dawuda ya ce, “To, yanzu me na yi? Ba zan ma yi magana ba?” Sai ya juya wajen wani kuma ya sāke kawo zancen, mutanen kuwa suka amsa masa kamar dā. Aka ji abin da Dawuda ya ce, aka kuwa gaya wa Shawulu, Shawulu kuma ya aika a kawo shi. Da Shawulu ya tambayi Dawuda, sai Dawuda ya ce masa, “Kada kowa yă damu saboda wannan Bafilistin. Bawanka zai je yă yi faɗa da shi.” Shawulu ya ce, “Ba za ka iya yin faɗa da wannan Bafilistin ba, ya daɗe yana yaƙi, ya yi yaƙi tun yana saurayi. Ga shi kuwa kai ɗan yaro ne kawai.” Amma Dawuda ya ce wa Shawulu, “Bawanka yana kiwon tumakin mahaifinsa. Sa’ad da zaki ko beyar ta zo ta kama tunkiya, ta tafi da ita. Nakan bi ta a baya in buga ta in kuma ƙwato tunkiyar daga bakinta. In kuma ta taso mini, nakan cafke ta a gashinta in buga ta in kashe. Bawanka ya kashe zaki da beyar, wannan Bafilistin marar kaciya zai zama kamar ɗaya daga cikinsu, domin ya rena rundunar Allah mai rai. Ubangiji wanda ya cece ni daga kumbar zaki da kuma kumbar beyar, zai cece ni daga hannun wannan Bafilistin.” Shawulu ya ce wa Dawuda, “Je ka, Ubangiji yă kasance tare da kai.” Sai Shawulu ya kawo kayan yaƙinsa ya sa wa Dawuda. Ya sa masa hular kwanon da aka yi da tagulla a kansa, ya kuma sa masa rigar ƙarfensa. Dawuda ya ɗaura māshin Shawulu a sulken, ya yi ƙoƙari yă zaga, sai ya ji ba zai iya ba saboda bai saba ba. Ya cewa Shawulu, “Ba zan iya tafiya da waɗannan ba, domin ban saba ba.” Don haka ya tuɓe su. Sai ya ɗauki sandansa, ya zaɓi duwatsu guda biyar masu sulɓi daga cikin rafi, ya sa su a ’yar jakarsa ta makiyaya; ya kuma ɗauki majajjawarsa, ya tafi, yă fuskanci Bafilistin. Ana ciki haka, sai Bafilistin nan shi ma ya fita yana gusowa zuwa wurin Dawuda. Mai riƙe masa garkuwar yaƙi kuwa yana tafe a gabansa. Bafilistin ya dubi Dawuda daga sama har ƙasa, ya gan dai ɗan yaro ne kawai, kyakkyawa kuma mai ƙoshin lafiya, sai ya rena shi. Ya ce masa, “Kana tsammani ni kare ne da za ka zo mini da sanda?” Sai ya la’anci Dawuda da sunayen allolin Filistiyawa. Ya ce, “Zo nan, ni kuwa zan ba da naman jikinka ga tsuntsayen sama da namun jeji su ci.” Dawuda ya ce wa Bafilistin, “Kana zuwa ka yaƙe ni da māshi da takobi da kere, amma ni ina zuwa in yaƙe ka a cikin sunan Ubangiji Maɗaukaki, Allah na rundunar Isra’ila, wanda ka rena. Yau nan, Ubangiji zai bashe ka a hannuna, zan kuwa kashe ka, in datse kanka. Yau, zan ba da gawawwakin rundunar Filistiyawa ga tsuntsayen sama da namun jeji, da haka duniya za tă sani lalle akwai Allah a cikin Isra’ila. Duk waɗanda suka taru a nan za su san cewa ba da māshi ko takobi ne Ubangiji yake ceto ba, gama yaƙin nan na Ubangiji ne, shi kuwa zai bashe ku duka a hannuwanmu.” Yayinda Bafilistin yana matsowa kusa domin yă fāɗa wa Dawuda, sai Dawuda ya ruga a guje zuwa bakin dāgā don yă same shi. Ya sa hannu a jakarsa ya ɗauki dutse, ya sa cikin majajjawa ya wurga, dutsen kuwa ya bugi Bafilistin a goshi, dutsen ya shiga cikin goshinsa, sai Bafilistin ya fāɗi rubda ciki. Da majajjawa da dutse kawai Dawuda ya ci nasara a kan Bafilistin. Ya buge shi, ya kashe shi ba tare da takobi a hannunsa ba. Dawuda ya ruga ya tsaya a bisan Bafilistin, ya zare takobin Bafilistin daga kubensa, ya datse masa kai da shi. Da Filistiyawa suka ga jaruminsu ya mutu, sai suka juya suka gudu. Mutanen Isra’ila da na Yahuda suka rugo gaba da babbar murya, suka fafari Filistiyawa har zuwa mashigin Gat da kuma ƙofofin Ekron. Gawawwakin Filistiyawa suka bazu a hanyar Sha’arayim zuwa Gat da kuma Ekron. Da Isra’ilawa suka komo daga bin Filistiyawa sai suka washe sansanin Filistiyawa. Dawuda ya ɗauki kan Bafilistin zuwa Urushalima. Sai Dawuda ya ajiye kayan yaƙin Bafilistin a tentinsa. Yayinda Shawulu yake kallon Dawuda sa’ad da za shi yă yaƙi Bafilistin, sai ya tambayi Abner, komandan rundunarsa ya ce, “Abner, ɗan wane ne wannan saurayi?” Abner ya ce ran sarki yă daɗe, “Ban sani ba.” Sarki ya ce, “Ka tambaya mini ko yaron wane ne wannan saurayi.” Dawuda yana dawowa daga karkashe Filistiyawa ke nan, sai Abner ya kai shi gaban Shawulu, riƙe da kan Bafilistin. Sai Shawulu ya ce, “Kai ɗan wane ne, saurayi?” Dawuda ya ce, “Ni ɗan bawanka Yesse ne, na Betlehem.” Bayan da Dawuda ya gama magana da Shawulu, sai Yonatan ɗan Shawulu ya ji zuciyarsa tana son Dawuda sosai. Yonatan kuwa yana ƙaunar Dawuda kamar ransa. Tun daga wannan rana Shawulu ya zaunar da Dawuda tare da shi, bai bar shi ya koma gidan mahaifinsa ba. Yonatan kuma ya yi yarjejjeniya da Dawuda saboda yana ƙaunarsa kamar ransa. Yonatan ya tuɓe doguwar taguwarsa da ya sa, ya ba wa Dawuda, tare da sulkensa, har ma da māshi da kibiyarsa, da kuma bel nasa. Duk abin da Shawulu ya aiki Dawuda yă yi yakan yi shi cikin aminci, har Shawulu ya ba shi babban makami a rundunarsa. Wannan ya faranta wa dukan mutane zuciya har ma da ma’aikatan Shawulu. Yayinda mutane suke dawowa gida bayan da Dawuda ya kashe Bafilistin, mata suka fito daga dukan biranen Isra’ila don su sadu da Sarki Shawulu, suna waƙoƙi da raye-raye masu farin ciki, da ganguna da sarewa. Suna rawa suna cewa, “Shawulu ya kashe dubbansa, Dawuda kuwa ya kashe dubun dubbai.” Shawulu kuwa ya ji fushi, wannan magana ba tă yi masa daɗi ba, ya yi tunani ya ce, “Suna yabon Dawuda cewa ya kashe dubun dubbai amma ni dubbai kawai. Me ya rage masa yanzu, in ba mulki ba?” Tun daga wannan lokaci zuwa gaba, Shawulu ya dinga kishin Dawuda. Kashegari, mugun ruhu daga Allah ya fāɗo wa Shawulu da tsanani. Yana annabci a gidansa, Dawuda kuwa yana bugan molo kamar yadda ya saba. Shawulu yana riƙe da māshi a hannunsa. Da ƙarfi yana magana da kansa yana cewa, “Zan kafe Dawuda da bango.” Amma Dawuda ya bauɗe masa sau biyu. Shawulu ya ji tsoron Dawuda don Ubangiji yana tare da shi, amma Ubangiji ya riga ya bar Shawulu. Saboda haka Shawulu bai yarda Dawuda yă zauna tare da shi ba, amma ya maishe shi shugaban sojoji dubu. Dawuda kuwa ya riƙa bi da su yana kaiwa yana kuma da tare da su. A kome da Dawuda ya yi yakan yi nasara gama Ubangiji yana tare da shi. Da Shawulu ya ga yadda yake cin nasara, sai ya ji tsoronsa. Amma dukan Isra’ila da Yahuda suka ƙaunaci Dawuda gama yana bin da su a yaƙe-yaƙensu. Shawulu ya ce wa Dawuda, “Ga diyata Merab zan ba ka ka aura, kai dai ka yi mini aiki da himma, ka kuma yi yaƙe-yaƙen Ubangiji.” Saboda Shawulu ya ce wa kansa, “Ba zan ɗaga hannuna a kansa ba, Filistiyawa ne za su yi wannan.” Amma Dawuda ya ce wa Shawulu, “Wane ni, wa ya san iyayena ko kabilar iyayena a Isra’ila da zan zama surukin sarki?” Da lokaci ya kai da Merab ’yar Shawulu za tă yi aure da Dawuda, sai aka aurar da ita wa Adriyel na Mehola. Mikal ’yar Shawulu kuwa tana ƙaunar Dawuda sosai. Da aka gaya wa Shawulu labarin, sai ya yi farin ciki, ya yi tunani ya ce, “Zan ba shi ita tă zama masa tarko, da haka Filistiyawa za su same shi.” Shawulu ya ce wa Dawuda, “Yanzu kana da dama sau na biyu ka zama surukina.” Sai Shawulu ya umarci ma’aikatansa cewa, “Ku yi magana da Dawuda asirce ku ce, ‘Duba, sarki yana farin ciki da kai, dukan ma’aikatansa kuma suna sonka, ka yarda ka zama surukinsa.’ ” Suka sāke yi wa Dawuda wannan magana amma Dawuda ya ce, “Kuna tsammani abu mai sauƙi ne mutum yă zama surukin sarki? Ni talaka ne, kuma ba sananne ba.” Da ma’aikatan Shawulu suka gaya masa abin da Dawuda ya faɗa. Sai Shawulu ya ce, “Ku gaya wa Dawuda, ‘Sarki ba ya bukatan kuɗin auren ’yarsa, sai dai loɓar Filistiyawa domin ramako a kan abokan gābansa.’ ” Shawulu yana shiri ne domin Dawuda yă fāɗa a hannun Filistiyawa. Da ma’aikatan suka gaya wa Dawuda waɗannan abubuwa, sai ya yi murna don zai zama surukin sarki. Amma kafin lokacin yă cika, Dawuda da mutanensa suka fita suka kashe Filistiyawa ɗari biyu, suka kawo loɓar suka miƙa wa sarki, domin yă zama surukin sarki. Sai Shawulu ya ba da ’yarsa Mikal aure ga Dawuda. Da Shawulu ya gane Ubangiji yana tare da Dawuda, ’yarsa Mikal kuma tana ƙaunarsa, sai Shawulu ya ƙara jin tsoron Dawuda har ya zama maƙiyinsa a dukan sauran rayuwarsa. Manyan sojojin Filistiyawa suka yi ta fita suna yaƙi da Isra’ilawa, amma kullum Dawuda yakan sami nasara fiye da sauran manyan sojojin Shawulu. Ta haka ya yi suna ƙwarai. Shawulu ya gaya wa ɗansa Yonatan da ma’aikatansa su kashe Dawuda. Amma Yonatan yana son Dawuda sosai. Sai ya gargaɗe shi ya ce, “Mahaifina Shawulu yana neman hanyar da zai kashe ka. Ka kula da kanka gobe da safe, ka tafi wani wuri ka ɓuya. Zan je in tsaya da mahaifina a fili inda kake, zan yi masa magana game da kai. Zan kuma gaya maka abin da na ji.” Yonatan ya yi magana mai kyau a kan Dawuda a wajen mahaifinsa ya ce, “Kada sarki yă yi wani mummunan abu wa bawansa Dawuda, gama bai yi maka wani abu marar kyau ba. Abin da ya yi ya amfane ka ƙwarai da gaske. Ya yi kasai da ransa sa’ad da ya kashe Bafilistin nan. Ubangiji ya ba wa dukan Isra’ila babban nasara, ka gani, ka kuma yi farin ciki. Don me za ka ci mutuncin amintaccen mutum kamar Dawuda ta wurin kashe shi ba tare da wani dalili ba?” Shawulu ya saurari Yonatan sai ya rantse ya ce, “Muddin Ubangiji yana a raye, ba za a kashe Dawuda ba.” Ta haka Yonatan ya kira Dawuda ya gaya masa dukan maganarsu. Ya kawo shi wurin Shawulu, Dawuda kuwa ya zauna tare da Shawulu kamar dā. Wani yaƙi ya sāke tashi, Dawuda kuwa ya fita ya yaƙi Filistiyawa, ya kai musu hari mai tsanani, sai da suka gudu a gabansa. Amma mugun ruhu daga Ubangiji ya sauko wa Shawulu yayinda yana zaune a cikin gidansa da māshi a hannunsa. Yayinda Dawuda yake bugan molo, Shawulu ya yi ƙoƙari yă kafe shi da bango da māshinsa, amma Dawuda ya goce sa’ad da Shawulu jefa māshin a bango. A daren nan Dawuda ya nemi hanya ya gudu. Shawulu ya aiki mutane zuwa gidan Dawuda su yi gadin gidan, su kuma kashe Dawuda. Amma Mikal matar Dawuda ta gargaɗe Dawuda, ta ce, “In ba ka gudu a daren nan ba, kashegari za a kashe ka.” Haka kuwa Mikal ta sauko da Dawuda ta taga ya gudu, ya tsere. Sai Mikal ta ɗauki gunki ta kwantar da shi a gādo, ta sa masa gashin akuya a kansa, sai ta rufe da mayafi. Da Shawulu ya aiki mutane su kama Dawuda. Mikal ta ce, “Ba shi da lafiya.” Sai Shawulu ya sāke aiki mutanen su ga Dawuda, ya ce musu, “Ku kawo shi a gādonsa domin in kashe shi.” Amma da mutanen suka shiga sai suka ga gunkin a gadon, a wajen kan kuwa akwai gashin akuya. Shawulu ya ce wa Mikal, “Don me kika ruɗe ni har kika bar maƙiyina ya gudu ya tsere?” Mikal ta ce masa, “Ya ce mini, ‘Idan ban bar shi ya tafi ba, zai kashe ni?’ ” Da Dawuda ya gudu ya tsere, sai ya tafi wurin Sama’ila a Rama ya gaya masa dukan abin da Shawulu ya yi masa. Da shi da Sama’ila suka tafi Nayiwot suka zauna a can. Shawulu ya sami labari cewa, “Dawuda yana Nayiwot a Rama.” Sai ya aiki mutane su je su kamo Dawuda, amma da suka ga ƙungiyar annabawa suna annabci tare da Sama’ila shugabansu a tsaye, sai Ruhun Allah ya sauko wa mutanen Shawulu, su ma suka fara yin annabci. Shawulu ya sami labari game da wannan, sai ya sāke aiken waɗansu da yawa. Su ma suka shiga yin annabci. Shawulu ya sāke aiken mutane sau na uku, su kuma suka shiga yin annabci. A ƙarshe, shi da kansa ya tashi ya tafi Rama. Ya bi ta babban rijiyar ruwan Seku. A can ya yi tambaya ya ce, “Ina Sama’ila da Dawuda suke?” Suka ce, “Suna cikin Nayiwot a Rama.” Saboda haka Shawulu ya tafi Nayiwot a Rama, amma Ruhun Allah ya sauko masa, shi ma ya yi tafiya yana annabci har sai da ya isa Nayiwot. Ya tuttuɓe rigunarsa, ya kuma yi annabci a gaban Sama’ila. Ya kwanta tsirara dukan yini da dukan dare. Abin da ya sa ke nan mutane suke cewa, “Shawulu ma yana cikin annabawa ne?” Sai Dawuda ya gudu daga Nayiwot a Rama ya je wurin Yonatan ya ce, “Me na yi? Wane laifi ne na yi? Ta wace hanya ce na yi wa mahaifinka laifi har da yake neman yă kashe ni?” Yonatan ya ce, “Faufau, ba za ka mutu ba! Ka ji nan, mahaifina ba ya yin kome ba tare da ya shawarce da ni ba. Me ya sa ya ɓoye mini wannan? Ba zai yiwu ba.” Sai Dawuda ya rantse ya ce, “Mahaifinka ya san cewa, na sami tagomashi a gare ka, domin haka ba zai sanar maka da wannan ba, don kada yă baƙanta maka rai. Na rantse da Ubangiji, da kai kuma, taki ɗaya kaɗai ya rage tsakanina da mutuwa.” Sai Yonatan ya ce, “Duk abin da kake so in yi maka zan yi.” Dawuda ya ce, “Gobe fa shi ne Bikin Sabon Wata, ya kamata in ci tare da sarki amma bari in tafi fili in ɓuya har jibi da yamma. In mahaifinka bai gan ni ba, ka gaya masa cewa, ‘Dawuda ya nemi izinina domin yă hanzarta yă tafi garinsa a Betlehem saboda ana hadaya ta shekara-shekara don dukan zuriyarsa.’ In ya yi na’am, to, bawanka ya tsira. Amma in ka ga ya damu, to, ka tabbata ya yi niyya yă kashe ni. Kai kuma, ka nuna alheri ga bawanka, gama ka riga ka yi yarjejjeniya da ni a gaban Ubangiji, in kuwa na yi laifi ne sai ka kashe ni da kanka. Don me za ka bashe ni ga mahaifinka?” Yonatan ya ce, “Labudda! In na ji ƙishin-ƙishin, cewa mahaifina yana neman yă kashe ka ashe, ba zan gaya maka ba?” Dawuda ya ce, “Wa zai gaya mini idan mahaifinka ya amsa maka da amsa marar daɗi?” Yonatan ya ce, “Zo mu fita zuwa fili.” Sai suka tafi tare. Sai Yonatan ya ce wa Dawuda, “Na yi rantse da Ubangiji, Allah na Isra’ila cewa war haka jibi, zan yi ƙoƙari in ji daga mahaifina, idan ya yi magana mai kyau game da kai, zan gaya maka. Amma in mahaifina ya sa zuciya yă cuce ka, Ubangiji yă hukunta ni da hukunci mai tsanani in ban gaya maka ba, in kuma sa ka ka tafi lafiya. Ubangiji yă kasance tare da kai kamar yadda ya kasance da mahaifina. Amma ka nuna mini alheri marar ƙarewa iri ta Ubangiji dukan rayuwata don kada a kashe ni. Kada kuma ka yanke alherinka ga iyalina ko da Ubangiji ya hallaka dukan maƙiyin Dawuda a duniya.” Saboda haka Yonatan ya yi yarjejjeniya da gidan Dawuda cewa Ubangiji yă kawo dukan maƙiyin Dawuda ga mutuwa. Yonatan kuwa ya sa Dawuda ya sāke tabbatar masa rantsuwansa game da abokantakarsa da shi, gama yana ƙaunar Dawuda kamar ransa. Sai Yonatan ya gaya wa Dawuda cewa, “Gobe ne Bikin Sabon Wata, za a rasa ka, da yake kujerarka za tă kasance ba kowa a kai. Jibi wajajen yamma, ka tafi wurin da ka ɓuya lokacin da wannan matsala ta fara, ka tsaya kusa da dutsen Etsel. Zan harbi kibiya uku ta wajen, sai ka ce dai ina harbin baka. Sa’an nan zan aiki yaro in ce masa, ‘Je ka nemo kibiyoyin.’ In na ce masa, ‘Duba, kibiyoyin suna wannan gefen da kake, kawo su,’ sai ka fito, wato, tabbatacce muddin Ubangiji yana raye, ka tsira, ba wani hatsari. Amma in na ce wa yaron, ‘Duba, kibiyoyin suna gaba da kai,’ sai ka tafi, gama Ubangiji ya sallame ka. Game da al’amarin da muka tattauna da ni da kai kuwa, ka tuna fa Ubangiji ne shaida tsakanina da kai har abada.” Dawuda ya tafi ya ɓuya a fili. Sa’ad da ranar Bikin Sabon Wata ta zo, sarki ya zauna don yă ci. Ya zauna a kujeransa inda ya saba zama kusa da bango yana fuskantar Yonatan, Abner kuma ya zauna kusa da sarki. Amma kujeran Dawuda ba kowa. Shawulu bai ce kome ba a ranar domin ya yi tsammani wataƙila wani abu ya faru da Dawuda ya mai da shi marar tsarki, tabbatacce ba shi da tsarki. Amma kashegari, rana ta biyu ga wata, kujeran Dawuda kuma ba kowa, sai Shawulu ya ce wa ɗansa Yonatan, “Me ya sa ɗan Yesse bai zo cin abinci, jiya da yau ba?” Yonatan ya ce, “Dawuda ya nemi izinina don yă tafi Betlehem. Ya ce, ‘Bari in tafi gama iyalinmu suna miƙa hadaya a gari, ’yan’uwana kuwa sun gayyace ni in kasance a can. In na sami yardarka, bari in tafi in ga ’yan’uwana.’ Dalilin ke nan da bai zo ci da sarki ba.” Fushin Shawulu ya ƙuna a kan Yonatan, sai ya ce masa, “Kai shege ne, haihuwar banzan mace; ai, na san kana goyon bayan ɗan Yesse don ka wulaƙantar da kanka da mahaifinka. Muddin ɗan Yesse yana da rai a duniya, ba za ka kahu ba. Sarautarka kuma ba za tă kahu ba. Yanzu sai ka je ka kawo mini shi. Dole yă mutu.” Yonatan ya ce wa mahaifinsa, “Me ya sa zai mutu? Me ya yi?” Amma Shawulu ya jefe shi da māshi don yă kashe shi. A nan ne Yonatan ya san lalle mahaifinsa ya yi niyya yă kashe Dawuda. Yonatan ya tashi daga tebur cin abincin da fushi. A rana ta biyun kuwa bai ci abinci ba, gama yana baƙin ciki game da rashin kunyar mahaifinsa game da Dawuda. Da safe Yonatan ya tafi domin yă sadu da Dawuda a fili. Ya tafi tare da wani ƙaramin yaro. Ya ce wa yaron, “Yi ruga da gudu ka nemo kibiyoyin da na harba.” Da yaron ya ruga sai ya harba kibiya a gaba da shi. Da yaron ya isa wurin da kibiyan Yonatan ya fāɗi, Yonatan ya kira shi ya ce, “Kibiyan na gabanka fa.” Sai ya tā da murya ya ce, “Maza, yi sauri kada ka tsaya.” Yaron ya ɗauko kibiya ya kawo wa maigidansa. (Yaron kuwa bai san kome game da wannan abu ba, sai Yonatan da Dawuda kawai.) Yonatan ya ba wa yaron makaman ya ce, “Ka ɗauka ka koma gari.” Da yaron ya tafi, sai Dawuda ya tashi daga inda ya ɓuya kusa da tarin duwatsu, ya rusuna har sau uku. Sa’an nan suka sumbaci juna, suka yi kuka, Dawuda kuwa ya yi kuka sosai. Yonatan ya ce wa Dawuda, “Sauka lafiya, mun riga mun yi rantsuwar abokantaka da juna a cikin sunan Ubangiji cewa, ‘Ubangiji ne shaida tsakanina da kai, tsakanin zuriyarka da zuriyata har abada.’ ” Sai Dawuda ya tafi, Yonatan kuwa ya koma gari. Dawuda ya tafi Nob a wurin Ahimelek firist. Da Ahimelek ya gan shi sai ya firgita ya ce, “Me ya sa kai kaɗai ne? Me ya sa ba wani tare da kai?” Dawuda ya ce wa Ahimelek firist, “Na zo aikin sarki ne, ya kuwa ce kada in sanar wa kowa abin da ya sa in yi. Na faɗa wa mutanena inda za su same ni. Yanzu, me kake da shi a hannu? Ka ba ni burodi guda biyar, ko wani abu da kake da shi a nan.” Amma firist ya ce wa Dawuda, “Ba ni da burodi iri na kowa da kowa, sai dai akwai burodin da aka tsarkake. Za ka iya ɗauka ku ci idan mutanenka ba su kwana da mata ba.” Dawuda ya ce, “Lalle ne a keɓe muke daga mata. Mutanena sukan keɓe kansu a koyaushe suka tashi ’yar tafiya, balle fa a yau!” Don haka firist ya ba shi keɓaɓɓen burodi, tun da yake babu wani burodi a can sai dai burodin Kasancewa da aka cire daga gaban Ubangiji, aka sa burodi mai zafi a maimakon wanda aka cire a ranar. A ranar kuwa, ɗaya daga cikin bayin Shawulu yana can, a tsare a gaban Ubangiji, sunansa Doyeg, mutumin Edom, shugaban makiyayan Shawulu. Dawuda ya ce wa Ahimelek, “Ba ka da māshi ko takobi a nan? Ban kawo māshina ko wani makami ba gama saƙon sarki ya zo mini da gaggawa.” Sai firist ya ce, “Takobin Goliyat Bafilistin nan wanda ka kashe a Kwarin Ela yana nan. An naɗe shi da ƙyallen aka ajiye a bayan Efod, in kana so, sai ka ɗauka. Ba wani takobi kuma sai wancan.” Dawuda ya ce, “Ba ni shi, ai, ba wani kamar sa.” A ranar, Dawuda ya gudu daga wajen Shawulu ya tafi wuri Akish sarkin Gat. Amma bayin Akish suka ce masa, “Wannan ba shi ne Dawuda sarkin ƙasar ba? Ashe, ba shi ne aka yi ta yin waƙoƙi a kansa, ana raye-raye, ana cewa, “Shawulu ya kashe dubbai, Dawuda kuwa ya kashe dubun dubbai?” Dawuda ya riƙe waɗannan kalmomi a zuciyarsa, ya kuma ji tsoron Akish sarkin Gat sosai. Don haka sai ya yi kamar ya taɓu a gabansu. A duk lokacin da yake tare da su, sai yă yi kamar ya haukace. Ya yi ta zāne-zāne a ƙofofi, ya bar miyau yana ta bin gemunsa. Akish ya ce wa bayinsa, “Duba, wannan mutum yana hauka. Me ya sa kuka kawo shi a wurina? Na rasa masu hauka ne da za ku kawo mini wannan mutum yă yi ta hauka a gabana? Dole ne wannan mutum yă shiga gidana?” Dawuda ya bar Gat, ya tsere zuwa kogon Adullam. Da ’yan’uwansa da kuma iyalan mahaifinsa suka ji labari, sai suka tafi can wurinsa. Dukan mutanen da suke cikin wahala, da waɗanda ake binsu bashi, da masu damuwoyi, suka tattaru a wurin Dawuda. Shi kuwa ya zama shugabansu. Yawansu ya kai ɗari huɗu. Daga can Dawuda ya tafi Mizfa a Mowab. Ya ce wa sarkin Mowab, “Za ka yarda mahaifina da mahaifiyata su zo su zauna a wurinka kafin in san abin da Allah zai yi da ni?” Saboda haka ya bar su a wurin sarkin Mowab, suka zauna da shi duk tsawon lokacin da Dawuda yake ta ɓuya a kogwannin duwatsu. Amma annabin nan Gad ya ce wa Dawuda, “Kada ka zauna a nan, maza ka tashi ka shiga ƙasar Yahuda”. Sai Dawuda ya tashi ya tafi jejin Heret. Sai Shawulu ya sami labari cewa an ga Dawuda da mutanensa. Shawulu kuwa yana zaune da māshinsa kusa a ƙarƙashin itacen tsamiya a tudun Gibeya, tare da dukan ma’aikatansa kewaye da shi. Ya ce musu, “Mutanen Benyamin, ku saurara; ɗan Yesse zai iya ba dukanku filaye da gonakin inabi ne? Zai ba dukanku shugabanci na dubbai ko shugabanci na ɗari-ɗari? Abin da ya sa dukanku kuka gama baki a kaina? Ba wanda ya gaya mini lokacin da ɗana ya yi yarjejjeniya da ɗan Yesse, ba wanda ya kulla da ni, ko ya gaya mini cewa ɗana ya sa bawana yă tayar mini, yana fakona kamar yadda yake a yau.” Amma Doyeg mutumin Edom da yake tsaye tare da fadawan Shawulu ya ce, “Na ga ɗan Yesse ya zo wurin Ahimelek ɗan Ahitub a Nob. Ahimelek ya roƙi Ubangiji saboda shi, ya kuma ba shi guzuri da takobin Goliyat Bafilistin.” Sai sarki ya aika aka kira masa Ahimelek firist ɗan Ahitub da dukan iyalin mahaifinsa. Dukansu suka zo wurin sarki. Shawulu ya ce, “Ka saurara yanzu, ɗan Ahitub.” Ya amsa ya ce, “Ina saurara, ranka yă daɗe.” Shawulu ya ce masa, “Don me ka gama baki da ɗan Yesse a kaina har ka ba shi burodi da takobin (Goliyat), ka kuma roƙi Allah don yă tayar mini, yă kuma yi fakona kamar yadda yake yi yau?” Ahimelek ya ce wa sarki, “A cikin bayinka duka, wa ke da aminci iri na Dawuda, surukin sarki, shugaban jarumanka wanda ake girmamawa da gaske a gidanka? A wannan rana ce da na fara roƙon Allah saboda shi? Kada sarki yă zargi bawansa ko wani daga iyalin mahaifinsa, gama bawanka bai san kome a kan dukan waɗannan al’amura ba.” Amma sarki ya ce, “Lalle Ahimelek za ka mutu, da kai da dukan iyalin mahaifinka.” Sai sarki ya umarci matsaran da suke tsaye kusa da shi ya ce, “Ku kakkashe firistocin Ubangiji, gama su ma sun goyi bayan Dawuda. Sun san yana gudu, duk da haka ba su gaya mini ba.” Amma ma’aikatan sarki ba su yarda su sa hannu su kashe firistocin Ubangiji ba. Sai sarki ya umarce Doyeg ya ce, “Ka juya ka kakkashe firistocin.” Doyeg mutumin Edom ya juya ya kakkashe firistocin. A ranar kuwa ya kashe mutum tamanin da biyar waɗanda suke sanye da efod na lilin. Ya kuma hallaka Nob birnin firistoci, ya kashe dukan mata, da maza, da yara, da jarirai, da shanu, da jakuna, da kuma tumaki. Amma Abiyatar ɗan Ahimelek jikan Ahitub ya tsere, ya gudu zuwa wurin Dawuda. Abiyatar gaya wa Dawuda cewa, “Shawulu ya hallaka firistocin Ubangiji.” Dawuda ya ce wa Abiyatar, “Lalle a wancan ranar, sa’ad da na ga Doyeg mutumin Edom a can, na san tabbatacce zai gaya wa sarki. Ni ne sanadin mutuwar dukan iyalin mahaifinka. Ka zauna tare da ni, kada ka ji tsoro mutumin da yake neman ranka, yana nema raina ma. Ka zauna lafiya tare da ni.” Sa’ad da aka ce wa Dawuda, “Duba ga Filistiyawa suna yaƙi da mutanen Keyila, suna kwashe musu hatsi a masussukai.” Sai Dawuda ya nemi nufin Ubangiji, ya ce, “In tafi in fāɗa wa Filistiyawa da yaƙi?” Ubangiji kuwa ya ce masa, “Jeka ka yi yaƙi da Filistiyawa, ka ceci Keyila.” Amma mutanen Dawuda suka ce masa, “Ga shi, a nan ma a Yahuda muna jin tsoro, balle mu tafi Keyila mu yi yaƙi da sojojin Filistiyawa!” Dawuda ya sāke nemi nufin Ubangiji, sai Ubangiji ya ce masa, “Tashi ka gangara zuwa Keyila, gama zan ba da Filistiyawa a hannunka.” Sa’an nan Dawuda da mutanensa suka tafi Keyila, suka yi yaƙi da Filistiyawa, suka kwashe musu shanunsu, suka jijji wa Filistiyawa ƙwarai, suka cece mutanen Keyila daga hannunsu. (Abiyatar ɗan Ahimelek ya zo da efod sa’ad da ya gudo zuwa wurin Dawuda a Keyila.) Shawulu ya sami labari cewa Dawuda ya tafi Keyila, sai ya ce, “Allah ya bashe shi a hannuna, domin Dawuda ya kulle kansa ke nan da ya shiga birnin da yake da ƙofofin da ake kulle da ƙarafa.” Shawulu ya kira dukan sojojinsa don yaƙi, su gangaro zuwa Keyila su mamaye Dawuda da mutanensa. Da Dawuda ya ji labari Shawulu yana shirya hanyar da zai kashe shi, sai ya ce wa Abiyatar firist, “Kawo mini efod a nan.” Dawuda ya ce, “Ya Ubangiji, Allah na Isra’ila, bawanka ya sami labari cewa tabbatacce Shawulu yana shirin zuwa Keyila yă hallaka garin saboda ni. Mutanen Keyila za su bashe ni a gare shi? Shawulu zai gangaro nan kamar yadda bawanka ya sami labari? Ya Ubangiji, Allah na Isra’ila, ka gaya wa bawanka.” Ubangiji ya ce, “Zai zo.” Dawuda ya sāke cewa, “Mutanen Keyila za su bashe ni da mutanena ga Shawulu?” Ubangiji ya ce, “Za su yi.” Saboda haka Dawuda da mutanensa wajen mutum ɗari shida suka bar Keyila, suka yi ta tafiya daga wannan wuri zuwa wancan. Sa’ad da aka gaya wa Shawulu cewa Dawuda ya tsere daga Keyila, sai ya fasa tafiya can. Dawuda ya zauna a jeji cikin kogunan duwatsu da kuma tuddan jejin Zif. Kowace rana Shawulu ya yi ta neman Dawuda amma Allah bai bashe Dawuda a hannunsa ba. A lokacin da Dawuda yana zaune a Horesh cikin jejin Zif, ya sami labari cewa Shawulu ya fito don yă kashe shi. Yonatan ɗan Shawulu kuwa ya tafi wurin Dawuda a Horesh, ya ƙarfafa shi yă dogara ga Allah. Ya ce, “Kada ka ji tsoro, mahaifina Shawulu ba zai taɓa sa hannu a kanka ba. Za ka zama sarki a Isra’ila, ni kuma in zama na biyu gare ka. Kai, ko mahaifina Shawulu ma ya san da haka.” Su biyunsu kuwa suka ɗaura yarjejjeniya a gaban Ubangiji. Sai Yonatan ya koma gida amma Dawuda ya zauna Horesh. Zifawa suka tafi wurin Shawulu a Gibeya suka ce masa, “Ashe, ba Dawuda ne yake ɓuya a cikinmu a kogwannin duwatsu a Horesh a bisan tudun Hakila, kudu da Yeshimon ba? Yanzu, ya sarki, ka gangaro, ka zo a duk lokacin da ka ga ya yi maka, ka zo mu kuma hakkinmu ne mu bashe shi a hannun sarki.” Shawulu ya ce, “ Ubangiji ya yi muku albarka, gama kun damu da ni. Ku tafi ku ƙara shiri. Ku san inda yakan tafi, wane ne kuma ya gan shi a can. An gaya mini cewa shi mai wayo ne sosai. Ku binciko duk wuraren da yakan ɓuya, sai ku dawo ku gaya mini tabbataccen labari. Sa’an nan zan tafi tare da ku in yana can. Zan nemi shi ko’ina cikin dukan kabilar Yahuda.” Sai suka tashi suka koma Zif, suka sha gaban Shawulu. Dawuda da mutanensa kuwa suna jejin Mawon cikin Araba, kudu da Yeshimon. Shawulu da mutanensa suka tafi neman Dawuda. Da Dawuda ya ji labari, sai ya gangara cikin duwatsu ya zauna a cikin jejin Mawon. Sa’ad da Shawulu ya ji haka, sai ya tafi jejin Mawon yana fafaran Dawuda. Shawulu yana tafiya a gefe ɗaya na dutsen, Dawuda da mutanensa kuma suna a wancan gefe, suna hanzari su ɓace wa Shawulu. Sa’ad da Shawulu da sojojinsa suka kusa cimma Dawuda da mutanensa don su kama su, sai wani manzo ya zo wurin Shawulu yana cewa, “Ka koma da sauri, Filistiyawa sun kawo wa ƙasar hari.” Shawulu kuwa ya janye daga fafaran Dawuda, ya tafi yă ƙara da Filistiyawa. Dalilin ke nan da ake kiran wannan wuri Sela Hammalekot, wato, dutsen tserewa. Dawuda kuwa ya haura daga can ya zauna a kogwannin duwatsun En Gedi. Bayan da Shawulu ya komo daga fafaran Filistiyawa, sai aka gaya masa cewa, “Dawuda yana can a Jejin En Gedi.” Saboda haka Shawulu ya zaɓi mutum dubu uku daga cikin dukan Isra’ila, suka fita neman Dawuda da mutanensa kusa da Duwatsun Awakin Jeji. Da Shawulu ya isa inda ake ajiye garken tumaki a bakin hanya inda akwai kogo, sai ya shiga ciki kogon don yă yi bayan gari. Dawuda da mutanensa kuwa suna can zaune a ƙurewar kogon. Mutanen Dawuda suka ce, wannan rana ce Ubangiji ya yi magana ya ce maka, “Zan ba da maƙiyinka a hannunka domin ka yi abin da ka ga dama da shi.” Sai Dawuda ya tashi a hankali ya je ya yanke shafin rigar Shawulu. Daga baya Dawuda ya damu domin ya yanke shafin rigar Shawulu. Ya ce wa mutanensa, “ Ubangiji yă sawwaƙe in yi abu haka ga shugabana da Ubangiji ya shafe, ko in ɗaga hannuna in kashe shi, gama shi shafaffe ne na Ubangiji.” Da wannan magana Dawuda ya kwaɓi mutanensa, bai yarda su fāɗa wa Shawulu ba. Shawulu kuwa ya bar kogon ya yi tafiyarsa. Daga baya Dawuda ya fita daga kogon sai ya kira Shawulu ya ce, “Ranka yă daɗe, sarki!” Da Shawulu ya waiwaya, sai Dawuda ya rusuna da fuskarsa har ƙasa. Ya ce wa Shawulu, “Me ya sa kake saurari mutanen da suke cewa, ‘Dawuda ya dāge yă cuce ka’? Yau ka ga da idonka yadda Ubangiji ya bashe ka a hannuna a cikin kogon nan. Waɗansu sun ce mini in kashe ka, amma na bar ka, na ce, ‘Ba zan sa hannuna a kan shugabana ba, gama shi shafaffe ne na Ubangiji.’ Babana, duba, ga shafin rigarka a hannuna, na yanke shafin rigarka amma ban kashe ka ba. Yanzu ka gane ka kuma sani cewa ba ni da laifin aikata kome ko tayarwa, ban yi maka laifi ba, amma kana farautar raina. Ubangiji zai shari’anta tsakanina da kai. Ubangiji zai sāka mini laifin da ka yi mini, amma ni kam ba zan taɓa ka ba. Kamar yadda karin maganan nan na dā ya ce, ‘Daga cikin masu mugunta, mugunta ke fitowa,’ hannuna dai ba zai taɓa ka ba. “Wane ne sarkin Isra’ila, ka fito kake bi? Wa kake kora? Kana bin mataccen kare ko kuɗin cizo? Ubangiji yă zama alƙali, yă yi shari’a tsakanina da kai, bari Ubangiji yă duba, yă tsaya mini, yă nuna ba ni da laifi.” Da Dawuda ya gama wannan magana, sai Shawulu ya ce, “Muryarka ke nan ɗana Dawuda?” Sai ya fasa da kuka. Ya ce, “Ka fi ni gaskiya, ka yi mini alheri, ni kuwa na yi maka mugunta. Ga shi yanzu ka faɗa mini alherin da ka yi mini. Ubangiji ya bashe ni a hannunka amma ba ka kashe ni ba. In mutum ya sami maƙiyinsa, zai bar shi yă tafi lafiya ba tare da yin masa rauni ba? Ubangiji yă sāka maka, gama ka nuna mini alheri a yau. Na sani tabbatacce za ka zama sarki. Masarautar Isra’ila za tă kahu a hannunka. Yanzu ka rantse mini da Ubangiji cewa ba za ka hallaka zuriyarta ko ka share sunana daga iyalin mahaifina ba.” Sai Dawuda ya rantse wa Shawulu. Sa’an nan Shawulu ya koma gida, amma Dawuda da mutanensa suka haura zuwa wurin ɓuya. Sama’ila ya rasu, sai dukan Isra’ila suka taru suka yi makoki saboda shi. Suka binne shi a gidansa a Rama. Sai Dawuda ya gangara zuwa cikin Jejin Faran. A Mawon, akwai wani mutum wanda yake da dukiya a Karmel, mutumin mai arziki ne ƙwarai. Yana da awaki dubu ɗaya, da tumaki dubu uku waɗanda yake wa aski a Karmel. Ana ce da shi Nabal, sunan matarsa kuwa Abigiyel. Tana da hikima ga ta kuma kyakkyawa, amma mijinta mai rowa ne marar mutunci. Shi daga kabilar Kaleb ne. Lokacin da Dawuda yake a jeji, ya ji labari cewa Nabal yana askin tumaki. Sai ya zaɓi samari goma ya aike su wurin Nabal a Karmel su gaishe shi a madadinsa, su ce masa, “Ranka yă daɗe, ina maka fatan alheri, kai da gidanka da dukan abin da kake da shi! “Na ji cewa, yanzu lokacin askin tumaki ne. Sa’ad da makiyayanka suke tare da mu, ba mu cuce su ba, kuma duk zamansu a Karmel ba abin da yake nasu da ya ɓata. Ka tambayi bayinka za su kuwa gaya maka. Saboda haka ka yi wa mutanena kirki, gama yau ranar biki ce. Ina roƙonka ka ba wa samarina, wato, bayinka, da ni ɗanka Dawuda, duk abin da kake iya ba su.” Da mutanen Dawuda suka isa wurin Nabal, suka ba wa Nabal wannan saƙo a sunan Dawuda, sai suka jira. Nabal ya ce wa mutanen Dawuda, “Wane ne wannan Dawuda? Wane ne wannan ɗan Yesse? Yawancin bayi suna tayar wa iyayengijinsu a kwanakin nan. Don me zan ɗauki burodina da ruwana, da kuma naman da na yanka saboda masu yin wa tumakina aski in ba mutanen da ban ma san inda suka fito ba?” Mutanen Dawuda suka juya suka koma. Da suka iso sai suka faɗa wa Dawuda abin da Nabal ya ce. Dawuda ya ce wa mutanensa, “Kowa yă rataya takobinsa.” Sai duk suka yi haka. Dawuda kuma ya rataya nasa. Mutum wajen ɗari huɗu suka tafi tare da Dawuda, mutum ɗari biyu kuwa suka zauna suna gadin kayansu. Ɗaya daga cikin bayin Nabal ya gaya wa Abigiyel matar Nabal cewa, “Dawuda ya aiko da bayinsa daga jeji su gai da maigida, amma maigida ya zazzage su. Waɗannan mutane kuwa sun yi mana kirki ƙwarai, ba su ba mu wata wahala ba. Babu abu guda da ya ɓace mana dukan lokacin da muke tare da su. Dare da rana sun zama mana katanga kewaya da mu, a duk tsawon lokacin da muke kiwon tumakinmu kusa da su. Ki yi nazari a kai, ki ga ko za ki iya yin wani abu, domin masifa yana nan rataye a wuyan maigidanmu da dukan iyalin gidansa. Shi mugun mutum ne wanda ba wani da zai iya yin masa magana.” Abigiyel ba tă ɓata lokaci ba. Ta ɗauki burodi guda ɗari biyu, da salkar ruwan inabi biyu da tumaki biyar da aka gyara, da soyayyen hatsi mudu biyar, da waina guda ɗari na ’ya’yan inabi, da masa ɗari biyu na kauɗar ɓaure ta labta wa jakuna. Sai ta ce wa bawanta, “Yi gaba, zan bi ka”. Amma ba tă gaya wa Nabal, mijinta ba. Da tana tafiya a kan jaki, ta kai gindin wani dutse ke nan, sai ga Dawuda da mutanensa suna gangarowa zuwa wajen da take. Sai ta tafi, ta sadu da su. Bai daɗe ba da Dawuda ya ce a ransa, “Ashe, a banza ne na yi ta lura da dukan abin da yake na mutumin nan a jeji, har ba abinsa da ya ɓace. Ga shi, ya rama mini alheri da mugunta. Bari Allah yă yi duk abin da ya ga dama da ni in na bar ko ɗaya daga mazan da suke da tare shi, gobe da safe.” Da Abigiyel ta ga Dawuda, sai ta gaggauta ta sauka daga kan jaki, ta rusuna a gaban Dawuda da fuskarta har ƙasa. Ta fāɗi a ƙafafunsa ta ce, “Bari laifin yă zama nawa, ranka yă daɗe. Ina roƙonka ka bar baiwarka ta yi magana, ka ji abin da baiwarka za tă ce. Kada ranka yă daɗe, yă kula da Nabal, mugun mutumin nan. Shi dai kamar sunansa ne, sunansa Wawa ne, kuma wawanci yana cikinsa. Amma ni baiwarka, ban ga mutanen da ranka yă daɗe ya aika ba. Da yake yanzu, ya mai girma, Ubangiji ya hana ka zubar da jini da kuma ɗaukan wa kanka fansa, muddin Ubangiji yana raye, kai kuma kana a raye, bari maƙiyinka da dukan waɗanda suke niyya su cuci shugabana su zama kamar Nabal. Bari kuma ka karɓi wannan kyautar da baiwarka ta kawo don samarin da suke binka. Ina roƙonka ka gafarta wa baiwarka laifinta gama tabbatacce Ubangiji zai ba shugabana dawwammamiyar sarauta, gama kana yin yaƙin Ubangiji ne. Kuma ba wani mugun abin da zai same ka muddin kana a raye. Ko da yake wani mutum yana fafaranka domin yă kashe ka, Ubangiji Allahnka zai kiyaye ranka. Amma za a wurgar da rayukan maƙiyanka kamar yadda ake wurga dutsen majajjawa. Sa’ad da Ubangiji ya cika kowane alherinsa da ya yi wa shugabana alkawari, ya kuma keɓe shi sarki a bisa Isra’ila, kada yă zama cewa zuciyarka ta ba ka laifi ko ka damu cewa kana da alhakin jini, kada ka yi ramuwa da kanka. Sa’ad da Ubangiji ya nuna maka alheri, ka tuna da ni, baiwarka.” Dawuda ya ce wa Abigiyel, “Yabo ya tabbata ga Ubangiji, Allah na Isra’ila, wanda ya aiko ki don ki same ni yau. Bari Allah yă albarkace ki saboda hikima yanke hukuncinki da kuma hana ni zubar da jini da ɗauka wa kaina fansa da hannuna a wannan rana. Ubangiji, ya hana ni in yi miki ɓarna. Da ba don kin zo kin sadu da ni ba, na rantse da Ubangiji, Allah na Isra’ila Mai Rai, babu ko ɗaya daga cikin mazan gidan Nabal da zai rage gobe da safe.” Sa’an nan Dawuda ya karɓi abin da ta kawo masa daga hannunta, ya kuma ce mata, “Ki koma gida kada ki damu, na ji koke-kokenki, zan kuma biya miki bukatarki.” Da Abigiyel ta kai gida sai ta sami Nabal cikin gida yana ta fama biki iri na sarakuna. Yana ji wa ransa daɗi, ya kuma bugu tilis, saboda haka ba tă ce masa kome ba sai da gari ya waye. Da safe sa’ad da Nabal ya natsu, sai matarsa ta gaya masa dukan abin da ya faru. Sai zuciyarsa ta tsinke, ya zama kamar dutse. Bayan kusan kwana goma, Ubangiji ya bugi Nabal, sai ya mutu. Da Dawuda ya sami labarin mutuwar Nabal, sai ya ce, “Yabo ya tabbata ga Ubangiji, wanda ya sāka mini a kan irin renin da Nabal ya yi mini. Ya hana bawansa yin mugunta, ga shi ya ɗora wa Nabal muguntar da ya yi.” Sai Dawuda ya aika wa Abigiyel cewa tă zama matarsa. Bayin Dawuda suka tafi Karmel suka ce wa Abigiyel, “Dawuda ya aike mu gare ki, mu zo mu ɗauke ki ki zama matarsa.” Sai ta rusuna da fuskarta har ƙasa ta ce, “Ni baranyarka ce, na shirya in bauta maka in kuma wanke ƙafafun bayin shugabana.” Abigiyel ta tashi da sauri ta hau jaki, ta kuma sa ’yan mata biyar da suke mata hidima su bi ta, suka tafi tare da ’yan saƙon Dawuda. Ta kuwa zama matarsa. Dawuda a lokacin ya riga ya auri Ahinowam daga Yezireyel, dukansu suka zama matansa. Amma Shawulu ya aurar da Mikal, ’yarsa, matar Dawuda, ga Falti ɗan Layish wanda yake daga Gallim. Zifawa suka je wurin Shawulu a Gibeya suka ce, “Ashe, ba Dawuda ne ya ɓuya a tudun Hakila da yake fuskantar Yeshimon ba?” Sai Shawulu ya tashi ya gangara zuwa Jejin Zif, tare da zaɓaɓɓun mutane dubu uku na Isra’ila. Suka fita neman Dawuda a can. Shawulu ya yi sansani a bakin hanyar zuwa tudun Hakila mai fuskantar Yeshimon. Amma Dawuda yana zaune a jeji. Sa’ad da ya ga Shawulu ya biyo shi har zuwa can, sai ya aiki ’yan leƙen asiri su tabbata lalle Shawulu ya iso can. Sai Dawuda ya kintsa ya tafi inda Shawulu ya yi sansani. Ya ga inda Shawulu da Abner ɗan Ner shugaban ƙungiyar soja suka kwanta. Shawulu yana kwance a cikin sansani tare da sojoji kewaye da shi. Sai Dawuda ya ce wa Ahimelek mutumin Hitti da Abishai ɗan Zeruhiya ɗan’uwan Yowab, “Wa zai gangara tare da ni zuwa sansanin Shawulu?” Sai Abishai ya ce, “Zan tafi tare da kai.” Saboda haka Dawuda da Abishai suka gangara zuwa wurin rundunar da dare, sai ga Shawulu kwance yana barci a cikin sansani da māshinsa a kafe a ƙasa kusa da kansa. Abner kuwa tare da sojoji suna kwance kewaye da shi. Abishai ya ce wa Dawuda, “Yau Allah ya ba da maƙiyinka a hannunka. Bari in kafe shi da ƙasa da māshina, zan soke shi da māshi sau ɗaya tak, ba na bukata in soke shi sau biyu.” Amma Dawuda ya ce wa Abishai, “Kada ka hallaka shi. Wa zai sa hannu a kan shafaffe na Ubangiji, har yă tsira? Muddin Ubangiji yana a raye, Ubangiji da kansa zai buge shi, ko yă mutu a lokacinsa, ko kuma yă mutu a wurin yaƙi. Amma Allah yă sawwaƙa in sa hannu a shafaffen Ubangiji, ka ɗauki māshin da butar ruwan da take kusa da kansa mu tafi.” Saboda haka Dawuda ya ɗauki māshin da butar ruwan da take kusa da Shawulu suka tafi. Ba wanda ya gan su, ba wanda ya san abin da ya faru, ba kuwa wanda ya farka, dukansu suna barci gama Ubangiji ya sa barci mai nauyi ya ɗauke su. Sa’an nan Dawuda ya haye zuwa wancan gefen kwarin, ya hau kan wani tudu mai ɗan nisa inda Shawulu tare da mutanensa suke. Akwai babban fili tsakaninsu. Sai Dawuda ya kira sojojin Shawulu da kuma Abner ɗan Ner ya ce, “Abner ba za ka amsa mini ba?” Abner ya ce, “Wane ne yake kira yana damun sarki haka?” Dawuda ya ce wa Abner, “Wane irin mutum ne kai? Ba kai ne soja mafi iya yaƙi a Isra’ila ba? Don me ba ka yi gadin ranka yă daɗe, sarki da kyau ba? Ɗazu wani ya shiga tsakiyarku don yă kashe ranka yă daɗe, sarki. Abin da ka yi bai yi kyau ba. Muddin Ubangiji yana a raye kai da mutanenka kun cancanci mutuwa, domin ba ku lura da maigidanku shafaffe na Ubangiji ba. Ka duba kewaye da kai, ina māshi da kuma butar ruwan da suke kusa da kansa?” Shawulu ya gane muryar Dawuda, sai ya ce, “Muryarka ke nan ɗana Dawuda?” Dawuda ya ce, “I, muryata ce ya ranka yă daɗe, sarki.” Ya ƙara da cewa, “Don me ranka yă daɗe, yake fafarata? Mene ne na yi? Wane abu ne aka same ni da laifi a kai? To, bari ranka yă daɗe, sarkina yă kasa kunne yă ji abin da zan faɗa. Idan Ubangiji ne ya sa ka yi fushi da ni, bari yă karɓi hadaya ta hatsi. Amma idan mutane ne suka sa ka, bari a la’anta su, Ubangiji ne shaidata. Gama sun kore ni don kada in sami rabo cikin gādon Ubangiji, suna cewa, ‘Ka je ka bauta wa waɗansu alloli.’ Kada ka yarda jinina yă zuba a ƙasa nesa da gaban Ubangiji. Sarkin Isra’ila ya fito yă nemi kuɗin cizo kamar mai farautar kazan duwatsu.” Sai Shawulu ya ce, “Na yi zunubi ka dawo Dawuda ɗana. Ba zan yi maka kome ba, domin ka darajarta raina yau. Lalle na yi wawanci! Na yi babban kuskure.” Dawuda ya ce, “Ga māshin sarki, ka aiko wani saurayi yă zo yă karɓa. Ubangiji yakan sāka wa kowa bisa ga adalcinsa da amincinsa. Ubangiji ya bashe ka a hannuna yau, amma ba zan sa hannuna a kan shafaffe na Ubangiji ba. Kamar yadda na ga darajar ranka yau. Haka ma bari Ubangiji yă ga darajar raina, yă cece ni daga dukan wahala.” Sai Shawulu ya ce wa Dawuda, “Allah yă albarkace ka ɗana, Dawuda, za ka yi manyan abubuwa, tabbatacce kuma ka yi nasara.” Sai Dawuda ya yi tafiyarsa, Shawulu kuwa ya koma gida. Dawuda ya yi tunani a ransa ya ce, “Wata rana Shawulu zai kashe ni, abu mafi kyau da zan yi shi ne in tsere zuwa ƙasar Filistiyawa. Da haka Shawulu zai fid da zuciya ga nemana a ƙasar Isra’ila, a can kuwa zan tsira daga hannunsa.” Sai Dawuda tare da mutanensa, mutum ɗari shida suka tashi suka haye zuwa wurin Akish ɗan Mawok, sarkin Gat. Dawuda da mutanensa suka zauna a Gat tare da Akish. Kowa ya kasance tare da iyalinsa. Dawuda kuwa yana tare da matansa biyu. Ahinowam daga Yezireyel da Abigiyel matar Nabal da ya mutu daga Karmel. Da Shawulu ya sami labari cewa Dawuda ya gudu zuwa Gat, bai ƙara fita nemansa ba. Sai Dawuda ya ce wa Akish, “In na sami tagomashi a gabanka ka ba ni wani wuri a cikin biranenka in zauna a can. Don me bawanka zai kasance tare da kai a gidan sarauta?” A ranar Akish ya ba shi Ziklag wanda tun dā take ta sarkin Yahuda. Dawuda ya zauna a yankin Filistiyawa shekara ɗaya da wata huɗu. Dawuda da mutanensa suka haura suka yaƙi Geshurawa, da Girziyawa, da Amalekawa. (Waɗannan su ne mazaunan ƙasar a dā, tun daga Shur har zuwa ƙasar Masar.) Duk lokacin da ya yaƙi wani wuri, ba ya barin namiji ko mace da rai, amma sai ya kwashe tumaki, da shanu, da jakuna, da raƙuma, da riguna, sa’an nan yă koma wurin Akish. Idan Akish ya ce, “Ina ka kai hari yau?” Sai Dawuda yă ce, “Na kai hari a Negeb ta Yahuda, ko Negeb ta Yerameyel, ko Negeb na Keniyawa.” Bai bar a kawo namiji ko mace da rai a Gat ba, gama yana tunani, “Za su ba da sanarwa a kanmu su ce, ‘Ga abin da Dawuda ya yi.’ ” Haka ya yi ta yi dukan rayuwarsa a ƙasar Filistiyawa. Akish ya amince da Dawuda sosai, har ya ce wa kansa, “Ga shi ya mai da kansa abin ƙi ga mutanensa Isra’ilawa, zai zama bawana har abada.” Filistiyawa suka tattara sojojinsu domin su yaƙi Isra’ila. Akish ya ce wa Dawuda, “Sai ka sani fa, kai da mutanenka za ku tafi tare da ni da sojojina.” Dawuda ya ce, “Kai da kanka za ka ga abin da bawanka zai yi.” Akish ya ce, “Da kyau, zan sa ka zama mai kāre ni.” Sama’ila dai ya riga ya rasu, dukan Isra’ila suka yi makokinsa suka binne shi a garinsa a Rama. Shawulu kuma ya kori duk masu duba da masu maitanci daga ƙasar. Filistiyawa suka tattaru suka yi sansani a Shunem. Shawulu ya tattara dukan Isra’ila suka yi sansani a Gilbowa. Da Shawulu ya ga sojojin Filistiyawa sai ya ji tsoro, ya firgita ƙwarai. Ya nemi nufin Ubangiji amma bai sami amsa daga wurin Ubangiji ko ta wurin mafarki, ko ta wurin Urim, ko ta wurin annabawa ba. Shawulu ya ce wa fadawansa, “Ku nemo mini wata mace mai duba domin in tafi wurinta in yi tambaya.” Suka ce, “Akwai guda a En Dor.” Sai Shawulu ya sa waɗansu tufafi ya ɓad da kama, shi da waɗansu mutum biyu suka tafi wurin matar da dare, ya ce mata, “Ki yi mini duba ta hanyar sihiri, ki hawar mini duk wanda zan faɗa miki.” Amma matar ta ce masa, “Tabbatacce ka dai san abin da Shawulu ya yi, ya karkashe masu duba da masu maitanci a ƙasar. Me ya sa kake sa mini tarko, don ka sa a kashe ni?” Shawulu ya rantse mata da Ubangiji. Ya ce, “Muddin Ubangiji yana a raye, ba za a hukunta ki a kan wannan ba.” Sai matar ta ce, “Wa kake so in hauro maka?” Sai ya ce, “Ki hauro mini da Sama’ila.” Da matar ta ga Sama’ila sai ta yi ihu da ƙarfi ta ce wa Shawulu, “Me ya sa ka ruɗe ni? Kai ne Shawulu!” Sai sarki ya ce mata, “Kada ki ji tsoro. Me kika gani?” Matar ta ce, “Na ga wani kurwa tana fitowa daga ƙasa.” Ya ce, “Yaya kamanninsa yake?” Ta ce, “Wani tsoho sanye da taguwa ne yake haurawa.” Shawulu ya gane cewa Sama’ila ne, sai ya rusuna da fuskarsa har ƙasa. Sama’ila ya ce wa Shawulu, “Don me ka dame ni, ta wurin hauro da ni?” Shawulu ya ce, “Ina cikin babban damuwa ce, Filistiyawa sun fāɗa mini, Allah kuma ya juya mini baya. Bai amsa mini, ko ta mafarki, ko kuma ta annabawa ba, saboda haka na kira ka don ka gaya mini abin yi.” Sama’ila ya ce, “Don me kake tambayata bayan Ubangiji ya rabu da kai? Ya zama maƙiyinka? Ubangiji ya cika abin da ya yi magana ta wurina. Ubangiji ya fizge mulki daga hannunka, ya ba maƙwabcinka Dawuda. Gama ba ka yi biyayya ga Ubangiji ba, ba ka zartar da hukuncinsa mai zafi a kan Amalekawa ba. Saboda haka Ubangiji ya yi maka haka yau. Ubangiji zai ba da Isra’ila da kuma kai ga Filistiyawa, gobe kuwa da kai da ’ya’yanka za ku kasance tare da ni. Ubangiji kuma zai ba da sojojin Isra’ila a hannun Filistiyawa.” Da jin maganar Sama’ila sai Shawulu ya faɗi ƙasa warwas. Tsoro ya kama shi ƙwarai. Ba shi kuma da ƙarfi domin bai ci kome ba dukan yini da kuma dukan dare. Da matar ta zo wurin Shawulu, ta ga shi a firgice, sai ta ce masa, “Duba baranyarka ta yi maka biyayya ta yi kasai da ranta, ta yi abin da ka ce ta yi. To, kai ma ka kasa kunne ga baranyarka, zan ba ka abinci ka ci don ka sami ƙarfin tafiya.” Sai ya ƙi. Ya ce, “Ba zan ci abinci ba.” Sai da bayinsa da matar suka roƙe shi, sa’an nan ya ji maganarsu, ya tashi daga ƙasa, ya zauna a bakin gado. Matar kuwa tana da maraƙin da take kiwo a gida, sai ta ɗauke shi nan da nan ta yanka. Ta ɗauki garin fulawa ta kwaɓa, ta yi waina marar yisti. Sai ta kawo wa Shawulu da bayinsa suka kuwa ci. A daren nan suka tashi suka tafi. Filistiyawa suka tattara dukan rundunoninsu a Afek. Isra’ila kuwa suka yi sansani kusa da maɓulɓular da take Yezireyel. Sa’ad da sarakuna Filistiyawa suke wucewa da rundunarsu na mutum ɗari-ɗari da na dubu-dubu. Dawuda da mutanensa suna biye a baya tare da Akish. Komandodin Filistiyawa suka ce, “Waɗannan Ibraniyawa kuma fa?” Akish ya ce, “Wannan shi ne Dawuda hafsan Shawulu, sarkin Isra’ila. Yana nan tare da ni shekara guda ke nan. Ban kuwa taɓa samunsa da wani lahani ba tun daga ranar da ya bar Shawulu.” Amma komandodin Filistiyawa suka yi fushi, suka ce, “Ka sa mutumin nan yă koma zuwa wurin da ka ba shi yă zauna. Ba zai bi mu zuwa wurin yaƙi ba. Yana iya juya a kanmu lokacin yaƙin. Zai iya yin amfani da wannan zarafi yă ciccire kawunanmu don yă faranta wa maigidansa rai? Tuna fa, ba shi ne Dawuda ɗin da ake girmama da rawa da waƙoƙi ana cewa, “ ‘Shawulu ya kashe dubbai, Dawuda kuwa dubbun dubbai ba’?” Saboda haka Akish ya kira Dawuda ya ce masa, “Muddin Ubangiji yana a raye, na amince da kai tun daga ranar da ka zo wurina har yă zuwa yau, ban same ka da wani laifi ba, na kuma yi farin ciki in sa ka a cikin sojojina don ka yi mini aiki. Amma masu mulki nawa ba su yarda da kai ba. Sai ka juya ka koma ka isa lafiya ba tare da ɓata wa masu mulkin Filistiyawa rai ba.” Dawuda ya ce wa Akish, “Me na yi? Ka taɓa samun bawanka da laifi tun daga ranar da na zo har zuwa yanzu? Ina dalilin da ba zan tafi tare da kai in yaƙi maƙiyin ranka yă daɗe, sarki ba?” Akish ya ce, “A ganina kai marar laifi ne kamar mala’ikan Allah, duk da haka shugabannin sojojin Filistiyawa sun ce, ‘Ba zai tafi yaƙi tare da mu ba.’ Ka tashi da sassafe, kai da bayin shugabanka da suka zo tare da kai. Da gari ya waye sai ku kama hanya.” Gari na wayewa tun da sassafe Dawuda da mutanensa suka tashi suka kama hanyar komawa ƙasar Filistiyawa. Filistiyawa kuwa suka haura zuwa Yezireyel. A rana ta uku, Dawuda da mutanensa suka isa Ziklag, sai suka tarar Amalekawa sun riga sun kawo wa Negeb da Ziklag hari. Suka cinye Ziklag, suka ƙone ta, suka kwashe mata, yara da tsofaffi da dukan abubuwan da suke cikin garin. Ba su kashe kowa ba, amma suka kwashe su, suka tafi. Da Dawuda da mutanensa suka isa Ziklag suka tarar an ƙone garin, an kuma kwashe matansu, da ’ya’yansu mata, da kuma ’ya’yansu maza ganima, sai Dawuda da mutanensa suka yi kuka, suka yi ta kuka har sai da ƙarfinsu ya ƙare. An kama matan Dawuda, wato, Ahinowam daga Yezireyel da Abigiyel matar Nabal mutumin Karmel wanda ya rasu. Dawuda kuwa ya damu ƙwarai domin mutanensa suna niyyar su jajjefe shi da duwatsu, kowannensu ransa ya ɓace saboda ’ya’yansa maza da mata, amma Dawuda ya sami ƙarfafawa a cikin Ubangiji Allahnsa. Sai Dawuda ya ce wa Abiyatar firist, ɗan Ahimelek, “Kawo mini efod.” Sai Abiyatar ya kawo masa. Dawuda kuwa ya nemi nufin Ubangiji ya ce, “In bi bayan ’yan harin nan? Zan ci musu?” Ubangiji ya ce, “Bi su, gama za ka ci musu, ka ƙwato abin da suka kwashe.” Dawuda da mutanensa ɗari shida suka kama hanya, da suka kai Kwarin Besor, waɗansunsu suka tsaya a can. Dawuda ya ci gaba da mutane ɗari huɗu, don mutane ɗari biyu sun gaji sosai har sun kāsa ƙetare rafin Besor. Suka sami wani mutumin Masar a fili suka kawo shi wurin Dawuda. Suka ba shi abinci ya ci, suka kuma ba shi ruwa ya sha. Suka ba shi saura wainan ’ya’yan ɓaure da kuma wainan ’ya’yan inabi, ya ci ya sami ƙarfi. Gama bai ci ba, bai sha ba, har yini uku da dare uku. Dawuda ya tambaye shi ya ce, “Wane ne ubangidanka, kuma daga ina ka fito?” Ya ce, “Ni mutumin Masar ne, bawan wani mutumin Amalek. Maigidana ya ƙyale ni sa’ad da na yi rashin lafiya kwanaki ukun da suka wuce. Mun kai hari a Negeb ta Keretawa ta Yahuda, da Negeb ta Kaleb, muka kuma ƙone Ziklag.” Dawuda ya ce masa, “Za ka iya kai ni wurin maharan nan?” Ya ce, “Idan ka rantse mini da Allah, ba za ka kashe ni ba, ba kuwa za ka mai da ni wurin ubangidana ba, sai in kai ka inda maharan suke.” Ya bi da Dawuda har zuwa can, sai ga su a baje ko’ina a ƙasa, suna ci, suna sha, suna annashuwa saboda yawan ganimar da suka kwashe daga ƙasar Filistiyawa da ƙasar Yahuda. Dawuda ya yaƙe su tun daga fāɗuwar rana har yammar kashegari. Ba ko ɗaya da ya tsira sai samari ɗari huɗu waɗanda suka tsere a kan raƙuma. Dawuda ya ƙwato kome da Amalekawa suka kwashe tare da matarsa biyu. Babu abin da ya ɓace, Dawuda ya dawo da kowa, manya da ƙanana, ’yan maza da ’yan mata duka, da dukan abubuwan da Amalekawa suka kwashe. Ya kuma ƙwato garkunan tumaki, da na awaki, da na shanu. Mutanensa suka koro shanun, suka yi gaba, suka ce, “Wannan shi ne ganimar Dawuda.” Da Dawuda ya zo wurin mutum ɗari biyu ɗin nan waɗanda suka tafke, suka kāsa binsa, waɗanda aka bari a bakin Kwarin Besor, sai suka taryi Dawuda da mutanensa da suka tafi tare da shi. Sa’ad da Dawuda ya zo kusa da su, sai ya gaishe su. Sai dukan mugaye da marasa kirki daga cikin mutanen da suka tafi tare da Dawuda suka ce, “Tun da yake ba su tafi tare da mu ba, ba za mu ba su kome daga cikin ganimar da muka ƙwato ba, sai dai kowane mutum yă ɗauki matarsa da ’ya’yansa yă tafi.” Dawuda ya ce, “A’a, ’yan’uwana ba za ku yi haka da abin da Ubangiji ya ba mu ba. Ya tsare mu, ya kuma bashe sojojin da suka yi gāba da mu a hannuwanmu. Wa zai goyi bayanku a kan wannan al’amari? Wanda ya tafi wurin yaƙi da wanda ya zauna wurin kaya, rabonsu zai zama daidai.” Dawuda ya sa wannan tă zama dawwammamiyar farilla ga Isra’ila tun daga wannan rana har yă zuwa yau. Da Dawuda ya iso Ziklag, sai ya aika wa abokansa, dattawan Yahuda da rabo daga cikin ganimar ya ce, “Ga kyauta dominku, daga cikin ganimar maƙiyan Ubangiji.” Kyautar domin waɗanda suke a Betel, da Ramot ta Negeb, da Yattir, da Arower, da Sifmot, da Eshtemowa, da Rakal, da garuruwan Yerameyelawa, da garuruwan Keniyawa, da Horma, da Bor-Ashan, da Atak, da Hebron, da dukan wuraren da Dawuda da mutanensa suka taɓa zagawa. Filistiyawa suka yi yaƙi da Isra’ilawa, sai Isra’ilawa suka gudu a gaban Filistiyawa, aka kuma karkashe da yawa a dutsen Gilbowa. Filistiyawa suka abka wa Shawulu da ’ya’yansa maza, suka kashe ’ya’yan Shawulu. Yonatan da Abinadab da Malki-Shuwa. Yaƙin ya yi zafi ƙwarai kewaye da Shawulu, har maharba suka ji masa ciwo sosai bayan sun sha ƙarfinsa. Sai Shawulu ya ce wa mai ɗauka masa makami, “Ka zare takobinka ka soke ni, kada waɗannan marasa kaciya su zo su ci mini mutunci, su kashe ni.” Amma mai ɗaukan makaman bai yarda ba don ya ji tsoro sosai. Sai Shawulu ya zāre takobinsa ya soki kansa. Da mai ɗaukar makamai ya ga Shawulu ya mutu, sai shi ma ya zāre takobinsa ya soki kansa ya mutu. Shawulu da yaransa uku da mai ɗaukar makamansa da dukan mutanensa suka mutu a rana ɗaya. Sa’ad da Isra’ilawa na bakin kwari da waɗanda suke hayin Urdun suka ga sojojin Isra’ila suna gudu, Shawulu da yaransa uku kuma duk sun mutu, sai suka bar mallakansu suka sheƙa da gudu. Filistiyawa kuwa suka zo suka mamaye wuraren. Kashegari, da Filistiyawa suka zo domin su washe kayan matattun, sai suka tarar Shawulu da ’ya’yansa uku duk sun mutu, a dutsen Gilbowa. Suka sare kansa suka tuɓe makamansa, suka aika manzanni a dukan ƙasar Filistiyawa, su ba da labarin a haikalin allolinsu da cikin mutanensu. Suka ajiye makaman Shawulu a cikin haikalin gumakan Ashtarot. Suka kafa gawarsa a kan katanga Bet-Shan. Sa’ad da mutanen Yabesh Gileyad suka sami labarin abin da Filistiyawa suka yi wa Shawulu. Sai dukan jarumawansu suka tashi cikin dare suka tafi Bet-Shan suka saukar da gawar Shawulu da na ’ya’yansa daga kan katangan Bet-Shan suka tafi Yabesh inda suka ƙone su. Sai suka kwashi ƙasusuwansu suka binne a gindin itace tsamiya a Yabesh, suka kuma yi azumi kwana bakwai. Bayan mutuwar Shawulu, Dawuda ya dawo daga karkashe Amalekawa. Sai ya zauna a Ziklag kwana biyu. A rana ta uku sai ga wani mutum ya zo daga sansanin Shawulu da yagaggen riga da ƙura a kansa. Da ya zo wurin Dawuda sai ya fāɗi a ƙasa don yă nuna bangirma. Dawuda ya tambaye shi ya ce, “Daga ina ka fito?” Ya amsa ya ce, “Na tsere ne daga sansanin Isra’ila.” Dawuda ya ce, “Gaya mini, me ya faru?” Sai ya ce, “Mutane sun gudu daga yaƙi, aka kuma karkashe yawancin mutane. Shawulu da ɗansa Yonatan ma sun mutu.” Sai Dawuda ya ce wa saurayin da ya kawo labarin, “Yaya ka san cewa Shawulu da ɗansa Yonatan sun mutu?” Saurayin ya ce, “Ina kan dutsen Gilbowa a lokacin sai na ga Shawulu jingine a māshinsa. Kekunan yaƙi da mahayansu suna matsowa kusa da shi. Da ya juya ya gan ni sai ya kira ni, na kuwa ce masa, ‘Ga ni?’ “Ya tambaye ni ya ce, ‘Wane ne kai?’ “Na ce, ‘Ni mutumin Amalek ne.’ “Sai ya ce mini, ‘Matso kusa ka kashe ni! Ina cikin azabar mutuwa, sai dai har yanzu ina da rai.’ “Saboda haka na matso kusa da shi na kashe shi, domin na san cewa ba zai yi rai ba, da yake ya riga ya fāɗi. Sai na cire rawanin da yake kansa, na kuma cire warwaron hannunsa, na kuwa kawo maka su duka, ranka yă daɗe!” Sai Dawuda da dukan mutanen da suke tare da shi suka yayyage rigunarsu. Suka yi makoki, da kuka, da azumi har yamma saboda Shawulu da ɗansa Yonatan, da saboda sojojin Ubangiji, da kuma gidan Isra’ila, gama an karkashe su a yaƙi. Dawuda ya ce wa saurayin da ya kawo labarin, “Daga ina ka fito?” Ya ce, “Ni ɗan wani baƙo ne, mutumin Amalek.” Dawuda ya ce masa, “Yaya ba ka ji tsoro ɗaga hannu ka hallaka shafaffe na Ubangiji ba?” Sai Dawuda ya kira ɗaya daga cikin mutanensa ya ce, “Je ka kashe shi!” Haka kuwa ya buge shi, ya kuwa mutu. Gama Dawuda ya riga ya ce masa, “Alhakin jininka yana bisa kanka tun da yake da bakinka ka ce, ‘Ni ne na kashe shafaffe na Ubangiji.’ ” Dawuda ya rera wannan makoki saboda Shawulu da ɗansa Yonatan. Ya umarta a koya wa mutanen Yahuda wannan waƙa mai suna Makokin Baka (tana a rubuce a Littafin Yashar), “Ya Isra’ila, an kashe darajarki a kan tuddanki. Ga shi, jarumawa sun fāɗi! “Kada a faɗe shi a Gat, kada a yi shelarsa a titunan Ashkelon, don kada ’yan matan Filistiyawa su yi murna don kada ’yan matan marasa kaciya su yi farin ciki. “Ya duwatsun Gilbowa, kada a sāke yin ruwa ko raɓa a kanku, balle gonakin da suke ba da hatsin hadaya su ƙara bayarwa. Gama a can ne garkuwoyin manyan sojoji suka kwanta, suka kwanta a wulaƙance. Garkuwar Shawulu kuwa, ba za a ƙara shafa mata mai ba. “Daga jinin waɗanda aka kashe, daga tsokar naman jarumi, bakan Yonatan bai juye baya ba, takobin Shawulu bai komo ba tare da gamsuwa ba. Shawulu da Yonatan, a raye ƙaunatattu ne da kuma bansha’awa, a mace kuma ba su rabu ba. Sun fi gaggafa sauri, sun fi zaki ƙarfi. “Ya ku ’yan matan Isra’ila, ku yi kuka saboda Shawulu, wanda ya suturta ku da jajjayen kayan ado, wanda ya yi wa rigunarku ado da zinariya. “Jarumawa sun fāɗi a yaƙi! Ga Yonatan matacce a tuddanku. Na yi baƙin ciki saboda kai, Yonatan ɗan’uwana; ƙaunatacce kake a gare ni. Ƙaunarka a gare ni abar al’ajabi ce, abar al’ajabi fiye da ta mace. “Jarumawa sun fāɗi! Makaman yaƙi sun hallaka!” Bayan ’yan kwanaki, sai Dawuda ya nemi nufin Ubangiji ya ce, “In haura zuwa ɗaya daga cikin biranen Yahuda?” Ubangiji ya ce, “Haura.” Dawuda ya ce, “Wanne zan tafi?” Ubangiji ya ce, “Je Hebron.” Saboda haka sai Dawuda ya tafi can tare da matansa biyu, Ahinowam daga Yezireyel da Abigiyel gwauruwar Nabal mutumin Karmel. Dawuda kuma ya tafi tare da dukan mutanen da suke tare da shi, kowa da iyalinsa, suka zauna a Hebron da garuruwansa. Sa’an nan mutanen Yahuda suka zo Hebron, a can kuwa suka naɗa Dawuda sarkin Yahuda. Sa’ad da aka gaya wa Dawuda cewa mutanen Yabesh Gileyad ne suka binne Shawulu, sai ya aiki manzanni zuwa Yabesh Gileyad a ce musu, “ Ubangiji yă albarkace ku saboda alherin da kuka nuna wa Shawulu ta wurin binne shi. Bari Ubangiji yă nuna muku ƙaunarsa da amincinsa, ni kuma zan nuna muku irin wannan alherin saboda kun yi haka. Yanzu fa, sai ku ƙarfafa, ku yi jaruntaka, gama Shawulu sarkinku ya mutu, gidan Yahuda kuwa sun naɗa ni sarki a kansu.” Ana cikin haka, Abner ɗan Ner, komandan sojojin Shawulu, ya ɗauki Ish-Boshet ɗan Shawulu ya kawo shi Mahanayim. Ya naɗa shi sarkin Gileyad, da na Ashuri, da na Yezireyel, da a kan Efraim, da Benyamin, da kuma na dukan Isra’ila. Ish-Boshet ɗan Shawulu yana da shekaru arba’in sa’ad da ya zama sarkin Isra’ila, ya kuma yi sarauta shekara biyu. Amma fa, gidan Yahuda, suka bi Dawuda. Tsawon lokacin da Dawuda ya yi mulki a Hebron a kan gidan Yahuda, shekara bakwai ne da wata shida. Abner ɗan Ner, tare da mutanen Ish-Boshet ɗan Shawulu, suka bar Mahanayim suka tafi Gibeyon. Yowab wanda ake ce mamarsa Zeruhiya tare da waɗansu mutanen Dawuda suka fito suka haɗu da su tafkin Gibeyon, Suka zauna, waɗannan a wannan gefe, waɗancan a wancan gefe. Sa’an nan Abner ya ce wa Yowab, “Bari mu bar waɗansu samari su tashi su yi faɗa hannu da hannu a gabanmu.” Yowab ya ce, “To, su tashi.” Saboda haka samarin suka tashi aka ƙidaya su, mutum sha biyu wajen Benyamin da Ish-Boshet ɗan Shawulu, sha biyu kuma wajen Dawuda. Sa’an nan kowannensu ya kama abokin gābansa a kā ya soki da wuƙa a jiki, sai duka suka fāɗi a ƙasa. Saboda haka ne ake kiran wannan wuri Helkat Hazzurim a Gibeyon. Faɗan ya yi zafi a ranar ƙwarai, mutanen Dawuda suka ci mutanen Abner da na Isra’ila. ’Ya’yan Zeruhiya, maza uku sun kasance a can. Su ne, Yowab, Abishai da Asahel. To, Asahel mai gudu ne kamar barewa. Ya fafari Abner, bai juya dama ko hagu ba, yayinda yake fafararsa. Abner ya waiga, sai ya ce, “Kai ne, Asahel?” Ya ce, “Ni ne.” Sai Abner ya ce masa, “Yi dama ko hagu ka runtumi ɗaya daga cikin samarin, ka ƙwace makamansa.” Amma Asahel bai bar fafararsa ba. Abner ya sāke gargaɗe shi ya ce, “Ka bar fafarata! Yaya zan kashe ka? Yaya zan yin ido biyu da ɗan’uwanka Yowab?” Amma Asahel ya ƙi yă bar fafararsa; saboda haka Abner ya soki Asahel da māshinsa a ciki; har māshin ya fita ta bayansa. Nan take ya fāɗi, ya mutu. Kowa da ya zo wurin da Asahel ya fāɗi, ya mutu, sai yă tsaya. Amma Yowab da Abishai suka fafari Abner, kuma da rana tana fāɗuwa sai suka iso tudun Amma, kusa da Giya, a hanyar zuwa jejin Gibeyon. Sa’an nan mutanen Benyamin suka haɗa kansu suka koyi bayan Abner. Suka zama ƙungiya guda, suka tsaya daram a kan tudu. Sai Abner ya kira Yowab ya ce, har abada ne māshi zai yi ta hallakarwa? Ba ka sani cewa ƙarshen zai zama da ɗaci ba. Sai yaushe za ka umarci mutanenka su daina fafaran ’yan’uwansu? Yowab ya ce, “Muddin Allah yana a raye, da ba a ce ka yi magana ba, da mutanen za su ci gaba da fafaran ’yan’uwansu har gari yă waye.” Sai Yowab ya busa ƙaho, dukan mutane kuwa suka tsaya; suka daina fafaran Isra’ila. Nan take faɗan ya tsaya. Abner da mutanensa suka ratsa kwarin Urdun dukan dare. Sa’an nan suka haye kogin, suka kuwa ci gaba dukan safe har suka zo Mahanayim. Da Yowab ya dawo daga fafaran Abner, sai ya tattara dukan mutanensa. Ban da Asahel, sai ya gane an rasa mutum goma sha tara na Dawuda. Amma mutanen Dawuda sun kashe mutum ɗari uku da sittin daga kabilar Benyamin da suke tare da Abner. Suka ɗauki gawar Asahel suka binne a kabarin mahaifinsa a Betlehem. Sa’an nan Yowab da mutanensa suka bi dare har suka iso Hebron da safe. Aka daɗe ana yaƙi tsakanin gidan Shawulu da gidan Dawuda. Dawuda kuwa ya yi ta ƙara ƙarfi, yayinda gidan Shawulu ya yi ta raguwa a ƙarfi. An haifa wa Dawuda ’ya’ya maza a Hebron. Ɗansa na fari shi ne Amnon, ɗan Ahinowam mutuniyar Yezireyel; na biyu shi ne Kileyab, ɗan Abigiyel gwauruwar Nabal mutumin Karmel; na uku shi ne Absalom, ɗan Ma’aka ’yar Talmai sarkin Geshur; na huɗu shi ne Adoniya, ɗan Haggit; na biyar shi ne Shefatiya, ɗan Abital; na shida kuma shi ne Itireyam, ɗan Egla matar Dawuda. An haifi waɗannan wa Dawuda a Hebron. Sa’ad da ake yaƙi tsakanin gidan Shawulu da gidan Dawuda, sai Abner ya yi ta ƙarfafa matsayinsa a gidan Shawulu. To, Shawulu yana da ƙwarƙwarar da ake kira Rizfa, ’yar Aiya. Sai Ish-Boshet ya ce wa Abner, “Don me kake kwana da ƙwarƙwarar mahaifina?” Abner ya husata saboda abin da Ish-Boshet ya ce, sai ya ce, “Kana tsammani ni mai cin amana ne? Kana zato ni mai goyon bayan Yahuda ne? Tun farko na nuna aminci ga gidan babanka Shawulu, da ’yan’uwansa, da abokansa! Ban kuwa ba da kai a hannun Dawuda ba. Ga shi yanzu a kan mace za ka ga laifina? Allah yă yi wa Abner hukunci mai tsanani, in ban goyi bayan Dawuda ya sami abin da Ubangiji ya yi masa alkawari da rantsuwa ba. Zan kuma mayar wa Dawuda sarautar gidan Shawulu, in kafa kursiyin Dawuda a kan Isra’ila, da kan Yahuda tun daga Dan har zuwa Beyersheba.” Ish-Boshet bai ƙara yin karambanin ce wa Abner kome ba, gama yana tsoronsa. Sai Abner ya aiki manzanni a madadinsa wurin Dawuda su ce masa, “Ƙasar ta wane ne? Ka yi yarjejjeniya da ni, zan kuwa taimake ka, in juye dukan Isra’ila zuwa ɓangarenka.” Dawuda ya ce, “Da kyau, zan yi yarjejjeniya da kai, amma fa ina bukata abu guda daga gare ka, kada ka zo gabana in ba tare da matata Mikal, ’yar Shawulu ba.” Sai Dawuda ya aiki manzanni zuwa wurin Ish-Boshet ɗan Shawulu cewa, “Ka ba ni matata Mikal wadda na biya sadakinta da loɓa ɗari na Filistiyawa.” Sai Ish-Boshet ya ba da umarni, aka kuwa ɗauke ta daga gidan mijinta Faltiyel ɗan Layish. Amma mijin ya raka ta, yana tafe yana kuka, ya bi ta har Bahurim. Sai Abner ya ce masa, “Koma gida!” Sai ya koma. Abner ya tattauna da dattawan Isra’ila ya ce, “An daɗe kuna nema ku naɗa Dawuda sarkinku. To, yanzu sai ku yi haka! Gama Ubangiji ya yi wa Dawuda alkawari ya ce, ‘Ta wurin bawana Dawuda zan ceci mutanena Isra’ila daga hannun Filistiyawa, da kuma hannun dukan abokan gābansu.’ ” Abner kuma ya yi magana da mutane Benyamin da kansa. Sa’an nan ya tafi Hebron yă gaya wa Dawuda ko mene ne Isra’ila da kuma dukan gidan Benyamin suke so su yi. Sa’ad da Abner wanda yake tare da mutane ashirin suka zo wurin Dawuda a Hebron, Dawuda ya shirya masa liyafa tare da mutanensa. Sai Abner ya ce wa Dawuda, “Bari in tafi nan da nan in tattara dukan Isra’ila wa ranka yă daɗe, sarki, saboda su yi alkawari da kai, ka kuma ka yi mulki bisa dukansu yadda ranka yake so.” Saboda haka Dawuda ya sallami Abner, ya kuwa tafi lafiya. Ba a jima ba sai mutanen Dawuda da Yowab suka dawo daga hari. Suka kawo ganima da yawa tare da su. Abner kuwa ya riga ya bar Dawuda a Hebron, domin Dawuda ya sallame shi, shi kuma ya tafi lafiya. Sa’ad da Yowab da dukan sojoji suka dawo, aka gaya masa cewa Abner ɗan Ner ya zo wurin sarki, sarki kuwa ya sallame shi, ya kuma tafi lafiya. Sai Yowab ya je wurin sarki ya ce, “Me ke nan ka yi? Abner ya zo wurinka. Don me ka ƙyale shi yă tafi? Ga shi kuwa ya tafi! Ka san Abner ɗan Ner ya zo ne yă ruɗe ka, yă ga fitarka da shigarka, yă kuma binciki kome da kake yi.” Yowab ya tashi daga gaban Dawuda ya tafi ya aika manzanni su bi Abner. Suka same shi a rijiyar Sira suka komo da shi, Dawuda kuwa bai sani ba. To, da Abner ya komo Hebron, Yowab ya ratse da shi zuwa hanyar shigar gari kamar zai gana da shi a kaɗaice. Amma a can ya soki Abner a ciki, ya kashe shi don yă rama mutuwar ɗan’uwansa Asahel. Daga baya, Dawuda ya ji labarin sai ya ce, “Ni da masarautata har abada ba mu da laifi a gaban Ubangiji game da jinin Abner ɗan Ner. Alhakin jininsa yă kasance a kan Yowab da kuma a kan dukan iyalin mahaifinsa! Kada gidan Yowab yă rasa mai ɗiga, ko kuturu, ko mai jingina ga sanda, ko wanda aka kashe da takobi, ko kuma wanda ba shi da abinci.” (Yowab da ɗan’uwansa Abishai suka kashe Abner don yă kashe ɗan’uwansu Asahel a yaƙin Gibeyon.) Sa’an nan Dawuda ya ce wa Yowab da dukan mutanen da suke tare da shi, “Ku yayyage rigunarku, ku sa tsummoki, ku yi tafiya kuna kuka a gaban Abner.” Sarki Dawuda kansa ya bi masu ɗauke da gawar daga baya. Suka binne Abner a Hebron, sarki kuwa ya ɗaga murya ya yi kuka a kabarin Abner. Sarki ya kuma yi wannan waƙar makoki domin Abner ya ce, “Daidai ne Abner yă mutu, kamar yadda marasa bin doka suke mutuwa? Hannuwanka ba a daure suke ba, ƙafafunka ba a tabaibaye suke ba. Ka mutu kamar waɗanda suke mutuwa a hannun mugaye.” Sai dukan mutane suka sāke fashe da kuka saboda shi. Sa’an nan duk suka zo suka roƙi Dawuda yă ci wani abu tun rana ba tă fāɗi ba; amma Dawuda ya rantse ya ce, “Bari Allah yă hukunta ni, in na ɗanɗana abinci ko wani abu kafin rana ta fāɗi!” Dukan mutane suka lura suka kuma ji daɗi ƙwarai, tabbatacce kome da sarki ya yi, ya gamshe su. Saboda haka a ranar dukan mutane da dukan Isra’ila suka gane sarki ba shi da hannu a kisan Abner ɗan Ner. Sa’an nan sarki ya ce wa mutanensa, “Ba ku gane cewa ɗan sarki kuma babban mutum ya mutu a ƙasar Isra’ila a yau ba? A yau, ko da yake ni naɗaɗɗen sarki ne, duk da haka na raunana, kuma waɗannan ’ya’yan Zeruhiya sun fi ƙarfina. Ubangiji yă sāka wa mai aikata mugunta da muguntar da ya aikata!” Sa’ad da Ish-Boshet ya ji labari cewa Abner ya mutu a Hebron, sai ya karaya, sai dukan hankalin Isra’ila ya tashi. To, ɗan Shawulu yana da ’ya’ya maza biyu da suke shugabannin ’yan hari. Ana kiran ɗaya Ba’ana, ɗayan kuma Rekab. Su ’ya’yan Rimmon mutumin Benyamin ne daga Beyerot, an lissafta Beyerot a ɓangaren Benyamin, domin mutanen Beyerot sun gudu zuwa Gittayim inda suke zaman baƙunci har wa yau. (Yonatan ɗan Shawulu yana da ɗa mai suna Mefiboshet wanda yake gurgu a duka ƙafafu. Yana da shekara biyar ne sa’ad da labarin mutuwar Shawulu da Yonatan ya zo daga Yezireyel. Sai mai renonsa ta ɗauke shi ta gudu, amma yayinda take hanzari tă gudu, sai ya fāɗo, ya gurgunce.) To, Rekab da Ba’ana, ’ya’yan Rimmon mutumin Beyerot, suka tafi gidan Ish-Boshet, suka isa can da tsakar rana yayinda yake hutun tsakar rana. Suka shiga sashe na cikin gida sai ka ce suna so su ɗibo alkama ne, suka soke shi a ciki. Sa’an nan Rekab da Ba’ana ɗan’uwansa suka zame suka ɓace. Sun shiga gidan yayinda yake kwance a gado a ɗakin barcinsa. Bayan sun soke shi sai suka kashe shi, suka kuma datse kansa. Suka ɗauke shi, suka yi tafiya dukan dare suka bi ta Araba. Suka kawo kan Ish-Boshet wa Dawuda a Hebron, suka ce wa sarki, “Ga kan Ish-Boshet ɗan Shawulu, maƙiyinka, wanda ya nemi yă kashe ka. A yau Ubangiji ya rama wa ranka yă daɗe sarki, a kan Shawulu da zuriyarsa.” Dawuda ya ce wa Rekab da ɗan’uwansa Ba’ana, ’ya’yan Rimmon mutumin Beyerot, “Muddin Ubangiji yana a raye, wanda ya kuɓutar da ni daga wahala, sa’ad da wani mutum ya ce mini, ‘Shawulu ya mutu,’ yana tsammani ya kawo labari mai daɗi ne, na kama shi na kashe a Ziklag. Ladar da na ba shi ke nan saboda labarinsa! Balle fa, sa’ad da mugayen mutane suka kashe marar laifi a gidansa, a bisa gadonsa, ashe, ba zan nemi jininsa daga hannunku in kawar da ku a duniya ba!” Saboda haka Dawuda ya umarci mutanensa, suka kuwa kashe su. Suka yayyanka hannuwansu da ƙafafunsu, suka kuma rataye jikunansu kusa da tafki a Hebron. Amma suka ɗauki kan Ish-Boshet suka binne a kabarin Abner a Hebron. Dukan kabilar Isra’ila suka zo wurin Dawuda a Hebron suka ce, “Mu nama da jininka ne. A dā da Shawulu yake sarauta a bisanmu, kai ne kake bi Isra’ilawa zuwa yaƙe-yaƙensu. Ubangiji kuwa ya ce maka, ‘Za ka zama makiyayi mutanena Isra’ila, za ka kuma zama sarkinsu.’ ” Sa’ad da dukan dattawan Isra’ila suka zo wurin Sarki Dawuda a Hebron, sarki ya yi yarjejjeniya da su a gaban Ubangiji, suka kuwa naɗa Dawuda sarki bisa Isra’ila. Dawuda yana da shekara talatin ɗaya sa’ad da ya zama sarki, ya kuma yi mulki shekara arba’in. A Hebron ya yi mulki a bisa Yahuda shekara bakwai da wata shida, a Urushalima kuma ya yi mulki a bisa Isra’ila da Yahuda shekara talatin da uku. Sarki da mutanensa suka tafi Urushalima don su kai wa Yebusiyawan da suke zaune a can hari, Yebusiyawa suka ce wa Dawuda, “Ba za ka shiga nan ba; ko makafi da guragu kaɗai ma za su kore ka.” Suka yi tsammani suna cewa, “Dawuda ba zai iya shiga can ba.” Duk da haka, Dawuda ya kame kagarar Sihiyona, wadda ta zama Birnin Dawuda. A ranar, Dawuda ya ce, “Duk wanda zai kame Yebusiyawa, dole yă yi amfani da wuriyar ruwa don yă kai ga waɗannan ‘guragu da makafi’ waɗanda suke abokan gāban Dawuda.” Shi ya sa suka ce, “ ‘Makafi da guragu’ ba za su shiga fadan sarki ba.” Sai Dawuda ya zauna a kagarar, ya kuma kira ta Birnin Dawuda. Ya gina wuraren da suke kewaye da ita, tun daga madogaran gini zuwa ciki. Ya yi ta ƙara ƙarfi, gama Ubangiji Allah Maɗaukaki yana tare da shi. To, Hiram sarkin Taya ya aiki manzanni wurin Dawuda tare da gumaguman itacen al’ul, da kafintoci, da kuma maginan duwatsu, suka kuwa gina wa Dawuda fada. Dawuda kuwa ya gane Ubangiji ya naɗa shi sarki bisa Isra’ila, ya kuma ɗaukaka masarautarsa saboda mutanensa Isra’ila. Bayan ya bar Hebron, Dawuda ya ƙara ɗauko wa kansa waɗansu ƙwarƙwarai da mata a Urushalima. Aka haifa masa ’ya’ya maza da mata. Waɗannan su ne sunayen ’ya’yan da aka haifa masa a can. Shammuwa, Shobab, Natan, Solomon, Ibhar, Elishuwa, Nefeg, Yafiya, Elishama, Eliyada da Elifelet. Da Filistiyawa suka ji labari an shafe Dawuda sarki a bisa Isra’ila, sai suka haura da ƙarfi sosai don su nema shi, amma Dawuda ya ji labarin sai ya gangara zuwa mafaka. To, fa, Filistiyawa suka zo suka baje ko’ina a cikin Kwarin Refayim; saboda haka Dawuda ya nemi nufin Ubangiji ya ce, “In tafi in kai wa Filistiya hari? Za ka bashe su a hannuna?” Ubangiji ya amsa masa ya ce, “Je ka, gama tabbatacce zan bashe Filistiyawa a hannunka.” Saboda haka Dawuda ya tafi Ba’al-Ferazim, a can ya ci su da yaƙi. Sai ya ce, “Kamar yadda ruwa yakan fasu, haka Ubangiji ya kakkarya abokan gābana a gabana.” Saboda haka aka kira wurin Ba’al-Ferazim. Filistiyawa suka bar gumakansu a can, Dawuda da mutanensa kuwa suka kwashe su. Har yanzu Filistiyawa suka sāke haurawa suka bazu a Kwarin Refayim; saboda haka Dawuda ya nemi nufin Ubangiji, ya kuwa ce, “Kada ka haura kai tsaye, amma ka kewaya ta bayansu ka fāɗa musu a gaban itatuwan balsam. Da zarar ka ji tafiya kamar na takawar sojoji tana a bisan itatuwan balsam, sai ka yi maza, gama wannan alama ce cewa Ubangiji ya sha gabanka don yă karkashe sojojin Filistiyawa.” Saboda haka Dawuda ya aikata yadda Ubangiji ya umarce shi, ya kuma karkashe Filistiyawa tun daga Geba har zuwa Gezer. Dawuda ya sāke tattara zaɓaɓɓun mutanen Isra’ila, dubu talatin. Shi, da dukan mutanensa suka tashi daga Ba’ala-Yahuda don su hauro da akwatin alkawarin Allah, wanda ake kira da Sunan Ubangiji Maɗaukaki, wanda yake zama a tsakanin kerubobin da suke a kan akwatin alkawarin. Suka ɗauko akwatin alkawarin Allah a sabuwar keken yaƙi, suka kawo shi daga gidan Abinadab, wanda yake bisa tudu. Uzza da Ahiyo, ’ya’yan Abinadab maza, suka bi da keken yaƙin da akwatin alkawarin Allah yake ciki suka bi da keken yaƙin da akwatin alkawarin Allah yake ciki. Ahiyo kuwa yana tafiya a gaban Abinadab. Dawuda da dukan gidan Isra’ila suka yi biki sosai da dukan ƙarfinsu a gaban Ubangiji, da waƙoƙi, da molaye, da garayu, da ganguna, da kacau-kacau da kuma kuge. Da suka kai masussukar Nakon, sai Uzza ya miƙa hannu don yă riƙe akwatin alkawarin Allah, gama shanun sun yi tuntuɓe. Fushin Ubangiji kuwa ya ƙuna a kan Uzza domin aikin rashin bangirma, saboda haka Allah ya buge shi ya kuma mutu a can kusa da akwatin alkawarin Allah. Ran Dawuda ya ɓace gama fushin Ubangiji ya ɓarke a kan Uzza. Shi ya sa har wa yau ana kira wurin Ferez Uzza. Dawuda ya ji tsoron Ubangiji a ranar, sai ya ce, “Yaya akwatin alkawarin Ubangiji zai iya zuwa wurina?” Bai so yă ɗauki akwatin alkawarin Ubangiji yă kasance tare da shi a Birnin Dawuda ba. A maimakon haka sai ya kai shi gidan Obed-Edom mutumin Gat. Akwatin Alkawarin Ubangiji ya kasance a gidan Obed-Edom mutumin Gat har tsawon wata uku, Ubangiji kuwa ya albarkace shi da dukan iyalinsa. To, sai aka faɗa wa Sarki Dawuda cewa, “ Ubangiji ya sa wa gidan Obed-Edom albarka da dukan abin da yake da shi, saboda akwatin alkawarin Allah.” Saboda haka sai Dawuda ya gangara ya hauro da akwatin alkawarin Allah daga gidan Obed-Edom zuwa Birnin Dawuda da farin ciki. Sa’ad da waɗanda suke ɗaukan akwatin alkawarin Ubangiji suka yi tafiya taki shida, sai yă yi hadayar bijimi da saniya mai ƙiba. Dawuda, sanye da efod lilin, ya yi ta rawa a gaban Ubangiji da dukan ƙarfinsa, yayinda shi da dukan gidan Isra’ila suka hauro da akwatin alkawarin Ubangiji da sowa da kuma busar ƙahoni. Sa’ad da akwatin alkawarin Ubangiji ya shiga Birnin Dawuda, sai Mikal ’yar Shawulu ta leƙa ta taga ta ga Dawuda sarki yana tsalle, yana rawa a gaban Ubangiji, sai ta rena shi a zuciyarta. Suka kawo akwatin alkawarin Ubangiji, aka ajiye shi a inda aka shirya masa a cikin tentin da Dawuda ya shirya dominsa. Dawuda kuma ya miƙa hadaya ta ƙonawa da hadaya ta salama a gaban Ubangiji. Bayan ya gama yin hadaya ta ƙonawa da hadaya ta salama, sai ya albarkaci mutane a cikin sunan Ubangiji Maɗaukaki. Sa’an nan ya rarraba abinci, da ƙosai, dabino, da waina ga kowane mutum a cikin dukan jama’ar Isra’ila, maza da mata. Dukan mutane kuwa suka watse zuwa gidajensu. Da Dawuda ya koma gida don yă sa wa gidansa albarka, sai Mikal ’yar Shawulu ta fito don tă tarye shi, sai ta ce, “Tabbas sarkin Isra’ila ya fiffita kansa yau, ya tuɓe a gaban bayinsa ’yan mata, kamar yadda duk marar kunya yakan yi!” Dawuda ya ce wa Mikal, “Na yi rawana domin in girmama Ubangiji ne, wanda ya zaɓe ni a maimakon mahaifinki ko wani daga cikin dukan gidansa, shi ne kuma ya sa ni sarki a kan Isra’ila, mutanen Ubangiji, zan yi biki a gaban Ubangiji. Zan ma mai da kaina abin reni fiye da haka, za a kuma zama abin reni a gare ki. Amma waɗannan bayi ’yan matan da kika yi magana a kai, za su gan ni da martaba.” Mikal ’yar Shawulu kuwa ba tă haifi ɗa ba har mutuwarta. Bayan sarki ya kama zama a fadansa Ubangiji kuma ya hutashe shi daga dukan abokan gābansa da suke kewaye da shi, sai ya ce wa annabi Natan, “Ga ni, ina zama a fadar katakon al’ul, amma akwatin alkawarin Allah yana zaune a tenti.” Natan ya amsa wa sarki ya ce, “Duk abin da yake a zuciyarka, sai ka yi, gama Ubangiji yana tare da kai.” A daren nan maganar Ubangiji ta zo wa Natan cewa, “Je ka faɗa wa bawana Dawuda, ‘Ga abin da Ubangiji ya ce, kai ne za ka gina mini gida in zauna? Ban taɓa zama a gida ba tun daga ranar da na fito da Isra’ilawa daga Masar har yă zuwa yau. Ina dai kai da kawowa a tenti, a matsayin mazaunina. A cikin kaiwa da kawowar da nake yi cikin dukan Isra’ilawa, na taɓa ce wa wani shugabanninsu wanda na umarta su lura da mutanena Isra’ila, “Don me ba ku gina mini mazauni da katakon al’ul ba?” ’ “Yanzu, ka gaya wa bawana Dawuda ‘Ga abin da Ubangiji Maɗaukaki ya ce, na ɗauko ka daga makiyaya, daga kuma garken tumaki ka zama sarki bisan mutane Isra’ila. Na kasance tare da kai duk inda ka tafi, na kuma kawar da dukan abokan gābanka a gabanka. Yanzu zan sa sunanka yă shahara kamar sunayen shahararrun mutanen duniya. Zan kuma tanada wa mutanena Isra’ila wuri, in kuma dasa su yadda za su kasance da gida kansu ba tare da an ƙara damunsu ba. Mugayen mutane ba za su ƙara wahalshe su kamar dā ba, yadda suka yi tun lokacin da na naɗa shugabanni bisan mutanena Isra’ila, zan kuma hutashe ka daga hannun abokan gābanka. “ ‘ Ubangiji ya furta maka cewa Ubangiji kansa zai kafa maka gida. Sa’ad da kwanakinka suka ƙare, za ka huta tare da kakanninka, zan tā da zuriyarka, na cikinka, zan kuma sa mulkinsa ya kahu. Shi zai gina gida domin Sunana, zan kuwa kafa gadon sarautarsa har abada. Zan zama Ubansa, shi kuma yă zama ɗana. Idan ya yi laifi, zan yi amfani da mutane in hukunta shi. Mutane ne za su zama bulalata. Amma ba za a taɓa ɗauke ƙaunata daga gare shi yadda na ɗauke ta daga wurin Shawulu ba, shi wannan wanda na kawar daga gabanka. Gidanka da kuma masarautarka za su dawwama har abada a gabana; gadon sarautarka kuma zai kahu har abada.’ ” Natan ya gaya wa Dawuda dukan abin da Allah ya bayyana masa. Sa’an nan Sarki Dawuda ya je ya zauna a gaban Ubangiji ya ce, “Wane ne ni, ya Ubangiji Mai Iko Duka, ko gidana, har da ka ɗaga mu zuwa wannan matsayi? Har ya zama kamar wannan bai isa ba a gabanka, ya Ubangiji Mai Iko Duka, ka kuma yi magana game da nan gaba na gidan bawanka. Haka ka saba yi da mutane, ya Ubangiji Mai Iko Duka? “Me kuma Dawuda zai ce maka? Gama ka san bawanka, ya Ubangiji Mai Iko Duka. Gama saboda maganarka da kuma bisa ga nufinka, ka aikata wannan babban abu, ka kuma sanar da bawanka. “Kai mai girma ne, ya Ubangiji Mai Iko Duka! Babu wani kamar ka, babu kuma wani Allah sai kai; kamar yadda muka ji da kunnuwanmu. Wane ne kuma yake kamar da mutanenka Isra’ila, al’umma guda a duniya wadda Allah ya fita don yă kuɓutar wa kansa, ya kuma yi suna wa kansa, ya kuma aikata manyan abubuwa da kuma al’amuran banmamaki ta wurin korin al’ummai da allolinsu daga gaban mutanenka, waɗanda ka kuɓutar daga Masar? Ka kafa mutanenka Isra’ila kamar naka na kanka har abada, kai kuma, ya Ubangiji, ka zama Allahnsu. “Yanzu kuwa, ya Ubangiji Allah, ka cika alkawarin da ka yi game da bawanka da gidansa. Ka yi kamar yadda ka alkawarta, domin sunanka yă kasance da girma har abada. Sa’an nan mutane za su ce, ‘ Ubangiji Maɗaukaki, Allah ne a bisa Isra’ila!’ Kuma gidan bawanka Dawuda zai kahu a gabanka. “Ya Ubangiji Maɗaukaki, Allah na Isra’ila, ka bayyana wa bawanka cewa, ‘Zan gina maka gida.’ Saboda haka bawanka ya sami ƙarfin hali yă miƙa maka wannan addu’a. Ya Ubangiji Mai Iko Duka, kai Allah ne! Maganarka da aminci take, ka kuma yi wa bawanka waɗannan abubuwa masu kyau. In ya gamshe ka, bari ka albarkaci gidan bawanka don yă dawwama a gabanka har abada; gama kai, ya Ubangiji Mai Iko Duka, ka riga ka yi magana, kuma saboda kai ka sa albarka ga gidan bawanka, lalle zai kasance da albarka har abada.” Ana nan, sai Dawuda ya ci Filistiyawa da yaƙi, ya kawo ƙarshen mulkinsu a ƙasar, ya kuma ƙwace ƙasar Meteg Amma daga hannun Filistiyawa. Haka kuma Dawuda ya ci Mowabawa. Ya sa suka kwanta a ƙasa, ya kuma auna su da igiya. Kowane awo biyu ya sa a kashe su, amma awo na uku sai yă sa a bar su da rai. Saboda haka Mowabawa suka zama bayin Dawuda, suka kuma kawo masa haraji. Ban da haka, Dawuda ya yaƙi Hadadezer ɗan Rehob, sarkin Zoba. Wannan ya faru a lokacin da Hadadezer yake kan hanyarsa zuwa Kogin Yuferites don yă sāke mai da wurin a ƙarƙashin ikonsa. Dawuda ya kame keken yaƙinsa guda dubu, mahayan keken yaƙinsa dubu bakwai, da sojojin ƙasa dubu ashirin. Ya yayyanke agaran dawakan duka amma ya bar dawakai kekunan yaƙi ɗari. Sa’ad da Arameyawan Damaskus suka zo don su taimaki Hadadezer sarkin Zoba, sai Dawuda ya karkashe dubu ashirin da biyunsu. Ya ajiye ƙungiyoyi sojoji a masarautar Arameyawan Damaskus, Arameyawa kuwa suka zama bayinsa, suka biya shi haraji. Ubangiji ya ba Dawuda nasara a duk inda ya tafi. Dawuda ya kwashe garkuwoyin zinariya na shugabannin sojojin Hadadezer ya kawo Urushalima. Daga Teba da Berotai, garuruwan da suke ƙarƙashin Hadadezer, Sarki Dawuda ya kwashe tagulla masu yawan gaske. Da Towu sarkin Hamat ya ji cewa Dawuda ya ci dukan rundunar Hadadezer, sai ya aiki ɗansa Yoram wurin Sarki Dawuda yă gaishe, yă kuma yi masa barka saboda nasarar da ya yi a kan Hadadezer, gama Hadadezer nan ya hana Towu sakewa. Yoram ya tafi ɗauke da kayan azurfa, da na zinariya, da na tagulla. Sarki Dawuda kuwa ya keɓe waɗannan kayayyaki wa Ubangiji, yadda ya yi da zinariya, da kuma azurfa daga dukan al’umman da ya mallaka, wato, azurfa da zinariyan mutanen Edom, da na Mowabawa, da na Ammonawa, da na Filistiyawa, da na Amalekawa, da ganimar Hadadezer ɗan Rehob, sarkin Zoba. Dawuda kuwa ya ƙara zama shahararre bayan ya dawo daga kai wa ƙasar Aram hari, daga nan sai ya je ya karkashe mutanen Edom dubu goma sha takwas a Kwarin Gishiri. Ya ajiye rundunar sojoji ko’ina a Edom, dukan mutanen Edom kuwa suka zama bayin Dawuda. Ubangiji ya ba wa Dawuda nasara a duk inda ya tafi. Dawuda ya yi mulkin dukan ƙasar Isra’ila, yana yin wa dukan jama’arsa shari’ar gaskiya da adalci. Yowab ɗan Zeruhiya ya zama shugaban sojoji; Yehoshafat ɗan Ahilud kuwa shi ne marubucin tarihi; Zadok ɗan Ahitub da Ahimelek ɗan Abiyatar, su ne firistoci; Serahiya kuma sakatare; Benahiya ɗan Yehohiyada ne shugaban Keretawa da Feletiyawa, wato, sojoji masu gadin Dawuda, sa’an nan ’ya’yan Dawuda maza su ne mashawartan sarki. Wata rana Dawuda ya yi tambaya ya ce, “Akwai wani har yanzu da ya rage a gidan Shawulu wanda zan nuna masa alheri saboda Yonatan?” To, akwai wani bawa na gidan Shawulu mai suna Ziba. Sai aka kira shi yă bayyana a gaban Dawuda, sarki ya ce masa, “Kai ne Ziba?” Sai ya ce, “I, ni ne, ranka yă daɗe.” Sa’an nan sarki ya yi tambaya ya ce, “Babu wani har yanzu da ya rage a gidan Shawulu don in nuna masa alherin Allah?” Ziba ya ce wa sarki, “Har yanzu akwai ɗan Yonatan da ya rage, sai dai shi gurgu ne a dukan ƙafafu.” Sarki ya ce, “Ina yake?” Ziba ya ce, “Yana a gidan Makir ɗan Ammiyel a Lo Debar.” Saboda haka Sarki Dawuda ya umarta aka kawo shi daga gidan Makir ɗan Ammiyel, daga Lo Debar. Sa’ad da Mefiboshet ɗan Yonatan, ɗan Shawulu, ya zo wurin Dawuda, sai ya rusuna har ƙasa ya yi gaisuwar bangirma. Dawuda ya ce, “Mefiboshet!” Shi kuwa ya amsa ya ce, “Ranka yă daɗe, ga ni, bawanka.” Dawuda ya ce, “Kada ka ji tsoro, gama tabbatacce zan nuna maka alheri saboda mahaifinka Yonatan. Zan mayar maka da dukan ƙasar da take ta kakanka Shawulu, kullum kuma za ka ci a teburina.” Mefiboshet ya rusuna ya ce, “Ni ne wa har da za ka kula da ni? Ai! Ni bawanka ne da bai ma fi mataccen kare daraja ba.” Sai sarki ya kira Ziba bawan Shawulu, ya ce masa, “Na ba wa jikan maigidanka kome da yake na Shawulu da iyalinsa Kai da ’ya’yanka maza da bayinka za ku riƙa yin masa noma, ku kuma kawo hatsin, don jikan maigidanka yă sami abinci. Mefiboshet kuma, jikan maigidanka, zai riƙa ci a teburina.” (Ziba kuwa yana da ’ya’ya maza goma sha biyar da kuma bayi ashirin.) Sai Ziba ya ce wa sarki, “Bawanka zai aikata dukan abin da ranka yă daɗe sarki, ya umarce shi.” Saboda haka Mefiboshet ya riƙa ci a teburin Dawuda kamar sauran ’ya’yan sarki. Mefiboshet yana da wani ƙaramin ɗa sunansa Mika, dukan iyalin gidan Ziba kuwa bayin Mefiboshet ne. Mefiboshet ya zauna a Urushalima, gama kullum yana ci a teburin sarki, shi kuwa gurgu ne a dukan ƙafafu. Ana nan sai sarkin Ammonawa ya rasu, ɗansa Hanun kuwa ya gāje shi a matsayin sarki. Dawuda ya yi tunani a ransa ya ce, “Zan yi wa Hanun ɗan Nahash alheri kamar yadda mahaifinsa ya yi mini.” Saboda haka sai Dawuda ya aiki jakadu su yi masa ta’aziyyar mutuwar mahaifinsa. Sa’ad da mutanen Dawuda suka isa ƙasar Ammonawa, sai manyan mutanen Ammonawa suka ce wa Hanun shugabansu, “Kana tsammani Dawuda yana girmama mahaifinka ne da ya aiko da jakadu su kawo maka ta’aziyya? Ai, wayo ya yi don yă ga asirin birninmu, yă san ƙarfinmu, yă kuma ci mu da yaƙi.” Saboda haka Hanun ya kama mutanen Dawuda ya aske rabin gemun kowannensu, ya yayyage rigunarsu daidai ɗuwawu, sa’an nan ya sallame su. Sa’ad da aka gaya wa Dawuda game da wannan, sai ya aiki manzanni su taryi waɗannan mutanen da aka ci mutuncinsu, gama an wulaƙanta su ƙwarai. Sai sarki ya ce musu, “Ku dakata a Yeriko har sai gemunku ya sāke girma, sa’an nan ku dawo.” Da Ammonawa suka gane cewa Dawuda ya ji fushi da su sosai saboda abin da suka yi, sai suka yi hayar sojojin ƙasar Arameyawa dubu ashirin daga Bet Rehob da Aram-Zoba, suka kuma yi hayar sarkin Ma’aka tare da mutum dubu ɗaya, suka kuma yi hayar maza dubu goma sha biyu daga Tob. Da jin haka, Dawuda ya tura Yowab da dukan sojojin yaƙi. Ammonawa suka fita suka ja dāgār yaƙi a ƙofar shiga birninsu, yayinda Aram-Zoba, da na Rehob, da mutane Tob, da kuma na Ma’aka, suka ja tasu dāgār a karkara. Yowab ya ga cewa an ja masa dāgār yaƙi gaba da baya; saboda haka sai ya zaɓi waɗansu shahararrun sojoji cikin Isra’ila, ya sa su gabza da Arameyawa. Ya sa sauran mutanen a ƙarƙashin Abishai ɗan’uwansa, ya sa su gabza da Ammonawa. Yowab ya ce, “In Arameyawa suka fi ƙarfina, sai ku kawo mini gudummawa; amma in Ammonawa suka fi ƙarfinku, sai mu kawo muku gudummawa. Ku yi ƙarfin hali, mu kuma yi yaƙi da ƙarfin zuciya saboda mutanenmu da kuma birane Allahnmu. Ubangiji zai yi abin da yake da kyau a idanunsa.” Sa’an nan Yowab da rundunar da take tare da shi suka ci gaba don su gabza da Arameyawa, Arameyawa kuwa suka gudu a gabansa. Da Ammonawa suka ga Arameyawa suna gudu, sai su ma suka ruga da gudu a gaban Abishai, suka shiga cikin birni. Sa’an nan Yowab ya komo Urushalima daga wurin yaƙin da ya yi da Ammonawa. Bayan Arameyawa suka ga Isra’ila ta ci su da yaƙi, sai suka sāke tattara kansu. Hadadezer sarkin Zoba ya aika a kawo Arameyawan da suke ƙetaren Kogin Yuferites. Suka iso Helam a ƙarƙashin shugabancin Shobak, shugaban dukan sojojin Hadadezer. Da aka gaya wa Dawuda wannan, sai ya tattara dukan Isra’ila, ya ƙetare Urdun, ya je Helam. Arameyawa suka ja dāgār yaƙinsu, suka kara da Dawuda. Amma Arameyawa suka gudu a gaban Isra’ila, Dawuda kuwa ya kashe mahayan keken yaƙinsu ɗari bakwai, da sojojin ƙasa dubu arba’in. Ya bugi Shobak, shugaban ƙungiyar sojansu ya kuwa mutu a can. Sa’ad da dukan sarakuna waɗanda suke abokan tarayya na Hadadezer suka ga Isra’ila sun ci su da yaƙi, sai suka yi sulhu da Isra’ilawa, suka kuma zama bayinsu. Wannan ya sa Arameyawa suka ji tsoron ƙara kai wa Ammonawa gudummawa. Da bazara, a lokacin da sarakuna sukan fita zuwa yaƙi, sai Dawuda ya aiki Yowab tare da mutanen sarki, da dukan Isra’ila. Suka je suka hallaka Ammonawa, suka kuma yi wa Rabba kwanton ɓauna. Amma Dawuda ya yi zamansa a Urushalima. Wata rana da yamma, Dawuda ya tashi daga gadonsa, ya zaga kewaye a rufin fadansa. Daga rufin ya ga wata mace tana wanka. Matar kyakkyawa ce ƙwarai. Sai Dawuda ya aiki wani yă bincika ko wace ce ita, sai mutumin ya dawo ya ce, “Wannan ba Batsheba ba ce, ’yar Eliyam matar Uriya, mutumin Hitti?” Sa’an nan Dawuda ya aiki manzanni su kawo masa ita. Ta zo wurinsa shi kuma ya kwana da ita (A lokacin kuwa ta gama tsarkake kanta ke nan daga jinin haila.) Sa’an nan ta tafi gida. Matar ta yi ciki, ta kuwa aika wa Dawuda, tana cewa, “Ina da ciki.” Saboda haka Dawuda ya aika saƙo wa Yowab ya ce, “Ka aiko mini da Uriya mutumin Hitti.” Yowab kuwa ya aika da shi wajen Dawuda. Da Uriya ya zo wurinsa, sai Dawuda ya tambaye shi lafiyar Yowab da sojojin, da kuma yaya yaƙin yake tafiya. Sa’an nan Dawuda ya ce wa Uriya, “Gangara gidanka ka wanke ƙafafunka.” Saboda haka Uriya ya bar fadar, sarki kuma ya aika masa da kyauta. Amma Uriya ya kwanta a ƙofar fada tare da dukan bayin maigidansa, bai kuwa tafi gidansa ba. Da aka gaya wa Dawuda, “Uriya bai tafi gida ba,” sai Dawuda ya tambaye shi ya ce, “Ba ka zo daga wuri mai nisa ba? Me ya sa ba ka je gida ba?” Sai Uriya ya ce wa Dawuda, “Akwatin Alkawari, da Isra’ila, da Yahuda suna zama cikin tentuna, kuma maigidana Yowab da mutanen ranka yă daɗe suna a sansani a fili. Yaya zan je gidana in ci in sha in kuma kwana da matata? Muddin kana a raye, ba zan yi irin wannan abu ba!” Sai Dawuda ya ce masa, “Ka ƙara dakata a nan kwana ɗaya, gobe kuwa in sallame ka.” Saboda haka Uriya ya dakata a Urushalima a ranar, da kuma ta biye. Dawuda ya gayyace shi, ya kuwa ci ya sha tare da shi, Dawuda ya sa ya bugu tilis. Amma da yamma Uriya ya koma ya kwanta a tabarmarsa cikin bayin maigidan sarki; bai je gida ba. Da safe Dawuda ya rubuta wa Yowab wasiƙa ya ba wa Uriya. A ciki wasiƙar ya rubuta, “Tura Uriya a gaba inda yaƙi ya fi zafi. Sa’an nan ka janye daga gare shi don a buge shi yă mutu.” Saboda haka yayinda Yowab ya kai yaƙi kusa da birnin, sai tura Uriya a inda ya sani akwai jarumawan Ammon na gaske. Sa’ad da mutanen garin suka fito suka yaƙi Yowab, sai waɗansu mutane daga sojojin Dawuda suka mutu; Uriya mutumin Hitti ma ya mutu. Yowab ya aika wa Dawuda cikakken labari batun yaƙin. Ya umarci manzon ya ce, “Da ka gama yin wa sarki wannan batun yaƙin, wataƙila sarki yă husata, yă tambaye ka, ‘Me ya sa kuka je kusa da birnin don ku yi yaƙi? Ba ku san cewa za su yi harbi daga katanga ba? Wane ne ya kashe Abimelek ɗan Yerub-Beshet? Ba mace ce ta jefa dutsen niƙa a kansa daga katanga, ta haka ya mutu a Tebez ba? Me ya sa kuka je kurkusa da katangar?’ In ya tambaye ka wannan, sai ka ce masa, ‘Har bawanka Uriya mutumin Hitti ma ya mutu.’ ” Manzon ya tashi ya tafi, da ya iso kuwa sai ya gaya wa Dawuda dukan abin da Yowab ya aike shi yă faɗa. Manzon ya ce wa Dawuda, “Mutanen sun sha kanmu suka fito suka yaƙe mu a fili, amma muka kore su har ƙofar birni. Sa’an nan maharba suka yi ta harbi daga katanga har waɗansu mutanen sarki suka mutu. Ban da haka ma, Uriya mutumin Hitti bawan sarki ya mutu.” Dawuda ya ce wa manzon, “Ka gaya wa Yowab, ‘Kada ka bar wannan yă dame ka; yadda takobi ya lamushe wannan, haka zai lamushe wancan ma. Ku ƙara matsa wa garin lamba, ku hallaka shi.’ Ka faɗa haka don ka ƙarfafa Yowab.” Da matar Uriya ta ji cewa mijinta ya mutu, sai ta yi makoki saboda shi. Bayan kwanakin makoki suka ƙare, Dawuda ya sa aka kawo ta gidansa, ta kuwa zama matarsa, ta kuma haifa masa ɗa. Sai dai abin da Dawuda ya yi bai gamshi Ubangiji ba. Ubangiji ya aiki Natan wurin Dawuda. Da ya tafi wajensa, sai ya ce, “An yi waɗansu mutum biyu a wani gari, ɗaya mai arziki, ɗayan kuma matalauci. Mai arzikin yana da babban garken tumaki, da kuma shanu, amma matalauci ba shi da kome sai ’yar tunkiyar da ya sayo. Ya yi kiwonta, ta kuwa yi girma tare shi da yaransa. Takan ci tare da shi ta sha ruwa a kwaf nasa, har ma ta kwanta a ƙirjinsa. Ta ma zama kamar ’ya a gare shi. “To, sai ga wani baƙo ya zo wurin mai arzikin nan, amma mai arzikin ya ƙi yă kama tunkiyarsa, ko saniyarsa yă yanka don yă shirya wa baƙon da ya zo abinci. A maimako, sai ya je ya kama ’yar tunkiyan nan ta matalaucin ya yanka ya shirya wa mutumin da ya zo masa.” Dawuda ya husata ƙwarai da mutumin, ya ce wa Natan, “Muddin Ubangiji yana a raye, mutumin da ya yi wannan ya cancanci yă mutu! Dole yă biya diyyar tunkiyan nan sau huɗu, domin ya aikata haka ba tausayi.” Sai Natan ya ce wa Dawuda, “Kai ne mutumin! Ga abin da Ubangiji, Allah ya ce, ‘Na naɗa ka sarki bisa Isra’ila, na kuma cece ka daga hannun Shawulu. Na ba ka gidan maigidanka, da matan maigidanka duka. Na ba ka gidan Isra’ila da Yahuda. Da a ce dukan waɗannan sun kāsa maka, ai, da na ƙara maka. Me ya sa ka rena maganar Ubangiji ta wurin yin mugunta haka a idonsa? Ka kashe Uriya mutumin Hitti da takobi, ka kuma ɗauki matarsa tă zama matarka. Ka kashe shi da takobin Ammonawa. To, fa, takobi ba zai taɓa rabu da gidanka ba, domin ka rena ni, ka kuma ƙwace matar Uriya mutumin Hitti ta zama matarka.’ “Ga abin da Ubangiji yana cewa, ‘Daga cikin iyalinka zan kawo masifa a kanka. A idanunka zan ɗauki matanka in ba wa wani da yake kusa da kai, zai kuwa kwana da su da rana tsaka. Ka aikata wannan a ɓoye, amma zan aikata wannan da rana tsaka, a gaban dukan Isra’ila.’ ” Sai Dawuda ya ce wa Natan, “Na yi wa Ubangiji zunubi.” Natan ya ce, “ Ubangiji ya yafe maka zunubin. Ba za ka mutu ba. Amma saboda ka yi haka ka sa abokan gāba suka rena Ubangiji, yaron da aka haifa maka zai mutu.” Bayan Natan ya tafi gida, sai Ubangiji ya bugi yaron da matar Uriya ta haifa wa Dawuda, ya kuwa kamu da ciwo. Dawuda ya roƙi Allah saboda yaron. Ya yi azumi, ya kuma shiga gidansa ya kwana kwance a ƙasa. Dattawan iyalinsa suka tsaya kusa da shi don su ɗaga shi daga ƙasa, amma ya ƙi, bai kuwa ci wani abu tare da su ba. A rana ta bakwai sai yaron ya rasu. Barorin Dawuda suka ji tsoro su gaya masa cewa yaron ya mutu, gama sun yi tunani cewa, “Yayinda yaron yake da rai, mun yi magana da Dawuda bai ji mu ba. Yaya za mu gaya masa yaron ya mutu? Ai, zai yi wa kansa ɓarna.” Dawuda ya gane bayinsa suna wa juna raɗan wani abu, sai ya gane yaron ya mutu. Sai ya ce, “Yaron ya rasu ko?” Suka ce, “I, ya rasu.” Sa’an nan Dawuda ya tashi daga ƙasa. Bayan ya yi wanka, ya shafa mai, ya kuma canja rigunarsa, sa’an nan ya shiga gidan Ubangiji ya yi sujada. Sai ya tafi gidansa, ya nemi a ba shi abinci, aka ba shi, ya kuwa ci. Barorinsa suka ce masa, “Me ya sa kake yin haka? Yayinda yaron yake da rai, ka yi azumi, ka kuma yi kuka, amma yanzu da yaron ya mutu, ka tashi, ka kuma ci abinci!” Ya ce musu, “Yayinda yaron yake da rai, na yi azumi, na kuma yi kuka. Na yi tunani na ce, ‘Wa ya sani? Ko Ubangiji zai yi mini alheri yă bar yaron yă rayu.’ Amma yanzu da ya mutu, me zai sa in yi azumi? Zan iya dawo da shi ne? Ni zan je wajensa, ba shi zai dawo wurina ba.” Sai Dawuda ya yi wa matarsa Batsheba ta’aziyya, ya kuma tafi wurinta ya kwana da ita. Ta kuma haifi ɗa, suka ba shi suna Solomon. Ubangiji ya ƙaunace shi; kuma saboda Ubangiji ya ƙaunace shi, sai ya aika da saƙo ta wurin annabi Natan yă ba shi suna Yedidiya. Ana cikin haka, sai Yowab ya yi yaƙi da Rabba na Ammonawa, ya kuma ƙwace babban birnin. Sa’an nan Yowab ya aika manzanni wurin Dawuda yana cewa, “Na yaƙi Rabba na kuma ƙwace hanyar samun ruwanta. Yanzu fa ka tattara saura rundunoni ka fāɗa wa birnin ka ci shi. In ba haka ba zan karɓe birnin, a kuma kira shi da sunana.” Saboda haka Dawuda ya tattara sauran rundunar sojojin suka tafi Rabba suka fāɗa masa suka kuma ci shi. Ya ɗauke rawanin daga kan sarkinsu, nauyinsa ya kai talenti, na zinariya, an kuma yi masa ado da duwatsu masu daraja, aka aza shi a kan Dawuda. Ya kuma kwashe ganima mai yawa daga garin. Ya fito da mutanen da suke a can, ya sa su su yi aiki da zarto, da diga, da kuma gatari, ya kuma sa su bugan bulok. Haka ya yi wa dukan garuruwan Ammonawa. Sa’an nan Dawuda da dukan sojoji suka koma Urushalima. Ana nan sai Amnon ɗan Dawuda ya fara son Tamar, kyakkyawar ’yar’uwar Absalom ɗan Dawuda. Amnon ya matsu ƙwarai har abin ya sa shi ciwo saboda ƙanuwarsa Tamar. Ya gane zai zama da wuya yă sadu da Tamar ita kaɗai, gama ba ta taɓa kwana da namiji ba. To, Amnon yana da wani aboki mai suna Yonadab, ɗan Shimeya, ɗan’uwan Dawuda. Yonadab dai mai wayo ne ƙwarai. Ya tambayi Amnon ya ce, “Don me kowace safiya fuskarka a ɓace take? Kai ba yaron sarki ba ne? Faɗa mini, me ke faruwa?” Amnon ya ce masa, “Ina son Tamar ƙanuwar wan nawa Absalom ne.” Yonadab ya ce, “Je gado ka kwanta kamar ba ka da lafiya. Sa’ad da mahaifinka ya zo ganinka, sai ka ce masa, ‘Ina so ƙanuwata Tamar tă kawo mini wani abu in ci. Bari tă shirya abincin a gabana don in ganta, in kuma ci daga hannunta.’ ” Sai Amnon ya kwanta sai ka ce yana ciwo. Da sarki ya zo don ganinsa, sai Amnon ya ce, “Zan so ƙanuwata Tamar tă zo tă shirya mini abinci a gabana, don in ci daga hannunta.” Dawuda kuwa ya aika wa Tamar a fada, ya ce, “Ki je gidan Amnon ɗan’uwanki, ki yi masa abinci.” Saboda haka Tamar ta tafi gidan ɗan’uwanta Amnon, wanda yake kwance. Ta ɗauki fulawa, ta kwaɓa, ta yi burodi a gabansa ta toya shi. Sa’an nan ta juye a kasko ta ba shi burodin, amma ya ƙi ci. Amnon ya ce, “A sa kowa yă fita daga nan.” Saboda haka kowa ya fita ya bar shi. Sa’an nan Amnon ya ce wa Tamar, “Kawo abincin a nan a cikin ɗakin kwanciyata, don in ci daga hannunki.” Tamar kuwa ta ɗauki burodin da ta toya, ta kawo wa ɗan’uwanta Amnon a ciki ɗakin kwanciyarsa. Amma da ta kai masa don yă ci, sai ya cafke ta ya ce, “Zo in kwana da ke, ’yar’uwata.” Ta ce, “Kada ka yi wannan ɗan’uwana! Kada ka tilasta ni. Bai kamata a yi irin wannan abu a Isra’ila ba! Kada ka yi wannan mugun abu. Ni fa, ina zan sa kaina saboda kunya? Kai kuma za ka zama kamar wani mugun wawa a Isra’ila. Ina roƙonka ka yi wa sarki magana; ba zai hana ni aurenka ba.” Amma Amnon ya ƙi yă saurare ta, da yake ya fi ta ƙarfi, sai ya yi mata fyaɗe. Bayan ya yi lalata da ita sai Amnon ya ƙi ta da mummunan ƙiyayya. Zahiri ya ƙi ta fiye da ya ƙaunace ta. Sai Amnon ya ce mata, “Tashi, ki fita!” Ta ce, “A’a! Korina zai fi muni da abin da ka riga ka yi mini.” Amma ya ƙi yă saurare ta. Sai ya kira bawansa ya ce, “Fitar da matan nan daga nan, ka rufe ƙofa.” Saboda haka bawansa ya fitar da ita, ya kuma sa aka rufe ƙofa. Tana sanye da doguwar riga mai kayan ado masu tsada, gama wannan ne irin kayan da budurwai ’ya’yan sarki mata suke sawa. Sai Tamar ta zuba toka a kanta, ta kuma yayyage doguwar riga mai kayan adon da take sanye da shi. Ta sa hannunta a kai, ta tafi tana kuka da ƙarfi. Absalom ɗan’uwanta ya ce mata, “Amnon, ɗan’uwanki ya ɓata ki ko? To, ki yi shiru ’yar’uwata; ai, ɗan’uwanki ne. Kada wannan abu yă dame ki.” Tamar kuwa ta zauna a gidan ɗan’uwanta Absalom, zaman kaɗaici. Da Sarki Dawuda ya ji dukan abin da ya faru, sai ya husata ƙwarai. Absalom kuwa bai yi wa Amnon wata magana ta alheri ko ta mugunta ba; ya ƙi jinin Amnon domin ya ci mutuncin ƙanuwarsa Tamar. Bayan shekaru biyu, sa’ad da masu askin tumakin Absalom suna Ba’al-Hazor, kusa da iyakar Efraim, sai ya gayyaci dukan ’ya’yan sarki maza a can. Sai Absalom ya je wurin sarki ya ce, “Bawanka ya sa masu askin tumaki sun zo. Ko sarki da fadawansa za su zo tare da ni?” Sarki ya ce, “A’a ɗana, bai kamata dukanmu mu tafi ba; don kada nauyi yă yi maka yawa.” Absalom dai ya dāge, duk da haka sarki ya ƙi yă je, sai dai ya albarkace shi. Sa’an nan Absalom ya ce, to, “In ba za ka ba, ina roƙonka bari Amnon ɗan’uwana yă zo tare da mu.” Sarki ya ce masa, “Don me zai tafi tare da kai?” Amma Absalom ya nace don sarki yă yarda, saboda haka sarki ya bar Amnon da sauran ’ya’yan sarki maza su tafi tare da shi. Absalom ya umarci mutanensa ya ce, “Ku saurara! Sa’ad da Amnon ya bugu sosai da giya na kuma ce muku, ‘Ku bugi Amnon,’ sai ku kashe shi. Kada ku ji tsoro. Ashe, ba ni ne na ba ku wannan umarni ba? Ku yi ƙarfin hali, ku kuma yi jaruntaka.” Saboda haka mutanen Absalom suka yi wa Amnon abin da Absalom ya umarta. Sai dukan sauran ’ya’yan sarki maza suka hau dawakansu suka gudu. Yayinda suke kan hanyarsu, sai labari ya kai kunnen Dawuda cewa, “Absalom ya kashe dukan ’ya’yan sarki maza; ko ɗayansu Absalom bai rage ba.” Sai sarki ya tashi, ya yage tufafinsa, ya kuma kwanta a ƙasa; dukan bayinsa kuwa suka tsaya da rigunansu yagaggu. Amma Yonadab, ɗan Shimeya ɗan’uwan Dawuda ya ce, “Kada ranka yă daɗe yă yi tunani cewa an kashe dukan ’ya’yan sarki maza; Amnon ne kaɗai ya mutu. Wannan ce niyyar Absalom tun lokacin da Amnon ya yi wa Tamar ’yar’uwansa fyaɗe. Kada mai girma sarki yă damu da jita-jitan nan cewa an kashe dukan ’ya’yan sarki maza. Amnon ne kaɗai ya mutu.” Ana cikin haka, sai Absalom ya gudu. To, mutumin da yake tsaro a wannan lokaci ya ɗaga kai sai ya ga mutane da yawa a hanya, yamma da shi, suna gangarowa daga gefen tudu. Sai mai tsaron ya je ya gaya wa sarki cewa, “Na ga mutane ta wajen Horonayim, a gefen tudu.” Yonadab ya ce wa Sarki, “Duba, ga ’ya’yan sarki maza sun zo; ya faru kamar dai yadda bawanka ya faɗa.” Yana gama magana, sai ga ’ya’yan sarki maza suka shigo suna kuka da ƙarfi. Sarki ma da dukan bayinsa suka yi kuka mai zafi. Absalom ya gudu ya tafi wurin Talmai ɗan Ammihud, sarkin Geshur. Amma Sarki Dawuda ya yi ta makokin ɗansa kowace rana. Bayan Absalom ya gudu sai ya je wurin Geshur, ya zauna a can shekara uku. Sai zuciyar sarki Dawuda ya komo kan Absalom, gama an yi masa ta’aziyya game da mutuwar Amnon. Yowab, ɗan Zeruhiya ya gane cewa zuriyar sarki ta koma ga Absalom. Saboda haka Yowab ya aiki wani zuwa Tekowa, ya sa a zo da wata mace mai hikima. Ya ce mata, “Ki yi kamar kina makoki. Ki sa rigar makoki, kada kuwa ki shafa mai. Ki yi kamar macen da ta yi kwanaki da yawa, tana makokin matattu. Sa’an nan ki je wurin sarki, ki ce masa haka.” Sai Yowab ya faɗa mata duk abin da za tă faɗa. Da macen da ta fito daga Tekowa ta je wajen sarki, sai ta rusuna har ƙasa don bangirma, sai ta ce, “Ka taimake ni, ya sarki!” Sarki ya ce mata, “Mece ce matsalarki?” Sai ta ce, “Tabbatacce, ni gwauruwa ce; mijina ya mutu. Baiwarka tana da ’ya’ya maza biyu. Suka yi faɗa da juna a fili, kuma ba wanda yake can don yă raba su. Ɗayan ya bugi ɗayan, ya kashe shi. To, ga duk iyali sun hau kan baiwarka, suna cewa, ‘Ki ba mu ɗayan da ya kashe ɗan’uwansa mu kashe don ran ɗan’uwansa da ya kashe; sa’an nan za mu hallaka magājin shi ma.’ Za su kashe garwashin wuta mai ci da nake da shi kaɗai, su bar mijina ba suna, ba jika, a duniya.” Sarki ya ce wa macen, “Koma gida, zan ba da umarni a madadinki.” Amma macen da ta fito daga Tekowa ta ce, “Ranka yă daɗe, sarki! Bari alhakin shari’arka yă kasance a kaina da gidan mahaifina, kai sarki da gidan mulkinka, ba ku da laifi a ciki.” Sai sarki ya ce, “In wani ya yi miki magana, ki kawo shi wurina, ba zai kuwa ƙara damunki ba.” Sai ta ce, “To, bari sarki yă rantse da Ubangiji Allahnsa don yă hana mai ramako yin ƙarin hallakawar da aka yi, domin kada a hallaka ɗana.” Sai ya ce, “Muddin Ubangiji yana a raye, babu gashi guda na ɗanki da zai fāɗi ƙasa.” Sai matar ta ce, “Bari baiwarka ta ƙara yin magana sau ɗayan nan wa ranka yă daɗe.” Ya ce, “Ki faɗa.” Matar ta ce, “To, don me ka yi wa mutanen Allah irin wannan abu? Sa’ad da sarki ya ce haka, ashe, ba ka hukunta kanka ke nan ba, tun da yake sarki bai yarda ɗansa yă komo gida ba? Kamar ruwan da ya zuba a ƙasa, wanda ba a iya kwasa, haka dole mu mutu. Amma Allah ba ya ɗaukan rai; a maimako, yakan ƙirƙiro hanyoyi domin mutumin da aka kora kada yă kasance yasasshe daga gare shi. “Yanzu ga shi na zo don in faɗa wannan wa ranka yă daɗe sarki, don mutane sun tsorata ni. Baiwarka ta yi tunani ta ce, ‘Zan yi magana wa sarki; wataƙila yă yi abin da baiwarsa ta roƙa. Wataƙila sarki zai yarda yă ceci baiwarsa daga hannun mutumin nan da yake ƙoƙari yă hallaka ni da ɗana daga gādon da Allah ya ba mu.’ “Yanzu kuwa baiwarka tana cewa, ‘Bari magana ranka yă daɗe sarki yă ba ni hutu, gama ranka yă daɗe sarki yana kama da mala’ikan Allah cikin rarrabe nagarta da mugunta. Bari Ubangiji Allahnka yă kasance tare da kai.’ ” Sai sarki ya ce wa matar, “Kada ki ɓoye mini kome daga abin da zan tambaye ki.” Matar ta ce, “Bari ranka yă daɗe sarki yă yi tambaya.” Sarki ya ce, “Anya, babu hannun Yowab a cikin dukan wannan?” Matar ta ce, “Muddin kana a raye, ranka yă daɗe sarki, ba wanda zai juya dama ko hagu daga wani abin da ranka yă daɗe sarki ya faɗa. I, bawanka Yowab ne ya umarce ni in yi wannan, shi ne kuma ya sa kalmomin nan a bakin baiwarka. Bawanka Yowab ne ya yi haka don yă daidaita al’amura. Ranka yă daɗe yana da hikima iri ta mala’ikan Allah, ya san dukan kome da yake faruwa a ƙasar.” Sarki ya ce wa Yowab, “To, da kyau, zan yi haka. Je ka, ka dawo da saurayin nan Absalom.” Yowab ya rusuna har ƙasa don bangirma, ya kuma yi wa sarki kyakkyawar fata. Yowab ya ce, “Yau, bawanka ya sani ya sami tagomashi a gare ka, ranka yă daɗe sarki, gama sarki ya ji roƙon bawansa.” Sa’an nan Yowab ya tafi Geshur ya dawo da Absalom Urushalima. Amma sarki ya ce, “Yă tafi gidansa; kada yă zo yă gan ni.” Saboda haka Absalom ya tafi gidansa, bai kuwa je ganin sarki ba. A cikin dukan Isra’ila babu wanda ake yabon kyansa kamar Absalom. Tun daga kansa har zuwa tafin ƙafansa babu tabo a jikinsa. A duk sa’ad da ya aske gashin kansa (yakan aske kansa lokaci-lokaci sa’ad da ya yi masa nauyi) yakan auna shi, nauyin gashin kuwa yakan kai wajen shekel ɗari biyu a ma’aunin da ake awo. Aka haifa wa Absalom ’ya’ya uku maza da ’ya mace guda. Sunanta Tamar, ta kuwa zama kyakkyawan mace ƙwarai. Absalom ya zauna a Urushalima shekara biyu amma ba tare da ganin fuskar sarki ba. Sai Absalom ya aika a kira masa Yowab don yă aike shi wurin sarki, amma Yowab ya ƙi zuwa. Saboda haka ya sāke aika sau na biyu, amma ya ƙi yă zo. Sai ya ce wa bayinsa, “Duba, gonar Yowab tana gab da tawa, kuma yana da sha’ir a can. Ku je ku sa mata wuta.” Sai bayin Absalom suka sa wa gonar wuta. Sa’an nan Yowab ya tafi gidan Absalom ya ce masa, “Me ya sa bayinka suka sa wa gonata wuta?” Absalom ya ce wa Yowab, “Kai, na aika, ‘Ka zo nan don in aike ka wurin sarki ka tambaya, “Me ya sa na dawo daga Geshur? Ai, ya fi mini a ce ina can har yanzu!” ’ Yanzu kuwa, ina so in ga sarki, kuma idan na yi wani laifi, to, yă kashe ni.” Saboda haka Yowab ya tafi wurin sarki ya gaya masa wannan. Sai sarki ya aika aka zo da Absalom, ya kuma rusuna da fuskarsa har ƙasa a gaban sarki. Sarki kuwa ya sumbaci Absalom. Ana nan sai Absalom ya samo wa kansa wata keken yaƙi da dawakai tare da mutum hamsin da za su sha gabansa. Absalom yakan tashi da sassafe yă tsaya a gefen hanyar shigar ƙofar birni. Duk sa’ad da wani ya zo da ƙara don a kai gaban sarki yă yi shari’a, Absalom yakan kira shi yă ce, “Daga wane gari ka fito?” Sai mutumin yă amsa yă ce, “Bawanka ya fito a ɗaya daga cikin kabilan Isra’ila.” Sai Absalom yă ce masa, “Ga shi, ƙararka daidai ne, tana kuma da gaskiya, sai dai ba wakilin sarkin da zai ji ka.” Absalom kuwa yakan ƙara da cewa, “Da a ce an naɗa ni alƙali a ƙasar mana! Da duk mai ƙara, ko kuka wanda zai zo wurina, zan in tabbatar an yi masa adalci.” Kuma duk sa’ad da wani ya zo wurin Absalom ya rusuna don yă gaishe shi, sai Absalom yă sa hannunsa yă ta da shi, yă kuma rungume shi. Absalom ya yi ta yin haka ga dukan Isra’ilawan da suka zo wurin sarki don neman adalci, ta haka kuwa ya saci zukatan mutanen Isra’ila. A ƙarshen shekara huɗu, Absalom ya ce wa sarki, “Bari in tafi Hebron in cika alkawarin da na yi wa Ubangiji. Yayinda bawanka yake zama a Geshur, a Aram, na yi wannan alkawari, na ce, ‘In Ubangiji ya komo da ni Urushalima, zan yi wa Ubangiji sujada a Hebron.’ ” Sarki ya ce, “Ka sauka lafiya.” Sai ya tafi Hebron. Sai Absalom ya aiki manzanni a asirce cikin dukan kabilan Isra’ila, ya ce musu su ce, “Da zarar kuka ji an busa ƙaho, sai ku ce, ‘Absalom sarki ne a Hebron.’ ” Mutum ɗari biyu daga Urushalima suka raka Absalom. An gayyace su a matsayin baƙi, suka kuwa tafi cikin rashin sani, ba su san wani abu game da al’amarin ba. Yayinda Absalom yake miƙa hadaya, ya aika a kira Ahitofel mutumin Gilo, mai ba wa Dawuda shawara, yă zo daga Gilo garinsa. Ta haka makircin ya ƙara ƙarfi, masu bin Absalom kuma suka yi ta ƙaruwa. Wani manzo ya zo wurin Dawuda ya ce masa, “Zukatan mutanen Isra’ila sun koma wajen Absalom.” Sai Dawuda ya ce wa dukan fadawansa da suke tare da shi a Urushalima, “Ku zo! Mu gudu, in ba haka ba, babu wanda zai tsira daga hannun Absalom. Dole mu bar nan, nan da nan, in ba haka ba zai tashi da sauri yă fāɗa mana, yă kuma hallaka garin da takobi.” Sai fadawan sarki suka ce masa, “Barorinka suna a shirye su yi duk abin da ranka yă daɗe, ya zaɓa.” Sarki ya kama hanya, dukan gidansa kuwa suna biye da shi; amma ya bar ƙwarƙwarai goma su lura da fada. Ta haka sarki ya kama hanya da dukan mutane suna biye da shi, suka yi sansani a wani wuri mai ɗan nisa da Urushalima. Dukan mutanensa suka wuce gabansa, tare da dukan Keretawa da Feletiyawa; da dukan mutane ɗari shida na Gittiyawan da suka raka shi daga Gat, suka wuce gaban sarki. Sarki ya ce wa Ittai mutumin Gat, “Don me za ka zo tare da mu? Ka koma ka zauna tare da Sarki Absalom. Kai baƙo ne, ɗan gudun hijira daga garinka. Jiya-jiya ka zo. Yau kuma in sa ka yi ta yawo tare da mu, ga shi ban ma san inda za ni ba? Koma, ka tafi da ’yan’uwanka. Bari alheri da amincin Ubangiji su kasance tare da kai.” Amma Ittai ya ce wa sarki, “Muddin Ubangiji yana a raye kuma muddin ranka yă daɗe yana a raye, duk inda ranka yă daɗe sarki zai kasance, ko a yi rai ko a mutu, a can bawanka zai kasance.” Dawuda ya ce wa Ittai, “Wuce gaba, taka mu je.” Sai Ittai mutumin Gat ya shiga layi tare da dukan mutanensa da iyalan da suke tare da shi. Dukan ƙauyuka suka yi ta kururuwa yayinda mutanen suke wucewa. Sarki shi ma ya haye ta Kwarin Kidron, mutane kuma suka ci gaba da tafiya zuwa wajen hamada. Zadok yana nan tare da su, kuma dukan Lawiyawan da suke tare da shi kuwa suna ɗauke da akwatin alkawarin Allah. Suka sauke akwatin alkawarin Allah, Abiyatar ya miƙa hadaya sai da mutane suka gama fita daga birnin. Sa’an nan sarki ya ce wa Zadok, “Ka komar da akwatin alkawarin Allah cikin birnin. Idan na sami tagomashi a idon Ubangiji, zai dawo da ni, yă kuma sa in sāke gan shi a mazauninsa. Amma in ya ce, ‘Ina baƙin ciki da kai,’ to, ina a shirye; bari yă yi abin da ya fi masa.” Sarki ya kuma ce wa Zadok firist, “Ashe, kai ba mai duba ba ne? Ka koma cikin birnin lafiya, tare da ɗanka Ahimawaz, da kuma Yonatan ɗan Abiyatar. Kai da Abiyatar ku tafi da ’ya’yanku biyu. Zan kuwa jira a mashigai a hamada, sai na ji daga gare ku.” Saboda haka Zadok da Abiyatar suka ɗauki akwatin alkawarin Allah suka komar da shi Urushalima, suka zauna a can. Amma Dawuda ya ci gaba yana hawan Dutsen Zaitun, yana kuka yayinda yake tafiya; kansa a rufe, kuma babu takalma a ƙafafunsa. Dukan mutanen da suke tare da shi suka rufe kawunansu suna ta kuka yayinda suke haurawa. To, an gaya wa Dawuda cewa, “Ahitofel yana cikin waɗanda suka hadasa maƙarƙashiya tare da Absalom.” Saboda haka Dawuda ya yi addu’a ya ce, “Ya Ubangiji ka mai da shawarar Ahitofel ta zama shiririta.” Da Dawuda ya isa ƙwanƙoli, inda mutane sun saba yi wa Allah sujada, Hushai, mutumin Arkitawa kuwa yana can don yă tarye shi, taguwarsa a yage, ga kuma ƙura a kansa. Sai Dawuda ya ce masa, “In ka tafi tare da ni, za ka zama mini kaya. Amma in ka koma birni, ka gaya wa Absalom, ‘Zan zama bawanka, ya sarki; dā ni bawan mahaifinka ne, amma yanzu zan zama bawanka,’ ta haka za ka watsar da shawarar Ahitofel. Ba Zadok da Abiyatar firistocin nan suna nan tare da kai ba? Ka gaya musu duk abin da ka ji a fadan sarki. ’Ya’yansu biyu maza, Ahimawaz ɗan Zadok, da kuma Yonatan ɗan Abiyatar, suna can tare da su. Ka aike su wurina da duk abin da ka ji.” Saboda haka Hushai abokin Dawuda ya isa Urushalima yayinda Absalom yake shigowa birnin. Sa’ad da Dawuda ya yi ɗan nesa da ƙwanƙolin, sai ga Ziba mai hidimar Mefiboshet, yana jira yă tarye shi. Yana da jerin jakuna da sirdi suna ɗauke da dunƙulen burodi ɗari biyu, da ƙosai busasshen inabi ɗari ɗaya, da kosan ’ya’yan itace ɓaure guda ɗari, da salka ruwan inabi. Sarki ya ce wa Ziba, “Me ya sa ka kawo waɗannan?” Ziba ya ce, “Jakuna domin iyalin gidan sarki su hau ne, burodi da ’ya’yan itace domin mutane su ci, ruwan inabi kuma domin waɗanda suka gaji a hamada.” Sai sarki ya ce, “Ina jikar maigidanka?” Ziba ya ce, “Yana zaune a Urushalima gama yana tsammani cewa, ‘Yau gidan Isra’ila za su mayar mini da sarautar kakana.’ ” Sai sarki ya ce wa Ziba, “Duk abin da yake na Mefiboshet, ya zama naka.” Ziba ya rusuna ya ce, “Bari in dinga samun tagomashi a gabanka ranka yă daɗe.” Yayinda Sarki Dawuda ya kusato Bahurim, sai ga wani mutumin dangin Shawulu ya fito daga can, sunansa Shimeyi ɗan Gera. Ya fito yana ta la’anta yayinda yake fitowa. Ya jajjefi Dawuda da dukan fadawan sarki da duwatsu, ko da yake sojoji da masu gadin sarki na musamman suna kewaye da sarki dama da hagu. Yayinda yake la’antar, Shimeyi ya ce, “Tafi daga nan, tafi daga nan, mai kisankai, mutumin banza kawai! Ubangiji ya kama ka saboda alhakin jinin gidan Shawulu, wanda kake sarauta a maimakonsa. Ubangiji ya ba da masarautar ga ɗanka Absalom. Hallaka ta zo maka domin kai mai kisankai ne!” Sai Abishai ɗan Zeruhiya ya ce wa sarki, “Ranka yă daɗe, don me wannan mataccen kare yake la’antarka? Bari in je in datse kansa.” Amma sarki ya ce, “Ba ruwana da ku, ku ’ya’yan Zeruhiya. Idan yana la’ana ne domin Ubangiji ya ce masa, ‘La’anci Dawuda,’ wa zai ce, ‘Don me kake haka?’ ” Sa’an nan Dawuda ya ce wa Abishai da dukan fadawansa, “Ɗana, na cikina, yana ƙoƙari yă kashe ni. Balle wannan mutumin Benyamin! Ku ƙyale shi, yă yi ta zargi, Ubangiji ne ya ce masa yă yi haka. Mai yiwuwa Ubangiji yă ga azabata, yă sāka mini da alheri saboda la’anar da nake sha a yau.” Saboda haka Dawuda da mutanensa suka ci gaba da tafiyarsu yayinda Shimeyi yana tafiya ɗaura da shi a gefen tudu, yana zagi, yana jifansa da duwatsu, yana tayar masa da ƙura. Sarki da dukan mutanen da suke tare da shi suka isa masauƙinsu a gajiye. A can fa ya huta. Ana cikin haka, Absalom da dukan Isra’ila suka iso Urushalima, Ahitofel kuwa yana tare da shi. Sai Hushai mutumin Arkitawa, abokin Dawuda ya je wurin Absalom ya ce masa, “Ran sarki yă daɗe! Ran sarki yă daɗe!” Absalom ya ce wa Hushai, “Ƙaunar da kake nuna wa abokinka ke nan? Me ya sa ba ka tafi tare da abokinka ba?” Hushai ya ce wa Absalom, “A’a, ai, wanda Ubangiji ya zaɓa ta wurin waɗannan mutane, da kuma ta wurin dukan mutane Isra’ila, shi zan zama nasa, zan kuma kasance tare da shi. Ban da haka ma, wane ne zan bauta wa? Ashe, ba ɗan ne zan bauta wa ba? Kamar dai yadda na bauta wa mahaifinka, haka zan bauta maka.” Absalom ya ce wa Ahitofel, “Ba mu shawararka. Me za mu yi?” Ahitofel ya ce wa Absalom, “Je ka kwana da ƙwarƙwaran mahaifinka waɗanda ya bari su lura da fada. Ta haka dukan Isra’ila za su ji cewa ka mai da kanka abin wari a hancin mahaifinka, dukan hannuwan waɗanda suke tare da kai kuwa za su sami ƙarfi.” Saboda haka suka kafa wa Absalom tenti a bisa rufin ɗaki, a can ya kwana da ƙwarƙwaran mahaifinsa a gaban dukan Isra’ila. To, a kwanakin nan shawarar da Ahitofel yakan bayar takan zama kamar wadda aka nemi daga Allah ne. Haka Dawuda da Absalom duk suke ɗaukan dukan shawarar Ahitofel. Ahitofel ya ce wa Absalom, “Zan zaɓi mutum dubu goma sha biyu su fita a daren nan in fafari Dawuda. Zan fāɗa masa sa’ad da yake cikin gajiya da karayar zuciya. Zan firgita shi, mutanen da suke tare da shi kuwa za su gudu. Sarki ne kaɗai zan kashe in dawo da dukan mutanen a gare ka. Mutuwar wanda kake nema zai zama dawowar duka; dukan mutanen ba za su cutu ba.” Wannan shawara ta gamshi Absalom da dukan dattawan Isra’ila. Amma Absalom ya ce, “A kira mini Hushai mutumin Arkitawan nan shi ma, mu ji abin da zai ce.” Da Hushai ya zo wurinsa, sai Absalom ya ce, “Ahitofel ya ba da wannan shawara. Mu yi abin da ya ce? In ba haka ba, sai ka ba mu ra’ayinka.” Hushai ya ce wa Absalom, “Shawarar da Ahitofel ya bayar a wannan lokaci kam, ba ta da kyau. Ka san mahaifinka da mutanensa mayaƙa ne, suna cikin fushi kamar mugun beyar da aka ƙwace mata ’ya’ya. Ban da haka ma, mahaifinka gogagge ne a yaƙi; ba zai kwana da rundunar ba. Kai, ko yanzu ma, ya riga ya ɓuya cikin kogo ko kuma a wani wuri. In har ya fara kai wa rundunarka hari duk wanda ya ji, zai ce, ‘An yi kaca-kaca da rundunar da suka bi Absalom.’ Kai, ko jarumi mai zuciya kamar na zaki ma, zai narke don tsoro, gama dukan Isra’ila sun sani mahaifinka mayaƙi ne, sun kuma san cewa waɗanda suke tare da shi jarumawa ne. “Saboda haka ina ba ka shawara, bari a tara maka dukan Isra’ila, daga Dan zuwa Beyersheba da yawansu ya yi kamar yashin bakin teku, kai kanka ka jagorance su zuwa fagen fama. Sa’an nan za mu fāɗa masa duk inda yake, za mu fāɗa masa kamar yadda raɓa takan fāɗo a bisa ƙasa. Da shi da mutanensa babu ko ɗaya da za a bari da rai. In ma ya janye zuwa cikin birni, sai dukan Isra’ila su kawo igiyoyi wa wannan birni, su ja shi zuwa kwari yă wargaje, yadda ba za a bar wani dutse a kan wani ba.” Absalom da dukan mutanen Isra’ila suka ce, “Shawarar Hushai mutumin Arkitawa ta fi ta Ahitofel kyau.” Gama Ubangiji ya ƙudura yă wofinta kyakkyawar shawarar Ahitofel, don yă jawo wa Absalom masifa. Hushai ya ce wa Zadok da Abiyatar, firistoci, “Ahitofel ya ba wa Absalom da dattawan Isra’ila shawara su yi kaza da kaza, amma na ba su shawara su yi haka, su yi haka. Yanzu sai ku aika wa Dawuda saƙo nan da nan ku ce masa, ‘Kada ka kwana a mashigai cikin hamada; ka tabbata ka haye ba faci, in ba haka ba sarki da dukan mutanensa za su hallaka.’ ” Yonatan da Ahimawaz suna zaune a En Rogel. Wata baranya ce za tă je ta faɗa musu, su kuma su tafi su gaya wa Sarki Dawuda don suna tsoro kada a ga suna shiga birnin. Amma wani saurayi ya gan su, ya gaya wa Absalom. Sai dukansu biyu suka tashi da sauri suka shiga gidan wani mutum a Bahurim. Yana da rijiya a cikin gida, sai suka shiga cikinta. Matarsa mutumin kuwa ta kawo tabarma ta shimfiɗa a bakin rijiyar, sai ta kawo hatsi ta baza a kanta. Ba kuwa wanda ya san abin da ta yi. Da mutanen Absalom suka zo wurin matan a gidan, suka ce, “Ina Yonatan da Ahimawaz?” Matar ta ce, “Tuni, sun haye rafi.” Sai mutanen suka yi ta nemansu amma ba su ga kowa, sai suka koma Urushalima. Bayan mutanen suka tafi, sai su biyun suka fito daga rijiyar suka je suka gaya wa Sarki Dawuda. Suka ce masa, “Maza ka ƙetare kogi; Ahitofel ya ba wa Absalom shawara a yi maka kaza da kaza.” Saboda haka Dawuda da dukan mutanen da suke tare da shi suka tashi suka ƙetare Urdun. Kafin wayewar gari, babu wanda ya rage da bai haye ba. Da Ahitofel ya ga ba a bi shawararsa ba, sai ya hau jakinsa ya koma gidansa a garinsu. Ya kintsa gidansa sa’an nan ya rataye kansa. Ta haka ya mutu, aka kuma binne shi a kabarin mahaifinsa. Dawuda kuwa ya tafi Mahanayim. Absalom kuma ya ƙetare Urdun tare da dukan mutanen Isra’ila. Absalom ya riga ya naɗa Amasa a kan sojoji a maimakon Yowab. Amasa kuwa ɗan wani mutum mai suna Itra ne, mutumin Ishmayel wanda ya auri Abigiyel, ’yar Nahash, ’yar’uwar Zeruhiya mahaifiyar Yowab. Isra’ilawa da Absalom suka kafa sansani a ƙasar Gileyad. Sa’ad da Dawuda ya zo Mahanayim, sai Shobi ɗan Nahash daga Rabba ta Ammonawa, da Makir ɗan Ammiyel daga Lo Debar, da Barzillai mutumin Gileyad daga Rogelim suka kawo wa Dawuda da mutanensa tabarmai, da kwanoni, da kayayyakin da aka yi da yumɓu. Suka kuma kawo alkama da sha’ir, da gari, da soyayyen hatsi, da wake, da waken barewa, da zuma, da kindirmo, da tumaki, da cukun madarar shanu wa Dawuda da mutanensa su ci. Gama sun ce, “Mutanen suna jin yunwa, sun kuma gaji, ga ƙishirwa a hamada.” Dawuda ya tattara mutanen da suke tare da shi, ya naɗa musu komandodi na dubu-dubu, da na ɗari-ɗari. Dawuda ya sa rundunoni kashi ɗaya bisa uku a ƙarƙashin Yowab, kashi ɗaya bisa uku a ƙarƙashin Abishai, ɗan’uwan Yowab ɗan Zeruhiya, kashi ɗaya bisa uku a ƙarƙashin Ittai mutumin Gat. Sai sarki ya ce wa rundunonin, “Tabbatacce zan tafi tare da ku.” Amma mutanen suka ce, “Ba za ka fita ba; gama in ya kasance tilas mu gudu, ba za su kula da mu ba. Ko da rabinmu sun mutu, ba za su damu ba; amma kai kanka ka fi mutum dubu goma namu. Zai fi maka ka zauna a cikin gari, ka dinga aika mana da taimako.” Sarki ya ce, “Zan yi duk abin da ya fi muku kyau.” Saboda haka sarki ya tsaya kusa da bakin ƙofa yayinda dukan mutane suke fitowa a ƙungiyar ɗari-ɗari da ta dubu-dubu. Sarki ya umarci Yowab, Abishai, da Ittai, ya ce musu, “Ku yi mini hankali da saurayin nan Absalom.” Dukan mutane kuwa suka ji yadda sarki yake ba wa kowane komanda umarni. Rundunonin suka tafi zuwa fili don su yi yaƙi da Isra’ila. Aka kuwa yi yaƙi a kurmin Efraim. A nan ne mutanen Isra’ila suka sha kashi a hannun mutanen Dawuda. Waɗanda suka yi rauni da kuma waɗanda suka mutu a ranar sun yi yawa, mutum dubu ashirin. Yaƙin ya bazu a duk fāɗin ƙauyukan, abin da kurmin ya ci kawai a ranar ya fi yawan abin da aka kashe da takobi. To, Absalom ya haɗu da mutanen Dawuda. Yana hawan dokinsa, kuma yayinda dokin ya kusa kai cikin rassan babban itacen oak, sai kan Absalom ya sarƙafe a kan itacen oak ɗin. Dokin ya wuce da gudu, shi kuwa ya rataye a can yana lilo. Sa’ad da wani daga cikin mutanen ya gan haka, sai ya gaya wa Yowab, “Na ga Absalom yana rataye a itacen oak.” Yowab ya ce wa mutumin da ya ba shi labarin, “Mene! Ka ga shi? Don me ba ka buge shi har ƙasa nan da nan ba? Ai, da na ba ka shekel goma na azurfa da abin ɗamarar jarumi.” Amma mutumin ya ce wa Yowab, “Ko da za a auna mini azurfa dubu a hannuna, ba zan miƙa hannuna in taɓa ɗan sarki ba. A kunnuwanmu fa sarki ya umarce ka, da Abishai, da Ittai cewa, ‘Ku tsare saurayin nan Absalom a madadina.’ Da na yi haka da na sa kaina a halin ƙaƙa-ni-ka-yi, kuma babu abin da zai ɓoyu ga sarki, kai kuwa za ka janye abinka daga gare ni.” Yowab ya ce, “Ba zan ɓata lokaci da kai ba.” Saboda haka sai ya ɗauki māsu uku a hannunsa ya zura su a ƙahon zuciyar Absalom, tun Absalom yana da sauran rai a maƙale a itacen oak. Masu ɗaukan kayan yaƙin Yowab goma kuwa sun kewaye Absalom, suka bubbuge shi suka kashe. Sa’an nan Yowab ya busa ƙaho, sai sojoji suka bar fafaran Isra’ila, gama Yowab ya tsai da su. Suka ɗauki Absalom, suka jefa shi cikin wani babban rami a kurmin, suka kuwa tula tsibin duwatsu a kansa. Ana cikin haka, sai dukan Isra’ilawa suka tsere zuwa gidajensu. A lokacin da Absalom yake da rai, Absalom ya gina wa kansa al’amudin tunawa, a Kwarin Sarki, gama ya yi tunani ya ce, “Ba ni da ɗa namiji wanda zai sa a riƙa tunawa da ni.” Sai ya kira ginshiƙin da sunansa, ana kuwa kira shi Al’amudin Absalom har wa yau. Ahimawaz ɗan Zadok ya ce, “Bari in ruga in kai wa sarki labari cewa Ubangiji ya cece shi daga hannun abokan gābansa.” Yowab ya ce, “Ba kai ba ne za ka kai wannan labari a yau ba. Kana iya kai labarin wani lokaci, amma yau kam ba zai yiwu ba, saboda ɗan sarki ya mutu.” Sai Yowab ya ce wa wani mutumin Kush, “Je ka faɗa wa sarki abin da ka gani.” Mutumin Kush ɗin kuwa ya rusuna wa Yowab, sai ya ruga a guje. Ahimawaz ɗan Zadok ya sāke ce wa Yowab, “Ko mene ne zai faru, ina roƙonka bari in bi bayan mutumin Kush nan.” Amma Yowab ya ce, “Ɗana me ya sa kake so ka je? Ba ka da labarin da zai jawo maka lada.” Ya ce, “Ko mene ne zai faru, ina so in ruga da gudu.” Sai Yowab ya ce, “Ruga!” Sai Ahimawaz ya sheƙa a guje ya bi ta hanyar fili ya riga mutumin Kush nan. Yayinda Dawuda yake zaune tsakanin ƙofofin ciki da na waje, sai mai tsaro ya hau rufin ginin da yake kan hanyar shiga ta wajen katanga. Da ya duba sai ya ga wani mutum shi kaɗai yana gudu. Mai tsaro ya tā da murya ya faɗa wa sarki. Sarki ya ce, “In shi kaɗai ne, ya kawo labari mai kyau ke nan.” Mutumin ya matso kusa-kusa. Sai mai tsaron ya ga wani mutum yana zuwa a guje. Sai ya tā da murya ya kira mai tsaron ƙofa ya ce, “Duba, ga wani mutum kuma yana gudu shi kaɗai!” Sarki ya ce, “Shi ma yana kawo labari mai daɗi ne.” Sai mai tsaron ya ce, “A ganina gudu na farin, ya yi kama da gudun Ahimawaz, ɗan Zadok.” Sarki ya ce, “Shi mutumin kirki ne, yana zuwa da saƙo mai kyau.” Sai Ahimawaz ya tā da murya ya ce wa sarki, “Kome lafiya yake!” Sai ya rusuna har ƙasa a gaban sarki ya ce, “Yabo ya tabbata ga Ubangiji Allahnka! Ya ba da mutanen da suka tayar wa ranka yă daɗe a hannunsa.” Sai sarki ya ce, “Saurayin nan Absalom yana nan da rai?” Ahimawaz ya ce, “Na ga wani babban rikicewar a daidai lokacin da Yowab yake gab da aikan bawan sarki da kuma ni, sai dai ban san ko mene ne ba.” Sai sarki ya ce, “Koma gefe ka jira a can.” Sai ya ja gefe ya tsaya. Sai ga mutumin Kush ya iso ya ce, “Ranka yă daɗe sarki, ka ji labari mai kyau! Ubangiji ya cece ka yau daga dukan waɗanda suka tayar maka.” Sarki ya ce wa mutumin Kush, “Saurayin nan Absalom, yana nan lafiya?” Mutumin Kush ya ce, “Allah yă sa abokan gāban ranka yă daɗe, da duk waɗanda suka tayar maka da mugunta, su zama kamar saurayin nan.” Sai gaban sarki ya faɗi. Ya haura zuwa ɗakin da yake kan katangar hanyar shiga ya yi kuka. Yayinda yake tafiya ya ce, “Ya ɗana Absalom! Ɗana, ɗana Absalom! Da ma a ce ni ne na mutu maimakonka. Ya Absalom, ɗana, ɗana!” Aka faɗa wa Yowab cewa, “Sarki yana kuka, yana kuma makoki saboda Absalom.” Saboda haka sai nasarar da aka yi a ranar ta zama makoki ga dukan sojoji, gama a ranar, rundunoni sun ji an ce, “Sarki yana baƙin ciki domin ɗansa.” Mutane fa suka shiga birni shiru, sai ka ce waɗanda sukan sace jiki don kunya sa’ad da suka gudo daga yaƙi. Sarki ya rufe fuskarsa ya yi kuka da ƙarfi yana cewa, “Ya ɗana Absalom! Ya Absalom ɗana, ɗana!” Sai Yowab ya shiga gidan sarki ya ce, “Yau ka kunyatar da dukan mutanenka, waɗanda ba da daɗewa ba sun ceci ranka, da rayukan ’ya’yanka maza, da na ’ya’yanka mata, da na matanka da kuma na ƙwarƙwaranka. Kana ƙaunar maƙiyinka, kana ƙin waɗanda suke ƙaunarka. Ka bayyana a fili cewa komandodi da sojojinsu ba kome ba ne a gare ka. Na ga cewa da za ka yi farin ciki, da a ce Absalom yana da rai a yau, dukanmu kuma mun mutu. Yanzu ka fita ka ƙarfafa mutanenka. Na rantse da Ubangiji, in ba ka fita ba, babu mutum guda da za a bari tare da kai a daren nan. Wannan zai fi maka muni fiye da kowace irin masifar da ta auko maka tun ƙuruciyarka har zuwa yanzu.” Saboda haka sarki ya tashi, ya zauna a bakin hanyar shiga. Da aka faɗa wa mutane cewa, “Sarki yana zaune a bakin hanyar shiga,” sai duk suka zo gabansa. Ana cikin haka, Isra’ilawa dai sun riga sun tsere zuwa gidajensu. Mutane ko’ina a kabilan Isra’ila, suka yi ta gardama da juna, suna cewa, “Sarki ne ya cece mu daga hannun abokan gābanmu, shi ne kuma ya kuɓutar da mu daga hannun Filistiyawa. Amma ga shi ya tsere daga ƙasar saboda Absalom; kuma shi Absalom, da muka naɗa yă yi mulkinmu, ya mutu a yaƙi. Saboda haka don me ba kwa ce wani abu game da dawo da sarki?” Sai Sarki Dawuda ya aika da saƙo zuwa wurin Zadok da Abiyatar, firistoci, ya ce, “Ku tambayi dattawan Yahuda, ‘Me ya sa ku ne za ku zama na ƙarshe a yin tunanin komar da sarki zuwa fada, da yake abin da ake faɗi ko’ina a Isra’ila ya kai kunnen sarki a mazauninsa? Ku ’yan’uwana ne, jikina, jinina kuma. To, don me za ku zama na ƙarshe na yarda a dawo da sarki zuwa fada?’ Ku kuma ce wa Amasa, ‘Ashe, kai ba jikina ba ne da jinina? Allah yă hukunta ni, da hukunci mai tsanani, idan daga yanzu ba ka zama komandan sojojina a maimakon Yowab ba.’ ” Ta haka ya rinjayi zukatan dukan mutane Yahuda, kamar mutum ɗaya. Suka aika da saƙo wurin sarki suka ce, “Ka dawo, kai da dukan mutanenka.” Sa’an nan sarki ya dawo, ya kuma tafi har zuwa Urdun. To, mutanen Yahuda suka zo Gilgal don su fita su taryi sarki, su kuma kawo shi ƙetaren Urdun. Shimeyi ɗan Gera, mutumin Benyamin daga Bahurim ya gaggauta, ya gangara tare da mutanen Yahuda don su taryi Sarki Dawuda. Tare da shi akwai kabilar Benyamin mutum dubu, tare da Ziba, mai hidimar gidan Shawulu, da ’ya’yansa maza goma sha biyar, da bayi ashirin. Suka ruga zuwa Urdun, inda sarki yake. Suka haye a mashigin don su ƙetaro da iyalin sarki, su kuma yi duk abin da yake so. Sa’ad da Shimeyi ɗan Gera ya haye Urdun, sai ya fāɗi rubda ciki a gaban sarki ya ce masa, “Ranka yă daɗe, ina roƙonka kada ka riƙe laifina a zuciya. Kada ka tuna da laifin da na yi maka ranka yă daɗe, ranan nan da kake gudu daga Urushalima. Kada ka tuna da shi ko kaɗan. Na sani ni bawanka na yi maka laifi. Shi ya sa na zama na farko daga dukan Gidan Yusuf, da mutanen Isra’ila wanda ya fito don yă tarye ka yau, ranka yă daɗe, sarki.” Sai Abishai ɗan Zeruhiya ya ce, “Bai kamata a kashe Shimeyi saboda wannan ba? Ya la’anci shafaffe na Ubangiji.” Dawuda ya ce, “Me ya haɗa ni da ku, ku ’ya’yan Zeruhiya? Yau ɗin nan kun zama maƙiyana! Ya kamata a kashe wani a Isra’ila a yau? Ban san cewa yau ni sarki ne a bisa Isra’ila ba?” Saboda haka sarki ya ce wa Shimeyi, “Ba za ka mutu ba.” Sarki kuwa ya yi alkawari har da rantsuwa. Mefiboshet, jikan Shawulu, shi ma ya gangara don yă taryi sarki. Tun daga ranar da sarki ya gudu har ran da ya komo lafiya, Mefiboshet bai lura da ƙafafunsa, ko yă aske gemunsa, ko yă wanke tufafinsa ba. Sa’ad da ya zo daga Urushalima don yă taryi sarki, sai sarki ya ce masa, “Me ya sa ba ka tafi tare da ni ba Mefiboshet?” Sai ya ce, “Ranka yă daɗe sarki, da yake bawanka gurgu ne, na ce, ‘A sa mini sirdi a kan jakina don in hau in tafi tare da sarki.’ Amma Ziba bawana ya bashe ni. Ya kuwa ɓata suna bawanka a gaban ranka yă daɗe, sarki. Ranka yă daɗe, sarki yana kama da mala’ikan Allah, ka yi abin da ka ga ya fi maka kyau. Duk zuriyar kakana ba su cancanci kome ba sai mutuwa daga ranka yă daɗe, amma ka ba wa bawanka wuri cikin mutanen da suke ci a teburinka. Saboda haka, wanda ’yanci nake da shi da zan yi wani ƙarin roƙo a wurin sarki?” Sarki ya ce masa, “Me ya sa kake zancen nan? Ai, na riga na umarta, da kai, da Ziba ku raba filayen.” Mefiboshet ya ce wa sarki, “Bari yă ɗauki kome, yanzu da ranka yă daɗe, sarki ya dawo gida lafiya.” Barzillai mutumin Gileyad shi ma ya zo daga Rogelim don yă ƙetare Urdun tare da sarki, yă kuma sallame shi daga can. To, Barzillai fa tsoho ne, mai shekara tamanin. Ya tanada wa sarki a lokaci da yake Mahanayim, gama shi attajiri ne. Sarki ya ce wa Barzillai, “Ka ƙetaro tare da ni ka zauna tare da ni a Urushalima, zan kuwa tanada maka.” Amma Barzillai ya ce wa sarki, “Shekara nawa ya rage mini har da zan tafi Urushalima da sarki? Yanzu ina da shekara tamanin. Zan iya bambanta abu mai daɗi da marar daɗi kuma ne? Bawanka zai iya jin ɗanɗano abin da yake ci, ko yake sha ne? Har yanzu zan iya jin muryoyin mawaƙan maza da mata? Don me bawanka zai zama ƙari kaya ga ranka yă daɗe? Bawanka zai ƙetare Urdun tare da sarki, yă ɗan yi maka rakiya kaɗan. Me ya sa ranka yă daɗe zai ba ni irin wannan lada. Ka bar bawanka yă koma, don in mutu a garina, kusa da kabarin mahaifina da mahaifiyata. Amma ga bawanka Kimham. Bari yă ƙetare tare da ranka yă daɗe, sarki. Ka yi abin da ka ga dama da shi.” Sarki ya ce, “Kimham zai ƙetare tare da ni, zan kuwa yi masa abin da ya gamshe ka. Kuma duk abin da kake bukata a wurina, zan yi maka.” Saboda haka dukan mutane suka ƙetare Urdun, sa’an nan kuma sarki ma ya ƙetare. Sarki ya yi wa Barzillai sumba ya albarkace shi, sa’an nan Barzillai ya koma gidansa. Sa’ad da sarki ya ƙetare zuwa Gilgal, Kimham ma ya ƙetare tare da shi. Dukan sojojin Yahuda da rabin sojojin Isra’ila suka ƙetare da sarki. Nan take sai ga mutane Isra’ila suna zuwa wurin sarki, suna cewa, “Don me ’yan’uwanmu, mutanen Yahuda, suka saci sarki, suka kawo shi da iyalinsa a ƙetaren Urdun, tare da dukan mutanensa?” Dukan mutanen Yahuda suka ce wa mutanen Isra’ila, “Mun yi haka domin sarki danginmu na kurkusa ne. Don me kuke fushi game da wannan? Mun ci wani abu daga cikin kayan sarki ne? Mun ɗauki wani abu wa kanmu ne?” Sa’an nan mutanen Isra’ila suka ce wa mutanen Yahuda, “Muna da rabo goma a wurin sarki; ban da haka ma, muna da hakki mafi yawa a wurin Dawuda fiye da ku. Don me kuke mana reni? Ba mu ne ma muka fara magana dawowa da sarki ba?” Amma mutanen Yahuda suka ɗauka maganar da zafi fiye da mutanen Isra’ila. Akwai wani mai tā-da-na-zaune-tsaye, sunansa Sheba, ɗan Bikri, daga kabilar Benyamin, a wurin. Sai ya busa ƙaho, ya yi ihu ya ce, “Ba mu da rabo a wurin Dawuda, ba mu da sashe a wurin ɗan Yesse! Kowa yă nufi tentinsa, ya Isra’ila!” Saboda haka dukan mutane Isra’ila suka bar Dawuda don su bi Sheba ɗan Bikri. Amma mutanen Yahuda suka kasance a wurin sarki tun daga Urdun har zuwa Urushalima. Da Dawuda ya komo fadarsa a Urushalima, sai ya ɗauko ƙwarƙwaran goma nan da ya bari su lura da fada, ya keɓe su a wani gida inda za a yi tsaronsu. Ya tanada musu, amma bai kwana da su ba. Aka sa su a keɓe har iyakar rayuwarsu, suka yi zama kamar gwauraye. Sa’an nan sarki ya ce wa Amasa, “Ka tattaro mutanen Yahuda su zo wurina cikin kwana uku, kai kuwa ka kasance a can kai kanka.” Amma da Amasa ya tafi kiran mutanen Yahuda, ya ɗauki lokaci fiye da lokacin da sarki ya ba shi. Dawuda ya ce wa Abishai, “Ina gani Sheba ɗan Bikri zai ba mu wuya fiye da Absalom. Ka ɗauki mutanen maigidanka ka fafare shi, don kada yă sami garuruwa masu katanga yă tsere mana.” Saboda haka mutanen Yowab da Keretawa da Feletiyawa da dukan jarumawa suka fita a ƙarƙashin Abishai. Suka fita daga Urushalima don su fafari Sheba ɗan Bikri. Yayinda suke a babban dutse a Gibeyon, Amasa ya zo don yă tarye su. Yowab kuwa yana sanye da doguwar rigar soja, a ɗamarar da ya sha kuwa akwai wuƙa a cikin kube. Da ya zo gaba sai wuƙar ta zāre daga kube ta fāɗi. Yowab ya ce wa Amasa, “Yaya kake, ɗan’uwana?” Sai Yowab ya kama gemun Amasa da hannun dama don yă yi masa sumba. Amasa kuwa bai lura da wuƙar da take hannun Yowab ba, Yowab kuwa ya soke shi da wuƙar a ciki, hanjinsa suka zube ƙasa. Ba tare da ƙarin suƙa ba, Amasa ya mutu. Sa’an nan Yowab da ɗan’uwansa Abishai suka fafari Sheba ɗan Bikri. Ɗaya daga cikin mutanen Yowab ya tsaya kusa da Amasa ya ce, “Duk mai son Yowab, kuma duk mai son Dawuda, yă bi Yowab!” Amasa kuwa yana kwance cikin tafkin jininsa a kan hanya, sai mutumin ya ga dukan sojoji suka zo suka tsaya cik a can. Da ya gane cewa duk wanda ya haura zuwa wurin Amasa sai ya tsaya, sai ya ja gawar Amasa daga hanyar ya kai can cikin wani fili ya rufe shi da zane. Bayan an ɗauke Amasa daga hanya, sai dukan mutane suka bi Yowab don fafaran Sheba ɗan Bikri. Sheba ya bi ta dukan kabilan Isra’ila zuwa Abel da kuma ta dukan yankin Beriyawa, waɗanda suka taru suka bi shi. Sai dukan rundunonin da suke tare da Yowab suka zo suka yi wa Sheba kwanton ɓauna a Abel-Bet-Ma’aka. Suka tara ƙasa kewaye da jikin katangar birnin daidai da tsayinta. Sa’an nan waɗansu kuma suna ƙoƙarin rushe katangar. Sai wata mata mai hikima ta yi kira daga ciki birnin ta ce, “Ku saurara! Ku saurara! Ku gaya wa Yowab yă zo nan ina so in yi magana da shi.” Ya tafi wurinta, sai ta ce, “Kai ne Yowab?” Ya ce, “Ni ne”. Ta ce, “Ka ji abin da zan ce maka.” Ya ce, “Ina jinki.” Ta ci gaba ta ce, “A dā can, akan ce, ‘Sami amsarka a Abel,’ shi ke nan an gama. Mu ne masu salama da kuma amintattu na Isra’ila. Kana ƙoƙari ka hallaka birnin da yake uwa a Isra’ila. Don me kake so ka hallakar da gādon Ubangiji?” Yowab ya ce, “Allah yă sawwaƙe! Allah yă sawwaƙe in hallaka, ko in lalace gādon Ubangiji. Ba haka ba ne batun. Wani mai suna Sheba ɗan Bikri ne, daga ƙasar tudun Efraim, ya tayar wa sarki, yana gāba da Dawuda. Ki ba mu wannan mutum, zan kuwa janye daga birnin.” Matar ta ce wa Yowab, “Za a jefa maka kansa daga katanga.” Sa’an nan matar ta tafi wurin dukan mutane da shawararta mai hikima, sai suka datse kan Sheba ɗan Bikri suka jefa wa Yowab. Saboda haka sai ya busa ƙaho, mutanensa kuwa suka watse daga birnin, kowa ya koma gidansa. Yowab kuma ya koma wurin sarki a Urushalima. Yowab ne yake shugabancin dukan rundunoni; Benahiya ɗan Yehohiyada ne yake shugabancin Keretawa da Feletiyawa; Adoniram kuwa shi ne shugaban aikin gandu; Yehoshafat ɗan Ahilud shi ne marubucin tarihi; Shewa kuwa magatakarda; Zadok da Abiyatar su ne firistoci; Ira mutumin Yayir kuwa shi ne firist na Dawuda. Lokacin da Dawuda yake mulki, an yi yunwa shekara uku a jere; saboda haka Dawuda ya nemi nufin Ubangiji. Ubangiji ya ce, “Saboda Shawulu ne da alhakin jinin gidansa; domin ya kashe Gibeyonawa.” Sai sarki ya tattara Gibeyonawa ya yi musu magana. (To, Gibeyonawa ba sashen Isra’ilawa ba ne, amma mutanen Amoriyawa ne da suka ragu, waɗanda Isra’ila ta rantse za tă bari da rai, amma Shawulu cikin kishinsa don Isra’ila da Yahuda ya yi ƙoƙari yă hallaka su duka.) Dawuda ya ce wa Gibeyonawa, “Me zan yi muku? Yaya zan yi kafara domin ku sa wa masu gādon Ubangiji albarka?” Gibeyonawa suka ce, “Ba mu da ’yanci mu nemi zinariya ko azurfa daga wurin Shawulu ko gidansa, ba mu kuwa da wani ’yanci mu sa a kashe wani a Isra’ila.” Dawuda ya ce, “To, me kuke so in yi muku?” Suka ce wa sarki, “Mutumin da ya hallaka mu ya kuma yi mana makirci don kada mu kasance tare da Isra’ilawa ko’ina a cikin ƙauyukansu, a ba mu zuriyarsa maza bakwai, mu kashe su, mu kuma rataye jikunansu a gaban Ubangiji a Gibeya na Shawulu wannan zaɓaɓɓen Ubangiji.” Sai sarki ya ce, “Zan ba ku su.” Sarki ya ware Mefiboshet ɗan Yonatan jikan Shawulu, saboda rantsuwar da take tsakanin Dawuda da Yonatan, ɗan Shawulu a gaban Ubangiji. Amma sarki ya ɗauki Armoni da Mefiboshet, ’ya’ya biyu maza waɗanda Rizfa ’yar Aiya ta haifa wa Shawulu, tare da ’ya’ya maza biyar na Merab ’yar Shawulu, waɗanda ta haifa wa Adriyel ɗan Barzillai, mutumin Mehola. Ya ba da su ga Gibeyonawa, waɗanda suka kashe su, suka kuma rataye jikunansu a gaban Ubangiji. Dukan bakwai ɗin an kashe su gaba ɗaya; an kashe su a farkon kwanankin girbi, daidai lokacin fara girbin sha’ir. Rizfa ’yar Aiya ta ɗauki tsumma ta yi wa kanta shimfiɗa a kan dutse. Tun daga farkon girbi har ruwa damina ya sauko a kan gawawwakin, ba tă yarda tsuntsayen sama su taɓa su da rana ko mugayen namun jeji da dare ba. Da aka gaya wa Dawuda abin da Rizfa ’yar Aiya ƙwarƙwaran Shawulu ta yi, sai ya je ya kwashe ƙasusuwan Shawulu da na ɗansa Yonatan daga mutanen Yabesh Gileyad (Gama mutanen sun saci gawawwakin Shawulu da Yonatan daga inda Filistiyawa suka kakkafa su a kan itace a filin Bet-Shan, bayan da Filistiyawa suka kashe su a Gilbowa.) Dawuda ya kawo ƙasusuwan Shawulu da na ɗansa Yonatan daga can, a kuma aka tattara dukan ƙasusuwan waɗanda Gibeyonawan suka kashe, suka kuma rataye. Suka binne ƙasusuwan Shawulu da na ɗansa Yonatan a kabarin Kish, mahaifin Shawulu, a Zela a Benyamin. Suka kuma yi kome da sarki ya umarta. Bayan wannan Allah ya ji addu’arsu a madadin ƙasar. Har yanzu yaƙi ya sāke ɓarke tsakanin Filistiyawa da Isra’ila. Sai Dawuda ya gangara tare da mutanensa don su yaƙi Filistiyawa, gajiya ta kama shi. Ishbi-Benob kuwa, wani daga zuriyar Rafa, wanda nauyin kan māshinsa na tagulla ya yi shekel ɗari uku, wanda yake kuma da sabon māshi, ya ce zai kashe Dawuda. Amma Abishai ɗan Zeruhiya ya kawo wa Dawuda gudummawa; ya bugi Bafilistin, ya kashe shi. Sa’an nan mutanen Dawuda suka rantse masa suka ce, “Ba za ka ƙara fita tare da mu wurin yaƙi ba, don kada fitilar Isra’ila tă mutu.” Ana nan, sai aka sāke yin wani yaƙin da Filistiyawa, a Gob. A lokacin Sibbekai mutumin Husha ya kashe Saf, wani daga zuriyar Rafa. Sai aka sāke yin wani yaƙin da Filistiyawa a Gob, Elhanan ɗan Ya’are-Oregim mutumin Betlehem ya kashe Goliyat mutumin Gat, wanda girmar sandan māshinsa ta yi kama da taɓarya. Har wa yau a wani yaƙin da aka yi a Gat, akwai wani ƙaton mutum mai yatsotsi shida a kowane hannu, da kuma yatsotsi shida a kowane ƙafa, yatsotsi ashirin da huɗu ke nan. Shi ma daga zuriya Rafa ne. Da ya yi wa Isra’ila reni, sai Yonatan ɗan Shimeya, ɗan’uwa Dawuda, ya kashe shi. Waɗannan huɗu zuriyar Rafa ne a Gat, suka kuwa mutu ta hannu Dawuda da mutanensa. Dawuda ya rera wannan waƙa ga Ubangiji, sa’ad da Ubangiji ya cece shi daga hannun dukan abokan gābansa, da kuma daga hannun Shawulu. Ya ce, “ Ubangiji shi ne dutsena, kagarata da kuma mai cetona; Allahna shi ne dutsena. A gare shi nake samun kāriya shi ne garkuwata da kuma ƙahon cetona. Shi ne mafakata, maɓuyata, da mai cetona. Daga mutane masu fitina, ka cece ni. “Na kira ga Ubangiji, wanda ya cancanci yabo, na kuwa tsira daga abokan gābana. Raƙumar ruwan mutuwa sun kewaye ni; raƙumar ruwan hallaka suna cin ƙarfina. Igiyoyin mutuwa sun nannaɗe ni; tarkuna kuma suka auka mini. “A cikin wahalata na yi kira ga Ubangiji; na yi kira ga Allahna. Daga cikin haikalinsa ya saurare muryata; kukata ta zo kunnensa. Ƙasa ta yi rawa ta kuma girgiza, harsashan sararin sama sun jijjigu; suka yi makyarkyata saboda yana fushi. Hayaƙi ya taso daga kafaffen hancinsa; harshen wuta mai cinyewa daga bakinsa, garwashi mai ƙuna daga bakinsa. Ya buɗe sararin sama, ya sauko ƙasa, girgije mai duhu suna ƙarƙashin ƙafafunsa. Ya hau kerubobi, ya tashi sama; ya yi firiya a fikafikan iska. Ya mai da duhu abin rufuwarsa gizagizai masu kauri cike da ruwa suka kewaye shi. Daga cikin hasken gabansa garwashi wuta mai ci ya yi walƙiya. Ubangiji ya yi tsawa daga sararin sama; aka ji muryar Mafi Ɗaukaka. Ya harbe kibiyoyi, ya wartsar da abokan gāba, da walƙiya kuma ya sa suka gudu. Aka bayyana kwarin teku, tushen duniya suka tonu. A tsawatawar Ubangiji, da numfashinsa mai ƙarfi daga hancinsa. “Daga sama ya miƙo hannu ya ɗauke ni, ya tsamo ni daga zurfafa ruwaye. Ya kuɓutar da ni daga hannun abokin gāba mai iko, daga maƙiyina da suka fi ƙarfina. Suka auka mini cikin ranar masifata, amma Ubangiji ya kiyaye ni. Ya fito da ni, ya kai ni wuri mafi fāɗi; ya kuɓutar da ni gama yana jin daɗina. “ Ubangiji ya sāka mini bisa ga adalcina; bisa ga tsabtar hannuwana ya sāka mini. Gama na kiyaye hanyoyin Ubangiji; ban yi wani mugun abu da zai juyar da ni daga Allahna ba. Dukan dokokinsa suna a gabana; ban ƙi ko ɗaya daga umarnansa ba. Ba ni da laifi a gabansa na kiyaye kaina daga yin zunubi. Ubangiji ya sāka mini bisa ga adalcina bisa ga tsarkina a gabansa. “Ga masu aminci, kakan nuna kanka mai aminci, ga marasa laifi, kakan nuna kanka marar laifi, ga masu tsarki, kakan nuna musu tsarki. Amma ga masu karkataccen hali, kakan nuna kanka mai wayo. Kakan ceci mai tawali’u, amma idanunka suna a kan masu girman kai don ka ƙasƙantar da su. Ya Ubangiji kai ne fitilata; Ubangiji ya mai da duhuna haske. Da taimakonka zan iya auka wa rundunar sojoji; tare da Allahna zan iya hawan katanga. “Ga Allah dai, hanyarsa cikakkiya ce; maganar Ubangiji babu kuskure. Shi garkuwa ce ga waɗanda suka nemi mafaka a gare shi. Gama wane ne Allah, in ba Ubangiji ba? Wane ne dutse kuma in ba Allahnmu ba? Allah ne ya ba ni ƙarfi, ya kuma mai da hanyata cikakkiya. Ya sa ƙafafuna kamar ƙafafun barewa; ya sa na iya tsayawa a kan duwatsu. Ya hori hannuwana don yaƙi, hannuwana za su iya tanƙware bakan tagulla. Ka ba ni garkuwar nasararka; ka sauko don ka sa in sami girma. Ka fadada hanya a ƙarƙashina domin kada idon ƙafana yă juya. “Na fafari abokan gābana, na murƙushe su; ban kuwa juya ba sai da na hallaka su. Na hallaka su ƙaƙaf, ba kuwa za su ƙara tashi ba, sun fāɗi a ƙarƙashin sawuna. Ka ba ni ƙarfi don yaƙi; ka sa maƙiyina suka rusuna a ƙafafuna. Ka sa abokan gābana suka juya a guje, na kuwa hallaka maƙiyina. Suka nemi taimako, amma babu wanda zai cece su, suka yi kira ga Ubangiji, amma ba a amsa musu ba. Na murƙushe su, suka yi laushi kamar ƙura; na daka na kuma tattake su kamar caɓi a kan tituna. “Ka kuɓutar da ni daga harin mutanena; ka kiyaye ni kamar shugaban al’ummai. Mutanen da ban sansu ba za su kasance a ƙarƙashina, baƙi kuma su na zuwa don su yi mini fadanci; da zarar sun ji ni, sukan yi mini biyayya. Zukatansu ta karaya; suka fito da rawan jiki daga kagararsu. “ Ubangiji yana a raye! Yabo ta tabbata ga Dutsena! Ɗaukaka ga Allah, Dutse, Mai Cetona! Shi ne Allahn da yake rama mini, wanda ya sa al’ummai a ƙarƙashina, wanda ya kuɓutar da ni daga maƙiyina. Ka ɗaukaka ni bisa maƙiyina; ka kiyaye ni daga hannun mugayen mutane. Saboda haka, zan yabe ka, ya Ubangiji cikin dukan al’ummai; Zan rera waƙoƙin yabo ga sunanka. “Ya ba wa sarkinsa kyakkyawan nasara; ya nuna madawwamiyar ƙauna ga shafaffensa, ga Dawuda da zuriyarsa har abada.” Waɗannan su ne kalmomin Dawuda na ƙarshe. “Abubuwan da Dawuda ɗan Yesse ya yi magana a kai, abubuwan da mutumin da Mafi Ɗaukaka ya girmama. Mutumin da Allah na Yaƙub ya zaɓa yă zama sarki, wanda kuma yake mawaƙi waƙoƙin Isra’ila. “Ruhun Ubangiji ya yi magana ta wurina; maganarsa tana a harshena. Allah na Isra’ila ya yi magana, Dutsen Isra’ila ya ce mini, ‘Sa’ad da wani ya yi mulkin mutane da adalci, sa’ad da ya yi mulki da tsoron Allah, yana kama da hasken safiya a safiya marar girgije, kamar haske bayan ruwan sama da yakan sa ciyawa ta tsiro daga ƙasa.’ “Ashe, gidana bai daidaita da Allah ba? Ashe, Allah bai yi madawwamiyar yarjejjeniya da ni shiryayye da ɗaurarre a kowane sashi ba? Ba zai kawo ga cikar cetona yă kuma biya duk bukatuna ba? Amma za a jefar da masu mugunta duka kamar ƙayayyuwan da ba a tattara da hannu. Duk wanda ya taɓa ƙaya yakan yi amfani da wani ƙarfe ne ko sandar māshi; akan ƙone su inda suke a zube.” Waɗannan su ne sunayen jarumawan Dawuda. Yosheb-Basshebet, mutumin Takemon ɗaya daga cikin shugabanni Uku; ya ɗaga māshinsa ya kashe mutum ɗari takwas a lokaci guda. Na biye da shi a matsayi cikin jarumawa ukun nan, shi ne Eleyazar ɗan Dodo, mutumin Aho. Eleyazar ya kasance tare da Dawuda sa’ad da suka fuskanci Filistiyawa waɗanda suka taru a Fas Dammim don yaƙi. Mutanen Isra’ila suka gudu, amma ya yi tsayi daka, ya bugi Filistiyawa sai da hannunsa ya gaji har ya liƙe wa māshinsa. Ubangiji kuwa ya sa aka yi babban nasara a ranar. Sauran sojoji suka komo wurin Eleyazar, don kawai su washe ganima. Na biye da Agiyi a matsayi, shi ne Shamma ɗan Agi, mutumin Harar. Sa’ad da Filistiyawa suka taru a wani wurin da take gona cike da waken barewa, sai rundunar Isra’ila suka gudu daga Filistiyawa. Amma Shamma ya yi tsayi daka a tsakiyar gonar. Ya kāre ta, ya kuma bugi Filistiyawa, Ubangiji kuwa ya sa aka yi babban nasara. A lokacin girbi, uku daga cikin shugabanni talatin suka gangaro zuwa wurin Dawuda a kogon Adullam. A lokacin kuwa sojojin Filistiyawa sun kafa sansani a Kwarin Refayim. Dawuda kuwa yana a mafaka. Wata ƙungiyar sojojin Filistiyawa kuma suna Betlehem. Dawuda ya ji ƙishirwa, sai ya ce, “Kash, da a ce wani yă samo mini ruwa daga rijiyar da take kusa da bakin ƙofar Betlehem mana!” Sai jarumawa ukun nan suka yi kukan ƙura, suka sheƙa a guje suka ratsa cikin sansanin Filistiyawa, suka ɗebo ruwa daga rijiyar da take kusa da bakin ƙofar Betlehem, suka kawo wa Dawuda. Amma Dawuda ya ƙi yă sha; a maimako sai ya zuba shi a gaban Ubangiji. Sai ya ce, “ Ubangiji yă sawwaƙe, in yi sha! Ba jinin mutanen da suka tafi a bakin ransu ba ne?” Dawuda kuwa bai sha ruwan ba. Irin abubuwan da jarumawa ukun nan suka yi ke nan. Abishai, ɗan’uwan Yowab, ɗan Zeruhiya shi shugaban Ukun nan. Ya ɗauki māshinsa ya kashe mutane ɗari uku, ta haka ya zama sananne kamar Ukun nan. Ashe, ba a girmama shi fiye da Ukun ba? Ya zama komandansu, ko da yake ba a haɗa shi a cikinsu ba. Benahiya, ɗan Yehohiyada mutumin Kabzeyel shi ma jarumi ne sosai, ya yi nasarori masu yawa. Ya bugi ƙwararrun jarumawan Mowab guda biyu. Ya kuma shiga rami wata ranar da ake ƙanƙara, ya kashe zaki. Ya kuma buge wani jibgaggen mutumin Masar. Duk da māshin da mutumin Masar yana riƙe a hannunsa, Benahiya ya kai masa hari da kulki. Ya ƙwace māshin daga hannunsa, ya kuma kashe shi da māshin. Irin nasarorin da Benahiya ɗan Yehohiyada ya yi ke nan; shi ma jarumi ne sosai kamar jarumawan nan uku. Aka fi ba shi girma fiye da talatin ɗin nan, amma ba ya cikin ukun. Dawuda ya sa shi yă zama ɗaya daga cikin masu tsaron lafiyarsa. Cikin talatin ɗin kuwa akwai, Asahel, ɗan’uwan Yowab, Elhanan, ɗan Dodo mutumin Betlehem, Shamma, mutumin Harod, Elika, mutumin Harod, Helez, mutumin Falti, Ira, ɗan Ikkesh mutumin Tekowa, Abiyezer, mutumin Anatot, da Mebunnai, mutumin Husha, Zalmon, mutumin Aho, da Maharai, mutumin Netofa, Heleb, ɗan Ba’ana daga Netofa, Ittai, ɗan Ribai mutumin Gibeya a Benyamin, Benahiya, mutumin Firaton, da Hiddai, daga rafuffukan Ga’ash, Abi-Albon, mutumin Arba, da Azmawet, mutumin Bahurim, Eliyaba, mutumin Sha’albo, ’Ya’yan Yashen, Yonatan, ɗan Shamma mutumin Harar, da Ahiyam, ɗan Sharar mutumin Harod. Elifelet, ɗan Ahasbai mutumin Ma’aka, Eliyam, ɗan Ahitofel mutumin Gilo, Hezro, mutumin Karmel, Fa’arai, mutumin Arbi, Igal, ɗan Natan mutumin Zoba, ɗan Hagiri, Zelek, mutumin Ammon Naharai, mutumin Beyerot mai ɗaukan wa Yowab, ɗan Zeruhiya makamai, Ira, mutumin Itra. Gareb, mutumin Itra, da kuma Uriya, mutumin Hitti. Su talatin da bakwai ne duka. Fushin Ubangiji ya sāke ƙuna a kan Isra’ila, sai ya zuga Dawuda, yana cewa, “Je ka ƙidaya Isra’ila da Yahuda.” Saboda haka sarki ya ce wa Yowab da komandodin da suke tare da shi, “Tafi cikin dukan kabilan Isra’ila, daga Dan har zuwa Beyersheba, ku ƙidaya mayaƙa don in san yawansu.” Amma Yowab ya ce wa sarki, “ Ubangiji Allahnka ya sa mayaƙan su ƙaru sau ɗari fiye da yadda suke, har ranka yă daɗe, sarki yă gani da idonsa. Me ya sa ranka yă daɗe, sarki yake so yă yi abu haka?” Duk da haka, maganar sarki ya rinjayi Yowab da komandodin soja, sai suka tashi daga gaban sarki, suka tafi su ƙirga mayaƙan Isra’ila. Bayan suka ƙetare Urdun, sai suka yi sansani kusa da Arower, kudu da garin da yake cikin kwari, sa’an nan suka ratsa ta wajen Gad, suka ci gaba zuwa Yazer. Suka tafi Gileyad ta yankin Tatim Hodshi, sa’an nan suka tafi Dan Ya’an, suka kuma yi wajen kewaye Sidon. Sa’an nan suka yi ta wajen kagarar Taya da dukan garuruwan Hiwiyawa da Kan’aniyawa. A ƙarshe, suka ci gaba zuwa Beyersheba a Negeb na Yahuda. Bayan suka ratsa dukan ƙasashen, a ƙarshe suka koma Urushalima, bayan wata tara da kwana ashirin. Yowab ya ba wa sarki jimillar yawan mayaƙan. A Isra’ila akwai mutum dubu ɗari takwas da za su iya riƙe takobi. A Yahuda kuwa mutum dubu ɗari biyar. Bayan Dawuda ya ƙidaya mayaƙan, lamirinsa ya kāshe shi, sai ya ce wa Ubangiji, “Ya Ubangiji na yi laifi ƙwarai a kan abin da na yi. Ina roƙonka ka gafarta wa bawanka. Na yi wauta ƙwarai.” Kafin Dawuda yă tashi da safe kashegari, maganar Ubangiji ta riga ta zo wa annabin nan Gad, mai duban nan na Dawuda. Ubangiji ya ce, “Je ka faɗa wa Dawuda, ‘Ga abin da Ubangiji ya ce, ina ba ka zaɓi uku. Ka zaɓi ɗaya daga cikinsu don in aikata maka shi.’ ” Sai Gad ya zo wurin Dawuda ya ce masa, “Kana so a yi yunwa shekara uku a ƙasarka? Ko kana so ka yi ta gudu a gaban abokan gābanka har wata uku? Ko kuwa ka fi so a yi annoba kwana uku a ƙasarka? Yanzu, sai ka yi tunani, ka yanke shawarar game da amsar da zan mayar wa wanda ya aiko ni.” Dawuda ya ce wa Gad, “Na shiga uku. Gara mu fāɗa a hannuwan Ubangiji gama alherinsa da girma yake. Amma fa kada ka bar ni in fāɗa a hannun mutane.” Saboda haka Ubangiji ya aika da annoba a kan Isra’ila tun daga safe har zuwa lokacin da aka ƙayyade, mutum dubu saba’in kuwa daga Dan zuwa Beyersheba suka mutu. Da mala’ikan Ubangiji ya miƙa hannunsa wajen Urushalima, don yă hallaka ta, sai Ubangiji ya tsai da masifar, ya ce wa mala’ikan da yake wahal da mutane, “Ya isa, ka janye hannunka.” A lokacin kuwa Mala’ikan Ubangiji yana tsaye a masussukar Arauna, mutumin Yebus. Da Dawuda ya ga mala’ikan da ya bubbugi mutane, sai ya ce wa Ubangiji, “Ni ne na yi zunubi, na kuma yi abin da ba daidai ba. Waɗannan tumaki ne kawai. Me suka yi? Bari hukuncinka yă sauko a kaina da iyalina.” A ranar, Gad ya koma wurin Dawuda ya ce, “Ka tashi, ka tafi ka gina wa Ubangiji bagade a masussukar Arauna, mutumin Yebus.” Saboda haka Dawuda ya haura, yadda Ubangiji ya umarta ta wurin Gad. Da Arauna ya hangi Dawuda da mutanensa suna zuwa wajensa, sai ya fita a guje, ya je ya rusuna a gaban sarki. Arauna ya ce, “Me ya sa ranka yă daɗe, sarki ya zo wajen bawansa?” Dawuda ya ce, “Don in saya masussukarka, saboda in gina wa Ubangiji bagade don a tsayar da annoban da suke a bisa mutane.” Arauna ya ce wa Dawuda, “Bari ranka yă daɗe, sarki yă ɗauki duk abin da ya ga dama yă miƙa shi. Ga shanu, don hadaya ta ƙonawa, ga kuma kayan masussuka da itacen shanu, don itace.” Dukan wannan, ranka yă daɗe, Arauna ya ba wa sarki. Arauna ya kuma ce, “Bari Ubangiji Allahnka yă karɓa.” Amma sarki ya ce wa Arauna, “A’a, dole in biya ka saboda waɗannan. Ba yadda zan miƙa wa Ubangiji Allahna hadayun ƙonawa da bai ci mini kome ba.” Sai Dawuda ya saya, ya kuma biya masussukar, da shanun a bakin shekel hamsin na azurfa. Dawuda ya gina wa Ubangiji bagade a wurin, ya kuma miƙa masa hadaya ta ƙonawa, da hadaya ta salama. Sa’an nan Ubangiji ya amsa addu’o’in a madadin ƙasar, aka kuma kawar wa Isra’ila annoban. Sa’ad da Sarki Dawuda ya tsufa ya kuma ƙara shekaru, ba ya iya jin ɗumi ko an rufe shi da abin rufuwa. Saboda haka bayinsa suka ce masa, “Bari mu nemi wata budurwa wadda za tă yi wa ranka yă daɗe, sarki hidima, tă kuma kula da shi. Za tă dinga kwanta kusa da ranka yă daɗe, yă ji ɗumi.” Suka nemi kyakkyawar yarinya cikin fāɗin Isra’ila, sai suka sami Abishag, mutuniyar Shunam, suka kawo ta wa sarki. Yarinyar kuwa kyakkyawa ce ƙwarai; ta kuwa lura da sarki, ta kuma yi masa hidima, amma sarki bai yi jima’i da ita ba. Adoniya, wanda mahaifiyarsa ce Haggit, ya fito ya ce, “Zan zama sarki.” Saboda haka ya nemi kekunan yaƙi, ya kuma shirya dawakai, tare da mutane hamsin da za su sha gabansa. (A duk rayuwarsa mahaifinsa bai taɓa tsawata masa yă ce, “Me ya sa kake yin haka ba?” Shi kuwa mai kyan gani ne ƙwarai, shi ne aka haifa bayan Absalom.) Adoniya ya haɗa baƙi da Yowab ɗan Zeruhiya da kuma Abiyatar firist, suka kuma ba shi goyon baya. Amma Zadok firist, Benahiya ɗan Yehohiyada, annabi Natan, Shimeyi, Reyi da kuma matsara na musamman na Dawuda ba su bi Adoniya ba. Wata rana Adoniya ya tafi Dutsen Zohelet kusa da En Rogel, inda ya yi hadayar tumaki, da shanun noma, da shanun da ake kiwo a gida. Ya kuma gayyaci ’yan’uwansa, wato, sauran ’ya’yan Sarki Dawuda, tare da dukan dattawan sarki da suka fito daga Yahuda, amma bai gayyaci annabi Natan, ko Benahiya, ko wani daga matsara na musamman, ko kuwa ɗan’uwansa Solomon ba. Sai Natan ya ce wa Batsheba, mahaifiyar Solomon, “Ki san cewa Adoniya, ɗan Haggit, ya zama sarki ba tare da sanin ranka yă daɗe, sarkinmu Dawuda ba? Yanzu bari in ba ki shawara yadda za ki cece ranki da kuma ran ɗanki Solomon. Ki shiga wurin Sarki Dawuda ki ce masa, ‘Ranka yă daɗe sarki, ba ka rantse mini ni baiwarka cewa, “Tabbatacce Solomon ɗanka ne zai zama sarki bayana, yă kuma zauna a kujerar sarautar ba”? To, me ya sa Adoniya ya zama sarki?’ Yayinda kike can kina magana da sarki, zan shiga in kuma tabbatar da abin da kika faɗa.” Saboda haka Batsheba ta je don tă ga sarki. A yanzu dai sarki ya tsufa, yana nan kuma a cikin ɗakinsa, inda Abishag mutuniya Shunam take masa hidima. Batsheba ta rusuna ta kuma durƙusa a gaban sarki. Sai sarki ya tambaye ta ya ce, “Me kike so?” Ta ce masa, “Ranka yă daɗe, kai kanka ka rantse mini ni baiwarka da sunan Ubangiji Allahnka cewa, ‘Solomon ɗanka zai zama sarki bayana, zai kuma zauna a kujerar sarautata.’ Amma yanzu Adoniya ya zama sarki, kai kuwa ranka yă daɗe sarki, ba ka san wani abu game da shi ba. Ya miƙa hadayun shanu, da shanun da ake kiwo a gida, da tumaki masu yawa, ya kuma gayyaci dukan ’ya’yan sarki maza, da Abiyatar firist, da Yowab shugaban mayaƙa, amma bai gayyaci Solomon bawanka ba. Ranka yă daɗe sarki, idanun dukan Isra’ila suna a kanka, domin su san wa zai zauna a kujerar ranka yă daɗe sarkina, a bayanka. In ba haka, bayan an binne ranka yă daɗe sarki, tare da kakanninsa, za a wulaƙance ni da Solomon ɗana, kamar masu laifi.” Yayinda take cikin magana tare da sarki, sai annabi Natan ya iso. Sai aka faɗa wa sarki, “Ga annabi Natan.” Da Natan ya je gaban sarki, sai ya rusuna da fuskarsa har ƙasa. Natan ya ce, “Ranka yă daɗe, sarki, ko ka furta cewa Adoniya ne zai zama sarki a bayanka, yă kuma zauna a kujerar sarautarka? Yau ya gangara, ya kuma miƙa hadayun shanu, da shanun da ake kiwo a gida, da tumaki masu yawa. Ya gayyaci dukan ’ya’yan sarki maza, da shugaban mayaƙa, da kuma Abiyatar firist. A yanzu haka suna ci, suna sha, tare da shi, suna cewa, ‘Ran Sarki Adoniya yă daɗe!’ Amma bai gayyace ni bawanka, da Zadok firist, da Benahiya ɗan Yehohiyada, da kuma bawanka Solomon ba. Ranka yă daɗe, sarki, ko ka tabbatar da haka, amma ba ka ko faɗa wa fadawanka, cewa ga wanda zai gāje Ranka yă daɗe, sarki ba?” Sai Dawuda ya ce, “Kira Batsheba tă shiga.” Sai ta zo gaban sarki ta kuma tsaya a gabansa. Sai sarki ya yi rantsuwa, “Muddin Ubangiji yana a raye, wanda ya cece ni daga kowace damuwa, tabbatacce a yau zan aikata abin da na yi miki rantsuwa da sunan Ubangiji, Allah na Isra’ila; Solomon ɗanki zai zama sarki bayana, kuma shi zai zauna a kan kujerar sarautata a maimakona.” Sai Batsheba ta rusuna da fuskarta har ƙasa, ta kuma durƙusa a gaban sarki ta ce, “Bari ran Sarkina Dawuda yă daɗe, har abada!” Sarki Dawuda ya ce, “Ku kira mini Zadok firist, annabi Natan, da Benahiya ɗan Yehohiyada.” Da suka zo gaban sarki, sai ya ce musu, “Ku ɗauki bayin sarki tare da ku, ku kuma sa ɗana Solomon a kan dokina, ku gangara da shi zuwa Gihon. A can ku sa Zadok firist, da annabi Natan su shafe shi sarki a bisa Isra’ila. Ku busa ƙaho, ku kuma yi ihu, kuna cewa, ‘Ran Sarki Solomon yă daɗe!’ Sa’an nan ku haura tare da shi, zai kuwa zo yă zauna a kujera sarautata, yă yi mulki a maimakona. Na naɗa shi mai mulki a bisa Isra’ila da Yahuda.” Benahiya ɗan Yehohiyada ya amsa wa sarki, ya ce, “Amin! Bari Ubangiji Allah na ranka yă daɗe sarkina, yă tabbatar da haka. Kamar yadda Ubangiji ya kasance da ranka yă daɗe, sarki, haka ma bari yă kasance da Solomon, yă kuma mai da kujerar sarautarsa tă fi kujerar sarautar ranka yă daɗe, Sarki Dawuda, girma!” Sai Zadok firist, annabi Natan, Benahiya ɗan Yehohiyada, Keretawa, da Feletiyawa suka gangara, suka sa Solomon a kan dokin Sarki Dawuda, suka raka shi zuwa Gihon. Zadok firist ya ɗauki ƙahon mai daga tenti mai tsarki, ya shafe Solomon. Sa’an nan suka busa ƙaho, sai dukan mutane suka yi ihu, suna cewa “Ran Sarki Solomon yă daɗe!” Dukan mutane kuwa suka haura suka bi shi, suna busan sarewa, suna farin ciki sosai, har ƙasa ta girgiza saboda sowa. Adoniya tare da dukan baƙin da suke tare da shi kuwa suka ji wannan sa’ad da suke gama bikinsu. Da jin busan ƙaho, sai Yowab ya yi tambaya, ya ce, “Me ya jawo surutu haka a birni?” Tun yana cikin magana, sai Yonatan ɗan Abiyatar ya iso. Adoniya ya ce, “Shigo! Ai, mutumin kirki irinka, lalle ka kawo labari mai daɗi ne.” Yonatan ya ce wa Adoniya, “A ina! Ranka yă daɗe, Sarkinmu Dawuda ya naɗa Solomon sarki. Sarki ya aika shi tare da Zadok firist, annabi Natan, Benahiya ɗan Yehohiyada, Keretawa, da Feletiyawa, suka sa shi a kan dokin sarki, Zadok firist kuwa da annabi Natan sun shafe shi sarki a Gihon. Daga can suka haura suna kirari, birni kuwa ta ɓarke da sowa. Surutun da kake ji ke nan. Ban da haka ma, Solomon ne sarki yanzu. Yanzu haka, fadawa sun zo suna wa ranka yă daɗe, Sarki Dawuda, sam barka, suna cewa, ‘Bari Allahnka yă sa sunan Solomon yă zama sananne fiye da naka, bari kuma sarautarsa tă fi taka girma!’ Sarki kuwa ya rusuna, ya yi sujada a kan gadonsa ya ce, ‘Yabo ga Ubangiji, Allah na Isra’ila, wanda ya bar idanuna suka ga magāji a kan kujerar sarautata a yau.’ ” A nan fa, dukan baƙin Adoniya suka taso da rawar jiki suka watse. Amma Adoniya, don tsoron Solomon, ya je ya kama ƙahon bagade ya riƙe. Sa’ad da aka faɗa wa Solomon cewa, “Adoniya yana tsoron Sarki Solomon, kuma ya manne wa ƙahonin bagade. Yana cewa, ‘Bari Sarki Solomon yă rantse mini a yau cewa ba zai kashe bawansa da takobi ba.’ ” Solomon ya amsa ya ce, “In ya nuna kansa mai biyayya, ba gashin kansa da zai fāɗi ƙasa; amma in aka same mugunta a cikinsa, zai mutu.” Sai Sarki Solomon ya aiki mutane, suka kuma sauko da shi daga bagade. Adoniya kuwa ya zo, ya rusuna wa Sarki Solomon, sai Solomon ya ce, “Tafi gidanka.” Da lokacin mutuwar Dawuda ya yi kusa, sai ya gargaɗe Solomon ɗansa, ya ce, “Ina gab da bin hanyar da kowa a duniya zai bi. Saboda haka ka yi ƙarfin hali, ka nuna kanka namiji, ka kiyaye abin da Ubangiji Allahnka yake bukata. Yi tafiya a hanyoyinsa, ka kiyaye ƙa’idodi, da umarnai, da dokoki, da kuma farillansa, kamar yadda suke a rubuce a Dokar Musa, don ka yi nasara a cikin kome da za ka yi, da kuma inda za ka tafi. Ubangiji kuwa zai kiyaye alkawarinsa gare ni da ya ce, ‘In zuriyarka suka lura da yadda suke rayuwa, in kuma suka yi tafiya da aminci a gabana da dukan zuciyarsu, da kuma dukan ransu, ba za ka kāsa samun mutum a kujerar sarautar Isra’ila ba.’ “Yanzu fa, kai kanka ka san abin da Yowab ɗan Zeruhiya ya yi mini. Abin da ya yi wa shugabanni biyun nan na mayaƙan Isra’ila, wato, Abner ɗan Ner, da Amasa ɗan Yeter. Ya kashe su, ya kuma zub da jininsu a lokacin salama sai ka ce a fage yaƙi, da wannan jini ya yi ɗamara a gindinsa, ya kuma sa takalma a ƙafafunsa. Ka yi da shi gwargwadon hikimarka, amma kada ka bari yă gangara kabari da furfura cikin salama. “Amma ka yi alheri ga ’ya’yan Barzillai mutumin Gileyad, ka sa su kasance a cikin waɗanda suke ci a teburinka. Sun goyi bayana sa’ad da nake gudu daga ɗan’uwanka Absalom. “Ka tuna, akwai kuma Shimeyi ɗan Gera, mutumin Benyamin daga Bahurim, wanda ya yi ta yin mini muguwar la’ana a ranar da na tafi Mahanayim. Sa’ad da ya gangara ya same ni a Urdun, na rantse masa da sunan Ubangiji na ce, ‘Ba zan kashe ka da takobi ba.’ Amma yanzu, kada ka ɗauke shi marar laifi. Kai mutum ne mai hikima; za ka san abin da za ka yi da shi. Ka kawo furfuransa zuwa kabari da jini.” Sa’an nan Dawuda ya huta tare da kakanninsa. Sai aka binne shi a Birnin Dawuda. Ya yi sarauta shekaru arba’in a bisa Isra’ila. Wato, shekaru bakwai a Hebron da kuma talatin da uku a Urushalima. Solomon kuwa ya zauna a kan kujerar sarautar mahaifinsa Dawuda, mulkinsa kuwa ya kahu sosai. To, sai Adoniya, ɗan Haggit ya tafi wurin Batsheba mahaifiyar Solomon. Ita kuwa ta tambaye shi ta ce, “Lafiya?” Ya amsa ya ce, “I, lafiya.” Sa’an nan ya ƙara da cewa, “Ina da ɗan wani abin da zan faɗa miki.” Ta ce, “Faɗa.” Sai ya ce, “Kamar yadda kika sani, mulkin nan nawa ne. Dukan Isra’ila suna ɗaukana a matsayin sarki. Amma abubuwa suka canja, sai mulkin ya koma ga ɗan’uwana; gama ya zo masa daga Ubangiji ne. Yanzu ina da roƙo guda da zan yi gare ki. Kada ki hana mini.” Ta ce, “Sai ka faɗa.” Sai ya ci gaba, “In kin yarda, ki yi magana da Sarki Solomon, gama ba zai ƙi jinki ba, ki ce yă ba ni yarinyan nan, Abishag, mutuniyar Shunam, tă zama matata.” Batsheba ta ce, “Da kyau, zan yi magana da sarki dominka.” Sai Batsheba ta tafi wurin Sarki Solomon don tă yi masa magana a kan Adoniya. Sarki ya miƙe tsaye don yă sadu da ita, ya rusuna mata, ya kuma zauna a kujerar sarautarsa. Ya sa aka kawo wa mahaifiyar sarki kujerar sarauta, ta kuwa zauna a gefen damansa. Ta ce, “Ina da ɗan roƙon da zan nema ka yi mini. Ina fata ba za ka hana ni ba.” Sai sarki ya amsa ya ce, “Mahaifiyata, sai ki faɗa in ji, ba zan hana miki ba.” Saboda haka sai ta ce, “Ka sa a ba wa ɗan’uwanka Adoniya, Abishag mutuniyar Shunam tă zama matarsa.” Sarki Solomon ya amsa wa mahaifiyarsa ya ce, “Me ya sa kika roƙar wa Adoniya Abishag mutuniyar Shunam kawai? Ki ma sa a ba shi mulkin mana. Ai, shi yayana ne. I, ki roƙa dominsa, da domin Abiyatar firist, da kuma domin Yowab ɗan Zeruhiya mana!” Sai Sarki Solomon ya rantse da sunan Ubangiji ya ce, “Bari Allah yă yi mini hukunci mai tsanani, idan ban sa Adoniya ya biya wannan roƙo da ransa ba! Yanzu kuwa, muddin Ubangiji yana a raye, shi wanda ya kafa ni sosai a kan kujerar sarautar mahaifina Dawuda, ya kuma kafa mini mulki kamar yadda ya yi alkawari; za a kashe Adoniya yau!” Saboda haka Sarki Solomon ya umarci Benahiya ɗan Yehohiyada yă kashe Adoniya; ya kuwa kashe shi. Ga Abiyatar firist kuwa sarki ya ce, “Tafi gonarka a Anatot. Ka cancanci ka mutu, amma ba zan kashe ka yanzu ba, domin ka ɗauki akwatin alkawarin Ubangiji Mai Iko Duka a gaban mahaifina Dawuda, ka kuma sha wahala tare mahaifina.” Saboda haka Solomon ya cire Abiyatar daga aikin firist na Ubangiji, ya cika maganar da Ubangiji ya yi a Shilo game da gidan Eli. Sa’ad da labarin ya kai wurin Yowab, wanda ya haɗa kai da Adoniya, ko da yake bai haɗa kai da Absalom ba, sai ya gudu zuwa tentin Ubangiji, ya kama ƙahonin bagade ya riƙe. Aka faɗa wa Sarki Solomon cewa Yowab ya gudu zuwa tentin Ubangiji, yana kuma kusa da bagade. Sai Solomon ya umarci Benahiya ɗan Yehohiyada ya ce, “Je ka kashe shi!” Sai Benahiya ya shiga tentin Ubangiji ya ce wa Yowab, “Sarki ya ce, ‘Ka fita!’ ” Amma Yowab ya amsa ya ce, “A’a, a nan zan mutu.” Sai Benahiya ya ce wa sarki, “Ga yadda Yowab ya amsa mini.” Sai sarki ya umarci Benahiya ya ce, “Yi kamar yadda ya faɗa. Ka kashe shi, ka kuma binne shi, ka wanke ni da gidan mahaifina daga laifin jini marasa laifin da Yowab ya zubar. Ubangiji zai sāka masa saboda jinin da ya zubar, domin ba da sanin mahaifina Dawuda ne ya fāɗa wa mutum biyun nan da takobi ba. Dukansu biyu, Abner ɗan Ner, shugaban mayaƙan Isra’ila, da Amasa ɗan Yeter, shugaban mayaƙan Yahuda, mutane ne mafi kyau da kuma mafi adalci fiye da shi. Bari alhakin jininsu yă koma a kan Yowab da kuma zuriyarsa har abada. Amma bari salamar Ubangiji tă kasance a kan Dawuda da zuriyarsa, da gidansa, da kuma mulkinsa, har abada.” Sai Benahiya ɗan Yehohiyada ya haura ya bugi Yowab, ya kashe shi, ya kuwa binne shi a gidansa a ƙauye. Sai sarki ya sa Benahiya ɗan Yehohiyada ya zama shugaba a bisa mayaƙa a matsayin Yowab, ya kuma sa Zadok firist a wurin Abiyatar. Sa’an nan sarki ya aika aka kawo Shimeyi, ya kuma ce masa, “Ka gina wa kanka gida a nan a Urushalima, ka zauna a ciki, kada ka kuskura ka tafi wani wuri. Gama ran da ka fita, ka haye Kwarin Kidron, ka tabbata za ka mutu, alhakin jininka kuwa zai koma kanka.” Shimeyi ya amsa wa sarki ya ce, “Abin da ka faɗa yana da kyau. Bawanka zai yi kamar yadda ranka yă daɗe sarki, ya faɗa.” Shimeyi kuwa ya yi zama a Urushalima na dogon lokaci. Amma bayan shekaru uku, biyu daga cikin bayin Shimeyi suka gudu zuwa wurin Akish ɗan Ma’aka, sarkin Gat. Aka faɗa wa Shimeyi cewa, “Bayinka suna a Gat.” Da jin haka, sai ya tashi ya shimfiɗa wa jakinsa abin zama, ya hau, ya tafi Gat wurin Akish domin neman bayinsa. Shimeyi kuwa ya dawo da su gida daga Gat. Da aka faɗa wa Solomon cewa Shimeyi ya bar Urushalima zuwa Gat, har ya dawo. Sai sarki ya aika a kawo Shimeyi, ya ce masa, “Ban sa ka rantse da sunan Ubangiji, na kuma ja maka kunne cewa, ‘A ranar da ka kuskura ka bar nan ka tafi wani wuri, ka tabbata za ka mutu ba’? A lokacin ka ce mini, ‘Abin da ka faɗa yana da kyau. Zan kuwa kiyaye.’ To, me ya sa ba ka kiyaye rantsuwar da ka yi ga Ubangiji, ka kuma yi biyayya da umarnin da na ba ka ba?” Sarki ya ce wa Shimeyi, “Ka sani a zuciyarka dukan muguntar da ka yi wa mahaifina Dawuda. Yanzu Ubangiji zai sāka maka saboda muguntarka. Amma za a yi wa Sarki Solomon albarka, sarautar Dawuda kuma za tă kasance a tsare a gaban Ubangiji har abada.” Sai sarki ya umarci Benahiya ɗan Yehohiyada, yă fita, yă bugi Shimeyi, yă kashe shi. Ya kuwa kashe shi. Mulki kuwa ya kahu sosai a hannun Solomon. Solomon ya haɗa kai da Fir’auna sarkin Masar, ya kuwa auri ’yarsa. Ya kawo ta cikin Birnin Dawuda kafin yă gama ginin fadarsa, da haikalin Ubangiji, da kuma katanga kewaye da Urushalima. A lokacin dai mutane suna miƙa hadaya a wurare a bisa tuddai, domin ba a riga an gina haikali saboda Sunan Ubangiji ba. Solomon ya ƙaunaci Ubangiji ta wurin yin tafiya bisa ga farillan mahaifinsa Dawuda, sai dai ya miƙa hadayu, ya kuma ƙone turare a wuraren nan na bisa tuddai. Sai sarki Solomon ya tafi Gibeyon don yă miƙa hadayu, gama a can ne wuri mafi muhimmanci na sujada. Solomon kuwa ya miƙa hadayun ƙonawa guda dubu a kan wannan bagade. A Gibeyon, Ubangiji ya bayyana ga Solomon da dare a mafarki, Allah ya ce, “Ka roƙi abin da kake so in ba ka.” Solomon ya amsa ya ce, “Ka nuna alheri mai girma ga bawanka, mahaifina Dawuda domin ya yi aminci gare ka da adalci, ya kuma kasance da zuciya mai gaskiya. Ka ci gaba da wannan alheri mai girma gare shi, ka ba shi ɗa don yă zauna a kujerar sarautarsa a wannan rana. “Yanzu, ya Ubangiji Allahna, ka sa bawanka a wurin mahaifina Dawuda. Amma ni ɗan yaro ne kawai, ban kuma san yadda zan yi ayyukana ba. Bawanka yana nan a cikin mutanen da ka zaɓa, mutane masu girma, waɗanda suka wuce ƙirge, ko a lissafta. Saboda haka ka ba bawanka zuciyar ganewa, don yă shugabanci mutanenka, yă kuma iya rarrabe tsakanin abin da yake daidai da abin da ba daidai ba. Gama wa zai iya shugabance wannan mutanenka masu girma haka?” Sai Ubangiji ya ji daɗi cewa Solomon ya roƙa wannan. Saboda haka Allah ya ce masa, “Da yake ka nemi wannan ne, ba ka kuwa nemi tsawon rai ko arziki wa kanka ba, ba ka kuma nemi mutuwar abokan gābanka ba, amma ka nemi ganewa a aikata gaskiya, zan yi abin da ka roƙa. Zan ba ka zuciya mai hikima da ta ganewa, har yă zama ba a taɓa samun wani kamar ka ba, ba kuwa za a taɓa samunsa ba. Ban da haka ma, zan ba ka abin da ba ka nema ba; arziki da girma, don a rayuwarka ba za ka kasance da wani kamar ka ba a cikin sarakuna. In kuma ka yi tafiya a hanyoyina, ka kuma yi biyayya da farillaina da umarnaina kamar yadda Dawuda mahaifinka ya yi, zan ba ka tsawon rai.” Sai Solomon ya farka, ya gane ashe mafarki ne. Ya koma Urushalima, ya tsaya a gaban akwatin alkawarin Ubangiji ya miƙa hadayun ƙonawa da hadayun salama. Sa’an nan ya shirya wa fadawansa biki. To, ana nan sai waɗansu karuwai biyu suka zo wurin sarki, suka tsaya a gabansa. Sai ɗaya ta ce, “Ranka yă daɗe, wannan mata da ni muna zama a gida ɗaya. Na haifi jariri yayinda take can tare da ni. Kwana uku bayan haihuwar jaririna, wannan mata ma ta haifi jariri. Mu dai kaɗai ne; babu wani a gidan sai mu biyu. “Da dare ɗan wannan matan ya mutu domin ta kwanta a kansa. Saboda haka ta tashi da tsakar dare ta ɗauki ɗana daga gefena yayinda baiwarka take barci. Sai ta sa shi kusa da ƙirjinta, ta kuma sa mataccen ɗanta kusa da ƙirjina. Kashegari, da na farka don in shayar da ɗana, sai na tarar ya mutu! Amma sa’ad da na dube shi da kyau da safe, sai na ga ashe ba ɗan da na haifa ba ne.” Amma ɗaya matar ta ce, “A’a! Mai rai ɗin ne ɗana; mataccen naki ne.” Amma ta farin ta nace, “A’a! Mataccen ne naki; mai ran ne nawa.” A haka suka yi ta gardama a gaban sarki. Sarki ya ce, “Wannan ta ce, ‘Ɗana ne a raye, naki ne matacce,’ yayinda ɗayan tana cewa, ‘A’a! Ɗanki ne mataccen, nawa ne a raye.’ ” Sai sarki ya ce, “Kawo mini takobi.” Sai aka kawo takobi wa sarki. Ya ba da umarni ya ce, “Yanka yaron nan mai rai, gida biyu, kowacce ta ɗauki rabi.” Ainihin mamar ɗan da yake a raye ta cika da tausayi saboda ɗanta, sai ta ce wa sarki, “Ina roƙonka, ranka yă daɗe, kada ka kashe yaron! Ka ba ta kawai!” Amma ɗayan matar ta ce, “Kada a ba kowa daga cikinmu ɗan da rai, a ci gaba a raba shi!” Sai sarki ya zartar da hukuncinsa ya ce, “A ba da jariri mai ran ga mata ta fari. Kada a kashe shi; ita ce ainihin mahaifiyarsa.” Sa’ad da dukan Isra’ila suka ji hukuncin da sarki ya zartar, suka girmama sarki sosai, domin sun gane cewa Allah ya ba shi hikimar yin shari’ar adalci. Sai Sarki Solomon ya yi mulki a bisa dukan Isra’ila. Waɗannan su ne manyan shugabanninsa. Azariya ɗan Zadok shi ne firist; Elihoref da Ahiya, ’ya’yan Shisha maza, su ne marubuta. Yehoshafat ɗan Ahilud, shi ne mai lura da takardu. Benahiya ɗan Yehohiyada, shi ne shugaban mayaƙa. Zadok da Abiyatar, su ne firistoci. Azariya ɗan Natan, shi ne mai lura da shugabannin yanki. Zabud ɗan Natan, shi ne firist da kuma mai wa sarki shawara. Ahishar, shi ne sarkin fada. Adoniram ɗan Abda, shi ne mai lura da aikin gandu. Solomon yana da gwamnoni yankuna goma sha biyu a bisa dukan Isra’ila, waɗanda suke tanaji abinci domin sarki da kuma gidan sarauta. Kowanne yakan tanada abinci na wata ɗaya a shekara. Ga sunayensu, Ben-Hur, shi ne a ƙasar tudun Efraim; Ben-Deker, shi ne a Makaz, Sha’albim, Bet-Shemesh da Elon Bet-Hanan; Ben-Hesed, shi ne a Arubbot (Soko da dukan ƙasar Hefer); Ben-Abinadab, shi ne a Nafot Dor (ya auri Tafat ’yar Solomon); Ba’ana ɗan Ahilud, shi ne a Ta’anak da Megiddo, da kuma dukan Bet-Sheyan biye da Zaretan ƙasa da Yezireyel, daga Bet-Sheyan zuwa Abel-Mehola a ƙetaren Yokmeyam; Ben-Geber, shi ne a Ramot Gileyad (Mazaunan Yayir ɗan Manasse a Gileyad suna a ƙarƙashinsa, haka ma yankin Argob a Bashan tare da manyan biranen sittin masu katanga da suke da ƙyamare na tagulla); Ahinadab ɗan Iddo, shi ne a Mahanayim; Ahimawaz, shi ne a Naftali (ya auri Basemat ’yar Solomon); Ba’ana ɗan Hushai, shi ne a Asher da Bayelot; Yehoshafat ɗan Faruwa, shi ne a Issakar; Shimeyi ɗan Ela, shi ne a Benyamin; Geber ɗan Uri, shi ne a Gileyad (ƙasar Sihon sarkin Amoriyawa da kuma Og sarkin Bashan). Shi ne kaɗai gwamna a bisa yankin. Mutanen Yahuda da na Isra’ila sun yi yawa sai ka ce yashi a bakin teku. Suka ci, suka sha, suka kuma yi farin ciki. Solomon kuwa ya yi mulki a bisa dukan masarautai daga Kogi zuwa ƙasar Filistiyawa, har zuwa iyakar Masar. Waɗannan ƙasashe sun yi ta kawo haraji, suka kuma zama bayin Solomon dukan kwanakin ransa. Tanajin Solomon na kowace rana su ne, garwa talatin na garin abinci, shanun da aka yi kiwo a gida guda goma, shanu ashirin da suka ƙoshi daga kiwo, tumaki da awaki ɗari; ban da ƙishimai, bareyi, batsiyoyi, da kaji masu ƙiba. Gama ya yi mulki a bisa dukan masarautai yamma da Kogi, daga Tifsa zuwa Gaza, aka kuwa sami zaman lafiya a kowane gefe. A kwanakin da Solomon yake raye, Yahuda da Isra’ila, daga Dan zuwa Beyersheba, sun zauna lafiya, kowane mutum ya zauna a ƙarƙashin itacen inabi da na ɓaurensa. Solomon yana da rumfunan dawakai masu jan kekunan yaƙi, dubu huɗu, da kuma dawakai dubu goma sha biyu Shugabannin yankuna, kowanne a watansa yakan yi tanajin abinci domin Sarki Solomon da kuma duk wanda ya zo teburin sarki. Sun tabbatar ba a rasa kome ba. Kowa a cikinsu, bisa ga lokacin da aka ba shi, yakan kai hatsin sha’ir da ciyawa domin dawakan-kekunan yaƙi, da sauran dawakai a inda aka ajiye su. Allah ya ba Solomon hikima da hangen nesa mai girma, da kuma fāɗin fahimta marar iyaka, kamar yashi a bakin teku. Hikimar Solomon ta fi hikimar mutanen Gabas, ta kuma fi dukan hikimar Masar girma. Ya fi kowane mutum hikima, har da Etan dangin Ezra ma. Yana da hikima fiye da Heman, Kalkol da Darda, ’ya’yan Mahol maza. Sunansa ya bazu ko’ina a ƙasashen da suke kewaye. Ya yi karin magana dubu uku. Waƙoƙinsa kuwa sun kai dubu ɗaya da biyar. Ya yi magana a kan rayuwar itatuwa, daga al’ul na Lebanon zuwa hizzob da yake girma a bangaye. Ya kuma yi koyarwa game da dabbobi, da tsuntsaye, da abubuwa masu rarrafe, da kuma kifi. Mutane suka yi ta zuwa daga ƙasashe dabam-dabam don su ji hikimar Solomon. Sarakuna daga ko’ina a duniya, sun ji labarin hikimarsa, suka kuma aika da mutane don su ji shi. Sa’ad da Hiram sarkin Taya ya ji an shafe Solomon sarki yă gāji mahaifinsa Dawuda, sai ya aika da jakadunsa zuwa wurin Solomon, gama shi da Dawuda abokai ne sosai dukan kwanakinsa. Solomon ya mayar da wannan saƙo ga Hiram ya ce, “Ka san cewa saboda yaƙe-yaƙen da abokan gāba suka yi da mahaifina a kowane gefe, ya sa bai iya gina haikali domin Sunan Ubangiji Allahnsa ba, sai da Ubangiji ya sa abokan gābansa a ƙarƙashin ƙafafunsa. Amma yanzu Ubangiji Allahna ya ba ni hutu a kowane gefe, babu kuma gāba ko masifa. Ina niyya in gina haikali domin Sunan Ubangiji Allahna, yadda Ubangiji ya faɗa wa mahaifina Dawuda, sa’ad da ya ce, ‘Ɗanka wanda zai gāje ka, shi zai gina haikali domin Sunana.’ “Don haka, ka ba da umarni a yanka mini itatuwan al’ul na ƙasar Lebanon. Ma’aikatana za su haɗa hannu da ma’aikatanka, ni kuwa zan biya ka albashin ma’aikatanka kamar yadda ka faɗa. Gama ka san cewa babu wani a cikinmu da ya iya yanka itacen katako kamar Sidoniyawa.” Da Hiram ya ji saƙon Solomon, sai ya ji daɗi ƙwarai, ya kuma ce, “Yabo ga Ubangiji a yau, gama ya ba wa Dawuda ɗa mai hikima yă yi mulki a bisa wannan al’umma mai girma.” Sai Hiram ya aike wa Solomon da kalmomin nan, “Na sami saƙon da ka aika mini, zan kuma yi duk abin da kake so ta wurin tanada katakan al’ul da na fir. Ma’aikatana za su gangara da su daga Lebanon zuwa bakin teku. Zan sa a ɗaɗɗaura su su bi ruwan teku daga Lebanon zuwa bakin Bahar Rum da za ka nuna mini. A can zan kunce maka su, sa’an nan ka kwashe. Kai kuma za ka biya bukatata ta wurin tanadin abinci wa gidana.” A haka Hiram ya ci gaba da aika wa Solomon al’ul da kuma fir da yake bukata. Solomon kuma ya ba wa Hiram mudu gari dubu ashirin na alkama a matsayin abinci domin gidansa, ya ƙara da garwa dubu ashirin na tataccen man zaitun. Solomon ya ci gaba da yin haka ga Hiram, shekara-shekara. Ubangiji ya ba wa Solomon hikima, kamar yadda ya yi masa alkawari. Dangantakar zaman lafiya ta kasance tsakanin Hiram da Solomon, su biyun suka yi yarjejjeniya. Sarki Solomon ya ɗebi ma’aikata daga dukan Isra’ila, su dubu talatin. Ya riƙa aika su dubu goma-goma zuwa Lebanon kowane wata, saboda su yi wata ɗaya a Lebanon, watanni biyu kuma a gida. Adoniram ne ya lura da aikin gandun. Solomon ya kasance da ’yan ɗauko guda dubu saba’in da masu yankan duwatsu guda dubu tamanin a cikin tuddai, ya kuma kasance da shugabanni dubu uku da ɗari uku waɗanda suke lura da aikin, su ne kuma suke bi da ma’aikatan. Bisa ga umarnin sarki sai suka cire manyan duwatsu masu kyau don a tanada tushen duwatsun da aka gyara domin haikalin daga wurin haƙar duwatsun. Gwanayen Solomon da na Hiram da kuma mutanen Gebal, su suka yanka, suka kuma shirya katako da dutse don ginin haikali. A shekara ta ɗari huɗu da tamani bayan fitowar Isra’ilawa daga Masar, a shekara ta huɗu ta mulkin Solomon a bisa Isra’ila, a watan Zif, wata na biyu, Solomon ya fara gina haikalin Ubangiji. Haikalin da Sarki Solomon ya gina wa Ubangiji, tsawonsa kamu sittin, fāɗinsa kamu ashirin, tsayinsa kuma kamu talatin ne. Shirayin da yake a gaban ainihin zauren haikalin, ya ƙara faɗin haikalin da kamu ashirin, ya kuma nausa daga gaban haikalin kamu goma. Ya yi tagogin da suka fi fāɗi daga ciki fiye da waje a haikalin. A jikin bangayen babban zaure da kuma cikin wuri mai tsarki, ya gina ɗakuna kewaye da ginin, inda akwai ɗakuna a gefe. Fāɗin ɗakunan ƙasa, kamu biyar ne, fāɗin ɗakunan tsakiya, kamu shida ne, fāɗin ɗakunan hawa na uku kuwa, kamu bakwai ne. Ya yi bangaye kewaye a waje da haikalin don kada a sa wani abu a bangayen haikali. A yin ginin haikalin, duwatsun da aka fafe ne kaɗai daga wurin fafe duwatsu aka yi amfani da su, ba a ji karar guduma ko gizago, ko wani abin da aka yi da ƙarfe a wurin ginin haikali yayinda ake gina shi ba. Ƙofar zuwa ɗakunan ƙasa tana gefen kudu na haikalin; akwai matakai da suka bi zuwa hawa na tsakiya, daga can kuma matakan sun wuce zuwa hawa na uku. A haka ya gina haikalin ya kuma gama shi, ya jinƙe shi da manyan katakai da kuma katakan al’ul. Ya kuma gina ɗakunan gefe duka a gefen haikalin. Tsayin kowanne, kamu biyar ne, aka haɗa su da haikalin da manyan katakan al’ul. Sai maganar Ubangiji ta zo wa Solomon ta ce, “Game da wannan haikalin da kake ginawa, in ka bi ƙa’idodina, ka cika farillaina, ka kiyaye dukan umarnaina, ka kuma yi biyayya da su, zan cika alkawarin da na yi wa mahaifinka Dawuda ta wurinka. Zan kuma zauna a cikin Isra’ilawa, ba kuwa zan taɓa rabuwa da su ba.” Saboda haka Solomon ya gina haikalin ya kuma gama shi. Ya rufe bangon ciki da katakan itacen al’ul tun daga ƙasa har zuwa sama, ya kuma rufe daɓen da katakan itacen fir. Ya gina Wuri Mafi Tsarki na can ciki, ya gina shi a can ƙuryar haikalin. Tsayinsa kamu ashirin ne, an manne masa katakan itacen al’ul tun daga ƙasa har zuwa sama. Tsawon babban zaure a gaban wannan ɗaki, kamu arba’in ne. An yi wa katakan itacen al’ul na cikin haikalin zāne mai fasalin gora da na buɗaɗɗun furanni. An rufe bangon ciki duka da itacen al’ul, har ba a ganin duwatsun ginin. Ya shirya wuri mai tsarki na ciki can cikin haikali don yă sa akwatin alkawarin Ubangiji a can. Tsawon wuri mai tsarki na ciki kamu ashirin, fāɗin kamu ashirin, tsayin kuma kamu ashirin. Ya dalaye cikin da zinariya zalla, ya kuma dalaye bagade al’ul ɗin. Solomon ya rufe cikin haikalin da zinariya zalla, ya kuma gifta sarƙoƙin zinariya a gaban wuri mai tsarki na ciki, wanda aka dalaye da zinariya. Haka ya dalaye dukan cikin da zinariya. Ya kuma dalaye bagade na cikin wuri mai tsarki da zinariya. A wuri mai tsarki na can ciki, ya yi kerubobi biyu na itacen zaitun, kowanne mai tsayi kamu goma. Fiffike ɗaya na kerub na fari tsawonsa kamu biyar ne, ɗayan fiffike kuma kamu biyar, kamu goma daga ƙarshen fiffike zuwa ƙarshen fiffike. Kerub na biyun shi ma kamu goma ne, gama kerubobi biyun sun yi kama da juna a girma da kuma siffa. Tsayin kowane kerub kamu goma ne. Ya ajiye kerubobin a ɗaki na can cikin haikalin, da fikafikansu a buɗe. Fiffiken kerub ɗaya ya taɓa bango guda, yayinda fiffiken ɗayan ya taɓa ɗayan bangon, kuma fikafikansu sun taɓa juna a tsakiyar ɗakin. Ya dalaye kerubobin da zinariya. A bangaye kewaye da haikali, a ɗakuna ciki da waje, ya zāzzāna kerubobi, itatuwan dabino, da furanni buɗaɗɗu. Ya kuma rufe ƙasan ɗakuna ciki da wajen haikali da zinariya. Don ƙofar shiga wuri mai tsarki na ciki kuwa, ya yi ƙofofin katakon zaitun da madogarai masu gefe biyar. A kan ƙofofin katakan zaitun kuwa ya zāzzāna kerubobi, itatuwa dabino, da furanni buɗaɗɗu, ya kuma dalaye kerubobin, da kuma itatuwan dabinon da zinariya. Haka ma ya yi madogarai masu gefe huɗu na katakon zaitun don ƙofar shiga zuwa babban zaure. Ya yi ƙofofi biyu na itacen fir, kowanne yana da shafi biyu da suke juyewa a maɗaurai. Ya zāzzāna kerubobi, itatuwan dabino, da kuma furanni buɗaɗɗu a kansu, ya kuma dalaye su da zinariyar da aka buga daidai a kan sassaƙa. Ya kuma gina filin ciki da sassaƙaƙƙun duwatsu, jeri uku, da jeri ɗaya na katakan itacen al’ul. An kafa tushen haikalin Ubangiji a shekara ta huɗu, a watan Zif. A shekara ta goma sha ɗaya, a watan Bul, wata na takwas ke nan, aka gama haikalin daidai yadda aka tsara shi bisa ga fasalinsa. Solomon ya ɗauki shekara bakwai yana ginin haikalin. Ya ɗauki Solomon shekaru goma sha uku kafin yă gama gina fadarsa. Ya gina fadarsa mai suna Kurmin Lebanon, tsawonsa kamu ɗari, fāɗinsa kamu hamsin, tsayinsa kuma kamu talatin, a bisa jeri huɗu na ginshiƙan itacen al’ul, aka shimfiɗa katakan itacen al’ul a bisa ginshiƙan. Aka yi rufin da al’ul bisa ginshiƙan da suke bisa ginshiƙai arba’in da biyar, goma sha biya a kowane jeri. Aka kuma yi tagogi masu sandunan ƙarfe, jeri uku, kowace taga tana ɗaura da ’yar’uwarta, har jeri uku. Dukan ƙofofin da madogaransu murabba’i ne, taga kuma tana ɗaura da ’yar’uwarta har jeri uku. Ya yi babban zaure mai ginshiƙai, tsawonsa kamu hamsin, fāɗinsa kuwa kamu talatin. A gabansa kuwa akwai shirayi, kuma a gaban wannan shirayi akwai ginshiƙai da kuma rufin da yake a shimfiɗe. Ya kuma gina shirayi ta sarauta, da ya kira Zauren Adalci, inda zai riƙa yin shari’a, ya kuma rufe dukan daɓensa da itacen al’ul daga ƙasa har sama. A fadar da zai zauna kuwa, wadda aka gina a can baya, ya yi ta da irin fasali guda. Solomon ya kuma yi wata fada kamar wannan zaure domin ’yar Fir’auna, wadda ya auro. Dukan waɗannan gine-gine, daga waje zuwa babban fili, da kuma daga tushen zuwa rufin, an yi su da duwatsun da aka yanka, aka kuma gyara da zarto a fuskokinsu na ciki da waje. Aka kafa tushen da manyan duwatsu masu kyau, tsayin waɗansunsu ya kai kamu goma, waɗansu kuma kamu takwas. A can bisa akwai duwatsu masu tsada da aka yayyanka bisa ga ma’auni, da kuma ginshiƙan al’ul. An kewaye babban filin da katanga da jerin uku-uku na duwatsun da aka gyara, da kuma jeri guda na gyararren al’ul, kamar yadda aka yi na filin cikin haikalin Ubangiji da shirayinsa. Sarki Solomon ya aika zuwa Taya aka kuma kawo Huram, wanda mahaifiyarsa gwauruwa ce daga kabilar Naftali, wanda kuma mahaifinsa mutumin Taya ne, shi Huram, gwani ne a aikin tagulla. Huram gwani ne sosai kuma ya saba da yin kowane irin aikin tagulla. Sai ya zo wurin Sarki Solomon ya kuma yi dukan aikin da aka sa shi. Ya yi ginshiƙan tagulla, kowanne tsayinsa kamu goma sha takwas, ya kuma yi guru mai kamu goma sha biyu, kewaye da shi. Ya yi dajiyoyi biyu na zubin tagulla don yă sa a bisa ginshiƙai; kowace dajiya tsayinta kamu biyar ne. Aka yi yanar tuƙaƙƙun sarƙoƙi aka ɗaura dajiyoyin a bisa ginshiƙai guda bakwai don kowace dajiya. Ya yi rumman jeri biyu kewaye da kowace yanar don yă yi adon dajiyoyin a bisa ginshiƙan. Haka kuma ya yi wa ɗaya dajiyar. Dajiyoyin da suke a bisa ginshiƙan a shirayi suna da fasalin furen bi-rana, tsayinsu kamu huɗu-huɗu ne. A inda kan ginshiƙin ya buɗu kamar kwano, sama da zāne-zānen sarƙar, an yi zāne-zānen rumman wajen ɗari biyu, layi-layi kewaye da kawunan ginshiƙan nan. Ya ta da ginshiƙai a shirayin haikali. Ya ba wa ginshiƙi na wajen kudu sunan Yakin, na wajen arewa kuma ya kira Bowaz. Dajiyoyin da suke a bisa suna da fasalin bi-rana ne. Ta haka aka gama aiki a kan ginshiƙan. Sai Huram ya yi wani ƙaton kwano na ƙarfen tagulla, da ya kira Teku. Zurfin kwanon nan kamu bakwai da rabi, fāɗinsa kamu goma sha biyar, da’irarsa kuma kamu talatin ne. A kewayen bakin ƙaton kwanon akwai layi biyu na siffofin goran ƙarfen tagulla, akwai gora shida cikin kowane ƙafa. An yi zubinsu haɗe da kwanon nan da kira Teku. Kwanon ya tsaya a kan siffofin bijimai goma sha biyu, uku suna fuskantar arewa, uku suna fuskantar yamma, uku suna fuskantar kudu, sa’an nan uku suna fuskantar gabas. Kwanon da ya kira Teku ya zauna a kansu, gindin siffofin bijimai goma sha biyun nan suna wajen tsakiya. Kaurin kwanon ya kai tafin hannu, kuma da’iransa ya yi kamar da’iran kwaf, kamar bi-ranar da ta buɗe. Wannan kwanon da aka kira Teku yakan ci garwa dubu biyu. Ya kuma yi dakalai guda goma na tagulla da ake iya matsar da su; kowane tsawonsa kamu huɗu ne, fāɗinsa kamu huɗu, tsayinsa kuma kamu uku. Ga yadda aka yi dakalan, dakalan suna da ɓangarori haɗe da mahaɗai. A bisa sassan tsakanin mahaɗan, akwai siffofin zakoki, bijimai da kuma kerubobi, suna a kan mahaɗan su ma. A sama da kuma ƙasan siffofin zakokin da na bijiman kuwa akwai hotunan furanni. Kowane dakali yana da ƙafa huɗu na tagulla kamar na keken yaƙi, da sandunan tagulla don sa kwanon nan da aka kira Teku. A kusurwoyin akwai abubuwan zubi don riƙe kwanon. An zāna furanni a kowane gefensu. A dakalin daga ciki, akwai bakin da yake da’ira, mai zurfi kamun guda. Bakin da’irar ne, yana da zāne-zānensa da ya kai kamu ɗaya da rabi. Kusa da bakin akwai zāne-zāne. Sassan dakalin murabba’i ne, ba da’ira ba ne. Ƙafafu huɗun suna a ƙarƙashin ɓangarorin, aka kuma haɗa gindin ƙafafun keken da dakalin. Tsayin kowace ƙafa kamu ɗaya da rabi ne. An yi ƙafafun kamar ƙafafun keken yaƙi ne; gindin, da’irar, gyaffan da kuma cibiyar duk an yi su da ƙarfe ne. Kowane dakali yana da hannuwa huɗu, ɗaya a kowane gefe, da yake nausawa daga dakalin. A bisa dakalin akwai da’irar da ta yi kamar gammo mai zurfi kamar rabin kamu. Abubuwan da suke riƙewa da kuma sassan, an haɗa su da bisa dakalin. Ya zāna siffofin kerubobi, zakoki da itatuwan dabino a saman abubuwan riƙewa da kuma a kan ɓangarorin, a kowane abin da ya ga akwai ɗan fili, ya zāna furanni. Haka ya yi dakalai goma. Duk an yi zubinsu iri ɗaya ne, girmansu da fasalinsu kuma iri ɗaya. Sa’an nan ya yi kwanoni goma na tagulla, kowane yana cin garwa arba’in, kuma kamu huɗu daga wannan zuwa wancan, kowane dakali yana da daro ɗaya. Ya sa dakalai biyar a gefen kudu na haikali, biyar kuma a arewa. Ya sa kwanon a gefen kudu, a gefen kudu maso gabas na haikalin. Ya kuma yi kwanoni da manyan cokula da kuma kwanonin yayyafawa. Ta haka Huram ya gama dukan aikin da ya yi wa Sarki Solomon a haikalin Ubangiji. Ya yi ginshiƙai biyun; dajiyoyi biyu masu fasalin kwano a kan ginshiƙan; ya yi yanar kashi biyu wa dajiyoyi masu fasalin kwano guda biyu a kan ginshiƙai; ya yi rumman guda ɗari huɗu na sashi yanar biyun (jeri biyu na rumman don kowace yanar, yana adon dajiyoyi masu fasalin kwano a kan ginshiƙai); ya yi dakalai goma da kwanoninsu goma; ya yi kwanon da ya kira Teku, da bijimai goma sha biyu a ƙarƙashinsa; ya yi tukwane, manyan cokula da kwanonin yayyafawa. Dukan waɗannan abubuwan da Huram ya yi wa Sarki Solomon saboda haikalin Ubangiji, an dalaye su da tagulla. Sarki ya sa aka yi zubi a abin yin tubalin laka a filin Urdun, tsakanin Sukkot da Zaretan. Solomon ya bar dukan waɗannan abubuwa ba tare da an auna su ba, domin sun yi yawa sosai; ba a san nauyin tagullar ba. Solomon ya kuma yi dukan kayayyakin da suke cikin haikalin Ubangiji. Ya yi bagaden zinariya; teburin zinariya, inda ake ajiye burodin Kasancewa; ya yi alkukai na zinariya zalla (Biyar a dama, biyar kuma a hagu, a gaban wuri mai tsarki na can cikin); ya yi zāne-zānen furannin zinariya da fitilu da kuma arautaki; ya yi kwanonin zinariya zalla, hantsuka, kwanonin yayyafawa, kwanoni, da kuma farantan wuta; ya yi wurin ajiye fitila na zinariya domin ƙofofi na ɗakin can ciki-ciki, da na ƙofofin Wuri Mafi Tsarki, da kuma domin ƙofofin babban zauren haikali. Sa’ad da aka gama aikin da Sarki Solomon sa a yi domin haikalin Ubangiji, sai ya kawo kayayyakin da mahaifinsa Dawuda ya keɓe, azurfa da zinariya da kayayyaki, ya sa su a ma’ajin haikalin Ubangiji. Sai Sarki Solomon ya tattara dattawan Urushalima a gabansa, da dukan shugabannin kabilu, da shugabannin iyalan Isra’ilawa, domin su kawo akwatin alkawarin Ubangiji daga Sihiyona, Birnin Dawuda. Dukan mutanen Isra’ila suka tattaru a gaban Sarki Solomon a lokacin biki, a watan Etanim, wato, wata na bakwai. Sa’ad da dukan dattawan Isra’ila suka iso, sai firistoci suka ɗauki akwatin alkawarin, suka haura da akwatin alkawarin Ubangiji da kuma Tentin Sujada, da dukan kayayyaki masu tsarkin da suke cikinsa. Firistoci da Lawiyawa suka ɗauko su, sai Sarki Solomon da dukan taron Isra’ila da suka tattaru kewaye da shi a gaban akwatin alkawari, suka yi ta miƙa hadayar tumaki da bijimai masu yawa da ba a iya lissaftawa, ko ƙirgawa. Sa’an nan firistoci suka kawo akwatin alkawarin Ubangiji inda aka shirya masa, can ciki cikin haikali, a Wuri Mafi Tsarki, aka kuma sa shi a ƙarƙashin fikafikan kerubobin. Kerubobin sun buɗe fikafikansu a bisa wurin da akwatin alkawarin yake, suka inuwartar da akwatin alkawarin da sandunan ɗaukansa. Waɗannan sandunan sun yi tsawo har ana iya ganin bakinsu daga Wuri Mai Tsarki a gaban wuri mai tsarki na can ciki, amma ba a iya ganinsu daga waje na Wuri Mai Tsarki ba. Suna nan kuwa a can har wa yau. Ba kome a cikin akwatin alkawarin, sai dai alluna na dutse guda biyu waɗanda Musa ya ajiye a ciki tun a Horeb, inda Ubangiji ya yi alkawari da Isra’ilawa bayan sun fito Masar. Sa’ad da firistoci suka janye daga Wuri Mai Tsarki, sai girgije ya cika haikalin Ubangiji. Firistocin kuwa ba su iya yin hidimarsu ba saboda girgijen, gama ɗaukakar Ubangiji ta cika haikalinsa. Sai Solomon ya ce, “ Ubangiji ya ce zai zauna a gizagizai masu duhu; ga shi na gina haikali mai daraja dominka, inda za ka zauna har abada.” Yayinda dukan taron Isra’ila suke tsattsaye a can, sai sarki ya juya ya albarkace su. Sa’an nan ya ce, “Ku yabi Ubangiji, Allah na Isra’ila, wanda da hannunsa ya cika abin da ya yi alkawari da bakinsa ga mahaifina Dawuda. Gama ya ce, ‘Tun ran da na fitar da mutanena Isra’ila daga Masar, ban zaɓi wani birni a cikin wata kabilar Isra’ila a gina haikali domin Sunana yă kasance a can ba, amma na zaɓi Dawuda yă yi mulkin mutanena Isra’ila.’ “Mahaifina Dawuda ya yi niyya a cikin zuciyarsa yă gina haikali saboda Sunan Ubangiji, Allah na Isra’ila. Amma Ubangiji ya ce wa mahaifina Dawuda, ‘Saboda yana a zuciyarka ka gina haikali domin Sunana, ka yi daidai da ka yi niyyar wannan a zuciyarka. Duk da haka, ba kai ba ne za ka gina haikali, amma ɗanka, wanda yake namanka da jininka, shi ne wanda zai gina haikali domin Sunana.’ “ Ubangiji ya kiyaye alkawarin da ya yi. Na gāje Dawuda mahaifina, yanzu kuma ga shi na zauna a kujerar sarautar Isra’ila, kamar dai yadda Ubangiji ya yi alkawari, na kuma gina haikali domin Sunan Ubangiji, Allah na Isra’ila. Na tanada wuri saboda akwatin alkawari, akwatin da ya ƙunshi alkawarin da Ubangiji ya yi da kakanninmu sa’ad da ya fitar da su daga Masar.” Sai Solomon ya tsaya a gaban bagaden Ubangiji, a gaban dukan taron Isra’ila, ya ɗaga hannuwansa sama, ya ce, “Ya Ubangiji, Allah na Isra’ila, babu Allah kamar ka a sama can bisa, ko a ƙasa can ƙarƙashi, kai da kake kiyaye alkawarinka na ƙauna ga bayinka waɗanda suke cin gaba a hanyarka da dukan zuciyarsu. Ka kiyaye alkawarinka da ka yi wa bawanka Dawuda mahaifina. Da bakinka ka yi alkawari, da hannunka kuma ka cika shi, yadda yake a yau. “Yanzu, ya Ubangiji, Allah na Isra’ila, bari ka cika wa bawanka Dawuda mahaifina alkawaran da ka yi masa sa’ad da ka ce, ‘Ba za ka taɓa rasa wani da zai zauna a gabana a kan kujerar sarautar Isra’ila ba, in kawai ’ya’yanka maza sun yi hankali cikin dukan abubuwan da suke yi, don su yi tafiya a gabana kamar yadda ka yi.’ Yanzu fa, ya Allah na Isra’ila, bari maganarka da ka yi wa bawanka Dawuda mahaifina tă cika. “Amma anya, Allah, za ka zauna a duniya? Sammai, har ma da saman sammai ba za tă iya riƙe ka ba, balle wannan haikalin da na gina! Duk da haka ka ji addu’ar bawanka da kuma roƙonsa don jinƙai, ya Ubangiji Allahna. Ka ji kuka da addu’ar da bawanka yake yi a gabanka a wannan rana. Bari idanunka su buɗe, su fuskanci wannan haikali dare da rana, wannan wurin da ka ce, ‘Sunana zai kasance a can,’ saboda ka ji addu’ar bawanka in yana fuskantar wannan wuri. Ka ji roƙon bawanka da kuma na mutanenka Isra’ila sa’ad da suka yi addu’a, suka fuskanci wannan wuri. Ka ji daga sama, mazauninka, kuma sa’ad da ka ji, ka gafarta. “Sa’ad da mutum ya yi abin da ba daidai ba ga maƙwabcinsa, an kuma bukace shi yă yi rantsuwa, sai ya zo ya rantse a gaban bagade a cikin haikalin nan, sai ka ji daga sama, ka kuma yi wani abu. Ka shari’anta tsakanin bayinka, ka hukunta mai laifi, ka mai da laifinsa a kansa, mai gaskiya kuma ka nuna shi marar laifi ne bisa ga gaskiyarsa. “Sa’ad da abokan gāba suka ci mutanenka Isra’ila a yaƙi saboda sun yi maka zunubi, sa’ad da kuma suka dawo gare ka don su furta sunanka, suna addu’a suna roƙo gare ka a wannan haikali, ka ji daga sama, ka gafarta zunubin mutanenka, ka kuma dawo da su ƙasar da ka ba wa kakanninsu. “Sa’ad da sammai sun kulle, babu kuma ruwan sama domin mutane sun yi maka zunubi, sa’ad da suka yi addu’a suna fuskantar wannan wuri, suka kuma furta sunanka, suka juye daga zunubinsu domin ka hore su, ka ji daga sama, ka kuma gafarta zunubin bayinka, mutanenka Isra’ila. Ka koya musu hanyar da ta dace ta rayuwa, ka kuma aika da ruwan sama a ƙasar da ka ba wa mutanenka gādo. “Sa’ad da yunwa ko annoba ta fāɗo a ƙasar, ko burtuntuna, ko fumfuna, ko fāri, ko tsutsa, ko kuwa abokan gāba sun yi musu kwanto, a wani daga cikin biranensu, duk wata cuta, ko ciwon da ya zo, in suka yi addu’a ko roƙo ta wurin wani daga cikin mutanenka Isra’ila, kowa ya san wahalar zuciyarsa, ya kuma buɗe hannuwansa yana fuskantar wannan haikali, sai ka ji daga sama, mazauninka. Ka gafarta, ka kuma yi wani abu. Ka yi da kowane mutum bisa ga dukan abin da ya yi, tun da yake ka san zuciyarsa (gama kai kaɗai ka san zukatan dukan mutane), saboda su ji tsoronka a kowane lokacin da suke zaune a ƙasar da ka ba wa kakanninmu. “Game da baƙo kuwa wanda shi ba na mutanenka Isra’ila ba, amma ya zo daga ƙasa mai nisa saboda sunanka, gama mutane za su ji game da girman sunanka, da ƙarfin hannunka, da kuma hannunka mai iko, sa’ad da ya zo, ya yi addu’a yana fuskantar wannan haikali, ka ji daga sama, mazauninka, ka kuma yi dukan abin da baƙon ya tambaye ka, saboda dukan mutanen duniya su san sunanka, su kuma ji tsoronka, kamar yadda mutanenka Isra’ila suke yi, bari kuma su san cewa wannan gidan da na gina, ya amsa Sunanka. “Sa’ad da mutanenka suka tafi yaƙi da abokan gābansu, a duk inda ka aike su, sa’ad da kuma suka yi addu’a ga Ubangiji suna fuskantar birnin da ka zaɓa, da kuma haikalin da na gina domin Sunanka, ka ji addu’arsu da roƙonsu daga sama, ka kuma biya musu bukatansu. “Sa’ad da suka yi maka zunubi, gama babu wanda ba ya zunubi, ka kuwa yi fushi da su, ka kuma ba da su ga abokin gāba, wanda ya kwashe su kamammu zuwa ƙasarsa, nesa ko kusa; in suka canja zuciyarsu a ƙasar da aka riƙe su kamammu, suka tuba, suka kuma roƙe ka a ƙasar waɗanda suka ci su da yaƙi, suka ce, ‘Mun yi zunubi, mun yi abin da ba daidai ba, mun yi mugunta’; in sun juye gare ka da dukan zuciyarsu, da dukan ransu a ƙasar abokan gābansu waɗanda suka kwashe kamammu, suka yi addu’a gare ka, suka fuskanci wajen ƙasar da ka ba wa kakanninsu, waje birnin da ka zaɓa, da kuma haikalin da na gina domin Sunanka; sai ka ji daga sama, mazauninka, ka ji addu’a da roƙonsu, ka kuma biya musu bukatansu. Ka gafarta wa mutanenka, waɗanda suka yi maka zunubi; ka gafarta dukan laifofin da suka yi maka, ka kuma sa waɗanda suka ci su a yaƙi su ji tausayinsu. Gama su mutanenka ne, abin gādonka, waɗanda ka fitar daga Masar, daga tanderu mai narken ƙarfe. “Bari idanunka su buɗe ga roƙon bawanka, ga roƙon mutanenka Isra’ila, bari kuma ka saurare su sa’ad da suka yi kuka gare ka. Gama ka ware su daga dukan al’umman duniya su zama abin gādonka, kamar yadda aka furta ta wurin bawanka Musa sa’ad da kai, ya Ubangiji Mai Iko Duka ka fitar da kakanninmu daga Masar.” Da Solomon ya gama dukan waɗannan addu’o’i da roƙe-roƙe ga Ubangiji, sai ya tashi daga gaban bagaden Ubangiji, inda ya durƙusa da hannuwansa a buɗe waje sama. Ya tashi ya kuma albarkaci dukan taron Isra’ila da babbar murya, yana cewa, “Yabo ya tabbata ga Ubangiji, wanda ya ba wa mutanensa hutu kamar dai yadda ya yi alkawari. Babu magana guda da ta kāsa cika cikin dukan alkawaransa masu kyau da ya yi ta wurin bawansa Musa. Bari Ubangiji Allah yă kasance tare da mu kamar yadda ya kasance da kakanninmu; kada yă taɓa rabu da mu, ko yă yashe mu. Bari yă juye zukatanmu gare shi, don mu yi tafiya a cikin dukan hanyoyinsa, mu kuma kiyaye umarnansa, ƙa’idodinsa, da kuma farillan da ya ba wa kakanninmu. Bari kuma waɗannan kalmomina, waɗanda na yi addu’a a gaban Ubangiji, su yi kusa da Ubangiji Allahnmu, dare da rana, don yă biya bukatan bawansa da na mutanensa Isra’ila, bisa ga bukatan kowa, saboda dukan mutanen duniya su san cewa Ubangiji, shi ne Allah, babu kuma wani. Amma dole ku miƙa zukatanku ga Ubangiji Allahnmu, don ku rayu, ta wurin bin ƙa’idodinsa, ku kuma yi biyayya da umarnansa, kamar yadda kuke yi a wannan lokaci.” Sai sarki da dukan Isra’ila, suka miƙa hadayu a gaban Ubangiji. Solomon ya miƙa hadaya ta salama ga Ubangiji, shanu dubu ashirin da biyu, tumaki da awaki dubu ɗari da dubu ashirin. Ta haka sarki da dukan Isra’ilawa suka keɓe haikalin Ubangiji. A wannan rana sarki ya tsarkake sashe na tsakiyar fili a gaban haikalin Ubangiji, a can kuma ya miƙa hadaya ta ƙonawa, hadaya ta gari, da kitsen hadaya ta salama, gama bagaden tagulla a gaban Ubangiji ya yi ƙanƙanta sosai da za a miƙa hadayun ƙonawa, hadayun hatsi, da kuma kitsen hadayun salama. Ta haka Solomon da dukan Isra’ila, wato, babban taro, suka yi bikin a lokacin. Mutane suka zo, tun daga Lebo Hamat har zuwa Rafin Masar. Suka yi biki a gaban Ubangiji Allahnmu, kwana bakwai. Suka kuma ƙara kwana bakwai, kwanaki goma sha huɗu gaba ɗaya. A rana ta biye sai ya sallame mutane. Suka sa wa sarki albarka, sa’an nan suka watse zuwa gida, da farin ciki, da murna a zukatansu saboda kyawawan abubuwan da Ubangiji ya yi domin bawansa Dawuda, da kuma mutanensa Isra’ila. Sa’ad da Solomon ya gama ginin haikalin Ubangiji da kuma fadan sarki, ya kuma yi dukan abin da yake so yă yi, sai Ubangiji ya bayyana gare shi sau na biyu, kamar yadda ya bayyana masa a Gibeyon. Ubangiji ya ce masa, “Na ji addu’arka da kuma roƙon da ka yi a gabana; na tsarkake wannan haikali wanda ka gina, ta wurinsa Sunana zai kasance a can har abada. Idanuna da zuciyata kullum za su kasance a can. “Kai kuwa, in ka yi tafiya a gabana da mutunci a zuci da kuma gaskiya, kamar yadda Dawuda mahaifinka ya yi, ka yi dukan abin da na umarta, ka kuma yi biyayya da ƙa’idodina da kuma dokokina, zan kafa kujerar sarautarka a bisa Isra’ila har abada, kamar yadda na alkawarta wa Dawuda mahaifinka sa’ad da na ce, ‘Ba za ka taɓa rasa wani a kan kujerar sarautar Isra’ila ba.’ “Amma in kai, ko ’ya’yanka maza, suka juye daga gare ni, ba ku kuma kiyaye umarnai da ƙa’idodin da na ba ku ba, kuka yi gaba, kuka bauta wa waɗansu alloli, kuka kuma yi musu sujada, sai in yanke mutanen Isra’ila daga ƙasar da na ba su, in kuma ƙi wannan haikalin da na tsarkake domin Sunana. Isra’ila kuwa za tă zama abin gori da abin dariya a cikin dukan mutane. Wannan haikali zai zama tarin juji. Duk wanda ya wuce ta hanyan nan kuwa zai ji tausayi, yă kuma yi tsaki yana cewa, ‘Me ya sa Ubangiji ya yi haka ga wannan ƙasa da kuma wannan haikali?’ Mutane za su amsa su ce, ‘Saboda sun yashe Ubangiji Allahnsu, wanda ya fitar da su daga Masar, suka rungumi waɗansu alloli, suna yin musu sujada, suna bauta musu ne, ya sa Ubangiji ya kawo dukan masifan nan a kansu.’ ” A ƙarshen shekaru ashirin da Solomon ya ɗauka yana gina haikalin Ubangiji da fadan sarki, sai Sarki Solomon ya ba wa Hiram sarkin Taya garuruwa ashirin a yankin Galili, gama Hiram ya tanada masa da dukan katakai al’ul da na fir, da kuma zinariyar da ya bukaci domin aiki. Amma sa’ad da Hiram ya zo daga Taya don yă ga garuruwan da Solomon ya ba shi, sai bai ji daɗi ba. Sai ya ce, “Wanda irin garuruwa ke nan ka ba ni, ɗan’uwana?” Saboda haka ya kira su Ƙasar Kabul, sunan da suke da shi har wa yau. Hiram kuwa ya aika wa sarki talenti 120 na zinariya. Ga lissafin ma’aikatan gandun da Sarki Solomon ya ɗauka don ginin haikalin Ubangiji, da fadarsa, da madogaran gini, da katangar Urushalima, da kuma Hazor Megiddo da Gezer. (Fir’auna sarkin Masar ya kai wa Gezer hari, ya kuma ci ta da yaƙi. Ya sa mata wuta, ya kashe Kan’aniyawanta mazaunan wurin, ya kuma ba da ita a matsayin kyautar aure ga ’yarsa, matar Solomon. Solomon kuwa ya sāke gina Gezer.) Ya gina Bet-Horon ta Kwari, da Ba’alat, da Tadmor a hamada, na cikin ƙasarsa. Haka kuma ya gina dukan biranen ajiyarsa, da garuruwa domin kekunan yaƙinsa, da garuruwa domin dawakansa. Ya gina duk abin da ya so yă ginawa a Urushalima, da Lebanon, da kuma ko’ina a dukan yankin da ya yi mulki. Dukan Amoriyawa, da Hittiyawa, da Ferizziyawa, da Hiwiyawa da Yebusiyawan da suka ragu a ƙasar (waɗanda ba Isra’ilawa ba ne), wato, waɗanda suka ragu a ƙasar, waɗanda Isra’ilawa ba su iya hallakawa ba, su ne Solomon ya ɗauka su zama bayinsa don aikin gandu, kamar yadda yake har wa yau. Amma Solomon bai mai da Isra’ilawa bayi ba; su ne mayaƙansa, shugabannin gwamnatinsa, dogarawansa, shugabannin sojojinsa, da shugabanninsa na kekunan yaƙi da mahayan kekunan yaƙinsa. Su ne kuma manyan shugabanni masu lura da ayyukan Solomon, su ne shugabanni 550 masu lura da mutanen da suke aiki. Bayan ’yar Fir’auna ta haura daga Birnin Dawuda zuwa fadan da Solomon ya gina mata, sai ya gina madogaran gini. Sau uku a shekara Solomon kan miƙa hadayun ƙonawa da hadayun salama a kan bagaden da ya gina wa Ubangiji, yana ƙone turare a gaban Ubangiji haɗe da su, ta haka ya cika abin da ake bukata na haikali. Sarki Solomon ya kuma gina jiragen ruwa a Eziyon Geber, wadda take kusa da Elot a Edom, a bakin Jan Teku. Hiram kuwa ya aiki mutanensa, masu tuƙan jirgin ruwa waɗanda suka san teku, don su yi hidima a jerin jiragen ruwa tare da mutanen Solomon. Suka tafi Ofir suka kuma dawo da talenti 420 na zinariya, wanda suka ba wa Sarki Solomon. Sa’ad da sarauniyar Sheba ta ji game da sunan da Solomon ya yi, da kuma dangantakarsa da Ubangiji, sai ta zo tă gwada shi da tambayoyi masu wuya. Ta iso Urushalima da tawaga mai yawa, tare da raƙuma masu ɗauke da kayan yaji, da zinariya masu yawa, da duwatsu masu daraja. Ta zo wurin Solomon ta kuwa yi magana da shi game da dukan abin da take da shi a ranta. Solomon ya amsa dukan tambayoyinta, ba abin da ya yi wa sarki wuyan bayyanawa mata. Da sarauniya Sheba ta ga dukan hikimar Solomon da fadan da ya gina. Da irin abincin da yake kan teburinsa, da irin zaman fadawansa, da irin rigunan masu hidimarsa, da irin masu shayarwarsa, da kuma hadayun ƙonawar da yake yi a haikalin Ubangiji, sai ta yi mamaki ƙwarai. Ta ce wa sarki, “Labarin da na ji a ƙasata game da abin da ka yi da kuma hikimarka gaskiya ne. Amma ban gaskata waɗannan abubuwa ba sai da na zo na gani da idanuna. Tabbatacce, ba a ma faɗa mini ko rabi ba. Gama cikin hikima da arziki, ka wuce labarin da na ji nesa ba kusa ba. Abin farin ciki ne ga mutanenka! Abin farin ciki ne ga fadawanka, waɗanda suke cin gaba da tsayawa a gabanka suna kuma jin hikimarka! Yabo ga Ubangiji Allahnka, wanda ya ji daɗinka, ya kuma sa ka a kujerar sarautar Isra’ila. Ubangiji ya naɗa ka sarki saboda madawwamiyar ƙaunar wa Isra’ila, don ka yi shari’a da adalci.” Ta kuma ba sarki talenti 120 na zinariya, da kayan yaji masu yawa, da kuma duwatsu masu daraja. Ba a taɓa kawo kayan yaji da yawa haka kamar yadda sarauniyar Sheba ta ba wa Sarki Solomon ba. (Jiragen ruwan Hiram suka kawo zinariya daga Ofir. Daga can kuma suka kawo kaya masu yawa na katakon almug, da kuma duwatsu masu daraja. Sarki ya yi amfani da almug don yă yi kayan ado wa haikalin Ubangiji da kuma don fadan sarki, don kuma yă yi molaye, da garayu saboda mawaƙa. Ba a taɓa yin jigilar katakon almug ko a gani irin yawan katakai haka ba har wa yau.) Sarki Solomon ya ba wa sarauniyar Sheba dukan abin da take so, da kuma duk abin da ta nema, ban da abin da ya ba ta daga yalwar fadan sarki. Sa’an nan ta koma tare da tawagarta zuwa ƙasarta. Nauyin zinariya da Solomon yake samun kowace shekara, talenti 666 ne. Ban da haraji daga ’yan kasuwa, da fatake, da kuma daga dukan sarakunan Arabiya, da gwamnonin ƙasar. Sarki Solomon ya yi manyan garkuwoyi ɗari biyu na zinariya. An yi kowace garkuwa da zinariya bekas ɗari shida. Ya kuma yi ƙananan garkuwoyi ɗari uku na zinariya. An yi kowane garkuwa da zinariya minas uku. Ya sa su a cikin Fadar Kurmin Lebanon. Sa’an nan sarki ya yi kujerar sarauta mai nauyin giram na hauren giwa, aka kuma dalaye ta da zinariya zalla. Kujera sarautar ta kasance da matakai shida, kuma bayanta tana da bisa mai kamannin gammo. A kowane gefen kujerar akwai wurin sa hannu, da kuma zaki tsaye kusa da kowannensu. Zakoki goma sha biyu suna tsaye a matakai shida, ɗaya a kowane gefen ƙarshen mataki. Babu ƙasar da an taɓa gina irin wannan kujerar mulki. Dukan kwaf Solomon zinariya ne, kuma dukan kayayyakin gida a Fadan da ake kira Kurmin Lebanon, zinariya ce zalla. Babu wani abin da aka yi da azurfa, domin ba a ɗauki azurfa a bakin kome ba a zamanin Solomon. Sarki yana da jerin jiragen ruwan kasuwanci a teku, tare da jiragen ruwan Hiram. Sau ɗaya kowace shekara uku jerin jiragen yakan dawo ɗauke da zinariya, da azurfa, da hauren giwa, da birai marasa wutsiya, da kuma gogon biri. Sarki Solomon ya yi suna a wadata fiye da dukan sarakunan duniya. Dukan duniya ta nemi su zo wurin Solomon don su ji hikimar da Allah ya sa a zuciyarsa. Kowace shekara, kowa da ya zo wurinsa yakan kawo kyautai, kayayyakin azurfa da na zinariya, riguna, makamai, da kayan yaji, dawakai da alfadarai. Solomon ya tara kekunan yaƙi da dawakai; ya kasance da kekunan yaƙi dubu goma sha huɗu, da dawakai dubu goma sha biyu waɗanda ya ajiye a biranen kekunan yaƙi, ya kuma ajiye tare da shi a Urushalima. Sarki ya mai da azurfa barkatai a cikin Urushalima kamar duwatsu, al’ul kuma da yawa kamar itatuwan fir na jumaiza a gindin tuddai. An yi jigilar dawakan Solomon daga Masar da kuma daga Kuye, ’yan kasuwan fadan sarki sun sayo su daga Kuye. Suka yi jigilar kekunan yaƙi daga Masar a bakin shekel ɗari shida na azurfa, doki ɗaya kuma a kan ɗari da hamsin. Sun kuma yi jigilarsu suna sayarwa ga dukan sarakunan Hittiyawa da na Arameyawa. Sarki Solomon ya ƙaunaci baƙin mata. Ban da ’yar Fir’auna, ya auri Mowabawa, Ammonawa, mutanen Edom, Sidoniyawa da Hittiyawa. Sun fito daga al’ummai da Ubangiji ya ce wa Isra’ilawa, “Kada ku yi aurayya da su, domin tabbatacce za su juye zukatanku zuwa ga waɗansu alloli.” Duk da haka Solomon ya manne musu, ya nace, yana ƙaunarsu. Ya auri mata ɗari bakwai, haifaffun gidan sarauta, da kuma ƙwarƙwarai ɗari uku. Matan nan nasa suka karkatar da shi. Yayinda Solomon yake tsufa, matansa suka juye zuciyarsa ga bin waɗansu alloli, zuciyarsa kuwa ba tă bi Ubangiji Allahnsa ɗungum kamar yadda zuciyar Dawuda mahaifinsa ta kasance ba. Ya bi Ashtarot, alliyar Sidoniyawa, da Molek, allahn da aka hana na Ammonawa. Saboda haka Solomon ya yi abin da yake mugu a gaban Ubangiji. Bai bi Ubangiji gaba ɗaya kamar yadda Dawuda mahaifinsa ya yi ba. A kan tudu, gabas da Urushalima, Solomon ya gina masujada a can domin Kemosh, allahn da aka hana na Mowab, da Molek, allahn da aka hana na Ammonawa. Ya yi haka domin dukan baƙin matansa, waɗanda suka ƙone turare suka kuma miƙa hadayu ga allolinsu. Ubangiji ya yi fushi da Solomon domin zuciyarsa ya juye daga Ubangiji, Allah na Isra’ila, wanda ya bayyana masa sau biyu. Ko da yake ya hana Solomon bin waɗansu alloli, Solomon bai kiyaye umarnin Ubangiji ba. Saboda haka Ubangiji ya ce wa Solomon, “Da yake halinka ke nan, ba ka kuma kiyaye alkawarina, da ƙa’idodina da na umarce ka ba, tabbatacce zan yage masarautar daga gare ka, in ba da ita ga ɗaya daga cikin bayinka. Amma saboda Dawuda mahaifinka, ba zan yi haka a zamaninka ba. Zan yage ta daga hannun ɗanka. Amma ba zan yage dukan masarautar daga gare shi ba, zan ba shi kabila ɗaya saboda Dawuda bawana, da kuma saboda Urushalima, wadda na zaɓa.” Sai Ubangiji ya tayar wa Solomon wani abokin gāba, mai suna Hadad, mutumin Edom daga gidan sarautar Edom. A shekarun baya Dawuda ya ci Edom da yaƙi. Yowab, shugaban sojojinsa ya tafi can domin yă binne Isra’ilawa waɗanda suka mutu a yaƙi. Sa’ad da suke a can, sojojin Isra’ila suka kashe kowane ɗa namiji a Edom. Yowab da dukan Isra’ilawa suka zauna a can, wata shida, sai da suka hallaka dukan mutane a Edom. Amma Hadad yana ɗan yaro a lokaci, wanda ya gudu zuwa Masar tare da shugabannin mutanen Edom waɗanda suka yi wa mahaifinsa hidima. Suka taso daga Midiyan suka tafi Faran. Sa’an nan suka ɗauki mutane daga Faran suka tafi Masar, zuwa wurin Fir’auna wanda ya ba wa Hadad gida da ƙasa, ya kuma tanada masa da abinci. Fir’auna ya ji daɗin Hadad har ya ba shi ’yar’uwar matarsa, Sarauniya Tafenes, aure. ’Yar’uwar Tafenes ta haifi masa ɗa wanda ya kira Genubat, wanda Tafenes ta yi renonsa a fadan sarki. A can, Genubat ya yi zama da ’ya’yan Fir’auna. Yayinda yake a Masar, Hadad ya ji Dawuda ya huta tare da kakanninsa, ya kuma ji cewa Yowab shugaban mayaƙa ya mutu. Sai Hadad ya ce wa Fir’auna, “Bari in tafi, don in koma ƙasata.” Fir’auna ya tambaye shi, ya ce, “Me ka rasa a nan da kake so ka koma garinka?” Ya ce, “Ba kome, amma ka dai bar ni in tafi!” Allah kuwa ya tayar wa Solomon wani abokin gāba, mai suna Rezon, ɗan Eliyada, wanda ya gudu daga maigidansa, Hadadezer sarkin Zoba. Rezon ya tattara mutane kewaye da shi, ya zama kuma shugaban ’yan tawaye sa’ad da Dawuda ya hallaka mayaƙan Zoba; ’yan tawayen suka tafi Damaskus, inda suka zauna, suka kuma yi mulki. Rezon ya zama babban abokin gāban Isra’ila cikin dukan kwanakin mulkin Solomon. Ya ƙara rikici a kan rikicin Hadad. Rezon ya ƙi mulkin Isra’ila da dukan ransa. Saboda haka Rezon ya yi mulki a Aram ya kuma ƙi jinin Isra’ila. Haka ma Yerobowam, ɗan Nebat, shi ma ya yi wa sarki tawaye. Shi ɗaya ne daga shugabannin Solomon, shi mutumin Efraim ne daga Zereda, mahaifiyarsa kuwa gwauruwa ce, mai suna Zeruwa. Ga yadda ya tayar wa sarki Solomon. Sarki Solomon ya gina madogaran gini, ya ciccika wurare a katangar birnin Dawuda mahaifinsa da ƙasa. To, Yerobowam mutum ne mai fasaha. Sa’ad da Solomon ya ga yadda matashin yake aiki da himma, sai ya sa shi yă lura da dukan aikin gandu na gidan Yusuf. Da Yerobowam ya fita Urushalima, sai annabi Ahiya, mutumin Shilo ya tarar da shi a hanya. Lokacin kuwa Ahiya yana saye da sabuwar riga, ba kowa a filin sai su biyu kaɗai. Sai Ahiya ya kama sabuwar rigar da yake saye da ita ya yage ta gida goma sha biyu. Sa’an nan ya ce wa Yerobowam, “Ɗauki gida goma wa kanka, gama abin da Ubangiji, Allah na Isra’ila ya ce ke nan, ‘Duba, zan yage masarauta daga hannun Solomon in ba ka kabilu goma. Amma saboda bawana Dawuda da kuma birnin Urushalima, wadda na zaɓa daga dukan kabilan Isra’ila, zai sami kabila guda. Zan yi wannan domin sun yashe ni, suka kuma yi wa Ashtarot, alliyar Sidoniyawa, da Kemosh, allahn Mowabawa, da kuma Molek, allahn Ammonawa sujada, ba su yi tafiya a hanyoyina ba, ba su kuwa yi abin da yake daidai a idanuna ba, ba su kiyaye farillaina da dokokina kamar yadda Dawuda, mahaifin Solomon ya yi ba. “ ‘Amma ba zan ɗauki dukan masarautar daga hannun Solomon ba; na naɗa shi sarki, dukan kwanaki ransa saboda Dawuda bawana, wanda na zaɓa, wanda kuma ya kiyaye umarnai da farillaina. Zan ɗauke masarautar daga hannuwan ɗansa ne, in ba ka kabilu goma. Zan ba da ɗaya ga ɗansa don kullum Dawuda bawana yă kasance da fitila a gabana a Urushalima, birnin da na zaɓa in sa Sunana. Amma fa, ga kai, zan ɗauke ka, za ka kuwa yi mulki bisa dukan abin da zuciyarka take so; za ka zama sarki a bisa Isra’ila. In ka aikata dukan abin da na umarce ka, ka yi tafiya a hanyoyina, ka kuma yi abin da yake daidai a idanuna ta wurin kiyaye farillaina da umarnaina, kamar yadda Dawuda bawana ya yi, zan kasance tare da kai. Zan gina maka masarauta mai dawwama kamar wadda na gina wa Dawuda, zan kuma ba da Isra’ila gare ka. Zan ƙasƙantar da zuriyar Dawuda saboda wannan, amma ba har abada ba.’ ” Solomon ya yi ƙoƙari yă kashe Yerobowam, amma Yerobowam ya tsere zuwa Masar, zuwa wurin sarki Shishak, ya zauna a can sai bayan mutuwar Solomon. Game da sauran ayyukan mulkin Solomon, da dukan abubuwan da ya yi, da hikimar da ya nuna, an rubuta su a littafin tarihin Solomon. Solomon ya yi mulki a Urushalima, a bisa dukan Isra’ila, shekaru arba’in. Sa’an nan ya huta tare da kakanninsa, aka kuma binne shi a birnin Dawuda mahaifinsa. Sai Rehobowam ɗansa ya gāje shi a matsayin sarki. Rehobowam ya tafi Shekem, gama dukan Isra’ila sun je can don su naɗa shi sarki. Sa’ad da Yerobowam ɗan Nebat ya ji labari (gama har yanzu yana a Masar, inda ya gudu daga Sarki Solomon), sai ya dawo daga Masar. Saboda haka mutane suka aika Yerobowam yă zo, sai shi da dukan taron Isra’ila suka tafi wurin Rehobowam, suka ce masa, “Mahaifinka ya sa mana kaya mai nauyin gaske, amma yanzu ka sassauta wannan aiki mai zafi, da kuma kaya masu nauyin da ya sa a kanmu, mu kuwa za mu bauta maka.” Rehobowam ya amsa, “Ku tafi, bayan kwana uku, ku dawo.” Sai mutane suka watse. Sai Sarki Rehobowam ya nemi shawarar dattawa waɗanda suka yi wa mahaifinsa Solomon, hidima a kwanakinsa. Ya ce, “Wace shawara ce za ku ba ni don in amsa wa waɗannan mutane?” Suka amsa, “In a yau za ka zama bawan waɗannan mutane, ka kuma yi musu hidima, ka ba su amsa mai kyau, kullum za su kasance bayinka.” Amma Rehobowam ya ƙi shawarar da dattawan suka ba shi, sai ya nemi shawarar matasa waɗanda suka yi girma tare, waɗanda kuma suke masa hidima. Ya tambaye su, “Mece ce shawararku? Yaya za mu amsa wa waɗannan mutane masu cewa, ‘Ka sassauta nauyin da mahaifinka ya sa a kanmu’?” Matasan, waɗanda suka yi girma tare da shi, suka amsa, “Faɗa wa waɗannan mutanen da suka ce maka, ‘Mahaifinka ya sa kaya masu nauyi a kanmu, amma ka sassauta kayanka.’ Ka ce musu, ‘Ƙaramin yatsana ya fi ƙugun tsohona kauri. Mahaifina ya sa muku kaya masu nauyi; ni zan ma sa su fi haka nauyi. Mahaifina ya hore ku da bulala; ni kuwa zan hore ku da kunamai.’ ” Bayan kwana uku, Yerobowam da dukan mutane suka dawo wurin Rehobowam yadda sarki ya faɗa, “Ku dawo gare ni cikin kwana uku.” Sai Sarki ya amsa wa mutane da zafi. Yana ƙin shawarar da dattawa suka ba shi. Ya bi shawarar matasa, ya ce, “Mahaifina ya sa muku kaya masu nauyi; ni zan ma sa su fi haka nauyi. Mahaifina ya hore ku da bulala; ni kuwa zan hore ku da kunamai.” Saboda haka sarki bai saurare mutane ba, gama wannan abin da ya faru daga wurin Ubangiji ne, don a cika maganar Ubangiji da ya yi wa Yerobowam ɗan Nebat ta wurin Ahiya, mutumin Shilo. Da dukan Isra’ila suka ga sarki ya ƙi yă saurare su, sai suka amsa wa sarki, “Ina ruwanmu da Dawuda! Ai! Ba mu da gādo wurin ɗan Yesse. Ya Isra’ila, kowa yă koma tentinsa! Dawuda, sai ka lura da gidanka!” Saboda haka Isra’ilawa suka watse zuwa gida. Amma ga Isra’ilawan da suke zama a garuruwan Yahuda kuwa, Rehobowam ya ci gaba da mulki a kansu. Sarki Rehobowam ya aiki Adoniram wanda yake shugaban aikin gandu, amma Isra’ila suka jajjefe shi da dutse har ya mutu. Sarki Rehobowam, ya sullale ya hau keken yaƙinsa ya tsere zuwa Urushalima. Tun daga wannan ranar ne mutanen Isra’ila suka shiga gāba da gidan Dawuda har wa yau. Sa’ad da dukan Isra’ilawa suka ji Yerobowam ya dawo, sai suka aika, suka kira shi zuwa taro, suka kuma naɗa shi sarki bisa dukan Isra’ila. Kabila Yahuda kaɗai ta kasance mai biyayya ga gidan Dawuda. Da Rehobowam ya isa Urushalima, ya tattara dukan gidan Yahuda da kabilar Benyamin, ya sami sun kai mayaƙa dubu da tamanin. Sai aka shirya don su yaƙi gidan Isra’ila, su kuma mayar da masarautar wa Rehobowam ɗan Solomon. Amma waɗannan kalmomin Allah suka zo wa Shemahiya, mutumin Allah, cewa, “Faɗa wa Rehobowam ɗan Solomon, sarkin Yahuda, ka faɗa wa dukan gidan Yahuda da Benyamin, da kuma dukan sauran mutane, ‘Ga abin da Ubangiji ya ce, “Kada ku haura don ku yi yaƙi da ’yan’uwanku, Isra’ilawa. Ku koma gida, kowannenku, gama wannan aikina ne.” ’ ” Saboda haka suka yi biyayya da maganar Ubangiji, suka sāke watse zuwa gida, yadda Ubangiji ya umarta. Sai Yerobowam ya ƙara gina Shekem a ƙasar tudu ta Efraim, ya zauna a can. Daga can ya tafi ya gina Fenuwel. Yerobowam ya yi tunani a ransa ya ce, “Mai yiwuwa mulkin yă koma gidan Dawuda. In waɗannan mutane sun riƙa haurawa don su miƙa hadayu a haikalin Ubangiji a Urushalima. Za su sāke nuna biyayya ga mai girma, Rehobowam, sarkin Yahuda. Za su kashe ni su kuma koma ga Sarki Rehobowam.” Bayan ya nemi shawara, sai sarki ya yi siffofin ’yan maruƙa biyu na zinariya. Ya ce wa mutane, “Kun daɗe kuna haurawa zuwa can Urushalima. Ga allolinku, ya Isra’ila, waɗanda suka fitar da ku daga ƙasar Masar.” Sai ya kafa ɗaya a Betel, ɗaya kuma a Dan. Wannan ya zama zunubi, gama mutane suna tafiya yin wa wannan da yake a Betel sujada, su kuma je har Dan don su yi wa ɗayan sujada. Yerobowam ya gina masujadai da suke kan tuddai, ya kuma naɗa firistoci barkatai daga cikin mutanen da ba na zuriyar Lawi ba. Ya kafa biki a rana ta goma sha biyar ta watan takwas, kamar bikin da ake yi a Yahuda, ya kuma miƙa hadayu a bisa bagade. Ya yi haka a Betel, yana miƙa wa siffofin maruƙan da ya yi hadayu. A Betel kuma ya naɗa firistoci a wuraren tudun da ya yi. A rana ta goma sha biyar ta watan takwas, watan da ya zaɓa, ya miƙa hadayu a bisa bagaden da ya gina a Betel. Saboda haka ya kafa biki don Isra’ilawa, ya kuma haura zuwa bagade don yă miƙa hadayu. Bisa ga umarnin Ubangiji, sai wani mutumin Allah ya zo daga Yahuda zuwa Betel, yayinda Yerobowam yake tsaye kusa da bagade don yă miƙa hadaya. Sai mutumin Allah ya tā da murya a kan bagade bisa ga umarnin Ubangiji ya ce, “Ya bagade, bagade! Ubangiji ya ce, ‘Za a haifi ɗa mai suna Yosiya wa gidan Dawuda. A kanka zai miƙa firistoci na masujadai kan tuddai masu miƙa hadayu a nan, za a kuma ƙone ƙasusuwan mutane a kanka.’ ” A wannan rana mutumin Allah ya ba da alama, “Ga alamar da Ubangiji ya furta. Wannan bagade zai tsage yă rabu kashi biyu, tokar da yake a kansa za tă zuba a ƙasa.” Sa’ad da Yerobowam ya ji abin da mutumin Allah ya tā da murya ya faɗa game da bagaden Betel, sai ya miƙa hannunsa daga bagaden ya ce, “Ku kama shi!” Amma sai hannun da ya miƙa ya yanƙwane, har bai iya janye shi ba. Haka ma, bagaden ya rabu, tokarsa kuma ya zuba, bisa ga alamar da mutumin Allah ya bayar, ta wurin kalmar Ubangiji. Sai sarki ya ce wa mutumin Allah, “Ka roƙi Ubangiji Allahnka, ka kuma yi addu’a domina don hannuna ya warke.” Saboda haka mutumin Allah ya yi roƙo ga Ubangiji, hannun sarki kuwa ya warke, ya kuma zama kamar yadda yake a dā. Sai sarki ya ce wa mutumin Allah, “Zo gida tare da ni, ka sami wani abu ka ci, zan kuwa yi maka kyauta.” Amma mutumin Allah ya amsa wa sarki, “Ko da za ka ba rabin mallakarka, ba zan tafi tare da kai ba, ba kuwa zan ci abinci, ko in sha ruwa a can ba. Gama an umarce ni ta wurin kalmar Ubangiji, aka ce, ‘Kada ka ci abinci, ko ka sha ruwa, ko ka koma ta hanyar da ka zo.’ ” Saboda haka ya ɗauki wata hanya, bai kuwa koma ta hanyar da ya zo Betel ba. To, fa, akwai wani tsohon annabi yana zama a Betel, wanda ’ya’yansa suka zo suka faɗa masa dukan abin da mutumin Allah ya yi a can, a ranar. Suka kuma faɗa wa mahaifinsu abin da ya faɗa wa sarki. Mahaifinsu ya tambaye su ya ce, “Wace hanya ce ya bi?” Sai ’ya’yansa suka nuna masa hanyar da mutumin Allah daga Yahuda ya bi. Sai ya ce wa ’ya’yansa, “Ku yi wa jakina shimfiɗa.” Da suka yi wa jakin shimfiɗa, sai ya hau. Ya bi bayan mutumin Allah. Ya same shi yana zama a ƙarƙashin itace oak, sai ya tambaye shi ya ce, “Kai ne mutumin Allah wanda ya zo daga Yahuda?” Ya amsa, “Ni ne.” Saboda haka annabin ya ce masa, “Zo gida tare da ni ka ci abinci.” Mutumin Allah ya ce, “Ba zan koma tare da kai ba, ko in ci abinci, ko in sha ruwa tare da kai a can ba. An faɗa mini ta wurin maganar Ubangiji, ‘Kada ka ci abinci, ko ka sha ruwa a can, ko ka koma ta hanyar da ka zo.’ ” Sai annabin ya amsa, “Ni ma annabi ne, kamar ka. Kuma mala’ika ya ce mini ta wurin kalmar Ubangiji, ‘Dawo da shi zuwa gidanka saboda yă ci abinci, yă kuma sha ruwa.’ ” (Amma yana masa ƙarya ne.) Sai mutumin Allah ya koma tare da shi ya kuma ci ya sha a gidansa. Yayinda suke zaune a teburi, sai maganar Ubangiji ta zo wa tsohon annabin da ya dawo da mutumin Allah. Sai tsohon annabin ya tā da murya wa mutumin Allah wanda ya zo daga Yahuda, “Ga abin da Ubangiji ya ce, ‘Ka ƙazantar da maganar Ubangiji, ba ka kuma kiyaye umarnin Ubangiji Allahnka ba. Ka dawo ka ci abinci, ka kuma sha ruwa a wurin da na faɗa maka kada ka ci, ko ka sha. Saboda haka ba za a binne jikinka a kabarin kakanninka ba.’ ” Sa’ad da mutumin Allah ya gama ci da sha, sai annabin da ya dawo da shi ya yi wa jakin mutumin Allah shimfiɗa. Yayinda yake kan hanyarsa, sai wani zaki ya sadu da shi ya kashe shi, aka kuma jefar da jikinsa a kan hanya, jakin da zakin suka tsaya kusa da gawar. Waɗansu mutane masu wucewa suka ga an yar da gawar a can, zaki yana tsaye kusa da gawar, sai suka tafi suka ba da labarin a birni inda tsohon annabin nan yake zama. Sa’ad da annabin da ya dawo da mutumin Allah ya ji, sai ya ce, “Mutumin Allah ne, wanda ya ƙazantar da maganar Ubangiji. Ubangiji ya bashe shi ga zaki, wanda ya yayyage shi ya kuma kashe shi, kamar yadda maganar Ubangiji ta gargaɗe shi.” Sai annabin ya ce wa ’ya’yansa, “Ku yi wa jakina shimfiɗa.” Sai suka yi. Sai ya fita ya sami an jefar da gawar a hanya, jakin da zakin suna tsaye kusa da shi. Zakin bai ci gawar ko yă yayyage jakin ba. Saboda haka annabin ya ɗauki gawar mutumin Allah, ya shimfiɗa shi a kan jaki, ya koma da shi cikin birninsa don yă yi makokinsa yă kuma binne shi. Sai ya kwantar da gawar a kabarinsa, suka yi makoki a kansa, ya kuma ce, “Ayya, abokina!” Bayan an binne shi, sai ya ce wa ’ya’yansa, “Sa’ad da na mutu, ku binne ni a kabarin da aka binne mutumin Allah; ku kwantar da ƙasusuwana kusa da ƙasusuwansa. Gama annabcin da ya yi ta maganar Ubangiji gāba da bagaden da yake cikin Betel da kuma wuraren sujada a tuddan da suke a biranen Samariya, ba shakka zai cika.” Har ma bayan wannan, Yerobowam bai canja daga mugayen hanyoyinsa ba, amma ya ƙara naɗa firistoci domin masujadai da suke kan tuddai daga kowane irin mutane. Duk wanda ya so yă zama firist sai yă naɗa shi don aiki a masujadai da suke kan tuddai. Wannan ne zunubin gidan Yerobowam da ya kai ga fāɗuwarsa da kuma hallakarsa daga fuskar duniya. A lokacin Abiya, ɗan Yerobowam ya kamu da ciwo, sai Yerobowam ya ce wa matarsa, “Ki tafi, ki ɓad da kama, don kada a gane ke a matsayin matar Yerobowam. Ki je Shilo. Annabi Ahiya yana a can, wannan wanda ya ce mini zan zama sarki a bisa wannan mutane. Ki ɗauki dunƙulen burodi goma tare da ke, da waina, da tulun zuma, ki tafi wurinsa. Zai faɗa miki abin da zai faru da yaron.” Saboda haka matar Yerobowam ta yi abin da ya faɗa, ta kuma tafi gidan Ahiya a Shilo. Yanzu dai Ahiya ba ya gani; idanunsa sun tafi saboda tsufa. Amma Ubangiji ya ce wa Ahiya, “Matar Yerobowam tana zuwa tă tambaye ka game da ɗanta, gama yana ciwo, za ka kuwa ba ta amsa kaza da kaza. Sa’ad da ta iso za tă yi kamar wata ce dabam.” Saboda haka sa’ad da Ahiya ya ji motsin sawunta a ƙofa, sai ya ce, “Ki shigo, matar Yerobowam. Me ya sa kike yi kamar wata ce dabam? An aiko ni wurinki da labari marar daɗi. Je ki faɗa wa Yerobowam cewa ga abin da Ubangiji, Allah na Isra’ila ya ce, ‘Na tā da kai daga cikin mutane, na mai da kai shugaba a bisa mutanena Isra’ila. Na yage mulki daga gidan Dawuda na ba da shi gare ka, amma ba ka zama kamar bawana Dawuda wanda ya kiyaye umarnaina ya kuma bi ni da dukan zuciyarsa, yana yin abin da yake daidai kaɗai a idanuna ba. Ka aikata mugunta fiye da dukan waɗanda suka rayu kafin kai. Ka yi wa kanka waɗansu alloli, gumakan da aka yi da ƙarfe; ka tsokane ni na yi fushi, ka kuma juye mini baya. “ ‘Saboda wannan, zan kawo masifa a gidan Yerobowam. Zan yanke kowane ɗa na ƙarshe a Isra’ila, bawa ko ’yantacce. Zan ƙone gidan Yerobowam kamar yadda mutum yakan ƙone juji, sai duk ya ƙone ƙurmus. Karnuka za su ci waɗanda suka mutu na Yerobowam a cikin birni, kuma tsuntsayen sararin sama za su cinye waɗanda suka mutu a jeji. Ni Ubangiji na faɗa!’ “Ke kuma, ki koma gida. Sa’ad da kika taka ƙafa a birninki, yaron zai mutu. Dukan Isra’ila kuwa za su yi makoki dominsa. Shi ne kaɗai na Yerobowam wanda za a binne, domin shi ne kaɗai a gidan Yerobowam wanda Ubangiji, Allah na Isra’ila ya sami wani ɗan abu mai kyau a kansa. “ Ubangiji zai tā da wani sarki wa kansa a bisa Isra’ila wanda zai hallaka iyalin Yerobowam. Ko yanzu ma, wannan zai fara faruwa. Ubangiji kuma zai bugi Isra’ila, har tă zama kamar kyauro mai girgiza a bakin rafi. Zai tumɓuke Isra’ila daga wannan ƙasa mai kyau da ya ba wa kakanninsu, yă watsar da su gaba da Kogin Yuferites domin sun tsokane Ubangiji har ya yi fushi, ta wurin yin ginshiƙan Ashera. Zai kuma ba da Isra’ila saboda zunuban da Yerobowam ya yi, da ya kuma sa Isra’ila suka yi.” Sai matar Yerobowam ta tashi ta tafi, ta kuwa tafi Tirza. Nan da nan da ta taka madogarar ƙofar gidan, sai yaron ya mutu. Suka binne shi, dukan Isra’ila kuwa suka yi makoki dominsa, yadda Ubangiji ya faɗa ta wurin bawansa annabi Ahiya. Sauran ayyukan sarautar Yerobowam, da yaƙe-yaƙensa, da yadda ya yi mulki, ba a rubuce suke a littafin tarihi na sarakunan Isra’ila ba? Ya yi mulki shekaru ashirin da biyu, sai ya huta tare da kakanninsa. Sai Nadab ɗansa ya gāje shi a matsayin sarki. Rehobowam ɗan Solomon ya zama sarki a Yahuda. Yana da shekara arba’in da ɗaya sa’ad da ya zama sarki, ya kuma yi mulki shekaru goma sha bakwai a Urushalima, birnin da Ubangiji ya zaɓa daga cikin dukan kabilan Isra’ila don yă sa Sunansa. Sunan mahaifiyarsa Na’ama, ita mutuniyar Ammon ce. Yahuda ya aikata mugunta a gaban Ubangiji. Ta wurin zunuban da suka yi, sun tā da fushin kishinsa fiye da yadda kakanninsu suka yi. Sun kuma kafa wa kansu masujadai da suke kan tuddai, da a kan keɓaɓɓun duwatsu, suka kuma gina ginshiƙan Ashera a kowane tudu, da kuma a ƙarƙashin kowane duhuwar itace. Har ma akwai maza karuwai na masujada. Mutane suka sa kansu ga yin kowane abin ƙyama na al’umman da Ubangiji ya kora kafin Isra’ilawa. A shekara ta biyar ta Sarki Rehobowam, Shishak sarkin Masar ya kai wa Urushalima yaƙi. Ya kwashe dukiyar haikalin Ubangiji da kuma dukiyar fadan sarki. Ya ɗauki kome, har da dukan garkuwoyi na zinariya da Solomon ya yi. Saboda haka sarki Rehobowam ya yi garkuwoyin tagulla ya mayar da su. Ya kuma naɗa waɗannan shugabannin matsara ya sa su aiki a ƙofar zuwa fadan sarki. Duk sa’ad da sarki ya tafi wurin haikalin Ubangiji, matsara sukan riƙe garkuwoyinsu, daga baya kuma sai su mai da su ɗakin tsaro. Game da sauran ayyukan mulkin Rehobowam kuwa, da kuma dukan abin da ya yi, duk a rubuce suke a cikin littafin tarihin sarakunan Yahuda. Aka ci gaba da yaƙe-yaƙe tsakanin Rehobowam da Yerobowam. Sai Rehobowam ya huta da kakanninsa, aka kuma binne shi tare da su a Birnin Dawuda. Sunan mahaifiyarsa Na’ama, ita kuwa mutuniyar Ammon ce. Sai Abiyam ɗansa ya gāje shi a matsayin sarki. A shekara ta goma sha takwas ta mulkin Yerobowam ɗan Nebat, Abiyam ya zama sarkin Yahuda, ya kuma yi mulki a Urushalima shekara uku. Sunan mahaifiyarsa Ma’aka ne, ’yar Abisalom. Shi ma ya aikata dukan irin zunubai da tsohonsa ya yi. Zuciyarsa ba tă bi Ubangiji Allahnsa, kamar yadda zuciyar Dawuda kakansa ta yi ba. Duk da haka, saboda Dawuda Ubangiji Allahnsa ya ba shi fitila a Urushalima ta wurin ta da wani da ya gāje shi, ta wurinsa kuma Urushalima ta yi ƙarfi. Gama Dawuda ya yi abin da yake daidai a gaban Ubangiji, bai kuma fasa kiyaye wani daga umarnan Ubangiji ba dukan kwanakinsa, sai dai a batun Uriya mutumin Hitti. Aka yi yaƙi tsakanin Rehobowam da Yerobowam a duk kwanakin Abiya. Game da sauran ayyukan mulkin Abiyam kuwa, duk a rubuce suke a cikin littafin tarihin sarakunan Yahuda. Aka yi yaƙi tsakanin Abiyam da Yerobowam. Sai Abiyam ya huta tare da kakanninsa, aka kuma binne shi a Birnin Dawuda. Asa kuwa ya gāje shi a matsayin sarki. A shekara ta ashirin ta Yerobowam sarkin Isra’ila, Asa ya zama sarkin Yahuda, ya yi mulki a Urushalima shekara arba’in da ɗaya. Sunan mahaifiya mahaifiyarsa, Ma’aka ne ’yar Abisalom. Asa ya yi abin da yake daidai a gaban Ubangiji, kamar yadda kakansa Dawuda ya yi. Ya kori dukan maza karuwai na masujadai daga ƙasar, ya kuma yi waje da dukan gumakan da mahaifinsa ya yi. Ya tuɓe mahaifiya mahaifiyarsa Ma’aka daga matsayinta na mahaifiyar sarauniya, gama ta gina ƙazantaccen ginshiƙin Ashera. Asa ya yanke ginshiƙin, ya kuma ƙone shi a Kwarin Kidron. Ko da yake bai cire masujadai da suke kan tuddai ba, zuciyar Asa ta kasance da aminci ɗungum ga Ubangiji dukan kwanakinsa. Ya kawo azurfa da zinariya da kayayyakin da shi da mahaifinsa suka keɓe a haikalin Ubangiji. Aka yi yaƙi tsakanin Asa da Ba’asha sarkin Isra’ila dukan kwanakin mulkinsu. Ba’asha sarkin Isra’ila ya haura, ya yi yaƙi da Yahuda, ya kuma gina Rama don yă hana wani daga fita ko shiga yankin Asa, sarkin Yahuda. Sai Asa ya ɗauki dukan azurfa da kuma zinariyar da suka rage a ma’ajin haikalin Ubangiji da kuma nasa fadan, ya ba da su ga wani shugabansa, ya kuma aika da su zuwa ga Ben-Hadad ɗan Tabrimmon, ɗan Heziyon, sarkin Aram, wanda yake mulki a Damaskus. Ya ce, “Bari yarjejjeniya ta kasance tsakanina da kai, kamar yadda ta kasance tsakanin mahaifina da mahaifinka. Duba, ina aika maka kyautai na azurfa da na zinariya. Yanzu fa sai ka janye yarjejjeniyarka da Ba’asha sarkin Isra’ila, don yă janye daga gare ni.” Ben-Hadad ya yarda da maganar Sarki Asa, ya kuma aika shugabannin sojojin mayaƙansa ya yi yaƙi da garuruwan Isra’ila. Ya kame Iyon, Dan, Abel-Bet-Ma’aka da dukan Kinneret, haɗe da Naftali. Da Ba’asha ya ji haka, sai ya daina ginin Rama, ya janye zuwa Tirza. Sai Sarki Asa ya ba da umarni ga dukan Yahuda, kuma babu wanda aka ware, kowa yă taimaka a kwashe duwatsu da katakan da Ba’asha yake amfani da su daga Rama. Da duwatsu da katakan ne Sarki Asa ya gina Geba a Benyamin da kuma Mizfa. Game da sauran ayyukan mulkin Asa, dukan nasarorinsa, dukan abin da ya yi, da kuma biranen da ya gina, duk a rubuce suke a cikin littafin tarihin sarakunan Yahuda. A tsufansa, sai ƙafafunsa suka kamu da cuta. Sai Asa ya huta tare da kakanninsa, aka kuma binne shi tare da su a birnin kakansa Dawuda. Sai Yehoshafat ɗansa ya gāje shi a matsayin sarki. Nadab ɗan Yerobowam ya zama sarkin Isra’ila a shekara ta biyu ta Asa sarkin Yahuda, ya kuma yi mulki a bisa Isra’ila shekara biyu. Ya yi mugunta a gaban Ubangiji, yana tafiya a hanyoyin mahaifinsa da kuma cikin zunubinsa, wanda ya sa Isra’ila suka yi. Ba’asha ɗan Ahiya na gidan Issakar ya yi maƙarƙashiya gāba da shi, ya buge shi a Gibbeton, a wani garin Filistiyawa, yayinda Nadab da dukan Isra’ila suke wa garin kwanto. Ba’asha ya kashe Nadab a shekara ta uku ta Asa sarkin Yahuda, ya kuma gāje shi a matsayin sarki. Nan da nan da ya fara mulki, sai ya kashe dukan iyalin Yerobowam. Bai bar wa Yerobowam wani da rai ba, amma ya hallaka su duka, bisa ga maganar Ubangiji da ya ba wa bawansa Ahiya, mutumin Shilo. Wannan abu ya faru saboda zunuban da Yerobowam ya yi, ya kuma sa Isra’ila ya yi, kuma saboda ya tsokane Ubangiji, Allah na Isra’ila, ya yi fushi. Game da sauran ayyukan mulkin Nadab da kuma dukan abin da ya yi, duk a rubuce suke a cikin littafin tarihin sarakunan Isra’ila. Aka yi yaƙi tsakanin Asa da Ba’asha sarkin Isra’ila dukan kwanakin mulkinsu. A shekara ta uku ta Asa sarkin Yahuda, Ba’asha ɗan Ahiya ya zama sarkin dukan Isra’ila a Tirza, ya kuma yi sarauta shekara ashirin da huɗu. Ya aikata mugunta a gaban Ubangiji, yana tafiya a hanyoyin Yerobowam da kuma cikin zunubinsa, wanda ya sa Isra’ila suka yi. Sai maganar Ubangiji ta zo wa Yehu ɗan Hanani game da Ba’asha, “Na ɗaga ka daga ƙura na mai da kai shugaban mutanena Isra’ila, amma ka yi tafiya a hanyoyin Yerobowam, ka kuma sa mutanena Isra’ila suka yi zunubi, ka tsokane ni na yi fushi ta wurin zunubansu. Saboda haka ina gab da cinye Ba’asha da gidansa, zan kuma mai da gidanka kamar na Yerobowam ɗan Nebat. Karnuka za su cinye waɗanda suke na Ba’asha da suka mutu a birni, tsuntsaye kuma za su cinye waɗanda suka mutu a jeji.” Game da sauran ayyukan mulkin Ba’asha, abin da ya yi, da kuma nasarorinsa, an rubuta su cikin littafin tarihin sarakunan Isra’ila. Ba’asha ya huta tare da kakanninsa, aka kuma binne shi a Tirza. Sai Ela ɗansa ya gāje shi a matsayin sarki. Ban da haka, maganar Ubangiji ta zo ta wurin annabi Yehu ɗan Hanani wa Ba’asha da gidansa, saboda dukan muguntar da ya aikata a gaban Ubangiji, ya tsokane shi yă yi fushi ta wurin abubuwan da ya yi, da kuma zama kamar gidan Yerobowam, da kuma domin ya hallaka gidan Yerobowam. A shekara ta ashirin da shida ta Asa sarkin Yahuda, Ela ɗan Ba’asha ya zama sarkin Isra’ila, ya kuma yi mulki a Tirza shekaru biyu. Zimri, ɗaya daga cikin shugabanni, wanda ya shugabanci rabin kekunan yaƙin Ela, ya yi maƙarƙashiya a kansa. Ela yana a Tirza a lokacin, ya bugu a gidan Arza, sarkin fada a Tirza. Zimri ya shiga, ya buge shi ya kashe a shekara ta ashirin da bakwai na Asa sarkin Yahuda. Sa’an nan ya gāje shi a matsayin sarki. Nan da nan sai ya fara mulki ya kuwa zauna a kujerar sarauta, ya kashe dukan iyalin Ba’asha. Bai bar namiji guda ɗaya ba, ko dangi, ko aboki. Ta haka Zimri ya hallaka dukan iyalin Ba’asha, bisa ga maganar da Ubangiji ya yi game da Ba’asha ta wurin annabi Yehu. Wannan ya faru saboda dukan zunuban Ba’asha da waɗanda ɗansa Ela ya yi, da ya sa Isra’ila suka yi, har suka tsokane Ubangiji, Allah na Isra’ila, yă yi fushi ta wurin gumakansu marasa amfani. Game da sauran ayyukan mulkin Ela, da dukan abin da ya yi, duk a rubuce suke a cikin littafin tarihin sarakunan Isra’ila. A shekara ta ashirin da bakwai na Asa sarkin Yahuda, Zimri ya yi mulki a Tirza kwana bakwai. Mayaƙa suka yi sansani kusa da Gibbeton, wani garin Filistiyawa. Sa’ad da Isra’ilawa a cikin sansani suka ji cewa Zimri ya yi maƙarƙashiya a kan sarki, ya kuma kashe shi, sai suka yi shela, suka naɗa Omri, shugaban mayaƙa ya zama sarki a bisa Isra’ila, a wannan rana a cikin sansani. Sai Omri da dukan Isra’ilawa suka janye daga Gibbeton, suka yi wa Tirza kwanto. Da Zimri ya ga cewa an kame birnin, sai ya je ya shiga hasumiya fadan sarki ya sa wa fadan wuta wutar kuwa ta ƙone shi ya mutu. Wannan ya faru saboda zunuban da ya yi, ya yi mugunta a gaban Ubangiji ya kuma yi tafiya a hanyoyin Yerobowam da kuma cikin zunubin da Yerobowam ya yi da ya sa Isra’ila suka yi. Game da sauran ayyukan mulkin Zimri, da tawayen da ya yi, duk a rubuce suke a cikin littafin tarihin sarakunan Isra’ila. Sai mutanen Isra’ila suka rabu kashi biyu; rabi guda sun goyi bayan Tibni ɗan Ginat yă zama sarki, ɗayan rabin kuma sun goyi bayan Omri. Amma mabiyan Omri suka nuna sun fi na Tibni ɗan Ginat ƙarfi. Sai Tibni ya mutu, Omri kuwa ya zama sarki. A shekara ta talatin da ɗaya na Asa sarkin Yahuda, Omri ya zama sarkin Isra’ila, ya kuma yi mulki shekara goma sha biyu, shekaru shida a Tirza. Ya saya tudun Samariya daga Shemer, a bakin talentin biyu na azurfa, ya kuma gina birni a kan tudun, ya kira shi Samariya, bayan Shemer, sunan mai tudun a dā. Amma Omri ya yi mugunta a gaban Ubangiji, ya kuma yi zunubi fiye da dukan waɗanda suka kasance kafin shi. Ya yi tafiya a dukan hanyoyin Yerobowam ɗan Nebat da kuma cikin zunubinsa wanda ya sa Isra’ila suka yi, har suka tsokane Ubangiji, Allah na Isra’ila yă yi fushi ta wurin gumakansu marasa amfani. Game da sauran ayyukan mulkin Omri, abin da ya yi, da kuma abubuwan da ya yi, duk a rubuce suke a cikin littafin tarihin sarakunan Isra’ila. Omri ya huta tare da kakanninsa, aka kuma binne shi a Samariya. Sai Ahab ya gāje shi a matsayin sarki. A shekara ta talatin da takwas ta Asa sarkin Yahuda, Ahab ɗan Omri ya zama sarkin Isra’ila, ya kuma yi mulki a Samariya a kan Isra’ila, shekara ashirin da biyu. Ahab ɗan Omri ya yi mugunta sosai a gaban Ubangiji fiye da wani daga cikin waɗanda suka riga shi. Bai zama masa wani abu mai wuya ba, yă yi zunuban Yerobowam ɗan Nebat, har ma ya auri Yezebel ’yar Etba’al sarkin Sidoniyawa, ya kuma fara bauta wa Ba’al, ya yi masa sujada. Ya kafa bagade domin Ba’al a haikalin Ba’al da ya gina a Samariya. Ahab ya gina ginshiƙin Ashera, ya kuma aikata abubuwa masu yawa don yă tsokane Ubangiji, Allah na Isra’ila yă yi fushi fiye da dukan sarakunan Isra’ila da suka riga shi. A lokaci Ahab ne, Hiyel mutumin Betel ya sāke gina Yeriko. Ya kafa tushensa a bakin ran ɗan farinsa Abiram, ya kuma kafa ƙofofinsa a bakin ran autansa Segub, bisa ga maganar Ubangiji da ya yi ta wurin Yoshuwa ɗan Nun. To, Iliya mutumin Tishbe, daga Tishbe a Gileyad, ya ce wa Ahab, “Muddin Ubangiji, Allah na Isra’ila wanda nake bauta wa yana a raye, ba za a yi raɓa ko ruwan sama a ’yan shekaru masu zuwa ba, sai ko na faɗa haka.” Sai maganar Ubangiji ta zo wa Iliya, ta ce, “Ka bar nan, ka nufi wajajen gabas, ka ɓuya a Rafin Kerit, gabas da Urdun. Za ka sha daga rafin, zan kuma umarci hankaki su ciyar da kai a can.” Saboda haka sai Iliya ya yi abin da Ubangiji ya faɗa masa. Ya tafi Rafin Kerit, gabas da Urdun, ya zauna a can. Hankaki suka riƙa kawo masa abinci da nama, safe da yamma, ya kuma sha daga rafin. Ana nan sai rafin ya bushe saboda ba a yi ruwan sama a ƙasar ba. Sai maganar Ubangiji ta zo wa Iliya cewa, “Je ka, nan take, zuwa Zarefat na Sidon, ka zauna a can. Na umarci wata gwauruwa a can tă ciyar da kai.” Saboda haka sai ya tafi Zarefat. Sa’ad da ya isa ƙofar gari, sai ga wata gwauruwa tana tattara ’yan itace. Sai ya kira ta, ya ce, “Ki kawo mini ɗan ruwa a tulu don in sha.” Da ta kama hanya za tă tafi tă kawo, sai ya sāke kiranta ya ce, “Ina roƙonki, ki kuma kawo mini ɗan abinci.” Sai ta ce masa, “Na rantse da Ubangiji Allahnka, ba ni da wani abinci, sai dai ɗan gari hannu guda a tulu, da kuma ɗan mai a kwalaba. Ina tattara ’yan itacen nan ne don in kai gida in yi abinci wa kaina da ɗana, don mu ci, mu mutu.” Iliya ya ce mata, “Kada ki ji tsoro. Ki tafi gida, ki yi yadda kika ce. Amma da farko ki yi mini ’yar wainar burodi daga abin da kike da shi ki kawo mini, sa’an nan ki yi wani abu wa kanki da kuma ɗanki. Gama abin da Ubangiji, Allah na Isra’ila ya ce, ‘Tulun garin ba zai ƙare ba, kwalabar man kuma ba zai bushe ba sai ranar da Ubangiji ya bayar da ruwan sama a ƙasar.’ ” Sai ta tafi, ta yi yadda Iliya ya faɗa mata. Saboda haka aka kasance da abinci kowace rana wa Iliya da kuma don macen da iyalinta. Gama tulun garin bai ƙare ba, kwalabar man kuma bai bushe ba, kamar yadda Ubangiji ya faɗa wa Iliya. Ana nan sai ɗan matan, wato, gwauruwan nan ya fara ciwo. Ciwon ya ƙara muni, daga ƙarshe sai ya daina numfashi. Sai ta ce wa Iliya, “Mutumin Allah, yaya haka? Ka zo ne domin ka nuna wa Allah zunubaina, ka kuma jawo mutuwar ɗana?” Iliya ya ce, “Ki miƙa mini ɗanki.” Sai ya ɗauke shi daga hannuwanta, ya kai shi ɗakin sama inda yake zama, ya kwantar da shi a gadonsa. Sa’an nan ya yi kuka ga Ubangiji ya ce, “Ya Ubangiji Allahna, don me ka kawo wannan masifa a kan gwauruwan nan? Kai ka ce in zauna tare da ita, ga shi yanzu ɗanta ya mutu.” Sai ya kwanta, ya miƙe kansa a kan yaron sau uku, ya kuma yi kuka ga Ubangiji ya ce, “Ya Ubangiji Allahna, ka mai da ran yaron nan!” Ubangiji kuwa ya ji kukan Iliya, sai ran yaron ya dawo masa, ya kuma rayu. Iliya ya ɗauki yaron ya sauko da shi daga ɗakin sama zuwa cikin gida. Ya ba da shi ga mahaifiyarsa, ya ce, “Duba, ɗanki yana da rai!” Sai matar ta ce wa Iliya, “Yanzu na san cewa kai mutumin Allah ne, Ubangiji kuma yana magana ta wurinka.” Bayan dogon lokaci, a cikin shekara ta uku, maganar Ubangiji ta zo wa Iliya, ta ce, “Tafi, ka gabatar da kanka ga Ahab, zan kuwa aika da ruwan sama a ƙasar.” Saboda haka Iliya ya tafi ya gabatar da kansa ga Ahab. Yanzu dai yunwa ta tsananta a Samariya, Ahab kuma ya aika a kawo Obadiya, sarkin fadansa (Obadiya dai cikakken mai gaskata da Ubangiji ne. Yayinda Yezebel tana kisan annabawan Ubangiji, Obadiya ya ɗauki annabawa ɗari ya ɓoye a kogwanni biyu, hamsin a kowanne, ya kuma tanada musu abinci da kuma ruwa.) Ahab ya ce wa Obadiya, “Ka ratsa ƙasar zuwa dukan maɓulɓulai da fadamu. Mai yiwuwa ka sami ciyawa mu ba dawakai da alfadarai don su rayu, don kada mu kashe dabbobinmu.” Saboda haka suka raba ƙasar da za su ratsa, Ahab zai tafi gefe ɗaya, Obadiya kuma yă bi gefe ɗaya. Yayinda Obadiya yana tafiya, sai Iliya ya sadu da shi. Obadiya ya gane shi, ya rusuna har ƙasa, ya ce, “Kai ne, shugabana, Iliya?” Iliya ya amsa, ya ce, “I, je ka faɗa wa maigidanka cewa, ‘Iliya yana a nan.’ ” Obadiya ya yi tambaya, “Me na yi da ba daidai ba, da kake miƙa bawanka ga Ahab don yă kashe? Na rantse da Ubangiji Allahnka, babu al’umma ko masarauta da mai girma sarki bai aika a nemo ka ba. In suka ce ba ka can, sai yă sa mulkin ko al’ummar su rantse, cewa ai, ba su same ka ba. Amma yanzu kana faɗa mini in tafi wurin mai girma in ce, ‘Iliya yana a nan.’ Ban san inda Ruhun Ubangiji zai kai ka sa’ad da na bar ka ba. In na tafi na faɗa wa Ahab bai kuma same ka a nan ba, zai sa a kashe ni. Tuna fa, ni bawanka, na yi wa Ubangiji sujada tun ina saurayi. Ranka yă daɗe, ashe, ba a faɗa maka abin da na yi lokacin da Yezebel ta karkashe annabawan Ubangiji ba? Yadda na ɓoye annabawa ɗari, na sa su hamsin-hamsin a kogwanni biyu, na yi ta ba su abinci da ruwa. Yanzu fa, kana ce in tafi wurin mai girma sarki, in ce, ‘Iliya yana a nan.’ Ai, zai kashe ni!” Iliya ya ce, “Na rantse da Ubangiji Maɗaukaki, wanda nake bauta wa, tabbatacce zan gabatar da kaina ga Ahab a yau.” Saboda haka sai Obadiya ya tafi wurin Ahab ya faɗa masa, Ahab kuwa ya tafi wurin Iliya. Sa’ad da Ahab ya ga Iliya, sai ya ce masa, “Kai ne wannan, kai mai tā-da-na-zaune-tsaye a Isra’ila?” Iliya ya amsa, ya ce, “Ban tā-da-na-zaune-tsaye a Isra’ila ba. Amma kai da iyalin mahaifinka, ku kuka tā-da-na-zaune-tsaye. Ka ƙyale umarnai Ubangiji, ka bi Ba’al. Yanzu ka tara mutane daga dukan Isra’ila su sadu da ni a kan Dutsen Karmel. Ka kuma kawo annabawa ɗari huɗu da hamsin na Ba’al, da kuma annabawa ɗari huɗu na Ashera, waɗanda suke ci a teburin Yezebel.” Sai Ahab ya aika a duk fāɗin Isra’ila, ya kuma tattara annabawan a kan Dutsen Karmel. Iliya ya je gaban mutane ya ce, “Har yaushe za ku yi ta yawo tsakanin ra’ayoyi biyu? In Ubangiji ne Allah, ku bi shi; amma in Ba’al Allah ne, ku bi shi.” Mutane dai ba su ce uffam ba. Sai Iliya ya ce musu, “Ni ne kaɗai annabin Ubangiji da ya rage, amma Ba’al yana da annabawa ɗari huɗu da hamsin. Ku samo mana bijimai biyu. Bari su zaɓa ɗaya wa kansu, bari kuma su yanka shi kucu-kucu su sa a itace, sai dai, kada su sa wuta a kansa. Ni kuwa zan shirya ɗaya bijimin in sa a kan itace, ni ma, ba zan sa wuta a kansa ba. Sa’an nan ku kira bisa sunan allahnku, ni kuwa zan kira bisa sunan Ubangiji. Duk allahn da ya amsa ta wurin wuta, shi ne Allah.” Sai dukan jama’a suka ce, “Abin nan da faɗa yana da kyau.” Iliya ya ce wa annabawan Ba’al, “Ku ku fara zaɓi bijimi ɗaya, ku shirya, da yake kuna da yawa. Ku kira a bisa sunan allahnku, amma kada ku ƙuna wuta.” Sai suka ɗauki bijimin da aka ba su suka shirya shi. Sa’an nan suka kira bisa sunan Ba’al daga safe har tsakar rana. Suna ihu, “Ya Ba’al, ka amsa mana!” Amma babu wata amsa, babu wani da ya amsa. Suka yi ta rawa kewaye da bagaden da suka yi. Da tsakar rana, Iliya ya fara yin musu ba’a. Ya ce, “Ku yi ihu da ƙarfi, tabbatacce shi allah ne! Mai yiwuwa yana cikin zurfin tunani, ko dai aiki ya yi masa yawa, ko ya yi tafiya. Mai yiwuwa yana barci ne, dole a tashe shi.” Sai suka yi ta ihu da ƙarfi suna tsattsaga kansu da takuba da māsu, yadda al’adarsu take, sai da jininsu ya yi ta zuba. Tsakar rana ta wuce, suka ci gaba da ƙoƙari, suna annabci har lokacin miƙa hadayar yamma ya yi. Amma babu wani da ya tanƙa, babu wani da ya amsa, babu wanda ya kula. Sa’an nan Iliya ya ce wa dukan mutane, “Ku zo nan wurina.” Suka zo wurinsa, ya kuma shirya bagaden Ubangiji, da ya riga ya zama kufai. Iliya ya ɗauki duwatsu goma sha biyu, ɗaya don kowace kabila zuriyar Yaƙub, wanda maganar Ubangiji ta zo masa, cewa, “Sunanka zai zama Isra’ila.” Da waɗannan duwatsun ya gina bagade cikin sunan Ubangiji, ya kuma haƙa wuriya kewaye da shi, isashe da zai ci garwa biyu na irin ƙwayar gyada. Ya shirya itace, ya yayyanka bijimin kucu-kucu, ya shimfiɗa shi a itacen. Sa’an nan ya ce musu, “Ku cika manyan tuluna da ruwa, ku zuba a kan hadayar da kuma a kan itacen.” Suka zuba. Ya ce, “Ku sāke yin haka,” sai suka sāke yin haka. Ya umarta, “Ku yi haka sau na uku,” suka kuma yi haka sau na uku. Ruwan ya gangara kewaye da bagaden har ma ya cika wuriyar. A lokacin hadaya, sai annabi Iliya ya zo gaba ya yi addu’a, ya ce, “Ya Ubangiji Allah na Ibrahim, na Isra’ila da kuma na Yaƙub, bari a sani a yau cewa kai Allah ne a cikin Isra’ila, a kuma san cewa ni bawanka ne, na kuma yi dukan waɗannan abubuwa bisa umarninka. Ka amsa mini, ya Ubangiji, ka amsa mini, saboda waɗannan mutane su san cewa kai, ya Ubangiji, kai ne Allah, su kuma san cewa kana sāke juye zukatansu zuwa gare ka.” Sai wutar Ubangiji ya fāɗo, ya cinye hadayar, itacen, duwatsun da kuma ƙasar, ya lashe ruwan da yake cikin wuriyar. Sa’ad da mutane suka ga wannan, sai suka rusuna, suka sunkuyar da kai suka ce, “ Ubangiji, shi ne Allah! Ubangiji, shi ne Allah!” Sa’an nan Iliya ya umarce su, ya ce, “Ku kama annabawan Ba’al, kada ku bar waninsu yă tsere!” Suka kama su, Iliya kuwa ya sa aka gangara da su zuwa Kwarin Kishon, aka yayyanka su a can. Sai Iliya ya ce wa Ahab, “Ka haura gida, ka ci, ka sha, gama ina jin motsin ruwan sama mai yawa.” Sai Ahab ya ruga don yă ci, yă sha, amma Iliya ya hau kan ƙwanƙolin Karmel, ya rusuna ƙasa, ya sa fuska a tsakanin gwiwarsa. Ya ce wa bawansa, “Tafi ka dubi wajen teku.” Sai bawan ya haura ya duba. Ya ce, “Ba kome a can.” Sau bakwai Iliya ya ce, “Koma.” Sau na bakwai, bawan ya ce, “Wani girgije ƙarami kamar hannun mutum yana tasowa daga teku.” Sai Iliya ya ce, “Je ka faɗa wa Ahab, ‘Shirya keken yaƙinka, ka gangara kafin ruwan sama yă tare ka.’ ” Ana cikin haka, sarari ya ƙara duhunta da girgije, iska ta taso, sai ruwan sama kamar da bakin kwarya ya sauko, Ahab kuwa ya hau zuwa Yezireyel. Ikon Ubangiji ya sauko a kan Iliya, ya sha ɗamara, ya ruga a guje a gaban Ahab har zuwa Yezireyel. Ahab fa ya faɗa wa Yezebel kome da Iliya ya yi, da yadda ya karkashe dukan annabawan da takobi. Saboda haka Yezebel ta aika da ɗan aika wa Iliya yă faɗa masa, “Bari alloli su hukunta ni da tsanani, in war haka gobe ban mai da ranka kamar na ɗaya daga cikin annabawan Ba’al ba.” Iliya ya ji tsoro, ya gudu don yă ceci ransa. Sa’ad da ya kai Beyersheba a Yahuda, sai ya bar bawansa a can. Shi kuma ya yi tafiya yini guda zuwa cikin hamada. Ya zo wurin wani itacen tsintsiya, ya zauna a ƙarƙashinsa, ya roƙa yă mutu. Ya ce, “Ya ishe ni haka, Ubangiji, ka ɗauki raina; ban fi kakannina ba.” Sa’an nan ya kwanta a ƙarƙashin itacen ya yi barci. Farat ɗaya sai wani mala’ika ya taɓa shi, ya ce, “Tashi ka ci abinci.” Ya duba kewaye, sai ga wainar burodi kusa da kansa a bisa garwashin wuta mai zafi, da kuma tulun ruwa. Ya ci, ya sha, sa’an nan ya sāke kwanta. Mala’ikan Ubangiji ya sāke dawowa sau na biyu ya taɓa shi, ya ce, “Tashi ka ci abinci, gama tafiyar za tă yi maka yawa.” Saboda haka ya tashi ya ci, ya kuma sha. Ta wurin ƙarfin da ya samu saboda wannan abinci, ya yi tafiya yini arba’in da dare arba’in, sai da ya kai Horeb, dutsen Allah. A can ya shiga kogo ya kwana. Sai maganar Ubangiji ta zo masa, ta ce, “Me kake yi a nan, Iliya?” Ya amsa, ya ce, “Ina kishi dominka Ubangiji, Allah Maɗaukaki. Isra’ilawa sun ƙi alkawarinka, suka rurrushe bagadanka, suka kuma kashe annabawanka da takobi. Ni ne kaɗai na rage, yanzu, ni ma suna ƙoƙari su kashe ni.” Sai Ubangiji ya ce, “Fita ka tsaya a kan dutse a gaban Ubangiji, gama Ubangiji yana shirin wucewa.” Sai ga babbar iska mai ƙarfi ta tsage duwatsu, ta kuma ragargaza duwatsu a gaban Ubangiji, amma Ubangiji ba ya cikin iskar. Bayan iskar sai aka yi girgizar ƙasa, amma Ubangiji ba ya cikin girgizar ƙasa. Bayan girgizar ƙasa, sai ga wuta, amma Ubangiji ba ya cikin wuta. Bayan wutar kuma sai ga wata ’yar murya. Sa’ad da Iliya ya ji ta, ya ja mayafinsa ya rufe fuskarsa, ya fita ya tsaya a bakin kogon. Sai ya ji murya ta ce masa, “Me kake yi a nan, Iliya?” Ya amsa, ya ce, “Ina kishi dominka Ubangiji, Allah Maɗaukaki. Isra’ilawa sun ƙi alkawarinka, suka rurrushe bagadanka, suka kuma kashe annabawanka da takobi. Ni ne kaɗai na rage, yanzu, ni ma suna ƙoƙari su kashe ni.” Sai Ubangiji ya ce masa, “Ka koma ta hanyar da ka zo, ka tafi Hamadan Damaskus. Sa’ad da ka kai can, ka shafe Hazayel yă zama sarki bisa Aram. Ka kuma shafe Yehu ɗan Nimshi yă zama sarkin Isra’ila, ka shafe Elisha ɗan Shafat daga Abel-Mehola yă gāje ka a matsayin annabi. Yehu zai kashe duk wani wanda ya tsere wa takobin Hazayel, Elisha kuwa zai kashe duk wani wanda ya tsere wa takobin Yehu. Duk da haka zan bar mutane dubu bakwai na Isra’ila waɗanda ba su rusuna da gwiwansu wa Ba’al ba, ba su kuma sumbace shi da bakinsu ba.” Sai Iliya ya tafi daga can ya sami Elisha ɗan Shafat, yana noma da shanu goma sha biyu masu garman noma, shi kansa yana jan na goma sha biyun. Iliya ya tafi wurinsa ya jefa mayafinsa a kan Elisha. Sai Elisha ya bar shanun, ya ruga ya bi Iliya. Ya ce, “Bari in sumbace mahaifina da mahaifiyata, in yi musu bankwana, sa’an nan in zo in bi ka.” Iliya ya ce, “Koma! Me na yi maka?” Sai Elisha ya bar shi, ya koma, ya ɗauki shanunsa ya yayyanka. Ya ƙone kayan garman noman don yă dafa naman, ya kuma ba wa mutane naman, suka kuwa ci. Sa’an nan ya tashi, ya bi Iliya, ya kuma zama mai hidimarsa. Ben-Hadad sarkin Aram kuwa ya tattara mayaƙansa gaba ɗaya. Sarakuna talatin da biyu suka tafi tare da shi haɗe da dawakansu da kekunan yaƙinsu. Ya haura ya yi wa Samariya kwanto, ya kuma yaƙe ta. Ya aika da ’yan aika zuwa cikin birnin wurin Ahab sarkin Isra’ila yana cewa, “Ga abin da Ben-Hadad ya ce, ‘Azurfarka da zinariyarka nawa ne. Mafi kyau cikin matanka da ’ya’yanka nawa ne.’ ” Sarkin Isra’ila ya amsa, ya ce, “Kamar dai yadda ka faɗa, ranka yă daɗe, sarki. Ni da dukan abin da nake da shi, naka ne.” Sai ’yan aikan suka sāke dawo suka ce, “Ga abin da Ben-Hadad ya ce, ‘Na aika ka ba da azurfarka da zinariyarka, matanka da kuma ’ya’yanka. Amma war haka gobe zan aika shugabannina su bincika fadanka da kuma gidajen shugabanninka. Za su kwashe dukan abubuwan da kake ganin darajarsu su tafi.’ ” Sarkin Isra’ila ya tattara dukan dattawan ƙasar, ya ce musu, “Ku duba fa, wannan mutum yana neman tsokana! Sa’ad da ya aika in ba shi matana da ’ya’yana, azurfana da zinariyana, ban hana masa ba.” Dattawa da dukan mutane suka amsa, suka ce, “Kada ka saurare shi ko ka yarda da abin da yake bukata.” Saboda haka ya ba wa ’yan aikan Ben-Hadad amsa, ya ce, “Ku faɗa wa ranka yă daɗe, sarki, ‘Bawanka zai yi dukan abin da ka bukaci da farko, amma wannan na ƙarshe ba zan iya yin ba.’ ” Suka tafi suka kai amsar wa Ben-Hadad. Sai Ben-Hadad ya aika da wani saƙo wa Ahab, ya ce, “Bari alloli su yi da ni yadda suke so, su kuma yi haka da tsanani, in isashen ƙura ta rage a Samariya da za a iya ba wa mutanena a tafin hannu.” Sarki Isra’ila ya amsa, ya ce, “Ku faɗa masa, ‘Wanda ya sa kayan yaƙinsa bai kamata yă yi fariya ba sai ya tuɓe su.’ ” Ben-Hadad ya ji wannan saƙo yayinda shi da sarakunan suke sha a cikin tentunansu, sai ya umarce mutanensa, ya ce, “Ku shirya don yaƙi.” Saboda haka suka shirya don su yaƙi birnin. Ana cikin haka sai wani annabi ya zo wurin Ahab sarkin Isra’ila ya sanar masa cewa, “Ga abin da Ubangiji ya ce, ‘Ka ga wannan ɗumbun mayaƙa? Zan ba da su cikin hannunka a yau, sa’an nan za ka san cewa ni ne Ubangiji.’ ” Ahab ya ce, “Amma wa zai yi haka?” Annabin ya amsa, “Ga abin da Ubangiji ya ce, ‘Sojoji matasa na shugabannin yankuna za su yi haka.’ ” Ya tambaya, “Wa kuma zai fara yaƙin?” Annabin ya amsa, “Kai za ka fara.” Saboda haka Ahab ya kira sojoji matasa na shugabannin yankuna, mutum 232. Sa’an nan ya tattara sauran Isra’ilawa su 7,000 gaba ɗaya. Suka fita da tsakar rana yayinda Ben-Hadad tare da sarakuna 32 masu goyon bayansa suke cikin tentunansu suna sha, suna buguwa. Sojojin nan matasa na shugabannin yankuna suka fara fita. Ben-Hadad kuwa ya riga ya aiki ’yan leƙen asiri, waɗanda suka ce, “Mutane suna zuwa daga Samariya.” Ya ce, “In sun fito don salama, ku kamo su da rai; in sun fito yaƙi ne, ku kamo su da rai.” Sojojin nan matasa na shugabannin yankuna suka taka suka fita daga birnin da mayaƙa a bayansu. Kowannensu kuwa ya buge abokin gābansa. Ganin wannan, sai Arameyawa suka gudu, Isra’ilawa suna bi. Amma Ben-Hadad na Aram ya tsere a kan dokinsa tare da waɗansu mahayan dawakansa. Sarki Isra’ila ya bi, ya kuma sha ƙarfin dawakan da keken yaƙin, ya kashe Arameyawa da yawa. Daga baya, annabin ya zo wurin sarkin Isra’ila ya ce, “Ka ƙarfafa matsayinka ka kuma ga abin da za a yi, gama a bazara mai zuwa sarkin Aram zai sāke kawo yaƙi.” Ana cikin haka, shugabannin sarkin Aram suka ba shi shawara, “Allolinsu, allolin tuddai ne. Shi ya sa suka fi mu ƙarfi. Amma in mun yaƙe su a fili, tabbatacce za mu fi su ƙarfi. Ka yi wannan. Ka cire dukan sarakuna daga matsayinsu ka sa waɗansu shugabanni a maimakonsu. Dole kuma ka tā da waɗansu mayaƙa kamar waɗanda ka rasa, doki don doki, keken yaƙi kuma don keken yaƙi, saboda mu iya yaƙe Isra’ila a fili. Ta haka tabbatacce za mu fi ƙarfinsu.” Sai ya yarda da su, ya kuma yi haka. Bazara na biye Ben-Hadad ya tattara Arameyawa, ya haura zuwa Afek don yă yaƙi Isra’ila. Sa’ad da aka tattara Isra’ilawa, aka kuma ba su guzuri, sai suka taka suka fita don su sadu da Arameyawa. Isra’ilawa suka kafa sansani ɗaura da su kamar ƙananan garkuna biyu na awaki, yayinda Arameyawa suka rufe dukan jejin. Sai mutumin Allah ya zo ya ce wa sarkin Isra’ila, “Ga abin da Ubangiji ya ce, ‘Domin Arameyawa suna tsammani Ubangiji allahn tuddai ne, ba allahn kwari ba, zan ba da wannan ɗumbun mayaƙa a hannuwanka, za ka kuwa sani ni ne Ubangiji.’ ” Kwana bakwai suka yi sansani ɗaura da juna, a rana ta bakwai sai yaƙi ya haɗu. Isra’ilawa suka kashe sojojin kafa na Arameyawa dubu ɗari a rana ɗaya. Sauransu suka tsere zuwa birnin Afek, inda katangar ya fāɗa a kan mutum dubu ashirin da bakwai. Sai Ben-Hadad ya gudu zuwa birni ya ɓuya a ciki cikin ɗaki. Fadawansa suka je suka ce masa, “Mun ji an ce sarakunan Isra’ila masu jinƙai ne, bari mu sa tufafin makoki, mu ɗaura igiyoyi a wuyanmu, sa’an nan mu tafi wurin sarkin Isra’ila, wataƙila zai bar ka da rai.” Saye da tufafin makoki kewaye a gindinsu, da kuma igiyoyi kewaye da kawunansu, suka tafi wurin sarkin Isra’ila, suka ce, “Bawanka Ben-Hadad ya ce, ‘Ina roƙonka bari in rayu.’ ” Sarki ya amsa, “Har yanzu yana da rai? Shi ɗan’uwana ne.” Da ma abin da fadawan suke so su ji ke nan, sai suka yi sauri, suka karɓi maganar a bakinsa, suka ce, “I, ɗan’uwanka, Ben-hadad!” Sarki ya ce, “Ku je ku kawo shi.” Da Ben-Hadad ya fita, sai Ahab ya sa aka kawo shi cikin keken yaƙinsa. Ben-Hadad ya ce, “Zan mayar da biranen mahaifinka da na ƙwace daga mahaifinka. Za ka iya sa wurin kasuwarka a cikin Damaskus, kamar yadda mahaifinka ya yi a Samariya.” Ahab ya ce, “Bisa wannan yarjejjeniya zan sake ka.” Saboda haka ya yi yarjejjeniya da shi, sai ya bar shi ya tafi. Ta wurin maganar Ubangiji, ɗaya daga cikin ’ya’ya maza na annabawa ya ce wa abokinsa, “Ka buge ni da makaminka,” amma mutumin ya ƙi. Sai annabin ya ce, “Domin ba ka yi biyayya da Ubangiji ba, da zarar ka bar ni zaki zai kashe ka.” Daga baya mutumin ya tafi, zaki ya same shi, ya kuma kashe shi. Annabin ya sami wani mutum ya ce, “Ka buge ni, ina roƙonka.” Sai mutumin ya buge shi, ya ji masa ciwo. Sa’an nan annabin ya tafi ya tsaya a bakin hanya yana jiran sarki. Ya ɓad da kamanni da ƙyalle a kansa. Ƙyallen ya sauka zuwa bisa idanunsa. Yayinda sarki yake wucewa, sai annabin ya yi kira da ƙarfi gare shi ya ce “Ni bawanka na tafi yaƙi, sai ga wani ya kawo mini wani mutum, ya ce, ‘Ka riƙe wannan mutum, kada ka bar shi yă kuɓuta ko da ƙaƙa, idan ka bari ya kuɓuta, a bakin ranka, ko kuwa ka biya talanti ɗaya na azurfa.’ Yayinda bawanka yana fama, yana kai da kawowa, sai mutumin ya ɓace.” Sai sarkin Isra’ila ya ce, “Hukuncinka ke nan, ka furta shi da kanka.” Sai annabin ya cire ƙyallen da sauri daga kansa, da ya rufe idanunsa, sarkin Isra’ila kuwa ya gane shi a matsayi ɗaya daga cikin annabawa. Sai ya ce wa sarki, “Ga abin da Ubangiji ya ce, ‘Ka saki mutumin da na ƙudura yă mutu. Saboda haka ranka zai zama a maimakon ransa, mutanenka a maimakon mutanensa.’ ” Cike da fushi, sarkin Isra’ila ya tafi fadarsa a Samariya. Ana nan bayan haka sai waɗannan abubuwa suka faru. Nabot mutumin Yezireyel yana da gonar inabi a Yezireyel, a yankin Samariya, kusa da gidan Sarki Ahab. Sai Ahab ya ce wa Nabot, “Ka ba ni gonar inabinka in yi amfani da ita don kayan lambu, da yake tana kusa da fadana. Zan ba ka wata gonar inabin da ta fi wannan, ko kuma in ka gwammace, sai in biya ka duk abin da ya dace da ita.” Amma Nabot ya amsa wa Ahab ya ce, “ Ubangiji yă sawwaƙe in ba ka gādon kakannina.” Ahab ya cika da fushi saboda Nabot, mutumin Yezireyel ya ce, “Ba zan ba ka gādon kakannina ba.” Ya kwanta a gadonsa yana zub da hawaye, ya kuma ƙi cin abinci. Matarsa Yezebel ta shiga ciki ta tambaye shi, ta ce, “Me ya sa ka kumbura? Me ya sa ba za ka ci abinci ba?” Sai ya amsa mata, ya ce, “Domin na ce wa Nabot mutumin Yezireyel, ‘Ka sayar mini gonar inabinka; ko kuwa in ka gwammace, zan ba ka wata gonar inabi a maimakonta.’ Amma ya ce, ‘Ba zan ba ka gonar inabina ba.’ ” Yezebel matarsa ta ce, “Yaya kake yi kamar ba kai ne sarki Isra’ila ba? Tashi ka ci abinci! Ka yi farin ciki. Zan ba ka gonar inabin Nabot mutumin Yezireyel.” Sai ta rubuta wasiƙu a sunan Ahab, ta buga hatiminsa a kansu, sa’an nan ta aika su ga dattawa da manyan gari waɗanda suke zama a birnin da Nabot yake. Cikin waɗannan wasiƙu ta rubuta, “Ku yi shelar ranar azumi, ku zaunar da Nabot a wuri mai martaba a cikin mutane. Amma ku zaunar da waɗansu ’yan iska biyu ɗaura da shi, ku sa su ba da shaida cewa ya zagi Allah da sarki. Sa’an nan ku ɗauke shi ku jajjefe shi da dutse sai ya mutu.” Sai dattawa da manyan gari, waɗanda suke zama a birnin da Nabot yake, suka yi kamar yadda Yezebel ta umarta a cikin wasiƙun da ta rubuta. Suka yi shelar azumi, suka kuma zaunar da Nabot a wuri mai martaba a cikin mutane. Sa’an nan ’yan iska biyu suka zo, suka zauna ɗaura da shi, suka kawo zarge a kan Nabot a gaban mutane, suna cewa, “Nabot ya zagi Allah da sarki.” Saboda haka aka ɗauke shi waje da birnin, aka jajjefe shi da dutse har ya mutu. Sa’an nan suka aika wa Yezebel. “An jajjefe Nabot, ya kuma mutu.” Nan da nan sa’ad da Yezebel ta ji cewa an jajjefe Nabot da dutse ya kuma mutu, sai ta ce wa Ahab, “Tashi ka mallaki gonar inabin Nabot mutumin Yezireyel wanda ya ƙi ya sayar maka. Ba shi da rai, ya mutu.” Da Ahab ya ji cewa Nabot ya mutu, sai ya tashi ya gangara don yă mallaki gonar inabin Nabot. Sai maganar Ubangiji ta zo wa Iliya mutumin Tishbe. Ta ce, “Gangara don ka sadu da Ahab sarkin Isra’ila, wanda yake mulki a Samariya. Yanzu yana a gonar inabin Nabot, inda ya tafi yă mallake ta. Ka ce masa, Ga abin da Ubangiji ya ce, ‘Ba ka kashe mutum ka kuma ƙwace kayansa ba?’ Sa’an nan ka ce masa ga abin da Ubangiji ya ce, ‘A inda karnuka suka lashe jinin Nabot, karnuka za su lashe jininka, I, naka!’ ” Ahab ya ce wa Iliya, “Wato, ka same ni kuma, abokin gābana!” Sai ya amsa ya ce, “Na same ka, domin ka sayar da kanka ga yin mugunta a gaban Ubangiji. ‘Zan kawo masifa a kanka. Zan kawar da zuriyarka, in kuma yanke daga Ahab kowane ɗa namiji na ƙarshe cikin Isra’ila, bawa ko ’yantacce. Zan mai da gidanka kamar gida Yerobowam ɗan Nebat, da na Ba’asha ɗan Ahiya, domin ka tsokane ni har na yi fushi, ka kuma sa Isra’ila ya yi zunubi.’ “Game da Yezebel kuwa Ubangiji ya ce, ‘Karnuka za su cinye Yezebel a katangar Yezireyel.’ “Karnuka za su cinye waɗanda suke na Ahab waɗanda suka mutu a cikin birni, tsuntsayen sararin sama kuma za su cinye waɗanda suka mutu a jeji.” (Babu wani mutum kamar Ahab, wanda ya ba da kansa ga aikata mugunta a gaban Ubangiji. Yezebel matarsa ce ta zuga shi. Ya yi abar ƙyama ƙwarai ta wurin bin gumaka, kamar Amoriyawan da Ubangiji ya kora a gaban Isra’ila.) Sa’ad da Ahab ya ji waɗannan kalmomi, sai ya yage rigarsa, ya sa rigunan makoki, ya kuma yi azumi. Ya kwanta a kayan makoki, ya kuma yi tafiya cikin sauƙinkai. Sai maganar Ubangiji ta zo wa Iliya mutumin Tishbe, ta ce, “Ka lura da yadda Ahab ya ƙasƙantar da kansa a gabana kuwa? Domin ya ƙasƙantar da kansa, ba zan kawo wannan masifa a kwanakinsa ba, amma zan kawo ta a kan gidansa a kwanakin ɗansa.” Aka yi shekaru uku ba a yi yaƙi tsakanin Aram da Isra’ila ba. Amma a shekara ta uku, Yehoshafat sarkin Yahuda ya gangara don yă ga sarki Isra’ila. Sarkin Isra’ila ya ce wa shugabanninsa, “Ba ku san cewa Ramot Gileyad namu ne ba, duk da haka ba mu yi kome ba don mu sāke karɓanta daga sarkin Aram?” Saboda haka ya tambayi Yehoshafat, ya ce, “Za ka tafi tare da ni don in yi yaƙi da Ramot Gileyad?” Yehoshafat ya amsa wa sarkin Isra’ila, ya ce, “Ni ma kamar ka ne, mutanena kuwa kamar mutanenka, dawakaina kamar dawakanka.” Amma Yehoshafat ya ce wa sarkin Isra’ila, “Da farko mu nemi nufin Ubangiji.” Saboda haka sarkin Isra’ila ya tattara annabawa, kamar ɗari huɗu, ya tambaye su, “In kai yaƙi a kan Ramot Gileyad, ko kada in kai?” Suka amsa, “Ka tafi, gama Ubangiji zai ba ka ita a hannunka.” Amma Yehoshafat ya yi tambaya, ya ce, “Babu wani annabin Ubangiji a nan da za mu tambaya?” Sarkin Isra’ila ya amsa wa Yehoshafat, ya ce, “Akwai mutum guda har yanzu wanda ta wurinsa za mu iya nemi nufin Ubangiji, amma na ƙi jininsa domin bai taɓa yin annabci wani abu mai kyau game da ni ba, sai dai mummuna kullum. Shi ne Mikahiya ɗan Imla.” Yehoshafat ya ce, “Kada sarki ya ce haka.” Saboda haka sarkin Isra’ila ya kira ɗaya daga cikin shugabanninsa ya ce, “Kawo Mikahiya ɗan Imla nan take.” Saye da rigunansu na sarauta, sarkin Isra’ila da Yehoshafat sarkin Yahuda suna zama a kujerun sarautarsu a masussuka ta mashigin ƙofar Samariya, tare da dukan annabawa suna ta annabci a gabansu. Zedekiya ɗan Kena’ana kuwa ya yi ƙahonin ƙarfe ya kuma furta, “Ga abin da Ubangiji ya ce, ‘Da waɗannan za ka tunkuyi Arameyawa har su hallaka.’ ” Dukan sauran annabawan suka yi annabci iri abu ɗaya. Suka ce, “Ka yaƙi Ramot Gileyad, ka kuma yi nasara, gama Ubangiji zai ba da ita cikin hannun sarki.” Ɗan aikan da ya je yă kawo Mikahiya, ya ce masa, “Duba, sauran annabawa suna maganar nasara wa sarki, sai ka ce mutum guda. Bari maganarka tă yarda da tasu, ka kuma yi maganar alheri.” Amma Mikahiya ya ce, “Na rantse da Ubangiji mai rai, zan faɗa masa kawai abin da Ubangiji ya faɗa mini.” Da suka kai, sai sarki ya tambaye shi, ya ce, “Mikahiya, mu kai yaƙi a kan Ramot Gileyad, ko kada mu kai?” Ya amsa ya ce, “Yaƙe ta, za ka kuwa yi nasara, gama Ubangiji zai ba da ita cikin hannun sarki.” Sai sarki ya ce masa, “Sau nawa ne zan sa ka rantse cewa ba za ka faɗa mini kome ba sai dai gaskiya a cikin sunan Ubangiji?” Sa’an nan Mikahiya ya amsa, “Na ga dukan Isra’ila a warwatse a kan tuddai kamar tumakin da ba su da makiyayi, kuma Ubangiji ya ce, ‘Waɗannan mutane ba su da maigida. Bari kowa yă tafi gida cikin salama.’ ” Sai sarkin Isra’ila ya ce wa Yehoshafat, “Ban faɗa maka cewa bai taɓa yin annabci wani abu mai kyau game da ni, sai mummuna kawai ba?” Mikahiya ya ci gaba, “Saboda haka ka ji maganar Ubangiji. I, na ga Ubangiji zaune a kursiyinsa tare da dukan rundunar sama tsaye kewaye da shi a dama da hagunsa. Kuma Ubangiji ya ce, ‘Wa zai ruɗi Ahab zuwa yaƙi da Ramot Gileyad, yă kuma kai shi mutuwarsa a can?’ “Wani ya ce wannan, wani ya ce wancan. A ƙarshe, wani ruhu ya zo gaba, ya tsaya a gaban Ubangiji ya ce, ‘Zan ruɗe shi.’ “Ubangiji ya yi tambaya ‘Ta wace hanya?’ Ya ce, “ ‘Zan tafi in zama ruhun ƙarya a bakunan dukan annabawansa.’ “Ubangiji ya ce, ‘Za ka yi nasara a ruɗinsa. Ka tafi, ka yi haka.’ “Saboda haka yanzu Ubangiji ya sa ruhun ƙarya a bakunan dukan annabawanka. Ubangiji ya zartar maka da masifa.” Sai Zedekiya ɗan Kena’ana ya hau ya mari Mikahiya a fuska. Ya yi tambaya, “A wace hanya ce ruhu daga Ubangiji ya bar ni ya yi maka magana?” Mikahiya ya amsa, “Za ka gane a ranar da ka je ka ɓuya a ciki cikin ɗaki.” Sa’an nan sarkin Isra’ila ya umarta, “Ku kama Mikahiya, ku kai shi wurin Amon, shugaban birnin, da wurin Yowash ɗan sarki. Ku ce ga abin da sarki ya ce, ‘Ku sa wannan mutum a kurkuku, kuma kada ku ba shi wani abu sai dai burodi da ruwa, sai na dawo lafiya.’ ” Mikahiya ya furta, “Idan har ka dawo lafiya, to, Ubangiji bai yi magana ta wurina ba.” Ya kuma ƙara da cewa, “Ku lura da maganata, dukanku mutane!” Sai sarkin Isra’ila da Yehoshafat sarkin Yahuda suka haura zuwa Ramot Gileyad. Sarkin Isra’ila ya ce wa Yehoshafat, “Zan ɓad da kama in shiga wurin yaƙi, amma ka sa kayan sarautarka.” Saboda haka sarkin Isra’ila ya ɓad da kama, ya shiga cikin yaƙi. Sarkin Aram kuwa ya umarci shugabanni kekunan yaƙinsa talatin da biyu, ya ce, “Kada ku yaƙe kowa, ƙarami ko babba, sai dai sarkin Isra’ila.” Sa’ad da shugabannin kekunan yaƙin suka ga Yehoshafat, suka yi tsammani, suka ce, “Tabbatacce wannan shi ne sarkin Isra’ila.” Saboda haka suka juye don su yaƙe shi, amma sa’ad da Yehoshafat ya yi ihu, sai shugabannin kekunan yaƙin suka ga ashe ba sarkin Isra’ila ba ne, sai suka daina binsa. Amma wani ya ja bakansa kawai ya bugi Ahab sarkin Isra’ila a tsakanin sassan kayan yaƙinsa. Sai sarki ya ce wa mahayin keken yaƙinsa, “Juye, ka fitar da ni daga yaƙin. An ji mini rauni.” Dukan yini aka yi ta yaƙi, aka kuma riƙe sarki a keken yaƙinsa yana fuskanci Arameyawa. Jini daga mikinsa ya yi ta zuba a ƙasan keken yaƙin, a wannan yamma kuwa ya mutu. Da rana tana fāɗuwa, sai kuka ta bazu cikin mayaƙa, “Kowane mutum ya tafi garinsu; kowa ya tafi ƙasarsa!” Sai sarki ya mutu, aka kuwa kawo shi Samariya, aka binne shi a can. Suka wanke keken yaƙi a tafki, a Samariya (inda karuwai suke wanka), sai karnuka suka lashe jininsa, kamar yadda maganar Ubangiji ta furta. Game da sauran ayyukan mulkin Ahab, haɗe da dukan abin da ya yi, da fadan da ya gina ya kuma shimfiɗa da hauren giwa, da biranen da ya gina, duk a rubuce suke a cikin littafin tarihin sarakunan Isra’ila. Ahab ya huta da kakanninsa. Ahaziya ɗansa ya gāje shi a matsayin sarki. Yehoshafat ɗan Asa ya zama sarkin Yahuda a shekara ta huɗu ta Ahab sarkin Isra’ila. Yehoshafat yana da shekara talatin da biyar sa’ad da ya zama sarki, ya kuma yi mulki a Urushalima shekaru ashirin da biyar. Sunan mahaifiyarsa, Azuba ’yar Shilhi. A cikin kome ya yi tafiya a hanyoyin mahaifinsa Asa, bai kuma kauce daga gare su ba; ya yi abin da yake daidai a gaban Ubangiji. Amma bai rurrushe masujadai da suke kan tuddai ba, mutane kuwa suka ci gaba da miƙa hadayu suna kuma ƙone turare a can. Yehoshafat kuma ya zauna lafiya da sarkin Isra’ila. Game da sauran ayyukan mulkin Yehoshafat da abubuwan da ya yi, da kuma yaƙe-yaƙensa, duk a rubuce suke a cikin littafin tarihin sarakunan Yahuda. Ya kawar da karuwai maza na masujadai da suke kan tuddai waɗanda suka rage tun mulkin mahaifinsa Asa. Babu sarki a lokacin Edom, saboda haka sai mataimaki ya yi mulki. To, Yehoshafat ya gina jerin jiragen ruwan kasuwanci don su je Ofir saboda zinariya, amma ba su yi tafiya ba, gama sun farfashe a Eziyon Geber. A lokacin Ahaziya ɗan Ahab ya ce wa Yehoshafat, “Bari mutanena su tafi tare da mutanenka,” amma Yehoshafat ya ƙi. Yehoshafat kuwa ya huta tare da kakanninsa, aka kuma binne shi tare da su a birnin Dawuda kakansa. Sai Yehoram ɗansa ya gāje shi. Ahaziya ɗan Ahab ya zama sarkin Isra’ila a Samariya a shekara ta goma sha bakwai ta Yehoshafat sarkin Yahuda, ya kuma yi mulki a bisa Isra’ila shekaru biyu. Ya aikata mugunta a gaban Ubangiji, domin ya yi tafiya a hanyoyin mahaifinsa da na mahaifiyarsa, da kuma a hanyoyin Yerobowam ɗan Nebat, wanda ya sa Isra’ila suka yi zunubi. Ya bauta, ya kuma yi wa Ba’al sujada, ya tsokane Ubangiji, Allah na Isra’ila yă yi fushi, kamar yadda mahaifinsa ya yi. Bayan mutuwar Ahab, Mowab ta yi wa Isra’ila tawaye. Ahaziya fa ya fāɗo daga tagar ɗakin samansa a Samariya ya ji rauni. Saboda haka ya aiki masinjoji, yana cewa, “Ku je ku tuntuɓi Ba’al-Zebub, allahn Ekron, ku ga ko zan warke daga wannan rauni.” Amma mala’ikan Ubangiji ya ce wa Iliya mutumin Tishbe, “Ka haura ka taryi masinjojin sarkin Samariya, ka tambaye su, ‘Don babu Allah ne a Isra’ila da za ku tafi ku tuntuɓi Ba’al-Zebub allahn Ekron?’ Saboda haka, ga abin da Ubangiji ya ce, ‘Ba za ka tashi daga inda kake kwance ba, ba shakka za ka mutu!’ ” Iliya ya yi kamar yadda Ubangiji ya umarce shi, sai ya tafi. Da masinjojin suka koma wurin sarki, sai sarki ya ce da su, “Don me kuka komo?” Sai suka amsa, “Wani mutum ya sadu da mu ya ce mana, ‘Ku koma wurin sarkin da ya aike ku, ku ce masa, “Ga abin da Ubangiji ya ce, don babu Allah ne a Isra’ila da ka aika a tuntuɓi Ba’al-Zebub allahn Ekron? Saboda haka ba za ka tashi daga gadon da kake kwance ba. Ba shakka za ka mutu!” ’ ” Sai Sarkin ya tambaye su ya ce, “Wanda irin mutum ne ya yi muku wannan magana?” Sai suka ce, “Mutumin ya sa riga mai gashi, ya kuma yi ɗamara da fata.” Sarkin ya ce, “Ai, Iliya mutumin Tishbe nan ne.” Sai sarki ya aiki kaftin da sojojin hamsin wurin Iliya. Kaftin ya haura wajen Iliya, wanda yake zaune a kan tudu, ya ce masa, “Mutumin Allah, sarki ya ce, ‘Ka sauko, ka zo!’ ” Iliya ya ce masa, “In ni mutumin Allah ne, bari wuta tă sauko daga sama tă cinye ka da sojojinka hamsin!” Sai wuta ta sauko daga sama ta cinye kaftin tare da sojojinsa hamsin. Da jin haka sai sarki ya sāke aiken wani kaftin tare da waɗansu sojojinsa hamsin wurin Iliya. Kaftin ya ce wa Iliya, “Mutumin Allah, ga abin da sarki ya ce, ‘Ka sauko, nan take ka zo!’ ” Sai Iliya ya amsa, “In ni mutumin Allah ne, bari wuta ta sauko daga sama ta cinye ka da sojojinka hamsin!” Sai wutar Allah ta sauko daga sama ta cinye shi da sojojinsa hamsin. Saboda haka sai sarki ya aiki kaftin na uku da sojojinsa hamsin. Wannan kaftin na ukun ya haura ya durƙusa a gaban Iliya, ya roƙe shi ya ce, “Mutumin Allah, ina roƙonka ka dubi darajar raina da na waɗannan sojoji hamsin, bayinka! Duba, wuta ta sauko daga sama ta cinye su kaftin nan biyu waɗanda suka zo da farko da dukan sojojinsu. To, yanzu dai, ka daraja raina!” Sai mala’ikan Ubangiji ya ce wa Iliya, “Sauka, ka tafi tare da shi; kada ka ji tsoro.” Saboda haka Iliya ya tashi ya sauko, ya tafi tare da shi wajen sarki. Iliya ya ce wa sarki, “Ga abin da Ubangiji ya ce, don babu Allah a Isra’ila ne wanda za ka tuntuɓa da ka aika a tuntuɓi Ba’al-Zebub, allahn Ekron? Domin ka yi haka, ba za ka tashi daga gadon da kake kwance ba, ba shakka za ka mutu!” Ya kuwa mutu yadda Ubangiji ya faɗa ta bakin Iliya. Da yake Ahaziya ba shi da ɗa, sai Yoram ya gāje shi, ya zama sarki a shekara ta biyu ta mulkin Yehoram, ɗan Yehoshafat, sarkin Yahuda. Game da dukan sauran abubuwan da suka faru a zamani Ahaziya, da abin da ya yi, ba a rubuce suke a littattafan tarihin sarakuna Isra’ila ba? Da lokaci ya yi da Ubangiji zai ɗauki Iliya zuwa sama cikin guguwa, Iliya da Elisha kuwa suna kan hanyarsu daga Gilgal. Sai Iliya ya ce wa Elisha, “Ka dakata a nan; Ubangiji ya aike ni Betel.” Amma Elisha ya amsa ya ce, “Muddin Ubangiji yana a raye, kai kuma kana a raye, ba zan rabu da kai ba.” Saboda haka suka gangara zuwa Betel. Sai ƙungiyar annabawa a Betel suka fito zuwa wajen Elisha suka ce masa, “Ka san cewa Ubangiji zai ɗauki maigidanka daga wurinka yau?” Sai ya ce, “I, na sani, amma kada ku yi magana game da wannan.” Sai Iliya ya ce masa, “Ka dakata a nan Elisha; Ubangiji ya aike ni Yeriko.” Sai ya ce masa, “Muddin Ubangiji yana a raye, kai ma kana a raye, ba zan rabu da kai ba.” Saboda haka sai suka tafi Yeriko. Ƙungiyar annabawa a Yeriko suka haura zuwa wajen Elisha suka ce, “Ko ka san Ubangiji zai ɗauki maigidanka daga gare ka yau?” Sai ya ce, “I, na sani, amma ku bar zancen nan tukuna.” Sai Iliya ya ce masa, “Ka dakata a nan, Ubangiji ya aike ni Urdun.” Sai Elisha ya ce masa, “Muddin Ubangiji yana a raye, kai kuma kana raye, ba zan rabu da kai ba.” Saboda haka suka ci gaba da tafiya tare. Mutum hamsin na ƙungiyar annabawa suka je suka tsaya da nisa, suna fuskantar inda Iliya da Elisha suka tsaya a Urdun. Sai Iliya ya tuɓe rigarsa, ya nannaɗe ya bugi ruwan Urdun da shi. Sai ruwan ya dāre gida biyu, suka haye a busasshiyar ƙasa. Da suka haye, sai Iliya ya ce wa Elisha, “Faɗi mini, abin da kake so in yi maka kafin a ɗauke ni daga gare ka!” Elisha ya amsa ya ce, “Bari in gāji ninki biyu na ruhunka.” Iliya ya ce, “Ka nemi abu mai wuya, amma in ka ga lokacin da aka ɗauke ni daga gare ka, zai zama naka, in ba haka ba, ba za ka samu ba ke nan.” Yayinda suke tafiya suna magana, sai kwatsam, keken yaƙin wuta da dawakan wuta suka ratse tsakaninsu, sai Iliya ya tafi sama a cikin guguwa. Da Elisha ya ga haka sai ya yi ihu yana cewa, “Babana! Babana! Kekunan yaƙin da mahayan dawakan Isra’ila!” Elisha kuwa bai sāke ganinsa ba. Sai ya kama tufafinsa ya yayyage. Sai ya ɗauki rigar da ta fāɗo daga Iliya ya koma ya tsaya a gaɓar Kogin Urdun. Sa’an nan Elisha ya ɗauki rigar da ta fāɗo daga Iliya ya bugi ruwan da shi. Ya ce, “Yanzu ina Ubangiji Allah na Iliya?” Da ya bugi ruwan sai ruwan ya dāre gida biyu, sai ya haye. Ƙungiyar annabawa daga Yeriko, waɗanda suke kallo, suka ce, “Ruhun Iliya yana a kan Elisha.” Sai suka je su tarye shi, suka rusuna har ƙasa a gabansa. Suka ce, “Duba, mu bayinka muna da masu ji da ƙarfi hamsin. Bari su je su nemi maigidanka. Wataƙila, Ruhun Ubangiji ya ɗauke shi ya ajiye bisa wani dutse, ko wani kwari.” Elisha ya ce, “A’a, kada ku aike su.” Amma suka matsa masa har ya ji ba ya iya hana su. Saboda haka ya ce, “Ku aike su.” Sai suka aiki mutane hamsin, suka yi ta nema har kwana uku amma ba su same Iliya ba. Da suka dawo wurin Elisha, wanda yake a Yeriko, sai ya ce musu, “Ban ce muku kada ku tafi ba?” Mutane garin suka ce wa Elisha, “Ranka yă daɗe, duba, garin yana da kyan gani, amma ruwan ba shi da kyau, ƙasar kuma ba ta ba da amfani.” Sai ya ce, “Ku kawo mini sabuwar ƙwarya, ku kuma sa gishiri a ciki.” Sai suka kawo masa. Sai ya tafi maɓulɓular ruwan yana watsa gishirin a ciki, yana cewa, “Ga abin da Ubangiji ya ce, ‘Na warkar da ruwan nan. Ba zai ƙara jawo mutuwa, ko yă hana ƙasar ba da amfani ba.’ ” Ruwan ya tsabtacce har yă zuwa yau, bisa ga faɗin Elisha. Daga nan sai Elisha ya tafi Betel. Yayinda yake tafiya a hanya, sai waɗansu matasa suka fito daga cikin gari, suka yi masa dariya suna cewa, “Ka haura, ya kai mai kai marar gashi! Ka haura, kai mai kai marar gashi!” Sai ya juya ya dube su, ya la’anta su da sunan Ubangiji. Sai beyar guda biyu suka fito daga jeji suka hallaka matasa arba’in da biyu daga cikinsu. Sai ya ci gaba zuwa Dutsen Karmel, daga can kuma ya koma Samariya. Yoram, ɗan Ahab ya zama sarki Isra’ila, a Samariya, a shekara ta goma sha takwas ta mulkin Yehoshafat, sarkin Yahuda, ya kuma yi mulki shekara goma sha biyu. Yoram ya aikata mugunta a gaban Ubangiji, amma ba kamar yadda mahaifinsa da mahaifiyarsa suka yi ba. Ya kawar da dutsen tsarkin Ba’al wanda mahaifinsa ya yi. Duk da haka ya manne wa zunuban Yerobowam ɗan Nebat, wanda ya sa Isra’ila ta aikata, bai rabu da su ba. Mesha, sarkin Mowab yana kiwon tumaki, ya kuma zama tilas yă biya haraji ga sarkin Isra’ila. Saboda haka yakan ba da ’yan tumaki dubu ɗari, da kuma gashin raguna dubu ɗari. Amma bayan mutuwar Ahab, sai sarkin Mowab ya yi wa sarkin Isra’ila tawaye. To, a lokacin, Sarki Yoram ya tashi daga Samariya, ya tattara sojoji daga dukan Isra’ila. Ya kuma aika da wannan saƙo ga Yehoshafat sarkin Yahuda cewa, “Sarkin Mowab ya yi mini tawaye. Za ka tafi tare da ni mu yaƙi Mowab?” Sai sarkin Yahuda ya ce, “I, ina shirye mu tafi. Ai, sojojina sojojinka ne, dawakaina kuma dawakanka ne.” Ya ƙara da cewa, “Wace hanya za mu bi?” Sai Yoram ya amsa ya ce, “Ta hanyar jejin Edom.” Saboda haka sarkin Isra’ila ya fita tare da sarkin Yahuda, da kuma sarkin Edom. Da suka yi kwana bakwai suna ta zagawa, sai sojoji da dabbobi suka rasa ruwan sha. Sai sarkin Isra’ila ya ce, “Mene! Ubangiji ya kira mu sarakunan nan uku don kawai yă ba da mu ga Mowab ne?” Amma Yehoshafat ya yi tambaya ya ce, “Babu wani annabin Ubangiji a nan da za mu nemi nufin Ubangiji ta wurinsa?” Wani hafsan sarkin Isra’ila ya amsa ya ce, “Ai, akwai Elisha ɗan Shafat, wanda dā ya yi wa Iliya hidima.” Yehoshafat ya ce, “Maganar Ubangiji tana tare da shi.” Saboda haka sarkin Isra’ila da Yehoshafat da kuma sarkin Edom suka tafi wurin Elisha. Elisha ya ce wa sarkin Isra’ila, “Ina ruwana da kai? Tafi wurin annabawan mahaifinka da annabawa mahaifiyarka.” Sai sarkin Isra’ila ya ce, “A’a, ai Ubangiji ne ya kira mu, mu sarakunan nan uku don yă bashe mu ga Mowab.” Sai Elisha ya ce, “Muddin Ubangiji Maɗaukaki yana a raye, wanda nake bauta, da ba don ina ganin girman Yehoshafat Sarkin Yahuda ba, da ko kallonka ba zan yi ba. Amma yanzu, a kawo mini makaɗin garaya.” Yayinda makaɗin garayan yake kiɗa, ikon Ubangiji ya sauko a kan Elisha ya kuma ce, “Ga abin da Ubangiji ya ce, zan cika kwarin nan da tafkunan ruwa. Gama ga abin da Ubangiji ya ce, ko da yake babu iska, ko ruwan sama, duk da haka kwarin nan zai cika da ruwa, har ku da dabbobinku da kuma sauran dabbobi ku sha. Wannan abu mai sauƙi ne a wurin Ubangiji; zai kuma ba da Mowab a gare ku. Za ku ci kowane birni mai katanga, da kowane babban gari. Za ku sare kowane itace mai kyau, ku kuma tattoshe maɓuɓɓugan ruwa. Za ku kuma yi amfani da duwatsu ku lalatar da kowace gona mai kyau.” Kashegari, daidai lokacin hadaya, sai ga ruwa yana gangarowa daga gefen Edom! Ƙasar kuwa ta cika da ruwa. To, dukan Mowabawa suka ji cewa sarakuna suna tafe don su yaƙe su; saboda haka aka kira kowane namiji, babba da yaro, wanda ya isa ɗaukan makami, aka jera su a bakin iyaka. Da suka tashi da sassafe, rana tana haska ruwa. Sai ruwan ya yi ja kamar jini a idanun Mowabawan da suke a ƙetare. Sai suka ce, “Jini ne! Ba shakka sarakunan nan sun yaƙe juna, suka karkashe juna. Ya Mowabawa, mu tafi mu kwashi ganima!” Amma da Mowabawa suka isa sansanin Isra’ila, sai Isra’ilawa suka taso suka auka musu har sai da suka gudu. Isra’ilawa kuwa suka kai musu hari, suka karkashe Mowabawa. Suka ragargaza garuruwa, kowane mutum kuwa ya jefa dutse a kowane gona mai kyau har sai da aka rufe gonakin gaba ɗaya. Suka tattoshe duk maɓulɓulan ruwa, suka kuma sare duk itace mai kyau. Kir Hareset ne kaɗai aka bari tare da duwatsunsa yadda suke, amma mutanen da suke da majajjawa suka yi wa birnin zobe, suka kai masa hari shi ma. Da sarkin Mowab ya ga yaƙi ya rinjaye shi, sai ya ɗauki mutane masu takobi ɗari bakwai, ya ratsa zuwa wajen sarkin Edom, amma ba su yi nasara ba. Sa’an nan ya ɗauki ɗansa na fari, wanda zai gāje shi, ya yi hadaya da shi a bisa katangan birnin. Isra’ilawa suka firgita ƙwarai; sai suka janye suka koma ƙasarsu. Matar wani daga ƙungiyar annabawa ta yi wa Elisha kuka ta ce, “Mijina, bawanka, ya mutu, ka kuma san yadda ya girmama Ubangiji. Amma ga shi yanzu mai binsa bashi ya zo yă kwashe ’ya’yana maza biyu su zama bayinsa.” Elisha ya amsa mata ya ce, “Me kike so in yi miki? Ki faɗa mini, me kike da shi a gidanki?” Sai ta ce, “Baiwarka ba ta da kome a can, sai ɗan tulun man zaitun.” Elisha ya ce, “Ki je wurin dukan maƙwabtanki, ki nemi tulunan da babu kome a ciki. Kada ki nemo kaɗan kawai. Sa’an nan ki shiga ciki, ki kulle ƙofar da ke da ’ya’yanki kuke ciki. Ku ɗuɗɗura man a dukan tulunan, sa’ad da kowanne ya cika, sai ki ajiye a gefe.” Ta tashi ta shiga tare da ’ya’yanta maza, suka kulle ƙofa. ’Ya’yanta suka kawo mata tuluna, ita kuma tana ɗurawa. Da dukan tulunan suka cika, sai ta ce wa ɗanta, “Kawo mini wani tulu.” Amma ya amsa ya ce, “Ai, ba saura.” Sa’an nan man ya daina zuba. Sai ta tafi ta faɗa wa mutumin Allah. Shi kuwa ya ce mata, “Tafi, ki sayar da man, ki biya bashinki. Ki biya bukatanki da na ’ya’yanki da sauran da ya rage.” Wata rana Elisha ya tafi Shunem. Akwai wata mai arziki a can wadda ta gayyace shi cin abinci. Sai ya zama duk lokacin da yake wucewa, yakan tsaya a can don cin abinci. Ta ce wa mijinta, “Na san cewa wannan mutum da kullum yake zuwa nan mai tsarki ne na Allah. Bari mu yi ɗan ɗaki a rufin gida mu kuma sa masa gado da tebur da kujera da kuma fitila. Saboda a duk lokacin da ya zo wurinmu, sai yă sauka a can.” Wata rana da Elisha ya zo, sai ya haura ɗakinsa ya kwanta. Ya ce wa bawansa Gehazi, “Kira mutuniyar Shunam nan.” Sai ya kira ta, ta zo ta tsaya a gabansa. Elisha ya ce masa, “Ka ce mata, ‘Kin yi duk wannan ɗawainiya saboda mu. Yanzu, me kike so a yi miki? Kina so mu yi magana a madadinki wa sarki ko babban hafsan mayaƙa?’ ” Sai ta ce, “A’a, ina da dukan abin da nake bukata a cikin jama’ata.” Sai Elisha ya tambayi Gehazi ya ce, “Me za mu yi mata?” Sai ya amsa ya ce, “Ba ta da ɗa, ga shi kuma mijinta ya tsufa.” Sai Elisha ya ce, “Ka kira ta.” Sai ya kira ta, ta zo ta tsaya a bakin ƙofa. Elisha ya ce mata, “War haka baɗi, za ki riƙe ɗa na kanki.” Sai ta ce masa, “A’a, ranka yă daɗe, mutumin Allah, kada ka ruɗi baiwarka!” Amma matan ta yi ciki, a shekara ta biye kuwa a daidai lokacin, sai ta haifi ɗa kamar yadda Elisha ya faɗa mata. Yaron ya yi girma, wata rana sai ya tafi wurin mahaifinsa, wanda yake tare da masu girbi. Ba zato sai ya ce wa mahaifinsa, “Wayyo! Kaina yana mini ciwo! Kaina yana mini ciwo!” Sai mahaifinsa ya ce wa bawansa, “Kai shi wurin mahaifiyarsa.” Bayan bawan ya ɗaga shi ya kai wurin mahaifiyarsa, sai yaron ya zauna a cinyarta har tsakar rana, sa’an nan ya mutu. Sai ta haura ta shimfiɗa shi a gadon mutumin Allah, ta rufe ƙofar, ta fita. Ta kira mijinta ta ce, “Ina roƙonka ka aika mini da ɗaya daga cikin bayi da kuma jaka, don in yi sauri in je wurin mutumin Allah in dawo.” Sai ya ce, “Me zai kai ki wurinsa, ai, yau ba Sabon Wata ba ne ko ranar Asabbaci?” Sai ta ce, “Ba kome.” Sai ta sa wa jakar sirdi ta ce wa bawanta, “Yi ta kora mini jakar, kada ka sassauta, sai na faɗa maka.” Ta haka ta kama hanya ta tafi wurin mutumin Allah a Dutsen Karmel. Da ya hange ta daga nesa, sai mutumin Allah ya ce wa bawansa Gehazi, “Duba! Ga mutuniyar Shunam nan can! Ka yi gudu ka tarye ta ka tambaye ta, ‘Lafiyarki? Mijinki yana nan lafiya? Yaronki yana nan lafiya?’ ” Ta amsa ta ce, “Kome lafiya yake.” Da ta isa wurin mutumin Allah a dutsen, sai ta kama ƙafafunsa. Sai Gehazi ya zo don yă ture ta, amma mutumin Allah ya ce, “Ka bar ta! Tana cikin baƙin ciki ƙwarai, amma Ubangiji ya ɓoye mini, bai kuma faɗa mini me ya sa ba.” Sai ta tambaya shi ta ce, “Na roƙe ka ɗa ne, ranka yă daɗe? Ba na ce maka, ‘Kada ka sa in fara bege ba’?” Elisha ya ce wa Gehazi, “Ka yi ɗamara, ka ɗauki sandana ka ruga a guje. Idan ka sadu da wani, kada ka gaishe shi, idan kuma wani ya gaishe ka, kada ka amsa. Ka shimfiɗa sandana a fuskar yaron.” Amma mahaifiyar yaron ta ce, “Muddin Ubangiji yana raye, kai kuma kana a raye, ba zan bar ka ba.” Saboda haka ya tashi ya bi ta. Gehazi ya yi gaba, ya shimfiɗa sandan a fuskar yaron, amma babu motsi, babu alamar rai. Saboda haka Gehazi ya koma ya taryi Elisha, ya faɗa masa, “Yaron bai tashi ba.” Da Elisha ya isa gidan, sai ga gawar yaron kwance a kan gadonsa. Sai ya shiga, ya rufe ƙofa, daga shi sai yaron, ya kuma yi addu’a ga Ubangiji. Sa’an nan ya hau gadon yă kwanta a bisa yaron, ya miƙe a kansa, baki da baki, ido da ido, hannu da hannu. Yayinda ya miƙe kansa a kan yaron, sai jikin yaron ya ɗau ɗumi. Elisha ya tashi, ya yi ta kai komo a cikin ɗakin. Sa’an nan ya sāke koma kan gadon yă miƙe a kan yaron, sai yaron ya yi atishawa sau bakwai, ya kuma buɗe idanunsa. Elisha ya kira Gehazi ya ce, “Kirawo mutuniyar Shunam.” Ya kuwa kira ta. Sa’ad da ta zo, sai Elisha ya ce mata, “Ɗauki ɗanki.” Sai ta shiga, ta fāɗi a ƙafafunsa ta rusuna har ƙasa. Sa’an nan ta ɗauki ɗanta ta fita. Sai Elisha ya koma Gilgal, a can kuwa ana yunwa a yankin. Yayinda ƙungiyar annabawa suke tattaunawa da shi, sai ya ce wa Gehazi bawansa, “Ka sa babban tukunya a wuta, ka yi wa mutanen nan fate.” Ɗaya daga cikin mutanen ya shiga gona don neman ganyaye, ya kuwa sami kabewar jeji. Ya tsinko ’ya’yanta cike da shafin rigarsa. Da ya dawo, sai ya yayyanka su ya zuba a cikin tukunyar faten, ko da yake ba wanda ya san ko mene ne. Sai aka zuba wa mutanen faten, amma da suka fara ci, sai suka yi ihu suna cewa, “Ya mutumin Allah, akwai dafi a cikin tukunyan nan!” Suka kuwa kāsa ci. Elisha ya ce, “Samo mini ɗan gari.” Aka kawo masa ya kuma sa a cikin tukunyan ya ce, “Raba wa mutanen su ci.” Ya kasance kuwa babu wani abin damuwa a tukunyar. Sai ga wani mutum ya zo daga Ba’al-Shalisha, ya kawo wa Elisha dunƙulen burodi guda ashirin na sha’ir da aka gasa daga nunan fari na hatsi, tare da kawunan sababbin hatsi. Sai Elisha ya ce, “Ka ba mutanen su ci.” Sai bawansa ya ce, “Yaya zan raba wa mutane ɗari wannan?” Amma Elisha ya amsa ya ce, “Ka raba wa mutane su ci, gama haka Ubangiji ya ce, ‘Za su ci har su bar saura.’ ” Sa’an nan ya ajiye a gabansu, suka kuwa ci har suka bar saura, bisa ga maganar Ubangiji. Na’aman babban hafsan hafsoshin rundunar sarkin Aram ne, kuma ƙasaitaccen mutum ne mai martaba a idon maigidansa, domin ta wurinsa Ubangiji ya ba Aram nasara. Na’aman jarumi ne ƙwarai, amma yana da kuturta. To, daga cikin hare haren da mutanen Aram suke kaiwa, sai suka kama wata yarinya daga ƙasar Isra’ila, aka sa ta zama mai yi wa matar Na’aman aiki. Sai ta ce wa uwargijiyarta, “Da dai shugabana zai ga annabin da yake Samariya, da annabin zai warkar da shi daga kuturtarsa.” Sai Na’aman ya je wurin maigidansa ya faɗa masa abin da yarinyan nan daga Isra’ila ta faɗa. Sarkin Aram ya ce, “Ko ta ƙaƙa, ka tafi, zan aika da wasiƙa ga sarkin Isra’ila.” Sai Na’aman ya tashi, ɗauke da talenti goma na azurfa, shekel dubu shida na zinariya, da tufafi kashi goma. Wasiƙar da ya kai wa sarkin Isra’ila ta ce, “Da wannan wasiƙa ina aika Na’aman gare ka don ka warkar da kuturtarsa.” Da sarkin Isra’ila ya karanta wasiƙar, sai ya yayyage tufafinsa, ya ce, “Ni Allah ne? Zan iya ɗauke rai ko in mai da shi? Me ya sa wannan mutum ya turo mini wannan mutum in warkar da kuturtarsa? Dubi fa yadda yake nemana da faɗa!” Da Elisha mutumin Allah ya ji cewa sarkin Isra’ila ya yayyage tufafinsa, sai ya aika masa da wannan saƙo, “Don me za ka yayyage tufafinka? Ka sa mutumin yă zo wurina, zai kuwa san cewa akwai annabi a Isra’ila.” Saboda haka Na’aman ya tafi da dawakansa da keken yaƙinsa, ya tsaya a ƙofar gidan Elisha. Sai Elisha ya aika ’yan saƙo su ce masa, “Je, ka nutse sau bakwai a Urdun, fatar jikinka za tă koma daidai, ka kuma tsarkaka.” Amma Na’aman ya tashi daga can da fushi yana cewa, “Na yi tsammani zai fito ne wurina yă tsaya, yă yi kira bisa ga sunan Ubangiji Allahnsa, yă kaɗa hannunsa inda kuturtar take, yă warkar da ni. Ashe, Amana da Farfa, kogunan da suke Damaskus, ba su fi dukan ruwan da suke Isra’ila ba? Me zai sa ba zan nutse cikinsu in tsarkaka ba?” Sai ya juya ya yi tafiyarsa da fushi. Sai bayin Na’aman suka je kusa da shi suka ce, “Baba, da a ce annabin ya ce ka yi wani abu mai wuya, da ba za ka yi ba? Balle fa cewa kawai ya yi, ‘Ka yi wanka ka kuma tsarkaka’!” Saboda haka Na’aman ya je ya nutse sau bakwai a Urdun, yadda mutumin Allah ya ce masa, sai fatarsa ta koma kamar ta ɗan yaro. Sai Na’aman da dukan masu hidimarsa suka koma wurin mutumin Allah. Na’aman ya tsaya a gaban mutumin Allah ya ce, “Yanzu na san cewa babu wani Allah a duk duniya sai a Isra’ila. Ina roƙonka ka karɓi kyauta daga hannun bawanka.” Annabin ya amsa ya ce, “Muddin Ubangiji wanda nake bauta masa yana a raye, ba zan karɓi kome ba.” Ko da yake Na’aman ya yi ta roƙonsa, amma ya ƙi. Sai Na’aman ya ce, “In ba za ka karɓa ba, ina roƙonka, bari a ba wa bawanka ƙasa gwargwadon abin da jakuna biyu za su iya ɗauka, gama bawanka ba zai sāke yin hadaya ta ƙonawa, ko wata hadaya ga wani allah ba, sai ga Ubangiji. Amma ina fata Ubangiji zai gafarta wa bawanka saboda abu guda. Bari yă gafarta mini sa’ad da na raka sarkina zuwa haikalin Rimmon domin yă yi sujada, bari Ubangiji yă yi wa bawanka gafara saboda wannan.” Sai Elisha ya ce, “Ka sauka lafiya.” Bayan Na’aman ya yi ɗan nisa, sai Gehazi, bawan Elisha mutumin Allah, ya yi tunani a ransa ya ce, “Maigidana ya yi wa Na’aman mutumin Aram nan ƙaramci da bai karɓi duk abin da ya kawo ba. Muddin Ubangiji yana a raye, zan bi shi a guje in karɓi wani abu daga gare shi.” Saboda haka Gehazi ya bi Na’aman a guje. Da Na’aman ya hango shi yana zuwa a guje, sai ya sauka daga keken yaƙinsa ya tarye shi ya ce, “Lafiya?” Gehazi ya amsa ya ce, “Lafiya ƙalau. Maigidana ne ya aiko ni cewa, ‘Samari biyu daga ƙungiyar annabawa sun ziyarce ni daga ƙasa mai duwatsu na yankin Efraim. Ina roƙonka ka ba su talenti na azurfa da tufafi kashi biyu.’ ” Na’aman ya ce, “Ba damuwa, karɓi talenti biyu.” Ya roƙi Gehazi yă karɓa, sa’an nan ya ƙunsa masa talentin biyu na azurfa ya sa masa a kan jakankuna biyu, ya haɗa da tufafi kashi biyu, ya ba bayinsa biyu suka ɗauka, ya ce su sha gaban Gehazi. Da Gehazi ya isa wani tudu, sai ya karɓi kayan daga wurin bayin ya shiga da su a ɓoye a cikin gida. Sa’an nan ya sallami mutanen suka tafi. Sa’an nan ya shiga ya tsaya a gaban maigidansa Elisha. Sai Elisha ya tambaye shi ya ce, “Ina ka je, Gehazi?” Sai Gehazi ya amsa ya ce, “Bawanka bai je ko’ina ba.” Amma Elisha ya ce masa, “Ashe, ba ina tare da kai a ruhu ba sa’ad da mutumin ya sauko daga keken yaƙinsa ya tarye ka. Kana gani wannan lokaci ne da za a karɓi kuɗi, da riguna, da gonar inabi, da tumaki, da bijimai, da bayi maza da mata? Kuturtar Na’aman zai manne maka da zuriyarka har abada.” Sai Gehazi ya fita daga gaban Elisha a kuturce, fari fat kamar dusar ƙanƙara. Sai ƙungiyar annabawa suka ce wa Elisha, “Duba, wurin da muke taruwa ya kāsa mana. Bari mu je Urdun, inda kowannenmu zai saro itace; mu gina inda za mu zauna.” Sai ya ce musu, “Ku je.” Sai ɗayansu ya ce, “Ba za ka zo tare da bayinka ba?” Sai Elisha ya ce “Zan zo.” Ya kuma tafi tare da su. Suka tafi Urdun suka fara saran itatuwa. Yayinda ɗayansu yake cikin saran itace, sai kan gatarin ya fāɗi a ruwa, sai ya ce, “Kash, ranka yă daɗe, kayan aro ne fa!” Sai mutumin Allah ya ce, “Daidai ina ya fāɗa?” Da ya nuna masa wurin, sai Elisha ya yanka ɗan sanda ya jefa a wurin, ya sa kan gatarin ya taso sama. Sai ya ce masa, “Ka ɗauko.” Sai mutumin ya miƙa hannu ya ɗauka. To, fa, sarkin Aram yana yaƙi da Isra’ila. Bayan ya tattauna da hafsoshinsa, sai ya ce, “Zan kafa sansanina a wurin kaza da kaza.” Sai mutumin Allah ya aika wa sarkin Isra’ila cewa, “Ka yi hankali da wuce wuri kaza, domin Arameyawa za su gangara can.” Saboda haka sarkin Isra’ila ya lura da inda mutumin Allah ya ambata. Sau da sau Elisha yakan yi wa sarki kashedi, don haka ya riƙa taka yi tsantsan a wuraren nan. Wannan ya husata sarkin Aram. Ya kira hafsoshinsa ya tambaye su ya ce, “Ku faɗa mini, wane ne a cikinmu yake gefen sarkin Isra’ila?” Sai ɗaya daga cikin hafsoshinsa ya ce, “Babu waninmu, ranka yă daɗe; Elisha, annabin da yake a Isra’ila ne, yake faɗa wa sarkin Isra’ila dukan zancen da ka yi a ɗakinka.” Sai sarki ya ba da umarni ya ce, “Ku je ku tabbatar da inda yake don in aika mutane a kamo shi.” Sai ya sami rahoto cewa, “Yana a Dotan.” Sai ya aika da dawakai da kekunan yaƙi da babban rukunin soja zuwa can. Suka bi dare, suka kewaye birnin. Sa’ad da bawan mutumin Allah ya farka ya kuma fita kashegari da sassafe, sai ga mayaƙa tare da dawakai da kekunan yaƙi sun kewaye birni. Sai bawan ya ce, “Ranka yă daɗe! Me za mu yi?” Sai annabin ya ce, “Kada ka ji tsoro, waɗanda suke tare da mu sun fi waɗanda suke tare da su.” Sa’an nan Elisha ya yi addu’a ya ce, “Ya Ubangiji, ka buɗe idanunsa yă gani!” Sai Ubangiji ya buɗe idanun bawan, ya duba, ya ga tuddai cike da dawakai da keken yaƙin wuta kewaye da Elisha. Yayinda abokan gāba suka gangaro wajensa, sai Elisha ya yi addu’a ga Ubangiji ya ce, “Ka sa mutanen nan su zama makafi.” Sai Ubangiji ya buge su da makanta kamar yadda Elisha ya roƙa. Elisha ya ce musu, “Wannan ba ita ce hanyar ba, ba kuma gari ke nan ba, ku bi ni, zan kuwa kai ku wurin mutumin da kuke nema!” Sai ya kai su Samariya. Bayan suka shiga birnin, sai Elisha ya ce, “ Ubangiji, ka buɗe idanun mutanen nan don su gani.” Sa’an nan Ubangiji ya buɗe idanunsu suka ga kansu a tsakiyar Samariya. Da sarkin Isra’ila ya gan su, sai ya tambayi Elisha ya ce, “In kashe su ne, mahaifina? In kashe su?” Elisha ya ce, “Kada ka kashe su. Za ka kashe mutanen da ka kame da takobi ko bakanka? Ka ba su abinci da ruwa su ci, su sha, sa’an nan su koma wurin maigidansu.” Saboda haka aka shirya musu babban liyafa, bayan sun ci, suka kuma sha, sai ya tura su zuwa wurin maigidansu. Ta haka ’yan harin Aram suka daina kai hari a yankin Isra’ila. Bayan wani lokaci, Ben-Hadad sarkin Aram ya tattara dukan rundunarsa, ya je ya kewaye Samariya da yaƙi. Aka yi babban yunwa a cikin birnin. Saboda daɗewar wannan kewayewar da aka yi wa birnin, sai yunwa ta ɓarke a birnin, har ana sayar da kan jaki a kan shekel tamanin, kashin kurciya kuma a kan shekel biyar. Yayinda sarkin Isra’ila yake wucewa kusa da katanga, sai wata mace ta yi masa kuka ta ce, “Ka taimake ni, ranka yă daɗe, sarki!” Sai sarki ya amsa ya ce, “In Ubangiji bai taimake ki ba, me zan iya yi? Ina da hatsi ko ruwan inabin da zan ba ki ne?” Sa’an nan ya tambaye ta ya ce, “Me ya faru?” Sai ta amsa ta ce, “Wannan mace ta ce mini, ‘Kawo ɗanki mu ci yau, gobe kuwa mu ci ɗana.’ Saboda haka muka dafa ɗana muka ci. Kashegari na ce mata, ‘Kawo ɗanki mu ci,’ amma ta ɓoye shi.” Da sarki ya ji maganar macen sai ya yage rigunansa. Sa’ad da sarki yake wucewa a kan katangar birnin, sai mutane suka gan yana saye da rigar makoki a ciki. Ya ce, “Bari Allah yă yi mini hukunci mai tsanani har ma fiye da haka, idan ban cire kan Elisha ɗan Shafat yau ba!” To, Elisha yana zaune a cikin gidansa, dattawa kuwa suna zaune tare da shi. Sai sarki ya aiki ɗan aika yă ci gaba, amma kafin ɗan aikan yă isa, Elisha ya ce wa dattawan, “Kun gani ko? Wannan mai kisa ya aiko a cire mini kai! To, idan ɗan aikan ya iso, sai ku rufe ƙofar da ƙarfi, ku bar shi a waje. Ba da jimawa ba, maigidansa zai bi bayansa?” Yana magana da su ke nan, sai ga ɗan aikan ya gangaro wajensa. Sarki kuma ya ce, “Wannan bala’in daga wurin Ubangiji ya fito. Don me zan sa zuciya ga Ubangiji kuma?” Sai Elisha ya ce, “Ku ji maganar Ubangiji. Ga abin da Ubangiji ya ce, gobe war haka, za a sayar da mudun gari mai laushi a farashin shekel guda, mudu biyu na sha’ir kuma a shekel ɗaya a ƙofar birnin Samariya.” Sai wani hafsa mataimakin sarki ya ce wa mutumin Allah, “Kai, ko da Ubangiji zai buɗe tagogin sama, wannan abu ba zai yiwu ba!” Sai Elisha ya ce, “Za ka gani da idanunka, zai faru, amma ba za ka ci ba!” To, akwai waɗansu kutare huɗu a ƙofar gari. Suka ce wa junansu, “Don me za mu zauna a nan sai mun mutu? In muka ce, ‘Za mu shiga cikin birni’ yunwa tana can, za mu kuwa mutu. Idan kuwa muka zauna a nan, za mu mutu. Saboda haka, bari mu ƙetare zuwa sansanin Arameyawa mu miƙa kai. Idan suka bar mu da rai, to; idan kuwa suka kashe mu, shi ke nan.” Da yamma sai suka tashi suka tafi sansanin Arameyawa. Yayinda suka shiga tsakiyar sansanin Arameyawa kuwa, sai suka tarar ba kowa a can, gama Ubangiji ya sa rundunar Arameyawa suka ji motsin kekunan yaƙi, da motsin dawakai, da na babban rundunar sojoji, saboda haka suka ce wa juna; “Duba, sarkin Isra’ila ya ɗauka hayar sarakuna Hittiyawa da sarakunan Masarawa don su yaƙe mu!” Saboda haka suka tashi, suka gudu da yamma, suka bar tentunansu, da dawakansu, da jakunansu. Suka bar sansanin yadda yake, suka gudu don su ceci rayukansu. Da kutaren nan suka kai bakin sansanin, sai suka shiga wani tenti, suka ci, suka sha, suka kwashi azurfa, da zinariya, da riguna, suka tafi, suka ɓoye su. Sa’an nan suka koma, suka shiga wani tenti, sai suka kwashi kaya daga ciki, suka kuma ɓoye su. Sa’an nan suka ce wa juna, “Ba mu yi abin kirki ba. Wannan rana ce ta albishiri amma muka yi shiru; in kuwa mun bari har gari ya waye, to, fa, wata masifa za tă fāɗo mana. Bari mu tafi nan take mu faɗa a fadan sarki.” Saboda haka suka je suka kira masu tsaron ƙofar birni, suka ce musu, “Mun je sansanin Arameyawa, ga shi kuwa ba mu iske kowa a can ba, babu ko motsin wani, sai dai dawakai da jakuna a daure, tentunan kuwa suna nan yadda suke.” Sai matsaran ƙofar suka sanar da labarin a cikin fada. Sai sarki ya tashi da daren nan ya ce wa hafsoshinsa, “Na san abin da Arameyawan suke shiri! Sun san game da yunwar da muke ciki a nan, domin haka sun bar sansaninsu suka shiga jeji suka ɓuya, suna nufin sa’ad da muka fita daga birni, sai su kama mu da rai, sa’an nan su shiga birnin.” Ɗaya daga cikin fadawan sarki ya ce, “A sa waɗansu mutane su ɗauki dawakai biyar da suka ragu cikin birni, idan ba su tsira ba, za su zama kamar sauran Isra’ilawan da suka riga suka mutu ne. Bari mu aika, mu gani.” Saboda haka suka zaɓi kekunan yaƙi biyu tare da dawakansu, sarki kuwa ya aike su su bi bayan sojojin Arameyawa. Ya umarci masu tuƙinsu ya ce, “Ku je ku bincika abin da ya faru.” Suka bi sawunsu har Urdun, suka ga tufafi da makamai barjat ko’ina a hanya waɗanda Arameyawa suka zubar yayinda suke gudu. Sai ’yan aika suka dawo suka ba wa sarki labari. Sa’an nan jama’a suka fita suka kwashi ganima a sansanin Arameyawa. Aka kuwa sayar da gari mai laushi a farashin shekel guda, mudu biyu na sha’ir kuma a shekel guda, yadda Ubangiji ya faɗi. Sai ya kasance cewa Sarki ya sa dogari wanda ya raka shi wajen Elisha ya tsare ƙofar birnin. Sai mutane suka tattake shi a ƙofar har ya mutu, kamar yadda annabi Elisha ya faɗa sa’ad da sarki ya tafi wurinsa. Haka kuwa ya kasance kamar yadda mutumin Allah ya ce wa sarki, “Gobe war haka, za a sayar da mudun gari shekel guda, mudun sha’ir biyu ma a shekel guda, a ƙofar Samariya.” Hafsan ya riga ya ce wa mutumin Allah, “Kai, ko da Ubangiji zai buɗe tagogin sama, wannan abu ba zai yiwu ba!” Mutumin Allah kuwa ya faɗa masa, “Za ka gani da idanunka sai dai ba za ka ci ba!” Haka kuwa ya kasance, gama mutane sun tattake shi a hanyar shiga, har ya mutu. To, Elisha ya riga ya ce wa matan da ya tā da ɗanta daga matattu, “Ki kwashe iyalinki ku tafi duk inda za ku tafi na ɗan lokaci, domin Ubangiji ya sa a yi yunwa na shekara bakwai a ƙasar.” Sai macen ta yi kamar yadda mutumin Allah ya faɗa. Ita da iyalinta suka tafi ƙasar Filistiyawa suka zauna shekara bakwai. A ƙarshen shekara bakwai ɗin sai ta dawo daga ƙasar Filistiyawa, ta kuma tafi wajen sarki ta roƙa a mayar mata da gidanta da filinta. Sarki kuwa yana magana da Gehazi bawan mutumin Allah, ya ce masa, “Ba ni labarin dukan abubuwan banmamakin da Elisha ya yi.” A sa’ad da Gehazi yana cikin ba shi labarin yadda Elisha ya tā da matacce ke nan, sai ga macen da aka tā da ɗanta daga matattu ta shigo don tă roƙi sarki yă mayar mata da gidanta da filinta. Gehazi ya ce, “Ranka yă daɗe, ai, ga macen, ga kuma ɗan da Elisha ya tā da daga matattu.” Sarki ya tambayi macen game da al’amarin, ita kuwa ta faɗa masa. Sa’an nan ya sa wani hafsa yă dubi damuwarta ya kuma ce masa, “Ka mayar mata kome da yake nata, haɗe da dukan kuɗin da aka samo daga filin, daga ranar da ta bar ƙasar har yă zuwa yanzu.” Sai Elisha ya tafi Damaskus, Ben-Hadad mutumin Aram kuwa yana ciwo. Sa’ad da aka faɗa wa sarki, “Mutumin Allah ya hauro tun daga can zuwa nan,” sai ya ce wa Hazayel, “Ɗauki wannan tare da kai ka tafi ka taryi mutumin Allah. Ka nemi nufin Ubangiji ta wurinsa; ka tambaye shi, ‘Zan warke daga ciwon nan?’ ” Sai Hazayel ya tafi taryen Elisha, ya ɗauka kyauta na kowane irin kaya masu kyau na Damaskus tare da shi a raƙuma arba’in. Ya shiga ya tsaya a gaban Elisha ya ce, “Ɗanka Ben-Hadad na Aram ya aike ni in tambaye ka, ‘Zan warke daga ciwon nan?’ ” Elisha ya amsa ya ce, “Je ka ce masa, ‘Ba shakka za ka warke’; amma Ubangiji ya nuna mini cewa ba shakka zai mutu.” Sai ya zuba wa Hazayel ido har sai da Hazayel ya ji kunya. Sa’an nan mutumin Allah ya fara kuka. Hazayel ya ce masa, “Me ya sa ranka yă daɗe yake kuka?” Elisha ya amsa, “Domin na san illar da za ka yi wa Isra’ilawa. Za ka ƙona biranensu masu katanga, ka karkashe majiya ƙarfinsu da takobi, ka fyaffyaɗe ƙananan yaransu da ƙasa, ka tsattsage matansu masu ciki.” Hazayel ya ce, “Yaya bawanka, wanda yake kare kawai, zai iya aikata wannan irin abu?” Elisha ya ce, “ Ubangiji ya nuna mini cewa za ka zama sarkin Aram.” Sai Hazayel ya rabu da Elisha ya koma wurin maigidansa. Da Ben-Hadad ya yi tambaya, “Me Elisha ya ce maka?” Sai Hazayel ya amsa, “Ya faɗa mini cewa tabbatacce za ka warke.” Amma kashegari sai ya ɗauki tsumma mai kauri, ya jiƙa shi, ya rufe fuskar sarki da shi, har sai da sarki ya mutu. Sai Hazayel ya gāje shi a matsayin sarki. A shekara ta biyar ta mulkin Yoram ɗan Ahab, sarkin Isra’ila, sa’ad da Yehoshafat yake sarautar Yahuda, Yoram ɗan Yehoshafat, ya fara mulkinsa a matsayin sarkin Yahuda. Yana da shekara talatin da biyu sa’ad da ya zama sarki, ya kuma yi mulki na tsawon shekara takwas a Urushalima. Ya bi gurbin sarakunan Isra’ila, yadda gidan Ahab ta yi, gama ya auri ’yar Ahab. Ya yi mugunta a gaban Ubangiji. Duk da haka, saboda bawansa Dawuda, Ubangiji bai ragargaza Yahuda ba. Ya riga ya yi alkawari zai bar wa Dawuda magāji har abada. A kwanakin Yoram, Edom ta yi wa Yahuda tawaye, ta naɗa wa kanta sarki. Saboda haka Yehoram ya tafi Zayir da dukan kekunan yaƙinsa. Sojojin Edom suka kewaye shi a can, amma da dare sai Yoram ya ɓarke ya gudu, sojojinsa kuma suka watse zuwa gidajensu. Har yă zuwa yau, Edom tana yi wa Yahuda tawaye. A lokaci ɗaya ne Libna ma ta yi tawaye. Game da waɗansu abubuwan da suka faru a zamanin Yoram, ba suna a rubuce a cikin littafin tarihin sarakunan Yahuda ba? Yoram ya huta tare da kakanninsa, aka kuma binne shi a birnin Dawuda. Sai Ahaziya ɗansa ya gāje shi a matsayin sarki. A shekara ta goma sha biyu ta Yoram ɗan Ahab, sarkin Isra’ila, Ahaziya ɗan Yehoram, sarkin Yahuda ya fara mulki. Ahaziya yana da shekara ashirin da biyu sa’ad da ya zama sarki, ya kuma yi mulki a Urushalima shekara ɗaya. Sunan mahaifiyarsa Ataliya, jikanyar Omri, sarkin Isra’ila. Ya bi gurbin gidan Ahab, ya yi mugunta a gaban Ubangiji yadda gida Ahab ta yi, gama yana da dangantaka ta aure da gidan Ahab. Ahaziya ya tafi tare da Yoram ɗan Ahab don su yaƙi Hazayel sarkin Aram a Ramot Gileyad. Arameyawa suka yi wa Yoram rauni; saboda haka Sarki Yoram ya koma zuwa Yezireyel don yă yi jinyar raunin da Arameyawa suka ji masa a Rama a yaƙinsa da Hazayel sarkin Aram. Sai Ahaziya ɗan Yehoram, sarkin Yahuda ya gangara zuwa Yezireyel yă dubi Yoram ɗan Ahab domin an yi masa rauni. Sai Elisha ya kira wani daga cikin ƙungiyar annabawa, ya ce masa, “Ka sha ɗamara, ka ɗauki wannan kwalabar mai ka je Ramot Gileyad. Da ka isa can, ka nemi Yehu ɗan Yehoshafat, ɗan Nimshi. Ka je wurinsa, ka ja shi gefe daga abokansa, ka shiga da shi ɗaki na ciki. Sa’an nan ka ɗauki kwalabar man ka zuba a kansa, ka ce, ‘Ga abin da Ubangiji ya faɗa, na naɗa ka sarkin Isra’ila.’ Sa’an nan ka buɗe ƙofa ka ruga a guje; kada ka ɓata lokaci!” Sai saurayin nan, annabi, ya tafi Ramot Gileyad. Da ya isa can, sai ya tarar da hafsoshin soji zaune a wuri guda. Sai ya ce, “Ina da saƙo dominka komanda.” Sai Yehu ya ce, “Wanne a cikinmu?” Sai ce, “Dominka, komanda.” Sai Yehu ya tashi ya shiga cikin gida. Sa’an nan annabin ya zuba wa Yehu mai a kā, ya ce, “Ga abin da Ubangiji, Allah na Isra’ila ya ce, ‘Na naɗa ka sarki a bisa jama’ar Ubangiji, wato, Isra’ila. Za aka hallaka gidan Ahab maigidanka, zan kuma ɗauki fansar jinin bayina annabawa da kuma jinin dukan bayin Ubangiji da Yezebel ta zub da. Dukan gidan Ahab zai hallaka. Zan kashe dukan ’ya’yan Ahab maza a Isra’ila, bayi ko ’yantattu. Zan mai da gidan Ahab kamar gidan Yerobowam ɗan Nebat da kuma kamar gidan Ba’asha ɗan Ahiya. Game da Yezebel kuwa, karnuka za su cinye ta a fili a Yezireyel, ba kuwa wanda zai binne ta.’ ” Sa’an nan ya buɗe ƙofa ya ruga a guje. Da Yehu ya koma wurin sauran hafsoshin sai ɗaya daga cikinsu ya tambaye shi, “Lafiya? Me ya kawo wannan mahaukaci a wurinka?” Sai Yehu ya ce, “Ka san mahaukacin nan da irin maganganunsa.” Suka ce masa, “Ba gaskiya ba ne, ka dai faɗa mana.” Yehu ya ce, “Ga abin da ya ce mini, ‘Ga abin da Ubangiji ya ce, na naɗa ka sarki a bisa Isra’ila.’ ” Sai suka yi sauri suka ɗauki rigunansu suka shimfiɗa a ƙasa, suka busa kakaki, suka yi ihu, suka ce, “Yehu ne sarki.” Saboda haka, Yehu ɗan Yehoshafat, ɗan Nimshi, ya ƙulla wa Yoram maƙarƙashiya (To, Yoram da dukan Isra’ila suna kāre Ramot Gileyad daga Hazayel sarkin Aram, amma Sarki Yoram ya koma Yezireyel don yă farfaɗo daga raunukan da Arameyawa suka ji masa a wata gabzawar da ya yi da Hazayel sarkin Aram.) Yehu ya ce, “In haka kuke ji, kada ku bar wani yă sulluɓe daga birnin yă kai labarin Yezireyel.” Sai ya tashi ya ɗauki keken yaƙinsa ya tafi Yezireyel gama Yoram yana hutawa a can. Ga kuma Ahaziya sarkin Yahuda ya je don yă gan shi. Mai tsaro kuwa yana tsaye a kan hasumiya a Yezireyel, sai ya hangi rundunar Yehu sa’ad da yake zuwa. Ya ce, “Na ga wata runduna.” Sai Yoram ya umarta, “Nemi mahayin doki a aike shi yă tarye su, yă kuma tambaye su, ‘Lafiya?’ ” Sai mahayin dokin ya hau, ya ruga, ya taryi Yehu, ya ce, “Ga abin da sarki ya ce, ‘Lafiya?’ ” Sai Yehu ya ce masa, “Ina ruwanka da zancen lafiya? Ka shiga layi.” Sai mai tsaron ya ce wa sarki, “Ɗan saƙon ya kai wurinsu, amma ba ya dawowa.” Saboda haka sarki ya sāke aika mahayin doki na biyu. Sa’ad da ya isa wurinsu sai ya ce, “Ga abin da sarki ya ce, ‘Lafiya?’ ” Yehu ya ce, “Ina ruwanka da zancen lafiya? Ka shiga layi.” Mai tsaro ya sāke cewa, “Ya kai wurinsu, amma shi ma ba ya dawowa. Ina ganin sukuwar kamar irin ta Yehu, jikan Nimshi, gama yakan yi sukuwa kamar mahaukaci.” Yoram ya umarta, “Haɗa mini keken yaƙi!” Da aka haɗa, sai Yoram sarkin Isra’ila, da Ahaziya sarkin Yahuda, suka hau suka tafi, kowa a keken yaƙinsa, don su taryi Yehu. Suka sadu da shi a filin da yake na Nabot mutumin Yezireyel. Sa’ad da Yoram ya ga Yehu sai ya tambaye shi, “Lafiya kuwa ka zo, Yehu?” Yehu ya ce, “Ina kuwa lafiya, da yake dukan bautar gumaka da bokancin mahaifiyarka Yezebel sun bazu ko’ina?” Yoram ya juya, ya gudu, yana ce wa Ahaziya, “Cin amana, Ahaziya!” Sai Yehu ya ja bakansa ya harbi Yoram a tsakanin kafaɗunsa. Kibiyar ta same shi a zuciyarsa sai ya fāɗi a cikin keken yaƙinsa. Yehu ya ce wa Bidkar, hafsan keken yaƙinsa, “Ka ɗauke shi ka jefar a filin da yake na Nabot mutumin Yezireyel. Ka tuna yadda ni da kai muke a kekunan yaƙi a bayan Ahab mahaifinsa sa’ad da Ubangiji ya yi wannan annabci game da shi, ‘Jiya na ga jinin Nabot da jinin ’ya’yansa, in ji Ubangiji, kuma ba shakka zan ɗauki fansa a wannan fili, in ji Ubangiji.’ Saboda haka, ka ɗauke shi ka jefar da shi a bisa wannan fegi, bisa ga faɗin Ubangiji. Saboda haka, ka ɗauke shi ka jefar a filin, in ji Ubangiji.” Sa’ad da Ahaziya sarkin Yahuda ya ga abin da ya faru, sai ya haura hanyar Bet Haggan a guje. Yehu ya bi shi yana ihu, “A kashe shi, shi ma!” Suka ji masa rauni a keken yaƙinsa a hanya zuwa Gur, kusa da Ibileyam amma ya tsere zuwa Megiddo ya mutu a can. Barorinsa suka ɗauke shi cikin keken yaƙi zuwa Urushalima suka binne shi a kabarinsa tare da kakanninsa a birnin Dawuda. (A shekara ta goma sha ɗaya ta Yoram ɗan Ahab, Ahaziya ya zama sarkin Yahuda.) Sa’an nan Yehu ya je Yezireyel. Sa’ad da Yezebel ta sami labari, sai ta sha kwalliya ta gyara gashin kanta, ta zauna tana kallo daga taga. Yayinda Yehu ya shiga ƙofa, sai ta ce, “Lafiya, kai Zimri, mai kashe maigidansa?” Sai ya ɗaga ido ya dubi tagan ya ce, “Wa yake gefena? Wane ne?” Sai bābānni biyu ko uku suka leƙo suka dube shi. Yehu ya ce musu, “Ku jefa ta ƙasa!” Sai suka jefar da ita, jininta ya fantsama a jikin bango da kuma a jikin dawakai yayinda suke tattaka ta. Yehu ya shiga ya ci, ya kuma sha. Ya ce, “Ku san yadda za ku yi da la’ananniyan nan, ku binne ta, gama ’yar sarki ce.” Amma sa’ad da suka je don su binne ta, ba su sami kome ba sai ƙoƙon kanta, ƙafafunta da kuma hannuwanta. Suka komo suka faɗa wa Yehu, wanda ya ce, “Wannan ita ce maganar da Ubangiji ya faɗa ta bakin bawansa Iliya mutumin Tishbe. A fili, a Yezireyel, karnuka za su cinye naman Yezebel. Gawar Yezebel zai zama kamar juji a ƙasa, a fili, a Yezireyel, har ba wanda zai iya cewa, ‘Wannan Yezebel ce.’ ” To, akwai ’ya’ya maza saba’in na gidan Ahab a Samariya. Saboda haka Yehu ya rubuta wasiƙu, ya aika su Samariya, zuwa ga shugabannin Yezireyel, da kuma ga masu lura da ’ya’yan Ahab. Ya ce, “Da zarar wasiƙan nan ta sadu da ku, da yake ’ya’yan maigidanku suna tare da ku, kuna kuma da kekunan yaƙi da dawakai, da birni mai katanga da makamai, sai ku zaɓi mafi cancanta a cikin ’ya’yan maigidanku ku sa shi a kan kursiyin mahaifinsa. Sa’an nan ku yi yaƙi don gidan maigidanku.” Amma suka razana suka ce, “Idan sarakuna biyu ba su iya yin tsayayya da shi ba, wane mu?” Saboda haka sarkin fada, da gwamnan birnin, da dattawa, da kuma masu lura da ’ya’yan suka aika da saƙo ga Yehu, cewa, “Mu bayinka ne, za mu kuma yi duk abin da ka ce. Ba za mu naɗa kowa sarki ba; sai ka yi abin da ka ga ya fi kyau.” Sai Yehu ya sāke rubuta musu wasiƙa ta biyu, ya ce, “In a gefena kuke, to, sai ku yi biyayya da ni, ku fille kawunan ’ya’yan maigidanku, ku kawo mini a Yezireyel war haka gobe.” To, ’ya’yan sarki, su saba’in, suna tare da manyan birni waɗanda suke lura da su. Sa’ad da wasiƙar ta iso, sai mutanen nan suka ɗauki dukan ’ya’yan sarkin nan saba’in, suka kashe su, suka sa kawunansu cikin kwanduna, suka aika wa Yehu a Yezireyel. Da ɗan saƙon ya iso, sai aka ce wa Yehu, “Sun kawo kawunan ’ya’yan sarki.” Sai Yehu ya ce, “Ku ajiye su kashi biyu a ƙofar gari har safiya.” Da gari ya waye, sai Yehu ya fita ya tsaya a gaban dukan jama’a ya ce, “Ba ku da laifi. Ni ne na ƙulla wa maigidana maƙarƙashiya, na kuma kashe shi, amma wa ya karkashe dukan waɗannan? Ku sani fa, ba kalmar da Ubangiji ya faɗa game da gidan Ahab da ba za tă cika ba. Ubangiji ya yi abin da ya alkawarta ta bakin bawansa Iliya.” Saboda haka Yehu ya kashe duk waɗanda suka rage na iyalin Ahab a Yezireyel, tare da dukan fadawansa da aminansa da firistocinsa, ba a bar masa kowa ba. Sa’an nan Yehu ya nufi Samariya. Da ya kai Bet-Eked na Makiyaya, sai ya gamu da waɗansu daga dangin Ahaziya sarkin Yahuda, sai ya tambaye su, ya ce, “Ku, su wane ne?” Suka ce, “Mu dangin Ahaziya ne, mun kuma zo ne mu gai da iyalan sarki da kuma mahaifiyar sarauniya.” Sai ya umarta ya ce, “A kama su da rai!” Aka kuwa kama su aka yayyanka kusa da rijiyar Bet-Eked, su arba’in da biyu. Ba a bar wani da rai ba. Bayan ya bar wurin, sai ya gamu da Yehonadab ɗan Rekab wanda yake kan hanyarsa don yă sadu da shi. Sai Yehu ya gaishe shi, ya ce, “Ka amince da ni yadda na amince da kai?” Yehonadab ya ce, “I.” Yehu ya ce, “To, in haka ne ka ba ni hannunka.” Sai ya miƙa masa, Yehu kuwa ya ja shi cikin keken yaƙin. Yehu ya ce, “Zo tare da ni ka ga himmata saboda Ubangiji.” Sa’an nan ya sa suka tafi tare cikin keken yaƙinsa. Da Yehu ya isa Samariya, sai ya karkashe dukan sauran iyalin Ahab, ya hallaka su, bisa ga maganar da Ubangiji ya faɗa ta bakin Iliya. Sa’an nan Yehu ya tattara dukan jama’a ya ce musu, “Ahab ya bauta wa Ba’al kaɗan ne kawai; amma Yehu zai bauta masa sosai. Yanzu sai ku kira dukan annabawan Ba’al, dukan masu yin masa hidima da kuma dukan firistocinsa. Ku tabbata ba a manta da wani ba, gama zan yi wa Ba’al babbar hadaya. Duk wanda bai zo ba, a bakin ransa.” Amma Yehu yana wayo ne domin yă hallaka masu yi wa Ba’al sujada. Yehu ya ce, “Ku kira jama’a don a girmama Ba’al.” Saboda haka suka yi shela. Sa’an nan ya aika saƙo ko’ina a Isra’ila, dukan masu yi wa Ba’al hidima kuwa suka tattaru, ba mutumin da bai zo ba. Suka yi cincirindo a haikalin Ba’al har sai da ya cika makil. Sai Yehu ya ce wa mai ajiyar tufafi, “Ka kawo riguna domin dukan masu yi wa Ba’al hidima.” Sai ya fito musu da riguna. Sa’an nan Yehu da Yehonadab ɗan Rekab, suka shiga haikalin Ba’al. Yehu ya ce wa masu yi wa Ba’al sujada, “Ku dudduba ku tabbatar cewa babu wani bawan Ubangiji a nan tare da ku, sai masu hidimar Ba’al kawai.” Saboda haka suka shiga don su miƙa hadayu da kuma hadaya ta ƙonawa. To, Yehu ya riga ya ba wa mutane takwas wannan kashedi a waje cewa, “In waninku ya bar ɗaya daga cikin mutanen nan da nake danƙa a hannunku ya tsere, to, a bakin ransa.” Nan da nan sa’ad da Yehu ya gama yin hadayar, sai ya umarci masu gadin da hafsoshi, “Ku shiga ku karkashe su; kada ku bar wani yă tsere.” Saboda haka suka karkashe su da takobi. Masu gadin da hafsoshin suka wuwwurga gawawwakinsu waje, suka kuma shiga ciki cikin haikalin Ba’al ɗin, suka fitar da dutsen tsafi daga haikalin Ba’al, suka kuma ƙone shi. Suka farfasa dutsen tsafin Ba’al, suka kuma rushe haikalin, mutane suka mai da wurin salga har yă zuwa yau. Ta haka Yehu ya hallaka butar Ba’al a Isra’ila. Duk da haka, bai rabu da zunuban Yerobowam ɗan Nebat, wanda ya sa Isra’ila ta aikata ba, wato, yin sujada ga siffofin maruƙa na zinariya a Betel da kuma Dan. Ubangiji ya ce wa Yehu, “Tun da yake ka aikata abin da yake mai kyau a idanuna, ka kuma yi wa gidan Ahab dukan abin da yake a zuciyata, ina yin maka alkawari cewa zuriyarka za su yi mulkin Isra’ila har tsara ta huɗu.” Duk da haka, Yehu bai mai da hankali ya kiyaye dokokin Ubangiji, Allah na Isra’ila da dukan zuciyarsa ba. Bai rabu da zunubin Yerobowam, wanda ya sa Isra’ila ta aikata ba. A kwanakin sai Ubangiji ya fara rage girman Isra’ila, Hazayel ya yi nasara a bisa Isra’ila a ko’ina a yankinsu gabas da Urdun, cikin dukan ƙasar Gileyad (yankin Gad, da na Ruben, da na Manasse), daga Arower wajen Kwarin Arnon ya ratsa Gileyad zuwa Bashan. Game da sauran ayyukan mulkin Yehu, da dukan abin da ya yi, a rubuce suke a cikin littafin tarihin sarakunan Isra’ila. Yehu ya huta tare da kakanninsa, aka binne shi a Samariya. Yehoyahaz kuma ya ci sarauta bayansa. Yehu ya yi sarautar Isra’ila a Samariya shekara ashirin da takwas. Da Ataliya mahaifiyar Ahaziya ta ga ɗanta ya mutu, sai ta shiga hallaka dukan iyalin gidan sarauta. Amma Yehosheba, ’yar Sarki Yoram, ’yar’uwar Ahaziya, ta ɗauki Yowash ɗan Ahaziya daga cikin ’ya’yan sarkin da ake shiri a kashe, ta ɓoye. Ta ɓoye shi daga Ataliya a wurin mai lura da shi a ɗakin kwana; don kada a kashe shi. Ya kasance a ɓoye, shi da mai lura da shi, a haikalin Ubangiji shekara shida yayinda Ataliya take mulkin ƙasar. A shekara ta bakwai sai Yehohiyada ya aika a kira komandodin sojoji ɗari-ɗari, da Keretawa, da matsara, ya sa aka kawo masa su a haikalin Ubangiji. Ya ƙulla yarjejjeniya da rantsuwa da su a haikalin Ubangiji, sa’an nan ya nuna musu ɗan sarki. Ya umarce su cewa, “Ga abin da za ku yi sa’ad da kuka zo aiki a Asabbaci, ku raba kanku kashi uku. Kashi ɗaya za su yi gadin gidan sarki, kashi ɗaya za su yi gadin Ƙofar Sur, kashi ɗaya kuma za su yi gadin ƙofar da take bayan ’yan gadin fada. Dukan waɗannan ƙungiyoyi uku za su yi gadin fadan, ku kuma da kuke a sauran ƙungiyoyi biyu da kun saba hutu a Asabbaci, duk za ku yi gadin haikali don sarki. Ku tsaya kewaye da sarki, kowane mutum da makaminsa a hannu. Duk wanda ya kusace ku, ku kashe shi. Ku manne wa sarki duk inda ya tafi.” Komandodin sojoji suka yi yadda Yehohiyada firist ya umarta. Kowa ya ɗauki mutanensa, waɗanda za su kama aiki Asabbaci da waɗanda za su kama hutun Asabbaci, suka zo wurin Yehohiyada firist. Sai ya ba komandodin māsu da garkuwoyi da dā suke na Dawuda, waɗanda suke a cikin haikalin Ubangiji. Matsaran kuma kowa da makaminsa a hannu, suka tsaya kewaye da sarki, kusa da bagade da kuma haikali, daga gefen kudu zuwa gefen arewa na haikalin. Sai Yehohiyada ya fito da ɗan sarki ya sa masa rawani a kā; ya ba shi shafin alkawari, ya kuma furta shi sarki. Suka shafe shi da mai, mutane kuma suka yi ta tafi suka ihu, suna cewa, “Ran sarki yă daɗe.” Sa’ad da Ataliya ta ji surutun matsara da na mutane, sai ta tafi wurin mutanen a haikalin Ubangiji. Da ta duba sai ga sarki, tsaye kusa da ginshiƙi, bisa ga al’ada. Hafsoshi da masu busa suna tsaye kusa da sarki, dukan mutanen ƙasar kuma suna farin ciki suna busa ƙahoni. Sai Ataliya ta keta tufafinta ta tā da murya tana cewa, “Kai! Wannan cin amana ne! Ai, wannan cin amana ne!” Yehohiyada ya umarci komandodin sojoji waɗanda suke lura da mayaƙa, ya ce, “Ku fitar da ita daga cikinku, ku kuma kashe duk wanda ya bi ta.” Gama firist ɗin ya ce, “Kada a kashe ta a cikin haikalin Ubangiji.” Saboda haka suka kama ta yayinda ta kai inda dawakai sukan shiga filin fada, a can kuwa aka kashe ta. Sa’an nan Yehohiyada ya yi alkawari tsakanin Ubangiji da sarki da kuma mutane cewa za su zama mutanen Ubangiji. Ya kuma yi alkawari tsakanin sarki da mutane. Sai dukan mutanen ƙasar suka tafi haikalin Ba’al suka rushe shi. Suka farfasa bagadai da kuma gumaka, suka kuma kashe Mattan wanda yake firist na Ba’al a gaban bagade. Sa’an nan Yehohiyada firist ya sa matsara a haikalin Ubangiji. Ya tafi tare da komandodin sojoji, Keretawa, matsara da kuma dukan mutanen ƙasar, tare kuwa suka kawo sarki daga haikalin Ubangiji zuwa cikin fada, ta ƙofar matsara. Sarki kuwa ya ɗauki mazauninsa a bisa kursiyin sarauta, dukan mutanen ƙasar suka yi murna. Birnin ya sami salama don an kashe Ataliya da takobi a fada. Yowash yana da shekara bakwai sa’ad da ya fara mulki. A shekara ta bakwai ta Yehu, Yowash ya zama sarki, ya kuma yi mulki a Urushalima na tsawon shekaru arba’in. Sunan mahaifiyarsa Zibiya ce; daga Beyersheba. Yowash ya aikata abin da yake daidai a idon Ubangiji domin Yehohiyada firist ya koya masa. Amma fa ba a kawar da masujadan kan tuddai ba; mutane suka ci gaba da miƙa hadayu da kuma ƙona turare a kan tuddai. Yowash ya ce wa firistoci, “Ku tattara dukan kuɗin da ake kawo a matsayin hadayu masu tsarki na haikalin Ubangiji, kuɗin da aka tattara a ƙidaya, kuɗin da aka tattara daga wa’adin da mutum ya yi, da kuma kuɗin da aka kawo na yardan rai a haikali. Bari kowane firist yă karɓi kuɗi daga masu ajiya, sa’an nan a yi amfani da su a gyara duk wani abin da ya lalace a haikali.” Amma har zuwa shekara ta ashirin da uku ta mulkin Yowash, firistocin ba su yi gyara haikalin ba. Saboda haka Sarki Yowash ya kira Yehohiyada firist da sauran firistoci ya tambaye su ya ce, “Me ya sa ba kwa gyaran abubuwan da suka lalace a haikali? Kada ku sāke karɓan kuɗi daga masu ajiya, amma a miƙa su domin gyaran haikali.” Firistoci suka yarda cewa ba za su sāke karɓan kuɗi daga mutane ba, kuma ba za su yi gyaran haikalin da kansu ba. Yehohiyada firist ya ɗauki akwatin ya huda rami a murfinsa. Ya ajiye shi kusa da bagade a hannun dama na haikalin Ubangiji. Firistocin da suke tsaron ƙofar suka zuba dukan kuɗin da aka kawo a haikalin Ubangiji a cikin akwatin. Duk sa’ad da suka ga kuɗin sun ƙaru a akwatin, sai marubucin fada da babban firist, su ƙirga kuɗin da aka kawo a haikalin Ubangiji su sa a jakankuna. Sa’ad da suka ga kuɗin ya yi yawa, sai su ba wa waɗanda aka zaɓa su lura da aikin haikalin. Da shi suka biya waɗanda suka yi aiki a haikalin Ubangiji, su kafintoci, da magina, masu gini, da masu fasa duwatsu. Suka sayi katakai da sassaƙaƙƙun duwatsu domin gyaran haikalin Ubangiji, suka kuma biya duk waɗansu kuɗin gyaran haikalin. Ba a yi amfani da kuɗin da aka kawo a haikali don yin manyan kwanonin azurfa, lagwani, abin yayyafa ruwa, kakaki ko wani abu na zinariya, ko na azurfa domin haikalin Ubangiji ba; an ba ma’aikatan da suka gyara haikalin ne. Ba su bukaci wani bayani daga waɗanda aka ba wa kuɗin don su biya ma’aikatan ba, domin sun yi aikinsu da aminci. Ba a kawo kuɗi daga hadayun laifi da na hadayun zunubi a haikalin Ubangiji ba, waɗannan na firistoci ne. A wannan lokaci, Hazayel sarkin Aram ya haura, ya kai wa Gat hari, ya kuma ci ta da yaƙi. Sa’an nan ya juya don yă yaƙi Urushalima. Amma Yowash sarkin Yahuda ya kwashe tsarkakan kayan da kakanninsa, Yehoshafat, Yehoram da Ahaziya, sarakunan Yahuda suka keɓe, da kyautai da shi kansa ya keɓe, da kuma dukan azurfan da aka samu a ɗakunan ajiya haikalin Ubangiji da na fada, ya aika da su wa Hazayel sarkin Aram, shi kuma ya janye daga Urushalima. Game da sauran ayyukan mulkin Yowash da duk abin da ya yi, duk a rubuce suke a cikin littafin tarihin sarakunan Yahuda. Hafsoshinsa suka yi masa maƙarƙashiya suka kashe shi a Bet Millo, a kan hanyar da ta gangara zuwa Silla. Hafsoshin da suka kashe shi kuwa su ne Yozabad ɗan Shimeyat da Yehozabad ɗan Shomer. Ya mutu, aka kuma binne shi tare da kakanninsa a Birnin Dawuda. Sai Amaziya ɗansa ya gāje shi a matsayin sarki. A shekara ta ashirin da uku ta Yowash ɗan Ahaziya, sarkin Yahuda, Yehoyahaz ɗan Yehu, ya zama sarkin Isra’ila a Samariya, ya kuwa yi mulki shekaru goma sha bakwai. Ya aikata mugunta a gaban Ubangiji ta wurin bin zunuban Yerobowam ɗan Nebat, wanda ya sa Isra’ila ta aikata, bai kuwa guje musu ba. Saboda haka fushin Ubangiji ya ƙuna a kan Isra’ila, kuma da daɗewa ya sa su a ƙarƙashin ikon Hazayel sarkin Aram da Ben-Hadad ɗansa. Sai Yehoyahaz ya nemi tagomashin Ubangiji, Ubangiji kuwa ya saurare shi, domin ya gan irin matsin da sarkin Aram yake yi wa Isra’ila. Sai Ubangiji ya tā da mai ceto wa Isra’ila, suka kuma kuɓuta daga ikon Aram. Ta haka Isra’ilawa suka yi zama a gidajensu yadda suka yi a dā. Sai dai ba su bar yin zunuban gidan Yerobowam ba, wanda ya sa Isra’ila ta aikata; suka ci gaba da yinsu. Haka ma, ginshiƙin Ashera ta kasance a tsaye a cikin Samariya. Ba abin da ya rage na rundunar Yehoyahaz sai mahayan dawakai hamsin, kekunan yaƙi goma da kuma sojoji ƙasa dubu goma. Gama sarkin Aram ya hallaka sauran, ya kuma yi kaca-kaca da su kamar ƙura a masussuka. Game da sauran ayyukan mulkin Yehoyahaz, dukan abubuwan da ya yi da kuma nasarorinsa, duk a rubuce suke a cikin littafin tarihin sarakunan Isra’ila. Yehoyahaz ya huta da kakanninsa, aka binne shi a Samariya, Yehowash ɗansa kuma ya gāje shi. A shekaru talatin da bakwai ta Yowash sarkin Yahuda, Yehowash ɗan Yehoyahaz ya zama sarkin Isra’ila a Samariya, ya kuma yi mulki shekaru goma sha shida. Ya aikata mugunta a gaban Ubangiji, bai juya ga barin zunuban Yerobowam ɗan Nebat ba, wanda ya sa Isra’ila ta aikata, ya ci gaba da yinsu. Game da sauran ayyukan mulkin Yowash, da dukan abubuwan da ya yi, da kuma nasarorinsa, haɗe da yaƙin da ya yi da Amaziya sarkin Yahuda, duk a rubuce suke a cikin littafin tarihin sarakunan Isra’ila. Yowash ya huta da kakanninsa, Yerobowam kuwa ya gāje shi. Aka binne Yehowash a Samariya tare da sarakunan Isra’ila. To, Elisha ya kamu da ciwon da ya kashe shi. Yowash sarkin Isra’ila ya gangara don yă gan shi, ya kuma yi kuka dominsa. Ya yi kuka yana cewa, “Babana! Babana, keken yaƙin Isra’ila da mahayan dawakanta!” Elisha ya ce wa Yehowash, “Ka samo baka da kibiyoyi,” ya kuwa yi haka. Sai ya ce wa Yehowash sarkin Isra’ila, “Ka ɗauki baka a hannunka.” Da ya ɗauka, sai Elisha ya sa hannunsa a hannuwan sarki. Ya ce masa, “Ka buɗe taga wajen gabas,” sai ya buɗe. Sai Elisha ya ce, “Ka harba!” Sai ya harba. Elisha ya ce, “Kibiyar nasara ta Ubangiji, kibiyar nasara a kan Aram! Za ka hallaka Arameyawa sarai a Afek.” Sa’an nan ya ce, “Ka ɗauki kibiyoyi,” sai sarkin ya ɗauko. Sai Elisha ya ce, “Ka caki ƙasa.” Sai ya caka sau uku sa’an nan ya daina. Sai mutumin Allah ya yi fushi da shi ya ce, “Da a ce ka caki ƙasar sau biyar ko shida; da za ka yi nasara a kan Aram ka kuma hallaka ta sarai. Amma yanzu za ka yi nasara a kanta sau uku ne kawai.” Elisha ya mutu, aka kuma binne shi. To, mahara Mowabawa sun saba kawo hari a ƙasar Isra’ila a kowace bazara. Wata rana yayinda waɗansu Isra’ilawa suke binne wani mutum, farat ɗaya sai ga mahara; saboda haka suka jefar da gawar mutumin a kabarin Elisha. Da gawar ta taɓa ƙasusuwan Elisha, sai mutumin ya farka, ya tashi ya tsaya da ƙafafunsa. Hazayel sarkin Aram ya musguna wa Isra’ila a duk tsawon mulkin Yehoyahaz. Amma Ubangiji ya nuna musu alheri, ya ji tausayinsu, ya kuma damu da su saboda alkawarinsa da Ibrahim, Ishaku da Yaƙub. Har yă zuwa yau bai yarda yă hallaka su ko yă shafe su daga gabansa ba. Hazayel sarkin Aram ya mutu, sai Ben-Hadad ɗansa ya gāje shi. Sa’an nan Yowash ya sāke ƙwato garuruwan da Ben-Hadad ya ci da yaƙi a hannun mahaifinsa Yehoyahaz. Sau uku Yehowash ya yi nasara a kansa, ta haka kuwa ya ƙwace garuruwan Isra’ilawa. A shekara ta biyu ta mulkin Yehowash ɗan Yehoyahaz sarkin Isra’ila, Amaziya ɗan Yowash sarkin Yahuda ya fara mulki. Ya zama sarki yana da shekaru ashirin da biyar, ya kuma yi mulki a Urushalima shekaru ashirin da tara. Sunan mahaifiyarsa Yehoyaddin, mutuniyar Urushalima. Ya aikata abin da yake daidai a gaban Ubangiji, sai dai ba kamar kakansa Dawuda ba. A kome dai ya bi gurbin mahaifinsa Yowash. Ba a dai kawar da masujadan kan tudu ba; mutane suka ci gaba da yin hadaya da ƙone turare a can. Bayan masarauta ta kahu a hannunsa, sai ya kashe fadawan da suka kashe mahaifinsa sarki. Duk da haka bai kashe ’ya’yan masu kisan ba, bisa ga abin da yake a rubuce a Dokar Musa inda Ubangiji ya umarta, “Ba za a kashe iyaye saboda laifin ’ya’ya ba, ko kuma ’ya’ya saboda laifin iyayensu ba, kowa zai mutu don zunubansa.” Shi ne kuma wanda ya ci mutanen Edom dubu goma a yaƙi, a Kwarin Gishiri, ya kuma ci Sela da yaƙi, ya ba ta suna Yokteyel, sunan da ake kiranta har wa yau. Sai Amaziya ya aika ’yan aika wurin Yehowash ɗan Yehoyahaz, ɗan Yehu, sarkin Isra’ila, yana tsokanarsa cewa, “Zo, mu sadu fuska da fuska.” Amma Yehowash sarkin Isra’ila ya mai da martani wa Amaziya sarkin Yahuda ya ce, “Wata ’yar ƙaya a kurmin Lebanon ta aika da saƙo wurin itacen al’ul a Lebanon cewa, ‘Ka ba ɗana ’yarka aure.’ Amma wani naman jeji ya zo ya tattake ƙayar. Tabbatacce ka ci Edom da yaƙi, yanzu kuwa kana ɗaga kai. To, ka gode da darajar da ka samu, amma ka zauna a gida! Don me kake neman faɗa kana neman fāɗuwarka da kuma ta Yahuda?” Amma Amaziya bai saurara ba, saboda haka Yehowash sarkin Isra’ila ya kai masa hari. Shi da Amaziya sarkin Yahuda suka fuskanci juna a Bet-Shemesh. Isra’ila suka fatattaki Yahuda, kowa kuwa ya tsere zuwa gidansa. Yehowash sarkin Isra’ila ya kama Amaziya sarkin Yahuda, ɗan Yowash, ɗan Ahaziya, a Bet-Shemesh. Sa’an nan Yehowash ya tafi Urushalima ya rushe katangar Urushalima daga Ƙofar Efraim har zuwa Ƙofar Kusurwa, ratarta ta kai wajen ƙafa ɗari shida. Ya kwashi ɗaukan zinariya da azurfa da duk kayan da aka samu a haikalin Ubangiji da kuma ma’ajin fadan. Ya kuma kwashi bayi sa’an nan ya koma Samariya. Game da sauran ayyukan mulkin Yehowash, abin da ya yi da kuma nasarorinsa, haɗe da yaƙinsa da Amaziya sarkin Yahuda, duk a rubuce suke a cikin littafin tarihin sarakunan Isra’ila. Ya huta da kakanninsa aka kuma binne shi a Samariya tare da sarakunan Isra’ila. Yerobowam ɗansa, ya kuma gāje shi. Amaziya ɗan Yowash sarkin Yahuda ya yi shekaru goma sha biyar bayan mutuwar Yehowash ɗan Yehoyahaz sarkin Isra’ila. Game da sauran ayyukan mulkin Amaziya, duk a rubuce suke a cikin littafin tarihin sarakunan Yahuda. Suka ƙulla masa maƙarƙashiya a Urushalima, ya gudu zuwa Lakish, amma suka aika har Lakish aka kashe shi a can. Aka ɗauko shi a kan doki aka kawo shi Urushalima, aka kuwa binne shi tare da kakanninsa, a Birnin Dawuda. Sa’an nan dukan mutanen Yahuda suka ɗauki Azariya, wanda yake ɗan shekaru goma sha shida da haihuwa, suka naɗa shi sarki a madadin mahaifinsa Amaziya. Shi ne ya sāke gina Elat, ya kuma maido da ita a hannun Yahuda bayan Amaziya ya huta da kakanninsa. A shekara ta goma sha biyar ta mulkin Amaziya ɗan Yowash sarkin Yahuda, Yerobowam ɗan Yehowash sarkin Isra’ila ya zama sarki a Samariya, ya kuma yi mulki na shekaru arba’in da ɗaya. Ya aikata mugunta a gaban Ubangiji bai kuwa kauce wa duk zunuban Yerobowam ɗan Nebat, wanda ya sa Isra’ila ta aikata ba. Shi ne ya maido da iyakokin Isra’ila daga Lebo Hamat zuwa Tekun Araba, bisa ga maganar Ubangiji, Allah na Isra’ila, da ya yi ta bakin bawansa Yunana ɗan Amittai, annabi daga Gat-Hefer. Ubangiji ya ga irin muguwar wahalar da ta shafi kowa a Isra’ila, ko bawa ko ’yantacce, babu mai taimakonsu. Da yake kuma Ubangiji bai ce zai shafe sunan Isra’ila daga fuskar duniya ba, sai ya cece su ta hannun Yerobowam ɗan Yowash. Game da sauran ayyukan mulkin Yerobowam, da dukan abin da ya yi, da yaƙe-yaƙen da ya yi, haɗe da sāke ƙwato wa Isra’ila Damaskus da Hamat waɗanda suke a hannun Yahuda, duk a rubuce suke a cikin littafin tarihin sarakunan Isra’ila. Yerobowam ya huta da kakanninsa, sarakunan Isra’ila. Zakariya ɗansa kuwa ya gāje shi. A shekara ta ashirin da bakwai ta mulkin Yerobowam sarkin Isra’ila, Azariya ɗan Amaziya, sarkin Yahuda ya fara mulki. Yana da shekara goma sha shida sa’ad da ya zama sarki, ya kuma yi mulki a Urushalima shekara hamsin da biyu. Sunan mahaifiyarsa Yekoliya daga Urushalima. Ya aikata abin da yake daidai a gaban Ubangiji, yadda mahaifinsa Amaziya ya yi. Amma bai kawar da masujadan kan tudu ba; mutane kuwa suka yi ta yin hadaya da ƙona turare a can. Ubangiji ya sa wa sarki ciwon kuturta har mutuwarsa, ya kuma zauna a keɓe. Yotam ɗan sarki, shi ne ya gudanar da sha’anin fada, ya kuma shugabanci mutanen ƙasar. Game da sauran ayyukan mulkin Azariya, duk a rubuce suke a cikin littafin tarihin sarakunan Yahuda. Azariya ya huta tare da kakanninsa, aka kuma binne shi kusa da su a Birnin Dawuda. Yotam ɗansa, kuma ya gāje shi. A shekara ta talatin da takwas ta mulkin Azariya sarkin Yahuda, Zakariya ɗan Yerobowam ya zama sarkin Isra’ila a Samariya, ya kuma yi mulki wata shida. Ya aikata mugunta a gaban Ubangiji yadda mahaifinsa ya yi. Bai bar aikata zunuban Yerobowam ɗan Nebat, wanda ya sa Isra’ila suka yi ba. Sai Shallum ɗan Yabesh ya ƙulla wa Zakariya maƙarƙashiya. Ya tasam masa a gaban jama’a, ya kashe shi, ya kuma gāje shi. Game da sauran ayyukan mulkin Zakariya, duk a rubuce suke a cikin littafin tarihin sarakunan Isra’ila. Ta haka maganar Ubangiji da ya yi wa Yehu ta cika, wadda ya ce, “Zuriyarka za tă zauna a kursiyin Isra’ila har tsara ta huɗu.” Shallum ɗan Yabesh ya zama sarki a shekara ta talatin da tara ta mulkin Uzziya sarkin Yahuda, ya kuma yi mulki na wata ɗaya a Samariya. Sa’an nan Menahem ɗan Gadi ya gangara daga Tirza ya haura zuwa Samariya. Ya tasam wa Shallum ɗan Yabesh a Samariya, ya kashe shi, ya kuma gāje shi. Game da sauran ayyukan mulkin Shallum, duk a rubuce suke a cikin littafin tarihin sarakunan Isra’ila. A lokacin nan sai Menahem ya taso daga Tirza, ya kai wa Tifsa hari da kowa wanda yake a birnin da kewayenta, don sun ƙi su buɗe ƙofofinsu. Ya kori Tifsa daga aiki, ya kuma tsattsaga cikin dukan mata masu juna biyu. A shekara ta talatin da takwas ta mulkin Azariya sarkin Yahuda, Menahem ɗan Gadi ya zama sarkin Isra’ila, ya yi mulki a Samariya shekara goma. Ya aikata mugunta a gaban Ubangiji. A duk tsawon mulkinsa, bai rabu da zunuban da Yerobowam ɗan Nebat ya sa Isra’ila suka aikata ba. Sai Ful sarkin Assuriya ya kai wa ƙasar hari, Menahem kuwa ya ba shi talenti dubu na azurfa don yă sami goyon bayansa, yă kuma ƙarfafa kahuwa mulkin. Menahem ya tara kuɗin ne ta hanyar haraji a Isra’ila inda ya sa kowane attajiri ya ba da shekel hamsin don a ba sarkin Assuriya. Sa’an nan sarkin Assuriya ya janye, bai ƙara kasance a ƙasar ba. Game da sauran ayyukan mulkin Menahem, duk a rubuce suke a cikin littafin tarihin sarakunan Isra’ila. Menahem ya huta tare da kakanninsa. Fekahiya ɗansa kuma ya gāje shi. A shekara ta hamsin ta mulkin Azariya sarkin Yahuda, Fekahiya ɗan Menahem ya zama sarkin Isra’ila a Samariya, ya kuma yi mulki shekara biyu. Fekahiya ya aikata mugunta a gaban Ubangiji, bai rabu da zunuban Yerobowam ɗan Nebat wanda ya sa Isra’ila ya aikata ba. Ɗaya daga cikin manyan fadawansa, Feka ɗan Remaliya, ya ƙulla masa maƙarƙashiya. Ɗauke da mutanen Gileyad hamsin, ya kashe Fekahiya tare da Argob da kuma Ariye a fadan sarki a Samariya. Ta haka Feka ya kashe Fekahiya ya kuma gāje shi. Game da sauran ayyukan mulkin Fekahiya, duk a rubuce suke a cikin littafin tarihin sarakunan Isra’ila. A shekara ta hamsin da biyu ta mulkin Azariya sarkin Yahuda, Feka ɗan Remaliya ya zama sarkin Isra’ila a Samariya, ya yi mulki shekara ashirin. Ya aikata mugunta a gaban Ubangiji. Bai kauce wa zunuban Yerobowam ɗan Nebat, wanda ya sa Isra’ila ta yi ba. A zamanin Feka sarkin Isra’ila, Tiglat-Fileser sarkin Assuriya ya zo ya kama Iyon, Abel-Bet-Ma’aka, Yanowa da Kedesh da kuma Hazor. Ya kame Gileyad da Galili, haɗe da dukan ƙasar Naftali, ya kuma kwashi mutanen zuwa Assuriya. Sa’an nan Hosheya ɗan Ela ya ƙulla wa Feka ɗan Remaliya maƙarƙashiya. Ya fāɗa masa ya kuma kashe shi, sa’an nan ya gāje shi a matsayin sarki a shekara ta shirin ta mulkin Yotam ɗan Uzziya. Game da sauran ayyukan mulkin Feka da duk abin da ya yi, duk a rubuce suke a cikin littafin tarihin sarakunan Isra’ila. A shekara ta biyu ta mulkin Feka ɗan Remaliya sarkin Isra’ila, Yotam ɗan Uzziya sarkin Yahuda ya fara mulki. Ya zama sarki yana da shekara ashirin da biyar, ya kuma yi mulki a Urushalima shekara goma sha shida. Sunan mahaifiyarsa Yerusha, ’yar Zadok. Ya aikata abin da yake daidai a gaban Ubangiji yadda mahaifinsa Uzziya ya yi. Duk da haka, bai kawar da masujadan kan tudu ba; mutane suka ci gaba da yin hadaya da ƙona turare a can. Yotam ya sāke gina Ƙofar Bisa ta haikalin Ubangiji. Game da sauran ayyukan mulkin Yotam da aikin da ya yi, duk a rubuce suke a cikin littafin tarihin sarakunan Yahuda. (A kwanakin nan Ubangiji ya fara aikan Rezin sarkin Aram da Feka ɗan Remaliya, su yi gāba da Yahuda.) Yotam ya huta tare da kakanninsa, aka kuma binne shi tare da su a Birnin Dawuda, birnin mahaifinsa. Ahaz ɗansa kuma ya gāje shi. A shekara ta goma sha bakwai ta mulkin Feka ɗan Remaliya, Ahaz ɗan Yotam sarkin Yahuda ya fara mulki. Ahaz ya zama sarki yana da shekara ashirin, ya kuma yi mulki shekara goma sha shida a Urushalima ba kamar Dawuda mahaifinsa ba. Ahaz bai yi abin da yake daidai a gaban Ubangiji Allahnsa ba. Ya yi tafiya a hanyoyin sarakunan Isra’ila har ya miƙa ɗansa hadaya a wuta, yana bin hanyoyin banƙyama na al’ummai da Ubangiji ya kora a gaban Isra’ilawa. Ya miƙa hadaya, ya kuma ƙona turare a masujadan tudu, da kan tuddai, da kuma a ƙarƙashin kowane babban itace. Sai Rezin sarkin Aram, da Feka ɗan Remaliya sarkin Isra’ila suka haura don su kai wa Urushalima hari, suka kuma kewaye Ahaz, amma ba su iya shan ƙarfinsa ba. A wannan lokaci, Rezin sarkin Aram ya sāke ƙwato Elat wa Aram ta wurin korar Yahuda. Sa’an nan mutanen Edom suka mamaye Elat suna kuwa zaune a can har yau. Ahaz ya aika a faɗa wa Tiglat-Fileser sarkin Assuriya cewa, “Ni abokin tarayyarka ne kuma mai dogara da kai. Ka haura ka cece ni daga hannun sarkin Aram da hannun sarkin Isra’ila waɗanda suke kawo mini hari.” Ahaz ya ɗauki azurfa da zinariyar da suke a haikalin Ubangiji da suke kuma a ma’ajin fada ya aika wa sarkin Assuriya kyauta. Sai sarkin Assuriya ya ji roƙonsa. Ya tashi ya fāɗa wa Damaskus da hari ya kuma kame ta. Ya kwashi mazaunanta zuwa Kir, ya kuma kashe Rezin. Sa’an nan sarki Ahaz ya tafi Damaskus don yă sadu da Tiglat-Fileser sarkin Assuriya. Da ya kai can sai ya ga wani bagade a Damaskus, sai ya aika wa Uriya firist, da siffar bagaden, da fasalinsa, da cikakken bayanin bagaden. Saboda haka Uriya firist ya gina bagaden bisa ga tsarin da Sarki Ahaz ya aika masa daga Damaskus, ya kuma gama shi kafin Sarki Ahaz yă dawo. Da sarki ya dawo daga Damaskus ya ga bagaden, sai ya tafi kusa da shi ya kuma miƙa hadaya a bisansa. Ya miƙa hadayarsa ta ƙonawa da ta hatsi, ya zuba hadayarsa ta sha, ya kuma yayyafa jinin hadayunsa ta zumunci a bisa bagaden. Sai ya cire bagaden tagulla wanda aka keɓe ga Ubangiji, ya sa shi a gaban haikalin wato, tsakanin ƙofar shiga haikalin Ubangiji da sabon bagaden. Ya ajiye shi a gefen arewa na sabon bagaden. Sarkin Ahaz ya umarci Uriya cewa, “A kan babban sabon bagade, ka miƙa hadayar ƙonawa ta safe, da hadayar hatsi ta yamma, da hadayar sarki ta ƙonawa da hadayarsa ta hatsi, da hadaya ta dukan jama’ar ƙasar, tare da hadayan hatsinsu da kuma ta sha. Ka yayyafa jinin hadayun ƙonawa a kan bagade. Amma zan yi amfani da bagaden tagulla don neman bishewa.” Uriya firist kuwa ya yi duk abin da Sarki Ahaz ya umarta. Sarkin Ahaz ya kawar da katakon ya kuma ɗauke tasoshin daga mazauninsu da ake iya matsarwa. Ya ɗauke ƙaton kwano mai suna Teku daga kan bijiman tagullar da ya tallafe su ya ajiye a kan mazaunin dutse. Ya kawar da rumfa Asabbacin da aka gina a haikalin, ya kuma kawar da mashigin sarki na waje da haikalin Ubangiji, duk dai don yă gamshi sarkin Assuriya. Game da sauran ayyukan mulkin Ahaz, abubuwan da ya yi, duk a rubuce suke a cikin littafin tarihin sarakunan Yahuda. Ahaz ya huta tare da kakanninsa, aka kuma binne shi da su a Birnin Dawuda. Hezekiya ɗansa kuma ya gāje shi. A shekara ta goma sha biyu ta mulkin Ahaz sarkin Yahuda, Hosheya ɗan Ela ya zama sarkin Isra’ila a Samariya, ya kuma yi mulki na shekara tara. Ya aikata mugunta a gaban Ubangiji, amma ba kamar na sarakunan Isra’ilan da suka riga shi ba. Shalmaneser sarkin Assuriya ya kawo wa Hosheya wanda dā abokin tarayyarsa ne, hari har Hosheya ya biya shi haraji. Amma sarkin Assuriya ya gane cewa Hosheya mai cin amana ne, gama ya aika da wakilai wurin So sarkin Masar, ya kuma daina aika wa sarkin Assuriya haraji yadda ya saba yi kowace shekara. Saboda haka Shalmaneser ya kama shi ya sa a kurkuku. Sarkin Assuriya ya kai wa ƙasar Hosheya gaba ɗaya farmaki, ya kewaye Samariya na tsawon shekara uku. A shekara ta tara ta sarautar Hosheya, sarkin Assuriya ya ci Samariya da yaƙi ya kuma kwashe Isra’ilawa zuwa Assuriya. Ya tsugunar da su a Hala, da a Gozan a bakin Kogin Habor da kuma a garuruwan Medes. Duk wannan ya faru ne saboda Isra’ilawa sun yi wa Ubangiji Allahnsu zunubi, shi wanda ya fitar da su daga Masar daga ƙarƙashin ikon Fir’auna sarkin Masar. Sun yi wa waɗansu alloli sujada suka kuma bi gurbin al’umman da Ubangiji ya kora a gabansu, da kuma ayyukan da sarakuna Isra’ila suka gabatar. Isra’ilawa a ɓoye sun aikata abubuwan da ba daidai ba ga Ubangiji Allahnsu. Tun daga hasumiyoyi har zuwa birane masu katanga, sun gina wa kansu wuraren sujada na tudu a dukan garuruwansu. Suka kafa keɓaɓɓun duwatsu da kuma ginshiƙan Ashera a kowane tudu mai tsayi da kuma a ƙarƙashin kowane babban itace. Suka ƙona turare a kan kowane tudu, kamar dai yadda al’umman da Ubangiji ya kora daga gabansu suka yi. Suka yi muguntan da ya sa Ubangiji ya yi fushi. Suka bauta wa gumaka, ko da yake Ubangiji ya ce, “Ba za ku yi wannan ba.” Ubangiji ya yi wa Isra’ila da Yahuda kashedi ta bakin dukan annabawansa da kuma masu duba, cewa, “Ku juyo daga mugayen ayyukanku. Ku yi biyayya da umarnai da farillaina, bisa ga dukan Dokar da na dokaci kakanninku su bi, waɗanda na kuma bayar ta wurin bayina, annabawa.” Amma ba su saurare ni ba don sun kangare kamar kakanninsu, waɗanda ba su amince da Ubangiji Allahnsu ba. Suka yi watsi da farillansa da yarjejjeniyar da ya ƙulla da kakanninsu, da kuma kashedin da ya yi musu. Suka bi gumaka marasa amfani, wannan ya sa su ma kansu suka zama marasa amfani. Suka kwaikwayi sauran ƙasashen da suke kewaye da su, ko da yake Ubangiji ya umarce su cewa, “Kada ku yi rayuwa irin tasu,” suka kuwa yi abin da Ubangiji ya hana su. Suka wofinta dukan umarnan Ubangiji Allahnsu, suka yi wa kansu gumakan zubi na siffar ’yan maruƙa biyu, da kuma ginshiƙin Ashera. Suka rusuna wa rundunan taurari, suka kuma yi wa Ba’al sujada. Suka miƙa ’ya’yansu maza da mata hadaya ta wuta. Suka yi duba, suka yi sihiri suka kuma ba da kansu ga mugunta a gaban Ubangiji; suka sa ya yi fushi. Saboda haka Ubangiji ya yi fushi ƙwarai da Isra’ila, ya kuma kawar da su daga gabansa. Kabilar Yahuda kaɗai aka bari, ko Yahuda ma ba su kiyaye umarnan Ubangiji Allahnsu ba. Sun bi gurbin da Isra’ila ta kawo. Saboda haka Ubangiji ya wofinta mutanen Isra’ila; ya azabtar da su, ya kuma ba da su a hannun masu kwasar ganima, sai da ya shafe su ƙaƙaf daga gabansa. Sa’ad da ya ware Isra’ila daga gidan Dawuda, sai suka naɗa Yerobowam ɗan Nebat sarki a kansu. Yerobowam ya rinjayi Isra’ila daga ƙin Ubangiji, ya sa suka aikata babban zunubi. Isra’ila suka nace cikin dukan zunuban Yerobowam, ba su kuwa rabu da su ba har Ubangiji ya kawar da su daga gabansa, kamar yadda ya gargaɗe su ta bakin bayinsa annabawa. Saboda haka aka kwashi mutanen Isra’ila daga ƙasarsu zuwa bauta a Assuriya, har wa yau kuwa suna can. Sarkin Assuriya ya kawo mutane daga Babilon, Kuta, Afa, Hamat da Sefarfayim ya zaunar da su a garuruwan Samariya don su maya gurbin Isra’ilawa. Suka mallaki Samariya suka kuma zauna a garuruwansu. Sa’ad da suka fara zama a can, ba su bauta wa Ubangiji ba; saboda haka ya aika da zakoki a tsakaninsu suka karkashe waɗansu mutane. Sai aka faɗa wa sarkin Assuriya cewa, “Mutanen da ka kwashe ka zaunar a garuruwan Samariya fa ba su san abin da allahn ƙasar yake bukata ba. Saboda haka allahn ƙasar ya tura zakoki a cikinsu, waɗanda suke karkashe su, domin mutanen ba su san abin da yake bukata ba.” Sai sarkin Assuriya ya ba da umarni cewa, “A sami wani daga cikin firistocin da aka kwaso zuwa bauta daga Samariya, yă koma yă zauna a can, yă koya wa mutanen abin da allahn ƙasar yake bukata.” Saboda haka ɗaya daga cikin firistocin da aka kawo bauta daga Samariya ya dawo ya zauna a Betel, ya koya musu yadda za su yi sujada ga Ubangiji. Duk da haka, jama’ar kowace ƙasa, suka ƙera tasu alloli a garuruwa masu yawa inda suke zaune, suka sa su a masujadan da mutanen Samariya suka gina a kan tuddai. Mutane daga Babilon suka ƙera Sukkot Benot, mutane daga Kut suka ƙera Nergal, mutane daga Hamat suka ƙera Ashima; Awwiyawa suka ƙera Nibhaz da Tartak, Sefarfayawa kuwa suka ƙone ’ya’yansu a wuta a matsayi hadayu ga Adrammelek da Anammelek allolin Sefarfayim. Sun yi wa Ubangiji sujada, amma kuma suka zaɓi mutanensu su yi musu hidima a matsayin firistoci a masujadan da suke kan tuddai. Sun yi wa Ubangiji sujada, amma kuma sun bauta wa allolinsu bisa ga al’adun ƙasashen da suka fito. Har yă zuwa yau, sun nace da ayyukansu na dā. Ba sa yin wa Ubangiji sujada, ba sa kuma bin dokoki da farillansa, dokoki da umarnan da Ubangiji ya ba wa zuriyar Yaƙub, wadda ya ba wa suna Isra’ila. Da Ubangiji ya ƙulla alkawari da Isra’ilawa, ya dokace su cewa, “Kada ku yi wa waɗansu alloli sujada ko ku durƙusa a gabansu ku bauta musu, ko ku miƙa musu hadaya. Amma Ubangiji wanda ya fito da ku daga Masar da iko mai girma da hannu mai ƙarfi, shi ne za ku yi masa sujada. Gare shi za ku durƙusa ku kuma miƙa masa hadayu. Dole kullum ku mai da hankali ga kiyaye ƙa’idodi da farillan, dokoki da umarnan da ya rubuta muku. Kada ku yi wa waɗansu alloli sujada. Kada ku manta da alkawarin da na ƙulla da ku, kada ku yi sujada ga waɗansu alloli. Maimakon haka, ku yi wa Ubangiji Allahnku sujada; shi ne zai cece ku daga hannun abokan gābanku.” Amma ba su saurara ba, suka nace da ayyukansu na dā. Ko ma yayinda mutanen nan suke yi wa Ubangiji sujada, ba su daina bauta wa gumakansu ba. Har yă zuwa yau, ’ya’yansu da jikokinsu sun ci gaba da bin gurbin kakanninsu. A shekara ta uku ta mulkin Hosheya ɗan Ela sarkin Isra’ila, Hezekiya ɗan Ahaz sarkin Yahuda ya fara mulki. Yana da shekara ashirin da biyar da ya zama sarki, ya kuma yi mulki shekara ashirin da tara a Urushalima. Sunan mahaifiyarsa Abiya ’yar Zakariya. Ya aikata abin da yake daidai a gaban Ubangiji yadda kakansa Dawuda ya yi. Ya kawar da masujadan kan tudu, ya farfasa keɓaɓɓun duwatsu, ya sassare ginshiƙan Ashera. Ya fashe macijin tagullan da Musa ya yi, gama har zuwa lokacin nan Isra’ilawa suna ƙona turare gare shi. (An ba shi suna Nehushtan.) Hezekiya ya dogara ga Ubangiji, Allah na Isra’ila. Ba a yi wani kamar sa ba cikin dukan sarakunan Yahuda; ko kafin shi, ko kuma bayansa. Ya manne wa Ubangiji, bai fasa binsa ba; ya yi biyayya da dokokin da Ubangiji ya ba wa Musa. Ubangiji kuma ya kasance tare da shi, ya yi nasara a duk abin da ya sa hannu. Ya yi tawaye ga sarkin Assuriya, ya ƙi yă bauta masa. Daga hasumiya zuwa birni mai katanga, ya ci Filistiyawa da yaƙi, har zuwa Gaza da kewaye. A shekara ta huɗu ta Hezekiya, wato, shekara ta bakwai ke nan ta mulkin Hosheya ɗan Ela sarkin Isra’ila; Shalmaneser Sarkin Assuriya ya tasam ma Samariya da yaƙi; ya kewaye ta. A ƙarshen shekara ta uku, Assuriyawa suka ci Samariya da yaƙi. An ci Samariya da yaƙi a shekara ta shida ta mulki Hezekiya, wanda ya zo daidai da shekara ta tara ta mulkin Hosheya sarkin Isra’ila. Sarkin Assuriya ya kwashe Isra’ila zuwa Assuriya ya zaunar da su a Hala, da Gozan a kogin Habor da kuma garuruwan Medes. Wannan ya faru ne domin ba su yi biyayya ga Ubangiji Allahnsu ba, amma suka karya alkawarinsu; da dukan abin da Musa bawan Ubangiji ya umarta. Ba su saurari umarnin ba, balle su kiyaye su. A shekara ta goma sha huɗu ta mulkin sarkin Hezekiya, sai sarki Sennakerib sarkin Assuriya ya kai farmaki wa biranen Yahuda masu katanga ya kuma kama su. Sai Hezekiya sarkin Yahuda ya aika saƙo ga sarkin Assuriya a Lakish cewa, “Na yi laifi, ka janye daga gare ni, zan kuma biya ka duk abin da ake bukata daga gare ni.” Sarkin Assuriya ya karɓi talenti ɗari uku na azurfa, da talenti talatin na zinariya daga hannun Hezekiya sarkin Yahuda. Ya zama kuwa cewa, Hezekiya ya bayar da dukan azurfan da suke a haikalin Ubangiji da kuma a ma’ajin fadan sarki. A wannan lokaci ne Hezekiya sarkin Yahuda ya ɓaɓɓalle zinariyan da aka dalaye ƙofofi da madogaran ƙofofin haikalin Ubangiji, ya ba sarkin Assuriya. Sai sarkin Assuriya ya aika da babban shugaban sojojinsa, da shugaban dattawansa, da wakilinsa daga birnin Lakish tare da ƙungiyar sojoji masu yawa zuwa Urushalima domin su yaƙi Sarki Hezekiya. Da suka haura sai suka tsaya a wurin lambatun da yake kawo ruwa daga Tafkin Tudu, kusa da hanyar Filin Mai Wanki. Suka kira sarki, sai Eliyakim ɗan Hilkiya sarkin fada, da Shebna magatakarda, da Yowa ɗan Asaf marubuci suka je wurinsu. Jagoran dogarawan sarkin Assuriya ya ce musu, “Ku ce wa Hezekiya, “ ‘Ga abin da babban sarkin Assuriya ya ce, da wa kake taƙama? Ka ce kana da dabara da ƙarfin soji, amma bagu kawai kake yi. Da wa ka dogara har da za ka yi mini tawaye? Na sani kana dogara da Masar, wadda take kamar karar masara, wadda in ka jingina a kai, za tă karye tă soki hannunka. Haka Fir’auna sarkin Masar yake ga dukan wanda ya dogara da shi. Sai ya ci gaba da cewa, in kuma ka ce mini “Muna dogara ga Ubangiji Allahnmu ne,” ba masujadansa da bagadansa ne Hezekiya ya ciccire, yana ce wa Urushalima da Yahuda, “Dole ku yi sujada a gaban wannan bagade a Urushalima”? “ ‘Yanzu, ka zo ku shirya da shugabana, sarkin Assuriya. Zan ba ka dawakai dubu biyu, in za ka sami mahayansu! Yaya za ka yi tsayayya da mafi ƙanƙantan hafsan shugabana, ko da kana dogara da Masar don kekunan yaƙi da mahaya dawakai? Ban da haka ma, kana gani cewa na zo in hallaka wannan wuri ne ba tare da na ji daga Ubangiji ba? Ubangiji da kansa ne ya ce da ni in kawo wa wannan ƙasa hari in hallaka ta.’ ” Sai Eliyakim ɗan Hilkiya, da Shebna, da Yowa suka ce wa jagoran dakarun, “Muna roƙonka ka yi wa bayinka magana da harshen Arameyik da yake muna ji. Kada ka yi mana magana da Yahudanci domin kada mutanen da suke bisa katanga su ji!” Amma shugaban sojojin ya ce, “Ai, ba gare ku da sarkinku kaɗai ne shugabana ya aike ni ba. Amma har ga mutanen da suke zaune a kan katangar birnin, waɗanda za su ci kashinsu, su sha fitsarinsu!” Sai shugaban sojojin ya yi kira da Yahudanci ya ce, “Ku ji muryar babban sarki, sarkin Assuriya! Ga abin da sarki ya faɗa; kada ku bar Hezekiya yă ruɗe ku. Ba zai iya cetonku daga hannuna ba. Kada ku yarda Hezekiya yă rinjaye ku cewa ku dogara ga Allah, sa’ad da ya ce da ku, ‘Ba shakka Ubangiji zai cece mu; yana ce da ku birnin nan ba zai faɗa a hannun sarkin Assuriya ba.’ “Kada ku saurari Hezekiya. Ga abin da sarkin Assuriya ya ce, ku shirya zaman lafiya da ni, ku fito zuwa wurina. Kowane ɗayanku kuwa zai ci ’ya’yan inabinsa da ’ya’yan ɓaurensa, yă kuma sha ruwa daga randarsa, har lokacin da zan zo in kwashe ku, in kai ku wata ƙasa mai kama da taku, ƙasa mai yalwar hatsi, da ruwan inabi, da abinci, da gonakin inabi, da itatuwan zaitun, da zuma, don ku rayu, kada ku mutu! “Kada ku saurari Hezekiya, don karya yake muku, sa’ad da ya ce, ‘Ubangiji zai cece mu.’ Akwai allahn wata al’ummar da ya taɓa ceton ƙasarsa daga hannun sarkin Assuriya? Ina allolin Hamat da na Arfad? Ina allolin Sefarfayim, da na Hena, da na Iffa? Sun cece Samariya daga hannuna? Wanne a cikin dukan allolin ƙasashen nan ya iya ceton ƙasarsa da gare ni? Shugaban sojojin ya kuma ci gaba da cewa, ta yaya Ubangiji zai ceci Urushalima daga hannuna?” Amma mutane suka yi shiru ba su amsa masa ba, domin sarki ya umarta cewa, “Kada ku amsa masa.” Sai Eliyakim ɗan Hilkiya, sarkin fada, da Shebna magatakarda, da Yowa ɗan Asaf, marubuci, suka je wurin Hezekiya da tufafinsu a kece, suka faɗa masa abin da shugaban sojojin ya faɗa. Da sarki Hezekiya ya ji haka, sai ya kyakketa tufafinsa, ya sa tufafin makoki, ya shiga haikalin Ubangiji. Ya aiki Eliyakim sarkin fada, Shebna marubuci da shugabannin firistoci, dukansu sanye da tufafin makoki, zuwa wurin annabi Ishaya ɗan Amoz. Suka ce masa, “Hezekiya ya ce, yau ranar wahala ce, da ta cin mutunci, da ta shan kunya, ga shi, ’ya’ya suna gab da a haife su, amma ba ƙarfin da za a yi yunƙuri a haife su. Mai yiwuwa Ubangiji Allahnka ya ji dukan maganganun sarkin yaƙi, wanda maigidansa, sarkin Assuriya, ya aiko don yă rena Allah mai rai. Bari Ubangiji Allahnka yă tsawata masa saboda maganar da ya ji. Saboda haka ka yi addu’a domin raguwar da har yanzu suke a raye.” Da fadawan sarki Hezekiya suka isa wurin Ishaya, Ishaya ya ce musu, “Ku faɗa wa maigidanku, in ji Ubangiji, ‘Kada abin da ka ji yă firgita ka, wato, waɗannan kalmomin da karen nan na sarkin Assuriya ya yi saɓo da su. Saurara! Zan sa masa wani ruhun da zai sa yă ji wata jita-jitar da za tă sa yă koma ƙasarsa. A can zan sa a kashe shi da takobi a ƙasarsa.’ ” Da sarkin yaƙin ya ji cewa sarkin Assuriya ya bar Lakish, sai ya janye, ya kuma iske sarkin yana yaƙi da Libna. To, Sennakerib ya sami labari cewa Tirhaka, mutumin Kush sarkin Masar, yana zuwa masa da yaƙi. Saboda haka ya sāke aika manzanni zuwa wurin Hezekiya cewa, “Ku faɗa wa Hezekiya sarkin Yahuda, kada ka bar allahn da kake dogara gare shi yă ruɗe ka cewa, ‘Urushalima ba za tă fāɗi a hannun sarkin Assuriya ba.’ Ba shakka ka riga ka ji abin da sarkin Assuriya ya yi da dukan ƙasashe, yana hallaka su gaba ɗaya. Kai kuwa kana ji za a cece ka? Allolin al’umman da kakannina suka hallaka, sun cece su ne, allolin Gozan, da na Haran, da na Rezef, da kuma na mutane Eden da suke a Tel Assar? Ina sarkin Hamat, da sarkin Arfad, da sarkin birnin Sefarfayim, ko na Hena da kuma na Iffa?” Hezekiya ya karɓi wasiƙar daga manzannin ya karanta. Sa’an nan ya tashi ya tafi haikalin Ubangiji ya shimfiɗa wasiƙar a gaban Ubangiji. Hezekiya kuwa ya yi addu’a ga Ubangiji ya ce, “Ya Ubangiji, Allah na Isra’ila, wanda yake zaune tsakanin kerubobi, kai kaɗai ne Allah bisa dukan mulkokin duniya. Kai ka yi sama da duniya. Ka kasa kunne, ya Ubangiji, ka ji; ka buɗe idanunka ya Ubangiji ka gani; ka saurari kalmomin da Sennakerib ya aiko don yă yi wa Allah mai rai ba’a. “Da gaske ne, ya Ubangiji, cewa sarakunan Assuriya sun hallakar da waɗannan al’ummai da ƙasashensu. Sun jefar da allolinsu cikin wuta, suka hallaka su, gama ba alloli ba ne, katakai ne da kuma duwatsu, ayyukan hannuwan mutane. To, ya Ubangiji Allahnmu, ka cece mu daga hannunsa, don dukan mulkokin duniya su san cewa kai kaɗai, ya Ubangiji ne Allah.” Sai Ishaya ɗan Amoz ya aika da saƙo zuwa wurin Hezekiya cewa, “Ga abin da Ubangiji, Allah na Isra’ila ya ce, na ji addu’arka game da Sennakerib sarkin Assuriya. Ga abin da Ubangiji yana cewa game da shi, “ ‘Budurwar Sihiyona ta rena ka tana kuma yin maka ba’a. Diyar Urushalima ta kaɗa kanta yayinda kake gudu. Wane ne ka zaga, ka kuma yi masa saɓo? Wa kake gāba da shi har ka ɗaga muryarka, har ka tā da idanunka da fahariya? Kana gāba da Mai Tsarki na Isra’ila! Ta wurin manzanninka ka tara wa Ubangiji zagi. Ka kuma ce, “Da yawa kekunan yaƙina na haye kan ƙwanƙolin duwatsu, wurin mafi tsawo na Lebanon. Na sassare itacen al’ul nasa mafi tsawo mafi daraja na itacen fir nasa. Na ratsa har can tsakiyar kurmi, mafi kyau na kurminsa. Na tona rijiyoyi a ƙasashen waje na kuma sha ruwa a can. Da tafin ƙafafuna na busar da dukan rafuffukan Masar.” “ ‘Ba ka taɓa ji ba? Tun da daɗewa na ƙaddara haka. Tuntuni kuwa na shirya shi; yanzu kuma na sa ya faru, cewa ka mai da birane masu katanga tarin duwatsu. Ƙarfin mutanensu ya tsiyaye, suka razana aka kuma kunyata su. Suna kama da tsirai a gona, kamar sabon toho kamar ciyawa mai tohuwa bisa rufin ɗaki wanda ya bushe saboda zafi, kafin yă yi girma. “ ‘Amma na san wurin zamanka da fitarka da shigarka da yadda kake fushi da ni. Domin kana fushi da ni reninka ya iso kunnuwata, zan sa ƙugiyata a hancinka da linzamina a bakinka, zan kuma sa ka koma a ta hanyar da ka zo.’ “Wannan zai zama alama a gare ka, ya Hezekiya, “Bana, za ku ci amfanin gonar da ya tsira da kansa, baɗi kuma amfanin gonar da ya tsiro daga na bara. Amma a shekara ta uku, za ku yi shuki, ku kuma girbe, ku dasa gonakin inabi, ku kuma ci ’ya’yansa. Sau ɗaya kuma ragowar masarautar Yahuda za tă yi saiwoyi a ƙasa ta kuma ba da ’ya’ya a bisa. Gama daga Urushalima za a sami ragowa, daga Dutsen Sihiyona kuma za a sami waɗanda suka tsira. Himmar Ubangiji Maɗaukaki za tă cika wannan. “Saboda haka ga abin da Ubangiji ya ce game da sarkin Assuriya, “Ba zai shiga birnin nan ba ko yă harba kibiya a nan. Ba zai kusace ta da garkuwa ko yă yi mata zoben yaƙi ba. Ta hanyar da ya zo ne zai koma; ba zai shiga birnin nan ba, in ji Ubangiji. Zan kāre birnin nan in cece ta, saboda kaina da kuma bawana Dawuda.” A daren nan mala’ikan Ubangiji ya fita ya kashe dakaru dubu ɗari da tamanin da biyu a sansanin Assuriyawa. Da mutane suka farka da safe, sai ga gawawwaki ko’ina. Saboda haka Sennakerib sarkin Assuriya ya tā da sansanin ya kuma janye. Ya koma Ninebe ya zauna a can. Wata rana yayinda yake sujada a haikalin Nisrok, allahnsa, sai ’ya’yansa maza, Adrammelek da Sharezer suka kashe shi da takobi, suka gudu zuwa ƙasar Ararat. Sai Esar-Haddon ɗansa ya gāje shi. A kwanakin nan sai Hezekiya ya kamu da rashin lafiya har ya kusa mutuwa. Sai annabi Ishaya ɗan Amoz ya zo wurinsa ya ce, “Ga abin da Ubangiji ya ce, ka kintsa gidanka domin za ka mutu, ba za ka warke ba.” Hezekiya ya juya fuskarsa wajen bango ya yi addu’a ga Ubangiji ya ce, “Ya Ubangiji, ka tuna yadda na yi tafiya a gabanka da aminci da zuciya ɗaya, na kuma aikata abin da yake daidai a gabanka.” Sai Hezekiya ya yi kuka mai zafi. Kafin Ishaya yă bar tsakiyar filin gida, sai maganar Ubangiji ta zo masa cewa, “Ka koma ka ce wa Hezekiya, shugaban mutanena, ‘Ga abin da Ubangiji Allah na mahaifinka Dawuda ya ce, na ji addu’arka na kuma ga hawayenka; zan warkar da kai. A rana ta uku daga yau za ka haura zuwa haikalin Ubangiji. Zan ƙara maka shekara goma sha biyar. Zan kuma cece ka daga hannun sarkin Assuriya. Zan kāre birnin nan saboda kaina da kuma bawana Dawuda.’ ” Sai Ishaya ya ce, “A kwaɓa ɓaure.” Sai aka yi haka, aka shafa wa marurun, ya kuma warke. Hezekiya ya tambayi Ishaya, “Wace alama ce za tă nuna cewa Ubangiji zai warkar da ni, kuma cewa in tafi haikalin Ubangiji kwana uku daga yanzu?” Sai Ishaya ya ce, “Ga alamar Ubangiji zuwa gare ka da za tă nuna cewa Ubangiji zai cika alkawarinsa. Kana so inuwa tă yi gaba da taki goma, ko tă koma baya da taki goma?” “Ai, abu mai sauƙi ne inuwa tă yi gaba da taki goma.” In ji Hezekiya, “Gwamma dai tă koma baya da taki goma.” Sai annabi Ishaya ya roƙi Ubangiji, Ubangiji kuwa ya sa inuwa ta koma baya da taki goma bisa ga magwajin rana wanda Sarki Ahaz ya gina. A wannan lokaci, Merodak-Baladan ɗan Baladan sarkin Babilon ya aika wa Hezekiya wasiƙu tare da kyauta, domin ya sami labarin rashin lafiyar Hezekiya. Hezekiya ya karɓi jakadun, ya nuna musu dukan abin da yake a ɗakunan ajiyarsa, azurfa, zinariya, kayan ƙanshi da mai, wurin ajiye makamansa da kuma dukan abin da aka samu a ɗakin ajiyarsa. Babu wani abu a fadansa ko a dukan mulkinsa da Hezekiya bai nuna musu ba. Sai annabi Ishaya ya tafi wurin Sarki Hezekiya ya tambaye shi ya ce, “Me mutanen nan suka ce, kuma daga ina suka fito?” Sai Hezekiya ya ce, “Daga ƙasa mai nisa. Daga Babilon.” Annabin ya yi tambaya, “Me suka gani a fadanka?” Hezekiya ya ce, “Ba abin da yake a ma’ajina da ban nuna musu ba.” Sai Ishaya ya ce wa Hezekiya, “Ka ji kalmar Ubangiji. Lokaci yana zuwa da za a kwashe kome a fadanka da kuma dukan abubuwan da kakanninka suka tara har yă zuwa yau, a kai su Babilon. Ba abin da za a rage, in ji Ubangiji. Za a kuma kwashe waɗansu daga cikin zuriyarka, na jiki da jininka waɗanda za a haifa maka, su zama bābānni a fadan sarkin Babilon.” Hezekiya ya ce, “Maganar Ubangiji da ka faɗa ta yi kyau.” Gama ya yi tunani cewa, “Ai, ba ni da damuwa, tun da yake za a yi zaman lafiya da salama a kwanakina.” Game da sauran ayyukan mulkin Hezekiya, dukan nasarorinsa da yadda ya yi tafki da kuma bututun ruwa inda ya kawo ruwa cikin birni, duk a rubuce suke a cikin littafin tarihin sarakunan Yahuda. Hezekiya ya huta tare da kakanninsa. Manasse ɗansa kuma ya gāje shi. Manasse yana da shekara goma sha biyu sa’ad da ya zama sarki, ya yi mulki shekara hamsin da biyar a Urushalima. Sunan mahaifiyarsa Hefziba. Ya aikata mugunta a gaban Ubangiji, ya bi munanan al’adun al’umman da Ubangiji ya kora a gaban Isra’ilawa. Ya sāke gina masujadan da mahaifinsa Hezekiya ya rurrushe. Ya kuma gina wa Ba’al bagadai. Ya kafa ginshiƙin Ashera kamar yadda Ahab sarkin Isra’ila ya yi. Ya durƙusa wa dukan rundunan taurari ya yi musu sujada. Ya gina bagadai a haikalin Ubangiji, wurin da Ubangiji ya ce, “A Urushalima ne zan sa Sunana.” Cikin filaye biyu na haikalin Ubangiji kuwa, ya gina bagadai na dukan rundunan taurari. Ya miƙa ɗansa hadaya ta ƙonawa, ya yi sihiri da tsubu, ya tuntuɓi masu duba da masu ruhohi. Ya aikata mugunta ƙwarai a gaban Ubangiji, ya sa Ubangiji ya yi fushi. Ya ɗauki siffar ginshiƙin Asherar da ya yi, ya sa a haikalin da Ubangiji ya ce wa Dawuda da ɗansa Solomon, “A cikin wannan haikali, da kuma cikin Urushalima inda na zaɓa daga kabilan Isra’ila, zan sa Sunana har abada. Ba zan ƙara sa Isra’ilawa su fita daga ƙasar da na ba kakanninsu ba, idan dai za su kula su aikata dukan abin da na umarce su, su kuma kiyaye dukan dokokin da na ba wa bawana Musa yă umarce su.” Amma mutanen ba su kasa kunne ba. Manasse ya ɓad da su, har suka yi muguntar da ta fi ta al’umman da Ubangiji ya hallaka a gaban Isra’ilawa. Ubangiji ya yi magana ta bakin bayinsa annabawa, “Manasse, sarkin Yahuda ya aikata waɗannan ƙazantattun zunubai. Ya aikata mugunta fiye da ta Amoriyawan da suka riga shi, ya kuma sa Yahuda ta bauɗe ta wurin yin zunubi saboda gumakansa. Saboda haka ga abin da Ubangiji, Allah na Isra’ila ya ce, zan jawo wa Urushalima da kuma Yahuda masifar da duk kunnen da ya ji, sai ya kusa suma. Zan auna Urushalima da ma’aunin da na yi amfani da shi a kan Samariya, zan kuma yi amfani da magwajin da na yi amfani da shi a kan gidan Ahab. Zan shafe Urushalima yadda mutum yake wanke kwano yă kife. Zan rabu da ragowar gādona, in kuma miƙa su ga maƙiyansu. Abokan gābansu za su washe suka kuma kwashi ganima daga gare su, domin sun aikata mugunta a idanuna, suka kuma tsokane ni tun daga ranar da kakanninsu suka fito daga Masar, har yă zuwa yau.” Ban da haka ma, Manasse ya zub da jinin marasa laifi har ya cika Urushalima daga wannan ɓangare zuwa wancan, ban da zunubin da ya sa Yahuda ta aikata, ta haka suka yi mugunta a gaban Ubangiji. Game da sauran ayyukan mulkin Manasse, da duk abin da ya yi, har da zunubin da ya aikata, duk a rubuce suke a cikin littafin tarihin sarakunan Yahuda. Manasse ya huta tare da kakanninsa, aka kuma binne shi a lambun fadansa, lambun Uzza. Sai Amon ɗansa ya gāje shi. Amon yana da shekara ashirin da biyu sa’ad da ya zama sarki, ya yi mulki shekara biyu a Urushalima. Sunan mahaifiyarsa Meshullemet ’yar Haruz; ita mutuniyar Yotba ce. Ya aikata mugunta a gaban Ubangiji, yadda Manasse mahaifinsa ya yi. Ya bi duk gurbin mahaifinsa a kome, ya yi sujada ga gumakan da mahaifinsa ya yi wa, ya kuma durƙusa musu. Ya rabu da Ubangiji Allah na kakanninsa, bai kuwa yi tafiya a hanyar Ubangiji ba. Fadawan Amon suka ƙulla maƙarƙashiya suka kashe shi a cikin fadarsa. Sai mutanen ƙasar suka kashe duk waɗanda suka ƙulla wa Sarki Amon maƙarƙashiya, sa’an nan suka naɗa ɗansa sarki a maimakonsa. Game da sauran ayyukan mulkin Amon, da abubuwan da ya aikata, duk a rubuce suke a cikin littafin tarihin sarakunan Yahuda. Aka binne shi a kabarinsa a lambun Uzza. Yosiya ɗansa kuma ya gāje shi. Yosiya yana da shekara takwas sa’ad da ya zama sarki, ya kuma yi mulki shekara talatin da ɗaya a Urushalima. Sunan mahaifiyarsa Yedida ’yar Adahiya; mutuniyar Bozkat. Ya aikata abin da yake daidai a gaban Ubangiji ya kuma bi dukan gurbin kakansa Dawuda, bai bauɗe hagu ko dama ba. A shekara ta goma sha takwas ta mulkinsa, Sarki Yosiya ya aiki Shafan ɗan Azaliya, ɗan Meshullam, magatakarda, zuwa haikalin Ubangiji. Ya ce, “Ka haura zuwa wurin Hilkiya babban firist ka sa yă shirya kuɗin da aka kawo a haikalin Ubangiji, wanda masu tsaron ƙofa suka tara daga mutane. Ka sa su danƙa su a hannun waɗanda aka zaɓa don biyan ma’aikatan da suka yi gyara a haikalin Ubangiji, wato, kafintoci, da magina, da masu tsara gini. Ka kuma sa su sayi katakai da sassaƙaƙƙun duwatsu don a gyara haikalin. Amma ba sa bukata su ba da bayanin kuɗin da aka danƙa musu domin suna aikinsu da aminci.” Hilkiya babban firist ya ce wa Shafan magatakarda, “Na sami Littafin Doka a haikalin Ubangiji.” Sai ya ba wa Shafan, shi kuma ya karanta. Sa’an nan Shafan ya koma wurin sarki ya ce masa, “Hafsoshinka sun kwashe kuɗin da suke a haikalin Ubangiji, suka ba wa masu aiki da masu lura da haikalin.” Sa’an nan Shafan magatakarda ya ce wa sarki, “Hilkiya firist ya ba ni wani littafi.” Sai Shafan ya karanta shi a gaban sarki. Da sarki ya ji kalmomin Littafin Doka, sai ya kece tufafinsa. Ya ba da waɗannan umarnai ga Hilkiya firist, da Ahikam ɗan Shafan, da Akbor ɗan Mikahiya, da Shafan magatakarda, da kuma Asahiya mai hidimar sarki, ya ce, “Ku je, ku nemi nufin Ubangiji saboda ni da saboda jama’a da kuma saboda dukan Yahuda game da abin da wannan littafi da aka samo ya ƙunsa. Fushin Ubangiji mai girma ne a kanmu domin kakanninmu ba su kiyaye kalmomin littafin nan ba; ba su aikata bisa ga abin da yake a rubuce game da mu ba.” Sai Hilkiya firist, da Ahikam, Akbor, da Shafan, da kuma Asahiya suka je don su yi magana da annabiya Hulda, matan Shallum ɗan Tikba, ɗan Harhas, mai ajiyar tufafi. Tana zama a Urushalima, a Yanki na Biyu. Sai ta ce musu, “Ga abin da Ubangiji, Allah na Isra’ila ya ce, ku faɗa wa mutumin da ya aike ku wurina, ‘Ga abin da Ubangiji ya ce, zan kawo masifa wa wannan wuri da kuma wa kan mutanen wurin, bisa ga dukan abubuwan da suke a rubuce a cikin littafin da sarkin Yahuda ya karanta. Domin sun yashe ni suka ƙona turare wa waɗansu alloli, suka tozarta ni da dukan gumakan da hannuwansu suka sassaƙa, fushina zai yi ƙuna a kan wannan wuri, ba kuwa zai huce ba.’ Ku faɗa wa sarkin Yahuda, wanda ya aike ku ku nemi nufin Ubangiji, ‘Ga abin da Ubangiji, Allah na Isra’ila yana cewa game da kalmomin da ka ji. Domin zuciyarka mai tuba ce, ka kuma ƙasƙantar da kanka a gaban Ubangiji sa’ad da ka ji abin da na faɗa game da wannan wuri da mutanen wurin, cewa za su zama la’antattu da kuma kango, domin kuma ka kece tufafinka, ka kuma yi kuka a gabana, na ji ka, in ji Ubangiji. Saboda haka zan haɗa ka da kakanninka, za a kuma binne ka cikin salama. Idanunka kuma ba za su ga dukan wannan masifan da zan jawo wa wurin nan ba.’ ” Sai suka kai wa sarki abin da ta faɗa. Sai sarki ya kira dukan dattawan Yahuda da Urushalima. Sai ya haura zuwa cikin haikalin Ubangiji tare da mutanen Yahuda, da na Urushalima, da firistoci, da annabawa, dukan mutane, manya da ƙanana. Ya karanta musu duk kalmomin Littafin Alkawari, wanda aka samu a haikalin Ubangiji. Sarki ya tsaya dab da ginshiƙi ya kuma sabunta alkawarin a gaban Ubangiji, ya ce zai bi Ubangiji, yă kiyaye dokokinsa, da ƙa’idodinsa, da farillansa, da dukan zuciyarsa da dukan ransa, ta haka ya tabbatar da kalmomin alkawarin da yake a rubuce a cikin littafin nan. Sa’an nan dukan mutane ma suka yi alkawari yin haka. Sai Yosiya ya umarci Hilkiya babban firist, tare da firistocin da suke taimakonsa, da masu tsaron ƙofa su kawar da dukan abubuwan da aka yi domin Ba’al, da domin Ashera, da kuma domin dukan rundunar taurari, daga haikalin Ubangiji. Ya ƙone su a bayan Urushalima a filayen Kwarin Kidron, ya kwashe tokan zuwa Betel. Ya kawar da firistocin gumakan da sarakunan Yahuda suka naɗa don su ƙona turare a masujadan kan tuddai na garuruwan Yahuda, da kuma waɗanda suke kewaye da Urushalima, masu ƙona turare wa Ba’al, rana da wata, ga rukunin taurari, da kuma ga dukan rundunan taurari. Ya ɗauke ginshiƙin Ashera daga haikalin Ubangiji zuwa Kwarin Kidron can bayan Urushalima, ya ƙone shi a can. Ya niƙa shi sai da ya zama toka, sai ya watsar da ƙurar a filin kabarin talakawa. Ya kuma rurrushe mazaunan karuwai mazan haikali waɗanda suke a haikalin Ubangiji, da kuma inda mata suke yi wa Ashera saƙa. Yosiya ya kawo dukan firistoci daga garuruwan Yahuda, ya kuma lalatar da masujadan kan tuddai daga Geba har zuwa Beyersheba, inda firistoci suke ƙona turare. Ya rurrushe matsafai a ƙofofi shigan gari na mashigi zuwa Ƙofar Yoshuwa, gwamnan birnin, wanda yake a hagu da ƙofar birnin. Ko da yake firistocin masujadan kan tuddai ba su yi hidima a bagaden Ubangiji a Urushalima ba, sun ci burodi marar yisti tare da sauran firistoci. Ya lalatar da Tofet, wanda yake a Kwarin Ben Hinnom, don kada kowa yă iya yin amfani da wurin don yă miƙa hadayar ɗansa, ko ’yarsa a wuta ga Molek. Ya kawar da dawakan nan da sarakunan Yahuda suka keɓe wa gumakan nan na rana daga mashigin haikalin Ubangiji. Waɗannan dawakan suna kusa da ɗakin Natan Melek, ɗaya daga cikin dattawan sarki. Yosiya ya kuma ƙone kekunan yaƙi a yin sujada ga gumakan nan rana. Ya rushe bagadan da sarakunan Yahuda suka kafa a kan ɗakin sama kusa da ɗakin sama na Ahaz, da kuma bagadai biyu da Manasse ya gina a filaye biyu na haikalin Ubangiji. Ya kawar da su daga can, ya farfashe su, ya zubar da tarkacen a Kwarin Kidron. Sarkin kuma ya lalatar da masujadan kan tuddan da suke gabas da Urushalima, kudu da Tudun Hallaka, waɗanda Solomon sarkin Isra’ila ya gina don Ashtarot, ƙazantacciyar alliyar Sidoniyawa, da Kemosh ƙazantaccen allah na Mowab, da kuma Molek allahn banƙyama na mutanen Ammon. Yosiya ya farfashe keɓaɓɓun duwatsu, ya rurrushe ginshiƙan Asheransu, ya baza ƙasusuwan mutane a can. Har ma da bagaden Betel, masujadan kan tudun da Yerobowam ɗan Nebat ya yi, wanda ya sa Isra’ila suka yi zunubi. Wannan bagade da masujadan kan tudun ma ya kawar, ya ƙone masujadan kan tudun, ya niƙa su, ya kuma ƙone ginshiƙin Ashera. Da Yosiya ya dubi kewaye da shi, ya ga kaburburan da suke can a gefen tudu, sai ya sa aka kwaso ƙasusuwan da suke cikinsu aka ƙone a kan bagade don yă lalatar da shi bisa ga maganar Ubangiji ta bakin mutumin Allah, wanda ya yi annabcin waɗannan abubuwa. Sarkin ya yi tambaya, ya ce, “Wane kabari ke nan nake gani?” Mutanen birnin suka ce, “Ai, kabarin annabin Allah ne wanda ya fito daga Yahuda, shi ne ya yi annabcin waɗannan abubuwan da ka aikata gāba da bagaden Betel.” Sai ya ce, “Ku rabu da shi, kada wani yă dami ƙasusuwansa.” Saboda haka suka bar kasusuwansa, da na annabin da ya fito Samariya. Kamar yadda ya yi a Betel, Yosiya ya kawar da dukan ɗakunan gumaka a kan tuddan da sarakunan Isra’ila suka gina a garuruwan Samariya, waɗanda suka tozarta Ubangiji. Yosiya ya yayyanka dukan firistoci na waɗannan masujadan kan tuddai, ya kuma ƙone ƙasusuwan mutane a kansu. Sa’an nan ya koma Urushalima. Sarkin ya ba da umarnin nan ga dukan mutane, cewa, “Ku yi Bikin Ƙetarewa ga Ubangiji Allahnku, yadda aka rubuta a Littafin Alkawari.” Ba a taɓa yin irin Bikin Ƙetarewa haka ba, tun zamanin da masu shari’a suke aiki a matsayin sarakuna, ko a kwanakin sarakunan Isra’ila, ko na Yahuda. Amma a shekara ta goma sha takwas ta mulkin sarki Yosiya, aka yi Bikin Ƙetarewan nan ga Ubangiji a Urushalima. Ban da haka, Yosiya ya kawar da masu duba, da masu maita, da allolin gidaje, da gumaka, da duk wani abin banƙyaman da ya gani a Yahuda da Urushalima. Ya yi wannan domin yă cika wa’adodin shari’a yadda suke a littafin da Hilkiya firist ya samu a haikalin Ubangiji. Babu wani sarki kafin Yosiya, ko kuma a bayansa, wanda ya juya ga Ubangiji da dukan zuciyarsa, da dukan ransa, da dukan ƙarfinsa bisa ga shari’ar Musa, kamar yadda ya yi. Duk da haka, Ubangiji bai huce daga zafin fushinsa wanda ya ƙuna game da Yahuda saboda abin da Manasse ya aikata don yă tozarta shi ba. Saboda haka Ubangiji ya ce, “Zan shafe Yahuda ma kamar yadda na shafe Isra’ila, daga gabana, zan ƙi Urushalima birnin da na zaɓa, da wannan haikali wanda na ce, ‘A can Sunana zai kasance.’ ” Game da sauran ayyukan mulkin Yosiya, da duk abin da ya yi, duk a rubuce suke a cikin littafin tarihin sarakunan Yahuda. Yayinda Yosiya yake sarki, Fir’auna Neko, sarkin Masar ya haura zuwa Kogin Yuferites don yă taimaki sarkin Assuriya da yaƙi. Sarki Yosiya kuwa ya yi ƙoƙari ya hana shi wucewa, sa’ad da Fir’auna Neko ya gan shi, sai ya kashe shi a filin yaƙi a Megiddo. Bayin Yosiya suka ɗauko gawarsa daga Megiddo suka kai Urushalima, suka binne shi a kabarinsa. Sai mutanen ƙasar suka ɗauki Yehoyahaz ɗan Yosiya suka naɗa shi sarki a madadin mahaifinsa. Yehoyahaz yana da shekara ashirin da uku sa’ad da ya zama sarki. Ya yi mulki na wata uku a Urushalima. Sunan mahaifiyarsa Hamutal ’yar Irmiya; mutuniyar Libna. Ya aikata mugunta a gaban Ubangiji, yadda kakanninsa suka yi. Fir’auna Neko ya sa shi a sarƙa a Ribla a ƙasar Hamat don kada yă yi mulki a Urushalima, sa’an nan ya sa wa Yahuda harajin talenti ɗari na azurfa, da talenti ɗaya na zinariya. Fir’auna Neko ya naɗa Eliyakim ɗan Yosiya sarki a maimakon mahaifinsa, ya kuma canja masa suna zuwa Yehohiyakim. Ya ɗauki Yehoyahaz ya kai Masar, a can ya mutu. Yehohiyakim ya riƙa biyan Fir’auna Neko azurfa da zinariyar da ya umarta. Don yă yi haka sai ya riƙa karɓar azurfa da zinariya daga mutanen ƙasar, kowa bisa ga ƙarfinsa. Yehohiyakim yana da shekara ashirin da biyar sa’ad da ya zama sarki, ya kuma yi mulki shekara goma sha ɗaya a Urushalima. Sunan mahaifiyarsa Zebuda ’yar Fedahiya, mutuniyar Ruma. Ya kuma aika mugunta a gaban Ubangiji yadda kakanninsa suka yi. A zamani Yehohiyakim, Nebukadnezzar sarkin Babilon ya kawo wa ƙasar farmaki, Yehohiyakim dai ya zama abokin tarayyarsa na tsawon shekara uku. Daga baya kuma sai ya canja ra’ayi ya yi wa Nebukadnezzar tawaye. Ubangiji ya aiki maharan Babiloniyawa, da na Arameyawa, da na Mowabawa, da na Ammonawa. Ya aike su su hallaka Yahuda bisa ga maganar Ubangiji wadda ya furta ta bakin bayinsa annabawa. Ba shakka waɗannan abubuwa sun faru da Yahuda bisa ga umarnin Ubangiji domin yă kawar da su daga gabansa saboda zunuban Manasse da dukan abin da ya yi, haɗe da zub da jinin marasa laifi. Gama ya ƙazantar da Urushalima da jinin marasa laifi. Ubangiji kuwa bai yi niyyar yafewa ba. Game da sauran ayyukan mulkin Yehohiyakim da abubuwan da ya aikata, duk a rubuce suke a cikin littafin tarihin sarakunan Yahuda. Yehohiyakim ya huta da kakanninsa. Yehohiyacin ɗansa ya gāje shi. Sarkin Masar bai sāke fita daga ƙasarsa don yaƙi ba domin sarkin Babilon ya mamaye yankin, daga Rafin Masar har zuwa Kogin Yuferites. Yehohiyacin yana da shekara goma sha takwas da ya zama sarki, ya kuma yi mulki wata uku a Urushalima. Sunan mahaifiyarsa Nehushta ’yar Elnatan, mutuniyar Urushalima. Ya aikata mugunta a gaban Ubangiji yadda mahaifinsa ya yi. A wannan lokaci, hafsoshin Nebukadnezzar sarkin Babilon suka kawo wa Urushalima yaƙi, suka kuma kewaye ta. Nebukadnezzar na Babilon da kansa kuwa ya zo birnin yayinda hafsoshinsa suka kewaye ta. Yehohiyacin sarkin Yahuda, da mahaifiyarsa, da masu yi masa hidima, da hakimansa, da kuma fadawansa duk suka miƙa kansu ga Nebukadnezzar. A shekara ta takwas ta mulkin sarkin Babilon, sarkin Babilon ya mai da Yehohiyacin ɗan kurkuku. Yadda Ubangiji ya faɗa, Nebukadnezzar ya kwashe dukan dukiyar haikalin Ubangiji, da ta fadan sarki, ya kuma kwashe dukan kayan zinariyar da Solomon sarkin Isra’ila ya ƙera domin haikalin Ubangiji. Ya kwashi dukan mutanen Urushalima zuwa bauta, ya kwashi dukan fadawa, da mayaƙa, da masu sana’a, da maƙera, yawansu ya kai dubu goma. Ba wanda ya ragu, sai matalautan ƙasar. Nebukadnezzar ya ɗauki Yehohiyacin ya kai bauta a Babilon. Ya kuma kwashe mahaifiyar sarki, da matansa, da fadawansa, da manyan mutanen ƙasar daga Urushalima ya kai Babilon. Sarkin Babilon kuma ya kwashe dukan mayaƙa dubu bakwai, ƙarfafu, shiryayyu don yaƙi, da masu sana’a, da maƙera dubu ɗaya, ya kai Babilon. Sarkin Babilon ya sa Mattaniya, ɗan’uwan mahaifin Yehohiyacin, ya zama sarki a madadinsa, ya canja masa suna zuwa Zedekiya. Zedekiya yana da shekara ashirin da ɗaya da ya zama sarki, ya kuma yi mulki shekara goma sha ɗaya a Urushalima. Sunan mahaifiyarsa Hamutal ’yar Irmiya; mutuniyar Libna. Ya aikata mugunta a gaban Ubangiji yadda Yehohiyakim ya yi. Saboda fushin Ubangiji ne dukan waɗannan abubuwa suka faru da Urushalima, da kuma Yahuda, a ƙarshe kuma ya kawar da su daga fuskarsa. To, sai Zedekiya ya yi wa sarkin Babilon tawaye. A rana ta goma ga wata na goma, a shekara ta tara ta mulkin Zedekiya ne Nebukadnezzar sarkin Babilon tare da dukan rundunan yaƙinsa, ya tasam wa Urushalima. Ya yi sansani a bayan birnin, ya kewaye ta da shirin yaƙi. Haka birnin ta kasance a kewaye har shekara ta goma sha ɗaya ta mulkin Zedekiya. A rana ta tara ta watan huɗu, lokacin da yunwa ta yi tsanani a birnin, babu kuma abinci domin mutane su ci. Sai aka huda katanga sa’an nan dukan sojoji suka tsere da dare a ƙofa tsakanin katanga biyu da suke kusa da lambun sarki, ko da yake Babiloniyawa sun kewaye birnin. Suka tsere suka nufi Araba. Amma sojojin Babiloniyawa suka bi sarki, suka cin masa a filayen Yeriko. Dukan sojojinsa kuwa suka rabu da shi suka watse. Aka kama shi, aka kai shi gaban sarkin Babilon a Ribla, inda aka yanke masa hukunci. Suka kashe ’ya’yan Zedekiya a gabansa, sa’an nan aka ƙwaƙule idanunsa. Suka daure shi da sarƙar tagulla, suka kai shi Babilon. A rana ta bakwai na watan biyar, wadda ta zama shekara ta goma sha tara ta mulkin Sarki Nebukadnezzar na Babilon, Nebuzaradan, babban hafsan matsaran sarki, kuma bafadan sarkin Babilon, ya zo Urushalima Ya cinna wa haikalin Ubangiji wuta, da fadan sarki, da kuma dukan gidajen Urushalima. Ya kuma ƙone duk wani gini mai muhimmanci. Dukan mayaƙan Babilon a ƙarƙashin umarnin babban hafsan matsaran sarki, suka rushe katangar Urushalima. Nebuzaradan babban hafsan matsaran, ya kwashi waɗanda suka rage a cikin birnin, tare da sauran jama’a, da waɗanda suka miƙa kansu ga sarkin Babilon, ya kai su bauta. Amma hafsan ya bar waɗansu daga cikin mafiya talauci na ƙasar don su yi aiki a lambunan inabi da kuma gonaki. Babiloniyawan kuma suka sassare ginshiƙan tagulla, da wuraren zama da za a iya matsar da su, da ƙaton kwano mai suna Teku na tagulla da yake a haikalin Ubangiji, suka kwashe tagullan zuwa Babilon. Suka ɗauke tukwane, da manyan cokula, da acibalbal, da kwanoni, da dai dukan kayan da aka yi da tagulla don hidima a haikalin Ubangiji. Babban hafsan matsaran sarkin ya kwashe har da kwanoni na kwashe garwashin wuta da sauran kwanoni, dukansu kuwa ƙeran zinariya ko azurfa tsatsa ne. Tagullar ginshiƙai biyun nan, da ta ƙaton kwanon da ake ce da shi Teku, da ta dukan amalanke masu riƙe ruwa waɗanda Sarki Solomon ya yi domin haikalin Ubangiji, sun fi gaba a auna su. Tsawon kowane ginshiƙi, ƙafa ashirin da bakwai ne. Hulunan tagullan da suke ƙwalƙwalin kowane ginshiƙi kuma yana da tsawon ƙafa huɗu da rabi. Kuma aka yi masa ado da saƙa da ’ya’yan itace kewaye da shi. Bayan ginshiƙin ma haka yake. Babban hafsan ya kwashi Serahiya babban firist, da Zefaniya na biye da shi a girma, da matsara ƙofofi uku. Daga cikin waɗanda suka rage a birnin, ya ɗauki hafsa mai kula da dakaru, da kuma mashawartan sarki guda biyar. Ya kuma tafi da magatakarda wanda yake babban jami’in soja mai ɗaukan dukan jama’an ƙasar, tare da mutanensa guda sittin waɗanda aka samu a birnin. Nebuzaradan, babban hafsan, ya kwashe su duka ya kawo su wurin sarkin Babilon a Ribla. A can Ribla, a ƙasar Hamat, sarkin Babilon ya sa aka kashe su. Haka Yahuda ta tafi bauta daga ƙasarta. Nebukadnezzar sarkin Babilon ya zaɓi Gedaliya ɗan Ahikam, ɗan Shafan yă zama shugaban sauran mutanen da suka rage a Yahuda. Sa’ad da dukan hafsoshin soja tare da mutanensu suka ji cewa sarkin Babilon ya naɗa Gedaliya a matsayin gwamna, sai suka zo wurin Gedaliya a Mizfa. Mutanen da suka zo su ne, Ishmayel ɗan Netaniya, Yohanan ɗan Kareya, Serahiya ɗan Tanhumet mutumin Netofa, Ya’azaniya ɗan mutumin Ma’aka, tare da mutanensu. Gedaliya ya tabbatar musu da rantsuwa cewa, “Kada ku ji tsoron jama’ar Babiloniyawa, muddin kun zauna lafiya, kun kuma bauta wa sarkin Babilon, kome zai yi muku kyau.” Amma a wata na bakwai, sai Ishmayel, ɗan Netaniya, ɗan Elishama, wanda yake daga gidan sarauta, ya zo tare da mutane goma, suka kashe Gedaliya duk da mutanen Yahuda, da na Babilon da suke tare da shi na Mizfa. Ganin haka sai dukan mutane, babba da ƙarami, tare da shugabannin sojoji, suka tashi suka gudu zuwa ƙasar Masar, gama suna tsoron mutanen Babilon. A shekara ta talatin da bakwai ta bautar Yehohiyacin sarkin Yahuda, a shekaran da Ewil-Merodak ya ci sarautan Babilon, sai ya saki Yehohiyacin daga jaru, ya sake shi a rana ashirin da bakwai ga watan goma sha biyu. Ya yi wa Yehohiyacin maganar alheri, ya kuma ɗaukaka shi sama da sauran sarakunan da suke tare da shi a Babilon. Don haka Yehohiyacin ya tuɓe kayan fursuna. Kowace rana kuwa yakan ci abinci a teburin sarki har iyakar ransa. Sarki kuma ya yanka masa kuɗin da za a dinga ba shi, kowace rana muddin ransa. Adamu, Set, Enosh, Kenan, Mahalalel, Yared, Enok, Metusela, Lamek, Nuhu. ’Ya’yan Nuhu maza su ne, Shem, Ham da Yafet. ’Ya’yan Yafet maza su ne, Gomer, Magog, Madai, Yaban, Tubal, Meshek da Tiras. ’Ya’yan Gomer maza su ne, Ashkenaz, Rifat da Togarma. ’Ya’yan Yaban maza su ne, Elisha, Tarshish, Kittim da Rodanim. ’Ya’yan Ham maza su ne, Kush, Masar Fut da Kan’ana. ’Ya’yan Kush maza su ne, Seba, Hawila, Sabta, Ra’ama da Sabteka. ’Ya’yan Ra’ama maza su ne, Sheba da Dedan Kush shi ne mahaifin Nimrod, wanda ya yi girma ya zama babban jarumi a duniya. Masar shi ne mahaifin Ludiyawa, Anamawa, Lehabiyawa, Neftuhawa, Fatrusawa, Kasluhiyawa (daga waɗanda Filistiyawa suka fito) da Kaftorawa. Kan’ana shi ne mahaifin Sidon ɗan farinsa, da Hittiyawa, Yebusiyawa, Amoriyawa, Girgashiyawa Hiwiyawa, Arkiyawa, Siniyawa, Arbadiyawa, Zemarawa da Hamawa. ’Ya’yan Shem maza su ne, Elam, Asshur, Arfakshad, Lud da Aram. ’Ya’yan Aram maza su ne, Uz, Hul, Geter da Meshek. Arfakshad shi ne mahaifin Shela, Shela kuwa shi ne mahaifin Eber. Aka haifa wa Eber ’ya’ya maza biyu. Aka kira ɗaya Feleg domin a lokacinsa ne aka raba duniya; sunan ɗan’uwansa kuwa shi ne Yoktan. Yoktan shi ne mahaifin Almodad, Shelef, Hazarmawet, Yera Hadoram, Uzal, Dikla, Ebal, Abimayel, Sheba, Ofir, Hawila da Yobab. Dukan waɗannan ’ya’yan Yoktan maza ne. Shem, Arfakshad, Shela, Eber, Feleg, Reyu Serug, Nahor, Tera da Abram (wato, Ibrahim). ’Ya’yan Ibrahim maza su ne, Ishaku da Ishmayel. Waɗannan su ne zuriyarsu. Nebayiwot ɗan farin Ishmayel, Kedar, Adbeyel, Mibsam, Mishma, Duma, Massa, Hadad, Tema Yetur, Nafish da Kedema. Waɗannan su ne ’ya’yan Ishmayel maza. ’Ya’yan Ketura maza, ƙwarƙwarar Ibrahim su ne, Zimran, Yokshan, Medan, Midiyan, Ishbak da Shuwa. ’Ya’yan Yokshan maza su ne, Sheba da Dedan. ’Ya’yan Midiyan maza su ne, Efa, Efer, Hanok, Abida da Elda’a. Dukan waɗannan su ne zuriyar Ketura. Ibrahim shi ne mahaifin Ishaku. ’Ya’yan Ishaku maza su ne, Isuwa da Isra’ila. ’Ya’yan Isuwa maza, su ne, Elifaz, Reyuwel, Yewush, Yalam da Kora ’Ya’yan Elifaz maza su ne, Teman, Omar, Zefi, Gatam, Kenaz, da Timna wanda aka haifa wa Amalek. ’Ya’yan maza Reyuwel su ne, Nahat, Zera, Shamma da Mizza. ’Ya’yan Seyir maza su ne, Lotan, Shobal, Zibeyon, Ana, Dishon, Ezer da Dishan. ’Ya’yan Lotan maza su ne, Hori da Homam. Timna ita ce ’yar’uwar Lotan. ’Ya’yan Shobal maza su ne, Alwan, Manahat, Ebal, Shefo da Onam. ’Ya’yan Zibeyon maza su ne, Aiya da Ana. Ɗan Ana shi ne, Dishon. ’Ya’yan Dishon maza su ne, Hemdan, Eshban, Itran da Keran. ’Ya’yan Ezer maza su ne, Bilhan, Za’aban da Ya’akan. ’Ya’yan Dishan maza su ne, Uz da Aran. Waɗannan su ne sarakunan da suka yi sarauta a Edom kafin wani sarkin mutumin Isra’ila yă yi sarauta. Bela ɗan Beyor, wanda aka kira birninsa Dinhaba. Sa’ad da Bela ya mutu sai Yobab ɗan Zera daga Bozra ya gāje shi a matsayin sarki. Da Yobab ya mutu, Husham daga ƙasar Temaniyawa ya gāje shi a matsayin sarki. Sa’ad da Husham ya mutu, Hadad ɗan Bedad, wanda ya ci Midiyan da yaƙi a cikin ƙasar Mowab, ya gāje shi a matsayin sarki. Aka kira birninsa Awit. Da Hadad ya mutu, Samla daga Masreka ya gāje shi a matsayin sarki. Sa’ad da Samla ya mutu, Sha’ul daga Rehobot na kogi ya gāje shi a matsayin sarki. Sa’ad da Sha’ul ya mutu, Ba’al-Hanan ɗan Akbor ya gāje shi a matsayin sarki. Sa’ad da Ba’al-Hanan ya mutu, Hadad ya gāje shi a matsayin sarki. Aka kira birninsa Fau, sunan matarsa kuwa Mehetabel ’yar Matired, ’yar Me-Zahab. Hadad shi ma ya mutu. Manyan Edom su ne, Timna, Alwa, Yetet Oholibama, Ela, Finon Kenaz, Teman, Mibzar, Magdiyel da Iram. Waɗannan su ne manyan Edom. Waɗannan su ne ’ya’yan Isra’ila maza. Ruben, Simeyon, Lawi, Yahuda, Issakar, Zebulun, Dan, Yusuf, Benyamin, Naftali, Gad da Asher. ’Ya’yan Yahuda maza su ne, Er, Onan da Shela. Waɗannan mutum uku Bat-shuwa mutuniyar Kan’ana ce ta haifa masa. Er, ɗan farin Yahuda mugu ne a gaban Ubangiji, saboda haka Ubangiji ya kashe shi. Tamar, surukar Yahuda, ta haifa masa Ferez da Zera. Yahuda ya haifi ’ya’ya maza biyar ne. ’Ya’yan Ferez maza su ne, Hezron da Hamul. ’Ya’yan Zera maza su ne, Zimri, Etan, Heman, Kalkol da Darda, su biyar ne. ’Ya’yan Karmi maza su ne, Akar wanda ya kawo masifa wa Isra’ila ta wurin yin abin da aka haramta. Ɗan Etan shi ne, Azariya. ’Ya’ya maza da aka haifa wa Hezron su ne, Yerameyel, Ram da Kaleb. Ram shi ne mahaifin Amminadab, Amminadab kuwa shi ne mahaifin Nashon, shugaban mutanen Yahuda. Nashon shi ne mahaifin Salma, Salma shi ne mahaifin Bowaz, Bowaz shi ne mahaifin Obed kuma Obed shi ne mahaifin Yesse. Yesse shi ne mahaifin. Eliyab ɗan farinsa, ɗansa na biyu shi ne Abinadab, na ukun Shimeya, na huɗun Netanel, na biyar Raddai, na shidan Ozem na bakwai kuma Dawuda. ’Yan’uwansu mata su ne Zeruhiya da Abigiyel. ’Ya’yan Zeruhiya maza guda uku su ne Abishai, Yowab da Asahel. Abigiyel ita ce mahaifiyar Amasa, wanda mahaifinsa shi ne Yeter mutumin Ishmayel. Kaleb ɗan Hezron ya haifi yara ta wurin matarsa Azuba (da kuma ta wurin Yeriyot). Waɗannan su ne ’ya’yan Azuba maza. Yesher, Shobab da Ardon. Da Azuba ta mutu, Kaleb ya auri Efrat, wadda ta haifa masa Hur. Hur shi ne mahaifin Uri, Uri kuma shi ne mahaifin Bezalel. Daga baya, Hezron ya kwana da ’yar Makir mahaifin Gileyad (ya aure ta sa’ad da take da shekara sittin), ta haifa masa Segub. Segub shi ne mahaifin Yayir, wanda ya yi mulkin garuruwa uku a Gileyad. (Amma Geshur da Aram suka ƙwace Hawwot Yayir da kuma Kenat tare da ƙauyukan kewayenta, garuruwa sittin.) Dukan waɗannan su ne zuriyar Makir mahaifin Gileyad. Bayan Hezron ya mutu a Kaleb Efrata, sai Abiya matar Hezron ta haifa masa Asshur mahaifin Tekowa. ’Ya’yan Yerameyel maza, ɗan farin Hezron su ne, Ram shi ne ɗan fari, sai Buna, Oren, Ozem da Ahiya. Yerameyel yana da wata mata, wadda sunanta Atara; ita ce mahaifiyar Onam. ’Ya’yan Ram maza ɗan farin Yerameyel su ne, Ma’az, Yamin da Eker. ’Ya’yan Onam maza su ne, Shammai da Yada. ’Ya’yan Shammai maza su ne, Nadab da Abishur. Sunan matar Abishur ita ce Abihayil, wadda ta haifa masa Aban da Molid. ’Ya’yan Nadab maza su ne, Seled da Affayim. Seled ya mutu babu yara. Ɗan Affayim shi ne, Ishi, wanda shi ne mahaifin Sheshan. Sheshan shi ne mahaifin Alai. ’Ya’yan Yada maza, ɗan’uwan Shammai su ne, Yeter da Yonatan. Yeter ya mutu babu yara. ’Ya’yan Yonatan maza su ne, Felet da Zaza. Waɗannan su ne zuriyar Yerameyel. Sheshan ba shi da ’ya’ya maza, sai ’ya’ya mata kawai. Yana da bawa mutumin Masar mai suna Yarha. Sheshan ya ba da ’yarsa aure ga bawansa Yarha, ta kuwa haifa masa Attai. Attai shi ne mahaifin Natan, Natan shi ne mahaifin Zabad, Zabad shi ne mahaifin Eflal, Eflal shi ne mahaifin Obed, Obed shi ne mahaifin Yehu, Yehu shi ne mahaifin Azariya, Azariya shi ne mahaifin Helez, Helez shi ne mahaifin Eleyasa, Eleyasa shi ne mahaifin Sismai, Sismai shi ne mahaifin Shallum Shallum shi ne mahaifin Yekamiya, Yekamiya kuma shi ne mahaifin Elishama. ’Ya’yan Kaleb maza, ɗan’uwan Yerameyel su ne, Mesha ɗan farinsa, wanda shi ne mahaifin Zif, da ɗansa Maresha, wanda shi ne mahaifin Hebron. ’Ya’yan Hebron maza su ne, Kora, Taffuwa, Rekem da Shema. Shema shi ne mahaifin Raham, Raham kuma shi ne mahaifin Yorkeyam. Rekem shi ne mahaifin Shammai. Ɗan Shammai shi ne Mawon, Mawon kuma shi ne mahaifin Bet-Zur. Efa ƙwarƙwarar Kaleb ita ce mahaifiyar Haran, Moza da Gazez. Haran shi ne mahaifin Gazez. ’Ya’yan Yadai maza su ne, Regem, Yotam, Geshan, Felet, Efa da Sha’af. Ma’aka ƙwarƙwarar Kaleb ita ce mahaifiyar Sheber da Tirhana. Ta kuma haifi Sha’af mahaifin Madmanna da kuma Shewa, mahaifin Makbena da Gibeya. ’Yar Kaleb ita ce Aksa. Waɗannan su ne zuriyar Kaleb. ’Ya’yan Hur maza, ɗan farin Efrata su ne, Shobal mahaifin Kiriyat Yeyarim, Salma mahaifin Betlehem, da kuma Haref mahaifin Bet-Gader. Zuriyar Shobal mahaifin Kiriyat Yeyarim su ne, Harowe, rabin Manahatiyawa, kuma gidan Kiriyat Yeyarim su ne, Itrayawa, Futiyawa, Shumatiyawa da Mishratiyawa. Daga waɗannan ne Zoratiyawa da Eshtawoliyawa suka fito. Zuriyar Salma su ne, Betlehem, Netofawa, Atrot Bet Yowab, rabin Manahatiyawa, Zoriyawa, kuma gidan marubuta waɗanda suke zama a Yabez su ne, Tiratiyawa, Shimeyatiyawa da Sukatiyawa. Waɗannan su ne Keniyawa waɗanda suka zo daga Hammat, mahaifin gidan Rekab. Waɗannan su ne ’ya’yan Dawuda maza da aka haifa masa a Hebron. Ɗan farinsa shi ne Amnon ɗan Ahinowam mutuniyar Yezireyel; na biyun, Daniyel ɗan Abigiyel mutuniyar Karmel; na ukun, Absalom ɗan Ma’aka ’yar Talmai sarkin Geshur; na huɗun, Adoniya ɗan Haggit; na biyar, Shefatiya ɗan Abital; da kuma na shida, Itireyam ta wurin matarsa Egla. Waɗannan su ne aka haifa wa Dawuda a Hebron, inda ya yi mulki shekaru bakwai da wata shida. Dawuda ya yi mulki a Urushalima shekaru talatin da uku, kuma waɗannan su ne yaran da aka haifa masa a can. Shimeya, Shobab, Natan da Solomon. Waɗannan huɗu ne Bat-shuwa ’yar Ammiyel ta haifa. Akwai kuma Ibhar, Elishama, Elifelet, Noga, Nefeg, Yafiya, Elishama, Eliyada da Elifelet, su tara ne duka. Dukan waɗannan ’ya’yan Dawuda ne maza, ban da ’ya’yansa maza ta wurin ƙwarƙwaransa. Tamar ita ce ’yar’uwarsu. Zuriyar Solomon su ne Rehobowam, da Abiya, da Asa, da Yehoshafat, da Yoram, da Ahaziya, da Yowash, da Amaziya, da Azariya, da Yotam, da Ahaz, da Hezekiya da Manasse, da Amon, da Yosiya. ’Ya’yan Yosiya maza su ne, Yohanan ɗan fari, Yehohiyakim ɗa na biyu, Zedekiya ɗa na uku Shallum ɗa na huɗu. Magādan Yehohiyakim su ne, Yekoniya ɗansa, da Zedekiya. Zuriyar Yekoniya kamamme su ne, Sheyaltiyel, Malkiram, Fedahiya, Shenazzar, Yekamiya, Hoshama da Nedabiya. ’Ya’yan Fedahiya su ne, Zerubbabel da Shimeyi. ’Ya’yan Zerubbabel maza su ne, Meshullam da Hananiya. Shelomit ce ’yar’uwarsu. Akwai kuma waɗansu biyar, Hashuba, Ohel, Berekiya, Hasadiya da Yushab-Hesed. Zuriyar Hananiya su ne, Felatiya da Yeshahiya, Refahiya, Arnan, Obadiya da Shekaniya. Zuriyar Shekaniya su ne, Shemahiya da ’ya’yansa maza. Hattush, Igal, Bariya, Neyariya da Shafat, su shida ne duka. ’Ya’yan Neyariya maza su ne, Eliyohenai, Hezekiya da Azrikam, su uku ne duka. ’Ya’yan Eliyohenai su ne, Hodawiya, Eliyashib, Felahiya, Akkub, Yohanan, Delahiya da Anani, su bakwai ne duka. Zuriyoyin Yahuda su ne, Ferez, Hezron, Karmi, Hur da Shobal. Reyahiya ɗan Shobal shi ne mahaifin Yahat, Yahat shi ne mahaifin Ahumai da Lahad. Waɗannan su ne gidajen Zoratiyawa. Waɗannan su ne ’ya’yan Etam. Yezireyel, Ishma da Idbash. ’Yar’uwarsu ita ce Hazzelelfoni. Fenuwel shi ne mahaifin Gedor, kuma Ezer shi ne mahaifin Husha. Waɗannan su ne zuriyar Hur, ɗan farin Efrata da mahaifin Betlehem. Asshur mahaifin Tekowa yana da mata biyu, Hela da Na’ara. Na’ara ta haifi Ahuzzam, Hefer, Temeni da Hawahashtari. Waɗannan su ne zuriyar Na’ara. ’Ya’yan Hela maza su ne, Zeret, Zohar, Etnan, da Koz. Koz ne mahaifin Anub da Hazzobeba, shi ne kuma kakan iyalin da suka fito daga zuriyar Aharhel ɗan Harum. Yabez ya fi ’yan’uwansa martaba. Mahaifiyarsa ta sa masa suna Yabez, tana cewa, “Na haife shi da azaba.” Yabez ya yi kuka ga Allah na Isra’ila ya ce, “Ka yi mini albarka ka fadada yankina! Bari hannunka yă kasance tare da ni, yă kuma kiyaye ni daga abin da zai cuce ni, don kada in shiga wahala.” Sai Allah ya ji roƙonsa. Kelub, ɗan’uwan Shuha, shi ne mahaifin Mehir, wanda shi ne mahaifin Eshton. Eshton shi ne mahaifin Bet-Rafa, Faseya da Tehinna wanda ya haifi Ir Nahash. Waɗannan su ne mutanen Reka. ’Ya’yan Kenaz maza su ne, Otniyel da Serahiya. ’Ya’yan Otniyel maza su ne, Hatat da Meyonotai. Meyonotai shi ne mahaifin Ofra. Serahiya shi ne mahaifin Yowab, mahaifin Ge-Harashim. An kira shi haka domin mutanensa masu sana’ar hannu ne. ’Ya’yan Kaleb ɗan Yefunne maza su ne, Iru, Ela da Na’am. Ɗan Ela shi ne, Kenaz. ’Ya’yan Yahallelel su ne, Zif, Zifa, Tiriya da Asarel. ’Ya’yan Ezra maza su ne, Yeter, Mered, Efer da Yalon. Ɗaya daga cikin matan Mered ta haifi Miriyam, Shammai da Ishba wanda ya haifi Eshtemowa. (Matarsa mutuniyar Yahuda kuwa ta haifi Yared mahaifin Gedor, Heber mahaifin Soko, da kuma Yekutiyel mahaifin Zanowa.) Waɗannan su ne ’ya’yan Bitiya ’yar Fir’auna, wadda Mered ya aura. ’Ya’yan matar Hodiya, ’yar’uwar Naham su ne, suka haifi Keyila Bagarme, da Eshtemowa mutumin Ma’aka. ’Ya’yan Shimon maza su ne, Amnon, Rinna, Ben-Hanan da Tilon. Zuriyar Ishi su ne, Zohet da Ben-Zohet. ’Ya’yan Shela ɗan Yahuda maza su ne, Er mahaifin Leka, La’ada mahaifin Maresha da kuma gidajen masu aikin lilin a Bet-Ashbeya, da Yokim, mutanen Kozeba, da Yowash da Saraf wanda ya yi mulkin Mowab da kuma Yashubi Lehem (Waɗannan rubutattun tarihi ne na tun dā.) Su ne maginan tukwane waɗanda suka zauna a Netayim da Gedera; sun zauna a can suka kuma yi wa sarki aiki. Zuriyar Simeyon su ne, Nemuwel, Yamin, Yarib, Zera da Shawulu; Shawulu ya haifi Shallum, Shallum ya haifi Mibsam. Mibsam ya haifi Mishma. Zuriyar Mishma su ne, Hammuwel ɗansa, wanda ya haifi Zakkur, shi Zakkur kuma ya haifi Shimeyi. Shimeyi yana da ’ya’ya maza goma sha shida da ’ya’ya mata shida, amma ’yan’uwansa ba su da ’ya’ya da yawa; saboda haka gidansu gaba ɗaya ba tă zama mai mutane da yawa kamar mutanen Yahuda ba. Sun zauna a Beyersheba, Molada, Hazar Shuwal, Bilha, Ezem, Tolad Betuwel, Horma, Ziklag, Bet-Markabot, Hazar-Susim, Bet-Biri da Sha’arayim. Waɗannan su ne garuruwansu har lokacin mulkin Dawuda. Ƙauyukan da suke kewayensu su ne Etam, Ayin, Rimmon, Token da Ashan, garuruwa biyar; da kuma dukan ƙauyuka kewaye da waɗannan garuruwa har zuwa Ba’al. Waɗannan ne wuraren zamansu. Suka kuma ajiye tarihin zuriya. Zuriyar Simeyon ta ƙunshi Meshobab, da Yamlek, da Yosha ɗan Amaziya. Akwai Yowel, da Yehu ɗan Yoshibiya. Yoshibiya ɗan Seraya ne. Serahiya kuma ɗan Asiyel ne. Akwai Eliyohenai da Ya’akoba, da Yeshohahiya, da Asahiya, da Adiyel, da Yesimiyel, da Benahiya. Akwai Ziza ɗan Shifi. Shifi ɗan Allon ne. Allon ɗan Yedahiya ne. Yedahiya ɗan Shimri ne. Shimri kuma ɗan Shemahiya ne. Mutanen da aka jera sunayensu a bisa, shugabannin gidajensu ne. Iyalansu sun ƙaru sosai, suka tafi bayan garin Gedor wajajen gabashin kwari suna neman makiyaya domin garkunansu. Suka sami makiyaya mai ciyawa mai kyau, ƙasar kuma tana da fāɗi, da salama, kuma zaman lafiya. A dā waɗansu mutanen Ham sun zauna a can. Mutanen da aka jera sunayensu sun zo ne a zamanin Hezekiya sarkin Yahuda. Suka yaƙi mutanen Ham a wuraren zamansu, haka kuma suka yi da Meyunawa da suke can, suka hallaka su ƙaƙaf, yadda yake har yă zuwa yau. Sa’an nan suka zauna a wurin, gama akwai makiyaya domin garkunansu. Mutum ɗari biyar na waɗannan mutane Simeyon, waɗanda Felatiya, Neyariya, Refahiya da Uzziyel, ’ya’yan Ishi maza suka jagorance, sun mamaye ƙasar tudu ta Seyir. Suka karkashe raguwar Amalekawan da suka tsere, suka kuma zauna a can har yă zuwa yau. ’Ya’yan Ruben maza ɗan farin Isra’ila (shi ne ɗan fari, amma sa’ad da ya ƙazantar da gadon auren mahaifinsa, sai aka ba wa ’yancin ɗan farinsa wa ’ya’yan Yusuf maza ɗan Isra’ila; don kada a lissafta shi a tarihin zuriya bisa ga matsayin haihuwarsa, ko da yake Yahuda shi ne mafi ƙarfi cikin ’yan’uwansa kuma mai mulki ya fito daga gare shi, ’yancin zaman ɗan fari na Yusuf ne), ’ya’yan Ruben ɗan farin Isra’ila maza su ne, Hanok, Fallu, Hezron da Karmi. Zuriyar Yowel su ne, Shemahiya, Gog, Shimeyi, Mika, Reyahiya, Ba’al, da Beyera, wanda Tiglat-Fileser sarkin Assuriya ya ɗauka zuwa zaman bauta. Beyera shi ne shugaban mutanen Ruben. Danginsu bisa ga iyalansu da aka jera bisa ga tarihin zuriyarsu su ne, Yehiyel shi ne sarki, akwai Zakariya, da Bela ɗan Azaz. Azaz ɗan Shema daga dangin Yowel. Yowel ya yi zama a yankin Arower har zuwa Nebo da Ba’al-Meyon. Ta waje gabas sun zauna a ƙasar har zuwa bakin hamadan da ya nausa zuwa Kogin Yuferites, domin dabbobinsu sun ƙaru a Gileyad. A zamanin Shawulu zuriyar Ruben sun yi yaƙi da Hagirawa, suka ci su da yaƙi, suka zauna a wuraren zaman Hagirawan ko’ina a dukan yankin gabashin Gileyad. Mutanen Gad sun zauna kusa da mutanen Ruben a Bashan, har zuwa Saleka. Yowel shi ne babba, sai Shafan na biyu, sa’an nan Yanai da Shafat, su ne tushen Bashan. Danginsu, bisa ga iyalai su ne, Mika’ilu, Meshullam, Sheba, Yorai, Yakan, Ziya da Eber, su bakwai ne duka. Waɗannan su ne ’ya’yan Abihayil ɗan Huri, ɗan Yarowa, ɗan Gileyad, ɗan Mika’ilu, ɗan Yeshishai, ɗan Yado, ɗan Buz. Ahi ɗan Abiyel, ɗan Guni, shi ne kan iyalinsu. Mutanen Gad sun zauna a Bashan da ƙauyukan da suke kurkusa da shi, da kuma a dukan makiyayan Sharon har zuwa iyaka inda suka kai. Dukan waɗannan sun shiga tarihin zuriya a lokacin mulkin Yotam sarkin Yahuda da Yerobowam sarkin Isra’ila. Mutanen Ruben, mutanen Gad da rabin kabilar Manasse sun kasance da mutane 44,760 shiryayyu don aikin soja, jarumawan da za su iya riƙe garkuwa da takobi, waɗanda suke iya yin amfani da baka, waɗanda kuma aka horar don yaƙi. Suka yi yaƙi da Hagirawa, Yetur, Nafish da Nodab. Aka taimake su a yaƙin, Allah kuma ya ba da Hagirawa da dukan abokansu gare su, domin sun yi kuka gare shi a lokacin yaƙin. Ya amsa addu’o’insu, domin sun dogara gare shi. Suka ƙwace dabbobin Hagirawa, raƙuma dubu hamsin, tumaki dubu ɗari biyu da hamsin da kuma jakuna dubu biyu. Suka kuma kame mutane dubu ɗari ɗaya, waɗansu suka mutu, domin yaƙin na Allah ne. Suka zauna a ƙasar har lokacin da aka kai su zaman bauta. Mutanen rabin kabilar Manasse sun yi yawa; suka zauna a ƙasar daga Bashan har zuwa Ba’al-Hermon, wato, zuwa Senir (Dutsen Hermon). Waɗannan su ne kawunan iyalansu. Efer, Ishi, Eliyel, Azriyel, Irmiya, Hodawiya da Yadiyel. Su jarumawa ne, sanannu, su ne kuma kawunan iyalansu. Amma ba su yi aminci da Allahn kakanninsu ba, suka kuma yi karuwanci ga waɗansu allolin mutanen ƙasar, waɗanda Allah ya hallaka a gabansu. Saboda haka Allah na Isra’ila ya zuga ruhun Ful sarkin Assuriya (wato, Tiglat-Fileser sarkin Assuriya), wanda ya kwashe mutanen Ruben, mutanen Gad da rabin kabilar Manasse zuwa zaman bauta. Ya kwashe su zuwa Hala, Habor, Hara da kuma kogin Gozan, inda suke har wa yau. ’Ya’yan Lawi maza su ne, Gershon, Kohat da Merari. ’Ya’yan Kohat maza su ne, Amram, Izhar, Hebron da Uzziyel. Yaran Amram su ne, Haruna, Musa da Miriyam. ’Ya’yan Haruna maza su ne, Nadab, Abihu, Eleyazar da Itamar. Eleyazar shi ne mahaifin Finehas, Finehas mahaifin Abishuwa, Abishuwa mahaifin Bukki, Bukki mahaifin Uzzi, Uzzi mahaifin Zerahiya, Zerahiya mahaifin Merahiyot, Merahiyot mahaifin Amariya, Amariya mahaifin Ahitub, Ahitub mahaifin Zadok, Zadok mahaifin Ahimawaz, Ahimawaz mahaifin Azariya, Azariya mahaifin Yohanan, Yohanan mahaifin Azariya (shi ne ya yi hidima a matsayin firist a haikalin da Solomon ya gina a Urushalima), Azariya mahaifin Amariya, Amariya mahaifin Ahitub, Ahitub mahaifin Zadok, Zadok mahaifin Shallum, Shallum mahaifin Hilkiya, Hilkiya mahaifin Azariya, Azariya mahaifin Serahiya, Serahiya kuwa mahaifin Yehozadak. Yehozadak ne aka ɗauka sa’ad da Ubangiji ya tura Yahuda da Urushalima zuwa zaman bauta ta hannun Nebukadnezzar. ’Ya’yan Lawi maza su ne, Gershom, Kohat da Merari. Waɗannan su ne sunayen ’ya’yan Gershom. Libni da Shimeyi. ’Ya’yan Kohat maza su ne, Amram, Izhar, Hebron da Uzziyel. ’Ya’yan Merari maza su ne, Mali da Mushi. Waɗannan suke gidajen Lawiyawan da aka jera bisa ga kakanninsu. Na Gershom su ne, Libni, Yahat, Zimma, Yowa, Iddo, Zera da Yeyaterai. Zuriyar Kohat su ne, Amminadab, Kora, Assir, Elkana, Ebiyasaf, Assir, Tahat, Uriyel, Uzziya da Shawulu. Zuriyar Elkana su ne, Amasai, Ahimot, Elkana, Zofai, Nahat, Eliyab Yeroham, Elkana da Sama’ila. ’Ya’yan Sama’ila maza su ne, Yowel ɗan fari da Abiya ɗa na biyu. Zuriyar Merari su ne, Mali, Libni, Shimeyi, Uzza, Shimeya, Haggiya da Asahiya. Waɗannan su ne mutanen da Dawuda ya sa su lura da waƙa a cikin gidan Ubangiji bayan da aka kawo akwatin alkawari yă huta a can. Suka yi hidima da waƙa a gaban tabanakul, Tentin Sujada, sai da Solomon ya gina haikalin Ubangiji a Urushalima. Suka yi ayyukansu bisa ga ƙa’idodin da aka shimfiɗa musu. Ga mutanen da suka yi hidimar, tare da ’ya’yansu maza. Daga mutanen Kohat akwai, Heman, mawaƙi ɗan Yowel, ɗan Sama’ila, ɗan Elkana, ɗan Yeroham, ɗan Eliyel, ɗan Towa, ɗan Zuf, ɗan Elkana, ɗan Mahat, ɗan Amasai, ɗan Elkana, ɗan Yowel, ɗan Azariya, ɗan Zefaniya ɗan Tahat, ɗan Assir, ɗan Ebiyasaf, ɗan Kora, ɗan Izhar, ɗan Kohat, ɗan Lawi, ɗan Isra’ila; da kuma Asaf ’yan’uwan Heman, waɗanda suka yi hidima a hannun damansa. Asaf ɗan Berekiya, ɗan Shimeya, ɗan Mika’ilu, ɗan Ba’asehiya, ɗan Malkiya, ɗan Etni, ɗan Zera, ɗan Adahiya ɗan Etan, ɗan Zimma, ɗan Shimeyi, ɗan Yahat, ɗan Gershom, ɗan Lawi; da kuma daga ’yan’uwansu, mutanen Merari, a hannun hagunsa. Etan ɗan Kishi, ɗan Abdi, ɗan Malluk, ɗan Hashabiya, ɗan Amaziya, ɗan Hilkiya, ɗan Amzi, ɗan Bani, ɗan Shemer, ɗan Mali, ɗan Mushi, ɗan Merari, ɗan Lawi. Aka ba ’yan’uwansu Lawiyawa dukan sauran ayyukan tabanakul, gidan Allah. Amma Haruna da zuriyarsa su ne waɗanda suke miƙa hadayu a kan bagaden hadaya ta ƙonawa da kuma a kan bagaden turare haɗe da dukan abin da ake yi a Wuri Mafi Tsarki, suna yin kafara domin Isra’ila, bisa ga dukan abin da Musa bawan Allah ya umarta. Waɗannan su ne zuriyar Haruna, Eleyazar, Finehas, Abishuwa, Bukki, Uzzi, Zerahiya, Merahiyot, Amariya, Ahitub, Zadok da Ahimawaz. Waɗannan su ne wuraren zamansu da aka ba su rabo su zama yankunansu (aka ba wa zuriyar Haruna waɗanda suke daga gidan Kohat, domin rabo na fari nasu ne): Aka ba su Hebron a Yahuda tare da wuraren kiwon da suke kewayenta. Amma filaye da ƙauyukan da suke kewayen birnin aka ba wa Kaleb ɗan Yefunne. Saboda haka aka ba wa zuriyar Haruna Hebron (birnin mafaka), da Libna, Yattir Eshtemowa, Hilen, Debir, Ashan, Yutta da Bet-Shemesh, tare da wuraren kiwonsu. Daga kabilar Benyamin kuma aka ba su Gibeyon, Geba, Alemet da Anatot, tare da wuraren kiwonsu. Waɗannan garuruwa waɗanda aka raba a tsakanin mutanen gidan Kohat, goma sha uku ne duka. Aka ba sauran zuriyar Kohat rabon garuruwa goma daga gidajen rabin kabilar Manasse. Aka ba zuriyar Gershom, gida-gida, rabon garuruwa goma sha uku daga kabilan Issakar, Asher da Naftali, da kuma daga sashen rabi kabilar Manasse da yake a Bashan. Aka ba zuriyar Merari, gida-gida, rabon garuruwa goma sha biyu daga kabilan Ruben, Gad da Zebulun. Saboda haka Isra’ilawa suka ba Lawiyawa waɗannan garuruwa da wuraren kiwonsu. Daga kabilan Yahuda, Simeyon da Benyamin suka ba su rabon sunayen garuruwan da aka ambata. Aka ba wa waɗansu na mutanen gidan Kohat yankin garuruwansu daga kabilar Efraim. A ƙasar tudun Efraim aka ba su Shekem (birnin mafaka), da Gezer, Yokmeyam, Bet-Horon, Aiyalon da Gat-Rimmon, tare da wuraren kiwonsu. Daga rabin kabilar Manasse kuwa, Isra’ilawa suka ba da Aner da Bileyam, tare da wuraren kiwonsu, ga sauran gidajen mutanen Kohat. Mutanen Gershom suka sami waɗannan. Daga gidan rabin kabilar Manasse, sun sami Golan a Bashan da kuma Ashtarot, tare da wuraren kiwonsu; daga kabilar Issakar suka sami Kedesh, Daberat, Ramot da Anem, tare da wuraren kiwonsu; daga kabilar Asher suka sami Mashal, Abdon, Hukok da Rehob, tare da wuraren kiwonsu; daga kabilar Naftali kuwa suka sami Kedesh a Galili, Hammon da Kiriyatayim, tare da wuraren kiwonsu. Mutanen Merari (sauran Lawiyawan) suka sami waɗannan. Daga kabilar Zebulun suka sami Yokneyam, Karta, Rimmon da Tabor, tare da wuraren kiwonsu; daga kabilar Ruben a hayin Urdun a gabashi Yeriko suka sami Bezer a hamada, Yahza, Kedemot da Mefa’at, tare da wuraren kiwonsu; daga kabilar Gad kuwa suka sami Ramot a Gileyad, Mahanayim, Heshbon da Yazer, tare da wuraren kiwonsu. ’Ya’yan Issakar maza su ne, Tola, Fuwa, Yashub da Shimron, su huɗu ne duka. ’Ya’yan Tola maza su ne, Uzzi, Refahiya, Yeriyel, Ibsam da Sama’ila, su ne kuma kawunan iyalansu. A zamanin mulkin Dawuda, an rubuta zuriyar Tola a matsayin mayaƙa a cikin tarihinsu, sun kai 22,600. Ɗan Uzzi shi ne, Izrahiya. ’Ya’yan Izrahiya maza su ne, Mika’ilu, Obadiya, Yowel da Isshiya. Dukansu biyar manya ne. Bisa ga tarihin iyalinsu, sun kai mutane 36,000 shiryayyu don yaƙi, gama suna da mata da ’ya’ya da yawa. Dangin da suke maza masu yaƙi sun kasance na dukan gidajen Issakar ne, kamar yadda aka rubuta a cikin tarihi, su 87,000 ne duka. ’Ya’ya uku maza na Benyamin su ne, Bela, Beker da Yediyayel. ’Ya’yan Bela maza su ne, Ezbon, Uzzi, Uzziyel, Yerimot da Iri, su ne kawunan iyalai, kuma su biyar ne duka. Rubutaccen tarihin zuriyarsu ya nuna suna mazan da sun isa yaƙi 22,034. ’Ya’yan Beker maza su ne, Zemira, Yowash, Eliyezer, Eliyohenai, Omri, Yeremot, Abiya, Anatot da Alemet. Dukan waɗannan ’ya’yan Beker maza ne. Rubutaccen tarihin zuriyarsu ya nuna suna da kawunan iyalai da mazan da suka isa yaƙi 20,200. Ɗan Yediyayel shi ne, Bilhan. ’Ya’yan Bilhan maza su ne, Yewush, Benyamin, Ehud, Kena’ana, Zetan, Tarshish da Ahishahar. Dukan waɗannan ’ya’yan Yediyayel maza kawunan iyalai ne. Akwai mazan da suka isa yaƙi waje 17,200. Shuffiyawa da Huffiyawa zuriyar Ir ne, kuma Hushiyawa zuriyar Aher ne. ’Ya’yan Naftali maza su ne, Yaziyel, Guni, Yezer da Shallum, su zuriyar Bilha ne. Zuriyar Manasse su ne, Asriyel zuriyarsa ne ta wurin ƙwarƙwararsa mutuniyar Aram. Ta haifa wa Makir mahaifin Gileyad. Makir ya auri mata daga cikin Huffiyawa da Shuffiyawa. ’Yar’uwarsa ita ce Ma’aka. Wani daga zuriyar, sunansa Zelofehad, shi yana da ’ya’yan mata ne kawai. Ma’aka matar Makir ta haifi ɗa ta kuma ba shi suna Feresh. Sunan ɗan’uwansa Sheresh, ’ya’yan Feresh maza kuwa su ne Ulam da Rakem. Ɗan Ulam shi ne, Bedan. Duka waɗannan zuriyar Gileyad ne. Gileyad ɗan Makir ne, Makir kuma ɗan Manasse. ’Yar’uwarsa Makir mai suna Hammoleket ta haifi Ishod, Abiyezer da Mala. ’Ya’yan Shemida maza su ne, Ahiyan, Shekem, Liki da Aniyam. Zuriyar Efraim su ne, Shutela, Bered, Tahat, Eleyada, Tahat Zabad da Shutela. Wani ɗan ƙasa haifaffen mutanen Gat ya kashe Ezer da Elad, sa’ad da suka gangara don su ƙwace dabbobinsu. Mahaifinsu Efraim ya yi makoki dominsu kwanaki masu yawa sai danginsa suka zo don su yi masa ta’aziyya. Sa’an nan ya sāke kwana da matarsa, sai ta yi ciki ta haifi ɗa. Ya ba shi suna Beriya, saboda masifar da ta auko a cikin iyalinsa. ’Yarsa ita ce Sheyera, wadda ta gina Bet-Horon na kwari da na tudu da kuma Uzzen-Sheyera. Zuriyarsa ita ce, Refa, Reshef, Tela, Tahan, Ladan, Ammihud, Elishama, Nun da kuma Yoshuwa. Ƙasarsu da wuraren zamansu sun haɗa da Betel da ƙauyukan kewayenta, Na’aran wajen gabas, Gezer da ƙauyukanta wajen yamma, da kuma Shekem da ƙauyukan da suka nausa har zuwa Aiya da ƙauyukanta. A iyakokin Manasse akwai Bet-Sheyan, Ta’anak, Megiddo da Dor, tare da ƙauyukansu. Zuriyar Yusuf ɗan Isra’ila ta zauna a waɗannan garuruwa. ’Ya’yan Asher maza su ne, Imna, Ishba, Ishwi da Beriya. ’Yar’uwarsa ita ce Sera. ’Ya’yan Beriya maza su ne, Heber da Malkiyel, wanda yake mahaifin Birzayit. Heber shi ne mahaifin Yaflet, Shomer da Hotam da kuma ’yar’uwarsu Shuwa. ’Ya’yan Yaflet maza su ne, Fasak, Bimhal da Ashwat. Waɗannan su ne ’ya’yan Yaflet maza. ’Ya’yan Shemer maza su ne, Ahi, Roga, Yehubba da Aram. ’Ya’yan ɗan’uwansa Helem su ne, Zofa, Imna, Shelesh da Amal. ’Ya’yan Zofa maza su ne, Suwa, Harnefer, Shuwal, Beri, Imra, Bezer, Hod, Shamma, Shilsha, Itran da Bera. ’Ya’yan Yeter maza su ne, Yefunne, Fisfa da Ara. ’Ya’yan Ulla maza su ne, Ara, Hanniyel da Riziya. Dukan waɗannan zuriyar Asher ne, kawunan iyalai, zaɓaɓɓun mutane, jarumawa sosai da kuma fitattun shugabanni. Yawan mutanen da suke a shirye don yaƙi, kamar yadda aka lissafta zuriyarsu, 26,000 ne. Benyamin shi ne mahaifin, Bela ɗansa na fari, Ashbel ɗansa na biyu, Ahara na uku, Noha na huɗu da Rafa na biyar. ’Ya’yan Bela maza su ne, Addar, Gera, Abihud Abishuwa, Na’aman, Ahowa, Gera, Shefufan da Huram. Waɗannan su ne zuriyar Ehud, waɗanda suke kawunan iyalan waɗanda suke zama a Geba waɗanda aka kuma kwasa zuwa Manahat. Na’aman, da Ahiya, da Gera. Gera ne shugabansu lokacin da aka kai su bauta, shi ne ya haifi Uzza da Ahilud. An haifa ’ya’ya maza wa Shaharayim a Mowab bayan ya saki matansa Hushim da Ba’ara. Ya haifi Yobab, Zibiya, Hodesh, Malkam, Yewuz, Sakiya da Mirma ta wurin Hodesh matarsa. Waɗannan su ne ’ya’yansa, kawunan iyalai. Ya haifi Abitub da Efa’al ta wurin Hushim. ’Ya’yan Efa’al maza su ne, Eber, Misham, Shemed (wanda ya gina Ono da Lod tare da ƙauyukan kewayensu), da Beriya da Shema, waɗanda suke kawunan iyalan waɗanda suke zama a Aiyalon waɗanda kuma suka kori mazaunan Gat. Ahiyo, Shashak, Yeremot Zebadiya, Arad, Eder, Mika’ilu, Isfa da Yoha su ne ’ya’yan Beriya maza. Zebadiya, Meshullam, Hizki, Heber, Ishmerai, Izliya da Yobab su ne ’ya’yan Efa’al maza. Yakim, Zikri, Zabdi, Eliyenai, Zilletai, Eliyel, Adahiya, Berahiya da Shimra su ne ’ya’yan Shimeyi maza. Ishfan, Eber, Eliyel, Abdon, Zikri, Hanan, Hananiya, Elam, Antotiya, Ifdehiya da Fenuwel su ne ’ya’yan Shashak maza. Shamsherai, Shehariya, Ataliya, Ya’areshiya, Iliya da Zikri su ne ’ya’yan Yeroham maza. Dukan waɗannan su ne kawunan iyalai, manya kamar yadda aka lissafta a cikin zuriyarsu, suka zauna a Urushalima. Yehiyel na Gibeyon ya zauna a Gibeyon. Sunan matarsa Ma’aka, ɗansa na fari kuwa shi ne Abdon, sai Zur, Kish, Ba’al, Ner, Nadab, Gedor, Ahiyo, Zeker da Miklot, wanda ya zama mahaifin Shimeya. Su ma sun zauna kusa da danginsu a Urushalima. Ner shi ne mahaifin Kish, Kish mahaifin Shawulu, kuma Shawulu ne mahaifin Yonatan, Malki-Shuwa, Abinadab da Esh-Ba’al. Ɗan Yonatan shi ne, Merib-Ba’al wanda ya zama mahaifin Mika. ’Ya’yan Mika maza su ne, Fiton, Melek, Tereya da Ahaz. Ahaz shi ne mahaifin Yehowadda, Yehowadda shi ne mahaifin Alemet, Azmawet da Zimri, Zimri kuwa shi ne mahaifin Moza. Moza shi ne mahaifin Bineya; Rafa, Eleyasa da kuma Azel. Azel yana da ’ya’ya maza shida, kuma ga sunayensu. Azrikam, Bokeru, Ishmayel, Sheyariya, Obadiya da Hanan. Dukan waɗannan ’ya’yan Azel maza ne. ’Ya’yan ɗan’uwansa Eshek su ne, Ulam ɗan farinsa, Yewush ɗansa na biyu da Elifelet na uku. ’Ya’yan Ulam maza jarumawa ne sosai waɗanda suke iya riƙe baka. Suna da ’ya’ya maza masu yawa da jikoki, 150 gaba ɗaya. Dukan waɗannan zuriyar Benyamin ne. Haka aka lissafta dukan Isra’ila a tarihin zuriyoyi a littafin sarakunan Isra’ila. Aka kwasa mutanen Yahuda zuwa zaman bauta a Babilon domin rashin aminci. To, na farkon da aka sāke zaunar da su a mallakarsu a garuruwansu, su ne waɗansu Isra’ilawa, firistoci, Lawiyawa da kuma masu hidimar haikali. Waɗanda suke daga Yahuda, daga Benyamin, da kuma daga Efraim da Manasse waɗanda suka zauna a Urushalima su ne, Uttai ɗan Ammihud, ɗan Omri, ɗan Imri, ɗan Bani, zuriyar Ferez ɗan Yahuda. Na mutanen Shilo kuwa su ne, Asahiya ɗan fari da ’ya’yansa maza. Na mutanen Zera su ne, Yewuyel. Mutane daga Yahuda sun kai 690. Na Benyamin su ne, Sallu ɗan Meshullam, ɗan Hodawiya, ɗan Hassenuwa; Ibnehiya ɗan Yeroham; Ela ɗan Uzzi, ɗan Mikri; da Meshullam ɗan Shefatiya, ɗan Reyuwel, ɗan Ibniya. Mutane daga Benyamin, kamar yadda aka lissafta zuriyarsu, sun kai 956. Dukan waɗannan mutane kawunan iyalansu ne. Na firistoci su ne, Yedahiya; Yehoyarib; Yakin; Azariya ɗan Hilkiya, ɗan Meshullam, ɗan Zadok, ɗan Merahiyot, ɗan Ahitub, shugaban da yake lura da gidan Allah; Adahiya ɗan Yeroham, ɗan Fashhur, ɗan Malkiya; da Ma’asai ɗan Adiyel, ɗan Yazera, ɗan Meshullam, ɗan Meshillemit, ɗan Immer. Firistocin da suke kawunan iyalai, sun kai 1,760. Dukansu ƙwararru ne, masu hakkin hidima a cikin gidan Allah. Na Lawiyawa su ne, Shemahiya ɗan Hasshub, ɗan Azrikam, ɗan Hashabiya, mutumin Merari; Bakbakkar, Heresh, Galal da Mattaniya ɗan Mika, ɗan Zikri, ɗan Asaf; Obadiya ɗan Shemahiya, ɗan Galal, ɗan Yedutun; da Berekiya ɗan Asa, ɗan Elkana, wanda ya zauna a ƙauyukan Netofawa. Matsaran ƙofofi su ne, Shallum, Akkub, Talmon, Ahiman da ’yan’uwansu. Shallum ne babbansu da aka ajiye a Ƙofar Sarki a gabas, har zuwa wannan lokaci. Waɗannan su ne matsaran ƙofofi na sansanin Lawiyawa. Shallum ɗan Kore, ɗan Ebiyasaf, ɗan Kora, da ’yan’uwansa matsaran ƙofofi daga iyalin (mutanen Kohat) su suke da hakkin tsaron madogaran ƙofar Tenti kamar dai yadda kakanninsu suka kasance da hakkin tsaron mashigin mazaunin Ubangiji. A dā Finehas ɗan Eleyazar ne yake lura da matsaran, kuma Ubangiji ya kasance tare da shi. Zakariya ɗan Meshelemiya shi ne mai tsaro a mashigin Tentin Sujada. Duka-duka, waɗanda aka zaɓa don su zama matsaran madogaran ƙofa sun kai 212. Aka rubuta su zuriya-zuriya a ƙauyukansu. Dawuda da Sama’ila mai duba ne suka sa matsaran a wurarensu na aminci. Su da zuriyarsu, su suke lura da tsaron ƙofofin gidan Ubangiji, gidan da ake kira Tenti. Matsaran suna a kusurwoyi huɗu, gabas, yamma, arewa da kudu. ’Yan’uwansu a ƙauyukansu sukan zo lokaci, lokaci su yi ayyukansu kwana bakwai, bakwai. Amma manyan matsara huɗu, waɗanda suke Lawiyawa, an danƙa musu hakkin lura da ɗakuna da kuma wuraren ajiya a gidan Allah. Sukan kwana a kewayen gidan Allah, domin dole su tsare shi; kuma su suke lura da mabuɗi don buɗewa a kowace safiya. Waɗansunsu su ne suke lura da kayayyakin da ake amfani da su a hidimar haikali; sukan ƙirga su sa’ad da ake shigar da su da sa’ad da ake fitar da su. An sa waɗansu su lura da kayayyakin da kuma dukan waɗansu kayan wuri mai tsarki, da kuma gari da ruwan inabi, da mai, turare da kuma kayan yaji. Amma waɗansu firistoci ne suke harhaɗa kayan yajin. Wani Balawe mai suna Mattitiya, ɗan farin Shallum mutumin Kora ne aka danƙa masa hakkin toya burodin miƙawa. Waɗansu ’yan’uwansu Kohatawa ne suke lura da shiryawa burodin da ake kaiwa a tebur a kowane Asabbaci. Waɗanda suke mawaƙa, kawunan iyalan Lawiyawa, sukan zauna a ɗakunan haikali kuma ba sa yin waɗansu ayyuka domin su suke da hakkin aiki dare da rana. Dukan waɗannan su ne kawunan iyalan Lawiyawa, manya kamar yadda aka lissafta su a zuriyarsu, kuma suna zama a Urushalima. Yehiyel mahaifin Gibeyon ya zauna a Gibeyon. Matarsa ita ce Ma’aka ɗansa na fari kuwa shi ne Abdon, sai Zur, Kish, Ba’al, Ner, Nadab, Gedor, Ahiyo, Zakariya da Miklot. Miklot shi ne mahaifin Shimeyam. Su ma sun zauna kusa da danginsu a Urushalima. Ner shi mahaifin Kish, Kish mahaifin Shawulu, kuma Shawulu shi ne mahaifin Yonatan, Malki-Shuwa, Abinadab da Esh-Ba’al. Ɗan Yonatan shi ne, Merib-Ba’al wanda shi ne mahaifin Mika. ’Ya’yan Mika maza su ne, Fiton, Melek, Tareya da Ahaz. Ahaz shi ne mahaifin Yada, Yada shi ne mahaifin Alemet, Azmawet da Zimri, Zimri kuwa shi ne mahaifin Moza. Moza shi ne mahaifin Bineya; Refahiya, Eleyasa da kuma Azel. Azel yana da ’ya’ya maza shida, kuma ga sunayensu. Azrikam, Bokeru, Ishmayel, Sheyariya, Obadiya da Hanan. Waɗannan su ne ’ya’yan Azel maza. To, fa, Filistiyawa suka yi yaƙi da Isra’ilawa; Isra’ilawa kuwa suka gudu a gabansu, da yawa kuma suka mutu a kan Dutsen Gilbowa. Filistiyawa suka matsa sosai suna bin Shawulu da ’ya’yansa maza, suka kuma kashe ’ya’yansa maza Yonatan, Abinadab da Malki-Shuwa. Yaƙin ya yi tsanani kewaye da Shawulu, kuma sa’ad da maharba suka rutsa shi, sai suka ji masa rauni. Sai Shawulu ya ce wa mai riƙe masa kayan yaƙi, “Zare takobinka ka soke ni, in ba haka ba waɗannan marasa kaciya za su zo su yi mini ba’a.” Amma mai ɗaukar masa kayan yaƙi ya ji tsoro bai kuwa yi haka ba; saboda haka Shawulu ya zāre takobinsa ya fāɗi a kansa. Da mai ɗaukar masa kayan yaƙi ya ga Shawulu ya mutu, sai shi ma ya fāɗi a kan takobinsa ya mutu. Ta haka Shawulu da ’ya’yansa maza uku suka mutu, dukan gidansa kuwa suka mutu tare. Sa’ad da dukan Isra’ilawa a cikin kwari suka ga cewa mayaƙansu suna gudu, kuma cewa Shawulu da ’ya’yansa maza sun mutu, sai suka bar garuruwansu suka gudu. Filistiyawa kuwa suka zo suka zauna a cikinsu. Kashegari, da Filistiyawa suka zo don su tuttuɓe waɗanda suka mutu, sai suka sami Shawulu da ’ya’yansa maza sun mutu a Dutsen Gilbowa. Suka tuttuɓe shi suka yanke kansa suka ɗauka duk da kayan yaƙinsa, suka kuma aika ’yan aika ko’ina a ƙasar Filistiyawa, a yi shela labarin a cikin gumakansu da kuma mutanensu. Suka sa kayan yaƙinsa a haikalin allahnsu suka kuma rataye kansa a haikalin Dagon. Sa’ad da mazaunan Yabesh Gileyad suka ji dukan abin da Filistiyawa suka yi wa Shawulu, sai dukan jarumawa suka tafi suka ɗauki jikunan Shawulu da na ’ya’yansa maza suka kawo Yabesh. Sa’an nan suka binne ƙasusuwan a ƙarƙashin babban itace oak a Yabesh, suka kuma yi azumi kwana bakwai. Shawulu ya mutu domin rashin aminci ga Ubangiji; bai kiyaye maganar Ubangiji ba, ya ma nemi shawarar mace mai duba, bai kuwa nemi nufin Ubangiji ba. Saboda haka Ubangiji ya kashe shi, ya miƙa mulkin ga Dawuda ɗan Yesse. Dukan Isra’ila fa suka taru wurin Dawuda a Hebron suka ce, “Mu jiki da jininka ne. A dā, ko a lokacin da Shawulu yake sarki, ai, kai ne kake shugabantar Isra’ila a yaƙe-yaƙe. Kuma Ubangiji Allahnka ya ce maka, ‘Za ka zama makiyayin mutanena Isra’ila, za ka kuma zama mai mulkinsu.’ ” Sa’ad da dukan dattawan Isra’ila suka zo wurin Sarki Dawuda a Hebron, suka yi yarjejjeniya da shi a gaban Ubangiji, suka kuwa shafe Dawuda ya zama sarki a bisa Isra’ila, yadda Ubangiji ya yi alkawari ta wurin Sama’ila. Dawuda tare da dukan Isra’ilawa suka taka zuwa Urushalima (wato, Yebus). Yebusiyawan da suke zama a wurin suka ce wa Dawuda, “Ba za ka shiga nan ba.” Duk da haka, Dawuda ya ci kagarar Sihiyona, Birnin Dawuda. Dawuda ya ce, “Duk wanda ya jagoranci yaƙi a kan Yebusiyawa zai zama babban shugaban mayaƙa.” Yowab ɗan Zeruhiya ya fara haurawa, ta haka ya zama shugaba. Dawuda zauna a kagarar, ta haka aka kira ta Birnin Dawuda. Sai ya gina birni kewaye da shi, daga madogaran gini zuwa katangar da take kewaye, yayinda Yowab ya maido da sauran birnin. Dawuda kuwa ya ƙara ƙarfi, domin Ubangiji Maɗaukaki yana tare da shi. Waɗannan su ne manyan jarumawan Dawuda, su ne, tare da dukan Isra’ila, suka ba wa mulkinsa goyon baya mai ƙarfi da ya kai bisa dukan ƙasar, yadda Ubangiji ya yi alkawari. Ga jerin sunayen jarumawan Dawuda. Yashobeyam wani ɗan Hakmoni, shi ne babban shugaba; ya ɗaga māshinsa a kan mutum ɗari uku, waɗanda ya kashe a ƙarawa guda kawai. Biye da shi, shi ne Eleyazar ɗan Dodo mutumin Aho, ɗaya daga cikin jarumawa uku. Yana tare da Dawuda a Fas Dammim sa’ad da Filistiyawa suka taru can don yaƙi. A wani wuri inda akwai gona cike da sha’ir, sojoji suka gudu daga Filistiyawa. Sai shi da Dawuda suka shiga gonar sha’ir ɗin, suka tsaya ciki don su tsare ta. Suka ragargaza Filistiyawa, Ubangiji kuma ya kawo babban nasara. Wata rana uku cikin manyan mutanen nan talatin suka gangara wurin Dawuda zuwa dutse a kogon Adullam, yayinda ƙungiyar Filistiyawa suke sansani a Kwarin Refayim. A lokacin Dawuda yana cikin mafaka, sojojin Filistiyawa kuma suna a Betlehem. Dawuda ya ji marmarin ruwan sha sai ya ce, “Kash, a ce wani zai sami mini ruwan sha daga rijiya kusa da ƙofar Betlehem mana!” Sai Ukun suka kutsa kai cikin sansanin Filistiyawa, suka ja ruwa daga rijiyar da take kusa da ƙofar Betlehem suka ɗauko shi suka kawo wa Dawuda. Amma ya ƙi yă sha; a maimako, sai ya zubar da shi a gaban Ubangiji. Ya ce, “Allah yă sawwaƙe in yi haka, ya kamata in sha jinin waɗannan mutanen da suka yi kasai da rayukansu?” Domin sun yi kasai da rayukansu don su dawo da shi, Dawuda bai sha shi ba. Irin abubuwan da jarumawa ukun nan suka yi ke nan. Abishai ɗan’uwan Yowab shi ma babba ne cikin Ukun nan. Ya ɗaga māshinsa a kan mutum ɗari uku, waɗanda ya kashe, ya kuma zama sananne kamar Ukun. Aka ninka girmama shi bisa Ukun, sai ya zama shugaba, ko da yake ba a haɗa shi a cikinsu ba. Benahiya ɗan Yehohiyada shi ma wani barden yaƙi ne daga Kabzeyel, wanda ya yi manyan abubuwa. Ya bugi gwanayen Mowab biyu. Ya kuma gangara zuwa cikin rami a ranar da aka yi dusar ƙanƙara ya kashe zaki. Ya kuma kashe wani mutumin Masar mai tsayi ƙafa bakwai da rabi. Ko da yake mutumin Masar yana da māshi kamar sandan masaƙa a hannunsa, Benahiya ya yaƙe shi da kulki. Ya ƙwace māshin daga hannun mutumin Masar ya kuma kashe shi da māshin nan nasa. Irin abubuwan da Benahiya ɗan Yehohiyada ya yi ke nan; shi ma sananne ne kamar waɗannan jarumawa uku. Aka ɗauka shi da bangirma fiye da Talatin nan, amma ba a haɗa shi cikin Ukun ba. Dawuda kuwa ya sa shi yă lura da masu tsaron lafiyarsa. Jarumawan nan su ne, Asahel ɗan’uwan Yowab, Elhanan ɗan Dodo daga Betlehem, Shammot mutumin Haror, Helez mutumin Felon, Ira ɗan Ikkesh daga Tekowa, Abiyezer daga Anatot, Sibbekai mutumin Husha, Ilai mutumin Aho, Maharai mutumin Netofa, Heled ɗan Ba’ana mutumin Netofa, Ittai ɗan Ribai daga Gibeya a Benyamin, Benahiya mutumin Firaton, Hurai daga kogunan Ga’ash, Abiyel mutumin Arba, Azmawet mutumin Harum, Eliyaba mutumin Sha’albo, ’ya’yan Hashem mutumin Gizon maza, Yonatan ɗan Shageye mutumin Harar, Ahiyam ɗan Sakar mutumin Harar, Elifal ɗan Ur, Hefer mutumin Mekerat, Ahiya mutumin Felon, Hezro mutumin Karmel, Na’arai ɗan Ezbai, Yowel ɗan’uwan Natan, Mibhar ɗan Hagiri, Zelek mutumin Ammon Naharai Baroti, mai ɗaukar kayan yaƙin Yowab ɗan Zeruhiya, Ira mutumin Itra, Gareb mutumin Itra, Uriya mutumin Hitti Zabad ɗan Alai, Adina ɗan Shiza mutumin Ruben, wanda shi ne babba na mutanen Ruben, kuma talatin suna tare da shi, Hanan ɗan Ma’aka, Yoshafat mutumin Mit, Uzziya mutumin Ashtarot, Shama da Yehiyel ’ya’yan Hotam mutumin Arower maza, Yediyayel ɗan Shimri, ɗan’uwansa Yoha mutumin Tiz, Eliyel mutumin Ma’aha, Yeribai da Yoshawiya ’ya’yan Elna’am maza, Itma mutumin Mowab, Eliyel, Obed da Ya’asiyel mutumin Mezob. Waɗannan su ne mutanen da suka zo wurin Dawuda a Ziklag, yayinda aka kore shi daga gaban Shawulu ɗan Kish (suna cikin jarumawan da suka taimake shi a yaƙi; suna da baka suna kuma iya harba kibiya, ko majajjawa da hannun dama ko na hagu; su ’yan’uwan Shawulu ne daga kabilar Benyamin): Ahiyezer babbansu da Yowash ’ya’yan Shema’a maza daga Gibeya; Yeziyel da Felet ’ya’yan Azmawet; Beraka, Yehu daga Anatot, da Ishmahiya daga Gibeyon, wani jarumi a cikin Talatin nan, wanda shi ne shugaban Talatin; Irmiya, Yahaziyel, Yohanan, Yozabad daga Gedera, Eluzai, Yerimot, Beyaliya, Shemariya da Shefatiya daga Haruf; Elkana, Isshiya, Azarel, Yoyezer da Yashobeyam daga Kora; da Yoyela da Zebadiya ’ya’yan Yeroham maza daga Gedor. Sai waɗansu mutanen Gad suka koma suna goyon bayan Dawuda suka kuma haɗa kai da shi a kagararsa a hamada. Su ƙwararrun mayaƙa ne, a shirye don yaƙi, kuma suna iya riƙe garkuwa da māshi. Fuskokinsu kamar fuskoki zakoki, kuma suna da sauri kamar bareyi a kan duwatsu. Ezer shi ne babba, Obadiya shi ne mai binsa a shugabanci, Eliyab na uku, Mismanna na huɗu, Irmiya na biyar, Attai na shida, Eliyel na bakwai, Yohanan na takwas, Elzabad na tara, Irmiya na goma da kuma Makbannai na goma sha ɗaya. Waɗannan mutanen Gad shugabannin mayaƙa ne; ƙarami a cikinsu zai iya ƙara da mutum ɗari, kuma babba a cikin zai iya ƙara da dubu. Su ne suka haye Urdun a wata na farko sa’ad da kogin ya yi ambaliya, suka kuma kori duk mai rai a kwarin, na wajen gabas da na wajen yamma. Sauran mutanen Benyamin da waɗansu mutanen Yahuda su ma suka zo wurin Dawuda a kagararsa. Sai Dawuda ya fita don yă tarye su, ya kuma ce musu, “In kun zo wurina da salama, don ku taimake ni, to, ina a shirye in bar ku ku haɗa kai tare da ni. Amma in kun zo don ku bashe ni ga abokan gābana sa’ad da hannuwana ba su da laifi a rikici, bari Allah na kakanninmu yă duba yă kuma shari’anta ku.” Sai Ruhu ya sauko a kan Amasai, shugaban Talatin nan, sai ya ce, “Mu naka ne, ya Dawuda! Muna tare da kai, ya ɗan Yesse! Nasara, nasara gare ka, nasara kuma ga waɗanda suke taimakonka. Gama Allahnka zai taimake ka.” Saboda haka Dawuda ya karɓe su ya kuma mai da su shugabannin ƙungiyoyin maharansa. Waɗansu mutanen Manasse suka haɗa kai da Dawuda sa’ad da ya tafi tare da Filistiyawa don yă yaƙi Shawulu (Shi da mutanensa ba su taimaki Filistiyawa ba domin bayan shawarwari, shugabanninsu suka salame shi. Sun ce, “Za mu biya da kawunanmu in ya koma ga maigidansa Shawulu.”) Da Dawuda ya tafi Ziklag, waɗannan mutanen Manasse ne suka haɗa kai da shi. Adna, Yozabad, Yediyayel, Mika’ilu, Yozabad, Elihu da Zilletai, shugabannin ƙungiyoyi na dubu a cikin Manasse. Suka taimaki Dawuda a kan ƙungiyoyin hari, gama dukansu jarumawa ne sosai, kuma su shugabanni ne a cikin mayaƙansa. Kowace rana mutane suka riƙa zuwa don su taimaki Dawuda, sai da ya kasance da runduna mai girma, kamar mayaƙan Allah. Ga yawan mutanen shiryayyu don yaƙi waɗanda suka zo wurin Dawuda a Hebron don su mai da mulkin Shawulu gare shi, yadda Ubangiji ya faɗa. Mutanen Yahuda, masu riƙe garkuwa da māshi, su 6,800 shiryayyu don yaƙi; mutanen Simeyon, jarumawa shiryayyu don yaƙi, su 7,100; mutanen Lawi, su 4,600, haɗe da Yehohiyada, shugaban iyalin Haruna tare da mutane 3,700, da Zadok, matashi jarumi sosai, tare da shugabanni su 22 daga iyalinsa; mutanen Benyamin, ’yan’uwan Shawulu, su 3,000, yawanci waɗanda suke biyayya ga gidan Shawulu sai lokacin; mutanen Efraim, jarumawa, sanannu cikin gidajensu, su 20 800; mutanen rabin kabilar Manasse, sanannu da sunaye suka zo suka mai da Dawuda sarki, su 18,000; mutanen Issakar, masu fahimtar lokuta suka kuma san abin da ya kamata Isra’ila ya yi, manya 200, tare da danginsu a ƙarƙashin shugabancinsu; mutanen Zebulun, ƙwararru sojoji shiryayyu don yaƙi da kowane irin makami, suka zo don su taimaki Dawuda da zuciya ɗaya, su 50,000; mutanen Naftali su 1,000 shugabanni, tare da mutane 37,000 masu riƙe garkuwa da masu; mutanen Dan, shiryayyu don yaƙi, su 28,600; mutanen Asher, ƙwararrun sojoji shiryayyu don yaƙi, su 40,000; kuma daga gabashin Urdun, mutanen Ruben, Gad da kuma rabin kabilar Manasse, masu kayan yaƙi iri-iri, su 120,000. Dukan waɗannan mayaƙa ne waɗanda suka ba da kansu da yardar rai su yi hidima. Suka zo Hebron da cikakken niyya don su naɗa Dawuda sarki a bisa dukan Isra’ila. Duka sauran Isra’ilawa su ma suka goyi baya a naɗa Dawuda sarki. Mutanen suka yi kwana uku a can tare da Dawuda, suna ci suna sha, gama iyalansu sun yi musu tanadi. Haka ma, maƙwabtansu daga nesa har Issakar, Zebulun da Naftali suka zo suka kawo abinci a kan jakuna, raƙuma, alfadarai da shanu. Akwai tanadin mai yawa na gari, kauɗar ɓaure, nonnan busassun ’ya’yan inabi, ruwan inabi, mai, shanu da tumaki. Duk an yi haka don a nuna farin ciki ƙwarai a cikin dukan ƙasar Isra’ila. Sai Dawuda ya tattauna da kowane ɗaya daga cikin shugabanninsa, shugabannin sojoji na dubu-dubu da na ɗari-ɗari. Sa’an nan ya ce wa dukan taron Isra’ila, “In ya yi muku kyau kuma in nufin Ubangiji Allahnmu ne, bari mu aika da saƙo nesa da kuma ko’ina zuwa ga sauran ’yan’uwanmu a duk iyakokin Isra’ila, da kuma zuwa ga firistoci da Lawiyawa waɗanda suke tare da su a garuruwansu da makiyayansu, su zo wurinmu. Bari mu ɗauko akwatin alkawarin Allahnmu mu kawo wurinmu, gama ba mu neme shi a lokacin mulkin Shawulu ba.” Dukan taron jama’a suka yarda su yi haka, domin ya yi daidai ga dukan mutane. Saboda haka Dawuda ya tattara dukan Isra’ilawa, daga Kogin Shihor a Masar zuwa Lebo Hamat, don su kawo akwatin alkawarin Allah daga Kiriyat Yeyarim. Dawuda da dukan Isra’ilawa tare da shi suka tafi Ba’ala na Yahuda (Kiriyat Yeyarim) don su haura daga can su kawo akwatin alkawarin Allah Ubangiji, wanda yake zama tsakanin kerubobi, akwatin alkawarin da ake kira da Sunan. Suka ɗauki akwatin alkawarin Allah daga gidan Abinadab a kan sabon keken shanu, Uzza da Ahiyo ne suke lura da shi. Dawuda da dukan Isra’ilawa suka yi shagali da dukan ƙarfinsu a gaban Allah, tare da waƙoƙi da garayu, molaye, ganguna, kuge da ƙahoni. Sa’ad da suka kai masussukar Kidon, Uzza ya miƙa hannunsa don yă gyara akwatin alkawarin, gama shanun sun yi tuntuɓe. Sai fushin Ubangiji ya ƙuna a kan Uzza, ya kuma buge shi domin ya sa hannunsa a kan akwatin alkawarin. Sai ya mutu a can a gaban Allah. Ran Dawuda ya ɓace domin Ubangiji ya husata a kan Uzza, kuma har wa yau ana ce da wannan wuri Ferez Uzza. Dawuda ya ji tsoron Allah a wannan rana ya kuma yi tambaya, “Yaya zan taɓa kawo akwatin alkawarin Allah gare ni?” Don haka bai ɗauki akwatin alkawarin ya kasance tare da shi a Birnin Dawuda ba. A maimakon haka, ya kai shi gidan Obed-Edom mutumin Gat. Akwatin Alkawarin Allah ya zauna tare da iyalin Obed-Edom a gidansa wata uku, Ubangiji kuwa ya albarkaci gidan Obed-Edom da kome da yake da shi. To, fa, Hiram sarkin Taya ya aika da ’yan aika zuwa wurin Dawuda, tare da gumaguman al’ul, maginan duwatsu da kafintoci, don su gina wa Dawuda fada. Dawuda kuwa ya san cewa Ubangiji ya kafa shi a matsayin sarki a bisa Isra’ila kuma cewa an ɗaukaka mulkinsa saboda mutanensa Isra’ila. A Urushalima, Dawuda ya ƙara auren waɗansu mata, ya kuma zama mahaifin ƙarin ’ya’yan maza da mata. Ga sunayen yaran da aka haifa masa a can. Shammuwa, Shobab, Natan, Solomon, Ibhar, Elishuwa, Elfelet, Noga, Nefeg, Yafiya, Elishama, Beyeliyada da Elifelet. Sa’ad da Filistiyawa suka ji an naɗa Dawuda sarki a bisa dukan Isra’ila, sai suka haura da cikakken mayaƙa don su neme shi, amma Dawuda ya ji game da wannan ya kuwa fita don yă ƙara da su. To, fa, Filistiyawa suka zo suka kai wa Kwarin Refayim hari; sai Dawuda ya roƙi Allah ya ce, “In tafi in yaƙi Filistiyawa? Za ka ba da su gare ni?” Ubangiji ya amsa masa ya ce, “Ka tafi, zan ba da su gare ka.” Saboda haka Dawuda da mutanensa suka haura zuwa Ba’al-Ferazim, a can kuwa suka ci Filistiyawa da yaƙi. Sai ya ce, “Kamar yadda ruwa kan raraki ƙasa, haka Allah ya raraki abokan gābana ta wurin hannuna.” Saboda haka aka kira wurin Ba’al-Ferazim. Filistiyawa suka yashe allolinsu, Dawuda kuma ya ba da umarnai a ƙone su a wuta. Filistiyawa suka sāke kai hari wa kwarin; sai Dawuda ya sāke roƙi Allah, Allah kuwa ya amsa masa, “Kada ka tafi kai tsaye, amma ka yi zobe kewaye da su, ka kuma fāɗa musu a gaban itatuwan tsamiya. Da zarar ka ji motsin takawa a sama itatuwan tsamiya, ka fita don yaƙi, domin wannan zai nuna cewa Allah ya fita a gabanka don yă bugi mayaƙan Filistiyawa.” Saboda haka Dawuda ya yi kamar yadda Allah ya umarce shi, suka kuma bugi mayaƙan Filistiyawa, tun daga Gibeyon har zuwa Gezer. Sai sunan Dawuda ya bazu ko’ina a ƙasar, Ubangiji kuwa ya sa dukan al’ummai suka ji tsoronsa. Bayan Dawuda ya yi gine-gine wa kansa a Birnin Dawuda, sai ya shirya wuri domin akwatin alkawarin Allah, ya kuma kafa tenti dominsa. Sa’an nan Dawuda ya ce, “Babu wani sai ko Lawiyawa kaɗai za su ɗauka akwatin alkawarin Allah, gama Ubangiji ya zaɓe su su ɗauka akwatin alkawarin Ubangiji su kuma yi hidima a gabansa har abada.” Dawuda ya tattara dukan Isra’ila a Urushalima don su haura da akwatin alkawarin Ubangiji zuwa wurin da aka shirya dominsa. Ya tattara zuriyar Haruna a wuri ɗaya da kuma Lawiyawa. Daga zuriyar Kohat, Uriyel shugaba da dangi 120; daga zuriyar Merari Asahiya shugaba da dangi 220; daga zuriyar Gershom, Yowel shugaba da dangi 130; daga zuriyar Elizafan, Shemahiya shugaba da dangi 200; daga zuriyar Hebron, Eliyel shugaba da dangi 80; daga zuriyar Uzziyel, Amminadab shugaba da dangi 112. Sa’an nan Dawuda ya kira Zadok da Abiyatar, firistoci, tare da Uriyel, Asahiya, Yowel, Shemahiya, Eliyel da Amminadab, Lawiyawa. Ya ce musu, “Ku ne kawunan iyalan Lawiyawa; ku da ’yan’uwanku Lawiyawa, sai ku tsarkake kanku ku hauro da akwatin alkawarin Ubangiji, Allah na Isra’ila, zuwa wurin da na shirya dominsa. Domin ku, Lawiyawa ba ku haura da shi da farko ba ne ya sa Ubangiji Allahnmu ya husata a kanmu. Ba mu tambaye shi game da yadda za mu yi shi a hanyar da aka ƙayyade ba.” Saboda haka firistoci da Lawiyawa suka tsarkake kansu don su hauro da akwatin alkawarin Ubangiji, Allah na Isra’ila. Sai Lawiyawa suka ɗauki akwatin alkawarin Allah da sanduna a kafaɗunsu, kamar yadda Musa ya umarta bisa ga maganar Ubangiji. Dawuda ya faɗa wa shugabannin Lawiyawa su sa ’yan’uwansu su zama mawaƙa don su rera waƙoƙi masu farin ciki, da kayayyakin bushe-bushe, da kaɗe-kaɗe, molaye, garayu da ganguna. Saboda haka Lawiyawa suka zaɓi Heman ɗan Yowel, da Asaf ɗan Berekiya daga cikin ’yan’uwansu. Daga iyalin Merari kuma aka zaɓi Etan ɗan Kushahiya. Tare da su kuma ’yan’uwansa da suke biye bisa ga matsayi. Wato, Zakariya, Ya’aziyel, Shemiramot, Yehiyel, Unni, Eliyab, Ben, Ma’asehiya, Mattitiya, Elifelehu, Miknehiya, Obed-Edom da Yehiyel, matsaran ƙofofi. Mawaƙan nan Heman, Asaf da Etan, ne za su buga kugen tagulla. Zakariya, Aziyel, Shemiramot, Yehiyel, Unni, Eliyab, Ma’asehiya da Benahiya, ne za su kaɗa molaye masu murya sama-sama, bisa ga alamot. Mattitiya, Elifelehu, Miknehiya, Obed-Edom, Yehiyel da Azaziya, ne za su ja garayu masu murya ƙasa-ƙasa bisa ga sheminit. Kenaniya, shugaban Lawiyawa, shi ne mai bi da waƙoƙi. Wannan hakkinsa ne, gama shi gwani ne a wannan fanni. Berekiya da Elkana, ne za su zama masu lura da ƙofofi domin akwatin alkawarin. Shebaniya, Yoshafat, Netanel, Amasai, Zakariya, Benahiya da Eliyezer firistoci, su ne za su busa ƙahoni a gaban akwatin alkawarin Allah. Obed-Edom da Yehiya su ma za su zama masu lura da ƙofofi domin akwatin alkawarin. Sai Dawuda da dattawan Isra’ila da shugabannin ƙungiyoyi dubu suka haura don su kawo akwatin alkawarin Ubangiji daga gidan Obed-Edom, da farin ciki. Domin Allah ya taimaki Lawiyawan da suke ɗaukar akwatin alkawarin Ubangiji, aka miƙa hadayar bijimai bakwai da raguna bakwai. To, fa, Dawuda yana saye da kyakkyawar rigar lilin, kamar yadda dukan Lawiyawa waɗanda suke ɗaukar akwatin alkawarin suka sa, da kuma yadda mawaƙa, da Kenaniya, wanda yake bi da waƙar mawaƙan ya sa. Dawuda kuma ya sa efod lilin. Sai dukan Isra’ila suka kawo akwatin alkawarin Ubangiji da sowa, da ƙarar ƙahonin raguna da busan ƙahoni, da na ganguna, suna kuma kaɗa molaye da garayu. Yayinda akwatin alkawarin Ubangiji yake shiga Birnin Dawuda, Mikal ’yar Shawulu ta leƙa daga taga. Sa’ad da ta ga Sarki Dawuda yana rawa yana shagali, sai ta rena masa wayo a zuciyarta. Suka fa kawo akwatin alkawarin Allah, suka sa a cikin tentin da Dawuda ya kafa dominsa, suka kuma miƙa hadayun ƙonawa da hadayu na salama a gaban Allah. Bayan Dawuda ya gama miƙa hadayu na ƙonawa da hadayu na salama, sai ya albarkaci mutane a cikin sunan Ubangiji. Sa’an nan ya ba da dunƙulen burodi da wainar dabino da kuma kauɗar zabibi ga kowane mutumin Isra’ila namiji da ta mace. Ya sa Lawiyawa su yi hidima a gaban akwatin alkawarin Ubangiji, su ɗaukaka, su gode, su kuma yabi Ubangiji, Allah na Isra’ila. Asaf shi ne babba, sai Zakariya na biye, sa’an nan Ya’aziyel, Shemiramot, Yehiyel, Mattitiya, Eliyab, Benahiya, Obed-Edom da Yehiyel. Su ne za su kaɗa molaye, da garayu, Asaf kuwa zai buga ganguna, Benahiya da Yahaziyel firistoci za su busa ƙahoni kullum a gaban akwatin alkawarin Allah. A wannan rana, da farko, Dawuda ya sa Asaf da ’yan’uwansa su rera wannan zabura ta yabo ga Ubangiji. Ku yi godiya ga Ubangiji, ku yi shelar sunansa; ku sanar a cikin al’ummai abin da ya yi. Ku rera gare shi, ku rera yabo gare shi; ku faɗa dukan ayyukan banmamakinsa. Ku ɗaukaka a cikin sunansa mai tsarki bari zukatan waɗanda suke neman Ubangiji su yi farin ciki. Ku dogara ga Ubangiji da kuma ƙarfinsa; ku nemi fuskarsa kullum. Ku tuna ayyukan banmamakin da ya aikata, mu’ujizansa da kuma hukuntai da ya yanke, Ya ku zuriyar Isra’ila bayinsa, Ya ku ’ya’yan Yaƙub maza, zaɓaɓɓunsa. Shi ne Ubangiji Allahnmu; hukuntansa suna a cikin dukan duniya. Yakan tuna da alkawarinsa har abada, maganar da ya umarta, har tsararraki dubu, alkawarin da ya yi wa Ibrahim rantsuwar da ya yi ga Ishaku. Ya tabbatar da shi ga Yaƙub kamar ƙa’ida, ga Isra’ila kamar madawwamin alkawari. “Gare ka zan ba da ƙasar Kan’ana kamar rabon da za ka gāda.” Sa’ad da suke kima, kima sosai, da kuma baƙi a cikinta, suka yi ta yawo daga al’umma zuwa al’umma, daga wannan mulki zuwa wancan. Bai bar wani ya zalunce su ba; saboda su ya tsawata wa sarakuna. “Kada ku taɓa shafaffuna; kada ku yi wa annabawana lahani.” Ku rera ga Ubangiji, ku duniya duka; ku yi shelar cetonsa kowace rana. Ku furta ɗaukakarsa a cikin al’ummai, ayyukansa masu al’ajabai a cikin mutane. Gama Ubangiji mai girma ne ya kuma cancanci yabo; dole a ji tsoronsa fiye da dukan alloli. Gama dukan allolin al’ummai gumaka ne, amma Ubangiji ya yi sammai. Daraja da ɗaukaka suna a gabansa; ƙarfi da farin ciki suna a wurin zamansa. Ku yabi Ubangiji, ku iyalan al’ummai, ku yabi ɗaukaka da ƙarfin Ubangiji, ku ba wa Ubangiji ɗaukakar da ta dace da sunansa. Ku kawo hadaya ku kuma zo gabansa; ku yi wa Ubangiji sujada cikin darajar tsarkinsa. Ku yi rawar jiki a gabansa, ya ku duniya duka! Duniya ta kahu sosai; ba za tă jijjigu ba. Bari sammai su yi farin ciki, bari duniya tă yi murna; bari su ce a cikin al’ummai, “ Ubangiji yana mulki!” Bari teku da kome da yake cikinsa su yi ruri; bari gonaki da kome a cikinsu su yi farin ciki! Sa’an nan itatuwan jeji za su rera, za su rera don farin ciki a gaban Ubangiji, gama ya zo don yă hukunta duniya. Ku yi godiya ga Ubangiji, gama shi nagari ne; ƙaunarsa madawwamiya ce. Ku yi kuka, ku ce, “Cece mu, ya Allah Mai Cetonmu; tara mu ka kuma cece mu daga al’ummai, don mu yi godiya ga sunanka mai tsarki, don mu ɗaukaka a cikin yabonka.” Yabi Ubangiji, Allah na Isra’ila, daga madawwami zuwa madawwami. Sai dukan mutane suka ce, “Amin.” Suka kuma “Yabi Ubangiji.” Dawuda ya bar Asaf da ’yan’uwansa a gaban akwatin alkawarin Ubangiji don su yi hidima a can kullum, bisa ga tsari na kowace rana. Ya kuma bar Obed-Edom da ’yan’uwansa sittin da takwas don su yi hidima tare. Obed-Edom ɗan Yedutun da Hosa kuma, su ne matsaran ƙofofi. Dawuda ya bar Zadok firist da ’yan’uwansa firistoci a gaban tabanakul na Ubangiji a tudun da yake a Gibeyon don su miƙa hadayun ƙonawa ga Ubangiji a kan bagaden hadaya ta ƙonawa kullum, da safe da kuma yamma, bisa ga kome da yake a rubutacce a cikin Dokar Ubangiji, da ya ba wa Isra’ila. Tare da su akwai Heman da Yedutun da sauran waɗannan zaɓaɓɓun da aka rubuta sunansu don yin godiya ga Ubangiji, “gama ƙaunarsa madawwamiya ce har abada.” Heman da Yedutun su ne da hakkin busa ƙahoni da kaɗa kuge da sauran kayan bushe-bushe da na kaɗe-kaɗe, waɗanda ake amfani da su lokacin da ake rera waƙoƙi masu tsarki. ’Ya’yan Yedutun maza, su aka ba wa aikin tsaron ƙofa. Sa’an nan dukan mutanen suka tashi, kowa ya koma gidansa, Dawuda ya koma gida yă sa wa iyalinsa albarka. Bayan Dawuda ya zauna a fadansa, sai ya ce wa annabi Natan, “Ga ni, ina zama a fadar da aka yi da al’ul, yayinda akwatin alkawarin Ubangiji yana a ƙarƙashin tenti.” Natan ya amsa wa Dawuda ya ce, “Duk abin da kake tunani a zuciya, ka yi, gama Allah yana tare da kai.” A daren nan maganar Allah ta zo wa Natan cewa, “Ka tafi ka faɗa wa bawana Dawuda, ‘Ga abin da Ubangiji ya ce ba kai ba ne za ka gida mini gidan da zan zauna a ciki. Ban taɓa zama a gida daga ranar da na fito da Isra’ila daga Masar ba har wa yau. Na yi ta yawo daga gefen da aka kafa tenti zuwa wani, daga wannan wuri zuwa wancan. Duk inda na tafi tare da Isra’ilawa, na taɓa ce wa wani daga cikin shugabanninsu waɗanda na umarta su yi kiwon mutanena, “Don me ba ku gida mini gidan al’ul ba?” ’ “Yanzu, ka faɗa wa bawana Dawuda, ‘Ga abin da Ubangiji Maɗaukaki ya ce, na ɗauke ka daga makiyaya da kuma daga bin garke, don ka zama mai mulki a bisa mutanena Isra’ila. Na kasance tare da kai ko’ina ka tafi, na kuma yanke dukan abokan gābanka a gabanka. Yanzu zan sa sunanka kamar sunayen mutane mafi girma na duniya. Zan kuma tanada wuri domin mutanena Isra’ila, zan kuma kafa su saboda za su kasance da gidan kansu ba kuwa za a ƙara damunsu ba. Mugayen mutane ba za su ƙara zaluntar su ba, yadda suka yi da farko da kuma suka yi tun lokacin da na sa shugabanni a bisa mutanen Isra’ila. Zan rinjaye dukan abokan gābanka. “ ‘Na furta maka cewa Ubangiji zai gina maka gida, sa’ad da kwanakinka suka ƙare ka kuma tafi don ka kasance da kakanninka, zan tā da ɗaya cikin ’ya’yanka maza, daga zuriyarka yă gāje ka, zan kuma kafa mulkinka. Shi ne zai gina gida domina, zan kuma kafa sarautarsa har abada. Zan zama Ubansa, zai kuma zama ɗana. Ba zan taɓa ɗauke ƙaunata daga gare shi, kamar yadda na ɗauke ta daga wanda ya riga ka ba. Zan sa shi a bisa gidana da mulkina har abada; kujerar sarautarsa za tă kahu har abada.’ ” Natan ya faɗa wa Dawuda dukan kalmomin wahayin nan. Sai Sarki Dawuda ya shiga ya zauna a gaban Ubangiji ya ce, “Wane ne ni, ya Ubangiji Allah, kuma wane ne iyalina, da ka kawo ni har zuwa nan? Kuma sai ka ce wannan bai isa ba a idonka, ya Allah, ka yi magana game da nan gaba na gidan bawanka. Ka dube ni sai ka ce ni ne mafi ɗaukaka cikin mutane, ya Ubangiji Allah. “Me kuma Dawuda zai ce maka saboda girmamawar da ka yi wa bawanka? Gama ka san bawanka, Ya Ubangiji. Gama saboda bawanka da kuma bisa ga nufinka, ka yi wannan babban abu, ka kuma sanar da dukan manyan alkawura. “Babu wani kamar ka, ya Ubangiji, babu kuma Allah sai kai, kamar yadda muka ji da kunnuwanmu. Wane ne kuma yake kamar mutanenka Isra’ila, al’umma guda a duniya wadda Allahnta ya fita don yă fanshi mutane wa kansa, ya kuma yi suna wa kansa, ya kuma aikata manyan abubuwa masu banmamaki masu banrazana ta wurin korin al’ummai daga gaban mutanenka, waɗanda ka fansa daga Masar? Ka mai da mutanenka Isra’ila na kanka har abada, kuma kai, ya Ubangiji, ka zama Allahnsu. “Yanzu kuwa, Ubangiji, bari alkawarin da ka yi game da bawanka da gidansa yă kahu har abada. Yi kamar yadda ka yi alkawari, saboda zai kahu kuma sunanka zai zama mai girma har abada. Sa’an nan mutane za su ce, ‘ Ubangiji Maɗaukaki, Allah a bisa Isra’ila, Allahn Isra’ila ne!’ Kuma gidan bawanka Dawuda zai kahu a gabanka. “Kai, Allahna, ka bayyana ga bawanka cewa za ka gina gida dominsa. Ta haka bawanka ya sami ƙarfin gwiwa ya yi addu’a gare ka. Ya Ubangiji, kai ne Allah! Ka yi alkawari abubuwa masu kyau wa bawanka. Yanzu ka ji daɗi don ka albarkace gidan bawanka, don yă ci gaba har abada a gabanka; gama kai, ya Ubangiji, ka albarkace shi, ya kuma sami albarka ke nan har abada.” Ana nan sai Dawuda ya ci Filistiyawa ya kuma rinjaye su, ya ƙwace Gat da ƙauyukan kewayenta daga mulkin Filistiyawa. Dawuda ya kuma ci Mowabawa, suka zama bayinsa suka kuma biya haraji. Ban da haka, Dawuda ya yaƙi Hadadezer sarkin Zoba, har can Hamat, sa’ad da ya je don yă kafa mulkinsa a wajen Kogin Yuferites. Dawuda ya kame keken yaƙinsa dubu ɗaya, da mahayan kekunan yaƙi dubu bakwai da sojojin kafa guda dubu ashirin. Ya yayyanke dukan agaran dawakansa, amma ya bar dawakai da suka isa jan kekunan yaƙi ɗari. Da Arameyawan Damaskus suka zo su taimaki Hadadezer sarkin Zoba, sai Dawuda ya bugi dubu ashirin da biyunsu. Ya sa ƙungiyoyin sojoji a masarautar Arameyawan Damaskus. Arameyawan kuwa suka zama bayinsa, suka kuma kawo haraji. Ubangiji ya ba Dawuda nasara a ko’ina da ya tafi. Dawuda ya kwashe garkuwoyin zinariyan da shugabannin sojojin Hadadezer suke riƙe, ya kawo su Urushalima. Daga Teba da Kun, garuruwan da suke ƙarƙashin Hadadezer, Dawuda ya kwashe tagulla da yawa sosai, wanda Solomon ya yi amfani don yă yi Tekun tagulla, ginshiƙai da kuma kayayyakin tagulla dabam-dabam. Sa’ad da Towu sarkin Hamat ya ji cewa Dawuda ya ci mayaƙan Hadadezer sarkin Zoba gaba ɗaya, sai ya aiki ɗansa Hadoram zuwa wurin Sarki Dawuda yă gaishe shi yă kuma yi masa barka da nasara a yaƙi a kan Hadadezer, wanda yake yaƙi da Towu. Hadoram ya kawo kowane irin kayayyakin zinariya da na azurfa da na tagulla. Sarki Dawuda ya miƙa waɗannan kayayyakin ga Ubangiji, kamar yadda ya yi da azurfa da kuma zinariyan da ya kwaso daga dukan waɗannan al’ummai. Edom da Mowab, Ammonawa da Filistiyawa, da kuma Amalek. Abishai ɗan Zeruhiya ya bugi mutanen Edom dubu goma sha takwas a Kwarin Gishiri. Ya sa ƙungiyoyin sojoji a Edom, dukan mutanen Edom kuwa suka zama bayin Dawuda. Ubangiji ya ba Dawuda nasara a ko’ina da ya tafi. Dawuda ya yi mulki a bisa dukan Isra’ila, yana yin abin da yake daidai da kuma gaskiya saboda dukan mutanensa. Yowab ɗan Zeruhiya shi ne shugaban mayaƙa; Yehoshafat ɗan Ahilud shi ne marubuci; Zadok ɗan Ahitub da Abimelek ɗan Abiyatar su ne firistoci; Shafsha shi ne magatakarda; Benahiya ɗan Yehohiyada shi ne shugaban Keretawa da Feletiyawa; ’ya’yan Dawuda maza su ne manyan ma’aikata a gefen sarki. Ana nan, sai Nahash sarkin Ammonawa ya mutu, sai ɗansa ya gāje shi a matsayin sarki. Dawuda ya yi tunani, “Zan nuna jinƙai ga Hanun ɗan Nahash, domin mahaifinsa ya nuna alheri gare ni.” Saboda haka Dawuda ya aika da tawaga don yă yi wa Hanun ta’aziyya game da mahaifinsa. Sa’ad da mutanen Dawuda suka iso wurin Hanun a ƙasar Ammonawa don su ta’azantar da shi, sai manyan Ammonawa suka ce wa Hanun, “Kana tsammani Dawuda yana girmama mahaifinka ne da ya aika mutanen nan wurinka su ta’azantar da kai? Ba mutanensa sun zo ne su bincika su kuma leƙi ƙasar su tumɓuke ta ba?” Saboda haka Hanun ya kama mutanen Dawuda, ya yi musu aski, ya yayyanka rigunansu a daidai ɗuwawunsu, sa’an nan ya sallame su. Da wani ya zo ya faɗa wa Dawuda game da mutanen, sai ya aiki ’yan aika su sadu da su, gama an ƙasƙantar da su ainun. Sarki ya ce, “Ku zauna a Yeriko har sai gemunku sun yi girma, sa’an nan ku dawo.” Sa’ad da Ammonawa suka gane cewa sun zama abin wurin a kafan hancin Dawuda, Hanun da Ammonawa suka aika da talenti dubu na azurfa don su yi haya da kekunan yaƙi da mahayan kekunan yaƙi daga Aram-Naharayim, Aram Ma’aka da Zoba. Suka yi hayar kekunan yaƙi da mahayan kekunan yaƙi dubu talatin da biyu, da kuma sarkin Ma’aka tare da mayaƙansa, waɗanda suka zo suka kafa sansani kusa da Medeba, yayinda Ammonawa suka tattaru daga garuruwansu suka fita yaƙi. Da jin haka, Dawuda ya aiki Yowab tare da dukan mayaƙa masu yaƙi. Ammonawa suka fito suka ja dāgā a ƙofar birninsu, yayinda sarakunan da suka zo, su kansu suka ware suna a fili. Yowab ya ga cewa akwai dāgā a gabansa da bayansa; sai ya zaɓi waɗansu mayaƙa mafi kyau a Isra’ila ya sa su a kan Arameyawa. Ya sa sauran mutanen a ƙarƙashin kulawar Abishai ɗan’uwansa, aka sa a kan Ammonawa. Yowab ya ce, “In Arameyawa suka fi ni ƙarfi, sai ka kawo mini ɗauke da ni; amma in Ammonawa sun fi ka ƙarfi, sai in kawo maka ɗauke. Ka yi ƙarfin hali bari mu yi yaƙi da jaruntaka saboda mutanenmu da biranen Allahnmu. Ubangiji zai yi abin da ya ga ya yi masa kyau.” Sai Yowab da ƙungiyoyin mayaƙan da suke tare da shi suka matso don su yi yaƙi da Arameyawa, Arameyawan kuwa suka gudu a gabansa. Sa’ad da Ammonawa suka ga Arameyawa suna gudu, sai su ma suka guda a gaban ɗan’uwansa Abishai suka shiga cikin birni. Sai Yowab ya koma Urushalima. Bayan Arameyawa suka ga cewa Isra’ila sun ci su da yaƙi, sai suka aiki ’yan aika suka sa aka kawo Arameyawan da suke hayen Kogi waɗanda Shobak shugaban mayaƙan Hadadezer yake shugabanta. Sa’ad da aka faɗa wa Dawuda wannan, sai tattara dukan Isra’ila ya haye Urdun; ya tafi wurinsu ya kuwa ja dāgā ɗaura da su. Dawuda ya ja dāgārsa don yă sadu da Arameyawa a yaƙi, su kuwa suka yi yaƙi da shi. Amma Arameyawa suka gudu a gaban Isra’ila, mutanen Dawuda kuwa suka kashe masu hawan keken yaƙinsu dubu bakwai da sojojin ƙasa dubu arba’in. Ya kuma kashe Shobak shugaban mayaƙansu. Da abokan tarayyar Hadadezer suka ga Isra’ila sun ci su da yaƙi, sai suka nemi salama da Dawuda suka kuma zama bayinsa. Saboda haka Arameyawa ba su ƙara yarda su taimaki Ammonawa ba. Da bazara, a lokacin da sarakuna kan tafi yaƙi, Yowab ya jagorance mayaƙa. Ya lalatar da ƙasar Ammonawa ya kuma tafi Rabba ya yi mata kwanto, amma Dawuda ya zauna a Urushalima. Yowab ya yaƙi Rabba, ya kuma bar ta kango. Dawuda ya ɗauki rawani daga kan sarkinsu, nauyinsa ya kai talenti na zinariya, aka kuma yi masa ado da duwatsu masu daraja, sai Dawuda kuwa ya sa a kansa. Ya kuma kwashi ganima mai yawa daga birnin ya kuma fitar da mutanen da suke can, ya sa su aiki da zartuna da makamai masu kaifi da kuma gatura. Dawuda ya yi haka da dukan garuruwan Ammonawa. Sa’an nan Dawuda da mayaƙansa gaba ɗaya suka koma Urushalima. Ana nan, sai yaƙi ya ɓarke a Gezer tsakanin Isra’ila da Filistiyawa. Sai Sibbekai mutumin Husha ya kashe Siffai, ɗaya daga cikin zuriyar Refahiyawa, ta haka kuma aka ci Filistiyawa da yaƙi. Yaƙi kuma ya sāke tashi tsakanin Isra’ilawa da Filistiyawa, Elhanan ɗan Yayir ya kashe Lahmi ɗan’uwan Goliyat mutumin Gat, wanda yake riƙe da māshi mai sandan masaƙa. Aka sāke yin wani yaƙin kuma, wanda ya faru a Gat, akwai wani ƙaton mutum mai yatsotsi shida a kowane hannu da kuma yatsotsi shida a kowace ƙafa, yatsotsi ashirin da huɗu ke nan. Shi ma daga zuriyar Rafa ce. Sa’ad da ya yi wa Isra’ila ba’a, sai Yonatan ɗan Shimeya, ɗan’uwan Dawuda ya kashe shi. Waɗannan su ne zuriyar Rafa a Gat, Dawuda da mutanensa sun kashe su. Sai Shaiɗan ya tashi gāba da Isra’ila, ya zuga Dawuda ya ƙidaya Isra’ila. Saboda haka Dawuda ya ce wa Yowab da shugabannin mayaƙa, “Ku tafi ku ƙidaya Isra’ilawa daga Beyersheba zuwa Dan. Ku kawo mini labarin saboda in san su nawa ne.” Amma Yowab ya amsa ya ce, “ Ubangiji ya riɓaɓɓanya mayaƙansa fiye da sau ɗari. Ranka yă daɗe sarki, dukansu ba bayin shugabana ba ne? Me ya sa ranka yă daɗe yake so yă yi haka? Me zai sa ka kawo laifi a kan Isra’ila?” Amma sarki ya nace a kan maganar da ya yi wa Yowab. Sai Yowab ya tashi ya tafi cikin dukan Isra’ila, ya kewaye sa’an nan ya dawo Urushalima. Yowab ya ba labarin yawan mayaƙan wa Dawuda. A cikin Isra’ila akwai mutum miliyon da dubu ɗari ɗaya waɗanda za su iya riƙe takobi, haɗe da dubu ɗari huɗu da saba’in a Yahuda. Amma Yowab bai haɗa da mutanen Lawi da na Benyamin a ƙidayar ba, domin bai ji daɗin umarnin sarki ba. Wannan umarnin mugu ne a gaban Allah; saboda haka ya hukunta Isra’ila. Sai Dawuda ya ce wa Allah, “Na yi zunubi ƙwarai ta wurin yin wannan. Yanzu, na roƙe ka, ka ɗauke laifin bawanka. Na yi wauta sosai.” Sai Ubangiji ya ce wa Gad, mai duba na Dawuda, “Tafi ka faɗa wa Dawuda, ‘Ga abin da Ubangiji ya ce ina ba ka abubuwa uku. Ka zaɓi ɗaya daga cikinsu don in aikata a kanka.’ ” Saboda haka Gad ya tafi wurin Dawuda ya ce masa, “Ga abin da Ubangiji ya ce, ‘Ka yi zaɓi, shekara uku na yunwa, wata uku na shan ɗibga a gaban abokan gābanka, sa’ad da za su bi suna kakkashe ku, ko kuwa kwana uku na takobin Ubangiji, ranakun annoba a cikin ƙasar, mala’ikan Ubangiji zai hallaka kowane sashe na Isra’ila.’ Yanzu sai ka yanke shawara yadda zan amsa wa wanda ya aiko ni.” Dawuda ya ce wa Gad, “Na shiga uku. Bari in fāɗa a hannuwan Ubangiji, gama jinƙansa yana da girma sosai; amma kada ka bari in fāɗa a hannuwan mutane.” Sai Ubangiji ya aiko da annoba a kan Isra’ila, mutane duba saba’in na Isra’ila suka mutu. Allah kuwa ya aiki mala’ika yă hallaka Urushalima. Amma yayinda mala’ikan yana gab da yin haka, sai Ubangiji ya gani ya kuma yi nadama saboda masifar, sai ya ce wa mala’ikan wanda yake hallaka mutane, “Ya isa! Janye hannunka.” Mala’ikan Ubangiji kuwa yana tsaye a masussukar Ornan mutumin Yebus. Sai Dawuda ya ɗaga ido ya ga mala’ikan Ubangiji tsaye tsakanin sama da duniya, da takobi a zāre a hannunsa ya miƙa a kan Urushalima. Sai Dawuda da dattawa, saye da rigunan makoki suka fāɗi rubda jiki. Dawuda ya ce wa Allah, “Ba ni ba ne na umarta a ƙidaya mayaƙan? Ni ne wanda ya yi zunubin da kuma abin da ba daidai ba. Waɗannan dai tumaki ne. Me suka yi? Ya Ubangiji Allahna, bari hannunka ya fāɗi a kaina da kuma iyalina, amma kada ka bar wannan annoba ya kasance a kan mutanenka.” Sa’an nan mala’ikan Ubangiji ya umarci Gad yă faɗa wa Dawuda yă haura yă gina bagade wa Ubangiji a masussukar Ornan mutumin Yebus. Saboda haka Dawuda ya haura cikin biyayya ga maganar da Allah ya yi da sunan Ubangiji. Yayinda Ornan yake sussukar alkama, sai ya juya ya ga mala’ika; ’ya’yansa maza guda huɗu da suke tare da shi suka ɓuya. Sai Dawuda ya kusato, sa’ad da Ornan ya duba sai ya gan shi, ya bar masussukar ya rusuna a gaban Dawuda da fuskarsa har ƙasa. Dawuda ya ce wa Ornan, “Ka ba ni masussukarka saboda in gina bagade wa Ubangiji, don annobar da take kan mutane tă daina. Ka sayar mini ita a cikakken kuɗinta.” Ornan ya ce wa Dawuda, “Ka karɓa! Bari ranka yă daɗe, sarki yă yi duk abin da ya ga ya yi masa kyau. Duba, zan ba da shanu domin hadaya ta ƙonawa, da itacen sussuka, da kuma alkama domin hadaya ta gari. Zan ba da dukan wannan.” Amma Sarki Dawuda ya amsa wa Ornan ya ce, “A’a, na nace zan biya cikakken kuɗinta. Ba zan karɓi abinka kawai don Ubangiji ba, ko in miƙa hadaya ta ƙonawar da ba tă ci mini wani abu ba.” Saboda haka Dawuda ya biya Ornan shekel ɗari shida na zinariya saboda wurin. Dawuda ya gina bagade wa Ubangiji a can ya kuma miƙa hadayu na ƙonawa da hadayu na salama, Ubangiji kuwa ya amsa masa ta wurin wuta daga sama a kan bagaden hadaya ta ƙonawa. Sa’an nan Ubangiji ya yi magana ga mala’ikan, ya kuma mayar da takobinsa a kube. A lokacin, sa’ad da Dawuda ya ga cewa Ubangiji ya amsa masa a masussukar Ornan mutumin Yebus, sai ya miƙa hadayu a can. Tabanakul na Ubangiji da Musa ya yi a hamada, da kuma bagaden hadaya ta ƙonawa a lokacin suna a tudun Gibeyon. Amma Dawuda bai iya zuwa gabansa don yă yi tambaya ga Allah ba, gama yana jin tsoron takobin mala’ikan Ubangiji. Sai Dawuda ya ce, “Gidan Ubangiji Allah zai kasance a nan, haka kuma bagaden hadaya ta ƙonawa don Isra’ila.” Dawuda kuwa ya umarta a tattara baƙin da suke zama a Isra’ila, daga cikinsu ya sa masu farfasa duwatsu don su shirya duwatsun da aka sassaƙa saboda ginin gidan Allah. Ya tanada ƙarfe mai yawa don ƙusoshi saboda ƙyamaren hanyoyin shiga da kuma saboda mahaɗai, da ƙarin tagulla fiye da ƙirge. Ya kuma tanada gumaguman al’ul masu yawa fiye da ƙirge, gama Sidoniyawa da mutanen Taya sun kawo su wa Dawuda da yawa. Dawuda ya ce, “Ɗana Solomon matashi ne kuma bai gogu ba, kuma gidan da za a gina wa Ubangiji zai zama mai ƙayatarwa ƙwarai, sananne da kuma mai daraja a idon dukan al’ummai. Saboda haka zan yi shirye-shirye saboda shi.” Sai Dawuda ya yi ɗumbun shirye-shirye kafin mutuwarsa. Sa’an nan ya kira ɗansa Solomon ya umarce shi yă gina gida domin Ubangiji, Allah na Isra’ila. Dawuda ya ce wa Solomon, “Ɗana, na yi niyya a zuciyata in gina gida saboda Sunan Ubangiji Allahna. Amma wannan maganar Ubangiji ta zo mini, ‘Ka zub da jini mai yawa ka kuma yi yaƙe-yaƙe masu yawa. Ba za ka gina gida domin Sunana ba, domin ka zub da jini da yawa a duniya a idona. Amma za ka haifi ɗa wanda zai zama mutumin salama da kuma hutu, zan kuma ba shi hutu daga dukan abokan gābansa a kowane gefe. Za a kira shi Solomon, zai kuma kawo wa Isra’ila salama da natsuwa a zamanin mulkinsa. Shi ne wanda zai gina gida saboda Sunana. Zai zama ɗana, ni kuma zan zama mahaifinsa. Zan kafa kujerar sarautarsa a bisa Isra’ila har abada.’ “Yanzu, ɗana, Ubangiji ya kasance tare da kai, bari kuma ka yi nasara ka kuma gina gidan Ubangiji Allahnka, kamar yadda ya ce za ka yi. Bari Ubangiji ya ba ka basira da fahimi sa’ad da ya sa ka shugaba a bisa Isra’ila, saboda ka kiyaye dokar Ubangiji Allahnka. Ta haka za ka yi nasara in ka mai da hankali ga kiyaye ƙa’idodi da dokokin da Ubangiji ya ba wa Musa saboda Isra’ila. Ka yi ƙarfin hali ka kuma ƙarfafa. Kada ka ji tsoro ko ka fid da zuciya. “Na sha wahala da yawa don in yi tanadi talentin dubu ɗari na zinariya, talenti miliyon na azurfa, ɗumbun tagulla da ƙarfe da suka wuce ƙirge da katako da dutse saboda haikalin Ubangiji. Za ka iya ƙara su. Kana da ma’aikata masu yawa, masu fafarshe duwatsu, masu gini da masu aikin katako, da kuma gwanaye a kowane irin aikin zinariya da azurfa, tagulla da ƙarfe, masu sana’a waɗanda suka wuce ƙirge. Yanzu ka fara aiki, Ubangiji kuma ya kasance tare da kai.” Sai Dawuda ya umarta dukan shugabannin Isra’ila su taimake ɗansa Solomon. Ya ce musu, “Ba Ubangiji Allahnku yana tare da ku ba? Bai kuma ba ku hutu a kowane gefe ba? Gama ya ba da mazaunan ƙasar gare ni, ƙasar kuma ta Ubangiji ce da mutanensa. Yanzu fa sai ku sa zuciyarku da ranku ga neman Ubangiji Allahnku. Ku fara ginin wuri mai tsarki na Ubangiji Allah, don ku kawo akwatin alkawarin Ubangiji da kayayyaki masu tsarki na Allah a cikin haikalin da za a gina saboda Sunan Ubangiji.” Sa’ad da Dawuda ya tsufa yana kuma da cikakken shekaru, ya sa ɗansa Solomon sarki bisa Isra’ila. Ya kuma tattara dukan shugabannin Isra’ila a wuri ɗaya, haka kuma ya yi da firistoci da Lawiyawa. Aka ƙidaya Lawiyawan da suke ’yan shekaru talatin da haihuwa ko fiye, suka kai wajen mutum dubu talatin da takwas. Dawuda ya ce, “Cikin waɗannan, dubu ashirin da huɗu za su lura da aikin haikalin Ubangiji, dubu shida su zama manyan na ma’aikata da alƙalai. Dubu huɗu su zama matsaran ƙofofi, dubu huɗu kuma su yabi Ubangiji da kayayyakin bushe-bushe da na kaɗe-kaɗe waɗanda na tanada saboda wannan manufa.” Dawuda ya rarraba Lawiyawa ƙungiya-ƙungiya bisa ga ’ya’yan Lawi maza. Gershon, Kohat da Merari. Na Gershonawa, Ladan da Shimeyi. ’Ya’yan Ladan maza su ne, Yehiyel na farko, Zetam da Yowel, su uku ne duka. ’Ya’yan Shimeyi maza su ne, Shelomot, Haziyel da Haran, su uku ne duka. Waɗannan su ne kawunan iyalan Ladan. ’Ya’yan Shimeyi maza kuwa su ne, Yahat, Zina, Yewush da Beriya. Waɗannan su ne ’ya’yan Shimeyi maza, su huɗu ne duka. Yahat shi ne na fari, Ziza kuma na biyu, amma Yewush da Beriya ba su haifi ’ya’ya maza da yawa ba; saboda haka aka ƙidaya su kamar iyali ɗaya a wurin rabon aiki. ’Ya’yan Kohat maza su ne, Amram, Izhar, Hebron da Uzziyel, su huɗu ne duka. ’Ya’yan Amram maza su ne, Haruna da Musa. Haruna shi ne aka keɓe, shi da zuriyarsa har abada, don su tsarkake kayayyakin mafi tsarki, su miƙa hadayu a gaban Ubangiji, su yi hidima a gabansa su kuma furta albarku a cikin sunansa har abada. An ƙidaya aka kuma haɗa ’ya’yan Musa maza mutumin Allah a sashen kabilar Lawi. ’Ya’yan Musa maza su ne, Gershom da Eliyezer. Zuriyar Gershom su ne, Shebuwel ne ɗan fari. Zuriyar Eliyezer su ne, Rehabiya ne ɗan fari. Eliyezer ba shi da waɗansu ’ya’ya maza, amma ’ya’yan Rehabiya maza sun yi yawa. ’Ya’yan Izhar maza su ne, Shelomit ne ɗan fari. ’Ya’yan Hebron maza su ne, Yeriya na fari, Amariya na biyu, Yahaziyel na uku da Yekameyam na huɗu. ’Ya’yan Uzziyel maza su ne, Mika na fari da Isshiya na biyu. ’Ya’yan Merari maza su ne, Mali da Mushi. ’Ya’yan Mali maza su ne, Eleyazar da Kish. Eleyazar ya mutu ba ’ya’yan maza, yana da ’ya’ya mata ne kawai. ’Yan’uwansu, ’ya’yan Kish maza, suka aure su. ’Ya’yan Mushi maza su ne, Mali, Eder da Yeremot, su uku ne duka. Waɗannan ne zuriyar Lawi bisa ga iyalansu, kawunan iyalai kamar yadda aka rubuta su a ƙarƙashin sunayensu aka kuma ƙirga kowa, wato, masu aikin da suke ’yan shekara ashirin da haihuwa ko fiye waɗanda suka yi hidima a cikin haikalin Ubangiji. Gama Dawuda ya ce, “Tun da Ubangiji, Allah na Isra’ila, ya ba da hutu ga mutanensa, ya kuma zo ya zauna a Urushalima har abada, Lawiyawa ba sa ƙara bukata su ɗauki tabanakul ko kuwa waɗansu kayayyakin da ake amfani da su a hidima.” Bisa ga umarnin ƙarshe na Dawuda, za a ƙidaya Lawiyawa daga ’yan shekara ashirin ko fiye. Aikin Lawiyawa shi ne su taimaki zuriyar Haruna a hidimar haikalin Ubangiji; su lura da filaye da kuma ɗakunan da suke gefe, su tsarkake dukan kayayyaki masu tsarki, su kuma yi waɗansu ayyuka a gidan Allah. Su ne za su lura da burodin da aka ajiye a tebur, lallausan gari don hadaya ta gari, waina marar yisti, toyawa da kwaɓawa, da kuma dukan awon yawa da kuma girman abubuwa. Su ne kuma za su tsaya kowace safiya su yi godiya, su kuma yabi Ubangiji. Za su kuma yi haka da yamma da kuma a duk sa’ad da aka miƙa hadayun ƙonawa ga Ubangiji a Asabbatai da bukukkuwan Sabon Wata da kuma a ƙayyadaddun bukukkuwa, za su yi hidima a gaban Ubangiji kullum bisa ga yawan da aka tsara da kuma a hanyar da aka tsara musu. A haka kuwa Lawiyawa suka yi ayyukansu don Tentin Sujada, don Wuri Mai Tsarki da kuma a ƙarƙashin ’yan’uwansu zuriyar Haruna, saboda hidimar haikalin Ubangiji. Waɗannan su ne sassan ’ya’yan Haruna maza. ’Ya’yan Haruna maza su ne Nadab, Abihu, Eleyazar da Itamar. Amma Nadab da Abihu sun mutu kafin mahaifinsu, ba su kuma haifi ’ya’ya maza ba; saboda haka Eleyazar da Itamar suka yi hidimar firistoci. Tare da taimakon Zadok zuriyar Eleyazar da Ahimelek wani zuriyar Itamar. Dawuda ya karkasa su zuwa ɓangarori don aikinsu bisa ga hidima. Akwai ɗumbun shugabanni a cikin zuriyar Eleyazar fiye da zuriyar Itamar, aka kuma karkasa su haka, kawuna goma sha shida daga zuriyar Eleyazar da kuma kawuna iyalai takwas daga zuriyar Itamar. Aka karkasa su babu sonkai ta wurin jifa ƙuri’a, gama akwai manyan ma’aikatan wuri mai tsarki da manyan ma’aikatan Allah a cikin zuriyar Eleyazar da Itamar. Shemahiya ɗan Netanel, wani Balawe ne marubuci, ya rubuta sunayensu a gaban sarki da kuma a gaban manyan ma’aikata. Zadok firist, Ahimelek ɗan Abiyatar da kuma kawunan iyalan firistoci da na Lawiyawa, iyali guda daga Eleyazar, guda kuma daga Itamar. Ƙuri’a ta farko ta faɗa a kan Yehoyarib, na biyu a kan Yedahiya, na uku a kan Harim, na huɗu a kan Seyorim, na biyar a kan Malkiya, na shida a kan Miyamin, na bakwai a kan Hakkoz, na takwas a kan Abiya, na tara a kan Yeshuwa, na goma a kan Shekaniya, na goma sha ɗaya a kan Eliyashib, na goma sha biyu a kan Yakim, na goma sha uku a kan Huffa, na goma sha huɗu a kan Yeshebeyab, na goma sha biyar a kan Bilga, na goma sha shida a kan Immer, na goma sha shida a kan Hezir, na goma sha takwas a kan Haffizzez, na goma sha tara a kan Fetahahiya, na ashirin a kan Ezekiyel, na ashirin da ɗaya wa Yakin, na ashirin da biyu a kan Gamul, na ashirin da uku wa Delahiya da kuma na ashirin da huɗu a kan Ma’aziya. Ga tsarin aikinsu na hidima sa’ad da suka shiga haikalin Ubangiji, bisa ga ƙa’idar da kakansu Haruna ya kafa, yadda Ubangiji, Allah na Isra’ila ya umarce shi. Game da sauran zuriyar Lawi kuwa, Daga ’ya’yan Amram maza. Shubayel; daga ’ya’yan Shubayel maza. Yedehiya. Game da Rehabiya kuwa, daga ’ya’yansa maza. Isshiya shi ne na fari. Daga mutanen Izhar, Shelomot; daga ’ya’yan Shelomot maza, Yahat. ’Ya’yan Hebron maza su ne, Yeriya na fari, Amariya na biyu, Yahaziyel na uku da Yekameyam na huɗu. Ɗan Uzziyel shi ne, Mika; daga ’ya’yan Mika maza, Shamir. Ɗan’uwan Mika shi ne, Isshiya; daga ’ya’yan Isshiya maza, Zakariya. ’Ya’yan Merari su ne, Mali da Mushi. Ɗan Ya’aziya shi ne, Beno. ’Ya’yan Merari su ne, daga Ya’aziya, Beno, Shoham, Zakkur da Ibri. Daga Mali, Eleyazar, wanda ba shi da ’ya’ya maza. Daga Kish, ɗan Kish shi ne, Yerameyel. Kuma ’ya’yan Mushi maza su ne, Mali, Eder da Yerimot. Waɗannan su ne Lawiyawa bisa ga iyalansu. Suka kuma jifa ƙuri’a, kamar dai yadda ’yan’uwansu zuriyar Haruna suka yi, a gaban Sarki Dawuda da gaban Zadok, Ahimelek, da kuma a gaban kawunan iyalan firistoci da na Lawiyawa. Aka yi da iyalan wa daidai da iyalan ƙane. Dawuda tare da shugabannin mayaƙa, suka keɓe waɗansu daga ’ya’yan Asaf, Heman da Yedutun don hidimar yin annabci, suna amfani da garayu, molaye da ganguna. Ga jerin mutanen da suka yi wannan hidima. Daga ’ya’yan Asaf, Zakkur, Yusuf, Netaniya da Asarela. ’Ya’yan Asaf sun kasance a ƙarƙashin kulawar Asaf, wanda ya yi annabci a ƙarƙashin kulawar sarki. Game da Yedutun kuwa, daga ’ya’yansa maza. Gedaliya, Zeri, Yeshahiya, Shimeyi, Hashabiya da Mattitiya, su shida ne duka, a ƙarƙashin kulawar mahaifinsu Yedutun, wanda ya yi annabci, yana amfani da garaya a yin godiya da yabon Ubangiji. Game da Heman kuwa, daga ’ya’yansa maza. Bukkiya, Mattaniya, Uzziyel, Shebuwel, Yerimot; Hananiya, Hanani, Eliyata, Giddalti, Romamti-Ezer, Yoshbekasha, Malloti, Hotir da Mahaziyot. Dukan waɗannan ’ya’yan Heman ne mai duba na sarki. An ba shi su ta wurin alkawarin Allah don yă ɗaukaka shi. Allah ya ba Heman ’ya’ya maza goma sha huɗu da ’ya’ya mata uku. Dukan waɗannan mutane suna a ƙarƙashin kulawar mahaifansu don kaɗe-kaɗe da bushe-bushe a cikin haikalin Ubangiji, da ganguna, molaye da garayu, don hidima a gidan Allah. Asaf, Yedutun da Heman suna ƙarƙashin kulawar sarki. Da su da danginsu, dukansu su 288 ne kuma horarru da ƙwararru ne a kaɗe-kaɗe da bushe-bushe domin Ubangiji. Baba ko yaro, malami ko ɗalibi, duk suka jefa ƙuri’a saboda ayyukan da za su yi. Ƙuri’a ta fari, wadda take don Asaf, ta fāɗo a kan Yusuf, ’ya’yansa maza da danginsa, 12 ta biyu a kan Gedaliya, danginsa da ’ya’yansa maza, 12 ta uku a kan Zakkur, ’ya’yansa da danginsa, 12 ta huɗu a kan Izri, ’ya’yansa maza da danginsa, 12 ta biyar a kan Netaniya, ’ya’yansa maza da danginsa, 12 ta shida a kan Bukkiya, ’ya’yansa maza da danginsa, 12 ta bakwai a kan Yesarela, ’ya’yansa maza da danginsa, 12 ta takwas a kan Yeshahiya, ’ya’yansa maza da danginsa, 12 ta tara a kan Mattaniya, ’ya’yansa maza da danginsa, 12 ta goma a kan Shimeyi, ’ya’yansa maza da danginsa, 12 ta goma sha ɗaya a kan Azarel, ’ya’yansa maza da danginsa, 12 ta goma sha biyu a kan Hashabiya, ’ya’yansa maza da danginsa, 12 ta goma sha uku a kan Shubayel, ’ya’yansa maza da danginsa, 12 ta goma sha huɗu a kan Mattitiya, ’ya’yansa maza da danginsa, 12 ta goma sha biya a kan Yeremot, ’ya’yansa maza da danginsa, 12 ta goma sha shida a kan Hananiya, na goma sha biya a kan Yerimot, ’ya’yansa maza da danginsa, 12 ta goma sha bakwai a kan Yoshbekasha, na goma sha biya a kan Yerimot, ’ya’yansa maza da danginsa, 12 ta goma sha takwas a kan Hanani, na goma sha biya a kan Yerimot, ’ya’yansa maza da danginsa 12 ta goma sha tara a kan Malloti, na goma sha biya a kan Yerimot, ’ya’yansa maza da danginsa, 12 ta ashirin a kan Eliyata, na goma sha biya a kan Yerimot, ’ya’yansa maza da danginsa, 12 ta ashirin da ɗaya a kan Hotir, na goma sha biya a kan Yerimot, ’ya’yansa maza da danginsa, 12 ta ashirin da biyu a kan Giddalti, na goma sha biya a kan Yerimot, ’ya’yansa maza da danginsa, 12 ta ashirin da uku a kan Mahaziyot, na goma sha biya a kan Yerimot, ’ya’yansa maza da danginsa, 12 ta ashirin da huɗu a kan Romamti-Ezer, na goma sha biya a kan Yerimot, ’ya’yansa maza da danginsa 12. Ɓangarorin Matsaran Ƙofofi su ne, Daga Korayawa, Meshelemiya ɗan Kore, ɗaya daga cikin ’ya’yan Asaf maza. Meshelemiya yana da ’ya’ya maza. Zakariya ɗan fari, Yediyayel na biyu, Zebadiya na uku, Yatniyel na huɗu, Elam na biyar, Yehohanan na shida da Eliyehoyenai na bakwai. Obed-Edom shi ma yana da ’ya’ya maza. Shemahiya ɗan fari, Yehozabad na biyu, Yowa na uku, Sakar na huɗu Netanel na biyar, Ammiyel na shida, Issakar na bakwai da Feyuletai na takwas. (Gama Allah ya albarkace Obed-Edom.) Ɗan Obed-Edom, wato, Shemahiya shi ma yana da ’ya’ya maza, waɗanda suke shugabanni a cikin iyalin mahaifinsu, gama su jarumawa ne ƙwarai. ’Ya’yan Shemahiya maza su ne, Otni, Rafayel, Obed da Elzabad; danginsa Elihu da Shemahiya su ma jarumawa ne. Ɗaukan waɗannan zuriyar Obed-Edom ne; su da ’ya’yansu maza da danginsu, jarumawa ne masu ƙarfin yin aiki. Zuriyar Obed-Edom, mutum 62 ne duka. Meshelemiya yana da ’ya’ya maza da kuma ’yan’uwa, waɗanda jarumawa ne, su 18 ne duka. Hosa dangin Merari yana da ’ya’ya maza. Shimri na fari (ko da yake ba shi ne ɗan fari ba, mahaifinsa ya sa shi na fari), Hilkiya ne na biyu, Tabaliya ne na uku sai kuma Zakariya na huɗu. ’Ya’ya da dangin Hosa su 13 ne duka. Waɗannan ɓangarori na matsaran ƙofofi, ta wurin manyansu, suna da ayyukan yin hidima a haikalin Ubangiji, kamar yadda danginsu suke da shi. Aka jefa ƙuri’u don kowace ƙofa bisa ga iyalansu, ƙarami da babba. Ƙuri’a don Ƙofar Gabas ta fāɗo a kan Shelemiya. Sai aka jefa ƙuri’u don ɗansa Zakariya, mai ba da shawara mai ma’ana, sai ƙuri’a ta ƙofar arewa ta fāɗo a kansa. Ƙuri’a don Ƙofar Kudu ta fāɗo a kan Obed-Edom, ƙuri’a don ɗakin ajiya kuwa ta fāɗo a kan ’ya’yansa maza. Ƙuri’u don Ƙofar Yamma da kuma Ƙofar Shalleket a hanyar bisa suka fāɗo a kan Shuffim da Hosa. Aikin tsaro bisa ga mai tsaro. Akwai Lawiyawa shida da suke tsaron ƙofar gabas, huɗu a ƙofar kudu, huɗu kuma a ƙofar arewa, biyu-biyu suke tsaron ɗakunan ajiya. Game da filin waje ta yamma kuwa, akwai masu tsaro huɗu a hanya da kuma biyu a filin kansa. Waɗannan su ne ɓangarori na matsaran ƙofofi waɗanda suke zuriyar Kora da Merari. ’Yan’uwansu Lawiyawa kuwa su ne suke lura da ma’ajin gidan Allah da kuma baitulmali don kayayyakin da aka keɓe. Ladan ɗan Gershon ne, kuma kaka ga iyalai masu yawa, har ma da iyalin ɗansa Yehiyeli, ’ya’yan Yehiyeli maza su ne, Zetam da ɗan’uwansa Yowel. Su ne suke kula da ma’ajin haikalin Ubangiji. Daga zuriyar Amram, Izhar, mutanen Hebron da kuma Uzziyel, su ma aka ba su aiki. Shebuwel ɗan Gershom, daga zuriyar Musa, shi ne babban jami’i mai lura da baitulmali. Danginsa na wajen Eliyezer su ne, Rehabiya, Yeshahiya, Yoram, Zikri da Shelomit. Shelomit da danginsa su ne suke lura da dukan baitulmali don kayayyakin da Sarki Dawuda ya keɓe, ta wajen kawunan iyalai waɗanda suke shugabannin dubu-dubu da shugabannin ɗari-ɗari, da kuma wajen sauran shugabannin mayaƙa. Sun keɓe waɗansu ganimar da aka kwaso a yaƙi don gyaran haikalin Ubangiji. Shelomit da ’yan’uwansa suka lura da dukan abubuwan da annabi Sama’ila da Shawulu ɗan Kish, da Abner ɗan Ner, da Yowab ɗan Zeruhiya suka keɓe. Daga mutanen Izhar, Kenaniya da ’ya’yansa maza su aka sa a ayyukan da ba na haikali ba, su suka zama manya da kuma alƙalai a bisa Isra’ila. Daga zuriyar Hebron, Hashabiya da danginsa, su jarumawa dubu ɗaya da ɗari bakwai ne, su suke lura da Isra’ila yamma da Urdun don dukan aikin Ubangiji da kuma hidimar sarki. Game da zuriyar Hebron kuwa, Yeriya ne babba bisa ga tarihin zuriyar iyalansu. A shekara ta arba’in ta sarautar Dawuda, sai aka yi binciken tarihi, aka tarar jarumawa cikin zuriyar Hebron suna zama a Yazer cikin Gileyad ne. Yeriya yana da ’yan’uwa guda dubu biyu da ɗari bakwai, jarumawa da kuma kawunan iyalai, sai Sarki Dawuda ya sa su lura da mutanen Ruben, Gad da rabin kabilar Manasse game da kome da ya shafi Allah da kuma al’amuran sarki. Wannan shi ne jerin Isra’ilawa, kawunan iyalai, shugabannin dubu-dubu da shugabannin ɗari-ɗari, da manyan ma’aikatansu, waɗanda suka yi wa sarki hidima a dukan abin da ya shafi ɓangarorin mayaƙan da suke aiki wata-wata a dukan shekara. Kowane sashe yana da mutane 24,000. Wanda yake lura da sashe na fari, na wata na farko, shi ne Yashobeyam ɗan Zabdiyel. Akwai mutane 24,000 a sashensa. Shi zuriyar Ferez ne kuma babba na dukan shugabannin mayaƙa don wata na farko. Wanda yake lura da sashen don wata na biyu shi ne Dodai mutumin Ahowa; Miklot ne shugaban sashensa. Akwai mutane 24,000 a sashensa. Shugaban mayaƙa na uku, don wata na uku, shi ne Benahiya ɗan Yehohiyada firist. Shi ne babba kuma akwai mutane 24,000 a sashensa. Wannan shi ne Benahiya wanda yake ɗaya daga cikin jarumawa Talatin nan kuma shi ne yake babba a cikin Talatin ɗin. Ɗansa Ammizabad ne yake lura da sashensa. Na huɗu, don wata na huɗu, shi ne Asahel ɗan’uwan Yowab; ɗansa Zebadiya shi ne magājinsa. Akwai mutane 24,000 a sashensa. Na biyar don wata na biyar, shi ne Shamhut mutumin Izhar shugaban mayaƙa. Akwai mutane 24,000 a sashensa. Na shida, don wata na shida, shi ne Ira ɗan Ikkesh mutumin Tekowa. Akwai mutane 24,000 a sashensa. Na Bakwai, don wata na bakwai, shi ne Helez mutumin Felon, mutumin Efraim. Akwai mutane 24,000 a sashensa. Na takwas, don wata na takwas, shi ne Sibbekai mutumin Husha, mutumin Zera. Akwai mutane 24,000 a sashensa. Na tara, don wata na tara, shi ne Abiyezer mutumin Anatot, mutumin Benyamin. Akwai mutane 24,000 a sashensa. Na goma, don wata na goma, shi ne Maharai mutumin Netofa, mutumin Zera. Akwai mutane 24,000 a sashensa. Na goma sha ɗaya, don wata goma sha ɗaya, shi ne Benahiya mutumin Firaton, mutumin Efraim. Akwai mutane 24,000 a sashensa. Na goma sha biyu don wata goma sha biyu, shi ne Heldai mutumin Netofa, daga iyalin Otniyel. Akwai mutane 24,000 a sashensa. Shugabannin da suke bisa kabilan Isra’ila, bisa mutanen Ruben su ne, Eliyezer ɗan Zikri; bisa mutanen Simeyon shi ne, Shefatiya ɗan Ma’aka bisa mutanen Lawi shi ne, Hashabiya ɗan Kemuwel; bisa mutanen Haruna shi ne, Zadok; bisa mutanen Yahuda shi ne, Elihu, ɗan’uwan Dawuda; bisa mutanen Issakar shi ne, Omri ɗan Mika’ilu; bisa mutanen Zebulun shi ne, Ishmahiya ɗan Obadiya; bisa mutanen Naftali shi ne, Yerimot ɗan Azriyel; bisa mutanen Efraim shi ne, Hosheya ɗan Azaziya; bisa rabin kabilar Manasse shi ne, Yowel ɗan Fedahiya; bisa ɗayan rabi kabilar Manasse a Gileyad shi ne, Iddo ɗan Zakariya; bisa mutanen Benyamin shi ne, Ya’asiyel ɗan Abner; bisa mutanen Dan shi ne, Azarel ɗan Yeroham. Waɗannan su ne shugabanni a bisa kabilan Isra’ila. Dawuda bai ƙirga mutanen da suke ’yan shekara ashirin ko ƙasa ba, domin Ubangiji ya yi alkawari zai sa Isra’ila su yi yawa kamar taurari a sararin sama. Yowab ɗan Zeruhiya ya fara ƙirgan mutanen amma bai gama ba. Hasala ta sauko a kan Isra’ila saboda wannan ƙirge, ba a kuma shigar da adadin a littafin tarihin Sarki Dawuda ba. Azmawet ɗan Adiyel shi ne mai lura da ɗakuna ajiyar fada. Yonatan ɗan Uzziya shi ne mai lura da ɗakunan ajiya a yankuna, cikin garuruwa, ƙauyuka da kuma hasumiyoyin tsaro. Ezri ɗan Kelub shi ne mai lura da ma’aikatan gona waɗanda suke nome ƙasar. Shimeyi mutumin Ramat shi ne mai lura da gonakin inabi. Zabdi mutumin Shifam shi ne mai lura da amfanin gonakin inabi don matsin ruwan inabi. Ba’al-Hanan mutumin Geder shi ne mai lura da itatuwan zaitun da na al’ul a gindin tuddan yamma. Yowash shi ne mai lura da tanadin man zaitun. Shitrai mutumin Sharon shi ne mai lura da garkuna masu kiwo a Sharon. Shafat ɗan Adlai shi ne mai lura da garkuna a kwari. Obil mutumin Ishmayel shi ne mai lura da raƙuma. Yedehiya mutumin Meronot shi ne mai lura da jakuna. Yaziz mutumin Hagiri shi ne mai lura da tumaki. Dukan waɗannan shugabanni ne masu lura da mallakar Sarki Dawuda. Yonatan, kawun Dawuda, shi ne mashawarci, mutum mai hangen nesa kuma marubuci. Yehiyel ɗan Hakmoni ne ya lura da ’ya’yan sarki maza. Ahitofel shi ne mashawarcin sarki. Hushai mutumin Arkitawa shi ne abokin sarki na kud da kud. Yehohiyada ɗan Benahiya da Abiyatar ne suka gāji Ahitofel. Yowab shi ne shugaban mayaƙan masarauta. Dawuda ya sa aka kira dukan shugabannin Isra’ila su taru a Urushalima, shugabannin kabilu, manyan hafsoshin ɓangarorin hidimar sarki, manyan hafsoshin dubu-dubu da manyan hafsoshin ɗari-ɗari, da kuma shugabanni masu lura da dukan mallaka da dabbobin da suke na sarki da kuma ’ya’yansa maza, tare da fadawa, jarumawa da kuma dukan mayaƙa masu kwarjini. Sarki Dawuda ya miƙe tsaye ya ce, “Ku saurare ni, ’yan’uwana da kuma mutanena. Na yi niyya in gina gida a matsayin wurin hutu domin akwatin alkawarin Ubangiji, domin zatin Allahnmu, na kuma yi shiri don in gina shi. Amma Allah ya ce mini, ‘Ba za ka gina gida domin Sunana ba, saboda kai mayaƙi ne ka kuma zub da jini.’ “Duk da haka Ubangiji, Allah na Isra’ila, ya zaɓe ni daga dukan iyalina don in zama sarki bisa Isra’ila har abada. Ya zaɓi Yahuda a matsayin shugaba, kuma daga gidan Yahuda ya zaɓi iyalina, daga ’ya’yan mahaifina maza kuwa ya gamsu ya mai da ni sarki bisa dukan Isra’ila. Cikin dukan ’ya’yana maza, Ubangiji kuwa ya ba ni su da yawa, ya zaɓi ɗana Solomon yă zauna a kujerar mulkin Ubangiji a bisa Isra’ila. Ya ce mini, ‘Solomon ɗanka shi ne wanda zai gina gidana da filayen da suke kewaye da shi, gama na zaɓe shi yă zama ɗana, ni kuma zan zama mahaifinsa. Zan kafa mulkinsa har abada in bai kauce ga kiyaye umarnaina da dokokina ba, yadda ake yi a wannan lokaci.’ “Saboda haka yanzu ina umartanku a gaban dukan Isra’ila da na taron jama’ar Ubangiji, da kuma a kunnuwan Allahnmu. Ku yi hankali ku kiyaye dukan umarnan Ubangiji Allahnku don ku mallaki wannan kyakkyawar ƙasa ku kuma bar wa zuriyarku gādo har abada. “Kai kuma ɗana Solomon, ka san Allah na mahaifinka, ka kuma yi masa hidima da dukan zuciya da kuma yardar rai, gama Ubangiji yana binciken zuciya, yana kuma gane dukan aniyar tunani. In ka neme shi, za ka same shi; amma in ka yashe shi, zai ƙi ka har abada. Ka lura fa, gama Ubangiji ya zaɓe ka don ka gina haikali a matsayin wuri mai tsarki. Ka yi ƙarfin hali ka kuma yi aiki.” Sa’an nan Dawuda ya ba ɗansa Solomon tsari domin shirayin haikalin, gine-ginensa, ɗakunan ajiyarsa, ɓangarorin bisansa, ɗakunan cikinsa da kuma wurin kafara. Ya ba shi tsarin dukan abin da Ruhu ya sa a zuciyarsa saboda filayen haikalin Ubangiji da ɗakunan kewaye, da ma’ajin haikalin Allah da kuma baitulmali na kayayyakin da aka keɓe. Ya ba shi tsari game ɓangarori na firistoci da Lawiyawa, da game dukan aikin hidima a cikin haikalin Ubangiji, da kuma game da dukan kayayyakin da za a yi amfani da su a hidima. Ya kimanta yawan zinariya don dukan kayayyakin zinariyar da za a yi amfani a kowane irin hidima, da yawan azurfa don dukan kayayyakin azurfan da za a yi amfani a kowace irin hidima. Da yawan zinariya don wurin ajiye fitilan fitilu da fitilunsu, da yawan zinariyan da za a yi amfani don kowace fitila da wurin ajiye fitilanta; da kuma yawan azurfa don kowane wurin ajiye fitila da fitilunsa bisa ga yadda za a yi amfani da kowane wurin ajiye fitila; yawan zinariya don kowane tebur saboda burodi mai tsaki; da kuma yawan azurfa saboda teburin azurfa; yawan zinariya zalla, don cokula masu yatsu, kwanonin yayyafawa ruwa da kuma tuluna; yawan zinariya don kowane kwanon zinariya; yawan azurfa don kowane kwanon azurfa; da kuma yawan tacecciyar zinariya don bagaden turare. Ya kuma ba shi tsari don keken yaƙi, wato, kerubobin zinariyar da suka miƙe fikafikansu suka inuwantar da akwatin alkawarin Ubangiji. Dawuda ya ce, “Dukan wannan, ina da shi a rubuce daga hannun Ubangiji zuwa gare ni, ya kuma ba ni ganewa cikin dukan tsarin fasalin, filla-filla.” Dawuda ya kuma ce wa Solomon ɗansa, “Ka yi ƙarfin hali, ka kuma yi aikin. Kada ka ji tsoro ko ka fid da zuciya, gama Ubangiji Allah, Allahna, yana tare da kai. Ba zai bari ka ji kunya ko yă yashe ka ba, sai an gama dukan aikin saboda hidimar haikalin Ubangiji. Sassan firistoci da na Lawiyawa suna a shirye domin dukan aiki a haikalin Allah, kuma kowane gwani mai niyya a kowace sana’a, zai taimake ka a cikin dukan aikin. Shugabanni da dukan mutane za su yi biyayya da kowane umarninka.” Sa’an nan Sarki Dawuda ya ce wa dukan taron, “Ɗana Solomon, wanda Allah ya zaɓa, matashi ne, kuma bai gogu ba. Aikin yana da yawa, domin wannan ƙasaitaccen ginin ba na mutum ba ne, na Ubangiji Allah ne. Na riga na tara dukan kayayyakin da na tanada saboda haikalin Allahna, zinariya saboda dukan ayyukan zinariya, azurfa saboda ayyukan azurfa, tagulla saboda ayyukan tagulla, ƙarfe saboda ayyukan ƙarfe da kuma katako saboda ayyukan katako, da onis don ado, turkuwoyis, duwatsu masu launi dabam-dabam, da kuma dukan duwatsu masu kyau da mabul, dukan waɗannan suna nan jingim. Ban da haka ma, cikin sa zuciyata ga haikalin Allahna, yanzu na ba da ma’ajina na zinariya da azurfa saboda haikalin Allahna, fiye da kome na tanada saboda wannan haikali, talenti dubu uku na zinariya (zinariyar Ofir) da tacecciyar azurfa dubu bakwai; don adon bangon gine-ginen, don aikin zinariya da kuma aikin azurfa, don kuma dukan aikin da gwanaye za su yi. Yanzu fa wa yake da niyya yă miƙa kansa a yau don Ubangiji?” Sai shugabannin iyalai, shugabannin kabilan Isra’ila, manyan hafsoshin mayaƙa dubu-dubu da manyan hafsoshi mayaƙa ɗari-ɗari, da shugabannin lura da ayyukan sarki suka yi bayarwa da yardar rai. Suka bayar talenti dubu biyar na zinariya, talenti dubu goma na azurfa, talenti dubu goma sha takwas na tagulla da talenti dubu ɗari na ƙarfe don aiki a haikalin Allah. Duk waɗanda suke da duwatsu masu daraja suka ba da su ga Yehiyel mutumin Gershon ma’ajin haikalin Ubangiji. Mutane suka yi farin ciki ganin yadda shugabanninsu suke bayarwa da yardar rai, gama sun bayar hannu sake da kuma dukan zuciya ga Ubangiji. Dawuda sarki shi ma ya yi farin ciki ƙwarai. Dawuda ya yabi Ubangiji a gaban dukan taron, yana cewa, “Yabo gare ka, ya Ubangiji, Allah na mahaifinmu Isra’ila, har abada abadin. Girma da iko da ɗaukaka, da daraja da kuma nasara naka ne, ya Ubangiji, gama kome a sama da ƙasa naka ne. Mulki kuma naka ne, ya Ubangiji; an kuma ɗaukaka ka a matsayin kai a bisa duka. Wadata da girma daga gare ka suke; kai ne mai mulkin dukan abubuwa. A hannuwanka ne ƙarfi da iko suke don ka ɗaukaka da kuma ba da ƙarfi ga duka. Yanzu fa, Allahnmu, muna gode maka, muna kuma yabon ɗaukakar sunanka. “Amma wane ni, kuma wace ce jama’ata da za mu iya ba ka a yalwace kamar haka? Kome daga gare ka suka fito, kuma mun ba ka abin da kawai ya fito daga hannunka ne. Mu bare ne kuma baƙi a gabanka, kamar yadda dukan kakanninmu suke. Kwanakinmu a duniya suna kamar inuwa ne, ba sa zuciya. Ya Ubangiji Allahnmu, game da dukan wannan yalwar da ka tanada saboda ginin haikali saboda Sunanka Mai Tsarki, sun fito daga hannunka ne, kuma dukan naka ne. Na sani, Allahna, cewa kakan gwada zuciya, kakan kuma gamsu da mutunci. Dukan waɗannan abubuwa na bayar da yardar rai da kuma kyakkyawar niyya. Yanzu kuma da farin ciki na ga yadda mutanenka waɗanda suke a nan da yardar rai suka ba ka. Ya Ubangiji Allah na kakanninmu Ibrahim, Ishaku da Isra’ila, ka sa wannan sha’awa a cikin zukatan mutanenka har abada, ka kuma bar zukatansu su yi maka biyayya. Ka kuma ba ɗana Solomon cikakkiyar zuciya don yă kiyaye umarnanka, farillanka da ƙa’idodinka yă kuma yi kome don yă gina ƙasaitaccen gini wanda na riga na yi tanadi dominsa.” Sa’an nan Dawuda ya ce wa dukan taron, “Ku yabi Ubangiji Allahnku.” Saboda haka suka yabi Ubangiji Allah na kakanninsu; suka rusuna suka kuma fāɗi rubda ciki a gaban Ubangiji da kuma sarki. Kashegari suka miƙa hadayu ga Ubangiji suka kuma miƙa hadayu bijimai dubu, raguna dubu da kuma ’yan raguna dubu na ƙonawa gare shi, tare da hadayunsu na sha da sauran hadayu a yalwace saboda dukan Isra’ila. Suka ci suka sha da farin ciki mai girma a gaban Ubangiji a wannan rana. Sa’an nan suka yarda da Solomon ɗan Dawuda a matsayin sarki sau na biyu, suka shafe shi a gaban Ubangiji don yă zama mai mulki, Zadok kuwa ya zama firist. Saboda haka Solomon ya zauna a kujerar sarautar Ubangiji a matsayin sarki a maimakon mahaifinsa Dawuda. Ya yi nasara, dukan Isra’ila kuwa suka yi masa biyayya. Dukan shugabanni da jarumawa, har ma da dukan ’ya’yan Sarki Dawuda maza, suka yi alkawari za su yi wa Sarki Solomon biyayya. Ubangiji ya ɗaukaka Solomon sosai a idon dukan Isra’ila, ya kuma ba shi darajar sarauta yadda babu sarki a Isra’ilan da ya taɓa samu. Dawuda ɗan Yesse ya zama sarki a bisa dukan Isra’ila. Ya yi mulki a bisa Isra’ila shekaru arba’in, shekaru bakwai a Hebron da kuma shekaru talatin da uku a Urushalima. Ya mutu a kyakkyawar tsufa, bayan ya more dogon rai, wadata da girma. Ɗansa Solomon ya gāje shi a matsayin sarki. Game da ayyukan mulkin Sarki Dawuda, daga farko har ƙarshe, an rubuta su a cikin tarihin Sama’ila mai duba, tarihin annabi Natan da kuma tarihin Gad mai duba, tare da yadda mulkinsa da ikonsa da yanayin da suka kewaye shi da Isra’ila da kuma dukan masarautai na dukan sauran ƙasashe. Solomon ɗan Dawuda ya kafa kansa sosai a bisa masarautarsa, gama Ubangiji Allahnsa yana tare da shi ya kuma sa ya zama mai girma sosai. Sai Solomon ya yi magana ga dukan Isra’ila, ga shugabannin mayaƙa dubu-dubu da shugabannin mayaƙa ɗari-ɗari, ga alƙalai da kuma ga dukan shugabanni a Isra’ila, kawunan iyalai, Solomon tare da dukan taron suka tafi masujadan kan tudu a Gibeyon, gama Tentin Sujadar Allah yana can, wanda Musa bawan Ubangiji ya yi a hamada. Dawuda ya riga ya haura da akwatin alkawarin Allah daga Kiriyat Yeyarim zuwa inda ya shirya dominsa, domin yă kafa masa tenti a Urushalima. Amma bagaden tagullar da Bezalel ɗan Uri, ɗan Hur, ya yi a Gibeyon a gaba tabanakul na Ubangiji; saboda haka Solomon da taron suka neme nufin Ubangiji a can. Solomon ya haura zuwa bagaden tagulla a gaban Ubangiji a cikin Tentin Sujada, ya kuma miƙa hadayu na ƙonawa dubbai a kansa. A wannan dare Allah ya bayyana ga Solomon, ya ce masa, “Roƙi duk abin da kake so in ba ka.” Solomon ya amsa wa Allah, “Ka nuna alheri mai girma ga Dawuda mahaifina ka kuma naɗa ni sarki a matsayinsa. To, yanzu, ya Ubangiji Allah, ka cika alkawarin da ka yi ga mahaifina Dawuda yă tabbata, gama ka naɗa ni sarki a bisa mutanen da suka wuce ƙirge kamar ƙurar ƙasa. Ka ba ni hikima da sani, don in iya jagorance wannan mutane, gama wa zai iya shugabance wannan jama’arka mai girma?” Allah ya ce wa Solomon, “Da yake wannan ne sha’awar zuciyarka, ba ka kuwa nemi wadata, arziki ko girma ba, ba ka kuma nemi mutuwar abokan gābanka ba, da yake kuma ba ka nemi tsawon rai ba, amma ka nemi hikima da sani don ka shugabanci jama’ata wadda na naɗa ka sarki, saboda haka za a ba ka hikima da sani. Zan kuma ba ka wadata, arziki da girma, waɗanda babu wani sarki kafin kai da ya taɓa kasance da su kuma babu wani a bayanka da zai kasance da su.” Sa’an nan Solomon ya tafi Urushalima daga masujadar kan tudu a Gibeyon, da kuma daga gaban Tentin Sujada. Ya kuma yi mulki a bisa Isra’ila. Solomon ya tara kekunan yaƙi da dawakai, ya kasance da kekunan yaƙi dubu da ɗari huɗu da kuma dawakai dubu goma sha biyu, waɗanda ya ajiye a biranen kekunan yaƙi, da kuma tare da shi a Urushalima. Sarki ya sa azurfa da zinariya suka zama barkatai a Urushalima kamar duwatsu, al’ul kuma kamar itatuwan fir a gindin tsaunuka. Aka shigo da dawakan Solomon daga Masar da kuma daga Kuye ’yan kasuwan fada suka saye su daga Kuye. Suka shigo da kekunan yaƙi daga Masar a kan shekel ɗari shida-shida na azurfa, doki kuma a kan shekel ɗari da hamsin-hamsin. Suka kuma riƙa fitar da su ƙasashen waje zuwa dukan sarakunan Hittiyawa da na Arameyawa. Solomon ya ba da umarni don a gina haikali domin sunan Ubangiji da kuma fada wa kansa. Ya ɗebi mutane dubu saba’in su zama ’yan ɗauko, mutane dubu tamanin su zama masu fasa dutse a tuddai, da kuma mutane dubu uku da ɗari shida su zama masu lura da su. Solomon ya aika wannan saƙo ga Hiram sarkin Taya. “Ka aika mini gumaguman al’ul kamar yadda ka yi wa mahaifina Dawuda sa’ad da ka aika masa al’ul don yă gina fada yă zauna a ciki. Yanzu ina shirin ginin haikali domin Sunan Ubangiji Allahna, in kuma keɓe shi gare shi don ƙona turare mai ƙanshi a gabansa, don kuma ajiyar burodi mai tsarki kullum, da kuma don miƙa hadayun ƙonawa kowace safiya, kowace yamma, da a Asabbatai da Sababbin Wata, da kuma a ƙayyadaddun bukukkuwan Ubangiji Allahnmu. Wannan dawwammamiyar farilla ce don Isra’ila. “Haikalin da zan gina zai zama mai girma, domin Allahnmu ya fi dukan sauran alloli girma. Amma wa zai iya gina haikali dominsa, shi wanda sammai, har ma da sama sammai, ba za su iya riƙe shi ba? To, wane ne ni da zan gina haikali dominsa, in ba dai wurin ƙona hadayu a gabansa ba? “Saboda haka sai ka aiko mini da mutum wanda ya gwanince a aiki da azurfa, tagulla, baƙin ƙarfe, da kuma shunayya, da garura, da shuɗɗan zare, da wanda kuma ya gwanince da aikin sassaƙa, domin yă yi aiki tare da gwanayen mutane da nake da su a Yahuda da Urushalima, waɗanda mahaifina Dawuda ya tanada. “Ka kuma aika mini al’ul, fir da gumaguman algum daga Lebanon, gama na san cewa mutanenka sun gwanince a yakan katakai a can. Mutanena kuwa za su yi aiki tare da naka don su tanada mini katakai da yawa, domin haikalin da zan gina dole yă zama mai girma da kuma ƙasaitacce. Zan ba wa bayinka masu yankan katakai waɗanda suka yanka katako, garwa niƙaƙƙen alkama dubu ashirin, garwan sha’ir dubu ashirin da randunan ruwan inabi dubu ashirin da kuma randunan man zaitun dubu ashirin.” Hiram sarkin Taya ya amsa ta wurin rubuta wasiƙa zuwa ga Solomon. “Domin Ubangiji yana ƙaunar mutanensa, ya naɗa ka sarkinsu.” Hiram ya ƙara da cewa, “Yabo ga Ubangiji, Allah na Isra’ila, wanda ya yi sama da ƙasa! Ya ba Sarki Dawuda ɗa mai hikima, cike da wayo da kuma sani, wanda zai gina haikali domin Ubangiji da kuma fada wa kansa. “Zan aika maka Huram-Abi, wani gwani wanda ya iya aiki, kuma mai hikima, wanda mahaifiyarsa ta fito daga Dan, mahaifinsa kuma daga Taya. An horar da shi a aikin zinariya, azurfa, tagulla, baƙin ƙarfe, dutse, itace, da kuma shuɗi, shunayya, garura, da lilin mai kyau. Ya gogu a kowane irin zāne-zāne, zai kuma iya yin kowane zānen da aka ba shi. Zai yi aiki tare da masu sana’arka, da kuma tare da waɗanda ranka yă daɗe, Dawuda mahaifinka ya tanada. “Yanzu fa, bari ranka yă daɗe, yă aiko wa bayinsa alkama da sha’ir da kuma man zaitun da ruwan inabin da ka alkawarta, za mu kuwa yanka dukan gumagumai daga Lebanon da kake bukata za mu kuwa yi fitonsu ta teku, su gangara zuwa Yaffa. Za ka iya kwashe su daga can ka haura zuwa Urushalima.” Solomon ya ƙidaya dukan baƙin da suke cikin Isra’ila, bayan ƙidayan da mahaifinsa Dawuda ya yi; aka kuma tarar sun kai 153,600. Ya sa 70,000 a cikinsu su zama ’yan ɗauko, 80,000 kuma su zama masu fasan dutse a tuddai, sa’an nan 3,600 su zama shugabanni masu lura da aiki. Sai Solomon ya fara ginin haikalin Ubangiji a Urushalima, a kan Dutsen Moriya, inda Ubangiji ya taɓa bayyana ga mahaifinsa Dawuda, inda kuma Dawuda ya riga ya shirya a daidai masussukar Ornan mutumin Yebus. Ya fara ginin a rana biyu ga wata na biyu a shekara ta huɗu ta mulkinsa. Tushen da Solomon ya kafa don ginin haikalin Allah tsawonsa kamun sittin, fāɗinsa kamun ashirin ne (bisa ga tsohon ma’auni). Shirayin da yake gaban haikalin kuma kamun ashirin ne da ya nausa ya ƙetare, fāɗin ginin kuma tsayinsa kamu ashirin ne. Ya shafe cikin da zinariya zalla. Ya shafe babban zauren da fir, ya kuma rufe shi da zinariya mai kyau; ya yi masa ado da zāne-zānen itatuwan dabino da kuma jerin zāne-zāne. Ya yi wa haikalin ado da duwatsu masu daraja. Zinariyar da ya yi amfani da su kuwa zinariya Farwayim ne. Ya shafe ginshiƙan saman ɗaki, madogaran ƙofofi, bangaye da kuma ƙofofin haikalin da zinariya, ya sassaƙa kerubobi a bangayen. Ya gina Wuri Mafi Tsarki, tsawonsa daidai da fāɗin haikalin. Tsawonsa kamu ashirin, fāɗinsa kuwa kamu ashirin. Ya shafe cikin da talenti ɗari shida na zinariya zalla. Nauyin ƙusoshin ya kai shekel hamsin na zinariya. Ya kuma shafe benaye da zinariya zalla. Cikin Wuri Mafi Tsarki ya yi kerubobi biyu, ya kuma shafe su da zinariya. Tsawon fikafikan kerubobin duka kamu ashirin ne, fiffike ɗaya, kamu biyar, ya taɓo bangon ɗakin, ɗaya fiffiken kuma wanda shi ma kamu biyar ne, ya taɓo fiffiken kerub ɗaya ɗin. Haka ma fiffiken kerub na biyu ɗin tsawonsa kamu biyar ne, ya taɓo bangon haikalin, ɗaya fiffiken shi ma tsawonsa kamu biyar ne, ya taɓo fiffiken kerub na farko. Tsawon fikafikan kerubobin ya kai kamu ashirin. Su kerubobin a tsaye suke, suna fuskantar babban zauren. Sai ya yi labule mai ruwan shuɗi, da shunayya, da garura, da lilin mai kyau, ya kuma ƙunshi hotunan kerubobin da aka saƙa a cikinsa. A gaban haikalin ya yi ginshiƙai biyu, waɗanda tsawonsu ya kai kamu talatin da biyar, ya yi wa ginshiƙan dajiya, tsayin kowace dajiya kamu biyar ne. Ya saƙa sarƙoƙi, ya kuma sa su a bisa ginshiƙan. Ya kuma yi rumman ɗari ya rataya wa sarƙoƙin. Ya kafa ginshiƙan a gaban haikalin, ɗaya a kudu, ɗaya kuma a arewa. Ya kira wanda yake kudun, Yakin, na arewan kuwa ya kira Bowaz. Ya yi bagaden tagulla mai tsawo kamu ashirin, fāɗinsa kamu ashirin, tsayinsa kuma kamu goma. Ya yi ƙaton kwano mai suna Teku na zubin ƙarfe, mai siffar da’ira, awonsa kamu goma ne daga da’ira zuwa da’ira tsayinsa kuma kamu biyar. Ya ɗauki magwaji mai tsawo kamu talatin ya auna shi kewaye. Ƙasa da da’ira kuwa, akwai siffofin bijimai kewaye da ita, goma ga kowane kamu guda. An yi zubin bijiman a jeri biyu a gefe guda na kwatarniya. Tekun ya tsaya a kan bijimai goma sha biyu, uku na fuskantar arewa, uku na fuskantar yamma, uku na fuskantar kudu, uku kuma na fuskantar gabas. Tekun ya zauna a kansu, kuma ƙarfafun bayansu suna wajen tsakiya. Kaurin ya kai tafin hannu, kuma da’iransa ya yi kama da’irar kwaf, kama furen da ya tohu. Ya riƙe randuna dubu uku. Sa’an nan ya yi daruna goma don wanki ya sa biyar a gefen kudu, biyar kuma a gefen arewa. A cikinsu kayan da za a yi amfani don ɗauraye hadayun ƙonawa, amma firistoci suna amfani da ƙaton kwano mai suna Teku don wanki. Ya yi wurin ajiye fitila goma na zinariya bisa ga tsari dominsu ya kuma sa su a haikali, biyar a gefen kudu, biyar kuma a gefen arewa. Ya yi tebur goma ya kuma sa su cikin haikalin, biyar a gefen kudu, biyar kuma a gefen arewa. Ya kuma yi kwanonin yayyafawa guda ɗari. Ya yi fili na firistoci da kuma babban fili da ƙofofi domin filin, ya shafe ƙofofin da tagulla. Ya sa ƙaton kwano mai suna Teku a gefen kudu, a kusurwa kudu maso gabas. Ya kuma yi tukwane da manyan cokula da kwanonin yayyafawa. Ta haka Huram ya gama aikin da ya yi wa Sarki Solomon a cikin haikalin Allah. Ginshiƙai biyu; kwanoni biyu masu siffar kwartaniya a bisa ginshiƙai; jeri biyu na tuƙaƙƙen adon kwanonin yayyafawa masu siffar kwartaniya a bisa ginshiƙai; rumman ɗari huɗu don jeri biyu na tuƙaƙƙe (layi biyu na rumman don kowane tuƙaƙƙe, mai adon kwano mai siffar kwartaniya a bisan ginshiƙai); dakalai da darunansu; ya yi kwanon da ya kira Teku, da bijimai goma sha biyu a ƙarƙashinsa; tukwane, manyan cokula, cokula masu yatsu don nama da dukan kayayyakin da suka shafi wannan. Dukan kayayyakin da Huram-Abi ya yi domin Sarki Solomon saboda haikalin Ubangiji an yi su da gogaggen tagulla ne. Sarki ya sa aka yi zubinsu a katakon yin tubali a filin Urdun tsakanin Sukkot da Zereda. Dukan waɗannan abubuwa da Solomon ya yi suna da tsada ƙwarai har suka kai nauyin tagullar da ya fi misali. Solomon ya kuma yi dukan kayayyakin da suke a cikin haikalin Allah. Bagaden zinariya; teburin da ake ajiye burodin Kasancewa; wurin ajiye fitila na zinariya zalla tare da fitilunsu, don ƙonawa a gaban wuri mai tsarki na ciki kamar yadda aka tsara; aikin zānen furannin zinariya da fitilu da abin ɗiban wuta (an yi su da zinariya zalla); arautaki; kwanonin yayyafawa, kwanoni da hantsuka; da kuma ƙofofin zinariya na haikali, ƙofofi na ciki zuwa Wuri Mafi Tsarki da kuma ƙofofin babban zaure. Sa’ad da dukan aikin da Solomon ya yi domin haikalin Ubangiji ya gama, sai ya kawo abubuwan da mahaifinsa Dawuda ya keɓe a ciki, azurfa da zinariya da kuma dukan kayayyaki, ya kuwa sa su a cikin ma’ajin haikalin Allah. Sa’an nan Solomon ya tattara zuwa Urushalima dattawan Isra’ila, dukan kawunan kabilu da manyan iyalan Isra’ilawa, don su haura da akwatin alkawarin Ubangiji daga Sihiyona, Birnin Dawuda. Dukan mutanen Isra’ila kuwa suka tattaru gaba ɗaya suka zo wurin sarki a lokacin biki a wata na bakwai. Sa’ad da dukan dattawan Isra’ila suka iso, Lawiyawa suka ɗauki akwatin alkawarin, suka haura da akwatin alkawarin da kuma Tentin Sujada da dukan kayayyaki masu tsarkin da yake cikinta. Firistoci, waɗanda suke Lawiyawa, suka ɗauke su; Sarki Solomon kuwa da taron Isra’ila gaba ɗaya da suka taru kewaye da shi suna a gaban akwatin alkawarin, suna miƙa tumaki da shanu masu yawa da suka wuce ƙirge ko lissafi. Sa’an nan firistoci suka kawo akwatin alkawarin Ubangiji zuwa wurinsa a ciki cikin wuri mai tsarki na haikali, Wuri Mafi Tsarki, suka sa shi ƙarƙashin fikafikan kerubobin. Kerubobin suka buɗe fikafikansu a bisa wurin akwatin alkawari suka kuma rufe akwatin alkawarin da sandunan ɗaukonsa. Waɗannan sanduna sun yi tsawo ƙwarai har ƙarshensu sun nausa daga akwatin alkawarin, ana iya ganinsu daga gaban ciki wuri mai tsarki na can ciki amma ba daga waje Wuri Mai Tsarki ba; kuma suna nan a can har wa yau. Babu wani abu a cikin akwatin alkawarin sai alluna biyu da Musa ya sa a cikinsa a Horeb, inda Ubangiji ya yi alkawari da Isra’ilawa bayan sun fito Masar. Sa’an nan firistoci suka janye daga Wuri Mai Tsarki. Dukan firistocin da suke can sun tsarkake kansu, ko daga wace ɓangarori suka fito. Dukan Lawiyawa waɗanda suke mawaƙa, Asaf, Heman, Yedutun da ’ya’yansu maza da dangoginsu, suka tsaya a gefen gabas na bagaden, saye da lilin mai kyau suna kuma kaɗa ganguna, garayu da molaye. Tare da su akwai firistoci 120 masu busan ƙahoni. Masu busan ƙahonin da mawaƙa suka haɗu da baki ɗaya sai ka ce murya guda ce, don su yabi su kuma yi godiya ga Ubangiji. Haɗe da busan ƙahoni, ganguna da sauran kayayyaki, suka tā da muryoyinsu cikin yabo ga Ubangiji suka rera, “Yana da kyau; ƙaunarsa dawwammamiya ce har abada.” Sai haikalin Ubangiji ya cika da girgije, Firistoci ba su iya yin hidimarsu ba saboda girgijen, gama ɗaukakar Ubangiji ta cika haikalin Allah. Sa’an nan Solomon ya ce, “ Ubangiji ya faɗa cewa zai zauna cikin duhun girgije; na gina ƙasaitaccen haikali dominka, wuri domin ka zauna har abada.” Yayinda dukan taron Isra’ila suke tsaye a can, sai sarki ya juya ya albarkace su. Sa’an nan ya ce, “Yabo ya tabbata ga Ubangiji, Allah na Isra’ila, wanda da hannuwansa ya cika abin da ya yi alkawari da bakinsa ga mahaifina Dawuda. Gama ya ce, ‘Tun ranar na da fitar da mutanena daga Masar, ban zaɓi wani birni a wata kabilar Isra’ila don a gina haikali domin Sunana ya kasance a can ba, ba kuwa zaɓi wani yă zama shugaba a bisa jama’ata Isra’ila ba. Amma yanzu na zaɓi Urushalima domin Sunana yă kasance a can, na kuma zaɓi Dawuda yă yi mulkin mutanena Isra’ila.’ “Mahaifina Dawuda ya yi niyya a zuciyarsa yă gina haikali domin Sunan Ubangiji, Allah na Isra’ila. Amma Ubangiji ya ce wa mahaifina Dawuda, ‘Domin yana a zuciyarka ka gina haikali domin Sunana, ka yi daidai da ka kasance da wannan a zuciyarka. Duk da haka, ba kai ba ne za ka gina haikalin, amma ɗanka wanda yake namanka da jininka, shi ne wanda zai gina haikali domin Sunana.’ “ Ubangiji ya kiyaye alkawarin da ya yi. Na gāje Dawuda mahaifina yanzu kuwa na zauna a kan kujerar sarautar Isra’ila, kamar dai yadda Ubangiji ya alkawarta, na kuma gina haikali domin Sunan Ubangiji, Allah na Isra’ila. A can na ajiye akwatin alkawari, inda alkawarin Ubangiji da ya yi da mutanen Isra’ila yake.” Sa’an nan Solomon ya tsaya a gaban bagaden Ubangiji a gaban dukan taron Isra’ila ya ɗaga hannuwansa sama. Dā ma ya riga ya gina dakalin tagulla, mai tsawo kamu biyar, fāɗi kamu biyar da kuma tsayi kamu uku, ya kuma sa shi a tsakiyar filin waje. Ya tsaya a kan dakalin ya kuma durƙusa a gaban dukan taron Isra’ila ya buɗe hannuwansa sama. Ya ce, “Ya Ubangiji, Allah na Isra’ila, babu Allah kamar ka a sama da kuma ƙasa, kai da kake kiyaye alkawarinka na ƙauna tare da bayinka waɗanda suke cin gaba da zuciya ɗaya a hanyarka. Ka kiyaye alkawarinka ga bawanka Dawuda mahaifina; da bakinka ka yi alkawari kuma da hannunka ka cika shi, yadda yake a yau. “Yanzu fa Ubangiji, Allah na Isra’ila, ka kiyaye wa bawanka Dawuda mahaifina alkawuran da ka yi masa sa’ad da ka ce, ‘Ba za ka kāsa kasance da mutumin da zai zauna a gabana a kan kujerar sarautar Isra’ila ba, in kawai ’ya’yanka maza za su kula cikin dukan abin da suke yi su yi tafiya a gabana bisa ga dokata, kamar yadda ka yi.’ Yanzu kuwa, ya Ubangiji, Allah na Isra’ila, bari maganarka da ka yi alkawarta wa bawanka Dawuda yă cika. “Amma tabbatacce Allah zai zauna a duniya tare da mutane? Sammai, har ma da saman sammai, ba za su iya riƙe ka ba. Balle wannan haikalin da na gina! Duk da haka ka mai da hankali ga addu’ar bawanka da kuma roƙo don jinƙai, ya Ubangiji, Allahna. Ka ji kuka da addu’ar da bawanka yake yi a gabanka. Bari idanunka su buɗu ta wajen wannan haikali dare da rana, wannan wurin da ka ce za ka sa Sunanka a can. Bari ka ji addu’ar da bawanka ke yi ta wajen wannan wuri. Ka ji roƙe-roƙen bawanka da na mutanenka Isra’ila sa’ad da suka yi addu’a suna duban wajen wannan wuri. Ka ji daga sama, mazauninka; kuma sa’ad da ka ji, ka gafarta. “Sa’ad da mutum ya yi wa maƙwabcinsa laifi aka kuma bukaci ya yi rantsuwa, ya kuma zo ya rantse a gaban bagadenka a cikin wannan haikali, sai ka ji daga sama ka kuma yi wani abu. Ka shari’anta tsakanin bayinka, kana sāka wa mai laifi ta wurin kawo a kansa hakkin abin da ya yi. Ka nuna cewa marar laifi ba shi da laifi, ta haka a fiffita rashin laifinsa. “Sa’ad da an ci mutanenka Isra’ila a yaƙi ta wurin abokin gāba domin sun yi maka zunubi kuma sa’ad da suka juya suka furta sunanka, suna addu’a suka kuma yin roƙe-roƙe a gabanka a wannan haikali, sai ka ji daga sama ka kuma gafarta zunubin mutanenka Isra’ila ka kuma dawo da su zuwa ƙasar da ka ba su da kuma kakanninsu. “Sa’ad da sammai suka rufu ba kuwa ruwan sama saboda mutanenka sun yi maka zunubi, sa’ad da kuwa suka yi addu’a suna duban waje wannan wuri suka kuma furta sunanka suka juye daga zunubinsu domin ka azabta su, sai ka ji daga sama ka kuma gafarta zunubin bayinka, mutanenka Isra’ila. Ka koya musu hanyar da ta dace da za su yi zama, ka kuma aika ruwan sama a ƙasar da ka ba mutanenka gādo. “Sa’ad da yunwa ko annoba ta fāɗo a ƙasar, ko wahala ko fumfuna, ko fāra ko fāra ɗango, ko sa’ad da abokan gāba sun yi musu ƙawanya a kowane daga biranensu, dukan wata masifa ko cutar da za tă zo, sa’ad da kuwa wani cikin mutanenka Isra’ila ya yi wata addu’a ko roƙo, kowa yana sane a azabarsa da kuma zafinsa, yana buɗe hannuwansa yana duban wajen wannan haikali, sai ka ji daga sama, mazauninka. Ka gafarta, ka kuma yi da kowane mutum gwargwadon duk abin da yake yi, da yake ka san zuciyarsa (gama kai kaɗai ka san zukatan mutane), don su ji tsoronka su kuma yi tafiya a hanyoyinka a kowane lokacin da suke zama a ƙasar da ka ba wa kakanninsu. “Game da baƙo wanda shi ba na mutanenka Isra’ila ba kuwa amma ya zo daga ƙasa mai nisa saboda sunanka mai girma da kuma hannunka mai iko da hannunka mai ƙarfi, sa’ad da ya zo ya yi addu’a yana duban wannan haikali, sai ka ji daga sama, mazauninka, ka kuma yi duk abin da baƙon ya nemi ka yi, saboda dukan mutanen duniya su san sunanka su kuma ji tsoronka, kamar yadda mutanenka Isra’ila suke yi, su kuma san cewa wannan gidan da na gina na Sunanka ne. “Sa’ad da mutanenka suka je yaƙi da abokan gābansu, ko’ina ka kai su, kuma sa’ad da suka yi addu’a gare ka suna duban wannan birnin da ka zaɓa da haikalin nan da na gina domin Sunanka, sai ka ji addu’arsu da kuma roƙonsu daga sama, ka kuma biya musu bukatarsu. “Sa’ad da suka yi maka zunubi, gama babu wani wanda ba ya zunubi, ka kuwa yi fushi da su ka miƙa su ga abokin gāba, wanda ya kai su zaman bauta a ƙasa mai nisa ko kuwa kusa; Kuma in suka canja zuciya a cikin ƙasar da suke zaman bauta, suka tuba suka roƙe ka a ƙasar zaman bautarsu suka kuma ce, ‘Mun yi zunubi, mu yi abin da ba daidai ba, mu kuwa yi mugunta’; in kuma sun juye gare ka da dukan zuciyarsu da ransu a ƙasar zaman bautarsu inda aka kai su, suka kuma dubi wajen ƙasar da ka ba wa kakanninsu, wajen birnin da ka zaɓa da kuma wajen haikalin da na gina domin Sunanka; to, daga sama, mazauninka, sai ka ji addu’arsu da kuma roƙe-roƙensu, ka kuwa biya musu bukatunsu. Ka gafarta wa mutanenka, waɗanda suka yi maka zunubi. “Yanzu, Allahna, bari idanunka su buɗu kunnuwanka kuma su saurara ga addu’o’in da ake miƙa a wannan wuri. “Yanzu ka tashi, ya Ubangiji Allah, ka zo wurin hutunka, kai da akwatin alkawarin ƙarfinka. Bari firistocinka, ya Ubangiji Allah, su sanye ceto, bari tsarkakanka su yi farin ciki cikin alherinka. Ya Ubangiji Allah, kada ka ƙyale shafaffenka. Ka tuna da ƙauna mai girma da ka alkawarta wa Dawuda bawanka.” Sa’ad da Solomon ya gama yin addu’a, sai wuta ya sauko daga sama ya cinye hadaya ta ƙonawa da kuma sadakokin, ɗaukakar Ubangiji kuwa ta cika haikalin. Firistoci ba su iya shiga haikalin Ubangiji ba domin ɗaukakar Ubangiji ta cika shi. Sa’ad da dukan Isra’ilawa suka ga wutar na saukowa, ɗaukakar Ubangiji kuma tana a bisa haikalin, sai suka durƙusa a dakali da fuskokinsu a ƙasa, suka yi sujada suka kuma yi godiya ga Ubangiji suna cewa, “ Ubangiji mai alheri ne, ƙaunarsa dawwammamiya ce har abada.” Sai sarki da dukan mutanen suka miƙa hadayu a gaban Ubangiji. Sarki Solomon kuwa ya miƙa hadayar bijimai dubu ashirin da biyu da kuma tumaki da awaki dubu ɗari da dubu ashirin. Ta haka sarki da dukan mutane suka keɓe haikalin Allah. Firistoci suka ɗauki matsayinsu, haka kuma Lawiyawa suka tsaya a matsayinsu riƙe da kayansu na bushe-bushe da na kaɗe-kaɗe na Ubangiji, waɗanda Sarki Dawuda ya yi domin yabon Ubangiji. An yi amfani da su sa’ad da ake godiya, ana kuma cewa, “Ƙaunarsa dawwammamiya ce har abada.” Kurkusa da Lawiyawa, firistoci suka busa ƙahoninsu, dukan Isra’ila kuwa suna a tsaye. Solomon ya tsarkake sashen tsakiya na filin da yake gaban haikalin Ubangiji, a can ya miƙa hadayun ƙonawa da kitsen hadayun salama domin bagaden tagullar da ya yi ba zai iya ɗaukan hadayun ƙonawa, hadayun hatsi da kuma ɓangarori na kitsen ba. Ta haka Solomon ya kiyaye bikin a wannan lokaci har kwana bakwai, dukan Isra’ila kuwa tare da shi, babban taro, mutane daga Lebo Hamat har zuwa Rafin Masar. A rana ta takwas sai suka yi taro, gama sun yi bikin keɓewar bagade na kwana bakwai da kuma biki na ƙarin kwana bakwai. A rana ta ashirin da uku na watan bakwai sai ya sallami mutane su tafi gidajensu da farin ciki da kuma murna a zuciya saboda abubuwa masu kyau da Ubangiji ya yi domin Dawuda da Solomon da kuma domin mutanensa Isra’ila. Sa’ad da Solomon ya gama haikalin Ubangiji da kuma fadan sarki ya kuma yi nasara a yin dukan abin da yake a zuciyarsa da zai yi a haikalin Ubangiji da kuma a fadarsa, sai Ubangiji ya bayyana gare shi a daren ya ce, “Na ji addu’arka na kuma zaɓi wannan wuri don kaina, a matsayin haikali don hadayu. “Sa’ad da na kulle sammai don kada a yi ruwan sama ko na umarci fāri su cinye amfanin ƙasar ko kuwa na aika da annoba a cikin mutanena, in mutanena, waɗanda ake kira da sunana, sun ƙasƙantar da kansu, suka kuma yi addu’a, suka nemi fuskata, suka kuma juye daga mugayen hanyoyinsu, zan ji daga sama in kuma gafarta zunubinsu in kuwa warkar da ƙasarsu. Yanzu, idanuna za su buɗu, kunnuwata kuma za su saurara ga addu’o’in da aka miƙa a wannan wuri. Na zaɓi na kuma tsarkake wannan haikali saboda Sunana yă kasance a can har abada. Idanuna da kuma zuciyata kullum za su kasance a can. “Game da kai kuwa, in ka yi tafiya a gabana kamar yadda Dawuda mahaifinka ya yi, ka kuma yi dukan abin da na umarta, ka kiyaye ƙa’idodina da dokokina, zan kafa kujerar sarautarka, yadda na alkawarta wa Dawuda mahaifinka sa’ad da na ce, ‘Ba za ka taɓa rasa wani mutumin da zai yi mulki a bisa Isra’ila ba.’ “Amma in ka juya daga gare ni ka yashe ƙa’idodi da umarnan da na ba ka, ka yi gaban kanka don ka bauta wa waɗansu alloli ka kuma yi musu sujada, zan tumɓuke Isra’ila daga ƙasata, wadda na ba su, zan kuma ƙi wannan haikalin da na tsarkake domin Sunana. Zan mai da shi abin karin magana da abin ba’a cikin dukan mutane. Ko da yake wannan haikali yanzu mai girma ne, dukan wanda ya wuce zai kaɗa kai yă ce, ‘Me ya sa Ubangiji ya yi irin wannan abu ga wannan ƙasa da kuma ga wannan haikali?’ Mutane za su amsa, ‘Domin sun yashe Ubangiji Allah na kakanninsu, wanda ya fitar da su daga Masar, suka rungumi waɗansu alloli, suna musu sujada, suna bauta musu, shi ya sa ya kawo dukan wannan masifa a kansu.’ ” A ƙarshen shekaru ashirin, a lokacin da Solomon ya gina haikalin Ubangiji da nasa fadan, Solomon ya sāke gina ƙauyukan da Hiram ya ba shi, ya kuma zaunar da Isra’ilawa a cikinsu. Sa’an nan Solomon ya tafi Hamat-Zoba ya ci ta da yaƙi. Ya kuma gina Tadmor a hamada da kuma dukan biranen ajiyar da ya gina a Hamat. Ya sāke gina Bet-Horon na Bisa da kuma Bet-Horon na Ƙasa a matsayin birane masu katanga, da bangaye da ƙofofi da kuma ƙyamare, haka kuma Ba’alat da dukan biranen ajiyarsa, da kuma dukan birane domin keken yaƙinsa da dawakansa, duk abin da ya so yă gina a Urushalima, a Lebanon da kuma dukan yankin da ya yi mulki, ya gina shi. Dukan mutanen da suka rage daga Hittiyawa, Amoriyawa, Ferizziyawa, Hiwiyawa da Yebusiyawa (waɗannan mutane ba Isra’ilawa ba ne), wato, zuriyarsu da suka ragu a ƙasar, wadda Isra’ilawa ba su hallaka ba, waɗannan ne Solomon ya mai da su bayinsa na aikin dole, kamar yadda yake har wa yau. Amma Solomon bai mai da Isra’ilawa bayi don aikinsa ba; su ne mayaƙansa, shugabannin hafsoshinsa, da shugabannin keken yaƙinsa da kuma mahayan keken yaƙinsa. Su ne kuma manyan ma’aikatan Sarki Solomon, manyan mutane ɗari biyu da hamsin masu lura da mutane. Solomon ya kawo ’yar Fir’auna daga Birnin Dawuda zuwa fadan da ya gina mata, gama ya ce, “Matata ba za tă zauna a fadan Dawuda sarkin Isra’ila ba, domin wuraren da akwatin alkawarin Ubangiji ya shiga masu tsarki ne.” A kan bagaden Ubangiji da ya gina a gaban shirayi, Solomon ya miƙa hadayun ƙonawa ga Ubangiji, bisa ga bukace-bukace na kullum don hadayun da Musa ya umarta don Asabbatai, Sabon Wata da kuma bukukkuwa uku na shekara, Bikin Burodi Marar Yisti, Bikin Makoni da Bikin Tabanakul. Bisa ga farillar mahaifinsa Dawuda, ya naɗa ɓangarori na firistoci don ayyukansu da Lawiyawa don su jagoranci yabo su kuma taimaki firistoci bisa ga bukace-bukacen kowace rana. Ya kuma naɗa matsara ƙofofi ɓangarori, ɓangarori don ƙofofi dabam-dabam domin abin da Dawuda mutumin Allah ya umarta ke nan. Ba a kuwa yi rashin biyayya ba game da abin da sarki ya umarta game da firistoci ko Lawiyawa a kan kayan haikalin ba. An yi dukan ayyukan Solomon, daga ranar kafa tushen haikalin Ubangiji har gamawarsa. Ta haka aka gama haikalin Ubangiji. Sa’an nan Solomon ya tafi Eziyon Geber da Elot a bakin tekun Edom. Sai Hiram ya aika masa jiragen ruwan da masu tuƙinsu waɗanda suka san teku sosai. Ma’aikatan Hiram suka tafi da na Solomon zuwa Ofir suka dawo da talentin zinariya ɗari huɗu da hamsin wa Sarki Solomon. Sa’ad da sarauniyar Sheba ta ji shahararr Solomon, sai ta zo Urushalima tă gwada shi da tambayoyi masu wuya. Ta iso tare da ayari mai girma, da raƙuma ɗauke da kayan yaji, zinariya mai yawa, da kuma duwatsu masu daraja, ta zo wurin Solomon ta kuma yi magana da shi game da dukan abin da yake zuciyarta. Solomon ya amsa dukan tambayoyinta; babu wani abin da ya yi masa wuya yă bayyana mata. Sa’ad da sarauniyar Sheba ta ga hikimar Solomon da kuma fadan da ya gina, ta ga abincin da yake teburinsa, ta ga zaman fadawansa, bayi masu yin masa hidima cikin rigunansu, ta ga masu riƙe kwaf cikin rigunansu da kuma hadayun ƙonawar da ya yi a haikalin Ubangiji, sai mamaki ya kama ta. Ta ce wa sarki, “Labarin da na ji a ƙasata game da nasarorinka da hikimarka, gaskiya ne. Amma ban gaskata abin da suka faɗa ba sai da na zo na kuma gani da idanuna. Tabbatacce, ko rabin girman hikimarka ba a faɗa mini ba, ka wuce labarin da na ji nesa ba kusa ba. Abin farin ciki ne ga mutanenka! Abin farin ciki ne ga fadawanka, waɗanda suke cin gaba da tsayawa a gabanka suna kuma jin hikimarka! Yabo ya tabbata ga Ubangiji Allahnka, wanda ya ji daɗi a cikinka ya sa ka a kan kujerar sarautarsa a matsayin sarki don ka yi mulkin domin Ubangiji Allahnka. Saboda ƙaunar Allahnka wa Isra’ila da kuma sha’awarsa na riƙe su har abada, ya naɗa ka sarki a bisansu, don ka yi adalci da kuma gaskiya.” Sa’an nan ta ba sarki talenti 120 na zinariya, kayan yaji masu yawa, da kuma duwatsu masu daraja. Ba a taɓa kasance da irin kayan yaji mai yawa kamar waɗanda sarauniyar Sheba ta ba wa sarki Solomon ba. (Mutanen Hiram da mutanen Solomon suka kawo zinariya daga Ofir, suka kuma kawo gungumen algum da duwatsu masu daraja. Sarki ya yi amfani da gungumen algum don matakalan haikalin Ubangiji da kuma na fadan sarki, ya kuma yi garayu da molaye don mawaƙa. Ba a taɓa gani irinsu a Yahuda ba.) Sarki Solomon ya ba sarauniyar Sheba duk abin da take so da kuma ta nema; ya ba ta fiye da abin da ta kawo masa. Sa’an nan ta tashi ta koma ƙasarta tare da masu rufe mata baya. Nauyin zinariyar da Solomon yake karɓa shekara-shekara talenti 666 ne, ban da harajin da fatakai da ’yan kasuwa suke biya. Haka kuma dukan sarakunan Arabiya da gwamnonin ƙasar suka kawo zinariya da azurfa wa Solomon. Sarki Solomon ya yi manyan garkuwoyi ɗari biyu da zinariya; an yi kowane garkuwa da bekas ɗari shida na zinariya. Ya kuma yi ƙanana garkuwoyi zinariya ɗari uku, da bekas ɗari uku na zinariya a kowanne. Sarki ya sa su a cikin Fadan da ake kira Kurmin Lebanon. Sai sarki ya yi wata kujerar sarauta mai girma da aka shafe ta da hauren giwa, aka kuma dalaye ta da zinariya zalla. Kujerar tana da matakalai shida, da wurin sa ƙafa na zinariya haɗe da ita. A kowane gefen wurin zama, akwai wurin ajiye hannu, da zaki tsaye kusa da kowannensu. Zakoki goma sha biyu sun tsaya a kan matakalai shida, ɗaya a ƙarshen matakala guda. Ba a taɓa yin irin wannan abu don wata masarauta ba. Dukan kwaf na Sarki Solomon zinariya ne, kuma dukan kayayyakin gida a Fadan da ake kira Kurmin Lebanon zinariya ne zalla. Ba a yi wani abu da azurfa ba, domin ba a ɗauki azurfa a zamanin Solomon a bakin kome ba. Sarki yana da jerin jiragen ruwa na kasuwanci waɗanda mutanen Hiram ne suke kula da su. Sau ɗaya kowace shekara uku sukan dawo ɗauke da zinariya, azurfa, hauren giwa, gogo da kuma birai. Sarki Solomon ya fi arziki da hikima in aka kwatanta da dukan sauran sarakunan duniya. Dukan sarakunan duniya sun nemi su sadu da Solomon don su ji hikimar da Allah ya sa a zuciyarsa. Shekara, shekara, duk wanda ya zo wurinsa yakan kawo kyauta, kayayyakin azurfa da na zinariya, da riguna, makamai da kayan yaji, da dawakai da kuma alfadarai. Solomon ya kasance da wuraren ajiye dawakai dubu huɗu don dawakai da kekunan yaƙi, yana da dawakai dubu goma sha biyu waɗanda ya ajiye a biranen kekunan yaƙi da kuma tare da shi a Urushalima. Ya yi mulki bisa dukan sarakuna daga Kogi Yuferites zuwa ƙasar Filistiyawa, har zuwa iyakar Masar. Sarki ya sa azurfa ta zama barkatai a Urushalima kamar duwatsu, al’ul kuma da yawa kamar itatuwan fir a gindin tsaunuka. An sayo dawakan Solomon daga Masar da kuma daga dukan sauran ƙasashe. Game da sauran ayyukan mulkin Solomon, daga farko har zuwa ƙarshe, an rubuta su a cikin tarihin annabi Natan, cikin annabcin Ahiya mutumin Shilo da kuma cikin wahayin Iddo mai gani game da Yerobowam ɗan Nebat. Solomon ya yi mulki a Urushalima a bisa dukan Isra’ila shekaru arba’in. Sa’an nan ya huta tare da kakanninsa, aka kuma binne shi cikin birnin Dawuda mahaifinsa. Rehobowam ɗansa kuwa ya gāje shi a matsayin sarki. Rehobowam ya tafi Shekem, gama dukan Isra’ilawa sun je can don su naɗa shi sarki. Da Yerobowam ɗan Nebat ya ji wannan (a lokacin yana a Masar, inda ya gudu daga Sarki Solomon ya tafi), sai ya dawo daga Masar. Saboda haka suka aika a zo da Yerobowam, sai shi da dukan Isra’ila suka je wurin Rehobowam suka ce masa. “Mahaifinka ya sa mana kaya masu nauyi a kanmu, amma yanzu ka sauƙaƙa mana aiki mai zafin nan da kuma kaya masu nauyin da ya sa a kanmu, mu kuwa za mu bauta maka.” Rehobowam ya amsa, “Ku dawo gare ni cikin kwana uku.” Saboda haka mutanen suka watse. Sai Sarki Rehobowam ya nemi shawarar dattawan da suka yi wa mahaifinsa Solomon hidima a lokacin da yake da rai, ya tambaye suya ce, “Wace shawara za ku ba ni don in amsa wa waɗannan mutane?” Suka amsa suka ce, “In za ka ji tausayi waɗannan mutane ka kuma gamshe su, ka kuma ba su amsar da ta dace, kullum za su zama bayinka.” Amma Rehobowam ya ƙi shawarar da dattawa suka ba shi ya kuma nemi shawarar matasan da suka yi girma tare, suke kuma yin masa hidima. Ya tambaye su ya ce, “Mece ce shawararku? Yaya zan amsa wa waɗannan mutanen da suke ce mini, ‘Ka sauƙaƙa nauyin da mahaifinka ya sa a kanmu’?” Matasan da suka yi girma tare shi suka amsa, “Faɗa wa mutanen da suke ce maka, ‘Mahaifinka ya sa kaya masu nauyi a kanmu, amma ka sauƙaƙa nauyinmu.’ Ka faɗa musu, ‘Ƙaramin yatsana ya fi ƙugun mahaifina kauri. Mahaifina ya sa muku kaya masu nauyi; zan ma sa mafi nauyi. Mahaifina ya bulale ku da bulala; zan bulale ku da kunamai.’ ” Bayan kwana uku sai Yerobowam da dukan mutane suka dawo wurin Rehobowam, yadda sarki ya ce, “Ku dawo gare ni cikin kwana uku.” Sarki ya amsa musu da kakkausar murya. Ya ƙi shawarar dattawan, ya kuma bi shawarar matasan ya ce, “Mahaifina ya sa muku kaya masu nauyi; zan ma sa mafi nauyi. Mahaifina ya bulale ku da bulala; zan bulale ku da kunamai.” Saboda haka sarki bai saurari mutane ba, gama wannan juyin al’amura daga Allah ne, don a cika maganar Ubangiji da ya yi ga Yerobowam ɗan Nebat ta wurin Ahiya mutumin Shilo. Sa’ad da Isra’ila suka ga sarki ya ƙi yă saurare su, sai suka amsa wa sarki, suka ce, “Wanda rabo muke da shi a wurin Dawuda, wanda sashe muke da shi daga ɗan Yesse? Kowa yă koma tentinsa, ya Isra’ila! Ka lura da gidanka, ya Dawuda!” Saboda haka dukan Isra’ilawa suka tafi gida. Amma game da Isra’ilawan da suke zama a garuruwan Yahuda kuwa, Rehobowam ya ci gaba da yin mulki a bisansu. Sarki Rehobowam ya aiki Hadoram wanda yake lura da aikin dole, amma Isra’ilawa suka jajjefe shi da duwatsu har ya mutu. Sarki Rehobowam kuwa ya gaggauta ya shiga keken yaƙinsa ya gudu zuwa Urushalima. Ta haka Isra’ila ya kasance cikin tawaye a kan gidan Dawuda har yă zuwa wannan rana. Sa’ad da Rehobowam ya iso Urushalima, ya tattara mayaƙa dubu ɗari takwas daga gidan Yahuda da Benyamin, don su yi yaƙi da Isra’ila su sāke mai da mulki wa Rehobowam. Amma wannan maganar Ubangiji ta zo ga Shemahiya mutumin Allah. “Faɗa wa Rehobowam ɗan Solomon sarkin Yahuda da kuma dukan Isra’ilawan da suke a Yahuda da Benyamin, ‘Ga abin da Ubangiji ya ce kada ku haura don ku yi yaƙi da ’yan’uwanku. Ku tafi gida kowannenku, gama wannan yi na ne.’ ” Saboda haka suka yi biyayya ga maganar Ubangiji suka kuma koma daga takawa don yaƙi da Yerobowam. Rehobowam ya zauna a Urushalima ya kuma gina garuruwa don kāriya a cikin Yahuda. Betlehem, Etam, Tekowa, Bet-Zur, Soko, Adullam, Gat, Maresha, Zif, Adorayim, Lakish, Azeka, Zora, Aiyalon da Hebron. Waɗannan su ne garuruwan katanga a cikin Yahuda da Benyamin. Ya ƙarfafa kāriyarsu ya kuma sa shugabannin mayaƙa a cikinsu, tare da tanadin abinci, man zaitun da kuma ruwan inabi. Ya sa garkuwoyi da māsu a cikin dukan biranen, ya kuma sa suka zama da ƙarfi. Saboda haka Yahuda da Benyamin suka zama nasa. Firistoci da Lawiyawa daga dukan yankuna ko’ina a Isra’ila suka haɗa kai da shi. Lawiyawa suka ma bar makiyayansu da mallakarsu, suka zo Yahuda da Urushalima domin Yerobowam da ’ya’yansa maza sun ƙi su a matsayin firistocin Ubangiji. Yerobowam ya naɗa firistocinsa domin masujadan kan tudu da kuma domin gumakan nan na akuya da maraƙin da ya yi. Waɗanda suke daga kowane kabilar Isra’ila waɗanda suka sa zuciya a kan neman Ubangiji, Allah na Isra’ila, suka bi Lawiyawa zuwa Urushalima don su miƙa hadayu ga Ubangiji Allah na kakanninsu. Suka ƙarfafa mulkin Yahuda suka kuma goyi bayan Rehobowam ɗan Solomon shekaru uku, suna tafiya a hanyoyin Dawuda da Solomon a wannan lokaci. Rehobowam ya auri Mahalat, ’yar Yerimot ɗan Dawuda wadda Abihayil ’yar Eliyab ɗan Yesse ta haifa. Ta haifa masa ’ya’ya maza. Yewush, Shemariya da Zaham. Sa’an nan ya auri Ma’aka ’yar Absalom, wadda ta haifa masa Abiya, Attai, Ziza da kuma Shelomit. Rehobowam ya ƙaunaci Ma’aka ’yar Absalom fiye da sauran matansa da ƙwarƙwaransa. Duka-duka dai ya auri mata goma sha takwas da ƙwarƙwarai sittin, yana da ’ya’ya maza ashirin da takwas da ’ya’ya mata sittin. Rehobowam ya naɗa Abiya ɗan Ma’aka yă zama babba yerima a cikin ’yan’uwansa, don dai yă naɗa shi sarki. Ya yi hikima, ya watsar da waɗansu ’ya’yansa a dukan yankunan Yahuda da Benyamin, da kuma a dukan birane masu katanga. Ya ba su tanadi mai yawa ya kuma aurar musu mata masu yawa. Bayan mulkin Rehobowam ya kahu kamar sarki ya kuma yi ƙarfi, shi da dukan Isra’ila suka yi biris da dokar Ubangiji. Domin sun yi rashin biyayya ga Ubangiji, saboda haka Shishak sarkin Masar ya yaƙi Urushalima a shekara ta biyar ta Sarki Rehobowam. Da kekunan yaƙi dubu ɗaya da ɗari biyu da kuma mahayan dawakai dubu haɗe da mayaƙan Libiyawa, Sukkatawa da kuma Kushawa waɗanda suka wuce ƙidaya suka zo tare da shi daga Masar, ya ci biranen katanga na Yahuda har zuwa Urushalima. Sai annabi Shemahiya ya zo wurin Rehobowam da kuma wajen shugabannin Yahuda waɗanda suka taru a Urushalima don tsoron Shishak, ya kuma faɗa musu, “Ga abin da Ubangiji ya ce, ‘Kun yi biris da ni; saboda haka, yanzu na bashe ku ga Shishak.’ ” Shugabannin Isra’ila da sarki suka ƙasƙantar da kansu suka ce, “ Ubangiji mai adalci ne.” Sa’ad da Ubangiji ya ga sun ƙasƙantar da kansu, sai wannan maganar Ubangiji ta zo wa Shemahiya, “Tun da yake sun ƙasƙantar da kansu, to, ba zan hallaka su ba, amma zan cece su, ba zan kwararo fushina ta hannun Shishak a kan Urushalima ba. Duk da haka za su zama bayinsa, don su san bambanci tsakanin yin mini bauta da kuma yin wa sarakunan sauran ƙasashe bauta.” Da Shishak sarkin Masar ya yaƙi Urushalima, sai ya kwashi ma’ajin haikalin Ubangiji da kuma ma’ajin fadan sarki. Ya kwashe kome da kome, har da garkuwoyin zinariyar da Solomon ya yi. Sai sarki Rehobowam ya ƙera garkuwoyin tagulla a madadin na zinariya, ya sa su a hannun shugabannin matsara na mashigin gidan sarki. Duk sa’ad da sarki ya tafi haikalin Ubangiji, masu tsaron sukan tafi tare da shi, suna riƙe da garkuwoyi, daga baya kuma su mai da su a ɗakin tsaro. Gama Rehobowam ya ƙasƙantar da kansa, fushin Ubangiji ya bar shi, ba a kuwa hallaka shi ƙaƙaf ba. Tabbatacce an yi ’yan abubuwa masu kyau a Yahuda. Sarki Rehobowam ya kafa kansa daram a Urushalima, ya kuma ci gaba a matsayin sarki. Yana da shekara arba’in da ɗaya sa’ad da ya zama sarki, ya kuma yi mulki shekara goma sha bakwai a Urushalima, birnin da Ubangiji ya zaɓa daga dukan kabilan Isra’ila wanda zai sa Sunansa. Sunan mahaifiyarsa Na’ama ce, ita mutuniyar Ammon ce. Ya aikata mugunta domin bai sa zuciyarsa ga neman Ubangiji ba. Game da ayyukan mulkin Rehobowam, daga farko zuwa ƙarshe, ba a rubuce suke a tarihin Shemahiya annabi da Iddo mai gani wanda yake zancen zuriyoyi ba? Aka kasance da yaƙe-yaƙe tsakanin Rehobowam da Yerobowam. Rehobowam ya huta da kakanninsa aka kuma binne shi a Birnin Dawuda. Abiya ɗansa kuma ya gāje shi a matsayin sarki. A shekara ta sha takwas ta sarautar Yerobowam, Abiya ya zama sarkin Yahuda, ya kuma yi mulki a Urushalima shekaru uku. Sunan mahaifiyarsa Mikahiya ce, ’yar Uriyel na Gibeya. Aka kasance da yaƙe-yaƙe tsakanin Abiya da Yerobowam. Abiya ya tafi yaƙi tare da mayaƙa dubu ɗari huɗu jarumawa, Yerobowam kuwa ya ja dāgār yaƙi a kan Abiya da mayaƙa dubu ɗari takwas jarumawa. Abiya ya tsaya a Dutsen Zemarayim, a ƙasar tudu ta Efraim ya ce, “Yerobowam da dukan Isra’ila, ku saurare ni! Ba ku san cewa Ubangiji, Allah na Isra’ila ya ba da sarautar Isra’ila ga Dawuda da zuriyarsa har abada ta wurin alkawarin gishiri ba? Duk da haka Yerobowam ɗan Nebat, ma’aikacin Solomon ɗan Dawuda, ya tayar wa maigidansa, sai ya tara wa kansa ’yan iska da mugayen mutane suka yi gāba da Rehobowam ɗan Solomon. Rehobowam lokacin kuwa ba shi da wayo, don haka bai iya tsai da su ba. “Yanzu kuna shirin yin tsayayya da mulkin Ubangiji, wanda yake a hannuwan zuriyar Dawuda. Tabbatacce ku ƙasaitacciyar mayaƙa ne kuma kuna tare da ku maruƙan zinariyar da Yerobowam ya yi domin su zama allolinku. Ba ku ne kuka kori firistocin Ubangiji, ’ya’yan Haruna maza, da Lawiyawa kuka kuma zaɓi firistocinku kamar yadda sauran al’ummai suke yi ba? Duk wanda ya zo ya miƙa ɗan bijimi da raguna bakwai don yă tsarkake kansa, ya zama firist na gumaka ke nan, ba na Allah ba. “Gare mu kuwa, Ubangiji shi ne Allah, kuma ba mu yashe shi ba. Firistocin da suke bauta wa Ubangiji ’ya’yan Haruna maza ne, Lawiyawa ne kuwa suke taimakonsu. Kowace safiya da kowace yamma sukan miƙa hadayun ƙonawa da turare mai ƙanshi ga Ubangiji. Sukan shirya burodi a tsarkaken tebur mai tsabta, sukan kuma ƙuna fitilu a alkukai kowace yamma. Muna kiyaye ƙa’idodin Ubangiji Allahnmu. Amma ku kun yashe shi. Allah yana tare da mu; shi ne shugabanmu. Firistocinsa tare da ƙahoni za su busa kirarin yaƙi a kanku. Mutanen Isra’ila, kada ku yi yaƙi da Ubangiji Allah na kakanninku, gama ba za ku yi nasara ba.” To, fa, Yerobowam ya aiki mayaƙa su zagaya daga baya, domin yayinda yake a gaban Yahuda, sai ’yan kwanto su kasance a bayansu. Yahuda ya juya sai ya ga cewa ana yaƙe su gaba da baya. Sai suka yi kuka ga Ubangiji. Firistoci suka busa ƙahoni mutanen Yahuda kuwa suka tā da kirarin yaƙi. Da ji kirarin yaƙi, Allah ya fatattake Yerobowam da dukan Isra’ila a gaban Abiya da Yahuda. Isra’ilawa suka gudu a gaban Yahuda, Allah kuwa ya bashe su a hannuwansu. Abiya da mutanensa suka kashe su sosai, har mutum dubu ɗari biyar suka mutu a cikin jarumawan Isra’ila. Aka cinye mutanen Isra’ila a wannan lokaci, mutanen Yahuda kuwa suka yi nasara domin sun dogara ga Ubangiji Allah na kakanninsu. Abiya ya kori Yerobowam ya kuma ƙwace garuruwan Betel, Yeshana da Efron, tare da ƙauyukan da suke kewaye daga gare shi. Yerobowam bai sāke yin ƙarfi a zamanin Abiya ba. Ubangiji ya buge shi ya kuma mutu. Amma Abiya ya ƙara ƙarfi. Ya auri mata goma sha huɗu, ya kuma kasance da ’ya’ya maza ashirin da biyu da kuma ’ya’ya mata goma sha shida. Sauran ayyukan sauratar Abiya, abin da ya yi da abin da ya faɗa, a rubuce suke a cikin rubuce-rubucen annabi Iddo. Abiya kuwa ya huta tare da kakanninsa, aka kuma binne shi a Birnin Dawuda. Asa ɗansa ya gāje shi a matsayin sarki, a zamaninsa kuma ƙasar ta zauna lafiya na shekara goma. Asa ya yi abin da yake da kyau da kuma daidai a gaban Ubangiji Allahnsa. Ya kawar da baƙin bagade da masujadai bisa tudu, ya farfashe keɓaɓɓun duwatsu, ya kuma sassare ginshiƙan Ashera. Ya umarci Yahuda su nemi Ubangiji Allah na kakanninsu, su kuma yi biyayya da dokoki da kuma umarnansa. Ya kawar da masujadan kan tudu da bagadan turare a kowane gari a Yahuda, masarautar kuwa ta zauna lafiya a ƙarƙashinsa. Ya gina biranen katanga na Yahuda, da yake ƙasar tana zaman lafiya. Babu wanda yake yaƙi da shi a waɗannan shekaru, gama Ubangiji ya ba shi hutu. Ya ce wa Yahuda, “Bari mu gina waɗannan garuruwa mu sa katanga kewaye da su, da hasumiyoyi, ƙofofi da ƙyamare. Ƙasar har yanzu tamu ce domin mun nemi Ubangiji Allahnmu, mun neme shi ya kuwa ba mu hutu a kowane gefe.” Saboda haka suka gina suka kuma yi nasara. Asa ya kasance da mayaƙa dubu ɗari uku daga Yahuda, kintsatse da manyan garkuwoyi da māsu, da kuma mayaƙa dubu ɗari biyu da dubu tamanin daga Benyamin, riƙe da ƙananan garkuwoyi da kuma baka. Dukan waɗannan jarumawa ne ƙwarai. Zera mutumin Kush ya taka ya fita don yă yaƙe su da babban runduna da kuma kekunan yaƙi ɗari uku, ya kuma zo har Maresha. Asa ya fita don yă ƙara da shi, suka ja dāgā yaƙi a Kwarin Zefata kusa da Maresha. Sai Asa ya kira ga Ubangiji Allahnsa ya ce, “ Ubangiji, babu wani kamar ka da zai taimaki marar ƙarfi a kan mai ƙarfi. Ka taimake mu, ya Ubangiji Allahnmu, gama mun dogara a gare ka, kuma a cikin sunanka muka fito don mu yaƙi wannan babbar runduna. Ya Ubangiji, kai ne Allahnmu; kada ka bar mutum yă yi nasara a kanka.” Ubangiji fa ya bugi mutanen Kush a gaban Asa da Yahuda. Mutanen Kush suka gudu, Asa kuwa da mayaƙansa suka bi su har Gerar. Mutanen Kush suka mutu a ranan nan har ba a iya ƙidaya, aka buge su a gaban Ubangiji da rundunansa. Mutanen Yahuda suka kwashi ganima sosai. Suka hallaka dukan ƙauyukan kewaye da Gerar, gama tsoron Ubangiji ya kama su. Suka kwashi ganima na dukan ƙauyukan nan, da yake akwai ganima sosai a can. Suka kuma yaƙi sansanin makiyaya suka kwashe tumaki da awaki da raƙuma. Suka koma Urushalima. Sai Ruhun Allah ya sauko a kan Azariya ɗan Oded. Ya fita ya je ya sadu da Asa ya kuma faɗa masa, “Ka saurare ni, Asa da kuma dukan Yahuda da Benyamin. Ubangiji yana tare da ku sa’ad da kuke tare da shi. In kuka neme shi, za ku same shi, amma in kuka yashe shi, zai yashe ku. Tun da daɗewa Isra’ila ba su da Allah na gaskiya, babu firist da zai koyar, kuma babu doka. Amma cikin wahalarsu suka juya ga Ubangiji, Allah na Isra’ila, suka kuma neme shi, suka kuwa same shi. A waɗancan kwanaki akwai hatsari a yin tafiye-tafiye, gama dukan mazaunan ƙasashe suna cikin babbar damuwa. Wata ƙasa takan murƙushe wata, wani birni kuma yakan murƙushe wani, domin Allah ya wahalshe su da kowace irin damuwa. Amma game da ku, ku ƙarfafa kada ku fid da zuciya, gama za a ba ku ladan aikinku.” Sa’ad da Asa ya ji waɗannan kalmomin da annabcin Azariya ɗan Oded annabi ya faɗa, sai ya sami ƙarfi hali. Ya kawar da gumaka masu banƙyama daga dukan ƙasar Yahuda da Benyamin da kuma daga garuruwan da ya ci da yaƙi a ƙasar tudu ta Efraim. Ya gyaggyara bagaden Ubangiji da yake a gaban shirayin haikalin Ubangiji. Sa’an nan ya tattara dukan Yahuda da Benyamin da kuma mutane daga Efraim, Manasse da Simeyon waɗanda suke zaune a cikinsu, gama jama’a mai girma ta zo wurinsa daga Isra’ila sa’ad da suka ga cewa Ubangiji Allahnsa yana tare da shi. Suka taru a Urushalima a wata na uku na shekara ta goma sha biyar ta mulkin Asa. A lokacin suka miƙa hadaya bijimai ɗari bakwai da tumaki da kuma awaki dubu bakwai ga Ubangiji daga ganimar da suka dawo da ita. Suka yi alkawari don su nemi Ubangiji Allah na kakanninsu, da dukan zuciyarsu da kuma dukan ransu. Aka kashe dukan waɗanda ba su nemi Ubangiji, Allah na Isra’ila ba, ko ƙarami ko babba, namiji ko ta mace. Suka yi rantsuwa ga Ubangiji da babbar murya, da ihu da garayu da ƙahoni. Dukan Yahuda suka yi farin ciki game da rantsuwar domin sun yi rantsuwar gabagadi. Suka nemi Allah da gaske, suka kuma same shi. Saboda haka Ubangiji ya ba su hutu a kowane gefe. Sarki Asa ya tuɓe mahaifiyar mahaifiyarsa daga matsayinta na mahaifiyar sarauniya, domin ta gina ginshiƙin banƙyama na Ashera. Asa ya rurrushe shi, ya farfasa shi ya kuma ƙone shi a Kwarin Kidron. Ko da yake bai kawar da masujadan kan tudu daga Isra’ila ba, zuciyar Asa ta cika da bin Ubangiji dukan kwanakinsa. Ya kawo azurfa da zinariya da kayayyaki a haikalin Allah waɗanda shi da mahaifinsa suka keɓe. Ba a ƙara yin yaƙi ba sai a shekara ta talatin da biyar ta mulkin Asa. A shekara ta talatin da shida ta mulkin Asa, Ba’asha sarkin Isra’ila ya haura don yă yaƙi Yahuda da Rama mai katanga, don kuma yă hana wani daga fita ko shiga yankin Asa sarkin Yahuda. Sai Asa ya ɗauki azurfa da zinariya daga ma’ajin haikalin Ubangiji da kuma na fadansa ya aika wa Ben-Hadad sarkin Aram, wanda yake mulki a Damaskus. Ya ce, “Bari yarjejjeniya ta kasance tsakani na da kai kamar yadda ya kasance tsakanin mahaifina da mahaifinka. Dubi ina aika maka azurfa da zinariya. Yanzu ka yanke yarjejjeniya da Ba’asha sarkin Isra’ila domin yă janye daga gare ni.” Ben-Hadad ya yarda da Sarki Asa ya kuma aika da manyan hafsoshin mayaƙansa a kan garuruwan Isra’ila. Suka ci Iyon, Dan, Abel-Mayim da kuma dukan biranen ajiya na Naftali. Da Ba’asha ya ji wannan, ya daina ginin Rama ya yashe aikinsa. Sa’an nan Sarki Asa ya kawo dukan mutanen Yahuda, suka kuma kwashe duwatsu da katako daga Rama waɗanda Ba’asha yake amfani da su. Da su ne Asa ya gina Geba da Mizfa. A lokacin Hanani mai duba ya zo wurin Asa sarkin Yahuda ya ce masa, “Don ka dogara ga sarkin Aram, ba kuwa ga Ubangiji Allahnka ba ne mayaƙan sarkin Aram sun kuɓuce daga hannunka. Ai, Kushawa da Libiyawa rundunar sojoji ne masu yawan gaske, suna kuma da kekunan yaƙi da mahayan dawakai masu yawa ƙwarai. Amma duk da haka, saboda ka dogara ga Ubangiji, ya kuwa ba da su cikin hannunka. Gama gaban Ubangiji yana ko’ina a duniya don yă ƙarfafa waɗanda zukatansu suke binsa cikin aminci. Ka yi wauta, daga yanzu nan gaba za ka yi ta yaƙi.” Sai Asa ya yi fushi sosai da mai duban saboda wannan; ya yi fushi ƙwarai har ya sa aka jefa shi a kurkuku. A lokaci guda kuma Asa ya fara gwada wa mutane azaba. Ayyukan mulkin Asa, daga farko zuwa ƙarshe, suna a rubuce a littafin sarakunan Yahuda da Isra’ila. A shekara ta talatin da tara ta mulkinsa, Asa ya kamu da wata cuta a ƙafarsa. Ko da yake cutar ta yi tsanani, duk d haka ma a cikin ciwonsa bai nemi taimako daga Ubangiji ba, sai dai daga likitoci. Sa’an nan a shekara ta arba’in da ɗaya ta mulkinsa, Asa ya mutu ya kuma huta tare da kakanninsa. Suka binne shi a kabarin da ya fafe wa kansa a Birnin Dawuda. Suka sa shi a makara wadda aka rufe da kayan yaji da kuma turare dabam-dabam da aka niƙa, suka kuma ƙuna babbar wuta don girmama shi. Yehoshafat ɗansa ya gāje shi a matsayin sarki ya kuma kahu sosai gāba da Isra’ila. Ya kafa mayaƙa a dukan biranen katangar Yahuda, ya kuma sa runduna a Yahuda da kuma a garuruwan Efraim da mahaifinsa Asa ya ci da yaƙi. Ubangiji kuwa yana tare da Yehoshafat domin a shekarunsa na farko-farko ya yi tafiya a hanyoyin da kakansa Dawuda ya bi. Bai nemi shawarar Ba’al ba amma ya nemi Allah na kakansa ya kuma bi umarnansa a maimakon ayyukan da Isra’ila ke yi. Ubangiji ya kafa mulkin a ƙarƙashin ikonsa; dukan Yahuda kuwa suka kawo kyautai wa Yehoshafat, ta haka ya yi arziki sosai da kuma girma. Zuciyarsa ta duƙufa ga hanyoyin Ubangiji, bugu da ƙari, ya kawar masujadan kan tudu da ginshiƙan Ashera daga Yahuda. A shekara ta uku ta mulkinsa, ya aiki ma’aikatansa Ben-Hayil, Obadiya, Zakariya, Netanel da Mikahiya su yi koyarwa a garuruwan Yahuda. Tare da su akwai waɗansu Lawiyawa, Shemahiya, Netaniya, Zebadiya, Asahel, Shemiramot, Yehonatan, Adoniya, Tobiya da Tob Adoniya, da kuma firistoci Elishama da Yehoram. Suka yi koyarwa a dukan Yahuda, suna ɗauke da Littafin Dokar Ubangiji tare da su; suka tafi ko’ina a dukan garuruwan Yahuda suka koyar da mutane. Tsoron Ubangiji ya kama dukan masarautun ƙasashen da suke kewaye da Yahuda, har ba su yi yaƙi da Yehoshafat ba. Waɗansu Filistiyawa suka kawo wa Yehoshafat kyautai da azurfa a matsayin haraji, Larabawa kuwa suka kawo masa garkuna, raguna dubu bakwai da ɗari bakwai da kuma awaki dubu bakwai da ɗari bakwai. Yehoshafat ya yi ta ƙaruwa a ƙarfi; ya gina katanga da biranen ajiya a Yahuda da kuma tanade-tanade masu yawa a garuruwan Yahuda. Ya kuma ajiye gogaggu mayaƙa a Urushalima. Ɗaukar da aka yi musu bisa ga iyalai yana kamar haka. Daga Yahuda, shugaban ƙungiya 1,000. Adna ne shugaba, tare da jarumawa 300,000; biye da shi, Yehohanan shi ne shugaba, yana da sojoji 280,000; biye da shi, Amasiya ɗan Zikri, wanda ya ba da kansa da yardar rai don hidimar Ubangiji, yana da sojoji 200,000. Daga Benyamin, Eliyada, jarumi soja, yana da sojoji 200,000 riƙe da baka da garkuwoyi; biye da shi, Yehozabad, yana da sojoji 18,000 shiryayyu don yaƙi. Waɗannan su ne suka yi wa sarki hidima, ban da waɗanda aka sa a biranen katanga ko’ina a Yahuda. Yanzu fa Yehoshafat ya wadace ƙwarai yana kuma da girma, ya kuma haɗa kansa da Ahab ta wurin aure. Bayan ’yan shekaru sai ya gangara don yă ziyarci Ahab a Samariya. Ahab kuwa ya yanka tumaki da shanu masu yawa dominsa da kuma mutanen da suke tare da shi, ya kuma lallashe shi yă yaƙi Ramot Gileyad. Ahab sarkin Isra’ila ya tambayi Yehoshafat sarkin Yahuda ya ce, “Za ka tafi tare da ni mu yaƙi Ramot Gileyad?” Yehoshafat ya amsa ya ce, “Ni kamar kai ne, kuma mutanena kamar naka ne; za mu tafi tare da kai a yaƙin.” Amma Yehoshafat ya kuma ce wa sarkin Isra’ila, “Da fari mu nemi bishewar Ubangiji.” Saboda haka sarkin Isra’ila ya tattara annabawa duka, mutane ɗari huɗu, ya kuma tambaye su, “Mu tafi yaƙi a kan Ramot Gileyad ko kada mu tafi?” Suka amsa “Tafi, gama Allah zai ba da shi cikin hannun sarki.” Amma Yehoshafat ya yi tambaya ya ce, “Babu wani annabin Ubangiji a nan da za mu tambaya?” Sarki Isra’ila ya amsa wa Yehoshafat, “Akwai guda har yanzu mai suna Mikahiya ɗan Imla, za mu iya nemi nufin Ubangiji daga gare shi, sai dai ba na sonsa domin bai taɓa yin annabci wani abu mai kyau game da ni ba, sai kullum masifa.” Yehoshafat ya amsa ya ce, “Kada sarki yă faɗa haka.” Saboda haka sarkin Isra’ila ya kira ɗaya daga cikin ma’aikatansa ya ce, “A kawo Mikahiya ɗan Imla nan da nan.” Saye da rigunan sarakuna, sarki Isra’ila da Yehoshafat sarkin Yahuda suna zaune a kan kujerunsu na mulki a masussuka ta ƙofar shigar Samariya, tare da dukan annabawa suna ta annabci a gabansu. To, fa, Zedekiya ɗan Kena’ana ya yi ƙahonin ƙarfe, ya kuma furta, “Ga abin da Ubangiji ya ce, ‘Da waɗannan za ka sassoki Arameyawa sai sun hallaka.’ ” Dukan sauran annabawan suka yi irin annabcin nan. Suka ce, “A haura zuwa Ramot Gileyad a yi nasara, gama Ubangiji zai ba da shi cikin hannun sarki.” Ɗan saƙon da ya tafi don yă kawo Mikahiya kuwa ya ce masa, “Duba, kowannen a cikin annabawa ya yi faɗin nasara wa sarki. Don haka kai ma ka yi maganar da za tă gamshi sarki kamar yadda suka yi.” Amma Mikahiya ya ce, “Na rantse da ran Ubangiji, zan faɗa masa kawai abin da Allahna ya faɗa.” Da suka iso, sarki ya tambaye shi, “Mika, mu tafi mu yaƙi Ramot Gileyad, ko kada mu tafi?” Ya amsa, “Kai masa yaƙi za ka kuwa yi nasara, gama za a ba da su a hannunka.” Sarki ya ce masa, “Sau nawa zan sa ka rantse don ka faɗa gaskiya a cikin sunan Ubangiji?” Sa’an nan Mikahiya ya amsa, “Na ga dukan Isra’ila sun warwatsu a kan tuddai kamar tumakin da ba su da makiyaya, kuma Ubangiji ya ce, ‘Waɗannan mutane ba su da maigida. Bari kowanne yă tafi gida cikin salama.’ ” Sarkin Isra’ila ya ce wa Yehoshafat, “Ban faɗa maka cewa bai taɓa yin annabci wani abu mai kyau game da ni, in ba masifa ba?” Mikahiya ya ci gaba, “Saboda haka sai ka ji maganar Ubangiji. Na ga Ubangiji yana zama a kan kursiyinsa tare da dukan rundunar sama tsaye a damansa da hagunsa. Ubangiji kuwa ya ce, ‘Wa zai ruɗe Ahab sarki Isra’ila zuwa yaƙi da Ramot Gileyad da kuma zuwa mutuwarsa a can?’ “Wani ya ba da wata shawara, wani kuma wata dabam. A ƙarshe, wani ruhu ya zo gaba, ya tsaya a gaban Ubangiji ya ce, ‘Zan ruɗe shi.’ “ Ubangiji ya yi tambaya, ‘Ta wace hanya?’ “Ya ce, ‘Zan tafi in zama ruhun ƙarya a bakunan dukan annabawansa.’ “ Ubangiji ya ce, ‘Za ka yi nasara a ruɗinsa. Ka tafi, ka yi haka.’ “To yanzu, Ubangiji ya sa ruhun ruɗu a bakunan waɗannan annabawanka. Ubangiji ya ƙayyade masifa dominka.” Sai Zedekiya ɗan Kena’ana ya haura ya mari Mikahiya a fuska. Ya ce, “Ta wace hanya ce ruhun Ubangiji ya fita daga gare ni ya zo ya yi magana da kai?” Mikahiya ya amsa ya ce, “Za ka gane a ranar da ka je ka ɓuya a can cikin ɗaki.” Sa’an nan sarkin Isra’ila ya umarta, “Ɗauki Mikahiya ku aika da shi zuwa ga Amon mai mulkin birni da kuma ga Yowash ɗan sarki, ku ce ga abin da sarki ya ce, ‘Ku jefa wannan mutum a kurkuku kada kuma ku ba shi wani abu sai dai burodi da ruwa har sai na dawo lafiya.’ ” Mikahiya ya furta ya ce, “Idan har ka dawo lafiya, to, Ubangiji bai yi magana ta wurina ba.” Ya kuma ƙara da cewa, “Dukanku mutane, ku lura da maganata!” Saboda haka sarkin Isra’ila da Yehoshafat sarkin Yahuda suka haura zuwa Ramot Gileyad. Sarkin Isra’ila ya ce wa Yehoshafat, “Zan ɓad da kama in shiga yaƙin, amma ka sa kayanka na sarauta.” Saboda haka sarkin Isra’ila ya ɓad da kama ya shiga cikin yaƙin. To, fa, sarkin Aram ya umarce shugabannin keken yaƙinsa ya ce, “Kada ku yaƙi kowa, ƙarami ko babba, sai dai sarkin Isra’ila.” Sa’ad da shugabannin kekunan yaƙi suka ga Yehoshafat, sai suka yi tsammani, “Wannan ne sarkin Isra’ila.” Saboda haka suka juya don su yaƙe shi, amma Yehoshafat ya yi ihu, Ubangiji kuma ya taimake shi. Allah ya janye su daga gare shi, gama sa’ad da shugabannin keken yaƙi suka ga cewa ba shi ne sarkin Isra’ila ba, sai suka daina binsa. Amma wani ya harba kibiya haka kawai, sai kibiyar ta sami sarki Ahab na Isra’ila a kafaɗa tsakanin rigar yaƙinsa na ƙarfe da ƙarfen ƙirjinsa. Sai sarki ya ce wa mai tuƙan keken yaƙi, “Juya ka fitar da ni daga wurin yaƙin. An ji mini rauni.” Duk yini yaƙi ya yi ta cin gaba, sarkin Isra’ila kuwa ya jingina kansa a cikin keken yaƙinsa yana duban Arameyawa har yamma. Sa’an nan a fāɗuwar rana sai ya mutu. Sa’ad da Yehoshafat sarkin Yahuda ya dawo zuwa fadansa a Urushalima lafiya, Yehu mai duba, ɗan Hanani, ya fita don yă tarye shi, ya kuma ce wa sarki, “Ya yi kyau ke nan da ka taimaki mugu ka kuma ƙaunaci waɗanda suke ƙin Ubangiji? Da yake ka yi haka fushin Ubangiji yana a kanka Duk da haka an sami wani abin kirki a wurinka, gama ka kawar da ginshiƙan Ashera a ƙasar, ka kuma sa zuciyarka a kan neman Allah.” Yehoshafat ya zauna a Urushalima, ya kuma fita yana shiga cikin mutane daga Beyersheba zuwa ƙasar tudun Efraim ya kuma juyar da su ga Ubangiji Allah na kakanninsu. Ya naɗa alƙalai a kowanne daga cikin biranen katanga na Yahuda a ƙasar. Ya faɗa musu, “Ku lura da abin da kuke yi, gama shari’ar da kuke yi ba ta mutum ba ce, amma ta Ubangiji ce, yana tare da ku sa’ad da kuke yanke shari’a. Yanzu fa ku ji tsoron Ubangiji. Ku yi hankali a kan abin da kuke yi, gama Ubangiji Allahnmu ba ya sonkai ko nuna wariya ko cin hanci.” A Urushalima kuma, Yehoshafat ya naɗa waɗansu Lawiyawa, firistoci da kawunan iyalan Isra’ilawa don su tabbatar da an bi dokar Ubangiji, su kuma sasanta tsakanin mutane. A Urushalima za su zauna. Ya ba su waɗannan umarnai, “Ku yi aikinku da aminci da tsoron Ubangiji da dukan zuciyarku. Cikin kowane batun da ya zo gabanku daga ’yan’uwanku waɗanda suke zama a birane, ko batun na kisa ne ko kuwa waɗansu batuttuwan da suka shafi doka, umarnai, ƙa’idodi ko farillai, dole ku ja musu kunne kada su yi wa Ubangiji zunubi; in ba haka ba fushinsa zai sauko a kanku da ’yan’uwanku. Ku yi wannan, ta haka ba za ku kuwa yi zunubi ba. “Amariya, babban firist, shi ne zai shugabance ku a kan dukan al’amuran da suke na wajen Ubangiji, Zebadiya ɗan Ishmayel kuwa, shugabanku a kan dukan al’amuran da suka shafi sarki, Lawiyawa kuma za su zama a matsayin manya a gabanku. Ku yi abubuwa da ƙarfin hali, bari kuma Ubangiji yă kasance tare da masu yin gaskiya.” Bayan wannan, Mowabawa da Ammonawa tare da waɗansu Meyunawa suka zo su yaƙi Yehoshafat. Sai waɗansu mutane suka zo suka faɗa wa Yehoshafat, “Ga babban runduna tana zuwa a kanka daga Edom, daga ƙetaren Teku, daga Aram. Ta ma kai Hazazon Tamar” (wato, En Gedi). A firgice, Yehoshafat ya yanke shawara yă nemi nufin Ubangiji, ya kuma yi shelar azumi a dukan Yahuda. Mutanen Yahuda suka taru gaba ɗaya don su nemi taimako daga wurin Ubangiji, tabbatacce suka fito daga kowane garin Yahuda don su neme shi. Sa’an nan Yehoshafat ya miƙe tsaye a taron Yahuda da Urushalima a haikalin Ubangiji a sabon filin ya ce, “Ya Ubangiji Allah na kakanninmu, ba kai ne Allah wanda yake sama ba? Kana mulki a bisa dukan mulkokin ƙasashe. Iko da girma suna a hannunka, kuma ba wanda zai iya tsayayya da kai. Ya Allahnmu, ba kai ba ne ka kore mazaunan wannan ƙasa a gaban mutanenka Isra’ila ka kuma ba da ita har abada ga zuriyar Ibrahim abokinka? Sun yi zama a cikinta suka kuma yi gina wuri mai tsarki a cikinta domin Sunanka cewa, ‘In masifa ta zo mana, ko takobin hukunci, ko annoba ko yunwa, za mu tsaya a gabanka a gaban wannan haikalin da yake ɗauke da Sunanka, mu kuma yi kuka gare ka cikin azaba, za ka kuwa ji mu, ka cece mu.’ “Yanzu kuma ga mutanen Ammon, da na Mowab, da na Dutsen Seyir, waɗanda ka hana Isra’ilawa su kai musu yaƙi sa’ad da suka fito daga ƙasar Masar, su ne mutanen da Isra’ila suka ƙyale, ba su hallaka su ba. Yau ga yadda suke so su biya mu. Su suke so su kore mu daga ƙasar da ka ba mu gādo. Ya Allahnmu, ba za ka hukunta su ba? Gama ba mu da ƙarfin fuskantar wannan babbar rundunar da take so ta yaƙe mu. Ba mu san abin da za mu yi ba, mu dai mun zuba maka ido.” Dukan mazan Yahuda, tare da matansu da yaransu da ƙananansu, suka tsaya a gaban Ubangiji. Sa’an nan Ruhun Ubangiji ya sauko a kan Yahaziyel ɗan Zakariya, ɗan Benahiya, ɗan Yehiyel, ɗan Mattaniya, wani Balawe kuma zuriyar Asaf, yayinda yake tsaye a cikin taron. Ya ce, “Saurara, Sarki Yehoshafat da dukan waɗanda suke zama a Yahuda da Urushalima! Ga abin da Ubangiji ya ce muku, ‘Kada ku ji tsoro ko ku fid da zuciya saboda wannan babbar runduna. Gama yaƙin ba naku ba ne, amma na Allah. Gobe ku fito ku gangara ku yaƙe su. Za su yi ta haurawa ta Mashigin Ziz, ku kuwa za ku same su a ƙarshen kwari a Hamadan Yeruwel. Ba lalle ba ne ku yi wannan yaƙi. Ku dai, ku ja dāgā, ku tsaya kurum ku ga nasarar da Ubangiji zai ba ku, ya Yahuda da Urushalima. Kada ku ji tsoro; kada ku karai. Ku fito don ku fuskance su gobe, Ubangiji kuwa zai kasance tare ku.’ ” Yehoshafat ya rusuna da fuskarsa har ƙasa, dukan mutanen Yahuda da Urushalima suka fāɗi rubda ciki suka yi sujada a gaban Ubangiji. Sa’an nan waɗansu Lawiyawa daga Kohatawa da Korayawa suka tashi tsaye suka yabe Ubangiji, Allah na Isra’ila, da babbar murya sosai. Da sassafe suka tashi suka nufi Hamadan Tekowa. Yayinda suka kama hanya, Yehoshafat ya tsaya ya ce, “Ku saurare ni, Yahuda da mutanen Urushalima! Ku amince da Ubangiji Allahnku za a kuwa kafa ku; ku amince da annabawansa za ku kuwa yi nasara.” Bayan suka yi shawara tare da shugabanni, sai ya zaɓi mutanen da za su ja gaban sojoji suna waƙa ga Ubangiji suna yabonsa saboda tsarkinsa suna cewa, “Ku yi godiya ga Ubangiji, gama ƙaunarsa dawwammamiya ce har abada.” Da suka fara waƙa, suna kuma yabo, sai Ubangiji ya kai hari a kan mutanen Ammon da Mowab da Dutsen Seyir, waɗanda suka kawo hari a Yahuda, aka kuwa ci su da yaƙi. Mutanen Ammon da Mowab suka tasar wa mazaunan Dutsen Seyir, suka hallaka su ƙaƙaf. Sa’ad da suka karkashe mazaunan Seyir sai suka fāɗa wa juna, suka yi ta hallaka juna. Sa’ad da mutanen Yahuda suka zo wurin da yake fuskantar hamada, suka duba ta wajen babban rundunar, sai suka ga gawawwaki birjik a ƙasa; babu wani wanda ya kuɓuta. Sa’ad da Yehoshafat da jama’arsa suka je kwasar ganima, sai suka sami shanu masu yawan gaske, da kayayyaki, da tufafi, da abubuwa masu daraja, waɗanda suka yi ta kwasa har suka gaji. Kwana uku suka yi suna kwasar ganimar saboda yawanta. A rana ta huɗu sai suka taru a Kwarin Beraka, inda suka yabi Ubangiji. Wannan ne ya sa ake kiransa Kwarin Beraka har wa yau. Sa’an nan Yehoshafat ya jagoranci dukan mutanen Yahuda da Urushalima suka dawo da farin ciki zuwa Urushalima, gama Ubangiji ya ba su dalilin farin ciki a kan abokan gābansu. Suka shiga Urushalima suka shiga haikalin Ubangiji da kiɗin molaye da sarewa da kuma garayu. Tsoron Allah ya kama dukan mulkokin ƙasashe sa’ad da suka ji yadda Ubangiji ya yi yaƙi a kan abokan gāban Isra’ila. Mulkin Yehoshafat kuwa ya zauna lafiya, gama Allahnsa ya ba shi hutu a kowane gefe. Ta haka Yehoshafat ya yi mulki a bisa Yahuda. Yana da shekara talatin da biyar sa’ad da ya zama sarkin Yahuda, ya kuma yi mulki a Urushalima shekara ashirin da biyar. Sunan mahaifiyarsa Azuba ce, ’yar Shilhi. Ya yi tafiya a hanyoyin mahaifinsa Asa bai kuwa kauce daga gare su ba; ya yi abin da yake daidai a gaban Ubangiji. Duk da haka ba a kawar da masujadai kan tudu ba, domin har yanzu mutanen ba su tsayar da zukatansu ga Allahn kakanninsu ba. Sauran ayyukan mulkin Yehoshafat, daga farko zuwa ƙarshe, an rubuta su a tarihin Yehu ɗan Hanani, waɗanda aka rubuta a littafin sarakunan Isra’ila. Daga baya, Yehoshafat sarkin Yahuda ya haɗa kai da Ahaziya sarkin Isra’ila, wanda yake da laifin mugunta. Ya yarda da shi su gina jiragen ruwan kasuwanci. Bayan aka gina waɗannan a Eziyon Geber, Eliyezer ɗan Dodabahu na Maresha ya yi annabci a kan Yehoshafat cewa, “Domin ka haɗa kai da Ahaziya, Ubangiji zai hallaka abin da ka yi.” Jiragen ruwan kuwa suka farfashe, ba a kuwa iya sa su je kasuwanci ba. Yehoshafat ya huta tare da kakanninsa, aka kuma binne shi tare da su a Birnin Dawuda. Sai Yehoram ɗansa ya gāje shi a matsayin sarki. ’Yan’uwan Yehoram, ’ya’yan Yehoshafat maza su ne, Azariya, Yehiyel, Zakariya, Azariyahu, Mika’ilu da Shefatiya. Dukan waɗannan su ne ’ya’yan Yehoshafat sarkin Isra’ila maza. Mahaifinsu ya ba su kyautai masu yawa na azurfa da zinariya da kayayyaki masu daraja, tare da birane masu katanga a Yahuda, amma ya ba da mulki ga Yehoram domin shi ne ɗan farinsa. Sa’ad da Yehoram ya kafa kansa sosai a bisa mulkin mahaifinsa, sai ya kashe dukan ’yan’uwansa da takobi tare da waɗansu sarakunan Isra’ila. Yehoram yana da shekara talatin da biyu sa’ad da ya zama sarki, ya kuma yi mulki a Urushalima shekara takwas. Ya yi tafiya a hanyoyin sarakunan Isra’ila, kamar yadda gidan Ahab ta yi, gama ya auri ’yar Ahab. Ya aikata mugayen ayyuka a idon Ubangiji. Duk da haka, domin alkawarin da Ubangiji ya yi wa Dawuda, Ubangiji bai so yă hallaka gidan Dawuda ba. Ubangiji ya riga ya yi alkawari zai ci gaba da riƙe fitila domin Dawuda da zuriyarsa har abada. A zamanin Yehoram, Edom ya tayar wa Yahuda ya kuma naɗa sarkinsa. Saboda haka Yehoram ya tafi can tare da shugabannin sojojinsa da kuma dukan keken yaƙinsa. Mutanen Edom suka kewaye shi da shugabannin keken yaƙinsa, amma ya tashi ya fatattaki su da dare. Har yă zuwa yau Edom na tawaye a kan Yahuda. Libna ya yi tawaye a lokaci guda, domin Yehoram ya yashe Ubangiji Allah na kakanninsa. Ya gina masujadan kan tudu a tuddan Yahuda, ya kuma sa mutanen Urushalima suka yi karuwanci, ya sa Yahuda suka kauce. Yehoram ya sami wasiƙa daga Iliya annabi, wadda ta ce, “Ga abin da Ubangiji Allah na kakanka Dawuda ya ce, ‘Ba ka yi tafiya a hanyoyin mahaifinka Yehoshafat ko Asa sarkin Yahuda ba. Amma ka yi tafiya a hanyoyin sarakunan Isra’ila, ka sa Yahuda ya kauce, ka kuma sa mutanen Urushalima suka yi karuwanci, kamar yadda gidan Ahab ta yi. Ka kuma kashe ’yan’uwanka, membobi gidan mahaifinka, mutanen da suka fi ka kirki. Saboda haka a yanzu Ubangiji yana shirin ya bugi mutanenka, ’ya’yanka maza, matanka da kuma kome da yake naka, da bugu mai ƙarfi. Kai kuma za ka kamu da ciwon hanji wanda zai yi ta cinka kowace rana sai har hanjinka sun fito.’ ” Ubangiji ya sa Filistiyawa da Larabawa waɗanda suke zama kusa da Kushawa su yi gāba da Yehoram Suka yaƙi Yahuda, suka kai masa hari, suka kwashe dukan abubuwa masu kyau da suka samu a fadan sarki, tare da ’ya’yansa maza da kuma matansa. Ba wanda aka bari, sai dai Ahaziya autansa. Bayan dukan wannan, sai Ubangiji ya sa wa Yehoram cuta marar warkarwa ta ciki. Cikin lokaci, a ƙarshen shekara ta biyu, sai hanjin cikinsa suka fito saboda cutar, ya kuma mutu cikin tsananin zafi. Mutanensa suka hura wuta don girmama shi, kamar yadda suka yi wa kakanninsa. Yehoram yana da shekara talatin da biyu sa’ad da ya zama sarki, ya kuma yi mulki a Urushalima shekara takwas. Ya mutu, ba ma wanda ya kula, aka kuma binne shi a Birnin Dawuda, amma ba a makabartan sarakuna ba. Mutanen Urushalima suka mai da Ahaziya, autan Yehoram, sarki a madadinsa, da yake ’yan hari, waɗanda suka zo tare da Larabawa cikin sansani, sun kashe dukan manyan ’ya’yansa. Saboda haka Ahaziya ɗan Yeroham sarkin Yahuda ya fara mulki. Ahaziya yana da shekara ashirin da biyu sa’ad da ya zama sarki, ya kuma yi mulki a Urushalima shekara guda. Sunan mahaifiyarsa Ataliya ce, jikanyar Omri. Shi ma ya yi tafiya a hanyoyin gidan Ahab, gama mahaifiyarsa ta ƙarfafa shi yă yi abin da ba shi da kyau. Ya aikata mugayen ayyuka a gaban Ubangiji, yadda gidan Ahab ta yi, gama bayan mutuwar mahaifinsa, sai gidan Ahab ta zama masu ba shi shawara, shawarar da ta kai shi ga lalacewa. Ya kuma bi shawararsu sa’ad da ya tafi tare da Yoram ɗan Ahab sarkin Isra’ila don yă yaƙi Hazayel sarkin Aram a Ramot Gileyad. Sai Arameyawa suka yi wa Yoram rauni; saboda haka ya dawo Yezireyel don yă yi jinyar raunin da suka yi masa a Rama cikin yaƙinsa da Hazayel sarkin Aram. Sa’an nan Azariya ɗan Yehoram sarkin Yahuda ya gangara zuwa Yezireyel don yă ga Yoram ɗan Ahab domin ya ji rauni. Ta wurin ziyarar Yoram, Allah ya kawo fāɗuwar Ahaziya. Sa’ad da Ahaziya ya iso, ya tafi tare da Yoram domin yă sadu da Yehu ɗan Nimshi, wanda Ubangiji ya shafe don yă hallaka gidan Ahab. Yayinda Yehu yake hukunta wa gidan Ahab, sai ya sami fadawan Yahuda da kuma ’ya’yan dangin Ahaziya maza, waɗanda suke yi wa Ahaziya hidima, sai ya kashe su. Ya kuma sa aka nemi Ahaziya. Aka kamo shi sa’ad da ya ɓuya a Samariya, suka kawo shi wurin Yehu, suka kashe shi, suka binne shi, gama sun ce, “Shi jikan Yehoshafat ne, wanda ya nemi Ubangiji da dukan zuciyarsa.” Ta haka babu wani a gidan Ahaziya da yake da ƙarfin cin gaba da mulkin. Sa’ad da Ataliya mahaifiyar Ahaziya ta ga cewa ɗanta ya mutu, sai ta tashi ta hallaka dukan ’yan gidan sarautar Yahuda. Amma Yehosheba, ’yar Sarki Yehoram, ta ɗauki Yowash ɗan Ahaziya ta sace shi daga cikin ’ya’yan gidan sarauta waɗanda ake shiri a kashe, ta sa shi tare da mai renonsa a ɗakin kwana. Haka fa, Yehosheba ’yar sarki Yoram, matar Yehohiyada firist, ta yi, gama ita ’yar’uwar Ahaziya ce, ta ɓoye Yowash don kada Ataliya tă kashe shi. Ya kasance a ɓoye tare da su a haikalin Allah shekara shida, yayinda Ataliya take mulkin ƙasar. A shekara ta bakwai Yehohiyada ya nuna ƙarfinsa. Ya yi alkawari da shugabanni na ɗari-ɗari, Azariya ɗan Yeroham, Ishmayel ɗan Yehohanan, Azariya ɗan Obed, Ma’asehiya ɗan Adahiya, da Elishafat ɗan Zikri. Suka ratsa cikin Yahuda suka tattara Lawiyawa da shugabannin iyalan Isra’ilawa daga dukan garuruwa. Sa’ad da suka zo Urushalima, dukan taron suka yi alkawari da sarki a haikalin Allah. Yehohiyada ya ce musu, “Ɗan sarki zai yi mulki yadda Ubangiji ya yi alkawari game da zuriyar Dawuda. Yanzu ga abin da za ku yi, shi ne, kashi ɗaya bisa uku na firistoci da Lawiyawa waɗanda za su yi aiki a Asabbaci su yi tsaro a ƙofofi, kashi ɗaya bisa ukunku a fadan sarki, kashi ɗaya bisa uku kuma, a Ƙofar Harsashi, sai kuma dukan sauran mutane su kasance a filayen haikalin Ubangiji. Babu wanda zai shiga haikalin Ubangiji sai firistoci da Lawiyawan da suke a aiki; za su iya shiga domin su tsarkaku ne, amma sauran mutane za su kiyaye abin da Ubangiji ya sa su yi. Lawiyawa za su tsaya kewaye da sarki, kowane mutum da makamansa a hannunsa. Duk wanda ya shiga haikali sai a kashe shi. Ku tsaya kusa da sarki a duk inda ya tafi.” Lawiyawa da dukan mutanen Yahuda suka yi yadda Yehohiyada firist ya umarta. Kowanne ya ɗauki mutanensa, waɗanda suke aiki a Asabbaci da waɗanda suka gama aiki, gama Yehohiyada firist bai bar waɗansu ɓangarori ba. Sa’an nan ya ba shugabannin māsu da garkuwoyi manya da ƙanana na sarki Dawuda, waɗanda suke cikin haikalin Allah. Ya kuma sa dukan mutane, kowanne da makaminsa a hannunsa, kewaye da sarki, kusa da bagade da kuma haikali, daga gefen kudu zuwa gefen arewa na haikali. Yehohiyada da ’ya’yansa maza suka fitar da ɗan sarki suka sa rawani a kansa; suka miƙa masa alkawarin, suka kuma yi shelarsa a matsayin sarki. Suka shafe shi suka kuma tā da murya suna cewa, “Ran sarki yă daɗe!” Sa’ad da Ataliya ta ji surutun mutane suna gudu suna yabon sarki, sai ta tafi wurinsu a haikalin Ubangiji. Ta duba, a can kuwa ga sarki, tsaye kusa da ginshiƙinsa a mashigi. Manyan sojoji da masu bushe-bushe suna kusa da sarki, dukan mutanen ƙasar kuwa suna farin ciki suna busa ƙahoni, mawaƙa kuma da kayan kiɗi suna bi da yabo. Sai Ataliya ta yage rigunanta ta yi ihu tana cewa, “Cin amanar ƙasa! Cin amanar ƙasa!” Yehohiyada firist ya fito da shugabanni waɗanda suke shugabancin rundunar sojoji, ya ce musu, “Ku fitar da ita tsakanin sojoji ku kuma kashe duk wanda ya bi ta da takobi.” Gama firist ya ce, “Kada ku kashe ta a haikalin Ubangiji.” Saboda haka suka kama ta yayinda take kaiwa mashigin Ƙofar Doki a filin fada, a can suka kashe ta. Sa’an nan Yehohiyada ya yi alkawari cewa shi da mutane da kuma sarki za su zama mutanen Ubangiji. Dukan mutane suka tafi haikalin Ba’al suka rurrushe shi. Suka farfashe bagadan da gumakan, suka kuma kashe Mattan firist na Ba’al a gaban bagadan. Sa’an nan Yehohiyada ya sa aikin lura da haikalin Ubangiji a hannuwan firistoci, waɗanda suke Lawiyawan da Dawuda ya ba su aikin haikali don su miƙa hadayun ƙonawa na Ubangiji kamar yadda yake a rubuce a Dokar Musa, da farin ciki da kuma rerawa, kamar yadda Dawuda ya umarta. Ya kuma sa matsaran ƙofofi a ƙofofin haikalin Ubangiji don kada wani da ba shi da tsarki yă shiga. Ya ɗauki shugabannin ɗari-ɗari, manyan gari, shugabannin mutane da dukan mutanen ƙasar tare da shi ya saukar da sarki daga haikalin Ubangiji. Suka shiga fada ta Ƙofar Bisa suka kuma zaunar da sarki a kujerar sarauta, sai dukan mutanen ƙasar suka yi farin ciki. Birnin kuwa ya samu zaman lafiya domin an kashe Ataliya da takobi. Yowash yana da shekara goma sha bakwai sa’ad da ya zama sarki, ya kuma yi sarauta a Urushalima shekara arba’in. Sunan mahaifiyarsa Zibiya ce; ita daga Beyersheba. Yowash ya yi abin da yake daidai a gaban Ubangiji duka shekarun Yehohiyada firist. Yehohiyada ya zaɓi mata biyu dominsa, yana kuma da ’ya’ya maza da ’ya’ya mata. Wani lokaci daga baya Yowash ya yanke shawara yă gyara haikalin Ubangiji. Ya tara firistoci da Lawiyawa wuri ɗaya ya ce musu, “Ku je garuruwan Yahuda ku karɓa kuɗin da ya kamata a biya shekara-shekara daga dukan Isra’ila, don gyaran haikalin Allahnku. Ku yi haka yanzu.” Amma Lawiyawa ba su yi haka nan da nan ba. Saboda haka sarki ya kira Yehohiyada babban firist ya ce masa, “Me ya sa ba ka bukaci Lawiyawa su kawo harajin da Musa bawan Ubangiji ya ce a biya daga Yahuda da Urushalima da kuma taron Isra’ila domin Tentin Sujada Shaida ba?” Yanzu ’ya’ya muguwar macen nan Ataliya maza sun fasa zuwa cikin haikalin Allah, suka kuma yi amfani da kayayyaki masu tsarki ma wa Ba’al. Bisa ga umarnin sarki, aka yi akwati aka sa a waje, a mashigin haikalin Ubangiji. Aka yi umarni a Yahuda da Urushalima cewa ya kamata suka kawo wa Ubangiji harajin da Musa bawan Allah ya bukaci daga Isra’ila a hamada. Dukan hafsoshi da dukan mutane suka kawo nasu kuɗin da aka sa musu da farin ciki, suna zuba su cikin akwatin sai da ya cika. Duk sa’ad da Lawiyawa suka fito da akwatin zuwa ga hafsoshin sarki, suka kuma ga cewa akwatin yana da kuɗi mai yawa, sai magatakardan fada da hafsan babban firist su zo su juya kuɗin daga akwatin su mai da shi wurinsa. Sun riƙa yin haka kullum suka tara kuɗi mai yawa. Sarki da Yehohiyada suka ba da shi ga mutanen da suka yi aikin da ake bukata don haikalin Ubangiji. Suka ɗauki masu gini da kafintoci don su gyara haikalin Ubangiji, da kuma ma’aikatan ƙarafa da tagulla don su gyara haikalin. Mutanen da suke lura da aikin natsattsu ne, kuma gyare-gyaren suka ci gaba a ƙarƙashinsu. Suka sāke gina haikalin Allah bisa ga ainihin fasalinsa suka ƙara masa ƙarfi. Da suka gama, suka kawo sauran kuɗin wa sarki da Yehohiyada, da su ne kuwa aka yi kayayyaki domin hidima da kuma domin hadayun ƙonawa, haka kuma kwanoni da sauran kayayyakin zinariya da azurfa. Muddin Yehohiyada yana raye, aka riƙa kawo hadayun ƙonawa a haikalin Ubangiji. Yanzu Yehohiyada ya tsufa kuma cike da shekaru, ya kuwa mutu yana da shekara ɗari da talatin. Aka binne shi tare da sarakuna a cikin Birnin Dawuda, saboda kirkin da ya yi a Isra’ila wa Allah da haikalinsa. Bayan mutuwar Yehohiyada, hafsoshin Yahuda suka zo suka yi mubaya’a wa sarki, ya kuma saurare su. Suka yashe haikalin Ubangiji Allah na kakanninsu, suka bauta wa ginshiƙan Ashera da kuma gumaka. Saboda laifinsu, fushin Allah ya sauko a kan Yahuda da Urushalima. Ko da yake Ubangiji ya aiki annabawa zuwa wurin mutane don su dawo da su gare shi, kuma ko da yake sun ba da shaida a kansu, ba su saurara ba. Sai Ruhun Allah ya sauko a kan Zakariya ɗan Yehohiyada firist. Ya tsaya a gaban mutane ya ce, “Ga abin da Allah ya ce, ‘Me ya sa ba ku yi biyayya da umarnan Ubangiji ba? Ba za ku yi nasara ba. Domin kun yashe Ubangiji, shi ma ya yashe ku.’ ” Amma suka yi masa maƙarƙashiya, kuma ta wurin umarnin sarki suka jajjefe shi da duwatsu har ya mutu a filin haikalin Ubangiji. Sarki Yowash bai tuna da alherin da Yehohiyada mahaifin Zakariya ya nuna masa ba, sai ya kashe ɗansa, wanda ya ce yayinda yake mutuwa, “Bari Ubangiji yă dubi wannan yă kuma sāka maka.” Da shekara ta kewaye, mayaƙan Aram suka yi gāba da Yowash suka kai hari wa Yahuda da Urushalima suka kuma kashe dukan shugabannin mutane, suka aika da dukan ganima zuwa ga sarkinsu a Damaskus. Ko da yake mayaƙan Arameyawa sun zo da mutane kaɗan kawai, Ubangiji ya sa suka ci nasara a kan sojojin Yahuda mafi yawa, don mutanen Yahuda sun rabu da Ubangiji Allah na kakanninsu, aka kuma hukunta Yowash. Sa’ad da Arameyawa suka janye, suka bar Yowash da mummunan rauni. Hafsoshinsa suka haɗa baki a kansa saboda kisan ɗan Yehohiyada firist da ya yi, suka kashe shi a kan gadonsa. Ta haka ya mutu aka kuma binne shi makabartan sarakuna. Waɗanda suka haɗa bakin kuwa su ne Zabad ɗan Shimeyat wata mutuniyar Ammon da Yehozabad ɗan Shimrit wata mutuniyar Mowab. Labarin ’ya’yansa maza, annabce-annabce masu yawa game da shi, da tarihin gyaran haikalin Allah suna a rubuce a rubuce-rubuce a littafin sarakuna. Amaziya ɗansa kuwa ya gāje shi a matsayin sarki. Amaziya yana da shekara ashirin da biyar sa’ad da ya zama sarki, ya kuma yi mulki a Urushalima shekara ashirin da tara. Sunan mahaifiyarsa Yehoyaddin ce; ita daga Urushalima ne. Ya yi abin da yake daidai a gaban Ubangiji, amma ba da dukan zuciyarsa ba. Bayan sarauta ta kahu a ƙarƙashinsa, sai ya kashe hafsoshin da suka kashe mahaifinsa sarki. Duk da haka bai kashe ’ya’yansu maza ba amma ya yi bisa ga abin da yake a rubuce a cikin Doka, a cikin Littafin Musa, inda Ubangiji ya umarta, “Ba za a kashe iyaye saboda ’ya’yansu ba; ba kuwa za a kashe ’ya’ya saboda iyayensu ba; kowa zai mutu saboda zunubansa ne.” Amaziya ya tattara mutanen Yahuda ya kuma ba su aiki bisa ga iyalansu, ya ba da aiki ga shugabannin dubu-dubu da shugabannin ɗari-ɗari, a dukan Yahuda da Benyamin. Ya kuma tattara waɗanda suke ’yan shekara ashirin da haihuwa ko fiye ya sami mutane dubu ɗari uku da suke a shirye don aikin soja, da suka isa riƙe māshi da garkuwa. Ya kuma ɗauko sojan haya jarumawa dubu ɗari ɗaya daga Isra’ila a kan talenti ɗari na azurfa. Amma mutumin Allah ya zo wurinsa ya ce, “Ya sarki, waɗannan runduna daga Isra’ila ba za su tafi tare da kai ba, gama Ubangiji ba ya tare da Isra’ila, ba ya nan da wani cikin mutanen Efraim. Ko da ma ya tafi ya yi faɗa da ƙwazo a cikin yaƙi, Allah zai tumɓuke shi a gaban abokan gāba, gama Allah yana da iko yă taimaka ko yă tumɓuke.” Amaziya ya tambayi mutumin Allah ya ce, “Amma game da talenti ɗarin da na biya saboda waɗannan rundunonin Isra’ila fa?” Mutumin Allah ya amsa, “ Ubangiji zai ba ka fiye da wannan.” Saboda haka Amaziya ya sallame rundunonin da suka zo daga Efraim, ya kuma mayar da su gida. Suka husata da Yahuda suka koma gida da fushi sosai. Sa’an nan Amaziya ya yi ƙarfin hali ya jagoranci mayaƙansa zuwa Kwarin Gishiri, inda ya kashe mutanen Seyir dubu goma. Mayaƙan Yahuda suka kuma kama mutane dubu goma da rai, suka ɗauke su zuwa ƙwanƙolin dutsen, suka yi ta tunkuɗa su ƙasa suka yi kaca-kaca. Ana cikin haka, sai rundunar da Amaziya ya mai da su gida, waɗanda ba a bari suka tafi yaƙin ba, suka kai wa garuruwan Yahuda daga Samariya zuwa Bet-Horon hari. Suka kashe mutane dubu uku suka kwashe ganima mai yawan gaske. Da Amaziya ya dawo daga kisan mutanen Edom, sai ya dawo da allolin mutanen Seyir. Ya kafa su a matsayin allolinsa, ya rusuna musu, ya kuma miƙa musu hadayun ƙonawa. Fushin Ubangiji ya yi ƙuna a kan Amaziya, sai ya aiki wani annabi wurinsa wanda ya ce, “Me ya sa ka nemi shawarar allolin mutanen nan, waɗanda ba za su cece mutanensu daga hannunka ba?” Tun yana cikin magana, sai sarki ya ce masa, “Yaushe muka naɗa ka mai ba sarki shawara? Rufe mana baki! Me zai hana a kashe ka?” Sai annabin ya yi shiru, amma ya ce, “Na dai sani Allah ya riga ya shirya zai hallaka ka, saboda ka aikata wannan, ba ka kuma saurari shawarata ba.” Bayan Amaziya sarkin Yahuda ya nemi shawara mashawartansa, sai ya kalubalanci Yowash ɗan Yehoyahaz, ɗan Yehu, sarkin Isra’ila, “Zo mu gamu fuska da fuska.” Amma Yowash sarkin Isra’ila ya amsa wa Amaziya sarkin Yahuda ya ce, “Wata ƙaya ce a Lebanon, ta aika da saƙo wa itacen al’ul na Lebanon cewa, ‘Ka ba ɗana ’yarka aure.’ Sai wani naman jeji na Lebanon ya zo ya tattake ƙayar. Ka ce wa kanka cewa ka ci Edom da yaƙi, yanzu kuwa kana fariya da ɗaga kai. Amma tsaya dai a gida! Me ya sa kake neman faɗa kana neman fāɗuwarka da ta Yahuda?” Amma Amaziya bai saurara ba gama Allah ya yi haka domin yă miƙa su ga Yehowash, domin sun nemi shawarar allolin Edom. Saboda haka Yowash sarkin Isra’ila ya kai yaƙi. Shi da Amaziya sarkin Yahuda suka fuskanci juna a Bet-Shemesh a Yahuda. Isra’ila ta fatattaki Yahuda, sai kowane mutum ya gudu zuwa gidansa. Yehowash sarkin Isra’ila ya kama Amaziya sarkin Yahuda, ɗan Yowash, ɗan Ahaziya a Bet-Shemesh. Sa’an nan Yehowash ya kawo shi Urushalima ya farfasa katangar Urushalima daga Ƙofar Efraim har zuwa Ƙofar Kusurwa, wani sashe mai tsawon ƙafa ɗari shida. Ya kwashe dukan zinariya da azurfa da dukan kayayyakin da aka samu a haikalin Allah waɗanda suke a ƙarƙashin kulawar Obed-Edom, da kaya masu daraja na gidan sarki, da waɗanda aka kamo cikin yaƙi, ya kawo Samariya. Amaziya ɗan Yowash sarkin Yahuda ya rayu shekara goma sha biyar bayan mutuwar Yehowash ɗan Yehoyahaz sarkin Isra’ila. Game da sauran ayyukan mulkin Amaziya, daga farko zuwa ƙarshe, an rubuta su a littafin sarakunan Yahuda da Isra’ila. Sa’ad da Amaziya ya bar bin Ubangiji, aka shirya masa maƙarƙashiya a Urushalima, sai ya gudu zuwa Lakish, amma suka aiki mutane suka bi shi zuwa Lakish, a can suka kashe shi. Aka dawo da shi a kan doki, aka binne shi tare da kakanninsa a Birnin Yahuda. Sai dukan mutanen Yahuda suka ɗauki Uzziya wanda yake da shekara goma sha shida da haihuwa, suka naɗa shi sarki a madadin mahaifinsa Amaziya. Shi ne wanda ya sāke gina Elot ya kuma mai da shi ga Yahuda bayan Amaziya ya huta tare da kakanninsa. Uzziya yana da shekara goma sha shida sa’ad da ya zama sarki, ya kuma yi mulki a Urushalima shekara hamsin da biyu. Sunan mahaifiyarsa Yekoliya ce; ita daga Urushalima ce. Ya yi abin da yake daidai a gaban Ubangiji, kamar dai yadda mahaifinsa Amaziya ya yi. Ya nemi Allah a kwanakin Zakariya, wanda ya koyar da shi a tsoron Allah. Muddin ya nemi Ubangiji, Allah ya ba shi nasara. Ya yi yaƙi da Filistiyawa ya kuma rushe katangar Gat, Yabne da kuma Ashdod. Sa’an nan ya sāke gina garuruwa kusa da Ashdod da sauran wurare a cikin Filistiyawa. Allah ya taimake shi a kan Filistiyawa da kuma a kan Larabawa waɗanda suke zama a Gur-Ba’al da kuma a kan Meyunawa. Ammonawa suka kawo haraji wa Uzziya, sunan da ya yi kuwa ya bazu har iyakar Masar, domin ya zama mai iko sosai. Uzziya ya gina hasumiyoyi a Urushalima a Ƙofar Kusurwa, a Ƙofar Kwari da kuma a kusurwar katanga, ya kuma yi musu katanga. Ya gina hasumiyoyi a hamada ya kuma haƙa rijiyoyi masu yawa, gama yana da dabbobi masu yawa a gindin duwatsu da kuma a kwari. Yana da mutane masu yin masa aiki a gonakinsa da gonakin inabinsa a tuddai da kuma a ƙasashe masu dausayi, gama yana son noma. Uzziya ya kasance da gogaggun mayaƙa, a shirye su fito ɓangarori-ɓangarori bisa ga yawansu yadda Yehiyel magatakarda, da Ma’asehiya jarumi, suka karkasa su bisa ga umarnin Hananiya, ɗaya daga cikin fadawa. Yawan shugabannin iyali a bisa jarumawa sun kai 2,600. A ƙarƙashin shugabancinsu akwai mayaƙa 307,500 horarru don yaƙi, mayaƙa masu ƙarfi don su taimaki sarki a kan abokan gābansa. Uzziya ya tanada garkuwoyi, māsu, hulunan kwano, kayan sulke, baka da majajjawa don mayaƙan gaba ɗaya. A Urushalima ya yi na’urori da gwanaye suka sarrafa don amfani a hasumiyoyi da kuma a kusurwar kāriya don harbin kibiyoyi da jefan manyan duwatsu. Sunansa ya bazu ko’ina, gama ya sami taimako sosai har ya zama mai iko. Amma bayan Uzziya ya zama mai iko, sai ɗaga kai ya kai shi ga fāɗuwa. Bai yi aminci ga Ubangiji Allahnsa ba, ya kuma shiga haikalin Ubangiji don yă ƙone turare a bagaden turare. Azariya firist tare da waɗansu firistoci tamanin na Ubangiji masu ƙarfin hali suka bi shi ciki. Suka kalubalance shi suka ce, “Ba daidai ba ne, Uzziya, ka ƙone turare ga Ubangiji. Wannan aikin firistoci zuriyar Haruna ne, waɗanda aka tsarkake don ƙone turare. Ka bar wuri mai tsarki, gama ka kasance marar aminci; kuma Ubangiji Allah ba zai girmama ka ba.” Uzziya wanda yake da farantin wuta a hannunsa a shirye don ƙone turare, ya husata. Yayinda yake fushi da firistocin a gabansu a gaban bagaden turare a haikalin Ubangiji, sai kuturta ta faso a goshinsa. Sa’ad da Azariya babban firist da dukan sauran firistoci suka dube shi, sai suka ga cewa yana da kuturta a goshinsa, saboda haka suka gaggauta tunkuɗa shi waje nan da nan. Tabbatacce, shi kansa ma ya yi marmari yă bar wurin domin Ubangiji ya buge shi. Sarki Uzziya ya kasance da kuturta har ranar mutuwarsa. Ya zauna a gidan da aka ware, da kuturci, aka kuma ware shi daga haikalin Ubangiji. Yotam ɗansa ya lura da fadan ya kuma yi mulkin mutanen ƙasar. Sauran ayyukan mulkin Uzziya daga farko zuwa ƙarshe, suna a rubuce ta hannun annabi Ishaya ɗan Amoz. Uzziya ya huta da kakanninsa aka kuma binne shi kusa da su a fili don binnewar da take ta sarakuna, domin mutane sun ce, “Yana da kuturta.” Sai Yotam ɗansa ya gāje shi a matsayin sarki. Yotam yana da shekara ashirin da biyar sa’ad da ya zama sarki, ya kuma yi mulki a Urushalima shekara goma sha shida. Sunan mahaifiyarsa Yerusha, ’yar Zadok. Ya yi abin da yake daidai a gaban Ubangiji, kamar yadda mahaifinsa Uzziya ya yi, sai dai bai kutsa cikin haikalin Ubangiji kamar mahaifinsa ba. Mutane kuwa, suka ci gaba da aikata ayyukan lalaci. Yotam ya sāke ginin Ƙofar Bisa na haikalin Ubangiji, ya kuma yi aiki sosai a katanga a tudun Ofel. Ya gina garuruwa a tuddan Yahuda, ya giggina katanga da gine-gine masu tsawo a wuraren da suke a kurmi. Yotam ya yi yaƙi da sarkin Ammonawa ya kuma ci su. A wannan shekara Ammonawa suka biya shi haraji talenti ɗari na azurfa, garwan alkama dubu goma da kuma garwa dubu goma na sha’ir. Ammonawa suka kawo masa wannan kuma a shekara ta biyu da ta uku. Yotam ya ƙaru a iko saboda ya daidaita al’amuransa a gaban Ubangiji Allahnsa. Sauran ayyuka a mulkin Yotam, haɗe da dukan yaƙe-yaƙensa da waɗansu abubuwan da ya yi, suna a rubuce a littafin sarakunan Isra’ila da na Yahuda. Yana da shekara ashirin da biyar sa’ad da ya zama sarki, ya kuma yi mulki a Urushalima shekara goma sha shida. Yotam ya huta tare da kakanninsa, aka kuma binne shi a Birnin Dawuda. Sai Ahaz ɗansa ya gāje shi a matsayin sarki. Ahaz yana da shekara ashirin sa’ad da ya zama sarki, ya kuma yi mulki a Urushalima shekara goma sha shida. Ba kamar Dawuda kakansa ba, bai yi abin da yake daidai a gaban Ubangiji ba. Ya yi tafiya a hanyoyin sarakunan Isra’ila ya kuma yi zubin gumaka domin a bauta wa Ba’al. Ya ƙone hadayu a Kwarin Ben Hinnom, ya kuma miƙa ’ya’yansa maza a cikin wuta, yana bin hanyoyi banƙyama na al’umman da Ubangiji ya kora a gaban Isra’ilawa. Ya miƙa hadayu, ya kuma ƙone turare a masujadan kan tudu, a bisa tuddai da kuma ƙarƙashin kowane itace mai inuwa. Saboda haka Ubangiji Allahnsa ya miƙa shi ga sarkin Aram. Arameyawa suka ci shi a yaƙi, suka kuma kwashe mutanensa da yawa a matsayin ’yan kurkuku, suka kawo Damaskus. Ya kuma ba da shi ga sarkin Isra’ila, wanda ya jijji masa a yaƙi. A rana ɗaya Feka ɗan Remaliya ya kashe sojoji dubu ɗari da dubu ashirin a Yahuda, domin Yahuda sun yashe Ubangiji Allah na kakanninsu. Zikri, wani jarumin Efraim, ya kashe Ma’asehiya ɗan sarki, Azrikam hafsa mai lura da fada, da kuma Elkana, mataimakin sarki. Isra’ilawa suka kame kamammu daga ’yan’uwansu mata, ’ya’ya maza da kuma ’ya’ya mata dubu ɗari biyu. Suka kuma kwashe ganima mai yawan gaske, waɗanda suka kwasa zuwa Samariya. Amma wani annabin Ubangiji mai suna Oded yana a can, sai ya fito don yă sadu da mayaƙa sa’ad da suke komowa zuwa Samariya. Ya ce musu, “Domin Ubangiji Allah na kakanninku yana fushi da Yahuda, ya ba da su cikin hannunku. Sai kuka kashe su cikin fushin da ya kai sama. Yanzu kuma kuna niyya ku mai da maza da matan Yahuda da Urushalima bayinku. Amma ku ɗin ba ku da laifin zunubi ga Ubangiji Allahnku ne? To, ku saurare ni! Ku mai da ’yan’uwanku da kuka kama a matsayin ’yan kurkuku, gama fushin Ubangiji yana a kanku.” Sai waɗansu shugabanni a Efraim, Azariya ɗan Yehohanan, Berekiya ɗan Meshillemot, Hezekiya ɗan Shallum da Amasa ɗan Hadlai, suka tasar wa waɗanda suke isowa daga yaƙi. Suka ce, “Dole ku kawo waɗannan ’yan kurkukun a nan, ko kuwa za ku yi laifi a gaban Ubangiji. Kuna niyya ku ƙara ga zunubinmu da kuma laifinmu? Gama laifinmu ya riga ya yi yawa, kuma fushinsa mai tsanani yana a kan Isra’ila.” Saboda haka sojoji suka ba da ’yan kurkukun da ganima a gaban hafsoshi da dukan taron. Sai mutanen da aka kira sunansu suka tashi, suka ɗauki kamammun, da ganimar, suka sa wa dukan waɗanda suke tsirara sutura. Suka sa musu sutura, suka ba su takalma, suka ba su abinci da abin sha, suka shafa musu mai. Suka hawar da dukan raunana a kan jakuna, suka kai su wurin ’yan’uwansu a Yeriko, wato, Birnin Itatuwan Dabino, sa’an nan suka koma Samariya. A lokacin nan Sarki Ahaz ya aika wurin sarkin Assuriya neman taimako. Mutanen Edom sun sāke zuwa suka yaƙi Yahuda suka kuma kwashe ’yan kurkuku, yayinda Filistiyawa suka kai hari wa garuruwa a gindin tuddai da kuma a Negeb na Yahuda. Suka kame su suka kuma zauna a Bet-Shemesh, Aiyalon da Gederot, haka ma Soko, Timna da Gimzo tare da ƙauyuka kewayensu. Ubangiji ya ƙasƙantar da Yahuda saboda Ahaz sarkin Isra’ila, gama ya hadasa mugunta a Yahuda kuma ya kasance marar aminci ga Ubangiji. Tiglat-Fileser sarkin Assuriya ya zo wurinsa, sai ya wahalar da sarki Ahaz maimakon taimakonsa. Ahaz ya ɗauki waɗansu abubuwa daga haikalin Ubangiji da kuma daga fadan sarki da kuma daga sarakuna, ya ba da su ga sarkin Assuriya, amma wannan bai taimake shi ba. Cikin lokacin wahalarsa Sarki Ahaz ya ƙara zama marar aminci ga Ubangiji. Ya miƙa hadayu ga allolin Damaskus, waɗanda suka ci shi a yaƙi; gama ya yi tunani, “Da yake allolin sarakunan Aram sun taimake su, zan miƙa hadayu domin su taimake ni.” Amma suka zama sanadin fāɗuwarsa da kuma fāɗuwar dukan Isra’ila. Ahaz ya tattara kayayyaki daga haikalin Allah ya kwashe su. Ya kulle ƙofofin haikalin Ubangiji ya kakkafa bagadai a kowace kusurwa a titin Urushalima. A kowane gari a Yahuda, ya gina masujadan kan tudu don ƙone hadayu ga waɗansu alloli, ya kuma tsokane Ubangiji Allah na kakanninsa ya yi fushi. Sauran ayyukan mulkinsa da dukan hanyoyinsa, daga farko zuwa ƙarshe, suna a rubuce a littafin sarakunan Yahuda da Isra’ila. Ahaz ya huta tare da kakanninsa, aka kuma binne shi a birnin Urushalima, amma ba a sa shi a makabartan sarakunan Isra’ila ba. Sai Hezekiya ɗansa ya gāje shi a matsayin sarki. Hezekiya yana da shekara ashirin da biyar sa’ad da ya zama sarki, ya kuma yi mulki a Urushalima shekara ashirin da tara. Sunan mahaifiyarsa Abiya, ’yar Zakariya. Ya yi abin da yake daidai a gaban Ubangiji, kamar dai yadda kakansa Dawuda ya yi. A wata na farkon a farkon shekarar mulkinsa, ya buɗe ƙofofin haikalin Ubangiji ya gyara su. Ya kawo firistoci da Lawiyawa, ya tattara su a filin da yake a gefen gabas ya kuma ce musu, “Ku saurare ni, Lawiyawa! Ku tsarkake kanku yanzu, ku kuma tsarkake haikalin Ubangiji Allah na kakanninku. Ku fid da ƙazanta daga wuri mai tsarki. Kakanninku ba su yi aminci ba; suka aikata abin da yake mugu a gaban Ubangiji Allahnmu, suka kuma yashe shi. Suka juya fuskokinsu daga mazaunin Ubangiji suka kuma juya masa baya. Suka kulle ƙofofin shirayi, suka kuma kashe fitilu. Ba su ƙone turare ko su miƙa hadayun ƙonawa a wuri mai tsarki ga Allah na Isra’ila ba. Saboda haka, fushin Ubangiji ya fāɗo a kan Yahuda da Urushalima; ya mai da su abin tsoro da abin banrazana da kuma abin ba’a, kamar yadda kuke gani da idanunku. Abin da ya sa ke nan kakanninmu suka fāɗi ta takobi, kuma shi ya sa aka kai ’ya’yanmu maza da ’ya’yanmu mata da matanmu bauta. Yanzu ina niyya in yi alkawari da Ubangiji, Allah na Isra’ila, domin fushinsa yă kauce daga gare mu. ’Ya’yana maza, kada ku yi sakaci yanzu, gama Ubangiji ya zaɓe ku don ku tsaya a gabansa ku kuma yi masa hidima, don ku yi hidima a gabansa ku kuma ƙone turare.” Sai waɗannan Lawiyawa suka shiga aiki, daga Kohatawa Mahat ɗan Amasai da Yowel ɗan Azariya. Daga Kabilar Merari, Kish ɗan Abdi da Azariya ɗan Yahallelel. Daga Gershonawa, Yowa ɗan Zimma da Eden ɗan Yowa. Daga zuriyar Elizafan, Shimri da Yehiyel. Daga zuriyar Asaf, Zakariya da Mattaniya. Daga iyalin Heman, Yehiyel da Shimeyi. Daga zuriyar Yedutun, Shemahiya da Uzziyel. Da suka tattara ’yan’uwansu suka kuma tsarkake kansu, sai suka shiga ciki suka tsarkake haikalin Ubangiji, kamar yadda sarki ya umarta, suna bin maganar Ubangiji. Firistoci suka shiga cikin wuri mai tsarki na Ubangiji suka tsarkake shi. Suka fitar da dukan abin da yake marar tsabta da suka samu a haikalin Ubangiji zuwa filin haikalin Ubangiji. Lawiyawa suka ɗauke su suka kai su Kwarin Kidron. Suka fara tsarkakewar a rana ta farko na farkon wata, a rana ta takwas na watan kuwa suka kai shirayin Ubangiji. Karin kwana takwas kuma suka tsarkake haikalin Ubangiji kansa, suka gama a rana ta goma sha shida na farkon wata. Sa’an nan suka tafi wurin Sarki Hezekiya suka faɗa masa, “Mun tsarkake haikalin Ubangiji gaba ɗaya, bagaden ƙone hadaya tare da dukan kayayyakinsa, da tebur don shirya tsarkaken burodi, tare da dukan kayayyakinsa. Mun shirya muka kuma tsarkake dukan kayayyakin da Sarki Ahaz ya cire cikin rashin amincinsa yayinda yake sarki. Yanzu suna a gaban bagaden Ubangiji.” Da sassafe kashegari Sarki Hezekiya ya tattara manyan birni wuri ɗaya, suka haura zuwa haikalin Ubangiji. Suka kawo bijimai bakwai, raguna bakwai, bunsurai bakwai da kuma awaki mata bakwai a matsayin hadaya don zunubi domin masarauta, domin wuri mai tsarki da kuma domin Yahuda. Sarki ya umarce firistoci, zuriyar Haruna, su miƙa waɗannan a bagaden Ubangiji. Saboda haka suka yayyanka bijiman, firistoci suka karɓi jinin suka yayyafa a kan bagade. Suka kuma yanka ragunan suka yayyafa jinin a bagaden. Haka kuma suka yanka ’yan ragunan suka yayyafa jinin a bagaden. Aka kawo awaki domin hadaya don zunubi a gaban sarki da taron, suka kuwa ɗibiya hannuwansu a kansu. Sa’an nan firistoci suka yayyanka awakin suka miƙa jininsu a bagade domin hadaya don zunubi don kafara saboda dukan Isra’ila, domin sarki ya umarta a yi hadaya ta ƙonawa da hadaya don zunubi domin dukan Isra’ila. Sarki Hezekiya ya ajiye Lawiyawa a cikin haikalin Ubangiji tare da ganguna, garayu da molaye, yadda Dawuda da Gad mai duba na sarki da kuma annabi Natan suka tsara. Ubangiji ne ya umarta wannan ta wurin annabawansa. Saboda haka Lawiyawa suka tsaya a shirye tare da kayan kiɗin Dawuda, firistoci kuma tare da ƙahoninsu. Hezekiya ya ba da umarni a miƙa hadaya ta ƙonawa a kan bagade. Yayinda aka fara miƙawa, ana rerawa ga Ubangiji, tare da bushe-bushe da kiɗe-kiɗen kayan waƙa na Dawuda sarkin Isra’ila. Dukan taron suka durƙusa suka yi sujada, yayinda mawaƙa suke rerawa, ana kuma busa ƙahoni, dukan wannan ya ci gaba sai da aka gama miƙa hadaya ta ƙonawa. Sa’ad da aka gama miƙawa, sai sarki da mutanen da suke tare da shi suka durƙusa suka yi sujada. Sarki Hezekiya da fadawansa suka umarci Lawiyawa su yabi Ubangiji da kalmomin Dawuda da na Asaf mai duba. Saboda haka suka rera yabai da murna, suka sunkuyar da kawunansu suka yi sujada. Sa’an nan Hezekiya ya ce, “Yanzu kun keɓe kanku ga Ubangiji. Ku zo ku kuma kawo hadayu da hadayun godiya zuwa ga haikalin Ubangiji.” Saboda haka taron suka kawo hadayu da hadayun godiya, da kuma dukan waɗanda suke da niyya suka kawo hadayun ƙonawa. Yawan hadayun ƙonawan da taron suka kawo, bijimai saba’in ne, raguna ɗari da kuma bunsurai ɗari biyu, dukansu kuwa domin hadayun ƙonawa ga Ubangiji ne. Dabbobin da aka tsarkake a matsayi hadayu sun kai bijimai ɗari shida da tumaki da kuma awaki dubu uku. Firistoci fa, suka kāsa sosai don fiɗan dukan dabbobin da za a miƙa don hadayun ƙonawa; saboda haka ’yan’uwansu Lawiyawa suka taimake su har aka gama aiki kafin sauran firistoci su sami damar tsarkake kansu. Gama Lawiyawa sun fi firistoci himma wajen tsarkakewar kansu. Aka kasance da hadayun ƙonawa a yalwace, tare da kitsen hadayun salama da hadayun sha da suke tafe da hadayun ƙonawa. Saboda haka aka sāke kafa hidimar haikalin Ubangiji. Hezekiya da dukan mutane suka yi farin ciki game da abin da Allah ya yi wa mutanensa, domin ya faru farat ɗaya. Sai Hezekiya ya aika wa dukan Isra’ila da Yahuda, ya kuma rubuta wasiƙu zuwa Efraim da Manasse, yana gayyatarsu su zo haikalin Ubangiji a Urushalima, su kuma yi Bikin Ƙetarewa ga Ubangiji, Allah na Isra’ila. Sarki da fadawansa da dukan taro a Urushalima suka yanke shawara su yi Bikin Ƙetarewa a wata na biyu. Ba su iya yinsa a daidai lokacinsa ba domin babu isashen firistocin da suka tsarkake kansu, mutane kuma ba su taru a Urushalima ba. Shirin ya yi kyau ga sarki da kuma dukan taron. Suka yanke shawara su yi shelar a ko’ina a Isra’ila, daga Beyersheba zuwa Dan, suna kiran mutane su zo Urushalima, suka kuma yi Bikin Ƙetarewa ga Ubangiji Allah na Isra’ila. Ba a yi bikin da mutane masu yawa bisa ga abin da aka rubuta ba. Bisa ga umarnin sarki, sai ’yan aika suka tafi ko’ina a Isra’ila da Yahuda da wasiƙu daga sarki da kuma daga fadawansa, wasiƙar tana cewa, “Mutanen Isra’ila, ku dawo ga Ubangiji Allah na Ibrahim, Ishaku da Isra’ila, domin yă dawo gare ku, ku da kuka tafi, ku da kuka kuɓuce daga hannun sarakuna Assuriya. Kada ku zama kamar iyayenku da ’yan’uwanku, waɗanda suka yi rashin aminci ga Ubangiji Allah na kakanninsu, har ya mai da su abin tsoro, yadda kuke gani. Kada ku yi taurinkai, yadda iyayenku suka yi; ku miƙa kai ga Ubangiji. Ku zo wuri mai tsarki, wanda ya tsarkake har abada. Ku bauta wa Ubangiji Allahnku, domin fushi mai zafi yă juye daga gare ku. In kuka dawo wurin Ubangiji, sa’an nan waɗanda suka kama ’yan’uwanku da ’ya’yanku za su nuna musu tausayi, su kuma dawo wannan ƙasa, gama Ubangiji Allahnku mai alheri ne mai jinƙai kuma. Ba zai kau da fuskarsa daga gare ku ba, in kuka dawo gare shi.” ’Yan aika suka tafi gari-gari a cikin Efraim da Manasse, har zuwa Zebulun, amma mutane suka yi musu dariyar reni, suka kuma yi musu ba’a. Duk da haka, waɗansu mutanen Asher, Manasse da Zebulun suka ƙasƙantar da kansu suka tafi Urushalima. Haka ma a Yahuda, hannun Allah yana a kan mutane don yă ba su zuciya ɗaya su yi abin da sarki da fadawansa suka umarta, suna bin maganar Ubangiji. Taron mutane mai girma ya haɗu a Urushalima don Bikin Burodi Marar Yisti a wata na biyu. Suka kawar da bagadai a Urushalima suka fid da bagadan turare suka zubar da su a Kwarin Kidron. Suka yanka ɗan ragon Bikin Ƙetarewa a rana ta goma sha huɗu na wata na biyu. Firistoci da Lawiyawa suka ji kunya suka tsarkake kansu, suka kawo hadayun ƙonawa a haikalin Ubangiji. Sa’an nan suka ɗauki matsayinsu na kullum yadda yake a Dokar Musa mutumin Allah. Firistoci suka yayyafa jinin da Lawiyawa suka ba su. Da yake da yawa cikin taron ba su tsarkake kansu ba, dole Lawiyawa su yanka ’yan ragunan Bikin Ƙetarewa domin dukan waɗanda ba su da tsarki, ba su kuma iya tsarkake ragunansu ga Ubangiji ba. Ko da yake yawancin mutanen da suka zo daga Efraim, Manasse, Issakar da Zebulun ba su tsarkake kansu ba, duk da haka suka ci Bikin Ƙetarewa, ba tare da bin abin da yake a rubuce ba. Amma Hezekiya ya yi addu’a dominsu cewa, “Bari Ubangiji, wanda yake nagari, yă gafarta wa kowa wanda ya sa zuciyarsa ga neman Allah, Ubangiji Allah na kakanninsa, ko da shi marar tsarki ne bisa ga dokokin wuri mai tsarki.” Ubangiji kuwa ya ji Hezekiya ya kuma warkar da mutane. Isra’ilawan da suka kasance a Urushalima suka yi Bikin Burodi Marar Yisti kwana bakwai da farin ciki mai girma, yayinda Lawiyawa da firistoci suke rera ga Ubangiji kowace rana, haɗe da kayan kiɗin yabon Ubangiji. Hezekiya ya yi magana mai ƙarfafawa ga dukan Lawiyawa waɗanda suka nuna ganewar fasaha a hidimar Ubangiji. Kwana bakwai suka ci rabonsu da aka tsara, suka miƙa hadayun salama, suka kuma yabi Ubangiji Allah na kakanninsu. Dukan mutanen suka yarda su ƙara kwana bakwai kuma, sai suka ci gaba da bikin cikin farin ciki har waɗansu kwana bakwai kuma. Hezekiya sarkin Yahuda ya tanada bijimai dubu ɗaya da tumaki da kuma awaki dubu bakwai wa taron, fadawa kuma suka tanada musu bijimai dubu da kuma tumaki da awaki dubu goma. Firistoci masu yawa suka tsarkake kansu. Taron gaba ɗaya na Yahuda suka yi farin ciki, tare da firistoci da kuma Lawiyawa da dukan waɗanda suka taru daga Isra’ila, har ma da baƙi waɗanda suka zo daga Isra’ila da waɗanda suke zama a Yahuda. Aka yi farin ciki mai girma a Urushalima, gama tun zamanin Solomon ɗan Dawuda sarkin Isra’ila, ba a taɓa yin wani abu kamar haka a Urushalima ba. Firistoci da Lawiyawa suka tsaya suka albarkace mutane, Allah kuma ya ji su, gama addu’arsu ya kai sama, mazauninsa mai tsarki. Sa’ad da aka gama dukan wannan, sai Isra’ilawan da suke can suka fita zuwa garuruwan Yahuda, suka rurrushe keɓaɓɓun duwatsu suka kuma farfashe ginshiƙan Ashera. Suka rurrushe masujadan kan tudu da bagadai, ko’ina a Yahuda da Benyamin da kuma cikin Efraim da Manasse. Bayan sun rurrushe dukansu, sai Isra’ilawa suka koma garuruwansu, kowanne zuwa mahallinsa. Hezekiya kuma ya raba firistoci da Lawiyawa kashi-kashi, kowanne da hidimarsa, firistoci da Lawiyawa, don hadayu na ƙonawa da na salama, su yi hidima, su yi godiya, su kuma rera yabai a ƙofofin mazaunin Ubangiji. Sarki ya ba da taimako daga mallakarsa domin hadayun ƙonawa, safe da yamma da kuma don hadayun ƙonawa a Asabbatai, Sabon Wata da kuma ƙayyadaddun bukukkuwa kamar yadda yake a rubuce a cikin Dokar Ubangiji. Ya umarci mutanen da suke zama a Urushalima su ba da rabon da yake na firistoci da Lawiyawa, don su ƙwallafa ransu ga Dokar Ubangiji. Nan da nan aka baza umarnin, sai Isra’ilawa suka bayar ’ya’yan farin hatsinsu, sabon ruwan inabi, mai da kuma zuma da dukan abin da gona ta bayar, hannu sake. Suka kawo zakan kowane abu da yawa. Mutanen Isra’ila da Yahuda waɗanda suke zama a garuruwan Yahuda, su ma suka kawo zakan shanu da na tumaki da kuma zakan abubuwa masu tsarki da aka keɓe ga Ubangiji Allahnsu, suka jibge su tsibi-tsibi. Sun fara yin haka a wata na uku, suka kuma gama a wata na bakwai. Sa’ad da Hezekiya da fadawansa suka zo suka ga tsibin, sai suka yabi Ubangiji, suka kuma albarkace mutanensa Isra’ila. Hezekiya ya tambayi firistoci da Lawiyawa game da tsibin; sai Azariya babban firist, daga iyalin Zadok ya amsa, “Tun daga lokacin da mutane suka fara kawo taimakonsu ga haikalin Ubangiji, muna da isashe don abinci da kuma da yawa da za mu rage, domin Ubangiji ya albarkaci mutanensa, saboda haka abin da ya ragu a rumbu yana da yawa.” Hezekiya ya ba da umarni a shirya ɗakunan ajiya a haikalin Ubangiji, aka kuwa yi haka. Sa’an nan cikin aminci suka kawo taimako, zakka da keɓaɓɓun kyautai. Konaniya, wani Balawe, shi ne ke lura da waɗannan abubuwa, kuma ɗan’uwansa Shimeyi shi ne na biye da shi. Yehiyel, Azaziya, Nahat, Asahel, Yerimot, Yozabad, Eliyel, Ismakiya, Mahat da Benahiya su ne shugabanni, mataimakan Konaniya da Shimeyi ɗan’uwansa, waɗanda sarki Hezekiya da Azariya babban shugaban haikalin Allah suka naɗa. Kore ɗan Imna Balawe, mai tsaron Ƙofar Gabas, shi ne yake lura da baikon yardan ran da aka yi wa Allah, don ya karkasa bayarwar da aka keɓe domin Ubangiji da hadayu mafi tsarki. Eden, Miniyamin, Yeshuwa, Shemahiya, Amariya da Shekaniya sun taimake shi da aminci a cikin garuruwan firistoci, suna ba da rabo wa ’yan’uwansu firistoci bisa ga sassansu, tsofaffi da yara. Bugu da ƙari, suka ba da rabo ga maza ’yan shekaru uku ko fiye waɗanda sunayensu suna a tarihin zuriya, dukan waɗanda ba za su iya shiga haikalin Ubangiji su yi ayyukansu na kullum ba, bisa ga nawayarsu da kuma sassansu. Suka kuma ba da rabo ga firistocin da aka rubuta ta iyalansu cikin tarihin zuriya, haka kuma ga Lawiyawa masu shekara ashirin ko fiye, bisa ga nawayarsu da kuma sassansu. Suka haɗa da dukan ƙanana ’ya’yansu, mata, da kuma ’ya’ya maza da ’ya’ya mata, al’umma gaba ɗaya da aka jera a waɗannan tarihin zuriya. Gama sun yi aminci cikin tsarkake kansu. Akwai mutane a garuruwa da yawa waɗanda aka sa don su rarraba wa ’ya’yan Haruna, firist, maza, waɗanda suke zaune a gonaki na ƙasar garuruwansu su ba kowane namijin da aka rubuta na Lawiyawa, rabonsa. Abin da Hezekiya ya yi ke nan ko’ina a Yahuda, yana yin abin da yake da kyau, daidai da kuma mai aminci a gaban Ubangiji Allahnsa. Cikin kome da ya yi cikin hidimar haikalin Allah, cikin biyayya kuma ga doka da umarnai, ya nemi Allahnsa, ya kuma yi aiki gabagadi. Ta haka kuwa ya yi nasara. Bayan dukan abin da Hezekiya ya yi cikin aminci, sai Sennakerib sarkin Assuriya ya zo ya yaƙi Yahuda. Ya yi kwanto wa biranen katanga, yana zato zai ci su da yaƙi wa kansa. Sa’ad da Hezekiya ya ga Sennakerib ya zo yana kuma niyya yă yaƙi Urushalima, sai ya yi shawara da fadawansa da hafsoshin mayaƙansa cewa su datse ruwa daga maɓulɓulan ruwan da yake waje da birnin, suka kuwa taimake shi. Sai babban taro suka haɗu suka datse dukan maɓulɓulai da rafuffukan da suke gudu cikin ƙasar. Suka ce “Me zai sa sarakunan Assuriya su zo su sami ruwa barkatai?” Sai suka yi aiki tuƙuru suna gyaran dukan sassan katangar da suka fāɗi, suna kuma gina hasumiya a kai. Ya gina wata katanga a waje da wannan, ya kuma ƙara ƙarfin madogaran gini na Birnin Dawuda. Ya yi makamai masu yawa da kuma garkuwoyi. Ya naɗa manyan hafsoshi a kan mutane, ya tattara su a gabansa a fili a ƙofar birni, ya kuma ƙarfafa su da waɗannan kalmomi. “Ku ƙarfafa, ku yi ƙarfin hali. Kada ku ji tsoro ko ku yi fargaba saboda sarkin Assuriya, da mayaƙan nan masu yawa da suke tare da shi, gama shi wanda yake tare da mu, ya fi wanda yake tare da su. Mayaƙa na jiki ne kawai suke tare da shi, amma Ubangiji Allahnmu ne yake tare da mu, zai kuwa taimake mu yă kuma yi yaƙinmu.” Mutane kuwa suka amince da maganar Hezekiya, Sarkin Yahuda. Daga baya, sa’ad da Sennakerib sarkin Assuriya da dukan mayaƙansa suke kwanto wa Lakish, sai ya aiki hafsoshinsa da wannan saƙo wa Hezekiya sarkin Yahuda da kuma wa dukan mutanen Yahuda waɗanda suke can cewa, “Ga abin da Sennakerib sarkin Assuriya ya ce ga me kake dogara, har da ka dāge cikin Urushalima da aka yi mata kwanto? Ai, Hezekiya, ruɗinku yake yi, don yă sa ku mutu da yunwa da ƙishirwa sa’ad da yake ce muku, ‘ Ubangiji Allahnmu zai cece mu daga hannun sarkin Assuriya.’ Hezekiya kansa bai rushe waɗannan masujadan kan tudu da bagadai, yana ce wa Yahuda da Urushalima, ‘Dole ku yi sujada a gaban bagade guda ku kuma ƙone hadayu a kansa ba’? “Ba ku san abin da ni da kuma kakannina suka yi wa dukan mutanen sauran ƙasashe ba? Allolin ƙasashen nan sun taɓa iya ceton ƙasarsu daga hannuna ne? Wanne a cikin dukan allolin waɗannan ƙasashe da kakannina suka hallaka ya taɓa iya ceton mutanensa daga gare ni? To, yaya Allahnku zai iya cetonku daga hannuna? Yanzu fa, kada ku bar Hezekiya yă ruɗe ku yă kuma ɓad da ku haka. Kada ku gaskata shi, gama babu allahn wata ƙasa ko masarautar da ya taɓa iya ceton mutanensa daga hannuna ko kuwa hannun kakannina. Balle har Allahnku yă cece ku daga hannuna!” Hafsoshin Sennakerib suka ci gaba da maganar banza wa Ubangiji Allah da kuma a kan bawansa Hezekiya. Sarki ya kuma rubuta wasiƙu yana zagin Ubangiji, Allah na Isra’ila, yana faɗin wannan a kansa, “Kamar yadda sauran allolin mutanen sauran ƙasashe ba su iya kuɓutar da mutane daga hannuna ba, haka Allahn Hezekiya ba zai kuɓutar da mutanensa daga hannuna ba.” Sa’an nan suka yi magana da ƙarfi cikin Yahudanci wa mutanen Urushalima waɗanda suke kan katanga, don su firgita su, su kuma sa su ji tsoro don su iya cin birnin. Suka yi magana game da Allah na Urushalima yadda suka yi game da allolin sauran mutanen duniya, aikin hannuwan mutane. Sarki Hezekiya da annabi Ishaya ɗan Amoz suka yi kuka cikin addu’a ga sama game da wannan. Sai Ubangiji ya aiki mala’ika, wanda ya karkashe dukan jarumawa da shugabanni da kuma hafsoshi a sansanin sarkin Assuriyawa. Saboda haka sai sarkin Assuriya ya janye zuwa ƙasarsa da kunya. Da ya shiga haikalin Allahnsa, sai waɗansu a cikin ’ya’yansa maza suka yanka shi da takobi. Ta haka Ubangiji ya ceci Hezekiya da mutanen Urushalima daga hannun Sennakerib sarkin Assuriya da kuma daga hannun dukan sauran. Ya magance su a kowane gefe. Yawanci mutane suka kawo hadayun ƙonawa zuwa Urushalima wa Ubangiji da kuma kyautai masu daraja wa Hezekiya sarkin Yahuda. Daga lokacin zuwa gaba dukan ƙasashe suka girmama shi. A kwanakin nan Hezekiya ya yi ciwo, ya yi kusan mutuwa. Sai ya yi addu’a ga Ubangiji, wanda ya amsa masa ya kuma ba shi alama. Amma zuciyar Hezekiya ta yi girman kai, bai kuwa yi amfani da alherin da aka nuna masa ba, saboda haka fushin Ubangiji ya sauko a kansa da kuma a kan Yahuda da Urushalima. Sai Hezekiya ya tuba daga girma kan zuciyarsa, haka ma mutanen Urushalima; saboda haka fushin Ubangiji bai zo a kansu a kwanakin Hezekiya ba. Hezekiya mai arziki da girma ne ƙwarai, ya kuma yi baitulmali domin azurfa da zinariyarsa da kuma domin duwatsu masu daraja, kayan yaji, garkuwoyi da kuma domin dukan kayayyaki masu daraja nasa. Ya kuma yi gine-gine domin ajiyar hatsi, sabon ruwa inabi da mai; ya kuma yi wuraren ajiyar kowane irin shanu dabam-dabam, da kuma turke domin tumaki. Ya gina ƙauyuka ya kuma samo shanu da garkuna masu yawa, gama Allah ya ba shi arziki mai yawa sosai. Hezekiya ne ya datse ruwan bisa na maɓulɓular Gihon, ya sa ruwan ya gangara zuwa gefe yamma na Birnin Dawuda. Ya yi nasara a kome da ya yi. Amma da masu mulkin Babilon suka aika da jakadu su tambaye shi game alamar da ta faru a ƙasar, Allah ya rabu da shi don yă gwada shi don yă kuma san kome da yake cikin zuciyarsa. Sauran ayyukan mulkin Hezekiya da kuma kyawawa ayyukansa, suna a rubuce a cikin wahayin annabi Ishaya ɗan Amoz, a cikin littafin sarakunan Yahuda da Isra’ila. Hezekiya ya huta tare da kakanninsa, aka kuma binne shi a kan tudu inda makabartan zuriyar Dawuda suke. Dukan Yahuda da kuma mutanen Urushalima suka girmama shi sa’ad da ya mutu. Sai Manasse ɗansa ya gāje shi a matsayin sarki. Manasse yana da shekara ashirin sa’ad da ya zama sarki, ya kuma yi mulki a Urushalima shekara hamsin da biyar. Ya yi abin da yake mugu a gaban Ubangiji, yana bin ayyukan banƙyama na al’umman da Ubangiji ya kora a gaban Isra’ilawa. Ya sāke gina masujadan kan tudun da mahaifinsa Hezekiya ya rurrushe; ya tā da bagadan Ba’al, ya kuma gina ginshiƙan Ashera. Ya rusuna wa dukan rundunonin taurari, ya kuma yi musu sujada. Ya gina bagadai cikin haikalin Ubangiji, waɗanda Ubangiji ya ce, “Sunana zai kasance cikin Urushalima har abada.” Cikin filayen haikalin Ubangiji, ya gina bagadai ga dukan rundunonin taurari. Ya miƙa ’ya’yansa maza hadaya a wuta cikin Kwarin Ben Hinnom, ya yi bokanci, ya yi duba, ya kuma yi maitanci, ya nemi shawarar mabiya da masu ruhohi. Ya yi abin da yake mugu ƙwarai a gaban Ubangiji, yana tsokanarsa yă yi fushi. Ya ɗauki siffar da aka sassaƙa wadda ya yi, ya sa ta a cikin haikalin Allah, wanda Allah ya ce wa Dawuda da kuma ɗansa Solomon, “Cikin wannan haikali da kuma cikin Urushalima, wanda na zaɓa daga cikin kabilan Isra’ila, zan sa Sunana har abada. Ba zan ƙara bari ƙafafun Isra’ilawa su bar ƙasar da na ba wa kakanninku ba, in dai suka yi hankali ga yin kome da na umarce su game da duka dokoki, ƙa’idodi da kuma farillai da na bayar ta wurin Musa.” Amma Manasse ya sa Yahuda da mutanen Urushalima suka kauce, har suka aikata mugunta fiye da al’umman da Ubangiji ya hallaka a gaban Isra’ilawa. Ubangiji ya yi magana da Manasse da mutanensa, amma ba su kula ba. Saboda haka Ubangiji ya kawo manyan hafsoshin mayaƙan sarkin Assuriya a kansu, waɗanda suka ɗauki Manasse a matsayi ɗan kurkuku, suka sa ƙugiya a hancinsa, suka daure shi da sarƙoƙin tagulla suka kuma kai shi Babilon. Cikin wahalarsa ya nemi tagomashin Ubangiji Allahnsa ya kuma ƙasƙantar da kansa sosai a gaban Allah na kakanninsa. Da ya yi addu’a gare shi, sai Ubangiji ya taɓu da tubansa, ya kuma saurari roƙonsa; saboda haka ya dawo da shi Urushalima da kuma zuwa mulkinsa. Sa’an nan Manasse ya san cewa Ubangiji shi ne Allah. Daga baya ya sāke gina katangar waje na Birnin Dawuda, yamma da maɓulɓular Gihon a cikin kwari, har zuwa mashigin Ƙofar Kifi, ya kuma kewaye tudun Ofel; ya yi ta da tsayi sosai. Ya sa hafsoshin mayaƙa cikin dukan biranen katanga a Yahuda. Ya fid da baƙin alloli, ya kuma fid da siffofi daga haikalin Ubangiji, haka ma dukan bagadan da ya gina a kan tudun haikali da kuma cikin Urushalima, ya zubar da su a bayan birni. Sa’an nan ya gyara bagaden Ubangiji ya kuma miƙa hadayun salama da kuma hadayun godiya a bagaden, ya kuma faɗa wa Yahuda su bauta wa Ubangiji, Allah na Isra’ila. Mutane dai suka ci gaba da miƙa hadayu a masujadai kan tudu, amma wa Ubangiji Allahnsu kaɗai. Sauran ayyukan mulkin Manasse, haɗe da addu’arsa ga Allahnsa da kuma kalmomin da mai duba ya yi masa cikin sunan Ubangiji, Allah na Isra’ila, suna a rubuce cikin tarihin sarakunan Isra’ila. Addu’arsa da yadda Allah ya taɓu ta wurin tubansa, da kuma dukan zunubansa da rashin biyayyarsa, da wuraren da ya gina masujadan kan tudu ya kuma kafa ginshiƙan Ashera da gumaka kafin ya ƙasƙantar da kansa, duka suna a rubuce cikin tarihin mai duba. Manasse ya huta tare da kakanninsa, aka kuma binne shi a fadansa. Sai Amon ɗansa ya gāje shi a matsayin sarki. Amon yana da shekara ashirin da biyu sa’ad da ya zama sarki, ya yi mulki a Urushalima shekara biyu. Ya yi abin da yake mugu a gaban Ubangiji kamar yadda mahaifinsa Manasse ya yi. Amon ya bauta ya kuma miƙa hadayu ga dukan gumakan da Manasse ya yi. Amma ba kamar mahaifinsa Manasse ba, bai ƙasƙantar da kansa a gaban Ubangiji ba; Amon ya ƙara laifinsa. Fadawan Amon sukan yi masa maƙarƙashiya, suka kashe shi a fadansa. Sa’an nan mutanen ƙasar suka kashe dukan waɗanda suka yi wa Sarki Amon maƙarƙashiya, suka naɗa Yosiya ɗansa sarki a maimakonsa. Yosiya yana da shekara goma sha takwas sa’ad da ya zama sarki, ya kuma yi mulki a Urushalima shekara talatin da ɗaya. Ya yi abin da yake daidai a gaban Ubangiji ya kuma yi tafiya a hanyoyin kakansa Dawuda, ba tare da juye dama ko hagu ba. A shekara ta takwas ta mulkinsa, yayinda yake matashi, sai ya fara neman Allah na kakansa Dawuda. A shekara ta goma sha biyunsa ya fara tsabtacce Yahuda da Urushalima daga masujadan kan tudu, ginshiƙan Ashera, sassaƙaƙƙun gumaka da kuma siffofin da aka yi zubi. A ƙarƙashin umarninsa aka rurrushe bagadan Ba’al, ya kuma tumɓuke bagadan ƙona turare waɗanda suke a bisansu, ya farfashe ginshiƙan Ashera da kuma sassaƙaƙƙun siffofi. Ya ragargaza waɗannan kucu-kucu, ya barbaɗa su a kan kaburburan waɗanda suka miƙa musu hadayu. Ya ƙone ƙasusuwan firistocin gumaka a kan bagaden da a dā suke miƙa hadayunsu, ta haka ya tsabtacce Yahuda da Urushalima. Ya yi haka cikin garuruwan Manasse, Efraim da Simeyon, har zuwa Naftali, da kuma cikin kangwayen kewayensu, ya farfashe bagadai da ginshiƙan Ashera; ya niƙa gumaka suka zama gari, ya kuma yayyanka dukan bagadan turare kucu-kucu ko’ina a Isra’ila. Sa’an nan ya koma Urushalima. A shekara ta goma sha takwas ta mulkin Yosiya, ya tsarkake ƙasar da haikalin, ya aiki Shafan ɗan Azaliya da Ma’asehiya mai mulkin birni, tare da Yowa ɗan Yowahaz, marubuci, su gyara haikalin Ubangiji Allah. Suka tafi wurin Hilkiya babban firist suka ba shi kuɗin da aka kawo cikin haikalin Allah, wanda Lawiyawa masu tsaron ƙofofi sun tattara daga mutanen Manasse, Efraim da dukan raguwar Isra’ila da kuma daga dukan mutanen Yahuda da Benyamin da kuma mazaunan Urushalima. Sa’an nan suka danƙa su ga mutanen da aka naɗa su lura da aiki a kan haikalin Ubangiji. Waɗannan mutane ne suke biyan ma’aikatan da suka gyara suka kuma mai da haikalin. Suka kuma ba da kuɗi ga kafintoci da magina don su sayi sassaƙaƙƙun duwatsu, da katakai don yin tsaiko da tankar ginin da sarakunan Yahuda suka bari yă fāɗi ya zama kango. Mutanen fa suka yi aiki da aminci. Shugabanninsu, su ne Yahat da Obadiya, Lawiyawa zuriyar Merari da Zakariya da Meshullam, zuriyar Kohat. Dukan Lawiyawa waɗanda suke gwanaye a kayan kiɗi, sun lura da ma’aikata, suka kuma lura da dukan masu aiki daga aiki zuwa aiki. Waɗansu Lawiyawan su ne marubuta, magatakarda da kuma masu tsaron ƙofofi. Yayinda suke fitar da kuɗin da aka kai cikin haikalin Ubangiji, sai Hilkiya firist ya sami Littafin Dokar Ubangiji da aka bayar ta wurin Musa. Hilkiya ya ce wa Shafan magatakarda, “Na sami Littafin Doka a cikin haikalin Ubangiji.” Sai ya ba wa Shafan. Sa’an nan Shafan ya ɗauki littafin zuwa wurin sarki, ya faɗa masa, “Manyan ma’aikatanka suna yin kome da aka sa su. Mun ɗauke kuɗin da an ajiye a haikalin Ubangiji muka ba wa masu aiki da waɗanda suke lura da su.” Sa’an nan Shafan magatakarda ya sanar da sarki ya ce, “Hilkiya firist ya ba ni wani littafi.” Sai Shafan ya karanta daga cikinsa a gaban sarki. Da sarki ya ji kalmomin Doka, sai ya yage rigunansa. Ya ba da waɗannan umarnai ga Hilkiya, Ahikam ɗan Shafan, Abdon ɗan Mika, Shafan magatakarda da kuma Asahiya mai hidimar sarki. Ya ce, “Ku tafi ku nemi nufin Ubangiji saboda ni da kuma saboda raguwa a Isra’ila da Yahuda game da abin da aka rubuta a wannan littafin da aka samu. Fushin Ubangiji mai girma ne da aka zuba a kanmu domin kakanninmu ba su kiyaye maganar Ubangiji ba; ba su aikata bisa ga dukan abin da yake a rubuce a wannan littafi ba.” Hilkiya tare da waɗanda sarki ya aika, suka tafi suka yi magana da annabiya Hulda, wadda take matar Shallum ɗan Tokhat ɗan Hasra, mai tsaron wurin ajiyar riguna. Tana zama a Urushalima, a Yanki na Biyu. Sai ta ce musu, “Ga abin da Ubangiji, Allah na Isra’ila ya ce faɗa wa mutumin da ya aike ku gare ni, ‘Ga abin da Ubangiji ya ce zai kawo masifa a wannan wuri da mutanensa, dukan la’anar da aka rubuta a cikin littafin da aka karanta a gaban sarkin Yahuda. Domin sun yashe ni suka kuma ƙone turare wa waɗansu alloli, suka tsokane ni in yi fushi ta wurin dukan abin da hannuwansu suka yi, fushina zai zuba a kan wannan wuri, ba kuma za a kwantar da shi ba.’ Ku faɗa wa sarkin Yahuda, wanda ya aike ku ku nemi nufin Ubangiji, ‘Ga abin da Ubangiji, Allah na Isra’ila yake cewa game da kalmomin da ka ji. Domin zuciyarka mai tuba ce, ka kuma ƙasƙantar da kanka a gaban Allah sa’ad da ka ji abin da ya yi magana a kan wannan wuri da mutanensa, domin kuma ka ƙasƙantar da kanka a gabana, ka yage rigunanka ka kuma yi kuka a gabana, na ji ka, in ji Ubangiji. Yanzu zan tara ka da kakanninka, za a kuma binne ka cikin salama. Idanunka ba za su ga dukan masifar da zan kawo a kan wannan wuri da kuma a kan waɗanda suke zama a nan ba.’ ” Sai suka kai amsar wa sarki. Sai sarki ya kira dukan dattawan Yahuda da Urushalima. Ya haura zuwa haikalin Ubangiji tare da mutanen Yahuda, mutanen Urushalima, firistoci da Lawiyawa, dukan mutane daga ƙarami zuwa babba. Ya karanta dukan kalmomin Littafin Alkawari wanda aka samu a cikin haikalin Ubangiji a kunnuwansu. Sai sarkin ya miƙe tsaye a inda yake, ya sabunta alkawari a gaban Ubangiji, don yă bi Ubangiji yă kiyaye umarnansa, ƙa’idodinsa da kuma farillansa da dukan zuciyarsa da kuma dukan ransa, ya kuma yi biyayya da kalmomin alkawarin da aka rubuta a cikin wannan littafi. Sa’an nan ya sa kowa a Urushalima da Benyamin ya yi alkawari ga wannan; mutanen Urushalima suka aikata wannan bisa ga alkawarin Allah, Allah na kakanninsu. Yosiya ya fitar da dukan gumakan banƙyama daga dukan yankunan Isra’ilawa, ya kuma sa dukan waɗanda suke a Isra’ila su bauta wa Ubangiji Allahnsu. Muddin ransa, ba su fasa bin Ubangiji Allah na kakanninsu ba. Yosiya ya yi Bikin Ƙetarewa ga Ubangiji a Urushalima, aka kuma yanka ɗan ragon Bikin Ƙetarewa a ranar goma sha huɗu ga wata na farko. Ya zaɓi firistoci su yi aikinsu, sai ya ƙarfafa su su yi aikin da kyau a hidimar haikalin Ubangiji. Ya ce wa Lawiyawa waɗanda suke koyar da dukan Isra’ila da kuma waɗanda aka tsarkake wa Ubangiji. “Ku sa akwatin alkawari mai tsarki a cikin haikalin da Solomon ɗan Dawuda sarkin Isra’ila ya gina. Ba za a riƙa ɗaukansa a kafaɗa ba. Yanzu ku bauta wa Ubangiji Allahnku da kuma mutanensa Isra’ila. Ku shirya kanku iyali-iyali a sassanku, bisa ga umarnan da Dawuda sarkin Isra’ila da kuma ɗansa Solomon suka rubuta. “Ku tsaya a tsattsarkan wuri, bisa ga ƙungiyoyin gidajen kakannin ’yan’uwanku, waɗanda su ba firistoci ba ne. Kowanne ya sami kashi daga cikin gidan Lawiyawa. Ku yanka ragunan Bikin Ƙetarewa, ku tsarkake kanku, ku kuma shirya raguna domin ’yan’uwanku, kuna yin abin da Ubangiji ya umarta ta wurin Musa.” Yosiya ya tanada wa dukan mutanen da ba firistoci ba ne waɗanda suke a wurin, tumaki da awaki dubu talatin don a yanka saboda hadayun Bikin Ƙetarewa, ya kuma ba su shanu dubu uku. Dukan dabbobin kuwa daga garken sarki ne. Fadawansa su ma suka ba da taimako da yardar rai ga mutane da kuma firistoci da Lawiyawa. Hilkiya, Zakariya da Yehiyel masu aiki a haikalin Allah, suka ba firistoci hadayun Bikin Ƙetarewa dubu biyu da ɗari shida da kuma shanu ɗari uku. Haka kuma Konaniya tare da Shemahiya da Netanel, ɗan’uwansa, da Hashabiya, Yehiyel da Yozabad, shugabannin Lawiyawa, suka tanadar da hadayun Bikin Ƙetarewa dubu biyar da kuma bijimai ɗari biyar domin Lawiyawa. Sa’ad da aka shirya kome don Bikin Ƙetarewar, sai Firistoci tare da Lawiyawa suka tsaya wurin tsayawarsu bisa ga umarnin sarki. Aka yanka ragunan Bikin Ƙetarewa, firistoci kuma suka yayyafa jinin da aka ba su, yayinda Lawiyawa suna fiɗan dabbobi. Suka keɓe hadayun ƙonawa don su ba da su ga ƙungiyoyin iyalan mutane don su miƙa ga Ubangiji, yadda yake a rubuce a Littafin Musa. Suka yi haka da shanun. Suka gasa dabbobin Bikin Ƙetarewa a bisa wuta yadda aka tsara, suka dafa hadayu masu tsarki a tukwane, da manyan tukwane, da kuma kwanoni, suka raba su nan da nan ga dukan mutane. Bayan wannan, suka shirya wa kansu da kuma wa firistoci, saboda firistoci, zuriyar Haruna, suna miƙa hadayun ƙonawa da sashen kitse daga safe har dare. Saboda haka Lawiyawa suka shirya wa kansu da kuma wa firistocin daga zuriyar Haruna. Mawaƙa zuriyar Asaf, suna a wuraren da Dawuda, Asaf, Heman da Yedutun mai duba na sarki suka tsara. Bai zama lalle matsaran ƙofofi a kowace ƙofa su bar wuraren aikinsu ba, domin ’yan’uwansu Lawiyawa sun yi shiri dominsu. Ta haka fa aka yi dukan hidimar Ubangiji a wannan rana, domin su kiyaye Bikin Ƙetarewa, domin kuma su miƙa hadayu na ƙonawa a bisa bagaden Ubangiji, yadda sarki Yosiya ya umarta. Isra’ilawan da suka kasance a can suka yi Bikin Ƙetarewa a wannan rana, suka kuma kiyaye Bikin Burodi Marar Yisti kwana bakwai. Ba a taɓa yin Bikin Ƙetarewa haka ba tun zamanin annabi Sama’ila; kuma babu sarkin Isra’ilan da ya taɓa yin irin Bikin Ƙetarewa kamar yadda Yosiya ya yi, tare da firistoci, Lawiyawa da kuma dukan Yahuda da Isra’ila, waɗanda suke can tare da mutanen Urushalima. An yi wannan Bikin Ƙetarewa a shekara ta goma sha takwas ta mulkin Yosiya. Bayan wannan duka, sa’ad da Yosiya ya shirya haikali, Neko sarkin Masar ya haura don yă yi yaƙi a Karkemish a Yuferites, sai Yosiya ya fita don yă fafata da shi a yaƙi. Amma Neko ya aiki ’yan saƙo ga Yosiya, yana cewa, “Me ya gama ni da kai, ya Sarkin Yahuda? Ban zo in yi yaƙi da kai ba. Na zo ne in yi yaƙi da gidan da yake gāba da ni! Ka ƙyale ni! Allah ne ya riga ya faɗa mini in hanzarta. Kada ka yi gāba da Allah, wanda yake tare da ni, don kada yă hallaka ka.” Yosiya fa, bai juya daga gare shi ba, amma ya ɓad da kama don yă yi yaƙin. Bai saurari abin da Neko ya faɗa bisa ga umarnin Allah ba, amma ya tafi ya yaƙe shi a filin Megiddo. Maharba suka harbi Yosiya, sai ya ce wa hafsoshinsa, “Ku ɗauke ni ku fita da ni daga nan; gama an yi mini mummunan rauni.” Saboda haka suka ɗauke shi a keken yaƙin, suka fitar da shi, suka sa shi a wata keken yaƙin da yake da shi, suka kawo shi Urushalima, inda ya mutu. Aka binne shi a makabartar kakanninsa, sai dukan Yahuda da Urushalima suka yi makoki dominsa. Annabin Irmiya ya tsara waƙoƙin makoki domin Yosiya, wanda har wa yau mawaƙa maza da mata suke rera game da Yosiya. Suka sa waɗannan su zama al’ada a Isra’ila, suna kuma a rubuce cikin Littafin Makoki. Sauran ayyukan mulkin Yosiya da kuma kyawawan abubuwan da ya yi, bisa ga abin da aka rubuta a Dokar Ubangiji, dukan ayyukan, daga farko har zuwa ƙarshe, suna a rubuce cikin littafin sarakunan Isra’ila da na Yahuda. Sai mutanen ƙasar suka ɗauki Yehoyahaz ɗan Yosiya suka naɗa shi sarki a Urushalima yă gāji mahaifinsa. Yehoyahaz yana da shekara ashirin da uku sa’ad da ya zama sarki, ya kuma yi mulki a Urushalima wata uku. Sarkin Masar ya tumɓuke shi a Urushalima, ya tilasta Yahuda su biya haraji talenti ɗari na azurfa da kuma talentin zinariya. Sarkin Masar ya naɗa Eliyakim, ɗan’uwan Yehoyahaz, sarki a bisa Yahuda da kuma Urushalima, ya kuma canja sunan Eliyakim zuwa Yehohiyakim. Amma Neko ya ɗauki Yehoyahaz ɗan’uwan Eliyakim ya kai Masar. Yehohiyakim yana da shekara ashirin da biyar sa’ad da ya zama sarki, ya kuma yi mulki a Urushalima shekara goma sha ɗaya. Ya yi abin da yake mugu a gaban Ubangiji Allahnsa. Nebukadnezzar sarkin Babilon ya hauro ya kara da shi. Ya kama shi, ya daure da sarƙoƙin tagulla, ya kuma kai shi Babilon. Nebukadnezzar sarkin Babilon ya kuma kwaso kayayyaki daga haikalin Ubangiji ya sa su a haikalinsa a can. Sauran ayyukan mulkin Yehohiyakim, ayyukan banƙyamar da ya aikata da dukan abubuwan da aka same shi da su, suna a rubuce cikin littafin sarakunan Isra’ila da na Yahuda. Sai Yehohiyacin ɗansa ya gāje shi a matsayin sarki. Yehohiyacin yana da shekara goma sha takwas sa’ad da ya zama sarki, ya kuma yi mulki a Urushalima wata uku da kwana goma. Ya yi abin da yake mugu a gaban Ubangiji. Da bazara, Sarki Nebukadnezzar ya aika a kawo Yehohiyacin, aka kuma kawo shi Babilon, tare da kayayyaki masu daraja daga haikalin Ubangiji, sai Sarki Nebukadnezzar ya naɗa kawunsa Zedekiya, sarki a bisa Yahuda da Urushalima. Zedekiya yana da shekara ashirin da ɗaya sa’ad da ya zama sarki, ya kuma yi mulki a Urushalima shekara goma sha ɗaya. Ya yi abin da yake mugu a gaban Ubangiji Allahnsa kuma bai ƙasƙantar da kansa a gaban Irmiya annabi, wanda ya yi magana kalmar Ubangiji ba. Ya tayar wa Sarki Nebukadnezzar, wanda ya sa ya yi rantsuwa da sunan Allah. Ya zama mai kunnen ƙashi da kuma taurin zuciya, bai kuwa juye ga Ubangiji, Allah na Isra’ila ba. Bugu da ƙari, dukan shugabannin firistoci da mutane suka ƙara zama marasa aminci, suna bin dukan abubuwan banƙyama na al’ummai, suka ƙazantar da haikalin Ubangiji, wanda ya tsarkake a Urushalima. Sai Ubangiji Allah na kakanninsu, ya yi ta aika da magana gare su ta wurin ’yan saƙonsa sau da sau, domin ya ji tausayi mutanensa da mazauninsa. Amma suka yi wa ’yan saƙon Allah ba’a, suka rena maganarsa, suka yi wa annabawansa dariyar reni, har sai da fushin Ubangiji ya tasar a kan mutanensa babu makawa. Ya bashe su ga sarkin Babiloniyawa wanda ya karkashe samarinsu da takobi a wuri mai tsarki, bai yi juyayin saurayi, ko budurwa, ko tsoho, ko gajiyayye ba. Allah ya bashe su duka ga Nebukadnezzar. Nebukadnezzar ya kwashe dukan kayayyaki daga haikalin Allah, babba da ƙarami, da ma’ajin haikalin Ubangiji da kuma ma’ajin sarki da na fadawansa zuwa Babilon. Suka cinna wa haikalin Allah wuta, suka rurrushe katangar Urushalima; suka ƙone dukan fada, suka kuma lalace kome mai amfani da yake can. Waɗanda ba a kashe ba kuwa Nebukadnezzar ya kwashe su, ya kai Babilon, suka zama bayinsa da na ’ya’yansa maza har zuwa kahuwar mulkin Farisa. Ƙasar ta more hutun Asabbacinta; a dukan lokacin zamanta kango ta huta, har sai da shekaru saba’in nan suka cika bisa ga maganar Ubangiji da Irmiya ya faɗi. Don a cika maganar da Ubangiji ya yi ta wurin Irmiya, a shekara farko ta Sairus sarkin Farisa, sai Ubangiji ya motsa zuciyar Sairus na Farisa don yă yi shela a dukan masarautarsa, ya kuma sa shi a rubuce cewa, “Ga abin da Sairus sarkin Farisa ya ce, “ ‘ Ubangiji Allah na sama, ya ba ni dukan mulkokin duniya, ya kuma naɗa ni in gina masa haikali a Urushalima a Yahuda. Duk wani na mutanensa a cikinku, bari yă haura yă tafi, bari kuma Ubangiji Allahnsa yă kasance tare da shi.’ ” A shekara ta farko ta mulkin sarkin Farisa, wato, sarki Sairus, domin a cika maganar Ubangiji da aka yi ta bakin Irmiya, sai Ubangiji ya taɓa zuciyar Sairus sarkin Farisa ya yi shela a duk fāɗin ƙasarsa, ya kuma rubuta cewa, “Ga abin da Sairus sarkin Farisa yake shela, “ ‘ Ubangiji Allah na sama ya ba ni iko in yi mulkin duniya duka, ya kuma zaɓe ni in gina masa haikali a Urushalima cikin Yahuda. Duk wanda yake nasa a cikinku bari Allahnsa yă kasance tare da shi, bari yă tafi Urushalima cikin Yahuda yă gina haikalin Ubangiji, Allah na Isra’ila, Allah wanda yake a Urushalima. Duk inda akwai mutumin Yahuda da ya rage, sai mutanen da suke zama kusa da shi, su taimake shi da azurfa, da zinariya, da kaya, da kuma dabbobi, tare da kyautai na yardar rai saboda Gidan Allah wanda yake a Urushalima.’ ” Sai shugabannin zuriyar Yahuda da na Benyamin, da firistoci da Lawiyawa, duk wanda Allah ya taɓa zuciyarsa, suka shirya don su je su gina haikalin Ubangiji a Urushalima. Dukan maƙwabtansu kuwa suka taimake su da gudummawa na kayan azurfa da na zinariya, da kaya, da dabbobi, da kuma kyautai masu daraja bisa bayarwar yardar rai da suka yi. Sai sarki Sairus ya fitar da kayan da suke na haikalin Ubangiji waɗanda Nebukadnezzar ya kwashe daga Urushalima ya sa a haikalin allahnsa. Sairus sarkin Farisa ya sa Mitredat ma’aji ya ƙirga su a gaban Sheshbazzar ɗan sarkin Yahuda. Ga lissafin kayan. Manyan kwanonin zinariya guda 30 Manyan kwanonin azurfa guda 1,000 Wuƙaƙe guda 29 Waɗansu kwanonin zinariya guda 30 Waɗansu kwanonin azurfa guda 410 da waɗansu kayayyaki guda 1,000 Dukan kayayyakin zinariya da na azurfa sun kai 5,400. Sheshbazzar ya kawo kayayyakin nan duka tare da shi lokacin da kamammun suka hauro daga Babilon zuwa Urushalima. Ga lissafin waɗanda suka dawo daga bauta a Babilon, waɗanda Nebukadnezzar sarkin Babilon ya kwasa zuwa bauta a ƙasar Babilon (sun dawo Urushalima da Yahuda, kowa ya koma garinsu. Sun komo tare da Zerubbabel, da Yeshuwa, da Nehemiya, da Serahiya, da Re’elaya, da Mordekai, da Bilshan, da Misfar, da Bigwai, da Rehum, da Ba’ana). Ga jerin mazan mutanen Isra’ila. Zuriyar Farosh mutum 2,172 ta Shefatiya 372 ta Ara 775 ta Fahat-Mowab (ta wurin Yeshuwa da Yowab) 2,812 ta Elam 1,254 ta Zattu 945 ta Zakkai 760 ta Bani 642 ta Bebai 623 ta Azgad 1,222 ta Adonikam 666 ta Bigwai 2,056 ta Adin 454 ta Ater (ta wurin Hezekiya) 98 ta Bezai 323 ta Yora 112 ta Hashum 223 ta Gibbar 95. Mutanen Betlehem 123 na Netofa 56 na Anatot 128 na Azmawet 42 na Kiriyat Yeyarim, da Kefira Beyerot 743 na Rama da Geba 621 na Mikmash 122 na Betel da Ai 223 na Nebo 52 na Magbish 156 na ɗayan Elam ɗin 1,254 na Harim 320 na Lod, da Hadid da Ono 725 na Yeriko 345 na Sena’a 3,630. Firistoci. Zuriyar Yedahiya (ta wurin iyalin Yeshuwa) 973 ta Immer 1,052 ta Fashhur 1,247 ta Harim 1,017. Lawiyawa. Lawiyawa na zuriyar Yeshuwa da Kadmiyel (ta wurin Hodawiya) mutum 74. Mawaƙa. Zuriyar Asaf mutum 128. Masu tsaron haikali. Zuriyar Shallum, Ater, Talmon, Akkub, Hatita, da Shobai mutum 139. Ma’aikatan haikali. Zuriyar Ziha, Hasufa, Tabbawot, Keros, Siyaha, Fadon, Lebana, Hagaba, Akkub, Hagab, Shamlai, Hanan, Giddel, Gahar, Reyahiya, Rezin, Nekoda, Gazzam, Uzza, Faseya, Besai, Asna, Meyunawa, Nefussiyawa, Bakbuk, Hakufa, Harhur, Bazlut, Mehida, Harsha, Barkos, Sisera, Tema, Neziya da Hatifa. Zuriyar bayin Solomon. Zuriyar Sotai, Hassoferet, Feruda, Ya’ala, Darkon, Giddel, Shefatiya, Hattil, Fokeret-Hazzebayim, da Ami. Dukan zuriyar ma’aikatan haikali, da kuma bayin Solomon 392. Waɗannan mutanen ne suka zo daga garuruwan Tel-Mela, Tel-Harsha, Kerub, Addan da Immer, amma ba su iya nuna ainihin tushensu daga Isra’ila ba. ’Yan zuriyar Delahiya, Tobiya, da Nekoda 652. Daga cikin firistoci kuma, zuriyar Hobahiya, Hakkoz da Barzillai (wanda ya auri diyar Barzillai mutumin Gileyad da ake kuma kira da wannan suna). Waɗannan sun nemi sunayen iyalansu a cikin littafin da ake rubuta sunayen amma ba su ga sunayensu ba, saboda haka sai aka hana su zama firistoci domin an ɗauka su marasa tsabta ne. Gwamna ya umarce su cewa kada su ci wani abinci mai tsarki sai firist ya yi shawara ta wurin Urim da Tummim tukuna. Yawan jama’ar duka ya kai mutum 42,360, ban da bayinsu maza da mata 7,337; suna kuma da mawaƙa maza da mata 200. Suna da dawakai guda 736, alfadarai 245, raƙuma 435, da jakuna 6,720. Sa’ad da suka isa haikalin Ubangiji a Urushalima, sai waɗansu shugabannin iyalai suka yi bayarwar yardar rai ta gudummawarsu domin sāke gina gidan Allah a wurin da yake. Bisa ga ƙarfinsu suka bayar da darik 61,000 na zinariya, da maina 5,000 na azurfa, da rigunan firistoci guda 100. Firistoci, da Lawiyawa, da mawaƙa, da masu tsaron ƙofofi, da masu aiki a haikali, tare da waɗansu mutane, da dukan sauran Isra’ilawa suka zauna a garuruwansu. Da tsayawar watan bakwai, sai Isra’ilawa waɗanda suka koma garuruwansu suka taru da nufi ɗaya a Urushalima. Sai Yeshuwa ɗan Yozadak da sauran firistoci, da Zerubbabel ɗan Sheyaltiyel da abokan aikinsa, suka fara gina bagaden Allah na Isra’ila don miƙa hadaya ta ƙonawa bisa ga abin da yake a rubuce a Dokar Musa mutumin Allah. Duk da tsoron da suke ji na mutanen da suke kewaye da su, sun gina bagaden a wurinsa, suka kuma miƙa hadaya ta ƙonawa a kan bagaden ga Ubangiji safe da yamma. Bisa ga abin da yake a rubuce kuma, suka yi biki Bikin Tabanakul, suka miƙa hadayu kowace rana gwargwadon yawan hadayun da ake bukata. Bayan wannan, suka miƙa hadayu na ƙonawa yadda aka saba. Suka miƙa hadayu na Sabon Wata, da hadayu na bukukkuwan Ubangiji, da kuma hadayun da aka bayar da yardar rai ga Ubangiji. A ranar farko ta watan bakwai, sai suka fara miƙa hadaya ta ƙonawa ga Ubangiji, ko da yake ba a riga an aza harsashin ginin haikalin Ubangiji ba. Sai suka ba wa magina da kafintoci kuɗi, suka ba wa mutanen Sidon da na Taya abinci, da abin sha, da mai, don su kawo itatuwan al’ul a Yaffa daga Lebanon ta teku, yadda Sairus sarkin Farisa ya ba da umarni. A wata na biyu na shekara ta biyu, bayan sun komo gidan Allah a Urushalima, sai Zerubbabel ɗan Sheyaltiyel, Yoshuwa ɗan Yozadak da sauran ’yan’uwansa (Firistoci da Lawiyawa da duk waɗanda suka komo Urushalima daga bauta) suka fara aiki, aka zaɓi Lawiyawa daga masu shekaru ashirin da haihuwa zuwa waɗanda suka wuce haka don su dubi aikin ginin gidan Ubangiji. Yeshuwa da ’ya’yansa maza, da ’yan’uwansa, da Kadmiyel da ’ya’yan Yahuda (’yan zuriyar Hodawiya), da ’ya’yan Henadad, da ’ya’yansu da ’yan’uwansu, dukansu Lawiyawa ne, suka haɗa kai cikin duban masu aikin gidan Allah. Da masu ginin suka aza harsashin ginin haikalin Ubangiji, sai firistoci suka sa kayansu na firistoci suka riƙe ƙahonin busa, Lawiyawa (’ya’yan Asaf) kuwa suka riƙe kuge, suka yi shiri domin su rera yabo ga Ubangiji kamar yadda Dawuda Sarkin Isra’ila ya ba da umarni. Suka rera waƙar yabo da godiya ga Ubangiji, suna cewa, “Shi nagari ne; ƙaunarsa kuwa ga Isra’ila har abada ce.” Dukan jama’a kuwa suka yabi Ubangiji da murya mai ƙarfi, domin an aza harsashin ginin gidan Ubangiji. Amma tsofaffin firistoci, da Lawiyawa, da shugabannin iyalai da yawa, waɗanda dā suka ga yadda haikali na farko yake, suka fashe da kuka mai ƙarfi sa’ad da suka ga an aza harsashin ginin wannan haikali, yayinda waɗansu kuma suka yi ihu da farin ciki. Ba wanda zai iya rabe tsakanin ihun farin ciki da na kuka, domin mutanen sun tā da murya sosai har aka ji su daga nesa. Sa’ad da abokan gāban Yahuda da na Benyamin suka ji cewa waɗanda suka dawo daga bauta suna gina haikalin Ubangiji, Allah na Isra’ila sai suka zo wurin Zerubbabel da kuma wurin shugabannin iyalai, suka ce, “Bari mu taimake ku ginin domin mu ma muna addu’a ga Allahnku yadda kuke yi, muna miƙa masa hadaya tun lokacin Esar-Haddon sarkin Assuriya wanda ya kawo mu nan.” Amma Zerubbabel, Yeshuwa, da sauran shugabannin iyalai na Isra’ila suka amsa suka ce, “Ba za ku sa hannu cikin gina wa Allahnmu haikali ba, mu kaɗai za mu gina wa Ubangiji, Allah na Isra’ila gini kamar yadda Sarki Sairus, sarkin Farisa, ya umarce mu.” Sai mutanen da suke zama a wurin suka fara yin ƙoƙari su sa mutanen Yahuda su karaya, suka sa su ji tsoron ci gaba da ginin. Suka yi hayar mashawarta don su ga cewa sun ɓata ƙoƙarinsu dukan kwanakin mulkin Sairus sarkin Farisa har zuwa kwanakin mulkin Dariyus sarkin Farisa. A farkon mulkin Zerzes, sai abokan gāba suka kawo ƙarar mutanen Yahuda da na Urushalima. A zamanin Artazerzes sarkin Farisa kuma, sai Bishlam, da Mitredat, da Tabeyel, da sauran abokansu suka rubuta wasiƙa zuwa ga Artazerzes. Aka rubuta wasiƙar da harufan Arameyik, aka kuma fassara ta a yaren Arameyik. Rehum shugaban rundunar soja, da Shimshai marubuci, suka rubuta wasiƙar a kan Urushalima zuwa ga sarki Artazerzes, suka ce. Rehum shugaban sojoji, da Shimshai marubuci, da sauran abokansu, wato, alƙalai, da masu riƙe da muƙamai daga Farisa, Uruk da Babilon, mutanen Elam da na Shusha, da sauran mutane waɗanda mai girma Osnaffar ya kwaso, ya zaunar da su cikin birnin Samariya da sauran wurare na Kewayen Kogin Yuferites. (Ga abin da suka rubuta.) Zuwa ga sarki Artazerzes. Daga bayinka, mutanen Kewayen Kogin Yuferites. Ya kamata sarki ya san cewa Yahudawan da suka hauro wurinmu daga wurinka, sun je Urushalima suna sāke gina wannan mugun birni mai tawaye. Suna sāke gyara katangar, suna kuma gyara harsashin katangar. Ya kamata fa, sarki ya san cewa in aka sāke gina wannan birni duk da katangar birnin, mutanen birnin ba za su dinga biyan haraji, da kuɗin shiga, da na fitar da kaya ba, wannan zai sa aljihun masarauta yă bushe. Tun da yake muna ƙarƙashin fada, bai kyautu mu bari a rena sarki ba, Saboda haka muke sanar da sarki, domin a bincika a littattafan tarihin kakanninka. Za ka ga cewa wannan birni mai tawaye ne. Tun daga zamanin dā wannan birnin yana ba sarakuna da yankuna damuwa. Wannan ne ya sa aka ragargazar da birnin. Muna sanar da sarki cewa in har aka sāke gina wannan birnin da katangarsa, zai zama ka rasa kome a gefen Kewayen Kogin Yuferites ke nan. Sarki ya aika da wannan amsa. Zuwa ga Rehum shugaban sojoji, Shimshai marubuci da kuma sauran abokansu waɗanda suke zama a Samariya da kuma sauran wurare a Kewayen Kogin Yuferites. Gaisuwa. An karanta, an kuma fassara mini wasiƙar da kuma aika. Na ba da umarni aka kuma yi bincike, aka tarar cewa wannan birni ya daɗe yana yi wa sarakuna tawaye, an yi tashin hankali a birnin. Urushalima ta yi sarakuna masu iko sosai waɗanda suka yi mulkin Kewayen Kogin Yuferites gaba ɗaya, an kuma biya masu haraji, da kuɗin shiga da na fita na kaya. Saboda haka sai ku ba da umarni yanzu cewa mutanen su daina wannan aiki sai lokacin da na ba da umarni. Ku tabbata ka ɗauki wannan da muhimmanci. Don me za a bari wannan abu yă zama abin damuwa ga sarauta? Da gama karanta wasiƙar sarki Artazerzes wa Rehum da Shimshai marubuci, da abokansu, sai suka yi sauri suka je wurin Yahudawa a Urushalima, suka hana su aikin ƙarfi da yaji. Saboda haka aikin a gidan Allah a Urushalima ya tsaya cik sai a shekara ta biyu ta mulkin Dariyus sarkin Farisa. Sai annabi Haggai, da annabi Zakariya zuriyar Iddo, suka yi wa Yahudawa a Yahuda da Urushalima annabci a cikin sunan Allah na Isra’ila wanda yake da mulki a kansu. Sa’an nan Zerubbabel ɗan Sheyaltiyel da Yeshuwa ɗan Yozadak suka yi shiri suka kama aikin sāke gina gidan Allah a Urushalima. Annabawan Allah kuwa suna tare da su, suna taimakonsu. A wannan lokaci, Tattenai gwamnan Kewayen Kogin Yuferites, da Shetar-Bozenai da abokansu suka je wurinsu suka tambaye su cewa, “Wa ya ba ku iko ku sāke gina wannan haikali har ku gyara katangar?” Suka kuma tambaye su “Ina sunayen waɗanda suke wannan gini?” Amma Allah yana tsaron dattawan Yahudawa, saboda haka ba a hana su aikin ba har sai rahoto ya kai wurin Dariyus aka kuma sami amsarsa a rubuce tukuna. Ga wasiƙar da Tattenai, gwamnan Kewayen Kogin Yuferites, da Shetar-Bozenai da abokansu masu riƙe da muƙamai a Kewayen Kogin Yuferites suka aika wa Sarki Dariyus. Ga rahoton da suka aika masa. Zuwa ga Sarki Dariyus. Gaisuwa da fatan alheri. Ya kamata sarki yă sani cewa mun je yankin Yahuda, zuwa gidan Allah mai girma. Muka ga mutanen suna ginin haikalin da manyan duwatsu, suna sa katakai a bangon. Ana aikin da ƙwazo, aikin kuma yana cin gaba sosai, suna kuma lura da shi. Mun tambayi dattawan muka ce musu, “Wa ya ba ku iko ku sāke gina wannan haikali, ku kuma sāke gyara katangarsa?” Muka kuma tambaye su sunayensu don mu rubuta mu sanar da kai waɗanda suke shugabanninsu. Wannan ita ce amsar da suka ba mu. “Mu bayin Allah na sama da ƙasa ne, muna sāke gina haikalin da aka gina tun shekaru da yawa da suka wuce, da wani babban sarkin Isra’ila ya gina ya kuma gama. Amma domin kakanninmu sun ɓata wa Allah na sama rai, sai ya bari suka fāɗa cikin hannun Nebukadnezzar mutumin Kaldiya, sarkin Babilon, wanda ya rushe wannan haikali, ya kuma kwashe mutane zuwa Babilon. “Duk da haka, a shekara ta farko ta mulkin Sairus sarkin Babilon, Sarki Sairus ya ba da umarni cewa a sāke gina wannan gidan Allah. Ya kuma kwashe kwanonin zinariya da azurfa na gidan Allah daga haikalin Babilon waɗanda Nebukadnezzar ya kwasa daga haikali a Urushalima. Sa’an nan sarki Sairus ya ba wa wani mutum mai suna Sheshbazzar umarni wanda ya sa ya zama gwamna, ya ce masa, ‘Ka kwashe kayan nan ka je ka zuba su a cikin haikalin Allah a Urushalima. Ka kuma sāke gina gidan Allah a wurin da yake a dā.’ “Saboda haka Sheshbazzar ya so ya aza harsashin gina gidan Allah a Urushalima. Tun daga wancan lokaci har zuwa yau ana kan gina shi amma ba a gama ba.” Yanzu in sarki yana so, bari a duba cikin littattafan tarihi na sarakuna na Babilon a gani ko lalle sarki Sairus ya ba da umarni a sāke gina gidan Allah a Urushalima. Bari sarki yă aiko mana da abin da ya gani game da wannan abu. Sarki Dariyus kuwa ya ba da umarni a bincika a duba cikin littattafan tarihin da suke a ajiye a wurin ajiyarsu a Babilon. Sai aka sami takarda a Ekbatana a yankin Mediya, ga kuma abin da yake rubuce a ciki. Abin tunawa. A shekara ta farko ta mulkin sarki Sairus, sarki ya ba da umarni game da haikalin Allah a Urushalima, ya ce, Bari a sāke gina haikalin yă zama wurin miƙa hadayu, a kuma aza harsashin ginin haikalin. Tsayinsa zai zama ƙafa tasa’in, fāɗinsa kuma kamu tasa’in. Za a jera manyan duwatsu jeri uku, da jeri ɗaya na katako. Daga asusun sarki kuma za a biya kuɗin aikin. Kwanonin zinariya da na azurfan gidan Allah waɗanda Nebukadnezzar ya kwashe daga haikali a Urushalima ya kawo Babilon, a mayar da su wurinsu a haikali a Urushalima; a sa su cikin gidan Allah. Saboda haka Tattenai, gwamnan Kewayen Kogin Yuferites, da Shetar-Bozenai, da ku masu muƙami na yankin, ku bar wurin. Kada ku hana wannan aiki na haikalin Allah. Bari gwamnan Yahudawa, da dattawan Yahudawa su sāke gina wannan gidan Allah a wurin da yake a dā. Na kuma ba da umarni game da abin da za ku yi wa dattawan Yahudawa cikin aikin ginin wannan gidan Allah. Daga asusun sarki a kuɗin da yake shigo wa Kewayen Kogin Yuferites za a biya mutanen nan duka, domin kada aikin yă tsaya. A tanada musu duk abin da suke bukata. A ba su ’yan bijimai, da raguna, da ’yan tumaki domin miƙa hadaya ta ƙonawa ga Allah na sama, haka kuma dole a tanada wa firistoci alkama, da gishiri, da ruwan inabi, da mai, kullum ba fasawa yadda firistoci suke yi a Urushalima domin su miƙa hadayu masu daɗi ga Allah na Sama, su kuma yi addu’a domin lafiyar sarki da ’ya’yansa. Na kuma yi umarni cewa duk wanda ya karya wannan doka sai a fitar da itace daga cikin gidansa, a fiƙe kan itacen, a tsire mutumin, sa’an nan a mai da gidansa juji. Bari Allah yă sa sunansa yă kasance, yă hamɓarar da duka wani sarki ko mutanen da za su sa hannu don a sāke wannan doka, ko kuma don su rushe haikalin nan a Urushalima. Ni Dariyus na ba da wannan umarni, bari a yi biyayya babu wasa. Saboda umarnin da sarki Dariyus ya aika, sai Tattenai, gwamnan Kewayen Kogin Yuferites da Shetar-Bozenai da abokansu suka yi biyayya da umarnin babu wasa. Dattawan Yahuda kuwa suka ci gaba da ginin suna yin nasara ta wurin wa’azin Haggai annabi da Zakariya ɗan Iddo. Suka kuma gama ginin haikalin bisa ga umarnin Allah na Isra’ila da kuma umarnin Sairus da Artazerzes, sarakunan Farisa. An gama ginin haikalin a rana ta uku na watan Adar a shekara ta shida ta mulkin Sarki Dariyus. Sai mutanen Isra’ila, firistoci, Lawiyawa da kuma sauran waɗanda suka dawo daga bauta suka yi bikin keɓe gidan Allah, cike da farin ciki. Suka miƙa bijimai guda ɗari, da raguna ɗari biyu, da ’yan raguna ɗari huɗu. Suka kuma miƙa hadayu don zunubi saboda dukan Isra’ila, suka kuma miƙa bunsurai guda goma sha biyu don hadaya ta zunubi, kowane bunsuru ɗaya don kowace kabila ta Isra’ila. Suka kuma naɗa firistoci a gundumominsu da kuma Lawiyawa a ƙungiyoyinsu don hidimar Allah a Urushalima, bisa ga abin da aka rubuta a Littafin Musa. A rana ta goma sha huɗu ga watan farko, sai waɗanda suka dawo daga bauta suka yi Bikin Ƙetarewa. Firistoci da Lawiyawa suka tsarkake kansu, suka zama da tsabta. Lawiyawa suka yanka ragon Bikin Ƙetarewa domin dukan waɗanda suka dawo daga bauta, da kuma domin ’yan’uwansu firistoci, da kuma domin kansu. Sai Isra’ilawa waɗanda suka dawo daga bauta suka ci tare da duk waɗanda suka keɓe kansu daga halin ƙazanta na Al’ummai maƙwabtansu, don su nemi Ubangiji, Allah na Isra’ila. Suka yi kwana bakwai suna Bikin Burodi Marar Yisti, suna cike da farin ciki, gama Ubangiji ya cika su da farin ciki don ya sa sarkin Assuriya ya canja tunaninsa, ya taimake su cikin aikin gidan Allah, Allah na Isra’ila. Bayan waɗannan abubuwa, a zamanin Artazerzes sarkin Farisa, sai Ezra ɗan Serahiya, ɗan Azariya, ɗan Hilkiya, ɗan Shallum, ɗan Zadok, ɗan Ahitub, ɗan Amariya, ɗan Azariya, ɗan Merahiyot, ɗan Zerahiya, ɗan Uzzi, ɗan Bukki, ɗan Abishuwa, ɗan Finehas, ɗan Eleyazar, ɗan Haruna babban firist. Shi Ezra ɗin ya zo daga Babilon. Shi malami ne ya kuma san Dokar Musa sosai wadda Ubangiji, Allah na Isra’ila ya bayar. Sarki ya ba shi duk abin da ya roƙa, gama Ubangiji Allahnsa yana tare da shi. Waɗansu Isra’ilawa, haɗe da firistoci, da Lawiyawa, da mawaƙa, da masu tsaron ƙofofi, da masu aiki a haikali su ma suka zo Urushalima a shekara ta bakwai a zamanin mulkin sarki Artazerzes. Ezra ya iso Urushalima a wata na biyar na shekara ta bakwai na kama mulkin sarkin. Ya fara tafiyarsa daga Babilon a rana ta farko ga watan farko, ya kuma iso Urushalima a rana ta farko ga watan biyar, gama alherin Allahnsa yana tare da shi. Gama Ezra ya miƙa kansa ga bincike da kuma kiyaye Dokar Ubangiji, da kuma koya wa Isra’ilawa dokoki da kuma umarnan Ubangiji. Ga wasiƙar da sarki Artazerzes ya ba Ezra wanda yake firist da kuma malami, mutumin da yake cike da sani game da dokoki da kuma umarnan Ubangiji wa Isra’ila. Artazerzes, sarkin sarakuna. Zuwa ga Ezra firist, malamin Dokar Allah na sama. Gaisuwa. Yanzu ina ba da umarni cewa duk wani mutumin Isra’ilan da yake cikin mulkina, haɗe da firistoci, da Lawiyawa, da suke so su tafi tare da kai zuwa Urushalima za su iya tafiya. Sarki ne da mashawartansa guda bakwai suka aike ka don ka je ka ga halin da Yahuda da Urushalima suke ciki game da dokokin Allahnka, waɗanda suke a hannunka. Za ka kuma tafi da zinariya da azurfa waɗanda sarki da mashawartansa suka ba da kyautar yardar rai ga Allah na Isra’ila, wanda haikalinsa ke a Urushalima, haɗe da duk zinariya da azurfan da za ka iya samu a Babilon, da kuma duk bayarwar yardar rai daga mutane da firistoci, domin haikalin Allahnsu da yake a Urushalima. Ka tabbata ka yi amfani da kuɗin nan don ka sayi bijimai, da raguna, da ’yan raguna, da hadayu na gari, da na sha, ka kuma miƙa su a kan bagade na haikalin Allahnka a Urushalima. Sa’an nan kai da ’yan’uwanka Yahudawa ku yi abin da kuka ga ya fi kyau da sauran zinariya da azurfa ɗin bisa ga nufin Allah. Ka kai wa Allah na Urushalima duk kayan da aka ba ka amanarsu don yin sujada a haikalin Allahnka. Duk kuma wani abin da ake bukata domin haikalin Allahnka, daga ɗakunan ajiya sarki za ka fitar da kuɗin. Yanzu fa ni, Sarki Artazerzes, ina ba da umarni ga kowane ma’aji na Kewayen Kogin Yuferites su tanada duk abin da Ezra firist, wanda kuma yake malamin Dokar Allah na sama zai bukaci, har zuwa talenti ɗari na azurfa, da mudu ɗari na alkama, da garwa ɗari na ruwan inabi, da garwa ɗari na man zaitun, da kuma gishiri ba iyaka. A yi duk abin da Allah na sama ya ce don haikalin Allah na sama, sai a yi shi da himma. Me zai sa a jawo wa sarki da ’ya’yansa fushin Allah? Ku kuma san cewa, ba ku da ikon sa firistoci, da Lawiyawa, da mawaƙa, da masu tsaron ƙofofin haikali, da masu aiki a gidan Allah, ko waɗansu masu aiki a haikali su biya haraji, ko kuɗin shiga. Kai kuma Ezra, bisa ga hikimar da Allah ya ba ka, sai ka zaɓi mahukunta da alƙalai waɗanda za su zama masu yanke hukunci ga dukan mutanen Kewayen Kogin Yuferites, duk waɗanda suka san dokokin Allahnka, ka kuma koya wa duk waɗanda ba su san dokokin ba. Ba shakka duk wanda bai yi biyayya da dokokin Allahnka ba, da kuma dokokin sarki ba dole a yanke masa hukuncin kisa, ko hukuncin kora, ko hukuncin raba shi da mallakarsa, ko kuma hukuncin kulle shi a kurkuku. Yabo ya tabbata ga Ubangiji Allah na kakanninmu, ya taɓa zuciyar sarki don yă kawo ɗaukaka ga haikalin Allah a Urushalima ta wannan hanya. Wanda kuma ya sa na sami tagomashi a gaban sarki da mashawartansa, da kuma duk manyan masu muƙami nasa. Gama Ubangiji Allahna yana tare da ni, sai na sami ƙarfin hali na tattara shugabannin mutane daga Isra’ila, don mu tafi tare. Waɗannan su ne shugabannin iyalai, da kuma waɗanda suka dawo tare da ni daga Babilon a zamanin mulkin Sarki Artazerzes. Daga zuriyar Finehas, Gershom ne shugaba; daga zuriyar Itamar, Daniyel ne shugaba; daga zuriyar Dawuda, Hattush ɗan zuriyar Shekaniya ne shugaba, daga zuriyar Farosh, Zakariya ne shugaba, tare da shi akwai mutum 150; daga Fahat-Mowab, Eliyehoyenai ɗan Zerahiya ne shugaba, tare da shi akwai mutum 200; daga zuriyar Zattu, Shekaniya ɗan Yahaziyel ne shugaba, tare da shi akwai mutum 300; daga zuriyar Adin, Ebed ɗan Yonatan ne shugaba, tare da shi akwai mutum 50; daga zuriyar Elam, Yeshahiya ɗan Ataliya ne shugaba, tare da shi akwai mutum 70; daga zuriyar Shefatiya, Zebadiya ɗan Mika’ilu ne shugaba, tare da shi akwai mutum 80; daga iyalin Yowab, Obadiya ɗan Yehiyel ne shugaba, tare da shi akwai mutum 218; daga Bani, Shelomit ɗan Yosifiya ne shugaba, tare da shi akwai mutum 160; daga Bebai, Zakariya ɗan Bebai ne shugaba, tare da shi akwai mutum 28; daga iyalin Azgad, Yohanan ɗan Hakkatan ne shugaba, tare da shi akwai mutum 110; zuriya ta Adonikam ne suka zo daga ƙarshe, sunayensu kuwa su ne Elifelet, Yehiyel da Shemahiya, tare da su akwai mutum 60; daga zuriyar Bigwai, Uttai da Zakkur ne shugabanni, tare da su akwai mutum 70. Na kuma tattara su a bakin rafi wanda yake gangarawa zuwa Ahawa, muka kafa sansani a can kwana uku. Da na bincika cikin mutane da firistoci, sai na tarar babu Lawiyawa. Saboda haka sai na aika a kira Eliyezer, da Ariyel, da Shemahiya, da Elnatan, da Yarib, da Natan, da Zakariya, da Meshullam waɗanda su ne shugabanni. Na kuma sa a kira Yohiyarib da Elnatan waɗanda masana ne. Na sa su je wurin Iddo wanda yake shugaba a Kasifiya. Aka gaya musu abin da za su gaya wa Iddo da ’yan’uwansa masu aiki a haikali a Kasifiya don su aiko mana waɗanda za su yi mana hidima a haikalin Allahnmu. Da yake Allah yana tare da mu, sai suka aiko mana da Sherebiya, wanda ya iya aiki, shi daga zuriyar Mali ɗan Lawi ne, ɗan Isra’ila. Sai ya zo tare da ’ya’yansa da kuma ’yan’uwansa. Dukansu dai mutum 18 ne. Suka kuma aika da Hashabiya tare da Yeshahiya daga zuriyar Merari, da ’yan’uwansu da kuma ’ya’yansu, su kuma mutum 20 ne. Sun kuma kawo masu aiki a haikali mutum 220, ƙungiyar da Dawuda da abokan aikinsa suka keɓe don su taimaki Lawiyawa aiki. Duk aka rubuta waɗannan da sunayensu. A can, a bakin rafin Ahawa, na sa mu yi azumi, domin mu ƙasƙantar da kanmu a gaban Allah, mu kuma roƙe shi yă kiyaye mana hanya, da mu da ’ya’yanmu da kayanmu duka. Na ji kunya in roƙi sarki yă haɗa mu da sojoji da masu dawakai don su yi mana rakiya su kāre mu daga magabta a kan hanya, gama mun ce wa sarki, “Alherin Allah yana tare da duk wanda yake dogara gare shi, amma kuma fushinsa yana kan duk wanda ya juya masa baya.” Saboda haka sai muka yi azumi, muka kai roƙonmu a wurin Allah, ya kuwa amsa mana. Sai na keɓe manyan firistoci guda goma sha biyu tare da Sherebiya, Hashabiya da kuma ’yan’uwansu guda goma. Na auna musu zinariya da azurfa, da kwanoni waɗanda sarki da mashawartansa, da sauran abokan aikinsa, da Isra’ilawan da suke can suka bayar domin haikalin Allahnmu. Na auna musu talenti 650 na azurfa, talenti ɗari na kwanonin azurfa, talenti 100 na zinariya, kwanonin zinariya guda 20 da darajarsu ya kai darik 1,000, da kwanoni biyu na gogaggen tagulla, wanda yake darajarsa daidai da zinariya. Na ce masa, “Ku da kayan nan tsarkaka ne ga Ubangiji. Azurfa da zinariya ɗin, bayarwa ce ta yardar rai ga Ubangiji, Allah na kakanninku. Ku lura da su da kyau har sai kun isa Urushalima. Ku auna su a shirayin haikalin Ubangiji a Urushalima, a gaban manyan firistoci, da Lawiyawa, da shugabannin iyalai na Isra’ila.” Sa’an nan sai firistoci, da Lawiyawa suka karɓi azurfa da zinariya da kuma tsarkakan kwanonin da aka auna don a kai haikalin Allahnmu a Urushalima. A rana ta goma sha biyu ga watan farko, muka tashi daga bakin rafin Ahawa don mu tafi Urushalima. Alherin Allahnmu yana tare da mu, ya kuma kāre mu daga magabta da ’yan fashi. Muka iso Urushalima, inda muka huta kwana uku. A rana ta huɗu muka tafi haikalin Allah, muka auna azurfa, da zinariya, da tsarkakan kwanonin, muka ba Meremot ɗan Uriya firist, da Eleyazar ɗan Finehas yana tare da shi, da kuma Lawiyawan nan, wato, Yozabad ɗan Yeshuwa, da Nowadiya ɗan Binnuyi. Aka yi lissafi aka auna kome aka tarar yana nan daidai, aka kuma rubuta yawan nauyin a lokacin. Sa’an nan sai waɗanda suka dawo daga bauta suka miƙa hadaya ta ƙonawa ga Allah na Isra’ila. Wato, bijimai guda goma sha biyu don Isra’ilawa duka, raguna tasa’in da shida, ’yan raguna saba’in da bakwai, bunsurai kuma guda goma sha biyu. Aka miƙa su hadaya don zunubi. Wannan duka hadaya ta ƙonawa ce ga Ubangiji. Suka kuma kai saƙon sarki zuwa ga wakilansa, da kuma gwamnoni na Kewayen Kogin Yuferites waɗanda suka taimaki mutane da kuma gidan Allah. Bayan an yi waɗannan abubuwa duka, sai shugabanni suka zo wurina suka ce, “Mutanen Isra’ila, har da firistoci da Lawiyawa ba su keɓe kansu daga maƙwabtansu ba, ba su kuma keɓe kansu daga irin rayuwar ƙazantar mutanen ƙasar ba, wato, rayuwar irinta Kan’aniyawa, da Hittiyawa, da Ferizziyawa, da Yebusiyawa, da Ammonawa, da Mowabawa, da Masarawa da Amoriyawa. Sun auro wa kansu da ’ya’yansu ’yan mata mutanen nan, ta haka aka kwaɓa zuriyar da aka tsarkake da ta mutanen nan da suke tare da su. Shugabanni da manyan ma’aikata su ne a gaba-gaba a aikata wannan abin kunya.” Sa’ad da na ji wannan, sai na yaga rigata da alkyabbata, na tsittsige gashin kaina da na gemuna, na zauna, na rasa abin da yake mini daɗi. Sai duk waɗanda suke tsoron maganar Allah na Isra’ila suka kewaye ni don su ji wannan rashin imani wanda waɗanda suka dawo bauta suka yi. Na kuwa zauna a can a rikice, har lokacin miƙa hadaya na yamma. Sa’an nan a lokacin miƙa hadaya na yamma, na tashi da ɓacin raina, da yagaggun kayana, na durƙusa na miƙa hannuwana sama ga Ubangiji Allahna na kuma yi addu’a, na ce, “Ya Allah, ina cike da kunya, ba zan iya ɗaga fuskata gare ka ba, ya Allahna, domin zunubanmu sun fi mu tsayi, tudunsu har ya kai sama. Tun daga zamanin kakanninmu har zuwa yanzu, zunubanmu suna da yawa. Domin zunubanmu, mu da sarakunanmu, da firistocinmu aka kama mu, aka wulaƙanta mu, muka zama bayi a hannun sarakuna waɗansu ƙasashe. “Amma a yanzu a wannan ɗan lokaci Ubangiji Allahnmu ya yi mana jinƙai, ya bar mana saura, ya kuma ba mu wuri a wurinsa mai tsarki, ya kuma ba mu ganin haske, ya ɗan rage mana nauyin bauta. Ko da yake mu bayi ne, Allahnmu bai yashe mu cikin daurin talala da muke ciki ba, ya sa sarakunan Farisa suka yi mana kirki. Ya ba mu sabuwar dama don mu sāke gina haikalin Allahnmu, mu kuma gyara katangar, ya kuma ba mu kāriya a Yahuda da Urushalima. “Amma yanzu, ya Allahnmu, me za mu ce game da wannan? Gama mun ƙi bin dokokin da ka bayar ta wurin annabawa lokacin da ka ce, ‘Ƙasar da za ku mallaka, ƙasa ce marar tsarki, mutanenta sun ɓata ta da ƙazamin hali, ƙazamin halinsu ya ɓata ko’ina. Saboda haka kada ku aurar musu da ’yan matanku, kada kuma ku auro wa ’ya’yanku maza ’yan matansu. Kada ku yi wata yarjejjeniya ta abokantaka da su. Idan kun yi biyayya za ku yi ƙarfi, ku kuma ci albarkar ƙasar, har ku bar wa ’ya’yanku gādo na har abada.’ “Abubuwan nan sun faru da mu sakamakon mugayen ayyukanmu ne, amma duk da haka ya Allahnmu, ba ka ba mu horo bisa ga yawan zunubanmu ba, ka kuma bar mana saura. Za mu sāke ƙin yin biyayya da umarninka mu yi auratayya da mutanen nan da suke aikata waɗannan abubuwan banƙyama? Ba za ka yi fushi da mu, ka ƙone mu da fushinka har babu ɗan saura ba? Ya Ubangiji Allah na Isra’ila, kai mai adalci ne! Yau an bar mu da sauran da ya tsira. Ga mu nan a gabanka masu zunubi, gama ba wanda zai iya tsayawa a gabanka.” Yayinda Ezra yake addu’a, yake kuma furta laifi, yana kuka, yana a durƙushe da kansa ƙasa a gaban gidan Allah, sai babban taron jama’ar Isra’ilawa, maza, mata da yara, suka taru a wurinsa. Su ma suka yi kuka mai zafi. Sai Shekaniya ɗan Yehiyel, daga zuriyar Elam ya ce wa Ezra, “Mun yi wa Allah rashin aminci ta wurin yin auratayya da maƙwabtanmu, amma duk da haka bai yashe mutanen Isra’ila ba. Yanzu bari mu yi alkawari da Allahnmu, mu kori matan da yaransu bisa ga abin da ranka yă daɗe da sauran shugabannin da kuke girmama umarnin Allah kuka shawarce mu, bari mu yi haka bisa ga doka. Sai ka tashi, gama wannan hakkinka ne, za mu ba ka goyon baya. Saboda haka ka yi ƙarfin hali ka aikata shi.” Sai Ezra ya tashi ya sa firistoci da suke shugabanni, da Lawiyawa, da dukan mutanen Isra’ila su rantse, cewa za su yi abin da aka ce. Sai suka yi rantsuwar. Sa’an nan Ezra ya tashi daga gidan Allah ya tafi gidan Yehohanan ɗan Eliyashib, a can ma bai ci wani abu ba, bai sha ruwa ba domin ya ci gaba da yin baƙin cikin rashin aminci na waɗanda suka dawo daga bauta. Aka yi shela a duk fāɗin Yahuda da Urushalima cewa dukan waɗanda suka dawo daga bauta su tattaru a Urushalima. Duk wanda bai zo a cikin kwana uku ba, za a washe shi, a kuma ware shi daga jama’ar da suka dawo daga bauta. Haka shugabanni da dattawa suka zartar. A cikin kwana uku duk mutanen Yahuda da na Benyamin suka taru a Urushalima. A ranar ashirin ga watan tara, dukan mutanen suka zauna a dandali a gaban gidan Allah cike da ɓacin rai saboda abin da ya faru da kuma ruwan da aka yi. Sai Ezra firist ya miƙe tsaye ya yi musu magana ya ce, “Kun yi rashin aminci; kun aure mata baƙi, ta haka kuka ƙara kan zunubin Isra’ila. Yanzu sai ku furta zunubanku ga Ubangiji, Allahn kakanninku, ku kuma yi nufinsa. Ku raba kanku da mutanen da suke kewaye da ku, ku kuma rabu da baƙin mata.” Mutanen kuwa suka tā da murya da ƙarfi suka ce, “Gaskiya ka faɗa, dole mu yi yadda ka ce, Amma akwai mutane da yawa, kuma lokacin damina ne; saboda haka ba za mu iya tsayawa a waje ba. Ban da haka ma, aikin nan ba na kwana ɗaya ko biyu ba ne, domin ba ƙaramin laifi muka yi ba. Bari shugabanninmu su yi wani abu a madadin mutane duka, sa’an nan sai duk wanda ya san ya auri baƙuwar mace a garuruwanmu, sai yă zo nan a lokacin da aka shirya tare da dattawa da alƙalan kowane gari, har sai Allah ya huce fushinsa mai zafi da yake kanmu.” Yonatan ɗan Asahel, da Yazehiya ɗan Tikba su ne kaɗai ba su yarda da wannan shirin ba, sai Meshullam da Shabbetai Balawe kuma suka goyi bayansu. Sai waɗanda suka dawo daga bauta suka yi yadda aka zartar. Ezra firist ya zaɓi mutane waɗanda su ne shugabannin iyalai, ɗaya daga kowane sashe, aka rubuta sunan kowannensu. A ranar ɗaya ga watan goma kuwa suka zauna don su yi binciken waɗannan abubuwa. A rana ta farko ga watan farko, suka gama da bincike duk waɗanda suka auri baƙin mata. A cikin zuriyar firistoci, ga waɗanda suka auri mata baƙi. Daga zuriyar Yeshuwa ɗan Yozadak da ’yan’uwansa, akwai Ma’asehiya, da Eliyezer, da Yarib, da Gedaliya. (Su ne suka miƙa hannuwansu suka nuna sun yarda su kori matansu baƙi, kowannensu kuma ya ba da rago daga cikin garkensa don a miƙa hadaya don zunubi.) Daga zuriyar Immer, akwai Hanani da Zebadiya. Daga zuriyar Harim, akwai Ma’asehiya, Iliya, Shemahiya, Yehiyel da Uzziya. Daga zuriyar Fashhur, akwai Eliyohenai, Ma’asehiya, Ishmayel, Netanel, Yozabad da Eleyasa. Cikin Lawiyawa, akwai Yozabad, Shimeyi, Kelaya (wato, Kelita), Fetahahiya, Yahuda, Eliyezer. Daga mawaƙa, akwai Eliyashib. Daga masu tsaron ƙofofin haikali, akwai Shallum, Telem da Uri. Ga sunayen sauran mutanen Isra’ilan da suke da wannan laifi. Daga zuriyar Farosh, akwai Ramiya, da Izziya, Malkiya, Miyamin, Eleyazar, Malkiya da Benahiya. Daga zuriyar Elam, akwai Mattaniya, Zakariya, Yehiyel, Abdi, Yeremot, da Iliya. Daga iyalin Zattu, akwai Eliyohenai, Eliyashib, Mattaniya Yeremot da Zabad da Aziza. Daga zuriyar Bebai, akwai Yehohanan, Hananiya, Zabbai, da Atlai. Daga zuriyar Bani, akwai Meshullam, Malluk, Adahiya, Yashub, Sheyal, da Ramot. Daga zuriyar Fahat-Mowab, akwai Adna, Kelal, Benahiya, Ma’asehiya, Mattaniya, Bezalel, Binnuyi, da Manasse. Daga zuriyar Harim, akwai Eliyezer, Isshiya, Malkiya, Shemahiya, Simeyon, Benyamin, Malluk da Shemariya. Daga zuriyar Hashum, akwai Mattenai, da Mattatta, Zabad, Elifelet, Irmai, Manasse, da Shimeyi. Daga zuriyar Bani, akwai Ma’adai, Amram, Yuwel, Benahiya, Bedeya, Keluhi, Baniya, Meremot, Eliyashib, Mattaniya, Mattenai da Ya’asu. Daga zuriyar Binnuyi, akwai Shimeyi, Shelemiya, Natan, Adahiya, Maknadebai, Shashai, Sharai, Azarel, Shelemiya, da Shemariya, Shallum da Amariya da Yusuf. Daga zuriyar Nebo, akwai Yehiyel, Mattitiya, Zabad, Zebina, Yaddai, Yowel da Benahiya. Dukan waɗannan sun auri baƙin mata, waɗansunsu suna da ’ya’ya. Kalmomin Nehemiya ɗan Hakaliya. A cikin watan Kisleb a shekara ta ashirin, yayinda nake a fadar Shusha. Hanani, ɗaya daga cikin ’yan’uwana, ya zo daga Yahuda tare da waɗansu mutane. Na kuwa tambaye shi game da raguwar Yahudawan da suka tsira daga kwasan zuwa zaman bauta, da kuma game da Urushalima. Suka ce mini, “Waɗanda suka tsira daga kwasan zuwa zaman bauta da kuma suka komo cikin yankin suna cikin babban damuwa da wulaƙanci. An rushe katangar Urushalima aka kuma ƙone ƙofofin da wuta.” Da na ji waɗannan abubuwa, sai na zauna na yi kuka. Na yi kwanaki ina makoki da azumi, na kuma yi addu’a a gaban Allah na sama. Na ce, “Ya Ubangiji Allah na sama, Allah mai girma da mai banrazana, wanda yake kiyaye alkawarinsa na ƙauna da waɗanda suke ƙaunarsa, suke kuma yin biyayya da umarnansa, ka sa kunne ka kuma buɗe idanunka ka ji addu’ar da bawanka yake yi a gabanka dare da rana saboda bayinka, mutanen Isra’ila. Na furta zunuban da mu Isra’ilawa, har da ni da kuma gidan mahaifina muka yi maka. Mun yi mugunta gare ka. Ba mu yi biyayya da umarnai, ƙa’idodi da kuma dokokin da ka ba wa bawanka Musa ba. “Ka tuna da umarnan da ka ba wa bawanka Musa, kana cewa, ‘In kun yi rashin aminci, zan warwatsar da ku a cikin al’ummai, amma in kuka dawo gare ni kuka kuma yi biyayya da umarnaina, to, ko mutanenku da aka kwasa zuwa zaman bauta suna can wuri mafi nisa, zan tattara su daga can in kawo su wurin da na zaɓa yă zama wurin zama don Sunana.’ “Su bayinka ne da kuma mutanenka da ka fansa ta wurin ƙarfinka mai girma da kuma hannunka mai iko. Ya Ubangiji, ka kasa kunne ga addu’ar wannan bawanka da kuma ga addu’ar bayinka waɗanda suke farin cikin girmama sunanka. Ka ba wa bawanka nasara a yau ta wurinsa yă sami tagomashi a gaban wannan mutum.” Ni ne mai riƙon kwaf sarki. A watan Nisan a shekara ta ashirin ta mulkin Sarki Artazerzes, sa’ad aka kawo masa ruwan inabi, sai na karɓa na ba shi. Ban taɓa ɓata fuskata a gabansa ba, sai wannan karo. Saboda haka sarki ya tambaye ni ya ce, “Me ya sa fuskarka ta ɓaci, ga shi, ba ciwo kake ba? Ba abin da ya kawo wannan, in ba dai kana baƙin ciki ba.” Sai na ji tsoro ƙwarai, na amsa na ce wa sarki, “Ran sarki yă daɗe! Me zai hana fuskata ta ɓaci, sa’ad da birnin da aka binne kakannina tana zaman kango, aka kuma rushe ƙofofinsa da wuta?” Sai sarki ya ce mini, “Me kake so?” Sai na yi addu’a ga Allah na sama, na kuwa ba wa sarki amsa, na ce, “In ya gamshi sarki, in kuma bawanka ya sami tagomashi a idonka, bari ka aike ni in tafi ƙasar Yahuda, birnin da aka binne kakannina, domin in sāke gina shi.” Sai sarki, a lokacin sarauniya da tana zama kusa da shi, ya tambaye ni, ya ce, “Kwana nawa tafiyar za tă ɗauke ka, kuma yaushe za ka dawo?” Ya gamshi sarki ya aike ni; saboda haka na shirya lokaci. Na kuma ce masa, “In ya gamshi sarki, zai yi kyau in sami wasiƙu zuwa ga gwamnonin Kewayen Kogin Yuferites, domin su tanada kāriya har sai na isa Yahuda? A kuma ba ni wasiƙa zuwa ga Asaf, sarkin daji, yă ba ni katako don yin ƙofofin kagara na kusa da fadar haikali da kuma don katangar birni, da na wurin da zan zauna?” Sarki kuwa ya ba ni abin da na roƙa, gama Allah yana tare da ni. Saboda haka na tafi wurin gwamnonin Kewayen Kogin Yuferites, na ba su wasiƙun sarki. Sarki kuma ya aika da hafsoshin mayaƙa da kuma mahayan dawakai tare da ni. Da Sanballat mutumin Horon da Tobiya wakilin ƙasar Ammon suka ji cewa wani ya zo domin yă ƙarfafa zaman lafiyar mutanen Isra’ila, sai suka damu ƙwarai. Sai na je Urushalima, bayan na zauna a can na kwanaki uku, sai na fita da dare tare da mutane kalila. Ban faɗa wa wani abin da Allahna ya sa a zuciyata in yi don Urushalima ba. Ba waɗansu dabbobi kuma tare da ni, sai dai dabbar da na hau. Da dare na fita ta Ƙofar Kwari wajen Rijiyar Dila da Ƙofar Juji, ina dudduba katangar Urushalima waɗanda aka rushe da kuma ƙofofinta waɗanda aka ƙone da wuta. Sa’an nan na ci gaba zuwa wajen Ƙofar Maɓuɓɓuga da kuma Tafkin Sarki, amma babu isashen wuri saboda abin da na hau yă bi; saboda haka na haura ta kwarin da dad dare, ina dudduba katangar. A ƙarshe, na juya na sāke shiga ta Ƙofar Kwari. Shugabanni ba su san inda na tafi, ko abin da nake yi ba, domin ban riga na faɗa wa Yahudawa, ko firistoci, ko manyan gari, ko shugabanni, ko sauran waɗanda za su yi aiki, kome ba. Sai na ce musu, “Kun ga matsalar da muke ciki, yadda Urushalima ta zama kango, an kuma ƙone ƙofofinta da wuta. Ku zo mu sāke gina katangar Urushalima, ba za mu ƙara shan kunya ba.” Na kuma faɗa musu game da yadda alherin Allahna yake tare da ni da kuma abin da sarki ya faɗa mini. Suka amsa, suka ce, “Mu tashi, mu kama gini.” Sai suka fara wannan aiki mai kyau. Amma sa’ad da Sanballat mutumin Horon da Tobiya wakilin ƙasar Ammon da kuma Geshem mutumin Arab suka ji game da wannan, sai suka yi mana ba’a suka kuma yi mana dariya. Suka ce, “Me kuke tsammani kuke yi? Kuna so ku yi wa sarki tawaye ne?” Na amsa musu na ce, “Allah na sama zai ba mu nasara. Mu bayinsa za mu tashi mu fara gini, amma game da ku kam, ba ku da rabo cikin Urushalima, ba ku da wani hakki ko wani abin tunawa.” Eliyashib babban firist da ’yan’uwansa firistoci suka tashi suka sāke gina Ƙofar Tumaki. Suka tsarkake ta, suka sa ƙofofinta a wurarensu, suka yi ginin har Hasumiyar Ɗari, wadda suka tsarkake, da kuma Hasumiyar Hananel. Mutanen Yeriko kuwa suka kama ginin daga mahaɗin, Zakkur ɗan Imri kuma ya fara ginin biye da su. ’Ya’yan Hassenaya ne suka gina Ƙofar Kifi. Suka kafa ginshiƙan, suka kuma sa ƙofofinta, da sakatunta, da kuma sandunan ƙarfenta a wurarensu. Kusa da su kuma, Meremot ɗan Uriya, ɗan Hakkoz ne ya yi gyare-gyaren. Biye da shi kuma sai Meshullam ɗan Berekiya, ɗan Meshezabel ya yi gyare-gyare. Kusa da shi Zadok ɗan Ba’ana shi ma ya yi gyare-gyare. Mutanen Tekowa ne suka yi gyare-gyare biye da shi, amma manyan garinsu suka ƙi su sa hannu cikin aikin da shugabanninsu suka bayar. Yohiyada ɗan Faseya, da Meshullam ɗan Besodehiya ne suka gyara Ƙofar Yeshana. Suka kafa katakanta, suka sa ƙyamarenta, da sandunan ƙarfe na kulle ƙofofinta. Biye da su, mutanen Gibeyon da Mizfa Melatiya na Gibeyon da Yadon Meronot waɗanda suke ƙarƙashin ikon gwamnan Kewayen Kogin Yuferites ne suka yi gyare-gyaren. Uzziyel ɗan Harhahiya, ɗaya daga cikin masu ƙeran zinariya ne ya yi gyare-gyaren sashe na biye; sai Hananiya, ɗaya daga cikin masu yin turare, ya yi gyare-gyaren biye da wannan. Suka gyara Urushalima har zuwa Katanga Mai Faɗi. Refahiya ɗan Hur, mai mulkin rabin yankin Urushalima, ya yi gyare-gyaren sashe na biye. Kusa da Refahiya, Yedahiya ɗan Harumaf ya yi gyare-gyaren daga gaban gidansa, sai Hattush ɗan Hashabnehiya ya yi gyare-gyaren biye da shi. Malkiya ɗan Harim, da Hasshub ɗan Fahat-Mowab ya yi gyare-gyaren wani sashe da kuma Hasumiyar Wurin Gashi. Shallum ɗan Hallohesh, mai mulkin ɗayan rabin yankin Urushalima ya yi gyare-gyaren sashe na biye tare da taimakon ’ya’yansa mata. Hanun da mazaunan Zanowa ne suka gyara Ƙofar Kwari. Suka sāke gina ta suka sa ƙofofinta, da sakatunta, da sandunan ƙarfenta a wurarensu. Suka kuma gyara yadi ɗari biyar na katangar har zuwa Ƙofar Juji. Malkiya ɗan Rekab mai mulkin yankin Bet-Hakkerem ne ya yi gyare-gyaren Ƙofar Juji. Ya sāke gina ta ya kuma sa sakatunta, da sanduna ƙarfenta a wurarensu. Shallum ɗan Kol-Hoze mai mulkin Mizfa ne ya yi gyare-gyaren Ƙofar Maɓuɓɓuga. Ya sāke gina ta, ya yi mata jinƙa yana sa ƙofofinta, da sakatunta, da kuma sandunan ƙarfenta a wurarensu. Ya kuma gyara katangar tafkin Silowam, ta Lambun Sarki, har zuwa matakalan da suka gangara daga Birnin Dawuda. Gaba da shi, Nehemiya ɗan Azbuk, mai mulkin rabin yankin Bet-Zur ne ya yi gyare-gyaren har zuwa kusa da kaburburan Dawuda, har zuwa haƙaƙƙen tafki da kuma Gidan Jarumawa. Biye da shi, Lawiyawa a ƙarƙashin Rehum ɗan Bani ne suka yi gyare-gyaren. Kusa da su, Hashabiya mai mulkin rabin yankin Keyila ne ya yi gyare-gyaren don yankinsa. Biye da shi, ’yan’uwansu Lawiyawa ne a ƙarƙashin Binnuyi ɗan Henadad, mai mulkin ɗayan rabin yankin Keyila suka yi gyare-gyaren. Biye da su, Ezer ɗan Yeshuwa, mai mulkin Mizfa, ya yi gyara wani sashe, daga inda yake fuskantar hawan gidan makamai har zuwa kusurwa. Biye da shi, Baruk ɗan Zakkai da ƙwazo ya gyara wani sashe, daga kusurwa zuwa mashigin gidan Eliyashib babban firist. Biye da shi, Meremot ɗan Uriya, ɗan Hakkoz, ya yi gyaran wani sashe, daga mashigin gidan Eliyashib zuwa ƙarshensa. Firistoci daga kewayen yankin ne suka yi gyare-gyaren biye da shi. Can gaba da su, Benyamin da Hasshub ne suka yi gyare-gyaren a gaban gidansu, biye da su kuwa, Azariya ɗan Ma’asehiya, ɗan Ananiya ne ya yi gyare-gyaren kusa da gidansa. Biye da shi, Binnuyi ɗan Henadad ya yi gyaran wani sashe, daga gidan Azariya zuwa kusurwa, sai Falal ɗan Uzai ya yi aiki ɗaura da kusurwa da kuma doguwar hasumiya daga fadar da take bisa kusa da shirayin masu tsaro. Biye da shi, Fedahiya ɗan Farosh da masu hidimar haikali da suke zama a tudun Ofel ne suka yi gyare-gyaren har zuwa wani wuri ɗaura da Ƙofar Ruwa wajen gabas da kuma doguwar hasumiya. Biye da su, mutanen Tekowa suka yi gyaran wani sashe, daga babbar doguwar hasumiya zuwa katangar Ofel. Daga Ƙofar Doki, firistoci ne suka yi gyare-gyaren, kowanne a gaban gidansa. Biye da su, Zadok ɗan Immer ya yi gyare-gyaren ɗaura da gidansa. Biye da shi, Shemahiya ɗan Shekaniya, mai tsaron Ƙofar Gabas ya yi gyare-gyare. Biye da shi, Hananiya ɗan Shelemiya, da Hanun, ɗa na shida na Zalaf, suka gyara wani sashe. Biye da su, Meshullam ɗan Berekiya ya yi gyare-gyaren ɗaura da wurin zamansa. Biye da shi, Malkiya, ɗaya daga cikin masu ƙera zinariya ya yi gyare-gyaren har zuwa gidan masu hidimar haikali da kuma ’yan kasuwa, ɗaura da Ƙofar Bincike, har zuwa ɗakin da yake bisa kusurwar. Maƙeran zinariya da ’yan kasuwa suka gyara wani sashi tsakanin ɗakin da yake bisa kusurwa da Ƙofar Tumaki. Da Sanballat ya ji cewa muna sāke ginin katangar, sai ya husata, ya haukace ƙwarai. Ya yi wa Yahudawa dariya, a gaban abokansa da kuma sojojin Samariya ya ce, “Me waɗancan Yahudawan nan marasa ƙarfi suke yi? Za su maido da katangarsu ne? Za su miƙa hadayu ne? Za su gama a rana ɗaya? Za su iya samun duwatsun gini daga tsibin matattun duwatsu?” Tobiya wakilin mutanen Ammon wanda yake a gefensa ya ce, “Abin nan da suke gini, ko dila ma ya hau, zai rushe shi!” Ka ji mu, ya Allahnmu, gama an rena mu. Bari zagin da suke yi mana yă koma kansu. Ka sa a kwashe su a kai su bauta a wata ƙasa. Kada ka rufe laifinsu, kada kuwa ka gafarta musu, gama sun ci mutuncinmu, mu da muke gini. Sai muka sāke ginin katangar sai da duka ta kai rabin tsayinta, gama mutane sun yi aiki da dukan ƙarfinsu. Amma da Sanballat, da Tobiya, da Larabawa, da Ammonawa, da kuma mutanen Ashdod suka ji cewa gyare-gyaren katangar Urushalima yana cin gaba, ana kuma tattoshe wuraren da suka tsattsaga, sai suka husata ƙwarai. Dukansu suka ƙulla su zo, su yi yaƙi da Urushalima, su tā da hankali a cikinta. Amma muka yi addu’a ga Allahnmu muka kuma sa masu tsaro da rana da kuma dare don mu magance wannan barazana. Ana cikin haka, mutane a Yahuda suka ce, “Ƙarfin ma’aikata yana kāsawa, akwai kuma sauran tarkace da yawa da ba za mu iya sāke gina katangar ba.” Abokan gābanmu sun ce, “Ba za su sani ba, ba kuwa za su gan mu ba, sai dai kawai su gan mu a cikinsu, za mu karkashe su, mu tsai da aikin.” Sau da yawa Yahudawan da suke da zama kusa da abokan gābanmu sun yi ta zuwa suna yin mana magana, suna cewa “Ko’ina muka juya, za su fāɗa mana.” Saboda haka na sa jama’a su ja ɗamara bisa ga iyalinsu a bayan katanga, a wuraren da ba a gina ba. Suna riƙe da takuba, da māsu, da bakkuna. Bayan na dudduba abubuwa, sai na miƙe tsaye na ce wa manyan gari da shugabanni da kuma sauran jama’a, “Kada ku ji tsoronsu. Ku tuna da Ubangiji, wanda yake mai girma da banrazana, ku yi yaƙi don ’yan’uwanku, da ’ya’yanku maza da mata, da matanku da kuma gidajenku.” Da abokan gābanmu suka ji muna sane da shirinsu, Allah kuma ya wargaje shirin nan, sai duk muka dawo ga katangar, kowa ya kama aikinsa. Daga wannan rana zuwa gaba, rabin mutane suka yi aiki, yayinda sauran rabin suka kintsa da māsu, da garkuwa, da bakkuna da makamai. Shugabanni suka goyi bayan dukan mutanen Yahuda waɗanda suke ginin katanga. Waɗanda suke ɗaukan kaya suka yi aikinsu da hannu ɗaya, suna kuma riƙe da makami a ɗaya hannun, kuma kowane mai gini ya ɗaura takobinsa a gefe yayinda yake aiki. Amma mutum mai busa ƙaho ya kasance tare da ni. Sai na ce wa manyan gari, da shugabanni, da sauran jama’a, “Aikin nan babba ne kuma mai yawa, ga shi muna a rarrabe nesa da juna a katangar. Duk inda kuka ji an busa ƙaho, sai ku taru a wurin. Allahnmu zai yi yaƙi dominmu!” Saboda haka muka ci gaba da aiki, rabin mutane suna riƙe da māsu, daga wayewar gari har zuwa fitowar taurari. A wannan lokaci na kuma ce wa mutane, “A sa kowane mutum da mataimakinsa su zauna a Urushalima da dare, domin a yi tsaro da dare, da safe kuma a kama aiki.” Saboda haka ni, da ’yan’uwana, da bayina, da matsaran da suke tare da ni, ba wanda ya tuɓe tufafinsa; kowa ya rataye makaminsa, ko ya je shan ruwa ma. To, sai maza da matansu suka tā da fara gunaguni mai tsanani a kan ’yan’uwansu Yahudawa. Waɗansu suka ce, “Mu da ’ya’yanmu maza da mata muna da yawa, muna bukatar hatsi domin mu ci mu rayu.” Waɗansu kuwa suka ce, “Saboda yunwa mun jinginar da gonakinmu, da gonakin inabinmu, da gidajenmu don mu sami hatsi.” Har illa yau waɗansu suka ce, “Mun ci bashin kuɗi don mu biya haraji a kan gonakinmu, da gonakin inabinmu. Ga shi kuwa, mu da su dangin juna ne, ’ya’yanmu da nasu kuma ɗaya ne, duk da haka an tilasta mu mu sa ’ya’yanmu mata da maza su zama bayi. Har ma an riga an bautar waɗansu daga cikin ’ya’yanmu mata, amma ba mu da iko mu ce kome, domin gonakinmu da gonakin inabinmu suna a hannun waɗansu mutane.” Sa’ad da na ji kukansu da waɗannan koke-koke, na husata ƙwarai. Na yi tunaninsu a zuciyata sa’an nan na zargi manyan gari da shugabanni. Na ce musu, “Kuna musguna wa ’yan’uwanku ta wurin ba su rance da ruwa!” Saboda haka na kira babban taro gaba ɗaya don a magance wannan. Na ce, “Da dukan iyakar ƙoƙarinmu, mun fanshi ’yan’uwanmu Yahudawan da aka sayar wa Al’ummai. Amma ga shi kuna sayar da ’yan’uwanku ga Al’ummai, don kawai a sāke sayar mana da su!” Saboda haka na ci gaba na ce, “Abin da kuke yi a yanzu ba daidai ba ne. Bai kamata ku yi tafiya cikin tsoron Allahnmu don mu guji ba’ar Al’ummai abokan gābanmu ba? Ni ma da ’yan’uwana da kuma mutanena muna ba wa mutane bashin kuɗi da kuma hatsi. Sai mu daina sha’anin ba da rance da ruwa! Yau sai ku mayar musu da gonakinsu, da gonakin inabinsu, da na zaitunsu, da gidajensu, da kashi ɗaya bisa ɗari na kuɗi, da na hatsi, da na ruwan inabi, da na mai, waɗanda kuka karɓa a wurinsu.” Suka ce, “Za mu mayar musu, kuma ba za mu bukaci wani abu daga gare su ba. Za mu yi yadda ka faɗa.” Sai na tattara firistoci na kuma sa manyan gari da shugabanni su yi rantsuwa don su yi abin da suka yi alkawari. Na kuma kakkaɓe hannuna, na ce, “Duk wanda ya karya wannan alkawari, haka Allah zai kakkaɓe shi daga gidansa da aikinsa. Allah zai kakkaɓe shi, yă wofintar da shi!” Da jin wannan, sai dukan taron suka ce, “Amin,” suka kuma yabi Ubangiji. Mutane kuwa suka yi kamar yadda suka yi alkawari. Ban da haka ma, daga shekara ta ashirin ta Sarki Artazerzes, sa’ad da aka naɗa ni in zama gwamnansu a ƙasar Yahuda, har zuwa shekara ta talatin da biyu na mulkinsa, shekara sha biyu ke nan, ko ni, ko ’yan’uwana, ba wanda ya ci abincin da akan ba wa gwamna. Amma gwamnonin farko, waɗanda suka riga ni, sun ɗaura wa mutane kaya mai nauyi suka karɓi shekel arba’in na azurfa daga gare su haɗe da abinci da kuma ruwan inabi. Har bayin masu mulki ma sun nawaya wa mutane. Amma ni ban yi haka ba, saboda ina tsoron Allah. A maimakon haka, na miƙa kaina ga aiki a kan wannan katanga. Na tattara dukan mutanena a can don aikin; ba mu samar wa kanmu wata gona ba. Bugu da ƙari, Yahudawa da shugabanni ɗari da hamsin suna ci daga teburina, haka ma waɗanda suka zo wurinmu daga ƙasashen da suke kewaye. Kowace rana akan shirya mini saniya ɗaya, zaɓaɓɓun tumaki shida da waɗansu kaji, kuma kowace kwana goma akan tanadar da ruwan inabi na kowane iri a yalwace. Duk da haka, ban taɓa nemi a ba ni abincin da akan ba wa gwamna ba, domin wahala ta yi wa jama’a yawa. Ka tuna da ni, ka yi mini alheri, ya Allah, saboda dukan abubuwan da na yi saboda waɗannan mutane. Sa’ad da magana ta zo kunnen Sanballat, da Tobiya, da Geshem mutumin Arab da kuma sauran abokan gābanmu cewa na sāke gina katangar har babu sauran tsaguwa da ta ragu, ko da yake har zuwa lokacin ban sa ƙofofi a ƙyamare ba Sanballat da Geshem suka aika mini wannan saƙo cewa, “Ka zo, mu sadu a wani ƙauye a filin Ono.” Amma makirci ne suke yi don su cuce ni; saboda haka sai na aika musu da wannan amsa, na ce, “Ina cikin babban aiki, ba zan kuwa iya gangarawa ba. Don me zan bar aikin yă tsaya don in gangara zuwa wurinku?” Suka yi ta aiko mini da wannan saƙo har sau huɗu, ni kuwa na yi ta ba su amsa irin ta dā. Sai sau na biya, Sanballat ya aiki mataimakinsa gare ni da irin saƙo guda, kuma a hannunsa akwai wasiƙar da ba a yimƙe ba wadda aka rubuta cewa, “An ba da labari cikin al’ummai, kuma Geshem ya ce gaskiya ne, cewa kai da Yahudawa kun shirya tawaye, saboda haka kuke sāke ginin katangar. Ban da haka ma, bisa ga waɗannan rahotanni kana shirin zaman sarkinsu har ma ka naɗa annabawa su yi wannan shela game da kai a Urushalima, su ce, ‘Akwai sarki a Yahuda!’ To, wannan rahoto zai koma wurin sarki; saboda haka ka zo, mu tattauna wannan batu.” Sai na aika masa wannan amsa, na ce, “Babu wani abu haka da yake faruwa; ka dai ƙaga wannan daga tunaninka ne.” Suka dai yi ƙoƙari su tsoratar da mu, suna cewa, “Hannuwansu za su rasa ƙarfin yin aiki, ba kuwa za su ƙare aikin ba.” Amma na yi addu’a na ce, “Yanzu, ya Allah, ka ƙarfafa hannuwana.” Wata rana na tafi gidan Shemahiya ɗan Delahiya, ɗan Mehetabel, wanda aka hana fita a gidansa. Ya ce mini, “Mu sadu gobe a gidan Allah, a cikin haikali, mu kuma kulle ƙofofin haikali, gama mutane suna zuwa su kashe ka, tabbatacce za su zo da dare su kashe ka.” Amma na ce, “Ya kamata mutum kamar ni yă gudu? Ko kuwa ya kamata wani kamar ni yă shiga cikin haikali don yă ceci ransa? Ba zan tafi ba!” Na gane cewa Allah bai aike shi ba, ya yi annabci a kaina domin Tobiya da Sanballat sun yi hayarsa ne. An yi hayarsa don yă sa in ji tsoro in yi zunubi ta yin haka, sa’an nan za su ba ni mugun suna, su wofinta ni. Ya Allahna, ka tuna da Tobiya da Sanballat, saboda abin da suka yi; ka kuma tuna da annabiya Nowadiya da sauran annabawa waɗanda suke ƙoƙari su tsorata ni. Cikin kwana hamsin da biyu aka gama gina katangar, a ranar ashirin da biyar ga watan Elul. Sa’ad da dukan abokan gābanmu suka ji haka, dukan al’umman da suke kewaye da mu suka ji tsoro, suka rasa ƙarfin halinsu, domin sun gane cewa wannan aiki an yi shi da taimakon Allahnmu ne. A waɗannan kwanaki, manyan garin Yahuda suka yi ta aika wasiƙu masu yawa zuwa ga Tobiya, shi kuma ya yi ta aika musu da amsoshi. Gama mutane da yawa a cikin Yahuda sun rantse wa Tobiya za su goyi bayansa, domin ya auri ’yar Shekaniya, ɗan Ara. Ɗansa kuma, wato, Yehohanan, ya auri ’yar Meshullam, ɗan Berekiya. Ban da haka ma, mutanen sun yi ta ba ni labarin ayyuka masu kyau da Tobiya ya yi, sa’an nan kuma suna faɗa masa duk abin da na faɗa. Tobiya kuwa ya aika wasiƙu don yă tsorata ni. Bayan an sāke gina katangar na kuma sa ƙofofi a wurarensu, sai aka naɗa masu tsaro, da mawaƙa, da Lawiyawa. Na sa ɗan’uwana Hanani tare da Hananiya shugaban fada aikin riƙon Urushalima, domin shi Hananiya mutum mai mutunci ne, mai tsoron Allah fiye da yawancin mutane. Na ce musu, “Kada a buɗe ƙofofin Urushalima da sassafe sai rana ta fito sosai. Yayinda matsaran ƙofofi suna aiki, a kulle ƙofofin a sa musu sakata kafin matsaran su tashi, wajen fāɗuwar rana. Ku kuma naɗa mazaunan Urushalima a matsayin masu tsaro, waɗansunsu a wuraren aiki, waɗansun kuma kusa da gidajensu.” Birnin Urushalima kuwa tana da fāɗi da girma, amma mutanen da suke zama a cikinta kaɗan ne, ba a kuma gina gidaje da yawa ba tukuna. Sai Allahna ya sa a zuciyata in tara manyan gari, shugabanni da talakawa don a rubuta su bisa ga iyalansu. Na sami littafin asali na waɗanda suka fara dawowa. Ga abin da na tarar an rubuta a ciki. Waɗannan su ne mutanen yankin da suka dawo daga zaman bautar da Nebukadnezzar sarkin Babilon ya kame (sun dawo Urushalima da Yahuda, kowanne zuwa garinsa. Sun dawo tare da Zerubbabel, da Yeshuwa, da Nehemiya, da Azariya, da Ra’amiya, da Nahamani, da Mordekai, da Bilshan, da Misfar, da Bigwai, da Nehum da kuma Ba’ana). Ga jerin mutanen Isra’ila. Zuriyar Farosh mutum 2,172 ta Shefatiya 372 ta Ara 652 ta Fahat-Mowab (ta wurin Yeshuwa da Yowab) 2,818 ta Elam 1,254 ta Zattu 845 ta Zakkai 760 ta Binnuyi 648 ta Bebai 628 ta Azgad 2,322 ta Adonikam 667 ta Bigwai 2,067 ta Adin 655 ta Ater (ta wurin Hezekiya) 98 ta Hashum 328 ta Bezai 324 ta Harif 112 ta Gibeyon 95. Mutanen Betlehem da na Netofa 188 na Anatot 128 na Bet-Azmawet 42 na Kiriyat Yeyarim, Kefira da na Beyerot 743 na Rama da na Geba 621 na Mikmash 122 na Betel da na Ai 123 na ɗayan Nebo 52 na ɗayan Elam 1,254 na Harim 2 320 na Yeriko 345 na Lod, da na Hadid, da na Ono 721 na Sena’a 3,930. Ga zuriyar Firistoci. Zuriyar Yedahiya (ta wurin iyalin Yeshuwa) 973 ta Immer 1,052 ta Fashhur 1,247 ta Harim 1,017. Ga zuriyar Lawiyawa. Zuriyar Yeshuwa da Kadmiyel (ta wurin Hodeba) 74. Mawaƙa. Zuriyar Asaf mutum 148. Ga zuriyar Matsaran Ƙofofi. Zuriyar Shallum, Ater, Talmon, Akkub, Hatita da Shobai 138. Ma’aikatan haikali. Zuriyar Ziha, Hasufa, Tabbawot, da ta Keros, da ta Siya, da ta Fadon, da ta Lebana, da ta Hagaba, da ta Shalmai, da ta Hanan, da ta Giddel, da ta Gahar, da ta Reyahiya, da ta Rezin, da ta Nekoda, da ta Gazzam, da ta Uzza, da ta Faseya, da ta Besai, da ta Meyunawa, da ta Nefussiyawa, da ta Bakbuk, da ta Hakufa, da ta Harhur, da ta Bazlit, da ta Mehida, da ta Harsha, da ta Barkos, da ta Sisera, da ta Tema, da ta Neziya, da kuma ta Hatifa. Ga zuriyar bayin Solomon. Zuriyar Sotai, da ta Soferet, da ta Ferida, da ta Ya’ala, da ta Darkon, da ta Giddel, Shefatiya, Hattil, Fokeret-Hazzebayim, da Amon. Zuriyar ma’aikatan haikali da ta bayin Solomon su 392. Waɗansu sun hauro daga garuruwan Tel-Mela, Tel-Harsha, Kerub, Addon da Immer, amma ba su iya nuna cewa iyalansu su zuriyar Isra’ila ce ba, zuriyar Delahiya, Tobiya, da Nekoda 642. Na wajen firistoci kuwa su ne, Zuriyar Hobahiya, da ta Hakkoz, da ta Barzillai (wani mutumin da ya auri ’yar Barzillai mutumin Gileyad, aka kuma kira shi da wannan suna). Waɗannan ne aka nemi sunayensu a cikin tarihin asalin iyalai, amma ba a same su a ciki ba, saboda haka aka hana su shiga cikin firistoci, sun zama kamar marasa tsarki. Sai gwamna ya umarce su kada su ci wani abinci mafi tsarki, sai akwai firist da zai nemi nufin Ubangiji ta wurin Urim da Tummim. Yawan jama’ar duka ya kai mutum 42,360, ban da bayinsu maza da mata 7,337. Suna kuma da mawaƙa maza da mata 245. Akwai dawakai 736, alfadarai 245 raƙuma 435, da kuma jakuna 6,720. Waɗansu shugabannin iyalai suka ba da kyautai domin taimakon aiki. Gwamna ya ba da darik 1,000 na zinariya, kwanoni 50, da riguna 530 don firistoci. Waɗansu shugabannin iyalai sun ba da darik 20,000 na zinariya da mina 2,200 na azurfa don aiki. Jimillar da sauran mutane suka bayar ta kai darik 20,000 na zinariya, minas 2,000 na azurfa, da riguna sittin da bakwai don firistoci. Firistoci, da Lawiyawa, da matsaran ƙofofi, da mawaƙa, da ma’aikatan haikali tare da waɗansu mutane da kuma sauran mutanen Isra’ila, suka zauna a garuruwansu. Da wata na bakwai ya zo, Isra’ilawa kuwa sun riga sun zauna a garuruwansu, sai dukan mutane suka taru kamar mutum guda a dandali a gaban Ƙofar Ruwa. Suka faɗa wa Ezra malamin Doka yă fitar da Littafin Dokar Musa, wanda Ubangiji ya umarta domin Isra’ila. Saboda haka a rana ta farko ga watan bakwai, Ezra firist, ya kawo Doka a gaban taro, wanda ya ƙunshi maza da mata da dukan waɗanda za su iya fahimta. Ya karanta Dokar da ƙarfi daga safe har tsakar rana yayinda yake a kan dandali da yake fuskantar dandali a gaban Ƙofar Ruwa, gaban maza, mata da kuma sauran mutanen da za su iya fahimta. Dukan mutane kuwa suka saurara a hankali ga karatun Littafin Dokar. Ezra malamin Doka ya tsaya a kan dakalin itacen da aka yi saboda wannan hidima. Kusa da shi a damansa, Mattitiya, Shema, Anahiya, Uriya, Hilkiya da Ma’asehiya suka tsaya; a hagunsa kuma Fedahiya, Mishayel, Malkiya, Hashum, Hashbaddana, Zakariya da Meshullam suka tsaya. Sai Ezra ya buɗe littafin. Dukan mutane kuwa suka gan shi domin yana tsaye a bisa fiye da inda mutane suke tsaye; yayinda ya buɗe littafin kuwa, dukan mutane suka miƙe tsaye. Ezra ya yabi Ubangiji, Allah mai girma; dukan mutane kuwa suka tā da hannuwansu suka amsa, “Amin! Amin!” Sa’an nan suka sunkuya suka yi wa Ubangiji sujada da fuskokinsu har ƙasa. Lawiyawa, wato, su Yeshuwa, Bani, Sherebiya, Yamin, Akkub, Shabbetai, Hodiya, Ma’asehiya, Kelita, Azariya, Yozabad, Hanan da Felahiya, suka koyar da mutane a cikin Dokar yayinda mutane suke a tsaye a can. Suka karanta daga Littafin Dokar Allah, suna sa kowa ya gane, suna kuma ba da fassarar domin mutane su fahimci abin da ake karatu. Sa’an nan Nehemiya gwamna, Ezra firist da kuma wanda yake malamin Doka, da Lawiyawa waɗanda suke koyar da mutane, suka ce musu duka, “Wannan rana mai tsarki ce ga Ubangiji Allahnku. Kada ku yi makoki ko kuka.” Gama dukan mutane suna ta kuka yayinda suke sauraran kalmomin Dokar. Nehemiya ya ce, “Ku koma gidajenku ku ci abinci mai kyau, ku sha abin sha mai zaƙi, ku kuma aika wa wanda ba shi da shi. Wannan rana mai tsarki ce ga Ubangijinmu. Kada ku yi baƙin ciki, gama farin cikin Ubangiji shi ne ƙarfinku.” Lawiyawa suka rarrashi mutane duka suna cewa, “Ku natsu, gama wannan rana ce mai tsarki. Kada ku yi baƙin ciki.” Sa’an nan dukan mutane suka koma gidajensu suka ci, suka sha, suka aika wa wanda ba shi da abinci, gama yanzu sun fahimci kalmomin da aka karanta musu. A rana ta biyu ga wata, shugabannin iyalai, tare da firistoci da Lawiyawa, suka taru kewaye da Ezra malamin Doka don su mai da hankali ga kalmomin Dokar. Suka tarar a rubuce a cikin Doka wadda Ubangiji ya umarta ta wurin Musa, cewa Isra’ilawa su zauna a bukkoki a lokaci bikin watan bakwai kuma cewa ya kamata su yi shelar wannan magana, su kuma yaɗa ta a duk garuruwansu da kuma cikin Urushalima cewa, “Ku fita zuwa cikin ƙasar tudu ku kawo rassa daga itatuwan zaitun da na zaitun jeji, da kuma daga dargaza, da dabino da itatuwa masu ganye, don yin bukkoki”, kamar yadda yake a rubuce. Sai mutanen suka fita suka dawo da rassa suka kuma yi wa kansu bukkoki a bisa rufin ɗakunansu, a cikin filaye, a shirayin gidan Allah, da ciki dandalin da yake kusa da Ƙofar Ruwa, da kuma a dandalin da yake a Ƙofar Efraim. Dukan jama’ar da suka komo daga zaman bauta suka yi bukkoki suka kuma zauna a cikinsu. Daga kwanakin Yoshuwa ɗan Nun har yă zuwa yau, Isra’ilawa ba su taɓa yin bikinsa haka ba. Mutane suka cika da farin ciki sosai. Kowace rana, daga rana farko zuwa ƙarshe, Ezra ya karanta daga Littafin Dokar Allah. Suka yi bikin kwana bakwai, a rana ta takwas kuma suka yi muhimmin taro bisa ga ƙa’ida. A rana ta ashirin da huɗu ga watan nan, Isra’ilawa suka taru, suna yin azumi, suna sa rigunan makoki, suna kuma zuba toka a kansu. Waɗanda suke zuriyar Isra’ilawa suka ware kansu daga dukan baƙi. Suka tsaya, suka kuma furta zunubansu da muguntar kakanninsu. Sa’ad da suke nan a tsaye, aka ɗauki awa uku ana karanta Littafin Dokar Ubangiji Allahnsu. Aka kuma ɗauki awa uku ana sujada ga Ubangiji Allahnsu. A kan dakalin kuwa akwai Lawiyawa, wato, Yeshuwa, Bani, Kadmiyel, Shebaniya, Bunni, Sherebiya, Bani da Kenani tsaye, waɗanda suka kira da babbar murya ga Ubangiji Allahnsu. Lawiyawan nan, Yeshuwa, Kadmiyel, Bani, Hashabnehiya, Sherebiya, Hodiya, Shebaniya da Fetahahiya, suka ce, “Ku miƙe tsaye ku yabi Ubangiji Allahnku, wanda yake har abada abadin.” “Albarka ta tabbata ga sunanka mai ɗaukaka, bari kuma a ɗaukaka shi bisa dukan albarka da yabo. Kai kaɗai ne Ubangiji. Kai ka yi sammai, har ma da sama sammai, da dukan rundunar taurari, da duniya da kuma dukan abin da yake cikinta, da tekuna da dukan abubuwan da suke cikinsu. Ka ba da rai ga kome, kuma rundunonin sama suna maka sujada. “Kai ne Ubangiji Allah, wanda ya zaɓi Abram, ya fitar da shi daga Ur na Kaldiyawa, ya kuma ba shi suna Ibrahim. Kai ka sami zuciyarsa da aminci a gare ka, ka kuma yi alkawari da shi cewa za ka ba zuriyarsa ƙasar Kan’aniyawa, da ta Hittiyawa, da ta Amoriyawa, da ta Ferizziyawa, da ta Yebusiyawa, da kuma ta Girgashiyawa. Ka kiyaye alkawarinka domin kai mai adalci ne. “Ka ga wahalar kakanninmu a Masar; ka kuwa ji kukansu a Jan Teku. Ka aika da alamu masu banmamaki da al’ajabai a kan Fir’auna, a kan dukan shugabanninsa da kuma a kan dukan mutanen ƙasarsa, gama ka ga irin danniyar da suka yi wa mutanenka. Ka samo wa kanka suna, wadda ta dawwama har yă zuwa yau. Ka raba teku a gaban kakanninmu, saboda su wuce cikinsa a busasshiyar ƙasa, amma ka hallaka masu binsu cikin zurfafa, nutse kamar dutse a cikin ruwa. Da rana ka bishe kakanninmu da girgije, da dare kuwa ka bishe su da ginshiƙin wuta don ka ba su haske a hanyar da za su bi. “Ka sauko a kan Dutsen Sinai; ka yi musu magana daga sama. Ka ba su ƙa’idodi da dokokin da suke masu adalci da kuma daidai, ka ba su farillai da umarnai da suke da kyau. Ka sanar da su Asabbacinka mai tsarki, ka kuma ba su umarnai, da farillai, da kuma dokoki ta wurin bawanka Musa. Cikin yunwansu ka ba su burodi daga sama, cikin ƙishirwansu kuma ka fitar musu ruwa daga dutse. Ka faɗa musu su shiga su mallaki ƙasar da ka rantse ta wurin ɗaga hannu cewa za ka ba su. “Amma su kakanninmu, suka yi fariya da taurinkai, ba su kuwa yi biyayya ga umarnanka ba. Suka ƙi su saurare ka, suka kāsa tuna da mu’ujizan da ka aikata a cikinsu. Suka yi taurinkai, cikin tawayensu kuma suka naɗa shugaba don su koma bautarsu. Amma kai Allah ne mai gafartawa, mai alheri da jinƙai, mai jinkirin fushi, mai yalwar ƙauna. Saboda haka ba ka yashe su ba, ko ma sa’ad da suka yi wa kansu siffar ɗan maraƙi, suka ce, ‘Wannan shi ne allahnku, wanda ya fitar da ku daga Masar,’ ko sa’ad da suka yi saɓo mai bantsoro. “Saboda jinƙanka mai girma, ba ka yashe su a hamada ba. Da rana, ginshiƙin girgije bai daina bishe su a hanyarsu ba, da dare kuma ginshiƙin wuta bai daina haskakawa a hanyar da za su bi ba. Ka ba da Ruhunka mai kyau don yă koyar da su. Ba ka janye Manna naka daga bakunansu ba, ka kuma ba su ruwa don ƙishirwansu. Shekaru arba’in ka riƙe su a cikin hamada; ba su rasa kome ba, rigunansu ba su yage ba, ƙafafunsu kuwa ba su kumbura ba. “Ka ba su mulkoki da al’ummai, kana ba su har ma da ƙasashen da suke jeji. Suka ci ƙasar Sihon na sarkin Heshbon da ƙasar Og inda sarkin Bashan yake mulki. Ka sa ’ya’yansu maza suka yi yawa kamar taurarin sararin sama, ka kuma kawo su cikin ƙasar da ka faɗa wa kakanninsu su shiga su mallake. ’Ya’yansu maza suka shiga suka kuma mallaki ƙasar. A gabansu ka rinjayi Kan’aniyawan da suke zama a cikin ƙasar; ka ba da Kan’aniyawa a gare su, tare da sarakunansu da kuma mutanen ƙasar, su yi da su yadda suke so. Suka kame birane masu katanga masu ƙarfi, da ƙasa masu ba da amfani; suka mallaki gidaje cike da kowane irin abu mai kyau, da rijiyoyin da aka riga aka haƙa, da gonakin inabi, da gonakin itatuwan zaitun da kuma itatuwan ba da ’ya’ya a yalwace a ciki. Suka ci suka ƙoshi, suka kuma yi ƙiba; suka ji daɗi cikin alherinka mai girma. “Amma suka yi rashin biyayya suka kuma yi tawaye gare ka; suka sa dokarka a bayansu. Suka kashe annabawanka waɗanda suka gargaɗe su don su mai da su gare ka; suka aikata saɓo mai bantsoro. Saboda haka ka miƙa su ga abokan gābansu waɗanda suka yi musu danniya. Amma sa’ad da ake danniyarsu sai suka yi kuka gare ka. Daga sama ka ji su, cikin jinƙanka mai girma kuwa ka ba su mai ceto, wanda ya fisshe su daga hannun abokan gābansu. “Amma nan da nan, da suka sami hutu, sai suka sāke aikata abin da yake mugu a idonka. Sai ka yashe su ga hannun abokan gābansu don su yi mulki a kansu. Sa’ad da suka yi kuka kuma gare ka, ka ji daga sama, cikin jinƙanka kuma ka fisshe su sau da sau. “Ka gargaɗe su su dawo ga dokarka, amma suka yi fariya, suka bijire wa umarnanka. Suka yi zunubi game da farillanka waɗanda ta wurinsu ne mutum zai rayu in ya yi biyayya da su. Cikin taurinkai suka juye bayansu daga gare ka, suka zama masu taurinkai, suka kuma ƙi su saurara. Shekaru masu yawa ka yi haƙuri da su. Ta wurin Ruhunka ka gargaɗe su ta wurin annabawa. Duk da haka ba su kasa kunne ba, saboda haka ka miƙa su ga maƙwabtansu. Amma cikin tausayinka mai girma ba ka kawo su ga ƙarshe ko ka yashe su ba, gama kai Allah ne mai alheri da kuma mai jinƙai. “To yanzu, ya Allahnmu, mai girma, mai iko, da kuma mai banrazana, wanda yake kiyaye alkawarinsa na ƙauna, kada ka bar dukan wannan wahala ta zama kamar marar muhimmanci a idanunka, wahalar da ta zo a kanmu, a kan sarakunanmu da shugabanni, a kan firistocinmu da annabawa, a kan kakanninmu da kuma dukan mutanenka, daga kwanakin sarakunan Assuriya har yă zuwa yau. Cikin dukan abubuwan da suka faru da mu, ka kasance mai adalci; ka yi aminci, yayinda mu kuwa muka aikata mugu. Sarakunanmu, da shugabanninmu, da firistocinmu da kuma kakanninmu ba su bi dokarka ba, ba su ma mai da hankali ga umarnanka ko gargaɗin da ka yi musu ba. Ko ma yayinda suke a masarautarsu, suna jin daɗin girmar kyautatawarka gare su, cikin ƙasar mai girma, da kuma mai fāɗin da ka ba su, ba su bauta maka ko su juye daga mugayen hanyoyinsu ba. “Amma duba, mu bayi ne a yau, bayi a ƙasar da ka ba kakanninmu don su ci amfaninta da kuma waɗansu abubuwa masu kyau da take bayarwa. Saboda zunubanmu, yalwar girbin da muke samu yana tafiya wurin sarakunan da ka sa a kanmu. Suna mulki bisa jikunanmu, da bisa garkenmu yadda suka ga dama. Muna cikin baƙin ciki. “Saboda wannan duka, muna yin zaunannen alkawari, muna sa shi a rubuce, shugabanninmu kuwa da Lawiyawanmu, da firistocinmu suna buga hatimansu a kai.” Waɗanda suka buga hatimin su ne, Nehemiya ɗan Hakaliya, wanda yake gwamna. Zedekiya da Serahiya, da Azariya, da Irmiya, da Fashhur, da Amariya, da Malkiya, da Hattush, da Shebaniya, da Malluk, da Harim, da Meremot, da Obadiya, da Daniyel, da Ginneton, da Baruk, da Meshullam, da Abiya, da Miyamin, da Ma’aziya, da Bilgai, da kuma Shemahiya. Waɗannan su ne Firistocin. Lawiyawan kuwa su ne, Yeshuwa ɗan Azaniya, da Binnuyi ɗan Henadad, da Kadmiyel, ’yan’uwansu kuwa su ne, Shebaniya, da Hodiya, da Kelita, da Felahiya, da Hanan, da Mika, da Rehob, da Hashabiya, da Zakkur, da Sherebiya, da Shebaniya, da Hodiya, da Bani da kuma Beninu. Shugabannin mutane su ne, Farosh, da Fahat-Mowab, da Elam, da Zattu, da Bani, da Bunni, da Azgad, da Bebai, da Adoniya, da Bigwai, da Adin, da Ater, da Hezekiya, da Azzur, da Hodiya, da Hashum, da Bezai, da Harif, da Anatot, da Nebai, da Magfiyash, da Meshullam, da Hezir, da Meshezabel, da Zadok, da Yadduwa da Felatiya, da Hanan, da Anahiya, da Hosheya, da Hananiya, da Hasshub, da Hallohesh, da Filha, da Shobek, da Rehum, da Hashabna, da Ma’asehiya da Ahiya, da Hanan, da Anan, da Malluk, da Harim da kuma Ba’ana. “Sauran mutane, wato, firistoci, Lawiyawa, matsaran ƙofofi, mawaƙa, ma’aikatan haikali da dukan waɗanda suka ware kansu daga maƙwabta saboda Dokar Allah, tare da matansu da dukan ’ya’yansu maza da mata waɗanda za su iya fahimta, dukan waɗannan yanzu suka sadu da manyan gari ’yan’uwansu, suka rantse, cewa la’ana ta same su idan ba su kiyaye Dokar Allah da aka bayar ta wurin Musa bawan Allah su kuma mai da hankali ga yin biyayya da dukan umarnai, ƙa’idodi da farillan Ubangiji shugabanmu ba. “Mun yi alkawari ba za mu ba da ’ya’yanmu mata aure ga mutanen da suke kewaye da mu ba, ba kuwa za mu auri ’ya’yansu mata wa ’ya’yanmu maza ba. “Sa’ad da maƙwabta suka kawo kayayyaki ko hatsi don su sayar a ranar Asabbaci, ba za mu saya daga gare su a ranar Asabbaci ko a rana mai tsarki ba. Kowace shekarar Asabbaci ba za mu nome ƙasa ba kuma za mu yafe kowane irin bashi. “Mun ɗauka hakkin bin umarnai na ba da kashi ɗaya bisa uku na shekel kowace shekara don hidimar gidan Allahnmu. Za mu tanada burodin da ake ajiye a kan tebur; za mu ba da hadayun hatsi da hadayun ƙonawa na kullum; za mu ba da hadayun Asabbatai, da na bukukkuwan Sabon Wata da na bukukkuwan da aka ƙayyade; za mu ba da hadayu masu tsarki; za mu ba da hadayun zunubi don a yi kafara domin Isra’ila; mu kuma ba da abubuwan da ake bukata dukan domin ayyukan gidan Allahnmu. “Mu, firistoci, da Lawiyawa da kuma mutane, mun jefa ƙuri’a don a san lokacin da kowane iyalinmu zai kawo sadakar itace don ƙonewa a gidan Allahnmu a ƙayyadaddun lokuta a bagaden Ubangiji Allahnmu, kamar yadda yake a rubuce a cikin Doka. “Mun kuma ɗauka hakkin kawo nunan fari na hatsinmu da kuma na kowane itace mai ba da ’ya’ya a gidan Ubangiji kowace shekara. “Kamar yadda yake a rubuce a cikin Doka, za mu kawo ɗan fari na ’ya’yanmu maza da na garken shanunmu, da na tumakinmu, da kuma na awakinmu a gidan Allahnmu, don firistocin da suke aikin a can. “Ban da haka ma, za mu kawo wa ɗakunan ajiyar gidan Allahnmu, abincinmu na farko daga ƙasa, na hadayun hatsinmu, na ’ya’yan dukan itatuwanmu da kuma na sabon ruwan inabinmu da mai namu wa firistoci. Za mu kuma kawo zakkar hatsinmu wa Lawiyawa, gama Lawiyawa ne ke karɓan Zakka cikin dukan garuruwan da muke noma. Firist wanda yake daga zuriyar Haruna zai raka Lawiyawa sa’ad da suke karɓan zakka, Lawiyawan kuma za su kawo kashi ɗaya bisa goma na zakka zuwa gidan Allahnmu, su kawo a ɗakunan ajiya na baitulmali. Mutanen Isra’ila haɗe da Lawiyawa, za su kawo sadakokinsu na hatsi, sabon ruwan inabi da mai a ɗakunan ajiya inda ake ajiyar kayayyakin wuri mai tsarki da kuma inda firistoci, matsaran ƙofofi da kuma mawaƙa suke zama. “Ba za mu ƙyale gidan Allahnmu ba.” To, fa, shugabannin mutane suka zauna a Urushalima, sauran mutanen kuma suka jefa ƙuri’a don su kawo mutum ɗaya daga kowane mutum goma don su zauna a Urushalima, birni mai tsarki, yayinda sauran tara suka zauna a garuruwansu. Sai mutane suka yaba wa dukan mutanen da suka ba da kansu da yardar rai su zauna a Urushalima. Waɗannan su ne shugabannin yankuna waɗanda suka zauna a Urushalima (ko da yake waɗansu Isra’ilawa, da firistoci, da Lawiyawa, da ma’aikatan haikali, da zuriyar bayin Solomon, suka yi zama a cikin garuruwan Yahuda, kowanne a mallakarsa cikin garuruwa dabam-dabam, yayinda sauran mutane daga Yahuda da Benyamin suka zauna a Urushalima). Daga zuriyar Yahuda akwai, Atahiya ɗan Uzziya, ɗan Zakariya, ɗan Amariya, ɗan Shefatiya, ɗan Mahalalel, wani zuriyar Ferez; da Ma’asehiya ɗan Baruk, ɗan Kol-Hoze, ɗan Hazahiya, ɗan Adahiya, ɗan Yohiyarib, ɗan Zakariya, zuriyar Shela. Zuriyar Ferez waɗanda suka zauna a Urushalima sun kai ɗari huɗu da sittin da takwas, dukansu kuwa muhimman mutane ne. Daga zuriyar Benyamin akwai, Sallu ɗan Meshullam, ɗan Yowed, ɗan Fedahiya, ɗan Kolahiya, ɗan Ma’asehiya, ɗan Itiyel, ɗan Yeshahiya, da mabiyansa, Gabbai da Sallai, mutum 928. Yowel ɗan Zikri ne babban shugabansu, Yahuda kuma ɗan Hassenuwa, ya shugabanci Yanki na Biyu na birni. Daga firistoci akwai, Yedahiya ɗan Yohiyarib, da Yakin, da Serahiya ɗan Hilkiya, ɗan Meshullam, ɗan Zadok, ɗan Merahiyot, ɗan Ahitub, mai lura da abubuwa a cikin gidan Allah, tare da ’yan’uwansu waɗanda suke aiki domin haikali, su 822 ne. Akwai kuma Adahiya ɗan Yeroham, ɗan Felaliya, ɗan Amzi, ɗan Zakariya, ɗan Fashhur, ɗan Malkiya, da ’yan’uwansa waɗanda suke shugabannin iyalai, su 242. Sai kuma Amashsai ɗan Azarel, ɗan Ahzai, ɗan Meshillemot, ɗan Immer, da ’yan’uwansa, su 128 ne muhimman mutane. Babban shugabansu shi ne Zabdiyel ɗan Haggedolim. Daga Lawiyawa kuwa akwai, Shemahiya ɗan Hasshub, ɗan Azrikam, ɗan Hashabiya, ɗan Bunni, da Shabbetai, da kuma Yozabad, biyu cikin shugabanni Lawiyawa waɗanda suke da nawayar aiki waje da gidan Allah. Sai kuma Mattaniya ɗan Mika, ɗan Zabdi, ɗan Asaf, shugaban da yake bi da hidimar godiya da kuma addu’a. Sai Bakbukiya, na biyu a cikin ’yan’uwansa; da Abda ɗan Shammuwa, ɗan Galal, ɗan Yedutun. Lawiyawan da suke cikin birni mai tsarki sun kai 284. Matsaran ƙofofi kuwa su ne, Akkub, da Talmon, da ’yan’uwansu waɗanda suke tsaron ƙofofi, su 172 ne. Sauran Isra’ilawa tare da firistoci, da Lawiyawa sun kasance a dukan garuruwan Yahuda, kowanne a mallakar kakansa. Ma’aikatan haikali sun zauna a kan tudun Ofel. Ziha, da Gishfa ne suke lura da su. Babban shugaban Lawiyawa a Urushalima shi ne Uzzi ɗan Bani, ɗan Hashabiya, ɗan Mattaniya, ɗan Mika. Uzzi yana ɗaya daga zuriyar Asaf, waɗanda suke mawaƙan da suke da nawayar hidima a gidan Allah. Mawaƙa sun bi umarnan sarki, a kan abin da za su yi kowace rana. Fetahahiya ɗan Meshezabel, ɗaya daga zuriyar Zera ɗan Yahuda ne, wakilin sarki cikin dukan al’amuran da suka shafi mutane. Game da ƙauyukan da filayensu, waɗansu mutanen Yahuda suka zauna a Kiriyat Arba da ƙauyukanta, da Dibon da ƙauyukanta, da Yekabzeyel da ƙauyukanta. Akwai su kuma a Yeshuwa, da Molada, da Bet-Felet, da Hazar Shuwal, da Beyersheba da ƙauyukanta. Akwai su a Ziklag, da Mekona da ƙauyukanta. Suna nan kuma a En Rimmon, da Zora, da Yarmut, da Zanowa, da Adullam da ƙauyukansu, da Lakish da gonakinta, da kuma Azeka da ƙauyukanta. Saboda haka sun yi zama tun daga Beyersheba har zuwa Kwarin Hinnom. Zuriyar mutanen Benyamin daga Geba sun zauna a Mikmash, da Aiya, da Betel da ƙauyukanta, da Anatot, da Nob, da Ananiya, da Hazor, da Rama, da Gittayim, da Hadid, da Zeboyim, da Neballat, da Lod, da Ono, da kuma a Kwarin Masu sana’a. Waɗansu gundumomin Lawiyawan Yahuda sun zauna a Benyamin. Waɗannan su ne firistoci da Lawiyawa waɗanda suka komo tare da Zerubbabel ɗan Sheyaltiyel da kuma Yeshuwa. Serahiya, Irmiya, Ezra, Amariya, Malluk, Hattush Shekaniya, Rehum, Meremot, Iddo, Ginneton, Abiya, Miyamin, Mowadiya, Bilga, Shemahiya, Yohiyarib, Yedahiya, Sallu, Amok, Hilkiya da Yedahiya. Waɗannan su ne shugabannin firistoci da ’yan’uwansu a kwanakin Yeshuwa. Lawiyawan su ne Yeshuwa, Binnuyi, Kadmiyel, Sherebiya, Yahuda, da kuma Mattaniya, wanda tare da ’yan’uwansa yake lura da waƙoƙin godiya. Bakbukiya da Unni, ’yan’uwansu sun tsaya ɗaura da su a hidimomi. Yeshuwa ne mahaifin Yohiyakim, Yohiyakim shi ne mahaifin Eliyashib, Eliyashib shi ne mahaifin Yohiyada, Yohiyada shi ne mahaifin Yonatan, Yonatan kuma mahaifin Yadduwa. A kwanakin Yohiyakim, waɗannan su ne shugabannin iyalan firistoci, na iyalin Serahiya, Merahiya; na iyalin Irmiya, Hananiya; na iyalin Ezra, Meshullam; na iyalin Amariya, Yehohanan; na iyalin Malluk, Yonatan; na iyalin Shebaniya, Yusuf; na iyalin Harim, Adna; na iyalin Merahiyot, Helkai; na iyalin Iddo, Zakariya; na iyalin Ginneton, Meshullam; na iyalin Abiya, Zikri; na iyalin Miniyamin da na Mowadiya, Filtai; na iyalin Bilga, Shammuwa; na iyalin Shemahiya, Yehonatan; na iyalin Yohiyarib, Mattenai; na iyalin Yedahiya, Uzzi; na iyalin Sallu, Kallai; na iyalin Amok, Eber; na iyalin Hilkiya, Hashabiya; na iyalin Yedahiya, Netanel. Shugabannin iyalin Lawiyawa a kwanakin Eliyashib, Yohiyada, Yohanan da Yadduwa, da kuma na firistoci, an rubuta su a zamanin mulkin Dariyus mutumin Farisa. Shugabannin iyali cikin zuriyar Lawi har zuwa lokacin Yohanan ɗan Eliyashib, an rubuta su a cikin littafin tarihi. Shugabannin Lawiyawa kuwa su ne Hashabiya, Sherebiya, Yeshuwa ɗan Kadmiyel, da ’yan’uwansu, waɗanda suka tsaya ɗaura da su don su yi yabo da kuma godiya, sashe ɗaya kan ba da amsa ga ɗaya sashen, kamar yadda Dawuda mutumin Allah ya umarta. Mattaniya, Bakbukiya, Obadiya, Meshullam, Talmon da Akkub su ne matsaran ƙofofi waɗanda suka yi tsaron ɗaukan ajiya a ƙofofi. Sun yi hidima a kwanakin Yohiyakim ɗan Yeshuwa, ɗan Yozadak, kuma a kwanakin Nehemiya gwamna da kuma na Ezra firist da kuma marubuci. A keɓewar katangar Urushalima, an nemi Lawiyawa daga inda suke zama aka kawo su Urushalima don su yi bikin miƙawa da farin ciki da waƙoƙin godiya da kuma kiɗin kuge, garaya da molo. Aka kuma tattara mawaƙa su ma daga yankin kewayen Urushalima, daga ƙauyukan Netofawa, daga Bet-Gilgal, da kuma daga wuraren Geba da Azmawet, gama mawaƙan sun gina wa kansu ƙauyuka kewaye da Urushalima. Sa’ad da firistoci da Lawiyawa suka tsarkake kansu da tsarki, sai suka tsarkake mutane, ƙofofi da kuma katanga. Sai na sa shugabannin Yahuda suka haura zuwa bisan katangar. Na kuma sa manyan ƙungiyoyi biyu na mawaƙa su miƙa godiya. Ɗaya ya haura zuwa bisan katangar zuwa dama, wajen Ƙofar Juji. Hoshahiya da rabin shugabannin Yahuda kuwa suka bi su, tare da Azariya, Ezra, Meshullam, Yahuda, Benyamin, Shemahiya, Irmiya, da waɗansu firistoci kuma da ƙahoni, da kuma Zakariya ɗan Yonatan, ɗan Shemahiya, ɗan Mattaniya, ɗan Mikahiya, ɗan Zakkur, ɗan Asaf, da ’yan’uwansa, Shemahiya, Azarel, Milalai, Gilalai, Ma’ai, Netanel, Yahuda da Hanani, tare da kayan kiɗi da Dawuda mutumin Allah ya umarta. Ezra malamin Doka ya jagoranci jerin gwanon. A Ƙofar Maɓuɓɓuga suka ci gaba kai tsaye suka haura matakalan Birnin Dawuda a kan hawa zuwa katangar suka wuce a bisa gidan Dawuda zuwa Ƙofar Ruwa wajen gabas. Ƙungiyar mawaƙa ta biyu suka yi jerin gwano a ɗaya gefen. Na bi su a bisan katangar, tare da rabin mutanen, muka wuce Hasumiya Tanderu zuwa Katanga Mai Faɗi, bisa Ƙofar Efraim, Ƙofar Yeshana, Ƙofar Kifi, Hasumiyar Hananel da kuma Hasumiya ɗari, har zuwa Ƙofar Tumaki. A Ƙofar Matsara suka tsaya. Ƙungiyoyin mawaƙa biyu da suka yi godiya suka ɗauki wurarensu a gidan Allah, haka ma ni, tare da rabin shugabanni, da kuma firistoci, Eliyakim, Ma’asehiya, Miniyamin, Mikahiya, Eliyohenai, Zakariya da Hananiya tare da ƙahoninsu, haka ma Ma’asehiya, Shemahiya, Eleyazar, Uzzi, Yehohanan, Malkiya, Elam da Ezer. Mawaƙan suka rera waƙoƙi a ƙarƙashin kulawar Yezrahiya. A rana ta uku kuma suka miƙa manyan hadayu, suna farin ciki domin Allah ya ba su farin ciki mai girma. Mata da yara suka yi farin ciki su ma. An ji ƙarar farin ciki da ake yi a Urushalima daga nesa. A lokacin an naɗa mutane su lura da ɗakunan ajiya don sadakoki, nunan fari da kuma zakka. Daga gonakin garuruwan da suke kewaye za su kawo sassan da Dokar ta umarta zuwa ɗakunan ajiya domin firistoci da Lawiyawa, gama Yahuda ya ji daɗin aikin firistoci da Lawiyawa. Sun yi hidimar Allahnsu da kuma hidimar tsarkakewa, kamar yadda mawaƙa da matsaran ƙofofi suka yi, bisa ga umarnin Dawuda da ɗansa Solomon. Gama tun dā, a kwanakin Dawuda da Asaf, akwai masu bi da mawaƙa da kuma na waƙoƙin yabo da na godiya ga Allah. Saboda haka a kwanakin Zerubbabel da Nehemiya, dukan Isra’ila suka ba da sashe na kowace rana domin mawaƙa da matsaran ƙofofi. Suka kuma keɓe sashe don sauran Lawiyawa, Lawiyawan kuma suka keɓe sashe don zuriyar Haruna. A wannan rana aka karanta Littafin Musa da ƙarfi a kunnuwan mutane aka kuma sami an rubuta cewa kada a karɓi mutumin Ammon ko mutumin Mowab cikin taron Allah, domin ba su taryi Isra’ila da abinci da ruwa ba amma suka yi hayar Bala’am don yă kira la’ana a kansu. (Amma Allahnmu, ya mai da la’anar ta zama albarka.) Sa’ad da mutane suka ji wannan doka, sai suka ware daga Isra’ila duk waɗanda suke na baƙon zuriya. Kafin wannan, an sa Eliyashib firist yă lura da ɗakuna ajiyar gidan Allahnmu. Yana da dangantaka na kurkusa da Tobiya, ya kuma tanada masa babban ɗakin da dā ake ajiyar hadayun hatsi da turare da kayayyaki haikali, da kuma zakan hatsi, sabon ruwan inabi da kuma mai da aka umarta don Lawiyawa, mawaƙa da kuma matsaran ƙofofi, da kuma sadakoki domin firistoci. Amma yayinda dukan wannan yake faruwa, ba ni a Urushalima, gama a shekara ta talatin da biyu na Artazerzes sarkin Babilon na dawo wurin sarki. A wani lokaci daga baya na nemi izininsa sai na koma zuwa Urushalima. A nan na ji game da mugun abin da Eliyashib ya aikata da ya tanada wa Tobiya ɗaki a filayen gidan Allah. Na ɓace rai ƙwarai na kuma zubar da dukan kayan gidan Tobiya daga ɗakin. Na umarta a tsarkake ɗakunan, sa’an nan na mayar da kayan gidan Allah a cikin ɗakunan, tare da hadayun hatsi da kuma turare. Na kuma ji cewa sassan da ake ba wa Lawiyawa ba a ba su ba, cewa kuma dukan Lawiyawa da mawaƙan da suke da hakkin hidima sun koma gonakinsu. Sai na tsawata wa shugabanni na kuma tambaye su na ce, “Me ya sa aka ƙyale gidan Allah?” Sa’an nan na kira su gaba ɗaya na sa su a wuraren aikinsu. Dukan Yahuda suka kawo zakan hatsi, sabon ruwan inabi da mai cikin ɗakunan ajiya. Na sa Shelemiya firist, Zadok marubuci, da wani Balawe mai suna Fedahiya su lura da ɗakunan ajiya na kuma sa Hanan ɗan Zakkur, ɗan Mattaniya ya zama mataimakinsu, domin an ɗauka waɗannan mutane amintattu ne. Aka ba su hakkin raban kayayyaki wa ’yan’uwansu. Ka tuna da ni saboda wannan, ya Allahna, kuma kada ka shafe abin da na yi da aminci domin gidan Allahna da kuma hidimarsa. A waɗannan kwanaki, na ga mutane a Yahuda suna matse ruwan inabi a ranar Asabbaci suna kuma kawo hatsi suna labta su a kan jakuna, tare da ruwan inabi, ’ya’yan inabi, ɓaure da kaya iri-iri. Suna kuma kawowa dukan wannan cikin Urushalima a ranar Asabbaci. Saboda haka na gargaɗe su a kan sayar da abinci a wannan rana. Mutane daga Taya waɗanda suke zama a Urushalima suna shigar da kifi da kaya iri-iri na ’yan kasuwa suna kuma sayar da su a Urushalima a ranar Asabbaci wa mutanen Yahuda. Sai na tsawata wa manyan Yahuda na ce musu, “Wanda irin mugun abu ke nan kuke yi, kuna ƙazantar da ranar Asabbaci? Kakanninku ba su yi irin waɗannan abubuwa ba, har Allahnmu ya kawo dukan masifun nan a kanmu da kuma a kan wannan birni? Yanzu kuna tsokanar fushi mai yawa a kan Isra’ila ta wurin ƙazantar da Asabbaci.” Sa’ad da inuwar yamma ya fāɗo a ƙofofin Urushalima kafin Asabbaci, na umarta a rufe ƙofofi kuma kada a buɗe sai Asabbaci ya wuce. Na kafa waɗansu mutanena a ƙofofin don kada a shigo da wani kaya a ranar Asabbaci. Sau ɗaya ko biyu, ’yan kasuwa da masu sayar da kowane irin kaya suka kwana waje da Urushalima. Amma na ja kunnensu na ce, “Me ya sa kuke kwana kusa da katanga? In kuka ƙara yin haka, zan kama ku.” Daga wannan lokaci har zuwa gaba ba su ƙara zuwa a ranar Asabbaci ba. Sai na umarci Lawiyawa su tsarkake kansu su kuma tafi su yi tsaron ƙofofi don a kiyaye ranar Asabbaci da tsarki. Ka tuna da ni saboda wannan shi ma, ya Allahna, ka nuna mini jinƙai bisa ga madawwamiyar ƙaunarka. Ban da haka, a waɗannan kwanakin na ga mutanen Yahuda waɗanda suka auri mata daga Ashdod, Ammon da Mowab. Rabin ’ya’yansu suna yaren Ashdod ko kuwa wani yare na waɗansu mutane, ba su kuwa san yadda za su yi Yahudanci ba. Na tsawata musu na kuma kira la’ana a kansu. Na bugi waɗansu mutane na kuma ja gashin kansu. Na sa suka yi rantsuwa da sunan Allah na ce, “Kada ku ba da ’ya’yanku mata aure ga ’ya’yansu maza, ba kuwa za ku auri ’ya’yansu mata wa ’ya’yanku maza ko wa kanku ba. Ba don aure-aure irin waɗannan ne Solomon sarkin Isra’ila ya yi zunubi ba? A cikin yawancin al’ummai babu sarki kamar sa. Allahnsa ya ƙaunace shi, Allah kuma ya mai da shi sarki a kan dukan Isra’ila, amma duk da haka baren mata suka rinjaye shi ga zunubi. Yanzu za mu ji cewa ku ma kuna yin duk wannan mugunta kuna zama marasa aminci ga Allahnmu ta wurin auren baren mata?” Ɗaya daga cikin ’ya’yan Yohiyada maza, ɗan Eliyashib babban firist, surukin Sanballat mutumin Horon ne. Na kuwa kore shi daga wurina. Ka tuna da su, ya Allahna, domin sun ƙazantar da aikin firist da kuma alkawarin aikin firist da na Lawiyawa. Saboda haka na tsarkake firistoci da Lawiyawa daga kowane baƙon abu, na kuma ba su aikinsu, kowa ga aikinsa. Na kuma yi tanadi don sadakokin itace a ƙayyadaddun lokuta, da kuma don nunan fari. Ka tuna da ni da alheri, ya Allahna. Ga abin da ya faru a zamanin Zerzes. Zerzes ya yi mulki bisan larduna 127 daga Indiya zuwa Kush. A lokacin nan, Sarki Zerzes ya yi mulki daga gadon sarauta, cikin mazaunin masarautar Shusha. A shekara ta uku ta mulkinsa, ya yi wa dukan hakimansa da ma’aikatansa liyafa. Shugabannin mayaƙan Farisa, da Mediya, da yerimai; da kuma hakimai na lardunan suka kasance. Kwanaki 180 cif, ya nuna yawan dukiyar masarautarsa, da ɗaukakarta da kuma darajar girmansa. Sa’ad da waɗannan kwanaki suka wuce, sai sarki ya yi liyafa a cikin lambun da aka shinge na fadar sarki wadda ta ɗauki kwana bakwai wa dukan mutane daga ƙarami har zuwa babba, waɗanda suke zama a masarautar Shusha. Lambun yana da fararen labulen da aka rataye da shunayya na lallausan lilin, da aka ɗaura da igiyoyin fararen lilin, da yadin jan garura, haɗe da zoban azurfa a kan ginshiƙin farin ƙasa. A nan, akwai kujeru na zinariya da na azurfa a kan daɓe mai ado da aka yi da duwatsu masu daraja, da farin ƙasa, da fararen duwatsun wuya, da waɗansu duwatsu masu tsada. Aka rarraba ruwan inabi cikin kwaf na zinariya, kowanne kuwa dabam yake da ɗayan. Ruwan inabin kuwa yana da yawa, bisa ga wadatar sarki. Bisa ga umarnin sarki, aka bar kowane baƙo yă sha yadda ya ga dama, gama sarki ya umarci dukan bayin da suke rarraba ruwan inabin su ba wa kowa abin da yake so. Sarauniya Bashti ita ma ta yi liyafa saboda mata a fadar Sarki Zerzes. A rana ta bakwai, sa’ad da Sarki Zerzes, ya yi tilis da ruwan inabi, sai ya umarci bābānni bakwai waɗanda suke yin masa hidima, wato, Mehuman, Bizta, Harbona, Bigta, Abagta, Zetar da Karkas, su kawo Sarauniya Bashti a gabansa, sanye da rawanin sarautarta, don ta nuna kyanta wa mutane da kuma hakimai, gama ita kyakkyawa ce ƙwarai. Amma da masu hidima suka ba da umarnin sarki, sai Sarauniya Bashti ta ƙi zuwa. Wannan ya ɓata wa sarki rai, ya kuma yi fushi ƙwarai. Da yake, al’ada ce sarki yă nemi shawara daga sanannu a batun doka da adalci, sai ya yi magana da masu hikima waɗanda suke fahimtar lokuta suke kuma mafi kusa da sarki. Waɗannan masu hikima kuwa su ne, Karshena, Shetar, Admata, Tarshish, Meres, Marsena da kuma Memukan. Su hakimai bakwai ne na Farisa da Mediya waɗanda suke da dama ta musamman ta kaiwa ga sarki, suke kuma da matsayi mafi girma a masarautar. Ya ce, “Bisa ga doka, me za a yi wa Sarauniya Bashti? Gama ta ƙi yin biyayya da umarnin sarki Zerzes da bābānni suka kai mata?” Sai Memukan ya amsa a gaban sarki da hakimai ya ce, “Sarauniya Bashti ta yi laifi, ba ga sarki kaɗai ba, amma ga dukan hakimai ma, da kuma mutanen dukan lardunan sarki Zerzes. Domin halin Sarauniya zai zama sananne ga dukan mata, ta haka kuwa za su ƙasƙantar da mazansu su kuma ce, ‘Sarki Zerzes ya umarta a kawo Sarauniya Bashti a gabansa, amma ta ƙi zuwa.’ Wannan rana matan hakiman Farisa da na Mediya waɗanda suka ji game da halin sarauniya, za su yi haka wa dukan hakiman sarki. Zai zama babu ƙarshen rashin bangirma da kuma reni. “Saboda haka, in ya gamshi sarki, bari yă ba da hatimi na sarauta, bari kuma a rubuta shi cikin dokokin Farisa da Mediya, wanda ba za a iya sokewa ba, cewa Bashti ba za tă ƙara zuwa gaban sarkin Zerzes ba. Bari kuma sarki yă ba da matsayinta na sarauta ga wata, wadda ta fi ta. Ta haka, sa’ad da aka yi shelar dokar sarki ko’ina a fāɗin masarautarsa, dukan mata za su ba wa mazansu girma, daga ƙarami har zuwa babba.” Sarki da hakimansa suka gamsu da wannan shawara. Saboda haka sarki ya yi kamar yadda Memukan ya faɗa. Ya aika da saƙo zuwa ga dukan ɓangarorin masarautar, zuwa ga kowane lardi a irin nasa rubutu, zuwa kuma ga kowane mutane a nasu harshe, ana shelar a kowane yare na mutane, cewa kowane mutum yă zama mai mulki bisa gidansa. Daga baya sa’ad da fushin Sarki Zerzes ya huce, sai ya tuna da Bashti da abin da ta yi, da kuma dokar da ya bayar game da ita. Sai masu hidimar sarki na musamman, suka kawo shawara cewa, “Bari a nemi, kyawawan budurwai saboda sarki. Bari sarki yă naɗa komishinoni a kowane yanki na masarautarsa, domin su kawo dukan waɗannan kyawawan ’yan mata cikin harabar mazaunin masarautar a Shusha. Bari a sa su a hannun Hegai, bābān sarki, wanda yake lura da mata, bari kuma a yi musu kulawa ta musamman. Sa’an nan bari yarinyar da ta gamshi sarki, tă zama sarauniya a maimakon Bashti.” Wannan shawara ta gamshi sarki, ya kuwa yi na’am da ita. To, a cikin mazaunin masarauta a Shusha, akwai wani mutumin Yahuda, daga Kabilar Benyamin mai suna Mordekai, ɗan Yayir, ɗan Shimeyi, ɗan Kish, wanda Nebukadnezzar sarkin Babilon ya ɗauka tare ’yan zaman bauta cikin waɗanda ya ɗauko daga Urushalima, tare da Yekoniya, sarkin Yahuda. Mordekai yana da wata ’yar kawunsa mai suna Hadassa, wanda ya yi reno, ba ta da mahaifi ko mahaifiya. Ita ce yarinyar da aka santa da suna Esta. Kyakkyawa ce ƙwarai. Mordekai dai ya ɗauke ta tamƙar ’yarsa sa’ad da mahaifinta da mahaifiyarta suka mutu. Da aka yi shelar umarni da dokar sarki, sai aka kawo ’yan mata masu yawa a mazaunin masarauta a Shusha, aka kuma sa su ƙarƙashin kulawar Hegai. Aka kawo Esta ma zuwa fadar sarki, aka danƙa ta wa Hegai, wanda yake lura da mata. Yarinyar ta gamshe shi, ta kuma sami tagomashinsa. Nan da nan ya tanada mata, ya ba ta man shafawa da abinci na musamman. Ya ba ta bayi mata bakwai da aka zaɓa daga fadar sarki. Ya kuma kai ta tare da bayinta zuwa wuri mafi kyau na gidan matan kulle. Esta ba tă bayyana asalin al’ummarta da na iyalinta ba, domin Mordekai ya hana yin haka. Kowace rana Mordekai yana kai da komowa kusa da harabar filin gidan matan kulle, domin ya san yadda Esta take, da kuma abin da yake faruwa da ita. Kafin a kai kowace yarinya wurin Sarki Zerzes, sai ta gama watanni goma sha biyu cif ana yin mata kwalliyar da aka tsara, akan ɗauki watanni shida ana shafa mata man mur, a ɗauki watanni shida kuma ana shafa mata man ƙanshi da kayan shafe-shafe. A kuma koya mata yadda za tă tafi wurin sarki. Aka ba ta duk abin da take so ta riƙe daga gidan matan kulle zuwa fadar sarki. Da yamma za tă tafi can, da safe kuma ta dawo wani ɓangaren gidan matan kullen da yake a ƙarƙashin kulawar Sha’ashgaz, bābā na sarki, wanda yake lura da ƙwarƙwarai. Ba ta dawowa wurin sarki sai in ta gamshe shi, sai ya kuma kira ta da suna. Sa’ad da lokaci ya yi da Esta (yarinyar da Mordekai ya ɗauka tamƙar ’yarsa, ’yar kawunsa Abihayil) za tă shiga wurin sarki, ba tă nemi a ba ta kome ba in ban da abin da Hegai, bābān sarki mai lura da gidan matan kulle, ya ba da shawara. Esta kuwa ta sami tagomashin kowa da ya ganta. Aka kai Esta wurin Sarki Zerzes a mazaunin sarauta a wata na goma, watan Tebet, a shekara ta bakwai ta mulkinsa. To, sarki ya so Esta fiye da duk sauran matan, ta kuma sami tagomashinsa da kuma yardarsa fiye da duk sauran budurwai. Saboda haka ya sa rawanin sarauta a kanta, ya kuma mai da ita sarauniya a maimakon Bashti. Sarki kuwa ya yi ƙasaitacciyar liyafa, liyafar Esta, wa dukan hakimansa da shugabannin masarautarsa. Ya yi shelar hutu ko’ina a larduna, ya kuma raba kyautai a yalwace irin na sarauta. Sa’ad da aka tara budurwai karo na biyu, Mordekai kuwa yana zama a bakin ƙofar sarki. Amma Esta ta ɓoye asalin iyalinta da na al’ummarta yadda Mordekai ya ce ta yi, gama ta ci gaba da bin umarnan Mordekai yadda take yi sa’ad da yake renonta. Sa’ad da Mordekai yake zaune a bakin ƙofar sarki, sai Bigtana da Teresh, biyu daga cikin hafsoshin sarki masu gadin ƙofar shiga, suka yi fushi, suka kuma ƙulla su kashe sarki Zerzes. Mordekai kuwa ya sami labarin makircin, ya kuma faɗa wa Sarauniya Esta, wadda ta faɗa wa sarki, ta kuma nuna masa cewa Mordekai ne ya ji. Sa’ad da aka bincika labarin aka kuma iske gaskiya ne, sai aka rataye hafsoshin nan biyu a wurin rataye mai laifi. Aka rubuta dukan wannan a cikin littafin tarihi a gaban sarki. Bayan waɗannan al’amura, sai Sarki Zerzes ya girmama Haman ɗan Hammedata, mutumin Agag, ya ɗaukaka shi, ya kuma ba shi matsayi mafi girma fiye da na dukan sauran hakiman. Dukan masu hidimar da suke a ƙofar sarki suka riƙa durƙusa suna ba wa Haman girma, gama sarki ya ba da umarni a yi masa haka. Amma Mordekai bai durƙusa ya ba shi girma ba. Sa’an nan masu hidimar da suke a ƙofar sarki suka tambaye Mordekai, “Me ya sa ba ka yin biyayya da umarnin sarki?” Kowace rana suna masa magana, amma ya ƙi yă yi. Saboda haka, suka faɗa wa Haman game da wannan don su ga ko za a jure da halin Mordekai, gama ya faɗa musu cewa shi mutumin Yahuda ne. Sa’ad da Haman ya ga cewa Mordekai ba ya durƙusa ko yă girmama shi, sai ya fusata. Da yake an faɗa masa asalin Mordekai, sai ya ga a kashe Mordekai kaɗai ba zai biya masa bukata ba. A maimakon haka, Haman ya nemi hanya a hallaka dukan mutanen Mordekai, wato, Yahudawa, a ko’ina a dukan masarautar Zerzes. A shekara ta goma sha biyu ta Sarki Zerzes, a wata na farko, watan Nisan, sai suka jefa fur (wato, ƙuri’a) a gaban Haman don a zaɓi rana da watan da zai dace da ƙulle-ƙullen. Sai ƙuri’a ta fāɗa a kan wata na goma sha biyu, wato, watan Adar. Sai Haman ya ce wa Sarki Zerzes, “Akwai waɗansu mutanen da suke a warwatse, sun kuma bazu a cikin mutane cikin dukan lardunan masarautarka, waɗanda al’adunsu sun yi dabam da na dukan sauran mutane. Mutanen nan ba sa biyayya da dokokin sarki; ba zai yi wa sarki kyau a jure su ba. In ya gamshi sarki, bari a yi doka, don a hallaka su, zan kuma sa talenti dubu goma na azurfa a cikin ma’ajin fada saboda mutanen da suka aikata wannan sha’ani.” Saboda haka sarki ya zare zoben hatimi daga yatsarsa, ya ba wa Haman ɗan Hammedata, mutumin Agag, abokin gāban Yahudawa. Sarki ya ce wa Haman, “Ka riƙe kuɗin, ka kuma yi da mutanen yadda ka ga dama.” Sa’an nan aka kira magatakardun sarki a rana ta goma sha uku na wata na fari. Suka rubuta dukan umarnin Haman a irin rubutun kowane lardi, kuma cikin harshen kowane mutane, zuwa ga shugabannin mahukuntai na sarki, da gwamnonin larduna dabam-dabam, da kuma hakiman mutane dabam-dabam. Aka rubuta waɗannan a sunan Sarki Zerzes da kansa, aka kuma hatimce da zobensa. Aka aika ’yan-kada-tă-kwana da saƙoni zuwa dukan lardunan sarki da umarni a hallaka, a karkashe, a kuma kawar da dukan Yahudawa, manya da ƙanana, mata da yara, a kuma washe kayayyakinsu. Za a ba da kofin rubutun a matsayin doka a kowane lardi, a kuma sanar da mutanen kowace al’umma, domin su zauna da shiri don wannan rana. Bisa ga umarnin sarki, sai ’yan-kada-tă-kwana, suka tafi da sauri. Aka ba da umarni a mazaunin masarauta da yake a Shusha. Sai Sarki da Haman suka zauna don su sha, amma birnin Shusha ya ruɗe. Sa’ad da Mordekai ya sami labari game da dukan abin da aka yi, sai ya yayyage rigunansa, ya sanya tsummokin makoki, ya zuba toka a kā, ya kuma shiga ciki birni yana kuka mai zafi da ƙarfi. Amma ya kai bakin ƙofar sarki ne kawai, gama ba a yarda wani sanye da tsummokin makoki yă shiga cikin birni ba. Aka yi makoki sosai da azumi, da kuka mai zafi a cikin Yahudawa a kowane lardin da aka kai doka da kuma umarnin sarki. Mutane da yawa suka kwanta a cikin tsummokin makoki da kuma toka. Sa’ad da bayi da bābānnin Esta suka zo suka faɗa mata game da Mordekai, sai ta damu ƙwarai. Ta aika masa da riguna domin yă sa a maimakon tsummokin makoki, amma ya ƙi. Sai Esta ta kira Hatak, ɗaya daga cikin bābānnin sarkin da aka ba shi aikin lura da ita, ta umarce shi yă yi tambaya me ke damun Mordekai da kuma me ya jawo haka. Saboda haka Hatak ya tafi wurin Mordekai a dandalin birni, a gaban ƙofar sarki. Mordekai ya faɗa masa duk abin da ya faru da shi, haɗe da yawan kuɗin da Haman ya yi alkawari zai zuba a ma’ajin fada don a hallaka Yahudawa. Ya kuma ba shi kofi na rubutaccen doka na kakkaɓe su, wanda aka wallafa a Shusha don yă nuna wa Esta, yă bayyana mata. Mordekai ya faɗa wa Hatak yă iza ta tă tafi gaban sarki domin tă yi roƙo don jinƙai, tă kuma roƙe shi saboda mutanenta. Hatak ya koma ya ba wa Esta rahoton abin da Mordekai ya faɗa. Sa’an nan Esta ta umarce Hatak yă ce wa Mordekai, “Dukan hafsoshin sarki da mutanen lardunan sarki sun san cewa duk wanda ya tafi wurin sarki a shirayi na ciki, mace ko namiji, ba tare da an kira shi ba, doka ɗaya ce take kan mutum, wato, kisa. Abu guda kawai da ya sha bamban shi ne sai wanda sarki ya miƙa wa sandan sarauta na zinariya don yă rayu. Kwana talatin ke nan ba a kira ni in tafi wurin sarki ba.” Sa’ad da aka kai wa Mordekai rahoton maganan Esta, sai ya mayar da wannan amsa wa Esta cewa, “Kada ki yi tsammani cewa don kina a cikin gidan sarki, ke kaɗai cikin dukan Yahudawa za ki tsira. Gama in kin yi shiru a wannan lokaci, taimako da ceto zai zo daga wani wuri saboda Yahudawa, amma ke da gidanki za ku hallaka. Wa ya san ko saboda irin wannan lokaci ne kika sami wannan muƙami?” Sai Esta ta aika da wannan amsa ga Mordekai cewa, “Ka tafi, ka tattara dukan Yahudawan da suke Shusha, ku yi azumi saboda ni. Kada ku ci ko ku sha, dare da rana har kwana uku. Ni kuwa da bayina za mu yi azumi yadda kuke yi. Idan aka yi haka, zan tafi wurin sarki, ko da yake wannan karya doka ce. Idan na hallaka, to, na hallaka.” Saboda haka, Mordekai ya tafi, ya aikata dukan umarnan Esta. A rana ta uku, Esta ta sanya rigunanta na sarauta, ta tafi ta tsaya a harabar fada, a gaban zaure sarki. Sarki yana zaune a kan gadon sarautarsa a zauren, yana fuskantar ƙofar shiga. Sa’ad da ya ga Sarauniya Esta tsaye a harabar, sai ya ji daɗin ganinta, ya miƙa mata sandan sarauta na zinariya da take hannunsa. Sai Esta ta matsa kusa ta taɓa kan sandan. Sai sarki ya ce mata, “Me kike so, Sarauniya Esta? Mene ne roƙonki? Kai, ko rabin masarautata ce, za a ba ki.” Esta ta ce, “In ya gamshi sarki, bari sarki, tare da Haman su zo wurin liyafar da na shirya wa sarki yau.” Sai sarki ya ce, “Maza a kawo Haman don mu yi abin da Esta ta roƙa.” Saboda haka, sarki da Haman suka tafi liyafar da Esta ta shirya. Yayinda suke shan ruwan inabi, sarki ya sāke ce wa Esta, “Yanzu, mece ce bukatarki? Za a biya miki shi. Kuma mene ne roƙonki? Kai, ko rabin masarautata ce, za a ba ki.” Esta ta amsa ta ce, “Bukatata da kuma roƙona shi ne, in na sami tagomashi a wurin sarki, in kuma sarki ya yarda yă biya mini bukatata, yă kuma ji roƙona, bari sarki da Haman su zo gobe wurin liyafar da zan shirya musu. Sa’an nan zan amsa tambayar sarki.” Haman ya fita a ranan da murna, ya kuma ji daɗi. Amma sa’ad da ya ga Mordekai a bakin ƙofar sarki, ya kuma lura cewa bai tashi, ko yă nuna bangirma a gabansa ba, sai ya cika da fushi. Duk da haka, Haman ya cije, ya tafi gida. Sai ya kira abokansa da kuma matarsa, Zeresh, ya yi ta taƙama game da ɗumbun wadatarsa, da yawan ’ya’yansa maza, da dukan yadda sarki ya girmama shi, ya kuma ɗaga shi bisan sauran hakimai da shugabanni. Haman ya ƙara da cewa, “Ba duka ke nan ba, kai, ni ne kaɗai mutumin da Sarauniya Esta ta gayyata yă tafi tare da sarki zuwa liyafar da ta shirya. Ta sāke gayyace ni tare da sarki gobe. Amma dukan wannan bai biya mini bukata ba, muddin ina ganin wannan mutumin Yahudan nan Mordekai, yana zama a bakin ƙofar sarki.” Matarsa Zeresh, da dukan abokansa suka ce masa, “Ka sa a gina wurin rataye mai laifi, mai tsawo, ƙafa saba’in da biyar, da safe kuwa ka ce wa sarki a rataye Mordekai a kansa. Sa’an nan ka tafi cin abincin dare tare da sarki da murna.” Wannan shawarar ta faranta wa Haman rai, ya kuma sa aka gina wurin rataye mai laifi. A daren nan, sarki bai iya barci ba, saboda haka ya ba da umarni a kawo, a kuma karanta masa littafin tarihi na shekara-shekara, da rubutaccen labarin mulkinsa. Aka tarar, a rubuce a ciki, cewa Mordekai ya tone ƙulle-ƙullen Bigtana da Teresh, biyu daga hafsoshin sarki, waɗanda suke tsaron mashigin ƙofa, waɗanda suka ƙulla su kashe Sarki Zerzes. Sarki ya ce, “Wace girma da daraja ce aka ba wa Mordekai saboda wannan?” Masu hidimarsa suka ce, “Ba a yi masa wani abu ba.” Sarki ya ce, “Wa yake a haraba?” Daidai lokacin kuwa Haman ya shigo harabar waje na fada don yă yi magana da sarki a kan a rataye Mordekai a wurin rataye mai laifin da ya shirya. Masu yi wa sarki hidima, suka amsa, “Haman yana tsaye a haraba.” Sarki ya umarta, “A kawo shi ciki.” Sa’an nan Haman ya shigo, sai sarki ya ce masa, “Me ya kamata a yi wa mutumin da sarki yake jin daɗi yă girmama?” Haman dai ya yi tunani a ransa ya ce, “Wane ne sarki zai girmama in ba ni ba?” Sai ya amsa wa sarki cewa, “Saboda mutumin da sarki yake jin daɗi yă girmama, bari a kawo rigar sarautar da sarki ya taɓa sawa, da kuma dokin da sarki ya taɓa hawa, wanda aka sa kambin sarauta a kai. Sa’an nan, bari a ba da rigar da kuma dokin wa ɗaya daga cikin manyan sarakuna mafi kirki na sarki. Bari shi kuma yă sa wannan riga wa mutumin da sarki yake jin daɗi yă girmama, a kuma bi da shi a bisan doki ko’ina a titunan birni, ana shela a gabansa ana cewa, ‘Wannan shi ne abin da ake yin wa mutumin da sarki yake jin daɗi yă girmama!’ ” Sarki ya umarci Haman ya ce, “Tafi yanzu ka karɓi rigar da dokin, ka kuma yi yadda ka shawarta wa Mordekai, mutumin Yahudan nan, wanda yake zama a bakin ƙofar sarki. Kada ka kāsa yin kome daga cikin abin da ka faɗa.” Saboda haka, Haman ya karɓo rigar da dokin. Ya sa wa Mordekai rigar, ya kuma bi da shi a kan doki ko’ina a titunan birnin, yana shela a gabansa yana cewa, “Wannan shi ne abin da ake yi wa mutumin da sarki yake jin daɗi yă girmama!” Daga baya, Mordekai ya dawo zuwa ƙofar sarki. Amma Haman ya ruga gida, kansa a rufe, saboda baƙin ciki. Ya je ya faɗa wa matarsa Zeresh, da dukan abokansa, me ya same shi. Masu ba shi shawara, da matarsa Zeresh, suka ce masa, “Idan Mordekai, wanda ka fara fāɗuwa a gabansa, daga zuriyar Yahudawa yake, to, ba za ka yi nasara a kansa ba, tabbatacce za ka fāɗi a gabansa!” Suna cikin magana da shi ke nan, sai ga bābānnin sarki, suka iso suka kuma hanzarta da Haman zuwa liyafar da Esta ta shirya. Saboda haka sarki da Haman suka tafi cin abinci wurin sarauniya Esta. Yayinda suke shan ruwan inabi a rana ta biyun nan, sai sarki ya sāke tambaya, “Sarauniya Esta, me kike so? Za a ba ki. Mene ne roƙonki? Ko da rabin masarautata ne, za a ba ki.” Sai Sarauniya Esta ta amsa ta ce, “In na sami tagomashi a wurinka, ya sarki, in kuma mai girma ya yarda, a bar ni da raina, wannan shi ne roƙona. Ka kuma sa kada a kashe mutanena, wannan ita ce bukata. Gama an sayar da ni da mutanena don a hallaka, a karkashe mu, a kuma ƙi mu. Da a ce an sayar da mu kamar bayi maza da mata ne, da na yi shiru, domin wannan zai zama abin da bai taka kara ya karye ba, har da za a dami sarki a kai.” Sarki Zerzes ya tambayi Sarauniya Esta ya ce, “Wane ne shi? Ina mutumin da ya yi ƙarfin halin yin wannan karambani?” Esta ta ce, “Maƙiyi da abokin gāban, shi ne wannan mugun Haman.” Sai Haman ya tsorota a gaban sarki da sarauniya. Sarki ya tashi cikin fushi, ya bar ruwan inabinsa, ya fita zuwa cikin lambun fada. Amma da Haman ya gane cewa sarki ya riga ya yanke shawara a kan ƙaddararsa, ya dakata domin yă roƙi sarauniya Esta saboda ransa. Sarki yana dawowa daga lambun fada zuwa babban zauren liyafan ke nan, sai ga Haman ya fāɗi a kan shimfiɗar da Esta take zaune. Sarki ya tā da murya da ƙarfi ya ce, “Har ma zai ci mutuncin sarauniya yayinda take tare da ni a cikin gida?” Sarki bai ma rufe baki ba, sai bayin sarki suka rufe fuskar Haman. Sai Harbona, ɗaya daga cikin bābānni masu yi wa sarki hidima ya ce, “Akwai wurin rataye mai laifi da tsayinsa ya kai ƙafa saba’in da biyar yana nan tsaye kusa da gidan Haman. Ya gyara shi ne domin a rataye Mordekai, wanda ya yi cece sarki wanda ya tone makircin masu niyya su hallaka sarki.” Sai sarki ya ce, “Ku rataye shi a kansa!” Saboda haka suka rataye Haman a kan wurin rataye mai laifin da shi Haman ya shirya saboda Mordekai. Sa’an nan sarki ya huce. A wannan rana, Sarki Zerzes ya ba wa Esta mallakar Haman, abokin gāban Yahudawa. Mordekai kuma ya zo gaban sarki, gama Esta ta faɗa yadda ta haɗa dangi da shi. Sarki ya cire zobensa na hatimi, wanda ya karɓo daga Haman ya ba Mordekai. Esta kuma ta naɗa shi a kan mallakar Haman. Esta ta sāke roƙon sarki, ta fāɗi a ƙafafunsa tana kuka. Ta roƙe shi yă kawo ƙarshen mugun shirin nan na Haman, mutumin Agag; wanda ya shirya a kan Yahudawa. Sai sarki ya miƙa wa Esta sandan sarauta na zinariya, ta kuwa tashi ta tsaya a gabansa. Ta ce, “In sarki ya yarda, in kuma na sami tagomashi daga gare shi, idan kuma ya gamshe shi yă yi abin da yake daidai, idan yana jin daɗina, bari a rubuta umarni a soke hukuncin saƙonin da Haman ɗan Hammedata, mutumin Agag, ya shirya ya kuma rubuta domin a hallaka Yahudawa a dukan lardunan sarki. Gama yaya zan jure da ganin masifa ta faɗa a kan mutanena? Yaya zan jure in ga an hallaka iyalina?” Sarki Zerzes ya amsa wa Esta da Mordekai mutumin Yahuda, “Domin Haman ya kai wa Yahudawa hari, na ba da mallakarsa ga Esta, an kuma rataye shi a wurin rataye mai laifi. Yanzu ku rubuta wata doka, a sunan sarki, a madadin Yahudawa, yadda kuka ga ya fi kyau ku kuma hatimce ta da zoben hatimin sarki, gama babu takardar da aka rubuta da sunan sarki, aka kuma hatimce da zobensa da za a iya sokewa.” Nan da nan aka kira magatakardun fada, a ranar ashirin da uku ga watan uku, wato, watan Siban. Suka rubuta dukan umarnan Mordekai ga Yahudawa, da kuma ga shugabanni, da gwamnoni, da hakiman larduna 127 tun daga Indiya har zuwa Kush. Aka rubuta waɗannan umarnan a rubutun kowane lardi, da kuma cikin harshen kowane mutane. Aka kuma rubuta ga Yahudawa a rubutunsu da harshensu. Mordekai ya yi rubutu da sunan Sarki Zerzes, ya hatimce saƙonin da zoben hatimin sarki, ya kuma aika da su ta hannun masu ’yan aika a kan dawakai, waɗanda sukan hau dawakai masu gudu sosai, da aka yi kiwonsu musamman saboda sarki. Dokar sarki ta ba wa Yahudawa a kowace birni izini su taru, su kuma kāre kansu, domin su hallaka, su kashe, su kuma hallaka kowace ƙungiyar mayaƙa, na kowace ƙasa, ko lardi, da wataƙila za su kai musu, da matansu, da yaransu hari; su kuma washe mallakar abokan gābansu. Ranar da aka shirya domin Yahudawa su yi wannan a dukan lardunan Sarki Zerzes, ita ce ranar goma sha uku ga watan goma sha biyu, wato, watan Adar. Za a ba da kofi na rubutacciyar dokar a matsayin ƙa’ida a kowane lardi, a kuma sanar wa mutanen kowace ƙasa, domin Yahudawa su zauna da shiri a ranar, domin su ɗau fansa a kan maƙiyansu. ’Yan aikan, a kan dawakan fada, suka fita a guje, umarnin sarki yana iza su. Aka kuma ba da dokar a mazaunin masarauta wadda take Shusha. Mordekai kuwa ya fita a gaban sarki da rigunan sarauta, masu ruwan shuɗi, da fari, da babban kambi na zinariya, da alkyabba ta lilin mai ruwan shunayya. Aka yi sowa don murna a birnin Shusha. Ga Yahudawa kuwa, lokaci ne na murna da farin ciki, da jin daɗi da bangirma. A kowane lardi da kowace birni, ko’ina da dokar sarki ta kai, aka yi farin ciki a cikin Yahudawa, cike da bukukkuwa. Yawan mutane da waɗansu ƙasashe suka zama Yahudawa, don tsoron Yahudawa ya kama su. A rana ta goma sha uku na watan goma sha biyu, wato, watan Adar ne za a aiwatar da dokar da sarki ya umarta. A wannan rana, abokan gāban Yahudawa suka sa zuciya za su sha ƙarfinsu, amma yanzu Zerzes ya canja, Yahudawa kuma suka yi galiba a bisa waɗanda suka ƙi jininsu. Yahudawa suka tattaru a cikin biranensu a dukan lardunan Sarki Zerzes don su kai wa waɗanda suka nemi a hallaka su hari. Babu wanda ya tasar musu domin mutanen dukan sauran al’ummai sun jin tsoronsu. Dukan sarakuna larduna, da hakimai, da gwamnoni da kuma ma’aikatan sarki suka taimaki Yahudawa, domin tsoron Mordekai ya kama su. Mordekai babban mutum ne a fada, sunansa ya kai ko’ina a lardunan, ikonsa ya yi ta ƙasaita gaba-gaba. Yahudawa suka karkashe dukan abokan gābansu da takobi, suka karkashe waɗanda suka ƙi jininsu, suka kuma hallaka su yadda suka ga dama. A mazaunin masarautar a Shusha, Yahudawa suka karkashe, suka kuma hallaka mutum ɗari biyar. Suka kuma kashe Farshandata, da Dalfon, da Asfata, da Forata, da Adaliya, da Aridata, da Farmashta, da Arisai, da Aridai da kuma Baizata, ’ya’ya maza goma na Haman ɗan Hammedata, abokin gāban Yahudawa. Amma ba su taɓa dukiyarsu ba. A wannan rana, aka ba wa sarki rahoton yawan mutanen da aka kashe a mazaunin masarauta, a Shusha. Sarki ya ce wa Sarauniya Esta, “Yahudawa sun karkashe, suka kuma hallaka mutum ɗari biyar, da kuma ’ya’ya maza goma na Haman a mazaunin masarauta a Shusha. Me suka yi a sauran lardunan sarki? Yanzu kuma mene ne roƙonki? Za a ba ki. Mece ce bukatarki? Za a biya miki.” Esta ta ce, “In sarki ya yarda, yă ba wa Yahudawa da suke Shusha izini su aikata dokan nan gobe kuma, bari kuma a rataye ’ya’ya maza goma na Haman a kan gumagumai.” Sai sarki ya ba da umarni a yi haka ɗin. Aka ba da doka a Shusha, aka kuma rataye ’ya’ya maza goma na Haman. Yahudawan da suke Shusha suka taru a ran goma sha huɗu na watan Adar suka kuma karkashe mutum ɗari uku a Shusha, amma ba su taɓa dukiyarsu ba. Ana cikin haka, sai saura Yahudawa waɗanda suke lardunan sarki su ma suka taru domin su kāre kansu su kuma sami hutu daga abokan gābansu. Suka karkashe mutum dubu saba’in da biyar amma ba su taɓa dukiyarsu ba. Wannan ya faru a ran goma sha uku na watan Adar. A rana ta goma sha huɗu kuwa suka huta, suka kuma mai da ita ranar biki da kuma ta farin ciki. Amma Yahudawan da suke a Shusha suka taru a rana ta goma sha uku da ta sha huɗu, sa’an nan a rana ta goma sha biyar suka huta, suka kuma mai da ita ranar biki da ta farin ciki. Shi ya sa Yahudawan ƙauyuka, waɗanda suke zama a karkara, suke kiyaye rana ta goma sha huɗu ta watan Adar a matsayin ranar farin ciki da ta biki, ranar ba da kyautai ga juna. Sai Mordekai ya rubuta waɗannan abubuwa, ya kuma aika wasiƙu ga dukan Yahudawa ko’ina a lardunan Sarki Zerzes, na kusa da na nesa. Ya sa su yi bikin kowace shekara a ranaku goma sha huɗu da goma sha biyar na watan Adar a matsayin lokacin da Yahudawa suka sami huta daga abokan gābansu, da kuma a matsayin watan da aka mai da baƙin cikinsu ya zama farin ciki, makokinsu kuma ya zama ranar biki. Ya rubuta musu su kiyaye ranakun a matsayin ranakun biki da na farin ciki. Su kuma ba da kyautai na abinci ga juna, da kuma kyautai ga matalauta. Ta haka, Yahudawa suka yarda su ci gaba da bikin da suka fara, suna aikata abin da Mordekai ya rubuta musu. Haman ɗan Hammedata, mutumin Agag, abokin gāban dukan Yahudawa, ya ƙulla maƙarƙashiya game da Yahudawa, domin a hallaka su, ya kuma jefa fur (wato, ƙuri’a) don yă hallaka su. Amma sa’ad da sarki ya sami labarin maƙarƙashiyar, sai ya ba da umarnai a rubuce cewa mugun shirin da Haman ya ƙulla a kan Yahudawa yă komo kansa, kuma cewa a rataye shi da ’ya’yansa maza a kan gumagumai. (Saboda haka, aka kira ranakun nan Furim, daga kalma fur ). Saboda dukan abin da aka rubuta cikin wannan wasiƙa da kuma abin da suka gani, da abin da ya same su. Yahudawa suka ɗauki nawayar kafa al’adar cewa su, da zuriyarsu, da dukan waɗanda suka haɗa hannun da su, za su kiyaye waɗannan kwanaki biyu, kowace shekara yadda aka tsara, a kuma lokacin da aka keɓe dominsu. Za a tuna, a kuma kiyaye waɗannan kwanaki a kowane zamani, cikin kowane iyali, da kuma cikin kowane lardi, da kowace birni. Kuma kada Yahudawa su fasa yin bikin waɗannan kwanakin Furim, ko su bar jikokinsu su manta da kiyaye waɗannan ranaku biyu. Saboda haka Sarauniya Esta, ’yar Abihayil, tare da Mordekai mutumin Yahuda, suka rubuta da cikakken iko, suka tabbatar da wannan wasiƙa ta biyu game da Furim. Mordekai kuwa ya aika da wasiƙu zuwa ga dukan Yahudawa cikin larduna 127 na masarautar Zerzes. Saƙon fatan alheri da na tabbaci, don a kafa waɗannan ranakun Furim a keɓaɓɓen lokacinsu, kamar yadda Mordekai mutumin Yahuda da Sarauniya Esta suka dokace su. Yadda kuma suka kafa wa kansu da zuriyarsu, game da lokutansu na azumi da makoki. Dokar Esta ta tabbatar da waɗannan umarnai game da Furim, aka kuma rubuta ta cikin tarihi. Sarki Zerzes ya sa a biya haraji a ko’ina a cikin daular, har zuwa ƙasashe masu nesa na bakin teku. Dukan ayyukan Sarki Zerzes masu iko da masu girma tare da cikakken rahoton girmama Mordekai wanda sarki ya yi masa, ba a rubuce suke a cikin littafin tarihin sarakunan Mediya da na Farisa ba? Mordekai mutumin Yahuda, shi ne na biyu a matsayi bayan Sarki Zerzes, mai farin ciki kuma a cikin Yahudawa, aka kuma ɗauke shi da martaba cikin ’yan’uwansa Yahudawa. Gama ya yi aiki don kyautatawar mutanensa, ya kuma yi magana don a kyautata rayuwar dukan Yahudawa. A ƙasar Uz akwai wani mutum mai suna Ayuba. Mutum ne marar laifi kuma mai adalci; yana tsoron Allah, ba ruwansa da mugunta. Yana da ’ya’ya maza bakwai da ’yan mata uku, yana da tumaki dubu bakwai, raƙuma dubu uku, shanu ɗari biyar, da jakuna ɗari biyar, yana kuma da masu yi masa aiki da yawa. A ƙasar Gabas ba wani kamar sa. ’Ya’yansa maza sukan yi biki a gidajensu, wannan yă yi yă ba wancan, sai su kira ’yan’uwansu mata ukun su ci, su sha tare. Bayan lokacin bikin ya wuce, sai Ayuba yă aika su zo don yă tsarkake su. Tun da sassafe zai miƙa hadaya ta ƙonawa domin kowannensu, don yana tunani cewa, “Mai yiwuwa ’ya’yana sun yi wa Allah zunubi, ko sun la’anta shi a cikin zuciyarsu.” Haka Ayuba ya saba yi. Wata rana mala’iku suka kawo kansu gaban Ubangiji, Shaiɗan shi ma ya zo tare da su. Ubangiji ya ce wa Shaiɗan, “Daga ina ka fito?” Shaiɗan ya amsa wa Ubangiji ya ce, “Daga yawo a duniya ina kai da kawowa a cikinta.” Sai Ubangiji ya ce wa Shaiɗan, “Ko ka ga bawana Ayuba? A cikin duniya babu wani kamar sa; shi marar laifi ne, adali kuma, mutum ne mai tsoron Allah, ba ruwansa da mugunta.” Sai Shaiɗan ya amsa ya ce, “Haka kawai Ayuba yake tsoron Allah? Ba ka kāre shi da iyalinsa gaba ɗaya da duk mallakarsa ba? Ka Albarkaci ayyukan hannunsa yadda dabbobinsa duk sun cika ko’ina. Ka ɗan miƙa hannunka ka raba shi da duk abin da yake da shi, ba shakka zai la’anta ka kana ji, kana gani.” Ubangiji ya ce wa Shaiɗan, “To, shi ke nan, duk abin da yake da shi yana hannunka, amma kada ka taɓa shi, shi kansa.” Sai Shaiɗan ya bar Ubangiji. Wata rana lokacin da ’ya’yan Ayuba suke cikin biki a gidan babban ɗansa, sai ɗan aika ya zo wurin Ayuba ya ce masa, “Shanu suna huɗa, jakuna kuma suna kiwo nan kusa, sai Sabenawa suka auka musu suka kwashe su suka tafi, suka karkashe masu yi maka aiki duka, ni kaɗai na tsira na zo in gaya maka!” Yana cikin magana sai ga wani ɗan aika ya zo ya ce, “Wutar Allah ta sauko daga sama ta ƙona dukan tumaki da masu lura da su, wato, bayinka, ni kaɗai na tsira na zo in gaya maka!” Yana cikin magana sai ga wani ɗan aika ya zo ya ce, “Ƙungiyoyin mahara uku na Kaldiyawa sun auka wa raƙumanka sun kwashe su duka, suka kuma karkashe masu yi maka aiki, ni kaɗai ne na tsira na zo in gaya maka!” Yana cikin magana, sai ga wani ɗan aika ya zo ya ce, “’Ya’yanka maza da mata suna biki, suna ci suna sha a gidan babban ɗanka, sai wata iska mai ƙarfi daga hamada ta auka ta rushe gidan, gidan kuwa ya fāɗi a kan ’ya’yanka ya kashe su, ni kaɗai na tsira na zo in gaya maka!” Da jin haka sai Ayuba ya tashi ya yayyaga tufafin jikinsa, ya aske kansa. Ya fāɗi a ƙasa ya yi sujada ya ce, “Tsirara na fito daga cikin mahaifiyata, tsirara kuma zan koma. Ubangiji ya bayar, Ubangiji kuma ya karɓa; yabo ya tabbata ga Ubangiji.” Cikin wannan duka Ayuba bai yi wa Allah zunubi ta wurin ba shi laifi ba. Wata rana kuma mala’iku suka sāke kawo kansu gaban Ubangiji, sai Shaiɗan shi ma ya zo tare da su yă nuna kansa a gabansa. Sai Ubangiji ya ce wa Shaiɗan, “Daga ina ka fito?” Shaiɗan ya amsa wa Ubangiji ya ce, “Daga yawo a duniya ina kai da kawowa a cikinta.” Sai Ubangiji ya ce wa Shaiɗan, “Ko ka ga bawana Ayuba? A cikin duniya babu wani kamar sa; shi marar laifi ne, adali kuma, mutum ne mai tsoron Allah ba ruwansa da mugunta. Kuma har yanzu bai fasa zama mai aminci ba duk da wahalar da ka sa na bari ka ba shi ba tare da wani dalili ba.” Shaiɗan ya amsa ya ce, “Fata don fata! Mutum zai iya rabuwa da duk abin da yake da shi domin ransa. Ka ɗan taɓa lafiyar jikinsa ka gani ba shakka zai la’anta ka kana ji kana gani.” Ubangiji ya ce wa Shaiɗan, “To, shi ke nan, duk abin da yake da shi yana hannunka, amma kada ka taɓa shi, shi kansa.” Sai Shaiɗan ya bar Ubangiji, ya je ya sa wa Ayuba ƙuraje masu zafi a jikinsa daga tafin ƙafafunsa har zuwa kansa. Sai Ayuba ya ɗauki kaskon tukunya yana ta sosa ƙurajen da shi, yayinda yake zaune cikin toka. Matarsa ta ce masa, “Har yanzu kana nan da amincinka? Ka la’anta Allah ka mutu!” Ya amsa ya ce, “Kina magana kamar wawiya. Alheri kaɗai za mu dinga samu daga Allah ban da wahala?” A cikin wannan duka Ayuba bai yi zunubi ba cikin maganarsa. Lokacin da abokan Ayuba su uku wato, Elifaz mutumin Teman, Bildad mutumin Shuwa, da Zofar mutumin Na’ama suka ji wahalar da ta auka wa Ayuba, sai suka shirya suka bar gidajensu suka je don su ta’azantar da shi. Sa’ad da suka gan shi daga nesa, da ƙyar suka gane shi; sai suka fara kuka da ƙarfi, suka yayyaga tufafinsu suka zuba toka a kawunansu, sai suka zauna da shi a ƙasa har kwana bakwai. Ba wanda ya ce masa kome, don sun ga tsananin wahalar da yake ciki. Bayan wannan Ayuba ya buɗe baki ya la’anta ranar da aka haife shi. Ayuba ya ce, “A hallaka ranar da aka haife ni, da kuma daren da aka ce, ‘An haifi jariri namiji!’ Bari ranan nan ta zama duhu; kada Allah yă kula da ita; kada rana tă yi haske a wannan rana. Bari duhu da inuwa mai duhu ta sāke rufe ta; gizagizai kuma su rufe ta; duhu kuma ya rufe haskenta. Bari duhu mai yawa yă rufe daren nan; kada a haɗa ta cikin kwanakin shekara, ko kuma cikin kwanakin watanni. Bari daren yă zama marar amfani; kada a ji wata sowa ta farin ciki. Bari waɗanda suke la’anta ranaku su la’anta wannan rana su waɗanda suke umartar dodon ruwa. Bari taurarinta na safe su zama duhu; bari ranar tă yi ta jiran ganin haske amma kada tă gani, gama ba tă hana uwata ɗaukar cikina, don ta hana ni shan wahalan nan ba. “Me ya sa ban mutu ba da za a haife ni, ko kuma in mutu sa’ad da ana haihuwata ba? Me ya sa aka haife ni, aka tanada nono na sha na rayu? Da yanzu ina kwance cikin salama; da ina barcina cikin salama tare da sarakuna da mashawarta a cikin ƙasa, waɗanda suka gina wa kansu wuraren da yanzu duk sun rushe, da shugabanni waɗanda suke da zinariya, waɗanda suka cika gidajensu da azurfa. Ko kuma don me ba a ɓoye ni a cikin ƙasa kamar jaririn da aka haifa ba rai ba, kamar jaririn da bai taɓa ganin hasken rana ba. A wurin mugaye za su daina yin mugunta, gajiyayyu kuma za su huta. Waɗanda aka daure za su sami jin daɗin; an sake su ba za su sāke jin ana tsawata masu ba. Manyan da ƙanana suna a can, bawa kuma ya sami ’yanci daga wurin maigidansa. “Don me ake ba da haske ga waɗanda suke cikin ƙunci, rai kuma ga masu ɗacin rai ga waɗanda suke neman mutuwa amma ba su samu ba, waɗanda suke nemanta kamar wani abu mai daraja a ɓoye, waɗanda suke farin ciki sa’ad da suka kai kabari? Don me aka ba mutum rai, mutumin da bai san wani abu game da kansa ba, mutumin da Allah ya kange shi. Baƙin ciki ya ishe ni maimakon abinci; ina ta yin nishi ba fasawa; Abin da nake tsoro ya faru da ni; abin da ba na so ya same ni. Ba ni da salama, ba natsuwa; ba ni da hutu, sai wahala kawai.” Sai Elifaz mutumin Teman ya amsa, “In wani ya yi maka magana, za ka ji haushi? Amma wa zai iya yin shiru? Ka tuna yadda ka yi wa mutane da yawa magana, yadda ka ƙarfafa hannuwa marasa ƙarfi. Maganarka ta ƙarfafa waɗanda suka yi tuntuɓe; ka ƙarfafa gwiwoyin da suka rasa ƙarfinsu. Amma yanzu wahala ta zo maka, sai ka karaya; wahala ta sa ka rikice. Ashe bai kamata ka dogara ga Allahnka ba, amincinka kuma yă zama begenka? “Ka duba ka gani yanzu. Wane marar laifi ne ya taɓa hallaka? Ko an taɓa hallaka masu adalci? Na kula cewa waɗanda suke huɗa gonar mugunta, da waɗanda suke shuka mugunta, su ne suke girbe mugunta. A sa’a ɗaya Allah yake hallaka su, cikin fushinsa yakan hallaka su. Zakoki suna ruri suna gurnani; duk da haka an karya haƙoran manyan zakoki. Zakoki suna mutuwa domin ba dabbar da za su kashe su ci, ’ya’yan zakanya kuma sun watse. “Asirce aka gaya mini maganan nan, da ƙyar kunnuwana suka iya ji. Cikin mafarki da tsakar dare, lokacin kowa yana zurfin barci, na sami saƙon nan. Tsoro da fargaba suka kama ni har duk ƙasusuwan jikina suka yi ta rawa. Wani iska ya taɓa mini fuska, sai tsigar jikina ta tashi. Ya tsaya cik, amma ban iya sani ko mene ne ba. Wani abu ya tsaya a gabana, na kuma ji murya. ‘Ko zai yiwu mutum yă fi Allah adalci, ko kuma mutum yă fi wanda ya halicce shi tsarki? In Allah bai yarda da bayinsa ba, in ya sami mala’ikunsa da laifi, to, su wane ne mutane masu zama a gidan da aka yi da laka, waɗanda da ƙura aka yi harsashensu, waɗanda za a iya murƙushe su kamar asu! Tsakanin safe da yamma mai yiwuwa ne ragargaza su; farat ɗaya, su mutu har abada. Ba a tuge igiyar tentinsu, don su mutu ba tare da hikima ba?’ “Ka yi kira in kana so, amma wa zai amsa maka? Wurin waɗanne tsarkaka za ka juya? Fushi yana kashe wawa, ƙyashi kuma yana kashe marar azanci. Ni ma na ga wawa yana cin gaba, amma nan da nan gidansa ya zama la’ananne. ’Ya’yansa suna cikin hatsari, ba wanda zai tsaya musu a gaban alƙali, mayunwata sun kwashe girbinsa, har abubuwan da suke cikin ƙaya, masu jin ƙishirwa kuma suna zuba ido ga dukiyarsa. Gama ba daga cikin ƙasa wahala take fitowa ba, ko kuma bala’i daga ƙasa. Duk da haka an haifi mutum don wahala ne, kamar yadda ba shakka tartsatsin wuta yake tashi. “Amma da a ce ni ne, da zan roƙi Allah; zan gaya masa damuwata. Yana yin abubuwan al’ajabi waɗanda ba a ganewa, mu’ujizai waɗanda ba a ƙirgawa. Yana zuba ruwan sama a ƙasa; yana zuba ruwa a gonaki. Yana ɗaukaka masu sauƙinkai, yana kāre waɗanda suke makoki. Yana dagula shirye-shiryen masu wayo don kada su yi nasara cikin abubuwan da suke shirin yi. Yana kama masu wayo cikin wayonsu, yana kawar da shirye-shiryensu ba za su yi nasara ba. Da rana sukan yi karo da duhu; da rana ma suna lallube kamar a duhun dare suke. Yana ceton matalauta daga takobin da za tă kashe su da shi; yana cetonsu daga hannun waɗanda suka fi su ƙarfi. Saboda haka matalauta suna da bege, rashin gaskiya kuma ta yi shiru. “Mai albarka ne wanda Allah yake yi masa gyara in mutumin ya yi kuskure; saboda haka kada ka guje wa horon Maɗaukaki. Ko da yake yana sa ciwo, shi ne kuma yake warkar da ciwon; ciwon da ya ji maka, shi da kansa zai warkar da shi. Zai cece ka daga bala’o’i guda shida; har bakwai ma ba abin da zai same ka. Lokacin yunwa yana tsare ka daga mutuwa, a cikin yaƙi kuma yana kāre ka daga sarar takobi. Zai kāre ka daga ɓata suna, kuma ba ka bukata ka ji tsoro in hallaka ta zo. Za ka yi wa hallaka da yunwa dariya; kuma ba ka bukata ka ji tsoron manyan namun jeji. Gama za ka zauna lafiya da duwatsu a gonaki, kuma manyan namun jeji za su yi zaman salama da kai. Za ka zauna lafiya a cikin tenti naka, za ka ƙirga kayanka za ka samu kome na nan. Za ka san cewa ’ya’yanka za su zama da yawa, zuriyarka kuma kamar ciyawa a ƙasa. Za ka yi kyakkyawan tsufa kafin ka mutu, kamar yadda ake tara dammuna a lokacin girbi. “Mun yi nazarin wannan, kuma gaskiya ne. Saboda haka ka ji, ka kuma yi amfani da shi.” Sa’an nan Ayuba ya amsa, “Da kawai za a iya auna wahalata a kuma sa ɓacin raina a ma’auni! Ba shakka da sun fi yashin teku nauyi, shi ya sa nake magana haka. Kibiyoyin Maɗaukaki suna a kaina, ruhuna yana shan dafinsa; fushin Allah ya sauka a kaina. Jaki yakan yi kuka sa’ad da ya sami ciyawar ci, ko saniya takan yi kuka in ta sami abincinta? Akan cin abinci marar ɗanɗano ba tare da an sa gishiri ba, ko akwai wani ƙanshin daɗi a cikin farin ruwan ƙwai? Na ƙi in taɓa shi; irin wannan abinci zai sa ni rashin lafiya. “Kash, da ma Allah zai ba ni abin da nake fatar samu, da ma Allah zai biya mini bukatata, wato, Allah yă kashe ni, yă miƙa hannunsa yă yanke raina! Da sai in ji daɗi duk zafin da nake sha ban hana maganar Mai Tsarkin nan cika ba. “Wane ƙarfi nake da shi, har da zan ci gaba da sa zuciya? Wane sa zuciya ne zai sa in yi haƙuri? Da ƙarfin dutse aka yi ni ne? Ko jikina tagulla ne? Ina da wani ikon da zan iya taimakon kai na ne, yanzu da aka kore nasara daga gare ni? “Duk wanda ya ƙi yă yi alheri ga aboki ya rabu ta tsoron Maɗaukaki. Amma ’yan’uwana sun nuna ba zan iya dogara gare su ba, kamar rafin da yakan bushe da rani, kamar rafin da yakan cika a lokacin ƙanƙara, yă kuma kumbura kamar ƙanƙarar da ta narke, amma da rani sai yă bushe, lokacin zafi ba a samun ruwa yana gudu a wurin. Ayari sukan bar hanyarsu; sukan yi ta neman wurin da za su sami ruwa, su kāsa samu har su mutu. Ayarin Tema sun nemi ruwa, matafiya ’yan kasuwa Sheba sun nema cike da begen samu. Ransu ya ɓace, domin sun sa zuciya sosai; sa’ad da suka kai wurin kuwa ba su sami abin da suka sa zuciyar samu ba. Yanzu kuma kun nuna mini ba ku iya taimako; kun ga abin bantsoro kuka tsorata. Ko na taɓa cewa, ‘Ku ba da wani abu a madadina, ko na roƙe ku, ku ba da wani abu domina daga cikin dukiyarku, ko kuma kun taɓa kuɓutar da ni daga hannun maƙiyina, ko kun taɓa ƙwato ni daga hannun marasa kirki’? “Ku koya mini, zan yi shiru; ku nuna mini inda ban yi daidai ba. Faɗar gaskiya tana da zafi! Amma ina amfanin gardamar da kuke yi? Ko kuna so ku gyara abin da na faɗi ne, ku mai da magana wanda yake cikin wahala ta zama ta wofi? Kukan yi ƙuri’a a kan marayu ku kuma sayar da abokinku. “Amma yanzu ku dube ni da kyau, zan yi muku ƙarya ne? Ku bi a hankali, kada ku ɗora mini laifi; ku sāke dubawa, gama ba ni da laifi. Ko akwai wata mugunta a bakina? Bakina ba zai iya rarrabewa tsakanin gaskiya da ƙarya ba? “Mutum bai sha wahalar aiki ba a duniya? Rayuwarsa ba kamar ta wanda aka yi hayarsa ba ne? Kamar yadda bawa yakan jira yamma ta yi, ko kuma kamar yadda wanda aka yi hayarsa yakan jira a biya shi kuɗin aikin da ya yi. Saboda haka rabona shi ne watanni na zama banza, kowane dare kuwa sai ɓacin rai nake samu. Lokacin da na kwanta ina tunani, ‘Har sai yaushe zan tashi?’ Gari ya ƙi wayewa, ina ta jujjuyawa har safe. Jikina duk tsutsotsi da ƙuraje sun rufe shi, fatar jikina ta ruɓe tana fitar da ruwan miki. “Kwanakina suna wucewa da sauri, fiye da yadda ƙoshiyar masaƙa take wucewa da sauri, za su kawo ga ƙarshe ba bege. Ka tuna, ya Allah, raina numfashi ne kawai; idanuna ba za su taɓa sāke ganin farin ciki ba. Idanun da suke ganina yanzu ba za su sāke ganina ba; za ku neme ni amma ba za ku same ni ba. Kamar yadda girgije yakan ɓace yă tafi, haka mutum yake shige zuwa kabari ba kuwa zai dawo ba. Ba zai taɓa zuwa gidansa ba; ba za a sāke san da shi ba. “Saboda haka ba zan yi shiru ba; zan yi magana cikin ɓacin raina, zan nuna ɓacin raina cikin ruhu, cikin ƙuncin raina. Ni teku ne, ko kuwa dodon ruwa, don me kake tsaro na? Lokacin da nake zato zan sami salama in na kwanta a gadona don in huta, duk da haka kana ba ni tsoro da mafarke-mafarke, kana tsorata ni da wahayi. Na gwammace a shaƙe ni in mutu maimakon in kasance cikin wannan jiki. Ba na so in zauna da rai; ba zan rayu ba har abada. Ku rabu da ni; rayuwata ba ta da amfani. “Mene ne mutum har da ka kula da shi haka, har ka mai da hankali a kansa, har kake duba shi kowace safiya, kake kuma gwada shi koyaushe? Ba za ka ɗan daina kallo na ba ko ka rabu da ni na ɗan lokaci? In na yi zunubi, me na yi maka, kai mai lura da mutane? Don me ka sa ni a gaba? Na zame maka kaya mai nauyi ne? Me ya sa ba za ka gafarta mini laifofina ba? Gama na kusa kwantawa cikin ƙasa; za ka neme ni, amma ba za ka same ni ba.” Sai Bildad mutumin Shuwa ya amsa, “Har yaushe za ka gama faɗa waɗannan abubuwa? Maganganunka ba su da amfani. Allah ba mai shari’ar gaskiya ba ne? Ko Maɗaukaki yakan yi abin da ba daidai ba? Lokacin da ’ya’yansa suka yi masa zunubi, yakan bar su su sha wahalar da zunubi yake kawowa. Amma in za ka dubi Allah ka roƙi Maɗaukaki, in kai mai tsarki ne, kuma mai adalci, ko yanzu ma zai taimake ka, yă mayar maka iyalinka da farin cikinka. Ko da yake za ka fara da kaɗan, duk da haka za ka gama da samu mai yawa. “Tambayi na gaba da kai ka ji abin da iyayenka suka koya gama jiya kaɗai aka haife mu ba mu san kome ba, kuma kwanakinmu a duniya masu wucewa ne. Ba za su bishe ka su kuma gaya maka abin da za ka yi ba? Ba za su yi magana daga cikin hikimar da suke da ita ba? Ko kyauro zai iya yi girma a wurin da ba ruwa? Ko za tă taɓa iya yin girma ba tare da ruwa ba? Yayinda take girma ba a yanka ta, takan mutu da sauri fiye da ciyawa. Abin da yake faruwa ke nan da duk wanda yake mantawa da Allah; waɗanda ba su da Allah, ba su da bege. Abin da yake dogara a kai ba shi da ƙarfi; abin da yake dogara a kai yanar gizo ce. Ya jingina ga yanar gizo, amma ba ta tare shi, sun kama ta, amma ba za tă taimake su tsayawa ba. Yana kama da shukar da aka ba ta ruwa sosai lokacin da akwai rana sosai, tana yaɗuwa da kyau; shukar tana bin yaɗuwa, jijiyoyinta suna nannaɗe duwatsu, suna neman wurin da za su kama sosai a cikin duwatsu. Amma lokacin da aka tuge shukar daga wurin da take, wurin ba zai san da ita kuma ba, wurin zai ce, ‘Ban taɓa ganin ki ba.’ Ba shakka shukar ta mutu ke nan, kuma waɗansu za su tsiro a wurin. “Ba shakka, Allah ba ya ƙin marar laifi, ko kuma yă ƙarfafa masu aikata mugunta. Sai dai yă cika bakinka da dariya, yă sa ka yi sowa ta murna. Maƙiyanka za su sha kunya, za a kawar da tentin mugaye.” Sai Ayuba ya amsa, “Lalle, na san wannan gaskiya ne. Amma ta yaya mutum zai iya zama mai adalci a gaban Allah? Ko da mutum yana so yă yi gardama da shi, ba zai taɓa amsa masa ba ko da sau ɗaya cikin dubu. Hikimarsa tana da zurfi, ikonsa yana da yawa. Wane ne ya taɓa yin faɗa da shi har ya yi nasara? Yana matsar da manyan duwatsu kafin su sani kuma yana juya su cikin fushinsa. Yana girgiza ƙasa, yana girgiza harsashenta. Yana magana da rana sai ta ƙi yin haske; yana hana taurari yin haske. Shi kaɗai ya shimfiɗa sammai ya kuma yi tafiya a kan raƙuman ruwan teku. Shi ne ya halicci Mafarauci da Kare da Zomo, da Kaza, da ’Ya’yanta da tarin taurari a sama, da taurarin kudu. Yana yin abubuwan banmamaki waɗanda ba a iya ganewa, mu’ujizai waɗanda ba a iya ƙirgawa. Ba na iya ganinsa lokacin da ya wuce ni; ba na sani ya wuce lokacin da ya wuce. Wane ne ya isa yă hana shi in ya ƙwace abu? Wa zai ce masa, ‘Me kake yi?’ Allah ba ya danne fushinsa; ko dodannin ruwan da ake kira ayarin Rahab ya tattake su. “Ta yaya zan iya yin faɗa da shi? Ina zan iya samun kalmomin da zan yi gardama da shi? Ko da yake ba ni da laifi, ba zan iya amsa masa ba; sai dai roƙon jinƙai zan iya yi ga mahukuncina. Ko da na yi kira gare shi ya amsa mini, ban yarda cewa zai saurare ni ba. Zai sa hadari yă danne ni yă ƙara mini ciwona ba dalili. Ba zai bari in yi numfashi ba, sai dai yă ƙara mini azaba. In maganar ƙarfi ne, shi babban mai ƙarfi ne! In kuma maganar shari’a ne, wa zai kai kararsa? Ko da ni marar ƙarfi ne, bakina ya isa yă sa in zama mai laifi; in ba ni da laifi, zai sa in yi laifi. “Ko da yake ba ni da laifi, ban damu da kaina ba; na rena raina. Ba bambanci; shi ya sa na ce, ‘Yana hallaka marasa laifi da kuma mugaye.’ Lokacin da bala’i ya kawo ga mutuwa, yakan yi dariyar baƙin cikin marasa laifi. Lokacin da ƙasa ta faɗa a hannun mugaye, yakan rufe idanun masu shari’a. In ba shi ba wa zai yi wannan? “Kwanakina sun fi mai gudu wucewa da sauri; suna firiya babu wani abin jin daɗi a cikinsu. Suna wucewa kamar jirgin ruwan da aka yi da kyauro, kamar jahurma da ta kai wa namanta cafka. ‘In na ce zan manta da abin da yake damu na, zan yi murmushi in daina nuna ɓacin rai,’ duk da haka ina tsoron duk wahalata, domin na san ba za ka ɗauke ni marar laifi ba. Tun da an riga an ɗauke ni mai laifi, duk ƙoƙarina a banza yake. Ko da na wanke jikina duka da sabulu, na wanke hannuwana kuma da soda, duk da haka za ka jefa ni cikin ƙazamin wuri, yadda ko rigunan jikina ma za su ƙi ni. “Shi ba mutum ba ne kamar ni wanda zan iya amsa masa, har da za mu yi faɗa da juna a wurin shari’a. In da akwai wanda zai iya shiga tsakaninmu, ya ɗora hannunsa a kanmu tare, wani wanda zai sa Allah yă daina duka na, don yă daina ba ni tsoro. Sa’an nan ne zan iya yin magana ba tare da jin tsoronsa ba, amma a yadda nake a yanzu ba zan iya ba. “Na gaji da rayuwa; saboda haka bari in faɗi zuciyata gabagadi yadda raina yake jin ba daɗi. Zan ce wa Allah, kada ka hukunta ni, amma ka gaya mini laifin da na yi maka. Kana jin daɗin ba ni wahala, don me ka yashe ni, abin da ka halitta da hannunka, yayinda kake murmushi game da shirye-shiryen mugaye? Idanunka irin na mutum ne? Kana gani yadda mutum yake gani ne? Kwanakinka kamar na mutane ne, ko shekarunka kamar na mutane ne da za ka neme ni da laifi ka hukunta ni? Ko da yake ka san ba ni da laifi, kuma ba wanda zai iya cetona daga hannunka. “Da hannuwanka ka ƙera ni, kai ka halicce ni. Yanzu kuma kai za ka juya ka hallaka ni? Ka tuna cewa ka mulmula ni kamar yumɓu. Yanzu za ka mai da ni in zama ƙura kuma? Ba kai ka zuba ni kamar madara ba, na daskare kamar cuku. Ka rufe ni da tsoka da fata, ka harhaɗa ni da ƙasusuwa da jijiyoyi? Ka ba ni rai ka kuma yi mini alheri, kuma cikin tanadinka ka kula da ruhuna. “Amma wannan shi ne abin da ka ɓoye a zuciyarka, na kuma san abin da yake cikin zuciyarka ke nan. In na yi zunubi kana kallo na kuma ba za ka fasa ba ni horo ba don laifin da na yi. Idan ina da laifi, kaitona! Ko da ba ni da laifi, ba zan iya ɗaga fuskata ba, gama kunya ta ishe ni duk ɓacin rai ya ishe ni. In na ɗaga kaina, za ka neme ni kamar zaki ka sāke nuna al’ajabin ikonka a kaina. Kana sāke kawo sababbin waɗanda za su ba da shaida a kaina kana ƙara haushinka a kaina; kana ƙara kawo mini hari. “Me ya sa ka fito da ni daga cikin uwata? Da ma na mutu kafin a haife ni. Da ma ba a halicce ni ba, da na mutu tun daga cikin cikin uwata na wuce zuwa kabari! ’Yan kwanakina ba su kusa ƙarewa ba ne? Ka rabu da ni don in ɗan samu sukuni na ɗan lokaci kafin in koma inda na fito, ƙasa mai duhu da inuwa sosai, zuwa ƙasa mai duhun gaske, da inuwa da hargitsi, inda haske yake kamar duhu.” Sa’an nan Zofar mutumin Na’ama ya amsa, “Duk surutun nan ba za a amsa maka ba? Ko mai surutun nan marar laifi ne? Ko maganganun nan naka marasa amfani za su sa mutane su yi maka shiru? Ba wanda zai kwaɓe ka lokacin da kake faɗar maganar da ba daidai ba? Ka ce wa Allah, ‘Abin da na gaskata ba laifi ba ne kuma ni mai tsabta ne a gabanka.’ Da ma Allah zai yi magana, yă buɗe baki yă faɗi wani abin da ka yi da ba daidai ba yă kuma buɗe maka asirin hikima, gama hikima ta gaskiya tana da gefe biyu. Ka san wannan, Allah ya riga ya manta da waɗansu zunubanka. “Ko za ka iya gane al’amuran Allah? Ko za ka iya gane girman asirin Maɗaukaki? Sun fi nisan sama tudu, me za ka iya yi? Sun fi zurfin kabari zurfi, me za ka sani? Tsayinsu ya fi tsawon duniya da kuma fāɗin teku. “In ya zo ya kulle ka a kurkuku ya ce kai mai laifi ne, wa zai hana shi? Ba shakka yana iya gane mutanen da suke marasa gaskiya; kuma in ya ga abin da yake mugu, ba ya kula ne? Amma daƙiƙin mutum ba ya taɓa zama mai hikima kamar dai a ce ba a taɓa haihuwar ɗan aholaki horarre. “Duk da haka in ka miƙa masa zuciyarka, ka kuma miƙa hannuwanka gare shi, in ka kawar da zunubin da yake hannunka, ba ka bar zunubi ya kasance tare da kai ba shi ne za ka iya ɗaga fuskarka ba tare da jin kunya ba; za ka tsaya da ƙarfi kuma ba za ka ji tsoro ba. Ba shakka za ka manta da wahalolinka, za ka tuna da su kamar yadda ruwa yake wucewa. Rayuwarka za tă fi hasken rana haske, duhu kuma zai zama kamar safiya. Za ka zauna lafiya, domin akwai bege; za ka duba kewaye da kai ka huta cikin kwanciyar rai. Za ka kwanta, ba wanda zai sa ka ji tsoro, da yawa za su zo neman taimako a wurinka. Amma idanun mugaye ba za su iya gani ba, kuma ba za su iya tserewa ba; begensu zai zama na mutuwa.” Sai Ayuba ya amsa, “Ba shakka ku ne mutanen nan, hikima za tă mutu tare da ku! Amma ni ma ina da hankali kamar ku; ba ku fi ni ba. Wane ne bai san duk waɗannan abubuwan ba? “Na zama abin dariya ga abokaina, ko da yake na yi kira ga Allah ya kuwa amsa mini, duk da haka suka yi mini riya ko da yake ni mai adalci ne kuma marar laifi! Mutanen da ba su da damuwa suna jin daɗin ganin waɗanda suke dab da fāɗuwa. Amma wurin zaman ’yan fashi yana nan ba mai damunsu, waɗanda kuma suke saɓa wa Allah suna zamansu lafiya, har ma da masu ɗaukar allahnsu a hannuwansu. “Amma ka tambayi dabbobi, za su kuma koya maka, ko kuma tsuntsayen sararin sama kuma za su gaya maka. Ko ka yi magana da duniya, za tă kuma koya maka, ko kuma ka bar kifin teku su sanar da kai. Wane ne cikin waɗannan bai san cewa hannun Ubangiji ne ya yi wannan ba? Ran kowace halitta yana a hannunsa, haka kuma numfashin dukan ’yan adam. Ko kunne ba ya gwada kalmomi kamar yadda harshe yake ɗanɗana abinci? Ko ba a wurin tsofaffi ake samun hikima ba? Ba tsawon rai yana kawo ganewa ba? “Allah ne mai iko da kuma hikima, shawara da ganewa nasa ne. Abin da ya rushe ba a iya ginawa ba; in ya kulle mutum ba a iya buɗe shi a sake shi ba. Idan ya hana ruwan sama, za a yi fări; in kuma ya saki ruwa za a yi ambaliya. Shi ne mai ƙarfi da kuma mai nasara; mai ruɗi da wanda aka ruɗa, duk nasa ne. Yakan sa mashawarta su zama marasa hikima yă kuma sa wawaye su zama masu shari’a. Yana cire sarƙar da sarakuna suka ɗaura yă kuma ɗaura musu wata tsumma a kwankwaso. Yakan ƙasƙantar da firistoci yă kuma tumɓuke masu ikon da aka kafa tun da daɗewa. Yana sa amintattun mashawarta su yi shiru yakan kawar da hikimar dattawa. Yakan sa masu iko su ji kunya yă kuma ƙwace ƙarfin masu ƙarfi. Yana buɗe abubuwan da suke cikin duhu yă kuma kawo haske a wuraren da ba haske; yana sa al’ummai su zama manya, sai kuma yă hallaka su; yana sa al’ummai su ƙasaita, yă kuma watsar da su. Yana hana shugabannin duniya ganewa; Ya bar su su yi ta makuwa, su ruɗe, su ɓata. Suna lallube cikin duhu ba haske; yă sa su yi ta tangaɗi kamar bugaggu. “Idanuna sun ga waɗannan duka, kunnuwana sun ji sun kuma gane. Abin da kuka sani, ni ma na sani; ba ku fi ni ba. Amma ina so in yi magana da Maɗaukaki, in kai kukana wurin Allah kai tsaye. Ku kuma kun ishe ni da ƙarairayi; ku likitocin wofi ne, dukanku! In da za ku yi shiru gaba ɗaya! Zai zama muku hikima. Ku ji gardamata yanzu; ku ji roƙon da zai fito daga bakina. Za ku iya yin muguwar magana a madadin Allah? Ko za ku yi ƙarya a madadinsa? Ko za ku nuna masa sonkai? Ko za ku yi gardama a madadinsa? In ya bincike ku zai tarar ba ku da laifi? Ko za ku iya ruɗe shi yadda za ku ruɗi mutane? Ba shakka zai kwaɓe ku in kun nuna sonkai a ɓoye. Ko ikonsa ba ya ba ku tsoro? Tsoronsa ba zai auka muku ba? Duk surutanku kamar toka suke; kāriyarku na yimɓu ne. “Ku yi shiru zan yi magana; sa’an nan abin da zai same ni yă same ni. Don me na sa kaina cikin hatsari na yi kasada da raina? Ko da zai kashe ni ne, begena a cikinsa zai kasance; ba shakka zan kāre kaina a gabansa lalle wannan zai kawo mini kuɓuta gama ba wani marar tsoron Allah da zai iya zuwa wurinsa! Ku saurara da kyau ku ji abin da zan faɗa; bari kunnuwanku su ji abin da zan ce. Yanzu da na shirya ƙarata, na san za a ce ba ni da laifi. Ko wani zai ce ga laifin da na yi? In an same ni da laifi, zan yi shiru in mutu. “Kai dai biya mini waɗannan bukatu biyu kawai ya Allah, ba zan kuwa ɓoye daga gare ka ba; Ka janye hannunka nesa da ni, ka daina ba ni tsoro da bantsoronka. Sa’an nan ka kira ni, zan kuwa amsa, ko kuma ka bar ni in yi magana sai ka amsa mini. Abubuwa nawa na yi waɗanda ba daidai ba, kuma zunubi ne? Ka nuna mini laifina da zunubina. Don me ka ɓoye mini fuskarka; ka kuma sa na zama kamar maƙiyinka? Ko za a wahalar da ganye wanda iska take hurawa? Ko za ka bi busasshiyar ciyawa? Gama ka rubuta abubuwa marasa daɗi game da ni; ka sa na yi gādon zunuban ƙuruciyata. Ka daure ƙafafuna da sarƙa; kana kallon duk inda na taka ta wurin sa shaida a tafin ƙafafuna. “Haka mutum yake lalacewa kamar ruɓaɓɓen abu, kamar rigar da asu ya cinye. “Mutum haihuwar mace kwanakinsa kaɗan ne, kuma cike da wahala. Yana tasowa kamar fure yana kuma shuɗewa; kamar inuwa, ba ya daɗewa. Za ka zura ido a kan irin wannan ne? Za ka kawo shi gaba don ka yi masa shari’a? Wane ne zai iya kawo abin da yake da tsarki daga cikin abu marar tsarki? Babu! An lissafta kwanakin mutum; ka riga ka ɗibar masa watanni, ka yi masa iyaka, ba zai iya wuce iyakar ba. Saboda haka ka kawar da kanka daga gare shi, ka rabu da shi har sai ya cika lokacinsa kamar mutumin da aka ɗauki hayarsa. “Aƙalla itace yana da bege. In an sare shi, zai sāke tsira, zai tohu da kyau. Ko da jijiyoyin itacen sun tsufa a cikin ƙasa kuma kututturensa ya mutu a cikin ƙasa. Daga ya ji ƙanshin ruwa zai tohu yă yi tsiro kamar shuka. Amma mutum yana mutuwa a bizne shi; daga ya ja numfashinsa na ƙarshe, shi ke nan. Kamar yadda ruwa yake bushewa a teku ko a gaɓar rafi sai wurin yă bushe, haka mutum zai kwanta ba zai tashi ba; har sai duniya ta shuɗe mutane ba za su farka ba, ba za su tashi daga barcinsu ba. “Da ma za ka ɓoye ni a cikin kabari ka ɓoye ni har sai fushinka ya wuce! In da za ka keɓe mini lokaci sa’an nan ka tuna da ni! In mutum ya mutu, ko zai sāke rayuwa? In haka ne zan daure kwanakin da nake shan wahala har su wuce. Za ka kira zan kuwa amsa maka; za ka yi marmarin abin da hannunka ya halitta. Ba shakka a lokacin ne za ka lura da matakaina amma ba za ka kula da zunubaina ba. Za a daure laifofina a cikin jaka; za ka rufe zunubaina. “Amma kamar yadda manyan duwatsu suke fāɗuwa su farfashe su kuma gusa daga wurarensu, yadda ruwa yakan zaizaye duwatsu ruwa mai ƙarfi kuma yă kwashe turɓayar ƙasa, haka kake barin mutum ba bege. Ka sha ƙarfinsa gaba ɗaya, sai ya ɓace, ka sauya yanayinsa ka kuma kore shi. Ko an martaba ’ya’yansa maza, ba zai sani ba; Ko an wulaƙanta su, ba zai gani ba. Zafin jikinsa kaɗai yake ji yana kuka wa kansa ne kaɗai.” Sai Elifaz mutumin Teman ya amsa, “Mutum mai hikima zai amsa da surutai marasa kan gado ko yă cika cikinsa da iskar gabas? Ko zai yi gardama da maganganun wofi maganganu marasa amfani? Amma ka ma rena Allah ka hana a yi addu’a gare shi. Zunubanka ne suke gaya maka abin da za ka ce; kana magana kamar mai wayo. Bakinka zai kai ka yă baro, ba nawa ba; maganar bakinka za tă juya a kanka. “Kai ne mutum na farko da aka fara haihuwa? Ko kai ne aka fara halitta kafin tuddai? Kana sauraron shawarar Allah? Ko kana gani kai kaɗai ne mai hikima? Me ka sani da ba mu sani ba? Wane fahimi kake da shi da ba mu da shi? Masu furfura da tsofaffi suna gefenmu mutanen da sun girme babanka. Ta’aziyyar Allah ba tă ishe ka ba. Maganarsa mai laushi ba tă ishe ka ba? Don me ka bar zuciyarka ta kwashe ka, kuma don me idanunka suke haske, har kake fushi da Allah kake kuma faɗar waɗannan maganganu daga bakinka? “Mene ne mutum, har da zai zama da tsarki, ko kuma mace ta haife shi, har yă iya zama mai adalci? In Allah bai nuna amincewa ga tsarkakansa ba, in har sammai ba su da tsarki a idonsa, mutum fa, wanda yake da mugunta da lalacewa, wanda yake shan mugunta kamar ruwa! “Ka saurare ni, zan kuma yi maka bayani; bari in gaya maka abin da na gani, abin da masu hikima suka ce, ba tare da sun ɓoye wani abu da suka samu daga wurin iyayensu ba (waɗanda su ne masu ƙasar kafin baƙi su shigo ƙasar). Dukan kwanakin ransa mugu yana shan wahala, wahala kaɗai zai yi ta sha. Ƙara mai bantsoro za tă cika kunnuwansa ’yan fashi za su kai masa hari. Yana jin tsoron duhu domin za a kashe shi da takobi. Yana ta yawo, abinci don ungulaye; ya san ranar duhu tana kusa. Ɓacin rai da baƙin ciki sun cika shi, kamar sarkin da yake shirin yaƙi, domin ya nuna wa Allah yatsa ya rena Allah Maɗaukaki, ya tasar masa da faɗa da garkuwa mai kauri da kuma ƙarfi. “Ko da yake fuskarsa ta cika da kumatu kuma yana da tsoka ko’ina, zai yi gādon garuruwan da suka lalace, da kuma gidajen da ba wanda yake zama a ciki, gidajen da sun zama tarkace. Ba zai sāke zama mai arziki ba, dukiyarsa ba za tă dawwama ba, abin da ya mallaka kuma ba zai bazu a ƙasar ba. Ba zai tsere wa duhu ba; wuta za tă ƙona rassansa, kuma numfashi daga bakin Allah zai hallaka shi. Kada yă ruɗi kansa ta wurin dogara ga abin da ba shi da amfani domin ba zai samu wani abu ba daga ciki. Kafin lokacinsa yă cika, za a gama biyansa duka, kuma rassansa ba za su ba da amfani ba. Zai zama kamar itacen inabi wanda ’ya’yansa suka kakkaɓe kafin su nuna, kamar itacen zaitun zai zubar da furensa. Gama marasa tsoron Allah za su zama marasa ba da ’ya’ya, wuta kuma za tă ƙona tenti na masu son cin hanci. Suna yin cikin rikici su kuma haifi mugunta; cikinsu yana cike da ruɗami.” Sai Ayuba ya amsa, “Na ji abubuwa da yawa kamar waɗannan; dukanku ba ku iya ta’aziyya ba! Dogayen surutanku ba sa ƙare ne? Me yake sa kuke ta yin waɗannan surutai har kuke cin gaba da yin gardama? Ni ma zan iya yin maganganu kamar yadda kuke yi in da kuna cikin halin da nake; zan iya faɗar duk abubuwan da kuke faɗi, in kaɗa muku kaina. Amma bakina zai ƙarfafa ku; ta’aziyyar da za tă fito daga bakina za tă kawar muku da ɓacin zuciyarku. “Duk da haka in na yi magana, ba na samun sauƙi; in ma na yi shiru zafin ba ya tafiya. Ba shakka ya Allah ka gajiyar da ni; ka ɓata gidana gaba ɗaya. Ka daure ni, ya kuma zama shaida; yadda na rame sai ƙasusuwa, wannan ya sa ake gani kamar don ni mai zunubi ne shi ya sa. Allah ya kai mini hari ya yi kaca-kaca da ni cikin fushinsa yana cizon haƙoransa don fushin da yake yi da ni; ya zura mini ido. Mutane suka buɗe baki suka yi mini riyar reni; suka yi mini ba’a suka haɗu suka tayar mini. Allah ya bashe ni ga mugayen mutane, ya jefa ni hannun mugaye. Dā ina zamana lafiya kome yana tafiya daidai; amma ya ragargaza ni; ya shaƙe ni a wuya; ya murƙushe ni na zama abin barata gare shi; maharbansa sun kewaye ni. Ba tausayi, ya soke ni a ƙodata har jini ya zuba a ƙasa. Ya ji mini rauni a kai a kai ya auko mini kamar mai yaƙi. “Ina makoki saye da tsummoki na ɓoye fuskata a cikin ƙura. Fuskata ta yi ja don kuka idanuna sun kukumbura; duk da haka hannuwana ba su aikata ɓarna ba kuma addu’ata mai tsabta ce. “Ya duniya, kada ki ɓoye jinina; bari yă yi kuka a madadina! Ko yanzu haka shaidata tana sama; wanda zai tsaya mini yana sama. Shi mai yin roƙo a madadina abokina ne yayinda nake kuka ga Allah; a madadin mutum ya yi roƙo ga Allah kamar yadda mutum yakan yi roƙo domin abokinsa. “Shekaru kaɗan suka rage in kama hanyar da ba a komawa. Na karaya, kwanakina sun kusa ƙarewa, kabari yana jirana. Ba shakka masu yi mini ba’a suna kewaye da ni; idanuna suna ganin tsokanar da suke yi mini. “Ya Allah, ka ba ni abin da ka yi mini alkawari. Wane ne zai kāre ni? Ka rufe zuciyarsu yadda ba za su iya ganewa ba, saboda haka ba za ka bari su yi nasara ba. In mutum ya juya wa abokansa baya don a ba shi wata lada ’ya’yansa za su makance. “Allah ya sa na zama abin da kowa yake magana a kai wanda kowa yake tofa wa miyau a fuska. Idanuna ba sa gani sosai don baƙin ciki; jikina ya zama kamar inuwa kawai Mutanen da suke masu adalci wannan abu ya ba su tsoro; marasa laifi sun tayar wa marasa tsoron Allah. Duk da haka, masu adalci za su ci gaba da tafiya a kan hanyarsu, waɗanda hannuwansu suke da tsabta kuma za su ƙara ƙarfi. “Amma ku zo dukanku, ku sāke gwadawa! Ba zan sami mutum ɗaya mai hikima ba a cikinku. Kwanakina sun wuce, shirye-shiryena sun ɓaci haka kuma abubuwan da zuciyata take so. Mutanen nan sun juya rana ta zama dare. A tsakiyar duhu suka ce, ‘Haske yana kusa.’ In kabari ne begen da nake da shi kaɗai, in na shimfiɗa gadona a cikin duhu, In na ce wa kabari, ‘Kai ne mahaifina,’ tsutsa kuma ke ce, ‘Mahaifiyata’ ko ‘’yar’uwata,’ To, ina begena yake? Wane ne zai iya ganin wani bege domina? Ko begena zai tafi tare da ni zuwa kabari ne? Ko tare za a bizne mu cikin ƙura?” Sai Bildad mutumin Shuwa ya amsa, “Yaushe za ka gama maganganun nan? Ka dawo da hankalinka sa’an nan za mu iya yin magana. Don me muke kamar shanu a wurinka, ka ɗauke mu mutanen wofi? Kai da ka yayyage kanka don haushi, za a yashe duniya saboda kai ne? Ko kuma duwatsu za su matsa daga wurinsu? “An kashe fitilar mugu; harshen wutarsa ya daina ci. Wutar cikin tentinsa ta zama duhu; fitilar da take kusa da shi ta mutu. Ƙarfin takawarsa ya ragu; dabararsa ta ja fāɗuwarsa. Ƙafafunsa sun kai shi cikin raga, yana ta yawo a cikin ragar. Tarko ya kama ɗiɗɗigensa; tarko ya riƙe shi kam. An ɓoye masa igiya da za tă zarge shi a ƙasa; an sa masa tarko a kan hanyar da zai bi. Tsoro duk ya kewaye shi ta kowane gefe yana bin shi duk inda ya je. Masifa tana jiransa; bala’i yana shirye yă fāɗa masa a lokacin da zai fāɗi. Ya cinye wani sashe na gaɓar jikinsa; ɗan fari na mutuwa ya cinye ƙafafunsa. An yage shi daga zaman lafiyar da yake yi a cikin tentinsa aka sa shi tsoro sosai. Wuta ta cinye tentinsa; farar wuta ta rufe wurin da yake zama. Jijiyoyinsa sun bushe a ƙasa rassansa sun mutu a sama. An manta da shi a duniya; ba wanda yake ƙara tunawa da shi. An tura shi daga cikin haske zuwa cikin duhu, an kore shi daga duniya. Ba shi da ’ya’ya ko zuriya cikin mutanensa, ba sauran wanda yake a raye a wurin da ya taɓa zama. Mutanen Yamma suna mamakin abin da ya faru da shi; tsoro ya kama mutanen gabas. Ba shakka haka wurin zaman mugun mutum yake, haka wurin zaman wanda bai san Allah ba yake.” Sai Ayuba ya amsa, “Har yaushe za ku yi ta ba ni azaba ku kuma murƙushe ni da maganganunku? Yanzu sau goma ke nan kuna wulaƙanta ni, kuna kai mini hari na rashin kunya. In gaskiya ne na yi laifi, kuskurena ya rage nawa. In kuwa za ku ɗaukaka kanku a kaina kuna ɗauka wahalar da nake sha domin na yi laifi ne, sai ku san cewa Allah ya yi mini ba daidai ba ya kewaye ni da ragarsa. “Ko da yake na yi kuka cewa, ‘An yi mini ba daidai ba!’ Ba a amsa mini ba; ko da yake na nemi taimako, ba a yi adalci ba. Ya tare mini hanya yadda ba zan iya wucewa ba; ya rufe hanyata da duhu. Ya cire darajar da nake da ita, ya kuma cire rawani daga kaina. Ya yi kaca-kaca da ni har sai da na ƙare; ya tuge begen da nake da shi kamar itace. Yana jin haushina ya lissafta ni cikin maƙiyansa. Rundunarsa ta zo da ƙarfi; suka kafa sansani kewaye da ni, suka zagaye tentina. “Ya raba ni da ’yan’uwana maza; abokaina sun zama baƙi gare ni. Dangina sun tafi; abokaina na kurkusa sun manta da ni. Waɗanda sukan ziyarce ni, da masu yi mini aiki mata sun ɗauke ni baƙo. Na kira bawana, amma bai amsa ba, ko da yake na roƙe shi da bakina. Numfashina yana ɓata wa matata rai; ’yan’uwana sun ƙi ni. Har ’yan yara suna rena ni; in sun gan ni sai su fara yi mini riyar reni. Duk abokaina sun yashe ni; waɗanda nake ƙauna sun zama ba sa ƙaunata. Ni ba kome ba ne sai dai fata da ƙashi, da ƙyar na tsira. “Ku tausaya mini, abokaina, ku ji tausayina, gama hannun Allah ya sauko a kaina. Don me kuke fafarata kamar yadda Allah yake yi? Ba ku gaji da yagar fatata ba? “Kash, da ma a ce ana rubuta maganganuna, da an rubuta su a littafi, a rubuta su da ƙarfe a kan dutse don su dawwama har abada! Na san wanda zai fanshe ni yana nan da rai, kuma a ƙarshe zai tsaya a kan duniya. Kuma bayan an hallaka fatata, duk da haka a cikin jiki zan ga Allah. Zan gan shi da kaina da idanuna, Ni, ba wani ba ne. Zuciyata ta cika da wannan tunani! “In kuka ce, ‘Za ku ci gaba da matsa mini, tun da shi ne tushen damuwa,’ sai ku ma ku ji tsoron takobin; gama fushi yakan kawo hukunci ta wurin takobi, sa’an nan za ku san cewa akwai shari’a.” Sai Zofar mutumin Na’ama ya amsa, “Tunanin da ya dame ni ya sa dole in amsa domin abin ya dame ni sosai. Na ji wani zargin da ka yi mini na reni, kuma yadda na gane, shi ya sa zan ba da amsa. “Ba shakka ka san yadda abin yake tuntuni, tun da aka sa mutum cikin duniya, mugun mutum bai taɓa daɗewa ba, farin cikin mutum na ɗan gajeren lokaci ne. Ko da ya ƙasaita ya kai sararin sama, kansa kuma yana taɓa gizagizai. Zai hallaka har abada, kamar bayan gidansa; waɗanda suka gan shi za su ce, ‘Ina yake?’ Kamar mafarki haka zai ɓace, ba za a ƙara ganinsa ba zai ɓace kamar wahayi da dare. Idon da ya gan shi ba zai ƙara ganinsa ba; wurin zamansa ba zai sāke ganinsa ba. Dole ’ya’yansa su mayar wa matalauta abin da ya kamata; dole hannuwansa su mayar da dukiyarsa. Jin ƙarfi da ya cika ƙasusuwansa zai kwantar da shi a cikin ƙura. “Ko da yake mugunta tana da daɗi a bakinsa kuma yana ɓoye ta a harshensa, ko da yake ba zai iya rabuwa da ita ba, yana kuma ajiye ta a bakinsa, duk da haka abincin da ya ci zai zama da tsami a cikin cikinsa; zai zama kamar dafin maciji a cikinsa. Zai haras da dukiyar da ya haɗiye; Allah zai sa cikinsa yă haras da su. Zai sha dafin maciji; sarar maciji mai dafi za tă tashe shi. Ba zai ji daɗin koguna da rafuffuka masu kwarara da zuma da madara ba. Dole yă ba da abin da ya yi gumi kafin yă samu, ba zai ci ba; ba zai ji daɗin ribar da ya samu daga kasuwancinsa ba. Gama ya ci zalin talakawa ya bar su cikin wahala; ya ƙwace gidajen da ba shi ya gina ba. “Ba shakka ba zai samu abin da yake ƙoƙarin samu ba, dukiyarsa ba za tă cece shi ba. Ba abin da ya ragu da zai ɗauka; arzikinsa ba zai dawwama ba. Yana cikin samun arziki, ɓacin rai zai auka masa; ƙunci mai ƙarfi zai zo masa. Lokacin da ya cika cikinsa, Allah zai zuba fushinsa a kansa, zai daddaka shi. Ko da yake yana guje wa makamin ƙarfe, kibiya mai bakin tagulla za tă huda shi. Zai zāre ta daga bayansa, tsinin zai fita daga hantarsa; tsoro zai cika shi; duhu kawai yake jiran dukiyarsa. Wutar da ba a fifita ba za tă cinye shi ta kuma ƙona duk abin da ya rage a tentinsa. Sammai za su fallasa laifinsa; duniya za tă yi gāba da shi. Ambaliyar ruwa za tă tafi da gidansa, ruwaye masu gudu a ranar fushin Allah. Abin da Allah zai sa yă faru da mugu ke nan, gādon da Allah ya ba shi ke nan.” Sai Ayuba ya amsa, “Ku saurare ni da kyau; bari wannan yă zama ta’aziyyar da za ku ba ni. Ku ba ni zarafi in yi magana, bayan na gama sai ku yi ba’arku. “A wurin mutum ne na kawo kukana? Don me ba zan kāsa haƙuri ba? Ku dube ni, ku kuma yi mamaki; ku rufe bakina da hannunku. Lokacin da na yi tunanin wannan, sai in ji tsoro; jikina yă fara rawa. Don me mugaye suke rayuwa har su tsufa, suna kuma ƙaruwa da iko? Suna ganin ’ya’yansu suna girma, suna ganin jikokinsu suna tasowa a kan idanunsu. Gidajensu suna zama cikin lafiya ba ruwansu da fargaba. Kuma Allah ba ya ba su horo. Shanunsu ba sa fasa haihuwa; suna haihuwa ba sa yin ɓari. Suna aika ’ya’yansu kamar garke; ’ya’yansu suna guje-guje da tsalle-tsalle. Suna rera da kayan kiɗa na ganga da garaya; suna jin daɗin busar sarewa. Suna yin rayuwarsu cikin arziki kuma su mutu cikin salama. Duk da haka suna ce wa Allah, ‘Ka rabu da mu.’ Ba ma so mu san hanyoyinka. Wane ne Maɗaukaki har da za mu bauta masa? Wace riba za mu samu ta wurin yin addu’a gare shi? Amma arzikinsu ba a hannunsu yake ba saboda haka ba ruwana da shawarar mugaye. “Duk da haka, sau nawa fitilar mugu take mutuwa? Sau nawa bala’i yake auka masa, ko Allah ya taɓa hukunta mugu cikin fushi? Sau nawa suke zama kamar tattaka a iska, ko kuma kamar ƙura da iskar hadari take kwashewa? An ce ‘Allah yana tara wa ’ya’yan mutum horon da zai ba mutumin.’ Bari yă ba mutumin horo don yă san ya yi haka! Bari idanunsa su ga yadda zai hallaka; bari yă sha daga fushin Maɗaukaki. Ko zai damu da iyalin da ya bari a baya sa’ad da kwanakinsa suka ƙare? “Wani zai iya koya wa Allah ilimi tun da yana shari’anta har da waɗanda suke manya masu iko? Wani mutum zai mutu cikin jin daɗi da kwanciyar hankali, jikinsa ɓulɓul, ƙasusuwansa da alamar ƙarfi. Wani kuma zai mutu cikin ɗacin rai, bai taɓa jin daɗin wani abu mai kyau ba. Dukansu kuwa za a bizne su a ƙasa, kuma tsutsotsi za su cinye su. “Na san duk abin da kuke tunani, yadda za ku saɓa mini. Kuna cewa, ‘Yanzu ina gidan babban mutumin nan, tenti wurin da mugaye suke zama?’ Ba ku taɓa tambayar waɗanda suke tafiya ba? Ba ku kula da labaransu, cewa an kāre mugu daga ranar bala’i, an kāre shi daga ranar fushi? Wane ne yake gaya masa abin da ya yi? Wane ne yake rama abin da ya yi? Za a bizne shi a kabari, a kuma yi tsaron kabarinsa. Akan mai da ƙasa a kan gawarsa a hankali; dukan jama’a suna binsa, da yawa kuma suna gabansa. “Saboda haka ta yaya za ku iya yi mini ta’aziyya da surutan banzan nan naku? Babu wani abu cikin amsarku sai ƙarya!” Sai Elifaz mutumin Teman ya amsa, “Mutum yana iya zama da amfani a wurin Allah? Mai hikima ma zai iya zama da amfani a wurin shi? Wane daɗi Allah zai ji in kai mai adalci ne? Wace riba zai samu in rayuwarka marar laifi ce? “Ko don kana tsoron Allah shi ya sa ya kwaɓe ka ya kuma bari haka yă same ka? Ba muguntarka ce ta yi yawa ba? Ba zunubanka ne ba iyaka ba? Ka sa ɗan’uwanka yă biya ka bashin da kake binsa ba dalili; ka ƙwace wa mutanen rigunansu ka bar su tsirara. Ba ka ba masu jin ƙishirwa su sha ba kuma ka hana wa masu jin yunwa abinci su ci. Ko da yake kai mai ƙarfi ne, ka mallaki ƙasa, mutum mai martaba kuma, kana zama cikin ƙasarka. Ka kori gwauraye hannu wofi, ka kuma karya ƙarfin marayu. Shi ya sa kake kewaye da tarkuna, shi ya sa ka cika da tsoron mugun abin da zai auko maka. An yi duhu ƙwarai, har ba ka iya gani, shi ya sa ambaliyar ruwa ta rufe ka. “Ba Allah ne a can sama ba? Dubi yadda taurarin sama suke can nesa a sama! Duk da haka ka ce, ‘Me Allah ya sani? A cikin duhu ne yake shari’a? Gajimare ya rufe shi, saboda haka ba ya ganinmu lokacin da yake takawa a cikin sammai.’ Za ka ci gaba da bin tsohuwar hanyar da mugayen mutane suka bi? An ɗauke su kafin lokacinsu yă cika, ruwa ya share tushensu. Suka ce wa Allah, ‘Ka rabu da mu! Me Maɗaukaki zai yi mana?’ Duk da haka kuwa shi ne ya cika gidajensu da abubuwa masu kyau, saboda haka ba ruwana da shawarar mugaye. “Masu adalci suna gani ana hallaka mugaye, suna jin daɗi; marasa laifi suna yi musu ba’a, suna cewa, ‘Ba shakka an hallaka maƙiyanmu, wuta kuma ta ƙona dukiyarsu.’ “Ka miƙa kanka ga Allah ka samu salamarsa; ta haka ne arziki zai zo maka. Ka bi umarnin da zai fito daga bakinsa kuma ka riƙe maganarsa a cikin zuciyarka. In ka komo ga Maɗaukaki, za ka warke. In ka kawar da mugunta daga cikin gidanka. Ka jefar da zinariyarka a ƙasa, ka jefar da zinariyar Ofir da ka fi so a cikin duwatsu, sa’an nan ne Maɗaukaki zai zama zinariyarka, zai zama azurfa mafi kyau a wurinka. Ba shakka a lokacin ne za ka sami farin ciki daga wurin Maɗaukaki, ku kuma ɗaga idanunku ga Allah Za ka yi addu’a zuwa gare shi, zai kuwa ji ka, kuma za ka cika alkawuranka. Abin da ka zaɓa za ka yi za ka yi nasara a ciki, haske kuma zai haskaka hanyarka. Sa’ad da aka ƙasƙantar da mutane ka kuma ce, ‘A ɗaga su!’ Sa’an nan zai ceci masu tawali’u. Zai ceci wanda ma yake mai laifi, wanda zai tsirar da shi ta wurin tsabtar hannuwanka.” Sa’an nan Ayuba ya amsa, “Ko a yau, ina kuka mai zafi; hannunsa yana da nauyi duk da nishin da nake yi. Da a ce na san inda zan same shi; da a ce zan iya zuwa wurin da yake zama! Zan kai damuwata wurinsa in yi gardama da shi. Zan nemi in san abin da zai ce mini, in kuma auna abin da zai ce mini. Zai yi gardama da ni da ikonsa mai girma? Babu, ba zai zarge ni da laifi ba. Mai adalci ne zai kawo ƙara a wurinsa, kuma zan samu kuɓuta daga wurin mai shari’an nan har abada. “Amma in na je gabas, ba ya wurin; in na je yamma, ba zan same shi ba. Sa’ad da yake aiki a arewa, ba ni ganinsa; sa’ad da ya juya zuwa kudu, ba na ganinsa. Amma ya san hanyar da nake bi; sa’ad da ya gwada ni zan fito kamar zinariya. Ƙafafuna suna bin ƙafafunsa kurkusa; na bi hanyarsa ba tare da na juya ba. Ban fasa bin dokokin da ya bayar ba; na riƙe maganarsa da muhimmanci fiye da abincin yau da gobe. “Amma ya tsaya shi kaɗai, kuma wa ya isa yă ja da shi? Yana yin abin da yake so. Yana yi mini abin da ya shirya yă yi mini, kuma yana da sauran irinsu a ajiye. Shi ya sa na tsorata a gabansa; sa’ad da na yi tunanin wannan duka, nakan ji tsoronsa. Allah ya sa zuciyata ta yi sanyi; Maɗaukaki ya tsorata ni. Duk da haka duhun bai sa in yi shiru ba, duhun da ya rufe mini fuska. “Domin me Maɗaukaki ba zai sa ranar shari’a ba? Don me waɗanda suka san shi suke faman samun irin ranakun nan? Mugaye suna satar fili ta wurin matsar da duwatsun da aka yi iyaka da su; suna satar dabbobi su kuma yi kiwon su. Suna ƙwace wa marayu jakunansu suna kuma ƙwace wa gwauruwa sa don suna binta bashi. Suna ture matalauta daga hanya suna kuma sa dole matalautan ƙasar su ɓoye. Kamar jakunan jeji a hamada, matalauta suna aikin neman abinci gonaki marasa amfani suna tanada abinci wa ’ya’yansu. Suna girbi a gonakin da ba nasu ba, suna yin kala a gonar inabi ta mugaye. Don ba su da tufafi, sukan kwana tsirara; ba su da wani abin da zai rufe su cikin sanyi. Sun jiƙe sharkaf da ruwan da yake kwararowa daga duwatsu, sun rungume duwatsu don rashin wurin fakewa. Ana ƙwace jinjiri mai shan mama; ana ƙwace ɗan yaron matalauci don biyan bashi. Don ba su da tufafi suna yawo tsirara; suna dakon dammunan hatsi amma duk da haka suna cikin shan yunwa. Suna matse zaitun a cikin kunyoyi suna kuma matse ruwan inabi daga ’ya’yan inabi, duk da haka suna fama da ƙishi. Ana jin nishin masu mutuwa daga birni, kuma rayukan waɗanda aka ji musu rauni suna kuka suna kira don taimako. Amma bai ba wani laifi ba. “Akwai waɗanda suke yi wa haske tawaye, waɗanda ba su san hanyoyinsa ba ko kuma ba su taɓa bin hanyoyinsa ba. Sa’ad da hasken yini ya tafi, mai kisankai yakan tashi; yă je yă kashe matalauta da masu bukata; a cikin dare yake shigowa kamar ɓarawo. Idanun mazinaci suna jiran yamma ta yi sosai; yana tunani cewa, ‘Ba wanda zai gan ni,’ sai kuma yă ɓoye fuskarsa. Cikin duhu mutane suna fasa gidaje, amma da rana sukan kulle kansu; ba sa so wani abu yă haɗa su da haske. Gama dukansu, duhu mai yawa shi ne safiyarsu; suna abokantaka da razanar duhu. “Duk da haka kamar abu marar nauyi suke a kan ruwa; gefen ƙasar da suke, an la’anta ta, yadda ba wanda yake zuwa gonar inabinsu. Kamar yadda zafi da fări suke shanye ƙanƙarar da ta narke, haka kabari zai ƙwace waɗanda suka yi zunubi. Waɗanda suka haife su za su manta da su, tsutsotsi za su cinye su; ba za a sāke tunawa da mugaye ba amma an sare su kamar itace. Suna cutar macen da ba ta da ɗa, suna nuna wa gwauruwa rashin alheri. Amma Allah cikin ikonsa yakan kawar da masu ƙarfi, ko da yake sun yi ƙarfi, ba su da tabbacin rayuwa. Mai yiwuwa zai bar su su zauna cikin kwanciyar hankali, amma idanunsa suna kansu. Sukan samu cin nasara na ɗan lokaci, amma kuma za su ɓace; za su fāɗi a tattara su kamar sauran; za a datse su kamar kan hatsi. “In wannan ba haka ba ne, wane ne zai shaida ƙarya nake yi har yă ƙi yarda da maganata?” Sai Bildad mutumin Shuwa ya amsa, “Mulki na Allah ne, dole a ji tsoronsa; yana tafiyar da kome yadda ya kamata a cikin sama. Za a iya ƙirga rundunarsa? A kan wane ne ba ya haska haskensa? Ta yaya mutum zai iya zama mai adalci a gaban Allah? Ta yaya mutumin da mace ta haifa zai zama mai tsarki? In har wata da taurari ba su da tsarki a idanunsa, mutum fa? Ai, wannan tsutsa ne, ɗan ƙwaro kawai. Me mutum ya daɗa a gaban Allah!” Sai Ayuba ya amsa, “Yadda ka taimaki marar ƙarfi! Yadda ka ceci marar ƙarfi! Ka ba marar hikima shawara! Ka nuna kana da ilimi sosai. Wane ne ya taimake ka ka yi waɗannan maganganu? Kuma ruhun wane ne ya yi magana ta bakinka? “Matattu suna cikin azaba, waɗanda suke ƙarƙashin ruwaye da dukan mazauna cikin ruwaye. Mutuwa tsirara take a gaban Allah; haka kuma hallaka take a buɗe. Ya shimfiɗa arewancin sararin sama a sarari; ya rataye duniya ba a jikin wani abu ba. Ya naɗe ruwaye a cikin gizagizansa, duk da haka girgijen bai yage saboda nauyi ba. Ya rufe fuskar wata, ya shimfiɗa gizagizai a kan shi, ya zāna iyakar fuskar ruwa a kan iyakar da take tsakanin duhu da haske. Madogaran sama sun girgiza, saboda tsawatawarsa. Da ikonsa ya kwantar da teku; da hikimarsa ya hallaka dodon ruwan nan Rahab. Da numfashinsa ya sa sararin sama ya yi kyau da hannunsa ya soke macijin nan mai gudu. Waɗannan kaɗan ke nan daga cikin ayyukansa masu yawa. Kaɗan kawai muke ji game da shi! Wane ne kuwa yake iya gane tsawar ikonsa?” Ayuba kuwa ya ci gaba da magana, “Na rantse da Allah mai rai, wanda ya danne mini gaskiyata, Maɗaukaki, wanda ya sa nake cikin ɗacin rai. Muddin ina da rai a cikina kuma numfashin Allah yana cikin hancina, bakina ba zai faɗi mugun abu ba, harshena kuma ba zai yi ƙarya ba. Ba zan taɓa yarda cewa kuna da gaskiya ba; har in mutu, ba zan daina kāre mutuncina ba. Zan ci gaba da adalcina, ba zan fasa ba; lamirina ba zai taɓa yashe ni ba, dukan kwanakin raina. “Bari maƙiyana su zama kamar mugaye, masu gāba da ni kuma su zama kamar marasa adalci. Gama wane bege marar tsoron Allah yake da shi, lokacin da aka datse shi, lokacin da Allah ya ɗauke ransa? Ko Allah yana sauraron kukansa lokacin da ƙunci ya auko masa? Ko zai sami farin ciki daga Maɗaukaki? Ko zai yi kira ga Allah a kowane lokaci? “Zan koya muku game da ikon Allah; ba zan ɓoye hanyoyin Maɗaukaki ba. Duk kun ga wannan ku da kanku saboda haka me ya sa kuke maganganun nan marasa ma’ana? “Ga abin da mugaye za su samu gādon da azzalumi zai samu daga Maɗaukaki. Kome yawan ’ya’yansa, takobi za tă gama da su; zuriyarsa ba za su taɓa samun isashen abinci ba. Waɗanda suka tsira annoba za tă kashe su, kuma gwaurayensu ba za su yi kukan mutuwarsu ba. Ko da yake ya tara azurfa kamar ƙasa, tufafi kuma kamar tarin ƙasa, abin da ya tara masu adalci za su sa marasa laifi za su raba azurfarsa. Gidan da ya gina kamar gidan gizo-gizo, kamar bukkar mai tsaro. Attajiri zai kwanta, amma daga wannan shi ke nan; lokacin da zai buɗe idanunsa, kome ya tafi. Tsoro zai kwashe shi kamar ambaliyar ruwa; Da dare iska za tă tafi da shi. Iskar gabas za tă tafi da shi; shi ke nan ya ƙare; za tă share shi daga wurinsa. Za tă murɗe shi ba tausayi, lokacin da yake guje wa ikon iskar. Zai tafa hannu yă yi tsaki yă kawar da shi daga wurinsa.” Akwai ramin azurfa akwai kuma wurin da ake tace zinariya. Daga cikin ƙasa ake ciro ƙarfe, ana kuma narkar da tagulla daga cikin dutse. Mutum ya kawo ƙarshen duhu; yakan bincike zuzzurfar iyaka, yana neman duwatsu a wuri mafi duhu. Nesa da inda mutane suke zama, yakan huda rami yă yi abin lilo, a wurin da mutane ba sa bi. Cikin ƙasa inda ake samun abinci, a ƙarƙashinta kuwa zafi ne kamar wuta; akwai duwatsu masu daraja a cikin duwatsunta, akwai kuma zinariya a cikin ƙurarta. Tsuntsu mai farauta bai san hanyarta ba, ba shahon da ya taɓa ganin ta. Manyan namun jeji ba su taɓa binta ba, ba zakin da ya taɓa binta. Hannun mutum ya iya sarrafa ƙanƙarar duwatsu, yă kuma tumɓuke tushen duwatsu. Yana tona rami a cikin duwatsu idanunsa suna ganin dukan dukiyar da ke cikin duwatsun. Yana nema daga ina ruwan rafi yake ɓulɓulowa yana kuma binciko abubuwan da suke a ɓoye yă kawo su cikin haske. Amma a ina ne za a iya samun hikima? Ina fahimta take zama? Mutum bai gane muhimmancinta ba, ba a samunta a ƙasar masu rai. Zurfi ya ce, “Ba ta wurina”; teku ya ce, “Ba ta wurina.” Ba irin zinariyar da za tă iya sayenta, ko kuma a iya auna nauyinta da azurfa. Ba za a iya sayenta da zinariyar Ofir, ko sauran duwatsu masu daraja ba. Zinariya da madubi ba za su iya gwada kansu da ita ba, ba kuwa za a iya musayarta da abubuwan da aka yi da zinariya ba. Kada ma a ce murjani da duwatsu masu walƙiya; farashin hikima ya fi na lu’ulu’ai. Ba za a iya daidaita darajarta da duwatsun Tofaz na Kush ba, zallar zinariya ma ba tă isa ta saye ta ba. “To, daga ina ke nan hikima ta fito? Ina fahimta take zama? An ɓoye ta daga idanun kowane abu mai rai, har tsuntsayen sararin sama ma an ɓoye masu ita. Hallaka da mutuwa suna cewa, ‘Jita-jitarta kaɗai muke ji.’ Allah ya gane hanyar zuwa wurinta. Shi ne kaɗai ya san inda take zama, Gama yana ganin iyakar duniya kuma yana ganin duk abin da yake ƙarƙashin sama. Lokacin da ya yi iska ya sa ta hura, ya kuma auna ruwaye. Lokacin da ya yi wa ruwan sama doka da kuma hanya domin walƙiya, sai ya dubi hikima ya auna ta; ya tabbatar da ita, ya gwada ta. Ya kuma ce wa mutum, ‘Tsoron Ubangiji shi ne hikima, kuma guje wa mugunta shi ne fahimi.’ ” Ayuba ya ci gaba da jawabinsa, “Da ma ina nan lokacin da ya wuce baya can, kwanakin da Allah yake lura da ni, lokacin da fitilarsa take haske a kaina na yi tafiya cikin duhu tare da haskensa. Kwanakin da nake tasowa, lokacin da abokantakar Allah ta sa wa gidana albarka, lokacin da Maɗaukaki yana tare da ni, kuma ’ya’yana suna kewaye da ni, lokacin da ake zuba madara a inda nake takawa, duwatsu kuma suna ɓulɓulo mini man zaitun. “Sa’ad da na je ƙofar birni na zauna a bainin jama’a, matasan da suka gan ni sukan ja gefe tsofaffi kuma suka tashi tsaye; sarakuna suka yi shiru suka rufe bakunansu da hannuwansu; Muryar manya ta yi tsit harshensu ya manne a rufin bakunansu. Duk wanda ya ji ni ya yaba mini waɗanda suka gan ni kuma sun amince da ni, domin na ceci matalauta waɗanda suka nemi taimako, da marasa mahaifi waɗanda ba su da wanda zai taimake su. Mutumin da yake bakin mutuwa ya sa mini albarka. Na faranta wa gwauruwa zuciya. Na yafa adalci ya zama suturata; gaskiya ita ce rigata da rawanina. Ni ne idon makafi kuma ƙafa ga guragu. Ni mahaifi ne ga masu bukata; na tsaya wa baƙo. Na karya ƙarfin mugaye na ƙwato waɗanda suke riƙe da haƙoransu. “Na yi tunani cewa, ‘Zan mutu a cikin gidana, kwanakina da yawa kamar turɓayar ƙasa. Jijiyoyina za su kai cikin ruwa, kuma raɓa za tă kwanta a rassana dukan dare. Ɗaukakata za tă kasance tare da ni garau, bakana koyaushe sabo ne a hannuna.’ “Mutane suna mai da hankali su saurare ni, suna yin shiru don su ji shawarata. Bayan da na yi magana, ba su ƙara ce kome ba. Maganata ta shige su. Sukan jira ni kamar yadda ake jiran ruwan sama. Sukan sha daga cikin maganganuna kamar mai shan ruwan bazara. Sa’ad da na yi musu murmushi da ƙyar sukan yarda; hasken fuskata yana da daraja a gare su. Na zaɓar masu inda za su bi na kuma zauna kamar sarkinsu; na zauna kamar sarki a cikin rundunansu; ina nan kamar mai yi wa masu makoki ta’aziyya. “Amma yanzu suna yi mini ba’a waɗanda na girme su, waɗanda iyayensu maza ba su isa su zama karnukan kiwon garken tumakina ba. Ina amfani ƙarfin hannuwansu gare ni, tun da ba su da sauran kuzari? Duk sun rame don rashi da yunwa, suna yawo a gaigayar ƙasa a kufai da dare. A cikin jeji suna tsinkar ganyaye marasa daɗi, jijiyoyin itacen kwakwa ne abincinsu. An kore su daga cikin mutanensu, aka yi musu ihu kamar ɓarayi. An sa dole su zauna a kwazazzabai da kuma cikin kogunan duwatsu da kuma cikin ramummuka cikin ƙasa. Suka yi ta kuka kamar dabbobi a jeji, suka taru a ƙarƙashin sarƙaƙƙiya. Mutane marasa hankali marasa suna, an kore su daga ƙasar. “Yanzu kuma ’ya’yansu maza su suke yi mini ba’a cikin waƙa na zama abin banza a gare su. Suna ƙyamata suna guduna; suna tofa mini miyau a fuska. Yanzu da Allah ya kunce bakana ya ba ni wahala sun raba ni da mutuncina. A hannun damana ’yan tā-da-na-zaune-tsaye sun tayar; sun sa tarko a ƙafafuna, sun yi shirin hallaka ni. Sun ɓata mini hanyata; sun yi nasara cikin hallaka ni, ba tare da wani ya taimake su ba. Suka nufo ni daga kowane gefe; suka auko mini da dukan ƙarfinsu. Tsoro ya rufe ni; an kawar mini mutuncina kamar da iska, dukiyata ta watse kamar girgije. “Yanzu raina yana ƙarewa; kwanakin wahala sun kama ni. Dare ya huda ƙasusuwana; ina ta shan azaba ba hutawa. A cikin girman ikonsa Allah ya zama kamar riga a jikina; ya shaƙe ni kamar wuyan rigata. Ya jefa ni cikin laka, na zama ba kome ba sai ƙura da toka. “Na yi kuka gare ka ya Allah, amma ba ka amsa mini ba. Na tashi tsaye, amma sai ka dube ni kawai. Ka dube ni ba tausayi; Ka kai mini hari da ƙarfin hannunka. Ka ɗaga ni sama ka ɗora ni a kan iska; ka jujjuya ni cikin hadari. Na san za ka sauko da ni ga mutuwa zuwa wurin da kowane mai rai zai je. “Ba shakka ba mai ɗora hannu a kan mutumin da yake cikin wahala. Lokacin da ya yi kukan neman taimako a cikin wahalarsa. Ashe ban yi kuka domin waɗanda suke cikin damuwa ba? Ko zuciyata ba tă yi baƙin ciki domin matalauta ba? Duk da haka sa’ad da nake begen abu mai kyau, mugun abu ne ya zo; Sa’ad da nake neman haske, sai duhu ya zo. Zuciyata ba tă daina ƙuna ba; ina fuskantar kwanakin wahala. Na yi baƙi ƙirin, amma ba rana ce ta ƙona ni ba. Na tsaya a cikin mutane, na kuma yi kuka don taimako. Na zama ɗan’uwan diloli, na zama abokan mujiyoyi. Fatar jikina ta yi baƙi tana ɓarewa; jikina yana ƙuna da zazzaɓi. Garayata ta zama ta makoki, sarewata kuma ta zama ta kuka. “Na yi alkawari da idanuna kada su dubi budurwa da muguwar sha’awa. Gama mene ne rabon mutum daga Allah a sama, gādonsa daga Maɗaukaki a sama? Ba masifa ba ne domin mugaye, hallaka kuma ga waɗanda suka yi ba daidai ba? Bai ga hanyoyina ba ne bai ƙirga kowace takawata ba? “In da na yi tafiya cikin rashin gaskiya ko kuma ƙafata ta yi sauri zuwa yin ƙarya, Bari Allah yă auna a kan ma’auni na gaskiya zai kuma san cewa ni marar laifi ne. In takawata ta kauce daga hanya, in zuciyata ta bi abin da idanuna ke so, ko kuma in hannuwana suna da laifi; bari waɗansu su ci abin da na shuka, kuma bari a tuge amfanin gonata. “In sha’awar mace ya shiga mini zuciya, ko kuma na laɓe a ƙofar maƙwabcina, sai matata ta niƙa hatsin wani kuma waɗansu maza su kwana da ita. Gama wannan zai zama abin kunya, zunubin da za a yi shari’a a kai. Wuta ce take ƙuna har ta hallakar; za tă cinye saiwar abin da na shuka ƙurmus. “In da na danne wa bayina maza da mata hakkinsu, sa’ad da suke da damuwa da ni, me zan yi lokacin da Allah ya tuhume ni? Me zan ce lokacin da ya tambaye ni? Shi wanda ya yi ni a cikin uwata ba shi ne ya yi su ba? Ba shi ne ya yi mu a cikin uwayenmu ba? “In na hana wa matalauta abin da suke so, ko kuma in sa idanun gwauruwa su yi nauyi don kuka, in na ajiye burodina don kaina kaɗai, ban kuwa ba wa marayu abinci sa’ad da suke jin yunwa, amma tun suna tasowa na lura da su, kamar yadda mahaifi zai lura da ɗa, kuma tun da aka haife ni ina lura da gwauruwa. In da na ga wani yana mutuwa don rashin sutura, ko wani mai bukata da ba shi da riga, kuma zuciyarsa ba tă gode mini ba don na yi masa sutura da gashin tumakina, in na ɗaga hannuna don in cuci maraya, domin na san in na faɗa za a ji ni a wurin masu shari’a, bari hannuna yă guntule daga kafaɗata, bari yă tsinke daga inda aka haɗa shi. Gama ina jin tsoron hallaka daga Allah, kuma domin tsoron ɗaukakarsa ba zan iya yin waɗannan abubuwa ba. “In na dogara ga zinariya ko kuma na ce wa zallan zinariya, ‘Gare ki nake dogara,’ in na yi fahariya don yawan dukiyata, arzikin da hannuwana suka samu. In na dubi rana cikin haskenta, ko kuma wata yana tafiyarsa, zuciyata ta jarrabtu gare su a ɓoye, hannuna kuma ya sumbace su. Waɗannan ma za su zama zunubin da za a shari’anta ke nan don zai zama na yi wa Allah na sama rashin aminci. “In na yi murna domin mugun abu ya faru da maƙiyina; ko kuma domin wahala ta same shi, ban bar bakina yă yi zunubi ta wurin la’anta shi ba, in mutanen gidana ba su taɓa cewa, ‘Wane ne bai ƙoshi da naman Ayuba ba?’ Ba baƙon da ya taɓa kwana a titi, gama koyaushe ƙofata tana buɗe domin matafiya, in na ɓoye zunubina yadda mutane suke yi, ta wurin ɓoye laifina a cikin zuciyata, domin ina tsoron taron mutane kuma ina tsoron wulaƙancin da dangina za su yi mini, sai na yi shiru kuma ban fita waje ba. (“Kash, da ina da wanda zai ji ni! Na sa hannu ga abin da na faɗa don kāre kaina, bari Maɗaukaki yă amsa mini; bari mai tuhumata da laifi yă yi ƙarata a rubuce. Ba shakka sai in ɗora a kafaɗata, zan aza a kaina kamar rawani. Zan ba shi lissafin duk abin da na taɓa yi; zan zo gabansa kamar ɗan sarki.) “In ƙasata tana kuka da ni kunyoyinta duk sun cika da hawaye, in na kwashe amfaninta ban biya ba ko kuma na kashe masu ita, bari ƙaya ta fito a maimakon alkama ciyawa kuma a maimakon sha’ir.” Maganar Ayuba ta ƙare. Sai mutanen nan uku suka daina amsa wa Ayuba, domin a ganinsa shi mai adalci ne. Amma Elihu ɗan Barakel mutumin Buz na iyalin Ram, ya ji haushi da Ayuba don yă nuna shi ne mai gaskiya ba Allah ba. Ya kuma ji haushin abokan nan guda uku, don sun kāsa amsa wa Ayuba ko da yake sun nuna Ayuba ne yake da laifi. Elihu ya jira sai a wannan lokaci ne ya yi magana da Ayuba, don shi ne yaro a cikinsu duka. Amma sa’ad da Elihu ya ga mutanen nan uku ba su da abin cewa, sai ya fusata. Sai Elihu ɗan Barakel mutumin Buz ya ce, “Ni ƙarami ne a shekaru, ku kuma kun girme ni; shi ya sa na ji tsoro na kāsa gaya muku abin da na sani. Na ɗauka ya kamata ‘shekaru su yi magana; ya kamata yawan shekaru su koyar da hikima.’ Amma ruhun da yake cikin mutum, numfashin Maɗaukaki shi ne yake ba shi ganewa. Ba tsofaffi ne kaɗai suke da hikima ba, ba masu yawan shekaru ne suke gane abin da yake daidai ba. “Saboda haka nake ce muku, ku saurare ni; ni ma zan gaya muku abin da na sani. Na jira sa’ad da kuke magana, na ji muhawwararku lokacin da kuke neman abin da za ku faɗa, na saurare ku da kyau. Amma ba waninku da ya nuna Ayuba yana da laifi; ba ko ɗayanku da ya amsa muhawwararsa. Kada ku ce, ‘Mun sami hikima; Allah ne kaɗai yake da ikon yin nasara da shi ba mutum ba.’ Amma ba da ni Ayuba ya yi gardama ba kuma ba zan amsa masa da irin amsarku ba. “Mamaki ya kama su kuma ba su da abin cewa; kalmomi sun kāsa musu. Dole ne in jira yanzu da suka yi shiru, yanzu da suke tsaye a wurin ba su da amsa. Ni ma zan faɗi nawa; ni ma zan faɗi abin da na sani. Gama ina cike da magana, kuma ruhun da yake cikina yana iza ni; a ciki ina kamar ruwan inabi wanda aka rufe a cikin kwalaba, kamar sabuwar salkar ruwan inabi mai shirin fashewa. Dole in yi magana in sami lafiya; dole in buɗe baki in ba da amsa. Ba zan nuna wa wani sonkai ba, ko kuma in yi wa wani daɗin baki ba; gama da a ce na iya daɗin baki, da wanda ya yi ni ya ɗauke ni daga nan tuntuni. “Amma yanzu, Ayuba, ka saurari abin da zan ce; ka sa hankali ga kowane abin da zan faɗa. Zan yi magana; kalmomina suna dab da fitowa daga bakina. Abin da zan faɗa gaskiya ne daga cikin zuciyata; bakina zai faɗi gaskiyar abin da na sani. Ruhun Allah ne ya yi ni; numfashin Maɗaukaki ya ba ni rai. Ka amsa mini in za ka iya; ka yi shirin fuskanta ta. Ni kamar ka nake a gaban Allah; ni ma daga ƙasa aka yi ni. Kada ka ji tsorona, ba abin da zai fi ƙarfinka. “Amma ka faɗa na ji, na ji daidai abin da ka faɗa, ‘ni mai tsarki ne marar zunubi; ina da tsabta kuma ba ni da laifi. Duk da haka Allah ya same ni da laifi; ya ɗauke ni maƙiyinsa, ya daure ƙafafuna da sarƙa; yana tsaron duk inda na bi.’ “Amma na gaya maka, a nan ba ka yi daidai ba, gama Allah ya fi mutum girma. Don me ka yi masa gunaguni cewa ba ya amsa tambayoyin mutum? Gama Allah yana magana, yanzu ga wannan hanya, yanzu kuma ga wata hanya ko da yake ba lalle mutum yă lura ba. A cikin mafarki, cikin wahayi da dare, sa’ad da barci mai zurfi ya fāɗo a kan mutane lokacin da suke cikin barci kan gadajensu, mai yiwuwa yă yi musu magana a cikin kunnuwansu yă razana su da gargaɗinsa, don a juyar da su daga abin da yake yi da ba daidai ba a kuma hana su daga girman kai, don a kāre su daga fāɗuwa cikin rami, a kāre su daga hallaka ta wurin takobi. “Ko kuma mutum yă sha horo ta wurin kwanciya da ciwo da rashin jin daɗi cikin ƙasusuwansa, yadda zai ji ƙyamar abinci, har yă ƙi son abinci mafi daɗi. Naman jikinsa ya lalace ba wani abu mai kyau a ciki kuma ƙasusuwansa da suke a rufe da tsoka yanzu duk sun fito. Ransa yana matsawa kusa da rami, ransa kuma kusa da ’yan aikan mutuwa. Duk da haka, in akwai mala’ika a gefensa kamar matsakanci, ɗaya daga cikin dubu, da zai gaya wa mutum abin da yake daidai gare shi, yă yi masa alheri yă ce, ‘Kada ka bari yă fāɗa cikin rami, na samu fansa dominsa.’ Sa’an nan fatar jikinsa za tă zama sabuwa kamar ta jariri; za tă zama kamar lokacin da yake matashi. Ya yi addu’a ga Allah ya kuwa samu alheri a wurinsa, yana ganin fuskar Allah yana kuma yin sowa don murna; Allah ya mayar da shi ya zama mai adalci. Sa’an nan sai ya zo wurin, wurin mutane ya ce, ‘Na yi zunubi, na kauce wa abin da yake daidai, amma ban samu abin da ya kamata in samu ba. Ya fanshi raina daga fāɗawa cikin rami, kuma zan rayu in ji daɗin hasken.’ “Allah ya yi wa mutum duk waɗannan, sau biyu, har ma sau uku. Ya juyo da ransa daga fāɗawa cikin rami, don hasken rai ya haskaka a kansa. “Ka sa hankali da kyau, Ayuba, ka saurare ni; ka yi shiru zan yi magana. In kana da abin da za ka ce, ka amsa mini; yi magana, domin ina so in ’yantar da kai. Amma in ba haka ba, sai ka saurare ni; yi shiru, zan kuma koya maka hikima.” Sa’an nan Elihu ya ce, “Ku ji maganata, ku masu hikima; ku saurare ni, ku masu ilimi. Gama kunne yana rarrabe magana kamar yadda harshe yake ɗanɗana abinci. Bari mu zaɓi abin da yake daidai, bari mu koyi abin da yake mai kyau tare. “Ayuba ya ce, ‘Ba ni da laifi, amma Allah ya hana mini hakkina. Ko da yake ina da gaskiya, an ɗauke ni maƙaryaci; ko da yake ba ni da laifi, kibiyoyinsa sun ji mini ciwo wanda ba ya warkewa.’ Wane mutum ne kamar Ayuba, wanda yake shan ba’a kamar ruwa? Yana abokantaka da masu aikata mugunta; yana cuɗanya da mugaye. Gama ya ce, ‘Ba ribar da mutum zai samu lokacin da yake ƙoƙari yă faranta wa Allah zuciya.’ “Saboda haka ku saurare ni, ku masu ganewa. Ko kaɗan Allah ba ya mugunta, Maɗaukaki ba ya kuskure. Yana biyan mutum bisa ga abin da ya yi; yana kawo masa abin da ayyukansa suka jawo. Ba zai yiwu Allah yă yi ba daidai ba, Maɗaukaki ba zai yi shari’a marar gaskiya ba. Wane ne ya ba shi iko yă lura da duniya? Wane ne ya ba shi iko kan dukan duniya? In nufinsa ne ya kuma janye ruhunsa da numfashinsa, ’yan adam duka za su hallaka tare, mutum kuma zai koma ƙasa. “In kana da ganewa sai ka saurari wannan; ka saurari abin da zan ce. Maƙiyin gaskiya zai iya yin mulki? Za ka iya ba mai gaskiya, Maɗaukaki laifi? Ba shi ne ya ce wa sarakuna, ‘Ba ku da amfani ba,’ ya ce wa manya ‘Ku mugaye ne,’ wanda ba ya nuna sonkai ga ’ya’yan sarki kuma ba ya goyon bayan masu arziki a kan matalauta, gama dukansu shi ya yi su da hannuwansa. Suna mutuwa nan take, a cikin tsakiyar dare; an girgiza mutanen amma sun wuce; an taɓa manya amma ba da hannun mutum ba. “Idanunsa suna kan al’amuran mutane; yana ganin tafiyarsu duka. Babu wuri mai duhu, babu inuwa mai duhu, inda masu aikata mugunta za su ɓoye. Allah ba ya bukata yă ci gaba da bincike mutane, har da za su zo gabansa don yă shari’anta su. Ba tare da tambaya ba yana ragargaza masu iko, yă kuma sa waɗansu a wurinsu. Gama yana sane da abubuwan da suke yi, yana hamɓarar da su da dare a kuma ragargaza su. Yana ba su horo, don muguntarsu, inda kowa zai gan su, domin sun juya daga binsa, kuma ba su kula da hanyoyinsa ba. Sun sa kukan matalauta ya kai wurinsa yadda ya kai ga jin kukan masu bukata. Amma in ya yi shiru, wa zai ba shi laifi? In ya ɓoye fuskarsa, wa zai gan shi? Duk da haka shi yake da iko kan mutum da al’umma duka, yana hana wanda bai san Allah ba yă yi mulki, ya hana shi sa wa mutane tarko. “A ce mutum ya ce wa Allah, ‘Na yi laifi, amma ba zan sāke saɓa wa wani ba. Ka koya mini abin da ba zan iya gani ba; in na yi ba daidai ba, ba zan sāke yi ba.’ Ya kamata Allah yă yi maka bisa ga abin da ka ce ne, sa’ad da ka ƙi ka tuba? Dole kai ka zaɓa, ba ni ba; yanzu ka gaya mini abin da ka sani. “Mutane masu ganewa za su ce, masu hikima waɗanda suka ji ni za su ce mini, ‘Ayuba ya yi magana cikin rashin sani; maganganunsa na marar hikima ne.’ Kash, da za a gwada Ayuba har ƙarshe, domin yana ba da amsa kamar mugun mutum. Ya ƙara tawaye a kan zunubansa; ya tafa hannuwansa na reni a cikinmu ya kuma ƙara yawan maganganunsa ga Allah.” Sai Elihu ya ce, “Ko kana tsammani wannan gaskiya ne? Kana cewa, ‘Ni mai adalci ne a gaban Allah.’ Duk da haka kana tambayarsa cewa, ‘Wace riba nake da ita, kuma mene ne zan samu ta wurin ƙin yin zunubi?’ “Zan so in ba ka amsa kai tare da abokanka. Ku ɗaga kai ku dubi sama ku gani; ku dubi gizagizai a samanku. In kun yi zunubi ta yaya wannan zai shafi Allah? In zunubanku sun yi yawa, me wannan zai yi masa? In kuna da adalci, me kuka ba shi, ko kuma me ya karɓa daga hannunku? Muguntarku takan shafi mutum kamar ku ne kaɗai, adalcinku kuma yakan shafi ’yan adam ne kaɗai. “Mutane suna kuka don yawan zalunci; suna roƙo don taimako daga hannu mai ƙarfi. Amma ba wanda ya ce, ‘Ina Allah wanda ya halicce ni, mai ba da waƙoƙi cikin dare, wanda ya fi koya mana fiye da dabbobin duniya ya kuma sa muka fi tsuntsayen cikin iska hikima.’ Ba ya amsawa lokacin da mutane suka yi kira don taimako domin girman kan mugaye. Lalle Allah ba ya sauraron roƙonsu na wofi; Maɗaukaki ba ya kula da roƙonsu. Ta yaya zai saurara sosai ko zai saurara lokacin da kake cewa ba ka ganinsa, cewa ka kawo ƙara a wurinsa kuma dole ka jira shi. Kuma ka ce, ba ya ba da horo cikin fushinsa ko kaɗan ba ya kula da mugunta. Saboda haka Ayuba ya buɗe baki yana magana barkatai; yana ta yawan magana ba tare da sani ba.” Elihu ya ci gaba, “Ka ɗan ƙara haƙuri da ni kaɗan, zan kuma nuna maka cewa akwai sauran abubuwan da zan faɗa a madadin Allah. Daga nesa na sami sanina; zan nuna cewa Mahaliccina shi mai gaskiya ne. Abin da zan gaya maka ba ƙarya ba ne; mai cikakken sani yana tare da kai. “Allah mai iko ne, amma ba ya rena mutane; shi mai girma ne cikin manufarsa. Ba ya barin mugaye da rai sai dai yana ba waɗanda ake tsanantawa hakkinsu. Ba ya fasa duban masu adalci; yana sa su tare da sarakuna yana ɗaukaka su har abada. Amma in mutane suna daure da sarƙoƙi, ƙunci kuma ya daure su, yana gaya musu abin da suka yi, cewa sun yi zunubi da girman kai. Yana sa su saurari gyara yă kuma umarce su su tuba daga muguntarsu. In sun yi biyayya suka bauta masa, za su yi rayuwa dukan kwanakinsu cikin wadata shekarunsu kuma cikin kwanciyar zuciya. Amma in ba su saurara ba, za su hallaka da takobi kuma za su mutu ba ilimi. “Waɗanda ba su da Allah a zuciyarsu su ne suke riƙe fushi; ko sa’ad da ya ba su horo, ba su neman taimakonsa. Suna mutuwa tun suna matasa, cikin ƙazamar rayuwar karuwanci. Amma yana kuɓutar da masu wahala; yana magana da su cikin wahalarsu. “Yana so yă rinjaye ka daga haƙoran ƙunci, zuwa wuri mai sauƙi inda ba matsi zuwa teburinka cike da abincin da kake so. Amma yanzu an cika ka da hukuncin da ya kamata a yi wa mugaye; shari’a da kuma gaskiya sun kama ka. Ka yi hankali kada wani yă ruɗe ka da arziki; kada ka bar toshiya ta sa ka juya. Dukiyarka ko dukan yawan ƙoƙarinka sun isa su riƙe ka su hana ka shan ƙunci? Kada ka yi marmari dare yă yi, don a fitar da mutane daga gidajensu. Ka kula kada ka juya ga mugunta, abin da ka fi so fiye da wahala. “An ɗaukaka Allah cikin ikonsa. Wane ne malami kamar sa? Wane ne ya nuna masa hanyar da zai bi, ko kuma wane ne ya ce masa, ‘Ba ka yi daidai ba?’ Ka tuna ka ɗaukaka aikinsa, waɗanda mutane suka yaba a cikin waƙa. Dukan ’yan adam sun gani; mutane sun hanga daga nesa. Allah mai girma ne, ya wuce ganewarmu! Yawan shekarunsa ba su bincikuwa. “Yana sa ruwa yă zama tururi yă zubo daga sama. Gizagizai suna zubo da raɓarsu kuma ruwan sama yana zubowa ’yan adam a wadace. Wane ne zai iya gane yadda ya shimfiɗa gizagizai yadda yake tsawa daga wurin zamansa? Dubi yadda ya baza walƙiyarsa kewaye da shi, tana haskaka zurfin teku. Haka yake mulkin al’ummai yana kuma tanada abinci a wadace. Yana cika hannuwansa da walƙiya kuma yana ba ta umarni tă fāɗi a inda ya yi nufi. Tsawarsa tana nuna cewa babbar iska da ruwa suna zuwa; ko shanu sun san da zuwansa. “Wannan ya sa gabana ya fāɗi, zuciyata ta yi tsalle. Ka saurara! Ka saurari rurin muryarsa, tsawar da take fita daga bakinsa. Ya saki walƙiyarsa, a ƙarƙashin dukan sammai ya kuma aika ta ko’ina a cikin duniya. Bayan wannan sai ƙarar rurinsa ta biyo; Ya tsawata da muryarsa mai girma. Sa’ad da ya sāke yin tsawa ba ya rage wani abu. Muryar Allah tana tsawatawa a hanyoyi masu ban al’ajabi; yana yin manyan abubuwa waɗanda sun wuce ganewarmu. Yakan ce wa dusar ƙanƙara, ‘Fāɗo a kan duniya,’ ya kuma ce wa ruwa, ‘Zubo da ƙarfi.’ Domin dukan mutanen da ya halitta za su san aikinsa, ya hana kowane mutum yin wahalar aiki. Dabbobi sun ɓoye; sun zauna cikin kogunansu. Guguwa tana fitowa daga inda take, sanyi kuma daga iska mai sanyi. Da numfashinsa Allah yana samar da ƙanƙara sai manyan ruwaye su zama ƙanƙara. Yana cika gizagizai da lema; yana baza walƙiyarsa ta cikinsu. Bisa ga bishewarsa suke juyawa a kan fuskar duniya, suna yin dukan abin da ya umarce su su yi. Yana aiko da ruwa domin horon mutane, ko kuma don yă jiƙa duniya yă kuma nuna ƙaunarsa. “Ka saurari wannan Ayuba; ka tsaya ka dubi abubuwan al’ajabi na Allah. Ko ka san yadda Allah yake iko da gizagizai ya kuma sa walƙiyarsa ta haskaka? Ko ka san yadda gizagizai suke tsayawa cik a sararin sama, waɗannan abubuwa al’ajabi na mai cikakken sani. Kai mai sa kaya don ka ji ɗumi lokacin da iska mai sanyi take hurawa, ko za ka iya shimfiɗa sararin sama tare da shi da ƙarfi kamar madubi? “Gaya mana abin da ya kamata mu ce masa; ba za mu iya kawo ƙara ba domin duhunmu. Ko za a gaya masa cewa ina so in yi magana? Ko wani zai nemi a haɗiye shi? Yanzu ba wanda zai iya kallon rana, yadda take da haske a sararin sama bayan iska ta share ta. Yana fitowa daga arewa da haske na zinariya, Allah yana zuwa da ɗaukaka mai ban al’ajabi. Maɗaukaki ya fi ƙarfin ganewarmu, shi babban mai iko ne, mai gaskiya da babban adalci, ba ya cutar mutum. Saboda haka, mutane suke girmama shi, ko bai kula da waɗanda suke gani su masu hikima ba ne?” Sa’an nan Ubangiji ya amsa wa Ayuba. Ya ce, “Wane ne wannan da yake ɓata mini shawarata da surutan wofi? Ka sha ɗamara kamar namiji; zan yi maka tambaya, za ka kuwa amsa mini. “Kana ina lokacin da na aza harsashen duniya? Gaya mini, in ka sani. Wane ne ya zāna girmanta? Ba shakka ka sani! Wane ne ya ja layin aunawa a kanta? A kan me aka kafa tushenta, ko kuma wa ya sa dutsen kan kusurwarta, yayinda taurarin safe suke waƙa tare dukan mala’iku kuma suka yi sowa don farin ciki. “Wane ne ya rufe teku a bayan ƙofofi, lokacin da ya burtsatso daga cikin ciki. Lokacin da na yi wa gizagizai riga na kuma naɗe su a cikin duhu sosai, sa’ad da na yi masa iyaka na sa masa ƙofofi da wurin kullewa. Sa’ad da na ce ga iyakar inda za ka kai, ga inda raƙuman ruwanka za su tsaya? “Ko ka taɓa ba safiya umarni ko kuma ka sa asuba ta fito, don ta kama gefen duniya ta kakkaɓe mugaye daga cikinta? Ƙasa ta sāke siffa kamar laka da aka yi wa hatimi; ta fito a fili kamar riga. An hana mugaye haskensu, hannun da suka ɗaga an karya shi. “Ko ka taɓa tafiya zuwa maɓulɓulan teku, ko kuma ka taɓa zuwa cikin zurfin lungun teku? Ko an taɓa nuna maka ƙofar mutuwa? Ko ka taɓa ganin ƙofar inuwar duhun mutuwa? Ko ka gane fāɗin duniya? Gaya mini, in ka san wannan duka. “Ina ne hanyar zuwa gidan haske? Kuma a ina duhu yake zama? Ko za ka iya kai su wurarensu? Ka san hanyar zuwa wurin da suke zama? Ba shakka ka sani, gama an riga an haife ka a lokacin! Ka yi shekaru da yawa kana rayuwa. “Ka taɓa shiga rumbunan dusar ƙanƙara ko ka taɓa ganin rumbunan ƙanƙara waɗanda nake ajiya domin lokacin wahala, domin kwanakin yaƙi da faɗa? Ina ne hanyar zuwa wurin da ake samun walƙiya, ko kuma inda daga nan ne ake watsa iskar gabas zuwa ko’ina cikin duniya? Wane ne ya yanka hanyar wucewar ruwa, da kuma hanyar walƙiyar tsawa don ba da ruwa a ƙasar da ba kowa a wurin jeji inda ba mai zama ciki don a ƙosar da wurin da ya bushe a sa ciyawa ta tsiro a can? Ruwan sama yana da mahaifi? Wa ya zama mahaifin raɓa? Daga cikin wane ne aka haifi ƙanƙara? Wane ne ya haifi jaura daga sammai lokacin da ruwa ya zama da ƙarfi kamar dutse, lokacin da saman ruwa ya daskare? “Za ka iya daure kyakkyawar kaza da ’ya’yanta? Ko za ka iya kunce igiyoyin mafarauci da kare da zomo? Za ka iya tattara taurari bisa ga lokacinsu ko kuma ka bi da beyar da ’ya’yanta zuwa waje? Ka san dokokin sammai? Ko za ka iya faɗar dangantakar Allah da duniya? “Za ka iya tsawata wa gizagizai ka kuma rufe kanka da ambaliyar ruwa? Kai ne kake aika walƙiya da tsawa zuwa inda suke zuwa? Ko suna zuwa wurinka su ce, ‘Ga mu nan mun zo?’ Wane ne yake cika zuciya da hikima ko kuma yake ba zuciya ganewa? Wane ne yake da hikimar iya ƙirga gizagizai? Wane ne zai iya karkato bakunan tulunan sammai sa’ad da ƙura ta yi yawa ta daskare a wuri ɗaya? “Za ka iya farauto wa zakanya nama, ka kuma kawar wa zakoki yunwarsu. Lokacin da suka kwanta cikin kogunansu, ko kuma lokacin da suke a wurin ɓuyansu? Wane ne yake ba hankaka abinci lokacin da ’ya’yansa suke kuka ga Allah, kuma suna yawo don rashin abinci? “Ka san lokacin da awakin kan dutse suke haihuwa? Ko ka taɓa lura da yadda batsiya take haihuwa? Kana ƙirga watanni nawa suke yi kafin su haihu? Ka san lokacin da suke haihuwa? Suna kwanciya su haifi ’ya’yansu; naƙudarsu ta ƙare bayan sun haihu. ’Ya’yansu suna girma kuma suna girma cikin ƙarfi a jeji; sukan tafi ba su dawowa. “Wane ne yake sakin jakin dawa yă bar shi? Wane ne yake kunce igiyoyinsu? Na sa jeji yă zama gidansa ƙasar gishiri kuma ta zama wurin zamansa. Yana dariyar hargitsin da yake faruwa a cikin gari; ba ya jin tsawar mai tuƙa shi. Yana kiwo a kan tuddai don abincinsa yana neman kowane ɗanyen abu mai ruwan ciyawa. “Ko ɓauna zai yarda yă zauna a wurin sa wa dabbobi abinci? Zai tsaya a ɗakin dabbobinka da dare? Ko za ka iya daure shi da igiya a kwarin kunya? Zai yi maka buɗar gonarka? Ko za ka dogara da shi don yawan ƙarfinsa? Za ka bar masa nauyin aikinka? Ko za ka amince da shi yă kawo maka hatsinka gida yă tattara shi a masussuka? “Fikafikan jimina suna bugawa cike da farin ciki amma ba za su gwada kansu da fikafikan da na shamuwa ba. Tana sa ƙwai nata a ƙasa kuma ta bar su su yi ɗumi a cikin ƙasa, ba tă damu ko za a taka su a fasa su, ko waɗansu manyan dabbobi za su tattake su. Tana tsananta wa ’ya’yanta kamar ba nata ba ba tă damu da wahalar da ta sha ba. Gama Allah bai ba ta hikima ba ko kuma iya fahimta. Duk da haka sa’ad da ta buɗe fikafikanta ta shara da gudu tana yi wa doki da mai hawansa dariya. “Ko kai ne kake ba doki ƙarfinsa kai kake rufe wuyansa da geza mai yawa? Ko kai kake sa shi yă yi tsalle kamar fāra, ba ya jin tsoro sai dai a ji tsoronsa. Yana takawa da ƙarfi yana jin daɗin ƙarfinsa yana shiga filin yaƙi gabagadi. Yana yi wa tsoro dariya ba ya jin tsoron kome; ba ya guje wa takobi. Kwari a baka yana lilo a gabansa kibiya da māshi suna wuce kansa. Yana kartar ƙasa da ƙarfi; ba ya iya tsayawa tsab sa’ad da ya ji busar ƙaho. Da jin ƙarar ƙaho sai ya ce, ‘Yauwa!’ Ya ji ƙanshin yaƙi daga nesa, da ihun shugabannin yaƙi. “Ko ta wurin hikimarka ce shirwa take firiya take kuma baza fikafikanta zuwa kudu? Ko da umarninka ne shaho yake firiya ya kuma yi sheƙarsa a can sama? Yana zama a kan dutse yă zauna a wurin da dare; cikin duwatsu ne wurin zamansa. Daga can yake neman abincinsa; idanunsa suna gani daga nesa. ’Ya’yansa suna shan jini, inda akwai waɗanda aka kashe nan za a same shi.” Ubangiji ya ce wa Ayuba, “Mai neman sa wa wani laifi zai iya ja da Maɗaukaki? Bari mai tuhumar Allah yă amsa masa.” Sai Ayuba ya amsa wa Ubangiji, “Ai, ni ba a bakin kome nake ba ne, ta yaya zan iya amsa maka? Na rufe bakina da hannuna. Na yi magana sau ɗaya amma ba ni da amsa, sau biyu, amma ba zan ƙara cewa kome ba.” Sa’an nan Ubangiji ya yi wa Ayuba magana ta cikin guguwa, “Ka tashi tsaye ka tsaya da ƙarfi kamar namiji; zan yi maka tambaya kuma za ka amsa mini. “Ko za ka ƙi yarda da shari’ata? Za ka ba ni laifi don ka nuna kai marar laifi ne? Ko hannunka irin na Allah ne, kuma ko muryarka za tă iya tsawa kamar ta Allah? Sai ka yi wa kanka ado da ɗaukaka da girma, ka yafa daraja da muƙami. Ka saki fushinka, ka dubi dukan wani mai girman kai ka wulaƙanta shi. Ka dubi duk wani mai girman kai ka ƙasƙantar da shi, ka tattake mugaye a inda ka tsaya. Ka bizne su duka tare ka rufe fuskokinsu a cikin kabari. Sa’an nan ni kaina zan shaida maka cewa hannun damanka zai iya cetonka. “Dubi dorina, wadda na halicce ku tare kuma ciyawa take ci kamar sa. Ga shi ƙarfinta yana a ƙugunta ikonta yana cikin tsokar cikinta. Wutsiyarta tana da ƙarfi kamar itacen al’ul; jijiyoyin cinyoyinta suna haɗe a wuri ɗaya. Ƙasusuwanta bututun tagulla ne, haƙarƙarinta kamar sandunan ƙarfe. Tana ta farko cikin ayyukan Allah, Mahaliccinta kaɗai yake iya tunkarar ta da takobi. Tuddai su suke tanada mata abinci a inda duk namun jeji suke wasa. Tana kwanciya a ƙarƙashin inuwar itacen lotus ta ɓuya cikin kyauro da fadama. Inuwa ta rufe ta da ƙaddaji, itatuwan wardi na rafi, sun kewaye ta. Sa’ad da kogi ya cika yana hauka, ba tă damu ba; ba abin da zai same ta ko da a gaban bakinta Urdun yake wucewa. Ko akwai wanda zai iya kama ta ba ta kallo, ko kuma a kama ta da tarko a huda hancinta? “Ko za ka iya kama dodon ruwa da ƙugiyar kamar kifi ko kuma ka daure harshenta da igiya? Za ka iya sa igiya a cikin hancinta ko kuma ka huda muƙamuƙanta da ƙugiya? Za tă ci gaba da roƙonka ka yi mata jinƙai? Ko za tă yi maka magana a hankali? Za tă yi yarjejjeniya da kai don ka ɗauke ta tă zama baiwa gare ka dukan kwanakin ranta? Za ka yi wasa da ita kamar yadda za ka yi da tsuntsu? Ko za ka daure ta da tsirkiya domin bayinka mata? ’Yan kasuwa za su saye ta ko za su raba ta a tsakaninsu? Ko za ka iya huda fatarta da kibiya ka kuma huda kansa da māsu? In ka ɗora hannunka sau ɗaya a kanta za ka tuna da yaƙin da ba za ka sāke yi ba! Duk ƙoƙarin kama ta banza ne; ganin ta kawai abin tsoro ne. Ba wanda ya isa yă tsokane ta. Wane ne kuma ya isa yă yi tsayayya da ni? Wane ne yake bi na bashi da dole in biya? Duk abin da yake ƙarƙashin sama nawa ne. “Ba zan daina magana game da gaɓoɓinta ba ƙarfinta da kuma kyan kamanninta ba. Wa zai iya tuɓe mata mayafinta? Wa zai iya shiga tsakanin ɓawonta. Wa zai iya buɗe ƙofofin bakinta? Haƙoranta ma abin tsoro ne? An rufe bayanta da jerin garkuwoyi aka manne su sosai. Suna kurkusa da juna yadda da ƙyar iska take iya wucewa tsakani. An haɗa su da juna sun mannu da juna kuma ba za a iya raba su ba. Numfashinta yana fitar da wuta; idanunta kamar hasken zuwan safe. Wuta tana fitowa daga bakinta; tartsatsin wuta suna fitowa, Hayaƙi yana fitowa daga hancinta kamar daga tukunya mai tafasa a kan wutar itace. Numfashinta yana sa garwashi yă kama wuta, harshen wuta yana fita daga bakinta. Akwai ƙarfi a cikin wuyanta; razana tana wucewa a gabanta. Namanta yana da kauri a manne da juna; naman yana da tauri ba ya matsawa. Ƙirjinta yana da ƙarfi kamar dutse, da ƙarfi kamar dutsen niƙa. Sa’ad da ta tashi, manya suna tsorata; suna ja da baya. Takobi ba ta iya yankanta, kibiya ko māshi ba sa iya huda ta. Ƙarfe kamar kara ne a wurinta tagulla kuma kamar ruɓaɓɓen katako ne a wurinta. Māsu ba su sa ta tă gudu; jifar majajjawa kamar na ciyawa ne gare ta. Kulki a gare ta kamar ciyawa ne, tana dariyar wucewar māshi. Cikinta yana rufe a ɓawo masu ƙarfi, tana kabtar ƙasa in tana tafiya. Tana sa zurfin kogi yă tafasa kamar tukunya, ta kuma sa teku yă zama kamar tukunyar man shafawa. A bayanta ya bar haske kamar zurfin ruwan da yana kumfa. Ba wani abu kamar ta a duniya, halitta marar tsoro. Tana rena duk masu girman kai. Ita take mulki kan duk masu girman kai.” Sa’an nan Ayuba ya amsa wa Ubangiji, “Na san cewa za ka iya yin dukan abubuwa; ba wanda zai iya ɓata shirinka. Ka yi tambaya, ‘Wane ne wannan da ya ƙi karɓar shawarata shi marar ilimi?’ Ba shakka na yi magana game da abubuwan da ban gane ba, abubuwan ban al’ajabi da sun fi ƙarfin ganewata. “Ka ce, ‘Saurara yanzu, zan kuma yi magana zan tambaye ka, kuma za ka amsa mini.’ Kunnuwana sun ji game da kai amma yanzu na gan ka. Saboda haka na rena kaina na kuma tuba cikin ƙura da toka.” Bayan Ubangiji ya gaya wa Ayuba waɗannan abubuwa, ya ce wa Elifaz mutumin Teman, “Ina fushi da kai da abokanka guda biyu domin ba ku faɗi abin da yake daidai game da ni ba, kamar yadda bawana Ayuba ya yi. Saboda haka yanzu sai ku ɗauki bijimai guda bakwai, da raguna bakwai, ku je wurin bawana Ayuba ku miƙa hadaya ta ƙonawa domin kanku. Bawana Ayuba zai yi muku addu’a zan kuwa karɓi addu’arsa in bi da ku nisa da wawancinku. Ba ku faɗi abin da yake daidai game da ni ba yadda bawana Ayuba ya yi ba.” Saboda haka Elifaz mutumin Teman, Bildad mutumin Shuwa da Zofar mutumin Na’ama, suka yi abin da Ubangiji ya gaya masu; Ubangiji kuma ya karɓi addu’ar Ayuba. Bayan Ayuba ya yi wa abokansa addu’a, Ubangiji ya sa shi ya sāke zama mai arziki ya ninka abin da yake da shi a dā sau biyu. Dukan ’yan’uwansa maza da mata da duk waɗanda suka san shi a dā suka zo suka ci abinci tare da shi a cikin gidansa. Suka ta’azantar da shi suka ƙarfafa shi game da duk wahalar da Ubangiji ya auka masa, kowannensu kuma ya ba shi azurfa da zobe na zinariya. Ubangiji ya albarkaci ƙarshen Ayuba fiye da farkonsa. Yana da tumaki guda dubu goma sha huɗu, raƙuma guda dubu shida; shanun noma guda dubu da jakuna guda dubu. Ya kuma haifi ’ya’ya maza bakwai, mata uku. ’Yar farko ya kira ta Yemima, ta biyun Keziya ta ukun Keren-Haffuk. Duk a cikin ƙasar ba a samu kyawawan mata kamar ’ya’yan Ayuba ba, kuma babansu ya ba su gādo tare ta ’yan’uwansu maza. Bayan wannan Ayuba ya rayu shekara ɗari da arba’in; ya ga ’ya’yansa da ’ya’yansu har tsara ta huɗu. Sa’an nan Ayuba ya rasu da kyakkyawan tsufa. Mai farin ciki ne mutumin da ba ya aiki da shawarar mugaye ko yă yi abin da masu zunubi suke yi ko yă zauna tare da masu yin ba’a. Amma yana jin daɗin bin dokar Ubangiji, kuma yana ta nazarinta dare da rana. Yana kama da itacen da aka shuka kusa da maɓulɓulan ruwa, wanda yake ba da amfani a daidai lokaci wanda kuma ganyensa ba sa bushewa. Duk abin da yake yi, yakan yi nasara. Ba haka yake da mugaye ba! Su kamar yayi ne da iska take kwashewa. Saboda haka mugaye ba za su iya tsayawa a shari’a ba, balle a sami masu zunubi a taron adalai. Gama Ubangiji yana lura da yadda adalai suke yin abubuwa, amma ayyukan mugaye za su kai su ga hallaka. Me ya sa ƙasashe suke haɗa baki mutane kuma suke ƙulla shawarwarin banza? Sarakunan duniya sun ɗauki matsayi masu mulki sun taru gaba ɗaya suna gāba da Ubangiji da kuma Shafaffensa. Suna cewa, “Bari mu tsittsinke sarƙoƙinsu, mu kuma ’yantar da kamammu daga kangin bautar Allah.” Mai zama a kursiyi a sama yana dariya; Ubangiji yana musu ba’a. Sa’an nan ya tsawata musu cikin fushinsa ya kuma razanar da su cikin hasalarsa, yana cewa, “Na kafa Sarkina a kan kursiyi a kan Sihiyona, dutsena mai tsarki.” Sarki ya yi shelar umarnin Ubangiji. Ubangiji ya ce mini, “Kai Ɗana ne; yau na zama Mahaifinka. Ka tambaye ni zan kuwa sa al’ummai su zama gādonka, iyakokin duniya su zama mallakarka. Za ka yi mulkinsu da sandan ƙarfe; za ka farfashe su kucu-kucu kamar tukunyar laka.” Saboda haka, ku sarakuna, ku yi wayo; ku shiga hankalinku, ku masu mulkin duniya. Ku bauta wa Ubangiji da tsoro ku kuma yi farin ciki kuna rawar jiki. Ku sumbaci Ɗan, don kada yă yi fushi ku hallaka a abubuwan da kuke yi, gama fushinsa zai iya kuna farat ɗaya. Masu farin ciki ne dukan waɗanda suke neman mafaka daga gare shi. Ya Ubangiji, abokan gābana nawa ne! Su nawa suke gāba da ni! Da yawa suna magana a kaina suna cewa, “Allah ba zai cece shi ba.” Amma kai ne garkuwa kewaye da ni, ya Ubangiji; ka ba ni ɗaukaka ka kuma ɗaga kaina. Ga Ubangiji na yi kuka mai ƙarfi, ya kuwa amsa mini daga tudunsa mai tsarki. Na kwanta na yi barci; na kuma farka, gama Ubangiji yana kiyaye ni. Ba zan ji tsoro ko dubu goma suka ja dāgā gāba da ni a kowane gefe ba. Ka tashi Ya Ubangiji! Ka cece ni, ya Allahna! Ka bugi dukan abokan gābana a muƙamuƙi; ka kakkarya haƙoran mugaye. Daga wurin Ubangiji ne ceto kan zo. Bari albarkanka yă kasance a kan mutanenka. Ka amsa mini sa’ad da na kira gare ka, Ya Allahna mai adalci. Ka ba ni sauƙi daga wahalata; ka ji tausayina ka kuma ji addu’ata. Har yaushe, ya ku mutane za ku mai da ɗaukakata abin kunya? Har yaushe za ku ƙaunaci ruɗu ku nemi allolin ƙarya? Ku san cewa Ubangiji ya keɓe masu tsoron Allah wa kansa; Ubangiji zai ji sa’ad da na yi kira gare shi. Cikin fushinku kada ku yi zunubi; sa’ad da kuke kan gadajenku, ku bincike zukatanku ku kuma yi shiru. Ku miƙa hadayun da suka dace ku kuma dogara ga Ubangiji. Yawanci suna cewa, “Wa zai yi mana alheri?” Bari hasken fuskarka yă haskaka a kanmu, ya Ubangiji. Ka cika zuciyata da farin ciki sa’ad da hatsinsu da sabon ruwan inabinsu ya yi yawa. Zan kwanta in kuma yi barci lafiya, gama kai kaɗai, ya Ubangiji, kake sa mazaunina yă kasance lafiya lau. Ka saurare kalmomina, ya Ubangiji, ka ji ajiyar zuciyata. Ka saurare kukata na neman taimako, Sarkina da Allahna, gama gare ka nake addu’a. Da safe, ya Ubangiji, ka ji muryata; da safe na gabatar da bukatuna a gabanka in kuma jira da sa zuciya. Kai ba Allahn da yake jin daɗin mugu ba ne; gama kana gāba da dukan masu aikata mugunta. Masu fariya ba za su iya tsaya a gabanka ba. Kana ƙin duk masu aikata abin da ba daidai ba. Kakan hallaka masu yin ƙarya. Masu kisankai da mutane masu ruɗu Ubangiji yana ƙyama. Amma ni, ta wurin jinƙanka mai girma, zan shiga gidanka; da bangirma zan durƙusa ga haikalinka. Ka bi da ni, ya Ubangiji, cikin adalcinka saboda abokan gābana, ka fayyace hanyarka a gabana. Babu ko kalma guda daga bakinsu da za a dogara da ita; marmarinsu kawai shi ne su hallakar da waɗansu. Maƙogwaronsu buɗaɗɗen kabari ne; da harshensu suna faɗin ƙarya. Ka furta su masu laifi, ya Allah! Bari makircinsu yă zama fāɗuwarsu. Ka kore su saboda yawan zunubansu, saboda sun tayar maka. Amma bari dukan waɗanda suke neman mafaka gare ka su yi murna; bari kullum su yi ta rerawa saboda farin ciki. Ka buɗe kāriyarka a bisansu, domin waɗanda suke ƙaunar sunanka su yi farin ciki a cikinka. Gama tabbatacce, ya Ubangiji, kakan albarkaci adalai; kakan kewaye su da tagomashinka kamar garkuwa. Ya Ubangiji, kada ka tsawata mini cikin fushinka ko ka hore ni cikin hasalarka. Ka yi mini jinƙai, Ubangiji, gama na suma; Ya Ubangiji, ka warkar da ni, gama ƙasusuwana suna zafin ciwo. Raina yana cikin wahala. Har yaushe, ya Ubangiji, har yaushe? Ka juyo, ya Ubangiji, ka cece ni; ka cece ni saboda madawwamiyar ƙaunarka. Babu wanda yakan tuna da kai sa’ad da ya mutu. Wa ke yabonka daga kabari? Na gaji tiƙis daga nishi. Dukan dare na jiƙe gadona da kuka na jiƙe kujerata da hawaye. Idanuna sun rasa ƙarfi da baƙin ciki; sun rasa ƙarfi saboda dukan abokan gābana. Ku tafi daga gare ni, dukanku masu aikata mugunta, gama Ubangiji ya ji kukata. Ubangiji ya ji kukata saboda jinƙansa; Ubangiji ya karɓi addu’ata. Dukan abokan gābana za su sha kunya su kuma karaya; za su juya da kunya nan da nan. Ya Ubangiji Allahna, na zo neman mafaka a wurinka; ka cece ni ka kuɓutar da ni daga dukan waɗanda suke bi na, in ba haka ba za su yayyage ni kamar zaki su ɓarke ni kucu-kucu ba tare da wani da zai cece ni ba. Ya Ubangiji Allahna, in na yi kuskure aka kuwa sami laifi a hannuwana, in na yi mugunta ga wanda yake zaman lafiya da ni ko kuwa ba da wani dalilin cuci abokin gābana, to, bari abokin gābana yă bi yă kuma cim mini; bari yă tattake raina a ƙasa ya sa in kwana a ƙura. Ka tashi, ya Ubangiji, cikin fushinka; ka tashi gāba da fushin abokan gābana. Ka farka, Allahna, ka umarta adalci. Bari taron mutane su taru kewaye da kai. Ka yi mulki a bisansu daga bisa; bari Ubangiji mai shari’ar mutane. Ka shari’anta ni Ya Ubangiji, bisa ga adalcina, bisa ga mutuncina, ya Mafi Ɗaukaka. Ya Allah mai adalci, wanda yake binciken tunani da zukata, ka kawo ƙarshen rikicin mugaye ka kuma sa adalai su zauna lafiya. Garkuwata shi ne Allah Mafi Ɗaukaka, wanda yake ceton masu tsabtar zuciya. Allah alƙali ne mai adalci, Allahn da yakan bayyana fushinsa kowace rana. In mutum bai tuba ba, Allah zai wasa takobinsa; zai tanƙware yă kuma ɗaura bakansa. Ya shirya makamansa masu dafi; ya shirya kibiyoyinsa masu wuta. Wanda yake da cikin mugunta ya kuma ɗauki cikin damuwa yakan haifi ƙarya. Wanda ya haƙa rami yakan fāɗa cikin ramin da ya haƙa. Damuwar da ya ja yakan sāke nannaɗe a kansa; fitinarsa takan sauka a kansa. Zan gode wa Ubangiji saboda adalcinsa zan kuma rera yabo ga sunan Ubangiji Mafi Ɗaukaka. Ya Ubangiji, shugabanmu, sunanka da girma take a cikin dukan duniya! Ka kafa ɗaukakarka bisa sammai. Daga leɓunan yara da jarirai ka kafa yabo domin su sa abokan gābanka da masu ɗaukan fansa su yi shiru. Sa’ad da na dubi sammai, aikin yatsotsinka, wata da taurari waɗanda ka ajiye a wurarensu, wane ne mutum da kake tunawa da shi, ɗan mutum da kake lura da shi? Ka yi shi ƙasa kaɗan da Allah ka yi masa rawani da ɗaukaka da girma. Ka mai da shi mai mulki bisa ayyukan hannuwanka; ka sa kome a ƙarƙashin ƙafafunsa, dukan shanu da tumaki, da kuma namun jeji, tsuntsayen sararin sama da kifin teku, da dukan abin da yake yawo a ƙarƙashin ruwan teku. Ya Ubangiji, shugabanmu, sunanka da girma take a cikin dukan duniya! Zan yabe ka, ya Ubangiji, da dukan zuciyata; zan faɗa dukan abubuwan banmamakinka. Zan yi murna in kuma yi farin ciki a cikinka; zan rera yabo ga sunanka, ya Mafi Ɗaukaka. Abokan gābana sun ja da baya; suka yi tuntuɓe suka hallaka a gabanka. Gama ka tabbata da gaskiyata da kuma abin da nake yi; ka zauna a kujerarka, kana yin shari’a da adalci. Ka tsawata wa ƙasashe ka kuma hallakar da mugaye; ka shafe sunansu har abada abadin. Lalaci marar ƙarewa ya cimma abokan gābanmu, ka tuttumɓuke biranensu; yadda ma ba aka ƙara tunaninsu. Ubangiji yana mulki har abada; ya kafa kujerarsa don shari’a. Zai hukunta duniya da adalci; zai yi mulkin mutane cikin gaskiya. Ubangiji shi ne mafakan waɗanda ake danniya, mafaka a lokutan wahala. Waɗanda suka san sunanka za su dogara da kai, gama kai, Ubangiji, ba ka taɓa yashe waɗanda suke nemanka ba. Rera yabai ga Ubangiji, wanda yake zaune a kursiyi a Sihiyona; yi shela a cikin al’ummai abin da ya aikata. Gama shi da yakan ɗauki fansa a kan mai kisa yakan tuna; ba ya ƙyale kukan masu wahala. Ya Ubangiji, dubi yadda abokan gābana suna tsananta mini! Ka yi jinƙai ka kuma ɗaga ni daga ƙofofin mutuwa, don in furta yabanka cikin ƙofofin ’Yar Sihiyona a can kuwa in yi farin ciki cikin cetonka. Al’umma sun fāɗa cikin ramin da suka haƙa wa waɗansu; aka kama ƙafafunsu a ragar da suka ɓoye. An san Ubangiji ta wurin gaskiyarsa; an kama mugaye da aikin hannuwansu. Mugaye za su koma kabari, dukan al’umman da suka manta da Allah. Amma har abada ba za a manta da mai bukata ba, ba kuwa sa zuciyar mai wahala zai taɓa hallaka. Ka tashi, ya Ubangiji, kada ka bar wani yă yi nasara; bari a hukunta al’ummai a gabanka. Ka buge su da rawar jiki, ya Ubangiji; bari al’ummai su sani su mutane ne kurum. Don me, ya Ubangiji, kake tsaya can da nesa? Me ya sa kake ɓoye kanka a lokutan wahala? Cikin fariyarsa mugun mutum yakan cuci marasa ƙarfi, waɗanda yake kama cikin makircin da ya shirya. Yakan yi taƙama da ƙulle-ƙullen zuciyarsa; yana albarkaci mai haɗama yana kuma ƙin Ubangiji. Cikin ɗaga kai mutum ba ya neman Allah; cikin tunaninsa ba ya ba da wata dama saboda Allah. Hanyoyinsa kullum sukan yi nasara; yana da girman kai kuma dokokinka suna nesa da shi; yakan yi wa dukan abokan gābansa duban reni. Yakan ce wa kansa, “Ba abin da zai girgiza ni; kullum zan yi murna ba zan taɓa shiga wahala ba.” Bakinsa ya cika da zage-zage da ƙarairayi da kuma barazana; wahala da mugunta suna a ƙarƙashin harshensa. Yakan yi kwanto kusa da ƙauyuka; daga kwanton yakan kashe marar laifi. Yana kallon waɗanda za su shiga hannunsa a ɓoye. Yakan yi kwanto a ɓoye kamar zaki. Yakan yi kwanto don yă kama marasa ƙarfi; yakan kama marasa ƙarfi yă ja su cikin ragarsa. Yakan ragargaza waɗanda suka shiga hannu, su fāɗi; sukan fāɗi a ƙarƙashin ƙarfinsa. Yakan ce wa kansa, “Ai, Allah ya manta; ya rufe fuskarsa ba ya gani.” Ka tashi, Ubangiji! Ka hukunta miyagu, ya Allah. Kada ka manta da marasa ƙarfi. Don me mugun mutum zai ƙi Allah? Don me yakan ce wa kansa, “Allah ba zai nemi hakki daga gare ni ba”? Amma kai, ya Allah, kana gani wahala da baƙin ciki; kana lura da yadda suke ɗaukansu a hannu. Marar taimako kan danƙa kansa gare ka; kai ne mai taimakon marayu Ka karye hannun mugaye da kuma mugun mutum; ka nemi hakki daga gare shi saboda muguntar da ba za a gane ba. Ubangiji Sarkin har abada abadin ne; al’ummai za su hallaka daga ƙasarsa. Kakan ji, ya Ubangiji sha’awar mai shan wahala; kakan ƙarfafa su, ka kuma saurari kukansu, kana kāre marayu da waɗanda aka danne, domin mutum, wanda yake na duniya kada ƙara haddasa wata razana. A wurin Ubangiji ne nake samun mafaka. Yaya za ku ce mini, “Ka yi firiya kamar tsuntsu zuwa duwatsu. Gama duba, mugaye sun tanƙware bakkunansu; sun kuma ɗana kibiyoyinsu don su harbi mutanen kirki a zuciya daga cikin duhu. Sa’ad da aka tumɓuke tushe, me adali zai iya yi?” Ubangiji yana cikin haikalinsa mai tsarki; Ubangiji yana a kursiyinsa a sama. Yana kallon ’ya’yan mutane; idanunsa suna bincike su. Ubangiji yana bincike adalai, amma ransa yana ƙi mugaye da masu son rikici. A kan mugaye zai zuba garwashin wuta mai zafi da kuma kibiritu; iska mai zafi zai zama rabonsu. Gama Ubangiji mai adalci ne, yana ƙaunar gaskiya masu adalci za su ga fuskarsa. Ka taimaka, Ubangiji, gama masu tsoron Allah ba sa nan kuma; masu aminci sun ɓace daga cikin mutane. Kowa yana yi wa maƙwabcinsa ƙarya; zaƙin bakinsu maganar ƙarya ce suna cike da ruɗu a zukatansu. Bari Ubangiji yă yanke dukan zaƙin bakinsu da kuma kowane harshe mai fariya, masu cewa, “Da harsunanmu za mu yi nasara; leɓunanmu za su kāre mu, wane ne maigidanmu?” “Saboda danniyar marasa ƙarfi da kuma nishin masu bukata, zan tashi yanzu,” in ji Ubangiji. “Zan kāre su daga masu yin musu sharri.” Kalmomin Ubangiji kuwa ba su da kuskure, kamar azurfan da aka tace cikin matoyan yumɓu, aka tsabtacce sau bakwai. Ya Ubangiji, za ka kiyaye mu lafiya ka tsare mu daga irin mutanen nan har abada. Mugaye suna yawo a sake sa’ad da ake girmama abin da ba shi da kyau a cikin mutane. Har yaushe, ya Ubangiji? Za ka manta da ni har abada ne? Har yaushe za ka ɓoye fuskarka daga gare ni? Har yaushe zan yi kokawa da tunanina kuma kowace rana in kasance da damuwa a zuciyata? Har yaushe abokin gābana zai yi nasara a kaina? Ka dube ni ka amsa mini, ya Ubangiji Allahna. Ka ba da haske ga fuskata, ko in yi barci cikin mutuwa; abokin gābana zai ce, “Na sha ƙarfinsa,” kuma abokan gābana za su yi murna sa’ad da na fāɗi. Amma na dogara a kan ƙaunarka marar ƙarewa; zuciyata tana farin ciki a cikin cetonka. Zan rera ga Ubangiji gama ya yi mini alheri. Wawaye sukan ce a ransu, “Ba Allah.” Sun lalace, ayyukansu kuwa mugaye ne; babu wani da yake yi abu mai kyau. Ubangiji ya duba daga sama a kan ’yan adam don yă ga ko akwai wani da ya gane, wani wanda yake neman Allah. Duka sun kauce, duka gaba ɗaya sun zama lalatattu; babu ɗaya wanda yake yin abu mai kyau, ba ko ɗaya. Masu aikata mugunta za su taɓa koyo. Suna cin mutane yadda mutane ke cin gurasa kuma waɗanda ba sa kira bisa Ubangiji? Ga su, tsoro ya sha kansu, gama Allah yana cikin ƙungiyar adalai. Ku masu mugunta kuna sa ƙoƙarin matalauta yă zama banza, amma Ubangiji ne mafakansu. Kash, da ceton Isra’ila zai fito daga Sihiyona mana! Sa’ad da Ubangiji zai maido da sa’ar mutanensa, bari Yaƙub yă yi farin ciki Isra’ila kuma yă yi murna! Ubangiji, wa zai zauna cikin wuri mai tsarkinka? Wa zai zauna a kan tudunka mai tsarki? Sai wanda ba shi da laifi kuma yana yin abin da yake daidai, wanda yake faɗin gaskiya daga zuciyarsa ba ya kuwa ɓata sunan wani da harshensa, wanda ba ya yi wa maƙwabcinsa mugunta ba ya kuwa baza jita-jita a kan ɗan’uwansa, wanda yake ƙin mugun mutum amma yakan girmama masu tsoron Ubangiji, yakan cika alkawarinsa ko da ma ya zafe shi, wanda yake ba da rance ba tare da ruwa ba kuma ba ya karɓan cin hanci don yă kā da marar laifi. Shi wanda yake yin waɗannan abubuwa ba zai taɓa jijjiguwa ba. Ka kiyaye ni, ya Allah, gama a cikinka nake samun mafaka. Na ce wa Ubangiji, “Kai ne shugabana; in ba tare da kai ba, ba ni da wani abu mai kyau.” Game da tsarkakan da suke cikin ƙasar kuwa, su ne masu ɗaukakar da dukan farin cikina ya dangana. Baƙin ciki zai ƙaru wa waɗanda suke bin waɗansu alloli. Ba zan zuba musu hadayarsu ta jini ba ko in ambaci sunayensu da bakina. Ubangiji, ka ba ni rabona da kwaf ɗin na; ka kiyaye rabona, Iyakoki sun fāɗo mini a wurare masu daɗi; tabbatacce ina da gādo mai bansha’awa. Zan yabi Ubangiji, wanda yake ba ni shawara; ko da dare ma zuciyata kan koya mini. Kullum nakan sa Ubangiji a gabana. Gama yana a hannun damana, ba zan jijjigu ba. Saboda haka zuciyata tana murna harshena kuma yana farin ciki; jikina kuma zai zauna lafiya, domin ba za ka yashe ni a kabari ba, ba kuwa za ka bar Mai Tsarkinka yă ruɓa ba. Ka sanar da ni hanyar rai; za ka cika ni da farin ciki a gabanka, da madawwamin jin daɗi a hannun damarka. Ka ji, ya Ubangiji, roƙona na adalci; ka saurari kukata. Ka kasa kunne ga addu’ata, ba ta fitowa daga leɓuna masu ƙarya. Bari fiffitawata tă zo daga gare ka; bari idanunka su ga abin da yake daidai. Ko ka duba zuciyata, ka kuma bincike ni da dare, ko ka gwada ni, ba za ka sami kome ba; na yanke shawara cewa bakina ba zai yi zunubi ba. Game da ayyukan mutane kuwa, ta wurin maganar leɓunanka na kiyaye kaina daga hanyoyin tashin hankali. Sawuna sun kama hanyoyinka ƙafafu kuwa ba za su yi santsi ba. Na kira gare ka, ya Allah, gama za ka amsa mini; ka kasa kunne ka kuma ji addu’ata. Ka nuna mini girmar ƙaunarka mai banmamaki, kai da kake ceton waɗanda suke neman mafaka daga abokan gābansu da hannunka na dama. Ka kiyaye ni yadda ake kiyaye ido; ka ɓoye ni cikin inuwar fikafikanka daga mugaye waɗanda suke kai mini hari, daga abokan gāba masu mutuwa waɗanda suka kewaye ni. Sun rufe zukatansu marar tausayi, da bakunansu suna magana da fariya. Sun sa mini ido, yanzu sun kewaye ni, a shirye suke, su jefa ni a ƙasa. Suna kama da zaki mai yunwan abinci, kamar babban zaki mai fako a maɓuya. Ka tashi, ya Ubangiji, ka yi arangama da su, ka durƙusar da su; ka cece ni daga mugaye ta wurin takobinka. Ya Ubangiji, da hannunka ka cece ni daga irin mutanen nan, daga mutanen duniyan nan waɗanda ladarsu yana a wannan rayuwa ne. Kakan cika yunwan waɗanda kake so; ’ya’yansu suna da isashe suna kuma ajiyar wadata wa ’ya’yansu. Amma ni, cikin adalci zan ga fuskarka; sa’ad da na farka, zan gamsu da ganin kamanninka. Ina ƙaunarka, ya Ubangiji, ƙarfina. Ubangiji shi ne dutsena, kagarata da kuma mai cetona; Allahna shi ne dutsena, a gare shi nake neman mafaka. Shi ne garkuwata da ƙahon cetona, mafakata. Na kira ga Ubangiji, wanda ya cancanci yabo, na kuwa kuɓuta daga abokan gābana. Igiyoyin mutuwa sun shaƙe ni; rigyawan hallaka sun sha kaina. Igiyoyin mutuwa sun nannaɗe kewaye da ni; tarkon mutuwa ya yi mini arangama. Cikin wahalata na yi kira ga Ubangiji; Na yi kuka ga Allahna don taimako. A Haikalinsa ya ji muryata, Kukana na neman taimako ya kai kunnensa. Ƙasa ta yi rawa ta kuma girgiza, tussan duwatsu sun girgiza; sun yi rawa domin ya yi fushi. Hayaƙi ya tashi daga kafan hancinsa; wuta mai ci daga bakinsa, garwashi wuta mai ci daga bakinsa. Ya buɗe sammai ya sauko; baƙaƙen gizagizai suna a ƙarƙashin ƙafafunsa. Ya hau kerubobi ya kuma yi firiya; ya yi shawagi a fikafikan iska. Ya mai da duhu abin rufuwarsa, rumfa kewaye da shi, baƙaƙen gizagizan ruwan sama na sarari, daga cikin hasken kasancewarsa gizagizai suka yi gaba, da ƙanƙara da kuma walƙiya. Ubangiji ya yi tsawa daga sama; muryar Mafi Ɗaukaka ya yi kāra. Ya harba kibiyoyinsa ya kuma watsar da abokan gāba, walƙiya mai girma ya fafare su. Kwarin teku sun bayyana tussan duniya sun bayyana a fili sa’ad da ka tsawata, ya Ubangiji, sa’ad da ka numfasa daga hancinka. Ya miƙa hannunsa daga sama ya kama ni; ya ja ni daga zurfin ruwaye. Ya cece ni daga abokin gābana mai ƙarfi, daga abokan gābana, waɗanda suka fi ƙarfina. Sun yi arangama da ni a ranar masifa, amma Ubangiji ya zama mai taimakona. Ya fitar da ni zuwa wuri mai sarari; ya kuɓutar da ni, gama yana jin daɗina. Ubangiji ya yi haka da ni bisa ga adalcina; bisa ga tsabtar hannuwana ya ba ni lada. Gama na kiyaye hanyoyin Ubangiji; ban yi mugunta ta wurin juyewa daga Allahna ba. Dukan dokokinsa suna a gābana; ban juye daga ƙa’idodinsa ba. Na kasance marar laifi a gabansa na kuma kiyaye kaina daga zunubi. Ubangiji ya ba ni lada bisa ga adalcina, bisa ga tsabtan hannuwana a gabansa. Ga mai aminci ka nuna kanka mai aminci, ga marar laifi ka nuna kanka marar laifi, ga mai tsabta ka nuna kanka mai tsabta, amma ga karkatacce, ka nuna kanka mai wayo. Kakan cece mai sauƙinkai amma kakan ƙasƙantar da masu girman kai. Kai Ya Ubangiji, ka sa fitilata ta yi ta ci; Allahna ya mai da duhu ya zama haske. Da taimakonka zan iya fāɗa wa runduna; tare da Allahna zan iya rinjayi katanga. Game da Allah kuwa, hanyarsa cikakkiya ce; maganar Ubangiji marar kuskure ne. Shi garkuwa ne ga dukan waɗanda suke neman mafaka a gare shi. Gama wane ne Allah in ba Ubangiji ba? Wane ne kuwa Dutse in ba Allahnmu ba? Allah ne ya ƙarfafa ni da ƙarfi ya kuma sa hanyarta ta zama cikakkiya. Ya sa ƙafafuna kamar ƙafafun barewa; ya sa na iya tsaya a kan ƙwanƙoli. Ya horar da hannuwana don yaƙi; hannuwana za su iya tanƙware bakan tagulla. Ka ba ni garkuwar nasara, kuma hannunka na dama yana riƙe ni; ya sunkuya don ka mai da ni mai girma. Ka fadada hanyar da yake a ƙarƙashina, don kada ɗiɗɗigena yă juya. Na bi abokan gābana na kuma cim musu; ban juya ba sai da na hallaka su. Na ragargaza su har ba za su iya tashi ba; sun fāɗi a ƙarƙashin ƙafafuna. Ka ƙarfafa ni da ƙarfi saboda yaƙi; ka sa abokan gābana suka rusuna mini. Ka sa abokan gābana suka juya suka gudu, na kuma hallaka abokan gābana. Sun nemi taimako, amma ba su sami wanda zai cece su ba, ga Ubangiji, amma bai amsa ba. Na murƙushe su kamar ƙura mai laushi da iska ke kwashewa; na zubar da su kamar laka a tituna. Ka cece ni daga harin mutane; ka mai da ni kan al’ummai. Mutanen da ban sani ba sun zama bayina, da zarar sun ji ni, sukan yi mini biyayya; baƙi suna rusuna a gabana. Duk sukan karai; suna zuwa da rawan jiki daga mafakansu. Ubangiji mai rai ne! Yabo ya tabbata ga Dutsena! Girma ya tabbata ga Allah Mai cetona! Shi ne Allah mai sāka mini, wanda yake sa al’ummai a ƙarƙashina, wanda yakan cece ni daga abokan gābana. Ana girmama ka bisa abokan gābana; daga masu tā-da-na-zaune-tsaye ka kuɓutar da ni. Saboda haka zan yabe ka a cikin al’ummai, ya Ubangiji; zan rera yabai ga sunanka. Yakan ba sarkinsa nasarori; yakan nuna alheri marar ƙarewa ga shafaffensa, ga Dawuda da zuriyarsa har abada. Sammai suna shelar ɗaukakar Allah; sararin sama suna furta aikin hannuwansa. Kowace rana tana yin jawabi; kowane dare yana nuna sani. Ba magana, ba kalmar da aka hurta, ba wani amon da aka ji daga gare su. Duk da haka muryarsu tana kaiwa ga dukan duniya, kalmominsu zuwa iyakokin duniya. A sammai Allah ya kafa tenti domin rana, wanda yake kamar ango mai fitowa daga rumfarsa, kamar gwani ɗan wasan da yake farin ciki yă yi tsere. Takan taso daga ƙarshen sammai ta kewaye zuwa wancan; babu abin da yake ɓuya wa zafinta. Dokar Ubangiji cikakkiya ce, takan wartsakar da rai. Farillan Ubangiji abin dogara ne, suna mai da hikima da sauƙi. Ƙa’idodin Ubangiji daidai ne, suna ba da farin ciki ga zuciya. Umarnan Ubangiji haske ne suna ba da haske ga idanu. Tsoron Ubangiji yakan kawo tsabtar zuciya, zai kasance har abada. Farillan Ubangiji tabbatattu ne, kuma gaba ɗaya masu adalci ne. Sun fi zinariya daraja, fiye da zalla zinariya nesa; sun fi zuma zaƙi fiye da zuma daga kaki. Ta wurinsu ana gargaɗe bawanka; a kiyaye su akwai lada mai girma. Wane ne zai iya rabe kurakuransa? Ya gafarta ɓoyayyun laifofinsa. Ka kiyaye bawanka daga zunubin ganganci; kada ka bari su yi mulki a kaina. Ta haka zan zama marar laifi; marar laifi na babban tawaye. Bari kalmomin bakina da tunanin zuciyata su zama abin gamsuwa a gabanka, Ya Ubangiji, Dutsena da Mai fansata. Ubangiji ya amsa maka sa’ad da ka yi kira cikin wahala; bari sunan Allah na Yaƙub yă kiyaye ka. Bari yă aiko maka da taimako daga wuri mai tsarki yă kuma ba ka gudummawa daga Sihiyona. Bari yă tuna da dukan sadakokinka yă kuma karɓi hadayunka na ƙonawa. Bari yă biya maka bukatan ranka yă kuma sa dukan shirye-shiryenka su yi nasara. Za mu yi sowa ta farin ciki sa’ad da ka yi nasara mu kuma ɗaga tutotinmu a cikin sunan Allahnmu. Bari Ubangiji yă biya maka dukan bukatunka. Yanzu na san cewa, Ubangiji yakan cece shafaffensa. Yakan amsa masa daga samansa mai tsarki da ikon ceto na hannun damansa. Waɗansu sun dogara a kekunan yaƙi waɗansu kuma a dawakai, amma mu, mun dogara a cikin sunan Ubangiji Allahnmu. Za a durƙusar da su, su kuma fāɗi, amma mu za mu tashi mu tsaya daram. Ya Ubangiji, ka ba da nasara ga sarki! Ka amsa mana sa’ad da muka yi kira! Ya Ubangiji, sarki yana farin ciki cikin ƙarfinka. Yana farin cikinsa ƙwarai cikin nasarorin da ka ba shi! Ka biya masa bukatar zuciyarsa ba ka kuwa hana masa roƙon da ya yi da leɓunansa ba. Ka marabce shi da yalwar albarka ka kuma sa masa rawanin zallan zinariya a kansa. Ya nemi ka ba shi rai, ka kuwa ba shi, tsawo kwanaki, har abada abadin Ta wurin nasarorin da ka ba shi, ɗaukakarsa mai girma ce; ka mayar masa ɗaukaka da kuma suna. Tabbatacce ka ba shi madawwamiyar albarka ka kuma sa shi murna da farin cikin kasancewarka. Gama sarki ya dogara gare ka Ubangiji ta wurin ƙauna marar ƙarewa ta Mafi Ɗaukaka ba zai jijjigu ba. Hannunka zai kakkama dukan abokan gābanka; hannunka na dama zai kakkama masu ƙinka. A lokacin bayyanarka za ka sa su zama kamar wutar matoya. Cikin fushinsa Ubangiji zai haɗiye su, kuma wutarsa za tă cinye su. Za ka hallaka ’ya’yansu daga duniya, zuriyarsu kuma daga ’yan adam. Ko da yake suna shirya maka mugunta suna kuma ƙirƙiro mugayen dabaru, ba za su yi nasara ba; gama za ka sa su juye bayansu sa’ad da ka auna su da bakan da ka ja. Ka sami ɗaukaka, ya Ubangiji cikin ƙarfinka; za mu rera mu kuma yabi ikonka. Ya Allahna, ya Allahna, don me ka yashe ni? Me ya sa ka yi nisa da cetona, ka yi nesa daga kalmomin nishina? Ya Allahna, na yi kuka da rana, amma ba ka amsa ba, da dare kuma ban yi shiru ba. Duk da haka kana a kursiyi a matsayin Mai Tsarkin nan; kai ne yabon Isra’ila. A gare ka ne kakanninmu suka sa bege; sun dogara ka kuwa cece su. Sun yi kuka gare ka suka kuma sami ceto; a gare ka suka dogara kuma ba su sha kunya ba. Amma ni dai tsutsa ne ba mutum ba, wanda mutane suke yi wa ba’a suka kuma rena shi. Duk wanda ya gan ni yakan yi mini ba’a; suna yin mini ashar, suna kaɗa kansu suna cewa, “Ya dogara ga Ubangiji; bari Ubangiji yă cece shi. Bari yă cece shi, da yake yana jin daɗinsa.” Duk da haka ka fitar da ni daga ciki; ka sa na dogara gare ka, ko ma a ƙirjin mahaifiyata. Daga haihuwa an jefa ni a kanka; daga cikin mahaifiyata kai ne Allahna. Kada ka yi nesa da ni, gama wahala na kusa kuma babu wani da zai taimaka. Bijimai masu yawa sun kewaye ni; bijimai masu ƙarfi na Bashan sun sa ni a tsaka. Zakoki masu ruri suna yayyage abin da suka kama sun buɗe bakunansu a kaina. An zubar da ni kamar ruwa, kuma dukan ƙasusuwana sun fiffito daga mahaɗai. Zuciyata ta zama kaki; ta narke a cikina. Ƙarfina ya bushe kamar kasko, harshena kuma ya manne wa dasashina na sama; ka kwantar da ni a ƙurar mutuwa. Karnuka sun kewaye ni; ƙungiyar mugaye sun sa ni a tsaka, sun soki hannuwana da ƙafafuna. Zan iya ƙirga ƙasusuwana; mutane suna farin ciki a kaina. Sun raba rigunana a tsakaninsu suka kuma jefa ƙuri’a a kan rigunana. Amma kai, ya Ubangiji, kada ka yi nisa; Ya Ƙarfina zo da sauri don ka taimake ni. Ka ceci raina daga takobi, raina mai daraja daga ikon karnuka. Ka cece ni daga bakin zakoki; ka cece ni daga ƙahonin ɓauna. Zan furta sunanka ga ’yan’uwana; cikin taron masu sujada zan yabe ka. Ku da kuke tsoron Ubangiji, ku yabe shi! Dukanku zuriyar Yaƙub, ku girmama shi! Ku girmama shi, dukanku zuriyar Isra’ila! Gama bai rena ko yă ƙyale wahalar masu shan wuya ba; bai ɓoye fuskarsa daga gare shi ba amma ya saurari kukansa na neman taimako. Daga gare ka yabona yake zuwa cikin babban taro; a gaban waɗanda suke tsoronka zan cika alkawarina. Matalauta za su ci su ƙoshi; su da suke neman Ubangiji za su yabe shi, bari zukatanku su rayu har abada! Dukan iyakokin duniya za su tuna su kuma juya ga Ubangiji, kuma dukan iyalan al’ummai za su rusuna a gabansa, gama mulki na Ubangiji ne kuma yana mulki a bisa al’ummai. Dukan attajiran duniya za su yi biki su kuma yi sujada; dukan waɗanda suka gangara zuwa ƙura za su durƙusa a gabansa, waɗanda ba za su iya bar kansu da rai ba. Zuriya masu zuwa za su yi masa hidima; za a faɗa wa zuriya na nan gaba game da Ubangiji. Za su yi shelar adalcinsa ga mutanen da ba a riga an haifa ba, gama ya aikata shi. Ubangiji ne yake kiwona, ba zan rasa kome ba, Yakan sa in kwanta a makiyaya mai ɗanyar ciyawa, yakan bi da ni kusa da ruwaye marar hayaniya, yakan maido da raina. Yakan bi da ni a hanyoyin adalci saboda sunansa. Ko da na yi tafiya ta kwari na inuwar mutuwa, ba zan ji tsoron mugu ba, gama kana tare da ni; bulalarka na dūka da kuma sandanka na tafiya, za su yi mini ta’aziyya. Ka shirya mini tebur a gaban abokan gābana. Ka shafe kaina da mai; kwaf nawa ya cika har yana zuba. Tabbatacce alheri da ƙauna za su bi dukan kwanakin raina, zan kuwa zauna a gidan Ubangiji har abada. Duniya ta Ubangiji ce da kome da yake cikinta, duniya, da dukan waɗanda suke zama a cikinta; gama ya gina ta a kan tekuna ya kafa ta a kan ruwaye. Wa zai iya hawan tudun Ubangiji? Wa zai iya tsaya a wurinsa mai tsarki? Sai wanda yake da hannu mai tsabta da kuma tsabtar zuciya, wanda ba ya ba da ransa ga bautar gunki ko ya rantse bisa abin da yake ƙarya. Zai sami albarka daga Ubangiji da fiffitawa daga Allah Mai cetonsa. Irin tsaran waɗanda suke nemansa ke nan, waɗanda suke neman fuskarka, ya Allah na Yaƙub. Ku ɗaga kawunanku, ya ku ƙofofi; ku ɗagu, ku daɗaɗɗun ƙofofi, don Sarkin ɗaukaka yă shiga. Wane ne wannan Sarkin ɗaukaka? Ubangiji ne mai ƙarfi mai iko, Ubangiji mai girma a yaƙi. Ku ɗaga kawunanku, ya ku ƙofofi; ku ɗagu, ku daɗaɗɗun ƙofofi, don Sarkin ɗaukaka yă shiga. Wane ne shi, wannan Sarkin ɗaukaka? Ubangiji Maɗaukaki, shi ne Sarkin ɗaukaka. A gare ka Ya Ubangiji, na miƙa raina. A gare ka na dogara, ya Allahna. Kada ka bari in sha kunya, ko ka bar abokan gābana su yi nasara a kaina. Ba wanda yake sa bege a gare ka da zai taɓa shan kunya, amma za su sha kunya su da suke tayarwa babu dalili. Ka nuna mini hanyoyinka, ya Ubangiji, ka koya mini hanyoyinka; ka bi da ni cikin gaskiyarka ka kuma koya mini, gama kai ne Allah Mai cetona, kuma begena yana a kanka dukan yini. Ka tuna, ya Ubangiji da jinƙai da kuma ƙaunarka mai girma, gama suna nan tun dā. Kada ka tuna da zunuban ƙuruciyata da kuma hanyoyin tawayena; bisa ga ƙaunarka ka tuna da ni, gama kai nagari ne, ya Ubangiji. Ubangiji nagari da mai adalci ne; saboda haka yakan koyar da masu zunubi a hanyoyinsa. Yakan bi da masu tawali’u cikin abin da yake daidai ya kuma koyar da su hanyoyinsa. Dukan hanyoyin Ubangiji ƙaunatattu ne da kuma aminci ga waɗanda suke kiyaye abin da alkawari ya bukaci. Saboda sunanka, ya Ubangiji, ka gafarta laifina, ko da yake mai girma ne. To wane ne mai tsoron Ubangiji? Zai koyar da shi a hanyar da ya zaɓa masa. Zai ci kwanakinsa a wadace, kuma zuriyarsa za su gāji ƙasar. Ubangiji yakan amince da waɗanda suke tsoronsa; yakan sa su san alkawarinsa. Idanuna kullum suna a kan Ubangiji, gama shi ne kaɗai zai kuɓutar da ƙafafuna daga tarko. Ka juye wurina ka kuma yi mini jinƙai, gama na kaɗaice ina kuma wahala. Damuwoyin zuciyata sun ninka; ka ’yantar da ni daga wahalata. Ka dubi wahalata da kuma azabata ka ɗauke mini dukan zunubaina. Dubi yadda abokan gābana sun ƙaru da kuma yadda suka ƙara ƙina! Ka tsare raina ka kuma kuɓutar da ni; kada ka bari in sha kunya, gama na nemi mafaka daga gare ka. Bari mutunci da adalci su tsare ni, domin begena yana a kanka. Ka fanshi Isra’ila, ya Allah, daga dukan wahalarsu! Ka nuna rashin laifina, ya Ubangiji, gama na yi rayuwa marar zargi; Na dogara ga Ubangiji ba tare da kaucewa ba. Ka jarraba ni, ya Ubangiji, ka kuma gwada ni, ka bincike zuciyata da tunanina; gama ƙaunarka kullum tana a gabana, kuma ina cin gaba da tafiya a cikin gaskiyarka. Ba na zama tare da masu ruɗu, ko in yi tarayya da masu riya; na ƙi jinin taron masu aikata mugunta na ƙi in zauna tare da mugaye. Na wanke hannuwana cikin rashin laifi, ina yawo a bagadenka Ya Ubangiji, ina shelar yabonka da ƙarfi ina faɗin dukan ayyukanka masu banmamaki. Ina ƙaunar gidan da kake zama, ya Ubangiji, wurin da ɗaukakarka ke zaune. Kada ka ɗauke raina tare da masu zunubi raina tare da masu son yin kisankai waɗanda akwai mugayen dabaru a hannuwansu, waɗanda hannuwansu na dama suna cike da cin hanci. Amma na yi rayuwa marar zargi; ka cece ni ka kuma yi mini jinƙai. Ƙafafuna suna tsaye daram; cikin taro mai girma zan yabi Ubangiji. Ubangiji ne haskena da cetona, wa zan ji tsoro? Ubangiji ne mafakar raina, wane ne zan ji tsoro? Sa’ad da mugaye suka tasar mini don su cinye ni, sa’ad da abokan gābana da maƙiyina suka kawo mini hari, sun yi tuntuɓe suka fāɗi. Ko da yake mayaƙa sun kewaye ni, zuciyata ba za tă ji tsoro ba; ko da yake ya ɓarke a kaina, duk da haka zan ƙarfafa. Abu guda na roƙi Ubangiji, wannan shi ne na nema, cewa in zauna a gidan Ubangiji dukan kwanakin raina, in dubi kyan Ubangiji in kuma neme shi a cikin haikalinsa. Gama a lokacin wahala, zai kiyaye ni lafiya a wurin zamansa; zai ɓoye ni cikin inuwar tabanakul nasa ya kuma sa ni can a bisa dutse. Sa’an nan kaina zai ɗaukaka a bisa abokan gābana waɗanda suka kewaye ni; a tabanakul nasa zan miƙa hadaya da sowa ta farin ciki; zan rera in kuma yi kiɗi ga Ubangiji. Ka ji muryata sa’ad da na yi kira, ya Ubangiji; ka yi mini jinƙai ka kuma amsa mini. Zuciyata kan faɗa game da kai, “Nemi fuskarsa!” Fuskarka, Ubangiji, zan nema. Kada ka ɓoye fuskarka daga gare ni, kada ka kore bawanka daga gare ka cikin fushi; kai ne ka kasance mai taimakona. Kada ka ƙi ni ko ka yashe ni, Ya Allah Mai cetona. Ko da mahaifina da mahaifiyata sun yashe ni, Ubangiji zai karɓe ni. Ka koya mini hanyarka, ya Ubangiji; ka bi da ni a miƙaƙƙiyar hanya saboda masu danne ni. Kada ka ba da ni da sha’awar maƙiyina, gama masu shaidar ƙarya sun taso a kaina, suna numfasa tashin hankali. Har yanzu ina da ƙarfin gwiwa a wannan cewa zan ga alherin Ubangiji; a ƙasar masu rai. Ka dogara ga Ubangiji, ka yi ƙarfin hali ka yi ƙarfin zuciya ka kuma dogara ga Ubangiji. A gare ka nake kira, ya Ubangiji Dutsena; kada ka yi mini kunnen ƙashi. Gama in ka yi shiru, zan zama kamar waɗanda suka gangara rami. Ka ji kukata ta neman jinƙai yayinda nake kira ka don neman taimako, yayinda nake daga hannuwana wajen Wurinka Mafi Tsarki. Kada ka ja ni tare da mugaye, tare da masu yin mugunta, masu magana kamar ta alheri ce da maƙwabtansu amma suna riƙe da su a zukatansu. Ka sāka musu da ayyukansu da kuma don mugun aikinsu; ka sāka musu saboda abin da hannuwansu suka yi ka kuma mayar musu abin da ya dace da su. Da yake ba su kula da ayyukan Ubangiji da abin da hannuwansa suka yi ba, zai rushe su ba kuwa zai ƙara gina su ba. Yabo ya tabbata ga Ubangiji, gama ya ji kukata na neman jinƙai. Ubangiji shi ne ƙarfina da garkuwata; zuciyata ta amince da shi, kuma na sami taimako. Zuciyata ta yi tsalle don farin ciki zan kuwa yi godiya gare shi cikin waƙa. Ubangiji shi ne ƙarfin mutanensa, kagarar ceto domin shafaffensa. Ka cece mutanenka ka kuma albarkace gādonka; ka zama mai kiwonsu ka kuma riƙe su har abada. Ku ba da girma ga Ubangiji, ya ku manya, ku ba da girma ga Ubangiji saboda ɗaukaka da kuma ƙarfinsa. Ku ba da girma ga Ubangiji, ɗaukakar da ta dace da sunansa; ku bauta wa Ubangiji cikin ɗaukakar tsarkinsa. Muryar Ubangiji tana a bisa ruwaye; Allah Maɗaukaki ya yi tsawa, Ubangiji ya yi tsawa a bisa manyan ruwaye. Muryar Ubangiji mai iko ce; muryar Ubangiji da girma take. Muryar Ubangiji ta kakkarya itatuwan al’ul na Lebanon. Ubangiji ya kakkarya itatuwan al’ul na Lebanon kucu-kucu. Ya sa dutsen Lebanon ya yi ta tsalle kamar ɗan maraƙi, Siriyon kuma kamar ɗan jakin jeji. Muryar Ubangiji ta buga da walƙatar walƙiya. Muryar Ubangiji ta girgiza hamada Ubangiji ya girgiza Hamadan Kadesh. Muryar Ubangiji ta murɗa itatuwan oak ya kakkaɓe itatuwan kurmi. Kuma a cikin haikalinsa kowa ya ce, “Ɗaukaka!” Ubangiji na zaune yana sarauta a bisa rigyawa; Ubangiji yana sarauta kamar Sarki har abada. Ubangiji kan ba da ƙarfi ga mutanensa; Ubangiji kan albarkace mutanensa da salama. Zan girmama ka Ya Ubangiji, gama ka tsamo ni daga zurfafa ba ka bar abokan gābana sun yi farin ciki a kaina ba. Ya Ubangiji Allahna, na yi kira gare ka don taimako ka kuwa warkar da ni. Ya Ubangiji, ka dawo da ni daga kabari; ka kiyaye ni daga gangarawa zuwa cikin rami. Ku rera ga Ubangiji, ku tsarkakansa; ku yabi sunansa mai tsarki. Gama fushinsa na ɗan lokaci ne amma alherinsa har matuƙa ne; mai yiwuwa a yi kuka da dare amma farin ciki kan zo da safe. Sa’ad da nake lafiya, na ce, “Ba zan jijjigu ba.” Ya Ubangiji, sa’ad da ka yi mini alheri, ka sa katangar dutsena ya tsaya daram; amma sa’ad da ka ɓoye fuskarka, sai in cika da tsoro. A gare ka, ya Ubangiji, na yi kira; a gare ka Ubangiji na yi kukan neman jinƙai. “Wace riba ce a hallakata, a kuma gangarawa ta zuwa cikin rami? Ƙura za tă yabe ka ne? Za tă iya yin shelar amincinka? Ka ji, ya Ubangiji, ka kuwa yi mini jinƙai; Ya Ubangiji, ka zama taimakona.” Ka mai da kukata ta zama rawa; ka tuɓe rigar makokina ka sa mini na farin ciki, don zuciyata za tă iya rera gare ka ba kuwa za tă yi shiru ba. Ya Ubangiji Allahna, zan yi maka godiya har abada. A gare ka, ya Ubangiji, na nemi mafaka; kada ka bari in taɓa shan kunya; ka cece ni cikin rahamarka. Ka juye kunnenka gare ni, ka zo da sauri ka cece ni; ka zama dutsen mafakata, mafaka mai ƙarfi na cetona. Da yake kai ne dutsena da kuma kagarata, saboda sunanka ka bi da ni ka kuma jagorance ni. Ka ’yantar da ni daga tarkon da aka sa mini, gama kai ne mafakata. Cikin hannuwanka na miƙa ruhuna; ka cece ni, ya Ubangiji Allah na gaskiya. Na ƙi waɗanda suke manne wa gumakan banza; na dogara ga Ubangiji. Zan yi murna in kuma yi farin ciki a cikin ƙaunarka, gama ka ga azabata ka kuma san wahalar raina. Ba ka ba da ni ga abokin gāba ba amma ka sa ƙafafuna a wuri mai sarari. Ka yi mini jinƙai, ya Ubangiji, gama ina cikin damuwa; idanuna sun gaji da baƙin ciki, raina da jikina sun tafke tilis. Baƙin ciki ya rufe raina shekaruna sun cika da nishi; ƙarfina ya karai saboda azaba, ƙasusuwana kuma sun gaji tiƙis. Saboda dukan abokan gābana, Na zama tamƙar abin reni na maƙwabtana; na zama abin tsoro ga abokaina, waɗanda suka gan ni a titi sukan gudu daga gare ni. An manta da ni sai ka ce na mutu; na zama kamar fasasshen kasko. Gama nakan ji raɗe-raɗen mutane masu yawa; akwai tsoro a kowane gefe; suna ƙulla maƙarƙashiya a kaina suna shirya su ɗauke raina. Amma na dogara gare ka, ya Ubangiji; na ce, “Kai ne Allahna.” Lokutana suna a hannuwanka; ka cece ni daga abokan gābana da kuma daga waɗanda suke fafara ta. Bari fuskarka ta haskaka a kan bawanka; ka cece ni da ƙaunarka marar ƙarewa. Kada ka bari in sha kunya, ya Ubangiji, gama na yi kuka gare ka; amma bari mugaye su sha kunya su kuma kwanta shiru a cikin kabari. Bari a rufe leɓunan ƙarairayinsu, gama da fariya da reni suna magana da girman kai a kan adalai. Alherinka da girma yake, wanda ka ajiye domin waɗanda suke tsoronka, wanda ka mayar a gaban mutane a kan waɗanda suke neman mafaka daga gare ka. Cikin inuwar kasancewarka ka ɓoye su daga makircin mutane; a wurin zamanka ka kiyaye su lafiya daga harsuna masu zagi. Yabo ya tabbata ga Ubangiji, gama ya nuna ƙaunarsa mai banmamaki gare ni sa’ad da aka yi mini kwanto kewaye da birni. Cikin tsorona na ce, “An yanke ni daga gabanka!” Duk da haka ka ji kukata na neman jinƙai sa’ad da na kira gare ka don taimako. Ku ƙaunaci Ubangiji, dukanku tsarkakansa! Ubangiji yakan adana amintattu, amma masu girman kai yakan sāka musu cikakke. Ku yi ƙarfin hali ku kuma ƙarfafa, dukanku masu sa bege a kan Ubangiji. Mai farin ciki ne shi wanda aka gafarta masa laifofinsa, wanda aka shafe zunubansa. Mai farin ciki ne mutumin da Ubangiji ba ya lissafin zunubinsa a kansa wanda kuma babu ruɗu a ruhunsa. Sa’ad da na yi shiru, ƙasusuwana sun yi ta mutuwa cikin nishina dukan yini. Gama dare da rana hannunka yana da nauyi a kaina; an shanye ƙarfina ƙaf sai ka ce a zafin bazara. Sa’an nan na furta zunubina a gare ka ban kuwa ɓoye laifina ba. Na ce, “Zan furta laifofina ga Ubangiji.” Ka kuwa gafarta laifin zunubina. Saboda haka bari duk mai tsoron Allah yă yi addu’a gare ka yayinda kake samuwa; tabbatacce sa’ad da manyan ruwaye suka taso, ba za su kai wurinsa ba. Kai ne wurin ɓuyata; za ka tsare ni daga wahala ka kewaye ni da waƙoƙin ceto. Zan umarce ka in kuma koyar da kai a hanyar da za ka bi; Zan ba ka shawara in kuma lura da kai. Kada ka zama kamar doki ko doki, wanda ba su da azanci wanda dole sai an bi da su da linzami da ragama in ba haka ba, ba za su zo wurinka ba. Azaban mugu da yawa suke, amma ƙaunar Ubangiji marar ƙarewa kan kewaye mutumin da ya dogara gare shi. Ku yi farin ciki a cikin Ubangiji ku kuma yi murna, ku adalai; ku rera, dukanku waɗanda zuciyarku take daidai! Ku rera da farin ciki ga Ubangiji ku adalai; daidai ne masu gaskiya su yabe shi. Ku yabi Ubangiji da garaya; ku yi kiɗi gare shi da molo mai tsirkiya goma. Ku rera masa sabuwar waƙa; ku yi kiɗi da gwaninta, ku kuma yi sowa don farin ciki. Gama maganar Ubangiji daidai ne da kuma gaskiya; yana da aminci cikin kome da yake yi. Ubangiji yana ƙaunar adalci duniya ta cika da ƙaunarsa marar ƙarewa. Ta wurin maganar Ubangiji aka yi sammai, rundunar taurarinsu kuwa da numfashin bakinsa. Ya tattara ruwan teku cikin tuluna; ya sa zurfafa cikin gidajen ajiya. Bari dukan duniya ta ji tsoron Ubangiji; bari dukan mutanen duniya su girmama shi. Gama ya yi magana, abu ya kuwa kasance; ya umarta, ya kuwa tsaya daram. Ubangiji yakan soke shirye-shiryen al’ummai; yakan wofintar da manufofin mutane. Amma shirye-shiryen Ubangiji kan tsaya daram har abada, manufofin zuciyarsa kuwa har dukan zamanai. Mai farin ciki ce al’ummar da Allah ne Ubangijinta, mutanen da ya zaɓa don gādonsa. Daga sama Ubangiji ya duba ya kuwa ga dukan ’yan adam; daga mazauninsa yana lura da dukan waɗanda suke zama a duniya, shi da ya yi zukatan duka, wanda yake kula da kome da suke yi. Babu sarkin da ake ceto ta wurin yawan mayaƙansa; ba jarumin da kan kuɓuta ta wurin yawan ƙarfinsa. Dogara a kan doki don ceto banza ne; duk da yawan ƙarfinsa ba ya ceto. Amma idanun Ubangiji suna a kan wanda yake tsoronsa, a kan waɗanda suke sa zuciya cikin ƙaunarsa marar ƙarewa, don yă cece su daga mutuwa ya bar su da rai a lokacin yunwa. Muna jiran Ubangiji da bege; shi ne taimakonmu da garkuwarmu. A cikinsa zukatanmu na farin ciki, gama mun dogara cikin sunansa mai tsarki. Bari ƙaunarka marar ƙarewa ta zauna a kanmu, ya Ubangiji, ko ma da muke sa begenmu a gare ka. Zan gode wa Ubangiji kullayaumi; yabonsa kullum za su kasance a leɓunana. Raina zai yi fariya a cikin Ubangiji; bari waɗanda suke wahala su ji su kuma yi farin ciki. Ku ɗaukaka Ubangiji tare da ni; bari mu ɗaukaka sunansa tare. Na nemi Ubangiji, ya kuwa amsa mini; ya cece ni daga dukan tsoro. Waɗanda suke dubansa sukan haskaka; fuskokinsu ba sa rufuwa da kunya. Wannan matalauci ya yi kira, Ubangiji kuwa ya ji shi; ya cece shi daga dukan wahalarsa. Mala’ikan Ubangiji ya kafa sansani kewaye da waɗanda suke tsoronsa, ya kuwa cece su. Ku gwada ku gani cewa Ubangiji yana da kyau; mai albarka ne mutumin da yake neman mafaka a gare shi. Ku ji tsoron Ubangiji, ku tsarkakansa, gama masu tsoronsa ba sa rasa kome. Zakoki za su iya rasa ƙarfi su kuma ji yunwa, amma waɗanda suke neman Ubangiji ba sa rasa abu mai kyau. Ku zo, ’ya’yana, ku saurare ni; zan koya muku tsoron Ubangiji. Duk waninku da yake ƙaunar rayuwa yana kuma so yă ga kwanaki masu kyau, ka kiyaye harshenka daga mugunta da kuma leɓunanku daga faɗar ƙarairayi. Juyo daga mugunta ku yi alheri; nemi salama ku kuma yi ƙoƙarin samunta. Idanun Ubangiji suna a kan masu adalci kuma kunnuwansa suna sauraran kukansu; fuskar Ubangiji yana gāba da waɗanda suke aikata mugunta, don yă sa a manta da su a duniya. Adalai kan yi kuka, Ubangiji kuwa yakan ji su; yakan cece su daga dukan wahalarsu. Ubangiji yana kusa da waɗanda suka karai ya kuma cece waɗanda aka ragargaza a ruhu. Adali zai iya kasance da wahala da yawa, amma Ubangiji yakan cece shi daga dukansu; yakan tsare dukan ƙasusuwansa, ba ko ɗayansu da zai karye. Mugunta zai kashe mugu; za a hukunta abokan gāban adalai. Ubangiji yakan cece bayinsa; ba wanda yake neman mafaka a wurinsa da za a hukunta. Yi hamayya, ya Ubangiji, da waɗanda suke hamayya da ni; yi faɗa da waɗanda suke faɗa da ni. Ka ɗauki garkuwa da kuma makami; ka tashi ka taimake ni. Ka ɗaga māshi da kuma abin da ake jefa a kan waɗanda suke fafarata. Ka ce wa raina, “Ni ne cetonka.” Bari waɗanda suke neman raina su sha kunya a kuma kunyatar da su; bari waɗanda suke shirya lalacewata su juya da baya su ruɗe. Bari su zama kamar yayi a gaban iska, mala’ikan Ubangiji kuma yana korarsu; bari hanyarsu tă yi duhu ta kuma yi santsi, mala’ikan Ubangiji kuma yana fafararsu. Da yake sun ɓoye tarko domina ba dalili kuma babu dalili suka haƙa mini rami, bari lalaci yă kama su ba zato, bari tarkon da suka ɓoye yă kama su, bari su fāɗa cikin ramin, yă kai ga lalacinsu. Sa’an nan raina zai cika da farin ciki a cikin Ubangiji in yi kuma murna a cikin cetonsa. Dukan raina zai ce, “Wane ne kamar ka, ya Ubangiji? Ka kuɓutar da matalauta daga waɗanda suka fi ƙarfinsu, matalauta da masu bukata daga waɗanda suke musu fashi.” Shaidu marasa imani sun fito; suna mini tambaya a kan abubuwan da ban san kome a kai ba. Suna sāka alherin da na yi musu da mugunta suka bar raina da nadama. Duk da haka sa’ad da suke ciwo, na sanya rigar makoki na ƙasƙantar da kaina da azumi. Sa’ad da aka mayar mini da addu’o’i babu amsa, nakan yi ta yawo ina makoki sai ka ce yadda nake yi wa abokina ko ɗan’uwana. Nakan sunkuyar da kaina cikin baƙin ciki sai ka ce ina kuka domin mahaifiyata. Amma sa’ad da na yi tuntuɓe, sukan taru suna murna; masu kai hari sun taru a kaina sa’ad da ban sani ba. Suna ɓata mini suna ba tsagaitawa. Kamar marasa sani Allah suna mini riyar ba’a; Suna hararata da ƙiyayya. Ya Ubangiji, har yaushe za ka ci gaba da zuba ido kawai? Ka kuɓutar da raina daga farmakinsu, raina mai daraja daga waɗannan zakoki. Zan yi godiya cikin taro mai girma; cikin ɗumbun mutane zan yabe ka. Kada ka bar maƙaryatan nan, su yi farin ciki a kaina; kada ka bar waɗanda suke ƙina ba dalili, su ji daɗin baƙin cikina. Ba sa maganar salama sukan ƙirƙiro zage-zagen ƙarya a kan waɗanda suka zama shiru a ƙasar. Sukan wage mini bakinsu suna cewa, “Allah yă ƙara! Da idanunmu mun gani.” Ya Ubangiji, ka ga wannan; kada ka yi shiru. Kada ka yi nisa da ni, ya Ubangiji. Ka farka, ka kuma tashi ka kāre ni! Ka yi mini faɗa, ya Allahna da shugabana. Ka nuna ni marar laifi ne ciki adalcinka, Ya Ubangiji Allahna; kada ka bari su yi farin ciki a kaina. Kada ka bari su ce wa kansu, “Allah yă ƙara, dā ma abin da mun so ke nan!” Ko su ce, “Mun haɗiye shi.” Bari dukan waɗanda suke farin ciki a kaina a wahalata su sha kunya su kuma ruɗe; bari dukan waɗanda suke ɗaukar kansu sun fi ni su sha kunya da wulaƙanci. Bari waɗanda suke murna saboda nasarata su yi sowa don farin ciki da murna; bari kullum su riƙa cewa, “A ɗaukaka Ubangiji, wanda yake farin ciki da zaman lafiyar bawansa.” Harshena zai yi zancen adalcinka da kuma yabonka dukan yini. Akwai magana a cikin zuciyata game da zunubin mugu. Babu tsoron Allah a idanunsa. Gama a idanunsa yana ganin kansa wani abu ne wanda ya sha ƙarfi a gane ko ya ƙi zunubinsa. Kalmomin bakinsa mugaye ne da kuma ruɗu; ya daina zama mai hikima da yin alheri. Ko a kan gadonsa ma yana shirya mugunta; yakan sa kansa ga aikata zunubi kuma ba ya ƙin abin da ba shi da kyau. Ƙaunarka, ya Ubangiji, kan kai sammai, amincinka har sararin sammai. Adalcinka yana kama da manyan duwatsu, hukuncinka kamar zurfi mai girma. Ya Ubangiji, kana lura da mutum da dabba. Ina misalin ƙaunarka marar ƙarewa! Mutane manya da ƙanana kan sami mafaka cikin inuwar fikafikanka. Suna biki a yalwar gidanka; kakan ba su sha daga rafin farin cikinka. Gama a gare ka akwai maɓulɓular rai cikin haskenka mukan ga haske. Ka ci gaba da ƙaunarka ga waɗanda suka san ka, adalcinka ga masu gaskiyar zuciya. Kada ka bari ƙafar mai girman kai yă fāɗa mini, ko hannun mugu ya kore ni. Dubi yadda masu aikata zunubi suka fāɗi, a zube, ba za su kuwa iya tashi ba! Kada ka tsorata saboda mugayen mutane ko ka yi kishin waɗanda suka aikata mugunta; gama kamar ciyawa za su bushe, kamar ɗanyun ganyaye za su mutu. Ka dogara ga Ubangiji ka kuma aikata alheri; yi zama cikin ƙasar ka kuma more makiyaya mai lafiya. Ka ji daɗinka a cikin Ubangiji zai kuwa biya bukatun zuciyarka. Ka sa kanka a hanyar Ubangiji; ka kuma dogara gare shi zai kuwa yi wannan. Zai sa adalcinka yă haskaka kamar hasken safiya, gaskiyarka kuma kamar rana a tsaka. Ka natsu a gaban Ubangiji ka kuma jira da haƙuri gare shi; kada ka tsorata sa’ad da mutane ke nasara a hanyoyinsu, sa’ad da suke aikata mugayen shirye-shiryensu. Kada ka yi fushi kada kuma ka yi hasala; kada ka tsorata, wannan yakan kai ga mugunta ne kawai. Gama za a datse mugayen mutane, amma waɗanda suke sa zuciya ga Ubangiji za su gāji ƙasar. A ɗan ƙanƙanen lokaci, mugaye za su shuɗe; ko ka neme su, ba za a same su ba. Amma masu tawali’u za su gāji ƙasar su kuma zauna da cikakkiyar salama. Mugaye sukan shirya wa adalai maƙarƙashiya su ciji baki a kansu; amma Ubangiji yakan yi dariyar mugaye, gama ya sani ranarsu tana zuwa. Mugaye sukan zare takobi su ja baka don su kashe matalauta da masu bukata, don su kashe waɗanda hanyoyinsu daidai suke. Amma takubansu za su soki zukatansu, kuma bakkunansu za su kakkarye. Ƙanƙanen abin da mai adalci yake da shi ya fi arzikin mugaye yawa; gama za a kakkarya ikon mugaye, amma Ubangiji zai riƙe mai adalci. Kwanakin marasa zarge suna sane ga Ubangiji, kuma gādonsu zai dawwama har abada. A lokutan masifu ba za su yanƙwane ba; a kwanakin yunwa za su sami a yalwace. Amma mugaye za su hallaka, Abokan gāban Ubangiji za su zama kamar kyan gonaki, za su ɓace, za su ɓace kamar hayaƙi. Mugaye kan yi rance ba sa kuma biya, amma masu adalci suna bayar hannu sake; waɗanda Ubangiji ya sa wa albarka za su gāji ƙasar, amma waɗanda ya la’anta, za a kore su. In Ubangiji ya ji daɗin hanyar da mutum yake bi, zai sa sawu su kahu; ko ya yi tuntuɓe, ba zai fāɗi ba, gama Ubangiji yakan riƙe shi da hannunsa. Dā ni yaro ne amma yanzu na tsufa, duk da haka ban taɓa ganin an yashe masu adalci ba ko a ce ’ya’yansu suna roƙon burodi. Kullum suna bayar hannu sake suna kuma ba da bashi ba da wahala ba, za a yi wa ’ya’yansu albarka. Ku juyo daga mugunta ku yi alheri; sa’an nan za ku zauna a ƙasar har abada. Gama Ubangiji yana ƙaunar masu aikata daidai kuma ba zai yashe amintattunsa ba. Za a hallaka masu aikata mugunta gaba ɗaya, ’ya’yan mugaye za su hallaka. Masu adalci za su gāji ƙasar su kuma zauna a cikinta har abada. Bakin mutum mai adalci yakan yi magana da hikima, harshensa kuwa yakan yi maganar abin da yake daidai. Dokar Allahnsa tana a cikin zuciyarsa; ƙafafunsa ba sa santsi. Mugaye suna fako suna jira masu adalci, suna ƙoƙari neman ransu; amma Ubangiji ba zai bar su a ikonsu ba ko ya bari a hukunta su sa’ad da aka kawo su shari’a ba. Ku sa zuciya ga Ubangiji ku kuma kiyaye hanyarsa. Zai ɗaukaka ku ku ci gādon ƙasar, sa’ad da aka kawar da mugaye, za ka gani. Na ga wani mugu, azzalumi, yana yaɗuwa kamar ɗanyen itace a asalin ƙasarsa, amma yakan mutu nan da nan kuma ba ya ƙara kasancewa; ko an neme shi, ba za a same shi ba. Ka dubi marasa zargi, ka lura da adali; akwai sa zuciya domin mutum mai salama. Amma za a hallaka dukan masu zunubi; za a yanke sa zuciya ta mugaye. Ceton adalai kan zo daga Ubangiji; shi ne mafaka a lokacin wahala. Ubangiji yakan taimake su yă kuma cece su; yakan kuɓutar da su daga mugaye yă kuma cece su, domin sukan nemi mafaka daga gare shi. Ya Ubangiji, kada ka tsawata mini cikin fushinka ko ka hore ni cikin hasalarka. Gama kibiyoyinka sun soke ni, hannunka kuma ya fāɗo a kaina. Saboda hasalarka babu lafiya a jikina; ƙasusuwana ba lafiya saboda zunubina. Laifofina sun mamaye ni kamar nauyin da ya sha ƙarfin ɗauka. Miyakuna sun ruɓe suna kuma wari saboda wawancina na zunubi. An tanƙware ni aka kuma ƙasƙantar da ni; dukan yini ina ta kuka. Bayana yana fama da zazzaɓi; babu lafiya a jikina. Na gaji sharkaf an kuma ragargaza ni; ina nishi da wahala a cikin zuciyata. Dukan bukatata tana a shimfiɗe a gabanka, ya Ubangiji; ajiyar zuciyata ba ta ɓoyuwa daga gare ka. Zuciyata na bugu, ƙarfina kuma ya ƙare, har ma haske ya rabu da idanuna. Abokaina da maƙwabtana sun guje ni saboda miyakuna; maƙwabtana ba sa zuwa kusa. Waɗanda suke neman raina sun sa tarkonsu, waɗanda suke so su cuce ni suna zance lalatar da ni; yini sukutum suna ƙulla mini maƙarƙashiya. Ni kamar kurma ne, wanda ba ya ji, kamar bebe, wanda ba ya iya buɗe bakinsa. Na zama kamar mutumin da ba ya ji, wanda bakinsa ba ya iya ba da amsa. Na dogara gare ka, ya Ubangiji; za ka amsa, ya Ubangiji Allahna. Gama na ce, “Kada ka bar su su yi farin ciki a kaina ko su yi kirari a kaina sa’ad da ƙafata ta yi santsi.” Gama ina gab da fāɗuwa, kuma cikin azaba nake kullum. Na furta laifina; na damu da zunubina. Da yawa ne masu gāba da ni da ƙarfi; waɗanda suke kina ba dalili sun yi yawa. Waɗanda suke sāka alherina da mugunta, suna cin zarafina sa’ad da nake bin abin da yake daidai. Ya Ubangiji, kada ka yashe ni; kada ka yi nesa da ni, ya Allahna. Zo da sauri ka taimake ni, Ya Ubangiji Mai Cetona. Na ce, “Zan lura da hanyoyina zan kuma kiyaye harshena daga zunubi; zan sa linzami a bakina muddin mugaye suna a gabana.” Na yi shiru, ban ce kome ba, Ko a kan abin da yake da kyau! Amma duk da haka wahalata sai ƙaruwa take yi; zuciyata ta ƙara zafi a cikina. Kuma sa’ad da nake tunani, wuta ta yi ta kuna; sai na yi magana da harshena na ce, “Nuna mini, ya Ubangiji, ƙarshen rayuwata da kuma yawan kwanakina; bari in san yadda rayuwata tana wucewa da sauri. Ka sa kwanakina suka zama tafin hannu ne kawai; yawan shekaruna kamar ba kome ba ne a gabanka. Duk ran mutum shaƙar iska ne kurum, har ma waɗanda suke tsammani suke da kāriya. “Mutum dai shirim ne kawai yayinda yake kai da komowa. Yana ta yawo, amma a banza ne kawai; yakan tara dukiya, ba tare da sanin wa zai more ta ba. “Amma yanzu, ya Ubangiji, me zan nema? Begena yana a gare ka. Ka cece ni daga dukan laifofina; kada ka sa in zama abin dariya ga wawaye. Na yi shiru; ba zan buɗe bakina ba, gama kai ne wanda ka aikata wannan. Ka ɗauke bulalarka daga gare ni; na ji jiki ta wurin bugun da hannunka ya yi mini. Kakan tsawata ka kuma hore mutane saboda zunubinsu; kakan cinye wadatarsu kamar yadda asu ke yi, kowane mutum dai shaƙar iska ne. “Ka ji addu’ata, ya Ubangiji, ka saurari kukata ta neman taimako; kada ka kurmance ga kukata. Gama ina zama tare da kai kamar baƙo, baƙo, kamar yadda dukan kakannina sun kasance. Ka kau da fuskarka daga gare ni, saboda in sāke yin farin ciki kafin in tafi in kuma rabu da nan.” Na jira da haƙuri ga Ubangiji; ya juya wurina ya kuma ji kukata. Ya ɗaga ni daga rami marar fāɗi, daga laka da taɓo; ya sa ƙafafuna a kan dutse ya kuma ba ni tsayayyen wuri don in tsaya. Ya sa sabuwar waƙa a bakina, waƙar yabo ga Allahna. Da yawa za su gani su tsorata su kuma dogara ga Ubangiji. Mai albarka ne mutumin da ya mai da Ubangiji abin dogararsa, wanda ba ya kula da masu girman kai, waɗanda suka juya ga allolin ƙarya. Da yawa ne, ya Ubangiji Allahna, abubuwan banmamakin da ka aikata. Abubuwan da ka shirya mana. Ba wanda zai iya faɗa maka su; a ce zan yi magana in faɗe su, za su wuce gaban misali a furta. Hadaya da sadaka ba ka sha’awa, amma kunnuwana ka huda; hadayun ƙonawa da hadayun zunubi ba ka bukata. Sa’an nan na ce, “Ga ni, na zo, kamar yadda yake a rubuce game da ni cikin littafi. Ina sha’awar aikata nufinka, ya Allahna; dokar tana cikin zuciyata.” Na yi shelar adalcinka cikin babban taro; ba na rufe leɓunana, kamar yadda ka sani, ya Ubangiji. Ba na ɓoye adalcinka cikin zuciyata; ina maganar amincinka da cetonka. Ban ɓoye ƙaunarka da gaskiyarka a gaban taron jama’arka mai girma ba. Kada ka hana mini jinƙanka, ya Ubangiji; bari ƙaunarka da gaskiyarka kullum su kāre ni. Gama damuwoyin da suka wuce misali sun kewaye ni; zunubaina sun mamaye ni, kuma ba na iya gani. Sun fi gashin kaina yawa, har ma na fid da zuciya. Ka ji daɗin cetona, ya Ubangiji; Ya Ubangiji, ka zo da sauri ka taimake ni. Bari masu neman raina su sha kunya su kuma rikice; bari dukan waɗanda suke neman lalacewata su koma baya da kunya. Bari masu ce mini, “Allah yă ƙara!” Su sha mamaki saboda kunyar da za su sha. Amma bari dukan masu nemanka su yi farin ciki su kuma yi murna a cikinka; bari waɗanda suke ƙaunar cetonka kullum su ce, “ Ubangiji mai girma ne!” Ni dai matalauci ne da mai bukata; bari Ubangiji yă tuna da ni. Kai ne taimakona da mai cetona; Ya Allahna, kada ka jinkirta. Mai albarka ne wanda yake jin tausayin marasa ƙarfi; Ubangiji yakan kuɓutar da shi a lokutan wahala. Ubangiji zai kāre shi yă kuma kiyaye ransa; zai albarkace shi a cikin ƙasar ba kuwa zai miƙa shi ga hannun maƙiyansa ba. Ubangiji zai ba shi ƙarfi a gadon rashin lafiyarsa ya mayar masa da lafiya daga ciwon da ya kwantar da shi. Na ce, “Ya Ubangiji, ka yi mini jinƙai; ka warkar da ni, gama na yi maka zunubi.” Abokan gābana suna muguwar magana a kaina cewa, “Yaushe zai mutu sunansa yă ɓace ne?” Duk sa’ad da wani ya zo ganina, yakan yi maganar ƙarya, yayinda zuciyarsa tana tattare da cin zarafi; sa’an nan yă fita yă yi ta bazawa ko’ina. Dukan abokan gābana suna raɗa tare a kaina; suna fata mugun abu ya same ni, suna cewa, “Mugun ciwo ya kama shi; ba zai taɓa tashi daga inda yake kwanciya ba.” Har abokina na kurkusa, wanda na amince da shi, wanda muke cin abinci tare, ya juya yana gāba da ni. Amma kai, ya Ubangiji, ka yi mini jinƙai, ka tā da ni, don in sāka musu. Na sani kana jin daɗina, gama abokin gābana ba zai ci nasara a kaina ba. Cikin mutuncina ka riƙe ni ka sa ni a gabanka har abada. Yabo ya tabbata ga Ubangiji, Allah na Isra’ila, har abada abadin. Amin kuma Amin. Kamar yadda barewa take marmarin ruwan rafuffuka, haka raina yake marmarinka, ya Allah. Raina yana ƙishin Allah, Allah mai rai. Yaushe zan tafi in sadu da Allah ne? Hawayena ne sun zama abincina dare da rana, yayinda mutane suke ce da ni dukan yini, “Ina Allahnka ɗin?” Waɗannan abubuwa ne nakan tuna sa’ad da nake faɗin abin da yake a raina, yadda dā nakan tafi tare da taron jama’a, ina bishe su a jere zuwa gidan Allah, da sowa ta farin ciki da kuma godiya a cikin taron biki. Me ya sa kake baƙin ciki, ya raina? Me ya sa ka damu a cikina? Ka dogara ga Allah, gama zai sāke yabe shi, Mai Cetona da kuma Allahna. Raina yana baƙin ciki a cikina; saboda haka zan tuna da kai daga ƙasar Urdun, a ƙwanƙolin Hermon, daga Dutsen Mizar. Zurfi kan kira zurfi cikin rurin matsirgar ruwanka; dukan raƙuma da igiyoyi sun sha kaina. Da rana Ubangiji yakan nuna ƙaunarsa, da dare waƙarsa tana tare da ni, addu’a ga Allah na raina. Na ce wa Allah Dutsena, “Me ya sa ka manta da ni? Me zai sa in yi ta yawo ina makoki, a danne a hannun abokin gāba?” Ƙasusuwana suna jin jiki da wahala yayinda maƙiyana suna mini ba’a, suna ce mini dukan yini, “Ina Allahnka ɗin?” Me ya sa kake baƙin ciki, ya raina? Me ya sa ka damu a cikina? Ka dogara ga Allah, gama zai sāke yabe shi, Mai Cetona da kuma Allahna. Ka nuna ni marar laifi ne, ya Allah, ka kuma nemi hakkina a kan al’ummai marasa sanin Allah. Ka kuɓutar da ni daga masu ruɗu da mugayen mutane. Kai ne Allah mafakata. Me ya sa ka ƙi ni? Me zai sa in yi ta yawo ina makoki, a danne a hannun abokin gāba? Ka aiko da haskenka da gaskiyarka, bari su bishe ni bari su kawo ni ga dutsenka mai tsarki, zuwa wurin da kake zama. Sa’an nan zan tafi bagaden Allah, ga Allah, farin cikina da murnata. Zan yabe ka da garaya, Ya Allah, Allahna. Me ya sa kake baƙin ciki, ya raina? Me ya sa ka damu a cikina? Ka dogara ga Allah, gama zai sāke yabe shi, Mai Cetona da Allahna. Mun ji da kunnuwanmu, ya Allah; kakanninmu sun faɗa mana abin da ka aikata a kwanakinsu, tun dā can. Da hannunka ka kori al’ummai ka kuma dasa kakanninmu; ka ragargaza mutanen ka kuma sa kakanninmu suka haɓaka. Ba da takobinsu ba ne suka ci ƙasar, ba kuwa ƙarfin hannunsu ne ya ba su nasara ba; hannun damanka ne, ƙarfin hannunka, da kuma hasken fuskarka, gama ka ƙaunace su. Kai ne Sarkina da kuma Allahna, wanda ya ba da nasarori wa Yaƙub. Ta wurinka mun tura abokan gābanmu baya; ta wurin sunanka muka tattake maƙiyanmu. Ba na dogara ga bakana, takobina ba ya kawo nasara; amma kana ba mu nasara a kan abokan gābanmu, ka sa abokan gābanmu suka sha kunya. A cikin Allah muke fariyarmu dukan yini, kuma za mu yabi sunanka har abada. Amma yanzu ka ƙi mu ka kuma ƙasƙantar da mu; ba ka ƙara fita tare da mayaƙanmu. Ka sa muka gudu a gaban abokin gāba, kuma abokan gābanmu suka washe mu. Ka ba da mu a cinye kamar tumaki ka kuma watsar da mu a cikin al’ummai. Ka sayar da mutanenka a kuɗin da bai taka ƙara ya karye ba babu wata riba daga sayar da su da ka yi. Ka mai da mu abin dariya ga maƙwabtanmu, abin dariya da reni ga waɗanda suke kewaye da mu. Ka sa muka zama abin ba’a a cikin al’ummai; mutanen suna kaɗa mana kai. Dukan yini ina cikin wulaƙanci, fuskata kuma ta rufu da kunya saboda ba’ar waɗanda suke zagi suke kuma ƙina, saboda abokan gābana, waɗanda suka sha alwashi sai sun yi ramuwa. Dukan wannan ya faru da mu, ko da yake ba mu manta da kai ba ko mu kasance masu ƙarya ga alkawarinka. Zukatanmu ba su juya baya; ƙafafunmu ba su kauce daga hanyarka ba. Amma ka ragargaza mu ka kuma maishe mu abin farautar karnukan jeji ka kuma rufe mu cikin duhu baƙi ƙirin. Da a ce mun manta da sunan Allahnmu ko mun miƙa hannuwanmu ga baƙin alloli, da Allah bai gane ba, da yake ya san asiran zuciya? Duk da haka saboda kai mun fuskanci mutuwa dukan yini; aka ɗauke mu kamar tumakin da za a yanka. Ka farka, ya Ubangiji! Don me kake barci? Ta da kanka! Kada ka ƙi mu har abada. Me ya sa ka ɓoye fuskarka ka manta da azabanmu da kuma danniyar da ake mana? An kai mu ƙasa zuwa ƙura; jikunanmu sun manne da ƙasa. Ka tashi ka taimake mu; ka cece mu saboda ƙaunarka marar ƙarewa. Zuciyata ta cika da kyakkyawan kan magana yayinda nake rera ayoyina wa sarki; harshena ne alƙalamin ƙwararren marubuci. Kai ne mafi kyau cikin mutane an kuma shafe leɓunanka da alheri, da yake Allah ya albarkace ka har abada. Ka ɗaura takobinka a gefenka, ya jarumi; ka rufe kanka da ɗaukaka da kuma daraja. Cikin darajarka ka hau zuwa nasara a madadin gaskiya, tawali’u da adalci; bari hannunka na dama yă nuna ayyukan banmamaki. Bari kibiyoyinka masu tsini su huda zukatan abokan gāban sarki; bari al’ummai su fāɗi ƙarƙashin ƙafafunka. Kursiyinka, ya Allah, zai kasance har abada abadin; sandar adalci zai zama sandar mulkinka. Kana ƙaunar abin da yake daidai kana kuma ƙin mugunta; saboda haka Allah, Allahnka, ya sa ka a bisa abokanka ta wurin shafe ka da man farin ciki. Dukan rigunanka suna ƙanshin turaren mur da na aloyes, da na kashiya; daga kowace fadan da aka yi masa ado da hauren giwa kaɗe-kaɗen tsirkiya kan sa ka murna. ’Ya’yan sarki mata suna cikin matan da ake girmama; a hannun damarka kuwa ga amarya, sarauniya saye da ofir zinariya. Ki saurara, ya ke diya, ki lura ku kuma kasa kunne, Ki manta da mutanenki da gidan mahaifinki. Sarki ya cika da sha’awar kyanki; ki girmama shi, gama shi ne maigidanki. Diyar Taya za tă zo da kyauta, mawadata za su nemi tagomashinki. Gimbiya tana fada, kyakkyawa ce ainun; an saƙa rigarta da zaren zinariya. Cikin riguna masu ado aka kai ta wurin sarki; abokanta budurwai suna biye da ita aka kuwa kawo su gare ka. Aka bi da su cikin farin ciki da murna; suka shiga fadan sarki. ’Ya’yanka maza za su maye matsayin kakanninka; za ka sa su yi mulki a duk fāɗin ƙasar. Zan sa a tuna da kai a dukan zamanai; saboda haka al’ummai za su yabe ka har abada abadin. Allah ne mafakarmu da ƙarfinmu, kullum yana a shirye yă taimaka a lokacin wahala. Saboda haka ba za mu ji tsoro ba, ko da ƙasa ta girgiza duwatsu kuma suka fāɗi cikin zurfin teku, ko da ruwansa suna ruri suna kumfa duwatsu kuma suna girgiza da tumbatsansu. Akwai kogi mai rafuffukan da suke sa birnin Allah murna, tsattsarkan wuri inda Mafi Ɗaukaka ke zama. Allah yana cikinta, ba za tă fāɗi ba; Allah zai taimake ta da safe. Al’ummai suna hayaniya, mulkoki sun fāɗi; ya ɗaga muryarsa, duniya ta narke. Ubangiji Maɗaukaki yana tare da mu; Allah na Yaƙub ne kagararmu. Zo ku ga ayyukan Ubangiji, kangon da ya kawo a kan duniya. Ya sa yaƙoƙi suka yi tsit ko’ina a duniya. Ya kakkarya bakkuna ya kuma ragargaza māsu, ya ƙone garkuwoyi da wuta. “Ku natsu ku kuma san cewa ni ne Allah; za a ɗaukaka ni a cikin al’ummai, za a ɗaukaka ni cikin duniya.” Ubangiji Maɗaukaki yana tare da mu; Allah na Yaƙub ne kagararmu. Ku tafa hannuwanku, dukanku al’ummai; ku yi sowa ga Allah da muryoyin farin ciki. Ubangiji Mafi Ɗaukaka mai banmamaki ne, Sarki ne mai girma a bisa dukan duniya! Ya rinjayi al’ummai a ƙarƙashinmu, mutane kuma a ƙarƙashin ƙafafunmu. Ya zaɓar mana gādonmu, abar taƙamar Yaƙub, wanda yake ƙauna. Allah ya haura a cikin sowa ta farin ciki, Ubangiji ya haura a cikin ƙarar ƙahoni. Ku rera yabai ga Allah, ku rera yabai; ku rera yabai ga Sarkinmu, ku rera yabai. Gama Allah shi ne Sarkin dukan duniya; ku rera zabura ta yabo gare shi. Allah yana mulki a bisa al’ummai; Allah yana zama a kan kursiyinsa mai tsarki. Manyan mutanen al’ummai sun taru a matsayin mutanen Allah na Ibrahim, gama sarkunan duniya na Allah ne; ana ɗaukaka shi ƙwarai. Ubangiji mai girma ne, kuma mafificin yabo, a birnin Allahnmu, dutsensa mai tsarki. Kyakkyawa ce cikin tsayinta, abin farin cikin dukan duniya. Kamar ƙwanƙoli mafi tsayi na Zafon ne Dutsen Sihiyona, birnin Babban Sarki. Allah yana cikin fadodinta; ya nuna kansa mafaka ce gare ta. Sa’ad da sarakuna suka haɗa rundunoni, sa’ad da suka yi gaba tare, sun gan ta suka kuwa yi mamaki; suka gudu don tsoro. Rawar jiki ya kama su a can, zafi kamar na mace mai naƙuda. Ka hallaka su kamar jiragen ruwan Tarshish da iskar gabas ta wargaje. Yadda muka ji, haka muka gani a cikin birnin Ubangiji Maɗaukaki, a cikin birnin Allahnmu. Allah ya sa ta zauna lafiya har abada. Cikin haikalinka, ya Allah, mun yi tunani a kan ƙaunarka marar ƙarewa. Kamar sunanka, ya Allah, yabonka ya kai iyakokin duniya; hannunka na dama ya cika da adalci. Dutsen Sihiyona ya yi farin ciki, ƙauyukan Yahuda suna murna saboda hukuntanka. Yi tafiya cikin Sihiyona, ku kewaye ta, ku ƙirga hasumiyoyinta, ku lura da katangarta da kyau, ku dubi fadodinta, don ku faɗe su ga tsara mai zuwa. Gama wannan Allah shi ne Allahnmu har abada abadin; zai zama jagorarmu har zuwa ƙarshe. Ku ji wannan, dukanku mutane; ku saurara, dukanku waɗanda suke zama a wannan duniya, babba da yaro mai arziki da talaka. Bakina zai yi maganar hikima; magana daga zuciyata za tă ba da ganewa. Zan juye kunnena ga karin magana; da garaya zan ƙarfafa kacici-kacicina. Don me zan ji tsoro sa’ad da mugayen kwanaki suka zo, sa’ad da mugaye masu ruɗu suka kewaye ni, waɗanda suka dogara ga arzikinsu suna kuma fariya a kan yawan arzikinsu? Ba wani da zai iya ceton ran wani ko yă ba wa Allah kuɗin fansa saboda shi, kuɗin fansa domin rai yana da tsada, babu abin da za a biya da ya taɓa isa, da zai sa yă ci gaba da rayuwa har abada yă hana shi shigan kabari yă ruɓa. Gama kowa na iya ganin masu hikima na mutuwa; wawaye da marasa azanci su ma kan hallaka su bar wa waɗansu arzikinsu. Kaburburansu za su ci gaba da zama gidajensu har abada, Can za su kasance har zamanai marasa ƙarewa, ko da yake sun ba wa filaye sunayen kansu. Amma mutum, kome arzikinsa, ba ya dawwama; shi kamar dabbobi ne da suke mutuwa. Wannan ne ƙaddarar waɗanda suke dogara a kansu, da kuma ta mabiyansu, waɗanda suka tabbatar da faɗinsu. Kamar tumaki an ƙaddara su ga kabari; za su kuwa zama abincin mutuwa amma masu gaskiya za su yi mulki a kansu da safe. Kamanninsu za su ruɓe a cikin kabari, nesa da gidajensu masu tsada. Amma Allah zai ceci raina daga kabari; tabbatacce zai ɗauke ni zuwa wurinsa. Kada ka razana da yawa sa’ad da mutum ya yi arziki sa’ad da darajar gidansa ta ƙaru; gama ba zai ɗauki kome tare da shi sa’ad da ya mutu ba, darajarsa ba za tă gangara tare da shi ba. Ko da yake yayinda yake a raye ya ɗauka kansa mai albarka ne, mutane kuma sun yabe ka sa’ad da kake cin nasara, zai gamu da tsarar kakanninsa, waɗanda ba za su taɓa ganin hasken rayuwa ba. Mutumin da yake da arziki ba tare da ganewa ba shi kamar dabbobi ne da suke mutuwa. Maɗaukaki, Allah, Ubangiji, ya yi magana ya kuma kira duniya daga fitowar rana zuwa inda take fāɗuwa. Daga Sihiyona, cikakkiya a kyau, Allah na haskakawa. Allahnmu yana zuwa ba kuwa zai yi shiru ba; wuta mai cinyewa a gabansa, babban hadari kuma ya kewaye shi. Ya kira sammai da suke bisa, da duniya, don yă shari’anta mutanensa. “Ku tattara mini shafaffuna, waɗanda suka yi alkawari da ni ta wurin hadaya.” Sammai kuwa sun yi shelar adalcinsa gama Allah kansa alƙali ne. “Ku ji, ya mutanena, zan kuwa yi magana, Ya Isra’ila, zan kuwa ba da shaida a kanku. Ni ne Allah, Allahnku. Ba na tsawata muku saboda hadayunku ko kuwa hadayunku na ƙonawa, waɗanda kuka taɓa kawo a gabana. Ba na bukatan bijimi daga turkenku ko awaki daga garkunanku, gama kowace dabbar kurmi nawa ne, da kuma shanu a kan dubban tuddai. Na san kowane tsuntsun da yake a duwatsu kuma halittun filaye nawa ne. Da a ce ina jin yunwa ai, ba sai na faɗa muku ba, gama duniyar nawa ne, da kome da yake cikinta. Ina cin naman bijimai ne ko ina shan jinin awaki ne? “Ku miƙa hadayar godiya ga Allah, ku cika alkawuranku ga Mafi Ɗaukaka, ku kira gare ni a ranar wahala; zan cece ku, za ku kuwa girmama ni.” Amma ga mugaye, Allah ya ce, “Wace dama ce kuke da ita na haddace dokokina ko na yin maganar alkawarina a leɓunanku? Kun ƙi umarnina kuka kuma zubar da kalmomina a bayanku Sa’ad da kuka ga ɓarawo, kukan haɗa kai da shi; kukan haɗa kai da mazinata. Kuna amfani da bakunanku don mugunta kuna kuma gyara harshenku don ruɗu. Kuna ci gaba da magana a kan ɗan’uwanku ku kuma yi maganar ƙarya a kan ɗan mahaifinku. Kun yi waɗannan abubuwa na kuwa yi shiru; kun ɗauka gaba ɗaya ni kamar ku ne. Amma zan tsawata muku in kuma zarge ku a fuskarku. “Ku lura da wannan, ku da kuka manta da Allah, ko kuwa in yayyage ku kucu-kucu, ba kuma wanda zai cece ku. Shi wanda ya miƙa hadayun godiya yakan girmama ni, ya kuma shirya hanya saboda in nuna masa ceton Allah.” Ka yi mini jinƙai, ya Allah, bisa ga ƙaunarka marar ƙarewa; bisa ga tausayinka mai girma ka shafe laifofina. Ka wanke dukan kurakuraina ka tsarkake ni daga zunubina. Gama ina sane da laifofina zunubaina kuma kullum suna a gabana. Kai kaɗai na yi wa zunubi na yi abin da yake mugu a idonka, ta haka an tabbatar kai mai gaskiya sa’ad da ka yi magana aka kuma nuna kai mai adalci ne sa’ad da ka hukunta. Tabbatacce ni mai zunubi ne tun haihuwa mai zunubi daga lokacin da mahaifiyata ta yi cikina. Tabbatacce kana son gaskiya a sassan ciki; ka koya mini hikima a wuri can ciki. Ka tsarkake ni da hizzob, zan kuwa zama tsab; ka wanke ni, zan kuma fi dusan ƙanƙara fari. Bari in ji farin ciki da murna; bari ƙasusuwan da ka ragargaza su yi farin ciki. Ka ɓoye fuskarka daga zunubaina ka kuma shafe dukan kurakuraina. Ka halitta zuciya mai tsabta a cikina, ya Allah, ka kuma sabunta tsayayyen ruhu a cikina. Kada ka fid da ni daga gabanka ko ka ɗauke Ruhunka Mai Tsarki daga gare ni. Ka mayar mini farin cikin cetonka ka kuma ba ni ruhun biyayya, yă riƙe ni. Ta haka zan koyar wa masu laifi hanyoyinka, masu zunubi kuma za su komo gare ka. Ka cece ni daga laifin jini, ya Allah, Allahn da ya cece ni, harshena kuwa zai rera adalcinka. Ya Ubangiji, ka buɗe leɓunana, bakina kuwa zai furta yabonka. Ba ka farin ciki a hadaya, ai da na kawo; ba ka jin daɗin hadayun ƙonawa. Hadayun Allah su ne karyayyen ruhu; karyayyiya da kuma zuciya mai tuba, Ya Allah, ba za ka ƙi ba. Cikin jin daɗinka ka sa Sihiyona ta yi nasara; ka gina katangar Urushalima. Ta haka za a kasance da hadayu masu adalci, hadayun ƙonawa ɗungum don su faranta ka; sa’an nan za a miƙa bijimai a bagadenka. Me ya sa kake fariya game da mugunta, kai babban mutum? Me ya sa kake fariya dukan yini, kai da kake abin kunya a idanun Allah? Harshenka kan shirya hallaka; yana nan kamar reza mai ci, kana ta ruɗu. Kana ƙaunar mugunta fiye da alheri, ƙarya a maimakon faɗin gaskiya. Kana ƙaunar kowace kalmar cutarwa, Ya kai harshe mai ruɗu! Tabbatacce Allah zai kai ka ga madawwamiyar hallaka. Zai fizge ka yă yayyage ka daga tentinka; zai tumɓuke ka daga ƙasar masu rai. Masu adalci za su ga su ji tsoro; za su yi masa dariya, suna cewa, “Yanzu, ga mutumin da bai mai da Allah mafakarsa ba amma ya dogara a yawan arzikinsa ya kuma yi ƙarfi ta wurin hallaka waɗansu!” Amma ni kamar itace zaitun ne ina haɓaka a gidan Allah; na dogara ga ƙauna marar ƙarewa ta Allah har abada abadin. Zan yabe ka har abada game da abin da ka yi; a cikin sunanka zan dogara, gama sunanka yana da kyau. Zan yabe ka a gaban tsarkakanka. Wawa ne kawai yakan ce a zuciyarsa, “Ba Allah.” Sun lalace, kuma hanyoyinsu ba su da kyau; babu wani mai aikata abu mai kyau. Allah yana duba daga sama a kan ’ya’yan mutane yă ga ko akwai wani wanda ya gane, wani wanda yake neman Allah. Kowa ya kauce, gaba ɗaya sun lalace; babu guda da yake aikata abu mai kyau, babu ko ɗaya. Masu aikata mugunta ba sa taɓa koyo? Suna cin mutanena kamar yadda ake cin burodi, ba sa kuma kira ga Allah. Ga shi fa, sun firgita don tsoro, ko da yake babu dalilin tsoro, gama Allah zai watsar da ƙasusuwan masu ƙinsa, za su sha kunya, gama Allah ya ƙi su. Kash, da ceton Isra’ila zai fito daga Sihiyona mana! Sa’ad da Allah ya sāke arzuta mutanensa, bari Yaƙub yă yi farin ciki Isra’ila kuma yă yi murna! Ka cece ni, ya Allah ta wurin sunanka; ka nuna ni marar laifi ne ta wurin ƙarfinka. Ka ji addu’ata, ya Allah; ka saurari maganar bakina. Baƙi suna kawo mini hari; mutane marasa imani suna neman raina, mutanen da ba sa tsoron Allah. Tabbatacce Allah ne mai taimakona, Ubangiji shi ne wanda yake riƙe ni. Bari mugunta ta shaƙe masu magana marar kyau a kaina; cikin amincinka ka hallaka su. Zan miƙa hadaya ta yardar rai gare ka; zan yabe sunanka, ya Ubangiji, gama yana da kyau. Gama ya cece ni daga dukan wahalolina, idanuna kuma sun ga an yi nasara a kan maƙiyana. Ka ji addu’ata, ya Allah, kada ka ƙyale roƙona; ka ji ni ka kuma amsa mini. Tunanina yana damuna na kuma gaji tilis hankalina ya tashi saboda yawan surutan masu ƙina, saboda danniyar mugaye. Gama sukan jawo mini wahala, suna jin haushina suna ƙina. Zuciyata tana wahala a cikina; tsorace-tsoracen mutuwa sun sha kaina. Tsoro da rawan jiki sun kama ni; razana ta sha kaina. Na ce, “Kash, da a ce ina da fikafikan kurciya mana! Ai, da na yi firiya na tafi na huta, da na tafi can da nisa na zauna a hamada; da na hanzarta na tafi wurin mafakata, nesa da muguwar iska da hadiri.” Ka rikitar da mugaye, ya Ubangiji, ka birkitar da maganarsu, gama na ga rikici da faɗa a cikin birni. Dare da rana suna yawo a kan katanga; mugun hali da zargi suna a cikinta. Rundunar hallaka suna aiki a cikin birni; barazana da ƙarairayi ba sa taɓa barin titunanta. Da a ce abokin gāba ne ke zagina, da na jure da shi; da a ce maƙiyi yana tā da kansa a kaina, da na ɓoye daga gare shi. Amma kai ne, mutum kamar ni, abokina, abokina na kurkusa, wanda na taɓa jin daɗin zumunci da shi sosai yayinda muke tafiya tare a taron jama’a a gidan Allah. Bari mutuwa ta ɗauki abokan gābana ba labari; bari su gangara da rai zuwa cikin kabari, gama mugunta tana samun masauƙi a cikinsu. Amma na kira ga Allah, Ubangiji kuwa ya cece ni. Safe, rana da yamma ina kuka da nishi, yakan kuwa ji muryata. Yakan fisshe ni lafiya daga yaƙin da ake yi da ni, ko da yake da yawa suna gāba da ni. Allah, yana mulki har abada, zai ji su yă kuma azabtar da su, mutanen da ba sa taɓa canja hanyoyinsu kuma ba sa tsoron Allah. Abokina ya kai wa abokansa hari; ya tā da alkawarinsa. Maganarsa tana da laushi kamar man zaitun, duk da haka yaƙi yana a cikin zuciyarsa; kalmominsa sun fi mai sulɓi, duk da haka takuba ne zārarru. Ku kawo damuwoyinku ga Ubangiji zai kuwa riƙe ku; ba zai taɓa barin mai adalci yă fāɗi ba. Amma kai, ya Allah, za ka kawar da mugaye zuwa cikin ramin lalacewa; masu kisa da mutane masu ruɗu ba za su kai rabin kwanakin rayuwarsu ba. Amma ni dai, na dogara gare ka. Ka yi mini jinƙai, ya Allah, gama mutane sun tasar mini da zafi; dukan yini suna matsa harinsu. Masu ɓata sunana suna bina dukan yini; da yawa suna kai mini hari cikin fariyarsu. Sa’ad da nake tsoro, zan dogara gare ka. Ga Allah wanda maganarsa nake yabo ga Allah na dogara; ba zan ji tsoro ba. Me mutum mai mutuwa zai yi mini? Dukan yini sun yi ta juya maganata; kullum suna ƙulle-ƙulle su cuce ni. Sun haɗa baki, sun ɓoye, suna kallon takawata suna a shirye su ɗauki raina. Sam, kada ka bari su kuɓuce; cikin fushinka, ya Allah, ka saukar da al’ummai. Ka lissafta makokina; ka jera hawayena a littafinka, ba a rubuce suke a cikin littafinka ba? Ta haka abokan gābana za su juya da baya sa’ad da na nemi taimako. Ta haka zan san cewa Allah yana tare da ni. Ga Allah, wanda nake yabon maganarsa, ga Ubangiji, wanda nake yabon maganarsa, ga Allah na dogara; ba zan ji tsoro ba. Me mutum zai iya yi mini? Ina ƙarƙashin alkawari gare ka, ya Allah; zan miƙa hadayuna na godiya gare ka. Gama ka cece ni daga mutuwa da kuma ƙafafun daga tuntuɓe, don in yi tafiya a gaban Allah cikin hasken rai. Ka yi mini jinƙai, ya Allah, ka yi mini jinƙai, gama a gare ka raina yake samun mafaka. Zan sami mafaka a inuwar fikafikanka sai masifar ta wuce. Na yi kuka ga Allah Mafi Ɗaukaka, ga Allah, wanda yake cika manufarsa gare ni. Ya aika daga sama ya kuwa cece ni, yana tsawata wa waɗanda suke fafarata da zafi; Allah yakan aika da ƙaunarsa da amincinsa. Ina tsakiyar zakoki; ina kwance a cikin namun jeji masu cin mutane, mutanen da haƙoransu masu ne da kuma kibiyoyi, waɗanda harshensu suna da kaifi kamar takobi. Bari a ɗaukaka ka, ya Allah, bisa sammai; bari ɗaukakarka ta kasance a dukan duniya. Sun shimfiɗa raga don su kama ƙafafuna, damuwa ta sha ƙarfina. Sun haƙa rami a hanyata, amma su kansu suka fāɗa a cikinta. Zuciyata tana nan daram, ya Allah, zuciyata tana nan daram; zan rera in kuma yi kaɗe-kaɗe. Ka farka, raina! Ku farka, garaya da molo! Zan sa safe yă farka. Zan yabe ka, ya Ubangiji, a cikin al’ummai; zan rera game da kai a cikin mutane. Gama ƙaunarka mai girma ce, tana kaiwa sammai; amincinka na kaiwa sarari. Bari a ɗaukaka ka, ya Allah, bisa sammai; bari ɗaukakarka ta kasance a dukan duniya. Ku masu mulki tabbatacce kuna magana daidai? Kuna yin shari’a daidai a cikin mutane? Sam, a zuciyarku kuna ƙirƙiro rashin adalci, da hannuwanku kuma kuna tā da hargitsi a duniya. Kai, tun haihuwa mugaye sukan kauce; daga cikin ciki, su lalatattu ne maƙaryata. Dafinsu ya yi kamar dafin maciji, kamar na gamsheƙan da ya toshe kunnuwansa, da ba ya jin muryar gardi, kome dabarar gwanin mai waƙar zai zama. Ka kakkarya haƙoran a bakunansu, ya Allah; ka yayyage fiƙoƙin zakoki, ya Ubangiji! Bari su ɓace kamar ruwa mai wucewa; sa’ad da suka ja bakansu, bari kibiyoyinsu su murtsuke. Kamar katantanwun da suke narkewa yayinda suke tafiya, kamar jinjirin da aka haifa matacce, kada su ga hasken rana. Kafin tukwanenka su ji zafin ƙayayyuwa, ko su kore ne ko busasshe, za a shafe mugaye. Masu adalci za su yi murna sa’ad da aka rama musu, sa’ad da suka wanke ƙafafunsu cikin jinin mugaye. Sa’an nan mutane za su ce, “Tabbatacce har yanzu ana sāka wa adalai; tabbatacce akwai Allahn da yake shari’anta duniya.” Ka cece ni daga abokan gābana, ya Allah; ka tsare ni daga waɗanda suka tayar mini. Ka kuɓutar da ni daga masu aikata mugunta ka kuma cece ni daga masu kisa. Duba yadda suka kwanta suna jirana! Mugaye suna ƙulle-ƙullen gāba da ni ba saboda wani dalili ko na yi wa wani zunubi ba, ya Ubangiji. Ban yi wani laifi ba, duk da haka suna a shirye su fāɗa mini. Tashi ka taimake ni; dubi halin da nake ciki! Ya Ubangiji Allah Maɗaukaki, Allah na Isra’ila, ka tashi ka hukunta dukan al’ummai; kada ka nuna jinƙai ga mugaye maciya amana. Sukan dawo da yamma, suna wage haƙora kamar karnuka, suna yawo a birni. Dubi abin da suke tofawa daga bakunansu, suna tofar da takuba daga leɓunansu, suna cewa, “Wa zai ji mu?” Amma kai, ya Ubangiji, kakan yi musu dariya; kana yi wa dukan waɗannan al’ummai ba’a. Ya ƙarfina, na dogara gare ka; kai, ya Allah, kai ne kagarata, Allah mai ƙaunata. Allah zai sha gabana zai kuma sa in yi dariya a kan waɗanda suke magana marar kyau a kaina. Amma kada ka kashe su, ya Ubangiji garkuwarmu, in ba haka mutanena za su manta. Cikin ikonka ka sa su yi ta yawo barkatai, ka kuma kawar da su. Saboda zunuban bakunansu, saboda maganganun leɓunansu, bari a kama su cikin fariyarsu. Saboda zage-zage da ƙarairayin da suke yi, ka cinye su da hasala, ka cinye su sarai. Sa’an nan za a sani a iyakar duniya cewa Allah yana mulki a bisa Yaƙub. Sukan dawo da yamma, suna wage haƙora kamar karnuka, suna yawo a birni. Suna ta yawo neman abinci su kuwa yi haushi in ba su ƙoshi ba. Amma zan rera game da ƙarfinka, da safe zan rera game da ƙaunarka; gama kai ne mafakata, kagarata a lokacin wahala. Ya ƙarfina, na rera yabo gare ka; kai, ya Allah, kai ne kagarata, Allah mai ƙaunata. Ka ki mu, ya Allah, ka kuma fashe kāriyarmu; ka yi fushi da mu, yanzu ka mai da mu! Ka girgiza ƙasar ka kuma tsaga ta; ka daure karayarta, gama tana rawa. Ka nuna wa mutanenka lokutan wahala; ka ba mu ruwan inabin da ya sa muka bugu. Amma ga waɗanda suke tsoronka, ka ɗaga tuta don a buɗe gāba da baka. Ka cece mu ka kuma taimake mu da hannunka na dama, domin waɗanda kake ƙauna su kuɓuta. Allah ya yi magana daga wurinsa mai tsarki, “Da nasara zan rarraba Shekem in kuma auna Kwarin Sukkot. Gileyad nawa ne, Manasse kuma nawa ne; Efraim shi ne hular kwanona, Yahuda kuma sandar mulkina. Mowab shi ne kwanon wankina, a kan Edom zan jefa takalmina; a bisa Filistiya zan yi kirarin nasara.” Wa zai kawo ni birnin katanga? Wa zai bishe ni zuwa Edom? Ba kai ba ne, ya Allah, kai da ka ƙi mu ba ka kuwa fita tare da mayaƙanmu? Ka ba mu gudummawa a kan abokin gāba, gama taimakon mutum banza ne. Tare da Allah za mu yi nasara, zai kuma tattake abokan gābanmu. Ka ji kukata, ya Allah; ka saurari addu’ata. Daga iyakar duniya na yi kira gare ka, na yi kira yayinda zuciyata ta karai; ka bishe ni zuwa dutsen da ya fi ni tsayi. Gama kai ne mafakata, hasumiya mai ƙarfi gāba da maƙiyi. Ina marmari in zauna a tentinka har abada in sami mafaka a cikin inuwar fikafikanka. Gama ka ji alkawarina, ya Allah; ka ba ni gādo na waɗanda suke tsoron sunanka. Ka ƙara kwanakin ran sarki, shekarunsa su kasance a zamanai masu yawa. Bari yă yi mulki a gaban Allah har abada; ka sa ƙaunarka da amincinka su tsare shi. Sa’an nan zan riƙa rera yabo ga sunanka in kuma cika alkawarina kowace rana. Raina na samun hutu a wurin Allah ne kaɗai; cetona na zuwa daga gare shi. Shi kaɗai ne dutsena da cetona; shi ne kagarata, ba zan jijjigu ba. Har yaushe za ku tasar wa mutum guda? Dukanku ne za ku kā da shi wannan jinganannen bango, wannan rusasshen katanga? Sun kintsa sosai su tumɓuke shi daga matsayinsa mai martaba; suna jin daɗi yin ƙarairayi. Sukan sa wa mutum albarka da bakinsu, amma a zuciyarsu la’antawa suke yi. Ka nemi hutu, ya raina, a wurin Allah kaɗai; dogarata kan zo daga gare shi ne. Shi ne kaɗai dutsena da cetona; shi ne kagarata, ba zan jijjigu ba. Cetona da girmata sun dangana ga Allah ne, shi ne dutsena mai ƙarfi, mafakata. Ku dogara a gare shi a duk lokuta, ya mutane; ku faɗi albarkaci bakin zukatanku a gare shi, gama Allah ne mafakarmu. Talakawa dai kamar shaƙar iska suke, Attajirai dai kamar shirim suke; in aka auna a ma’auni, su ba wani abu ba ne; dukansu dai kamar shaƙar iska ne kawai. Kada ku dogara a kan ƙwace ko yin fariya a kayan sata; ko arzikinku ya ƙaru, kada ku sa zuciyarku a kansu. Abu guda Allah ya ce, abubuwa biyu na ji, “Cewa kai, ya Allah, kake mai ƙarfi, kuma cewa kai, ya Ubangiji, mai ƙauna ne. Tabbatacce za ka sāka wa kowane mutum bisa ga abin da ya yi.” Ya Allah, kai ne Allahna, da nacewa na neme ka; raina yana ƙishinka, jikina yana marmarinka, cikin busasshiyar ƙasar da ta zozaye inda babu ruwa. Na gan ka a wuri mai tsarki na kuma dubi ikonka da ɗaukakarka. Domin ƙaunarka ta fi rai kyau, leɓunana za su ɗaukaka ka. Zan yabe ka muddin raina, kuma a cikin sunanka zai ɗaga hannuwana. Raina zai ƙoshi kamar da abinci mafi kyau; da leɓunan rerawa bakina zai yabe ka. A gadona na tuna da kai; ina tunaninka dukan dare. Domin kai ne mai taimakona, ina rera a cikin inuwar fikafikanka. Raina ya manne maka; hannunka na dama yana riƙe da ni. Su da suke neman raina za su hallaka; za su gangara zuwa zurfafan duniya. Za a bayar da su ga takobi su kuma zama abincin karnukan jeji. Amma sarki zai yi farin ciki ga Allah; dukan waɗanda suke rantse da sunan Allah za su yabe shi, amma za a rufe bakunan maƙaryata. Ka ji ni, ya Allah, yayinda nake faɗin abin da yake damuna; ka tsare raina daga barazanan abokin gāba. Ka ɓoye ni daga ƙulle-ƙullen mugaye, daga daure dauren wannan taro masu aikata mugunta. Sukan wāsa harsunansu kamar takuba su harba kalmominsu kamar kibiyoyi masu kisa. Sukan yin kwanto su harbi marar laifi; sukan yi harbi nan da nan, ba tsoro. Sukan ƙarfafa juna a mugayen ƙulle-ƙullensu, sukan yi magana yadda za su ɓoye tarkunansu; su ce, “Wa zai gan su?” Sukan yi ƙulle-ƙullen rashin adalci su ce, “Mun gama ƙulla cikakkiyar maƙarƙashiya tsab!” Zuciyar mutum da tunaninsa, suna da wuyar ganewa. Amma Allah zai harbe su da kibiyoyi; nan da nan za a buge su su fāɗi. Zai juya harshensu a kansu yă kuma kawo su ga hallaka; duk waɗanda suka gan su za su kaɗa kai, suna musu ba’a. Dukan mutane za su ji tsoro; za su yi shelar ayyukan Allah su kuma yi tunanin abin da ya aikata. Bari masu adalci su yi farin ciki a cikin Ubangiji su kuma nemi mafaka a gare shi; bari dukan masu gaskiya a zuciya su yabe shi! Yabo ya dace da kai, ya Allah, a Sihiyona; a gare ka za mu cika alkawuranmu Ya kai wanda yake jin addu’a a gare ka dukan mutane za su zo. Sa’ad da zunubai suka sha ƙarfinmu, ka gafarta laifofinmu. Masu albarka ne waɗanda ka zaɓa ka kawo kusa don su zauna a filayenka! Mun cika da abubuwa masu kyau na gidanka, na haikalinka mai tsarki. Ka amsa mana da ayyuka masu banmamaki na adalci, Ya Allah Mai Cetonmu, begen dukan iyakar duniya da kuma na tekuna masu nesa, wanda ya yi duwatsu ta wurin ikonka, bayan ka kintsa kanka da ƙarfi, wanda ya kwantar da rurin tekuna, rurin raƙumansu, da kuma tumbatsar al’ummai. Waɗanda suke zama can da nesa sukan ji tsoron manyan ayyukanka; inda safe ke haskaka yamma kuma ta shuɗe kakan sa a yi waƙoƙin farin ciki. Kana kula da ƙasa kana kuma yi mata banruwa; kana azurta ta a yalwace. Rafuffukan Allah sun cika da ruwa don su ba mutane hatsi, don haka ne ka ƙaddara. Ka kwarara ta da ruwa ka kuma baje kunyoyinta; ka sa ta yi laushi da yayyafi ka kuma albarkaci tsire-tsirenta. Saboda alherinka, ya Allah, an sami kaka mai albarka, amalankenka kuwa sun cika har suna zuba. Makiyayan hamada sun cika har suna zuba; tuddai sun rufu da murna. Wurin dausayin kiwo sun rufu da garkuna kwari kuma sun cika da hatsi; suna sowa don farin ciki. Ku yi sowa ta farin ciki ga Allah, dukan duniya! Ku rera ɗaukaka ga sunansa; ku sa yabonsa yă zama da ɗaukaka! Ku ce wa Allah, “Ayyukanka da banmamaki suke! Ikonka da girma yake har abokan gābanka suna durƙusa a gabanka. Dukan duniya sun rusuna a gabanka suna rera yabo gare ka, suna rera yabo ga sunanka.” Ku zo ku ga abin da Allah ya yi, ayyukansa masu banmamaki a madadin mutum! Ya juya teku zuwa busasshiyar ƙasa, sun wuce cikin ruwaye da ƙafa, ku zo, mu yi farin ciki a cikinsa. Yana mulki har abada ta wurin ikonsa, idanunsa suna duban al’ummai, kada ’yan tawaye su tayar masa. Ku yabi Allahnku, ya mutane, bari a ji ƙarar yabonsa; ya adana rayukanmu ya kuma kiyaye ƙafafunmu daga santsi. Gama kai, ya Allah, ka gwada mu; ka tace mu kamar azurfa. Ka kawo mu cikin kurkuku ka kuma jibga kaya masu nauyi a bayanmu. Ka bar mutane suka hau a kawunanmu; mun bi ta wuta da ruwa, amma ka kawo mu zuwa wurin yalwa. Zan zo haikalinka da hadayun ƙonawa zan kuwa cika alkawurana gare ka, alkawuran da leɓunana suka yi alkawari bakina kuma ya faɗa sa’ad da nake cikin wahala. Zan miƙa kitsen dabbobi gare ka da kuma baye-baye na raguna; zan miƙa bijimai da awaki. Ku zo ku saurara, dukanku waɗanda suke tsoron Allah; bari in faɗa muku abin da ya yi mini. Na yi kuka gare shi da bakina; yabonsa yana a harshena. Da a ce na ji daɗin zunubi a zuciyata, da Ubangiji ba zai saurara ba; amma tabbatacce Allah ya saurara ya kuma ji muryata a cikin addu’a. Yabo ga Allah, wanda bai ƙi addu’ata ba ko yă janye ƙaunarsa daga gare ni! Bari Allah yă yi mana alheri yă kuma albarkace mu yă kuma sa fuskarsa ta haskaka a kanmu, don a san hanyoyinka a duniya, cetonka kuma a cikin dukan al’ummai. Bari mutane su yabe ka, ya Allah; bari dukan mutane su yabe ka. Bari al’ummai su yi murna su kuma rera don farin ciki, gama kana mulkin mutanenka da adalci kana kuma bi da al’umman duniya. Bari mutane su yabe ka, ya Allah; bari dukan mutane su yabe. Sa’an nan ƙasa za tă ba da girbinta Allah kuma, Allahnmu, zai albarkace mu. Allah yă sa mana albarka, dukan iyakar duniya kuma su ji tsoronsa. Bari Allah yă tashi, bari a watsar da abokan gābansa; bari maƙiyansa su gudu a gabansa. Kamar yadda iska take hura hayaƙi, bari yă hura su haka; kamar yadda kaki kan narke a gaban wuta, bari mugaye su hallaka a gaban Allah. Amma bari adalai su yi murna su kuma yi farin ciki a gaban Allah; bari su yi murna da farin ciki. Rera wa Allah, rera yabo ga sunansa, ku ɗaukaka wanda yake hawa a kan gizagizai; sunansa Ubangiji ne, ku kuma yi farin ciki a gabansa. Uba ga marayu, mai kāre gwauraye, shi ne Allah a mazauninsa mai tsarki. Allah ya shirya masu kaɗaici a cikin iyalai, ya jagorance ’yan kurkuku da waƙoƙi; amma ’yan tawaye suna zama a ƙasa mai zafin rana. Sa’ad da ka fito a gaban mutanenka, ya Allah, sa’ad da ka taka ta cikin ƙasar da take wofi, duniya ta girgiza, sammai suka zuba ruwan sama, a gaban Allah, wanda ya bayyana a Sinai, a gaban Allah, Allah na Isra’ila. Ka ba da yayyafi a yalwace, ya Allah; ka rayar da gādonka da ya gāji. Mutanenka suka zauna a cikinsa, kuma daga yalwarka, ya Allah, ka tanada wa matalauta. Ubangiji ya yi umarni, mutane masu yawa ne suka yi shelarsa, “Sarakuna da mayaƙa suka gudu a gaggauce; cikin sansani mutane sun raba ganima. Har yayinda kuke barci a cikin garken tumaki, an dalaye fikafikan kurciya da azurfa, fikafikanta da zinariya mai ƙyalli.” Sa’ad da Maɗaukaki ya watsar da sarakuna a cikin ƙasa, sai ya zama kamar ƙanƙara ta sauka a kan Zalmon. Duwatsun Bashan, duwatsu masu alfarma ne; duwatsun Bashan masu wuyar hawa ne. Don me kuke duba da kishi, ya duwatsu masu wuyan hawa, a kan dutsen da Allah ya zaɓa yă yi mulki, inda Ubangiji kansa zai zauna har abada? Karusan Allah ninkin dubbai goma ne da kuma dubu dubbai; Ubangiji ya zo daga Sinai ya shiga cikin haikalinsa. Sa’ad da ka hau bisa, ka bi da kamammu cikin tawagarka; ka karɓi kyautai daga mutane, har ma daga ’yan tawaye, don kai, ya Ubangiji Allah, za ka zauna a can. Yabo ya tabbata ga Ubangiji, ga Allah Mai Cetonmu, wanda kullum yake ɗaukan nauyinmu. Allahnmu shi ne Allah wanda yake ceto; daga Ubangiji Mai Iko Duka kuɓuta yake zuwa daga mutuwa. Tabbatacce Allah zai murƙushe kawunan abokan gābansa, rawanin gashi na waɗanda suke ci gaba cikin zunubansa. Ubangiji ya ce, “Zan kawo su daga Bashan; zan kawo su daga zurfafan teku, don ku wanke ƙafafunku a cikin jinin maƙiyanku, yayinda harsunan karnukanku su sami rabonsu.” Jerin gwanonka ya zo a bayyane, ya Allah, jerin gwanon Allahna da Sarkina zuwa cikin wuri mai tsarki. A gaba akwai mawaƙa, a bayansu akwai makaɗa; tare da su akwai ’yan mata suna bugan ganguna. Ku yabi Allah cikin taro mai girma; yabi Ubangiji cikin taron Isra’ila. Ga ƙaramar kabilar Benyamin, suna jagorance su, ga babbar ƙungiya shugabannin Yahuda, ga kuma shugabannin Zebulun da na Naftali. Ka bayyana ikonka, ya Allah; ka nuna ƙarfinka, ya Allah, kamar yadda ka yi a dā. Saboda haikalinka a Urushalima sarakuna za su kawo maka kyautai. Ka tsawata wa naman jejin nan a cikin kyauro, garken bijimai a cikin ’yan maruƙan al’ummai. Ka ƙasƙantar, bari yă kawo sandunan azurfa. Ka watsar da al’ummai waɗanda suke jin daɗin yaƙi. Jakadu za su zo daga Masar; Kush za tă miƙa kanta ga Allah. Ku rera wa Allah, ya masarautan duniya, ku rera yabo ga Ubangiji, gare shi wanda yake hawan daɗaɗɗen sararin sama, wanda yake tsawa da babbar murya. Ku yi shelar ikon Allah, wanda ɗaukakarsa take a bisa Isra’ila, wanda ikonsa yake a cikin sarari. Kai mai banmamaki ne, ya Allah, cikin wurinka mai tsarki; Allah na Isra’ila yakan ba da iko da kuma ƙarfi ga mutanensa. Yabo ya tabbata ga Allah! Ka cece ni, ya Allah, gama ruwa ya kai wuyata Na nutse cikin laka mai zurfi, inda babu wurin tsayawa. Na shiga cikin ruwaye masu zurfi; rigyawa ya sha kaina. Na gaji da kira ina neman taimako; maƙogwarona ya bushe idanuna sun dushe, suna neman Allahna. Waɗanda suke ƙina ba dalili sun fi gashin kaina yawa; da yawa ne abokan gābana babu dalili, su da suke nema su hallaka ni. An tilasta mini in mayar da abin da ban sata ba. Ka san wautata, ya Allah; laifina ba a ɓoye yake daga gare ka ba. Bari waɗanda suke sa zuciya gare ka kada su sha kunya saboda ni, Ya Ubangiji, Ubangiji Maɗaukaki; bari waɗanda suke neman ka kada su sha kunya saboda ni, Ya Allah na Isra’ila. Gama na jimre da ba’a saboda kai, kunya kuma ta rufe fuskata. Ni baƙo ne a cikin ’yan’uwana, bare kuma ga ’ya’yan mahaifiyata maza; gama himma da nake yi wa gidanka yana ƙunata, kuma zagi na masu zaginka yana fāɗuwa a kaina. Sa’ad da na yi kuka na kuma yi azumi dole in jimre da ba’a; sa’ad da na sanya rigunan makoki, mutane suna maishe ni abin dariya. Masu zama a ƙofa suna mini ba’a, na zama waƙa a bakin bugaggu da giya. Amma na yi addu’a gare ka, ya Ubangiji, a lokacin da ka ga dama; a cikin ƙaunarka mai girma, ya Allah, ka amsa mini da tabbacin ceto. Ka fid da ni daga laka, kada ka bari in nutse; ka cece ni daga waɗanda suke ƙina, daga rurin ruwaye. Kada ka bar rigyawa yă sha kaina ko zurfafa su haɗiye ni ko rami yă rufe bakinsa a kaina. Ka amsa mini, ya Ubangiji cikin alherin ƙaunarka; cikin jinƙanka mai girma ka juyo gare ni. Kada ka ɓoye fuskarka daga bawanka; ka amsa mini da sauri, gama ina cikin wahala. Ka zo kusa ka kuɓutar da ni; ka fanshe ni saboda maƙiyana. Ka san yadda ake mini ba’a, ake kunyatar da ni da kuma yadda nake shan kunya; dukan abokan gābana suna a gabanka. Ba’a ta sa zuciyata ta karai ta bar ni ba mataimaki; Na nemi a ji tausayina, amma ban sami ko ɗaya ba, na nemi masu ta’aziyya, amma ban sami ko ɗaya ba. Sun sa abin ɗaci cikin abincina suka kuma ba ni ruwan inabi mai tsami sa’ad da nake jin ƙishi. Bari teburin da aka shirya a gabansu yă zama musu tarko; bari yă zama sakamakon laifi da kuma tarko. Bari idanunsu yă dushe don kada su gani, bayansu kuma yă tanƙware har abada. Ka kwarara fushinka a kansu; bari fushinka mai zafi yă ci musu. Bari wurinsu yă zama kufai; kada ka bar wani yă zauna a tentunansu. Gama sun tsananta wa waɗanda ka hukunta suna kuma taɗin wahalar waɗanda ka ji musu rauni. Ka neme su da laifi a kan laifi; kada ka bar su su sami rabo a cikin cetonka. Bari a shafe su sarai daga littafin rai kada a kuma lissafta su tare da adalai. Ina cikin zafi da kuma azaba; bari cetonka, ya Allah, yă tsare ni. Zan yabe sunan Allah cikin waƙa in kuma ɗaukaka shi tare wurin yin godiya. Wannan zai gamshi Ubangiji fiye da saniya, fiye da bijimi da ƙahoninsa da kuma kofatansa. Matalauta za su gani su kuma yi murna, ku da kuke neman Allah, bari zukatanku su rayu! Ubangiji yakan ji masu bukata ba ya kuwa ƙyale kamammun mutanensa. Bari sama da ƙasa su yabe shi, tekuna da dukan abin da yake motsi a cikinsu, gama Allah zai cece Sihiyona yă sāke gina biranen Yahuda. Sa’an nan mutane za su zauna a can su mallake ta, ’ya’yan bayinsa za su gāje ta, waɗanda kuma suna ƙaunar sunansa za su zauna a can. Ka hanzarta, ya Allah, ka cece ni; Ya Ubangiji, zo da sauri ka taimake ni. Bari masu neman raina su sha kunya su kuma rikice; bari dukan masu sha’awar gani lalacewata su juye baya da kunya. Bari masu ce mini, “Allah yă ƙara!” Su juye baya saboda kunyansu. Amma bari dukan masu nemanka su yi farin ciki su kuma yi murna a cikinka; bari waɗanda suke ƙaunar cetonka kullum su ce, “Bari Allah yă sami ɗaukaka!” Duk da haka ni matalauci ne da kuma mai bukata; ka zo da sauri gare ni, ya Allah. Kai ne mai taimakona da mai cetona; Ya Ubangiji, kada ka yi jinkiri. A gare ka, ya Ubangiji, na nemi mafaka; kada ka taɓa sa in sha kunya. Ka kuɓutar da ni ka cece ni cikin adalcinka; ka juya kunnenka gare ni ka kuma cece ni. Ka zama dutsena da kagarata, inda kullum zan je. Ka ba da umarni a cece ni, gama kai ne dutsen ɓuyana da katangata. Ka cece ni, ya Allahna, daga hannun mugaye, da kuma daga ikon mugaye da masu mugunta. Gama kai ne abin sa zuciyata, ya Ubangiji Mai Iko Duka, ƙarfin zuciyata tun ina yaro. Daga haihuwa na dogara gare ka; kai ka kawo ni daga cikin mahaifiyata. Kullayaumi zan yabe ka. Na zama kamar abin sa zuciya ga yawanci, amma kai ne katangata mai ƙarfi. Bakina ya cika da yabonka, ina furta darajarka dukan yini. Kada ka yar da ni sa’ad da na tsufa; kada ka yashe ni sa’ad da ƙarfina ya ƙare. Gama abokan gābana suna magana a kaina; waɗanda suke jira su kashe ni suna haɗa baki tare. Suna cewa, “Allah ya yashe shi; mu fafare shi mu kama shi, gama ba wanda zai kuɓutar da shi.” Kada ka yi nisa da ni, ya Allah; zo da sauri, ya Allahna, ka taimake ni. Bari masu zagina su hallaka da kunya; bari waɗanda suke so su cutar da ni su sha ba’a da kuma kunya. Amma game da ni, kullayaumi zan kasance da sa zuciya; zan yabe ka sau da sau. Bakina zai ba da labarin adalcinka, zai yi maganar cetonka dukan yini, ko da yake ban san yawansa ba. Zan zo in furta in kuma yi shelar ayyukanka masu girma, ya Ubangiji Mai Iko Duka; zan yi shelar adalcinka, naka kaɗai. Tun ina yaro, ya Allah, ka koya mini har wa yau ina furta ayyukanka masu banmamaki. Ko sa’ad da na tsufa da furfura, kada ka yashe ni, ya Allah, sai na furta ikonka ga tsara mai zuwa, ƙarfinka ga dukan waɗanda suke zuwa. Adalcinka ya kai sararin sama, ya Allah, kai da ka yi manyan abubuwa. Wane ne kamar ka, ya Allah? Ko da yake ka sa na ga wahaloli, masu yawa da kuma masu ɗaci, za ka sāke mayar mini da rai; daga zurfafan duniya za ka sāke tā da ni. Za ka ƙara girmana ka sāke ta’azantar da ni. Zan yabe ka da garaya saboda amincinka, ya Allah; zan rera yabo gare ka da molo, Ya Mai Tsarki na Isra’ila. Leɓunana za su yi sowa don farin ciki sa’ad da na rera yabo gare ka, ni, wanda ka fansa. Harshena zai ba da labarin ayyukanka masu adalci dukan yini, gama waɗanda suka so su cutar da ni sun sha kunya suka kuma rikice. Ka tanada sarki da shari’arka ta gaskiya, ya Allah, ɗan sarki da adalcinka. Zai shari’anta mutanenka da adalci, marasa ƙarfinka da shari’ar gaskiya. Duwatsu za su kawo wadata ga mutane, tuddai kuma su ba da amfani na adalci. Zai kāre marasa ƙarfi a cikin mutane yă kuma cece ’ya’yan masu bukata; zai murƙushe masu danniya. Zai jimre muddin rana tana nan, muddin akwai wata, har dukan zamanai. Zai zama kamar ruwan sama mai fāɗuwa a filin ciyayin da aka yanka, kamar yayyafi mai ba wa duniya ruwa. A kwanakinsa adalai za su haɓaka wadata za tă yalwata har sai babu sauran wata. Zai yi mulki daga teku zuwa teku kuma daga Kogi zuwa iyakar duniya. Kabilun hamada za su rusuna a gabansa abokan gābansa kuwa za su lashe ƙura. Sarakunan Tarshish da na bakin kogi masu nisa za su ba da gandu gare shi; sarakunan Sheba da Seba za su ba shi kyautai. Dukan sarakuna za su rusuna masa kuma dukan al’ummai za su bauta masa. Gama zai ceci masu bukatan da suka yi kuka, marasa ƙarfin da ba su da mai taimako. Zai ji tausayin gajiyayyu da masu bukata yă ceci masu bukata daga mutuwa. Zai kuɓutar da su daga danniya da rikici, gama jininsu yake a gabansa. Bari yă yi doguwar rayuwa! Bari a ba shi zinariya daga Sheba. Bari mutane su riƙa yin addu’a dominsa su kuma albarkace shi dukan yini. Bari hatsi yă yalwata a duk fāɗin ƙasar; bari yă cika bisan tuddai. Bari ’ya’yan itatuwansa su haɓaka kamar Lebanon; bari yă bazu kamar ciyayi a gona. Bari sunansa yă dawwama har abada; bari yă ci gaba muddin rana tana nan. Dukan al’ummai za su sami albarka ta wurinsa, za su kuma ce da shi mai albarka. Yabo ya tabbata ga Ubangiji Allah, Allah na Isra’ila, wanda shi kaɗai ya aikata abubuwa masu banmamaki. Yabo ya tabbata ga sunansa mai ɗaukaka har abada; bari dukan duniya ta cika da ɗaukakarsa. Amin kuma Amin. Wannan ya kammala addu’o’in Dawuda ɗan Yesse. Tabbatacce Allah mai alheri ne ga Isra’ila, ga waɗanda suke masu tsabta a zuciya. Amma game da ni, ƙafafuna suna gab da yin santsi; tafin ƙafana ya yi kusan zamewa. Gama na yi kishin masu girman kai sa’ad da na ga cin gaban da masu mugunta suke yi. Ba sa yin wata fama; jikunansu lafiya suke da kuma ƙarfi. Ba sa shan wata wahalar da sauran mutane ke sha; ba su da damuwa irin na ’yan adam. Saboda girman kai ya zama musu abin wuya; tā da hankali ya zama musu riga. Daga mugayen zukatansu laifi kan fito mugaye ƙulle-ƙullen da suke cikin zukatansu ba su da iyaka. Suna ba’a, suna faɗin mugayen abubuwa; cikin girman kan suna barazana yin danniya. Bakunansu na cewa sama na su ne, kuma harsunansu sun mallaki duniya. Saboda haka mutanensu sun juya gare su suna kuma shan ruwa a yalwace. Suna cewa, “Yaya Allah zai sani? Mafi Ɗaukaka yana da sani ne?” Ga yadda mugaye suke, kullum ba su da damuwa, arzikinsu yana ta ƙaruwa. Tabbatacce a banza na bar zuciyata da tsabta; a banza na wanke hannuwa don nuna rashin laifi. Dukan yini na sha annoba; an hukunta ni kowace safiya. Da na ce, “Zan faɗa haka,” da na bashe ’ya’yanka. Sa’ad da na yi ƙoƙari in gane wannan, sai ya zama danniya a gare ni sai da na shiga wuri mai tsarki na Allah; sa’an nan na gane abin da ƙarshensu zai zama. Tabbatacce ka sa su a ƙasa mai santsi; ka jefar da su ga hallaka. Duba yadda suka hallaka farat ɗaya, razana ta share su gaba ɗaya! Kamar yadda mafarki yake sa’ad da mutum ya farka, haka yake sa’ad da ka farka, ya Ubangiji, za ka rena su kamar almarai. Sa’ad da zuciyata ta ɓaci hankalina kuma ya tashi, na zama marar azanci da jahili; na zama kamar dabba a gabanka. Duk da haka kullum ina tare da kai; ka riƙe ni a hannun damana. Ka bishe ni da shawararka, bayan haka kuma za ka kai ni cikin ɗaukaka. Wa nake da shi a sama in ba kai ba? Ba na kuma sha’awar kome a duniya in ban da kai. Jikina da zuciyata za su iya raunana, amma Allah ne ƙarfin zuciyata da kuma rabona har abada. Waɗanda suke nesa da kai za su hallaka; kakan hallaka dukan waɗanda suke maka rashin aminci. Amma game da ni, yana da kyau in kasance kusa da Allah. Na mai da Ubangiji Mai Iko Duka mafakata; zan yi shelar dukan ayyukanka. Me ya sa ka ƙi mu har abada, ya Allah? Me ya sa fushinka yake a kan tumakin kiwonka? Ka tuna da mutanen da ka saya tun da daɗewa, kabilar gādonka, wadda ka fansa, Dutsen Sihiyona, inda ka zauna. Ka juye sawunka wajen waɗannan madawwamin kufai, dukan wannan hallakar da abokin gāba ya yi wa wuri mai tsarki. Maƙiyanka sun yi ruri a inda ka sadu da mu; suka kakkafa tutotinsu a matsayin alamu. Sun yi kamar mutane masu wāshin gatura don yanka itatuwa a kurmi. Sun ragargaje dukan sassaƙar katako da gatura da kuma gudumarsu. Suka ƙone wurinka mai tsarki ƙurmus; suka ƙazantar da mazaunin Sunanka. Suna cewa a zukatansu, “Za mu murƙushe su sarai!” Suka ƙone ko’ina aka yi wa Allah sujada a ƙasar. Ba a ba mu wata alama mai banmamaki ba; ba sauran annabawan da suka ragu, kuma babu waninmu da ya sani har yaushe wannan zai ci gaba. Har yaushe abokan gāba za su yi mana ba’a, ya Allah? Maƙiya za su ci gaba da ɓata sunanka har abada ne? Me ya sa ka janye hannunka, hannunka na dama? Ka fid da shi daga rigarka ka hallaka su! Amma kai, ya Allah, kai ne sarki tun da daɗewa; ka kawo ceto a kan duniya. Kai ne ka raba teku ta wurin ikonka; ka farfashe kawunan dodo a cikin ruwaye. Kai ne ka murƙushe kawunan dodon ruwa ka kuma ba da shi yă zama abinci ga halittun hamada. Kai ne ka bubbuɗe maɓulɓulai da rafuffuka; ka busar da koguna masu ruwa. Yini naka ne, dare kuma naka ne; ka kafa rana da wata. Kai ne ka kafa dukan iyakokin duniya; ka yi rani da damina. Ka tuna da yadda abokin gāba ya yi maka ba’a, ya Ubangiji, yadda wawaye suka ɓata sunanka. Kada ka ba da ran kurciyarka ga namun jeji; kada ka manta har abada da rayukan mutanenka masu shan azaba. Ka kula da alkawarinka, domin akwai tashin hankali a kowane lungu mai duhu na ƙasar. Kada ka bar waɗanda ake danniya su sha kunya; bari matalauta da mabukata su yabe sunanka. Ka tashi, ya Allah, ka kāre muradinka; ka tuna yadda wawaye suka yi maka ba’a dukan yini. Kada ka ƙyale surutan ban haushi na maƙiyanka, ihun abokan gābanka, waɗanda suke ci gaba da yi. Muna maka godiya, ya Allah, muna maka godiya, gama Sunanka yana kusa; mutane na faɗin ayyukanka masu banmamaki. Ka ce, “Na zaɓi ƙayyadadden lokaci; ni ne wanda yake shari’ar gaskiya. Sa’ad da duniya da dukan mutanenta suka girgiza, ni ne wanda na riƙe ginshiƙan daram. Ga masu girman kai na ce, ‘Kada ku ƙara taƙama,’ ga mugaye kuma, ‘Kada ku ɗaga ƙahoninku. Kada ku ɗaga ƙahoninku gāba da sama; kada ku yi magana da miƙaƙƙen wuya.’ ” Ba wani daga gabas ko yamma ko hamada da zai ɗaukaka mutum. Amma Allah ne mai yin shari’a, yakan saukar da wannan, yă kuma tayar da wani. A hannun Ubangiji akwai kwaf cike da ruwan inabi mai kumfa gauraye da kayan yaji; yakan zuba shi, dukan mugayen duniya kuwa su sha shi tas. Game da ni dai, zan furta wannan har abada; zan rera yabo ga Allah na Yaƙub, wanda ya ce, “Zan yanke ƙahonin dukan mugaye, amma za a ɗaga ƙahonin adalai sama.” A cikin Yahuda an san Allah; sunansa da girma yake a cikin Isra’ila. Tentinsa yana a Salem mazauninsa yana a Sihiyona. A can ya kakkarya kibiyoyin wuta, garkuwoyi da takuban, makaman yaƙi. Darajarka tana da haske, fiye da darajar tuddai waɗanda suke cike da namun jeji masu yawa. Jarumawa sun zube kamar ganima sun yi barcinsu na ƙarshe; ba ko jarumi guda da zai iya ɗaga hannuwansa. A tsawatawarka, ya Allah na Yaƙub, doki da keken yaƙi suka kwanta ba motsi. Kai kaɗai ne za a ji tsoro. Wane ne zai iya tsayawa sa’ad da ka yi fushi? Daga sama ka yi shelar hukunci, ƙasa kuwa ta ji tsoro ta kuwa yi tsit, sa’ad da kai, ya Allah, ka tashi don ka yi shari’a, don ka cece dukan masu shan wahala a ƙasar. Tabbatacce fushinka a kan mutane kan jawo maka yabo, waɗanda suka tsira daga fushinka za su zama kamar rawaninka. Ku yi alkawari wa Ubangiji Allahnku ku kuma cika su; bari dukan ƙasashen maƙwabta su kawo kyautai ga Wannan da za a ji tsoro. Ya kakkarya ƙarfin masu mulki; sarakunan duniya suna tsoronsa. Na yi kuka ga Allah don taimako; na yi kuka ga Allah don yă ji ni. Sa’ad da nake cikin damuwa, na nemi Ubangiji; da dare na miƙa hannuwa ba gajiya raina kuma ya ƙi yă ta’azantu. Na tuna da kai, ya Allah, na kuma yi nishi; na yi nishi, ƙarfina kuwa duk ya raunana. ka hana idanuna rufewa; na damu ƙwarai har ba na iya magana. Na yi tunani kwanakin da suka wuce, shekarun da suka wuce da daɗewa; na tuna da waƙoƙina da dare. Zuciyata ta yi nishi, ƙarfina kuwa ya nemi yă sani. “Ubangiji zai ƙi ne har abada? Ba zai taɓa nuna alherinsa kuma ba? Ƙaunarsa marar ƙarewa ta ɓace ke nan har abada? Alkawarinsa ya kāsa ke nan a dukan lokaci? Allah ya manta yă yi jinƙai? Cikin fushinsa ya janye tausayinsa ne?” Sai na yi tunani, “Zan yi roƙo saboda wannan, shekarun da Mafi Ɗaukaka ya miƙa hannunsa na dama.” Zan tuna da ayyukan Ubangiji; I, zan tuna mu’ujizanka na tun dā. Zan yi tunani a kan dukan ayyukanka in lura da dukan manyan abubuwan da ka aikata. Hanyoyinka, ya Allah, masu tsarki ne. Wanda allah ne yake da girma kamar Allahnmu? Kai ne Allahn da yakan aikata mu’ujizai; ka nuna ikonka a cikin mutane. Da hannunka mai ƙarfi ka fanshi mutanenka, zuriyar Yaƙub da Yusuf. Ruwaye sun gan ka, ya Allah, ruwaye sun gan ka suka firgita; zurfafan gaske sun girgiza. Gizagizai sun sauko da ruwa, sararin sama suka buga tsawa; kibiyoyinka suka yi ta kai komo da walƙiya. Aka ji tsawanka a cikin guguwa, walƙiyarka ta haskaka duniya; duniya ta yi rawar jiki ta girgiza. Hanyarka ta bi ta cikin teku, hanyarka ta bi cikin manyan ruwaye, duk da haka ba a ga sawunka ba. Ka bi da mutanenka kamar garke ta hannun Musa da Haruna. Ya mutanena, ku ji koyarwata; ku saurari kalmomin bakina. Zan buɗe bakina da misalai, zan faɗi ɓoyayyun abubuwa, abubuwan dā, abin da muka ji muka kuma sani, abubuwan da kakanninmu suka faɗa mana. Ba za mu ɓoye su wa ’ya’yanmu ba; za mu faɗa wa tsara mai zuwa ayyukan da suka zama yabo na Ubangiji, ikonsa, da abubuwan banmamakin da ya aikata. Ya kafa ƙa’idodi wa Yaƙub ya kuma kafa doka a cikin Isra’ila, wadda ya umarce kakanni-kakanninmu su koya wa ’ya’yansu, don tsara na biye su san su, har da ’ya’yan da ba a riga an haifa ba, su kuma su faɗa wa ’ya’yansu. Ta haka za su dogara ga Allah ba kuwa za su manta da ayyukansa ba amma za su kiyaye umarnansa. Ba za su zama kamar kakanni kakanninsu ba, masu taurinkai da kuma tsara masu tayarwa, waɗanda zukatansu ba su yi biyayya ga Allah ba, waɗanda zukatansu ba su yi aminci ga Allah ba. Mutanen Efraim, ko da yake suna da bakkuna, suka juya da baya a ranar yaƙi; ba su kiyaye alkawarin Allah ba suka kuma ƙi su yi rayuwa ta wurin dokarsa. Suka manta da abin da ya aikata, abubuwan banmamakin da ya nuna musu. Ya yi mu’ujizai a idanun kakanninsu a ƙasar Masar, a yankin Zowan. Ya raba teku ya kuma bi da su ciki; ya sa ruwa ya tsaya daram kamar bango. Ya bishe su da girgije da rana da kuma haske daga wuta dukan dare. Ya tsage duwatsu a cikin hamada ya kuma ba su ruwaye a yalwace kamar tekuna; ya fid da rafuffuka daga dutsen da ya tsaga ya sa ruwa ya gudu kamar koguna. Amma suka ci gaba da yin masa zunubi, suna tayarwa a cikin hamada a kan Mafi Ɗaukaka. Da gangan suka gwada Allah ta wurin neman abincin da suke kwaɗayi. Suka yi magana a kan Allah, suna cewa, “Allah zai iya shimfiɗa tebur a cikin hamada? Sa’ad da ya bugi dutse, ruwa ya ɓulɓulo, rafuffuka suka yi gudu a yalwace. Amma zai iya ba mu abinci? Zai iya tanada wa mutanensa nama?” Sa’ad da Ubangiji ya ji su, ya yi fushi ƙwarai; wutarsa ta ɓarke a kan Yaƙub, hasalarsa kuwa ta tashi a kan Isra’ila, gama ba su gaskata ga Allah ba ko su dogara ga cetonsa. Duk da haka ya ba da umarni ga sarari a bisa ya kuma buɗe ƙofofin sammai; ya sauko da Manna wa mutanensa don su ci, ya ba su hatsin sama. Mutane suka ci burodin mala’iku; ya aika musu dukan abincin da za su iya ci. Ya saki iskar gabas daga sammai ya kuma saki iskar yamma ta wurin ikonsa. Ya sauko da nama a kansu kamar ƙura, tsuntsaye masu firiya kamar yashi a bakin teku. Ya sa suka sauka a cikin sansaninsu, ko’ina kewaye da tentunansu. Suka ci har suka sami fiye da abin da ya ishe su, gama ya ba su abin da suka yi kwaɗayi. Amma kafin su juyo daga abincin da suka yi kwaɗayi, kai tun ma yana a bakunansu, fushin Allah ya ƙuna a kansu; ya karkashe waɗanda suka fi ƙiba a cikinsu, yana yankan matasan Isra’ila. Duk da haka, suka ci gaba da yin zunubi; duk da abubuwan banmamakinsa, ba su gaskata ba. Saboda haka ya sa kwanakinsu suka ƙare a banza shekarunsu kuma cikin masifa. A duk sa’ad da Allah ya kashe su, sai su neme shi; sukan juyo a natse gare shi. Sun tuna cewa Allah ne Dutsensu, cewa Allah Mafi Ɗaukaka ne Mai fansarsu. Amma sai su yi ta yin masa zaƙin baki, suna masa ƙarya da harsunansu; zukatansu ba sa biyayya gare shi, ba su da aminci ga alkawarinsa. Duk da haka ya kasance mai jinƙai; ya gafarta laifofinsu bai kuwa hallaka su ba. Sau da sau ya janye fushinsa bai kuwa sa fushinsa yă ƙuna ba. Ya tuna cewa su naman jiki ne kawai, iska mai wucewa da ba ta dawowa. Sau da yawa sun tayar masa a cikin hamada suka kuma ɓata masa rai a jeji! Sau da sau suka riƙa gwada Allah; suka tsokane Mai Tsarki na Isra’ila. Ba su tuna da ikonsa, a ranar da ya fanshe su daga mai danniya, ranar da ya nuna mu’ujizansa a Masar abubuwan banmamakinsa a yankin Zowan ba. Ya mai da kogunansu suka zama jini; ba su iya sha daga rafuffuka ba. Ya aika da tarin ƙudajen da suka cinye su, da kwaɗin da suka wahalshe su. Ya ba da hatsinsu ga fāra, amfanin gonakinsu ga ɗango. Ya lalace inabinsu da ƙanƙara itatuwan al’ul nasu kuma da jaura. Ya miƙa shanunsu ga ƙanƙara, tumakinsu ga aradun tsawa. Ya saki musu fushinsa mai zafi, hasalarsa, zafin rai da kuma ɓacin ransa, ƙungiyar mala’iku masu hallakarwa. Ya shirya hanya wa fushinsa; bai tsare ransu daga mutuwa ba amma ya miƙa su ga annoba. Ya bugi kowane ɗan fari na Masar, mafari ƙarfin mazantakansu a tentunan Ham. Amma ya fitar da mutanensa kamar garke; ya bi da su kamar tumaki ta cikin hamada. Ya bi da su lafiya ƙalau, don kada su ji tsoro; amma teku ya cinye abokan gābansu. Ta haka ya kawo su iyakar ƙasa mai tsarki, zuwa ƙasar tudun da hannunsa na dama ya kame. Ya kori al’ummai a gabansu ya rarraba ƙasashensu gare su a matsayin gādo; ya zaunar da kabilan Isra’ila a gidajensu. Amma suka gwada Allah suka tayar wa Mafi Ɗaukaka; ba su kiyaye ƙa’idodinsa ba. Kamar kakanninsu suka zama marasa biyayya da marasa aminci, marar tabbas kamar tanƙwararren baka. Suka ba shi haushi da masujadansu na kan tudu; suka tayar da kishinsa da gumakansu. Sa’ad da Allah ya ji su, ya yi fushi ƙwarai; ya ƙi Isra’ila gaba ɗaya. Ya yashe tabanakul na Shilo, tentin da ya kafa a cikin mutane. Ya aika da akwatin alkawarin ƙarfinsa zuwa bauta, darajarsa zuwa cikin hannuwan abokin gāba. Ya ba da mutanensa ga takobi; ya yi fushi ƙwarai da gādonsa. Wuta ta cinye matasansu maza, ’yan matansu kuma ba su da waƙoƙin aure; aka karkashe firistocinsu, gwaurayensu kuwa ba su iya makoki ba. Sa’an nan Ubangiji ya farka sai ka ce daga barcinsa, kamar yadda mutum kan farka daga buguwar ruwan inabi. Ya kori abokan gābansa; ya sa suka sha madawwamiyar kunya. Sa’an nan ya ƙi tentunan Yusuf, bai zaɓi kabilar Efraim ba; amma ya zaɓi kabilar Yahuda, Dutsen Sihiyona, wanda ya ƙaunaci. Ya gina wurinsa mai tsarki kamar bisa, kamar duniyar da ya kafa har abada. Ya zaɓi Dawuda bawansa ya kuma ɗauke shi daga ɗakin tumaki; daga kiwon tumaki ya kawo shi don yă kuma zama makiyayin mutanensa Yaƙub, na Isra’ila gādonsa. Dawuda kuwa ya zama makiyayinsu da mutuncin zuciya; da hannuwa masu gwaninta ya bi da su. Ya Allah, al’ummai sun mamaye gādonka; sun ƙazantar da haikalinka mai tsarki, sun bar Urushalima kufai. Sun ba da gawawwakin bayinka kamar abinci ga tsuntsayen sararin sama, nama jikin tsarkakanka ga namun jejin duniya. Sun zubar da jini kamar ruwa ko’ina a Urushalima, kuma babu wani da zai binne matattu. Mun zama abin reni ga maƙwabta, abin ba’a da reni ga waɗanda suke kewaye da mu. Har yaushe, ya Ubangiji za ka yi ta fushi? Har abada ne? Har yaushe kishinka zai yi ta ƙuna kamar wuta? Ka zuba fushinka a kan al’umman da ba su yarda da kai ba, a kan mulkokin da ba sa kira bisa sunanka; gama sun cinye Yaƙub suka lalatar da ƙasar zamansa. Kada ka riƙe zunubai kakanni a kanmu; bari jinƙanka yă zo da sauri yă sadu da mu, gama mun fid da zuciya sarai. Ka taimake mu, ya Allah Mai Cetonmu, saboda ɗaukakar sunanka; ka cece mu ka kuma gafarta mana zunubanmu saboda sunanka. Don me al’ummai za su ce, “Ina Allahnsu yake?” A idanunmu, ka sanar wa al’ummai cewa kana ɗaukan fansar jinin bayinka da aka zubar. Bari nishe-nishen ’yan kurkuku su zo gabanka; ta wurin ƙarfin hannunka ka kiyaye waɗanda aka yanke wa hukuncin mutuwa. Ka sāka a cinyoyin maƙwabtanmu sau bakwai zage-zagen da suka yi ta yi maka, ya Ubangiji. Sa’an nan mu mutanenka, tumakin makiyayarka, za mu yabe ka har abada; daga tsara zuwa tsara za mu yi ta ba da labarin yabonka. Ka ji mu, ya Makiyayin Isra’ila, kai da ka bishe Yusuf kamar garke. Kai da kake zaune a kursiyi tsakanin kerubobi, ka haskaka a gaban Efraim, Benyamin da Manasse. Ka tā da ƙarfinka; ka zo ka cece mu. Ka mai da mu, ya Allah; ka sa fuskarka ta haskaka a kanmu, za mu kuwa cetu. Ya Ubangiji Allah Maɗaukaki, har yaushe fushinka zai yi ta ƙuna a kan addu’o’in mutanenka? Ka ciyar da su da burodin hawaye; ka sa suka sha hawaye ta cikakken kwaf. Ka mai da mu abin faɗa ga maƙwabtanmu, kuma abokan gābanmu suna mana ba’a. Ka mai da mu, ya Allah Maɗaukaki; ka sa fuskarka ta haskaka a kanmu za mu kuwa cetu. Ka fitar da inabi daga Masar; ka kori al’ummai ka kuma dasa shi. Ka gyara wuri saboda shi, ya kuwa yi saiwa ya cike ƙasa. Aka rufe duwatsu da inuwarsa, manya-manyan itatuwan al’ul da rassansa. Ya miƙe rassansa zuwa Teku tohonsa har zuwa Kogi. Me ya sa ka rurrushe bangayensa don duk masu wucewa su tsinke ’ya’yan inabinsa? Aladu daga kurmi suna ɓarnatar da shi halittun gonaki kuma suna cinsa. Ka komo wurinmu, ya Allah Maɗaukaki! Ka duba daga sama ka gani! Ka lura da wannan inabi, saiwar da hannun damarka ya dasa, ɗan da ka renar wa kanka. An yanke inabinka, an ƙone shi da wuta; a tsawatawarka mutanenka sun hallaka. Bari hannunka yă zauna a kan mutumin da yake hannun damarka, ɗan mutum da ka renar wa kanka. Ta haka ba za mu juye mu bar ka ba; ka rayar da mu, za mu kuwa kira bisa sunanka. Ka mai da mu, ya Ubangiji Allah Maɗaukaki; ka sa fuskarka ta haskaka a kanmu, za mu kuwa cetu. Ku rera don farin ciki ga Allah ƙarfinmu; ku yi sowa ga Allah na Yaƙub! Ku fara kaɗe-kaɗe, ku buga ganga, ku kaɗa garaya da molo masu daɗi. Ku busa ƙahon rago a Sabon Wata, da kuma sa’ad da wata ya kai tsakiya, a ranar Bikinmu; wannan ƙa’ida ce domin Isra’ila, farilla ta Allah na Yaƙub. Ya kafa shi a matsayin ƙa’ida domin Yusuf sa’ad da ya fito daga Masar. Muka ji yaren da ba mu fahimta ba. Ya ce, “Na kau da nauyi daga kafaɗunku; an ’yantar da hannuwansu daga kwando. Cikin damuwarku kun yi kira na kuwa kuɓutar da ku, na amsa muku daga girgijen tsawa; na gwada ku a ruwan Meriba. “Ku ji, ya mutanena, zan kuwa gargaɗe ku, in ba za ku saurare ni ba, ya Isra’ila! Kada ku kasance da baƙon allah a cikinku; ba za ku rusuna ga baƙon allah ba. Ni ne Ubangiji Allahnku wanda ya fitar da ku daga Masar. Ku buɗe bakinku zan kuwa cika shi. “Amma mutanena ba su saurare ni ba; Isra’ila bai miƙa kansa gare ni ba. Saboda haka na ba da su ga zukatansu da suka taurare don su bi dabararsu. “A ce mutanena za su saurare ni, a ce Isra’ila zai bi hanyoyina, da nan da nan sai in rinjayi abokan gābansu in kuma juye hannuna a kan maƙiyansu! Waɗanda suke ƙin Ubangiji za su fāɗi a gabansa da rawar jiki, hukuncinsu kuma zai dawwama har abada. Amma za a ciyar da ku da alkama mafi kyau; da zuma daga dutsen da zai ƙosar da ku.” Allah yana shugabanta cikin babban taro; yakan zartar da hukunci a cikin “alloli”. “Har yaushe za ku kāre marasa adalci ku kuma goyi bayan mugaye? Ku tsare mutuncin marasa ƙarfi da marayu; ku kāre hakkin matalauta da waɗanda ake danniya. Ku ceci marasa ƙarfi da masu bukata; ku kuɓutar da su daga hannun mugaye. “Ba su san kome ba, ba su fahimci kome ba. Suna yawo cikin duhu; an girgiza dukan tussan duniya. “Na ce, ‘Ku “alloli” ne; dukanku ’ya’yan Mafi Ɗaukaka’ ne. Amma za ku mutu kamar mutum kurum; za ku fāɗi kamar duk wani mai mulki.” Ka tashi, ya Allah, ka shari’anta duniya, gama dukan al’ummai gādonka ne. Ya Allah, kada ka yi shiru; kada ka tsaya cik, ya Allah, kada ka daina motsi. Dubi yadda abokan gābanka suke fariya, dubi yadda maƙiyanka suke ɗaga kansu. Da wayo suna ƙulle-ƙulle a kan mutanenka; suna shirya maƙarƙashiya a kan waɗanda kake so. Suna cewa, “Ku zo, bari mu hallaka su ɗungum a matsayin al’umma, don kada a ƙara tuna da sunan Isra’ila.” Da zuciya ɗaya suka yi ƙulle-ƙulle tare; suka haɗa kai gāba da kai, tentunan Edom da na mutanen Ishmayel, na Mowab da kuma na Hagirawa, Gebal, Ammon da Amalek, Filistiya, tare da mutanen Taya. Har Assuriya ma ta haɗa kai da su don ta ba da ƙarfi ga zuriyar Lot. Ka yi musu abin da ka yi wa Midiyan, yadda ka yi wa Sisera da Yabin a kogin Kishon, waɗanda suka hallaka a En Dor suka zama kamar juji a ƙasa. Ka mai da manyansu kamar Oreb da Zeyib, dukan sarakunansu kamar Zeba da Zalmunna, waɗanda suka ce, “Bari mu mallaki wuraren kiwon Allah.” Ka mai da su kamar ɗan tsiron da kan karye, iska ta yi ta turawa, ya Allahna, kamar yayin da iska take hurawa, kamar yadda wuta ke cin kurmi ko harshen wutar da take ci a kan duwatsu, haka za ka kore su da iska mai ƙarfi ka kuma firgita su da guguwarka. Ka rushe fuskokinsu da kunya don mutane su nemi sunanka, ya Ubangiji. Bari su kasance cikin kunya da taƙaici; bari su hallaka cikin wulaƙanci. Bari su san cewa kai, wanda sunansa ne Ubangiji, cewa kai kaɗai ne Mafi Ɗaukaka a bisa dukan duniya. Ina misalin kyan wurin zamanka, Ya Ubangiji Maɗaukaki! Raina yana marmari, har yana suma, don filayen gidan Ubangiji; zuciyata da namana na tā da murya domin Allah mai rai. Har tsada ma ta sami gida, tsatsewa kuma ta yi wa kanta sheƙa, inda za tă ƙyanƙyashe ’ya’yanta, wuri kusa da bagadenka, Ya Ubangiji Maɗaukaki, Sarkina da kuma Allahna. Masu albarka ne waɗanda suke zama a gidanka; kullum suna ta yabonka. Masu albarka ne waɗanda ƙarfinsu yana daga gare ka, waɗanda suka kafa zukatansu a yin tafiya zuwa wuri mai tsarki ne. Yayinda suke wuce ta Kwarin Baka, sukan mai da shi wurin maɓulɓulai; ruwan sama na farko kuma kan rufe shi da tafkuna. Suna ta ƙara ƙarfi, har sai kowanne ya bayyana a gaban Allah a Sihiyona. Ka ji addu’ata, ya Ubangiji Allah Maɗaukaki; ka saurare ni, ya Allah na Yaƙub. Ka dubi garkuwarmu, ya Allah; ka duba da alheri a kan shafaffenka. Rana guda a filayen gidan sun fi dubu a wani wuri dabam; zan gwammaci in zama mai tsaron ƙofa a gidan Allahna da in zauna a tentunan mugaye. Gama Ubangiji Allah rana ne da kuma garkuwa; Ubangiji yakan yi alheri da kuma daraja; ba ya hana kowane abu mai kyau wa waɗanda suke aikata abin da yake daidai. Ya Ubangiji Maɗaukaki, mai albarka ne mutumin da ya dogara gare ka. Ka nuna wa ƙasarka alheri, ya Ubangiji; ka mai da nasarorin Yaƙub. Ka gafarta laifin mutanenka ka kuma shafe dukan zunubansu. Ka kau da dukan fushinka ka kuma juye daga hasalar fushinka. Ka sāke mai da mu, ya Allah Mai Cetonmu, ka kau da rashin jin daɗinka daga gare mu. Za ka ci gaba da fushi da mu har abada ne? Za ka ja fushinka cikin dukan tsararraki? Ba za ka sāke raya mu ba, don mutanenka su yi farin ciki a cikinka? Ka nuna mana ƙaunarka marar ƙarewa, ya Ubangiji, ka kuma ba mu cetonka. Zan saurari abin da Allah Ubangiji zai faɗa; ya yi alkawarin salama ga mutanensa, tsarkakansa, amma kada su koma ga wauta. Tabbatacce cetonsa yana kusa da waɗanda suke tsoronsa, don ɗaukakarsa ta zauna a cikin ƙasarmu. Ƙauna da aminci za su sadu; adalci da salama za su yi wa juna sumba. Aminci zai ɓulɓulo daga ƙasa, adalci kuma yă duba daga sama. Ubangiji tabbatacce zai bayar da abin da yake da kyau, ƙasarmu kuwa za tă ba da amfaninta. Adalci na tafiya a gabansa yana shirya hanya domin ƙafafunsa. Ka ji, ya Ubangiji, ka kuma amsa mini, gama ni matalauci ne mai bukata kuma. Ka tsare raina, gama na ba da kaina gare ka. Kai ne Allahna; ka ceci bawanka wanda ya dogara gare ka. Ka yi mini jinƙai, ya Ubangiji, gama na yi kira gare ka dukan yini. Ka ba bawanka farin ciki gama gare ka, ya Ubangiji, na miƙa raina. Kai mai gafartawa da kuma mai alheri ne, ya Ubangiji, cike da ƙauna ga dukan waɗanda suke kira gare ka. Ka ji addu’ata, ya Ubangiji; ka saurari kukata na neman jinƙai. A lokacin wahala zan yi kira gare ka, gama za ka amsa mini. A cikin alloli babu kamar ka, ya Ubangiji; babu ayyukan da za a kwatanta da naka. Dukan al’umman da ka yi za su zo su yi sujada a gabanka, ya Ubangiji; za su kawo ɗaukaka ga sunanka. Gama kai mai girma ne kana kuma aikata ayyuka masu banmamaki; kai kaɗai ne Allah. Ka koya mini hanyarka, ya Ubangiji, zan kuwa yi tafiya cikin gaskiyarka; ka ba ni zuciya wadda ba tă rabu ba, don in ji tsoron sunanka. Zan yabe ka, ya Ubangiji Allahna, da dukan zuciyata; zan ɗaukaka sunanka har abada. Gama ƙaunarka da girma take gare ni; kai ka cece ni daga zurfafa, daga mazaunin matattu. Masu girman kai suna kai mini hari, ya Allah; ƙungiyar marasa imani suna neman raina, mutanen da ba su kula da kai ba. Amma kai, ya Ubangiji, kai Allah mai tausayi ne da kuma mai alheri, mai jinkirin fushi, mai yawan ƙauna da aminci. Ka juyo gare ni ka yi mini jinƙai; ka ba wa bawanka ƙarfi; ka ceci ni gama na bauta maka yadda mahaifiyata ta yi. Ka ba ni alamar alherinka, don abokan gābana su gani su kuma sha kunya, gama kai, ya Ubangiji, ka taimake ni ka kuma ta’azantar da ni. Ya kafa harsashinsa a kan dutse mai tsarki. Ubangiji yana ƙaunar ƙofofin Sihiyona fiye da dukan wuraren zaman Yaƙub. Ana faɗin abubuwa masu ɗaukaka game da ke Ya birnin Allah, “Zan lissafta Rahab a cikin waɗanda suka san ni, Filistiya ita ma, da Taya, tare da Kush, zan kuma ce, ‘An haifi wannan a Sihiyona.’ ” Tabbatacce, game da Sihiyona za a ce, “Wannan da wancan an haifa a cikinta, Mafi Ɗaukaka kansa zai kafa ta.” Ubangiji zai rubuta a littafin sunayen mutanensa, “An haifi wannan a Sihiyona.” Yayinda suke kaɗe-kaɗe za su rera, “Dukan maɓulɓulaina suna cikinki.” Ya Ubangiji, Allah wanda ya cece ni, dare da rana ina kuka a gabanka. Bari addu’ata ta zo a gabanka; ka kasa kunne ga kukata. Gama raina yana cike da wahala rayuwata tana gab da kabari. An lissafta ni cikin waɗanda suka gangara zuwa cikin rami; ni kamar mutumin da ba shi da ƙarfi ne. An ware ni tare da matattu, kamar waɗanda aka kashe da suke kwance a kabari, waɗanda ba ka ƙara tunawa, waɗanda aka yanke daga taimakonka. Ka sa ni a ramin da yake can ƙasa cikin zurfafa mafi duhu. Hasalarka tana da nauyi a kaina; ka turmushe ni da dukan raƙumanka. Ka ɗauke abokaina na kurkusa daga gare ni ka sa na zama abin ƙyama a gare su. An kange ni, ba yadda zan kuɓuta idanuna ba sa gani sosai saboda baƙin ciki. Ina kira gare ka, ya Ubangiji, kowace rana; na tā da hannuwana zuwa gare ka. Kakan nuna wa matattu ayyukanka na banmamaki ne? Waɗanda suka mutu sukan tashi su yabe ka ne? Ana furta ƙaunar a cikin kabari ne, ana zancen amincinka a cikin Hallaka ne? An san ayyukanka masu banmamaki a wurin duhu ne, ko ayyukan adalcinka a lahira? Amma ina kuka gare ka neman taimako, ya Ubangiji; da safe addu’ata kan zo gabanka. Don me, ya Ubangiji, ka ƙi ni ka kuma ɓoye fuskarka daga gare ni? Tun ina ƙarami na sha wahala na kuma yi kusa in mutu; na sha wahalar razanarka kuma na kuma fid da zuciya. Hasalarka ta sha kaina; razanarka ta hallaka ni. Dukan yini sun kewaye ni kamar rigyawa; sun mamaye ni ɗungum. Ka ɗauke abokaina da ƙaunatattuna daga gare ni; duhu ne abokina na kurkusa. Zan rera game da ƙauna mai girma ta Ubangiji har abada; da bakina zan sanar da amincinka a dukan zamanai. Zan furta cewa ƙaunarka tana nan daram har abada, cewa ka kafa amincinka a sama kanta. Ka ce, “Na yi alkawari da zaɓaɓɓena, na rantse wa Dawuda bawana, cewa ‘Zan kafa zuriyarka har abada in kuma sa kursiyinka yă tsaya daram dukan zamanai.’ ” Sammai na yabon abubuwan banmamakinka, ya Ubangiji, amincinka shi ma, a cikin taron tsarkakanka. Gama wane ne a sarari za a iya kwatanta da Ubangiji? Wane ne yake kamar Ubangiji a cikin talikan samaniya? Cikin taron tsarkaka Allah ne aka fi tsoro; shi ne mafi bantsoro fiye da dukan waɗanda suka kewaye shi. Ya Ubangiji Allah Maɗaukaki, wane ne kamar ka? Kai mai iko ne, ya Ubangiji, kuma amincinka ya kewaye ka. Kana mulkin teku mai tumbatsa; sa’ad da raƙuma sun tashi, kakan kwantar da su. Ka ragargaza Rahab kamar waɗanda aka kashe; da hannunka mai ƙarfi ka watsar da abokan gābanka. Sammai naka ne, haka kuma duniya; ka kafa duniya da dukan abin da yake cikinta. Ka halicce arewa da kudu; Tabor da Hermon suna rera don farin ciki ga sunanka. Hannunka mai iko ne; hannunka yana da ƙarfi, hannunka na dama ya sami ɗaukaka. Adalci da gaskiya su ne tushen kursiyinka; ƙauna da aminci suna tafiya a gabanka. Masu albarka ne waɗanda suka koyi yin maka kirari waɗanda suke tafiya cikin hasken da yake gabanka, Ubangiji. Suna farin ciki a cikin sunanka dukan yini; suna samun ɗaukaka cikin adalcinka. Gama kai ne ɗaukakarsu da ƙarfinsu, kuma ta wurin alherinka ka ɗaukaka ƙahonka. Tabbatacce, garkuwarmu ta Ubangiji ce, ta sarkinmu ce, da kuma ta Mai Tsarki na Isra’ila ce. Ka taɓa yin magana cikin wahayi, ga mutanenka masu aminci ka ce, “Na ba wa jarumi ƙarfi; na ɗaukaka saurayi daga cikin mutane. Na sami Dawuda bawana; da mai na mai tsarki na shafe shi. Hannuna zai kasance tare da shi; tabbatacce hannuna zai ƙarfafa shi. Babu abokin gāban da zai sa yă biya haraji; babu mugun mutumin da zai danne shi. Zan murƙushe maƙiyansa a gabansa in kashe dukan abokan gābansa. Amintacciya ƙaunata za tă kasance tare da shi, kuma ta wurin sunana za a ɗaukaka ƙahonsa. Zan sa hannunsa a bisa teku, hannunsa na dama a bisa koguna. Zai yi kira gare ni yă ce, ‘Kai ne Mahaifina, Allahna, Dutse mai cetona.’ Zan kuma naɗa shi ɗan farina, mafi ɗaukaka cikin sarakunan duniya. Zan ci gaba da ƙaunarsa har abada, alkawarina da shi ba zai taɓa fasa ba. Zan kafa zuriyarsa har abada, kursiyinsa muddin sammai suna nan. “In ’ya’yansa maza suka yashe dokata ba su kuwa bi ƙa’idodina ba, in suka take ƙa’idodina suka kuma kāsa kiyaye umarnaina, zan hukunta zunubinsu da sanda, laifinsu da bulala; amma ba zan ɗauke ƙaunata daga gare shi ba, ba kuwa zan taɓa rasa cika amincina ba. Ba zan take alkawarina ba ko in canja abin da leɓunana suka ambata. Sau ɗaya ba ƙari, na rantse da tsarkina, ba kuwa zan yi ƙarya wa Dawuda ba, cewa zuriyarsa za tă ci gaba har abada kuma kursiyinsa zai dawwama a gabana kamar rana; zai kahu har abada kamar wata, amintacciyar shaida a cikin sarari.” Amma ka ƙi, ka yi ƙyama ka kuma yi fushi sosai da shafaffenka. Ka soke alkawarin da ka yi da bawanka ka kuma ƙazantar da rawaninsa a ƙura. Ka rurrushe dukan katangansa ka sa kagaransa suka zama kufai. Dukan waɗanda suka wuce sun washe shi; ya zama abin dariya wajen maƙwabtansa. Ka ɗaukaka hannun dama na maƙiyansa; ka sa dukan abokan gābansa suna farin ciki. Ka juye bakin takobinsa ba ka kuma taimake shi a cikin yaƙi ba. Ka kawo ƙarshen darajarsa ka kuma jefar da kursiyinsa ƙasa. Ka rage kwanakin ƙuruciyarsa; ka rufe shi da mayafin kunya. Har yaushe, ya Ubangiji za ka ɓoye? Za ka ɓoye har abada ne? Har yaushe fushinka zai yi ta ci kamar wuta? Ka tuna yadda raina mai wucewa ne. Gama ka halicce dukan mutane ba amfani! Wanda mutum ne zai rayu da ba zai ga mutuwa ba, ko yă cece kansa daga ikon kabari? Ya Ubangiji, ina ƙaunar mai girma ta dā, wadda cikin amincinka ka rantse wa Dawuda? Ka tuna, Ubangiji, yadda aka yi wa bawanka ba’a, yadda na jimre a zuciyata da zage-zagen dukan al’ummai, zage-zagen da abokan gābanka suka yi mini, ya Ubangiji, da suka yi wa kowane matakin da shafaffenka ya ɗauka. Yabo ya tabbata ga Ubangiji har abada! Amin kuma Amin. Ubangiji kai ne mazauninmu cikin dukan zamanai. Kafin a haifi duwatsu ko a fid da ƙasa da duniya, daga madawwami zuwa madawwami kai Allah ne. Ka komar da mutane zuwa ƙura, kana cewa, “Ku koma ƙura, ya ku ’ya’yan mutane.” Gama shekaru dubu a gabanka kamar kwana ɗaya ne da ya wuce, ko sa’a guda na dare. Ka share mutane cikin barcin mutuwa; suna kama da sabuwa ciyawar safiya, ko da yake da safe takan yi sabuwar huda da yamma sai ta bushe ta kuma yanƙwane. An cinye mu ta wurin fushinka mun kuma razana ta wurin hasalarka. Ka ajiye laifinmu a gabanka, asirin zunubanmu a hasken kasancewarka. Dukan kwanakinmu sun wuce ƙarƙashin fushinka; mun gama shekarunmu da nishi. Tsawon kwanakinmu shekaru saba’in ne, ko tamanin, in muna da ƙarfi; duk da haka tsawonsu wahaloli ne kawai da ɓacin rai, gama da sauri suke wucewa, ta mu kuma ta ƙare. Wa ya san ƙarfin fushinka? Gama hasalarka tana da girma kamar tsoron da ya dace da kai. Ka koya mana yawan kwanakinmu daidai, don mu sami zuciyar hikima. Ka ji mu, ya Ubangiji! Har yaushe zai ci gaba? Ka ji tausayin bayinka. Ka ƙosar da mu da safe da ƙaunarka marar ƙarewa, don mu rera don yabo, mu kuma yi murna dukan kwanakinmu. Faranta mana zuciya kamar yawan kwanakin da muka sha azaba, kamar yawan shekarun da muka ga wahala. Bari a nuna ayyukanka ga bayinka, darajarka ga ’ya’yansu. Bari alherin shugabanmu Allah yă kasance a kanmu; ka albarkaci mana aikin hannuwanmu, I, ka albarkaci aikin hannuwanmu. Shi wanda yake zama a wurin Mafi Ɗaukaka zai huta a cikin inuwar Maɗaukaki. Zan ce game da Ubangiji, “Shi ne mafakata da kagarata, Allahna, wanda nake dogara.” Tabbatacce zai cece ka daga tarkon mai farauta da kuma daga cututtuka masu kisa. Zai rufe ka da fikafikansa, a ƙarƙashin fikafikansa kuwa za ka sami mafaka; amincinsa zai zama maka garkuwa da katanga. Ba za ka ji tsoron razanar dare, ko kibiyoyi da suke firiya da rana ba, ko bala’in da yake aukowa cikin duhu, ko annobar da take hallakarwa da tsakar rana. Dubu za su iya fāɗuwa a gefenka, dubu goma a hannun damanka, amma ba abin da zai zo kusa da kai. Za ka dai gan da idanunka yadda ake hukunta mugaye. In ka mai da Mafi Ɗaukaka wurin zamanka, har ma Ubangiji wanda yake mafakata, to, babu wani mugun abin da zai same ka, ba masifar da za tă zo kusa da tentinka. Gama zai umarci mala’ikunsa game da kai don su tsare ka a dukan hanyoyinka; za su tallafe ka da hannuwansu, don kada ka buga ƙafarka a kan dutse. Za ka taka zaki da gamsheƙa; za ka tattake babban zaki da maciji. Ubangiji ya ce, “Domin ya ƙaunace ni, zan kuɓutar da shi; zan kiyaye shi, gama ya yarda da sunana. Zai kira bisa sunana, zan kuma amsa masa; zan kasance tare da shi a lokacin wahala, zan kuɓutar da shi in kuma girmama shi. Da tsawon rai zan ƙosar da shi in kuma nuna masa cetona.” Yana da kyau a yabi Ubangiji a kuma yi kiɗi ga sunanka, ya Mafi Ɗaukaka, don a yi shelar ƙaunarka da safe amincinka kuma da dare, da kiɗin molo mai tsirkiya goma da kuma ƙarar garaya. Gama ka sa na yi murna ta wurin ayyukanka, ya Ubangiji; na rera don farin ciki saboda ayyukan hannuwanka. Ina misalin ayyukanka, ya Ubangiji, tunaninka da zurfi suke ƙwarai! Mutum marar azanci ba zai sani ba, wawa ba zai gane ba, cewa ko da yake mugaye suna girma kamar ciyawa kuma dukan masu aikata mugunta suna haɓaka, za a hallaka su har abada. Amma kai, ya Ubangiji, za a ɗaukaka har abada. Gama tabbatacce abokan gābanka, ya Ubangiji, tabbatacce abokan gābanka za su hallaka; za a watsar da dukan masu aikata mugunta. Ka ɗaukaka ƙahona kamar na ɓauna; an zubo mai masu kyau a kaina. Idanuna sun ga fāɗuwar maƙiyana; kunnuwana sun ji kukan mugayen maƙiyana. Adalai za su haɓaka kamar itacen dabino, za su yi girma kama al’ul na Lebanon; da aka daddasa a gidan Ubangiji, za su haɓaka a filayen gidan Allahnmu. Za su ci gaba da ba da ’ya’ya a tsufansu, za su kasance ɗanye kuma kore shar, suna shela cewa, “ Ubangiji adali ne; shi ne Dutsena, kuma babu mugunta a cikinsa.” Ubangiji yana mulki, yana sanye da ɗaukaka; Ubangiji yana sanye da ɗaukaka yana kuma sanye da ƙarfi. An kafa duniya daram; ba za a iya matsar da ita ba. An kafa kursiyin tun da daɗewa; kana nan tun fil azal. Tekuna sun taso, ya Ubangiji, tekuna sun ta da muryarsu; tekuna sun tā da ta raƙumansu masu tumbatsa. Mafi ƙarfi fiye da tsawan manyan ruwaye, mafi ƙarfi fiye da ikon raƙuman ruwan teku, Ubangiji mai zama a bisa mai girma ne. Ƙa’idodinka suna nan daram; tsarki ya yi wa gidanka ado har kwanaki marar ƙarewa, ya Ubangiji. Ya Ubangiji, Allahn da yake ramuwa, Ya Allah wanda yake ramuwa, ka haskaka. Ka tashi, ya Alƙalin duniya; ka sāka wa masu girman kai abin da ya dace da su. Har yaushe mugaye, ya Ubangiji har yaushe mugaye za su yi ta murna? Suna ta yin maganganun fariya; dukan masu aikata mugunta sun cika da fariya. Suna murƙushe mutanenka, ya Ubangiji; suna danne gādonka. Suna kashe gwauraye da kuma baƙi; suna kisan marayu. Suna ce, “ Ubangiji ba ya gani; Allah na Yaƙub bai kula ba.” Ku mai da hankali, ku marasa azanci a cikin mutane; ku wawaye, yaushe za ku zama masu hikima? Shi da ya sa kunne ba don a ji ba ne? Shi da ya yi ido ba don yă gani ba ne? Shi da yake yi wa al’ummai horo ba ya hukunci ne? Shi da yake koya wa mutum ba shi da sani ne? Ubangiji ya san tunanin mutum; ya san cewa tunaninsu banza ne. Mai albarka ne mutumin da ka yi masa horo, ya Ubangiji, mutumin da ka koyar daga dokarka; kana ba shi sauƙi a lokacin wahala, sai har an haƙa rami wa mugaye. Gama Ubangiji ba zai ƙi mutanensa ba; ba zai taɓa yashe gādonsa ba. Za a sāke kafa hukunci a kan adalci, kuma dukan masu adalci a zuciya za su bi shi. Wane ne zai yi gāba da mugaye domina? Wane ne zai ɗauki matsayi ya yi gāba da masu aikata mugunta domina? Da ba don Ubangiji ya yi mini taimako ba, da tuni na zauna shiru a wurin mutuwa. Sa’ad da na ce, “Ƙafata na santsi,” ƙaunarka, ya Ubangiji, ta riƙe ni. Sa’ad da alhini ya yi yawa a cikina, ta’aziyyarka ta kawo farin ciki wa raina. Zai yiwu kursiyin da ya cika da lalaci yă haɗa kai da kai, wanda yake kawo azaba ta wurin abin da ya zartar? Sun yi ƙungiya tare a kan mai adalci suka yanke wa marar laifi hukuncin mutuwa. Amma Ubangiji ya zama kagarata, Allahna kuma dutsen da nake samun mafaka. Zai sāka musu saboda zunubansu yă kuma hallaka su saboda muguntarsu; Ubangiji Allahnmu zai hallaka su. Ku zo, bari mu rera don farin ciki ga Ubangiji; bari mu yi sowa da ƙarfi ga Dutsen cetonmu. Bari mu zo gabansa da godiya mu rera gare shi da kiɗi da waƙa. Gama Ubangiji Allah mai girma ne, babban Sarki a bisa dukan alloli. A hannunsa ne zurfafan duniya suke, ƙwanƙolin dutse kuma nasa ne. Teku nasa ne, gama shi ne ya yi shi, da hannuwansa kuma ya yi busasshiyar ƙasa. Ku zo, bari mu rusuna mu yi sujada, bari mu durƙusa a gaban Ubangiji Mahaliccinmu; gama shi ne Allahnmu mu mutanen makiyayansa ne, garke kuwa a ƙarƙashin kulawarsa. Yau, in kuka ji muryarsa, “Kada ku taurare zukatanku kamar yadda kuka yi a Meriba, kamar yadda kuka yi a wancan rana a Massa a hamada, inda kakanninku suka gwada suka kuma jarraba ni, ko da yake sun ga abin da na yi. Shekara arba’in na yi fushi da wancan tsara; na ce, ‘Su mutane ne waɗanda zukatansu suka kauce, kuma ba su san hanyoyina ba.’ Saboda haka na yi rantsuwa cikin fushina, ‘Ba za su taɓa shiga hutuna ba.’ ” Ku rera sabuwar waƙa ga Ubangiji; ku rera ga Ubangiji, ku duniya duka. Ku rera ga Ubangiji, ku yabe sunansa; ku yi shelar cetonsa kowace rana. Ku furta ɗaukakarsa a cikin al’ummai, manyan ayyukansa a cikin dukan mutane. Gama da girma Ubangiji yake, ya kuma cancanci yabo; tilas a ji tsoronsa fiye da dukan alloli. Gama dukan allolin al’ummai gumaka ne, amma Ubangiji ne ya yi sammai. Daraja da ɗaukaka suna a gabansa; ƙarfi da ɗaukaka suna a cikin tsarkakar wurinsa. Ku ba wa Ubangiji, ya iyalan al’ummai ku ba wa Ubangiji ɗaukaka da kuma ƙarfi. Ku ba wa Ubangiji ɗaukakar da ta dace da sunansa; ku kawo sadaka ku kuma zo cikin filayen gidansa. Ku bauta wa Ubangiji da darajar tsarkinsa; ku yi rawar jiki a gabansa, dukan duniya. Ku faɗa cikin al’ummai, “ Ubangiji yana mulki.” Duniya ta kahu daram, ba za a iya matsar da ita ba; zai yi wa mutane hukunci da gaskiya. Bari sammai su yi farin ciki, bari duniya tă yi murna; bari teku tă yi ruri, da kuma dukan abin da yake cikinsa; bari gonaki su yi tsalle da murna, da kuma kome da yake cikinsu. Ta haka dukan itatuwan kurmi za su rera don farin ciki; za su rera a gaban Ubangiji, gama yana zuwa, yana zuwa don yă hukunta duniya. Zai hukunta duniya cikin adalci mutane kuma cikin amincinsa. Ubangiji yana mulki, bari duniya tă yi murna; bari tsibirai masu nesa su yi farin ciki. Gizagizai da baƙin duhu sun kewaye shi; adalci da gaskiya su ne tushen kursiyinsa. Wuta tana tafiya a gabansa tana kuma cinye maƙiyansa a kowane gefe. Walƙiyarsa ta haskaka duniya; duniya ta gani ta kuma yi rawar jiki. Duwatsu sun narke kamar kakin zuma a gaban Ubangiji, a gaban Ubangijin dukan duniya. Sammai sun yi shelar adalcinsa, dukan mutane kuma suka ga ɗaukakarsa. Dukan waɗanda suke bauta wa siffofi sun sha kunya, waɗanda suke fariya da gumaka, ku yi masa sujada, dukanku alloli! Sihiyona ta ji ta kuma yi farin ciki kuma dukan ƙauyukan Yahuda suna murna saboda hukunce-hukuncenka, ya Ubangiji. Gama kai, ya Ubangiji, kai ne Mafi Ɗaukaka a bisa dukan duniya; ana darjanta ka fiye da dukan alloli. Bari masu ƙaunar Ubangiji su ƙi mugunta, gama yana tsaron rayukan amintattunsa yana kuma kuɓutar da su daga hannun mugaye. An haskaka haske a kan masu adalci da kuma farin ciki a kan masu gaskiya a zuciya. Ku yi farin ciki a cikin Ubangiji, ku da kuke masu adalci, ku kuma yabi sunansa mai tsarki. Ku rera sabuwar waƙa ga Ubangiji, gama ya yi abubuwa masu banmamaki; hannunsa na dama da hannunsa mai tsarki sun yi masa aikin ceto. Ubangiji ya sanar da cetonsa ya kuma bayyana adalcinsa ga al’ummai. Ya tuna da ƙaunarsa da kuma amincinsa ga gidan Isra’ila; dukan iyakar duniya sun ga ceton Allahnmu. Ku yi sowa don farin ciki ga Ubangiji, dukan duniya, ku ɓarke da waƙa ta murna tare da kiɗi; ku yi kiɗi ga Ubangiji da garaya, da garaya da ƙarar rerawa, tare da bushe-bushe da karar ƙahon rago, ku yi sowa don farin ciki a gaban Ubangiji, Sarki. Bari teku su yi ruri, da kuma kome da yake cikinsa, duniya da kuma kome da yake cikinta. Bari koguna su tafa hannuwansu, bari duwatsu su rera tare don farin ciki; bari su rera a gaban Ubangiji, gama yana zuwa domin yă hukunta duniya. Zai hukunta duniya da adalci mutane kuma cikin gaskiya. Ubangiji yana mulki, bari al’ummai su yi rawan jiki; yana zaune a kursiyi tsakanin kerubobi, bari duniya ta girgiza. Ubangiji mai girma yana a Sihiyona; an ɗaukaka shi a bisa dukan al’ummai. Bari mu yabi girmanka da sunanka mai banrazana, shi mai tsarki ne. Sarki mai iko ne, yana ƙaunar adalci ka kafa gaskiya; a cikin Yaƙub ka yi abin da yake mai adalci da kuma daidai. Ku ɗaukaka Ubangiji Allahnmu ku kuma yi masa sujada a wurin sa ƙafafunsa; shi mai tsarki ne. Musa da Haruna suna cikin firistocinsa, Sama’ila yana cikin waɗanda suka kira bisa sunansa; sun kira ga Ubangiji ya kuwa amsa musu. Ya yi magana da su daga ginshiƙin girgije; ya kiyaye farillansa da ƙa’idodin da ya ba su. Ya Ubangiji Allahnmu, ka amsa musu; ka kasance wa Isra’ila Allah mai gafartawa, ko da yake ka hukunta ayyukansu marasa kyau. Ku ɗaukaka Ubangiji Allahnmu ku kuma yi sujada a dutsensa mai tsarki, gama Ubangiji Allahnmu mai tsarki ne. Ku yi sowa don farin ciki ga Ubangiji, dukan duniya. Yi wa Ubangiji sujada da murna; ku zo gabansa da waƙoƙin farin ciki. Ku san cewa Ubangiji shi ne Allah. Shi ne ya yi mu, mu kuwa nasa ne; mu mutanensa ne, tumakin makiyayarsa. Ku shiga ƙofofinsa da godiya filayen gidansa kuma da yabo; ku gode masa ku kuma yabi sunansa. Gama Ubangiji yana da kyau kuma ƙaunarsa madawwamiya ce har abada; amincinsa na cin gaba a dukan zamanai. Zan rera wa ƙauna da adalcinka; gare ka, ya Ubangiji, zan rera yabo. Zan yi hankali ga yin rayuwa marar zargi, yaushe za ka zo gare ni? Zan bi da sha’anin gidana da zuciya marar abin zargi Ba zan kafa a gaban idanuna 1 wani abu marar kyau ba. Na ƙi jinin ayyukan mutane marasa aminci; ba za su manne mini ba. Mutane masu mugun zuciya za su nesa da ni; ba abin da zai haɗa ni da mugunta. Duk wanda ya yi ɓatanci wa maƙwabcinsa a ɓoye shi za a kashe; duk mai renin wayo da mai girman kai, ba zan jure masa ba. Idanuna za su kasance a kan amintattu a cikin ƙasar, don su zauna tare da ni; tafiyarsa ba ta da zargi zai yi mini hidima. Babu mai ruɗun da zai zauna a gidana; babu mai ƙaryan da zai tsaya a gabana. Kowace safiya zan rufe bakunan dukan mugaye a ƙasar; zan yanke kowane mai aikata mugunta daga birnin Ubangiji. Ka ji addu’ata, ya Ubangiji; bari kukata ta neman taimako ta zo gare ka. Kada ka ɓoye fuskarka daga gare ni sa’ad da nake cikin damuwa. Ka juye kunnenka gare ni; sa’ad da na yi kira, ka amsa mini da sauri. Gama kwanakina sun ɓace kamar hayaƙi; ƙasusuwana suna ƙuna kamar jan wuta. Zuciyata ta kamu da ciwo ta kuma bushe kamar ciyawa; na manta in ci abinci. Saboda nishina mai ƙarfi na rame na bar ƙasusuwa kawai. Ni kamar mujiyar jeji ne, kamar mujiya a kufai. Na kwanta a faɗake; na zama kamar tsuntsun da yake shi kaɗai a kan rufin ɗaki. Dukan yini abokan gābana suna tsokanata; waɗanda suke mini ba’a suna amfani da sunana yă zama abin la’ana. Gama ina cin toka a matsayin abincina ina kuma gauraye abin sha nawa da hawaye saboda fushinka mai girma, gama ka ɗaga ni sama ka yar a gefe. Kwanakina suna kamar inuwar yamma; na bushe kamar ciyawa. Amma kai, ya Ubangiji, kana zaune a kursiyinka har abada; sunan da ka yi zai dawwama a dukan zamanai. Za ka tashi ka kuma ji tausayin Sihiyona, gama lokaci ne na nuna alheri gare ta; ƙayyadadden lokacin ya zo. Gama duwatsunta suna da daraja ga bayinka; ƙurarta kawai kan sa su ji tausayi. Al’ummai za su ji tsoron sunan Ubangiji, dukan sarakunan duniya za su girmama ɗaukakarka. Gama Ubangiji zai sāke gina Sihiyona ya kuma bayyana a ɗaukakarsa. Zai amsa addu’ar marasa ƙarfi; ba zai ƙyale roƙonsu ba. Bari a rubuta wannan don tsara mai zuwa, cewa mutanen da ba a riga an halitta ba za su yabi Ubangiji, “ Ubangiji ya duba ƙasa daga wurinsa mai tsarki a bisa, daga sama ya hangi duniya, don yă ji nishe-nishen ’yan kurkuku yă kuma saki waɗanda aka yanke musu hukuncin mutuwa.” Saboda haka za a furta sunan Ubangiji a Sihiyona yabonsa kuma a Urushalima sa’ad da mutane da mulkoki suka tattaru don su yi wa Ubangiji sujada. Cikin rayuwata, ya karye ƙarfina; ya gajartar da kwanakina. Sai na ce, “Kada ka ɗauke ni a tsakiyar kwanakina, ya Allah; shekarunka suna bi cikin dukan zamanai. A farkon fari ka kafa tushen duniya, sammai kuma aikin hannuwanka ne. Za su hallaka, amma za ka ci gaba; duk za su tsufe kamar riga. Kamar riga za ka canja su za a kuwa zubar da su. Amma kana nan yadda kake, kuma shekarunka ba za su taɓa ƙarewa ba. ’Ya’yan bayinka za su zauna a gabanka; zuriyarsu za su kahu a gabanka.” Yabi Ubangiji, ya raina; dukan abin da yake cikin cikina, yabi sunansa mai tsarki. Yabi Ubangiji, ya raina, kada kuma ka manta dukan alheransa, wanda yake gafarta dukan zunubai yake kuma warkar da dukan cututtuka, wanda ya fanshi ranka daga rami ya naɗa maka rawani da ƙauna da kuma tausayi, Wanda ya ƙosar da kai da abubuwa masu kyau domin a sabunta ƙuruciyarka kamar na gaggafa. Ubangiji yana aikata adalci da kuma gaskiya ga duk waɗanda aka danne. Ya sanar da hanyoyinsa wa Musa, ayyukansa ga mutanen Isra’ila. Ubangiji mai tausayi ne da kuma alheri, mai jinkirin fushi, cike da ƙauna. Ba zai yi ta zargi ba ba kuwa zai yi ta jin fushi har abada ba; ba ya yin da mu gwargwadon zunubanmu ko yă sāka mana bisa ga laifofinmu. Gama kamar yadda sammai suke can bisa duniya, haka girmar ƙaunarsa yake wa masu tsoronsa; kamar yadda gabas yake daga yamma, haka ya cire laifofinmu daga gare mu. Kamar yadda mahaifi yake jin tausayin ’ya’yansa, haka Ubangiji yake jin tausayin waɗanda suke tsoronsa; gama ya san yadda aka yi mu, ya tuna cewa mu ƙura ne. Game da mutum dai, kwanakinsa suna kamar ciyawa da suke haɓaka kamar fure a gona; iska kan hura a kansa sai ya ɓace ba a kuwa sāke tuna da inda dā yake. Amma daga madawwami zuwa madawwami ƙaunar Ubangiji tana tare da waɗanda suke tsoronsa, adalcinsa kuma tare da ’ya’yansu, tare da waɗanda suke kiyaye alkawarinsa suna kuma tuna su yi biyayya da farillansa. Ubangiji ya kafa kursiyinsa a sama, masarautarsa kuwa na mulki a bisa duka. Yabi Ubangiji, ku mala’ikunsa, ku jarumawa masu yi masa aiki, waɗanda suke yin biyayya da maganarsa. Yabi Ubangiji, dukanku rundunarsa ta sama, ku bayinsa waɗanda kuke aikata nufinsa. Yabi Ubangiji, dukanku ayyukansa ko’ina a mulkinsa. Yabi Ubangiji, ya raina. Yabi Ubangiji, ya raina. Ya Ubangiji Allahna, kana da girma ƙwarai; kana saye da daraja da ɗaukaka. Ubangiji ya naɗe kansa da haske kamar riga ya shimfiɗa sammai kamar tenti ya kafa ginshiƙan ɗakin samansa a kan ruwaye. Ya maido da gizagizai suka zama keken yaƙinsa yana hawa a kan fikafikan iska. Ya mai da iska suka zama ’yan saƙonsa harsunan wuta kuma bayinsa. Ya kafa duniya a kan tussanta; ba za a iya matsar da ita ba. Ka rufe ta da zurfi kamar da riga ruwaye sun tsaya a bisa duwatsu. Amma a tsawatawarka ruwaye suka gudu da jin ƙarar tsawanka suka ruga da gudu; suka gudu a bisa duwatsu, suka gangara zuwa cikin kwaruruka, zuwa wurin da ka shirya musu. Ka kafa iyakar da ba a iya tsallakawa; ba za su ƙara rufe duniya ba. Ya sa maɓulɓulai suka zuba ruwa cikin kwaruruka; yana gudu tsakanin duwatsu. Suna ba da ruwa ga dukan namun jeji; jakunan jeji suna kashe ƙishirwansu. Tsuntsaye sarari suna sheƙunansu kusa da ruwan; suna rera cikin rassa. Yana wa duwatsu banruwa daga ɗakinsa na sama; ƙasa tana ƙoshiya da amfanin aikinsa. Yana sa ciyawa tă yi girma saboda shanu, tsire-tsire domin mutum ya nome, suna fid da abinci daga ƙasa, ruwan inabi yakan sa zuciyar mutum tă yi murna, mai kuwa yakan sa fuska tă yi haske, abinci kuma da yake riƙe zuciyarsa. Ana yi wa itatuwan Ubangiji banruwa sosai, al’ul na Lebanon da ya shuka. A can tsuntsaye suke sheƙunnansu; shamuwa tana da gidanta a itatuwan fir. Manyan duwatsu na awakin jeji ne; tsagaggun duwatsun mafaka ne ga rema. Wata ne ke ƙididdigar lokuta, rana kuma ta san sa’ad da za tă fāɗi. Ka yi duhu, sai ya zama dare, sai dukan namun jeji a kurmi suka fito a maƙe. Zakoki sun yi ruri sa’ad da suke farauta suna kuma neman abincinsu daga Allah. Rana ta fito, sai suka koma shiru; suka koma suka kwanta a kogwanninsu. Mutum yakan tafi aikinsa, zuwa wurin aikinsa har yamma. Ina misalin yawan aikinka, ya Ubangiji! Cikin hikima ka yi su duka; duniya ta cika da halittunka. Akwai teku, babba da kuma fāɗi, cike da halittun da suka wuce ƙirga, abubuwa masu rai babba da ƙarami. A can jiragen ruwa suna kai komo, kuma dodon ruwan da ka yi, yă yi wasa a can. Waɗannan duka suna dogara gare ka don ka ba su abincinsu a daidai lokaci. Sa’ad da ba su da shi, sai su tattara shi; sa’ad da ka buɗe hannunka, sukan ƙoshi da abubuwa masu kyau. Sa’ad da ka ɓoye fuskarka, sai su razana; sa’ad da ka ɗauke numfashinsu, sai su mutu su kuma koma ga ƙura. Sa’ad da ka aika da Ruhunka, sai su halittu, su kuma sabunta fuskar duniya. Bari ɗaukakar Ubangiji ta dawwama har abada; bari Ubangiji yă yi farin ciki cikin aikinsa, shi wanda ya dubi duniya, sai ta razana, wanda ya taɓa duwatsu, sai suka yi hayaƙi. Zan rera ga Ubangiji dukan raina; zan rera yabo ga Allahna muddin ina raye. Bari tunanina yă gamshe shi, yayinda nake farin ciki a cikin Ubangiji. Amma bari masu zunubi su ɓace daga duniya mugaye kuma kada a ƙara ganinsu. Yabi Ubangiji, ya raina. Yabi Ubangiji. Ku yi godiya ga Ubangiji, ku kira bisa sunansa; ku sanar a cikin al’ummai abin da ya yi. Ku rera gare shi, ku rera yabo gare shi; ku faɗa dukan abubuwan mamakin da ya aikata. Ku ɗaukaka a cikin sunansa mai tsarki; bari zukatan waɗanda suke neman Ubangiji su yi farin ciki. Ku sa rai ga Ubangiji da kuma ƙarfinsa; ku nemi fuskarsa kullum. Ku tuna da abubuwan mamakin da ya yi, mu’ujizansa, da kuma hukunce-hukuncen da ya zartar, Ya ku zuriyar Ibrahim bawansa, Ya ku ’ya’yan Yaƙub, zaɓaɓɓensa. Shi ne Ubangiji Allahnmu; kuma hukunce-hukuncensa suna a cikin dukan duniya. Yana tuna da alkawarinsa har abada, maganar da ya umarta, har tsararraki dubu, alkawarin da ya yi da Ibrahim, rantsuwar da ya yi wa Ishaku. Ya tabbatar da shi ga Yaƙub a matsayin ƙa’ida, Isra’ila a matsayin madawwamin alkawari, “Gare ka zan ba da ƙasar Kan’ana a matsayin rabo za ka yi gādo.” Sa’ad da suke kima kawai, kima sosai, da kuma baƙi a cikinta, suka yi ta yawo daga al’umma zuwa al’umma, daga masarauta zuwa wata. Bai bar kowa yă danne su ba; saboda su, ya tsawata wa sarakuna, “Kada ku taɓa shafaffena; kada ku yi wa annabawa lahani.” Ya sauko da yunwa a kan ƙasa ya kuma lalace dukan tanadinsu na abinci; ya kuma aiki mutum a gabansu, Yusuf, da aka sayar a matsayin bawa. Suka raunana ƙafafunsa da sarƙa aka sa wuyansa cikin ƙarafa, sai abin da ya rigafaɗi ya cika sai da maganar Ubangiji ta tabbatar da shi mai gaskiya. Sarki ya aika aka kuma sake shi, mai mulkin mutane ya ’yantar da shi. Ya mai da shi shugaban gidansa, mai mulki a bisa dukan abin da ya mallaka, don yă umarci sarakunansa yadda ya ga dama yă kuma koya wa dattawa hikima. Sa’an nan Isra’ila ya shiga Masar; Yaƙub ya yi zama kamar baƙo a ƙasar Ham. Ubangiji ya mai da mutanensa suka yi ta haihuwa; ya sa suka yi yawa suka fi ƙarfin maƙiyansu, waɗanda ya juya zukatansu su ƙi mutanensa don su haɗa baki a kan bayinsa. Ya aiki Musa bawansa, da Haruna, wanda ya zaɓa. Suka yi mu’ujizansa a cikinsu, abubuwan mamakinsa a cikin ƙasar Ham. Ya aiko da duhu ya kuma sa ƙasar tă yi duhu, ba domin sun yi tawaye a kan maganarsa ba? Ya mai da ruwaye suka zama jini, ya sa kifayensu suka mutu. Ƙasarsu ta yi ta fid da kwaɗi, waɗanda suka haura cikin ɗakunan kwana na masu mulkinsu. Ya yi magana, sai tarin ƙudaje suka fito, cinnaku kuma ko’ina a ƙasar. Ya mai da ruwan samansu ya zama ƙanƙara, da walƙiya ko’ina a ƙasarsu; ya lalace inabinsu da itatuwan ɓaurensu ya ragargaza itatuwan ƙasarsu. Ya yi magana, sai fāri ɗango suka fito, fāran da ba su ƙidayuwa; suka cinye kowane abu mai ruwan kore a cikin ƙasarsu, suka cinye amfanin gonarsu Sa’an nan ya karkashe dukan ’yan fari a cikin ƙasarsu, nunan fari na dukan mazantakarsu. Ya fitar da Isra’ila, ɗauke da azurfa da zinariya, kuma daga cikin kabilansu babu wani da ya kāsa. Masar ta yi murna sa’ad da suka tafi, saboda tsoron Isra’ila ya fāɗo musu. Ya shimfiɗa girgije kamar mayafi, da kuma wuta don ta ba su haske da dare. Suka roƙa, ya kuwa ba su makware ya kuma ƙosar da su da abinci daga sama. Ya buɗe dutse, sai ruwa ya ɓulɓulo, kamar kogi ya gudu zuwa cikin hamada. Ya tuna da alkawarinsa mai tsarki da ya ba wa bawansa Ibrahim. Ya fitar da mutanensa da farin ciki, zaɓaɓɓunsa da sowa ta farin ciki; ya ba su ƙasashen al’ummai, suka kuma sami gādon abin da waɗansu sun sha wahala a kai, don su kiyaye farillansa su kuma kiyaye dokokinsa. Yabo ga Ubangiji. Yabi Ubangiji. Yi godiya ga Ubangiji, gama nagari ne shi; ƙaunarsa madawwamiya ce har abada. Wane ne zai furta manyan ayyukan Ubangiji ko yă furta cikakken yabonsa? Masu albarka ne waɗanda suke yin adalci, waɗanda kullum suke yin abin da yake daidai. Ka tuna da ni, ya Ubangiji, sa’ad da ka nuna alheri ga mutanenka, ka zo ka taimake ni sa’ad da ka cece su, don in ji daɗin nasarar zaɓaɓɓunka, don in sami rabo cikin farin cikin al’ummarka in kuma shiga gādonka cikin yin yabo. Mun yi zunubi, kamar yadda kakanninmu suka yi; mun yi ba daidai ba muka kuma aikata mugunta. Sa’ad da kakanninmu suke a Masar, ba su damu da mu’ujizanka ba; ba su tuna yawan alheranka ba, suka kuma yi tayarwa a teku, Jan Teku. Duk da haka ya cece su saboda sunansa, don yă sanar da ikonsa mai girma. Ya tsawata wa Jan Teku, ya kuwa bushe; ya bi da su ta cikin zurfafa sai ka ce a hamada. Ya cece su daga hannun maƙiyi; daga hannun abokin gāba ya fanshe su. Ruwaye suka rufe abokan gābansu; babu ko ɗaya da ya tsira. Sa’an nan suka gaskata alkawarinsa suka kuma rera yabonsa. Amma nan da nan suka manta abin da ya yi ba su kuwa jira shawararsa ba. A cikin hamada suka bar sha’awarsu ta mamaye su a ƙasar da babu kome suka gwada Allah. Sai ya ba su abin da suka roƙa, amma ya aika musu da muguwar cuta. A sansani suka ji kishin Musa da kuma Haruna, wanda Ubangiji ya keɓe. Ƙasa ta buɗe ta haɗiye Datan ta binne iyalin Abiram. Wuta ta ƙuno a cikin mabiyansu; harshen wuta ya cinye mugaye. A Horeb suka yi ɗan maraƙi suka yi wa gunkin zubi daga ƙarfe sujada. Suka sauke Ɗaukakarsu saboda siffar bijimi, wanda yake cin ciyawa. Suka manta da Allahn da ya cece su, wanda ya aikata manyan abubuwa a Masar, mu’ujizai a ƙasar Ham ayyukan banrazana a Jan Teku. Don haka ya ce zai hallaka su, amma Musa, zaɓaɓɓensa, ya yi godo a gabansa don yă kau da hasalarsa daga hallaka su. Sai suka rena ƙasa mai ni’ima; ba su gaskata alkawarinsa ba. Suka yi gunaguni a tentunansu ba su kuwa yi biyayya da Ubangiji ba. Saboda haka ya rantse musu ya kuma ɗaga hannu cewa zai sa su mutu a cikin hamada, ya sa zuriyarsu su mutu a cikin al’ummai ya kuma watsar da su cikin dukan ƙasashe. Suka haɗa kai da Ba’al-Feyor suka kuma ci hadayun da aka miƙa wa allolin da ba su da rai; suka tsokane Ubangiji ya yi fushi ta wurin mugayen ayyukansu, sai annoba ta ɓarke a cikinsu. Amma Finehas ya miƙe tsaye ya ɗauki mataki, sai annobar ta daina. An ayana masa wannan a matsayin adalci har zamanai marar matuƙa masu zuwa. A ruwan Meriba suka ba Ubangiji fushi, sai wahala ta zo wa Musa saboda su; saboda sun yi tayarwa a kan Ruhun Allah, har mugayen kalmomi suka fito daga leɓunan Musa. Ba su hallakar da mutanen yadda Ubangiji ya umarce su ba, amma suka yi cuɗanya da al’ummai suka ɗauki al’adunsu. Suka yi wa gumakansu sujada, waɗanda suka zama tarko gare su. Suka miƙa ’ya’yansu maza hadaya ’yan matansu kuma ga aljanu. Suka zub da jini marar laifi, jinin ’ya’yansu maza da mata, waɗanda suka miƙa hadaya ga gumakan Kan’ana, ƙasar kuwa ta ƙazantu ta wurin jininsu. Suka ƙazantar da kansu ta wurin abin da suka yi; ta wurin ayyukansu suka yi karuwanci. Saboda haka Ubangiji ya yi fushi da mutanensa ya ji ƙyamar gādonsa. Ya miƙa su ga al’ummai, maƙiyansu kuma suka yi mulki a kansu. Abokan gābansu suka danne su suka sa su a ƙarƙashin ikonsu. Sau da yawa ya cece su, amma sun nace su yi tawaye suka kuma lalace cikin zunubinsu. Amma ya lura da wahalarsu sa’ad da ya ji kukansu; saboda su ya tuna da alkawarinsa kuma daga yawan ƙaunarsa ya ji tausayi. Ya sa aka ji tausayinsu a wurin dukan waɗanda suka kame su. Ka cece mu, Ubangiji Allahnmu, ka kuma tattara mu daga al’ummai, don mu yi wa sunanka mai tsarki godiya mu kuma ɗaukaka cikin yabonka. Yabo ga Ubangiji, Allah na Isra’ila, daga madawwami zuwa madawwami. Bari dukan mutane su ce, “Amin!” Yabo ga Ubangiji. Ku yi godiya ga Ubangiji, gama nagari ne shi; ƙaunarsa madawwamiya ce har abada. Bari fansassu na Ubangiji su faɗa wannan, su da aka fansa daga hannun maƙiyi, su da ya tattara daga ƙasashe, daga gabas da yamma, daga arewa da kudu. Waɗansu sun yi ta yawo a jejin hamada, ba su sami hanya zuwa birnin da za su zauna ba. Sun ji yunwa da ƙishirwa, suka kuma fid da zuciya. Sa’an nan suka yi kuka ga Ubangiji cikin wahalarsu, ya kuma cece su daga damuwarsu. Ya bishe su ta miƙaƙƙiyar hanya zuwa birnin da za su zauna. Bari su yi godiya ga Ubangiji saboda ƙaunarsa marar ƙarewa da kuma ayyukansa masu banmamaki saboda mutane, gama yana shayar da masu ƙishirwa yana kuma ƙosar da mayunwata da abubuwa masu kyau. Waɗansu sun zauna a cikin duhu da kuma zurfin ɓacin rai, ’yan kurkuku suna wahala cikin sarƙoƙin ƙarfe, gama sun yi tayarwa a kan maganar Allah suka ƙi shawarar Mafi Ɗaukaka. Saboda haka ya ba da su ga aiki mai wuya; suka yi tuntuɓe, kuma ba mai taimako. Sa’an nan suka yi kuka ga Ubangiji cikin wahalarsu, ya kuwa cece su daga damuwarsu. Ya fitar da su daga duhu da zurfin ɓaci rai ya tsintsinke sarƙoƙinsu. Bari su yi godiya ga Ubangiji saboda ƙaunarsa marar ƙarewa da kuma ayyukansa masu banmamaki saboda mutane, gama ya farfashe ƙofofin tagulla ya kuma ragargaza ƙyamaren ƙarfe. Waɗansu suka zama wawaye ta wurin hanyoyinsu na tayarwa suka kuwa sha wahala saboda laifofinsu. Ba su so su ga abinci ba suka kuwa kai bakin mutuwa. Sa’an nan suka yi kuka ga Ubangiji cikin wahalarsu, ya kuwa cece su daga damuwarsu. Ya ba da umarninsa ya kuma warkar da su ya kuɓutar da su daga kabari. Bari su yi godiya ga Ubangiji saboda ƙaunarsa marar ƙarewa da kuma ayyukansa masu banmamaki saboda mutane. Bari su miƙa hadaya ta godiya su kuma ba da labarin ayyukansa da waƙoƙin farin ciki. Waɗansu suka yi tafiya a teku cikin jiragen ruwa; su ’yan kasuwa ne a manyan ruwaye. Sun ga ayyukan Ubangiji, ayyukansa masu banmamaki a cikin zurfin teku. Gama ya yi magana ya kuma sa iska mai ƙarfi ta tashi ya ɗaga raƙuman ruwa sama. Suka hau zuwa sammai suka kuma tsinduma cikin zurfafa; a cikin azabarsu sai ƙarfin halinsu ya karai. Suka yi tangaɗi suna tuntuɓe kamar bugaggu; suka kuma kai ga ƙarshen dabararsu. Sai suka yi kuka ga Ubangiji cikin wahalarsu, ya kuwa fitar da su daga damuwarsu. Ya kwantar da hadiri suka yi tsit; raƙuman ruwan teku suka yi shiru. Suka yi murna sa’ad da wuri ya kwanta, ya kuma bishe su zuwa inda suka so su kai. Bari su yi godiya ga Ubangiji saboda ƙaunarsa marar ƙarewa da kuma ayyukansa masu banmamaki saboda mutane. Bari su ɗaukaka shi cikin taron mutane su kuma yabe shi cikin taron dattawa. Ya mai da koguna suka zama hamada, maɓulɓulai masu gudu suka zama ƙasa mai ƙishirwa, ƙasa mai amfani kuma suka zama gishiri marar amfani, saboda muguntar waɗanda suka zauna a can. Ya mai da hamada ya zama tafkunan ruwa busasshiyar ƙasa kuma zuwa maɓulɓulai masu gudu; a can ya kai mayunwata su yi zama, ya kuma samo birnin da za su zauna. Suka yi shuka a gonaki suka dasa inabi suka kuma girbe amfani gona; ya albarkace su, yawansu kuma ya ƙaru, bai kuwa bar garkunansu suka ragu ba. Sa’an nan yawansu ya ragu, aka kuma ƙasƙantar da su ta wurin danniya, bala’i da kuma baƙin ciki; shi da yake kawo reni a kan manyan mutane ya sa suka yi ta yawo a cikin jejin da ba hanya. Amma ya fid da mabukata daga wahalarsu ya kuma ƙara iyalansu da tumakinsu. Masu yin gaskiya suka gani suka yi farin ciki amma dukan mugaye suka rufe bakunansu. Duk mai hikima, bari yă ji waɗannan abubuwa yă kuma lura da ƙauna mai girma ta Ubangiji. Zuciyata tsayayyiya ce, ya Allah; zan rera in kuma yi kiɗi da dukan raina. Ku farka, garaya da molo! Zan farkar da rana. Zan yabe ka, ya Ubangiji, a cikin al’ummai; zan rera game da kai cikin mutane. Gama ƙaunarka da girma take, bisa fiye da sammai; amincinka ya kai sarari. A ɗaukaka ka, ya Allah, a bisa sammai, bari kuma ɗaukakarka ta kasance a bisa dukan duniya. Ka cece mu ka kuma taimake mu da hannunka na dama, domin waɗanda kake ƙauna su kuɓuta. Allah ya yi magana daga wurinsa mai tsarki, “Ciki nasara zan raba Shekem in kuma auna Kwarin Sukkot. Gileyad nawa ne, Manasse nawa ne; Efraim shi hulan kwanona, Yahuda ne sandana na sarauta. Mowab shi ne kwanon wankina, a kan Edom zan jefa takalmina; a bisa Filistiya zan yi kirari cikin nasara.” Wa zai kawo ni birni mai katanga? Wa zai jagorance ni zuwa Edom? Ba kai ba ne, ya Allah, kai da ka ƙi mu ba ka kuwa fita tare da mayaƙanmu? Ka ba mu taimako a kan abokin gāba, gama taimakon mutum banza ne. Tare da Allah za mu yi nasara, zai kuma tattaka abokan gābanmu. Ya Allah, wanda nake yabo, kada ka yi shiru, gama mugaye da masu ruɗu sun buɗe bakunansu a kaina; sun yi magana a kaina da harsunan ƙarya. Da kalmomin ƙiyayya sun kewaye ni; sun tasar mini ba dalili. A maimakon ƙauna sun sāka mini da zargi, amma ni mutum ne mai addu’a. Sun sāka mini alheri da mugunta, ƙauna kuma da ƙiyayya. Ka naɗa mugun mutum yă yi hamayya da shi; bari mai zargi yă tsaya a hannun damansa. Sa’ad da aka yi masa shari’a, bari a same shi da laifi, bari kuma addu’o’insa su hukunta shi. Bari kwanakinsa su zama kaɗan; bari wani yă ɗauki wurinsa na shugabanci. Bari ’ya’yansa su zama marayu matarsa kuma gwauruwa. Bari ’ya’yansa su zama masu yawo suna bara; bari a yi ta koransu daga gidajensu da suke kufai. Bari mai binsa bashi yă ƙwace dukan abin da yake da shi; bari baƙi su washe amfanin aikinsa. Bari kada kowa yă yi masa alheri ko yă ji tausayin marayunsa. Bari duk zuriyarsa su mutu, a shafe sunayensu daga tsara mai zuwa. Bari a tuna da laifin kakanninsa a gaban Ubangiji; bari kada a taɓa shafe zunubin mahaifiyarsa. Bari zunubansu su kasance a gaban Ubangiji kullum, don yă sa a manta da su daga duniya. Gama bai taɓa yin tunanin yin alheri ba, amma ya tsananta wa matalauta da mabukata da kuma masu fid da zuciya har suka mutu. Yana jin daɗin la’antarwa, bari yă dawo a kansa; ba ya son sa albarka, bari kada kowa yă sa masa albarka. Ya sa la’antarwa kamar rigarsa; ta shiga cikin jikinsa kamar ruwa, cikin ƙasusuwansa kamar mai. Bari tă zama kamar mayafin da aka ɗaura kewaye da shi, kamar ɗamara da aka ɗaura kewaye da shi har abada. Bari wannan yă zama sakayyar Ubangiji ga masu zargina, ga waɗanda suke mugayen maganganu a kaina. Amma kai, ya Ubangiji Mai Iko Duka, ka yi da ni da kyau saboda sunanka; ta alherin ƙaunarka, ka cece ni. Gama ni matalauci ne mai bukata kuma, zuciyata kuwa ta yi rauni a cikina. Na ɓace kamar inuwar yamma; ana kakkaɓe ni kamar fāra. Gwiwoyina suna mutuwa saboda azumi; jikina ya rame ba kuma ƙarfi. Na zama abin dariya ga masu zargina; sa’ad da suka gan ni, suka kaɗa kawunansu. Ka taimake ni, ya Ubangiji Allahna; ka cece ni bisa ga ƙaunarka. Bari su san cewa hannunka ne, cewa kai ne, ya Ubangiji, ka yi shi. Za su iya la’anta, amma kai za ka sa albarka; sa’ad da suka tasar za su sha kunya, amma bawanka zai yi farin ciki. Masu zargina za su sha kunya za a rufe su da kunya kamar mayafi. Da bakina zan ɗaukaka Ubangiji sosai; cikin babban taro zan yabe shi. Gama yana tsaya a hannun damar mai bukata, don yă cece ransa daga waɗanda suke hukunta shi. Ubangiji ya ce wa Ubangijina, “Zauna a hannun damana, sai na sa abokan gābanka su zama matashin sawunka.” Ubangiji zai fadada ikon sandan mulkinka daga Sihiyona za ka yi mulki a tsakiyar abokan gābanka. Rundunarka za su so yin yaƙi a ranarka ta yaƙi. Saye cikin ɗaukaka mai tsarki, daga cikin ciki na safiya za ka karɓi raɓar ƙuruciyarka. Ubangiji ya rantse ba zai kuma canja zuciyarsa ba, “Kai firist ne har abada, bisa ga tsarin Melkizedek.” Ubangiji yana a hannun damanka; zai murƙushe sarakuna a ranar fushinsa. Zai hukunta al’ummai, yana tarawa gawawwaki yana kuma murƙushe masu mulkin dukan duniya. Zai sha daga rafin da yake kusa da hanya; saboda haka zai ɗaga kansa sama. Yabi Ubangiji. Zan ɗaukaka Ubangiji da dukan zuciyata a cikin majalisar masu aikata gaskiya da kuma a cikin taro. Ayyukan Ubangiji da girma suke; dukan waɗanda suke farin ciki da su suna tunaninsu. Ayyukansa masu ɗaukaka da kuma daraja ne, adalcinsa kuma zai dawwama har abada. Ya sa a tuna da abubuwa masu banmamaki nasa; Ubangiji mai alheri ne mai tausayi kuma. Yana ba da abinci ga waɗanda suke tsoronsa; yakan tuna da alkawarinsa har abada. Ya nuna wa mutanensa ikon ayyukansa, yana ba su ƙasashen waɗansu al’ummai. Ayyukan hannuwansa masu aminci ne da kuma gaskiya; dukan farillansa abin dogara ne. Tsayayyu ne har abada abadin, ana yinsu cikin aminci da kuma gaskiya. Yana ba da ceto ga mutanensa; ya kafa alkawarinsa har abada, tsarki da banrazana ne sunansa. Tsoron Ubangiji ne mafarin hikima; dukan waɗanda suke bin farillansa suna da ganewa mai kyau. Gare shi ne madawwamin yabo. Yabi Ubangiji. Mai albarka ne mutumin da yake tsoron Ubangiji, wanda yakan sami farin ciki mai girma a umarnansa. ’Ya’yansa za su zama manya a ƙasar; tsaran masu aikata gaskiya za su sami albarka. Wadata da arziki suna a cikin gidansa, adalcinsa zai dawwama har abada. Ko a cikin duhu haske kan haskaka wa mai aikata gaskiya, mai alheri mai tausayi da kuma mai adalci. Abu mai kyau zai zo masa shi da yake kyauta yake kuma ba da bashi hannu sake, shi da yake yin al’amuransa cikin gaskiya. Tabbatacce ba zai taɓa jijjigu ba; za a tuna da mai adalci har abada. Ba zai ji tsoron labari marar daɗi ba; zuciyarsa tsayayyiya ce, tana dogara ga Ubangiji. Zuciyarsa tana da kāriya, ba zai ji tsoro ba; a ƙarshe zai zama mai nasara a kan maƙiyansa. Ya rarraba kyautansa ga matalauta, adalcinsa zai dawwama har abada; za a ɗaga ƙahonsa sama da bangirma. Mugun mutum zai gani yă kuma yi fushi, zai ciza haƙora yă kuma lalace; sha’awace-sha’awacen mugaye za su zo ga ƙarshe. Yabi Ubangiji. Ku yabe shi, ya ku bayin Ubangiji, ku yabi sunan Ubangiji. Bari a yabi sunan Ubangiji, yanzu da har abada kuma. Daga fitowar rana zuwa inda take fāɗuwa, a yabi sunan Ubangiji. Ana ɗaukaka Ubangiji a bisa dukan al’ummai, ɗaukakarsa a bisa sammai Wane ne yake kamar Ubangiji Allahnmu, Wannan mai zama a kursiyi can bisa, wanda yake sunkuya yă dubi sammai da duniya? Yakan tā da matalauta daga ƙura yakan ɗaga mabukata daga tarin toka; ya zaunar da su tare da sarakuna, tare da sarakunan mutanensu. Yakan zaunar da matar da ba haihuwa a gidanta ta zama kamar mahaifiyar ’ya’ya mai farin ciki. Yabi Ubangiji. Sa’ad da Isra’ila ya fito daga Masar, gidan Yaƙub daga mutane masu baƙon harshe, Yahuda ya zama wuri mai tsarki na Allah, Isra’ila mallakarsa. Teku ya kalla ya kuma gudu, Urdun ya juye da baya; duwatsu suka yi tsalle kamar raguna, tuddai kamar tumaki. Me ya sa, ya teku, kika gudu, Ya Urdun, ka juya baya, ku duwatsu, kuka yi tsalle kamar raguna, ku tuddai, kamar tumaki? Ki yi rawar jiki, ya duniya, a gaban Ubangiji, a gaban Allah na Yaƙub, wanda ya juye dutse ya zama tafki, dutse mai ƙarfi zuwa maɓulɓulan ruwa. Ba gare mu ba, ya Ubangiji, ba gare mu ba amma ga sunanka yă sami ɗaukaka, saboda ƙaunarka da amincinka. Me ya sa al’ummai suke cewa, “Ina Allahnsu?” Allahnmu yana a sama; yana yin duk abin da ya ga dama. Amma gumakansu azurfa da zinariya ne, da hannuwan mutane suka yi. Suna da bakuna, amma ba sa magana, idanu, amma ba sa gani; suna da kunnuwa, amma ba sa ji, hanci, amma ba sa jin ƙanshi suna da hannuwa, amma ba sa iya taɓa kome, ƙafafu, amma ba sa iya tafiya; ba sa iya ce wani abu da maƙogwaronsu. Masu yinsu za su zama kamar su, haka kuma zai kasance da duk wanda ya dogara da su. Ya gidan Isra’ila, ku dogara ga Ubangiji, shi ne mai taimakonsu da garkuwarsu. Ya gidan Haruna, ku dogara ga Ubangiji, shi ne mai taimakonsu da garkuwarsu. Ku da kuke tsoronsa, ku dogara ga Ubangiji, shi ne mai taimakonsu da garkuwarsu. Ubangiji yakan tuna da mu zai kuma albarkace mu. Zai albarkace gidan Isra’ila, zai albarkace gidan Haruna, zai albarkace waɗanda suke tsoron Ubangiji, manya da ƙanana duka. Bari Ubangiji yă sa ku ƙaru, da ku da ’ya’yanku. Bari Ubangiji yă albarkace ku, shi Mahalicci sama da ƙasa. Saman sammai na Ubangiji ne, amma ya ba da duniya ga mutum. Ba matattu ba ne masu yabon Ubangiji, waɗanda suke gangara zuwa wurin da ake shiru; mu ne masu ɗaukaka Ubangiji, yanzu da har abada kuma. Yabi Ubangiji. Ina ƙaunar Ubangiji, gama ya ji muryata; ya ji kukata ta neman jinƙai. Domin ya juye kunnensa gare ni, zan kira gare shi muddin ina da rai. Igiyoyin mutuwa sun shaƙe ni, wahalar kabari sun zo a kaina; na cika da wahala da ɓacin rai. Sai na kira ga sunan Ubangiji na ce, “Ya Ubangiji, ka cece ni!” Ubangiji mai alheri ne da kuma mai adalci; Allahnmu yana cike da tausayi. Ubangiji yana tsare masu tawali’u; sa’ad da nake cikin tsananin bukata, ya cece ni. Ka kwantar da hankali, ya raina, gama Ubangiji mai alheri ne a gare ka. Gama kai, ya Ubangiji, ka ceci raina daga mutuwa, idanuna daga hawaye, ƙafafuna daga tuntuɓe, don in iya tafiya a gaban Ubangiji a ƙasar masu rai. Na gaskata, saboda haka na ce, “An azabtar da ni ƙwarai.” Kuma cikin rikicewana na ce, “Dukan mutane maƙaryata ne.” Yaya zan sāka wa Ubangiji saboda dukan alherinsa gare ni? Zan daga kwaf na ceto in kuma kira ga sunan Ubangiji. Zan cika alkawurana ga Ubangiji a gaban dukan mutanensa. Abu mai daraja a gaban Ubangiji shi ne mutuwar tsarkakansa. Ya Ubangiji, da gaske ni bawanka ne; ni bawanka ne, ɗan baiwarka; ka ’yantar da ni daga sarƙoƙi. Zan yi hadayar godiya gare ka in kuma kira bisa sunan Ubangiji. Zan cika alkawurana ga Ubangiji a gaban dukan mutanensa, a filayen gidan Ubangiji, a tsakiyarki, ya Urushalima. Yabi Ubangiji. Yabi Ubangiji, dukanku al’umma; ku ɗaukaka shi, dukanku mutane. Gama ƙaunarsa da girma take gare mu, amincin Ubangiji kuma madawwami ne har abada. Yabi Ubangiji. Ku gode wa Ubangiji, gama nagari ne shi; ƙaunarsa madawwamiya ce har abada. Bari Isra’ila yă ce, “Ƙaunarsa madawwamiya ce har abada.” Bari gidan Haruna yă ce, “Ƙaunarsa madawwamiya ce har abada.” Bari waɗanda suke tsoron Ubangiji su ce, “Ƙaunarsa madawwamiya ce har abada.” Cikin azabata na yi kuka ga Ubangiji, ya kuwa amsa ta wurin ’yantar da ni. Ubangiji yana tare da ni; ba zan ji tsoro ba. Me mutum zai yi mini? Ubangiji yana tare da ni; shi ne mai taimakona. Zan yi nasara a kan abokan gābana. Ya fi kyau in nemi mafaka a wurin Ubangiji da in dogara ga mutum. Ya fi kyau in nemi mafaka a wurin Ubangiji da in dogara ga sarakuna. Dukan al’ummai sun kewaye ni, amma a cikin sunan Ubangiji na hallaka su. Sun kewaye ni a kowane gefe, amma a cikin sunan Ubangiji na hallaka su. Sun rufe ni kamar ƙudan zuma, amma suka mutu nan da nan kamar ƙayayyuwa masu cin wuta; a cikin sunan Ubangiji na hallaka su. An ture ni baya na kusa fāɗuwa, amma Ubangiji ya taimake ni. Ubangiji ne ƙarfina da waƙata; ya zama mai cetona. Sowa ta farin ciki da nasara sun fito a cikin tentunan adalai, “Hannun dama na Ubangiji ya aikata manyan abubuwa! An ɗaga hannun dama na Ubangiji sama; hannun dama na Ubangiji ya aikata manyan abubuwa!” Ba zan mutu ba amma zan rayu, zan kuwa yi shelar abin da Ubangiji ya yi. Ubangiji ya hore ni sosai, amma bai ba da ni ga mutuwa ba. Buɗe mini ƙofofin adalci; zan shiga in kuma yi godiya ga Ubangiji. Wannan ne ƙofar Ubangiji inda adalai za su shiga. Zan yi maka godiya, domin ka amsa mini; ka zama mai cetona. Zabura Dutsen da magina suka ƙi ya zama mai amfani; Ubangiji ne ya yi haka, kuma abu mai daraja ne a idanunmu. Wannan ita ce ranar da Ubangiji ya yi; bari mu yi farin ciki mu kuma yi murna a cikinta. Ya Ubangiji, ka cece mu; Ya Ubangiji, ka ba mu nasara. Mai albarka ne shi mai zuwa cikin sunan Ubangiji. Daga gidan Ubangiji muna sa muku albarka. Ubangiji shi ne Allah ya kuma sa haskensa ya haskaka a kanmu. Da kwanoni a hannunmu, muka shiga jerin gwanon biki ku kai su ƙahoni na bagade. Kai ne Allahna, zan kuwa yi maka godiya; kai ne Allahna, zan kuwa ɗaukaka ka. Ku gode wa Ubangiji, gama nagari ne shi; ƙaunarsa madawwamiya ce har abada. Albarka ta tabbata ga waɗanda rayuwarsu ba ta da abin zargi, waɗanda suke tafiya bisa ga dokar Ubangiji. Albarka ta tabbata ga waɗanda suke kiyaye ƙa’idodinsa suke kuma nemansa da dukan zuciyarsu. Ba sa yin wani abin da ba daidai ba; suna tafiya a hanyoyinsa. Ka shimfiɗa farillan da dole a yi biyayya da su. Kash, da a ce hanyoyina tsayayyu ne a yin biyayya da ƙa’idodinka mana! Da ba zan sha kunya ba sa’ad da na lura da dukan umarnanka. Zan yabe ka da zuciya ta gaskiya yayinda nake koyon dokokinka masu adalci. Zan yi biyayya da ƙa’idodinka; kada ka yashe ni ɗungum. Yaya matashi zai kiyaye hanyarsa da tsabta? Sai ta yin rayuwa bisa ga maganarka. Na neme ka da dukan zuciyata; kada ka bar ni in kauce daga umarnanka. Na ɓoye maganarka a cikin zuciyata don kada in yi maka zunubi. Yabo ya tabbata gare ka, ya Ubangiji; ka koya mini ƙa’idodinka. Da leɓunana na ba da labarin dukan dokokin da suka fito bakinka. Na yi farin ciki da bin farillanka yadda mutum yakan yi farin ciki da arziki mai yawa. Na yi tunani a kan farillanka na kuma lura da hanyoyinka. Na yi murna a cikin ƙa’idodinka; ba zan ƙyale maganarka ba. Ka yi alheri ga bawanka, zan kuwa rayu; zan yi biyayya da maganarka. Ka buɗe idanuna don in iya gani abubuwan banmamaki a cikin dokarka. Ni baƙo ne a duniya; kada ka ɓoye mini umarnanka. Zuciyata ta ƙosa saboda marmari don dokokinka koyaushe. Ka tsawata wa masu fariya, waɗanda suke la’anta waɗanda kuma suka kauce daga umarnanka. Ka cire mini ba’a da reni, gama ina kiyaye farillanka. Ko da yake masu mulki sun zauna tare suna ɓata mini suna, bawanka zai yi tunani a kan ƙa’idodinka. Farillanka ne abin farin cikina; su ne mashawartana. An kwantar da ni ƙasa cikin ƙura; ka kiyaye raina bisa ga maganarka. Na ba da labari hanyoyina ka kuma amsa mini; ka koya mini ƙa’idodinka. Bari in gane koyarwar farillanka; sa’an nan zan yi tunani a kan abubuwan banmamakinka. Raina ya gaji da baƙin ciki; ka ƙarfafa ni bisa ga maganarka. Ka kiyaye ni daga hanyoyin ruɗu; ka yi mini alheri ta wurin dokokinka. Na zaɓi hanyar gaskiya; na sa zuciyata a kan dokokinka. Na riƙe farillanka kankan, ya Ubangiji; kada ka sa in sha kunya. Ina gudu a kan hanyar umarnanka, gama ka ’yantar da zuciyata. Ka koya mini Ya Ubangiji, don in bi ƙa’idodinka; sa’an nan zan kiyaye su har ƙarshe. Ka ba ni ganewa, zan kuwa kiyaye dokarka in kuma yi biyayya da ita da dukan zuciyata. Ka bi da ni a hanyar umarnanka, gama a can zan sami farin ciki. Ka juye zuciyata wajen farillanka ba wajen riba ta sonkai ba. Ka juye idanuna daga abubuwa marasa amfani; ka kiyaye raina bisa ga maganarka. Ka cika alkawarinka ga bawanka, saboda a ji tsoronka. Ka kawar da shan kunyar da nake tsoro, gama dokokinka nagari ne. Ina marmarin farillanka ƙwarai! Ka kiyaye raina cikin adalcinka. Bari ƙaunarka marar ƙarewa ta zo gare ni, ya Ubangiji, cetonka bisa ga alkawarinka; sa’an nan zan amsa wa masu cin mutuncina, gama na dogara ga maganarka. Kada ka ƙwace maganarka daga bakina, gama na sa zuciyata a dokokinka. Kullayaumi zan yi biyayya da dokokinka, har abada abadin. Zan yi ta yawo a sake gama na nemi farillanka. Zan yi maganar farillanka a gaban sarakuna ba kuwa za a kunyata ni ba, gama ina farin ciki da umarnanka saboda ina ƙaunarsu. Na ɗaga hannuwana ga umarnanka, waɗanda nake ƙauna, ina kuma tunani a kan ƙa’idodinka. Tuna da maganarka ga bawanka, gama ka ba ni bege. Ta’aziyyata cikin wahalata ita ce alkawarinka yana kiyaye raina. Masu fariya suna yi mini ba’a ba tare da an hana su ba, amma ban rabu da dokar ba. Na tuna da dokokinka na tun dā, ya Ubangiji, na kuwa sami ta’aziyya a cikinsu. Fushi ya kama ni saboda mugaye, waɗanda suka keta dokokinka. Ƙa’idodinka su ne kan waƙata a duk inda na sauka. Da dare na tuna da sunanka, ya Ubangiji, zan kuwa kiyaye dokarka. Wannan shi ne na saba yi, ina yin biyayya da farillanka. Kai ne rabona, ya Ubangiji; na yi alkawarin in kiyaye maganarka. Na nemi fuskarka da dukan zuciyata; ka yi mini alheri bisa ga alkawarinka. Na lura da hanyoyina na kuma mayar da matakaina ga farillanka. Zan gaggauta ba zan ɓata lokaci ba in yi biyayya da umarnanka. Ko da yake mugaye sun ɗaura ni da igiyoyi, ba zan manta da dokokinka ba. Da tsakar dare nakan tashi in gode maka saboda dokokinka masu adalci. Ni aboki ne ga duk mai tsoronka, ga duk wanda yake bin farillanka. Duniya ta cika da ƙaunarka, ya Ubangiji; ka koya mini ƙa’idodinka. Ka yi wa bawanka alheri bisa ga maganarka, ya Ubangiji. Ka koya mini sani da kuma hukunci mai kyau, gama na gaskata a umarnanka. Kafin in sha wahala na kauce, amma yanzu ina biyayya da maganarka. Kai nagari ne, kuma abin da kake yi yana da kyau; ka koya mini ƙa’idodinka. Ko da yake masu fariya sun shafe ni da ƙarairayi, na kiyaye farillanka da dukan zuciyata. Zukatansu sun yi tauri da kuma marasa tausayi amma ina farin ciki a dokarka. Ya yi kyau da na sha wahala don in koyi ƙa’idodinka. Doka daga bakinka ya fi mini daraja fiye da azurfa da zinariya guda dubu. Hannuwanka ne suka yi suka kuma siffanta ni; ka ba ni ganewa don in koyi umarnanka. Bari waɗanda suke tsoronka su yi farin ciki sa’ad da suke gan ni, gama na sa zuciyata a maganarka. Ya Ubangiji na sani, cewa dokokinka masu adalci ne, kuma cikin aminci ka hore ni. Bari ƙaunarka marar ƙarewa tă yi mini ta’aziyya, bisa ga alkawarinka ga bawanka. Bari tausayinka yă zo mini don in rayu, gama dokarka ce farin cikina. Bari masu girman kai su sha kunya saboda abubuwa marasa kyau da suke yi mini ba dalili; amma zan yi tunani a kan farillanka. Bari waɗanda suke tsoronka su juya gare ni, waɗanda suka gane da farillanka. Bari zuciyata ta kasance marar abin zargi wajen ƙa’idodinka, don kada in sha kunya. Raina ya tafke da marmari don cetonka, amma na sa zuciyata a maganarka. Idanuna sun gaji, suna jiran alkawarinka; Na ce, “Yaushe za ka ta’azantar da ni?” Ko da yake ni kamar salkar ruwan inabi ne a cikin hayaƙi, ban manta da ƙa’idodinka ba. Har yaushe bawanka zai yi ta jira? Yaushe za ka hukunta masu tsananta mini? Masu girman kai sun haƙa mini rami, sun ƙetare dokarka. Dukan umarnanka abin dogara ne; ka taimake ni, gama mutane suna tsananta mini ba dalili. Sun kusa gama da ni a duniya, amma ban bar bin farillanka ba. Ka kiyaye raina bisa ga ƙaunarka, zan kuwa yi biyayya da farillan bakinka. Maganarka, ya Ubangiji madawwamiya ce; tana nan daram a cikin sammai. Amincinka yana cin gaba cikin dukan zamanai; ka kafa duniya ta kuma dawwama. Dokokinka sun dawwama har yă zuwa yau, gama dukan abubuwa suna maka hidima. Da ba don dokarka ce farin cikina ba, da na hallaka a cikin azabana. Ba zan taɓa manta da farillanka ba, gama ta wurinsu ne ka kiyaye raina. Ka cece ni, gama ni naka ne; na yi ƙoƙarin neman farillanka. Mugaye suna jira su hallaka ni, amma zan yi ta tunani a kan farillanka. Ga duk cikakke na ga kāsawa; amma umarnanka ba su da iyaka. Kash, ga yadda nake ƙaunar dokarka! Ina tunani a kanta dukan yini. Umarnanka suna sa in zama mai hikima fiye da abokan gābana, gama kullum suna tare da ni. Ina da ganewa sosai fiye da dukan malamaina, gama ina tunani a kan farillanka. Ina da ganewa fiye da dattawa, gama ina biyayya da farillanka. Na kiyaye ƙafafuna daga kowace muguwar hanya domin in yi biyayya da maganarka. Ban rabu da dokokinka ba, gama kai da kanka ne ka koya mini. Ɗanɗanon maganarka akwai zaki, sun ma fi zuma zaki a bakina! Na sami ganewa daga farillanka; saboda haka ina ƙin kowace hanyar da ba daidai ba. Maganarka fitila ce ga ƙafafuna haske kuma a kan hanyata. Na yi rantsuwa na kuma tabbatar da shi, cewa zan bi dokokinka masu adalci. Na sha wahala sosai; ka kiyaye raina, ya Ubangiji, bisa ga maganarka. Ka karɓi yabon bakina da nake yi da yardar rai, ya Ubangiji, ka kuwa koya mini dokokinka. Ko da yake kullum ina riƙe da raina a hannuwana, ba zan manta da dokarka ba. Mugaye sun kafa mini tarko, amma ban kauce daga farillanka ba. Farillanka su ne gādona har abada; su ne farin cikin zuciyata. Zuciyata ta shirya a kan kiyaye ƙa’idodinka har ƙarshe. Na ƙi mutane masu baki biyu, amma ina ƙauna dokarka. Kai ne mafakata da garkuwata; na sa zuciyata a maganarka. Ku rabu da ni, ku masu aikata mugunta, don in kiyaye umarnan Allahna! Ka raya ni bisa ga alkawarinka, zan kuwa rayu; kada ka bari a gwale sa zuciyata. Ka riƙe ni za a kuma cece ni; kullayaumi zan ɗauka ƙa’idodinka da muhimmanci. Ka ki dukan waɗanda suka kauce daga ƙa’idodinka, gama yaudararsu banza ne. Dukan mugayen duniya ka zubar kamar datti; saboda haka nake ƙaunar farillanka. Naman jikina na rawan jiki don tsoronka; na cika da tsoron dokokinka. Na aikata abin da yake mai adalci da kuma daidai; kada ka ni a hannun masu danne ni. Ka tabbatar da lafiyar bawanka; kada ka bar masu girman kai su danne ni. Idanuna sun gaji, da jiran cetonka, da jiran alkawarinka mai adalci. Ka yi da bawanka bisa ga ƙaunarka ka kuma koya mini ƙa’idodinka. Ni bawanka ne, ka ba ni fahimi don in gane farillanka. Lokaci ya yi da za ka yi wani abu, ya Ubangiji; ana karya dokarka. Saboda ina ƙaunar umarnanka fiye da zinariya, kai, fiye da zinariya zalla, saboda kuma ina lura da dukan farillanka da kyau, na ƙi kowace hanyar da ba daidai ba. Farillanka masu banmamaki ne; saboda haka nake yin biyayya da su. Fassarar maganganunka sukan ba da haske; sukan ba da ganewa ga marar ilimi. Ina hakkin da bakina a buɗe, ina marmarin umarnanka. Ka juye wurina ka kuma yi mini jinƙai, yadda kullum ka yi wa waɗanda suke ƙaunar sunanka. Ka bi da sawuna bisa ga maganarka; kada ka bar zunubi yă mallake ni. Ka fanshe ni daga mutane masu danniya, don in yi biyayya da farillanka. Ka sa fuskarka ta haskaka a kan bawanka ka kuma koya mini ƙa’idodinka. Hawaye suna malalowa daga idanuna kamar rafi, gama ba a biyayya da dokarka. Mai adalci ne kai, ya Ubangiji, dokokinka kuma daidai ne. Farillan da ka shimfiɗa masu adalci ne; su kuma abin dogara ne ƙwarai. Kishina ya cinye ni ɗungum, gama abokan gābana sun yi biris da maganganunka. An gwada alkawuranka sarai, bawanka kuwa yana ƙaunarsu. Ko da yake ni ba kome ba ne an kuwa rena ni, ba na manta da farillanka. Adalcinka dawwammame ne dokar kuma gaskiya ce. Wahala da damuwa suna a kaina, amma umarnanka su ne farin cikina. Farillanka daidai ne har abada; ka ba ni ganewa don in rayu. Na yi kira da dukan zuciyata; ka amsa mini, ya Ubangiji, zan kuwa yi biyayya da ƙa’idodinka. Na yi kira gare ka; ka cece ni zan kuwa kiyaye farillanka. Na tashi kafin fitowar rana na kuma yi kukan neman taimako; na sa zuciyata a maganarka. Ban rufe idanuna ba dukan dare, don in yi tunani a kan alkawuranka. Ka ji muryata bisa ga ƙaunarka; ka kiyaye raina, ya Ubangiji, bisa ga dokokinka. Waɗanda suke ƙirƙiro mugayen dabaru suna nan kusa, amma suna nesa da dokarka. Duk da haka kana kusa, ya Ubangiji, kuma dukan umarnanka gaskiya ne. Tun tuni na koyi daga farillanka cewa ka kafa su su kasance har abada. Ka dubi wahalata ka cece ni, gama ban manta da dokarka ba. Ka kāre manufata ka kuma fanshe ni, ka cece rai na kamar yadda ka alkawarta! Ceto yana nesa da mugaye, gama ba sa neman ƙa’idodinka. Tausayinka da girma yake, ya Ubangiji; ka kiyaye raina bisa ga dokokinka. Maƙiya masu yawa ne suke tsananta mini, amma ban rabu da farillanka ba. Na dubi marasa aminci da ƙyama, gama ba sa yin biyayya da maganarka. Dubi yadda nake ƙaunar farillanka; ka kiyaye raina, ya Ubangiji, bisa ga ƙaunarka. Dukan maganganunka gaskiya ne; dukan dokokinka masu adalci madawwami ne. Masu mulki suna tsananta mini ba dalili, amma zuciyata na rawan jiki game da maganarka. Ina farin ciki da alkawarinka kamar yadda wani kan sami ganima mai girma. Na ƙi ina kuma ƙyamar ƙarya amma ina ƙaunar dokarka. Sau bakwai a rana ina yabonka saboda dokokinka masu adalci. Waɗanda suke ƙaunar dokarka suna da babban salama, kuma babu abin da zai sa su yi tuntuɓe. Ina jiran cetonka, ya Ubangiji, ina kuma bin umarnanka. Ina biyayya da farillanka, gama ina ƙaunarsu ƙwarai. Ina biyayya da farillanka da kuma koyarwarka, gama dukan hanyoyina sanannu ne gare ka. Bari kukata ta zo gare ka, ya Ubangiji; ka ba ni ganewa bisa ga maganarka. Bari roƙona yă zo gabanka; ka cece ni bisa ga alkawarinka. Bari leɓunana su cika da yabonka, gama ka koya mini ƙa’idodinka. Bari harshena yă rera game da maganarka, gama dukan umarnanka masu adalci ne. Bari hannunka yă kasance a shirye don yă taimake ni, gama na zaɓi farillanka. Ina marmarin cetonka, ya Ubangiji, dokarka kuwa ita ce farin cikina. Bari in rayu don in yabe ka, bari kuma dokokinka su raya ni. Na kauce kamar ɓatacciyar tunkiya. Ka nemi bawanka, gama ban manta da umarnanka ba. Na yi kira ga Ubangiji cikin damuwata, ya kuwa amsa mini. Ka cece ni, ya Ubangiji, daga leɓuna masu ƙarya da kuma daga harsuna masu yaudara. Me zai yi maka, me kuma ya fi, ya kai harshe mai yaudara? Zai hukunta ku da kibiyoyi masu tsini na jarumi, tare da garwashin wuta na itacen tsintsiya. Kaitona da nake zama a Meshek, da nake zama a ciki tentunan Kedar! Da daɗewa na zauna a cikin waɗanda suke ƙin salama. Ni mutum ne mai salama; amma sa’ad da na yi magana, su sai su yi ta yaƙi. Na tā da idanuna zuwa wajen tuddai, ta ina ne taimakona zai zo? Taimakona zai zo daga wurin Ubangiji, wanda ya kafa sama da ƙasa. Ba zai bari ƙafarka tă yi santsi ba, shi da yake tsaronka ba zai yi gyangyaɗi ba; tabbatacce, shi da yake tsaron Isra’ila ba ya gyangyaɗi ko barci. Ubangiji yana tsaronka, Ubangiji ne inuwa a hannun damanka; rana ba za tă buge ka cikin yini ba balle wata da dare. Ubangiji zai kiyaye ka daga dukan masifa, zai tsare ranka; Ubangiji zai kiyaye shigarka da fitarka yanzu da har abada kuma. Na yi farin ciki tare da waɗanda suka ce da ni, “Bari mu tafi gidan Ubangiji.” Ƙafafunmu suna tsaye a ƙofofinki, ya Urushalima. An gina Urushalima kamar birnin da aka yi a harhaɗe wuri guda. A can ne kabilu suke haurawa, kabilan Ubangiji, don su yabi sunan Ubangiji bisa ga farillan da aka ba wa Isra’ila. A can kursiyoyin shari’a yake tsaye, kursiyoyin gidan Dawuda. Ku yi addu’a don salamar Urushalima, “Bari waɗanda suke ƙaunarki su zauna lafiya. Bari salama ta kasance a katangarki zaman lafiya kuma a fadodinki.” Saboda ’yan’uwana da kuma abokaina, zan ce, “Salama tă kasance tare da ke.” Saboda gidan Ubangiji Allahnmu, zan nemi wadatarki. Na tā da idanuna gare ka, gare ka da kursiyinka yake cikin sama. Kamar yadda idanun bayi suna duban hannun maigidansu, kamar yadda idanun baiwa suna duban hannun uwargijiyarta, haka idanunmu suna duban Ubangiji Allahnmu, sai ya nuna mana jinƙansa. Ka yi mana jinƙai, ya Ubangiji, ka yi mana jinƙai, gama mun jimre da reni mai yawa. Mun jimre da wulaƙanci daga masu girman kai, reni mai yawa daga masu fariya. Da ba don Ubangiji ya kasance a gefenmu ba, bari Isra’ila yă ce, da ba don Ubangiji ya kasance a gefenmu ba sa’ad da aka auka mana, sa’ad da fushinsu ya ƙuna a kanmu, ai, da sun haɗiye mu da rai; da rigyawa ta kwashe mu, da ambaliya ta rufe mu. Da ruwa mai hauka ya share mu ƙaf. Yabo ya tabbata ga Ubangiji, wanda bai bari aka yayyage mu da haƙoransu ba. Mun tsira kamar tsuntsu daga tarkon mai farauta; an tsinke tarko, muka kuwa tsira. Taimakonmu yana a sunan Ubangiji, Wanda ya yi sama da ƙasa. Waɗanda suke dogara ga Ubangiji suna kama da Dutsen Sihiyona, wanda ba ya jijjiguwa amma dawwammame ne har abada. Kamar duwatsun da sun kewaye Urushalima, haka Ubangiji ya kewaye mutanensa yanzu da har abada kuma. Sandar mulkin mugaye ba zai ci gaba da kasance a kan ƙasar da take rabon adalai ba, domin kada masu adalci su yi amfani da hannuwansu su aikata mugunta. Ka yi alheri, ya Ubangiji, ga waɗanda suke nagartattu, ga waɗanda suke masu aikata gaskiya a zuciyarsu. Amma waɗanda suka juye ga karkatattun hanyoyi Ubangiji zai kore su tare da masu aikata mugunta. Salama tă kasance tare da Isra’ila. Sa’ad da Ubangiji ya dawo da kamammu zuwa Sihiyona, mun kasance kamar mutanen da suka yi mafarki. Bakunanmu sun cika da dariya, harsunanmu da waƙoƙin farin ciki. Sai ana faɗi a cikin al’ummai, “ Ubangiji ya aikata manyan abubuwa dominsu.” Ubangiji ya aikata manyan abubuwa dominmu, mun kuwa cika da farin ciki. Ka maido da wadatarmu, ya Ubangiji kamar rafuffuka a Negeb. Waɗanda suka yi shuka da hawaye za su yi girbi da waƙoƙin farin ciki. Shi da ya fita yana kuka, riƙe da iri don shuki, zai dawo da waƙoƙin farin ciki, ɗauke da dammuna. In ba Ubangiji ne ya gina gida ba, masu gininta suna wahala a banza ne. In ba Ubangiji ne yake tsaron birni ba, masu tsaro suna yin tsaro a banza. Banza ne ka farka da wuri ka koma da latti, kana fama don abincin da za ka ci, gama yakan ba da barci ga waɗanda yake ƙauna. ’Ya’ya maza gādo ne daga Ubangiji, yara lada ne daga gare shi. Kamar kibiyoyi a hannun jarumi haka ’ya’ya mazan da aka haifa wa mutum a ƙuruciya. Mai albarka ne mutumin da korinsa sun cika da su. Ba za a kunyata su ba sa’ad da suke ƙarawa da abokan gābansu a ɗakin shari’a. Masu albarka ne dukan masu tsoron Ubangiji, waɗanda suke tafiya a hanyoyinsa. Za ka ci amfanin aikinka; albarku da wadata za su zama naka. Matarka za tă zama kamar kuringar inabi mai ’ya’ya a cikin gidanka; ’ya’yanka maza za su zama kamar tohon zaitun kewaye da teburinka. Ta haka mai albarka yake wanda yake tsoron Ubangiji. Bari Ubangiji ya albarkace ka daga Sihiyona dukan kwanakin ranka; bari ka ga wadatar Urushalima, bari kuma ka rayu ka ga ’ya’ya ’ya’yanka. Salama tă kasance tare da Isra’ila. Sun yi mini danniya ƙwarai tun ina ƙarami, bari Isra’ila yă ce, sun yi mini danniya ƙwarai tun ina ƙarami, amma ba su yi nasara a kaina ba. Manoma sun nome bayana suka yi kunyoyinsu da tsayi. Amma Ubangiji mai adalci ne; ya ’yantar da ni daga igiyoyin mugaye. Bari dukan waɗanda suke ƙin Sihiyona a juye da su baya da kunya. Bari su zama kamar ciyawa a kan rufi, wadda takan bushe kafin tă yi girma; da ita mai girbi ba ya iya cika hannuwansa, balle wanda yake tarawa yă cika hannuwansa. Kada masu wuce su ce, “Albarkar Ubangiji ta kasance a kanku; muna sa muku albarka a cikin sunan Ubangiji.” Daga cikin zurfafa na yi kuka gare ka, ya Ubangiji; Ya Ubangiji, ka ji muryata. Bari kunnuwanka su saurara ga kukata ta neman jinƙai. In kai, ya Ubangiji, za ka lissafta zunubai, Ya Ubangiji, wa zai tsaya? Amma tare da kai akwai gafartawa, saboda haka ake tsoronka. Zan jira Ubangiji, raina zai jira, kuma a cikin maganarsa na sa zuciyata. Raina na jiran Ubangiji fiye da yadda mai tsaro yakan jira safiya, fiye da yadda mai tsaro yakan jira safiya. Ya Isra’ila, sa zuciya ga Ubangiji, gama tare da Ubangiji akwai ƙauna marar ƙarewa kuma tare da shi akwai cikakkiyar fansa. Shi kansa zai fanshi Isra’ila daga dukan zunubansu. Zuciyata ba mai girman kai ba ce, ya Ubangiji, idanuna ba sa fariya; ban dami kaina da manyan al’amura ba ko abubuwan da suka sha ƙarfina. Amma na haƙura na kuma kwantar da raina; kamar yaron da aka yaye tare da mahaifiyarsa, kamar yaron da aka yaye haka raina yake a cikina. Ya Isra’ila, sa zuciyarka ga Ubangiji yanzu da har abada kuma. Ya Ubangiji, ka tuna da Dawuda da kuma dukan irin wuyan da ya jimre. Ya yi rantsuwa ga Ubangiji ya kuma yi alkawari ga Maɗaukaki na Yaƙub cewa, “Ba zan shiga gidana ko in kwanta a gado ba, ba zan ba wa idanuna barci ba, ba gyangyaɗi wa idanuna, sai na sami wuri wa Ubangiji, mazauni domin Maɗaukaki na Yaƙub.” Mun ji haka a Efrata, muka yi ƙaro da shi a filayen Ya’ar, “Bari mu tafi wurin zamansa; bari mu yi sujada a wurin sa ƙafafunsa, ka tashi, ya Ubangiji, ka kuma zo wurin hutunka, kai da akwatin alkawarin ƙarfinka. Bari a suturta firistocinka da adalci; bari tsarkakanka su rera don farin ciki.” Saboda Dawuda bawanka, kada ka ƙi shafaffenka. Ubangiji ya rantse wa Dawuda tabbataccen rantsuwa cewa ba zai janye ba cewa, “Ɗaya daga cikin zuriyarka zan sa a kan kursiyinka, in ’ya’yanka maza za su kiyaye alkawari da farillan da na koya musu, to ’ya’yansu maza za su zauna a kan kursiyinka har abada abadin.” Gama Ubangiji ya zaɓi Sihiyona, ya so ta zama mazauninsa, “Wannan shi ne wurin hutuna har abada abadin; a nan zan zauna ina mulki gama ina son ta, zan albarkace ta da tanade-tanade masu yawa; matalautanta za su ƙoshi da abinci. Zan suturta firistocinta da ceto, tsarkakanta kuma kullum za su rera don farin ciki. “A nan zan sa ƙaho ya yi girma wa Dawuda in kuma kafa fitila saboda shafaffena. Zan suturta abokan gābansa da kunya, amma rawanin da yake a kansa zai yi ta walƙiya.” Abu mai kyau ne, mai daɗi kuma sa’ad da ’yan’uwa suna zaman lafiya! Yana kamar mai mai darajar da aka zuba a kai, yana gangarawa a gemu, yana gangarawa a gemun Haruna, har zuwa wuyan rigunansa. Yana kamar raɓar Hermon da take zubowa a kan Dutsen Sihiyona. Gama a can Ubangiji ya tabbatar da albarkarsa, har ma rai na har abada. Yabi Ubangiji, dukanku bayin Ubangiji waɗanda kuke hidima da dare a gidan Ubangiji. Ku tā da hannuwanku a cikin wurinsa mai tsarki ku kuma yabi Ubangiji. Bari Ubangiji, Mahaliccin sama da ƙasa, ya albarkace ku daga Sihiyona. Yabi Ubangiji. Yabi sunan Ubangiji; yabe shi, ku bayin Ubangiji, ku waɗanda kuke hidima a gidan Ubangiji, cikin filayen gidan Allahnmu. Yabi Ubangiji, gama Ubangiji nagari ne; rera yabo ga sunansa, gama wannan yana da kyau. Gama Ubangiji ya zaɓi Yaƙub ya zama nasa, Isra’ila ya zama mallakarsa mai daraja. Na san cewa Ubangiji yana da girma, cewa shugabanmu ya fi dukan alloli girma. Ubangiji yana yin abin da ya ga dama, a sammai da kuma a duniya, cikin tekuna da kuma cikin dukan zurfafansu. Yakan sa gizagizai su taso daga iyakokin duniya; yakan aika da walƙiya tare da ruwan sama ya fito da iska daga ɗakunan ajiyarsa. Ya kashe ’ya’yan fari na Masar, ’ya’yan fari na mutane da na dabbobi. Ya aiko da alamu da abubuwan banmamaki a tsirkiyarku, ya Masar, a kan Fir’auna da kuma dukan bayinsa. Ya bugi al’ummai masu yawa ya kuma karkashe manyan sarakuna, Sihon sarkin Amoriyawa, Og sarkin Bashan da kuma dukan sarakunan Kan’ana, ya kuma ba da ƙasarsa kamar abin gādo, abin gādo ga mutanensa Isra’ila. Sunanka, ya Ubangiji, dawwammame ne har abada, sanin da aka yi maka, ya Ubangiji, yana nan cikin dukan zamanai. Gama Ubangiji zai nuna cewa mutanensa ba su da laifi ya kuma ji tausayin bayinsa. Gumakan al’ummai azurfa ne da zinariya, da hannuwan mutane suka yi. Suna da bakuna, amma ba sa magana, idanu, amma ba sa gani; suna da kunnuwa, amma ba sa ji, ba kuwa numfashi a bakunansu. Waɗanda suka yi su za su zama kamar su, haka kuma zai zama da dukan waɗanda suke dogara gare su. Ya gidan Isra’ila, yabi Ubangiji; Ya gidan Haruna, yabi Ubangiji; Ya gidan Lawi, yabi Ubangiji; ku da kuke tsoronsa, yabi Ubangiji. Yabo ya tabbata ga Ubangiji daga Sihiyona, gare shi wanda yake zama a Urushalima. Yabi Ubangiji. Ku yi godiya ga Ubangiji, gama nagari ne shi. Ƙaunarsa madawwamiya ce. Ku yi godiya ga Allahn alloli. Ƙaunarsa madawwamiya ce. Ku yi godiya ga Ubangijin iyayengiji. Ƙaunarsa madawwamiya ce. Gare shi wanda shi kaɗai yake aikata abubuwan banmamaki, Ƙaunarsa madawwamiya ce. Wanda ta wurin ganewarsa ya yi sammai, Ƙaunarsa madawwamiya ce. Wanda ya shimfiɗa duniya a kan ruwaye, Ƙaunarsa madawwamiya ce. Wanda ya yi manyan haskoki, Ƙaunarsa madawwamiya ce. Rana don tă yi mulkin yini, Ƙaunarsa madawwamiya ce. Wata da taurari kuma don su yi mulkin dare; Ƙaunarsa madawwamiya ce. Gare shi wanda ya kashe ’ya’yan fari Masar Ƙaunarsa madawwamiya ce. Ya kuma fitar da Isra’ila daga cikinsu Ƙaunarsa madawwamiya ce. Da hannu mai ƙarfi da hannu mai iko; Ƙaunarsa madawwamiya ce. Gare shi wanda ya raba Jan Teku biyu Ƙaunarsa madawwamiya ce. Ya kawo Isra’ila ta tsakiyarsa, Ƙaunarsa madawwamiya ce. Amma ya share Fir’auna da mayaƙansa cikin Jan Teku; Ƙaunarsa madawwamiya ce. Gare shi wanda ya bi da mutanensa cikin hamada, Ƙaunarsa madawwamiya ce. Wanda ya buge manyan sarakuna, Ƙaunarsa madawwamiya ce. Ya karkashe manyan sarakuna, Ƙaunarsa madawwamiya ce. Sihon sarkin Amoriyawa Ƙaunarsa madawwamiya ce. Da kuma Og sarkin Bashan, Ƙaunarsa madawwamiya ce. Ya kuma ba da ƙasarsu gādo, Ƙaunarsa madawwamiya ce. Gādo ga bawansa Isra’ila; Ƙaunarsa madawwamiya ce. Shi wanda ya tuna da mu cikin ƙasƙancinmu Ƙaunarsa madawwamiya ce. Ya kuma ’yantar da mu daga abokan gābanmu, Ƙaunarsa madawwamiya ce. Wanda kuma ke ba da abinci ga kowace halitta. Ƙaunarsa madawwamiya ce. Ku yi godiya ga Allah na sama. Ƙaunarsa madawwamiya ce. A bakin kogunan Babilon muka zauna muka yi kuka sa’ad da muka tuna da Sihiyona. A can a kan rassan itatuwa muka rataye garayunmu, gama a can masu kamunmu suka sa mu yi waƙoƙi, masu ba mu azaba suka nema waƙoƙin farin ciki; suka ce, “Ku rera mana ɗaya daga cikin waƙoƙin Sihiyona!” Yaya za mu rera waƙoƙin Ubangiji a baƙuwar ƙasa? In na manta da ke, ya Urushalima, bari hannuna na dama manta da iyawarsa. Bari harshena yă manne wa rufin bakina in ban tuna da ke ba, in ban so Urushalima farin cikin mafi girma ba. Ka tuna, ya Ubangiji, abin da mutanen Edom suka yi a ranar da Urushalima ta fāɗi. Suka yi ihu suka ce, “A ragargaza ta, A ragargaza ta har tushenta!” Ya Diyar Babilon, an ƙaddara ke zuwa hallaka, mai farin ciki ne wanda ya sāka miki saboda abin da kika yi mana, shi da ya ƙwace jariranki ya fyaɗa su a kan duwatsu. Zan yabe ka, ya Ubangiji, da dukan zuciyata; a gaban “alloli” zan rera yabo. Zan rusuna ta wajen haikalinka mai tsarki zan kuma yabi sunanka saboda ƙaunarka da amincinka, saboda ka ɗaukaka a bisa kome sunanka da kuma maganarka. Sa’ad da na kira, ka amsa mini; ka sa na zama mai ƙarfin hali ka kuma ƙarfafa ni. Bari dukan sarakunan duniya su yabe ka, ya Ubangiji, sa’ad da suka ji maganganun bakinka. Bari su rera game da hanyoyin Ubangiji, gama ɗaukakar Ubangiji da girma take. Ko da yake Ubangiji yana bisa, yakan dubi kāsassu, amma tun da nesa ya san masu girman kai. Ko da na yi tafiya a tsakiyar wahala, kana kiyaye raina; ka miƙa hannunka a kan fushin maƙiyana, da hannunka na dama ka cece ni. Ubangiji zai cika manufarsa a kaina; ƙaunarka, ya Ubangiji, madawwamiya ce har abada, kada ka ƙyale ayyukan hannuwanka. Ya Ubangiji, ka bincike ni ka kuwa san ni. Ka san sa’ad da na zauna da sa’ad da na tashi; ka san tunanina daga nesa. Ka san fitata da kuma kwanciyata; ka saba da dukan hanyoyina. Kafin in yi magana da harshena ka santa gaba ɗaya, ya Ubangiji. Ka kewaye ni, gaba da baya; ka sa hannunka a kaina. Irin wannan sanin game da ni ya fi ƙarfin magana, ya fi ƙarfi in gane. Ina zan tafi daga Ruhunka? Ina zan gudu in tafi daga gabanka? In na haura zuwa sammai, kana a can; in na yi gado a zurfafa, kana a can. In na tashi a fikafikan safiya, in na sauka a gefe mai nisa na teku, can ma hannunka zai bishe ni, hannunka na dama zai riƙe ni gam. In na ce, “Tabbatacce duhu zai ɓoye ni haske kuma zai zama dare kewaye da ni,” duhu ma ba zai zama duhu gare ka ba; dare zai haskaka kamar rana, gama duhu ya yi kamar haske gare ka. Gama ka halicci ciki-cikina; ka gina ni gaba ɗaya a cikin mahaifar mahaifiyata. Ina yabonka domin yadda ka yi ni abin tsoro ne da kuma abin mamaki; ayyukanka suna da banmamaki, na san da haka sosai. Ƙasusuwana ba a ɓoye suke a gare ka ba sa’ad da aka yi ni asirce. Sa’ad da saƙa ni gaba ɗaya a zurfafan duniya. Idanunka sun ga jikina marar fasali; dukan kwanakin da aka tsara mini a rubuce suke a littafinka kafin ɗayansu yă kasance. Tunaninka suna da daraja gare ni, ya Allah! Yawansu ba su da iyaka! A ce zan iya ƙirgansu, za su fi yashin teku yawa. Sa’ad da na farka, ina nan tare da kai har yanzu. Da kawai za ka kashe mugaye, ya Allah! Ku rabu da ni, ku masu kisankai! Suna magana game da kai da mugun nufi; maƙiyanka suna ɗaukan sunanka a banza. Ba ina ƙin masu ƙinka ba, ya Ubangiji, ina kuma ƙyamar waɗanda suke tayar maka ba? Ba ni da wani abu da nake musu sai kiyaye kawai; na ɗauke su abokan gābana. Ka bincike ni, ya Allah ka kuma san zuciyata; ka gwada ni ka kuma san damuwata. Duba ko akwai wani laifi a cikina, ka bishe ni a madawwamiyar hanya. Ka cece ni, ya Ubangiji, daga mugaye; ka tsare ni daga mutane masu rikici, masu shirya maƙarƙashiya a zukatansu suna kuma kawo yaƙi kullum. Suna sa harsunansu su yi kaifi kamar na maciji; dafin gamsheƙa yana a leɓunansu. Ka kiyaye ni, ya Ubangiji, daga hannuwan mugaye; ka tsare ni daga mutane masu rikici waɗanda suke shirin kwashe ni a ƙafafu. Masu girman kai sun sa mini tarko; sun shimfiɗa igiyoyin ragarsu sun kuma shirya mini tarko a hanyata. Ya Ubangiji, na ce maka, “Kai ne Allahna.” Ka ji kukata ta neman jinƙai, ya Ubangiji. Ya Ubangiji Mai Iko Duka, mai fansana mai ƙarfi, wanda yake garkuwoyin kaina a ranar yaƙi. Kada ka biya wa mugaye bukatunsu, ya Ubangiji; kada ka bar shirinsu su yi nasara, in ba haka ba za su yi fariya. Bari kawunan waɗanda suka kewaye ni su rufu da masifun da leɓunansu suka jawo. Bari garwashin wuta yă zubo a kansu; bari a jefar da su cikin wuta, cikin rami mai zurfi, kada su sāke tashi. Kada masu ɓata suna su taɓa kahu a ƙasar; bari masifa ta farauci mutane masu rikici. Na san cewa Ubangiji ya shirya wa matalauta adalci yana kuma yi wa mabukata adalci. Tabbatacce masu adalci za su yabi sunanka masu aikata gaskiya kuma za su zauna a gabanka. Na yi kira gare ka, ya Ubangiji; ka zo da sauri. Ka ji muryata sa’ad da na yi kira. Bari a sa addu’ata a gabanka kamar turaren ƙonawa; bari ɗagawa hannuwana ta zama kamar hadayar yamma. Ka sa mai tsaro a bakina, ya Ubangiji; ka yi tsaron ƙofar leɓunana. Kada ka bar zuciyata ta juya ga yin abin da yake mugu, ta sa kai ga aikata mugayen ayyuka tare da mutane masu aikata mugunta; kada ka bari in ci abincinsu. Bari mutum mai adalci yă buge ni, alheri ne; bar shi yă tsawata mini, mai ne a kaina. Kaina ba zai ƙi shi ba, duk da haka addu’ata kullum tana gāba da mugayen ayyuka. Za a jefar da masu mulkinsu ƙasa daga ƙwanƙolin dutse, mugaye kuwa za su san cewa maganata daidai ne. Za su ce, “Kamar yadda mutum kan yi huda yă tsage ƙasa, haka aka watsar da ƙasusuwanmu a bakin kabari.” Amma na kafa idanuna a kanka, ya Ubangiji Mai Iko Duka; a cikinka ina neman mafaka, kada ka miƙa ni ga mutuwa. Ka kiyaye ni daga tarkon da aka sa mini, daga tarkon da mugaye suka sa. Bari mugaye su fāɗa a cikin ragarsu, amma bari ni in zo in wuce lafiya. Na yi kuka mai ƙarfi ga Ubangiji; na tā da muryata ga Ubangiji neman jinƙai. Na kawo gunagunina a gabansa; a gabansa na faɗa wahalata. Sa’ad da ƙarfina ya kāre a cikina, kai ne wanda ya san hanyata. A hanyar da nake tafiya mutane sun kafa mini tarko. Duba ta damata ka gani; babu wanda ya kula da ni. Ba ni da mafaka; babu wanda ya kula da raina. Na yi kuka gare ka, ya Ubangiji; Na ce, “Kai ne mafakata, rabona a ƙasar masu rai.” Ka saurari kukata, gama ina cikin matsananciyar bukata; ka cece ni daga waɗanda suke fafarata, gama sun fi ni ƙarfi sosai. Ka ’yantar da ni daga kurkuku, don in yabi sunanka. Ta haka masu adalci za su taru kewaye da ni saboda alherinka gare ni. Ya Ubangiji, ka ji addu’ata, ka saurari kukata don neman jinƙai; cikin amincinka da adalcinka ka amsa mini. Kada ka gabatar da bawanka a gaban shari’a, gama babu wani mai rai da yake adali a gabanka. Abokin gāba yana fafarata, ya murƙushe ni har ƙasa; ya sa ina zama a cikin duhu kamar waɗanda suka mutu tun tuni. Ta haka ƙarfina ya ƙare a cikina zuciyata ta damu ƙwarai. Na tuna da kwanakin baya na yi tunani a kan dukan ayyukanka na kuma lura da abin da hannuwanka suka yi. Na buɗe hannuwana gare ka; raina yana jin ƙishinka kamar busasshiyar ƙasa. Ka amsa mini da sauri, ya Ubangiji; ƙarfina ya ƙare. Kada ka ɓoye fuskarka daga gare ni in ba haka ba zan zama kamar waɗanda suka gangara zuwa rami. Bari safiya ta kawo mini maganar ƙaunarka marar ƙarewa, gama na sa zuciyata a gare ka. Ka nuna mini hanyar da zan bi, gama a gare ka na miƙa raina. Ka cece ni daga abokan gābana, ya Ubangiji, gama na ɓoye kaina a gare ka. Ka koya mini in yi nufinka, gama kai ne Allahna; bari nagarin Ruhunka yă bi da ni a ƙasar da ba gargaɗa. Saboda sunanka, ya Ubangiji, ka kiyaye raina; a cikin adalcinka, ka fid da ni daga wahala. A cikin ƙaunarka marar ƙarewa, ka rufe bakunan abokan gābana; ka hallaka dukan maƙiyana, gama ni bawanka ne. Yabo ya tabbata ga Ubangiji dutsena, wanda ya horar da hannuwana don yaƙi, yatsotsina don faɗa. Shi ne Allah mai ƙaunata da kuma kagarata, katangata da mai cetona, garkuwata, wanda nake neman mafaka daga gare shi, wanda ya sa mutane a ƙarƙashina. Ya Ubangiji, wane ne mutum da ka kula da shi, ɗan mutum da har za ka yi tunaninsa? Mutum yana kama da numfashi; kwanakinsa suna wucewa kamar inuwa. Ka tsage sammanka, ya Ubangiji, ka sauko; ka taɓa duwatsu, domin su yi hayaƙi. Ka aiko da walƙiya ka watsar da abokan gāba; ka karɓa kibiyoyinka ka sa su gudu. Ka miƙa hannunka daga bisa; ka cece ni ka kuma kuɓutar da ni daga manyan ruwaye, daga hannuwan baƙi waɗanda bakunansu sun cika da ƙarya, waɗanda hannuwansu na dama masu ruɗu ne. Zan rera sabuwar waƙa gare ka, ya Allah; a kan molo mai tsirkiya goma zan yi maka kiɗi, ga Wannan wanda yake ba wa sarakuna nasara, wanda ya cece bawansa Dawuda. Daga takobin kisa. Ka cece ni ka kuma kuɓutar da ni daga hannuwan baƙi waɗanda bakunansu sun cika da ƙarya, waɗanda hannuwansu na dama masu ruɗu ne. Ta haka ’ya’yanmu maza a ƙuruciyarsu za su zama kamar tsire-tsiren da aka kula da su, ’ya’yanmu mata kuma za su zama kamar ginshiƙai da sassaƙa don adon fada. Rumbunanmu za su cika da kowane irin tanadi. Tumakinmu za su ƙaru ninki dubu, ninki dubu goma-goma a filayenmu; shanunmu za su ja kaya masu nauyi. Ba za a sami tashin hankali a katangarmu ba, ba zuwan zaman bauta, ba jin kukan damuwa a titunanmu. Masu albarka ne mutanen da wannan zai zama haka; masu albarka ne mutanen da Allah ne Ubangiji. Zan ɗaukaka ka, ya Allahna, Sarki; zan yabi sunanka har abada abadin. Kowace rana zan yabe ka in kuma ɗaukaka sunanka har abada abadin. Ubangiji da girma yake ya kuma cancanci yabo girmansa ya fi ƙarfin ganewar mutum. Tsara guda za tă yi maganar ayyukanka ga wata tsara; za su yi magana game da manyan ayyukanka. Za su yi zancen ɗaukakarka mai daraja, zan kuma yi tunani a kan ayyukanka masu banmamaki. Za su yi magana game da ikon ayyukanka masu bantsoro, zan kuma yi shelar manyan ayyukanka. Za su yi bikin yalwar alherinka suka kuma rera adalcinka da farin ciki. Ubangiji mai alheri da kuma tausayi, mai jinkirin fushi cike kuma da ƙauna. Ubangiji nagari ne ga duka; yana tausayin dukan abubuwan da ya yi. Dukan abubuwan da ka yi za su yabe ka, ya Ubangiji; tsarkakanka za su ɗaukaka ka. Za su yi maganar ɗaukakar mulkinka za su kuma yi zancen ikonka, saboda dukan mutane su san manyan ayyukanka da ɗaukakar darajar mulkinka. Mulkinka madawwamin mulki ne, sarautarka kuma za tă dawwama cikin dukan zamanai. Ubangiji mai aminci ne ga dukan alkawuransa mai ƙauna kuma ga dukan abubuwan da ya yi. Ubangiji yana riƙe da dukan waɗanda suka faɗi yana kuma ɗaga dukan waɗanda aka rusunar da su ƙasa. Idanun kowa yana dogara gare ka, kana kuma ba su abincinsu a lokacin da ya dace. Ka buɗe hannunka ka kuma ƙosar da sha’awar kowane abu mai rai. Ubangiji mai adalci ne cikin dukan hanyoyinsa yana kuma nuna ƙauna ga dukan abubuwan da ya yi. Ubangiji yana kusa da kowa da ya kira gare shi, ga duk wanda ya kira gare shi cikin gaskiya. Yakan cika sha’awar waɗanda suke tsoronsa; yakan ji kukansu yă kuma cece su. Ubangiji yakan lura da dukan waɗanda suke ƙaunarsa, amma dukan mugaye zai hallaka su. Bakina zai yi magana cikin yabon Ubangiji. Bari kowace halitta ta yabi sunansa mai tsarki har abada abadin. Yabi Ubangiji. Yabi Ubangiji, ya raina. Zan yabi Ubangiji dukan kwanakina; zan rera yabo ga Allahna muddin raina. Kada ka sa zuciyarka ga sarakuna, ga mutane masu mutuwa, waɗanda ba sa iya ceto. Sa’ad da numfashinsu ya rabu da su sai su koma ƙasa; a wannan rana shirye-shiryensu sun zama banza. Mai albarka ne wanda Allah na Yaƙub ne taimakonsa, wanda sa zuciyarsa yana a kan Ubangiji Allahnsa. Mahaliccin sama da ƙasa, teku, da kome da yake cikinsu, Ubangiji, wanda yake mai aminci har abada. Yakan biya bukatun mutanen da aka danne ya kuma ba da abinci ga mayunwata. Ubangiji yakan ’yantar da ’yan kurkuku, Ubangiji yakan ba wa makafi ido, Ubangiji yakan ɗaga waɗanda aka rusunar da su ƙasa, Ubangiji yana ƙaunar masu adalci. Ubangiji yana tsaron baƙi yana kuma lura da marayu da kuma gwauruwa, amma yakan lalatar da hanyoyin mugaye. Ubangiji yana mulki har abada, Allahnki, ya Sihiyona, daga zamani zuwa zamani. Yabi Ubangiji. Yabi Ubangiji. Yana da kyau a rera yabai ga Allahnmu, abu mai daɗi ne daidai ne kuma a yabe shi! Ubangiji ya gina Urushalima; ya tattara kamammu na Isra’ilan da aka kai bauta. Ya warkar da masu raunanar zuciya ya ɗaɗɗaura miyakunsu. Ya lissafta yawan taurari ya kuma kira kowannensu da suna. Shugabanmu mai girma ne mai iko duka; ganewarsa ba shi da iyaka. Ubangiji yana kula da masu sauƙinkai yakan yar da mugaye a ƙasa. Rera wa Ubangiji waƙar godiya; ku kada garaya ga Allahnmu. Ya rufe sararin sama da gizagizai; yana tanada wa duniya ruwan sama yana kuma sa ciyawa tă yi girma a kan tuddai. Yakan tanada wa shanu abinci da kuma saboda ’ya’yan hankaki sa’ad da suka yi kira. Jin daɗinsa ba ya a ƙarfin doki, balle farin cikinsa yă kasance a ƙafafun mutum; Ubangiji yakan yi farin ciki a waɗanda suke tsoronsa, waɗanda suke sa zuciya a ƙaunarsa marar ƙarewa. Ki ɗaukaka Ubangiji, ya Urushalima; ki yabi Allahnki, ya Sihiyona. Gama yana ƙarfafa ƙyamaren ƙofofinki yana kuma albarkace mutanenki a cikinki. Yana ba da salama ga iyakokinki yana kuma ƙosar da ke da alkama mafi kyau. Yana ba da umarninsa ga duniya; maganarsa tana tafiya da sauri. Yana shimfiɗa ƙanƙara kamar ulu yă kuma watsar da hazo kamar toka. Yana zuba ƙanƙara kamar ƙananan duwatsu. Wa zai iya jure wa sanyin da ya aiko? Yakan aiki maganarsa ta kuwa narkar da su; yakan tā da iskarsa, ruwaye kuwa su gudu. Ya bayyana maganarsa ga Yaƙub, dokokinsa da ƙa’idodinsa ga Isra’ila. Bai yi wannan ga wata al’umma ba; ba su san dokokinsa ba. Yabi Ubangiji. Yabi Ubangiji. Yabi Ubangiji daga sammai, yabe shi a bisa sammai. Yabe shi, dukanku mala’ikunsa, yabe shi, dukanku rundunarsa na sama. Yabe shi, rana da wata, yabe shi, dukanku taurari masu haskakawa. Yabe shi, ku bisa sammai da kuma ku ruwan bisa sarari. Bari su yabi sunan Ubangiji, gama ya umarta aka kuwa halicce su. Ya sa su a wurarensu har abada abadin; ya ba da umarnin da ba zai taɓa shuɗe ba. Yabi Ubangiji daga duniya, ku manyan halittun teku da kuma dukan zurfafan teku, walƙiya da ƙanƙara, dusar ƙanƙara da gizagizai, hadirin iskar da suke biyayya da umarnansa, ku duwatsu da dukan tuddai, itatuwa masu ’ya’ya da dukan al’ul, namun jeji da dukan dabbobin gida, ƙanana halittu da tsuntsaye masu firiya, sarakunan duniya da dukan al’ummai, ku sarakuna da dukan masu mulkin duniya, samari da ’yan mata, tsofaffi da yara. Bari su yabi sunan Ubangiji, gama sunansa ne kaɗai mafi ɗaukaka; darajarsa ta fi ƙarfin duniya da sammai. Ya tayar wa mutanensa ƙaho, yabon dukan tsarkakansa, na Isra’ila, mutanen da suke kurkusa da zuciyarsa. Yabi Ubangiji. Yabi Ubangiji. Ku rera sabuwar waƙa ga Ubangiji, yabonsa a cikin taron tsarkaka. Bari Isra’ila su yi farin ciki da Mahaliccinsu; bari mutanen Sihiyona su yi murna da Sarkinsu. Bari su yabi sunansa tare da rawa suna kuma yin kiɗi gare shi da ganga da garaya. Gama Ubangiji yana jin daɗin mutanensa; yakan darjanta masu sauƙinkai da ceto. Bari tsarkaka su yi farin ciki a wannan bangirma su kuma rera don farin ciki a kan gadajensu. Bari yabon Allah yă kasance a bakunansu takobi mai kaifi kuma a hannuwansu, don su ɗau fansa a kan al’ummai da kuma hukunci a kan mutane, don su ɗaura sarakuna da sarƙoƙi, manyan garinsu da sarƙoƙin ƙarfe, don su yi hukuncin da aka rubuta a kansu. Wannan ne ɗaukakar dukan tsarkakansa. Yabi Ubangiji. Yabi Ubangiji. Yabi Allah a cikin wurinsa mai tsarki; yabe shi a cikin sammai na ikonsa. Yabe shi saboda ayyukansa masu iko; yabe shi saboda mafificin girmansa. Yabe shi da ƙarar kakaki, yabe shi da garaya da molo, yabe shi da ganga kuna taka rawa, yabe shi da kayan kiɗi na tsirkiya kuna kuma busa, yabe shi da kuge mai ƙara, yabe shi da kuge masu ƙara sosai. Bari kowane abu mai numfashi yă yabi Ubangiji. Yabi Ubangiji. Karin maganar Solomon ɗan Dawuda, sarkin Isra’ila. Ga karin magana da za su taimake ka don samun hikima da horo; don ganewa kalmomi masu zurfi; don neman rayuwa ta horo da kuma ta hankali, kana yin abin da yake daidai, mai adalci da kuma wanda ya dace; don sa marar azanci yă yi hankali, yă sa matasa su sani, su kuma iya rarrabewa, bari masu hikima su saurara, su kuma ƙara ga saninsu, bari masu tunani kuma su sami jagora, don su fahimci karin magana da kuma misalai, kalmomi da kuma kacici-kacici masu hikima. Tsoron Ubangiji shi ne masomin ilimi, amma wawaye sun rena hikima da horo. Ɗana, ka saurari umarnin mahaifinka kada kuma ka ƙyale koyarwar mahaifiyarka. Za su zama kayan ado don su inganta ka da kuma sarƙar wuya don su yi wa wuyanka ado. Ɗana, in masu zunubi sun jarabce ka, kada ka yarda. In suka ce, “Zo mu tafi; mu yi kwanton ɓauna, mu nemi wani mu kashe, mu fāɗa wa marasa laifi; mu haɗiye su da rai gaba ɗaya kamar kabari, kamar waɗanda suke gangarawa zuwa rami; za mu sami dukiya masu daraja iri-iri, mu kuma cika gidajenmu da ganima; ka haɗa kai da mu, za mu kuwa raba abin da muka sato” ɗana, kada ka tafi tare da su, kada ka taka ƙafarka a hanyarsu; gama ƙafafunsu kan yi sauri ga yin zunubi, suna saurin yin kisankai. Ba shi da amfani a kafa tarko a idanun dukan tsuntsaye! Waɗannan irin mutane kansu suke kafa wa tarko; ba sa kama kome, sai rayukansu! Dukan waɗanda suke neman ribar da ba a samu a hanya mai kyau; ƙarshen wannan yakan ɗauke rayukansu. Hikima tana kira da ƙarfi a kan titi, tana ɗaga muryarta a dandalin taron jama’a; tana kira da ƙarfi a kan tituna masu surutu, tana yin jawabinta a hanyoyin shiga gari. “Har yaushe ku da kuke marasa azanci za ku ci gaba a hanyoyinku marasa azanci? Har yaushe ku masu ba’a za ku yi ta murna cikin ba’arku wawaye kuma ku ƙi ilimi? Da a ce kun saurari tsawatata, da na faɗa muku dukan abin da yake zuciyata in kuma sanar da ku tunanina. Amma da yake kun ƙi ni sa’ad da na yi kira ba kuma wanda ya saurara sa’ad da na miƙa hannuna, da yake kun ƙi dukan shawarata ba ku kuma yarda da tsawatata ba, Zan yi muku dariya sa’ad da masifa ta same ku, zan yi muku ba’a sa’ad da bala’i ya same ku, sa’ad da bala’i ya sha kanku kamar hadiri, sa’ad da masifa ta share ku kamar guguwa, sa’ad damuwa da wahala suka mamaye ku. “Sa’an nan za su kira gare ni amma ba zan amsa ba; za su neme ni amma ba za su same ni ba. Da yake sun ƙi sani ba su kuwa zaɓi tsoron Ubangiji ba, da yake ba su karɓi shawarata ba suka kuwa yi kunnen ƙashi ga tsawatata, za su sami sakayyar abubuwan da suka yi su kuma ƙoshi da sakayyar makircinsu. Gama rashin hankalin marasa azanci zai kashe su, rashin kulawar wawaye kuma zai hallaka su; amma duk wanda ya saurare ni, zai zauna lafiya yă kuma kasance da rai kwance, ba tare da tsoron lahani ba.” Ɗana, in ka yarda da kalmomina ka kuma ajiye umarnaina a cikinka, kana kasa kunne ga abin da yake na hikima, kana kuma yin ƙoƙari ka fahimce shi, in kuma ka kira ga tsinkaya ka kuma kira da ƙarfi don ganewa, in ka neme shi yadda ake neman azurfa ka kuma neme shi kamar yadda ake neman ɓoyayyiyar dukiya, to, za ka gane tsoron Ubangiji ka kuma sami sanin Allah. Gama Ubangiji yana ba da hikima, daga bakinsa kuma, sani da ganewa sukan fito. Yana riƙe da nasara a ma’aji don masu yin gaskiya, shi ne mafaka ga waɗanda tafiyarsu ba ta da laifi, gama yana tsare abin da masu adalci suke bukata yana kuma tsare hanyar amintattunsa. Sa’an nan za ku fahimci abin da yake daidai da abin da yake na adalci da abin da yake gaskiya, da kowace hanya mai kyau. Gama hikima za tă shiga cikin zuciyarka, sani kuma zai faranta maka rai. Tsinkaya za tă tsare ka, ganewa kuma za tă yi maka jagora. Hikima za tă cece ka daga hanyoyin mugayen mutane, daga kalmomin mutane masu ɓatanci, waɗanda suke barin miƙaƙƙun hanyoyi don su yi tafiya a hanyoyi masu duhu, waɗanda suke jin daɗin yin abin da ba shi da kyau suna kuma farin ciki a mugayen ɓatanci, waɗanda hanyoyinsu karkatattu ne waɗanda kuma suke cuku-cuku a hanyoyinsu. Zai kiyaye ku kuma daga mazinaciya, daga mace mai lalata, mai ƙoƙarin kama ka da daɗin bakinta, wadda ta bar mijin ƙuruciyarta ta kuma ƙyale alkawarin da ta yi a gaban Allah. Gama gidanta yana kai ga mutuwa hanyarta kuma ga ruhohin matattu. Duk wanda ya ziyarce ta ba ya ƙara komowa ba zai ƙara komowa ga hanyar rai. Don haka dole ku yi tafiya a hanyoyin mutanen kirki ku kuma yi ta bi hanyoyin adalai. Gama masu aikata gaskiya za su zauna a cikin ƙasar, marasa laifi kuma za su kasance a cikinta; amma za a fid da mugaye daga ƙasar, za a tumɓuke marasa aminci kuma daga gare ta. Ɗana, kada ka manta da koyarwata, amma ka kiyaye umarnaina a cikin zuciyarka, gama za su ƙara maka tsawon rai da shekaru masu yawa su kuma kawo maka wadata. Kada ka bar ƙauna da aminci su rabu da kai; ka ɗaura su kewaye da wuyanka, ka rubuta su a allon zuciyarka. Sa’an nan za ka sami tagomashi da kuma suna mai kyau a gaban Allah da kuma a gaban mutane. Ka dogara ga Ubangiji da dukan zuciyarka kada kuma ka dangana ga ganewarka; cikin dukan hanyoyinka ka amince da shi, zai kuwa sa hanyoyinka su miƙe. Kada ka zama mai hikima a ganinka; ka ji tsoron Ubangiji ka kuma guji mugunta. Wannan zai ba wa jikinka lafiya yă kuma adana ƙasusuwanka. Ka girmama Ubangiji da dukan dukiyarka, ta wurin miƙa masa nunan fari na dukan amfanin gonarka; ta haka rumbunanka za su cika har su zuba, randunanka kuma su cika har baki da sabon ruwan inabi. Ɗana, kada ka rena horon Ubangiji kada kuma ka ƙi tsawatawarsa, domin Ubangiji yakan hori waɗanda yake ƙauna, kamar yadda mahaifi yake yin wa ɗa da yake fariya da shi. Mai albarka ne mutumin da ya sami hikima, mutumin da ya sami fahimi, gama ta fi azurfa riba tana kuma da amfani fiye da zinariya. Ta fi lu’ulu’u daraja; ba a kwatanta abin da ka fi sha’awa da ita. Tsawon rai yana a cikin hannunta na dama; a hannunta na hagu kuwa akwai arziki da bangirma. Hanyoyinta hanyoyi ne masu daɗi, dukan hanyoyinta kuma salama ne. Ita itacen rai ne ga waɗanda suka rungume ta; waɗanda suke riƙe da ta za su zama masu albarka. Ta wurin hikima Ubangiji ya kafa harsashin duniya, ta wurin fahimi ya shirya sammai inda suke; ta wurin sani aka rarraba zurfafa, gizagizai kuma suka zubo raɓa. Ɗana, ka riƙe sahihiyar shari’a da kuma basira, kada ka bar su su rabu da kai; za su zama rai a gare ka, abin adon da zai gyara wuyanka. Sa’an nan za ka bi hanyarka lafiya, ƙafarka kuwa ba zai yi tuntuɓe ba; sa’ad da ka kwanta, ba za ka ji tsoro ba; sa’ad da ka kwanta, barci zai yi maka daɗi. Kada ka ji tsoron masifar da za tă faru farat ɗaya ko lalacin da yakan auka wa mugaye, gama Ubangiji zai zama ƙarfin halinka zai kuwa kiyaye ƙafarka daga fāɗawa a tarko. Kada ka ƙi yin alheri ga duk wanda ya dace, sa’ad da kana iya yin haka. Kada ka ce wa maƙwabcinka “Ka yă dakata sai gobe,” idan kana iya taimakonsa yanzu. Kada ka shirya kome da zai cuci maƙwabcinka, wanda yake zama da aminci kusa da kai. Kada ka zargi mutum ba dalili, sa’ad da bai yi laifi ba. Kada ka ji kishin mai tā-da-na-zaune-tsaye ko ka yi sha’awar aikata ayyukansu. Gama Ubangiji yana ƙyama mai aikata mugunta amma yakan rungumi adalin da ya amince da shi. La’anar Ubangiji tana a gidan mugaye, amma yakan albarkaci gidan adali. Yakan yi wa masu girman kai ba’a amma yakan yi wa mai sauƙinkai alheri. Masu hikima sukan sami kyakkyawan suna, amma wawaye sukan ƙara wa kansu shan kunya. Ku saurara ’ya’yana ga koyarwar mahaifinku; ku mai da hankali, ku sami fahimi. Ina ba ku sahihiyar koyarwa, saboda haka kada ku ƙyale koyarwata. Sa’ad da nake yaro a gidan mahaifina, yaro kaɗai kuma na mahaifiyata, ya koya mini ya ce, “Ka riƙe kalmomina da dukan zuciyarka; ka kiyaye umarnaina za ka kuwa rayu. Ka nemi hikima, ka nemi fahimi; kada ka manta da kalmomina ko ka kauce daga gare su. Kada ka ƙyale hikima, za tă kuwa tsare ka; ka ƙaunace ta, za tă kuwa lura da kai. Hikima ce mafi girma duka; saboda haka ka nemi hikima. Ko da za tă ci duk abin da kake da shi, ka dai nemi fahimi. Ka ƙaunace ta, za tă ɗaukaka ka; ka rungume ta, za tă kuwa girmama ka. Za tă zama kayan ado da za su inganta kanka tă kuma zamar maka rawanin ɗaukaka.” Ka saurara, ɗana, ka yarda da abin da na faɗa, shekarun rayuwarka kuwa za su zama masu yawa. Na bishe ka a hanyar hikima na kuma jagorance ka a miƙaƙƙun hanyoyi. Sa’ad da kake tafiya, ba abin da zai sa ka tuntuɓe; sa’ad da kake gudu, ba za ka fāɗi ba. Ka riƙe umarni, kada ka bari yă kuɓuce; ka tsare shi sosai, gama ranka ne. Kada ka sa ƙafa a kan hanyar mugaye kada ka bi gurbin mugaye. Ka guji mugunta, kada ka yi tafiya a kanta; juya daga gare ta ka yi tafiyarka. Mugaye ba sa iya barci, sai sun aikata mugunta; ba su barci sai sun cuci wani. Mugunta da ta’adi kamar ci da sha suke a gare su. Hanyar adali kamar fitowar rana ce, sai ƙara haske take yi, har ta kai tsaka. Amma hanyar mugaye kamar zurfin duhu ne; ba sa sanin abin da ya sa suke tuntuɓe. Ɗana, ka kula da abin da nake faɗa, ka saurara sosai ga kalmomina. Kada ka bari su rabu da kai, ka kiyaye su a cikin zuciyarka; gama rai ne ga waɗanda suke nemansu da kuma lafiya ga dukan jikin mutum. Fiye da kome duka, ka tsare zuciyarka, gama maɓulɓulan ruwan rijiyar rai ne. Ka kau da muguwar magana daga bakinka; ka yi nesa da magana marar kyau daga leɓunanka. Bari idanunka su dubi gaba sosai, ka kafa idanunka kai tsaye a gabanka. Ka san inda ƙafafunka suke takawa ka bi hanyoyin da suke daram kawai. Kada ka kauce dama ko hagu; ka kiyaye ƙafarka daga mugunta. Ɗana, ka mai da hankali ga hikimata ka saurara da kyau ga kalmomin basirata, don ka ci gaba da yin kome daidai leɓunanka za su adana sani. Gama leɓunan mazinaciya na ɗigan zuma, maganarta tana da sulɓi fiye da mai; amma a ƙarshe tana da ɗaci kamar tafashiya, mai ci kamar takobi mai kaifi biyu. Ƙafafunta na kaiwa ga mutuwa; sawunta na jagora kai tsaye zuwa kabari. Ba ta wani tunanin rayuwa; hanyoyinta karkatacce ne, amma ba tă sani ba. Yanzu fa, ’ya’yana, ku saurare ni; kada ku juye daga abin da nake faɗa. Ku yi nesa da hanyarta, kana ku je kusa da ƙofar gidanta, don kada ku ba da ƙarfi mafi kyau ga waɗansu da kuma shekarunku ga wani marar imani, don kada baƙi su yi biki a kan dukiyarku wahalarku ta azurta gidan wani mutum dabam. A ƙarshen rayuwarku za ku yi ta nishi, sa’ad da namanku da jikinku suka zagwanye. Za ku ce, “Me ya sa na ƙi horo! Me ya sa zuciyata ta ƙi gyara! Ban yi biyayya da malamaina ba ko in saurari masu koyar da ni. Na zo gab da hallaka gaba ɗaya a tsakiyar dukan taron.” Ku sha ruwa daga tankinku, ruwa mai gudu daga rijiyarku. In maɓulɓulanku suka cika suna malala har waje, rafuffukan ruwanku a dandalin jama’a? Bari su zama naka kaɗai, don kada ka raba da baƙi. Bari maɓulɓulanka ya zama mai albarka, bari kuma ka yi farin ciki da matar ƙuruciyarka. Ƙaunatacciyar mariri, barewa mai kyan gani, bari mamanta su ishe ka kullum, bari ƙaunarta ta ɗauke hankalinka kullum. Ɗana, me ya sa za ka bari mazinaciya ta ɗauke maka hankali? Don me za ka rungume matar wani? Gama hanyar mutum a bayyane take a gaban Ubangiji, yana kuma lura da dukan hanyoyinsa. Ayyukan mugunta na mugun mutum tarko ne gare shi; igiyoyin zunubinsa za su daure shi kankan. Zai mutu saboda rashin ɗa’a yawan wawancinsa zai sa yă kauce. Ɗana, in ka shirya tsaya wa maƙwabcinka don yă karɓi bashi, in ka sa hannunka don ɗaukar lamunin wani, in maganarka ta taɓa kama ka, ko kalmomin bakinka sun zama maka tarko, to, sai ka yi haka, ɗana don ka ’yantar da kanka; da yake ka shiga hannuwan maƙwabcinka, ka tafi ka ƙasƙantar da kanka; ka roƙi maƙwabcinka! Ka hana kanka barci, ko gyangyaɗi a idanunka ma. Ka ’yantar da kanka, kamar barewa daga hannun mai farauta, kamar tsuntsu daga tarkon mai kafa tarko. Ku tafi wurin kyashi, ku ragwaye; ku lura da hanyoyinsa ku zama masu hikima! Ba shi da jagora ba shugaba ko mai mulki, duk da haka yakan yi tanade-tanadensa da rani ya kuma tattara abincinsa a lokacin girbi. Har yaushe za ku kwanta a can, ku ragwaye? Yaushe za ku farka daga barcinku? Ɗan barci, ɗan gyangyaɗi, ɗan naɗin hannuwa don a huta, talauci kuwa zai zo kamar ’yan hari rashi kuma kamar ɗan fashi. Sakare da mutumin banza wanda yana yawo da magana banza a baki, wanda yake ƙyifce da ido, yana yi alama da ƙafafunsa yana kuma nuni da yatsotsinsa, wanda yake ƙulla mugunta da ruɗu a cikin zuciyarsa, kullum yana tā-da-na-zaune-tsaye Saboda haka masifa za tă fāɗa farat ɗaya; za a hallaka shi nan da nan, ba makawa. Akwai abubuwa shida da Ubangiji ya ƙi, abubuwa bakwai da suke abin ƙyama gare shi, duban reni, harshe mai ƙarya, hannuwa masu zub da jinin marar laifi, zuciyar da take ƙulla mugayen dabaru, ƙafafun da suke sauri zuwa aikata mugunta, mai shaidar ƙarya wanda yake zuba ƙarairayi, da kuma mutumin da yake tā-da-na-zaune-tsaye a cikin ’yan’uwa. Ɗana, ka kiyaye umarnan mahaifinka kada kuma ka ƙyale koyarwar mahaifiyarka. Ka ɗaura su a zuciyarka har abada; ka ɗaura su kewaye da wuyanka. Sa’ad da kake tafiya, za su bishe ka; sa’ad da kake barci, za su lura da kai; sa’ad da ka farka, za su yi maka magana. Gama waɗannan umarnai fitila ne, wannan koyarwa haske ne, kuma gyare-gyaren horo hanyar rayuwa ce, suna kiyaye ka daga mace marar ɗa’a daga sulɓin harshen mace marar aminci. Kada ka yi sha’awarta a cikin zuciyarka kada ka bar ta tă ɗauki hankalinka da idanunta. Gama karuwa takan mai da kai kamar burodin kyauta, mazinaciya kuma takan farauci ranka. Mutum zai iya ɗiba wuta ya zuba a cinyarsa ba tare da rigunansa sun ƙone ba? Mutum zai iya yin tafi a garwashi wuta mai zafi ba tare da ƙafafunsa sun ƙone ba? Haka yake da wanda ya kwana da matar wani; babu wanda ya taɓa ta da zai tafi babu hukunci. Mutane ba sa ƙyale ɓarawo in ya yi sata don yă ƙosar da yunwarsa sa’ad da yake jin yunwa. Duk da haka in aka kama shi, dole yă biya sau bakwai ko da yake abin zai ci dukan arzikin gidansa. Amma mutumin da ya yi zina ba shi da hankali; duk wanda ya yi haka yana hallaka kansa ne. Dūka da kunya ne za su zama rabonsa, kuma kunyarsa za tă dawwama. Gama kishi kan tā da hasalar miji, kuma ba zai ji tausayi ba sa’ad da yake ramawa. Ba zai karɓi duk wata biya ba; zai ƙi cin hanci, kome yawansu. Ɗana, ka kiyaye kalmomina ka kuma ajiye umarnaina a cikinka. Ka kiyaye umarnaina za ka kuwa rayu; ka tsare koyarwata kamar ƙwayar idonka. Ka daure su a yatsotsinka; ka rubuta su a allon zuciyarka. Ka faɗa wa hikima, “Ke ’yar’uwata ce,” ka kuma kira fahimi danginka; za su kiyaye ka daga mazinaciya, daga mace marar aminci da kalmominta masu ɗaukan hankali. A tagar gidana na leƙa ta labule mai rammuka. Sai na gani a cikin marasa azanci, na lura a cikin samari, wani matashi wanda ba shi da hankali. Yana gangarawa a titi kusa da kusurwarta, yana tafiya a gefen wajen gidanta da magariba, yayinda rana tana fāɗuwa, yayinda duhun dare yana farawa. Sai ga mace ta fito don ta sadu da shi, saye da riga kamar karuwa shirye kuma don ta yaudare shi. (Ba ta jin tsoro, ko kuma kunya, ƙafafunta ba sa zama a gida; wani lokaci a titi, wani lokaci a dandali, tana yawo a kowace kusurwa.) Sai ta kama shi ta rungume shi da duban soyayya a fuskarta ta ce, “Ina da hadaya ta salama a gida; yau zan cika alkawarina. Saboda haka na fito don in sadu da kai; na neme ka na kuma same ka! Na lulluɓe gadona da lili masu launi dabam-dabam daga Masar. Na yayyafa turare a gadona da mur, aloyes da kuma kirfa. Zo, mu sha zurfin ƙauna har safe; bari mu ji wa ranmu daɗi da ƙauna! Mijina ba ya gida; ya yi tafiya mai nisa. Ya ɗauki jakarsa cike da kuɗi ba zai kuwa dawo gida ba sai tsakiyar wata.” Da kalmomin rarrashi ta sa ya kauce; ta ɗauki hankalinsa da sulɓin maganarta. Nan take, ya bi ta kamar saniyar da za a kai mayanka, kamar wawa zuwa wurin da za a ba shi horo sai da kibiya ta soki hantarsa, kamar tsuntsun da ya ruga cikin tarko, ba tare da sani zai zama sanadin ransa ba. Yanzu fa, ’ya’yana, ku saurare ni; ku kasa kunne ga abin da nake faɗa. Kada ku bar zuciyarku ta juya zuwa hanyoyinta ko ku kauce zuwa hanyoyinta. Ta zama sanadin fāɗuwar yawanci; kisan da ta yi ba ta ƙidayuwa. Gidanta babbar hanya ce zuwa kabari mai yin jagora zuwa ɗakunan lahira. Hikima ba ta yin kira ne? Fahimi ba ya tā da muryarsa ne? A ƙwanƙoli a kan hanya, inda hanyoyi suka haɗu, ta ɗauki matsayinta; kusa da ƙofofin shiga cikin birni, a mashigai, ta tā da murya, “Gare ku, ya mutane, nake kira; na tā da muryata ga dukan ’yan adam. Ku da kuke marasa azanci, ku yi hankali; ku da kuke wawaye, ku nemi fahimi. Ku saurara, gama ina da abubuwa masu darajan da zan faɗa; na buɗe leɓunana don in faɗa abin da yake daidai. Bakina yana magana abin da yake gaskiya, gama leɓunana sun ƙi mugunta. Dukan kalmomin bakina suna da adalci; babu waninsu da ya karkace ko kuwa ƙarya ne. Ga mai tunani dukansu daidai ne; ba su da laifi ga waɗanda suke da sani. Ku zaɓi umarnina a maimakon azurfa, sani a maimakon zinariya zalla, gama hikima ta fi lu’ulu’ai daraja, kuma ba abin da kake sha’awa da za a kwatanta da ita. “Ni, hikima, ina zama tare da hankali; ina da sani da iya rarrabewa. Jin tsoron Ubangiji shi ne ƙin mugunta; ina ƙin girman kai da fariya, halin mugunta da kuma muguwar magana. Shawara da yin tunani mai kyau nawa ne; ina da fahimi da kuma iko. Ta wurina sarakuna suke mulki masu mulki kuma suke yin dokokin da suke da adalci; ta wurina sarakuna suke mulki, da kuma dukan manyan mutanen da suke mulkin duniya. Ina ƙaunar waɗanda suke ƙaunata, kuma waɗanda suke nemana sukan same ni. Tare da ni akwai wadata da girmamawa, dukiya da wadata masu dawwama. ’Ya’yan itacena sun fi zinariya zalla; amfanin gonar da nake bayar ya fi azurfa mafi kyau. Ina tafiya a hanyar adalci, a kan hanyoyin gaskiya, ina ba da wadata ga waɗanda suke ƙaunata ina sa wuraren ajiyarsu su cika. “ Ubangiji ya kawo ni a matsayi na farko na ayyukansa, kafin ayyukansa na tuntuni; an naɗa ni tun fil azal, daga farko, kafin duniya ta kasance. Sa’ad da babu tekuna, aka haife ni, sa’ad da babu maɓulɓulai masu ruwa; kafin a kafa duwatsu a wurarensu, kafin tuddai ma, an haife ni, kafin ya yi duniya ko gonaki ko wata ƙurar duniya. Ina nan sa’ad da ya kafa sammai a wurarensu, sa’ad da ya shata sararin sama a kan fuskar zurfafa, sa’ad da ya kafa gizagizai a bisa ya kuma kafa maɓulɓulan zurfafa daram, sa’ad da ya ba wa teku iyakarsa domin kada ruwaye su zarce umarninsa, da kuma sa’ad da ya shata tussan duniya. A lokacin ni ne mai tsara abubuwa a gefensa. Na cika da murna kowace rana, kullum ina farin ciki a gabansa, ina farin ciki da dukan duniyarsa ina murna da ’yan adam. “Yanzu fa, ’ya’yana, ku saurare ni; masu albarka ne waɗanda suke kiyaye hanyoyina. Ku saurari umarnina ku kuma zama masu hikima; kada ku ƙyale ta. Mai albarka ne wanda ya saurare ni; yana tsaro kullum a ƙofofina, yana jira a ƙofar shigata. Gama duk wanda ya same ni ya sami rai zai kuma sami tagomashi daga Ubangiji. Amma duk wanda ya kāsa samuna ya cuci kansa; dukan waɗanda suke ƙina suna ƙaunar mutuwa ke nan.” Hikima ta gina gidanta; ta yi ginshiƙansa bakwai. Ta shirya abincinta gauraye da ruwan inabinta; ta kuma shirya teburinta. Ta aiki bayinta mata, tana kuma kira daga wurare masu tsayi na birnin. “Bari dukan waɗanda suke marasa azanci su zo nan ciki!” Tana faɗa wa marasa hankali. “Ku zo, ku ci abincina da ruwan inabin da na gauraye. Ku bar hanyoyinku marasa hankali za ku kuwa rayu; yi tafiya a hanyar fahimi. “Duk wanda ya yi wa mai ba’a gyara yana gayyatar zagi duk wanda ya tsawata wa mugu yakan gamu da cin mutunci. Kada ka tsawata wa masu ba’a gama za su ƙi ka; ka tsawata wa mai hikima zai kuwa ƙaunace ka. Ka koya wa mai hikima zai kuwa ƙara hikima; ka koya wa mai adalci zai kuwa ƙara koyonsa. “Tsoron Ubangiji shi ne mafarin hikima, sanin Mai Tsarki kuwa fahimi ne. Gama ta wurina kwanakinka za su yi yawa, za a kuwa ƙara wa ranka shekaru. In kana da hikima, hikimarka za tă ba ka lada; in kai mai ba’a ne, kai kaɗai za ka sha wahala.” Wawancin mace a bayyane yake; ba ta da ɗa’a kuma ba ta da sani. Takan zauna a ƙofar gidanta, a wurin zama a wurin mafi tsayi na birni, tana kira ga masu wucewa, waɗanda suke tafiya kai tsaye a hanyarsu. “Bari dukan waɗanda suke marasa azanci su zo cikin nan!” Tana ce wa marasa hankali. “Ruwan da aka sata ya fi daɗi; abincin da aka ci a ɓoye ya fi daɗi!” Amma ba su san cewa matattu suna a can ba, cewa baƙinta suna a can cikin zurfin kabari ba. Karin maganar Solomon. Ɗa mai hikima yakan kawo wa mahaifinsa farin ciki, amma wawan ɗa kan sa wa mahaifiyarsa baƙin ciki. Dukiyar da aka samu a hanyar da ba tă dace ba, ba ta da albarka, amma adalci kan ceci mutum daga mutuwa. Ubangiji ba ya barin mai adalci da yunwa amma yakan lalace burin mugu. Ragwanci kan sa mutum yă zama matalauci, amma aiki tuƙuru kan ba da dukiya. Shi da ya tattara hatsi da rani ɗa ne mai hikima, amma shi da yakan yi barci a lokacin girbi ɗa ne wanda ya zama abin kunya. Albarka kan zauna a kan mai adalci kamar rawani, amma rikici kan sha bakin mugu. Tunawa da mai adalci albarka ne amma sunan mugu zai ruɓe. Mai hikima a zuciya yakan yarda da umarni amma surutun wawa kan kai ga lalaci. Mai mutunci yana tafiya lafiya, amma shi da yake tafiya a karkatattun hanyoyi za a kama shi. Shi da ya ƙyifta ido da mugunta kan jawo baƙin ciki surutun wawa kuma kan zo da lalaci. Bakin adali maɓulɓulan rai ne, amma kalmar mugun takan ɓoye makircinsa. Ƙiyayya kan haddasa wahala, amma ƙauna kan rufe dukan laifofi. Ana samun hikima a leɓunan masu fahimi, amma bulala domin bayan marasa azanci ne. Mai hikima kan yi ajiyar sani, amma bakin wawa kan gayyaci lalaci. Dukiyar masu arziki yakan zama mafakar birninsu, amma talauci shi ne lalacin matalauci. Hakkin adalai kan kawo musu rai, amma albashin mugaye kan kawo musu hukunci. Duk wanda ya mai da hankali ga horo kan nuna hanyar rai, amma duk wanda ya ƙyale gyara kan sa waɗansu su kauce. Duk wanda ya ɓoye ƙiyayyarsa yana da ƙarya a leɓunansa, duk kuma wanda yake baza ƙarairayi wawa ne. Sa’ad da magana ta yi yawa, ba a rasa zunubi a ciki, amma shi da ya ƙame harshensa mai hikima ne. Harshen adali azurfa ce zalla, amma zuciyar mugu ba ta da wani amfani. Leɓunan adalai kan amfane yawanci, amma wawa kan mutu saboda rashin azanci. Albarkar Ubangiji kan kawo wadata, ba ya kuma ƙara wahala a kai. Wawa yakan ji daɗi halin mugunta, amma mutum mai fahimi kan ji daɗin hikima. Abin da mugu ke tsoro shi ne zai same shi; abin da adali ke bukata yakan sami biyan bukata. Sa’ad da hadiri ya taso, yakan watsar da mugaye, amma adalai za su tsaya daram har abada. Kamar yadda ruwan tsami yake ga haƙora hayaƙi kuma ga idanu, haka malalaci yake ga wanda ya aike shi. Tsoron Ubangiji kan ƙara tsawon rai, amma akan gajartar da shekarun mugaye. Abin da adali yake sa rai yakan kai ga farin ciki, amma sa zuciyar mugu ba ya haifar da kome. Hanyar Ubangiji mafaka ce ga adalai amma lalaci ne ga waɗanda suke aikata mugunta. Ba za a taɓa tumɓuke masu adalci ba, amma mugaye ba za su ci gaba da kasance a ƙasar ba. Bakin adalai kan fitar da hikima, amma za a dakatar da mugun harshe. Leɓunan adalai sun san abin da ya dace, amma bakunan mugaye sun san abin da yake mugu ne kawai. Ubangiji yana ƙyamar ma’aunan zamba, amma ma’aunin da suke daidai ne abin farin cikinsa. Sa’ad da girman kai ya zo, sai shan kunya ta zo, amma hikima kan zo tare da ƙasƙantar da kai. Mutuncin masu aikata gaskiya takan bi da su, amma marasa aminci sukan hallaka ta wurin cin amanar da suke yi. Dukiya ba ta da amfani a ranar fushi, amma adalci kan yi ceto daga mutuwa. Adalcin marasa laifi kan miƙe hanyarsu, amma akan ƙasƙantar da mugaye ta wurin muguntarsu. Adalcin masu aikata gaskiya kan cece su, amma rashin aminci tarko ne ga mugayen sha’awace-sha’awace. Sa’ad da mugu ya mutu, sa zuciyarsa kan hallaka; dukan abin da ya sa zuciya daga ikonsa ba ya amfana kome. Akan kuɓutar da mai adalci daga wahala, sai ta dawo wa mugu a maimako. Da bakinsa marar sanin Allah kan hallaka maƙwabcinsa, amma ta wurin sani mai adalci kan kuɓuta. Sa’ad da adali ya yi nasara, birnin kan yi farin ciki; sa’ad da mugu ya hallaka, akwai sowa ta farin ciki. Ta wurin albarkar mai aikata gaskiya birni kan ƙasaita, amma ta wurin bakin mugu akan hallaka birnin. Mutum da ba shi da azanci kan ki maƙwabci, amma mutum mai fahimi kan ƙame harshensa. Gulma yakan lalace yarda, amma mutum mai aminci kan kiyaye asiri. Saboda rashin jagora al’umma takan fāɗi, amma masu ba da shawara da yawa kan tabbatar da nasara. Duk wanda ya ɗauki lamunin wani tabbatacce zai sha wahala, amma duk wanda ya ƙi ya sa hannu a ɗaukar lamuni ba ruwansa. Mace mai hankali na samu bangirma, amma azzalumai za su sami dukiya. Mutumin kirki kan ribance kansa, amma mugu kan kawo wa kansa wahala. Mugun mutum kan sami albashin ƙarya amma shi da ya shuka adalci zai girbe lada tabbatacce. Mutum mai adalci da gaske yakan sami rai, amma shi da ya duƙufa ga aikata mugunta kan tarar da mutuwarsa. Ubangiji yana ƙyamar mutane masu muguwar zuciya amma yana jin daɗin waɗanda hanyoyinsu ba su da laifi. Ka tabbata da wannan. Mugaye ba za su tafi babu hukunci ba, amma waɗanda suke masu adalci za su tafi babu hukunci. Kamar zinariya a hancin alade haka kyan mace wadda ba ta da hankali. Sha’awar adalai kan ƙare kawai a aikata alheri, amma sa zuciyar mugaye kan ƙarasa kawai a fushi. Wani mutum kan bayar hannu sake, duk da haka yakan sami fiye; wani yakan riƙe abin da ba nasa ba, amma sai ya ƙarasa cikin talauci. Mutum mai kyauta zai azurta; shi da yakan taimake waɗansu, za a taimake shi. Mutane kan la’anci mai ɓoye hatsi yana jira ya yi tsada, amma albarka kan zauna a kan wanda yake niyya ya sayar. Duk mai nema alheri kan sami alheri, amma mugu kan zo wa wanda yake nemansa. Duk wanda ya dogara ga arzikinsa zai fāɗi, amma adali zai yi nasara kamar koren ganye. Duk wanda ya kawo wahala wa iyalinsa zai gāji iska kawai, kuma wawa zai zama bawan masu hikima. ’Ya’yan itacen adali itacen rai ne, kuma duk mai samun rayuka mai hikima ne. In masu adalci sun sami abin da ya dace da su a duniya, yaya zai zama ga marasa sanin Allah da kuma masu zunubi! Duk mai ƙaunar horo yana ƙaunar sani, amma duk mai ƙin gyara wawa ne. Mutumin kirki kan sami tagomashi daga Ubangiji, amma Ubangiji yakan hukunta mai son yin wayo. Ba yadda mutum zai kahu ta wurin aikata mugunta, amma ba za a tumɓuke adali ba. Mace mai halin kirki rawanin mijinta ne, amma mace marar kunya tana kama da ciwo a ƙasusuwansa. Shirye-shiryen masu adalci daidai ne, amma shawarar mugaye ruɗu ne. Kalmomin mugu sukan kwanta suna jira su yi kisankai, amma jawabin masu aikata gaskiya kan kuɓutar da su. Akan tumɓuke mugaye ba a ƙara ganinsu, amma gidan masu adalci kan tsaya daram. Akan yabi mutum bisa ga hikimarsa, amma mutane marasa azanci akan rena su. Gara ka zama kai ba kome ba ne amma kana da bawa da ka mai da kanka kai wani ne alhali kuwa ba ka da abinci. Mai adalci kan kula da bukatun dabbobinsa, amma halaye mafi kyau na mugaye su ne ƙeta. Duk wanda ya nome gonarsa zai sami abinci a yalwace, amma shi da yake naushin iska marar azanci ne. Mugaye suna sha’awar ganimar mugayen mutane, amma saiwar masu adalci kan haɓaka. Mugun mutum kan fāɗa a tarkon maganarsa ta zunubi, amma adali kan kuɓuta daga wahala. Daga abubuwan da suke fitowa daga leɓunansa mutum kan cika da abubuwa masu kyau tabbatacce yadda aikin hannuwansa suke ba shi lada. Hanyar wawa daidai take a gare shi, amma mai hikima kan saurari shawara. Wawa kan nuna fushinsa nan take, amma mai la’akari kan ƙyale zargi. Mashaidin gaskiya kan ba da shaidar gaskiya, amma mashaidin ƙarya yana baza ƙarairayi ne. Maganganun rashin tunani sukan soki mutum kamar takobi, amma harshen mai hikima kan kawo warkarwa. Leɓunan gaskiya kan dawwama har abada, amma harshen ƙarya yakan dawwama na ɗan lokaci ne kawai. Akwai ruɗu a zukatan waɗanda suke ƙulla mugunta, amma waɗanda suke aikata alheri za su yi farin ciki. Ba wani lahanin da zai sami masu adalci, amma mugaye suna da nasu cike da wahala. Ubangiji yana ƙyamar leɓunan masu ƙarya, amma yana jin daɗin mutanen da suke masu gaskiya. Mai la’akari kan kiyaye saninsa wa kansa, amma zuciyar wawa kan yi ta tallar wawanci. Hannuwan masu aiki tuƙuru za su yi mulki, amma ragwanci kan ƙarasa a aikin bauta. Zuciya mai damuwa takan naƙasar da mutum, amma maganar alheri kan faranta masa rai. Adali yakan yi hankali a abokantaka, amma hanyar mugaye kan kai su ga kaucewa. Rago ba ya gashin abin da ya kama daga farauta, amma mai aiki tuƙuru yakan ɗauki mallakarsa da muhimmanci. A hanyar adalci akwai rai; a wannan hanya akwai rashin mutuwa. Ɗa mai hikima yakan mai da hankali ga umarnin mahaifinsa, amma mai ba’a ba ya sauraran kwaɓi. Daga abin da ya fito leɓunan mutum ne mutum kan ji daɗin abubuwa masu kyau, amma marar aminci yakan ƙosa ya tā-da-na-zaune-tsaye. Duk mai lura da leɓunansa yakan lura da ransa, amma duk mai magana da haushi zai kai ga lalaci. Rago ya ƙosa ya sami wani abu ainun amma ba ya samun kome, amma sha’awar mai aiki tuƙuru yakan ƙoshi sosai. Adali yana ƙin abin da yake ƙarya, amma mugu kan jawo kunya da ƙasƙanci. Adalci yakan lura da mutum mai mutunci, amma mugunta takan sha kan mai zunubi. Wani mutum yakan ɗauki kansa mai arziki ne, alhali ba shi da kome, wani ya ɗauki kansa shi matalauci ne, alhali shi mawadaci ne ƙwarai. Arzikin mutum zai iya kuɓutar da ransa, amma matalauci ba ya jin barazana. Hasken masu adalci kan haskaka ƙwarai, amma fitilar mugaye mutuwa take. Girmankai kan jawo faɗa ne kawai, amma hikima tana samuwa a waɗanda suke jin shawara. Kuɗin da aka same su a rashin gaskiya yakan ɓace da sauri, amma duk wanda ya tara kuɗi kaɗan-kaɗan za su yi ta ƙaruwa. Sa zuciyar da aka ɗaga zuwa gaba kan sa zuciya tă yi ciwo, amma marmarin da aka ƙosar yana kamar itacen rai. Duk wanda ya rena umarni zai ɗanɗana ƙodarsa, amma duk wanda ya yi biyayya da umarni zai sami lada. Koyarwar mai hikima maɓulɓulan rai ne, mai juyar da mutum daga tarkon mutuwa. Fahimta mai kyau kan sami tagomashi, amma hanyar marar aminci tana da wuya. Kowane mai azanci yakan nuna sani, amma wawa yakan yi tallen wawancinsa. Mugun ɗan saƙo kan shiga wahala, amma jakadan da mai aminci yakan kawo warkarwa. Duk wanda ya ƙyale horo yakan kai ga talauci da kuma kunya, amma duk wanda ya karɓi gyara yakan sami girma. Marmarin da aka cika yana da daɗi ga rai, amma wawa yana ƙyamar juyewa daga mugunta. Shi da yake tafiya tare da masu hikima yakan ƙaru da hikima, amma abokin wawaye zai yi fama da lahani. Rashin sa’a kan fafare mai zunubi, amma wadata ce ladar adali. Mutumin kirki kan bar gādo wa ’ya’ya ’ya’yansa, amma arzikin mai zunubi ajiye ne da aka yi wa mai adalci. Gonar matalauci za tă iya ba da abinci a yalwace, amma rashin adalci kan share shi tas. Duk wanda ba ya horon ɗansa ba ƙaunarsa yake yi ba, amma duk mai ƙaunarsa yakan kula ya hore shi. Masu adalci sukan ci isashen abinci, amma cikin mugaye na fama da yunwa. Mace mai hikima kan gina gidanta, amma da hannunta wawiya takan rushe shi ƙasa. Wanda tafiyarsa ta aikata gaskiya ce kan ji tsoron Ubangiji, amma wanda hanyoyinsa ba a kan gaskiya ba ne yakan rena shi. Maganar wawa kan kawo sanda a bayansa, amma leɓunan masu hikima kan tsare su. Inda ba shanu, wurin sa wa dabbobi abinci zai kasance ba kome, amma daga ƙarfin saniya ce yalwar girbi kan fito. Mashaidi na gaskiya ba ya ruɗu, amma mashaidin ƙarya kan baza ƙarairayi. Mai ba’a kan nemi hikima amma ba ya samun kome, amma sani kan zo a sawwaƙe ga mai basira. Ka guji wawa, gama ba za ka sami sani a leɓunansa ba. Hikima masu la’akari shi ne su yi tunani a kan hanyoyinsu, amma wautar wawaye ruɗu ne. Wawaye kan yi ba’a a gyaran zunubi, amma fatan alheri yana samuwa a cikin masu aikata gaskiya. Kowace zuciya ta san ɓacin ranta, kuma babu wani dabam da zai yi rabon jin daɗinsa. Za a rushe gidan mugu, amma tentin mai aikata gaskiya zai haɓaka. Akwai hanyar da ta yi kamar tana daidai ga mutum, amma a ƙarshe takan kai ga mutuwa. Ko cikin dariya zuciya takan yi ciwo, kuma farin ciki kan iya ƙarasa a baƙin ciki. Marasa bangaskiya za su sami sakamako cikakke saboda hanyoyinsu, kuma mutumin kirki zai sami lada saboda nasa. Marar azanci kan gaskata kome, amma mai la’akari kan yi tunani game da matakinsa. Mai hikima kan ji tsoron Ubangiji ya kuma guji mugunta, amma wawa yana da girman kai yakan yi kome da garaje. Mutum mai saurin fushi yakan yi ayyukan wauta, akan kuma ƙi mai son nuna wayo. Marar azanci kan gāji wauta, amma mai la’akari kan sami rawanin sani. Masu mugunta za su rusuna a gaban masu kirki, mugaye kuma za su yi haka a ƙofofin adalai. Maƙwabta sukan gudu daga matalauta, amma masu arziki suna da abokai da yawa. Duk wanda ya rena maƙwabci ya yi zunubi, amma mai albarka ne wanda yake alheri ga mabukata. Ba waɗanda suke ƙulla mugunta sukan kauce ba? Amma waɗanda suke ƙulla abin da yake mai kyau sukan sami ƙauna da aminci. Duk aiki tuƙuru yakan kawo riba, amma zama kana surutu kan kai ga talauci kawai. Dukiyar masu hikima ita ce rawaninsu, amma wautar wawaye kan haifar da wauta ne kawai. Mashaidin gaskiya kan ceci rayuka, amma mashaidin ƙarya mai ruɗu ne. Duk mai tsoron Ubangiji yana da zaunannen mafaka, kuma ga ’ya’yansa zai zama mafaka. Tsoron Ubangiji shi ne maɓulɓular rai yakan juye mutum daga tarkon mutuwa. Yawan mutane shi ne ɗaukakar sarki, amma in ba tare da mabiya ba sarki ba kome ba ne. Mutum mai haƙuri yana da fahimi mai yawa, amma mai saurin fushi yakan nuna wautarsa a fili. Zuciya mai salama kan ba jiki rai, amma kishi kan sa ƙasusuwa su yi ciwo. Duk wanda ya zalunci matalauci ya zagi Mahaliccinsu ke nan, amma duk wanda ya yi alheri ga mabukata yana girmama Allah ne. Sa’ad bala’i ya auku, mugaye kan fāɗi, amma ko a mutuwa masu adalci suna da mafaka. Hikima tana a zuciyar mai azanci, kuma ko a cikin wawaye takan sa a santa. Adalci yakan ɗaukaka al’umma, amma zunubi kan kawo kunya ga kowane mutane. Sarki yakan yi murna a kan bawa mai hikima, amma bawa marar kunya kan jawo fushinsa. Amsa da tattausar harshe kan kwantar da fushi, amma magana da kakkausan harshe kan kuta fushi. Harshen mai hikima kan yi zance mai kyau a kan sani, amma bakin wawa kan fitar da wauta. Idanun Ubangiji suna a ko’ina, suna lura da masu aikata mugunta da masu aikata alheri. Harshen da ya kawo warkarwa shi ne itacen rai, amma harshe mai ƙarya kan ragargaza zuciya. Wawa yakan ƙi kulawa da horon da mahaifinsa yake masa, amma duk wanda ya yarda da gyara kan nuna azanci. Gidan adali yana da dukiya mai yawa, amma albashin mugaye kan kawo musu wahala. Leɓunan masu hikima sukan baza sani; ba haka zukatan wawaye suke ba. Ubangiji yana ƙyamar hadayar mugaye, amma addu’ar masu aikata gaskiya kan sa ya ji daɗi. Ubangiji yana ƙin hanyar mugaye amma yana ƙaunar waɗanda suke neman adalci. Horo mai tsanani yana jiran duk wanda ya bar hanya; wanda ya ƙi gyara zai mutu. Mutuwa da Hallaka suna nan a fili a gaban Ubangiji, balle fa zukatan mutane! Mai yin ba’a yakan ƙi gyara; ba zai nemi shawara mai hikima ba. Zuciya mai farin ciki kan sa fuska tă yi haske, amma ciwon zuciya kan ragargaza rai. Zuciya mai la’akari kan nemi sani, amma bakin wawa wauta ce ke ciyar da shi. Dukan kwanakin mutumin da ake danniya fama yake yi, amma zuciya mai farin ciki yana yin biki kullum. Gara a kasance da kaɗan da tsoron Ubangiji da a kasance da arziki mai yawa game da wahala. Gara a ci abincin kayan ganye inda akwai ƙauna da a ci kiwotaccen saniya inda ƙiyayya take. Mutum mai zafin rai kan kawo faɗa, amma mutum mai haƙuri kan kwantar da faɗa. An tare hanyar rago da ƙayayyuwa, amma hanyar mai aikata gaskiya buɗaɗɗiyar hanya ce. Ɗa mai hikima kan kawo farin ciki wa mahaifinsa, amma wawa yakan rena mahaifiyarsa. Wauta kan sa mutum marar azanci ya yi farin ciki, amma mai basira kan kiyaye abin da yake yi daidai. Shirye-shirye sukan lalace saboda rashin neman shawara, amma tare da mashawarta masu yawa za su yi nasara. Mutum yakan yi farin ciki a ba da amsar da take daidai, kuma ina misali a yi magana a lokacin da ya dace! Hanyar rai na yin jagora ya haura wa masu hikima don ta kiyaye shi daga gangarawa zuwa kabari. Ubangiji yakan rushe gidan mai girman kai amma yakan kiyaye iyakokin gwauruwa daidai. Ubangiji yana ƙyamar tunanin mugaye, amma waɗanda suke da tunani masu tsabta yakan ji daɗinsu. Mutum mai haɗama kan kawo wahala ga iyalinsa, amma wanda yake ƙin cin hanci zai rayu. Zuciyar mai adalci takan auna amsoshinta, amma bakin mugu yakan fitar da mugunta. Ubangiji yana nesa da mugaye amma yakan ji addu’ar adalai. Fuska mai fara’a takan kawo farin ciki ga zuciya, kuma labari mai daɗi na kawo lafiya ga ƙasusuwa. Duk wanda ya mai da hankali sa’ad da ake tsawata masa ba zai kasance dabam a cikin masu hikima ba. Duk waɗanda suka ƙi horon sun rena kansu ke nan, amma duk waɗanda sun yarda da gyara sukan ƙara basira. Tsoron Ubangiji yakan koya wa mutum hikima, kuma sauƙinkai kan zo kafin girmamawa. Ga mutum ne shirye-shiryen zuciya suke, amma daga Ubangiji ne amshin harshe kan zo. Dukan hanyoyin mutum sukan yi kamar marar laifi ne gare shi, amma Ubangiji yakan auna manufofi. Ka miƙa wa Ubangiji dukan abin da kake yi, shirye-shiryenka kuwa za su yi nasara. Ubangiji yana yin kome domin amfaninsa, har ma da mugaye domin ranar masifa. Ubangiji yana ƙyamar dukan zuciya mai girman kai. Ka tabbata da wannan. Ba za su kuɓuta daga hukunci ba. Ta wurin ƙauna da aminci akan yi kafarar zunubi; ta wurin tsoron Ubangiji mutum kan guji mugunta. Sa’ad da hanyoyin mutum sun gamshi Ubangiji, yakan sa abokan gāban mutumin ma su zauna lafiya da shi. Gara ka sami kaɗan ta hanyar adalci da sami riba mai yawa ta hanyar rashin gaskiya. ’Yan Adam sukan yi shirye-shiryensu a zukatansu, amma Ubangiji ne yake da ikon cika matakansa. Leɓunan sarki kan yi magana kamar ta wurin ikon Allah, kuma bai kamata bakinsa ya yi kuskure a yanke shari’a ba. Ma’aunai da magwajin gaskiya daga Ubangiji ne; dukan ma’aunai da suke cikin jaka yinsa ne. Sarakuna suna ƙyamar abin da ba shi da kyau, gama an kafa kujerar sarauta ta wurin adalci ne. Sarakuna sukan ji daɗi leɓuna masu yin gaskiya; sukan darjanta mutumin da yake faɗin gaskiya. Fushin sarki ɗan saƙon mutuwa ne, amma mai hikima yakan faranta masa rai. Sa’ad da fuskar sarki ta haska, yana nufin rai ke nan; tagomashinsa yana kamar girgijen ruwa a bazara. Ya ma fi kyau ka sami hikima fiye da zinariya, ka zaɓi fahimi a maimakon azurfa! Buɗaɗɗiyar hanyar masu aikata gaskiya kan guje wa mugunta; duk wanda yake lura da hanyarsa yakan lura da ransa. Girmankai yakan zo kafin hallaka, girman kai yakan zo kafin fāɗuwa. Gara ka zama ɗaya daga cikin matalauta masu sauƙinkai, da ka raba ganima da masu girman kai. Duk wanda ya mai da hankali ga umarni yakan yi nasara, kuma mai albarka ne wanda yake dogara ga Ubangiji. Akan ce da masu hikima a zuciya hazikai, kuma kalmomi masu daɗi kan inganta umarni. Fahimi shi ne maɓulɓular rai ga waɗanda suke da shi, amma wauta kan kawo hukunci ga wawaye. Zuciyar mai hikima kan bi da bakinsa, kuma leɓunansa kan inganta umarni. Kalmomi masu daɗi suna kama da kakin zuma, mai zaƙi ga rai da kuma warkarwa ga ƙasusuwa. Akwai hanyar da ta yi kamar daidai ga mutum, amma a ƙarshe takan kai ga mutuwa. Marmarin cin abinci yakan yi wa ɗan ƙodago aiki; yunwarsa kan sa ya ci gaba. Mutumin banza yakan ƙulla mugunta, kuma jawabinsa yana kama da wuta mai ƙuna. Fitinannen mutum yakan zuga tashin hankali, mai gulma kuma yakan raba abokai na kusa. Mutum mai tā-da-na-zaune-tsaye yakan ruɗi maƙwabcinsa ya kai shi a hanyar da ba ta da kyau. Duk wanda ya ƙyifce da idonsa yana ƙulla maƙarƙashiya ce; duk wanda ya murguɗa leɓunansa yana niyya aikata mugunta ke nan. Furfura rawani ne mai daraja; akan same ta ta wurin yin rayuwa ta adalci. Gara ka zama mai haƙuri da ka zama jarumi, ya fi kyau ka iya mallakar kanka fiye da mallakar birane. Akan jefa ƙuri’a a kan cinya, amma kowace shawara mai kyau daga Ubangiji ne. Gara ka ci busasshen burodi da kwanciyar rai kuma shiru da ka je cin abinci a gidan da ke cike da biki amma da ɓacin rai. Bawa mai hikima zai yi mulki a kan da mai rashin kunya, kuma zai raba gādo kamar ɗaya daga cikin ’yan’uwansa. Ana gwajin azurfa da kuma zinariya da wuta, amma Ubangiji ne mai gwajin zuciya. Mugun mutum kan mai da hankali ga mugayen leɓuna; maƙaryaci yakan kasa kunne ga harshen ƙarairayi. Duk wanda yake wa matalauta ba’a yana zagin Mahaliccinsu ne; duk wanda ya yi murna akan masifar da ta sami wani za a hukunta shi. Jikoki rawanin tsofaffi ne, kuma iyaye su ne abin taƙamar ’ya’yansu. Leɓunan basira ba su dace da wawa ba, ya ma fi muni a ce mai mulki yana da leɓunan ƙarya! Cin hanci kamar sihiri yake ga wanda yake ba da shi; ko’ina ya juye, yakan yi nasara. Duk wanda ya rufe laifi yana inganta ƙauna ne, amma duk wanda ya yi ta maimaita batu yakan raba abokai na kusa. Tsawata kan sa mutum ya koyi basira fiye da abin da wawa zai koya ko da an dūke shi sau ɗari. Mugayen mutane sukan kuta tawaye da Allah; za a aika manzo mutuwa a kansu. Gara a haɗu da beyar da aka ƙwace wa ’ya’ya fiye da a sadu da wawa cikin wautarsa. In mutum ya sāka alheri da mugunta, mugunta ba za tă taɓa barin gidansa ba. Farawar faɗa tana kamar ɓarkewa madatsar ruwa ne, saboda haka ka bar batun kafin faɗa ta ɓarke. Baratar da mai laifi a kuma hukunta mai adalci, Ubangiji ya ƙi su biyu. Mene ne amfanin kuɗi a hannun wawa, da yake ba shi da sha’awar samun hikima? Aboki yakan yi ƙauna a koyaushe, ɗan’uwa kuma, ai, don ɗaukar nawayar juna ne aka haife shi. Mutumin da ba shi da azanci yakan ɗauki lamunin wani ya kuma ɗauki nauyin biyan basusuwan maƙwabci. Duk mai son faɗa yana son zunubi, duk wanda ya gina ƙofar shiga mai tsawo yana gayyatar hallaka. Mutum mai muguwar zuciya ba ya cin gaba; duk wanda yake da harshen ruɗu kan shiga wahala. Kasance da wawa kamar ɗa yakan kawo baƙin ciki babu farin ciki ga mahaifin wawa. Zuciya mai farin ciki magani ne mai kyau, amma bakin rai kan busar da ƙasusuwa. Mugun mutum yakan karɓa cin hanci a asirce don yă lalace yin adalci. Mutum mai basira kan kafa idonsa a kan hikima, amma idanun wawa suna a kan ƙarshen duniya. Da yake wawa yakan kawo baƙin ciki ga mahaifinsa da ɓacin rai ga wanda ya haife shi. Ba shi da kyau a hukunta marar laifi, ko a bulale shugaba saboda mutuncinsu. Mutum mai sani yakan yi la’akari da amfani da kalmomi, mutum mai basira kuma natsattse ne. Ko wawa in bai buɗe bakinsa ba, za a zaci shi mai hikima ne, da kuma mai basira inda ya ƙame bakinsa. Mutumin da ba ya abokantaka yakan nema ya cika burinsa ne kaɗai; yakan ƙi yarda da kowace maganar da take daidai. Wawa ba ya sha’awa ya sami fahimta amma abin da yake so ya yi kaɗai, shi ne ya ba da ra’ayinsa. Sa’ad da mugunci ya zo, reni ma kan zo, haka kuma sa’ad da kunya ta zo, shan kunya kan biyo. Kalmomin bakin mutum suna da zurfi kamar ruwaye, amma maɓulɓulan hikima rafi ne mai gudu. Ba shi da kyau ka yi wa mugu alheri ko ka hana wa marar laifi adalci. Leɓunan wawa kan jawo masa faɗa, bakinsa kuma kan gayyaci dūka. Bakin wawa lalatar da kansa yake yi leɓunansa kuma tarko ne ga ransa. Kalmomin mai gulma kamar abinci mai daɗi suke; sukan gangara zuwa can cikin gaɓoɓin mutum. Wanda yake ragwanci a aikinsa ɗan’uwa ne ga wanda yakan lalatar da abubuwa. Sunan Ubangiji hasumiya ce mai ƙarfi; masu adalci kan gudu zuwa wurinta don su zauna lafiya. Dukiyar masu arziki ita ce birninsu mai katanga; suna gani cewa ba za a iya huda katangar ba. Kafin fāɗuwarsa zuciyar mutum takan yi girman kai, amma sauƙinkai kan zo kafin girmamawa. Duk wanda yakan ba da amsa kafin ya saurara, wannan wauta ce da kuma abin kunya. Sa rai da mutum ke yi kan taimake shi sa’ad da yake ciwo, amma in ya karai, to, tasa ta ƙare. Zuciya mai la’akari kan nemi sani; kunnuwan mai hikima kan bincika don yă koya. Kyauta kan buɗe hanya wa mai bayarwa yakan kuma kai shi a gaban babban mutum. Wanda ya fara mai da jawabi yakan zama kamar shi ne mai gaskiya, sai wani ya fito ya yi masa tambaya tukuna. Jefa ƙuri’a kan daidaita tsakanin masu faɗa ta kuma ajiye masu faɗan a rabe. Ɗan’uwan da aka yi wa laifi ya fi birni mai katanga wuyan shiryawa, kuma faɗace-faɗace suna kama da ƙofofin ƙarfe na fada. Daga abin da baki ya furta ne cikin mutum kan cika; girbi daga leɓunansa kuma yakan ƙoshi. Harshe yana da ikon rai da mutuwa, kuma waɗanda suke ƙaunarsa za su ci amfaninsa. Duk wanda ya sami mace ya sami abu mai kyau ya kuma sami tagomashi daga Ubangiji. Matalauci kan yi roƙo da taushi, amma mawadaci kan amsa da kakkausar murya. Mutum mai abokai masu yawa kan lalace, amma akwai abokin da yakan manne kurkusa fiye da ɗan’uwa. Gara matalauci wanda yake marar laifi da wawa wanda leɓunansa masu ƙarya ne. Ba shi da kyau ka kasance da niyya babu sani, ko ka kasance mai garaje ka ɓace hanya. Wautar mutum kan lalatar da ransa, duk da haka zuciyarsa kan ba wa Ubangiji laifi. Wadata kan kawo abokai da yawa, amma abokin matalauci kan bar shi. Mai ba da shaidar ƙarya ba zai tafi babu hukunci ba, kuma duk wanda ya baza ƙarairayi ba zai kuɓuta ba. Kowa na ƙoƙari ya sami farin jini wurin mai mulki, kuma kowa na so a ce shi abokin mutumin nan mai yawan kyauta ne. ’Yan’uwan matalauci sukan guje shi, balle abokansa, su ma za su guje shi. Ko da yake matalaucin yana binsu yana roƙo, ba zai sam su ba. Duk wanda ya sami hikima yana ƙaunar ransa; duka wanda yake jin daɗi fahimi kan ci gaba. Mai shaidar ƙarya ba zai tafi babu hukunci ba, kuma duk mai baza ƙarairayi zai hallaka. Bai dace da wawa ya yi rayuwa cikin jin daɗi ba, haka ya fi muni bawa ya yi mulki a kan sarki! Hikimar mutum kan ba shi haƙuri; ɗaukakarsa ce ya ƙyale laifi. Fushin sarki yana kama da rurin zaki, amma tagomashinsa yana kama da raba a kan ciyawa. Wawan yaro lalacin mahaifinsa ne, mace mai yawan faɗa tana kama da ɗiɗɗigar ruwa. Ana gādon dawakai da wadata daga iyaye ne, amma mace mai basira daga Ubangiji ne. Ragwanci kan jawo zurfin barci, mutum mai sanyin jiki kuma yana tare da yunwa. Duk wanda ya bi umarnai kan tsare ransa, amma duk wanda ya ƙi binsu zai mutu. Duk wanda yake kirki ga matalauta yana ba wa Ubangiji bashi ne, zai kuwa sami lada game da abin da ya yi. Ka hori ɗanka, gama yin haka akwai sa zuciya; kada ka goyi baya lalacewarsa. Dole mai zafin rai yă biya tara; in ka fisshe shi sau ɗaya, to, sai ka sāke yin haka. Ka kasa kunne ga shawara ka kuma yarda da umarni, a ƙarshe kuwa za ka yi hikima. Da yawa ne shirye-shiryen zuciyar mutum, amma manufar Ubangiji ce takan cika. Abin da mutum yake sha’awa shi ne ƙauna marar ƙarewa; gara ka zama matalauci da ka zama maƙaryaci. Tsoron Ubangiji yakan kai ga rai. Sa’an nan mutum ya sami biyan bukata, ba abin da zai cuce shi. Rago kan sa hannunsa a kwano ba ya ma iya ɗaga shi ya kai bakinsa! Ka bulale mai ba’a, marasa azanci kuwa za su yi la’akari; ka tsawata wa mai basira, zai kuwa ƙara sani. Duk wanda ya yi wa mahaifinsa fashi ya kuma kori mahaifiyarsa ɗa ne da kan kawo kunya da wulaƙanci. In ka daina jin umarni, ɗana, za ka kuwa kauce daga kalmomin sani. Mai shaidar da yake malalaci yana wa shari’a ba’a ne, bakin mugaye kuma na haɗiye mugunta. An shirya tara saboda masu ba’a ne, dūka kuma saboda bayan wawaye. Ruwan inabi mai yin ba’a ne, barasa kuma mai rikici ne; duk wanda suka sa ya kauce marar hikima ne. Fushin sarki yana kama da rurin zaki; duk wanda ya sa shi fushi zai rasa ransa. Bangirma ne ga mutum ya guji faɗa, amma kowane wawa yana saurin yin faɗa. Rago ba ya noma a lokacin noma; saboda haka a lokacin girbi ba ya bukata samun kome. Manufofin zuciyar mutum zurfafan ruwaye ne, amma mutum mai basira yakan jawo su. Kowane mutum gani yake shi mai ƙauna marar ƙarewa ne, amma ina? Da ƙyar ka sami amintacce mutum guda. Mai adalci kan yi rayuwa marar abin zargi; masu albarka ne ’ya’yan da za su biyo bayansa. Sa’ad da sarki ya zauna kan kujerarsa don yă yi shari’a, yakan ga dukan mugunta da idanunsa. Wa zai iya cewa, “Na kiyaye zuciyata da tsarki; ni mai tsabta ne marar zunubi kuma”? Ma’auni marar gaskiya da magwajin da ba daidai ba, Ubangiji ya ƙi su duka. Akan san ƙananan yara ta ayyukansu, ana iya sani ko rayuwarsu amintattu ne, mai nagarta. Kunnuwan da suke ji da kuma idanun da suke gani, Ubangiji ne ya yi su duka. Kada ka so barci in ba haka ba za ka talauce; ka zauna a faɗake za ka kuwa kasance da sauran abinci. “Kai, ya yi tsada, ya yi tsada!” In ji mai saya; sa’ad da ya tafi yana taƙama a kan ya iya ciniki. Zinariya akwai ta, lu’ulu’u kuma ga shi a yalwace, amma leɓunan da suke magana da sani suna da wuyan samu kamar duwatsu masu daraja. A karɓi rigunan wanda ya ɗauki lamunin baƙo; a riƙe shi jingina in ya yi shi don mace marar aminci. Abincin da aka samu ta hanyar zamba yakan zama da daɗi, amma mutum zai ƙarasa da baki cike da yashi. Ka yi shirye-shirye ta wurin neman shawara; in kana yaƙi, ka sami bishewa. Mai gulma yakan lalace yarda; saboda haka ka guji mutum mai yawan surutu. In mutum ya zargi mahaifinsa ko mahaifiyarsa, fitilarsa za tă mutu a tsakiyar duhu. Gādon da aka samu da sauri a farkon farawa ba zai zama mai albarka a ƙarshe ba. Kada ka ce, “Zan rama wannan abin da aka yi mini!” Ka dogara ga Ubangiji, zai kuwa fisshe ka. Ubangiji ya ƙi ma’aunin da ba daidai ba, da kuma magwajin da ba su gamshe shi ba. Ubangiji ne yake bi da matakan mutum, Ta yaya wani zai fahimci hanyarsa? Tarko ne ga mutum ya keɓe wani abu da ba tunani daga baya kuma ya yi la’akari da alkawarinsa. Sarki mai hikima yakan gane mugunta; ya hukunta su ba tausayi. Fitilar Ubangiji kan bincika zuciyar mutum takan bincika lamirinsa. Ƙauna da aminci kan kiyaye sarki lafiya; ta wurin ƙauna sarautarsa za tă zauna a kafe. Ɗaukakar matasa maza ita ce ƙarfinsu, furfura ita ce darajar tsofaffi. Naushi da rauni kan share mugunta, dūka kuma kan tsabtacce lamiri. A hannun Ubangiji zuciyar sarki kamar ruwan rafi ne wanda yake bi da shi duk inda ya so. Mutum zai yi tunani hanyoyinsa daidai suke, amma Ubangiji yakan auna zuciya. Yin abin da yake daidai da kuma nagari Ubangiji ya fi yarda da shi fiye da hadaya. Girmankai da fariya, su ne fitilar mugaye, wannan kuwa zunubi ne! Shirye-shiryen mai aiki tuƙuru kan kai ga riba in kuwa ka cika gaggawa zai kai ga talauci. Dukiyar da aka samu ta wurin harshe mai yin ƙarya tarin tururi ne da kuma mugun tarko. Rikicin mugaye zai yi gāba da su, gama sun ƙi su yi abin da yake daidai. Hanyar mai laifi karkatacciya ce, amma halin marar laifi sukan aikata gaskiya. Gara a zauna a kusurwar rufin ɗaki da a zauna a gida ɗaya da mace mai fitina. Mugun mutum yakan zaƙu ya aikata mugunta; maƙwabcinsa ba ya samun jinƙai daga gare shi. Sa’ad da aka hukunta mai ba’a marasa azanci suka yi wayo; sa’ad da aka yi wa mai hikima umarni yakan sami sani. Mai Adalci kan lura da gidan mugu kan kuma zama sanadin lalacin mugu. In mutum ya toshe kunnuwansa ga kukan matalauci, shi ma zai yi kukan neman taimako ba kuwa zai sami amsa ba. Kyautar da aka yi a asirce takan kwantar da fushi, kuma cin hancin da aka rufe a cikin riga kan tā da fushi mai tsanani. Sa’ad da aka yi adalci, yakan kawo farin ciki ga mai adalci amma fargaba ga masu aikata mugunta. Mutumin da ya kauce daga hanyar fahimi kan zo ga hutu a ƙungiyar matattu. Duk mai son jin daɗi zai zama matalauci; duk mai son ruwan inabi da mai ba zai taɓa zama mai arziki ba. Mugu kan zama abin fansa don adali, marar aminci kuma don mai aikata gaskiya. Gara a zauna a hamada da a zauna da mace mai fitina da kuma mugun hali. A gidan mai hikima akwai wuraren ajiya na abinci da mai masu kyau, amma wawa kan cinye duk abin da yake da shi. Duk wanda ya nemi adalci da ƙauna kan sami rai, wadata da girmamawa. Mutum mai hikima kan fāɗa wa birnin jarumawa ya kuma rushe katangar da suka dogara a kai. Duk wanda yake lura da bakinsa da kuma harshensa kan kiyaye kansa daga masifa. Mai girmankai da kuma mai fariya, “Mai ba’a” ne sunansa; yana yin abubuwa da girmankai ainun. Marmarin rago zai zama mutuwarsa, domin hannuwansa sun ƙi su yi aiki. Dukan yini yana marmari ya sami ƙari, amma mai adalci yakan bayar hannu sake. Hadayar mugaye abin ƙyama ne, balle ma in aka kawo da mugun nufi! Mai ba da shaidar ƙarya zai hallaka, kuma duk wanda ya saurare shi zai hallaka har abada. Mugun mutum kan yi tsayin daka, amma mai aikata gaskiya kan yi tunani a kan abin da yake yi. Babu hikima, babu tunani, babu shirin da zai yi nasara a kan Ubangiji. Akan shirya doki domin ranar yaƙi, amma nasara tana ga Ubangiji ne. An fi son suna mai kyau fiye da wadata mai yawa; tagomashi kuma ya fi azurfa ko zinariya. Mawadaci da matalauci suna da abu guda. Ubangiji ne Mahaliccinsu duka. Mai basira kan ga damuwa tana zuwa yă nemi mafaka, amma marar azanci kan yi ta tafiya yă kuma sha wahala. Sauƙinkai da tsoron Ubangiji sukan kawo wadata da girmamawa da kuma rai. A hanyoyin mugu akwai kaya da tarko, amma duk wanda ya kiyaye ransa kan kauce musu. Ka hori yaro a hanyar da ya kamata yă bi, kuma sa’ad da ya tsufa ba zai bar ta ba. Mawadaci yakan yi mulki a kan matalauci, mai cin bashi kuwa bawan mai ba da bashi ne. Duk wanda ya shuka mugunta yakan girbe wahala, za a kuma hallaka sandar fushinsa. Mai bayarwa hannu sake shi kansa zai sami albarka, gama yakan raba abincinsa da matalauta. Ka hori mai ba’a, hatsaniya kuwa za tă yi waje; fitina da zargi kuma za su ƙare. Duk mai son tsabtar zuciya wanda kuma jawabinsa mai alheri ne zai zama aminin sarki. Idanun Ubangiji na lura da sani, amma yakan ƙi kalmomin marar aminci. Rago kan ce, “Akwai zaki a waje!” Ko kuma “Za a kashe ni a tituna!” Bakin mazinaciya rami ne mai zurfi; duk wanda yake a ƙarƙashin fushin Ubangiji zai fāɗa a ciki. Wauta tana da yawa a zuciyar yara, amma sandar horo zai kore ta nesa da su. Duk wanda yake danne matalauta don yă azurta kuma duk wanda yake kyauta ga mawadata, dukansu kan talauta. Ka kasa kunne ka kuma saurara ga maganganu masu hikima; ka yi amfani da abin da nake koyarwa, gama yana da daɗi sa’ad da ka kiyaye su a zuciyarka ka kuma kasance da su a shirye a leɓunanka. Domin dogarawarka ta kasance ga Ubangiji, ina koya maka yau, har kai ma. Ban rubuta maka maganganu talatin ba, maganganun shawara da sani, ina koya maka gaskiya da kalmomin da za ka dogara a kai, saboda ka iya ba da amsa daidai ga duk wanda ya aike ka? Kada ka zalunci matalauta a kan suna matalauta kada kuma ka ƙwari wanda ba shi da mai taimako a gaban shari’a, gama Ubangiji zai yi magana dominsu zai kuwa washe waɗanda suka washe su. Kada ka yi abokantaka da mai zafin rai, kada ka haɗa kai da wanda ba shi da wuya ya yi fushi, in ba haka ba za ka koyi hanyoyinsa ka kuma sa kanka a tarko. Kada ka zama mai ɗaukar lamuni ko ka ba da jingina saboda bashi; gama in ka kāsa biya za a ƙwace gadon da kake kwanciya a kai ma. Kada ka matsar da shaidar kan iyakar da kakanninka suka kafa. Kana ganin mutumin da yake da gwaninta a cikin aikinsa? Zai yi wa sarakuna hidima; ba zai yi hidima wa mutanen da ba su iya ba. Sa’ad da ka zauna domin cin abinci da mai mulki, ka lura sosai da abin da yake gabanka, ka kuma sa wuƙa a maƙogwaronka in kai mai ci da yawa ne. Kada ka yi marmarin abincinsa mai daɗi gama wannan abinci ruɗu ne. Kada ka gajiyar da kanka don ka yi arziki; ka kasance da hikimar dainawa. Da ƙyiftawar ido a kan wadata ta ɓace, gama tabbatacce sukan yi fikafikai sukan tashi sama kamar gaggafa. Kada ka ci abincin mai rowa, kada ka yi marmarin abincinsa mai daɗi; gama shi wani irin mutum ne wanda kullum yana tunani game da tsadar abincin. Zai ce maka, “Ci ka sha,” amma zuciyarsa ba ta tare da kai. Za ka yi amai ɗan abin da ka ci dukan daɗin bakinka kuwa zai tafi a banza. Kada ka yi magana da wawa, gama zai yi wa maganar hikimarka ba’a. Kada ka kawar da shaidar iyaka ta dā ko ka ɗiba gonar marayu, gama mai Kāriyarsu yana da ƙarfi; zai kuwa yi magana dominsu. Ka mai da hankali ga umarni ka kuma kasa kunne ga kalmomin sani. Kada ka bar yaro ba horo; in ka yi masa horo da sanda, ba zai mutu ba. Ka hukunta shi da sanda ka ceci ransa daga mutuwa. Ɗana, in zuciyarka mai hikima ce, to, zuciyata za tă yi murna; cikin cikina zai yi farin ciki in leɓunanka suna maganar abin da yake daidai. Kada ka bar zuciyarka tă yi ƙyashin masu zunubi, amma kullum tsoron Ubangiji za ka yi kishi. Tabbatacce akwai sa zuciya ta nan gaba dominka, kuma sa zuciyarka ba za tă zama a banza ba. Ka saurara, ɗana, ka zama mai hikima, ka kafa zuciyarka a hanyar da take daidai. Kada ka haɗa kai da waɗanda suke shan ruwan inabi da yawa ko masu haɗama kansu da abinci, gama bugaggu da ruwan inabi da masu yawan ci sukan zama matalauta, gama jiri yakan yi musu sutura da tsummoki. Ka kasa kunne ga mahaifinka, wanda ya ba ka rai, kada kuwa ka rena mahaifiyarka sa’ad da ta tsufa. Ka saye gaskiya kada kuwa ka sayar da ita; ka nemi hikima, horo da fahimi. Mahaifin adali yana da farin ciki sosai; duk wanda yake da ɗa mai hikima yakan ji daɗinsa. Bari mahaifinka da mahaifiyarka su yi murna; bari wadda ta haife ka tă yi farin ciki! Ɗana, ka ba ni zuciyarka bari kuma idanunka su kiyaye hanyoyina, gama karuwa rami ne mai zurfi mace marar aminci matsattsiyar rijiya ce. Kamar ’yan fashi, takan kwanta tana jira tana kuma ninka rashin aminci a cikin maza. Wa yake wayyo? Wa yake baƙin ciki? Wa yake neman fada? Wa yake gunaguni? Wa yake da raunuka ba dalili? Wa yake da jan idanu? Waɗanda suke daɗe suna shan ruwan inabi, waɗanda suke neman ƙoƙon damammen ruwan inabi. Kada ka ƙyifce ido a ruwan inabi sa’ad da ya yi ja, sa’ad da yana da kyan gani a cikin ƙwarya, sa’ad da yana gangarawa sumul a maƙogwaro! A ƙarshe yana sara kamar maciji da kuma dafi kamar gamsheƙa. Idanunka za su riƙa gane-gane, zuciyarka kuma za su riƙa tunani abubuwa masu rikitarwa. Za ka zama kamar wanda yake barci a tsakiyar tekuna, kwance a sama itacen jirgin ruwa. Za ka ce “Sun buge ni, amma ban ji ciwo ba! Sun daddoke ni, amma ba na jin zafinsa! Yaushe zan farka don in ƙara shan wani?” Kada ka yi ƙyashin mugaye, kada ka yi sha’awar ƙungiyarsu; gama leɓunansu suna maganar tā-da-na-zaune-tsaye ne. Ta wurin hikima ce ake gina gida, kuma ta wurin fahimi ake kafa ta; ta wurin sani ɗakunanta sukan cika da kyawawan kayayyaki masu daraja. Mutum mai hikima yana da iko sosai, kuma mutum mai sani yakan ƙaru da ƙarfi; don yin yaƙi kana bukatar bishewa, kuma don ka yi nasara kana bukatar mashawarta masu yawa. Hikima ta yi wa wawa nisa ƙwarai a cikin taro a ƙofar gari ba shi da ta cewa. Duk mai ƙulla mugunta za a ɗauka shi mai kuta hargitsi ne. Makircin wawa zunubi ne, mutane kuma sukan yi ƙyamar mai ba’a. In ba ka da ƙarfi a lokacin wahala, ka tabbatar kai marar ƙarfi ne sosai! Ka kuɓutar da waɗanda ake ja zuwa inda za a kashe su; ka riƙe waɗanda suke tangaɗi zuwa wajen yanka. In kuka ce, “Ai, ba mu san wani abu a kai wannan ba,” shi da yake awon ba shi da zuciyar ganewa ne? Shi da yake tsare ranka bai sani ba ne? Ba zai sāka wa kowane mutum bisa ga abin da ya aikata ba? Ka sha zuma, ɗana, ka sha zuma gama tana da kyau; zuma daga kaki yana da zaƙi a harshenka. Ka kuma san cewa hikima tana da zaƙi ga rai; in ka same ta, akwai sa zuciya ta nan gaba dominka, kuma sa zuciyarka ba za tă zama a banza ba. Kada ka kwanta kana fako kamar ɗan iska don ƙwace gidan adali, kada ka ƙwace masa wurin zama; gama ko da adali ya fāɗi sau bakwai, yakan tashi kuma, amma bala’i kan kwantar da mugaye. Kada ka yi dariya sa’ad da abokin gāba ya fāɗi; sa’ad da ya yi tuntuɓe, kada ka yi farin ciki, in ba haka ba in Ubangiji ya gani ba zai amince ba ya kuma juye fushinsa daga gare shi. Kada ka ji tsoro saboda masu mugunta ko ka yi ƙyashin mugaye, gama mugu ba shi da zuciya ta nan gaba, kuma fitilar mugaye za tă mutu. Ka ji tsoron Ubangiji da kuma sarki, ɗana, kuma kada ka haɗa kai da masu tayarwa, gama za a tura waɗannan biyu zuwa hallaka nan da nan, kuma wa ya sani irin bala’in da za su iya kawowa? Waɗannan ma maganganun masu hikima ne, Nunan sonkai a shari’a ba shi da kyau. Duk wanda ya ce wa mai laifi, “Ba ka da laifi”, mutane za su la’ance shi al’umma kuma za tă ce ba a san shi ba. Amma zai zama da lafiya ga duk waɗanda suka hukunta masu laifi, kuma babban albarka zai zo a kansu. Amsa da take ta gaskiya tana kamar sumba a leɓuna. Ka gama aikinka ka kuma shirya gonakinka; bayan haka, ka gina gidanka. Kada ka ba da shaida a kan maƙwabcinka ba tare da isashen dalili ba, ko ka yi amfani da leɓunanka ka yi ruɗu. Kada ka ce, “Zan yi masa kamar yadda ya yi mini; zan rama abin da wannan mutum ya yi mini.” Na wuce cikin gonar rago, na wuce cikin gonar inabin mutumin da ba shi da azanci; ƙayayyuwa sun yi girma ko’ina, ciyayi sun rufe ƙasar, katangar duwatsu duk ta rushe. Na yi tunani a zuciyata na kuwa koyi darasi daga abin da na gani. Ɗan barci, ɗan gyangyaɗi, ɗan naɗin hannuwa don a huta, sai talauci ya shigo maka kamar ’yan fashi rashi kuma ya zo maka kamar mai hari. Waɗannan ƙarin karin maganar Solomon ne waɗanda mutanen Hezekiya sarkin Yahuda suka tara. Ɗaukakar Allah ce a ɓoye batun; a bayyana batun kuwa ɗaukakar sarakuna ne. Kamar yadda sammai suna can bisa duniya kuma tana da zurfi, haka zukatan sarakuna suka wuce a bincika. Ka tace azurfa sai kayan su fito don maƙerin azurfa; ka cire mugaye daga gaban sarki, kursiyinsa kuwa zai kahu ta wurin adalci. Kada ka ɗaukaka kanka a gaban sarki, kada kuma ka nemi wa kanka wuri a cikin manyan mutane; gara ya ce maka, “Ka hauro nan,” da a ƙasƙantar da kai a gaban wani mai makami. Abin da ka gani da idanunka kada ka yi garaje kai ƙara a majalisa, gama me za ka yi a ƙarshe in maƙwabcinka ya ba ka kunya? In kai da maƙwabcinka kuka yi gardama, kada ka tona asirin wani, in ba haka ba duk wanda ya ji zai kunyata ka ba za ka kuma taɓa rabuwa da wannan mummuna suna ba. Kalmar da aka faɗa daidai tana kamar zubin zinariyar da aka yi a mazubin azurfa. Kamar ’yan kunnen zinariya ko kuwa kayan ado na zinariya zalla haka yake da tsawatawar mai hikima ga kunne mai saurarawa. Kamar sanyin ƙanƙara a lokacin girbi haka ɗan saƙo mai aminci wanda aka aika; ya wartsakar da ran waɗanda suka aike shi. Kamar gizagizai da kuma iska marar ruwan sama haka mutumin da yake fariya a kan kyautan da ba ya bayarwa. Ta wurin haƙuri akan rinjaye mai mulki, magana mai hankali kan karye ƙashi. In ka sami zuma, ka sha isashe kawai, in ya yi yawa, za ka yi amai. Kada ka cika ziyarar gidan maƙwabcinka yawan ganinka zai sa ya ƙi ka. Kamar sanda ko takobi ko kibiya mai tsini haka yake da mutumin da yake ba da shaidar ƙarya a kan maƙwabcinsa. Kamar haƙori mai ciwo ko yin tafiya da gurguwar ƙafa haka yake ga mai dogara da marasa aminci a lokacin wahala. Kamar wanda ya tuɓe riga a ranar da ake sanyi, ko kuwa kamar zuba ruwan tsami a kanwa, haka yake da mai rera waƙoƙi ga mai baƙin ciki. In abokin gābanka yana jin yunwa, ka ba shi abinci ya ci; in yana jin ƙishi, ka ba shi ruwa ya sha. Ta yin haka, za ka tara garwashin wuta mai ci a kansa, Ubangiji kuma zai sāka maka. Kamar yadda iskar arewa kan kawo ruwan sama, haka jita-jita kan kawo fushi. Gara a zauna a kusurwar rufin ɗaki da a zauna a gida ɗaya da mace mai fitina. Kamar ruwan sanyi ga ran da ya gaji haka yake da jin labari mai daɗi daga ƙasa mai nisa. Kamar rafi mai laka ko rijiyar da ta gurɓace haka yake da mai adalci wanda ya miƙa wuya ga mugaye. Ba shi da kyau ka sha zuma da yawa, haka ma ba shi da kyau ka nemi girma wa kanka. Kamar birni da katangarsa sun rushe haka yake da mutumin da ba ya iya danne fushinsa. Kamar ƙanƙara a rani ko ruwan sama a lokacin girbi, haka girmamawa bai dace da wawa ba. Kamar gwara mai yawo ko alallaka mai firiya, haka yake da la’anar da ba tă dace tă kama ka ba take. Bulala don doki, linzami don jaki, sanda kuma don bayan wawaye! Kada ka amsa wa wawa bisa ga wautarsa, in ba haka ba kai kanka za ka zama kamar sa. Ka amsa wa wawa bisa ga wautarsa, in ba haka ba zai ga kansa mai hikima ne. Kamar datsewar ƙafafun wani ko shan dafi haka yake da a aika da saƙo ta hannun wawa. Kamar ƙafafun gurgun da suka yi laƙwas haka karin magana yake a bakin wawa. Kamar ɗaura dutse a majajjawa haka yake da girmama wawa. Kamar suƙar ƙaya a hannun wanda ya bugu haka karin magana yake a bakin wawa. Kamar maharbi wanda yake jin wa kowa rauni haka yake da duk wanda ya yi hayan wawa ko wani mai wucewa. Kamar yadda kare kan koma ga amansa, haka wawa kan maimaita wautarsa. Gwamma riƙaƙƙen wawa da mutum mai ganin kansa mai hikima ne. Rago yakan ce, “Akwai zaki a kan hanya, zaki mai faɗa yana yawo a tituna!” Kamar yadda ƙofa kan juya a ƙyaurensa, haka rago yake jujjuya a gadonsa. Rago kan sa hannunsa a kwano ba ya ma iya ɗaga shi ya kai bakinsa. Rago yana gani yana da hikima fiye da mutane bakwai da suke ba da amsa da dalilai a kan ra’ayinsu. Kamar wani da ya kama kare a kunnuwa haka yake da mai wucewa da ya tsoma baki a faɗan da ba ruwansa. Kamar yadda mahaukaci yake harbin cukwimai ko kibiyoyi masu dafi haka yake da mutumin da ya ruɗe maƙwabci sa’an nan ya ce, “Wasa ne kawai nake yi!” In ba itace wuta takan mutu; haka kuma in ba mai gulma ba za a yi faɗa ba. Kamar yadda gawayi yake ga murhu, itace kuma ga wuta, haka mutum mai neman faɗa yake ga faɗa. Kalmomin mai gulma suna kama da burodi mai daɗi; sukan gangara can cikin cikin mutum. Kamar kaskon da aka dalaye da azurfar da ba a tace ba haka leɓuna masu mugun zuciya. Mai yin ƙiyayya yakan ɓoye kansa da maganar bakinsa, amma a cikin zuciyarsa yana cike da munafunci Ko da jawabinsa ya ɗauki hankali, kada ka gaskata shi, gama abubuwa ƙyama guda bakwai sun cika zuciyarsa. Wataƙila ya ɓoye ƙiyayyarsa da ƙarya, duk da haka za a tone muguntarsa a cikin taro. In mutum ya haƙa rami, shi zai fāɗi a ciki; in mutum ya mirgino dutse, dutsen zai mirgine a kansa. Harshe mai faɗin ƙarya yana ƙin waɗanda yake ɓata musu rai, daɗin baki kuma yakan aikata ɓarna. Kada ka yi fariya a kan gobe gama ba san abin da ranar za tă kawo ba. Ka bar wani ya yabe ka, ba kai kanka ba; wani dabam, ba leɓunanka ba. Dutse yana da nauyi yashi kuma wahala ce, amma tsokanar wawa ta fi su duka nauyi. Fushi mugun abu ne mai hallakarwa, amma wa zai iya tsaya a gaban kishi? Gara tsawatawar da ake yi a fili da ƙaunar da ake yi a ɓoye. Za a iya amince da rauni daga aboki, amma abokin gāba ko da ya sumbace ka kada ka sake da shi! Duk wanda ya ƙoshi da zuma, ba ya marmarinsa kuma amma wanda yake yunwa ko abin da yake da ɗaci ma zai ji shi da zaƙi. Kamar tsuntsun da ya ɓace daga sheƙarsa haka yake da mutumin da ya bar gidansa. Man shafawa mai ƙanshi da kuma turare kan faranta zuciya, gaisuwar amini kuma takan fito daga shawarar kirki. Kada ka manta da abokinka da kuma abokin mahaifinka, kuma kada ka tafi gidan ɗan’uwanka sa’ad da masifa ta same ka, gara ka je wurin maƙwabci na kusa da ka je wurin ɗan’uwan da yake da nisa. Ka zama mai hikima, ɗana, ka kuma faranta mini zuciya; zan iya amsa kowace irin suƙar da wani zai yi mini. Mai basira kan hango hatsari ya kuma kauce, marar azanci zai yi ta kutsa kai ciki, daga baya ya yi da na sani. A karɓe rigunan wanda ya ɗauki lamunin baƙo; a riƙe shi jingina in ya yi shi don mace marar aminci. In mutum ya albarkaci maƙwabcinsa da murya mai ƙarfi da sassafe, za a ɗauka shi a matsayin la’ana. Mace mai fitina kamar ɗiɗɗigar ruwa take ba ƙaƙƙautawa; hana ta yana kamar yin ƙoƙari tsai da iska ne ko yin ƙoƙarin cafke mai a tafin hannunka. Kamar yadda ƙarfe kan wasa ƙarfe haka mutum kan koyi daga mutum. Duk wanda ya lura da itacen ɓaure, zai ci ’ya’yansa, kuma duk wanda ya lura da maigidansa za a girmama shi. Kamar yadda ruwa kan nuna yadda fuska take, haka zuciyar mutum kan nuna irin mutumin. Mutuwa da Hallaka ba sa ƙoshi, haka idanun mutum ba sa ƙoshi da gani. Ana gwajin azurfa da kuma zinariya da wuta, amma akan gwada mutum ta wurin yabon da ya samu. Ko da ka daka wawa a turmi, kana daka shi kamar hatsi da taɓarya, ba za ka fid da wauta daga gare shi ba. Ka tabbata ka san lafiyar garken tumakinka, ka mai da hankali ga garken shanunka; domin dukiya ba ta dawwama har abada, ba a kuma kasance da rawani daga tsara zuwa tsara. Sa’ad da aka yanki ingirci sabon toho kuma ya bayyana aka kuma tattara ciyawa daga tuddai, gashin raguna za su tanada maka tufafi, za ka iya sayi gonaki masu kyau da kuɗin awaki. Za ka kasance da madarar awaki mai yawa don ka ciyar da kanka da kuma iyalinka ka kuma inganta bayinka mata. Mugu yakan gudu ko babu wanda yake korarsa, amma adalai suna da ƙarfin hali kamar zaki. Sa’ad da ƙasa ta yi tayarwa, takan kasance da masu mulki da yawa, amma mai fahimi da sani kan mai da zaman lafiya. Mai mulkin da ya danne talakawa yana kama da ruwan saman da ya lalatar da hatsi. Duk waɗanda ba sa bin doka yabon mugaye suke yi, amma waɗanda suke yin biyayya da doka suna gāba da mugaye ke nan. Mugaye ba su san gaskiya ba, amma waɗanda suke neman Ubangiji sun santa sosai. Gara matalauci wanda yake tafiya babu abin zargi da mai arziki wanda hanyoyinsa mugaye ne. Duk wanda ya kiyaye doka ɗa ne mai la’akari, amma wanda yake abokantaka da masu zari yakan jawo wa mahaifinsa kunya. Duk wanda ya tara dukiyarsa ta wurin ba da bashi da ruwan da ya wuce misali yana tara wa wani ne wanda zai yi wa talakawa alheri. In wani ya yi kunnuwa ƙashi ga doka ko addu’arsa ma abar ƙyama ce. Duk wanda ya jagorance masu aikata gaskiya a hanyar mugunta zai fāɗa cikin tarkonsa amma marasa abin zargi za su sami gādo mai kyau. Mai arziki zai yi zato shi mai hikima ne a ganinsa, amma matalauci mai basira ya fi shi sanin abin da yake daidai. Sa’ad da adalai suka yi nasara, kowa yakan yi biki; amma sa’ad da mugu ya samu shugabanci, mutane sukan yi ta ɓuya. Duk wanda ya ɓoye zunubansa ba ya taɓa cin nasara, amma duk wanda ya furta ya kuma ƙi su yakan sami jinƙai. Mai albarka ne mutumin da kullum yake jin tsoron Allah, amma duk wanda ya taurare zuciyarsa yakan shiga wahala. Kamar rurin zaki ko sanɗar beyar haka mugun mutum mai mulki a kan mutane marasa ƙarfi yake. Mugu mai mulki ba shi da azanci, amma duk wanda yake ƙin ƙazamar riba yakan yi tsawon rai. Mutumin da laifin kisa ya yi ta damunsa zai zama mai gudu don tsoro har mutuwa; kada wani ya taimake shi. Duk wanda ya yi tafiya marar abin zargi zai zauna lafiya, amma duk wanda hanyoyinsa mugaye ne zai fāɗi nan da nan. Duk wanda ya nome gonarsa zai sami amfani a yalwace, amma duk wanda yake zaman banza zai zama matalauci a koyaushe. Mutum mai aminci zai cika da albarka, amma duk mai son yin arziki dare ɗaya zai sha hukunci. Nuna sonkai ba shi da kyau, duk da haka mutum zai aikata abin da ba daidai ba saboda ’yar ƙaramar rashawa. Mai rowa yana alla-alla ya yi arziki bai san cewa talauci ne ke jiransa ba. Duk wanda ya tsawata wa wani mutum zai sami yabo a ƙarshe fiye da wanda yake mai daɗin baki. Duk wanda ya yi wa mahaifin ko mahaifiyarsa sata ya kuma ce, “Ai, ba laifi ba ne” abokin mai hallakarwa ne shi. Mai haɗama yakan jawo tā-da-na-zaune-tsaye, amma duk wanda ya dogara ga Ubangiji zai yi nasara. Duk mai dogara ga kansa wawa ne, amma duk wanda yake tafiya da hikima zai zauna lafiya. Duk wanda yake bayarwa ga matalauta ba zai rasa kome ba, amma duk wanda bai kula da su ba yana samu la’ana masu yawa. Sa’ad da mugu ya samu shugabanci, mutane sukan yi ta ɓuya; amma sa’ad da mugu ya hallaka, adali kan ci gaba cikin arziki da lafiya. Mutumin da ya ci gaba da taurinkai bayan an kwaɓe shi ba da daɗewa ba zai hallaka ba makawa. Sa’ad da masu adalci suke cin nasara, mutane kan yi farin ciki sa’ad da mugaye suke mulki, mutane kan yi nishi. Duk mai ƙaunar hikima kan kawo wa mahaifinsa farin ciki, amma wanda yake ma’amala da karuwai kan lalatar da dukiyarsa. Ta wurin yin adalci sarki kan sa ƙasa tă yi ƙarƙo amma duk mai haɗama don cin hanci kan rushe ƙasar. Duk wanda yake wa maƙwabcinsa daɗin baki yana sa wa ƙafafunsa tarko ne. Mugun mutum tarko ne ta wurin zunubinsa, amma mai adalci zai iya rera ya kuma yi murna. Masu adalci sun damu game da adalci don talakawa, amma mugaye ba su da wannan damuwa. Masu ba’a kan kuta faɗa a birni, amma masu hikima sukan kwantar da fushi. In mai hikima ya je wurin shari’a da wawa, wawa kan yi ta fushi yana ta dariya, ba kuwa za a sami salama ba. Masu kisankai sukan ƙi mutum mai mutunci su kuma nema su kashe mai aikata gaskiya. Wawa yakan nuna fushinsa a fili, amma mai hikima kan kanne fushinsa. In mai mulki yana sauraran ƙarairayi, dukan ma’aikatansa za su zama mugaye. Matalauci da azzalumi suna da wannan abu ɗaya. Ubangiji ne yake ba dukansu gani. In sarki yana hukunta talakawa da adalci kursiyinsa kullum zai kasance lafiya. Sandar gyara kan ba da hikima, amma yaron da aka bari ba horo kan jawo kunya ga mahaifiyarsa. Sa’ad da mugaye suke cin nasara, haka zunubi zai yi ta ƙaruwa, amma masu adalci za su ga fāɗuwar waɗannan mutane. Ka hori ɗanka, zai kuwa ba ka salama; zai ba ka farin cikin da kake so. Inda ba wahayi, mutane kan kangare; amma masu albarka ne waɗanda suke kiyaye doka. Ba a yi wa bawa gyara ta wurin magana kawai; ko da ya fahimta ma, ba zai kula ba. Ka ga mutum mai yin magana da garaje? To, gara a sa zuciya ga wawa da a sa zuciya gare shi. In mutum ya yi wa bawansa shagwaɓa tun yana yaro, zai jawo baƙin ciki a ƙarshe. Mutum mai cika fushi yakan tā da faɗa, mai zafin rai kuma kan yi zunubai masu yawa. Fariyar mutum kan jawo masa ƙasƙanci amma mai sauƙinkai kan sami girmamawa. Duk wanda yake abokin ɓarawo abokin gāban kansa ne; yana jin sa yana ta rantsuwa, amma bai isa ya ce kome ba. Jin tsoron mutum tarko ne, amma duk wanda ya dogara ga Ubangiji zai zauna lafiya. Mutane sukan nemi samun farin jini daga wurin sarki, amma daga wurin Ubangiji ne mutum kan sami adalci. Masu adalci suna ƙyamar masu rashin gaskiya; mugaye sukan yi ƙyamar masu aikata gaskiya. Maganganun Agur ɗan Yake, magana ce horarriya. Wannan mutum ya furta wa Itiyel da kuma ga Ukal, “Ni ne mafi jahilci a cikin mutane; ba ni da fahimi irin na mutum. Ban koyi hikima ba, ba ni kuma da sani game da Mai Tsarkin nan, Wane ne ya taɓa haura zuwa sama ya dawo? Wane ne ya tattara iska a tafin hannuwansa? Wane ne ya nannaɗe ruwaye a cikin rigarsa? Wane ne ya kafa dukan iyakokin duniya? Mene ne sunansa, da kuma sunan ɗansa? Faɗa mini in ka sani! “Kowace maganar Allah ba ta da kuskure; shi ne garkuwa ga waɗanda suke neman mafaka daga gare shi. Kada ka ƙara ga maganarsa, in ba haka ba zai tsawata maka ya kuma nuna kai maƙaryaci ne. “Abu biyu ina roƙonka, ya Ubangiji; kada ka hana ni kafin in mutu. Ka kawar da ƙarya da kuma ƙarairayi nesa da ni; kada ka ba ni talauci ko arziki, amma ka ba ni abincina na yini kaɗai. In ba haka ba, zan wadace in ƙi ka har in ce, ‘Wane ne Ubangiji?’ Ko kuwa in zama matalauci in yi sata ta haka in kunyata sunan Allahna. “Kada ka baza ƙarairayi game da bawa ga maigidansa, in ba haka ba, zai la’ance ka, za ka kuwa sha wahala a kan haka. “Akwai waɗanda sukan zagi mahaifinsu ba sa kuma sa wa mahaifiyarsu albarka; waɗanda sukan ɗauka su tsarkaka ne a ganinsu alhali kuwa ƙazamai ne su; waɗanda kullum idanunsu masu kallon reni ne, waɗanda kallon da suke yi na daurin gira ne; waɗanda haƙoransu takuba ne waɗanda kuma muƙamuƙansu tarin wuƙaƙe ne don su cinye matalauta daga duniya da kuma mabukata daga cikin mutane. “Matsattsaku tana da ’ya’ya mata biyu. Suna kuka suna cewa, ‘Ba ni! Ba ni!’ “Akwai abubuwa uku da ba sa taɓa ƙoshi, guda huɗu ba sa taɓa cewa, ‘Ya isa!’ Kabari, mahaifar da ba ta haihuwa, ƙasa, wadda ba ta taɓa ƙoshi da ruwa, da kuma wuta, wadda ba ta taɓa cewa ‘Ya isa!’ “Idon da yake yi wa mahaifi ba’a, wanda yake wa mahaifiya dariyar rashin biyayya, hankakin kwari za su ƙwaƙule masa ido, ungulai za su cinye su. “Akwai abubuwa uku da suke ba ni mamaki, abubuwa huɗu da ba na iya fahimtarsu, yadda gaggafa take firiya a sararin sama, yadda maciji yake tafiya a kan dutse, yadda jirgin ruwa yake tafiya a teku, da kuma sha’ani tsakanin namiji da ’ya mace. “Ga yadda mazinaciya take yi. Takan ci ta share bakinta ta ce, ‘Ban yi wani abu marar kyau ba.’ “Akwai abubuwa uku da duniya kan yi rawan jiki, abubuwa huɗu da ba ta iya jurewa, bawan da ya zama sarki, wawan da ya ƙoshi da abinci, macen da ba a ƙauna wadda ta sami miji, da kuma baiwar da ta ɗauki matsayin uwargijiyarta. “Akwai abubuwa huɗu a duniya da suke ƙanana, duk da haka suna da hikima ƙwarai. Kyashi halittu ne da ba su da ƙarfi sosai, duk da haka suna ajiyar abincinsu da rani; remaye halittu ne da ba su da ƙarfi sosai, duk da haka sukan yi gidajensu a duwatsu; fāra ba su da sarki, duk da haka suna tafiya tare bisa ga girma; ana iya kama ƙadangare da hannu, duk da haka akan same shi a fadodin sarakuna. “Akwai abubuwa uku da suke jan jiki da kuma taƙama a tafiyarsu abubuwa huɗu waɗanda suke kwarjini da taƙama a tafiyarsu, zaki mai ƙarfi a cikin namun jeji, wanda ba ya ratse wa kowa; zakara mai taƙama, da bunsuru, da kuma sarki mai sojoji kewaye da shi. “In ka yi wauta ka kuma ɗaukaka kanka, ko kuwa wani yana ƙulla maka mugunta, ka dāfa hannunka a bisa bakinka! Gama kamar yadda kaɗaɗɗen madara takan kawo mai, murɗa hanci kuma takan sa a yi haɓo, haka tsokanar fushi takan kawo faɗa.” Maganganun Sarki Lemuwel, magana ce horarriya mahaifiyarsa ta koya masa, “Ka saurara, ya ɗana! Ka saurara, ɗan cikina! Ka saurara, ya ɗan amshin addu’ata! Kada ka ba da ƙarfinka a kan mata, ƙarfinka ga waɗanda suka hallaka sarakuna. “Ba na sarakuna ba ne, ya Lemuwel, ba na sarakuna ba ne su sha ruwan inabi, ba na masu mulki ba ne su yi marmarin barasa, don kada su sha su manta da abin da doka ta umarta, su hana wa waɗanda aka danne hakkinsu. A ba da barasa ga waɗanda suke cikin halin ƙaƙa naka yi, ruwan inabi ga waɗanda suke cikin wahala; bari su sha su manta da talaucinsu kada kuma su ƙara tunawa da ɓacin ransu. “Yi magana domin bebaye, domin hakkin dukan waɗanda suke naƙasassu. Yi magana a kuma yi shari’ar adalci; a tsare hakkin talakawa da masu bukata.” Wa yake iya samun mace mai halin kirki? Darajarta ta fi ta lu’ulu’ai. Mijinta yana da cikakken amincewa da ita kuma ba ya rasa wani abu mai daraja. Takan yi masa alheri ba mugunta ba, dukan kwanakin ranta. Takan zaɓi ulu da lilin ta yi ta saƙa da hannuwanta da farin ciki. Ita kamar jirgin ’yan kasuwa ne tana kawo abincinta daga nesa. Takan farka tun da sauran duhu; ta tanada wa iyalinta abinci ta kuma shirya wa ’yan matan gidanta ayyukan da za su yi. Takan lura da gona sosai ta kuma saye ta; daga abin da take samu na kuɗin shiga take shuka gonar inabi. Takan himmantu tă yi aikinta tuƙuru; hannuwanta suna da ƙarfi domin ayyukanta. Takan tabbata akwai riba a kasuwancinta, kuma fitilarta ba ya mutuwa da dare. Da hannunta take riƙe abin kaɗi ta kuma kama abin saƙa da yatsotsinta. Takan marabci talakawa takan kuma taimaki masu bukata. Sa’ad da ƙanƙara ta fāɗi, ba ta jin tsoro saboda gidanta; gama dukansu suna da tufafi masu kauri. Takan yi wa gadonta kayan shimfiɗa; tufafinta kuma na lilin ne mai laushi na shunayya. Ana girmama mijinta a ƙofar shiga birni inda yakan zauna a cikin dattawan gari. Takan yi riguna na lilin ta sayar; takan kuma sayar wa ’yan kasuwa da ɗamara. Ƙarfi da mutunci su ne suturarta; za tă iya yin dariyar kwanaki masu zuwa. Tana magana da hikima, kuma umarnai mai aminci yana a harshenta. Tana lura da sha’anin gidanta kuma ba ta cin abincin ƙyuya. ’Ya’yanta sukan tashi su ce da ita mai albarka; haka mijinta ma, yakan kuma yabe ta yana cewa, “Mata da yawa suna yin abubuwan yabo, amma ke kin fi su duka.” Kayan tsari yana ruɗu, kyau kuma kan shuɗe; amma mace mai tsoron Ubangiji abar yabo ce. Ka ba ta ladar da ya dace tă samo wa kanta, bari kuma ayyukanta su kawo mata yabo a ƙofar shiga birni. Kalmomin Malami, ɗan Dawuda, Sarki a Urushalima. “Ba amfani! Ba amfani!” In ji Malami. “Gaba ɗaya ba amfani! Kome ba shi da amfani!” Wace riba ce mutum yake samu daga wahalar da yake fama a duniya? Zamanai sukan zo zamanai su wuce, amma duniya tana nan har abada. Rana takan fito rana ta kuma fāɗi, ta kuma gaggauta zuwa inda takan fito. Iska takan hura zuwa kudu ta kuma juya zuwa arewa; tă yi ta kewayewa, tă yi ta koma inda take fitowa. Dukan rafuffuka sukan gangara zuwa teku, duk da haka teku ba ya cika. Daga inda rafuffukan suke fitowa, a can suke komawa kuma. Dukan abubuwa suna kawo gajiya, gaban magana. Ido ba ya gaji da gani, haka ma kunne yă ƙoshi da ji. Abin da ya taɓa kasancewa, zai sāke kasance, abin da aka yi za a sāke yi kuma; babu wani abu sabo a duniya. Akwai wani abin da za a ce, “Duba! Ga wani abu sabo”? Abin yana nan, tun dā can, ya kasance kafin lokacinmu. Ba a tunawa da mutanen dā, haka su ma da ba a haifa ba tukuna waɗanda za su biyo bayansu ba za a tuna da su ba. Ni, Malami, sarki ne bisa Isra’ila a Urushalima. Na dauri aniyata in gwada don in bincika ta wurin hikima dukan abin da ake yi a duniya. Kaya mai nauyi ne Allah ya ɗora a kan mutane! Na ga dukan abubuwan da ake yi a duniya, dukansu ba su da amfani, naushin iska ne kawai. Abin da yake tanƙwararre ba zai miƙu ba; ba za a kuma iya ƙidaya abin da ba shi ba. Na yi tunani a raina na ce, “Duba, na yi girma, na kuma ƙaru da hikima fiye da duk wanda ya taɓa mulki a bisa Urushalima kafin ni; na ɗanɗana hikima mai yawa da kuma ilimi.” Sa’an nan na ɗaura aniyata ga fahimtar hikima, in kuma san bambanci tsakanin hauka da wauta, amma na koyi cewa wannan ma, naushin iska ne kawai. Gama yawan hikima yakan kawo yawan baƙin ciki; yawan sani, yawan ɓacin rai. Na ce wa kaina, “Zo, zan gwada ka da jin daɗi don in ga abin da yake da kyau.” Amma wannan ma ya zama ba amfani. Sai na ce, “Dariya hauka ce. Kuma me jin daɗi yake kawowa?” Na yi ƙoƙari in sa raina yă yi farin ciki da ruwan inabi, in kuma rungumi wauta, hankalina kuma yana yin mini jagora da hikima. Na so in ga abin da yake da daraja ga mutane a duniya a ’yan kwanakinsu. Na yi ayyuka masu girma. Na gina gidaje wa kaina na kuma shuka gonakin inabi. Na yi lambuna da wuraren shaƙatawa, na shuka itatuwa masu ’ya’ya iri-iri a cikinsu. Na yi tankuna don in yi banruwan kurmin itatuwa. Na sayi bayi mata da maza, ina kuma da waɗansu bayin da aka haifa a gidana. Ina da garkunan shanu da na tumaki da na awaki fiye da duk wanda ya taɓa zama a Urushalima kafin ni. Na tara wa kaina azurfa da zinariya, ina da ma’ajin sarakuna da yankuna. Na samo wa kaina mawaƙa mata da maza, da dukan irin matan da kowane namiji zai so. Na ƙasaita fiye da kowane mutumin da ya riga ni zama a Urushalima. Cikin dukan wannan, hikimata ba tă rabu da ni ba. Ban hana kaina duk wani abin da idona ya yi sha’awarsa ba; ban hana zuciyata wani jin daɗi ba. Zuciyata ta yi murna da dukan aikina, wannan kuwa shi ne ladan dukan famata. Duk da haka sa’ad da na duba dukan aikin hannuwana, da abin da na yi fama don in samu, sai kome ya zama ba shi da amfani, naushin iska ne kawai; babu wata riba a duniya. Sai na juya ga tunanina don in lura da hikima, da kuma hauka da wauta. Me ya rage wa magājin sarki yă yi fiye da abin da aka riga aka yi? Na ga cewa hikima ta fi wauta, kamar yadda haske ya fi duhu. Mai hikima ya san inda ya nufa, wawa kuwa yana tafiya a cikin duhu; amma sai na gane cewa ƙaddara ɗaya ce take samunsu. Sai na yi tunani a zuciyata, “Ƙaddarar wawa za tă same ni ni ma. Wace riba ce hikimata za tă jawo mini?” Na ce a zuciyata, “Wannan ma ba shi da amfani.” Gama ba za a ƙara tunawa da mai hikima ko wawa ba; nan gaba za a manta da su. Yadda wawa zai mutu, haka ma mai hikima! Don haka na ƙi jinin rayuwa, gama aikin da ake yi a duniya yana ɓata mini rai. Dukan abin da yake cikinta kuwa ba shi da amfani, naushin iska ne kawai. Na ƙi jinin dukan abubuwan da na yi wahala ina yi a duniya, gama dole in bar su wa na bayana. Wa ya sani ko zai zama mai hikima ko kuma wawa? Duk da haka zai mallaki dukan aikin da na yi da ƙoƙarina da kuma dabarata a duniya. Wannan ma ba shi da amfani. Saboda haka zuciyata ta fara karaya a kan dukan faman aikina a duniya. Gama mutum zai yi aikinsa da dukan hikimarsa, da saninsa, da gwanintarsa, sa’an nan dole yă bar dukan abin da ya mallaka ga wani wanda bai yi wahalar kome a ciki ba. Wannan ma ba shi da amfani, hasara ce mai yawa. Me mutum zai samu daga aikin da ya yi duka, da irin ɗawainiyar da ya sha a kan yin aikin a duniya? Dukan kwanakinsa aikinsa damuwa ce da ɓacin zuciya; ko da dare ma hankalinsa ba a kwance yake ba. Wannan ma ba shi da amfani. Ba abin da mutum zai yi da ya fi yă ci, yă sha, yă ji wa ransa daɗi daga aikinsa. Na lura cewa wannan ma, ya fito daga hannun Allah ne, gama in ba tare da shi ba, wa zai iya ci yă sha yă kuma ji daɗi? Ga wanda ya gamshe shi, Allah yakan ba da hikima da sani da farin ciki, amma ga mai zunubi yakan ba shi aikin tarawa da ajiyar dukiya domin yă miƙa wa wanda ya gamshi Allah. Wannan ma ba shi da amfani, naushin iska ne kawai. Akwai lokaci domin kowane abu, da kuma lokaci domin kowane aiki a duniya. Lokacin haihuwa da lokacin mutuwa, lokacin shuki da lokacin tumɓukewa. Lokacin kisa da lokacin warkarwa, lokacin rushewa da lokacin ginawa. Lokacin kuka da lokacin dariya, lokacin makoki da lokacin rawa. Lokacin warwatsa duwatsu da lokacin tara su, lokacin runguma da lokacin dainawa. Lokacin nema, da lokacin fid da zuciya, lokacin ajiyewa da lokacin zubarwa. Lokacin yagewa da lokacin ɗinkewa, lokacin yin shiru da lokacin magana. Lokacin ƙauna da lokacin ƙiyayya, lokacin yaƙi da lokacin salama. Wace riba ce ma’aikaci yake da ita saboda wahalarsa? Na ga nawayar da Allah ya ɗora a kan mutane. Ya yi kowane abu da kyau a lokacinsa. Ya kuma sa matuƙa a zukatan mutane, duk da haka sun kāsa gane abin da Allah ya yi daga farko zuwa ƙarshe. Na san ba abin da ya fi wa mutane kyau fiye da su ji daɗi su kuma yi alheri yayinda suke da rai. Cewa kowa yă ci, yă sha, yă kuma ji daɗi cikin dukan aikinsa, wannan kyautar Allah ce. Na san cewa duk abin da Allah ya yi zai dawwama har abada; ba abin da za a ƙara ko a rage. Allah ya yi haka domin mutane su girmama shi. Duk abin da yana nan ya taɓa kasancewa, kuma abin da zai kasance, ya taɓa kasancewa; Allah kuma zai nemi bayanin abubuwan da suka wuce. Sai na ga wani abu kuma a duniya, a wurin shari’a, akwai mugunta a can, a wurin adalci, akwai mugunta a can. Sai na yi tunani a zuciyata, “Allah zai shari’anta masu adalci da masu mugunta, gama za a kasance da lokaci domin kowane aiki, lokaci domin kowane abu.” Na sāke yin tunani, “Game da mutane kam, Allah kan gwada su don su san cewa ba su fi dabba ba. Ƙaddarar mutum ɗaya take da ta dabba; ƙaddara ɗaya ce take jiransu biyu. Yadda ɗayan yake mutuwa, haka ma ɗayan. Dukansu numfashinsu iri ɗaya ne; mutum bai fi dabba ba. Kowane abu ba shi da amfani. Duka wuri ɗaya za su tafi; gama duka daga turɓaya suka fito, kuma ga turɓaya duka za su koma. Wa ya tabbatar cewa ruhun mutum yakan tashi sama sa’an nan na dabba yă sauka ƙasa?” Saboda haka na ga babu abin da ya fi kyau wa mutum fiye da yă more wahalar aikinsa, domin wannan ne rabonsa. Gama wa zai kawo shi yă ga abin da zai faru a bayansa? Na sāke dubawa sai na ga zaluncin da ake yi a duniya. Na ga hawayen waɗanda ake zalunta kuma ba su da mai taimako; masu iko suna goyon bayan masu zalunci, ga shi ba su da mai taimako. Sai na furta cewa matattu, waɗanda suka riga suka mutu, sun fi waɗanda suke a raye farin ciki, waɗanda har yanzu suke da rai. Amma wanda ya fi su duka shi ne wanda bai riga ya kasance ba, wanda bai ga muguntar da ake yi a duniya ba. Sai na gane cewa, duk wata fama da duk wata nasara sun samo asali daga kishin da mutum yake yi na maƙwabcinsa ne. Wannan ma ba shi da amfani, naushin iska ne kawai. Wawa yakan kame hannuwansa yă kuma lalatar da kansa. Gara tafin hannu guda cike da kwanciyar rai da tafin hannu biyu cike da tashin hankali da harbin iska kawai. Na kuma ga wani abu marar amfani a duniya. Akwai wani mutum shi kaɗai; bai shi da ɗa ko ɗan’uwa. Ba shi da hutu daga wahalarsa, duk da haka bai ƙoshi da dukiyarsa ba. Ya tambayi kansa, “Ma wane ne nake wannan wahala, kuma me ya sa nake hana kaina jin daɗi?” Wannan ma ba shi da amfani, harkar baƙin cikin ne kawai! Biyu sun fi ɗaya, gama suna samun riba mai kyau na aikinsu. In ɗaya ya fāɗi, abokinsa zai taimake shi yă tashi. Amma abin tausayi ne ga mutumin da ya fāɗi ba shi kuma da wanda zai taimake shi yă tashi! In mutum biyu sun kwanta tare, za su ji ɗumin juna. Amma yaya mutum ɗaya zai ji ɗumi yana shi kaɗai? Ana iya shan ƙarfin mutum ɗaya, mutum biyu za su iya kāre kansu. Igiya riɓi uku tana da wuya tsinkawa. Gara saurayi wanda yake matalauci amma yake da hikima da sarkin da ya tsufa mai wauta, wanda ba ya karɓar shawara. Yana yiwuwa saurayin yă fito daga kurkuku yă hau gadon sarauta, ko kuma dai an haife shi cikin talauci a ƙasarsa. Na ga cewa dukan waɗanda suka rayu suka kuma yi tafiya a duniya sun bi saurayin, magājin sarkin. Babu ƙarshe ga dukan mutanen da suka riga su. Amma waɗanda suka zo daga baya, ba su gamsu da magājin ba. Wannan ma ba shi da amfani, naushin iska ne kawai. Ka lura da matakanka sa’ad da ka tafi gidan Allah. Ka je kusa don ka saurara a maimakon miƙa hadaya kamar wawaye, waɗanda ba su san sun yi laifi ba. Kada ka yi subul da bakinka, kada zuciyarka tă yi garajen furta wani abu a gaban Allah. Allah yana sama kai kuma kana duniya, saboda haka, kada kalmominka su zama da yawa. Kamar yadda son cika buri yakan zo sa’ad da kana da yawan damuwa, haka jawabin wawa yake sa’ad da yake yawan magana. Sa’ad da ka yi alkawari ga Allah, kada ka ɓata lokaci wajen cika shi. Ba ya jin daɗin wawaye; ka cika alkawarinka. Gara kada ka yi alkawari, da ka yi amma ba ka cika ba. Kada ka bar bakinka ya kai ga yin zunubi. Kada kuma ka kai ƙara wurin ɗan saƙon haikali cewa, “Alkawarin da na yi kuskure ne.” Me ya sa Allah yake fushi a kan abin da ka faɗa har yă lalatar da aikin hannuwanka? Yawan buri da yawan magana ba su da amfani. Saboda haka, ka ji tsoron Allah. In ka ga ana zaluntar matalauta a wani yanki, ba a yin adalci, ana kuma tauye hakki, kada ka yi mamakin waɗannan abubuwa; domin akwai wani jami’in da yake bisa da wani, a bisansu biyu kuwa akwai wani. Kowa yakan amfana da bunkasar amfanin ƙasa, sarki kansa yana samun riba daga gonaki. Duk mai ƙaunar kuɗi ba ya samun isashe; duk ma ƙaunar dukiya ba ya ƙoshi da abin da yake samu. Wannan ma ba shi da amfani. Kamar yadda kaya suke haɓaka, haka ma masu amfani da su. Kuma wane amfani ne suke ga mai shi in ba ciyar da idanunsa a kansu ba? Barcin ma’aikaci daɗi gare shi, ko yă ci kaɗan ko da yawa, amma yalwar mai arziki ba ta barinsa yă iya yin barci. Na ga wani mugun abu a duniya, arzikin da aka ajiye don yă cuce mai shi, ko kuwa dukiyar da ta ɓace ta wata hasara, har ya zama sa’ad da ya haifi ɗa, babu abin da ya bar masa. Tsirara mutum yakan fito daga cikin mahaifiyarsa, kuma kamar yadda ya fito, haka zai koma. Ba ya ɗaukan kome daga wahalarsa da zai riƙe a hannunsa. Wannan ma mugun abu ne, Yadda mutum ya zo, haka zai koma, to, wace riba ce ya ci, da yake ya yi wahalar iska ce kawai? Duk rayuwarsa ya ci abinci a cikin duhu, da ɓacin rai mai tsanani, da azaba, da fushi. Sa’an nan na gane cewa abu mai kyau ne, daidai ne kuma mutum yă ci, yă sha, yă kuma ji daɗin aikin da ya yi a ’yan kwanakin da Allah ya ba shi, gama wannan shi aka ƙaddara wa mutum daga faman wahalarsa a duniya a cikin ’yan kwanakin da Allah ya ba shi a duniya, gama wannan shi ne rabonsa. Ban da haka ma, sa’ad da Allah ya ba wa mutum dukiya da wadata, ya kuma ba shi zarafi yă ji daɗinsu, ya kuma amince da rabonsa, sai yă ji daɗin aikinsa, wannan kyauta ce ta Allah. Da ƙyar yake tunani a kan kwanakin rayuwarsa, domin Allah ya yarje masa, yă zauna da farin ciki. Na ga wani mugun abu a duniya, ya kuma nawaita wa mutane ƙwarai. Allah yakan ba mutum dukiya, da wadata da kuma girma, don kada yă rasa abin da ransa yake so, amma Allah bai ba shi zarafin more su ba, a maimakon haka ma sai baƙo ne yă more su. Wannan ba shi da amfani, mugun abu ne ƙwarai. Mutum zai iya kasance da ’ya’ya ɗari, yă kuma yi shekaru masu yawa; duk da haka kome daɗewarsa, in bai more wadatarsa ba, bai kuma sami kyakkyawar binnewa ba, na ce, gara wanda aka haife shi gawa. Haihuwa ba tă amfane wanda aka haifa gawa ba, gama ya zo daga duhu ya koma duhu inda aka manta da shi. Ko da yake bai ga hasken rana ba, bai kuma san kome ba, duk da haka ya dai huta, fiye da mutumin da bai more wa ransa ba, ko da ya yi shekara dubu biyu amma bai more wadatarsa ba. Ba wuri ɗaya dukansu biyu za su tafi ba? Dukan ƙoƙarin da mutum yake yi, yana yi ne domin bakinsa, duk da haka bai taɓa gamsar da abin da yake marmari. Da me mai hikima ya fi wawa? Wace riba ce matalauci yakan samu don yă iya zama da mutane? Gara abin da ido ya gani da kwaɗayin da bai sami biyan bukata ba. Wannan ma ba shi da amfani, naushin iska ne kawai. Duk abin da ya kasance, to, yana da suna, kuma duk abin da mutum yake, an riga an sani. Ba mutumin da zai iya ƙarawa da wanda ya fi shi ƙarfi. Yadda yawan magana take haka ƙarancin amfaninta, yaya wannan zai amfane wani? Gama wa ya san abin da ya fi dacewa ga mutum a ’yan kwanakinsa marasa amfani da sukan wuce kamar inuwa? Wa kuma zai iya faɗa masa abin da zai faru a duniya bayan ya rasu? Suna mai kyau ya fi turare mai ƙanshi, kuma ranar mutuwa ta fi ranar haihuwa. Gara a tafi gidan makoki da a je gidan biki, gama mutuwa ce ƙaddarar kowane mutum; ya kamata masu rai su lura da haka. Baƙin ciki ya fi dariya, gama baƙin ciki yakan kawo gyara. Zuciyar masu hikima tana a gidan makoki, amma zuciya wawaye tana a gidan shagali. Gara ka saurari tsawatawar mai hikima da ka saurari waƙar wawaye. Kamar ƙarar ƙayar da take karce gindin tukunya, haka dariyar wawaye take. Wannan ma ba shi da amfani. Zalunci yakan mai da mutum mai hikima wawa, cin hanci kuma yakan lalace hali. Ƙarshen abu ya fi farkonsa, haƙuri kuma ya fi girman kai. Kada ranka yă yi saurin tashi, gama fushi yana zama a cinyar wawaye. Kada ka ce, “Me ya sa kwanakin dā sun fi waɗannan?” Gama ba daidai ba ne a yi irin waɗannan tambayoyi. Hikima, kamar gādo, abu mai kyau ne tana kuma da amfani ga waɗanda suka ga rana. Hikima mafaka ce takan kāre mutum kamar yadda kuɗi suke yi. Kiyayewar da hikima takan yi wa mai ita ita ce amfanin ilimi. Ku lura da abin da Allah ya yi. Wa zai iya miƙe abin da ya tanƙware? Sa’ad da al’amura suke tafiya daidai, ka yi farin ciki, amma sa’ad da suka lalace, ka tuna, Allah ne ya yi wancan shi ne kuma ya yi wannan. Saboda haka, mutum ba zai san wani abu game da nan gabansa ba. A cikin rayuwan nan ta rashin amfani nawa, na lura da waɗannan abubuwa biyu, mai adalci yana hallakawa cikin adalcinsa, mai mugunta kuma yana tsawon rai cikin muguntarsa. Kada ka cika yin adalci, fiye da kima, kada kuma ka cika yin hikima, don me za ka hallaka kanka! Kada ka cika yin mugunta, kada kuma ka cika yin wauta, don me za ka mutu kafin lokacinka? Yana da kyau ka kama ɗaya ba tare da ka saki wancan ba. Mai tsoron Allah zai guji wuce gona da iri. Hikima takan sa mutum guda mai hikima yă yi ƙarfi fiye da masu mulki goma a cikin birni. Babu mai adalci a duniya wanda yake yin abin da yake daidai da bai taɓa yin zunubi ba. Kada ka mai da hankali ga dukan abin da mutane suke faɗi, in ba haka ba wata rana za ka ji bayinka suna zaginka. Gama kai kanka ka sani cewa sau da yawa ka zagi waɗansu. Dukan waɗannan na gwada su ta wurin hikima na kuma ce, “Na ƙudurta in zama mai hikima,” amma abin ya fi ƙarfina. Ko da me hikima take, Abin ya yi mana zurfi ƙwarai, yana da wuyar ganewa, wa zai iya gane shi? Saboda haka na mai da hankalina ga fahimi, don in bincika in nemi hikima da yadda aka tsara abubuwa, in kuma fahimci wawancin mugunta da haukar wauta. Sai na iske wani abin da ya fi mutuwa ɗaci mace wadda take tarko ne, wadda zuciyarta tarko ne wadda kuma hannuwanta sarƙa ne. Mutumin da ya gamshi Allah zai tsere mata, amma za tă kama mai zunubi. Malami ya ce, “Duba, abin da na gane ke nan. “Na tara abu guda da wani, don in gane tsarin abubuwa, yayinda nake cikin nema amma ban samu ba, sai na sami adali guda cikin dubu, amma ba mace mai adalci guda a cikinsu duka. Wannan ne kaɗai abin da na gane. Allah ya yi mutum tsab amma sai muka rikitar da kanmu.” Wa yake kama da mai hikima? Wa ya san bayanin abubuwa? Hikima takan haskaka fuskar mutum, ta kuma kawo sakin fuska. Ka yi biyayya da umarnin sarki, na ce, saboda alkawarin da ka yi a gaban Allah. Kada ka yi hanzarin tashi daga gaban sarki. Kada ka kāre abin da ba daidai ba, gama zai iya yin duk abin da ya ga dama. Da yake maganar sarki ita ce mafificiya, wa zai iya ce masa, “Me kake yi?” Duk wanda ya yi biyayya da umarninsa ba zai sami lahani ba, zuciya mai hikima kuma zai san lokacin da ya dace da kuma hanyoyin da suka fi. Gama akwai lokaci da hanyoyin da suka dace da yin kowane abu, ko da yake wahalar mutum ta yi masa yawa. Da yake ba wanda ya san nan gaba, wa zai iya faɗa masa abin da zai faru? Ba wanda yake da iko a kan iska har da zai riƙe ta, saboda haka babu mai iko kan ranar mutuwarsa. Kamar yadda ba a sallamar mutum a lokacin yaƙi, haka ma mugunta ba za tă saki masu aikata ta ba. Na ga dukan waɗannan, yayinda na lura da kowane abin da ake yi a duniya. Akwai lokacin da mutum yakan nauyaya wa waɗansu ba da sonsa ba. Sa’an nan kuma, na ga an binne masu mugunta, waɗanda suke shiga da fita daga tsattsarkan wuri suke kuma samun yabo a birnin da suka yi wannan. Wannan ma ba shi da amfani. In ba a hanzarta aka yanke hukunci a kan laifi ba, zukatan mutane sukan cika da ƙulle-ƙullen aikata abubuwan da ba daidai ba. Ko da yake mugu ya aikata laifi ɗari ya kuma yi tsawon rai, na san cewa zai fi wa masu tsoron Allah kyau, waɗanda suke girmama Allah. Duk da haka, domin masu mugunta ba su ji tsoron Allah ba, abubuwa ba za su yi musu kyau ba, ransu kamar inuwa yake ba zai yi tsawo ba. Akwai kuma wani abu marar amfani da yake faruwa a duniya, masu adalci sukan sha hukuncin da ya dace da masu mugunta, masu mugunta kuma sukan karɓi sakayyar da ya cancanci masu adalci su samu. Na ce, wannan ma, ba shi da amfani. Saboda haka abin da na ce, shi ne mutum yă ji daɗi, domin iyakar jin daɗinsa a wannan rai, shi ne yă ci, yă sha, yă ji wa kansa daɗi. Aƙalla yana iya yin wannan in ya yi aiki a kwanakin da Allah ya ba shi a wannan duniya. Da na mai da hankalina don in sami hikima in kuma lura da wahalar mutum a duniya, ko da a ce idanunsa ba sa barci dare da rana, sam, ba zai taɓa fahimci abin da Allah yake yi ba. Iyakar ƙoƙarin da ka yi duk ba za ka iya ganewa ba. Masu hikima suna iya cewa sun sani, amma kuwa ba su sani ba. Sai na yi tunani a kan wannan na kuma gane cewa masu adalci da masu hikima da kuma abubuwan da suke yi suna a hannun Allah ne, amma ba wanda ya san ko ƙauna ko ƙiyayya ce take jiransa. Dukansu makomarsu ɗaya ce, masu adalci da masu mugunta, masu kirki da marasa kirki, masu tsabta da marasa tsabta, masu miƙa hadaya da waɗanda ba sa yi. Kamar yadda yake ga mutumin kirki, haka yake ga mai zunubi. Kamar yadda yake ga masu yin rantsuwa, haka ma da masu tsoron yi. Wannan ita ce muguntar da take faruwa a cikin dukan abubuwa a duniya. Ƙaddara ɗaya ce take a kan kowa. Amma zukatan mutane cike suke da mugunta, akwai kuma hauka a zukatansu yayinda suke a raye, bayan haka kuma sai su mutu. Duk wanda yake da rai a wannan duniya ta rayayyu, yana sa zuciya, gara rayayyen kare da mataccen zaki! Gama rayayyu sun san za su mutu, amma matattu ba su san kome ba; ba su da wata lada nan gaba an manta da su ke nan gaba ɗaya. Ƙaunarsu, ƙiyayyarsu, da kuma kishinsu tuni sun ɓace; ba za su taɓa zama sashen wani abin da yake faruwa a duniya ba. Yi tafiyarka, ka ci abincinka da farin ciki, ka sha ruwan inabinka da farin zuciya, gama abin da ka yi duka daidai ne a wurin Allah. Kullum ka kasance cikin farin riguna, ka kuma shafe kanka da mai kullum, Ka more rayuwa da matarka, wadda kake ƙauna, dukan kwanakin nan marasa amfani da Allah ya ba ka a duniya. Gama wannan ne rabonka a rayuwa da kuma na faman aikinka a duniya. Duk abin da hannunka yake yi, ka yi shi da dukan ƙarfinka, gama a cikin kabari in da za ka, babu aiki ko shirye-shirye, ko sani, ko hikima. Na kuma ga wani abu a duniya. Ba kullum maguji ne yake nasara a tsere ba, ba kullum jarumi ne yake yin nasara ba, ba kullum mai hikima ne da abinci ba ba kullum mai basira ne yake da wadata ba ba kullum gwani ne yake samun tagomashi ba; amma sa’a, da tsautsayi, sukan sami kowannensu. Ban da haka ma, ba wanda ya san sa’ad da lokacin mutuwarsa zai yi. Kamar yadda akan kama kifi a muguwar raga, ko a kama tsuntsu a tarko, haka mugun lokaci yakan auko wa mutane, ba tsammani. Na kuma ga wani misali game da hikima a duniya wanda ya burge ni sosai. An yi wani ɗan ƙaramin birni mai mutane kaɗan a ciki. Sai wani babban sarki ya kawo masa yaƙi, ya kafa masa babban sansani. A cikin birnin nan kuwa akwai wani mutum matalauci amma mai hikima, ya kuma ceci birnin ta wurin hikimarsa. Amma ba wanda ya tuna da matalaucin nan. Sai na ce, “Hikima ta fi ƙarfe ƙarfi.” Amma aka rena hikimar matalaucin, ba a ma jin maganarsa. Raɗar mai hikima da aka saurara cikin natsuwa ta fi ihun mai mulkin wawaye. Hikima ta fi kayan yaƙi, amma mai zunubi ɗaya yakan rushe alheri mai yawa. Kamar yadda matattun ƙudaje sukan ɓata ƙanshin turare, haka ’yar wauta takan ɓata hikima da daraja. Zuciyar mai hikima takan karkata ga yin abin da yake daidai, amma zuciyar wawa takan karkata ga yin mugun abu. Ko yayinda yake tafiya a kan hanya wawa yakan nuna cewa ba shi da hankali, yakan nuna wa kowa wawancinsa. In hankalin mai mulki ya tashi game da kai, kada ka bar inda kake, gama kwantar da hankali yakan sa a yafe manyan laifofi. Akwai muguntar da na gani a duniya, irin kuskuren da yake fitowa daga masu mulki. Akan sa wawaye a manyan matsayi, yayinda masu arziki suna ƙarƙashi. Na taɓa ganin bayi a kan dawakai, yayinda ’ya’yan sarki suna takawa a ƙasa kamar bayi. Duk wanda ya haƙa rami shi ne zai fāɗa a ciki; duk wanda ya rushe katanga, shi maciji zai sara. Duk mai farfasa duwatsu shi za su yi wa rauni; duk mai faskaren itace yana cikin hatsarinsu. In gatari ya dakushe ba a kuma wasa shi ba, dole a yi amfani da ƙarfi da yawa, amma ƙwarewa yana kawo nasara. In maciji ya sari mutum kafin a ba shi makarin gardi, ina amfanin maganin? Kalmomi daga bakin mai hikima alheri ne, amma maganganun wawa za su hallaka shi. Farkon maganarsa wauta ce, ƙarshenta kuma takan zama muguwar hauka, wawa kuma yakan yi ta surutu. Ba wanda ya san abin da zai zo wa zai iya faɗa masa abin da zai faru bayan rasuwarsa? Aikin wawa yakan gajiyar da shi, har bai san hanyar zuwa gari ba. Kaitonki, ya ke ƙasa wadda sarkinki bawa ne wadda kuma hakimanta ke ta shagali tun da safe. Mai albarka ce, ya ke ƙasa wadda sarkinki haifaffen gidan sarauta ne, wadda hakimanta suke samun abincinsu a daidai lokacin don samun ƙarfi ba don buguwa ba. In mutum rago ne, sai tsaiko yă lotsa, in hannuwansa ba masa yin kome, ɗaki yakan yi yoyo. Akan shirya abinci don jin daɗi, ruwan inabi kuwa don faranta zuciya, amma kuɗi ne amsar kome. Kada ka zagi sarki ko da a cikin tunaninka ne, ko ka zagi mai arziki ko da a ɗakin kwananka ne, gama tsuntsun sararin sama zai iya ɗauki maganarka, tsuntsu mai fikafikai zai sanar da abin da ka ce. Ka jefa burodinka a bisa ruwaye, gama bayan kwanaki masu yawa, za ka sāke samunsa. Ka raba abin hannunka ga mutum bakwai, I, har ma takwas, gama ba ka san bala’in da zai auko wa ƙasar ba. In gizagizai sun cika da ruwa, sukan zub da ruwan sama bisa duniya. Itace ya fāɗi, ko wajen kudu ne, ko wajen arewa, inda ya fāɗi a nan zai kwanta. Duk mai la’akari da iska, ba zai yi shuka ba, mai la’akari da gizagizai kuma, ba zai yi girbi ba. Kamar yadda ba ka san hanyar iska ba, ko yadda aka siffanta jiki a cikin mahaifiya, haka ba za ka fahimci aikin Allah Mahaliccin dukan abubuwa ba. Ka shuka irinka da safe, da yamma kuma kada ka janye hannunka, gama ba ka san wanda zai yi albarka ba, ko wannan ko wancan, ko kuma duka biyunsu su yi albarka. Haske da yana da kyau, abu mai kyau ne kuma idanu su dubi rana. Kome tsawon rayuwar mutum, bari yă more su duka. Amma bari kuma yă tuna da kwanakin duhu, gama su ma za su yi yawa. Duk abin da zai faru ba shi da amfani. Ka yi murna, kai matashi, a ƙuruciyarka, bari zuciyarka kuma tă yi farin ciki a kwanakin ƙuruciyarka. Ka bi shawarar zuciyarka da kuma duk abin da idanunka suka gani, amma ka sani fa, cikin dukan al’amuran nan Allah zai shari’anta ka. Saboda haka, ka fid da tsoro daga zuciyarka ka kakkaɓe duk wani abin da ya dami rayuwarka, gama ƙuruciya da ƙarfi ba su da amfani. Ka tuna da Mahaliccinka a kwanakin ƙuruciyarka, kafin lokacin wahala ta zo shekaru kuma su ƙarato sa’ad da za ka ce, “Ba na jin daɗinsu,” kafin rana da haske wata da taurari su daina haske, gizagizai kuma su tattaru bayan da suka sheƙa ruwa; sa’ad da masu tsaron gida suke rawar jiki, majiya ƙarfi kuma suka rasa ƙarfi, sa’ad da masu niƙa suka daina don ba su da yawa, idanun da suke duba ta taga suka duhunta; sa’ad da aka rufe ƙofofin shiga tituna ƙarar niƙa kuma ya tsagaita; sa’ad da kukan tsuntsaye ta farkar da mutane, ba a kuwa jin waƙoƙinsu, sa’ad da mutane suke jin tsoron tudu da kuma hatsarori a tituna; sa’ad da itacen almon ya toho, fāra kuma ya yi ta jan jikinsa da ƙyar, sha’awace-sha’awace sun kafe. Daga nan mutum ya tafi madawwamiyar gidansa ya bar masu makoki suna ta yi. Ka tuna da shi, kafin igiyar azurfa ta katse, ko tasar zinariya ta fashe; kafin tulu yă ragargaje a maɓulɓula, ko guga ta tsinke a rijiya, turɓaya ta koma ƙasar da ta fito, rai kuma yă koma ga Allah wanda ya ba da shi. “Ba amfani! Ba amfani!” In ji Malami, “Gaba ɗaya ba amfani!” Ba kawai Malami ya kasance mai hikima ba, amma kuma ya koyar da mutane. Ya yi tunani ya kuma yi binciken da ya tsara karin magana masu yawa. Malami ya yi bincike don yă sami kalmomin da suka dace, kuma abin da ya rubuta daidai ne da kuma gaskiya. Kalmomin masu hikima kamar tsinken tsokanar dabba ne, tarin maganganunsu kuma kamar ƙusoshi ne da aka kafa daram, da aka ba wa Makiyayi guda. Ka yi hankali ɗana, game da duk wani ƙari a kan waɗannan. Wallafa littattafai ba shi da iyaka, kuma yawan karatu yakan gajiyar da jiki. Yanzu an ji kome; ga ƙarshen magana. Ka ji tsoron Allah ka kuma kiyaye umarnansa, gama wannan shi ne dukan hakkin mutum. Gama Allah zai shari’anta kowane irin aiki, har da waɗanda aka yi a ɓoye, ko nagari ne, ko mugu. Waƙar Waƙoƙin Solomon. Bari yă sumbace ni da sumbar bakinsa, gama ƙaunarka ta fi ruwan inabi zaƙi. Ƙanshin turarenka mai daɗi ne; sunanka kuwa kamar turaren da aka tsiyaye ne. Shi ya sa mata suke ƙaunarka! Ka ɗauke ni mu gudu, mu yi sauri! Bari sarki yă kai ni gidansa. Muna farin ciki muna kuma murna tare da kai, za mu yabi ƙaunarka fiye da ruwan inabi. Daidai ne su girmama ka! Ni baƙa ce, duk da haka kyakkyawa. Ya ku ’yan matan Urushalima, ni baƙa ce kamar tentunan Kedar, kamar labulen tentin Solomon. Kada ku harare ni domin ni baƙa ce, gama rana ta dafa ni na yi baƙa. ’Ya’yan mahaifiyata maza sun yi fushi da ni suka sa ni aiki a gonakin inabi; na ƙyale gonar inabi na kaina. Faɗa mini, kai da nake ƙauna, ina kake kiwon garkenka kuma ina kake kai tumakinka su huta da tsakar rana. Me ya sa zan kasance kamar macen da aka lulluɓe kusa da garkunan abokanka? Ke mafiya kyau a cikin mata, in ba ki sani ba, to, ki dai bi labin da tumaki suke bi ki yi kiwon ’yan awakinki kusa da tentunan makiyaya. Ina kwatanta ke ƙaunatacciyata, da goɗiya mai jan keken yaƙin kayan Fir’auna. ’Yan kunne sun ƙara wa kumatunki kyau, wuyanki yana da jerin kayan wuya masu daraja. Za mu yi ’yan kunnenki na zinariya, da adon azurfa. Yayinda sarki yake a teburinsa, turarena ya bazu da ƙanshi. Ƙaunataccena yana kamar ƙanshin mur a gare ni, kwance a tsakanin ƙirjina. Ƙaunataccena kamar tarin furanni jeji ne gare ni daga gonakin inabin En Gedi. Ke kyakkyawa ce, ƙaunatacciyata! Kai, ke kyakkyawa ce! Idanunki kamar na kurciya ne. Kai kyakkyawa ne, ƙaunataccena! Kai, kana ɗaukan hankali! Gadonmu koriyar ciyawa ce. Al’ul su ne ginshiƙan gidanmu; fir su ne katakan rufin gidanmu. Ni furen bi-rana ne na Sharon, furen bi-rana na kwari. Kamar furen bi-rana a cikin ƙayayyuwa haka ƙaunatacciyata take a cikin ’yan mata. Kamar itacen gawasa a cikin itatuwan jeji haka ƙaunataccena yake a cikin samari. Ina farin ciki in zauna a inuwarsa, ’ya’yan itacensa suna da daɗin ɗanɗanon da nake so Ya kai ni babban zauren da ake liyafa, ƙauna ita ce tutarsa a gare ni. Ka ƙarfafa ni da zabibi ka wartsake ni da gawasa, gama ina suma don ƙauna. Hannunsa na hagu yana a ƙarƙashin kaina, hannunsa na dama kuma ya rungume ni. ’Yan matan Urushalima, ku yi mini alkawari da bareyi da ƙishimai na jeji. Ba za ku tā da ko ku farka ƙauna ba sai haka ya zama lalle. Saurara! Ƙaunataccena! Duba! Ga shi ya iso, yana tsalle a duwatsu, yana rawa a bisa tuddai. Ƙaunataccena yana kama da barewa ko sagarin ƙishimi Duba! Ga shi can tsaye a bayan katangarmu, yana leƙe ta tagogi, yana kallo ta cikin asabari. Ƙaunataccena ya yi magana ya ce mini, “Tashi, ƙaunatacciyata, kyakkyawata, ki zo tare da ni. Duba! Damina ta wuce; ruwan sama ya ɗauke ya kuma ƙare. Furanni sun hudo a duniya; lokaci yin waƙa ya zo, ana jin kukan kurciyoyi ko’ina a ƙasarmu. Itacen ɓaure ya fid da ’ya’yansa da sauri; tohon inabi suna ba da ƙanshinsu. Tashi, zo, ƙaunatacciyata; kyakkyawata, zo tare da ni.” Kurciyata a kogon dutse, a wuraren ɓuya a gefen dutse, nuna mini fuskarki, bari in ji muryarki; gama muryarki da daɗi take, fuskarki kuma kyakkyawa ce. Kama mana ɓeraye, ƙananan ɓerayen da suke lalatar da gonakin inabi, gonakin inabinmu da suke cikin yin fure. Ƙaunataccena nawa ne ni kuma tasa ce; yana kiwon garkensa a cikin furannin bi-rana. Sai gari ya waye inuwa kuma ta watse, ka juye, ƙaunataccena, ka zama kamar barewa ko kamar sagarin ƙishimi a kan tuddai masu ciyawa. Dare farai a kan gadona na nemi wanda zuciyata take ƙauna; na neme shi amma ban same shi ba. Zan tashi yanzu in zagaya gari, in ratsa titunansa da dandalinsa; zan nemi wanda zuciyata take ƙauna. Saboda haka na neme shi, amma ban same shi ba. Masu tsaro suka gamu da ni yayinda suke kai kawo a cikin birni, sai na ce, “Kun ga mini wanda zuciyata take ƙauna?” Rabuwata da su ke nan sai na sami wanda zuciyata take ƙauna. Na riƙe shi, ban yarda yă tafi ba sai da na kawo shi gidan mahaifiyata, zuwa ɗakin wadda ta yi cikina. ’Yan matan Urushalima, ku yi mini alkawari da bareyi da ƙishimai na jeji. Ba za ku tā da ko ku farka ƙauna ba sai haka ya zama lalle. Wane ne wannan mai zuwa daga hamada kamar tunnuƙewar hayaƙi, cike da ƙanshin turaren mur da lubban da aka yi da kayan yajin ’yan kasuwa? Duba! Abin ɗaukar Solomon ne, jarumawa sittin suke rakiya, zaɓaɓɓun sojojin Isra’ila, dukansu suna saye da takobi dukansu ƙwararru ne a yaƙi, kowanne da takobinsa a rataye a gefensa, a shirye don abubuwan bantsoro na dare. Sarki Solomon ya yi wa kansa abin ɗauka; ya yi shi da katako daga Lebanon. An yi sandunansa da azurfa, aka yi ƙasarsa da zinariya. An lulluɓe wurin zaman da zanen shunayya, ’yan matan Urushalima sun yi mata irin yayen da ake yi na ƙauna. Fito, ku ’yan matan Sihiyona, ku ga Sarki Solomon yana saye da rawani, rawanin da mahaifiyarsa ta naɗa masa, a ranar aurensa, a ranar da zuciyarsa ta yi farin ciki. Ke kyakkyawa ce, ƙaunatacciyata! Kai, ke kyakkyawa ce! Idanunki sun yi kamar na kurciya a cikin lulluɓinki. Gashinki ya yi kamar garken awaki da suke gangarawa daga Dutsen Gileyad. Haƙoranki sun yi kamar garken tumakin da ba a daɗe da yin musu sausaya ba, da suke haurawa daga inda aka yi musu wanka. Kowanne yana tare da ɗan’uwansa; babu waninsu da yake shi kaɗai. Leɓunanki kamar zaren jan garura bakinki yana da kyau. Kumatunki sun yi kamar rumman da aka tsaga biyu a cikin lulluɓinki. Wuyanki ya yi kamar hasumiyar Dawuda, da aka gina da daraja; a kansa an rataye garkuwoyi dubu, dukansu garkuwoyin jarumawa ne. Nonanki biyu sun yi kamar bareyi biyu, kamar tagwayen barewa da suke kiwo a cikin furen bi-rana. Sai gari ya waye inuwa kuma ta watse, zan je dutsen mur da kuma tudun turare. Duk, ke kyakkyawa ce, ƙaunatacciyata; babu wani lahani a cikinki. Ki tare da ni daga Lebanon, amaryata, zo tare da ni daga Lebanon. Ki gangara daga ƙwanƙolin Amana, daga ƙwanƙolin Senir, ƙwanƙolin Hermon, daga ramin zaki da kuma dutsen da damisoshi suke zama. Kin saci zuciyata, ’yar’uwata, amaryata; kin saci zuciyata da hararar idanunki, da dutse mai daraja guda na abin wuyanki. Ƙaunarki abar farin ciki ne, ’yar’uwata, amaryata! Ƙaunarki ta fi ruwan inabi gamsuwa, ƙanshin turarenki kuma ya fi duk wani kayan yaji! Leɓunanki suna zub da zaƙi kamar kakin zuma, amaryata; madara da zuma suna a ƙarƙashin harshenki. Ƙanshin rigunanki ya yi kamar na Lebanon. Ke lambu ne da aka kulle, ’yar’uwata, amaryata; ke maɓulɓula ce da aka kewaye, maɓulɓular da aka rufe. Shuke-shukenki gonar rumman ne da ’ya’yan itace masu kyau na lalle da nardi, nardi, da asfaran, kalamus, da kirfa, da kowane irin itacen turare, da mur da aloyes da kuma dukan kayan yaji masu kyau. Ke lambun maɓulɓula ne, rijiya mai ruwan da yake gudu yana gangarawa daga Lebanon. Farka, iskar arewa, ki kuma zo, iskar kudu! Hura a kan lambuna, don ƙanshinsa yă bazu har waje. Bari ƙaunataccena yă zo cikin lambunsa yă ɗanɗana ’ya’yan itacensa mafi kyau. Na zo lambuna, ’yar’uwata, amaryata; na tattara mur nawa da kayan yajina. Na sha zumana da kuma kakinsa na sha ruwan inabina da kuma madarana. Ku ci, ku kuma sha, ya ku ƙawaye; ku sha ku ƙoshi, ya ƙaunatattu. Na yi barci amma zuciyata tana a farke. Ku saurara! Ƙaunataccena yana ƙwanƙwasa ƙofa. “Buɗe mini, ’yar’uwata, ƙaunatacciyata, kurciyata, marar laifina. Kaina ya jiƙe da raɓa, gashina ya yi danshin ɗiɗɗigar dare.” Na tuɓe rigata, sai in sāke sa ta kuma? Na wanke ƙafafuna, sai in sāke ɓata su? Ƙaunataccena ya turo hannunsa ta cikin ramin ƙofar; zuciyata ta fara juyayi a kansa. Na tashi don in buɗe wa ƙaunataccena, sai hannuna ya jiƙe sharkaf da mur, yatsotsina suna ɗiga da mur, a hannuwan ƙofar. Na buɗe wa ƙaunataccena ƙofa, amma ƙaunataccena ba ya nan, ya riga ya tafi. Zuciyata ta damu da tafiyarsa. Na neme shi amma ban same shi ba. Na yi ta kiransa amma bai amsa ba. Masu gadi suka gamu da ni yayinda suke kai kawo a cikin birni. Suka yi mini dūka, suka yi mini rauni; suka ƙwace gyalena waɗannan masu gadin katanga! ’Yan matan Urushalima, ina roƙonku, in kun sami ƙaunataccena me za ku ce masa? Ku ce masa na suma saboda ƙauna. Mafiya kyau a cikin mata me ya sa ƙaunataccenki ya fi sauran? Don me kike roƙonmu mu faɗa masa yadda kike ji? Ƙaunataccena kyakkyawa ne ƙaƙƙarfa kuma, da ƙyar a sami irinsa ɗaya a cikin dubu goma. Kansa zinariya ce zalla; gashinsa dogaye ne baƙi wuluk kamar hankaka. Idanunsa sun yi kamar na kurciyoyin da suke kusa da ruwan rafi, da aka wanke da madara aka kuma kafa kamar kayan ado masu daraja. Kumatunsa kamar lambun kayan yaji suna ba da turare. Leɓunansa sun yi kamar furen bi-rana suna ɗiga da mur. Hannuwansa kamar sandunan zinariyar da aka sa musu duwatsu masu daraja. Jikinsa ya yi kamar gogaggen hauren giwan da aka yi masa ado da duwatsun saffaya. Ƙafafunsa sun yi kamar ginshiƙan dutsen alabastar da aka kafa su a cikin rammukar zinariya. Kamanninsa ya yi kamar Lebanon, mafi kyau kamar itacen al’ul nasa. Bakinsa zaƙi ne kansa; komensa yana da kyau. Haka ƙaunataccena, abokina, yake ’yan matan Urushalima. Ina ƙaunataccenki ya tafi, yake mafiya kyau cikin mata? Wace hanya ce ƙaunataccenki ya bi, don mu taimake ki nemansa. Ƙaunataccena ya gangara zuwa lambunsa, zuwa inda fangulan kayan yaji suke, don yă yi kiwo a cikin lambun don kuma yă tattara furen bi-rana. Ni na ƙaunataccena ce, ƙaunataccena kuma nawa ne; yana kiwo a cikin furen bi-rana. Ke kyakkyawa ce, ƙaunatacciyata, kamar Tirza, kyakkyawa kuma kamar Urushalima, mai daraja kamar mayaƙa da tutoti. Ki kau da idanu daga gare ni; gama suna rinjayata. Gashinki yana kama da garken awakin da suke gangarawa daga Gileyad. Haƙoranki suna kama da garken tumakin da suke haurawa daga inda aka yi musu wanka. Kowanne yana tare da ɗan’uwansa; babu waninsu da yake shi kaɗai. Kumatunki sun yi kamar rumman da aka tsaga biyu a cikin lulluɓinki. Sarauniyoyi sittin za su iya kasance a can, da ƙwarƙwarai tamanin da kuma budurwai da suka wuce ƙirge; amma kurciyata, cikakkiyata, dabam take, tilo kuwa ga mahaifiyarta, ’yar lele ga wadda ta haife ta. ’Yan mata sun gan ta suka ce da ita mai albarka; sarauniyoyi da ƙwarƙwarai sun yabe ta. Wace ce wannan da ta bayyana sai ka ce ketowar alfijir? Kyakkyawa kamar wata, mai haske kamar rana, mai daraja kamar taurari a jere? Na gangara zuwa cikin itatuwan almon don in ga ƙananan itatuwan da suke girma a kwari, don in ga ko inabi sun yi ’ya’ya ko rumman suna fid da furanni. Kafin in san wani abu, sha’awarta ta sa ni a cikin keken yaƙin sarkin mutanena. Ki dawo, ki dawo, ya Bashulammiya; ki dawo, ki dawo, don mu dube ki! Don me kuke duban Bashulammiya sai ka ce rawar Mahanayim? Ƙafafunki a cikin takalma kyakkyawa ne, Ya diyar sarki! Tsarin ƙafafunki sun yi kamar kayan ado masu daraja, aikin hannun gwanin sassaƙa. Cibinki kamar kwaf ne da bai taɓa rasa gaurayayyen ruwan inabi ba. Kwankwasonki ya yi kamar damin alkama wanda furen bi-rana ya kewaye. Nonanki sun yi kamar bareyi biyu, tagwayen barewa. Wuyanki ya yi kamar hasumiyar hauren giwa. Idanunki sun yi kamar tafkin Heshbon kusa da ƙofar Bat Rabbim. Hancinki ya yi kamar hasumiyar Lebanon wadda take duban Damaskus. Kanki ya yi miki rawani kamar Dutsen Karmel. Gashinki ya yi kamar shunayya; yakan ɗauke hankalin sarki. Kai! Ke kyakkyawa ce kuma kina sa ni jin daɗi, Ya ƙaunatacciya, da farin cikin da kike kawo! Tsayinki ya yi kamar itacen dabino, kuma nonanki sun yi kamar ’ya’yan itace. Na ce, “Zan hau itacen dabino; zan kama ’ya’yansa.” Bari nonanki su zama kamar nonna kuringa, ƙanshin numfashinki ya yi kamar gawasa, kuma bakinki ya yi kamar ruwan inabi mafi kyau. Bari ruwan inabi yă wuce kai tsaye zuwa ga ƙaunataccena, yana gudu a hankali a leɓuna da kuma haƙora. Ni ta ƙaunataccena ce, kuma sha’awarsa domina ne. Ka zo, ƙaunataccena, bari mu je bayan gari, bari mu kwana a ƙauye. Bari mu tafi gonar inabi da sassafe don mu ga ko kuringar ta yi ’ya’ya, ko furanninsu sun buɗe, ko rumman sun yi fure, a can zan nuna maka ƙaunata. Manta-uwa sun ba da ƙanshinsu, a bakin ƙofa kuwa akwai kowane abinci mai daɗi, sabo da tsoho, da na ajiye dominka, ƙaunataccena. Da a ce kai ɗan’uwa ne gare ni, wanda nonon mahaifiyata sun shayar! Da in na same ka a waje, na sumbace ka, babu wanda zai rena ni. Da sai in bi da kai in kawo ka gidan mahaifiyata, ita da ta koyar da ni. Da na ba ka ruwan inabi gaurayayye da kayan yaji ka sha, zaƙin rumman nawa. Hannunsa na hagu yana a ƙarƙashin kaina, hannunsa na dama kuma ya rungume ni. ’Yan matan Urushalima, ku yi mini alkawari. Ba za ku tā da ko ku farka ƙauna ba sai haka ya zama lalle. Wace ce wannan da take haurawa daga hamada tana dogara a kan ƙaunataccenta? A ƙarƙashin itacen gawasa na farkar da ke, a wurin da aka haife ki, wurin da mahaifiyarki ta haife ki. Ka sa ni kamar hatimi a zuciyarka, kamar hatimi a hannunka; gama ƙauna tana da ƙarfi kamar mutuwa, kishinta yana kamar muguntar kabari, yana ƙuna kamar wuta mai ci, kamar gagarumar wuta. Ruwa da yawa ba zai iya kashe ƙauna ba, koguna ba za su iya kwashe ta ba. In wani zai bayar da dukan dukiyar gidansa don ƙauna, za a yi masa dariya ne kawai. Muna da ƙanuwa, nonanta ba su riga sun yi girma ba. Me za mu yi da ƙanuwarmu a ranar da za a yi maganar sonta? Da a ce ita katanga ce, da sai mu gina hasumiyar azurfa a kanta. Da a ce ita ƙofa ce, da sai mun yi mata ƙyauren itacen al’ul. Ni katanga ce kuma nonaina sun yi kamar hasumiya. Ta haka na zama idanunsa kamar wanda yake kawo gamsuwa. Solomon ya kasance da gonar inabi a Ba’al-Hamon; ya ba da hayar gonar inabi ga ’yan haya. Kowanne zai biya shekel dubu na azurfa don ’ya’yan inabin. Amma gonar inabina nawa ne da zan bayar; shekel dubu naka ne, ya Solomon, kuma ɗari biyu na waɗanda suke lura da ’ya’yan itatuwansa ne. Ke da kike zaune a cikin lambu da ƙawaye suna lura da ke, bari in ji muryarki! Ka zo, ƙaunataccena, ka zama kamar barewa ko kuwa kamar ’yar batsiya a kan dutsen da kayan yaji suke a shimfiɗe. Wahayi game da Yahuda da Urushalima wanda Ishaya ɗan Amoz ya gani a zamanin da Uzziya, Yotam, Ahaz da Hezekiya, suka yi mulkin Yahuda. Ku kasa kunne, ya sammai! Ki saurara, ya duniya! Gama Ubangiji ya yi magana, “Na yi renon ’ya’ya, na kuma raya su, amma sun tayar mini. Saniya ta san maigidanta, jaki ya san wurin sa wa dabbobi abinci maigidansa, amma Isra’ila ba su sani, mutanena ba su gane ba.” Kash, ya ke al’umma mai zunubi, mutane cike da laifi, tarin masu aikata mugunta, ’ya’yan da aka miƙa wa lalaci! Sun yashe Ubangiji; sun rena Mai Tsarkin nan na Isra’ila suka juya masa baya. Me ya sa za a ƙara yin muku dūka? Me ya sa kuka nace ga yin tayarwa? An yi wa dukan kanku rauni, zuciyarku duk tana ciwo. Daga tafin ƙafarku zuwa saman kanku ba lafiya, sai miyaku da ƙujewa da manyan gyambuna, ba a tsabtacce su ba ko a daure ko shafa musu magani. Ƙasarku ta zama kufai, an ƙone biranenku da wuta; baƙi suna ƙwace gonakinku a idanunku, ta zama kango kamar sa’ad da baƙi suka rushe ta. An bar diyar Sihiyona kamar rumfar mai ƙumu a gonar inabi, kamar bukka a gonar kabewa, kamar birnin da aka kewaye da yaƙi. Da ba a ce Ubangiji Maɗaukaki ya bar mana raguwar masu rai ba, da mun zama kamar Sodom, da mun zama kamar Gomorra. Ku saurari maganar Ubangiji, ku masu mulkin Sodom; ku kasa kunne ga dokar Allahnmu, ku mutanen Gomorra! Ubangiji ya ce, “Yawan hadayunku, mene ne suke a gare ni?” Ina da isashen hadayun ƙonawa, na raguna da na kitsen dabbobi masu ƙiba; ba na jin daɗin jinin bijimai da na tumaki da kuma na awaki. Sa’ad da kuka zo don ku bayyana a gabana, wa ya nemi wannan daga gare ku, da kuke kai da kawowa a filayen gidana? Ku daina kawo hadayu marasa amfani! Turarenku abin ƙyama ne gare ni. Ina ƙin bukukkuwanku na Sabon Wata, da na ranakun Asabbaci, da taronku na addini, ba zan iya jure wa mugun taronku ba. Bukukkuwanku na Sabon Wata da na tsarkakan ranaku na ƙi su. Sun zama mini kaya; na gaji da ɗaukansu. Sa’ad da kuka ɗaga hannuwanku wajen yin addu’a, zan ɓoye fuskata daga gare ku; ko da kun miƙa addu’o’i masu yawa, ba zan kasa kunne ba. Hannuwanku sun cika da jini! Ku yi wanka ku kuma tsabtacce kanku. Ku kawar da mugayen ayyukanku daga gabana; Ku daina aikata mugunta. Ku koyi yin nagarta; ku nemi adalci. Ku ƙarfafa waɗanda aka zalunta. Ku ba wa marayu hakkinsu, ku taimaki gwauruwa. Ubangiji ya ce, “Yanzu fa ku zo, bari mu dubi batun nan tare, Ko da zunubanku sun yi ja kamar garura, za su zama fari kamar ƙanƙara; ko da sun yi ja kamar mulufi, za su zama kamar ulu. In kuna da niyya kuna kuma yi mini biyayya, za ku ci abubuwa masu kyau daga ƙasar; amma in kuka yi tsayayya kuka kuma yi tayarwa, za a kashe ku da takobi.” Ni Ubangiji na faɗa. Dubi yadda amintacciyar birni ta zama karuwa! Dā ta cika da yin gaskiya; dā masu adalci a can suke zama, amma yanzu sai masu kisankai kaɗai! Azurfarki ta zama jebu, an gauraye ruwan inabinki mafi kyau da ruwa. Masu mulkinki ’yan tawaye ne, abokan ɓarayi; dukansu suna ƙaunar cin hanci suna bin kyautai. Ba sa taɓa tsare marayu a ɗakin shari’a; ba sa taimakon gwauruwa. Saboda haka Ubangiji, Ubangiji Maɗaukaki, Mai Iko nan na Isra’ila, ya furta, “Kai, zan sami hutu daga maƙiyana in kuma yi ramuwa a kan abokan gābana. Zan juye hannuna a kanki; zan wanke ke sarai in fitar da dukan ƙazantarki. Zan maido da alƙalanki kamar yadda suke a dā can, mashawartanki kamar yadda suke da fari. Bayan haka za a ce da ke Birnin Masu Adalci, Amintacciyar Birni.” Za a fanshi Sihiyona da adalci, masu tubanta kuma da aikin gaskiya. Amma za a karye ’yan tawaye da masu zunubi, waɗanda suka rabu da Ubangiji kuma za su hallaka. “Za ku ji kunya saboda masujadan ƙarƙashin itatuwan oak da kuka yi farin ciki; za a kunyata ku saboda lambun da kuka zaɓa. Za ku zama kamar itacen oak mai busasshen ganyaye, kamar lambu marar ruwa. Mutum mai ƙarfi zai zama kamar rama, aikinsa kuma kamar tartsatsin wuta; duka za su ƙone tare, ba kuwa wanda zai kashe wutar.” Ga abin da Ishaya ɗan Amoz ya gani game da Yahuda da Urushalima. A kwanaki masu zuwa za a kafa dutsen haikalin Ubangiji a matsayin babba cikin duwatsu; za a daga shi bisa tuddai, kuma dukan al’ummai za su bumbunto zuwa gare shi. Mutane da yawa za su zo su ce, “Ku zo, bari mu haura zuwa dutsen Ubangiji, zuwa gidan Allah na Yaƙub. Zai koya mana hanyoyinsa, domin mu yi tafiya cikin hanyoyinsa.” Dokar za tă fito daga Sihiyona, maganar Ubangiji daga Urushalima. Zai shari’anta tsakanin al’ummai zai kuma sulhunta faɗar mutane masu yawa. Za su mai da takubansu su zama garemani māsunsu su zama wuƙaƙen askin itatuwa. Al’umma ba za tă ƙara ɗauki takobi a kan al’umma ba, ba kuwa za su ƙara yin horarwar yaƙi. Ki zo, ya gidan Yaƙub, bari mu yi tafiya a hasken Ubangiji. Ka rabu da mutanenka, gidan Yaƙub. Sun cika da ayyukan sihiri da aka kawo daga Gabas; suna yin duba kamar Filistiyawa suna tafa hannuwa tare da marasa sanin Allah. Ƙasarsu ta cika da azurfa da zinariya; dukiyarsu kuma ba iyaka. Ƙasarsu ta cika da dawakai; kekunan yaƙinsu kuma ba iyaka. Ƙasarsu ta cika da gumaka; sukan rusuna ga aikin hannuwansu, ga abin da yatsotsinsu suka yi. Saboda an jawo mutum ƙasa aka kuma ƙasƙantar da ɗan adam, kada ku gafarta musu. Ku tafi cikin duwatsu, ku ɓuya cikin ƙasa daga razanar Ubangiji da kuma darajar ɗaukakarsa! Za a ƙasƙantar da mai girman kai za a kuma lalatar da fariyar masu ɗaga kai; Ubangiji kaɗai za a ɗaukaka a wannan rana. Ubangiji Maɗaukaki yana da rana ajiye domin dukan masu girman kai da masu fariya domin dukan waɗanda aka ɗaukaka (zai kuwa ƙasƙantar da su), domin dukan al’ul na Lebanon, masu tsayi da masu fariya, da kuma dukan itatuwan oak na Bashan, domin dukan dogayen duwatsu da kuma tuddai masu tsayi, domin kowace doguwar hasumiya da kowace katanga mai ƙarfi, domin kowane jirgin ruwan kasuwanci da kuma jirgi mafi girma mafi kyau. Za a jawo mai girman kai ƙasa a kuma ƙasƙantar da mai ɗaga kai; Ubangiji kaɗai za a ɗaukaka a wannan rana, za a kuma kawar da gumaka ƙaƙaf. Mutane za su gudu zuwa kogwannin duwatsu da kuma ramummuka a ƙasa daga razanar Ubangiji da kuma darajar ɗaukakarsa, sa’ad da ya tashi don yă girgiza duniya. A wannan rana mutane za su zubar wa jaba da jamage gumakansu na azurfa da gumakansu na zinariya da suka yi don su bauta musu. Za su gudu zuwa kogwannin duwatsu da kuma zuwa tsagaggun duwatsu daga razanar Ubangiji da kuma darajar ɗaukakarsa, sa’ad da ya tashi don yă girgiza duniya. Ku daina dogara ga mutum, wanda numfashi ne kawai yake da shi a hancinsa. Wace daraja gare shi? Yanzu ka duba fa, Ubangiji, Ubangiji Maɗaukaki, yana shirin yă ɗauke kowane tanadi da taimako daga Urushalima da Yahuda dukan tanade-tanaden abinci da kuma dukan tanade-tanaden ruwa, jarumi, da soja, alƙali da annabi masu duba da dattijo, shugaban sojojin hamsin da mutum mai makami, mai ba da shawara, gwanin sarrafa abubuwa da mai gwanintan dabo. “Zan sa ’yan yara su zama shugabanninsu; ’yan yara kurum za su yi mulkinsu.” Mutane za su zalunci juna mutum da mutum, maƙwabci da maƙwabci. Yara za su rena tsofaffi, ƙasƙantacce zai rena mai daraja. Mutum zai kama ɗaya daga cikin ’yan’uwansa a gidan mahaifinsa ya ce, “Kana da abin sawa, ka zama shugabanmu; wannan kango kuma yă zama a ƙarƙashinka!” Amma a ranan nan zai tā da murya ya ce, “Ba ni ba dai. Ba ni da abinci ko abin sawa a gidana; kada ka mai da ni shugaban mutane.” Urushalima tana tangaɗi, Yahuda yana fāɗuwa; maganganunsu da ayyukansu suna gāba da Ubangiji, suna rena ɗaukakar kasancewarsa. Fuskokinsu shaidu ne a kansu; suna nuna zunubinsu a fili kamar yadda Sodom ya yi; ba sa ma ɓoye shi. Kaitonsu! Sun jawo wa kansu masifa. Ku faɗa wa masu adalci cewa kome zai zama musu da kyau, gama za su ji daɗin aikin da hannuwansu suka yi. Kaiton masu mugunta! Masifa tana a kansu! Za a rama abin da hannuwansu suka yi. Matasa suna zalunta mutanena, mata suna mulki a bisansu. Ya mutanena, jagorarinku suna ɓad da ku; suna karkatar da ku daga hanya. Ubangiji ya ɗauki mazauninsa a cikin ɗakin shari’a; ya tashi don yă shari’anta mutane. Ubangiji yana shari’a da dattawa da kuma shugabannin mutanensa, “Ku ne kuka lalace gonar inabina; ganimar talakawa suna a gidajenku. Ina dalilin da kuke marmatsa mutanena kuna gurgurje fuskokin talakawa?” Ni Ubangiji Maɗaukaki na faɗa. Ubangiji ya ce, “Matan Sihiyona suna da girman kai, suna tafiya da wuya a miƙe, da idanu masu yaudara, suna takawa ɗaya-ɗaya a hankali, da mundaye a ƙafafunsu, suna cas-cas. Saboda haka Ubangiji zai kawo gyambuna a kawunan matan Sihiyona; Ubangiji zai sa a aske kawunansu, a bar su ƙwal.” A wannan rana Ubangiji zai ƙwace abin da suke taƙama da shi, mundayensu, ɗankwalin kansu da abin wuyansu, ’yan kunnensu, kwandagansu da lulluɓinsu, kitsonsu, sarƙar da suke sa wa damatsansu da ɗamararsu, kwalabai turare da layu, da ƙawanen da suka sa a yatsotsinsu da hancinsu, tufafi masu kyau, da manyan rigunansu, da mayafansu, da jakar kuɗinsu da madubi, da kuma tufafin lilin da adikai, da gyale. A maimakon ƙanshi, wari ne za a ji; a maimakon abin ɗamara, igiya ce za a samu; a maimakon kyakkyawan gashi, sanƙo za su kasance da shi a kai; a maimakon tufafi masu kyau, za su sa tsummoki; a maimakon kyau, za su zama munana. Mazanku za su mutu ta wurin takobi, jarumawanku za su mutu a yaƙi. Ƙofofin Sihiyona za su yi makoki su kuma yi kuka; za tă zama wofi, za tă zauna a ƙasa. A wannan rana mata guda bakwai za su cafke namiji guda su ce, “Ma ciyar da kanmu mu kuma yi wa kanmu sutura; ka dai bari mu ce kai ne mijinmu. Ka ɗauke mana kunyar da za mu sha.” A wannan rana Reshen Ubangiji zai zama kyakkyawa da kuma ɗaukaka, kuma amfanin ƙasar zai zama abin fariya da ɗaukakar waɗanda suka rayu a Isra’ila. Waɗanda suka rage a Sihiyona, waɗanda suka rage a Urushalima, za a ce da su masu tsarki, wato, dukan waɗanda aka rubuta a cikin masu rai a Urushalima. Ubangiji zai wanke duk wani ƙazantar matan Sihiyona; ya tsabtacce jinin da aka zubar daga Urushalima ta wurin ruhun hukunci da yake ƙuna kamar wuta. Sa’an nan Ubangiji zai sa girgijen hayaƙi da rana da harshen wuta da dare a bisa dukan Dutsen Sihiyona da kuma bisa waɗanda suka tattaru a can; a bisa duka kuwa ɗaukakar za tă zama rumfa. Za tă zama rumfa da inuwar da za tă tare zafin rana, da kuma mafaka da wurin ɓuya daga hadari da ruwan sama. Zan rera waƙa wa ƙaunataccena waƙa game da gonar inabinsa. Ƙaunataccena yana da gonar inabi a gefen tudu mai dausayi. Ya haƙa ƙasa ya kuma tsintsince duwatsun ya shuka mata inabi mafi kyau. Ya gina hasumiyar tsaro a cikinta ya kuma shirya wurin matsin ruwan inabi. Sa’an nan ya sa rai ga samun girbi mai kyau na inabin, amma sai ga shi inabin ya ba da munanan ’ya’ya. “Yanzu fa ku mazauna cikin Urushalima da mutanen Yahuda, ku shari’anta tsakanina da gonar inabina. Me kuma ya rage da za a yi wa gonar inabina fiye da abin da na yi mata? Da na nemi inabi masu kyau, me ya sa ta ba da munana ’ya’ya? Yanzu zan faɗa muku abin da zan yi da gonar inabina. Zan cire katangar da ta kewaye ta, za tă kuwa lalace; zan rushe bangonta, za a kuwa tattake ta. Zan mai da ita kango, ba zan aske ta ba, ba kuwa zan nome ta ba, sarƙaƙƙiya da ƙayayyuwa kuwa za su yi girma a can Zan umarci gizagizai kada su yi ruwan sama a kanta.” Gonar inabin Ubangiji Maɗaukaki ita ce gidan Isra’ila, mutanen Yahuda kuma su ne lambun farin cikinsa. Yana kuma nema ganin gaskiya, amma sai ga zub da jini; yana neman adalci, amma sai ga shi kukan azaba yake ji. Kaitonku ku waɗanda kuke ƙara wa kanku gidaje kuke kuma haɗa gonaki da gonaki har babu sauran filin da ya rage ku kuma zauna ku kaɗai a ƙasar. Ubangiji Maɗaukaki ya furta a kunnuwana, “Tabbatacce manyan gidajen za su zama kango, za a bar kyawawan gidajen nan ba kowa. Kadada goma na gonar inabi zai ba da garwan ruwan inabi ɗaya kaɗai, mudu guda na iri kuma zai ba da efa na hatsi guda kurum.” Kaiton waɗanda suke tashi da sassafe don su nufi wurin shaye-shaye, waɗanda suke raba dare har sai sun bugu da ruwan inabi. Suna kaɗa garaya, da molaye a bukukkuwansu, ganguna da busa da ruwan inabi, amma ba su kula da ayyukan Ubangiji ba, ba sa biyayya ga aikin hannuwansa. Saboda haka mutanena za su yi zaman bauta domin rashin fahimi; manyan mutanensu za su mutu da yunwa talakawansu kuma su mutu da ƙishirwa. Saboda haka kabari ya fadada marmarinsa ya kuma buɗe bakinsa babu iyaka; cikinsa manyan mutanensu da talakawansu za su gangara tare da dukan masu hayaniyarsu da masu murnansu. Ta haka za a ƙasƙantar da mutum kuma za a ƙasƙantar da ’yan adam, za a ƙasƙanta da masu girman kai. Amma Ubangiji Maɗaukaki zai sami ɗaukaka ta wurin aikata gaskiya, kuma Allah mai tsarki zai nuna kansa ta wurin adalcinsa. Sa’an nan tumaki za su yi kiwo kamar yadda suke yi a wurin kiwonsu; raguna za su yi kiwo cikin abubuwa masu kyau da suka lalace. Kaiton waɗanda suke jan zunubi da igiyar ruɗu, da kuma mugunta da igiyoyin keken yaƙin, waɗanda suke cewa, “Bari Allah yă gaggauta, bari yă hanzarta aikinsa don mu gani. Bari yă iso, bari shirin Mai Tsarkin nan na Isra’ila yă zo, don mu sani.” Kaiton waɗanda suke ce da mugunta nagarta nagarta kuma mugunta, waɗanda suke mai da duhu haske haske kuma duhu, waɗanda suke mai da ɗaci zaƙi zaƙi kuma ɗaci. Kaiton waɗanda suke tsammani suna da hikima da kuma wayo a idonsu. Kaiton waɗanda suke jarumawa a shan ruwan inabi da gwanaye a haɗin abubuwan sha, waɗanda suke ƙyale masu laifi don sun ba da cin hanci, amma su hana a yi gaskiya wa marasa laifi. Saboda haka kamar yadda harshen wuta yakan lashe kara kuma kamar yadda busasshiyar ciyawa takan ƙone ƙurmus a cikin wuta, haka saiwarsu za su ruɓa iska kuma ta hura furanninsu kamar ƙura; gama sun ƙi dokar Ubangiji Maɗaukaki suka kuma ƙyale maganar Mai Tsarkin nan na Isra’ila. Saboda haka fushin Ubangiji ya yi ƙuna a kan mutanensa; ya ɗaga hannunsa ya kuma buge su. Duwatsu sun jijjigu, gawawwaki kuwa suka zama kamar juji a tituna. Saboda wannan duka, fushinsa bai huce ba, bai kuwa janye hannunsa ba. Ya ɗaga tuta don al’ummai masu nisa, ya yi feɗuwa wa waɗanda suke a iyakar duniya. Ga shi sun iso, da sauri da kuma gaggawa! Babu ko ɗayansu da ya gaji ko ya yi tuntuɓe, babu ko ɗaya da ya yi gyangyaɗi ko barci; babu abin ɗamarar da ya kunce a gindi, ba igiyar takalmin da ta tsinke. Kibiyoyinsu masu tsini ne, an ɗaura dukan bakkunansu; kofatan dawakansu sun yi kamar dutsen ƙanƙara, ƙafafun keken yaƙinsu kamar guguwa ne. Rurinsu ya yi kamar na zaki, suna ruri kamar ’yan zakoki; suna yin gurnani yayinda suke kamun abin da suke farauta su ɗauke shi ba mai ƙwace shi. A wannan rana za su yi ta ruri a kansa kamar rurin teku. Kuma in wani ya dubi ƙasar, zai ga duhu da damuwa; haske ma zai zama duhu ta wurin gizagizai. A shekarar da Sarki Uzziya ya mutu, na ga Ubangiji zaune a kan kujerar sarauta a sama cike da ɗaukaka, zatinsa ya cika haikali. A bisansa akwai serafofi, kowanne yana da fikafikai shida. Fikafikai biyu sun rufe fuskokinsu, da biyu suka rufe ƙafafunsu, biyu kuma da su suke tashi. Suna kiran juna, “Mai Tsarki, Mai Tsarki, Mai Tsarki! Ubangiji Maɗaukaki ne; duniya ta cika da ɗaukakarsa.” Da jin ƙarar muryoyinsu madogarai da madogaran ƙofa suka girgiza, haikali kuma ya cika da hayaƙi. Sai na tā da murya na ce, “Kaitona! Na shiga uku! Gama ni mutum ne mai leɓuna marar tsarki, kuma ina raye a cikin mutane masu leɓuna marasa tsarki, idanuna kuma sun ga Sarki, Ubangiji Maɗaukaki.” Sai ɗaya daga cikin serafofin ya yi firiya zuwa wurina tare da garwashi mai wuta a hannunsa, wanda ya ɗiba da arautaki daga bagade. Da shi ne ya taɓa bakina ya ce, “Duba, wannan ya taɓa leɓunanka, yanzu fa an kawar da laifofinka, an kuma gafarta maka zunubanka.” Sa’an nan na ji muryar Ubangiji tana cewa, “Wa zan aika? Wa zai tafi mana?” Sai na ce, “Ga ni! Ka aike ni!” Ya ce, “Je ka ka faɗa wa wannan mutane, “ ‘Kome yawan kasa kunne da za ku yi, ba za ku fahimta ba; Kome yawan dubar da za ku yi, ba za ku san abin da yake faruwa ba.’ Ka sa zuciyar mutanen nan ta dushe; kunnuwansu su kurunce, idanunsu kuma su makance. In ba haka ba za su iya gani da idanunsu, su ji da kunnuwansu, su fahimta da zuciyarsu, su kuma juyo a kuma warkar da su.” Sa’an nan na ce, “Har yaushe, ya Ubangiji?” Ya kuma amsa, “Sai an lalatar da biranen ba kowa a ciki, sai an mai da gidaje kangwaye ƙasa kuma ta zama kango ba amfani, sai lokacin da Ubangiji ya kori kowa aka kuma yashe ƙasar gaba ɗaya. Ko da yake kashi ɗaya bisa goma zai ragu a ƙasar, za tă sāke zama kango. Amma kamar yadda katambiri da itacen oak sukan bar kututturai sa’ad da aka yanke su, haka iri mai tsarkin nan zai zama kututture a ƙasar mai tsarki.” Sa’ad da Ahaz ɗan Yotam, ɗan Uzziya, yake sarkin Yahuda, Sarki Rezin na Aram da Feka ɗan Remaliya sarkin Isra’ila suka haura don su yaƙi Urushalima, amma ba su iya cinta da yaƙi ba. Sai fa aka faɗa wa gidan Dawuda cewa, “Aram ya haɗa kansa da Efraim”; saboda haka zuciyar Ahaz da ta mutanensa suka firgita, sai ka ce itatuwa a kurmin da iska ta girgiza. Sai Ubangiji ya ce wa Ishaya, “Fita, kai da ɗanka Sheyar-Yashub, don ku sadu da Ahaz a ƙarshen wuriyar da take kawo ruwa daga Tafkin Tudu, a hanyar Filin Mai Wanki. Ka faɗa masa, ‘Ka yi hankali, ka natsu kada kuma ka ji tsoro ko ka damu, kada ka ji tsoron fushin sarki Rezin da na Aram da na ɗan Remaliya, ba wani abu mai hatsari ba ne, bai fi hayaƙin ’yan ƙirare biyu da suke cin wuta ba. Aram, Efraim da ɗan Remaliya sun ƙulla maƙarƙashiya, suna cewa, “Bari mu kai wa Yahuda hari; bari mu yayyage su mu rarraba su a tsakaninmu, mu naɗa Tabeyel sarki a kansu.” Duk da haka ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka ya ce, “ ‘Ba zai faru ba, ba zai auku ba, gama kan Aram shi ne Damaskus, kan Damaskus kuma kawai shi ne Rezin. Cikin shekaru sittin da biyar za a wargaje Efraim har ba za tă iya rayuwa ta zama al’umma ba. Kan Efraim shi ne Samariya, kan Samariya kuma kawai shi ne ɗan Remaliya. In ba ku tsaya da ƙarfi cikin bangaskiyarku ba, ba za ku dawwama ba.’ ” Ubangiji ya kuma yi magana wa Ahaz ya ce, “Ka roƙi Ubangiji Allahnka yă ba ka alama, ko daga zurfafa masu zurfi ko kuwa daga can cikin sama.” Amma Ahaz ya ce, “Ba zan nema ba; ba zan gwada Ubangiji ba.” Sa’an nan Ishaya ya ce, “To, ku saurara, ya ku gidan Dawuda! Abin kirki kuke yi ne da kuka ƙure haƙurin jama’a? Ko haƙurin Allah ne kuma kuke so ku ƙure? Saboda haka Ubangiji kansa zai ba ku alama. Ga shi budurwa za tă yi ciki, za tă haifi ɗa, za tă kuwa kira shi Immanuwel. In ya yi girma har ya isa yanke shawara don kansa, madara da zuma ne abincinsa. Amma kafin yaron yă isa yanke shawara yă ƙi abin da yake mummuna, yă zaɓi abin da yake nagari, ƙasashen sarakunan nan biyu da kuke tsoro za su zama kango. Ubangiji zai aukar maka da kwanakin wahala, kai da jama’arka, da dukan iyalin gidan sarauta, waɗanda suka fi muni tun lokacin da aka raba mulkin Efraim daga na Yahuda, zai kawo sarkin Assuriya.” A wannan rana Ubangiji zai yi feɗuwa yă kira ƙudaje daga rafuffuka masu nisa na Masar da kuma ƙudan zuma daga ƙasar Assuriya. Za su zo su mamaye kwazazzabai da kogwanni cikin duwatsu, a kan dukan ƙayayyuwa da dukan rammukan ruwa. A wannan rana Ubangiji zai yi amfani da rezan da aka yi haya daga ƙetaren Kogi, sarkin Assuriya ke nan, yă aske kanku da gashin ƙafafunku, zai kuma aske gemunku. A ranar, mutum zai bar karsana ɗaya da awaki biyu da rai. Kuma saboda yalwa madarar da suke bayarwa, zai kasance da madarar da zai sha. Dukan waɗanda suka rage a ƙasar za su sha madara da zuma. A wannan rana, a kowane wuri inda akwai kuringa dubu da kuɗinsu ya kai shekel dubu na azurfa, ƙayayyuwa da sarƙaƙƙiya ne kawai za su kasance a can. Mutane za su je can da baka da kibiyoyi, gama ƙayayyuwa da sarƙaƙƙiya ne za su rufe ƙasar. Game da dukan tuddai da dā ake nome da garemani kuwa, ba za ku ƙara je wurin ba saboda tsoron ƙayayyuwa da sarƙaƙƙiya; za su zama wuraren da ake kai shanu a sake su su yi ta yawo da kansu, tumaki kuma su yi ta gudu. Ubangiji ya ce mini, “Ka ɗauki naɗaɗɗen littafi mai girma ka yi rubutu a kai da alƙalami kurum, Maher-Shalal-Hash-Baz. Zan kuma kira Uriya firist da Zakariya ɗan Yeberekiya su zama mini amintattun shaidu.” Sa’an nan na tafi na yi jima’i da annabiya, ta kuwa yi ciki ta haifi ɗa. Ubangiji kuma ya ce mini, “Raɗa masa suna, Maher-Shalal-Hash-Baz. Kafin yaron yă san yadda zai ce ‘Babana’ ko ‘Mamana,’ sarkin Assuriya zai kwashe arzikin Damaskus da ganimar Samariya.” Ubangiji ya sāke yi mini magana ya ce, “Domin wannan jama’a ta ƙi natsattsen ruwan rafin Shilowa suka yi ta farin ciki a kan Rezin ɗan Remaliya, saboda haka Ubangiji yana shirin yă kawo musu rigyawar ruwan Kogi, wato, sarkin Assuriya da dukan sojojinsa. Zai cika dukan gaɓoɓinsa, yă kuma malala har zuwa bakin kogi. Yă yi ta malala har zuwa cikin Yahuda, yă shafe ta, yana ratsa ta ciki har yă kai kafaɗa. Fikafikansa da ya buɗe za su rufe fāɗin ƙasarka, Ya Immanuwel!” Ku yi kururuwar yaƙi, ku ƙasashe, ku kuma ji tsoro! Ku saurara, dukanku manisantan ƙasashe. Ku shirya don yaƙi, ku kuma ji tsoro! Ku ƙirƙiro dabarunku, amma ba za su yi nasara ba; ku ƙulla shirye-shiryenku, amma ba za su yi amfani ba, gama Allah yana tare da mu. Ubangiji ya yi mini magana da hannunsa mai ƙarfi a kaina, yana yi mini gargaɗi kada in bi hanyar waɗannan mutane. Ya ce, “Kada ka kira wani abu makirci game da kome da waɗannan mutane suke kira makirci; kada ji tsoron abin da suke tsoro, kada kuma ka firgita game da shi. Ubangiji Maɗaukaki shi ne za ka ɗauka a matsayi mai tsarki, shi ne wanda za ka ji tsoro, shi ne za ka yi rawar jiki a gabansa, zai kuwa kasance a wuri mai tsarki; amma ga dukan gidajen Isra’ila zai zama dutsen da zai sa mutane su yi tuntuɓe dutse kuma da zai sa su fāɗi. Ga dukan mutanen Urushalima kuma zai zama tarko da raga. Yawancinsu za su yi tuntuɓe; za su fāɗi a kuwa ragargaza su, za a sa musu tarko a kuma kama su.” Ɗaura shaidar nan ta gargadi ka kuma yimƙe umarnin Allah a cikin almajiraina. Zan saurari Ubangiji, wanda ya ɓoye fuskarsa daga gidan Yaƙub. Zan dogara gare shi. Ga ni, da yaran da Ubangiji ya ba ni. Mu alamu ne da shaidu a cikin Isra’ila daga Ubangiji Maɗaukaki, wanda yake zama a Dutsen Sihiyona. Sa’ad da mutane suka ce muku ku nemi shawarar ’yan bori da masu sihiri, waɗanda suke shaƙe murya har ba a jin abin da suke faɗi, bai kamata mutane su nemi shawara daga Allahnsu ba? Me zai sa ku nemi shawara daga matattu a madadin masu rai? Nemi umarnin Allah da kuma shaidar jan kunne. Duk wanda bai yi magana bisa ga wannan kalma ba, ba su da amfani. Cikin matsuwa da yunwa, za su yi ta kai komo ko’ina a ƙasar; sa’ad da suka ji yunwa, za su yi fushi su tā da idanu sama, su zagi sarkinsu da Allahnsu. Sa’an nan za su zura wa ƙasa idanu, abin da za su gani kawai shi ne matsuwa da duhu da kuma abin banrazana, za a kuma jefa su cikin baƙin duhu. Duk da haka, babu sauran baƙin ciki ga waɗanda suke shan azaba. Dā ya ƙasƙantar da ƙasar kabilan Zebulun da ƙasar Naftali, amma nan gaba zai girmama Galili na Al’ummai, ta hanyar teku wadda take ta Urdun. Mutanen da suke tafiya cikin duhu sun ga babban haske; a kan waɗanda suke zama a ƙasar inuwar mutuwa haske ya haskaka. Ka fadada al’umma ka kuma ƙara farin cikinsu; suna farin ciki a gabanka yadda mutane sukan yi murna a lokacin girbi, kamar yadda mutane sukan yi farin ciki sa’ad da suke raba ganima. Gama kamar yadda yake a kwanakin da aka ci Midiyan da yaƙi, kuka ji tsoro nauyin da ya nawaita musu, sandar da yake a kafaɗunsu, sandar masu zaluncinsu. Kowane takalmin jarumin da aka yi amfani da shi a yaƙi da kuma kowane rigar da ka naɗe cikin jini zai kasance an ƙone shi zai kuma zama abin hura wuta. Gama a gare mu an haifa mana yaro, a gare mu an ba da ɗa, gwamnati za tă kasance a kafaɗarsa. Za a ce da shi Mashawarci Mai Banmamaki, Allah Maɗaukaki Uban Madawwami, Sarkin Salama. Game da girmar gwamnatinsa da salama babu iyaka. Zai gāji sarki Dawuda, yă yi mulki a matsayinsa, zai kafa mulkinsa a kan adalci da gaskiya, tun daga yanzu har zuwa ƙarshen zamani. Ubangiji Maɗaukaki ne ya yi niyyar aikata wannan duka. Ubangiji ya aika da saƙon gāba da Yaƙub; zai auka wa Isra’ila. Dukan mutane za su san shi, Efraim da mazaunan Samariya, waɗanda suke magana da fariya suna kuma ɗaga kai, “Tubalai sun zube a ƙasa, amma za mu sāke gina su da dutse; an sassare itatuwan ɓaure, amma za mu maya su da al’ul.” Amma Ubangiji ya ƙarfafa maƙiyan Rezin gāba da su ya kuma ingiza abokan gāba. Arameyawa daga gabas da Filistiyawa daga yamma sun cinye Isra’ila da buɗaɗɗen baki. Duk da haka, fushinsa bai huce ba, hannunsa har yanzu yana a miƙe. Amma mutanen ba su juyo wurin wanda ya buge su ba, balle su nemi Ubangiji Maɗaukaki. Saboda haka Ubangiji zai yanke Isra’ila kai da wutsiya, da reshen dabino da iwa a rana guda; dattawa da manyan mutane su ne kai, annabawa waɗanda suke koyar da ƙarairayi su ne wutsiya. Waɗanda suke jagorar wannan mutane suna ɓad da su, su ne waɗanda ake jagora aka sa suka kauce. Saboda haka Ubangiji ba zai ji daɗin matasa ba, ba kuwa zai ji tausayin marayu da gwauraye ba, gama kowa marar sanin Allah ne da kuma mugu, kowane baki yana faɗin mugayen maganganu. Duk da haka, fushinsa bai huce ba, hannunsa har yanzu yana a miƙe. Tabbatacce mugunta tana ƙuna kamar wuta; tana cin ƙayayyuwa da sarƙaƙƙiya, ta sa wuta a jeji mai itatuwa masu yawa, don yă yi murtuke hayaƙi har zuwa sama. Ta wurin fushin Ubangiji Maɗaukaki ƙasar za tă ci wuta mutane kuma za su zama abin hura wutar, babu wanda zai ji tausayin ɗan’uwansa. A dama za su ci, amma su ci gaba da jin yunwa; a hagu za su ci, amma ba za su ƙoshi ba. Kowa zai mai da naman ’ya’yansa abinci. Manasse zai mai da Efraim abinci, Efraim kuma yă cinye Manasse; tare za su yi gāba da Yahuda. Duk da haka, fushinsa bai huce ba, hannunsa har yanzu yana a miƙe. Kaiton waɗanda suke kafa dokokin rashin gaskiya, waɗanda suke ba da ƙa’idodin danniya, don su hana matalauta hakkinsu su kuma ƙi yin shari’ar gaskiya a kan waɗanda suke zaluntar mutanena, suna ƙwace wa gwauraye dukiyarsu suna kuma yi wa marayu ƙwace. Me za ku yi a ranan nan ta hukunci, sa’ad da masifa ta zo daga nesa? Ga wa za ku tafi don neman taimako? Ina za ku bar dukiyarku? Babu abin da zai rage sai cizon haƙora a cikin kamammu ko mutuwa cikin waɗanda aka kashe. Duk da haka, fushinsa bai huce ba, hannunsa har yanzu yana a miƙe. “Kaiton Assuriya, sandar fushina, a hannun da kulkin fushina yake! Na aike shi gāba da al’umma marar sanin Allah, na tura shi gāba da mutanen da suka ba ni fushi, don yă kwashe ganima yă kuma yi wason ganima, yă tattake su kamar laka a tituna. Amma ba abin da ya yi niyya ke nan ba, ba abin da yake da shi a zuciya ba; manufarsa shi ne yă hallaka, yă kuma kawo ƙarshen al’ummai da yawa. Ya ce, ‘Dukan shugabannin yaƙina ba sarakuna ba ne?’ ‘Kalno bai kasance kamar Karkemish ba? Hamat bai zama kamar Arfad Samariya kuma kamar Damaskus ba? Yadda hannuna ya ƙwace mulkokin gumaka, mulkokin da siffofinsu suka fi na Urushalima da Samariya, ba zan yi da Urushalima da siffofinta yadda na yi da Samariya da gumakanta ba?’ ” Sa’ad da Ubangiji ya gama dukan aikinsa gāba da Dutsen Sihiyona da Urushalima, zai ce, “Zan hukunta sarkin Assuriya saboda fariya na gangancin zuciyarsa da kuma kallon reni na idanunsa. Gama ya ce, “ ‘Ta wurin ƙarfin hannuna ne na aikata wannan, da kuma ta wurin hikimata, gama ina da fahimi. Na kau da iyakokin ƙasashe, na washe dukiyarsu; a matsayina na mai iko, na mamaye sarakunansu. Kamar yadda mutum yakan miƙa hannu cikin sheƙar tsuntsu haka hannuna ya je ya washe dukiyar al’ummai; kamar yadda mutane sukan tattara ƙwai, haka na tattara dukan ƙasashe; ba tsuntsun da ya kakkaɓe fikafiki, ko yă buɗe baki don yă yi kuka.’ ” Gatari ya taɓa fin wanda yake amfani da shi girma, ko zarto yă yi wa wanda yake amfani da shi taƙama? Sanda za tă girgiza mutumin da yake riƙe da ita, ko kuwa kulki yă jijjiga mutumin da yake riƙe da katako! Saboda haka Ubangiji Maɗaukaki, zai aukar da cuta mai kisa a kan ƙosassu jarumawa; a ƙarƙashin sansaninsa zai ƙuna wuta kamar harshen wuta. Hasken Isra’ila zai zo kamar wuta, Mai Tsarkinsu zai zama kamar wuta; a rana guda zai ƙone yă kuma cinye ƙayayyuwa da sarƙaƙƙiyarsa. Darajar jejinsa da gonakinsa masu dausayi za a hallaka su ɗungum, kamar yadda ciwo yakan kashe mutum. Sauran itatuwan jejinsa kuma za su ragu ko ɗan ƙaramin yaro ma zai iya ƙidaya su. A wannan rana raguwar Isra’ila, waɗanda suka ragu na gidan Yaƙub, ba za su ƙara dogara ga wanda ya kusa hallaka su ba amma za su dogara ga Ubangiji, Mai Tsarkin nan na Isra’ila. Raguwa za tă komo, raguwar Yaƙub za su komo ga Maɗaukaki Allah. Ko da yake mutanenka, ya Isra’ila, sun zama kamar yashin bakin teku, raguwa ce kurum za tă komo. A ƙaddara hallaka, mai mamayewa da mai adalci. Ubangiji Maɗaukaki, zai sa hallakar da aka ƙaddara a kan dukan ƙasa ta faru. Saboda haka, ga abin da Ubangiji Maɗaukaki ya ce, “Ya mutanena masu zama a Sihiyona, kada ku ji tsoron Assuriyawa, waɗanda suka dūke ku da sanda suka kuma ɗaga kulki a kanku, kamar yadda Masar ta yi. Ba da daɗewa ba fushina a kanku zai zo ga ƙarshe hasalata kuma za tă koma ga hallakarsu.” Ubangiji Maɗaukaki zai bulale su da tsumagiya, kamar sa’ad da ya bugi Midiyan a dutsen Oreb; zai kuma ɗaga sandarsa a bisa ruwaye, yadda ya yi a Masar. A wannan rana zai ɗauke nauyi daga kafaɗarku, nauyinsu daga wuyanku; za a karye karkiya domin kun yi ƙiba ƙwarai. Sun shiga Ayiyat; sun bi ta Migron; sun adana tanade-tanade a Mikmash. Suka ƙetare ta hanya, suka kuma ce, “Za mu kwana a Geba.” Rama ta firgita; Gibeya ta Shawulu ta gudu. Ki yi ihu, ya Diyar Gallim! Ki saurara, ya Layisha! Kayya, Anatot abin tausayi! Madmena tana gudu; mutanen Gebim sun ɓuya. A wannan rana za su dakata a Nob; za su jijjiga ƙarfinsu a dutsen Diyar Sihiyona, a tudun Urushalima. Duba, Ubangiji Maɗaukaki, zai ragargaza rassa da iko mai girma. Za a sassare itatuwa masu ganyaye, za a yanke dogayen itatuwa har ƙasa. Zai sassare itatuwan jeji da gatari har ƙasa; Lebanon zai fāɗi a gaban Mai Iko. Toho zai fito daga kututturen Yesse; daga saiwarsa Reshe zai ba da ’ya’ya. Ruhun Ubangiji zai kasance a kansa, Ruhun hikima da na fahimta, Ruhun shawara da na iko, Ruhun sani da na tsoron Ubangiji, zai kuwa ji daɗin tsoron Ubangiji. Ba zai yi hukunci ta wurin abin da ya gani da idanunsa ba, ba zai kuwa yanke shawara ta wurin abin da ya ji da kunnuwansa ba; amma da adalci zai yi wa masu bukata shari’a, da gaskiya zai yanke shawarwari saboda matalautan duniya. Kamar sanda zai bugi duniya da maganar bakinsa; da numfashin leɓunansa zai yanke mugaye. Adalci ne zai zama abin ɗamararsa aminci kuma igiyar da zai ɗaura kewaye da gindinsa. Kyarkeci zai zauna tare da ɗan rago damisa za tă kwanta tare da akuya, ɗan maraƙi da zaki da ɗan saniya za su yi kiwo tare; ɗan yaro ne zai lura da su. Saniya da beyar za su yi kiwo tare, ƙananansu za su kwanta tare, zaki kuma zai ci ciyawa kamar saniya. Jariri zai yi wasa kurkusa da ramin gamsheƙa, ɗan yaro kuma zai sa hannunsa a ramin maciji mai mugun dafi. Ba za su yi lahani ko su hallaka wani a dutsena mai tsarki ba, gama duniya za tă cika da sanin Ubangiji kamar yadda ruwaye suka rufe teku. A wannan rana Saiwar Yesse zai miƙe kamar tuta don mutanenta; al’ummai za su tattaru wurinsa, wurin hutunsa kuma zai zama mai daraja. A wannan rana Ubangiji zai miƙa hannunsa sau na biyu don yă maido da raguwar da ta rage na mutanensa daga Assuriya, daga Masar ta Ƙasa, daga Masar ta Bisa, daga Kush, daga Elam, daga Babiloniya, daga Hamat da kuma daga tsibiran teku. Zai tā da tuta saboda al’ummai yă kuma tattara masu zaman bauta na Isra’ila; zai tattara mutanen Yahuda da suke a warwatse kusurwoyi huɗu na duniya. Kishin Efraim zai ɓace, za a kuma kau da abokan gāban Yahuda; Efraim ba zai yi kishin Yahuda ba, haka ma Yahuda ba zai yi gāba da Efraim ba. Tare za su fāɗa wa Filistiyawa da yaƙi daga yamma; tare za su washe mutane wajen gabas. Za su ɗibiya hannuwa a kan Edom da Mowab, Ammonawa kuma za su yi musu biyayya. Ubangiji zai busar da bakin tekun Masar; da iska mai zafi zai share hannunsa a bisa Kogin Yuferites Zai rarraba shi yă zama ƙanana rafuffuka bakwai saboda mutane su iya hayewa da ƙafa. Za a yi babbar hanya saboda raguwa mutanensa da ta rage daga Assuriya, kamar yadda ta kasance wa Isra’ila sa’ad da suka fito daga Masar. A wannan rana za ku ce, “Zan yabe ka, ya Ubangiji. Ko da yake a dā ka yi fushi da ni, amma yanzu ka daina fushi da ni ka kuwa ta’azantar da ni. Tabbatacce Allah shi ne mai cetona; zan dogara gare shi ba kuwa zan ji tsoro ba. Ubangiji, Ubangiji, ne ƙarfina da waƙata; ya zama mai cetona.” Da farin ciki zan ɗebo ruwa daga rijiyoyin ceto. A wannan rana za ku ce, “Yi godiya ga Ubangiji, ku kira bisa sunansa; a sanar da wannan abin da ya aikata a cikin al’ummai, a kuma yi shela cewa sunansa mai girma ne. Ku rera ga Ubangiji, gama ya aikata manyan abubuwa; bari a sanar da wannan ga dukan duniya. Ku tā da murya ku kuma rera don farin ciki, ya ku mutanen Sihiyona, gama Mai Tsarki na Isra’ila da girma yake a cikinku.” Abubuwan da Allah ya yi magana a kai game da Babilon da Ishaya ɗan Amoz ya gani. A tā da tuta a kan tudun da yake mai fili, ka tā da murya gare su; ka ɗaga hannu ka ba su alama don su shiga ƙofofi masu alfarma. Na umarci tsarkakana; na umarci jarumawan yaƙina su gamsar da fushina, waɗanda suke farin ciki a nasarata. Ka saurara, akwai surutu a kan duwatsu, sai ka ce na babban taron jama’a! Ka saurara, akwai hayaniya a cikin mulkoki, sai ka ce al’ummai ne suna ta tattaruwa! Ubangiji Maɗaukaki yana shirya mayaƙa don yaƙi. Suna zuwa daga ƙasashe masu nesa, daga iyakokin duniya, Ubangiji da kuma fushinsa, zai hallaka dukan ƙasar. Ku yi ihu, gama ranar Ubangiji ta yi kusa za tă zo kamar hallaka daga Maɗaukaki. Saboda wannan, hannun kowane mutum zai yi rauni, ƙarfin halin kowane mutum zai kāsa. Tsoro zai kama su, zafi da azaba za su ci ƙarfinsu; za su yi ta murɗewa kamar mace mai naƙuda. Za su dubi juna a tsorace, fuskokinsu a ɓace. Duba, ranar Ubangiji tana zuwa, muguwar rana, mai hasala da zafin fushi, don ta mai da ƙasar kango ta kuma hallakar da masu zunubi da suke cikinta. Taurarin sama da ƙungiyoyinsu ba za su ba da haskensu ba. Rana za tă yi duhu wata kuma ba zai ba da haskensa ba. Zan hukunta duniya saboda muguntarta, mugaye saboda zunubansu. Zan kawo ƙarshe ga girman kan masu taƙama in kuma ƙasƙantar da ɗaga kan marasa tausayi. Zan sa mutum yă fi zinariya zalla wuyar samuwa, fiye da zinariyar Ofir wuyan gani. Saboda haka zan sa sammai su yi rawar jiki; duniya kuma za tă girgiza daga inda take a fushin Ubangiji Maɗaukaki, a ranar fushinsa mai ƙuna. Kamar barewar da ake farautarta kamar tumaki marasa makiyayi, haka nan kowane mutum zai koma ga mutanensa, kowane mutum zai gudu zuwa ƙasarsa. Duk wanda aka kama za a soke shi yă mutu; dukan waɗanda aka kama za su mutu ta takobi. Za a fyaɗa ’ya’yansu a ƙasa su yi kucu-kucu a idanunsu; za a washe gidajensu, a kuma kwana da matansu. Duba, zan zuga mutanen Medes su yi gāba da su, su da ba su kula da azurfa ba kuma ba sa damuwa da zinariya. Bakkunansu za su kashe samari; ba za su ji tausayin jarirai ba ba za su kuwa nuna jinƙai ga ’yan yara ba. Babilon, kayan daraja na mulkoki, abin fariyar Babiloniyawa, Allah zai kaɓantar da ita kamar yadda ya yi da Sodom da Gomorra. Ba za ƙara kasance da mazauna kuma ba ko a yi zama a cikinta dukan zamanai; Ba wani mutumin Arab da zai kafa tentinsa a can, ba makiyayin da zai taɓa kiwon garkensa a can. Amma halittun hamada za su kwanta a can, diloli za su cika gidajenta; a can mujiyoyi za su zauna, a can kuma awakin jeji za su yi ta tsalle. Kuraye za su yi ta kuka a kagarorinta, diloli kuma a cikin fadodinta masu alfarma. Lokacinta ya yi kusa, kwanakinta kuma ba za su yi tsawo ba. Ubangiji zai yi wa Yaƙub jinƙai; zai sāke zaɓi Isra’ila yă kuma zaunar da su a ƙasarsu. Baƙi ma za su zo su zauna tare da su su haɗa kai da gidan Yaƙub. Al’ummai za su ɗauke su su kuma kawo wurin da yake nasu. Gidan Isra’ila kuwa za tă mallaki al’ummai a matsayin bayi maza da mata a ƙasar Ubangiji. Za su mai da waɗanda suka kama su su zama kamammu su kuma yi mulki a kan waɗanda suka taɓa danne su. A ranar da Ubangiji ya hutashe ku daga wahala da azaba da muguwar bauta, za ku yi wa sarkin Babilon wannan ba’a. Mai danniya ya zo ga ƙarshe! Dubi yadda fushinsa ya ƙare! Ubangiji ya karye sandar mugaye, sandan mulkin masu mulki, wanda cikin fushi ya kashe mutane da bugu marar ƙarewa, kuma cikin fushi ya mamaye al’ummai da fushi ba ƙaƙƙautawa. Dukan ƙasashe suna hutawa suna kuma cikin salama; sun ɓarke da waƙa. Har itatuwan fir ma da kuma al’ul na Lebanon suna murna a kanka suna cewa, “Yanzu da aka ƙasƙantar da kai, babu wani mai yankan katakon da ya zo yă yanka mu.” Kabari a ƙarƙashi duk ya shirya don yă sadu da kai a zuwanka; yana tā da ruhohin da suka rasu don su gaishe ka, dukan waɗanda sun taɓa zama shugabanni a duniya; ya sa suka tashi daga kujerun sarauta, dukan waɗanda suke sarakuna a kan al’ummai. Duk za su amsa, za su ce maka, “Ashe kai ma raunana ne, kamar mu; ka zama kamar mu.” An yi ƙasa da dukan alfarmarka zuwa kabari, tare da surutan garayunka; tsutsotsi sun bazu a ƙarƙashinka tsutsotsi kuma suka rufe ka. Yaya aka yi ka fāɗo daga sama Ya tauraron safiya, ɗan hasken asuba! An fyaɗa ka da ƙasa, kai da ka taɓa ƙasƙantar da al’ummai! Ka yi tunani a ranka ka ce, “Zan hau zuwa sama; zan ɗaga kursiyina sama da taurarin Allah; zan zauna a kursiyi a kan dutsen taro, a can ƙurewar saman dutse mai tsarki. Zan haura can bisa gizagizai; zan mai da kaina kamar Mafi Ɗaukaka.” Amma ga shi an gangara da kai zuwa kabari, zuwa zurfafan rami. Waɗanda suka gan ka sun zura maka ido, suna tunani abin da zai same ka. “Wannan mutumin ne ya girgiza duniya ya kuma sa mulkoki suka razana, mutumin da ya mai da duniya ta zama hamada, wanda ya tumɓuke biranenta bai kuma bar kamammunsa suka tafi ba?” Dukan sarakunan duniya suna kwance a mace, kowa a kabarinsa. Amma an jefar da kabarinka kamar reshen da aka ƙi; an rufe ka da waɗanda aka kashe, tare da waɗanda aka soke da takobi, waɗanda suka gangara zuwa duwatsun rami. Kamar gawar da aka tattake da ƙafa, ba za a haɗa ka tare da su a jana’iza ba, gama ka hallaka ƙasarka ka kuma kashe mutanenka. Ba za a ƙara ambaci zuriyarka masu aikata mugunta ba. A shirya wuri don a yayyanka ’ya’yansa maza saboda zunuban kakanninsu; kada a reno su su gāji ƙasar su cika duniya da biranensu. “Zan yi gāba da su,” in ji Ubangiji Maɗaukaki. “Zan kau da sunan Babilon da waɗanda suka rage da rai a cikinta, ’ya’yanta da zuriyarta,” in ji Ubangiji. “Zan mai da ita wuri domin mujiyoyi da kuma fadama; zan share ta da tsintsiyar hallaka,” Ni Ubangiji Maɗaukaki na faɗa. Ubangiji Maɗaukaki ya rantse, “Tabbatacce, kamar yadda na riga na shirya, haka zai kasance, kuma kamar yadda na nufa, haka zai zama. Zan ragargazar da Assuriya a cikin ƙasata; a kan duwatsuna zan tattake shi. Za a ɗauke nauyin da ya sa wa mutanena, a kuma ɗauke nauyinsa daga kafaɗunsu.” Wannan shi ne shirin da na yi domin dukan duniya; wannan shi ne hannun da aka miƙa a bisa dukan al’ummai ke nan. Gama Ubangiji Maɗaukaki ya ƙudura ya yi wannan, wa kuwa zai hana shi? Ya riga ya miƙa hannunsa, wa zai komar da shi? Wannan abin da Allah ya yi magana ya zo ne a shekarar da Sarki Ahaz ya mutu. Kada ku yi farin ciki, dukanku Filistiyawa, cewa sandar da ta buge ku ta karye; daga saiwar wannan maciji wani mugun maciji mai dafi zai taso, ’ya’yansa za su zama wani maciji masu dafi mai tashi sama. Mafi talauci na matalauta zai sami wurin kiwo, mabukata kuma za su kwana lafiya. Amma zan hallakar da saiwarka da matsananciyar yunwa; za tă kashe naka da suka rage da rai. Ki yi ihu, ya ke ƙofa! Yi kururuwa, ya ke birni! Ku razana, dukanku Filistiyawa! Ƙunshin hayaƙi yana tasowa daga arewa, kuma babu matsorata a cikin sojojinsa. Wace amsa ce za a bayar wa jakadun wannan al’umma? “ Ubangiji ya kafa Sihiyona, kuma a cikinta mutanensa masu shan azaba za su sami mafaka.” Abin da Allah ya yi magana a kan Mowab shi ne, An lalatar da Ar a Mowab, an hallaka ta da dare! An lalatar da Kir a Mowab, an hallaka ta da dare! Dibon ya haura zuwa haikalinta, zuwa masujadan kan tudu don tă yi kuka; Mowab ta yi ihu a kan Nebo da Medeba. An aske kowane kai an kuma yanke kowane gemu. A tituna sun sa tsummoki a jikunansu; a kan rufin ɗakuna da kuma dandalin taruwa dukansu sai makoki suke yi, sun kwanta suna kuka. Heshbon da Eleyale sun yi kuka da ƙarfi, aka ji muryoyinsu ko’ina har zuwa Yahaz. Saboda haka mayaƙan Mowab suka yi kuka da ƙarfi, har zuciyarsu ta karai. Zuciyata ta yi kuka a kan Mowab; mutanenta sun gudu har zuwa Zowar, har zuwa Eglat Shelishiya. Sun haura zuwa Luhit, suna tafe suna kuka; a kan hanyar zuwa Horonayim suna makoki saboda hallakawarsu. Ruwayen Nimrim sun ƙafe ciyayin kuma sun bushe; tsire-tsire duk sun ɓace babu sauran ɗanyen abu. Saboda haka dukiyar da suka tara suka kuma ajiye sun ɗauka suka ƙetare Rafin Arabim da su. Ƙugin kukansu ya kai ko’ina a iyakar Mowab; kururuwarsu ta kai har zuwa Eglayim, makokinsu ya kai har zuwa Beyer-Elim. Ruwayen Dimon sun cika da jini, amma zan yi ƙari a kan Dimon, zan kawo zaki a kan masu gudu na Mowab da kuma a kan waɗanda suka ragu a ƙasar. Ku aiko da raguna a matsayin haraji ga mai mulkin ƙasar, daga Sela a hamada, zuwa dutsen Diyar Sihiyona. Kamar tsuntsaye masu firiya da aka kora daga sheƙa, haka matan Mowab suke a kogunan Arnon. “Ku ba mu shawara, ku yanke shawara. Ku mai da inuwarku kamar dare, a tsakar rana. Ku ɓoye masu gudun hijira, kada ku bashe masu neman mafaka. Ku bar Mowabawa masu gudun hijira su zauna tare da ku; ku zama mafakarsu daga mai neman hallaka su.” Mai danniya zai zo ga ƙarshe hallaka kuma za tă daina; masu lalatar da ƙasa za su kare Da ƙauna za a kafa kursiyi; da aminci mutum zai zauna a kansa, wani daga gidan Dawuda, wani wanda ta shari’antawa yakan nuna gaskiya ya hanzarta yin adalci. Mun ji fariyar Mowab, mun ji yawan fariyarta da girmankanta, fariyarta da reninta, amma taƙamarsu ta banza ce. Saboda haka Mowabawa za su yi kuka mai zafi, za su yi kuka mai zafi tare saboda Mowab. Ku yi makoki ku kuma yi baƙin ciki saboda ƙosai da kuka riƙa ci a Kir Hareset. Gonakin Heshbon sun bushe, inabin Sibma ma haka. Masu mulkin al’ummai sun tattake inabi mafi kyau, waɗanda suka taɓa yaɗuwa zuwa Yazer suka bazu ta wajen hamada. Tohonsu sun buɗu suka kai har teku. Saboda haka na yi kuka, yadda Yazer take kuka, saboda inabin Sibma. Ya Heshbon, ya Eleyale, na cika ku da hawaye! Sowa ta murna a kanku saboda ’ya’yan itatuwanku da suka nuna da kuma girbinku sun ɓace. An ɗauke farin ciki da murna daga gonakin itatuwa masu ’ya’ya; babu wanda yake rerawa ko yake sowa a cikin gonakin inabi; babu wanda yake matsin ruwan inabi a wuraren matsi, gama na kawo ƙarshen yin sowa. Zuciyata tana makoki saboda Mowab kamar garaya, na yi baƙin ciki saboda Kir Hareset. Sa’ad Mowab ta bayyana a masujadar bisa tudu, tana gajiyar da kanta ne kawai; sa’ad da ta tafi wurin tsafinta don tă yi addu’a, babu wani amfani. Wannan ita ce maganar da Ubangiji ya riga ya yi game da Mowab. Amma yanzu Ubangiji ya ce, “Cikin shekara uku, kamar yadda bawan da aka bautar da shi bisa ga yarjejjeniya zai lissafta, haka za a mai da daraja da kuma dukan yawan mutanen Mowab abin reni, daga ɗumbun mutanenta, ’yan kaɗan ne kaɗai za su ragu, za su kuma zama marasa ƙarfi.” Abin da Allah ya faɗa game da Damaskus. “Duba, Damaskus ba za tă ƙara zama birni ba amma za tă zama tsibin juji. Za a watse a bar biranen Arower a bar wa tumaki da shanu, waɗanda za su kwanta, ba tare da wani wanda zai tsorata su ba. Birni mai katanga za tă ɓace daga Efraim, ikon sarauta kuma daga Damaskus; raguwar Aram za tă zama kamar darajar Isra’ila,” in ji Ubangiji Maɗaukaki. “A wannan rana ɗaukakar Yaƙub za tă ƙare; kitsen jikinsa zai lalace. Zai zama kamar sa’ad da mai girbi ya tara hatsin da yake tsaye ya kuma girbe hatsin da hannunsa kamar sa’ad da mutum ya yi kala kawunan hatsi a Kwarin Refayim. Duk da haka waɗansu kala za su ragu, sai ka ce sa’ad da an karkaɗe itace zaitun, aka bar ’ya’yan zaitun biyu ko uku a can ƙwanƙolin rassan, ko kuma aka bar huɗu ko biyar a rassa na gefe na itace mai ’ya’ya,” in ji Ubangiji, Allah na Isra’ila. A wannan rana mutane za su nemi Mahaliccinsu su kuma juye idanunsu ga Mai Tsarkin nan na Isra’ila. Ba za su dubi bagade ba, waɗanda suke aikin hannuwansu, ba za su kuma kula da ginshiƙan Ashera ba da kuma bagadan turaren da yatsotsinsu suka yi. A wannan rana biranensu masu ƙarfi, waɗanda suka bari saboda Isra’ilawa, za su zama kamar wuraren da aka ƙyale suka zama kufai a jeji. Za su kuma zama kango. Kun manta da Allah Mai Cetonku; ba ku tuna da Dutse, kagararku ba. Saboda haka, ko da yake kun fita ku shuka tsire-tsire mafi kyau kuka kuma shuka inabin da aka sayo daga waje, ko da yake a ranar kun shuka su, kuka sa su yi girma, da safe kuma sa’ad da kuka shuka su, kuka sa suka yi toho suka yi fure, duk da haka girbin ba zai zama kome ba a ranar cuta da zafin da ba ta da magani. Kash, ga hayaniyar al’ummai masu yawa suna hayaniya kamar rurin teku! Kash, ga fushin mutane suna ruri kamar rugugi kamar manyan ruwaye! Ko da yake mutane suna ruri kamar sukuwar raƙuman ruwa, sa’ad da ya tsawata musu za su gudu can da nisa, aka kore su kamar yayinda iska ya hura a kan tuddai, kamar tattake kuma a cikin guguwa. Da yamma, sai razana ba tsammani! Kafin safiya, duk sun ɓace! Wannan ne rabon waɗanda suka washe mu, rabon waɗanda suka yi mana ƙwace. Kaiton ƙasar da ake jin ƙarar fikafikai a bakin kogunan Kush, wadda ta aiko da jakadu ta teku cikin jiragen ruwan da aka yi da kyauro a bisa ruwa. Ku tafi, ku ’yan saƙo masu sauri, zuwa ga dogayen mutane masu sulɓin jiki, zuwa ga mutanen da ake jin tsoro a ko’ina, al’umma mai ƙarfin iko tana jawabin da ba a saba ji ba, mai ƙasar da koguna suka raba. Ku dukan mutanen duniya, ku da kuke zama a duniya, sa’ad da aka ɗaga tutar a kan duwatsu, za ku gan shi, sa’ad da kuma aka busa ƙaho, za ku ji shi. Ga abin da Ubangiji ya faɗa mini, “Zan yi shiru in kuma duba a hankali daga mazaunina, kamar ƙuna mai zafi a hasken rana, kamar girgijen raba a lokacin girbi.” Gama kafin girbi, sa’ad da furanni suka karkaɗe furanni kuma suka zama ’ya’yan inabin da suka nuna, zai faffalle rassan kuringar inabi da wuƙa, ya yanke ya kuma kwashe rassan da suka bazu. Duk za a bar su wa tsuntsayen dutse su ci da kuma namun jeji; tsuntsaye kuma za su ci rani a kansu, namun jeji kuma za su yi damina a kansu. A wannan lokaci za a kawo kyautai wa Ubangiji Maɗaukaki daga dogayen mutane masu sulɓin jiki, daga mutanen da ake jin tsoro a ko’ina, al’umma mai ƙarfin iko na jawabin da ba a saba ji ba, mai ƙasar da koguna suka raba. Za a kawo kyautai zuwa Dutsen Sihiyona, wurin da Sunan Ubangiji Maɗaukaki yake. Abin da Allah ya faɗa game da Masar, Duba, Ubangiji yana a kan girgije a sukwane yana kuwa zuwa Masar. Gumakan Masar sun firgita a gabansa, zukatan Masarawa sun karai. “Zan tā da hargitsi tsakanin mutumin Masar da mutumin Masar, ɗan’uwa zai yi gāba da ɗan’uwa maƙwabci ya yi gāba da maƙwabci, birni ya yi gāba da birni, mulki ya yi gāba da mulki. Masarawa za su karai, zan kuma sa shirye-shiryensu su zama banza; za su nemi shawarar gumaka da kuma ruhohin matattu, za su nemi shawarar mabiya da na masu duba. Zan ba da Masarawa ga ikon azzalumi shugaba, mugun sarki kuma zai yi mulki a kansu,” in ji mai girma, Ubangiji Maɗaukaki. Ruwayen kogi za su ƙafe, bakin kogi zai shanye yă kuma bushe. Wuriyoyi za su yi wari; rafuffukan Masar za su yi ta raguwa har su ƙafe. Iwa da jema za su bushe, haka ma tsire-tsire kusa da Nilu, a bakin kogi. Kowane abin da aka shuka a gefen Nilu zai bushe, iska ta kwashe su ƙaf. Masu kamun kifi za su yi nishi su kuma yi makoki, dukan waɗanda suke jefan ƙugiyoyi a Nilu; waɗanda suke jefan abin kamun kifi a ruwa abin kamun kifin za su zama marasa amfani. Waɗanda suke aiki da kaɗin auduga za su karai, masu yin lilin mai kyau za su fid da zuciya. Masu aikin tufafi ransu zai ɓace, kuma dukan masu samun albashi za su damu. Shugabannin Zowan ba kome ba ne, wawaye ke kawai; mashawarta masu hikima na Fir’auna suna ba da shawarwari marasa amfani. Yaya za ka ce wa Fir’auna, “Ni ɗaya ne cikin masu hikima, almajirin sarakuna na dā can”? Ina masu hikima suke yanzu? Bari su nuna maka su kuma sanar da abin da Ubangiji Maɗaukaki ya shirya a kan Masar. Shugabannin Zowan sun zama wawaye, an ruɗe shugabannin Memfis dutsen kan kusurwa na mutanenta su sa Masar ta kauce. Ubangiji ya sa zuba musu ruhun jiri; suka sa Masar ta yi tangaɗi cikin kome da take yi, kamar yadda mutumin da ya bugu yake tangaɗi cikin amansa. Babu abin da Masar za tă yi, kai ko wutsiya, reshen dabino ko iwa. A wannan rana Masarawa za su zama kamar mata. Za su yi rawar jiki lokacin da Ubangiji Maɗaukaki ya ɗaga hannu a kansu. Ƙasar Yahuda kuma za kawo fargaba ga Masarawa; kowanne da Yahuda ya ambace zai firgita, saboda abin da Ubangiji Maɗaukaki yake shiri a kansu. A wannan rana birane biyar a Masar za su yi yaren Kan’ana su kuma miƙa kai cikin yarjejjeniya ga Ubangiji Maɗaukaki. Za a ce da ɗayansu Birnin Hallaka. A wannan rana za a kasance da bagade ga Ubangiji a tsakiyar Masar, da kuma ginshiƙin dutse Ubangiji a iyakarta. Zai zama alama da kuma shaida ga Ubangiji Maɗaukaki a ƙasar Masar. Sa’ad da suka yi kuka ga Ubangiji saboda masu zaluntarsu, zai aiko musu mai ceto da mai kāriya, zai kuma cece su. Saboda haka Ubangiji zai sanar da kansa ga Masarawa, kuma a wannan rana za su yarda da Ubangiji. Za su yi masa sujada da hadayu da hadayun hatsi; za su yi alkawura ga Ubangiji su kuma kiyaye su. Ubangiji zai bugi Masar da annoba; zai buge su ya kuma warkar da su. Za su juyo wurin Ubangiji, zai amsa roƙonsu ya kuma warkar da su. A wannan rana za a kasance da babban hanya daga Masar zuwa Assuriya. Assuriyawa za su tafi Masar, Masarawa kuma za su tafi Assuriya. Masarawa da Assuriyawa za su yi sujada tare. A wannan rana Isra’ila za tă zama na uku, tare da Masar da Assuriya, abin albarka ga duniya. Ubangiji Maɗaukaki zai albarkace su, yana cewa, “Albarka ta tabbata ga Masar, mutanena, Assuriya aikin hannuna, da kuma Isra’ila gādona.” A shekarar da babban shugaban yaƙin da Sargon sarkin Assuriya ya aika, ya zo Ashdod ya kuma fāɗa mata ya kuma ci ta da yaƙi, a wannan lokaci Ubangiji ya yi magana ta wurin Ishaya ɗan Amoz. Ya ce masa, “Tuɓe tsummokin da kake saye da su, da kuma takalman da ka sa a ƙafafu.” Ya kuwa yi haka, yana yawo tsirara kuma ba takalma a ƙafa. Sa’an nan Ubangiji ya ce, “Kamar dai yadda bawana Ishaya ya yi ta yawo tsirara kuma ba takalmi a ƙafa shekara uku, a matsayin alama da shaida a kan Masar da Kush, haka sarkin Assuriya zai kwashe kamammun Masarawa da Kushawa tsirara kuma ba takalma a ƙafa, yaro da babba, asirinsu a tsiraice, don a kunyata Masar. Waɗanda suka dogara ga Kush suka yi taƙama da Masar za su ji tsoro su kuma sha kunya. A wannan rana mutanen da suke zama a bakin teku za su ce, ‘Dubi abin da ya faru da waɗanda muka dogara a kai, waɗanda muka gudu muka je don neman taimako da ceto daga sarkin Assuriya! Yaya za mu tsira?’ ” Abin da Allah ya faɗa game da Hamada da take kusa da Teku. Kamar guguwa mai share cikin ƙasar kudu, mai hari ya zo daga hamada, daga ƙasar mai banrazana. An nuna mini mugun wahayi, mai bashewa ya bashe, mai washewa ya washe. Elam, ki yi yaƙi! Mediya, ki yi kwanto! Zan kawo ƙarshen dukan nishe-nishen da ta jawo. Game da wannan jikina yana ciwo, zafi ya kama ni, kamar na mace mai naƙuda; na razana game da abin da na ji, na yi mamakin abin da na gani. Gabana tana ta fāɗuwa, tsoro ya sa ina rawan jiki; hasken da nake marmari ya zo da razana gare ni. Sun shirya teburori, sun shimfiɗa dardumai, sun ci, sun sha! Tashi, ku hafsoshi, sa mai a garkuwoyi! Ga abin da mai girma ya ce mini, “Tafi, ka sa mai tsaro ka kuma sa ya ba da rahoton abin da ya gani. Sa’ad da ya ga kekunan yaƙi tare da ƙungiyoyin dawakai, mahaya a kan jakuna, ko mahaya a kan raƙuma, to, fa ya zauna a faɗake, ya kintsa sosai.” Mai tsaron kuma ya yi ihu, “Kowace rana, ranka yă daɗe, nakan tsaya a hasumiyar tsaro; kowane dare nakan tsaya a wurin aikina. Duba, ga wani mutum tafe a keken yaƙin tare da ƙungiyar dawakai. Ya kuma mayar da amsa, ‘Babilon ta fāɗi, ta fāɗi! Dukan siffofin allolinta kwance a ragargaje a ƙasa!’ ” Ya mutanena, an ragargaje ku a masussuka, na faɗa muku abin da na ji daga Ubangiji Maɗaukaki, daga Allah na Isra’ila. Abin da Allah ya faɗa game da Duma, Wani ya kira ni daga Seyir, “Mai tsaro, me ya rage a daren? Mai tsaro, me ya rage a daren?” Mai tsaro ya amsa, “Safiya ta gabato, haka kuma dare. In za ka yi tambaya, to, yi tambaya; sai ka sāke zuwa, ka tambaya.” Abin da Allah ya faɗa game da Arabiya. Ku ayarin Dedanawa, ku da kuka sauka a jejin Arabiya, ku kawo ruwa don ƙishirwa; ku da kuke zama a Tema, ku kawo abinci don masu gudun hijira. Sun gudu daga takobi, daga takobin da aka janye, daga bakan da aka tanƙware da kuma daga zafin yaƙi. Ga abin da mai girma ya ce mini, “Cikin shekara ɗaya, kamar yadda bawan da aka bautar da shi bisa ga yarjejjeniya zai lissafta, dukan sojojin Kedar za su zo ga ƙarshe. Waɗanda suka yi rai na maharba, jarumawan Kedar, za su zama kaɗan.” Ubangiji, Allah na Isra’ila, ya faɗa. Abin da Allah ya faɗa game da Kwarin Wahayi. Mene ne ya dame ku a yanzu, da dukanku kuka hau kan rufin gidaje. Ya kai gari cike da hayaniya, Ya ke birnin tashin hankali da alkarya mai murna? Mutanenki ba su mutu ta wurin takobi ba, ba kuwa za su mutu a yaƙi ba. Dukan shugabanninki sun gudu gaba ɗaya; an kama su ba tare da an yi amfani da baka ba. Dukanku da aka kama an kwashe ku ɗaurarru gaba ɗaya, kun gudu tun abokin gāba yana da nisa. Saboda haka na ce, “Ƙyale ni kurum; bari in yi kuka mai zafi. Kada ka yi ƙoƙarin ta’azantar da ni a kan hallakar mutanena.” Ubangiji, Ubangiji Maɗaukaki, yana da ranar giggicewa da tattakewa da banrazana a cikin Kwarin Wahayi, ranar ragargazawar katanga da ta yin kuka ga duwatsu. Elam ya ɗauki kwari da baka, tare da mahayan kekunan yaƙinta da dawakai; Kir ta buɗe garkuwoyi. Kwarurukanku mafi kyau sun cika da kekunan yaƙi, an kuma tsai da mahayan dawakai a ƙofofin birni. An rurrushe kāriyar Yahuda, a ranan nan kuwa kun yi la’akari da makamai a cikin Fadan Kurmi; kuka ga cewa Birnin Dawuda tana da wuraren kāriya masu yawa da suka tsattsage; kuka tattara ruwa a Tafkin Ƙasa. Kuka ƙirga gine-gine a Urushalima kuka kuma rurrushe gidaje don ku ƙarfafa katanga. Kuka gina matarar ruwa tsakanin katanga biyu saboda ruwan Tsohon Tafki, amma ba ku yi la’akari da Wannan da ya yi su ba, ko ku kula da Wannan da ya shirya shi tuntuni. Ubangiji, Ubangiji Maɗaukaki ya kira ku a wannan rana don ku yi kuka ku yi ihu, don ku aske gashinku ku kuma sa tsummoki. Amma duba, sai ga shi kuna farin ciki kuna kuma murna, kuna yankan shanu kuna kashe tumaki, kuna cin nama kuna kuma shan ruwan inabi! Kuna cewa, “Bari mu ci mu kuma sha, gama gobe za mu mutu!” Ubangiji Maɗaukaki ya bayyana wannan a kunnena cewa, “Har ranar mutuwarka ba za a yi kafarar wannan zunubi ba,” in ji mai girma Ubangiji Maɗaukaki. Ga abin da Ubangiji, Ubangiji Maɗaukaki, ya faɗa, “Je, ka faɗa wa wannan mai hidima, Shebna, sarkin fada. Mene ne kake yi a nan kuma wa ya ba ka izini ka haƙa kabari wa kanka a nan, kana fafe kabarinka a bisa kana sassaƙa wurin hutunka a dutse? “Ka yi hankali, Ubangiji yana shirin ya kama ka da ƙarfi ya kuma ɗauke ka, ya kai mai ƙarfi. Zai dunƙule ka kamar ƙwallo ya jefa ka a cikin ƙasa mai girma. A can za ka mutu a can kuma kekunan yaƙinka masu daraja za su kasance, abin kunya kake ga gidan maigidanka! Zan tumɓuke ka daga makaminka, za a kuma kore ka daga matsayinka. “A wannan rana zan kira bawana, Eliyakim ɗan Hilkiya. Zan rufe shi da rigarka in kuma yi masa ɗamara in miƙa masa ikonka. Zai zama mahaifi ga waɗanda suke zama a Urushalima da kuma gidan Yahuda. Zan sa mabuɗin gidan Dawuda a kafaɗarsa; abin da ya buɗe ba mai rufewa, kuma abin da ya rufe ba mai buɗewa. Zan kafa shi kamar turke a tsayayyen wuri; zai zama mazaunin daraja domin gidan mahaifinsa. Dukan ɗaukakar iyalinsa za tă rataya a kansa daga ’ya’yansa da zuriyarsa har zuwa dukan ƙananan kayan aikinsa, wato, daga kwanoni har zuwa tuluna. “A ranan nan, in ji Ubangiji Maɗaukaki, turken da aka kafa a tsayayyen wuri zai sumɓule; za a sare shi ya fāɗi, za a kuma datse nauyin da yake rataya a kansa.” Ni Ubangiji na faɗa. Abin da Allah ya faɗa game da Taya. Ku yi kuka mai zafi, ya jiragen ruwan Tarshish! Gama an hallaka Taya aka kuma bar su babu gida ko tasha. Daga ƙasar Saifurus magana ta zo musu. Ku yi shiru, ku mutanen tsibiri da ku ’yan kasuwan Sidon waɗanda masu ciniki a teku suka azurta. A manyan ruwaye hatsin Shihor suka iso; girbin Nilu ne kuɗin shiga na Taya ta kuma zama kasuwar al’ummai. Ki ji kunya, ya ke Sidon, da ke kuma, kagarar teku, gama teku ya yi magana ya ce, “Ban taɓa naƙuda ba balle in haifi ’ya’ya; ban taɓa goyon ’ya’ya maza ba balle in reno ’ya’ya mata.” Sa’ad da magana ta kai Masar, za su razana da jin labari daga Taya. Ku haye zuwa Tarshish; ku yi kuka mai zafi, ku mutanen tsibiri. Wannan ce birnin murnanku, birnin nan na tun dā wadda ƙafafunta suka kai ta zama a ƙasashe masu nesa? Wane ne ya ƙulla wannan a kan Taya ita da take ba da rawanin sarauta, wadda ’yan kasuwanta sarakuna ne, wadda masu cinikinta sanannu ne a duniya? Ubangiji Maɗaukaki ya ƙulla shi, don yă kawo ƙarshen girman kan dukan darajarta ya kuma ƙasƙantar da dukan waɗanda suke sanannu a duniya. Ki nome ƙasarki har zuwa wajen Nilu, Ya Diyar Tarshish, gama ba ki da tashan jirgin ruwa kuma. Ubangiji ya miƙa hannunsa a bisa teku ya kuma sa mulkokinsa suka yi rawar jiki. Ya ba da umarni game da Funisiya cewa a hallaka kagararta. Ya ce, “Ba za ki ƙara yin murna ba, Ya ke Budurwa Diyar Sidon, yanzu da kike ragargajiya! “Tashi, ki ƙetare zuwa Saifurus; a can ɗin ma ba za ki huta ba.” Dubi ƙasar Babiloniyawa, wannan mutanen da yanzu ba su da wani amfani! Assuriyawa sun mai da ita wurin zaman halittun hamada; sun gina hasumiyoyin kwanto, suka ragargaza kagararta ƙaf suka mai da ita kango. Ku yi kuka mai zafi, ku jiragen ruwan Tarshish; an rurrushe kagararku! A wannan lokaci za a manta da Taya har shekaru saba’in, tsawon rayuwar sarki. Amma a ƙarshen waɗannan shekaru saba’in, zai zama wa Taya kamar yadda yake a waƙar karuwa cewa, “Ɗauki garaya, ki ratsa birni, Ya ke karuwar da aka manta da ita; kaɗa garaya da kyau, ki rera waƙoƙi masu yawa, saboda a tuna da ke.” A ƙarshen shekaru saba’in, Ubangiji zai magance Taya. Za tă koma ga aikinta na karuwanci za tă kuma yi kasuwancinta da dukan mulkokin duniya. Duk da haka za a keɓe ribarta da kuɗin shigarta wa Ubangiji; ba za a yi ajiyarsu ko a ɓoye su. Ribarta za tă tafi ga waɗanda suke yi wa Ubangiji sujada, don su sami yalwataccen abinci da tufafi masu kyau. Duba, Ubangiji zai wofinta duniya ya kuma yi kaca-kaca da ita; zai ɓata fuskarta ya watsar da mazaunanta, zai zama abu ɗaya ga firist kamar yadda yake ga mutane, ga maigida kamar yadda yake ga bawa, ga uwargijiya kamar yadda yake ga baiwa, ga mai sayarwa kamar yadda yake ga mai saya, ga mai karɓan rance kamar yadda yake ga mai ba da rance, ga mai karɓan bashi kamar yadda yake ga mai ba da bashi. Za a wofinta duniya ƙaƙaf a kuma washe ta sarai. Ubangiji ne ya faɗa haka. Duniya ta bushe ta kuma yanƙwane, duniya tana shan azaba ta kuma raunana, masu daraja na duniya suna shan azaba. Duniya ta ƙazantu ta wurin mutanenta sun ƙi yin biyayya da dokoki, sun keta farillai suka kuma karya madawwamin alkawari. Saboda haka la’ana za tă auko wa duniya; dole mutanenta su ɗauki hakkin laifinsu. Saboda haka aka ƙone mazaunan duniya, kuma kaɗan ne kurum suka rage. Sabon ruwan inabi ya bushe kuringar inabi kuma sun yanƙwane; dukan masu farin ciki suna nishi. Kaɗe-kaɗen garayu sun yi shiru, surutun masu murna ya daina, garayan farin ciki ya yi shiru. Babu sauran shan ruwan inabi suna rera waƙa; barasa ya zama da ɗaci ga masu shanta. Birnin da aka birkice ta zama kango; an kulle ƙofar shiga kowane gida. A tituna suna kukan neman ruwan inabi; dukan farin ciki ya dawo baƙin ciki, an hana dukan kaɗe-kaɗe a duniya. An bar birnin kango, aka yi kaca-kaca da ƙofofinta. Haka zai zama a duniya da kuma a cikin al’ummai, kamar sa’ad da akan karkaɗe itacen zaitun, ko kuma kamar sa’ad da ake barin kala bayan an girbe inabi. Sun daga muryoyinsu, sun yi sowa ta farin ciki; daga yamma sun furta darajar Ubangiji. Saboda haka a gabas sun ɗaukaka Ubangiji, a ɗaukaka sunan Ubangiji, Allah na Isra’ila, a cikin tsibiran teku. Daga iyakokin duniya mun ji waƙoƙi, “Ɗaukaka ga Mai Adalcin nan.” Amma na ce, “Na lalace, na lalace! Kaitona! Munafukai sun ci amana! Da munafunci munafukai sun ci amana!” Razana da rami da tarko suna jiranku, Ya mutanen duniya. Duk wanda ya yi ƙoƙarin tserewa daga ƙarar razana zai fāɗa cikin rami; wanda kuma ya tsere daga rami za a kama shi a tarko. An buɗe ƙofofin ambaliyar ruwan sama, harsashen ginin duniya suna rawa. An tsage duniya, duniya ta farfashe ta wage, an girgiza duniya ƙwarai. Duniya tana tangaɗi kamar mashayi, tana lilo kamar rumfa a cikin iska; laifin tayarwarta ya yi nauyi sosai har ta fāɗi ba kuwa za tă ƙara tashi ba. A wannan rana Ubangiji zai hukunta ikokin da suke cikin sama da kuma sarakunan da suke a duniya. Za a tattara su tare kamar ɗaurarru a kurkuku; za a rufe su a kurkuku a kuma hukunta su bayan kwanaki masu yawa. Sa’an nan wata zai ruɗe, rana ta ji kunya; gama Ubangiji Maɗaukaki zai yi mulki a kan Dutsen Sihiyona da kuma a cikin Urushalima, da kuma a gaban dattawanta, da ɗaukaka. Ya Ubangiji, kai ne Allahna; zan ɗaukaka ka in kuma yabi sunanka, gama cikin cikakken aminci ka yi abubuwa masu banmamaki, abubuwan da aka shirya tun da. Ka mai da birnin tsibin tarkace, ka lalatar da gari mai katanga, birnin baƙi mai ƙarfi, ta ɓace; ba za a ƙara gina ta ba. Saboda haka mutane masu ƙarfi za su girmama ka; biranen mugayen al’ummai za su ji tsoronka. Kai ka zama mafakar matalauta, mafaka don mabukata cikin damuwa, wurin ɓuya daga hadari, inuwa kuma daga zafin rana. Gama numfashin mugaye yana kamar da hadari mai bugun bango kuma kamar zafin hamada. Ka kwantar da hayaniyar baƙi; kamar yadda inuwar girgije kan rage zafin rana, haka ake kwantar da waƙar mugaye. A kan wannan dutse Ubangiji Maɗaukaki zai shirya bikin abinci mai kyau don dukan mutane, liyafar ajiyayyen ruwan inabi da nama mafi kyau da ruwan inabi mafi kyau. A wannan dutse zai kawar da baƙin cikin da ya lulluɓe dukan mutane, ƙyallen da ya rufe dukan al’ummai; zai haɗiye mutuwa har abada. Ubangiji Mai Iko Duka zai share hawaye daga dukan fuskoki; zai kawar da kunyar mutanensa daga dukan duniya. Ubangiji ne ya faɗa. A wannan rana za su ce, “Tabbatacce wannan shi ne Allah; mun dogara a gare shi, ya kuma cece mu. Wannan shi ne Ubangiji, mun dogara a gare shi; bari mu yi murna mu kuma yi farin ciki a cikin cetonsa.” Hannun Ubangiji zai zauna a kan wannan dutse; amma za a tattake Mowab a ƙarƙashinsa kamar yadda ake tattaka kara a cikin taki. Za su buɗe hannuwansa a cikinsa, yadda mai iyo kan buɗe hannuwansa don yă yi iyo. Allah ya ƙasƙantar da girmankansu duk da wayon hannuwansu. Zai rurrushe manyan katangar kagaru ya kuma ƙasƙantar da su; zai rushe su har ƙasa, su zama ƙura. A wannan rana za a rera wannan waƙa a ƙasar Yahuda. Muna da birni mai ƙarfi; Allah yake ceton katanga da kuma kagarunta. A buɗe ƙofofi saboda al’umma mai adalci ta shiga, al’ummar da mai aminci. Za ka kiyaye shi da cikakken salama shi wanda ya kafa zuciyarsa gare ka, domin ya dogara a gare ka. Ku dogara ga Ubangiji, gama shi Ubangiji, ne madawwamin Dutse. Yakan ƙasƙantar da waɗanda suke zama a bisa ya kawar da birni mai alfarma ƙasa; ya rusa ta har ƙasa ya jefar da ita cikin ƙura. Ƙafafu sukan tattake ta, ƙafafu waɗanda aka zalunta, wato, sawun matalauta. Hanyar masu adalci sumul take; Ya Mai Aikata Gaskiya, ka sa hanyar masu adalci ta yi sumul. I, Ubangiji, cikin tafiya a hanyar dokokinka, muna sa zuciya gare ka; sunanka da tunani a kanka su ne marmarin zukatanmu. Raina yana marmarinka da dare; da safe kuma raina yana son ganinka. Sa’ad da hukunce-hukuncenka suka sauko duniya, mutanen duniya kan koyi adalci. Ko da yake akan nuna wa mugaye alheri, ba sa koyi adalci; har ma a ƙasar masu aikata gaskiya sukan ci gaba da aikata mugunta ba sa ganin girmar darajar Ubangiji. Ya Ubangiji an ɗaga hannunka sama, amma ba sa ganinsa. Bari su ga himmarka don mutanenka su kuma sha kunya; bari wutar da aka ajiye don abokan gābanka ta cinye su. Ubangiji ka kafa salama dominmu; duk abin da muka iya yi kai ne ka yi mana. Ya Ubangiji, Allahnmu, waɗansu iyayengiji ban da kai sun yi mulki a kanmu, amma sunanka kaɗai muka girmama. Yanzu duk sun mutu, ba za su ƙara rayuwa ba; waɗannan ruhohin da suka rasu ba za su tashi ba. Ka hukunta su ka kuma kawo su ga hallaka; ka sa ba za a ƙara tunawa da su ba. Ka fadada al’umma, ya Ubangiji; ka fadada al’umma. Ka samo wa kanka ɗaukaka; ka fadada dukan iyakokin ƙasar. Ubangiji, sun zo gare ka a cikin damuwarsu; sa’ad da ka hore su, da ƙyar suna iya yin addu’a. Kamar mace mai ciki da take gab da haihuwa takan yi ta murɗawa tana kuka saboda zafi, haka muka kasance a gabanka, ya Ubangiji. Muna da ciki, mun yi ta murɗewa saboda zafi, amma mun haifi iska. Ba mu kawo ceto ga duniya ba; ba mu haifi mutanen duniya ba. Amma matattunka za su rayu; jikunansu za su tashi. Ku da kuke zama a ƙura, ku farka ku kuma yi sowa don farin ciki. Raɓarka kamar raɓar safiya ce; duniya za tă haifi matattunta. Ku tafi, mutanena, ku shiga ɗakunanku ku kuma kulle ƙofofi; ku ɓoye kanku na ɗan lokaci sai ya huce fushinsa. Duba, Ubangiji yana fitowa daga mazauninsa don yă hukunta mutanen duniya saboda zunubansu. Duniya za tă bayyana zub da jinin da aka yi a kanta; ba za tă ƙara ɓoye waɗanda aka kashe a cikinta ba. A wannan rana, Ubangiji zai yi hukunci da takobi, takobinsa mai tsanani, mai ƙarfi da kuma mai muguwar ɓarna, zai hukunta dodon ruwa macijin nan da ya kanannaɗe, dodon ruwa macijin nan mai murɗewa; zai kashe dodon nan na teku. A wannan rana, “Ku rera game da gonar inabi mai ba da ’ya’ya ku ce Ni, Ubangiji na lura da ita; na yi ta yin mata banruwa. Na yi tsaronta dare da rana don kada wani yă yi mata ɓarna. Ban yi fushi ba. Da a ce ƙayayyuwa da sarƙaƙƙiya ne suke kalubalanta na mana! Zan fita in yi yaƙi da su; da na sa musu wuta duka. Ko kuma bari su zo wurina don mafaka; bari su yi sulhu da ni, I, bari su yi sulhu da ni.” A kwanaki masu zuwa Yaƙub zai yi saiwa, Isra’ila zai yi toho ya kuma yi fure ya cika dukan duniya da ’ya’ya. Ubangiji ya buge shi kamar yadda ya bugi waɗanda suka buge shi? An kashe shi kamar yadda aka kashe waɗanda suka kashe shi? Ta wurin yaƙi da zaman bauta ka hukunta shi, da tsananin tsawa kuma ka kore shi, kamar a ranar da iskar gabas ta hura. A ta haka fa, za a yi kafarar laifin Yaƙub, wannan kuma zai zama cikakken amfanin kau da zunubinsa. Sa’ad da ya niƙa duwatsun bagade suka zama kamar allin da aka farfashe kucu-kucu, har ba sauran ginshiƙan Ashera ko bagadan ƙona turare da za a bari a tsaye. Birni mai katanga ya zama kufai, yasasshen mazauni, an yashe shi kamar hamada; a can ’yan maruƙa suke kiwo, a can suke kwance; sun kakkaɓe rassanta ƙaf. Sa’ad da rassanta suka bushe, sai su kakkarye su mata kuma su zo su yi itacen wuta da su. Gama mutane ne marar azanci; saboda haka Mahaliccinsu bai ji tausayinsu ba, Mahaliccinsu bai nuna musu jinƙai ba. A wannan rana Ubangiji zai tankaɗe daga Yuferites mai gudu zuwa Rafin Masar, ku kuma, ya Isra’ilawa, za a tattara ku ɗaya-ɗaya. Kuma a wannan rana zai busa ƙaho mai kāra sosai. Waɗanda suke mutuwa a Assuriya da kuma waɗanda aka kai zaman bauta a Masar za su zo su kuma yi wa Ubangiji sujada a dutse mai tsarki a Urushalima. Kaito ga wannan rawani, girman kai na mashayan Efraim, ga fure mai yanƙwanewa, darajar kyansa, da aka sa a kan kwari mai ba da amfani, ga birnin nan, wadda take girman kan waɗanda aka ƙasƙantar da ruwan inabinsu! Duba, Ubangiji yana da wanda yake da iko da kuma ƙarfi. Kamar dutsen ƙanƙara da kuma iska mai ɓarna, kamar kwararowar ruwa da rigyawa mai kirmewa, zai jefa shi har ƙasa da ƙarfi. Za a tattaka wannan rawani, girman kai na mashayan Efraim da ƙafa. Wannan fure mai yanƙwanewa, darajarar kyansa, da aka sa a kan kwari mai ba da amfani, zai zama kamar ’ya’yan ɓaure, nunan fari, da zarar wani ya gani ya kuma tsinka, zai haɗiye shi. A wannan rana Ubangiji Maɗaukaki zai zama rawani mai daraja kyakkyawan rawani wa mutanensa da suka ragu. Zai zama ruhun adalci gare shi wanda yake zaune a kujerar shari’a, wurin samun ƙarfi ga waɗanda suka kori abokan gāban da suka fāɗa musu da yaƙi a ƙofofi. Da waɗannan kuma masu tangaɗi saboda sun sha ruwan inabi suke jiri don sun sha barasa Firistoci da annabawa suna tangaɗi saboda sun sha barasa sun kuma yi tatur da ruwan inabi; suna jiri saboda sun sha barasa, suna tangaɗi sa’ad da suke ganin wahayi, suna tuntuɓe sa’ad da suke ba da shawara. Duk amai ya rufe teburori kuma babu wani wurin da ba a ɓata ba. “Wane ne yake so ya koyar? Ga wa yake bayyana saƙonsa? Ga yaran da aka yaye, ga waɗanda ba a daɗe da yayewa ba ne? Gama haka yake. Yi ka kuma yi, yi ka kuma yi, mulki a kan mulki, mulki a kan mulki; nan kaɗan, can kaɗan.” To da kyau, da leɓunan baƙi da ku harsunan da ba sani ba Allah zai yi magana da wannan mutane, waɗanda zai ce, “Wannan shi ne wurin hutu, bari waɗanda suka gaji su huta”; da kuma, “Wannan shi ne wurin wartsakewa” amma sun ƙi su saurara. Saboda haka fa, maganar Ubangiji gare su za tă zama, Yi ka kuma yi, yi ka kuma yi, mulki akan mulki, mulki a kan mulki; nan kaɗan, can kaɗan, domin su tafi su kuma fāɗi da baya, su ji rauni a kuma kama su da tarko, a kai su zaman bauta. Saboda haka ku saurari maganar Ubangiji, ku masu ba’a ku da kuke mulkin wannan mutane a Urushalima. Kuna fariya cewa, “Mun yi alkawari da mutuwa, mun kuma yi yarjejjeniya da kabari. Sa’ad da zafi ya ratsa, ba zai taɓa mu ba, gama mun mai da ƙarya mafakarmu ruɗu kuma wurin ɓuyanmu.” Saboda haka ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka ya ce, “Duba, na kafa dutse a Sihiyona, dutsen da aka gwada, dutsen kusurwa mai daraja don tabbataccen tushe; wanda ya dogara gare shi ba zai taɓa shan kunya ba. Zan mai da gaskiya igiyar gwaji adalci kuma ɗan katakon gwajin ginin; ƙanƙara za tă share mafakarku, ƙarya, da ruwa kuma za su mamaye maɓuyanku. Za a soke alkawarinku da mutuwa; yarjejjeniyarku da kabari ba zai zaunu ba. Sa’ad da zafi mai ɓarna ya ratsa, zai hallaka ku. A duk sa’ad da ya zo; ko da safiya, ko dare ko kuma da rana, zai yi ta ratsawa yana kwasanku.” Za ku zama kamar mutumin da ya zama abin karin magana, wanda ya yi ƙoƙari yă kwanta a gajeren gado, yă kuma rufa da ɗan siririn bargo. Ubangiji zai tashi kamar yadda ya yi a Dutsen Feratsim, zai tā da kansa kamar a Kwarin Gibeyon don yă aikata aikinsa, aikinsa da ba a saba gani ba, yă kuma yi aikinsa, baƙon aikinsa. Yanzu ku daina ba’arku, in ba haka ba sarƙoƙinku za su ƙara nauyi; Ubangiji, Ubangiji Maɗaukaki, ya faɗa mini game da hallakar da aka ƙaddara a kan dukan ƙasar. Ku saurara ku kuma ji muryata; ku kasa kunne ku kuma ji abin da na faɗa. Sa’ad da manomi ya yi noma don shuki, yakan ci gaba da noma ne? Yakan ci gaba da sara yana yin kunyoyi a ƙasa ne? Sa’ad da ya shirya wuri da kyau, ba yakan shuka kanumfari ya kuma yayyafa ɗaɗɗoya ba? Ba yakan shuka alkama a kunyoyinsa sha’ir a kunyoyinsa, tamba kuma a filinsa ba? Allahnsa ya umarce shi ya kuma koya masa hanyar da take daidai. Ba a bugan kanumfari da ƙaton sanda ko a yi ta jujjuye ƙafar keke a kan ɗaɗɗoya; akan buga kanumfari da siririn sanda ɗaɗɗoya kuma da tsumagiya. Dole a niƙa hatsi don a yi burodi; saboda haka mutum ba zai yi ta bugun alkama, har yă ɓata tsabar ba. Ya san yadda zai sussuke alkamarsa, ba tare da ya ɓata tsabarta ba. Dukan wannan hikimar takan zo daga Ubangiji Maɗaukaki ne, shi da yake mashawarci mai banmamaki, mafifici kuma cikin hikima. Kaitonki, Ariyel, Ariyel birnin da Dawuda ya zauna! Ƙara shekara ga shekara a kuma bar shagulgulanki su yi ta kewayewa. Duk da haka zan yi wa Ariyel kwanto za tă kuma yi kuka da makoki, za tă zama mini kamar bagaden jini. Zan kafa sansani kewaye da ke duka; zan kewaye ki da hasumiyoyi in tasar miki da ayyukan kwantona na yaƙi. Za a ƙasƙantar da ke, za ki ƙi yin magana daga ƙasa; maganarki za tă yi ƙasa-ƙasa daga ƙura. Muryarki za tă zama kamar fatalwa daga ƙasa; daga ƙura maganarki zai fito ƙasa-ƙasa. Amma abokan gābanki masu yawa za su zama kamar ƙura mai laushi, sojojinsu masu firgitarwa za su yi ta tashi kamar yayin da iska ta hura. Farat ɗaya, cikin ɗan lokaci, Ubangiji Maɗaukaki zai zo da tsawa da rawar ƙasa da ƙara mai girma, da hadarin iska da guguwa da harshe na wuta mai ci. Sa’an nan sojojin dukan al’umman da suka yi yaƙi da Ariyel, da suka fāɗa mata da kagararta suka kuma yi mata kwanto, za su zama kamar yadda yake da mafarki, wahayi da dare, kamar sa’ad da mai yunwa yana mafarki cewa yana cin abinci, amma sai ya farka, yunwan tana nan; kamar sa’ad da mai ƙishirwa yana mafarki cewa yana shan ruwa, amma sai ya farka yana suma, da ƙishinsa. Haka zai zama da sojoji na dukan al’ummai da suka yi yaƙi da Dutsen Sihiyona. Ku firgita ku kuma yi mamaki, ku makance kanku ku kuma zama a makance; ku bugu, amma ba da ruwan inabi ba, ku yi tangaɗi, amma ba daga barasa ba. Ubangiji ya kawo muku barci mai nauyi, Ya rufe idanunku (annabawa); ya rufe kawunanku (masu duba). Gare ku duk wannan wahayi ba kome ba ne sai dai maganganun da aka rufe a cikin littafi. In kuma kun ba da littafin ga wani wanda zai iya karanta, kuka kuma ce masa, “Karanta wannan, muna roƙonka,” zai amsa ya ce, “Ba zan iya ba; an rufe shi.” Ko kuwa in kun ba da littafin ga wani wanda ba zai iya karantawa ba, kuka kuma ce, “Karanta wannan, muna roƙonka,” zai amsa ya ce, “Ban iya karatu ba.” Ubangiji ya ce, “Waɗannan mutane sun zo kusa da ni da bakinsu suka kuma girmama ni da leɓunansu, amma zukatansu suna nesa daga gare ni. Sujadar da suke mini cike take da dokokin da mutane suka koyar. Saboda haka zan firgita waɗannan mutane sau ɗaya da abubuwan banmamaki a kan abubuwan banmamaki; hikimar masu hikima za tă lalace, azancin masu azanci zai ɓace.” Kaiton waɗanda suke zuwa manyan zurfafa don su ɓoye shirye-shiryensu daga Ubangiji, waɗanda suke aikinsu cikin duhu su yi tunani, “Wa yake ganinmu? Wa zai sani?” Kuna birkitar abubuwa, sai ka ce an mayar da mai ginin tukwane ya zama yumɓu! Abin da aka yi zai ce wa wanda ya yi shi, “Ba shi ne ya yi ni ba”? Tukunya za tă iya ce wa mai ginin tukwane, “Ba ka san kome ba”? Cikin ɗan lokaci, za a mai da Lebanon gona mai taƙi kuma gona mai taƙi za tă zama kamar kurmi? A wannan rana kurame za su ji maganganun littafi, daga duruduru da duhu kuma idanun makafi za su gani. Masu tawali’u za su sāke yin farin ciki a cikin Ubangiji; mabukata za su yi farin ciki cikin Mai Tsarkin nan na Isra’ila. Masu zalunci za su ƙare, masu ba’a za su ɓace, kuma dukan waɗanda suke da ido don mugunta za su hallaka, waɗanda ta magana kawai sukan mai da mutum mai laifi, waɗanda suke kafa tarko wa mai ba da kāriya a ɗakin shari’a da shaidar ƙarya kuma su hana marar laifi samun shari’ar adalci. Saboda haka ga abin da Ubangiji wanda ya fanshi Ibrahim, ya ce wa gidan Yaƙub, “Ba za a ƙara kunyata Yaƙub ba; fuskokinsu kuma ba za su ƙara yanƙwanewa ba. Sa’ad da suka ga ’ya’yansu a tsakiyarsu, aikin hannuwansu, za su kiyaye sunana da tsarki; za su san tsarkin Mai Tsarkin nan na Yaƙub, za su kuma ji tsoron Allah na Isra’ila. Su da suke marasa azanci a ruhu za su sami fahimtar; waɗanda suke gunaguni za su yarda da koyarwa.” “Kaiton ’ya’ya masu tayarwa,” in ji Ubangiji, “ga waɗanda suke ƙulle-ƙullen da ba nawa ba, suna yin yarjejjeniya, amma ba ta Ruhuna ba, suna jibga zunubi a kan zunubi; waɗanda suka gangara zuwa Masar ba tare da sun nemi shawarata; waɗanda suke neman taimakon kāriyar Fir’auna, don neman inuwar mafakar Masar. Amma kāriyar Fir’auna za tă zama muku abin kunya, inuwar Masar za tă jawo muku kunya. Ko da yake suna da shugabanni a Zowan kuma jakadunsu sun iso Hanes, kowa zai sha kunya saboda mutanen da ba su da amfani gare su, waɗanda ba sa taimako ko amfani, sai dai jawo kunya da da-na-sani.” Allah ya faɗa game da dabbobin Negeb cewa, Ta cikin ƙasa mai wahala da mai hatsari inda zakoki da zakanya, inda macizai masu dafi da macizai masu tashi sama suke, jakadu na ɗaukan arzikinsu a kan jakuna, dukiyarsu a kan raƙuma, zuwa ƙasan nan marar riba, zuwa Masar, wadda taimakonta marar amfani ne. Saboda haka na yi mata laƙabi Rahab Marar Yin Kome. Tafi yanzu, ka rubuta musu a kan allo, ka rubuta shi a kan littafi, cewa kwanaki suna zuwa zai zama madawwamin shaida. Waɗannan mutane masu tawaye, ’ya’ya masu ruɗu, ’ya’yan da ba sa niyya su saurara ga umarnan Ubangiji. Sukan ce wa masu gani, “Kada ku ƙara ganin wahayi!” Ga annabawa kuwa sukan ce, “Kada ku ƙara ba mu wahayin abin da yake daidai! Faɗa mana abubuwan da muke so mu ji ne kawai, ku yi annabcin abin da zai ruɗe mu. Ku bar wannan hanya, ku tashi daga wannan hanya, ku kuma daina kalubalantarmu da Mai Tsarkin nan na Isra’ila!” Saboda haka, ga abin da Mai Tsarkin nan na Isra’ila yake cewa, “Saboda haka kun ƙi wannan saƙo, kuka dogara ga aikin kama-karya kuka kuma dogara ga yin ruɗu, wannan zunubi zai zama muku kamar bango mai tsayi, tsagagge da yake kuma fāɗuwa, da zai rushe nan da nan, ba tsammani. Zai rushe kucu-kucu kamar tukunyar yumɓu, ya ragargaje ƙaf har cikin gutsattsarinsa ba za a sami ko ɗan katanga don ɗiba garwashin wuta ko a ɗiba ruwa daga tanki ba.” Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka, Mai Tsarkin nan na Isra’ila ya faɗa, “Cikin tuba da hutu ne kaɗai cetonku yake, cikin shiru da dogara gare ni ne za ku sami ƙarfinku, amma ba za ku sami ko ɗaya a cikinsu ba. Kun ce, ‘A’a, za mu gudu a kan dawakai.’ Saboda haka za ku gudu! Kun ce, ‘Za mu hau dawakai masu sauri mu gudu.’ Saboda haka masu fafararku za su fi ku gudu! Dubu za su gudu don barazanar mutum guda; da jin barazanar mutane biyar dukanku za ku yi ta gudu sai an bar ku kamar sandar tuta a kan dutse, kamar tuta a kan tudu.” Duk da haka Ubangiji yana marmari ya yi muku alheri; ya tashi don yă nuna muku jinƙai. Gama Ubangiji Allah ne mai aikata gaskiya. Masu albarka ne dukanku waɗanda suke dogara gare shi! Ya mutanen Sihiyona, waɗanda suke zama a Urushalima, ba za ku ƙara kuka ba. Zai zama mai alheri sa’ad da kuka yi kukan neman taimako! Da zarar ya ji, zai amsa muku. Ko da yake Ubangiji yakan ba da abincin azaba da ruwan wahala, ba za a ƙara ɓoye malamanku ba; da idanunku za ku gan su. Ko kun juye dama ko hagu, kunnuwanku za su ji murya a bayanku tana cewa, “Ga hanya; ku yi tafiya a kai.” Sa’an nan za ku ƙazantar da gumakanku da kuka dalaye da zinariya; za ku zubar da su kamar rigar al’adar mace ku kuma ce musu, “Ku ɓace mana da gani!” Zai kuma aiko muku da ruwan sama don shuki a ƙasa, kuma abincin da zai fito daga gona zai zama mai albarka da kuma mai yawa. A wannan rana shanu za su yi kiwo a wadatacciyar makiyaya. Shanunku da jakunanku da suke huɗar gonakinku za su ci harawa mafi kyau, wanda an sheƙe shi da babban cokali mai yatsu da kuma babban cokali. A ranar babban kisa, sa’ad da hasumiyoyi za su fāɗi, rafuffukan ruwa za su malalo a kan kowane dutse da kowane tudu mai tsawo. Wata zai yi haske kamar rana, kuma hasken rana zai ma yi sau bakwai na haskenta, kamar hasken cikakku ranaku bakwai, sa’ad da Ubangiji zai ɗaura raunukan mutanensa ya kuma warkar da raunukan da ya yi musu. Duba, Sunan Ubangiji yana zuwa daga nesa, tare da fushi mai ƙuna da kuma baƙin hayaƙi; leɓunansa sun cika da fushi, harshensa kuma wuta ce mai cinyewa. Numfashinsa kamar raƙuman ruwa masu gudu yana tashi har zuwa wuya. Yakan tankaɗe al’ummai cikin lariyar hallaka; yakan sa a muƙamuƙan mutane linzamin da zai jagorance su su kauce. Za ku kuma rera kamar a daren da kuke shagalin biki mai tsarki; zukatanku za su yi farin ciki kamar sa’ad da mutane sukan haura da busa zuwa dutsen Ubangiji, zuwa Dutse na Isra’ila. Ubangiji zai sa mutane su ji muryarsa mai daraja ya kuma sa su ga hannunsa na saukowa tare da fushi mai ƙuna da kuma wuta mai cinyewa, gizagizai za su ɓarke, za a yi hadarin tsawa da ƙanƙara. Muryar Ubangiji za tă firgita Assuriya da sandar mulkinsa zai kashe su. Kowane bugun da Ubangiji zai yi musu da bulalarsa na hukunci zai zama kiɗi ga ganguna da garaya, yayinda yake yaƙi da su da naushin hannunsa. An riga an shirya wurin ƙonawa; an shirya shi saboda sarki. An haƙa ramin wutarsa da zurfi da kuma fāɗi, da isashen wuta da itacen wuta; numfashin Ubangiji, yana kamar kibiritu mai ƙuna, da aka sa masa wuta. Kaiton waɗanda suka gangara zuwa Masar don neman taimako, waɗanda suke dogara ga dawakai, waɗanda suke dogara ga yawan kekunan yaƙinsu da kuma a girman ƙarfin mahayan dawakansu, amma ba sa dogara ga Mai Tsarkin nan na Isra’ila, ko ya nemi taimako daga Ubangiji. Shi ma yana da hikima kuma zai iya kawo masifa; ba ya janye kalmominsa. Zai yi gāba da gidan mugu, gāba da waɗanda suke taimakon masu aikata mugunta. Amma Masarawa mutane ne ba Allah ba; dawakansu nama da jini ne ba ruhu ba. Sa’ad da Ubangiji ya miƙa hannunsa, shi da yake taimako zai yi tuntuɓe shi da aka taimaka zai fāɗi; dukansu biyu za su hallaka tare. Ga abin da Ubangiji ya faɗa mini, “Kamar yadda zaki kan yi ruri babban zaki a kan abin da ya yi farauta, kuma ko da yake dukan ƙungiyar makiyaya sun taru wuri ɗaya a kansa, ba zai jijjigu ta wurin ihunsu ba ko ya damu da kiraye-kirayensu, ta haka Ubangiji Maɗaukaki zai sauko don yă yi yaƙi a kan Dutsen Sihiyona da kuma a kan ƙwanƙolinsa. Kamar tsuntsaye masu shawagi a sama haka Ubangiji Maɗaukaki zai kiyaye Urushalima; zai kāre ta ya kuma fanshe ta, zai ‘ƙetare’ ta ya kuma kuɓutar da ita.” Ku dawo gare shi ku da kuka yi masa babban tayarwa, ya Isra’ilawa. Gama a wannan rana kowannenku zai ƙi gumakan azurfa da zinariya da hannuwanku masu zunubi suka yi. “Za a karkashe Assuriyawa da takobin da ba na yin mutum ba; takobi, da ba na yin mutum ba, zai cinye. Za su gudu daga takobi za a kuma sa samarinsu aikin dole. Kagararsu za tă fāɗi saboda razana; da ganin matsayin yaƙin, shugabannin yaƙinsu za su firgita,” in ji Ubangiji, wanda wutarsa tana a Sihiyona, wanda matoyarsa tana a Urushalima. Duba, sarki zai yi mulki cikin adalci masu mulki kuma su yi mulki da adalci. Kowane mutum zai zama kamar wurin fakewa daga iska mafaka kuma daga hadari, kamar rafuffukan ruwa a hamada da kuma inuwar babban dutse a ƙeƙasasshiyar ƙasa. Sa’an nan idanun waɗanda suka gani ba za su ƙara rufewa ba, kunnuwan waɗanda suka ji kuma za su saurara. Zuciya marasa haƙuri za su sani su kuma fahimta, harshen masu ana’ana kuma zai sāke su yi magana sosai. Ba za a ƙara ce da wawa mai girma ba ko kuwa a ɗaukaka mazambaci. Gama wawa maganar wauta yakan yi, zuciyarsa ta cika da mugunta, yana aikata abubuwan rashin sanin Allah yana baza kurakurai game da Ubangiji; yana barin mayunwata da yunwa ya kuma hana masu ƙishirwa ruwan sha. Matakan mazambaci mugaye ne, yana ƙulla mugayen shirye-shirye don yă hallaka talakawa da ƙarairayi, ko sa’ad da roƙon mai bukata da gaskiya ne. Amma mutumin kirki kan yi shirye-shirye masu kirki, kuma yakan tsaya a kan ayyukan kirki. Ku matan da kuke zaman jin daɗi, ku tashi ku saurare ni; ku ’yan matan da kuke tsammani kuna da kāriya, ku ji abin da zan faɗa! Cikin ɗan lokaci ƙasa da shekara guda ku da kuke tsammani kuna da kāriya za ku yi rawar jiki; girbin ’ya’yan inabi zai kāsa, girbin ’ya’yan itatuwa kuma ba zai zo ba. Ku yi rawar jiki, ku mata masu jin daɗi, ku sha wahala, ku ’yan matan da kuke tsammani kuna da kāriya! Ku tuɓe rigunanku, ku ɗaura tsummoki a kwankwasonku. Ku bugi ƙirjinku don gonaki masu kyau don ’ya’yan inabi da kuma don ƙasar mutanena, da ƙasar da ƙayayyuwa da sarƙaƙƙiya ne suka yi girma, I, ku yi kuka saboda dukan gidajen da dā ake biki da kuma domin wannan birnin da dā ake murna a ciki. Za a ƙyale kagarar, a gudu a bar birnin da dā ake hayaniya; mafaka da hasumiyar tsaro za su zama kango har abada, jin daɗin jakuna, makiyaya don garkuna, sai an zubo Ruhu a kanmu daga sama, hamada kuma ta zama ƙasar mai taƙi, gona mai taƙi kuma ta zama kamar kurmi. Aikin gaskiya zai zauna a hamada adalci kuma zai zauna a ƙasa mai taƙi. Aikin adalci zai zama salama; tasirin adalci zai zama natsuwa da tabbaci har abada. Mutanena za su zauna lafiya a wuraren salama, a gidaje masu kāriya, a wuraren hutun da babu fitina. Ko da yake ƙanƙara za tă fāɗo a jeji, a kuma rurrushe birni gaba ɗaya, zai zama muku da albarka, ku da kuke shuki iri kusa da kowane rafi, kuna kuma barin lafiyayyiyar makiyaya domin shanu da jakunanku. Kaitonka, ya kai mai hallakarwa, kai da ba a hallakar da kai ba! Kaitonka, ya maciya amana, kai da ba a ci amanarka ba! Sa’ad da ka daina hallakarwa, za a hallaka ka; sa’ad da ka daina cin amana, za a ci amanarka. Ya Ubangiji, ka yi mana jinƙai; muna marmarinka. Ka zama ƙarfinmu kowace safiya, cetonmu a lokacin damuwa. Da tsawar muryarka, mutane za su gudu; sa’ad da ka tashi, al’ummai za su watse. Ganimarku, ya al’ummai ƙanana fāri sun girbe; kamar tarin fārin da mutane sun fāɗa wa. Ubangiji da girma yake, gama yana zaune a bisa; zai cika Sihiyona cikin gaskiya da adalci. Zai zama tabbataccen harsashi na koyaushe, ma’ajin ceto da hikima da sani a yalwace; tsoron Ubangiji shi ne mabuɗin wannan dukiya. Duba, jarumawansu suna kuka da ƙarfi a tituna; jakadun salama suna kuka mai zafi. An gudu an bar manyan hanyoyi, babu matafiye a kan hanyoyi. Aka keta yarjejjeniya, an rena shaidunsa ba a kuwa ganin girman kowa. Ƙasa tana kuka an kuma gudu an bar ta, Lebanon ta sha kunya ta kuma yanƙwane; Sharon ta zama kamar Araba, Bashan da Karmel sun kakkaɓe ganyayensu. “Yanzu zan tashi,” in ji Ubangiji. “Yanzu ne za a ɗaukaka ni; yanzu za a ɗaga ni sama. Kun yi cikin yayi, kuka haifi kara; numfashinku wuta ne da zai cinye ku. Za a ƙone mutane kamar da ƙuna farar ƙasa; kamar ƙayayyuwan da aka sare aka kuma sa musu wuta.” Ku da kuke da nesa, ku ji abin da na yi; ku da kuke kusa, ku san ikona! Masu zunubi a Sihiyona sun firgita; rawar jiki ya kama marasa sanin Allah suna cewa, “Wane ne a cikinmu zai iya zama da wuta mai ci? Wane ne a cikinmu zai iya zama da madawwamiyar ƙonewa?” Shi da yake tafiya cikin adalci yana kuma magana abin da yake daidai, wanda yake ƙin riba daga cuta yana kuma kiyaye hannunsa daga karɓan cin hanci, wanda yake hana kunnuwansa daga ƙulla kisa ya kuma rufe idanunsa a kan tunanin aikata mugunta, shi ne mutumin da zai zauna a bisa, wanda mafakarsa za tă zama kagarar dutse. Za a tanada abincinsa, kuma ruwa ba zai kāsa masa ba. Idanunku za su ga sarki a cikin kyansa ku kuma hangi ƙasar da take shimfiɗe can da nisa. Cikin tunaninku za ku yi tunani firgitar da ta faru tun dā kuna cewa, “Ina hafsan nan? Ina wannan wanda yake karɓar haraji? Ina hafsan da yake lura da hasumiyoyi?” Ba za ku ƙara ganin waɗannan mutane masu girman kai kuma ba, waɗannan mutane masu magana da harshen da ba ku fahimta ba. Ku duba Sihiyona, birnin shagulgulanmu; idanunku za su ga Urushalima, mazauni mai lafiya, tentin da ba za a taɓa gusar ba; wanda ba a taɓa tumɓuke turakunsa ba, ko a tsinke igiyoyinta. A can Ubangiji zai zama Mai Iko Duka namu. Zai zama kamar inda manyan koguna da rafuffuka suke. Matuƙan jirgin ruwa ba za su kai wurinsu ba, manyan jiragen ruwa ba za su yi zirga-zirga a kansu ba. Gama Ubangiji ne alƙalinmu, Ubangiji ne mai ba mu dokoki, Ubangiji ne sarkinmu; shi ne wanda zai cece mu. Maɗaurinku sun kunce ƙarfafan itacen jirgin ba su da kāriya, fikafikan jirgin ba su buɗu ba. Ta haka za a raba yalwar ganima har ma guragu za su kwashe ganimar. Ba wani mazauna a Sihiyona da zai ce, “Ina ciwo”; za a kuma gafarta zunuban waɗanda suke zama a can. Ku zo kusa, ku al’ummai, ku kuwa saurara ku kasa kunne, ku mutane! Bari duniya ta ji, da kuma dukan abin da yake cikinta, duniya, da dukan abin da yake fitowa daga gare ta! Ubangiji yana fushi da dukan al’ummai; hasalarsa tana a kan mayaƙansu. Zai hallaka su tas, zai ba da su a karkashe. Za a jefar da waɗanda aka kashe gawawwakinsu za su yi wari; duwatsu za su jiƙu da jininsu. Za a tumɓuke dukan taurarin sammai za a kuma nannaɗe sararin sama kamar littafi; dukan rundunar sama za su fāffāɗi kamar ganyayen da suka yanƙwane daga kuringa, kamar ’ya’yan ɓauren da suka bushe daga itacen ɓaure. Takobina ya sha zararsa a cikin sammai; duba, ya sauko cikin hukunci a kan Edom, mutanen da zan hallaka tas. Takobin Ubangiji ya jiƙu da jini, ya rufu da kitse, jinin raguna da na awaki, kitse daga ƙodar raguna. Gama Ubangiji ya yi hadayar Bozra da kuma babban kisa a Edom. Babban bijimin jeji zai fāɗi tare da su, maruƙan bijimi da manyan bijimai. Ƙasarsu za tă cika da jini, ƙura kuma zai cika da kitse. Gama Ubangiji yana da ranar ɗaukar fansa, shekarar ramuwa, don biya wa Sihiyona bukata. Za a mai da rafuffukan Edom rami, ƙurarta za tă zama kibiritun farar wuta; ƙasarta za tă zama rami mai ƙuna! Ba za a kashe ta ba dare da rana; hayaƙinta za tă yi ta tashi har abada. Daga tsara zuwa tsara za tă zama kango; babu wani da zai ƙara wucewa ta wurin. Mujiyar hamada da mujiya mai kuka za su mallake ta; babban mujiya da hankaka za su yi sheƙa a can. Allah zai miƙe a kan Edom magwajin bala’i da ma’aunin kango. Sarakunanta ba za su kasance da wani abin da ake kira masarauta ba, dukan sarakunanta za su ɓace. Ƙayayuwa za su mamaye fadodinta ƙayayyuwa da sarƙaƙƙiya za su cika kagaranta. Za tă zama mazaunin diloli da gida don mujiyoyi. Halittun hamada za su sadu da kuraye, awakin jeji za su yi ta kiran juna; a can halittun dare su ma za su huta su kuma nemi wurin hutu wa kansu. Mujiya za tă yi sheƙa a can ta zuba ƙwai; za tă ƙyanƙyashe su, ta kuma kula da ’ya’yanta a inuwar fikafikanta; a can kuma shirwa za su taru, kowa da abokinsa. Duba a cikin littafin Ubangiji ka kuma karanta. Babu wani a cikin waɗannan da ya ɓace, babu ko ɗaya da ba ta da abokiya. Gama bakinsa ne ya ba da umarni, Ruhunsa kuma zai tara su wuri ɗaya. Ya ba su rabonsu; hannunsa ya rarraba musu ta wurin awo. Za su mallake ta har abada su kuma zauna a can daga tsara zuwa tsara. Hamada da ƙeƙasasshiyar ƙasa za su yi murna; jeji zai yi farin ciki ya kuma hudo. Kamar fure, zai buɗu ya hudo; zai yi farin ciki mai girma ya kuma yi sowa don farin ciki. Za a maido wa Lebanon da darajarta, darajar Karmel da Sharon; za su ga ɗaukakar Ubangiji, darajar Allahnmu. Ku ƙarfafa hannuwa marasa ƙarfi, ku ƙarfafa gwiwoyin da suka gaji; ku faɗa wa waɗanda suka karai a zukata, “Ku yi ƙarfin hali, kada ku ji tsoro; Allahnku zai zo, zai zo domin ya ɗau fansa; da ramuwar Allah zai zo don yă cece ku.” Sa’an nan idanun makafi za su buɗe kunnuwan kurame kuma su ji. Sa’an nan guragu za su yi tsalle kamar barewa, bebaye kuma su yi sowa don farin ciki. Ruwa zai kwararo daga jeji rafuffuka kuma a cikin hamada. Yashi mai ƙuna zai zama tafki, ƙeƙasasshiyar ƙasa kuma za tă cika da maɓulɓulan rafuffuka. A mazaunin diloli, inda suka taɓa zama, ciyawa da iwa da kyauro za su yi girma. Kuma babbar hanya za tă kasance a can; za a ce ta ita Hanyar Mai Tsarki. Marasa tsarki ba za su yi tafiya a kanta ba; za tă zama domin waɗanda suka yi tafiya a wannan Hanya ce; mugaye da wawaye ba za su yi ta yawo a kanta ba. Zaki ba zai kasance a can ba, balle wani naman jeji mai faɗa ya haura kanta; ba za a same su a can ba. Amma fansassu ne kaɗai za su yi tafiya a can, kuma fansassu na Ubangiji za su komo. Za su shiga Sihiyona da rerawa; matuƙar farin ciki zai mamaye su. Murna da farin ciki za su sha kansu, baƙin ciki kuma da nishi za su gudu. A shekara ta goma sha huɗu ta mulkin Sarki Hezekiya, Sennakerib sarkin Assuriya ya kai wa dukan birane masu kagaran Yahuda yaƙi ya kuma kame su. Sai sarkin Assuriya ya aiki sarkin yaƙinsa tare da mayaƙa masu yawa daga Lakish zuwa wurin Sarki Hezekiya a Urushalima. Sa’ad da sarkin yaƙi ya tsaya a wuriyar Tafkin Tudu, a hanya zuwa Filin Mai Wanki, Eliyakim ɗan Hilkiya sarkin fada, Shebna magatakarda, da Yowa ɗan Asaf marubuci suka fita zuwa wurinsa. Sai sarkin yaƙin ya ce musu, “Ku faɗa wa Hezekiya. “ ‘Ga abin da babban sarki, sarkin Assuriya, ya faɗa. A kan me kake dangana wannan ƙarfin halinka? Ka ce kana da dabara da kuma ƙarfin mayaƙa, amma kana magana banza ce kawai. Ga wa ka dogara, da kake tayar mini? Yanzu duba, kana dogara ga Masar, wannan ɗan tsinken kyauron dogarawa, wanda zai soki hannun mutum yă kuma ji masa rauni in ya dangana a kansa! Haka Fir’auna sarkin Masar yake ga duk wanda ya dogara da shi. Kuma in ka ce mini, “Mun dogara ga Ubangiji Allahnmu ne” ba shi ba ne Hezekiya ya rurrushe masujadan kan tudunsa da bagadansa, yana ce wa Yahuda da Urushalima, “Dole ku yi sujada wa gaban wannan bagade”? “ ‘Yanzu fa, bari in yi ciniki da maigidana, sarki Assuriya. Zan ba ka dawakai dubu biyu, in za ka sa mahaya a kansu! Yaya za ka ƙi hafsan mafi ƙanƙanci na hafsoshin maigidana, ko da yake kana dogara ga Masar don kekunan yaƙi da mahayan dawakai? Ban da haka kuma, na zo ne in faɗa in kuma hallaka wannan ƙasa ba tare da Ubangiji ba? Ubangiji kansa ya faɗa mini in tasar wa wannan ƙasa in kuma hallaka ta.’ ” Sai Eliyakim, Shebna da Yowa suka ce wa sarkin yaƙin, “Ka yi haƙuri ka yi wa bayinka magana da Arameyanci, da yake muna jinsa. Kada ka yi mana magana da Yahudanci a kunnen mutanen da suke kan katanga.” Amma sarkin yaƙin ya amsa ya ce, “Kuna tsammani ga maigidanku da ku ne kawai maigidana ya aiko ni in yi waɗannan maganganu, ba ga mutanen da suke zama a kan katanga ba, waɗanda kamar ku, za su ci kashinsu su kuma sha fitsarinsu?” Sa’an nan sarkin yaƙin ya tsaya ya kuma yi kira da Yahudanci ya ce, “Ku ji kalmomin babban sarki, sarkin Assuriya! Ga abin da sarki ya ce kada ku bar Hezekiya ya ruɗe ku. Ba zai cece ku ba! Kada ku bar Hezekiya ya rarashe ku ku dogara ga Ubangiji sa’ad da ya ce, ‘Tabbatacce Ubangiji zai cece mu; ba za a ba da wannan birni a hannun sarkin Assuriya ba.’ “Kada ku saurari Hezekiya. Ga abin da sarkin Assuriya ya faɗa. Ku nemi salama da ni ku kuma fito zuwa wurina. Ta haka kowa zai ci daga kuringarsa da kuma itacen ɓaurensa ya kuma sha ruwa daga tankinsa, sai na zo na kuma kwashe ku zuwa ƙasa kamar taku, ƙasar hatsi da kuma sabon ruwan inabi, ƙasar abinci da gonakin inabi. “Kada ku bar Hezekiya ya ruɗe ku sa’ad da ya ce, ‘ Ubangiji zai cece mu.’ Allahn wata al’umma ya taɓa ceci ƙasarsa daga hannun sarkin Assuriya? Ina allolin Hamat da na Arfad? Ina allolin Sefarfayim? Sun fanshi Samariya daga hannuna? Wanne cikin dukan allolin ƙasashen nan ya iya ceton ƙasarsa daga gare ni? Yaya kuwa Ubangiji zai iya ceci Urushalima daga hannuna?” Amma mutanen suka yi shiru ba su kuwa ce kome ba, gama sarki ya yi umarni cewa, “Kada ku amsa masa.” Sai Eliyakim ɗan Hilkiya sarkin fada, Shebna magatakarda, da kuma Yowa ɗan Asaf marubuci suka tafi wurin Hezekiya, da rigunansu a kyakkece, suka kuwa faɗa masa abin da sarkin yaƙin ya yi ta farfaɗa. Sa’ad da Sarki Hezekiya ya ji haka, sai ya kyakkece rigunansa ya kuma sanya tsummoki ya tafi ya shiga haikalin Ubangiji. Ya aiki Eliyakim sarkin fada, Shebna magatakarda da kuma manyan firistoci, duka sanye da tsummoki, wurin Ishaya ɗan Amoz. Suka faɗa masa cewa, “Ga abin da Hezekiya ya ce wannan rana ce ta baƙin ciki da tsawatawa da shan kunya, sai ka ce sa’ad da ’ya’ya kan zo matakin haihuwa sa’an nan a rasa ƙarfin haihuwarsu. Mai yiwuwa Ubangiji Allahnka zai ji maganganun sarkin yaƙin da maigidansa, sarkin Assuriya, ya aika don yă zagi Allah mai rai, ya kuma tsawata masa saboda maganganun da Ubangiji Allahnka ya ji. Saboda haka ka yi addu’a saboda raguwar da suke da rai.” Sa’ad da shugabannin Sarki Hezekiya suka zo wurin Ishaya, sai Ishaya ya ce musu, “Ku faɗa wa maigidanku cewa, ‘Ga abin da Ubangiji ya faɗa. Kada ka ji tsoron abin da ka ji, maganganun nan da bayin sarkin Assuriya suka yi mini saɓo. Ka saurara! Zan sa ruhuna a cikinsa saboda sa’ad da ya ji wani labari, zai koma zuwa ƙasarsa, a can kuwa zan sa a kashe shi da takobi.’ ” Sa’ad da sarkin yaƙin ya ji cewa sarkin Assuriya ya bar Lakish, sai ya janye ya kuma sami sarki yana yaƙi da Libna. To, fa, Sennakerib ya sami labari cewa Tirhaka, mutumin Kush sarkin Masar, yana fitowa don yă yi yaƙi da shi. Sa’ad da ya ji haka, sai ya aiki jakadu zuwa wurin Hezekiya da wannan magana. “Ku faɗa wa Hezekiya sarkin Yahuda cewa kada ka bar allahn da ka dogara a kai ya ruɗe ka sa’ad da ya ce, ‘Ba za a ba da Urushalima ga sarkin Assuriya ba.’ Tabbatacce ka ji abin da sarakunan Assuriya suka aikata ga dukan ƙasashe, suna hallaka su tas. Kai kuwa za ka tsira ne? Allolin al’umman da kakannina suka hallaka sun cece su ne, allolin Gozan, Haran, Rezef da kuma na mutanen Eden waɗanda suke zama a Tel Assar? Ina sarkin Hamat yake, sarkin Arfad fa, sarkin Sefarfayim, ko na Hena ko na Iffa?” Hezekiya ya karɓi wasiƙar daga jakadun ya karanta ta. Sa’an nan ya haura zuwa haikalin Ubangiji ya shimfiɗa ta a gaban Ubangiji. Sai Hezekiya ya yi addu’a ga Ubangiji ya ce, “Ya Ubangiji Allah Maɗaukaki, Allah na Isra’ila, zaune a tsakanin kerubobi, kai kaɗai ne Allah a kan dukan masarautan duniya. Ka kasa kunne, ya Ubangiji, ka kuma ji; ka buɗe idanunka, ya Ubangiji, ka kuma gani; ka saurara ga dukan maganganun da Sennakerib ya aika don yă zagi Allah mai rai. “Gaskiya ce, ya Ubangiji, cewa sarakunan Assuriyawa sun mai da dukan waɗannan mutane da ƙasashensu kango. Sun jefar da gumakansu cikin wuta suka kuma hallaka su, gama su ba alloli ba ne itace ne kawai da dutse, da hannuwan mutane suka sarrafa. Yanzu, ya Ubangiji Allahnmu, ka cece mu daga hannunsa, saboda masarautai a duniya su san cewa kai kaɗai ne, ya Ubangiji, Allah.” Sa’an nan Ishaya ɗan Amoz ya aika da saƙo wa Hezekiya cewa, “Ga abin da Ubangiji, Allah na Isra’ila, ya faɗa. Saboda ka yi addu’a gare ni game da Sennakerib sarkin Assuriya, ga abin da maganar Ubangiji ya faɗa a kansa, “Budurwa Diyar Sihiyona ta rena tana kuma maka ba’a. Diyar Urushalima tana kada kai yayinda kake gudu. Wane ne ka zargi ka kuma yi wa saɓo? A kan wa ka tā da muryarka ka kuma daga idanu cikin fariya? A kan Mai Tsarkin nan na Isra’ila! Ta wurin jakadunka ka jibge zage-zage a kan Ubangiji. Ka kuma ce, ‘Da kekunan yaƙina masu yawa na hau ƙwanƙolin duwatsu, ƙwanƙolin mafi tsayi na Lebanon. Na sassare al’ul mafi tsayi fir mafi kyau. Na kai can wuri mafi nisa na kurminsa. Na haƙa rijiyoyi a baƙuwar ƙasa na kuma sha ruwa a can. Da tafin ƙafafuna na busar da dukan rafuffukan Masar.’ “Ba ka ji ba cewa tun dā can na shirya ya zama haka? A kwanakin dā na kafa shi; yanzu na sa ya faru, cewa ka mai da birane masu mafaka zuwa tsibin ɓuraguzai. Mutanensu, suka rasa ƙarfi, sun firgita suka kuma sha kunya. Suka zama kamar tsire-tsire a gona, kamar tsire-tsiren ta suka tohu, kamar ciyawar da ya tsiro a kan rufi, wadda zafi ya yi wa ƙuna kafin tă yi girma. “Amma na san inda kake zama da sa’ad da kakan fita ka kuma koma da yadda ka harzuƙa gāba da ni. Saboda ka harzuƙa gāba da ni kuma saboda girmankanka ya kai kunnuwana, zan sa ƙugiya a hancinka linzamina a bakinka, zan kuma sa ka koma ta hanyar da ka zo. “Wannan zai zama alama gare ka, ya Hezekiya, “Wannan shekara za ka ci abin da ya yi girma da kansa, shekara ta biyu kuma abin da ya tsiro daga wancan. Amma a shekara ta uku za ka yi shuki ka kuma girba, za ka dasa gonakin inabi ka kuma ci ’ya’yansu. Sauran da suka rage na gidan Yahuda kuwa za su yi saiwa a ƙarƙashi su kuma ba da ’ya’ya a bisa. Gama daga Urushalima raguwa za tă fito, kuma daga Dutsen Sihiyona ƙungiyar waɗanda suka tsira. Himmar Ubangiji Maɗaukaki zai cika wannan. “Saboda haka ga abin da Ubangiji yana cewa game da sarkin Assuriya, “Ba zai shiga wannan birni ba ya harbe kibiya a nan. Ba zai zo gabansa da garkuwa ba ko ya gina mahaurai kewaye a kansa ba. Ta hanyar da ya zo da ita zai koma; ba zai shiga wannan birni ba,” in ji Ubangiji. “Zan kāre wannan birni in kuma cece shi, saboda girmana da kuma saboda sunan Dawuda bawana!” Sai mala’ikan Ubangiji ya fita ya kuma karkashe mutane dubu ɗari da dubu tamanin da dubu biyar a sansanin Assuriya. Sa’ad da mutane suka farka kashegari, sai ga gawawwaki duk a kwance! Saboda haka Sennakerib sarkin Assuriya ya janye. Ya koma zuwa Ninebe ya zauna a can. Wata rana, yayinda yake yin sujada a haikalin allahnsa Nisrok, ’ya’yansa maza Adrammelek da Sharezer suka kashe shi da takobi, suka kuma gudu zuwa ƙasar Ararat. Esar-Haddon ɗansa kuwa ya gāje shi a matsayin sarki. A kwanakin nan sai Hezekiya ya kamu da ciwo ya kuma kusa ya mutu. Annabi Ishaya ɗan Amoz ya tafi wurinsa ya kuma ce, “Ga abin da Ubangiji ya ce ka shirya gidanka, domin za ka mutu; ba za ka warke ba.” Hezekiya ya juye fuskarsa wajen bango ya kuma yi addu’a ga Ubangiji, “Ka tuna, ya Ubangiji, yadda na yi tafiya a gabanka da aminci da dukan zuciya na kuma yi abin da yake nagari a idanunka.” Sai Hezekiya ya yi kuka mai zafi. Sai maganar Ubangiji ta zo wa Ishaya cewa, “Ka tafi ka faɗa wa Hezekiya, ‘Ga abin da Ubangiji Allah na kakanka Dawuda, ya ce na ji addu’arka na kuma ga hawayenka; zan ƙara maka shekaru goma sha biyar ga rayuwarka. Zan kuwa cece ka da wannan birni daga hannun sarkin Assuriya. Zan kiyaye wannan birni. “ ‘Ga alamar Ubangiji gare ka cewa Ubangiji zai aikata kamar yadda ya yi alkawari. Zan sa inuwar da rana ta yi a kan matakalar Ahaz ta koma baya da taki goma.’ ” Saboda haka inuwar ta koma da baya daga fuskar rana har taki goma. Rubutun Hezekiya sarkin Yahuda bayan ciwonsa da kuma warkarwarsa. Na ce, “Cikin tsakiyar rayuwata dole in bi ta ƙofofin mutuwa a kuma raba ni da sauran shekaruna?” Na ce, “Ba zan ƙara ganin Ubangiji ba, Ubangiji a ƙasa ta masu rai; ba zan ƙara ga wani mutum, ko in kasance tare da waɗanda suke zama a wannan duniya ba. Kamar tentin makiyayi an rushe gidana aka kuma ƙwace ta daga gare ni. Kamar mai saƙa, na nannaɗe rayuwata, ya kuma yanke ni daga sandar saƙa; dare da rana ka kawo ni ga ƙarshe. Na yi jira da haƙuri har safiya, amma kamar zaki ya kakkarya ƙasusuwana duka; dare da rana ka kawo ni ga ƙarshe. Na yi kuka kamar mashirare ko zalɓe, na yi kuka kamar kurciya mai makoki. Idanuna suka rasa ƙarfi yayinda na duba sammai. Na damu; Ya Ubangiji, ka taimake ni!” Amma me zan ce? Ya riga ya yi mini magana, shi kansa ne kuma ya aikata. Zan yi tafiya da tawali’u dukan kwanakina saboda wahalar raina. Ubangiji, ta waɗannan abubuwa ne mutane suke rayuwa; ruhuna kuma yana samun rai a cikinsu shi ma. Ka maido mini da lafiya ka kuma sa na rayu. Tabbatacce wannan kuwa saboda ribata ne cewa in sha irin wahalan nan. Cikin ƙaunarka ka kiyaye ni daga ramin hallaka; ka sa dukan zunubaina a bayanka. Gama kabari ba zai yabe ka ba, matattu ba za su rera yabonka ba; waɗanda suka gangara zuwa rami ba za su sa zuciya ga amincinka ba. Masu rai, masu rai, su suke yabonka, kamar yadda nake yi a yau; iyaye za su faɗa wa ’ya’yansu game da amincinka. Ubangiji zai cece ni, za mu kuma rera da kayan kiɗi masu tsirkiya dukan kwanakinmu a cikin haikalin Ubangiji. Ishaya ya riga ya ce, “Ku shirya curin da aka yi da ’ya’yan ɓaure ku kuma shafa a marurun, zai kuwa warke.” Hezekiya ya riga ya yi tambaya ya ce, “Me zai zama alama ta cewa zan haura zuwa haikalin Ubangiji?” A wannan lokaci Merodak-Baladan ɗan Baladan sarkin Babilon ya aika wa Hezekiya wasiƙu da kuma kyauta, domin ya ji rashin lafiyarsa da kuma warkarwarsa. Hezekiya ya marabci jakadun da murna ya kuma nuna musu abin da gidajen ajiyarsa sun ƙunsa, azurfa, zinariya, yaji, tatsatsen mai, dukan kayan yaƙinsa da kuma kome da yake a ma’ajinsa. Babu abin da yake a cikin fadansa ko cikin dukan masarautarsa da Hezekiya bai nuna musu ba. Sai Ishaya annabi ya tafi wurin Sarki Hezekiya ya kuma tambaye shi ya ce, “Mene ne waɗannan mutane suka faɗa, kuma daga ina suka fito?” Hezekiya ya amsa ya ce, “Daga ƙasa mai nisa. Sun zo ne daga Babilon.” Annabi ya yi tambaya ya ce, “Mene ne suka gani a fadanka?” Hezekiya ya ce, “Sun ga kome da kome a fadana. Babu abin da ban nuna musu a cikin ma’ajina ba.” Sai Ishaya ya ce wa Hezekiya, “Ka ji maganar Ubangiji Maɗaukaki. Tabbatacce lokaci yana zuwa sa’ad da kome da yake cikin fadanka, da kuma dukan abin da kakanninka suka ajiye har yă zuwa yau, za a kwashe zuwa Babilon babu abin da za a bari, in ji Ubangiji. Waɗansu cikin zuriyarka, nama da jininka waɗanda za a haifa maka, za a kwashe su a tafi, za su zama bābānni a fadan sarkin Babilon.” Hezekiya ya ce, “Maganar Ubangiji da ka yi tana da kyau.” Gama ya yi tunani a ransa cewa, “Salama da kāriya za su kasance a zamanina.” Ta’aziyya, ku ta’azantu mutanena, in ji Allahnku. Yi magana mai kwantar da rai ga Urushalima, ku kuma furta mata cewa aiki mai zafinta ya isa, cewa an fanshi zunubinta, cewa ta karɓi daga hannun Ubangiji ninki biyu saboda dukan zunubanta. Muryar wani tana kira cewa, “A cikin hamada ku shirya hanya saboda Ubangiji; ku miƙe manyan hanyoyi domin Allahnmu a cikin jeji. Za a cike kowane kwari, a baje kowane dutse da kowane tudu; za a mayar da karkatattun wurare su zama sumul, munanan wurare kuma su zama da kyau. Za a kuma bayyana ɗaukakar Ubangiji, dukan mutane kuwa za su gan ta. Gama Ubangiji da kansa ne ya yi magana.” Muryar tana cewa, “Ka yi shela.” Na kuwa ce, “Me zan yi shelar?” “Dukan mutane kamar ciyawa suke, kuma dukan ɗaukakarsu kamar furannin jeji ne. Ciyawa takan yanƙwane, furanni kuma su yi yaushi, domin Ubangiji ya hura iska a kansu. Tabbatacce mutane ciyawa ne. Hakika ciyawa takan yanƙwane, furanni kuma su yi yaushi, amma maganar Allahnmu tana nan daram har abada.” Kai da ka kawo labari mai daɗi wa Sihiyona, ka haura a bisa dutse. Kai da ka kawo labari mai daɗi wa Urushalima, ka tā da muryarka ka yi ihu, ka ɗaga ta, kada ka ji tsoro; faɗa wa garuruwan Yahuda, “Ga Allahnku!” Duba, Ubangiji Mai Iko Duka yana zuwa da iko, hannunsa kuma yana yin mulki dominsa. Duba, ladarsa tana tare da shi, sakamakonsa kuma na rakiyarsa. Yakan lura da garkensa kamar makiyayi. Yakan tattara tumaki wuri ɗaya yă riƙe su kurkusa da ƙirjinsa; a hankali kuma yakan bi da masu ba da mama. Wane ne ya auna ruwaye a tafin hannunsa, ko kuwa ya gwada tsawon sammai da fāɗin tafin hannunsa? Wane ne ya riƙe ƙurar ƙasa a kwando, ko kuwa ya auna nauyin duwatsu a magwaji, tuddai kuma a ma’auni? Wane ne ya fahimci zuciyar Ubangiji, ko kuwa ya koya masa a matsayin mashawarcinsa? Wane ne Ubangiji ya nemi shawararsa don yă ganar da shi, wane ne kuma ya koya masa hanyar da ta dace? Wane ne ya koya masa sani ko ya nuna masa hanyar fahimta? Tabbatacce al’ummai suna kama da ɗigon ruwa a cikin bokiti an ɗauke su a matsayin ƙura a kan magwaji; yakan auna tsibirai sai ka ce ƙura mai laushi. Itatuwan Lebanon ba su isa a yi wutar bagade da su ba, balle dabbobinsa su isa yin hadayun ƙonawa. A gabansa dukan al’ummai ba kome ba ne; ya ɗauke su ba a bakin kome ba kuma banza ne kurum. To, ga wane ne za ka kwatanta Allah? Wace siffa za ka kwatanta shi da ita? Gunki dai, maƙeri kan yi zubinsa, maƙerin zinariya kuma yă ƙera shi da zinariya yă kuma sarrafa masa sarƙoƙin azurfa. Mutumin da talauci ya sha kansa da ba zai iya miƙa irin hadayar nan ba kan zaɓi itacen da ba zai ruɓe ba. Yakan nemi gwanin sassaƙa don yă sassaƙa masa gunkin da ba zai fāɗi ba. Ba ku sani ba? Ba ku taɓa ji ba? Ba a faɗa muku daga farko ba? Ba ku fahimta ba tun kafawar duniya? Yana zaune a kursiyi a bisa iyakar duniya, kuma mutanenta suna kama da fāra. Ya miƙa sammai kamar rumfa, ya kuma shimfiɗa su kamar tentin da za a zauna a ciki. Yakan mai da sarakuna ba kome ba yă mai da masu mulkin wannan duniya wofi. Ba da jimawa ba bayan an shuka su, ba da jimawa ba bayan an dasa su, ba da jimawa ba bayan sun yi saiwa a ƙasa, sai yă hura musu iska su yanƙwane, guguwa kuma ta kwashe su kamar yayi. “Ga wa za ku kwatanta ni? Ko kuwa wa yake daidai da ni?” In ji Mai Tsarkin nan. Ku ɗaga idanunku ku duba sammai. Wane ne ya halicce dukan waɗannan? Wane ne ya fitar da rundunar taurari ɗaya-ɗaya, yana kiransu, kowanne da sunansa. Saboda ikonsa mai girma da kuma ƙarfinsa mai girma, babu ko ɗayansu da ya ɓace. Ya Yaƙub, ya Isra’ila, me ya sa kake ce kana kuma gunaguni cewa, “Hanyata tana a ɓoye daga Ubangiji; Allah bai kula da abin da yake damuna ba”? Ba ku sani ba? Ba ku ji ba? Ubangiji madawwamin Allah ne, Mahaliccin iyakokin duniya. Ba zai taɓa gaji ko yă kasala ba, kuma fahimtarsa ya wuce gaban ganewar mutum. Yakan ba da ƙarfi ga waɗanda suka gaji yă kuma ƙara ƙarfi ga marasa ƙarfi. Ko matasa ma kan gaji su kuma kasala, samari kuma kan yi tuntuɓe su fāɗi; amma waɗanda suka dogara ga Ubangiji za su sabunta ƙarfinsu. Za su yi firiya da fikafikai kamar gaggafa; za su kuma yi gudu ba kuwa za su gaji ba, za su yi tafiya ba kuwa za su kasala ba. “Ku yi shiru a gabana, ku tsibirai! Bari al’ummai su sabunta ƙarfinsu! Bari su zo gaba su yi magana; bari mu sadu a wurin shari’a. “Wa ya zuga wannan daga gabas, yana kiransa cikin adalci ga yin hidima? Ya miƙa masa al’ummai ya kuma yi nasara da sarakuna a gabansa. Ya mai da su ƙura da takobinsa, zuwa inda iska ke hurawa ta wurin bugun da ya yi musu. Ya fafare su ya kuma yi tafiyarsa lafiya ƙalau, a hanyar da ƙafafunsa ba su taɓa bi ba. Wane ne ya taɓa yin haka ya kuma sa ya faru, yana kira ga tsararraki daga farko? Ni, Ubangiji ina can tun farkonsu ni kuma ina can har ƙarshe, Ni ne shi.” Tsibirai sun gan shi suka kuma ji tsoro; iyakokin duniya sun yi rawar jiki. Suka kusato suka kuma zo gaba; kowa na taimakon wani yana ce wa ɗan’uwansa, “Ka ƙarfafa!” Masassaƙi yakan ƙarfafa maƙerin zinariya, kuma shi mai gyara da guduma ya yi sumul yakan ƙarfafa mai harhaɗawa. Ya ce game da haɗin, “Ya yi kyau.” Yakan buga ƙusoshi su riƙe gunkin don kada yă fāɗi. “Amma kai, ya Isra’ila, bawana, Yaƙub, wanda na zaɓa, zuriyar Ibrahim abokina, na ɗauke ka daga iyakar duniya, daga kusurwoyi masu nesa na kira ka. Na ce, ‘Kai bawana ne’; na zaɓe ka ban kuwa ƙi ka ba. Saboda haka kada ka ji tsoro, gama ina tare da kai; kada ka karai, gama ni ne Allahnka. Zan ƙarfafa ka in kuma taimake ka; zan riƙe ka da hannun damana mai adalci. “Duk wanda ya yi fushi da kai tabbatacce zai sha kunya da ƙasƙanci; waɗanda suka yi hamayya da kai za su zama kamar ba kome ba su kuma hallaka. Ko ka nemi abokan gābanka, ba za ka same su ba. Waɗanda suke yaƙi da kai za su zama kamar ba kome ba. Gama ni ne Ubangiji Allahnka, wanda ya riƙe ka da hannun damana ya kuma ce maka, Kada ka ji tsoro; zan taimake ka. Kada ka ji tsoro, ya Yaƙub marar ƙarfi, ya ƙaramin Isra’ila, gama ni kaina zan taimake ka,” in ji Ubangiji, Mai Fansarka, Mai Tsarkin nan na Isra’ila. “Duba, zan sa ka cikin abin sussuka, saboda kuma mai kaifi mai haƙora da yawa. Za ka yi sussukar duwatsu ka ragargaza su, ka kuma farfashe tuddai su zama kamar yayi. Za ka tankaɗe su, iska kuma ta kwashe su, guguwa kuma za tă warwatsa su. Amma za ka yi farin ciki a cikin Ubangiji ka kuma ɗaukaka a cikin Mai Tsarkin nan na Isra’ila. “Matalauta da mabukata suna neman ruwa, amma babu kome; harsunansu sun bushe saboda ƙishi. Amma Ni Ubangiji zan amsa musu; Ni, Allah na Isra’ila, ba zan yashe su ba. Zan sa koguna su malalo a ƙeƙasassun tuddai, maɓulɓulan ruwa kuma a kwaruruka. Zan mai da hamada tafkunan ruwa, busasshiyar ƙasa kuma ta zama maɓulɓulan ruwa. Zan sa a hamada ta tsiro da al’ul da itacen ƙirya, da itacen ci-zaƙi, da zaitun. Zan sa itace mai girma a ƙasashe masu sanyi ya tsiro a ƙeƙasasshiyar ƙasa, tare da fir da kuma saifires, don mutane su gani su kuma sani, su lura su kuma fahimci, cewa hannun Ubangiji ne ya aikata haka, cewa Mai Tsarkin nan na Isra’ila ya sa abin ya faru. “Ka gabatar da damuwarka,” in ji Ubangiji. “Ka kawo gardandaminka,” in ji Sarki na Yaƙub. “Ka shigar da gumakanka don su faɗa mana abin da zai faru. Faɗa mana abubuwan da suka riga suka faru, domin mu lura da su mu kuma san abin da zai faru a ƙarshe. Ko kuwa ku furta mana abubuwan da za su faru, faɗa mana abin da nan gaba ta ƙunsa, don mu san cewa ku alloli ne. Ku yi wani abu, mai kyau ko mummuna, don mu ji tsoro da fargaba. Amma ku ba kome ba ne kuma ayyukanku banza da wofi ne; duk wanda ya zaɓe ku abin ƙyama ne. “Na zuga wani daga arewa, ya kuwa zo, wani daga inda rana ke fitowa wanda yake kira bisa sunana. Yana takawa a kan masu mulki kamar da taɓarya, sai ka ce maginin tukwane yana taka laka. Wa ya faɗi wannan tun daga farko, don mu sani, ko kafin ya faru, don mu ce, ‘Ya faɗi daidai’? Ba wanda ya faɗa wannan, ba wanda ya riga faɗe shi, ba wanda ya ji wata magana daga gare ku. Ni ne na farkon da ya ce wa Sihiyona, ‘Duba, ga su nan!’ Na ba wa Urushalima saƙon labari mai daɗi. Na duba amma ba kowa ba wani a cikinsu da zai ba da shawara, ba wani da zai ba da amsa sa’ad da na tambaye su. Duba, dukansu masu ƙarya ne! Ayyukansu ba su da riba; siffofinsu iska ne kawai da ruɗami. “Ga bawana, wanda na ɗaukaka, zaɓaɓɓen nan nawa wanda nake jin daɗi; Zan sa Ruhuna a cikinsa zai kuwa kawo adalci ga al’ummai. Ba zai yi ihu ko ya tā da murya, ko ya daga muryarsa a tituna ba. Iwan da ta tanƙware ba zai karye ba, ba zai kashe lagwani mai hayaƙi ba. Cikin aminci zai kawo adalci; ba zai kāsa ko ya karai ba sai ya kafa adalci a duniya. Cikin dokarsa tsibirai za su sa zuciya.” Ga abin da Allah Ubangiji ya ce, shi da ya halicci sammai ya kuma miƙe su, wanda ya shimfiɗa duniya da dukan abin da ya fito cikinta, wanda ya ba wa mutanenta numfashi, da rai ga waɗanda suke tafiya a kanta. “Ni Ubangiji, na kira ka cikin adalci; zan riƙe hannunka. Zan kiyaye ka in kuma sa ka zama alkawari ga mutane haske kuma ga Al’ummai, don ka buɗe idanun makafi ka ’yantar da kamammu daga kurkuku kuma kunce ɗaurarrun kurkuku masu zama cikin duhu. “Ni ne Ubangiji; sunana ke nan! Ba zan ba da ɗaukakata ga wani ba ko yabona ga gumaka. Duba, abubuwan da sun tabbata, sababbin abubuwa kuwa nake furtawa; kafin ma su soma faruwa na sanar da su gare ku.” Ku rera sabuwar waƙa ga Ubangiji, ku yi yabonsa daga iyakar duniya, ku da kuka gangara zuwa teku, da kome da yake cikinsa, ku tsibirai, da waɗanda suke zama a cikinsu. Bari hamada da garuruwanta su tā da muryoyinsu; bari wuraren zaman da Kedar ke zama su yi farin ciki. Bari mutanen Sela su rera don farin ciki; bari su yi sowa daga ƙwanƙolin duwatsu. Bari su ɗaukaka Ubangiji su kuma yi shelar yabonsa a tsibirai. Ubangiji zai fita ya yi yaƙi kamar mai ƙarfi, kamar jarumi zai yi himma; da ihu zai tā da kirarin yaƙi zai kuma yi nasara a kan abokan gābansa. “Na daɗe ina shiru, na yi shiru na kuma ƙame kaina. Amma yanzu, kamar mace mai naƙuda, na yi ƙara, ina nishi ina kuma haki. Zan lalatar da duwatsu da tuddai in busar da dukan itatuwansu; zan mai da koguna su zama tsibirai in kuma busar da tafkuna. Zan yi wa makafi jagora a hanyoyin da ba su taɓa sani ba, a hanyoyin da ba a saba ba zan bishe su; zan mai da duhu ya zama haske a gabansu in kuma mai da ƙasa mai kururrumai ta zama sumul. Abubuwan da zan yi ke nan; ba zan yashe su ba. Amma waɗanda suka dogara ga gumaka, waɗanda suke ce wa siffofi, ‘Ku ne allolinmu,’ za a mai da su baya da kunya. “Ka ji, kai kurma; duba, kai makaho, ka kuma gani! Wane ne makaho in ba bawana ba, da kuma kurma in ba ɗan aikan da na aika ba? Wane ne makaho kamar wanda ya miƙa kai gare ni, makaho kamar bawan Ubangiji? Kun ga abubuwa masu yawa, amma ba ku kula ba; kunnuwanku suna a buɗe, amma ba kwa jin wani abu.” Yakan gamsar da Ubangiji saboda adalcinsa ya sa dokarsa ta zama mai girma da kuma mai ɗaukaka. Amma ga mutanen da aka washe aka kuma kwashe ganima, an yi wa dukansu tarko a cikin rammuka ko kuma an ɓoye su cikin kurkuku. Sun zama ganima, babu wani da zai kuɓutar da su; an mai da su ganima, ba wanda zai ce, “Mayar da su.” Wane ne a cikinku zai saurari wannan ko ya kasa kunne sosai a cikin kwanaki masu zuwa? Wa ya ba da Yaƙub don yă zama ganima Isra’ila kuma ga masu kwasar ganima? Ba Ubangiji ba ne, wanda kuka yi wa zunubi? Gama ba su bi hanyoyinsa ba; ba su yi biyayya da dokarsa ba. Saboda haka ya zuba musu zafin fushinsa, yaƙi mai tsanani. Ya rufe su cikin harsunan wuta, duk da haka ba su gane ba; ya cinye su, amma ba su koyi kome ba. To, fa, ga abin da Ubangiji yana cewa, shi da ya halicce ka, ya Yaƙub, shi da ya siffanta ka, ya Isra’ila, “Kada ka ji tsoro, gama na fanshe ka; na kira ka da suna; kai nawa ne. Sa’ad da kuka bi ta ruwaye, zan kasance tare da ku; sa’ad da kuka bi ta koguna, ba za su kwashe ku ba. Sa’ad da kuke tafiyata cikin wuta, ba za tă ƙone ku ba; harsunan wutar ba za su ƙone ku ba. Gama ni ne Ubangiji, Allahnku, Mai Tsarkin nan na Isra’ila, Mai Cetonku; na bayar da Masar don fansa, Kush da Seba a maimakonku. Da yake ku masu daraja da kuma girma ne a idona, saboda kuma ina ƙaunarku, zan ba da mutane a maimakonku, al’umma kuma domin ranku. Kada ku ji tsoro, gama ina tare da ku; zan kawo yaranku daga gabas in kuma tattara ku daga yamma. Zan ce wa arewa, ‘Ku miƙa su!’ Ga kudu kuma, ‘Kada ku riƙe su.’ Kawo ’ya’yana maza daga nesa ’ya’yana mata kuma daga iyakar duniya, kowa da ake kira da sunana, wanda aka halitta saboda ɗaukakata, wanda na siffanta na kuma yi.” Jagoranci waɗanda suke da idanu amma suke makafi, waɗanda suke da kunnuwa amma suke kurame. Dukan al’ummai su taru mutane kuma su tattaru. Wane ne a cikinsu ya yi faɗar wannan ya kuma yi mana shelar abubuwan da suka riga suka faru? Bari su kawo shaidunsu don su tabbatar cewa sun yi daidai, don waɗansu su ji su kuma ce, “Gaskiya ne.” “Ku ne shaiduna,” in ji Ubangiji, “bawana kuma wanda na zaɓa, saboda ka sani ka kuma gaskata ni ka kuma fahimci cewa ni ne shi. Kafin ni babu allahn da aka siffanta, ba kuwa za a yi wani a bayana ba. Ni kaɗai, ni ne Ubangiji, kuma in ban da ni babu wani mai ceto. Na bayyana na ceci na kuma furta, Ni ne, ba wani baƙon allah a cikinku. Ku ne shaiduna,” in ji Ubangiji, “cewa ni ne Allah. I, kuma tun fil azal ni ne shi. Babu wani da zai amshi daga hannuna. Sa’ad da na aikata, wa zai iya sauyawa?” Ga abin da Ubangiji yana cewa, Mai Fansarku, Mai Tsarkin nan na Isra’ila, “Saboda ku zan aika Babilon in kawo dukan Babiloniyawa kamar masu gudun hijira, a cikin jiragen ruwa waɗanda suke taƙama da su. Ni ne Ubangiji, Mai Tsarkin nan, Mahaliccin Isra’ila, Sarkinku.” Ga abin da Ubangiji yana cewa, shi da ya yi hanya ta cikin teku, hanya ta cikin manyan ruwaye, wanda ya ja kekunan yaƙi da dawakai, mayaƙa da kuma ƙarin mayaƙa tare ya kwantar da su a can, ba kuwa za su ƙara tashi ba, ya kashe hayaƙi daga lagwani, “Ku manta da abubuwan da suka riga suka faru; kada ku yi tunanin abin da ya riga ya wuce. Duba, ina yi abu sabo! Yanzu yana faruwa; ba ku gan shi ba? Ina yin hanya a cikin hamada rafuffuka kuma a cikin ƙeƙasasshiyar ƙasa. Namun jeji suna girmama ni, diloli da mujiyoyi ma haka, domin na tanada musu ruwa a hamada da rafuffuka a ƙeƙasasshiyar ƙasa, don a ba da abin sha ga mutanena, zaɓaɓɓuna, mutanen da na yi saboda kaina don su furta yabona. “Duk da haka ba ku kira bisa sunana ba, ya Yaƙub, ba ku gajiyar da kanku saboda ni ba, ya Isra’ila. Ba ku kawo mini tumaki don hadaya ta ƙonewa ba, balle ku girmama ni da hadayunku. Ban nawaita muku da hadaya ta gari ba balle in gajiyar da ku da bukatar turare. Ba ku saya wani turaren kalamus domina ba ko ku gamshe ni da kitsen hadayunku. Amma kun nawaita ni da zunubanku kuka kuma gajiyar da ni da laifofinku. “Ni kaɗai ne na shafe laifofinku, saboda sunana, ban kuma ƙara tunawa da zunubanku ba. Ku tunashe ni abin da ya riga ya wuce, bari mu yi muhawwara wannan batu tare; ku kawo hujjarku na nuna rashin laifinku. Mahaifinku na farko ya yi zunubi; masu magana a madadinku suka yi mini tayarwa. Saboda haka zan kunyata manyan baƙi na haikalinku, zan tura Yaƙub ga hallaka Isra’ila kuwa yă zama abin dariya. “Amma yanzu ka saurara, ya Yaƙub, bawana, Isra’ila, wanda zaɓa. Ga abin da Ubangiji yana cewa, shi wanda ya yi ka, wanda ya siffanta ka a cikin mahaifa, wanda kuma zai taimake ka. Kada ka ji tsoro, ya Yaƙub, bawana, Yeshurun, wanda na zaɓa. Gama zan zuba ruwa a ƙeƙasasshiyar ƙasa, rafuffuka kuma a busasshiyar ƙasa; zan ba da Ruhuna ga ’ya’yanka, albarkata kuma ga zuriyarka. Za su tsiro kamar ciyawa a wuriyar ruwa, kamar kurmi kusa da rafuffuka masu gudu. Wani zai ce, ‘Ni na Ubangiji ne’; wani kuma zai kira kansa da sunan Yaƙub; har yanzu wani zai rubuta a hannunsa, ‘Na Ubangiji,’ ya kuma ɗauki sunan Isra’ila. “Ga abin da Ubangiji yana cewa, Sarki da kuma Mai Fansar Isra’ila, Ubangiji Maɗaukaki. Ni ne farko ni ne kuma ƙarshe; in ban da ni babu wani Allah. Wane ne kuwa kama da ni? Ya faɗa a ji. Bari yă yi shela ya kuma nuna shi a gabana mene ne ya faru tun da na kafa mutanena na dā, mene ne kuma bai riga ya faru ba, I, bari yă faɗa abin da zai zo. Kada ku firgita kada kuma ku ji tsoro. Ban furta wannan na kuma yi faɗar haka tuntuni ba? Ku ne shaiduna. Akwai wani Allah in ban da ni? A’a, babu wani Dutse; ban san da wani ba.” Duk masu yin gumaka ba kome ba ne, da kuma abubuwan da suke ɗauka da daraja banza ne. Waɗanda za su yi magana a madadinsu makafi ne; jahilai ne, marasa kunya. Waɗanda suke siffanta allah su kuma yi zubin gunki, waɗanda ba za su yi musu ribar kome ba? Shi da irinsa za su sha kunya; masu sassaƙa ba kome ba mutane ne kurum. Bari su tattaru su ɗauki matsayinsu; za su firgita su kuma sha mummunan kunya. Maƙeri yakan ɗauki kayan aiki ya yi aiki da shi a cikin garwashi; ya ƙera gunki da guduma, ya gyara shi da hannuwansa masu ƙarfi. Yakan ji yunwa ya kuma rasa ƙarfi; yakan sha ruwa ya kuma ji gajiya. Kafinta yakan gwada katako yă kuma zāna siffar da alli; yă goge shi da kayan aiki yă kuma zāna shi da alƙalami. Yă siffanta shi a kamannin mutum, mutum cikin dukan darajarsa, don yă ajiye shi a cikin masujada. Yakan ka da itacen saifires, ko kuwa ya ɗauki saifires ko oak. Yă bar shi yă yi girma a cikin itatuwan kurmi, ko yă shuka itacen fir, ruwan sama kuma yă sa yă yi girma. Abin hura wutar mutum ne; yakan ɗebi waɗansu yă hura wuta don yă ji ɗumi, ya hura wuta yă gasa burodi. Amma yakan ƙera zinariya yă kuma yi masa sujada; yakan yi gunki sa’an nan yă rusuna masa. Rabin katakon yakan ƙone a wuta; a kansa yakan dafa abincinsa, yă gasa namansa yă kuma ci sai ya ƙoshi. Yakan ji ɗumi yă kuma ce, “Aha! Na ji ɗumi; na gan wutar.” Da sauran itacen yakan yi allah, gunkinsa; yă rusuna masa yă kuma yi sujada. Yakan yi masa addu’a yă ce, “Ka cece ni; kai ne allahna.” Ba su san kome ba, ba su fahimci kome ba; an rufe idanunsu don kada su gani, tunaninsu kuma a rufe don kada su fahimta. Ba wanda yakan dakata ya yi tunani, ba wanda yake da sani ko fahimi ya ce, “Da rabinsa na yi amfani da shi don hura wuta; na ma gasa burodi a kan garwashinsa, na gasa nama na kuma ci. Ya kamata in yi abin ƙyama daga abin da ya rage? Ya kamata in rusuna wa guntun katako?” Yana cin toka, zuciyar da ta ruɗe tana ɓad da shi; ba zai iya cece kansa ba, ko ya ce, “Wannan abin da yake hannun dama na ba ƙarya ba ne?” “Tuna da waɗannan abubuwa, ya Yaƙub, gama kai bawana ne, ya Isra’ila. Na yi ka, kai bawana ne; Ya Isra’ila, ba zan manta da kai ba. Na shafe laifofinka kamar girgije, zunubanka kamar hazon safe. Ka komo wurina, gama na kuɓutar da kai.” Ku rera don farin ciki, ya sammai, gama Ubangiji ya aikata wannan; ku yi sowa, ya duniya a ƙarƙashi. Ku ɓarke da waƙoƙi, ku duwatsu, ku jeji da dukan itatuwanku, gama Ubangiji ya kuɓutar da Yaƙub, ya nuna ɗaukakarsa a cikin Isra’ila. “Ga abin da Ubangiji yana cewa, Mai Fansarka, wanda ya yi ka a cikin mahaifa. “Ni ne Ubangiji, wanda ya yi dukan abubuwa, wanda ya shimfiɗa sammai ya kuma kafa harsashen duniya da kansa, wanda ya sassāke alamun annabawan ƙarya ya masu duba suka zama wawaye, wanda ya tumɓuke koyon masu hikima ya mai da shi banza, wanda ya tabbatar da maganganun bayinsa ya kuma cika annabce-annabcen ’yan aikansa, “wanda ya ce game da Urushalima, ‘Za a zauna a cikinta,’ game da garuruwan Yahuda, ‘Za a gina su,’ wanda ya ce wa zurfin ruwaye, ‘Ku bushe, zan kuma busar da rafuffukanku,’ wanda ya yi zancen Sairus ya ce, ‘Shi ne makiyayina zan kuma cika dukan abin da na gan dama; zai yi zancen Urushalima cewa, “Bari a sāke gina ta,” game da haikali kuma cewa, “Bari a kafa harsashinsa.” ’ “Ga abin da Ubangiji ya faɗa wa shafaffensa, ga Sairus, wanda hannun damansa yana riƙe da shi don yă ci al’ummai a gabansa ya kuma tuɓe makaman sarakuna, don yă buɗe ƙofofi a gabansa don kada a kulle ƙofofi. Zan sha gabanka in baje duwatsu; zan farfashe ƙofofin tagulla in kuma kakkarye ƙyamaren ƙarfe. Zan ba ka dukiyar duhu, arzikin da aka ajiye a asirtattun wurare, saboda ka san cewa ni ne Ubangiji, Allah na Isra’ila, wanda ya kira ka da suna. Saboda sunan Yaƙub bawana, Isra’ila zaɓaɓɓena, na kira ka da suna na ba ka matsayin bangirma, ko da yake ba ka san ni ba. Ni ne Ubangiji, kuma babu wani; in ban da ni babu wani Allah. Zan ƙarfafa ka, ko da yake ba ka san ni ba, saboda daga fitowar rana har zuwa fāɗuwarta mutane za su san cewa babu wani in ban da ni. Ni ne Ubangiji, kuma babu wani. Ni ne na siffanta haske na kuma halicci duhu, ni ne nake ba da nasara in kuma jawo bala’i; ni, Ubangiji ne ke aikata dukan waɗannan abubuwa. “Ku sammai, ku sauko da adalci kamar ruwan sama; bari gizagizai su zubar da yayyafi kamar adalci. Bari ƙasa ta buɗe, bari ceto ya tsiro, bari adalci ya yi girma tare da shi; ni, Ubangiji ne, na sa ya faru. “Kaitonka mai gardama da Wanda ya yi ka, da wanda yake kasko a cikin kasko a ƙasa. Yumɓu ya iya ce wa magini, ‘Me kake yi?’ Aikinka na iya cewa, ‘Ba shi da hannuwa’? Kaiton wanda yake cewa mahaifinsa, ‘Me ka manta?’ Ko kuwa ga mahaifiyarsa, ‘Me kin haifa?’ “Ga abin da Ubangiji yana cewa, Mai Tsarkin nan na Isra’ila, da kuma Mahaliccinsa. Game da abubuwan da ke zuwa, kun tambaye ni game da ’ya’yana, ko kuwa kun ba ni umarni game da aikin hannuwana? Ai, ni ne wanda ya yi duniya na kuma halicci mutum a kanta. Hannuwana ne sun miƙe sammai; na umarci rundunar sararin sama. Zan tā da Sairus cikin adalcina. Zan sa dukan hanyoyinsa su miƙe. Zai sāke gina birnina ya kuma ’yantar da mutanena masu bautar talala, amma ba don wata haya ko lada ba, in ji Ubangiji Maɗaukaki.” Ga abin da Ubangiji yana cewa, “Kayayyakin Masar da hajar Kush, da waɗannan dogayen Sabenawa, za su ƙetaro zuwa wurinku za su kuma zama naku; za su bi bayanku, suna zuwa cikin sarƙoƙi. Za su rusuna a gabanku su roƙe ku, suna cewa, ‘Tabbas Allah yana tare da ku, babu kuma wani; babu wani allah.’ ” Tabbatacce kai ne Allah wanda ya ɓoye kanka, Ya Allah da Mai Ceton Isra’ila. Dukan masu yin gumaka za su sha kunya; za su fita da kunya gaba ɗaya. Amma Ubangiji zai ceci Isra’ila da madawwamin ceto; ba za ku sāke shan kunya ko ƙasƙanci ba, har abada. Gama ga abin da Ubangiji yana cewa, shi da ya halicci sammai, shi ne Allah; shi da ya sarrafa ya kuma yi duniya, ya kafa ta; bai halicce ta don ta zama ba kome ba, amma ya yi ta don a zauna a ciki, ya ce, “Ni ne Ubangiji, kuma babu wani. Ban yi magana asirce ba, daga wani wuri a ƙasar duhu ba; ban faɗa wa zuriyar Yaƙub, ‘Ku neme ni a banza ba.’ Ni, Ubangiji maganar gaskiya nake yi; na furta abin da yake daidai. “Ku tattaru ku zo; ku taru, ku masu gudun hijira daga al’ummai. Masu jahilci ne waɗanda suke ɗaukan gumakan katakai suna yawo, waɗanda suke addu’a ga allolin da ba za su cece su ba. Furta abin da zai kasance, ku gabatar da shi, bari su yi shawara tare. Wa ya faɗa wannan tuntuni, wa ya yi shelar sa a kwanakin dā? Ba ni ba ne, Ubangiji? Kuma babu Allah in ban da ni, Allah mai adalci da kuma Mai Ceto; babu wani sai ni. “Ku juyo gare ni ku sami ceto, dukanku iyakokin duniya; gama ni ne Allah, kuma babu wani. Da kaina na rantse, bakina ya furta cikin dukan mutunci kalmar da ba za a janye ba. A gabana kowace gwiwa za tă durƙusa; ta wurina kowane harshe zai rantse. Za su yi zance game da ni su ce, ‘A cikin Ubangiji kaɗai akwai adalci da kuma ƙarfafawa.’ ” Duk wanda ya yi fushi da shi zai zo wurinsa ya kuma sha kunya. Amma a cikin Ubangiji dukan zuriyar Isra’ila za su sami adalci za su kuwa yi yabo. Bel ya rusuna, Nebo ya durƙusa ƙasa; ana ɗaukan gumakansu a kan dabbobi ne. Siffofin da ake yawo da su nawaya ne, kayan nauyi masu gajiyarwa. Sun durƙusa suka kuma rusuna tare; ba su iya kuɓutar da nauyin kaya su kansu sukan tafi bauta. “Ku kasa kunne gare ni, ya ku gidan Yaƙub, dukanku waɗanda kuka rage na gidan Isra’ila, ku da na lura da ku tun da aka yi cikinku, na kuma riƙe ku tun haihuwarku. Har lokacin da kuka tsufa kuka yi furfura ni ne shi, ni ne shi wanda zai lura da ku. Na yi ku zan kuma riƙe ku; zan lura da ku in kuma kuɓutar da ku. “Da wa za ku kwatanta ni ko ku ɗauka daidai da ni? Da wa nake kama da har da za ku kwatanta ni? Waɗansu sukan zubar da zinariya daga jaka su kuma auna azurfa a ma’auni; sukan yi haya maƙerin zinariya don yă ƙera allah, su kuma rusuna su yi masa sujada. Sukan daga shi a kafaɗunsu su kuma ɗauke shi; sukan kafa shi a tsaye a wurinsa, a can kuwa zai tsaya. Daga wannan wuri ba zai iya gusawa ba. Ko da wani ya nemi taimakonsa, ba ya amsawa; ba zai iya cetonsa daga wahala ba. “Ku tuna da wannan, ku sa shi a zuciya, ku riƙe shi a zuciya, ku ’yan tawaye. Ku tuna da abubuwan da suka riga suka faru, waɗannan na tun dā; ni ne Allah, kuma babu wani; ni ne Allah kuma babu wani kamar ni. Nakan sanar da ƙarshe tun daga farko, daga fil azal, abin da yake zuwa nan gaba. Na ce nufina zai tabbata, kuma zan aikata dukan abin da na gan dama. Daga gabas na kira tsuntsun da yake farauta; daga can ƙasa mai nesa, wani mutumin da zai cika nufina. Abin da na riga na faɗa, shi zan sa ya faru; abin da na shirya, shi zan aikata. Ku kasa kunne, ku masu taurinkai, ku da kuke nesa da adalci. Ina kawo adalcina kusa, ba shi da nisa; kuma cetona ba zai jinkirta ba. Zan yi wa Sihiyona ceto, darajata ga Isra’ila. “Ki gangara, ki zauna a ƙura, Budurwa Diyar Babilon; ki zauna a ƙasa ba tare da rawani ba, Diyar Babiloniyawa. Ba za a ƙara kira ke marar ƙarfi ’yar gata ba. Ɗauki dutsen niƙa ki niƙa gari; ki kware lulluɓinki. Ki ɗaga fatarinki ki bar ƙafafunki tsirara, ki kuma yi ta ratsa cikin rafuffuka. Tsirararki zai bayyana za a kuma buɗe kunyarki. Zan ɗauki fansa; ba zan bar wani ba.” Mai Fansarmu, Ubangiji Maɗaukaki shi ne sunansa, shi ne Mai Tsarkin nan na Isra’ila. “Zauna shiru, tafi cikin duhu, Diyar Babiloniya; ba za a ƙara kira ke sarauniyar masarautai. Na yi fushi da mutanena na ƙazantar da gādona; na ba su ga hannunki, ba ki kuwa nuna musu jinƙai ba. Har ma da tsofaffi kin jibga musu kaya masu nauyi sosai. Kika ce, ‘Zan ci gaba har abada, madawwamiyar sarauniya!’ Amma ba ki lura da waɗannan abubuwa ko ki yi la’akari a kan abin da zai faru ba. “To, yanzu fa, ki kasa kunne, ke mai ƙaunar nishaɗi, mai zama da rai kwance kina kuma ce wa kanki, ‘Ni ce, kuma babu wani in ban da ni. Ba zan taɓa zama gwauruwa ko in sha wahalar rashin ’ya’ya ba.’ Duk waɗannan za su sha kanki cikin farat ɗaya, a rana guda, rashin ’ya’ya da gwauranci. Za su zo a kanki da cikakken minzani, duk da yawan masu dubanki da kuma dukan sihirinki. Kin dogara a muguntarki kika kuma ce, ‘Babu wanda ya gan ni.’ Hikimarki da saninki sun ɓad da ke sa’ad da kika ce wa kanki, ‘Ni ce, kuma babu wani in ban da ni.’ Bala’i zai fāɗo a kanki, kuma ba za ki san yadda za ki rinjaye shi yă janye ba. Masifa za tă fāɗo a kanki da ba za ki iya tsai da ita da kuɗin fansa ba; lalacewar da ba ki taɓa mafarkinta ba za tă auko miki nan da nan. “Ki dai ci gaba, da sihirinki da kuma makarunki masu yawa, waɗanda kika yi ta wahala tun kina jaririya. Mai yiwuwa ki yi nasara, mai yiwuwa ki jawo fargaba. Dukan shawarwarin da kika samu sun dai gajiyar da ke ne kawai! Bari masananki na taurari su zo gaba, waɗannan masu zāna taswirar sammai suna kuma faɗa miki dukan abin da zai faru da ke wata-wata, bari su cece ki daga abin da zai faru da ke. Tabbas suna kama da bunnu; wuta za tă cinye su ƙaf. Ba za su ma iya ceton kansu daga ikon wutar ba. Ba wutar da wani zai ji ɗumi; ba wutar da za a zauna kusa da ita. Abin da za su iya yi miki ke nan kawai, waɗannan da kika yi ta fama da su kika kuma yi ciniki da su tun kina jaririya. Kowannensu zai tafi cikin kuskurensa; babu ko ɗayan da zai cece ki. “Ku kasa kunne ga wannan, ya gidan Yaƙub, waɗanda ake kira da sunan Isra’ila suka kuma fito daga zuriyar Yahuda, ku da kuke yin rantsuwa da sunan Ubangiji kuna kuma kira sunan Allah na Isra’ila, amma ba da gaskiya ko adalci ba, ku da kuke kiran kanku ’yan ƙasar birni mai tsarki kuna kuma dogara ga Allah na Isra’ila, Ubangiji Maɗaukaki ne sunansa, na nanata abubuwan da suka riga suka faru tuntuni, bakina ya yi shelar su na kuma sanar da su; sai nan da nan na aikata, suka kuma faru. Gama na san yadda kuke da taurinkai; jijiyoyin wuyanku ƙarafa ne, goshinku tagulla ne. Saboda haka na faɗa waɗannan abubuwa tuntuni; kafin su faru na yi shelarsu gare ku saboda kada ku ce, ‘Gumakana ne suka yi su; siffar itacena da allahn zinariyana ne ya ƙaddara su.’ Kun riga kun ji waɗannan abubuwa; kuka gan su duka. Ba za ku yarda da su ba? “Daga yanzu zuwa gaba zan faɗa muku sababbin abubuwa, na ɓoyayyun abubuwan da ba ku sani ba. Yanzu an halicce su, ba da daɗewa ba; ba ku riga kun ji game da su kafin yau ba. Saboda haka ba za ku ce, ‘I, na san da su ba.’ Ba ku ji ko balle ku gane ba; tun da kunnenku bai buɗu ba. Tabbatacce na san yadda kun zama masu tayarwa; an kira ku ’yan tawaye daga haihuwa. Saboda girman sunana na jinkirta fushina; saboda girman yabona na janye shi daga gare ku, don dai kada a yanke ku. Duba, na tace ku, ko da yake ba kamar azurfa ba; na gwada ku cikin wutar wahala. Saboda girmana, saboda girmana, na yi haka. Yaya zan ƙyale a ƙazantar da kaina? Ba zan raba ɗaukakata da wani ba. “Ka kasa kunne gare ni, ya Yaƙub, Isra’ila, wanda na kira cewa, Ni ne shi; ni ne na farko ni ne kuma na ƙarshe. Hannuna ne ya kafa harsashen duniya, hannuna na dama kuma ya shimfiɗa sammai; sa’ad da na kira su, duka suka miƙe tsaye gaba ɗaya. “Ku tattaru, dukanku ku kuma saurara, Wanne a cikin gumakan ya iya faɗa waɗannan abubuwa? Zaɓaɓɓen da Ubangiji yake ƙauna zai aikata nufinsa a kan Babilon; hannunsa zai yi gāba da Babiloniyawa. Ni kaina, na faɗa; I, na kira shi. Zan kawo shi, zai kuma yi nasara a cikin aikinsa. “Ku zo kusa da ni ku kuma saurari wannan. “Daga farkon shela ban yi magana a ɓoye ba; a lokacin da ya faru, ina nan a wurin.” Yanzu kuwa Ubangiji Mai Iko Duka ya aiko ni, da Ruhunsa. Ga abin da Ubangiji yana cewa, Mai Fansarku, Mai Tsarkin nan na Isra’ila ya ce, “Ni ne Ubangiji Allahnku, wanda ya koya muku abin da ya fi muku kyau, wanda ya muku hanyar da za ku bi. Da a ce kawai za ku mai da hankali ga umarnaina, da salamarku ta zama kamar kogi, adalcinku kamar raƙuman teku. Da zuriyarku ta zama kamar yashi, ’ya’yanku kamar tsabar hatsin da ba a iya ƙidayawa; da ba za a taɓa yanke sunansu balle a hallaka su daga gabana ba.” Ku bar Babilon, ku gudu daga Babiloniyawa! Ku yi shelar wannan da sowa ta farin ciki ku kuma furta shi. Ku aika shi zuwa iyakokin duniya; ku ce, “ Ubangiji ya fanshi bawansa Yaƙub.” Ba su ji ƙishi ba sa’ad da ya bishe su a cikin hamada; ya sa ruwa ya malalo dominsu daga dutse; ya tsage dutse ruwa kuwa ya kwararo. “Babu salama ga mugaye” in ji Ubangiji. Ku kasa kunne gare ni, ku tsibirai; ku ji wannan, ku al’ummai masu nesa. Kafin a haife Ni Ubangiji ya kira ni; tun daga haihuwata ya ambaci sunana. Ya yi bakina kamar takobi mai kaifi, cikin inuwar hannunsa ya ɓoye ni; ya sa na zama kamar kibiya mai tsini ya kuma ɓoye ni cikin kwarinsa. Ya ce mini, “Kai bawana ne, Isra’ila, a cikinka zan bayyana darajata.” Amma na ce, “Na yi aiki a banza; na kashe duk ƙarfina a banza da wofi. Duk da haka abin da yake nawa yana a hannun Ubangiji, ladana kuma tana a wurin Allahna.” Yanzu fa Ubangiji ya ce ya siffanta ni a cikin mahaifa don in zama bawansa don in dawo da Yaƙub gare shi in kuma tattara Isra’ila gare shi, gama an girmama ni a gaban Ubangiji Allahna kuma ne ƙarfina ya ce, “Ɗan ƙaramin abu ne ka zama bawana don ka maido da kabilar Yaƙub ka kuma dawo da waɗannan na Isra’ilawan da na kiyaye. Zan kuma mai da kai haske ga Al’ummai, don ka kawo cetona zuwa iyakokin duniya.” Ga abin da Ubangiji yana cewa, Mai Fansa da kuma Mai Tsarkin nan na Isra’ila gare shi wanda al’ummai suka rena suka kuma ki, ga bawan masu mulki. “Sarakuna za su gan ka su kuma miƙe tsaye, sarakuna za su gani su kuma rusuna, saboda Ubangiji, wanda yake mai aminci, Mai Tsarkin nan na Isra’ila, wanda ya zaɓe ka.” Ga abin da Ubangiji yana cewa, “A lokacin tagomashina zan amsa muku, kuma a ranar ceto zan taimake ku; zan kiyaye ku zan kuma sa ku zama alkawari ga mutane, don ku maido da ƙasa ku kuma sāke raba gādon kufai, don ku ce wa waɗanda suke cikin kurkuku, ‘Ku fito,’ ga waɗanda suke cikin duhu kuma, ‘Ku ’yantu!’ “Za su yi kiwo kusa da hanyoyi su kuma sami wurin kiwo a kowane tudu. Ba za su taɓa jin yunwa ko ƙishi ba, ba kuwa zafin hamada ko rana ta buge su ba. Shi da ya yi musu jinƙai zai jagorance su ya kuma bishe su kusa da maɓulɓulan ruwa. Zan mayar da dukan duwatsu su zama hanyoyi, a kuma gyara manyan hanyoyina. Duba, za su zo daga nesa waɗansu daga arewa, waɗansu daga yamma, waɗansu daga yankin Aswan.” Ku yi sowa don farin ciki, ya ku sammai; ki yi farin ciki, ya ke duniya; ku ɓarke da waƙa, ya ku duwatsu! Gama Ubangiji ya ta’azantar da mutanensa zai kuma ji tausayin mutanensa da suke shan wahala. Amma Sihiyona ta ce, “ Ubangiji ya yashe ni, Ubangiji ya manta da ni.” “Yana yiwuwa mahaifiya ta manta da jariri a ƙirjinta ta kuma kāsa nuna tausayi ga yaron da ta haifa? Mai yiwuwa ta manta, amma ba zan taɓa manta da ke ba! Duba, na zāna ki a tafin hannuwana; katangarki kullum suna a gabana. ’Ya’yanki maza su komo da gaggawa, waɗanda suka lalatar da ke kuwa za su bar ki. Ki ɗaga idanunki ki duba kewaye; dukan ’ya’yanki sun taru suka kuma dawo gare ki. Muddin ina raye,” in ji Ubangiji, “Za ki yafa su duka kamar kayan ado; za ki yi ado da su, kamar amarya. “Ko da yake an lalatar da ke aka kuma mai da ke kufai ƙasarki kuma ta zama kango, yanzu za ki kāsa sosai saboda yawan mutanenki, kuma waɗanda suka cinye ki za su kasance can da nisa. ’Ya’yan da aka haifa a lokacin baƙin cikinki za su ce a kunnenki, ‘Wannan wuri ya yi mana kaɗan ƙwarai; ki ƙara mana wurin zama.’ Sa’an nan za ki ce a zuciyarki, ‘Wa ya haifa waɗannan? Na yi baƙin ciki na kuma zama wadda ba ta haihuwa; an yi mini daurin talala aka kuma ƙi ni. Wane ne ya yi renon waɗannan? An bar ni ni kaɗai, amma waɗannan, ina suka fito?’ ” Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka ya ce, “Duba, zan yi alama wa Al’ummai, zan ɗaga tutana wa mutane; za su kawo ’ya’yanki maza a hannuwansu su riƙe ’ya’yanki mata a kafaɗunsu. Sarakuna za su zama kamar iyayen reno, sarauniyoyinsu kuma za su yi renonku kamar uwaye. Za su rusuna a gabanki da fuskokinsu har ƙasa; za su lashe ƙura a ƙafafunki. Sa’an nan za ki san cewa ni ne Ubangiji; waɗanda suke sa zuciya gare ni ba za su sha kunya ba.” Za a iya ƙwace ganima daga jarumawa, ko a kuɓutar da kamammu daga hannun marasa tsoro? Amma ga abin da Ubangiji yana cewa, “I, za a ƙwace kamammu daga jarumawa, a kuma karɓe ganima daga hannun marasa tsoro; zan gwabza da waɗanda suke gwabzawa da ke, zan kuwa ceci ’ya’yanki. Zan sa masu zaluntarki su ci naman jikinsu; za su bugu da jininsu, sai ka ce sun sha ruwan inabi. Sa’an nan dukan mutane za su sani cewa ni, Ubangiji, ni ne Mai Cetonki, Mai Fansarki, Maɗaukakin nan na Yaƙub.” Ga abin da Ubangiji yana cewa, “Ina takardar shaida na saki mahaifiyarka daga aure wadda na kora? Ko kuwa ga wanda mutumin da nake bin bashi ne na sayar da kai? Saboda zunubanka aka sayar da kai; saboda laifofinka ne ya sa aka kori mahaifiyarka. Sa’ad da na zo, me ya sa babu kowa? Sa’ad da na yi kira, me ya sa babu wani da ya amsa? Hannuna ya kāsa ne sosai don fansarka? Na rasa ƙarfin kuɓutar da kai ne? Ta wurin tsawatawa kawai na busar da teku, na mai da koguna hamada; kifayensu duk sun ruɓe saboda rashin ruwa suka kuma mutu saboda ƙishi. Na suturar da sararin sama da duhu na kuma mai da tsummoki abin rufuwarsa.” Ubangiji Mai Iko Duka ya ba ni harshen umarni, don in san maganar da za tă ƙarfafa gajiyayye. Ya farkar da ni da safe, ya farkar da kunnena don in saurara kamar wanda ake koya masa. Ubangiji Mai Iko Duka ya buɗe kunnuwana, kuma ban yi tayarwa ba; ban ja da baya ba. Na ba da bayana ga masu dūkana, kumatuna ga masu jan gemuna; ban ɓoye fuskata daga masu ba’a da masu tofa mini miyau ba. Gama Ubangiji Mai Iko Duka zai taimake ni, ba zan sha kunya ba. Saboda haka na kafa fuskata kamar dutsen ƙanƙara, na kuma sani ba zan sha kunya ba. Gama shi da zai tabbatar da ni, marar laifi ne yana kusa. Wane ne zai kawo ƙararraki game da ni? Bari mu je ɗakin shari’a tare! Wane ne mai zargina? Bari yă kalubalance ni! Ubangiji Mai Iko Duka ne zai taimake ni. Wane ne zai iya tabbatar da ni mai laifi? Duk za su koɗe kamar riga; asu za su cinye su. Wane ne a cikinku yake tsoron Ubangiji yana kuma yin biyayya ga maganar bawansa? Bari wanda yake tafiya cikin duhu, wanda ba shi da haske, ya dogara a sunan Ubangiji ya kuma dogara ga Allahnsa. Amma yanzu fa, dukanku waɗanda kuke ƙuna wuta kuna kuma tanada wa kanku fitilu masu ci, ku je ku yi tafiya a cikin hasken wutarku da na fitilun da kuka ƙuna. Abin da za ku karɓa ke nan daga hannuna. Za ku kwanta a cikin azaba. “Ku kasa kunne gare ni, ku da kuna neman adalci kuke kuma neman Ubangiji. Dubi dutse daga inda aka yanke ku da kuma mahaƙar duwatsu inda aka fafe ku; dubi Ibrahim, mahaifinku, da Saratu, wadda ta haife ku. Sa’ad da na kira shi kaɗai ne, na kuma albarkace shi na kuma mai da shi da yawa. Tabbatacce Ubangiji zai ta’azantar da Sihiyona zai kuma duba da tausayi a kan dukan kufanta; zai sa hamadanta ta zama kamar Eden, ƙeƙasasshiyar ƙasarta kamar lambun Ubangiji. Za a sami farin ciki da murna a cikinta, godiya da ƙarar rerawa. “Ku kasa kunne gare ni, mutanena; ku ji ni, al’ummata. Doka za tă fito daga gare ni; shari’ata za tă zama haske ga al’ummai. Adalcina na zuwa da sauri, cetona yana a kan hanya, hannuna kuma zai kawo adalci ga al’ummai. Tsibirai za su dube ni su kuma jira da sa zuciya don hannuna. Ku daga idanunku zuwa sammai ku dubi duniya a ƙasa; sammai za su ɓace kamar hayaƙi, duniya za tă shuɗe kamar riga mazaunanta kuma su mutu kamar ƙudaje. Amma cetona zai dawwama har abada, adalcina ba zai taɓa kāsa ba. “Ku ji ni, ku da kuka san abin da yake daidai, ku mutanen da kuke da dokata a zukatanku. Kada ku ji tsoron ba’ar da mutane suke yi ko ku firgita saboda zargin da suke yi. Gama asu za su cinye su kamar riga; tsutsotsi za su cinye su kamar ulu. Amma adalcina zai dawwama har abada, cetona har dukan zamanai.” Ka tashi, ka tashi! Ka yafa wa kanka ƙarfi, Ya hannun Ubangiji; ka farka, kamar a kwanakin da suka wuce, kamar a zamanai na dā. Ba kai ba ne wanda ya yayyanka Rahab gunduwa-gunduwa, wanda ya soki dodon ruwan nan? Ba kai ba ne ka busar da teku, ka busar da ruwan zurfafa masu girma, wanda ya yi hanya a cikin zurfafan teku saboda fansassu su ƙetare? Waɗanda Ubangiji ya fansar za su dawo. Za su shiga Sihiyona da waƙoƙi; madawwamin farin ciki zai rufe kansu da rawani. Murna da farin ciki zai cika su, baƙin ciki da nishi zai ɓace. “Ni kaɗai ne na ta’azantar da ku. Wane ne ku da kuke tsoron mutane masu mutuwa, ’ya’yan mutane waɗanda suke ciyawa ne kawai, har da kuka manta da Ubangiji Mahaliccinku, wanda ya shimfiɗa sammai ya kuma kafa harsashen duniya, har kuna zama da tsoro kowace rana saboda fushin masu zalunci, waɗanda sun ƙudura sai sun hallaka? Gama ina fushin mai zalunci? Ba da daɗewa za a ’yantar da ’yan kurkuku; ba za su mutu a kurkuku ba, ba kuwa za su rasa abinci ba. Gama ni ne Ubangiji Allahnku, wanda ya dama teku domin raƙumansa su yi ruri, Ubangiji Maɗaukaki ne sunansa. Na sa maganata a bakinka na kuma rufe ka da inuwar hannuna, Na shimfiɗa sammai, na kafa harsashen duniya, na kuma ce wa Sihiyona, ‘Ku mutanena ne.’ ” Ki farka, ki farka! Ki tashi, ya Urushalima, ke da kika sha daga hannun Ubangiji kwaf na fushinsa, ke da kika shanye har ƙasar kwaf kwaf da ya sa mutane suna tangaɗi. Cikin dukan ’ya’yan da ta haifa; cikin dukan ’ya’yan da ta yi reno babu wani da zai kama hannunta. Waɗannan masifu riɓi biyu sun auko miki, wa zai ta’azantar da ke? Lalaci da hallaka, yunwa da takobi, wa zai ƙarfafa ki? ’Ya’yanki sun sume; sun kwanta kusurwar kowane titi, kamar barewar da aka kama da tarko. Sun cika da fushin Ubangiji da kuma tsawatawar Allahnki. Saboda haka ki ji wannan, ke mai wahala, wadda ta bugu, amma ba da ruwan inabi. Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa, Allahnki, wanda ya kāre mutanensa, “Duba, na ƙwace daga hannunki kwaf da ya sa ki tangaɗi; daga wannan kwaf, kwaf na fushina, ba za ki ƙara sha ba. Zan sa shi a hannuwan masu gwada miki azaba, waɗanda suke ce miki, ‘Fāɗi rubda ciki don mu iya taka a kanki.’ Kika kuma mai da bayanki kamar ƙasa, kamar titin da ake takawa a kai.” Ki farka, ki farka, ya Sihiyona, ki sanya wa kanki ƙarfi. Ki sa rigarki na daraja, Ya Urushalima, birni mai tsarki. Marasa kaciya da maƙazanta ba za su shi cikinki ba. Ki kakkaɓe ƙurarki; ki tashi, ki zauna a kursiyinki, ya Urushalima. Ki ’yantar da kanki daga sarƙoƙi a wuyanki, Ke kamammiyar Diyar Sihiyona. Gama ga abin Ubangiji yana cewa, “An sayar da ke ba da kuɗi ba, kuma ba da kuɗi za a fanshe ki ba.” Gama ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa, “Da farko mutanena suka gangara zuwa Masar don su zauna; a baya-bayan nan, Assuriya sun zalunce su. “Yanzu kuma me nake da shi a nan?” In ji Ubangiji. “Gama an kwashe mutanena ba a bakin kome ba kuma waɗanda suka mallake su sun yi musu ba’a, Kullum ana cin gaba da yin wa sunana saɓo. Saboda haka mutanena za su san sunana; saboda haka a wannan rana za su san cewa ni ne wanda ya faɗa wannan. I, ni ne.” Me ya fi wannan kyau a kan duwatsu a ga ƙafafu na masu kawo labari mai daɗi waɗanda suke shelar salama, waɗanda suke kawo labari mai daɗi, waɗanda suke shelar ceto, waɗanda suke ce wa Sihiyona, “Allahnki yana mulki!” Ki kasa kunne! Masu tsaronki sun tā da muryoyinsu; tare sun yi sowa ta farin ciki. Sa’ad da Ubangiji ya komo Sihiyona, za su gan shi da idanunsu. Ku ɓarke cikin waƙoƙin farin ciki gaba ɗaya, kangonki na Urushalima, gama Ubangiji ya ta’azantar da mutanensa, ya fanshi Urushalima. Ubangiji zai nuna hannunsa mai tsarki a fili a idanun dukan al’ummai, da kuma dukan iyakokin duniya za su gani ceton Allahnmu. Ku fita, ku fita daga can! Kada ku taɓa wani abu marar tsarki! Ku fita daga cikinta ku zama da tsarki, ku da kuke ɗaukan kayan aikin Ubangiji. Amma ba za ku fita a gaggauce ba ko ku tafi da gudu; gama Ubangiji zai ja gabanku, Allah na Isra’ila zai kasance mai tsaron bayanku. Duba, bawana zai aikata abubuwa da hikima; za a tā da shi a kuma ɗaga shi da ɗaukaka ƙwarai. Kamar dai yadda aka kasance da mutane masu yawa waɗanda suka giggice sa’ad da suka gan shi, kamanninsa ya lalace ƙwarai fiye da na kowane mutum siffarsa kuma ta yi muni fiye da yadda ta mutum take, haka zai ba al’ummai masu yawa mamaki, sarakuna kuma za su riƙe bakunansu don mamaki. Gama abin da ba a faɗa musu ba, shi za su gani, kuma abin da ba su ji ba, shi za su fahimta. Wa ya gaskata saƙonmu kuma ga wa hannun Ubangiji ya bayyana? Ya yi girma kamar dashe marar ƙarfi, kamar saiwa kuma daga ƙeƙasasshiyar ƙasa. Ba shi da kyan gani ko wani makamin da zai ja hankalinmu, babu wani abin da yake da shi da zai sa mu yi sha’awarsa. Mutane suka rena shi suka ƙi shi, mutum ne cike da baƙin ciki, ya kuma saba da wahala. Kamar wanda mutane suna ɓuya fuskokinsu daga gare shi aka rena shi aka yi banza da shi. Tabbatacce ya ɗauki cututtukanmu ya kuma daure da baƙin cikinmu duk da haka muka ɗauka Allah ya hukunta shi ne, ya buge shi ya kuma sa ya sha azaba. Amma aka yi masa rauni saboda laifofinmu, aka ƙuje shi saboda kurakuranmu; hukuncin da ya kawo mana salama ya kasance a kansa, kuma ta wurin mikinsa ya sa muka warke. Dukanmu, muna kama da tumakin da suka ɓata, kowannenmu ya kama hanyarsa; Ubangiji kuwa ya sa hukunci ya auko a kansa hukuncin da ya wajaba a kanmu. Aka wulaƙanta shi aka kuma yi masa azaba, duk da haka bai buɗe bakinsa ba; aka kai shi kamar ɗan rago zuwa wurin yanka, kuma kamar tunkiya a gaban masu askinta tana shiru, haka bai buɗe bakinsa ba. Da wulaƙanci da kuma hukunci aka ɗauke shi aka tafi. Wa kuwa zai yi maganar zuriyarsa? Gama an kawar da shi daga ƙasar masu rai; saboda laifin mutanena aka kashe shi. Aka yi jana’izarsa tare da mugaye, aka binne shi tare da masu arziki, ko da yake bai taɓa yin wani tashin hankali ba, ko a sami ƙarya a bakinsa. Duk da haka nufin Ubangiji ne a ƙuje shi yă kuma sa yă sha wahala, kuma ko da yake Ubangiji ya sa ransa ya zama hadaya don zunubi, zai ga zuriyarsa zai kuma kawo masa tsawon rai, nufin Ubangiji kuma zai yi nasara a hannunsa. Bayan wahalar ransa, zai ga hasken rai, ya kuma gamsu; ta wurin saninsa bawana mai adalci zai ’yantar da mutane masu yawa, zai kuma ɗauki laifofinsu. Saboda haka zan ba shi rabo tare da manya, zai kuma raba ganima tare da masu ƙarfi, domin ya ba da ransa har mutuwa, aka kuma lissafta shi tare da masu laifofi. Gama ya ɗauki zunubin mutane masu yawa, ya kuma yi roƙo saboda laifofinsu. “Ki rera, ya ke bakararriya, ke da ba ki taɓa haihuwa ba; ki ɓarke da waƙa, ki yi sowa don farin ciki, ke da ba ki taɓa naƙuda ba; domin ’ya’yan mace mai kaɗaici sun fi na mai miji yawa,” in ji Ubangiji. “Ki fadada wurin tentinki, ki miƙe labulen tentinki da fāɗi, kada ki janye; ƙara tsawon igiyoyinta, ki kuma ƙara ƙarfin turakunta. Gama za ki fadada zuwa dama da hagu; zuriyarki za su kori al’ummai su kuma zauna a kufan biranensu. “Kada ki ji tsoro; ba za ki sha kunya ba. Kada ki ji tsoron wulaƙanci, ba za a ƙasƙantar da ke ba. Za ki manta da kunyar ƙuruciyarki ba kuwa za ki tuna da zargin zaman gwauruwarki ba. Gama Mahaliccinki shi ne mijinki, Ubangiji Maɗaukaki ne sunansa, Mai Tsarkin nan na Isra’ila ne Mai Fansarki; ana ce da shi Allahn dukan duniya. Ubangiji zai kira sai ka ce ke mace ce da aka yashe ta tana kuma damuwa a ranta, macen da ta yi aure a ƙuruciya, sai kawai aka ƙi ta,” in ji Allahnki. “Gama a ɗan ƙanƙanen lokaci na rabu da ke, amma da ƙauna mai zurfi zan sāke dawo da ke. Cikin fushi mai zafi na ɓoye fuskata daga gare ki na ɗan lokaci, amma da madawwamin alheri zan ji tausayinki,” in ji Ubangiji Mai Fansarki. “A gare ni wannan ya yi kamar kwanakin Nuhu, sa’ad da na rantse cewa ruwan Nuhu ba za su ƙara rufe duniya ba. Yanzu fa na rantse ba zan yi fushi da ke ba, ba zan ƙara tsawata miki kuma ba. Ko da duwatsu za su girgiza a kuma tumɓuke tuddai, duk da haka madawwamiyar ƙaunata da nake yi miki ba za tă jijjigu ba ba kuwa za a kawar da alkawarin salamata ba,” in ji Ubangiji, wanda ya ji tausayinki. “Ya ke birni mai shan azaba, wadda hadari ya bulale ki ba a kuma ta’azantar da ke ba, zan gina ke da duwatsu turkuwoyis, zan kafa harsashenki da duwatsun saffaya. Zan gina hasumiyarki da jan yakutu, ƙofofinki kuma da duwatsu masu haske, dukan katangarki kuma da duwatsu masu daraja. Ubangiji zai koya wa dukan ’ya’yanki maza, da girma kuma salamar ’ya’yanki zai zama. Da adalci za a kafa ke. Zalunci zai yi nesa da ke; ba za ki kasance da wani abin da za ki ji tsoro ba. Za a kawar da duk wani abin banrazana; ba zai yi kusa da ke ba. In wani ya far miki, ba daga wurina ba ne; duk wanda ya far miki zai miƙa wuya gare ki. “Duba, ni ne wanda na halicci maƙeri wanda yake zuga garwashi ya zama harshen wuta ya kuma ƙera makamin da ya dace da aikinsa. Ni ne kuma na halicci mai hallakarwa ya yi ɓarna; ba makamin da aka ƙera don yă cuce ki da zai yi nasara, za ki kuma mayar da magana ga duk wanda ya zarge ki. Wannan ne gādon bayin Ubangiji, kuma wannan ita ce nasararsu daga gare ni,” in ji Ubangiji. “Ku zo, dukanku masu jin ƙishi, ku zo wurin ruwaye; ku kuma da ba ku da kuɗi, ku zo, ku saya ku kuma ci! Ku zo, ku saya ruwan inabi da madara ba tare da kuɗi ba ba za ku kuma biya kome ba. Don me za ku kashe kuɗi a kan abin da ba abinci ba, ku kuma yi wahala a kan abin da ba za ku ƙoshi ba? Ku saurara, ku saurare ni, ku kuma ci abin da yake da kyau, ranku kuma zai ji daɗin abinci mafi kyau. Ku kasa kunne ku kuma zo gare ni; ku saurare ni, don ranku ya rayu. Zan yi madawwamin alkawari da ku, zan nuna muku ƙaunata marar ƙarewa da na yi wa Dawuda alkawari. Duba, na mai da shi shaida ga mutane, shugaba da kuma jagorar mutane. Tabbatacce za ku kira al’umman da ba ku sani ba, kuma al’umman da ba ku sani ba za su sheƙo a guje zuwa wurinku, saboda Ubangiji Allahnku, Mai Tsarkin nan na Isra’ila, gama ya darjanta ku.” Ku nemi Ubangiji tun yana samuwa; ku yi kira gare shi tun yana kusa. Bari mugu ya bar irin halinsa mugu kuma ya sāke irin tunaninsa. Bari yă juyo ga Ubangiji, zai kuwa ji tausayinsa, ya juyo ga Allahnmu kuma, gama shi mai gafartawa ne a sauƙaƙe. “Gama tunanina ba tunaninku ba ne, yadda kuke yin abubuwa ba yadda nake yin abubuwa ba ne,” in ji Ubangiji. “Kamar yadda sammai suke can nesa da ƙasa, haka yadda nake yin abubuwa suke dabam da yadda kuke yin abubuwa tunanina kuma dabam da naku. Kamar yadda ruwan sama da dusar ƙanƙara suke saukowa daga sama, ba sa komowa ba tare da sun jiƙe duniya sun kuma sa su yi ’ya’ya su kuma yi toho, don su ba da iri ga mai shuki da kuma abinci ga mai ci, haka maganata da take fitowa daga bakina. Ba za tă koma gare ni wofi ba, amma za tă cika abin da nake so ta kuma cika abin da na aike ta tă yi. Za ku fita da farin ciki a kuma bi da ku da salama; duwatsu da tuddai za su ɓarke da waƙa a gabanku, dukan itatuwan jeji kuma za su tafa hannuwansu. A maimakon sarƙaƙƙiya, itacen fir ne zai tsiro, a maimakon ƙayayyuwa kuma, itacen ci-zaƙi ne zai tsiro. Wannan zai zama matuni na abin da Ni Ubangiji na yi, madawwamiyar alama ce, wadda ba za a datse ba.” Ga abin da Ubangiji yana cewa, “Ku riƙe gaskiya ku yi abin da yake daidai, gama cetona yana kusa za a kuma bayyana adalcina nan da nan. Mai albarka ne mutumin da ya aikata wannan, mutumin da ya riƙe kam yana kiyaye Asabbaci ba tare da ƙazantar da shi ba, yana kuma kiyaye kansa daga yin mugun abu.” Kada baƙon da ya miƙa kansa ga Ubangiji ya ce, “Ai Ubangiji zai ware ni daga mutanensa.” Kada kuma wani bābā ya yi gunaguni cewa, “Ni busasshen itace ne kawai.” Gama ga abin da Ubangiji ya faɗa, “Wa bābānnin da suna kiyaye Asabbatai, waɗanda suka zaɓi yin abin da ya gamshe ni suna kuma riƙe da alkawarina kankan, a gare su cikin haikalina da kuma bangayensa zan ba da matuni da kuma suna mafi kyau fiye da ’ya’ya maza da kuma ’ya’ya mata; zan ba su madawwamin sunan da ba za a raba su da shi ba. Baƙin da suka miƙa kansu ga Ubangiji don su bauta masa, su kuma ƙaunaci sunan Ubangiji, waɗanda kuma suke yin masa sujada, duk waɗanda suka kiyaye Asabbaci ba tare da ƙazantar da shi ba suka kuma riƙe alkawarina kankan, waɗannan ne zan kai tsattsarkan dutsena in sa su yi farin ciki a gidana na addu’a. Hadayunsu na ƙonawa da sadakokinsu za su zama abin karɓa a bagadena; gama za a ce da gidana gidan addu’a domin dukan al’ummai.” Ubangiji Mai Iko Duka ya furta cewa, zai tattara korarru na Isra’ila, “Zan ƙara tattaro waɗansu bayan waɗanda na riga na tattara.” Ku zo, dukanku namun jeji, ku zo ku ci, dukanku namun jeji! Matsaran Isra’ila makafi ne, dukansu jahilai ne; dukansu bebayen karnuka ne ba za su iya haushi ba; suna kwance ne kawai suna mafarki, suna son barci ba dama. Su karnuka ne masu kwaɗayi; ba su taɓa ƙoshi. Su makiyaya ne marasa ganewa; duk sun nufi inda suka ga dama, kowa yana nemar wa kansa riba. Kowanne yakan ce, “Zo, bari in samo ruwan inabi! Bari mu cika cikinmu da barasa! Gobe ma zai zama kamar yau, ko ma fiye da haka.” Mai adalci yakan mutu, ba kuwa wanda yakan yi tunani a zuciyarsa; an kwashe mutanen kirki, ba kuwa wanda ya fahimta cewa an kwashe masu adalci don a tsame su daga mugunta. Waɗanda suke aikata abin da yake daidai sukan shiga da salama; sukan huta yayinda suka kwanta cikin kabari. “Amma ku, ku matso nan, ku ’ya’ya maza na masu sihiri, ku zuriyar mazinata da karuwai! Wane ne kuke yi wa ba’a? Ga wa kuke masa gwalo kuna kuma fitar da harshe? Ashe, ku ba tarin ’yan tawaye ba ne, zuriyar maƙaryata? Kuna cike da muguwar sha’awa mai ƙonawa a cikin itatuwan oak da kuma a ƙarƙashin kowane itace mai inuwa; kuna miƙa hadayar ’ya’yanku a rafuffuka da kuma a ƙarƙashin tsagaggun duwatsu. Gumakan da suke cikin duwatsu masu sulɓi su ne rabonku; su ɗin, su ne rabonku. I, gare su kuka kwarara hadayu na sha kuka kuma miƙa hadayu na gari. Saboda waɗannan abubuwa, zan yi haƙuri? Kun yi gadonku a dogayen duwatsu masu tsayi da kuma a tudu mai tsawo; a can kuka haura don ku miƙa hadayunku. A bayan ƙofofi da madogaran ƙofofi kuka kafa alamun gumakanku. Kuka yashe ni, kuka kware gadonku, kuka kwanta a kansa kuka fadada shi; kuka kuma ƙulla yarjejjeniya da waɗanda kuke ƙaunar gadajensu, kuka dubi tsiraicinsu. Kuka tafi wurin Molek da man zaitun kuka kuma riɓaɓɓanya turarenku. Kuka aika jakadunku can da nisa; kuka gangara zuwa cikin kabari kansa! Kuka gaji cikin dukan al’amuranku, amma ba ku iya cewa, ‘Aikin banza ne ba.’ Kuka sami sabuntar ƙarfinku, ta haka ba ku suma ba. “Wa ya sa ku fargaba, kuna jin tsoro har kuka yi mini ƙarya, ba ku kuma tuna da ni ba balle ku yi tunanin wannan a zukatanku? Ba don na daɗe ina shiru ba ne ya sa ba kwa tsorona? Zan bayyana adalcinku da kuma ayyukanku, ba kuwa za su amfane ku ba. Sa’ad da kuka nemi taimako, bari tarin gumakanku su cece ku! Iska za tă kwashe dukansu tă tafi, ɗan numfashi kawai zai hura su. Amma mutumin da ya mai da ni mafakarsa zai gāji ƙasar ya kuma mallaki dutsena mai tsarki.” Za a kuma ce, “Ku gina, ku gina, ku gyara hanya! Ku kawar da abubuwan sa tuntuɓe a hanyar mutanena.” Gama abin da Maɗaukaki da kuma Mai daraja ya faɗa wanda yake raye har abada, wanda sunansa mai tsarki ne, “Ina zama a bisa da kuma a tsattsarkan wuri, amma kuma tare da shi wanda yake mai halin tuba mai tawali’u a ruhu, don in farfaɗo da ruhu mai tawali’u in kuma farfaɗo da zuciyar mai halin tuba. Ba zan tuhume su har abada ba, ba kuwa kullum zai yi fushi ba, gama a haka ruhun mutumin zan yi suma a gabana, shi numfashin mutumin da na halitta. Na yi fushi saboda kwaɗayin zunubinsa; na yi masa horo, na kuma ɓoye fuskata saboda fushi, duk da haka ya ci gaba da ayyukan zunubinsa. Na ga al’amuransa, amma zan warkar da shi; zan bi da shi in mayar da ta’aziyya a gare shi, ina ƙirƙiro yabo a leɓunan masu makoki a Isra’ila. Salama, salama, ga waɗanda suke nesa da kuma kusa,” in ji Ubangiji. “Zan kuma warkar da su.” Amma mugaye suna kama da tumbatsar teku, wanda ba ya natsuwa, wanda raƙumansa sukan kawo gurɓacewa da tabo. “Babu salama ga mugaye,” in ji Allahna. “Ku yi ihu da ƙarfi, ba ƙaƙƙautawa. Ku tā da muryarku kamar busar ƙaho. Ku furta wa mutanena tawayensu da kuma ga gidan Yaƙub zunubansu. Gama kowace rana suna nemana; suna marmarin sanin hanyoyina, sai ka ce al’ummar da take yin abin da yake daidai ba ta kuma yashe umarnan Allahnta ba. Sun nemi shawarwaran da suke daidai daga gare ni suna kuma marmari Allah ya zo kusa da su. Suna cewa, ‘Don me muka yi azumi, ba ka kuma gani ba? Me ya sa muka ƙasƙantar da kanmu, ba ka kuma lura da wannan ba?’ “Duk da haka a ranar azuminku, kuna yi yadda kuka ga dama kuna kuma zaluntar dukan ma’aikata. Azuminku yakan ƙare a faɗa da kuma hargitsi, kuna ta naushin juna da mugayen naushe-naushe. Ba za ku iya azumi kamar yadda kuke yi a yau ku zaci za a ji muryarku can sama. Irin azumin da na zaɓa ke nan, rana guda kawai don mutum ya ƙasƙantar da kansa? Sunkuyar da kanku kamar iwa kawai kuna kuma kwance a tsummoki da toka? Abin da kuke kira azumi ke nan rana yardajje ga Ubangiji? “Irin azumin da na zaɓa shi ne, a kunce sarƙoƙin rashin adalci a kuma kunce igiyoyin karkiya, a ’yantar da waɗanda ake zalunta a kuma kakkarye kowace karkiya? Ba shi ne ku rarraba abincinku da mayunwata ku kuma tanada wa matalauta masu yawo mahalli, sa’ad da kuka ga wanda yake tsirara, ku yi masa sutura, kada kuma ku ba wa namanku da jininku baya? Sa’an nan haskenku zai keto kamar ketowar alfijir, warkarwarku kuma zai bayyana nan da nan; sa’an nan adalcinku zai tafi a gabanku, ɗaukakar Ubangiji kuma zai tsare ku daga baya. Sa’an nan za ku yi kira, Ubangiji kuma zai amsa; za ku yi kuka don neman taimako, zai kuwa ce ga ni nan. “In kuka kawar da karkiyar zalunci, kuka daina nuna wa juna yatsa da kuma faɗar mugayen maganganu, in kuma kuka ɗauki lokaci kuka ƙosar da mayunwata kuka kuma biya bukatun waɗanda suke shan tsanani, sa’an nan ne haskenku zai haskaka cikin duhu darenku kuma zai zama kamar tsakar rana. Ubangiji zai bishe ku kullum; zai biya muku bukatunku a ƙasa mai zafin rana ya kuma ƙarfafa ƙasusuwanku. Za ku zama kamar lambun da aka yi masa banruwa, kamar rafin da ruwansa ba ya ƙafewa. Mutanenku za su sāke gina kufai na da su kuma daga tsofaffin harsashai; za a ce da ku Masu Gyaran Katangar da ta Rushe, Masu Farfaɗo da Tituna da kuma Wuraren zama. “In kun kiyaye ƙafafunku daga take Asabbaci da kuma daga aikata abin da kuka gan dama a ranata mai tsarki, in kuka kira Asabbaci ranar murna rana mai tsarki ta Ubangiji kuma mai bangirma, in kuka girmama ta ta wurin ƙin yin abin da kuka gan dama da kuma yin al’amuranku ko yin mugayen maganganu, sa’an nan za ku yi farin ciki a cikin Ubangiji, zan kuma sa ku a kan maɗaukaka ƙasashe ku kuma yi biki a gādon mahaifinku Yaƙub.” Ni Ubangiji ne na faɗa. Tabbatacce hannun Ubangiji bai kāsa yin ceto ba, kunnensa kuma bai kurmance da zai kāsa ji ba. Amma laifofinku sun raba ku da Allahnku; zunubanku sun ɓoye fuskarsa daga gare ku, saboda kada yă ji. Gama hannuwanku sun ƙazantu da jini, yatsotsinku kuma da alhaki. Leɓunanku suna faɗin ƙarairayi, harshenku kuma yana raɗar mugayen abubuwa. Babu wani mai ce a yi adalci; babu wani mai nema a dubi al’amarinsa da mutunci. Sun dogara a gardandamin banza suna ƙarairayi; suna ɗaukar cikin ɓarna, su haifi mugunta. Suna ƙyanƙyashe ƙwan kāsā su kuma saƙa yanar gizo-gizo. Duk wanda ya ci ƙwansu zai mutu, kuma sa’ad da ƙwan ya fashe, zai ƙyanƙyashe kububuwa. Yanar gizo-gizonsu ba amfani don tufa; ba za su iya rufuwa da abin da suka yi ba. Ayyukansu mugaye ne, ayyukan tā da hargitsi kuma suna a hannuwansu. Ƙafafunsu sukan gaggauta zuwa aikata zunubi; suna da saurin zub da jini. Tunaninsu mugaye ne; lalaci da hallaka sun shata hanyoyinsu. Ba su san hanyar salama ba; babu adalci a hanyoyinsu. Sun mai da su karkatattun hanyoyi; babu wanda zai yi tafiya a kansu ya sami salama. Saboda haka gaskiya ta yi nisa da mu, adalci kuma ba ya kaiwa gare mu. Muna neman haske, sai ga duhu; muna neman haske, sai muka yi ta tafiya cikin baƙin inuwa. Kamar makafi, sai lallubar bango muke yi, muna lallubawar hanyarmu kamar marasa idanu. Da tsakar rana muna tuntuɓe sai ka ce wuri ya fara duhu; cikin ƙarfafa, mun zama kamar matattu. Muna gurnani kamar beyar; muna ta ƙugi kamar kurciyoyi. Muna ta neman adalci amma ina; mun nemi fansa, amma yana can da nisa. Gama laifofinmu suna da yawa a gabanka, zunubanmu kuma suna ba da shaida gāba da mu. Laifofinmu kullum suna a gabanmu, muna kuma sane da laifofinmu, tawaye da mūsun Ubangiji, mun juye bayanmu ga Allahnmu, zugawa a yi zalunci da tayarwa, faɗin ƙarairayi da zukatanmu suka shirya. Saboda haka aka kau da yin gaskiya adalci kuma ya tsaya can da nesa; gaskiya ta yi tuntuɓe a tituna, sahihanci ba zai shiga ba. Gaskiya ta ɓace gaba ɗaya, kuma duk wanda ya guji mugunta zai zama ganima. Ubangiji ya duba bai kuwa ji daɗi cewa babu adalci ba. Ya ga cewa babu wani, ya yi mamaki cewa babu wanda zai shiga tsakani; saboda haka hannunsa ya aikata masa ceto, adalcinsa kuma ya raya shi. Ya yafa sulke a matsayin rigar ƙirji, da hulan kwanon ceto a kansa; ya sa rigunan ɗaukar fansa ya kuma nannaɗe kansa da kishi kamar a cikin alkyabba. Bisa ga abin da suka yi, haka za a sāka fushi a kan abokan gābansa ramuwa kuma a kan maƙiyansa; zai sāka wa tsibirai abin da ya dace da su. Daga yamma, mutane za su ji tsoron Ubangiji, daga mafitar rana kuma, za su girmama ɗaukakarsa. Gama zai zo kamar rigyawa mai tsananin gudu cewa numfashin Ubangiji zai tafi tare da shi. “Mai fansa zai zo Sihiyona, zuwa waɗanda suke cikin Yaƙub da suka tuba daga zunubansu,” in ji Ubangiji. “Game da ni dai, ga alkawarina da su,” in ji Ubangiji. “Ruhuna, wanda yake a kanka, da kuma maganata da na sa a bakinka ba za tă rabu da bakinka ba, ko daga bakunan ’ya’yanka ba, ko kuwa daga bakunan zuriyarsu ba daga wannan lokaci zuwa gaba da kuma har abada,” in ji Ubangiji. “Ki tashi, ki haskaka, gama haskenki ya zo, ɗaukakar Ubangiji ya taso a kanki. Duba, duhu ya rufe duniya duhu mai kauri kuma yana bisa mutane, amma Ubangiji ya taso a kanki ɗaukakarsa kuma ya bayyana a bisanki. Al’ummai za su zo wurin haskenki, sarakuna kuma zuwa asubahin sabon yininki. “Ki ɗaga idanunki ki duba kewaye da ke. Duka sun tattaru suka kuma zo wurinki; ’ya’yanki maza daga nesa, ana kuma ɗaukan ’ya’yanki mata a hannu. Sa’an nan za ki duba ki kuma haskaka zuciyarki zai motsa ya kuma cika da farin ciki; za a kawo miki wadata daga tekuna, za a kawo miki arzikin al’ummai. Manyan ayarin raƙuma za su cika ƙasar, ƙananan raƙuma ke nan daga Midiyan da Efa. Daga Sheba kuma duka za su zo, suna ɗauke da zinariya da turare suna shelar yabon Ubangiji. Dukan garkunan Kedar za su taru a wurinki ragunan Nebayiwot za su yi miki hidima; za a karɓe su kamar hadayu a kan bagadenki, zan kuma darjanta haikalina mai ɗaukaka. “Su wane ne waɗannan da suke firiya kamar gizagizai, kamar kurciyoyi suna zuwa sheƙarsu? Babu shakka tsibirai suna dogara gare ni; jiragen Tarshish kuma su ne a gaba, suna kawo ’ya’yanki maza daga nesa, tare da azurfa da zinariya, domin su girmama Ubangiji Allahnki, Mai Tsarkin nan na Isra’ila, gama ya cika ki da daraja. “Baƙi za su sāke gina katangarki, sarakunansu kuma za su yi miki hidima. Ko da yake a cikin fushi na buge ki, da tagomashi zan yi miki jinƙai. Ƙofofinki kullum za su kasance a buɗe, ba za a ƙara rufe su da rana ko da dare ba, saboda mutane su kawo miki dukiyar al’ummai, sarakunansu za su kasance a gaba a jerin gwanon nasara. Gama al’umma ko masarautar da ba tă bauta miki ba, za tă hallaka; za tă lalace sarai. “Darajar Lebanon za tă zo wurinki, itatuwan fir da dai ire-irensu da kuma itatuwan saifires duka za su zo don su ƙayatar da wurina mai tsarki; zan kuma ɗaukaka wurin ƙafafuna. ’Ya’ya maza masu zaluntarku za su zo suna rusunawa a gabanki; dukan waɗanda suka rena ki za su rusuna a ƙafafunki su kuma ce da ke Birnin Ubangiji, Sihiyona na Mai Tsarkin nan na Isra’ila. “Ko da yake an yashe ki aka kuma ƙi ki, har babu wani da ya ratsa a cikinki, zan mai da ke madawwamiyar abar taƙama da kuma farin cikin dukan zamanai. Za ki sha madarar al’ummai a kuma shayar da ke da nonon sarauta. Sa’an nan za ki san cewa ni, Ubangiji, ni ne Mai Cetonki, Mai Fansarki, Mai Ikon nan na Yaƙub. A maimakon tagulla zan kawo zinariya, azurfa kuma a maimakon baƙin ƙarfe. A maimakon katako zan kawo tagulla, baƙin ƙarfe kuma a maimakon duwatsu. Zan sa salama ta zama gwamnarki adalci kuma mai mulkinki. Ba za a ƙara jin hayaniyar tashin hankali a ƙasarki ba, balle lalacewa ko hallaka a cikin iyakokinki, amma za ki kira katangarki Ceto ƙofofinki kuma Yabo. Rana ba za tă ƙara zama haskenki a yini ba, balle hasken wata ya haskaka a kanki, gama Ubangiji zai zama madawwamin haskenki, Allahnki kuma zai zama ɗaukakarki. Ranarki ba za tă ƙara fāɗuwa ba watanki kuma ba zai ƙara shuɗewa ba; Ubangiji zai zama madawwamin haskenki, kwanakin baƙin cikinki za su ƙare. Sa’an nan dukan mutanenki za su zama masu adalci za su kuma mallaki ƙasar har abada. Su ne reshen da na shuka, aikin hannuwana, don nuna darajata. Mafi ƙanƙanta a cikinki za tă zama dubu, ƙarami zai zama al’umma mai girma. Ni ne Ubangiji, cikin lokacinsa zan yi haka da sauri.” Ruhun Ubangiji Mai Iko Duka yana a kaina, domin Ubangiji ya shafe ni domin in yi wa’azi labari mai daɗi ga matalauta. Ya aiko ni in warkar da waɗanda suka karai a zuci, don in yi shelar ’yanci don ɗaurarru in kuma kunce ’yan kurkuku daga duhu don in yi shelar shekarar tagomashin Ubangiji da kuma ranar ɗaukan fansar Allahnmu, don in ta’azantar da dukan waɗanda suke makoki, in tanada wa waɗanda suke baƙin ciki a Sihiyona, in maido musu rawani mai kyau a maimako na toka, man murna a maimako na makoki, da kuma rigar yabo a maimako na ruhun fid da zuciya. Za a ce da su itatuwan oak na adalci, shukin Ubangiji don bayyana darajarsa. Za su sāke gina kufai na dā su raya wurare da aka lalace tun da daɗewa; za su sabunta biranen da aka rurrushe da aka lalace tun zamanai masu yawa da suka wuce. Baƙi za su yi kiwon garkunanki; baƙi za su yi miki noman gonaki da gonakin inabinki. Za a kuma kira ku firistocin Ubangiji, za a kira ku masu hidimar Allahnmu. Za ku ci wadatar waɗansu al’ummai, kuma a cikin dukiyarsu za ku yi taƙama. A maimakon kunyarsu mutanena za su sami rabi riɓi biyu, a maimakon wulaƙanci za su yi farin ciki cikin gādonsu; ta haka za su gāji rabo riɓi biyu a ƙasarsu, da kuma madawwamin farin ciki zai zama nasu. “Gama ni, Ubangiji, ina ƙaunar adalci; na ƙi fashi da aikata laifi. Cikin adalcina zan sāka musu in kuma yi madawwamin alkawari da su. Za a san da zuriyarsu a cikin al’ummai ’ya’yansu kuma a cikin mutane. Dukan waɗanda suka gan su za su san cewa su mutane ne da Ubangiji ya sa wa albarka.” Ina jin daɗi ƙwarai a cikin Ubangiji; raina yana farin ciki a cikin Allahna. Gama ya suturce ni da rigunan ceto ya yi mini ado da rigar adalci, yadda ango yakan yi wa kansa ado kamar firist kamar kuma yadda amarya takan sha ado da duwatsunta masu daraja. Gama kamar yadda ƙasa takan sa tsire-tsire su tohu lambu kuma ya sa iri ya yi girma, haka Ubangiji Mai Iko Duka zai sa adalci da yabo su tsiro a gaban dukan al’ummai. Saboda Sihiyona ba zan yi shiru ba, saboda Urushalima ba zan huta ba, sai adalcinta ya haskaka kamar hasken safiya, cetonta kuma ya haskaka kamar fitila mai haske. Al’ummai za su ga adalcinki, sarakuna kuma za su ga ɗaukakarki; za a kira ki da sabon suna sunan da bakin Ubangiji zai ambata. Za ki zama rawanin daraja a hannun Ubangiji, rawanin sarauta a hannun Allahnki. Ba za a ƙara ce da ke Yasasshiya ba, ko a kira ƙasarki Kango. Amma za a ce da ke Hefziba ƙasarki kuma Bewula; gama Ubangiji zai ji daɗinki, ƙasarki kuma za tă yi aure. Kamar yadda saurayi kan auri yarinya, haka ’ya’yanki maza za su aure ki; kamar kuma yadda ango yakan yi farin ciki da amaryarsa, haka Allahnki zai yi farin ciki da ke. Na sa matsara a kan katangarki, ya Urushalima; ba za su taɓa yin shiru ba, dare da rana. Ku da kuke kira bisa sunan Ubangiji, kada ku ba kanku hutu, kuma kada ku ba shi hutu sai ya kafa Urushalima ya kuma mai da ita yabon duniya. Ubangiji ya rantse da hannunsa na dama ta hannunsa kuma mai iko cewa, “Ba zan ƙara ba da hatsinki ya zama abinci ga abokan gābanki ba, baƙi kuma ba za su ƙara shan ruwan inabin wanda kika sha wahala samu ba; amma waɗanda suka girbe shi za su ci shi su kuma yabi Ubangiji, waɗanda kuma suka tattara ’ya’yan inabi za su sha shi a filayen wurina mai tsarki.” Ku wuce, ku wuce ƙofofi! Ku shirya hanya saboda mutane. Ku gina, ku gina babbar hanya! Ku kawar da duwatsu. Ku ɗaga tuta saboda al’ummai. Ubangiji ya yi shela ga iyakokin duniya cewa, “Faɗa wa Diyar Sihiyona, ‘Ga Mai Cetonki yana zuwa! Ga ladarsa tana tare da shi, sakamakonsa yana raka shi.’ ” Za a ce da shi Tsattsarkar Mutane, Fansassu na Ubangiji; za a kuma ce da ke Wadda Aka Nema Birnin da Ba Za a Ƙara Yashe ta ba. Wane ne wannan mai zuwa daga Edom, daga Bozra, saye da jajjayen rigunarsa? Wane ne wannan, sanye cikin daraja, tafe cikin girmar ƙarfinsa? “Ni ne, mai magana cikin adalci, mai ikon ceto.” Me ya sa rigunanka suka yi ja, sai ka ce na wanda yake tattaka ’ya’yan inabi? “Na tattake ’ya’yan inabi ni kaɗai; cikin al’ummai kuma babu wani tare da ni. Na tattake su cikin fushina Na matse su cikin hasalata; jininsu ya fantsamar wa rigunana, na kuma ɓata dukan tufafina. Gama ranar ɗaukan fansa tana a cikin zuciyata, kuma shekarar fansata ta zo. Na duba, amma babu wanda zai taimaka, na yi mamaki cewa ba wanda ya goyi baya; saboda haka hannuna ya yi mini ceto, fushina kuma ya rayar da ni. Na tattake al’ummai cikin fushina; cikin hasalata kuma na sa sun bugu na kuma zub da jininsu a ƙasa.” Zan ba da labarin alherin Ubangiji, ayyukan da suka sa a yabe shi, bisa ga dukan abubuwan da Ubangiji ya yi mana, I, ayyuka masu kyan da ya yi domin gidan Isra’ila, bisa ga jinƙansa da yawan alheransa. Ya ce, “Babu shakka su mutanena ne, ’ya’ya maza waɗanda ba za su ruɗe ni ba”; ta haka ya zama Mai Cetonsu. Cikin dukan damuwarsu shi ma ya damu, mala’ikan da yake gabansa ya cece su. Cikin ƙauna da jinƙai ya fanshe su; ya kuma ɗaga su ya riƙe su dukan kwanakin dā Duk da haka suka yi tawaye suka ɓata wa Ruhu Mai Tsarki rai. Saboda haka ya juya ya kuma zama abokin gābansu shi kansa kuma ya yaƙe su. Sa’an nan mutanensa suka tuna kwanakin dā, kwanakin Musa da mutanensa, ina yake shi wanda ya fitar da su ta teku, da makiyayan garkensa? Ina shi yake wanda ya sa Ruhunsa Mai Tsarki a cikinsu, wanda ya aika hannu ɗaukakarsa mai iko ya kasance a hannun dama na Musa, wanda ya raba ruwaye a gabansu, don yă sami wa kansa madawwamin suna, wanda ya bishe su cikin zurfafa? Kamar doki a fili, ba su yi tuntuɓe ba; kamar shanun da suke gangarawa zuwa kwari, haka Ruhun Ubangiji ya ba su hutu. Ga yadda ka bishe mutanenka don ka ba wa kanka suna mai ɗaukaka. Ka duba daga sama ka gani daga kursiyinka da yake bisa, mai tsarki da kuma mai ɗaukaka. Ina kishinka da kuma ikonka? Ka janye juyayi da kuma tausayin da kake yi mana daga gare mu. Amma kai Ubanmu ne, ko Ibrahim bai san mu ba Isra’ila kuma bai yarda da mu ba; kai, ya Ubangiji, kai ne Ubanmu, Mai Fansarmu tun fil azal ne sunanka. Don me, ya Ubangiji, ka sa muna barin hanyoyinka muka kuma taurare zukatanmu don kada mu girmama ka? Ka komo domin darajar bayinka, kabilan da suke abin gādonka. Gama a ɗan lokaci mutanenka suka mallaki wurinka mai tsarki, amma yanzu abokan gābanmu sun tattake wurinka mai tsarki. Mu naka tun fil azal; ba ka taɓa yin mulki a kansu ba, ba a taɓa kira su da sunanka ba. Da ma za ka tsage sammai ka sauko, ai, da duwatsu za su yi rawar jiki a gabanka! Kamar sa’ad da wuta takan ci rassa ta sa ruwa ya tafasa, ka sauko ka sanar da sunanka ga abokan gābanka ka kuma sa al’ummai su yi rawan jiki a gabanka! Gama sa’ad da ka aikata abubuwan bantsoron da ba mu sa tsammani ba, ka sauko, duwatsu kuma suka yi rawar jiki a gabanka. Tun fil azal babu wanda ya taɓa ji, babu kunnen da ya gane, babu idon da ya ga wani Allah in ban da kai, wanda ya aikata waɗannan al’amura a madadin waɗanda suke sa zuciya a gare shi. Kakan taimaki waɗanda suke murnan yin abin da yake daidai, waɗanda sukan tuna da hanyoyinka. Amma sa’ad da muka ci gaba da yin zunubi, kakan yi fushi. Ta yaya za mu sami ceto ke nan? Dukanmu mun zama kamar wanda yake marar tsabta, kuma dukan ayyukanmu masu adalci sun zama kamar ƙazaman tsummoki; duk mun zama kamar busasshen ganye, kamar iska haka zunubanmu sukan share mu. Babu wanda yake kira bisa sunanka ko ya yi ƙoƙarin riƙe ka; gama ka ɓoye fuskarka daga gare mu ka kuma sa muka lalace saboda zunubanmu. Duk da haka, Ubangiji, kai ne Ubanmu. Mu yumɓu ne, kai kuma mai ginin tukwane; dukanmu aikin hannunka ne. Kada ka yi fushi fiye da kima, ya Ubangiji; kada ka tuna da zunubanmu har abada. Da ma ka dube mu, muna roƙonka, gama dukanmu mutanenka ne. Biranenka masu tsarki sun zama hamada; har Sihiyona ma ta zama hamada; Urushalima ta zama kango. Haikalinmu mai tsarki da kuma mai daraja, inda kakanninmu suka yabe ka, an ƙone da wuta, kuma dukan abubuwan da muke ƙauna sun lalace. Bayan dukan wannan, ya Ubangiji, ba za ka yi wani abu ba? Za ka yi shiru ka hore mu fiye da kima? “Na bayyana kaina ga waɗanda ba su tambaye ni ba; ina samuwa ga waɗanda ba su neme ni ba. Ga al’ummar da ba tă kira bisa sunana ba, Na ce, ‘Ga ni, ga ni.’ Dukan yini ina miƙa hannuwana ga mutane masu tayarwa, waɗanda suna tafiya a hanyoyin da ba su da kyau, suna bin tunaninsu, mutanen da suna cin gaba da tsokanata a fuskata, suna miƙa hadayu a gonaki suna ƙone turare a bagadan tubali; suna zama a kaburbura su kwana suna yin asirtattun ayyuka; suna cin naman aladu, tukwanensu kuma sun cika da nama marar tsabta; suna cewa, ‘Ku tsaya a can; kada ku yi kusa da ni, gama na fi ku tsarki!’ Irin mutanen nan hayaƙi ne a hancina, wuta kuma da take cin gaba da ci dukan yini. “Ga shi, yana nan a rubuce a gabana cewa ba zan ƙyale ba, zan yi cikakken ramuwa; zan yi ramuwa a cinyoyinsu saboda zunubanku da kuma zunuban kakanninku,” in ji Ubangiji. “Gama sun ƙone turare a kan duwatsu suka kuma ƙazantar da ni a kan tuddai, zan yi musu awo in zuba a cinyoyinsu cikakken ramuwa saboda ayyukansu na dā.” Ga abin da Ubangiji yana cewa, “Kamar sa’ad da ruwan ’ya’yan itace yana samuwa a cikin tarin ’ya’yan inabi mutane kuma su ce, ‘Kada a lalace shi, har yanzu akwai abu mai kyau a ciki,’ haka nan zan yi a madadin bayina; ba zan hallaka su duka ba. Zan fitar da zuriyar Yaƙub, daga Yahuda kuma waɗanda za su mallaki duwatsuna; zaɓaɓɓun mutanena za su gāje su, a can kuma bayina za su zauna. Sharon zai zama wurin kiwo don shanu, Kwarin Akor kuma wurin hutun garkuna, domin mutanena da suke nemana. “Amma game da ku waɗanda kuka yashe Ubangiji kuka manta da dutsena mai tsarki kuwa, ku da kuka shimfiɗa tebur don sa’a kuka kuma cika darunan ruwan inabin da aka dama don Ƙaddara, zan ƙaddara ku ga kaifin takobi, dukanku kuma za ku sunkuya wa mai yanka; gama na yi kira amma ba ku amsa ba, na yi magana amma ba ku saurara ba. Kuka aikata mugunta a gabana kuka kuma zaɓi abin da ba na jin daɗi.” Saboda haka ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa, “Bayin za su ci, amma ku za ku ji yunwa; bayina za su sha, amma ku za ku ji ƙishi; bayina za su yi farin ciki amma ku za ku sha kunya. Bayina za su rera da farin cikin zukatansu, amma ku za ku yi kuka daga wahalar zuciya ku kuma yi kururuwa da karayar zuci. Za ku bar sunanku ga zaɓaɓɓuna yă zama abin la’antarwa; Ubangiji Mai Iko Duka zai kashe ku, amma ga bayina zai ba su wani suna. Duk wanda zai roƙi albarka a cikin ƙasar zai yi haka da gaskiyar Allah; wanda zai yi rantsuwa a cikin ƙasar zai rantse da gaskiyar Allah. Gama za a manta da wahalolin baya a kuma ɓoye su daga idanuna. “Ga shi, na halicci sabuwar sama da kuma sabuwar duniya. Abubuwa na dā za a manta da su, ba kuwa za a ƙara tuna da su ba. Amma ku yi murna ku kuma yi farin ciki har abada a abin da na halitta, gama zan halicci Urushalima ta zama abin murna mutanenta kuwa abin farin ciki. Zan yi farin ciki a kan Urushalima in kuma yi murna saboda mutanena; a can ba za a ƙara jin karar makoki da na kuka ba. “A cikinta ba za a ƙara jin jariri ya rayu na ’yan kwanaki kawai ba, ko kuwa wani tsohon da bai cika kwanakinsa ba; duk wanda ya mutu yana da shekaru ɗari za a ce ya mutu a kurciya ne kawai; duk wanda bai kai ɗari ba za a ɗauka la’antacce ne. Za su gina gidaje su kuma zauna a cikinsu; za su yi shuki a gonakin inabi su kuma ci ’ya’yansu. Ba za su ƙara gina gidaje waɗansu kuma su zauna a cikinsu ba, ko su yi shuki waɗansu kuma su ci ba. Gama kamar yadda kwanakin itace suke, haka kwanakin mutanena za su kasance; zaɓaɓɓuna za su daɗe suna jin daɗin ayyukan hannuwansu. Ba za su yi wahala a banza ba ko su haifi ’ya’yan da aka ƙaddara da rashin sa’a; gama za su zama mutanen da Ubangiji ya yi wa albarka, su da zuriyarsu tare da su. Kafin su yi kira zan amsa; yayinda suke cikin magana zan ji. Kyarketai da ’yan raguna za su ci abinci tare, zaki kuma zai ci buɗu kamar yadda shanu suke yi, amma ƙura ce za tă zama abincin maciji. Ba za su ƙara cuci ko su yi ɓarna a kan dukan dutsena mai tsarki ba,” in ji Ubangiji. Ga abin da Ubangiji yana cewa, “Sama kursiyina ce, duniya kuma matashin sawuna. Ina gidan da za ku gina mini? Ina wurin hutuna zai kasance? Ba hannuna ba ne ya yi dukan waɗannan abubuwa, ta haka suka kasance?” In ji Ubangiji. “Wannan mutum ne nake jin daɗi, shi da yake mai ƙasƙanci da kuma zuciyar yin tuba, yana kuma rawar jiki ga maganata. Amma duk ya miƙa hadayar bijimi yana kama da wanda ya kashe mutum, kuma duk wanda ya miƙa ɗan rago, kamar wanda ya karye wuyan kare; duk wanda ya miƙa hadaya ta gari yana kama da wanda ya yi sadakar jinin alade, kuma duk wanda ya ƙone turaren tuni, kamar wanda yake bauta gunki ne. Sun zaɓi hanyoyinsu, rayukansu kuma suna jin daɗin abubuwan banƙyamarsu; saboda haka ni ma zan aukar musu da masifa mai zafi in kuma kawo musu abin da suke tsoro. Gama sa’ad da na yi kira, ba wanda ya amsa, sa’ad da na yi magana, ba wanda ya saurara, Sun aikata mugunta a idona suka kuma zaɓa abin da ba na jin daɗi.” Ku ji maganar Ubangiji, ku da kuke rawar jiki ga maganarsa, “’Yan’uwanku da suke ƙinku, suna kuma ware ku saboda sunana, sun ce, ‘Bari a ɗaukaka Ubangiji, don mu ga farin cikinku!’ Duk da haka za su sha kunya. Ku ji wannan hayaniya daga birni, ku ji surutu daga haikali! Amon Ubangiji ne yana sāka wa abokan gābansa abin da ya dace da su. “Kafin naƙuda ya fara mata, ta haihu; kafin zafi ya zo mata, ta haifi ɗa. Wa ya taɓa jin irin wannan abu? Wa ya taɓa gani irin abubuwan nan? Za a iya ƙirƙiro ƙasa a rana ɗaya ko a haifi al’umma farat ɗaya? Duk da haka da zarar Sihiyona ta fara naƙuda sai ta haifi ’ya’yanta. Zan kai mace har haihuwa in kuma sa ta kāsa haihu?” In ji Ubangiji. “Zan rufe mahaihuwa sa’ad da lokacin haihuwa ya yi?” In ji Allahnku. “Ku yi farin ciki tare da Urushalima ku kuma yi murna saboda ita, dukanku waɗanda kuke ƙaunarta; ku yi farin ciki matuƙa tare da ita, dukanku waɗanda kuke makoki a kanta. Gama za ku tsotsa ku kuma ƙoshi da nonon ta’aziyyarta; za ku sha sosai ku kuma ji daɗin yalwarta.” Gama ga abin da Ubangiji ya faɗa, “Zan fadada salama gare ta kamar kogi, wadatar al’ummai kuma kamar rafi mai gudu; za ku tsotsa a kuma riƙe ku a hannunta ku kuma yi wasa a gwiwoyinta. Kamar yadda uwa takan ta’azantar da ɗanta haka zan ta’azantar da ku; za ku kuma ta’azantu a Urushalima.” Sa’ad da kuka ga wannan, zuciyarku za tă yi farin ciki za ku kuma haɓaka kamar ciyawa; za a sanar da hannun Ubangiji ga bayinsa, amma za a nuna wa maƙiyansa fushinsa. Ga shi, Ubangiji yana zuwa da wuta, kuma kekunan yaƙinsa suna kama da guguwa; zai sauko da fushinsa da zafi, tsawatawarsa kuma da harsunan wuta. Gama da wuta da kuma takobi Ubangiji zai yi hukunci a kan dukan mutane, kuma yawanci za su kasance waɗanda Ubangiji zai kashe. “Waɗanda suka tsarkake suka kuma tsabtacce kansu don su je lambu, suna bin wannan da yake tsakiya waɗannan da suke cin naman aladu da ɓeraye da waɗansu abubuwan banƙyama, za su sadu da ƙarshensu tare,” in ji Ubangiji. “Ni kuwa, saboda ayyukansu da kuma tunaninsu, ina dab da zuwa in tattara dukan al’ummai da harsuna, za su kuma zo su ga ɗaukakata. “Zan kafa alama a cikinsu, zan kuma aika waɗansu da suka tsira zuwa al’ummai, zuwa Tarshish, zuwa Libiya da Lidiya (sanannun ’yan aika), zuwa Tubal da kuma Girka, da kuma zuwa manisantan tsibirai da ba su taɓa jin labarin sunana ba ko su ga ɗaukakata. Za su yi shelar ɗaukakata a cikin al’ummai. Za su kuma dawo da dukan ’yan’uwanku, daga dukan al’ummai, zuwa dutsena mai tsarki a Urushalima kamar hadaya ga Ubangiji, a kan dawakai, a kekunan yaƙi da wagonu, da kuma a kan alfadarai da kuma raƙuma,” in ji Ubangiji. “Za su kawo su, kamar yadda Isra’ilawa suke kawo hadayun hatsi, zuwa haikalin Ubangiji a cikin tsabtatattun kore. Zan kuwa zaɓa waɗansunsu kuma su zama firistoci da Lawiyawa,” in ji Ubangiji. “Kamar yadda sabuwar duniya da sabuwar sama za su tabbata a gabana,” in ji Ubangiji, “haka sunanku da zuriyarku za su tabbata. Daga wannan sabon wata zuwa wancan, kuma daga wannan Asabbaci zuwa wancan, dukan mutane za su zo su rusuna a gabana,” in ji Ubangiji. “Za su kuma fita su ga gawawwakin mutanen da suka yi mini tayarwa; tsutsotsin da suke cinsu ba za su taɓa mutuwa ba, balle wutar da take ƙona su ta mutu, za su kuma zama abin ƙyama ga dukan mutane.” Kalmomin Irmiya ɗan Hilkiya, ɗaya daga cikin firistoci a Anatot a yankin Benyamin. Maganar Ubangiji ta zo gare shi a shekara ta goma sha uku ta sarautar Yosiya ɗan Amon sarkin Yahuda, da kuma a zamanin Yehohiyakim ɗan Yosiya sarkin Yahuda, har zuwa watan biyar na shekara goma sha ɗaya na Zedekiya ɗan Yosiya sarkin Yahuda, sa’ad da aka kai mutanen Urushalima zaman bauta. Maganar Ubangiji ta zo mini cewa, “Kafin in siffanta ka a cikin ciki na san ka, kafin a haife ka, na keɓe ka; na naɗa ka ka zama annabi ga al’ummai.” Sai na ce, “Kayya, Ubangiji Mai Iko Duka, ban iya magana ba; ni ɗan yaro ne kawai.” Amma Ubangiji ya ce mini, “Kada ka ce, ‘Ni ɗan yaro ne kawai.’ Dole ka je wurin kowane mutumin da na aike ka ka kuma faɗa abin da na umarce ka. Kada ka ji tsoronsu, gama ina tare da kai kuma zan kiyaye ka,” in ji Ubangiji. Sai Ubangiji ya miƙa hannunsa ya taɓa bakina ya ce mini, “Yanzu na sa kalmomina a bakinka. Duba, yau na naɗa ka a kan al’ummai da mulkoki don ka tumɓuke ka kuma rusar, ka hallaka ka kuma kakkaɓe, ka gina ka kuma shuka.” Maganar Ubangiji ta zo mini cewa, “Me ka gani, Irmiya?” Sai na amsa na ce, “Na ga reshen itacen almon.” Ubangiji ya ce mini, “Daidai ne ka gani, gama ina lura in ga cewa maganata ta cika.” Maganar Ubangiji ta sāke zo mini cewa, “Me ka gani?” Na amsa na ce, “Na ga tukunya tana tafasa, tana juyewa daga arewa.” Ubangiji ya ce mini, “Daga arewa za a zubo masifa a kan dukan mazaunan ƙasar. Ina shirin kiran dukan mutanen masarautar arewanci,” in ji Ubangiji. “Sarakunansu za su zo su kafa kursiyoyinsu a mashigin ƙofofin Urushalima; za su zo su kewaye dukan katangarta su kewaye dukan garuruwan Yahuda. Zan furta hukunci a kan mutanena saboda muguntarsu na yashe ni, suna ƙona turare ga waɗansu alloli suna kuma bauta wa abin da hannuwansu suka yi. “Ka kintsa kanka! Ka tashi tsaye ka faɗa musu abin da na umarce ka. Kada su firgita ka, in ba haka ba zan firgita ka a gabansu. Yau na mai da kai birni mai katanga, ginshiƙin ƙarfe da bangon tagulla don ka tsaya gāba da dukan ƙasar, ya kuma yi gāba da sarakunan Yahuda da fadawan, da firistoci da kuma mutanenta. Za su yi yaƙi da kai amma ba za su ci nasara a kanka ba, gama ina tare da kai, zan kuma kiyaye ka,” in ji Ubangiji. Maganar Ubangiji ta zo mini cewa, “Tafi ka yi shela a kunnuwar Urushalima cewa, “ ‘Na tuna da amincin ƙuruciyarki, yadda kamar amarya kika ƙaunace ni kika kuma bi ni cikin hamada, cikin ƙasar da ba a yi shuka ba. Isra’ila tsattsarka ce ga Ubangiji, nunan fari na girbinsa; dukan waɗanda suka cinye ta an same su da laifi, masifa kuwa ta same su,’ ” in ji Ubangiji. Ka saurari maganar Ubangiji, ya gidan Yaƙub, dukanku zuriyar gidan Isra’ila. Ga abin da Ubangiji yana cewa, “Wane laifi ne kakanninku sun same ni da shi, da suka tsaya nesa da ni? Sun bi gumakan banza su kansu suka kuma zama banza da kansu. Ba su yi tambaya, ‘Ina Ubangiji, wanda ya fitar da su daga Masar ya bishe su cikin jeji cikin hamada da kwazazzabai ƙasa mai fări da kuma duhu, ƙasar da ba kowa mai ratsa ta ba kowa kuma mai zama a cikinta?’ Na kawo ku zuwa ƙasa mai albarka don ku ci amfaninta da abubuwa masu yalwar da take bayarwa. Amma kuka zo kuka ƙazantar da ƙasata kuka kuma mai da gādona abin ƙyama. Firistoci ba su yi tambaya, ‘Ina Ubangiji ba.’ Waɗanda suke amfani da doka ba su san ni ba; shugabanni suka yi mini tawaye. Annabawa suka yi annabci ta wurin Ba’al, suna bin gumakan banza. “Saboda haka ina sāke tuhumarku,” in ji Ubangiji. “Zan kuma tuhumi ’ya’ya ’ya’yanku. Ku ƙetare zuwa tsibiran Kittim ku gani, ku aika zuwa Kedar ku duba da kyau; ku ga ko an taɓa yin wani abu haka. Akwai wata al’ummar da ta canja allolinta? (Duk da haka su ba alloli ba ne sam.) Amma mutanena sun musayar da ɗaukakarsu da gumakan banza. Ku girgiza saboda wannan, ya sammai, ku kuma razana don tsoro mai girma,” in ji Ubangiji. “Mutanena sun aikata zunubai guda biyu. Sun rabu da ni, ni da nake maɓulɓular ruwan rai, sun kuma haƙa tankunan ruwansu, tankuna ruwan da suka fashe da ba za su iya riƙe ruwa ba. Isra’ila bawa ne, bawa ne ta wurin haihuwa? Me ya sa ya zama ganima? Zakoki sun yi ruri; sun yi masa ruri. Sun lalatar da ƙasarsa; an ƙone garuruwansa aka kuma watse daga ciki. Haka ma, mutanen Memfis da Tafanes sun aske rawanin kanka Ba kai ne ba ka jawo wa kanka ba ta wurin rabuwa da Ubangiji Allahnka sa’ad da ya bi da kai a hanya? To, me ya sa za ka Masar don shan ruwa daga Shihor? Kuma me ya sa za ka Assuriya don shan ruwa daga Kogi? Muguntarka za tă hukunta ka; jan bayanka zai tsawata maka. Sai ka lura ka kuma gane yaya mugu da kuma ɗaci suke a gare ka sa’ad da ka rabu da Ubangiji Allahnka kuma ba ka tsorona,” in ji Ubangiji Maɗaukaki. “Tun da daɗewa ka karya karkiyarka ka kuma tsintsinke sarƙoƙinka; sai ka ce, ‘Ba zan bauta maka ba!’ Tabbatacce, a kan kowane tudu mai tsayi da kuma a ƙarƙashin kowane ɗanyen itace ka kwanta kamar karuwa. Na shuka ka kamar zaɓaɓɓen inabi iri mai kyau da kuma wanda za a dogara a kai. Yaya kuma ka juya kana gāba da ni ka lalace, ka zama inabin jeji? Ko da yake ka wanke kanka da sabulu ka yi amfani da sabulu mai yawa, duk da haka har yanzu tabon laifinka yana nan a gabana,” in ji Ubangiji Mai Iko Duka. “Yaya za ka ce, ‘Ban ƙazantu ba; ban bi Ba’al ba’? Duba yadda ka yi a cikin kwari; ka ga abin da ka yi. Kai kamar makwaɗaciyar raƙuma ce mai zafin gudu kana gudu nan da can, kamar jakar jejin da ta saba da hamada, mai busar iska cikin son barbaranta sa’ad da take son barbara wa zai iya hana ta? Jakin da yake nemanta, ba ya bukatar wahalar da kansa; a lokacin barbara za a same ta. Kada ka yi gudu har ƙafafunka su zama ba takalma maƙogwaronka kuma ya bushe. Amma sai ka ce, ‘Ba amfani! Ina ƙaunar baƙin alloli kuma dole in bi su.’ “Kamar yadda akan kunyatar da ɓarawo sa’ad da aka kama shi, haka gidan Isra’ila zai sha kunya, su, sarakunansu da shugabanninsu, firistocinsu da kuma annabawansu. Kuna ce wa itace, ‘Kai ne mahaifina,’ ga dutse kuma, ‘Kai ne ka haife ni.’ Sun juye mini bayansu ba fuskokinsu ba; duk da haka sa’ad da suna cikin wahala, sukan ce, ‘Zo ka cece mu!’ To ina allolin da kuka yi wa kanku? Bari su zo in suna iya cetonku sa’ad da kuke cikin wahala! Gama kuna da alloli masu yawa kamar yadda kuke da garuruwa, ya Yahuda. “Me ya sa kuke tuhumana? Dukanku kun yi mini tawaye,” in ji Ubangiji. “A banza na hukunta mutanenku; ba su yi gyara ba. Takobinku ya cinye annabawanku kamar zaki mai jin yunwa. “Ku na wannan zamani, ku saurari maganar Ubangiji. “Na zama wa Isra’ila hamada ne ko ƙasa mai babban duhu? Me ya sa mutanena suke cewa, ‘Muna da ’yanci mu yi ta yawo; ba za mu ƙara zuwa wurinka ba’? Budurwa za tă manta da kayan adonta amarya ta manta da kayan adon aurenta? Duk da haka mutanena sun manta da ni, kwanaki ba iyaka. Kuna da azanci sosai a bin masoya! Kai, ko mafiya muni cikin mata tana iya koya daga hanyoyinku. A rigunanku mutane kan sami jinin matalauta marasa laifi, ko da yake ba ku kama su suna fasawa su shiga ba. Duk da haka kuna cewa, ‘Ba ni da laifi; ba ya fushi da ni.’ Amma zan zartar da hukunci a kanku domin kun ce, ‘Ban yi zunubi ba.’ Don me kuke yawo da yawa haka, kuna ta canjin hanyoyinku? Masar za tă kunyata ku yadda kuka sha kunya a wurin Assuriya. Za ku kuma bar wurin da hannuwanku a kanku, gama Ubangiji ya ƙi waɗanda kuka amince da su; ba za ku zama abin taimako a gare su ba. “In mutum ya saki matarsa ta kuwa bar shi ta auri wani mutum, zai iya komo da ita kuma? Ƙasar ba za tă ƙazantu gaba ɗaya ba? Amma kun yi rayuwa kamar karuwa da masoya masu yawa yanzu za ki komo wurina?” In ji Ubangiji. “Ta da idanu ki duba tsaunuka ki gani. Akwai wani wurin da ba a kwana da ke ba? A gefen hanya kin zauna kina jiran masoyanki, kin zauna kamar makiyayi a hamada. Kin ƙazantar da ƙasar da karuwancinki da muguntarki. Saboda haka an hana yayyafi, kuma babu ruwan bazara da ya sauka. Duk da haka kina da irin kallon da karuwa takan yi; kin ƙi ki ji kunya. Yanzu ba kin kira ni, ‘Mahaifina, abokina daga ƙuruciyata ba, kullum za ka riƙa fushi? Hasalarka za tă ci gaba har abada ne?’ Haka kike magana, amma kina aikata dukan muguntar da kika iya yi.” A zamanin Sarki Yosiya, Ubangiji ya ce mini, “Ka ga abin da marar amincin nan, Isra’ila ta yi? Ta haura kan kowane tudu mai tsayi da kowane gindin itace mai duhuwa ta yi zina a can. Na yi zaton bayan ta yi wannan duka, za tă komo wurina amma ba tă yi haka ba, ’yar’uwarta marar aminci nan Yahuda ta gani. Na ba wa Isra’ila marar bangaskiya takardar saki na kuwa kore ta saboda duk zinanta. Duk da haka na ga cewa ’yar’uwarta marar amincin nan Yahuda ba ta da tsoro; ita ma ta fita ta yi zina. Domin fasikancin Isra’ila bai yi tasiri gare ta ba, sai ta ƙazantar da ƙasar ta kuma yi zina da dutse da kuma itace. Duk da wannan duka, Yahuda ’yar’uwarta rashin amincin ba tă komo gare ni da dukan zuciyarta ba, sai a munafunce,” in ji Ubangiji. Ubangiji ya ce mini, “Isra’ila marar bangaskiya ta fi Yahuda marar aminci. Ka tafi, ka yi shelar saƙon nan wajen arewa cewa, “ ‘Ki komo, Isra’ila marar bangaskiya,’ in ji Ubangiji, ‘Ba zan ƙara yin fushi da ke ba, gama ni mai jinƙai ne,’ in ji Ubangiji, ‘Ba zan yi fushi da ke har abada ba. Ki dai yarda da laifinki kin yi wa Ubangiji Allahnki tawaye, kin watsar da alheranki ga baƙin alloli a ƙarƙashin kowane itace mai duhuwa, ba ki kuwa yi mini biyayya ba,’ ” in ji Ubangiji. “Ku komo, ku mutane marasa bangaskiya,” in ji Ubangiji, “gama ni ne mijinku. Zan ɗauke ku, ɗaya daga garuruwanku da kuma biyu daga zuriyarku in kawo ku a Sihiyona. Sa’an nan zan ba ku makiyaya da suke yin abin da zuciyata take so, waɗanda za su bishe ku da sani da kuma fahimi. A kwanakin, sa’ad da kuka ƙaru sosai a ƙasar,” in ji Ubangiji, “mutane ba za su ƙara yin magana a kan, ‘Akwatin alkawarin Ubangiji ba.’ Ba zai ƙara shiga zuciyarsu ko su tuna ba; ko su bukace shi, ko kuwa su yi wani irinsa ba. A lokacin za su ce da Urushalima Kursiyin Ubangiji, kuma dukan al’ummai za su taru a Urushalima don su girmama sunan Ubangiji. Ba za su ƙara bin taurinkai zuciyarsu mai mugunta ba. A kwanakin gidan Yahuda zai haɗu da gidan Isra’ila, tare kuma za su zo daga ƙasar da take wajen arewa zuwa ƙasar da na ba kakanninsu gādo. “Ni kaina na faɗa, “ ‘Da farin ciki zan ɗauke ki kamar ’ya’yana maza in ba ki ƙasa mai daɗi, gādo mafi kyau da wata al’umma.’ Na zaci za ki kira ni ‘Mahaifi’ ba za ki ƙara rabuwa da bina ba. Amma kamar mace marar aminci ga mijinta, haka kika kasance marar aminci gare ni, ya gidan Isra’ila,” in ji Ubangiji. An ji kuka a filayen tuddai, kuka da roƙon mutanen Isra’ila, domin sun lalace hanyoyinsu sun kuma manta da Ubangiji Allahnsu. “Ku komo, mutane marasa bangaskiya; zan warkar da ku daga ja da bayanku.” “I, za mu zo wurinka, gama kai ne Ubangiji Allahnmu. Tabbatacce hayaniyar bin gumaka a kan tuddai da duwatsu banza ne; tabbatacce a wurin Ubangiji Allahnmu ne akwai ceton Isra’ila. Daga ƙuruciyarmu allolin kunya sun cinye mu amfanin wahalar kakanninmu garkunan tumakinsu da na awakinsu, yaransu maza da mata. Bari mu kwanta mu sha kunya, bari kuma kunyarmu ta rufe mu. Mun yi wa Ubangiji Allahnmu zunubi, da mu da kakanninmu; daga ƙuruciyarmu har yă zuwa yau ba mu yi wa Ubangiji Allahnmu biyayya ba.” “In za ka komo, ya Isra’ila, ka komo gare ni,” in ji Ubangiji. “In ka kau da gumakanka masu banƙyama daga gabana ba ka ƙara karkace ba, kuma in cikin gaskiya da adalci ka rantse, ‘Muddin Ubangiji yana raye,’ to al’ummai za su sami albarka ta wurinsa kuma a cikinsa za su ɗaukaka.” Ga abin da Ubangiji yana ce wa mutanen Yahuda da kuma na Urushalima. “Ku nome ƙasarku kuma kada ku yi shuka cikin ƙayayyuwa. Ku yi wa kanku kaciya ga Ubangiji ku yi wa zukatanku kaciya, ku mutanen Yahuda da mutanen Urushalima, in ba haka ba hasalata za tă sauko ta ci kamar wuta saboda muguntar da kuka aikata za tă ci ba wanda zai kashe ta. “Ku yi shela a Yahuda ku kuma furta a Urushalima ku ce, ‘Ku busa ƙaho a ko’ina a ƙasar!’ Ku tā da murya da ƙarfi ku ce, ‘Ku tattaru! Bari mu gudu zuwa birane masu katanga!’ Ku tā da tuta don zuwa Sihiyona! Ku gudu ku nemi mafaka ba tare da jinkiri ba! Gama ina kawowa masifa daga arewa, mummunan hallaka kuwa.” Zaki ya fito daga ruƙuƙinsa; mai hallakarwar al’ummai ya kama hanya. Ya bar wurinsa don yă lalace ƙasarku. Garuruwanku za su zama kufai babu mazauna. Saboda haka ku yafa tufafin makoki, ku yi makoki da kuka, gama fushin Ubangiji bai juye daga gare mu ba. “A wannan rana,” in ji Ubangiji, “sarki da shugabanni za su fid da zuciya, firistoci za su razana, annabawa kuma za su yi mamaki.” Sai na ce, “Kash, Ubangiji Mai Iko Duka, yaya ka ruɗi mutanen nan da kuma Urushalima gaba ɗaya haka ta wurin cewa, ‘Za ku zauna lafiya,’ sa’ad da takobi yana a maƙogwaronmu.” A lokacin za a faɗa wa mutanen nan da kuma Urushalima cewa, “Iska mai zafi daga tuddan hamada za tă hura zuwa wajen mutanena, amma ba don ta sheƙe ko ta rairaye; ba; iska mafificin ƙarfi da ta fito daga gare ni. Yanzu na zartar da hukuncina a kansu.” Duba! Yana zuwa kamar gizagizai, kekunan yaƙinsa suna zuwa kamar guguwa, dawakansa sun fi gaggafa sauri. Kaiton mu! Mun shiga uku! Ya Urushalima, ki wanke mugunta daga zuciyarki ki sami ceto. Har yaushe za ki zauna riƙe da mugayen tunani? Murya ta shela daga Dan, tana furtawa masifa daga tuddan Efraim. “A faɗa wa al’ummai wannan, a furta wannan game Urushalima. ‘Sojoji masu ƙawanya suna zuwa daga ƙasa mai nisa, suna tā da kirarin yaƙi a kan biranen Yahuda. Sun kewaye ta kamar masu gadin fili, domin ta yi mini tawaye,’ ” in ji Ubangiji. “Halinki da ayyukanki sun kawo wannan a kanki. Hukuncinki ke nan. Yana da ɗaci! Ya soke ki har zuciyarki!” Azabana, azabana! Ina birgima cikin zafi. Azabana, azabar zuciyata! Zuciyata yana bugu a cikina, Ba zan yi shiru ba. Gama na ji karan ƙaho; na ji kirarin yaƙi. Masifa kan masifa; dukan ƙasar ta zama kufai. Cikin ɗan lokaci aka rurrushe tentuna nawa, mafakata ba zato. Har yaushe zan dubi tutar yaƙi in kuma ji karar ƙaho? “Mutanena wawaye ne; ba su san ni ba. Su ’ya’ya ne marasa azanci; ba su da fahimi. Suna da dabarar aikata mugunta; ba su san yadda za su aikata alheri ba.” Na dubi duniya, na ga cewa marar siffa ce babu kome; sammai kuma, haskensu ya tafi. Na dubi duwatsu, sai na ga suna makyarkyata; dukan tuddai kuwa suna lilo. Na duba, sai na ga ba kowa; kowane tsuntsu a sarari da ya tsere. Na duba, sai na ga ƙasa mai amfani ta zama hamada; dukan garuruwanta sun zama kufai a gaban Ubangiji, a gaban zafin fushinsa. Ga abin da Ubangiji yana cewa, “Dukan ƙasar za tă zama kufai, ko da yake ba zan hallaka ta gaba ɗaya ba. Saboda haka duniya za tă yi kuka sammai a bisa kuma za su yi duhu, domin na yi magana kuma ba zan fasa ba, na yanke shawara ba kuwa zan janye ba.” Da jin motsin mahayan dawakai da maharba kowane gari ya ruga da gudu. Waɗansu suka shiga kurmi; waɗansu suka hau cikin duwatsu. Dukan garuruwan sun fashe tas; babu wani da yake zama a ciki. Me kike yi, ya wadda aka ragargaza? Me ya sa kika sanya mulufi kika sa kayan adon zinariya? Me ya sa kika sa wa idanunki tozali? Kin yi kwalliyarki a banza. Masoyanki sun bar ki; suna neman ranki. Na ji kuka kamar na mace mai naƙuda, nishi kamar na wadda take haihuwa ɗanta na fari, kukan Diyar Sihiyona tana haki, da ƙyar take numfashi, tana miƙa hannuwanta tana cewa, “Wayyo ni kaina! Na suma; an ba da raina ga masu kisana.” “Ku yi ta kai da kawowa a titunan Urushalima, ku dudduba ko’ina ku kuma lura, ku bincika cikin dandalinta. Ko za ku sami mutum guda wanda yake aikata adalci wanda yake kuma son bin gaskiya, sai in gafarta wa wannan birni. Ko da yake suna cewa, ‘Muddin Ubangiji yana raye,’ duk da haka suna rantsuwar ƙarya.” Ya Ubangiji, idanunka ba sa ganin gaskiya? Ka buge su, amma ba su ji zafi ba; ka ragargaza su, amma suka ƙi su gyara. Fuskarsu ta ƙeƙashe fiye da dutse suka ƙi su tuba. Na yi tunani, “Waɗannan ne kawai matalauta; su wawaye ne, gama ba su san hanyar Ubangiji ba, ko abubuwan da Allahnsu yake bukata ba. Saboda haka zan tafi wurin shugabanni in yi musu magana; tabbatacce sun san hanyar Ubangiji, da abubuwan da Allahnsu yake bukata.” Amma da nufi guda su ma suka karye karkiyar suka tsintsinke sarƙoƙin. Saboda haka zaki daga kurmi zai fāɗa musu, kyarkeci kuma daga hamada zai cinye su, damisa za tă yi musu ƙawanya kusa da garuruwansu yă yayyage duk wanda ya kuskura ya fita, gama tawayensu da girma yake jan bayansu kuma yana da yawa. “Me zai sa in gafarta muku? ’Ya’yanku sun yashe ni sun yi rantsuwa da allolin da ba alloli ba ne. Na biya musu dukan bukatunsu, duk da haka suka yi zina suka tattaru a gidajen karuwai. An ciyar da su sosai, kamar ƙosassun ingarmu, masu jaraba, kowanne yana haniniya, yana neman matar maƙwabcinsa. Ba zan hukunta su saboda wannan ba?” In ji Ubangiji. “Bai kamata in yi ramuwa a kan irin al’ummar nan ba? “Ku ratsa cikin gonakin inabinta ku cinye su, amma kada ku hallaka su gaba ɗaya. Ku kakkaɓe rassanta, gama waɗannan mutane ba na Ubangiji ba ne. Gidan Isra’ila da gidan Yahuda sun zama marasa aminci gaba ɗaya gare ni” in ji Ubangiji. Sun yi ƙarya a kan Ubangiji; sun ce, “Ba zai yi kome ba! Ba wata masifar da za tă same mu; ba za mu taɓa ganin takobi ko yunwa ba. Annabawa holoƙo ne kawai maganar kuwa ba ta cikinsu; saboda haka bari abin da suke faɗi ya koma kansu.” Saboda haka ga abin Ubangiji Allah Maɗaukaki yana cewa, “Domin mutanen sun yi waɗannan maganganu, zan mai da maganata a bakinku wuta waɗannan mutane kuwa su zama itacen da za tă ci. Ya gidan Isra’ila,” in ji Ubangiji, “Ina kawo al’umma daga nesa a kanku al’umma ce ta tun dā mai ƙarfin hali, mutane ne da ba ku san harshensu ba, waɗanda ba za ku fahimci abin da suke faɗa ba. Kwarinsu kamar buɗaɗɗen kabari ne; dukansu jarumawa ne. Za su cinye amfanin gonakinku da abincinku, za su cinye ’ya’yanku maza da mata; za su cinye garkunan tumakinku da na awakinku, za su cinye ’ya’yan inabinku da na ɓaurenku. Da takobi za su hallaka biranenku masu katanga. “Amma ko a cikin waɗancan kwanaki,” in ji Ubangiji, “ba zan hallaka ku gaba ɗaya ba. Sa’ad da kuma mutanen suka yi tambaya, ‘Me ya sa Ubangiji Allahnmu ya yi dukan wannan gare mu?’ Sai ka amsa musu, ‘Yadda kuka yashe ni kuka kuma bauta wa baƙin alloli a ƙasarku, haka yanzu za ku bauta wa baƙi a ƙasar da ba taku ba.’ “Ka sanar da wannan ga gidan Yaƙub ka yi shelarsa a Yahuda. Ku ji wannan, ku wawaye marasa azanci, waɗanda suke da idanu amma ba sa gani, waɗanda suke da kunnuwa amma ba sa ji. Bai kamata ku ji tsorona ba?” In ji Ubangiji. “Bai kamata ku yi rawar jiki a gabana ba? Na sa yashi ya zama iyakar teku, madawwamiyar iyakar da ba zai tsallake ba. Raƙuman ruwa za su iya yin hauka, amma ba za su iya haye ta ba; za su iya yin ruri, amma ba za su iya ƙetare ta ba. Amma mutanen nan suna da tauraren zukata, kuma ’yan tawaye ne; sun kauce suka kuma rabu da ni. Ba sa faɗa wa kansu, ‘Bari mu ji tsoron Ubangiji Allahnmu, wanda yake ba mu ruwan sama a kan kari na kaka da na bazara, wanda kullum yake tabbatar mana da girbi.’ Laifofinku sun raba ku da waɗannan abubuwa; zunubanku sun hana ku samun alheri. “A cikin mutanena an sami mugaye waɗanda suke kwanton ɓauna kamar masu sa tarko wa tsuntsaye kamar waɗanda suke kafa tarko don su kama mutane. Kamar keji cike da tsuntsaye, gidajensu sun cika da ruɗu; sun yi arziki suka kuma zama masu iko suka kuma yi ƙiba, suka yi bul-bul. Mugayen ayyukansu ba su da iyaka; ba sa wa marayu shari’ar adalci, ba sa kāre ’yancin matalauta. Bai kamata in hukunta su saboda wannan ba?” In ji Ubangiji. “Bai kamata in yi ramuwa a kan irin al’umma kamar wannan ba? “Abin banmamaki da bantsoro ya faru a ƙasar. Annabawa suna annabcin ƙarya, firistoci suna mulki da ikon kansu, mutanena kuma suna son haka. Amma me za ku yi a ƙarshe? “Ku gudu neman mafaka, mutanen Benyamin! Ku gudu daga Urushalima! Ku busa ƙaho a Tekowa! Ku ba da alama a Bet-Hakkerem! Gama masifa tana zuwa daga arewa, mummunar hallaka ce kuwa. Zan hallaka Diyar Sihiyona, kyakkyawa da kuma mai laulayi. Makiyaya da garkunansu za su taso mata; za su kafa tentunansu kewaye da ita, kowanne yana lura da sashensa.” “Mu shirya don yaƙi da ita! Ku tashi, bari mu fāɗa mata da tsakar rana! Amma, kaito, rana tana fāɗuwa, inuwar yamma kuwa sai ƙaran tsawo take. Saboda haka ku tashi, bari mu fāɗa mata da dare mu rurrushe kagaranta!” Ga abin da Ubangiji Maɗaukaki yana cewa, “Ku sassare itatuwan ku tula ƙasa kewaye da Urushalima. Dole a hukunta wannan birni; saboda ya cika da zalunci. Kamar yadda rijiya takan ba da ruwarta, haka birnin yake da muguntarsa. Ana jin labarin rikici da hallaka a cikinsa; ciwonsa da mikinsa kullum suna a gabana. Ki ji gargaɗi, ya Urushalima, ko kuwa in juya daga gare ki in mai da ƙasarki kufai don kada wani ya zauna a cikinta.” Ga abin da Ubangiji Maɗaukaki yana cewa, “Bari su yi kalan raguwar Isra’ila a yi kalan sarai yadda ake yi wa inabi; ka sāke miƙa hannunka a kan rassan, kamar mai tattara inabi.” Ga wa zan yi magana in kuma gargaɗar? Wa zai saurare ni? Kunnuwansu sun toshe don kada su ji. Maganar Ubangiji ta zama abin zargi a gare su; ba sa jin daɗinta. Amma ina cike da fushin Ubangiji, kuma ba na iya kannewa. “Ka kwararo shi a kan yara a titi da kuma a kan samarin da suka tattaru; za a kama miji da mata a cikinsa, tsofaffi da suka tsufa tukub. Za a ba da gidajensu ga waɗansu, tare da gonakinsu da matansu, sa’ad da na miƙa hannuna gāba da waɗanda suke zama a ƙasar,” in ji Ubangiji. “Daga ƙarami zuwa babba, dukansu masu haɗama ne don riba; har da annabawa da firistoci, dukansu suna aikata rashin gaskiya. Sukan ɗaura mikin mutanena sai ka ce mikin ba shi da matsala. Suna cewa, ‘Lafiya, Lafiya,’ alhali kuwa ba lafiya. Suna jin kunyar halinsu na banƙyama? A’a, ba sa jin kunya sam; ba su ma san yadda za su soke kai ba. Saboda haka za su fāɗi tare da fāɗaɗɗu; za a hamɓarar da su sa’ad da na hukunta su,” in ji Ubangiji. Ga abin da Ubangiji yana cewa, “Ku tsaya kan hanyoyi, ku duba; ku nemi hanyoyin dā, ku tambaya inda hanyar mai kyau take, ku yi tafiya a kanta, za ku kuwa sami hutu wa rayukanku. Amma kun ce, ‘Ba za mu bi ta ba.’ Na naɗa muku masu tsaro a kanku na kuma ce, ‘Ku saurari karan ƙaho!’ Amma kuka ce, ‘Ba za mu saurara ba.’ Saboda haka ku, ya al’ummai; ku lura Ya shaidu, abin da zai faru da su. Ki ji, ya duniya. Zan kawo masifa a kan waɗannan mutane, sakayyar ƙulle-ƙullensu, domin ba su saurari maganata ba suka kuma ƙi dokata. Babu riba a kawo mini turare daga Sheba ko rake mai zaƙi daga ƙasa mai nisa? Ba zan karɓi hadayunku na ƙonawa ba; ba na jin daɗin sadakokinku.” Saboda haka ga abin da Ubangiji yana cewa, “Zan sa abin tuntuɓe gaban mutanena. Mahaifi da ’ya’yansa maza za su yi tuntuɓe a kan juna; maƙwabci da abokansa za su hallaka.” Ga abin da Ubangiji yana cewa, “Duba, sojoji suna zuwa daga ƙasar arewa; babbar al’umma ce ta yunƙuro daga iyakokin duniya. Suna riƙe da baka da māshi; mugaye ne kuma marasa tausayi. Motsinsu kamar ƙugin teku ne yayinda suke hawan dawakansu; suna zuwa a jere kamar wanda ya yi shirin yaƙi don su fāɗa miki, ya Diyar Sihiyona.” Mun ji labari a kansu, hannuwanmu kuwa suka yi laƙwas. Azaba ta kama mu, zafi kamar na mace mai naƙuda. Kada ku fita zuwa gonaki ko ku yi tafiya a hanyoyi, gama abokin gāba yana da takobi, kuma akwai razana ko’ina. Ya mutanena, ku sanya tufafin makoki ku yi birgima a toka; ku yi kuka mai zafi irin wanda akan yi wa ɗa tilo, gama nan da nan mai hallakarwa zai auko mana. “Na maishe ka mai jarrabawar ƙarfe mutanena ne kuwa ƙarfen, don ka lura ka kuma gwada hanyoyinsu. Su duka masu taurinkai ne, ’yan tawaye, suna yawo suna baza jita-jita. Su tagulla ne da ƙarfe; dukansu lalatattu ne. Mazuga yana zuga da ƙarfi don yă ƙone dalma da wuta, amma tacewa yana tafiya a banza; ba a fitar da mugaye. Ana ce da su azurfar da aka ƙi, gama Ubangiji ya ƙi su.” Maganar da ta zo wa Irmiya ke nan daga Ubangiji. “Ka tsaya a ƙofar gidan Ubangiji, a can kuwa ka yi shelar wannan saƙo. “ ‘Ku ji maganar Ubangiji, dukanku mutanen Yahuda waɗanda suke shiga ta waɗannan ƙofofi don yin sujada ga Ubangiji. Ga abin da Ubangiji Maɗaukaki, Allahna Isra’ila, yana cewa ku gyara hanyoyinku da ayyukanku, zan kuwa bar ku ku zauna a wannan wuri. Kada ku dogara ga maganganun nan na ruɗarwa cewa, “Wannan shi ne haikalin Ubangiji, haikalin Ubangiji, haikalin Ubangiji!” In dai kuka canja hanyoyinku da ayyukanku kuma kuna aikata adalci da junanku, in ba ku zalunci baƙo, maraya ko gwauruwa ba kuma in ba ku zub da jinin marar laifi a wannan wuri ba, in kuma ba ku bi waɗansu alloli da za su cuce ku ba, to, zan bar ku ku zauna a wannan wuri, a ƙasar da na ba kakanninku har abada abadin. Amma ga shi, kuna dogara ga maganganu na ruɗami marasa amfani. “ ‘Za ku yi sata da kisa, ku yi zina da rantsuwar ƙarya, kuna ƙone turare wa Ba’al kuna kuma bin waɗansu allolin da ba ku sani ba, sa’an nan ku zo ku tsaya a gabana a wannan gida, wanda ake kira da Sunana, kuna cewa, “An cece mu,” mun dace mu aikata waɗannan abubuwa banƙyama? Wannan gidan da ake kira da Sunana ya zama kogon ’yan fashi ne a gare ku? Amma ina kallo! In ji Ubangiji. “ ‘Yanzu ku fita zuwa Shilo inda na fara maishe shi wurin zama don Sunana, ku ga abin da na yi masa saboda muguntar mutanen Isra’ila. Yayinda kuke yin dukan waɗannan abubuwa, in ji Ubangiji, na yi muku magana sau da sau, amma ba ku ji ba; na kira ku, amma ba ku amsa ba. Saboda haka, abin da na yi wa Shilo shi ne yanzu zan yi wa gidan da ake kira da Sunana, haikalin da kuka dogara a kai, wurin da na ba ku da kuma kakanninku. Zan kore ku daga gabana, kamar yadda na yi ga dukan ’yan’uwanku, mutanen Efraim.’ “Saboda haka kada ka yi addu’a don wannan mutane ko ka yi wani kuka ko roƙo dominsu, gama ba zan ji ka ba. Ba ka gani abin da suke yi a biranen Yahuda da kuma a titunan Urushalima? Yara sukan tara itace, iyaye suka hura wuta, mata kuma sukan kwaɓa kullu don su yi wa Sarauniyar Sama waina. Sukan miƙa hadayun sha ga waɗansu alloli don su tsokane ni in yi fushi. Amma ni ne suke tsokana? In ji Ubangiji Ashe, ba kansu ne suke cuta, suna kunyata kansu ba? “ ‘Saboda haka ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa fushina da hasalata za su kwarara a wannan wuri, a kan mutum da dabba, a kan itatuwan fili da a kan amfanin gona, za su yi ta kuna, ba kuwa za a kashe ba. “ ‘Ga abin da Ubangiji Maɗaukaki, Allah na Isra’ila yana cewa ci gaba, ku ƙara hadayun ƙonawarku da sauran sadakoki ku kuma yi ta cin naman! Gama sa’ad da na fitar da kakanninku daga Masar na kuma yi musu magana, ban ba su dokoki kawai game da hadayun ƙonawa da sadakoki ba, amma na ba su wannan umarni cewa ku yi mini biyayya, zan kuwa zama Allahnku ku kuma ku zama mutanena. Ku yi tafiya cikin dukan hanyoyin da na umarce ku, don ku zauna lafiya. Amma ba su saurara ba, ba su kuwa kula ba; a maimako, suka bi shawarar kansu da ta taurare muguwar zukatansu. Su ja da baya a maimakon yin gaba. Daga lokacin da kakanninku suka bar Masar har yă zuwa yau, kullum na yi ta aikan bayina annabawa. Amma ba su saurare ni ba, ba su kula ba. Sai suka taurare zukatansu suka aikata mugun abu fiye da na kakanninsu.’ “Sa’ad da ka faɗa musu wannan duka, ba za su saurare ka ba; sa’ad da ka kira su, ba za su amsa ba. Saboda haka ka faɗa musu cewa, ‘Wannan ce al’ummar da ba tă yi biyayya ga Ubangiji Allahnta ba, ba kuwa ta karɓi gyara ba. Gaskiya ta ƙare; ta ɓace gaba ɗaya daga leɓunansu. “ ‘Ku aske gashin kanku ku zubar; ku yi makoki a filayen tuddai, gama Ubangiji ya ƙi ’yan zamanin nan ya kuma rabu da su saboda fushin da suka ba shi. “ ‘Mutanen Yahuda sun yi mugunta a gabana, in ji Ubangiji. Sun kafa gumakansu masu banƙyama a gidan da ake kira da Sunana suka ƙazantar da shi. Sun gida masujadan Tofet a Kwarin Ben Hinnom don miƙa ’ya’yansu maza da mata a wuta, abin da ban yi umarni ba, ba kuwa yi tunaninsa ba. Saboda haka ku yi hankali, kwanaki suna zuwa in ji Ubangiji, sa’ad da mutane ba za su ƙara kira wurin Tofet ko Kwarin Ben Hinnom ba, amma Kwarin Kisa, gama za su binne matattu a Tofet sai har ba sauran wuri. Sa’an nan gawawwakin wannan mutane za su zama abinci ga tsuntsayen sama da kuma namun jeji, ba za a kuwa sami wani da zai kore su ba. Zan kawo ƙarshen muryar murna da farin ciki da muryar amarya da ango a garuruwan Yahuda da kuma a titunan Urushalima, gama ƙasar za tă zama kufai. “ ‘A wancan lokaci, in ji Ubangiji, za a fitar da ƙasusuwan sarakuna da na shugabannin Yahuda, ƙasusuwan firistoci da na annabawa, da kuma ƙasusuwan mutanen Urushalima daga kaburbura. Za a shimfiɗa su a rana da wata da kuma dukan taurarin sammai, waɗanda suka ƙaunata suka kuma bauta wa, waɗanda suka bi suka nemi shawarar suka kuma yi wa sujada. Ba za a tattara su ko a binne su ba, amma za su zama kamar juji a jibge a ƙasa. Duk inda na kore su zuwa, dukan waɗanda suka ragu na wannan muguwar al’umma za su gwammaci mutuwa da rai, in ji Ubangiji Maɗaukaki.’ “Fada musu cewa, ‘Ga abin da Ubangiji yana cewa, “ ‘Sa’ad da mutane suka fāɗi, ba sa tashi ne? Sa’ad da mutum ya kauce, ba ya dawowa? To, me ya sa waɗannan mutane suka kauce? Me ya sa Urushalima kullum take kaucewa? Sun manne wa ƙarya; suka ƙi su dawo. Na saurara sosai, amma ba su faɗi wata maganar kirki ba. Ba wanda ya tuba daga muguntarsa, sai ma cewa yake, “Me na yi?” Kowa ta kai-ta-kai yake kamar dokin da ya kutsa kai a fagen fama. Ko shamuwa ta sararin sama ma takan san lokutan da aka tsara mata, kurciya, mashirare da kuma zalɓe sukan lura da lokacin ƙauransu. Amma mutanena ba su san abubuwan da Ubangiji yake bukata ba. “ ‘Yaya za ku ce, “Muna da hikima, gama muna da dokar Ubangiji,” alhali alƙalamin ƙarya na magatakarda ya yi ƙarya? Za a kunyatar da masu hikima; za su yi fargaba a kuma kama su. Da yake sun ƙi maganar Ubangiji, wace irin hikima kuka ce kuke da ita? Saboda haka zan ba da matansu ga waɗansu gonakinsu kuma ga waɗansu da suka ci da yaƙi. Tun daga ƙarami har zuwa babba, kowannensu yana haɗamar cin muguwar riba; har da annabawa da firistoci ma, kowannensu yana ƙarya. Sukan ɗaura mikin mutanena sai ka ce mikin ba shi da matsala. Suna cewa, “Lafiya, Lafiya,” alhali kuwa ba lafiya. Sukan ji kunyar halin banƙyamarsu kuwa? Sam, ba su da kunya ko kaɗan; ba su ma san yadda za su ji kunya ba. Saboda haka sukan fāɗi tare da fāɗaɗɗu; za su fāɗi sa’ad da aka hukunta su, in ji Ubangiji. “ ‘Zan ƙwace girbinsu, in ji Ubangiji. Ba a za sami inabi a kuringa ba. Ba za a sami ’ya’ya a itacen ɓaure ba, ganyayensu kuwa za su bushe. Abin da na ba su za a ƙwace.’ ” Me ya sa muke zama a nan? Mu tattaru! Mu gudu zuwa birane masu katanga mu mutu a can! Gama Ubangiji Allahnmu ya ƙaddara mana mutuwa ya kuma ba mu ruwan dafi mu sha, domin mun yi masa zunubi. Mun sa zuciya ga salama amma ba lafiya, mun sa zuciya ga lokacin warkarwa amma sai ga razana. Daga Dan ana jin tirjin dawakan abokin gāba; da jin haniniyar ingarmunsu dukan ƙasar ta girgiza. Sun zo su cinye ƙasar da kome da yake cikinta, birni da dukan mazaunanta. “Duba, zan aika macizai masu dafi a cikinku, kāsā, waɗanda ba su da maƙari, za su kuwa sassare ku,” in ji Ubangiji. Ya mai ta’aziyyata a cikin baƙin ciki, zuciyata ta ɓaci ƙwarai. Ka saurari kukan mutanena daga ƙasa mai nisa suna cewa, “ Ubangiji ba ya a Sihiyona ne? Sarkinta ba ya can ne kuma?” “Me ya sa suka tsokane ni da gumakansu har na yi fushi, da baƙin gumakansu marasa amfani?” “Girbi ya wuce, damuna ta ƙare, ba a kuwa cece mu ba.” Da yake an ragargazar da mutanena, an ragargaza ni ke nan; na yi kuka, tsoro ya kama ni. Ba magani ne a Gileyad? Ba likita ne a can? To, me ya sa ba warkarwa wa raunin mutanena? Da ma kaina maɓulɓulan ruwa ne idanuna kuma maɓulɓulan hawaye! Da sai in yi kuka dare da rana saboda mutanena da aka kashe. Da ma a hamada ina da wurin da matafiye za su sauka, don in bar mutanena in tafi in bar su; gama dukansu mazinata ne, taron mutane marasa aminci. “Sun tanƙwasa harshensu kamar baka, don su harba ƙarya; ba da gaskiya ba ne suke nasara a cikin ƙasar. Sukan tashi daga wannan zunubi zuwa wancan; ba su san ni ba,” in ji Ubangiji. “Ka yi hankali da abokanka; kada ka amince da ’yan’uwanka. Gama kowane ɗan’uwa munafuki ne, kowane aboki kuma mai kushe ne. Aboki kan ruɗi aboki, ba mai faɗar gaskiya. Sun koya wa harshensu faɗar ƙarya; sun gajiyar da kansu da yin zunubi. Kai kana zama a tsakiyar ruɗu; cikin ruɗunsu sun ƙi su san ni,” in ji Ubangiji. Saboda haka ga abin da Ubangiji Maɗaukaki yana cewa, “Ga shi zan tace in kuma gwada su, gama me kuwa zan yi saboda zunubin mutanena? Harshensu kibiya ce mai dafi; yana magana da ruɗu. Da bakinsa kowa yana maganar alheri da maƙwabcinsa, amma a zuciyarsa ya sa masa tarko. Bai kamata in hukunta su saboda wannan ba?” In ji Ubangiji. “Bai kamata in ɗau fansa a kan irin al’umma kamar wannan ba?” Zan yi kuka in yi kururuwa saboda duwatsu in kuma yi makoki game da wuraren kiwon hamada. Sun zama kango ba wanda yake bi cikinta, ba a kuma jin kukan shanu. Tsuntsaye sararin sama sun gudu namun jeji ma duk sun watse. “Zan mai da Urushalima tsibin kufai, wurin zaman diloli; zan kuma lalace garuruwan Yahuda saboda haka ba wanda zai zauna a can.” Wane mutum ne yana da isashiyar hikimar fahimtar wannan? Wa Ubangiji ya umarta da zai iya yin bayani? Me ya sa aka lalace ƙasar ta zama kufai kamar hamada da ba wanda zai iya ratsa ta? Ubangiji ya ce, “Domin sun bar dokata, wadda na sa a gabansu; ba su yi biyayya da ni ko su bi dokata ba. A maimako, sun bi taurin zuciyarsu; suka bi Ba’al, yadda kakanninsu suka koya musu.” Saboda haka, ga abin da Ubangiji Maɗaukaki, Allah na Isra’ila yana cewa, “Ga shi zan sa wannan mutane su ci abinci mai ɗaci su kuma sha ruwan dafi. Zan watsar da su a cikin al’ummai da su da kakanninsu ba su sani ba, zan kuma fafare su da takobi sai na hallaka su.” Ga abin da Ubangiji Maɗaukaki yana cewa, “Ku lura yanzu! Ku kira mata masu makoki su zo ku aika wa gwanaye a cikinsu su zo. Bari su zo da sauri su yi kuka a kanmu sai idanunmu sun cika da hawaye giranmu kuma su jiƙe sharkaf. An ji karar kuka daga Sihiyona cewa, ‘Duba yadda muka lalace! Duba irin babban kunyar da muka sha! Dole mu bar ƙasar domin gidajenmu sun lalace.’ ” Yanzu, ya mata, ku ji maganar Ubangiji; ku buɗe kunnuwanku ga maganar bakina. Ku koya wa ’yan matanku yadda za su yi kuka; ku koya wa juna makoki. Mutuwa ta haura ta tagoginmu ta kuma shiga katangarmu; ta karkashe ’ya’ya a tituna ta kuma karkashe samari a dandali. Ka ce, “Ga abin da Ubangiji ya furta, “ ‘Gawawwakin mutane za su fāɗi kamar juji a fili, kamar hatsin da aka yanka a bayan mai girbi, da ba mai tara su.’ ” Ga abin da Ubangiji yana cewa, “Kada mai hikima ya yi fariya da hikimarsa ko mai ƙarfi ya yi fariya da ƙarfinsa ko mai arziki ya yi fariya da arzikinsa, amma bari shi wanda yake taƙama ya yi taƙama da wannan, cewa ya fahimci ya kuma san ni, cewa ni ne Ubangiji, wanda yake yin alheri, gaskiya da kuma adalci a duniya, gama a waɗannan ne nake jin daɗi,” in ji Ubangiji. “Kwanaki suna zuwa,” in ji Ubangiji, “sa’ad da zan hukunta dukan waɗanda aka yi musu kaciya kawai a jiki, Masar, Yahuda, Edom, Ammon, Mowab da dukan waɗanda suke zaune a hamada a wurare masu nisa. Gama dukan waɗannan al’ummai marasa kaciya ne, har dukan gidan Isra’ila ma marasa kaciya ne a zuciya.” Ku ji abin da Ubangiji yana ce muku, ya gidan Isra’ila. Ga abin da Ubangiji yana cewa, “Kada ku koyi hanyoyin al’ummai ko ku razana game da alamun sararin sama, ko da yake al’ummai sun razana saboda su. Gama al’adun mutane banza ne; sukan yanke itace daga kurmi, sai mai sassaƙa yă sassaƙa shi da gizago. Sukan yi masa ado da azurfa da kuma zinariya; sukan ɗauki guduma su kafa shi da ƙusoshi, don kada yă fāɗi. Kamar dodon gona cikin gonar kabewa, haka gumakansu ba sa iya magana; dole a yi ta ɗaukansu domin ba za su iya tafiya ba. Kada ku ji tsoronsu; ba za su iya yi wa wani lahani ba ba sa iya yin wani abin kirki.” Babu wani kamar ka, ya Ubangiji; kai mai girma ne, kuma sunanka yana da girma da kuma iko. Wane ne ba zai girmama ka ba, Ya Sarkin al’ummai? Tsoronka wajibi ne. A cikin dukan masu hikima na al’ummai kuma cikin dukan mulkokinsu, babu kamar ka. Dukansu marasa azanci ne wawaye; gumakan itacen banza ne suke koya musu. An kawo ƙeraren azurfa daga Tarshish zinariya kuma daga Ufaz. Abin da gwani da maƙerin zinariya suka yi sa’an nan aka yi masa ado da mulufi da shunayya dukan aikin gwanaye. Amma Ubangiji shi ne Allah na gaskiya; shi ne Allah mai rai, madawwamin sarki. Sa’ad da ya yi fushi, ƙasa takan girgiza; al’ummai ba sa iya jure da hasalarsa. “Ka faɗa musu wannan, ‘Waɗannan alloli, waɗanda ba su yi sammai da ƙasa ba, za su hallaka daga duniya da kuma daga ƙarƙashin sammai.’ ” Amma Allah ya yi duniya ta wurin ikonsa; ya kafa duniya ta wurin hikimarsa ya shimfiɗa sammai ta wurin fahiminsa. Sa’ad da ya yi tsawa, ruwaye a cikin sammai sukan yi ƙugi; yakan sa gizagizai su taso daga iyakokin duniya. Yakan aiki walƙiya da ruwan sama ya fitar da iska daga gidajen ajiyarsa. Kowa marar azanci ne, marar ilimi; kowane maƙerin zinariya zai sha kunya saboda gumakansa. Siffofinsa ƙarya ne; ba su da numfashi a cikinsu. Su ba kome ba ne, aikin ruɗami ne; Sa’ad da hukuncinsu ya yi za su lalace. Shi da yake Rabon Yaƙub ba kamar waɗannan yake ba, gama shi ne Mahaliccin abubuwa duka, har da Isra’ila, kabilar gādonsa Ubangiji Maɗaukaki ne sunansa. Ku tattara kayayyakinku don ku bar ƙasar, ku da kuke zaune a wurin da aka kewaye da yaƙi. Gama haka Ubangiji ya faɗa, “A wannan lokaci zan jefar da waɗanda suke zaune a ƙasar; zan kawo damuwa a kansu domin a kama su.” Tawa ta ƙare, saboda raunin da aka yi mini! Raunina ba mai warkewa ba ne! Duk da haka na ce wa kaina, “Wannan ciwona ne, dole kuma in jure da shi.” An lalatar da tentina; dukan igiyoyinsa sun tsintsinke. ’Ya’yana maza sun bar ni ba sa nan; ba wanda aka bari da zai kafa tentina ko ya kafa mini mafaka. Makiyaya marasa azanci ne kuma ba sa neman nufin Ubangiji; saboda haka ba sa nasara dukan garkensu kuwa ya watse. Ku saurara! Rahoto yana zuwa babban hargitsi daga ƙasar arewa! Zai mai da garuruwan Yahuda kufai, mazaunin diloli. Na sani, ya Ubangiji, cewa ran mutum ba nasa ba ne; ba mutum ne yake kiyaye takawarsa ba. Ka yi mini gyara, Ubangiji, amma fa da adalci kaɗai ba cikin fushinka ba, don kada ka wofinta ni. Ka zuba hasalarka a kan al’umman da ba su san ka ba, a kan mutanen da ba sa kira bisa sunanka. Gama sun cinye Yaƙub; sun cinye shi gaba ɗaya suka kuma lalace wurin zamansa. Ga maganar da ta zo wa Irmiya daga wurin Ubangiji. “Ka saurari zancen wannan alkawari ka kuma faɗe su ga mutanen Yahuda da kuma waɗanda suke zaune a Urushalima. Ka faɗa musu cewa ga abin da Ubangiji, Allah na Isra’ila yana cewa, ‘La’ananne ne wanda bai kula da zancen alkawarin nan ba, zancen da na umarci kakanni-kakanninku sa’ad da na fitar da su daga Masar, daga cikin tanderun narkewar ƙarfe.’ Na ce, ‘Ku yi mini biyayya ku kuma aikata kowane abin da na umarce ku, za ku kuwa zama mutanena, ni kuwa zan zama Allahnku. Sa’an nan zan cika rantsuwar da na yi wa kakanni-kakanninku, da zan ba su ƙasa mai zub da madara da kuma zuma’ ƙasar da kuka mallaka a yau.” Sai na amsa na ce, “Amin, Ubangiji.” Sai Ubangiji ya ce mini, “Ka yi shelar dukan maganan nan a biranen Yahuda da titunan Urushalima duka cewa, ‘Su saurari zancen alkawarin nan, su aikata. Daga lokacin da na fitar da kakanni-kakanninku daga Masar har yă zuwa yau, na gargaɗe su sau da sau, ina cewa, “Ku yi mini biyayya.” Amma ba su kasa kunne ko su saurara ba, a maimako, sai suka bi taurinkai na mugayen zukatansu. Saboda haka na kawo musu dukan la’anonin alkawarin da na riga na umarce su, su bi amma ba su kiyaye ba.’ ” Sa’an nan Ubangiji ya ce mini, “Akwai maƙarƙashiya a cikin mutanen Yahuda da waɗanda suke zaune a Urushalima. Sun koma ga zunuban kakanni kakanninsu, waɗanda suka ƙi su saurari maganata. Suka bi waɗansu alloli don su bauta musu. Da gidan Isra’ila da kuma gidan Yahuda duk sun take alkawarin da na yi da kakanni kakanninsu. Saboda haka ga abin da Ubangiji yana cewa, ‘Zan kawo masifa a kansu wadda ba za su iya tsere mata ba. Ko da yake suna kuka gare ni, ba zan saurare su ba. Garuruwan Yahuda da mutanen Urushalima za su tafi su yi kuka ga allolin da suke ƙona wa turare, amma ba za su taimake su ba sam sa’ad da masifar ta auku. Kuna da alloli masu yawa yadda kuke da garuruwa, ya Yahuda; kuma bagadan da kuka yi don ƙona turare wa allahn nan Ba’al abin kunya sun yi yawa kamar titunan Urushalima.’ “Kada ka yi addu’a domin wannan mutane ko ka miƙa wani roƙo ko kuka dominsu, domin ba zan saurara ba sa’ad da suka kira gare ni a lokacin ƙuncinsu. “Mene ne ƙaunatacciyata take yi a haikali da yake ta yin ƙulle-ƙullen mugayen makircinta tare da mutane masu yawa? Tsarkakar nama zai iya kawar da hukuncinki? Sa’ad da kike yin muguntarki sa’an nan ki yi farin ciki.” Ubangiji ya kira ki itacen zaitun mai inuwa kyakkyawa mai ’ya’ya masu kyau. Amma da ƙugin babbar hadari zai cinna masa wuta, rassansa za su kakkarye. Ubangiji Maɗaukaki, wanda ya dasa ki, ya furta miki masifa, domin gidan Isra’ila da kuma gidan Yahuda sun aikata mugunta suka kuma tsokane ni in yi fushi ta wurin ƙona wa Ba’al turare. Domin Ubangiji ya bayyana mini maƙarƙashiyarsu, na santa, gama a wannan lokaci ya nuna mini abin da suke yi. Na kasance kamar ɗan rago marar faɗa wanda aka kai mayanka; ban gane cewa sun ƙulla mini maƙarƙashiya, suna cewa, “Bari mu lalatar da itacen duk da ’ya’yansa; bari mu datse shi daga ƙasar masu rai, har da ba za a ƙara tunawa da sunansa ba.” Amma, ya Ubangiji Maɗaukaki, kai da kake yin shari’a da adalci kake gwada zuciya da kuma tunani, ka sa in ga sakayyar da za ka yi musu, gama a gare ka na danƙa maganata. “Saboda haka ga abin da Ubangiji yana cewa game da mutanen Anatot, waɗanda suke neman ranka suna kuma cewa, ‘Kada ka yi annabci da sunan Ubangiji in ba haka za ka mutu a hannunmu’ saboda haka ga abin da Ubangiji Maɗaukaki yana cewa, ‘Zan hukunta su. Samarinsu za su mutu ta wurin takobi, ’ya’yansu maza da mata kuwa ta wurin yunwa. Babu raguwar da za a bar musu, domin zan kawo masifa a kan mutanen Anatot a shekarar hukuncinsu.’ ” Kullum kai mai adalci ne, ya Ubangiji, sa’ad da na kawo ƙara a gabanka. Duk da haka zan yi magana da kai game da shari’arka. Me ya sa mugaye suke nasara? Me ya sa dukan maciya amana suke zama ba damuwa? Ka dasa su, sun kuwa yi saiwa; sun yi girma suna ba da ’ya’ya. Kullum sunanka yana a bakinsu amma kana nesa da zuciyarsu. Duk da haka ka san ni, ya Ubangiji; kana ganina ka kuma gwada tunanina game da kai. Ka ja su kamar tumakin da za a yanka! Ka ware su don ranar yanka! Har yaushe ƙasar za tă kasance busasshiya ciyawar kowane fili ta bushe? Domin waɗanda suke zaune cikinta mugaye ne, dabbobi da tsuntsaye sun hallaka. Ban da haka ma, mutane suna cewa, “Ba zai ga abin da yake faruwa da mu ba.” “In ka yi tsere da mutane a ƙafa suka kuma gajiyar da kai, yaya za ka yi gasa da dawakai? In ka yi tuntuɓe a lafiyayyiyar ƙasa, ƙaƙa za ka yi a kurmin Urdun? ’Yan’uwanka, iyalinka har su ma sun bashe ka; sun tā da kuka mai ƙarfi a kanka. Kada ka amince da su, ko da yake suna faɗa maganganu masu kyau game da kai. “Zan yashe gidana, in rabu da gādona; Zan ba da wadda nake ƙauna a hannuwan abokan gābanta. Gādona ya zama mini kamar zaki a kurmi. Yana mini ruri; saboda haka na ƙi shi. Ashe, gādona bai zama mini kamar dabbare dabbaren tsuntsu mai cin nama da sauran tsuntsaye masu cin nama suka kewaye shi da faɗa ba? Tafi ka tattaro dukan namun jeji; ka kawo su su ci. Makiyaya masu yawa za su lalace gonar inabina su tattake gonata; za su mai da gonata mai kyau kango marar amfani. Za tă zama kango, busasshiya da kuma kango a gabana; ƙasar duka za tă zama kango domin ba wanda ya kula. A kan dukan tsaunukan nan na hamada masu hallakarwa za su zo, gama takobin Ubangiji zai ci daga wannan iyaka ƙasa zuwa wancan; ba wanda zai zauna lafiya. Za su shuka alkama, su girbe ƙayayyuwa; za su gajiyar da kansu, ba za su kuwa sami kome ba. Saboda haka ku sha kunyar abin da kuka girbe saboda zafin fushin Ubangiji.” Ga abin da Ubangiji yana cewa, “Game da dukan mugayen maƙwabtana waɗanda suka ƙwace gādon da na ba wa mutanena Isra’ila kuwa, zan tumɓuke su daga ƙasashensu zan kuma tumɓuke gidan Yahuda daga cikinsu. Amma bayan na tumɓuke su, zan sāke jin tausayi in komo da kowannensu zuwa gādonsa da kuma ƙasarsa. In kuma suka koyi al’amuran mutanena sosai suka kuma yi rantsuwa da sunana, suna cewa, ‘Muddin Ubangiji yana raye’ kamar yadda sun taɓa koya wa jama’ata yin rantsuwa da Ba’al, sa’an nan za su kahu a cikin jama’ata. Amma duk al’ummar da ba tă saurara ba, zan tumɓuke ta ɗungum in kuma hallaka ta,” in ji Ubangiji. Ga abin da Ubangiji ya faɗa mini, “Tafi ka sayo abin ɗamara na lilin ka sha ɗamara da shi, amma kada ka bari yă taɓa ruwa.” Saboda haka na sayo abin ɗamara, yadda Ubangiji ya umarce ni, na kuwa sha ɗamara da shi. Sai maganar Ubangiji ta zo mini sau na biyu cewa, “Ka ɗauki abin ɗamara da ka sayo, wanda ka ɗaura, ka tafi yanzu zuwa Fera ka ɓoye shi a cikin kogon dutse.” Saboda haka na tafi na ɓoye shi a Fera, yadda Ubangiji ya ce mini. Bayan ’yan kwanaki sai Ubangiji ya ce mini, “Tafi yanzu zuwa Fera ka ɗauko abin ɗamara da na ce maka ka ɓoye a can.” Sai na tafi Fera da haka na ɗauko abin ɗamara daga wurin da na ɓoye shi, amma abin ɗamara yanzu ya lalace ya zama ba shi da amfani sam. Sai maganar Ubangiji ta zo mini cewa, “Ga abin da Ubangiji yana cewa, ‘Haka zan lalatar da alfarmar Yahuda da yawan alfarmar Urushalima. Waɗannan mugayen mutane, waɗanda suka ƙi saurari maganata, waɗanda suka biye wa taurin zuciyarsu suka bi waɗansu alloli don su bauta su kuma yi musu sujada, za su zama kamar wannan abin ɗamara gaba ɗaya marasa amfani! Gama kamar yadda abin ɗamara kan kame gindin mutum tam, haka zan daure dukan gidan Isra’ila da dukan gidan Yahuda gare ni,’ in ji Ubangiji, ‘domin su zama jama’a, da suna, da yabo, da daraja a gare ni, amma sun ƙi ji.’ “Faɗa musu cewa, ‘Ga abin da Ubangiji, Allah na Isra’ila, yana cewa a cika kowace salkar ruwan inabi da ruwan inabi.’ In kuwa suka ce maka, ‘Ba mu san cewa ya kamata a cika kowace salkar ruwan inabi da ruwan inabi ba?’ Sai ka ce musu, ‘Ga abin da Ubangiji yana cewa, zan cika dukan waɗanda suke zama a ƙasar da buguwa, har ma da sarakunan da suke zama a kursiyin Dawuda, firistoci, annabawa da dukan waɗanda suke zaune a Urushalima. Zan fyaɗe su a kan juna, iyaye da ’ya’yansu maza, in ji Ubangiji. Tausayi ko jinƙai, ko juyayi ba zai hana ni hallaka su ba.’ ” Ku ji ku kuma saurara, kada ku yi girman kai, gama Ubangiji ya yi magana. Ku ɗaukaka Ubangiji Allahnku kafin ya kawo duhu, kafin ƙafafunku su yi tuntuɓe a kan tuddai masu duhu. Za ku sa zuciya ganin haske amma zai mai da shi duhu mai kauri ya kuma canja shi zuwa duhu baƙi ƙirin. Amma in ba ku saurara ba, zan yi kuka a ɓoye saboda girmankanku; idanuna za su yi kuka mai zafi, suna zub da hawaye ƙwarai, domin zan kwashe garken Ubangiji zuwa zaman bauta. Ka faɗa wa sarki da kuma mahaifiyar sarauniya cewa, “Ku sauko daga kursiyinku, gama rawaninku na ɗaukaka za su fāɗi daga kawunanku.” Za a kulle biranen da suke a Negeb, kuma babu wanda zai buɗe su. Za a kwashe dukan Yahuda zuwa zaman bauta, za a kwashe su tas. Ku tā da idanunku ku ga waɗanda suke zuwa daga arewa. Ina garken da aka ba ku tumakin da kuke taƙama a kai? Me za ku ce sa’ad da Ubangiji ya naɗa muku waɗanda ku kanku kuka koya musu a matsayi abokai na musamman? Ashe, azaba ba za tă auko muku kamar na mace mai naƙuda ba? In kuma kuka tambaye kanku “Me ya sa wannan ya faru da mu?” Wannan kuwa saboda yawan zunubanku ne ya sa fatarinku ya yage aka kuma wahalshe jikinku. Mutumin Habasha zai iya canja launin fatar jikinsa ko damisa ta canja dabbare dabbarenta? Ba za ku iya yin alheri ku da kuka saba da yin mugunta ba. “Zan watsar da ku kamar yayin da iskar hamada take hurawa. Rabonku ne wannan, sashen da na auka muku,” in ji Ubangiji “domin kun manta da ni kuka kuma dogara ga allolin ƙarya. Zan kware fatarinku sama ya rufe fuskarku don a iya ga tsiraicinku zinace zinacenku da haniniya kamar dawakai, karuwancinku na bankunya! Na ga ayyukanku na banƙyama a kan tuddai da kuma a filaye. Kaitonki, ya Urushalima! Har yaushe za ki ci gaba da rashin tsarki?” Ga maganar Ubangiji da ta zo wa Irmiya game da fări cewa, “Yahuda tana makoki biranenta suna fama; suna kuka saboda ƙasar, kuka kuma tana tasowa daga Urushalima. Manyan mutane suna aika bayinsu su ɗebo ruwa a maɓulɓulai amma babu ruwa. Suka dawo da tulunansu haka nan; da kunya da kuma ƙasƙanci, da kawunansu a rufe. Ƙasa ta tsattsage saboda babu ruwan sama a ƙasar; manoma sun sha kunya suka kuma rufe kawunansu. Har barewa a kurmi ma ta gudu ta bar ’ya’yan da ta haihu sababbi saboda babu ciyawa. Jakan jeji suna tsaye a kan tuddai suna haki kamar diloli; idanunsu sun kāsa gani saboda rashin makiyaya.” Ko da yake zunubanmu suna ba da shaida a kanmu, Ya Ubangiji, ka yi wani abu saboda sunanka. Gama jan bayanmu ya yi yawa; mun yi maka zunubi. Ya kai, Sa Zuciyar Isra’ila, Mai Cetonsa a lokutan wahala, me ya sa kake yi kamar baƙo a ƙasar, kamar matafiyi wanda yake shirya wuri don yă kwana gari ya waye ya wuce? Me ya sa kake yi kamar mutumin da aka far masa kwasam ba zato, kamar jarumi marar ƙarfin ceto? Kana a cikinmu, ya Ubangiji, da sunanka ake kiranmu; kada ka yashe mu! Ga abin da Ubangiji ya ce game da wannan mutane, “Suna son yawace-yawace ƙwarai; ba sa hana ƙafafunsu yawo. Saboda haka Ubangiji bai yarda da su ba; yanzu zai tuna da muguntarsu zai kuma hukunta su saboda zunubansu.” Sa’an nan Ubangiji ya ce mini, “Kada ka yi addu’a domin zaman lafiyar mutanen nan. Ko da yake suna azumi, ba zan saurari kukansu ba, ko da yake suna miƙa hadayun ƙonawa da hadayun gari, ba zan yarda da su ba. A maimako zan hallaka su da takobi, yunwa da annoba.” Amma na ce, “A, Ubangiji Mai Iko Duka, annabawa sun riƙa ce musu, ‘Ba za ku ga takobi ko ku yi fama da yunwa ba. A maimako, zan ba ku madawwamiyar salama.’ ” Sai Ubangiji ya ce mini, “Annabawa suna ta annabcin ƙarya da sunana. Ban aike su ba, ban kuma naɗa su ba, ban yi musu magana ba. Suna muku annabci wahayin ƙarya, suna muku duba marar amfani, suna bautar gumaka suna kuma bayyana tunanin kansu ne. Saboda haka, ga abin da Ubangiji ya ce game da annabawan da suke annabci da sunana. Ban aike su ba, duk da haka suna cewa, ‘Babu takobi ko yunwar da zai taɓa wannan ƙasa.’ Waɗannan annabawa takobi da yunwa za su hallaka su. Mutanen da suke musu annabcin kuwa za a kore su zuwa titunan Urushalima saboda yunwa da kuma takobi. Babu wanda zai binne su, ko ya binne matansu, ko ’ya’yansu maza da mata. Zan aukar musu da masifar da ya dace da su. “Ka yi musu wannan magana, “ ‘Bari idanuna su yi ta zub da hawaye dare da rana kada su daina; saboda ’yata budurwa, mutanena, sun sha wahalar babban rauni, an yi musu bugu mai ragargazawa. In na shiga cikin ƙasar, na ga waɗanda takobi ya kashe; in na shiga cikin birni, na ga waɗanda suke fama da yunwa. Da Annabi da firist duk sun tafi ƙasar da ba su sani ba.’ ” Ka ƙi Yahuda ɗungum ke nan? Kana ƙyamar Sihiyona ne? Me ya sa ka buge mu don kada mu warke? Mun sa zuciya ga salama babu abin alherin da ya zo, mun sa rai ga lokacin warkarwa amma sai ga razana. Ya Ubangiji, mun gane da muguntarmu da kuma laifin kakanninmu; tabbatacce mun yi maka zunubi. Saboda sunanka kada ka ƙi mu; kada ka ƙasƙantar da kursiyoyinka mai ɗaukaka. Ka tuna da alkawarinka da mu kada ka tā da shi. Akwai wani daga cikin gumaka marasa amfani na al’ummai da ya kawo ruwan sama? Sararin sama kansu sukan yi yayyafi? A’a, kai ne, ya Ubangiji Allahnmu. Saboda haka sa zuciyarmu tana a kanka, gama kai ne kake yi wannan duka. Sai Ubangiji ya ce mini, “Ko da Musa da Sama’ila za su tsaya a gabana, zuciyata ba za tă komo ga mutanen nan ba. Ka kore su daga gabana! Su tafi! In kuma suka tambaye ka, ‘Ina za mu tafi?’ Sai ka faɗa musu, ‘Ga abin da Ubangiji yana cewa, “ ‘Waɗanda aka ƙaddara ga mutuwa, ga mutuwa za su; waɗanda aka ƙaddara ga takobi, ga takobi za su; waɗanda aka ƙaddara ga yunwa, ga yunwa za su; waɗanda aka ƙaddara ga zaman bauta, ga zaman bauta za su.’ “Zan aika musu da iri masu hallakarwa guda huɗu,” in ji Ubangiji, “takobi zai kashe, karnuka za su kwashe, tsuntsaye da namun jeji kuma su cinye su kuma hallaka. Zan sa su zama abin ƙyama ga dukan mulkokin duniya saboda abin da Manasse ɗan Hezekiya sarkin Yahuda ya aikata a Urushalima. “Wa zai ji tausayinki, ya Urushalima? Wa zai yi makoki dominki? Wa zai dakata ya tambayi lafiyarki? Kin ƙi ni,” in ji Ubangiji. “Ki ci gaba da ja da baya. Ta haka zan ɗibiya hannuwana a kanki in hallaka ki; ba zan ƙara nuna miki jinƙai ba. Zan sheƙe ki da abin sheƙewa a ƙofofin birnin ƙasar. Zan kawo baƙin ciki da hallaka a kan mutanena, gama ba su canja hanyoyinsu ba. Zan ƙara yawan gwaurayensu su fi yashin teku yawa. Da tsakar rana zan kawo mai hallakarwa a kan iyaye mata na samarinsu; farat ɗaya zan kawo musu wahala da razana. Mahaifiya ’ya’ya bakwai za tă suma ta ja numfashinta na ƙarshe. Ranarta zai fāɗi tun lokacin bai yi ba; za tă sha kunya a kuma wulaƙanta ta. Zan sa a kashe raguwa da takobi a gaban abokan gābansu,” in ji Ubangiji. Kaitona, mahaifiyata, da kika haife ni, mutumin da dukan ƙasa take faɗa take kuma gardama da shi! Ban ba da bashi ko in ci bashi ba, duk da haka kowa yana zagina. Ubangiji ya ce, “Tabbatacce zan cece ka don alheri; tabbatacce zan sa abokan gābanka su yi roƙo gare ka a lokacin masifa da kuma lokacin wahala. “Mutum zai iya karye ƙarfe ƙarfe daga arewa, ko tagulla? “Dukiyarku da arzikinku zan ba da su ganima, babu tara, saboda duka zunubanku ko’ina a ƙasar. Zan bautar da ku ga abokan gābanku a ƙasar da ba ku sani ba, gama fushina zai yi ƙuna kamar wuta da za tă yi ƙuna a kanku.” Ka gane, ya Ubangiji; ka tuna da ni ka kuma lura da ni. Ka yi mini ramuwa a kan masu tsananta mini. Cikin jimirinka, kada ka ɗauke ni; ka tuna yadda na sha zagi saboda kai. Sa’ad da maganganunka suka zo, na cinye su; suka zama abin farin ciki zuciyata kuma ta yi murna, gama ana kirana da sunanka, Ya Ubangiji Allah Maɗaukaki. Ban taɓa zauna a cikin ’yan tawaye ba, ban taɓa yi murna da su ba; na zauna ni kaɗai domin hannunka yana a kaina ka kuma sa na cika da haushi. Me ya sa wahalata ba ta ƙarewa mikina kuma ba ya warkuwa? Za ka zama mini kamar rafi mai yaudara ne, kamar maɓulɓulan da ta kafe ne? Saboda haka ga abin da Ubangiji yana cewa, “In ka tuba, zan maido da kai don ka bauta mini; in ka ambaci maganganu masu kyau, ba marasa kyau ba, za ka zama kakakina. Bari wannan mutane su juyo gare ka, amma kada ka juye gare su. Zan mai da kai katanga ga wannan mutane, katanga mai ƙarfi na tagulla; za su yi yaƙi da kai amma ba za su yi nasara a kanka ba, gama ina tare da kai don in kuɓutar in kuma cece ka,” in ji Ubangiji. “Zan cece ka daga hannuwan mugaye in ɓamɓare ka daga hannun marasa tausayi.” Sai maganar Ubangiji ta zo mini cewa, “Kada ka yi aure ka haifi ’ya’ya maza da mata a wannan wuri.” Gama ga abin da Ubangiji yana cewa game da ’ya’ya maza da matan da aka haifa a wannan ƙasa da kuma game da matan da suke iyayensu da suke mazan da iyayensu. “Za su mutu da muguwar cuta. Ba za a yi kuka dominsu ba, ba kuwa za a binne su ba, amma za a bar su a juji. Takobi da yunwa ne za su hallaka su, gawawwakinsu za su zama abincin tsuntsayen sararin sama da kuma namun jeji na duniya.” Gama ga abin da Ubangiji yana cewa, “Kada ka shiga gidan da akwai abincin makoki; kada ka tafi ka yi makoki ko ka nuna juyayi, domin na janye albarkata, ƙaunata da tausayina daga wannan mutane,” in ji Ubangiji. “Manya da ƙanana duka za su mutu a wannan ƙasa. Ba za a binne su ba, ba kuwa za a yi makokinsu ba, kuma ba wanda zai tsaga kansa ko ya aske kansa saboda su. Ba wanda zai ba da abinci don yă ta’azantar da waɗanda suke makoki saboda matattu, kai, ko saboda mahaifi ko mahaifiya ma ba kuwa wani da zai ba da abin sha don yă ta’azantar da su. “Kada kuma ka shiga gidan da ake biki ka zauna don ci da sha. Gama ga abin da Ubangiji Maɗaukaki, Allah na Isra’ila, yana cewa a idanunka da kuma a kwanakinka zan kawo ƙarshen muryar farin ciki da murna da kuma muryoyin amarya da ango a wannan wuri. “Sa’ad da ka faɗa wa waɗannan mutane wannan duka suka kuma tambaye ka, ‘Me ya sa Ubangiji ya ƙaddara irin wannan babban masifa a kanmu? Wace mugunta muka yi? Wane zunubi muka aikata wa Ubangiji Allahnmu?’ Sai ka ce musu, ‘Wannan ya zama haka domin kakanninku sun rabu da ni,’ in ji Ubangiji, ‘suka bi waɗansu alloli suka kuma bauta musu. Suka rabu da ni, ba su kuwa kiyaye dokata ba. Amma kun yi laifi fiye da kakanninku. Duba yadda kowannenku yana bin taurin muguwar zuciyarsa a maimakon yin mini biyayya. Saboda haka zan fitar da ku daga wannan ƙasa zuwa wata ƙasar da ku da kakanninku ba ku taɓa sani ba, a can kuwa za ku bauta wa waɗansu alloli dare da rana, gama ba zan nuna muku tagomashi ba.’ “Amma fa, kwanaki suna zuwa,” in ji Ubangiji, “da mutane ba za su ƙara cewa, ‘Muddin Ubangiji yana raye, wanda ya fitar da Isra’ilawa daga Masar,’ amma za su ce, ‘Muddin Ubangiji yana raye, wanda ya fitar da Isra’ilawa daga ƙasar arewa da kuma daga dukan ƙasashe da ya kora su.’ Gama zan komo da su zuwa ƙasar da na ba wa kakanninsu. “Amma yanzu zan aiko a kira masunta masu yawa su zo,” in ji Ubangiji, “za su kuma kama su. Bayan wannan zan aiko a kira mafarauta su zo, su farauce su daga kowane dutse da tudu da kuma daga kogwannin duwatsu. Idanuna suna a kan dukan hanyoyinsu; ba a ɓoye suke daga gare ni, kuma zunubansu ba a ɓoye suke a idanuna ba. Zan riɓaɓɓanya sakayyar da zan yi musu saboda muguntarsu da zunubinsu, domin sun ƙazantar da ƙasata da ƙazantattun gumakansu marasa rai, suka kuma cika abin gādona da gumakansu na banƙyama.” Ya Ubangiji, ƙarfina da katangana, mafakata a lokacin damuwa, gare ka al’ummai za su zo daga iyakokin duniya su ce, “Kakanninmu ba su mallaki kome ba sai allolin ƙarya, gumakan banza da ba su yi musu amfani ba. Mutane kan yi allolinsu ne? I, amma waɗannan ba alloli ba ne!” “Saboda haka zan koya musu a wannan lokaci zan koya musu ikona da ƙarfina. Sa’an nan za su sani cewa sunana Ubangiji ne. “An rubuta zunubin Yahuda da alƙalamin ƙarfe, an rubuta da tsinin dutse, a kan allunan zukatansu da kuma a kan ƙahonin bagadansu. Har ’ya’yansu ma sun tuna bagadansu da ginshiƙan Asheransu kusa da itatuwa masu duhuwa da kuma a kan tuddai masu tsayi. Dutsena a ƙasar da dukiyarku na ƙasar da dukan arzikinku za a ba da su ganima, tare da masujadanku na kan tuddai, saboda zunubi ko’ina a ƙasarku. Saboda laifinku za ku rasa gādon da na ba ku. Zan bautar da ku ga abokan gābanku a ƙasar da ba ku sani ba, domin kun husata ni, zai kuwa ci har abada.” Ga abin da Ubangiji yana cewa, “La’ananne ne mutumin da yake dogara ga mutum, wanda ya dogara ga jiki don ƙarfi wanda kuma zuciyarsa ta juya wa Ubangiji baya. Zai zama kamar ɗan kurmi a ƙasar da take kango; ba za su ga arziki sa’ad da ya zo ba. Za su zauna a busassun wuraren hamada, a cikin ƙasar gishiri inda ba kowa. “Amma mai albarka ne mutumin da yake dogara ga Ubangiji, wanda ƙarfin halinsa yana daga Ubangiji. Za su zama kamar itacen da aka dasa kusa da ruwa wanda ya miƙa saiwoyinsa zuwa cikin rafi. Ba ya jin tsoro sa’ad da zafi ya zo; ganyayensa kullum kore suke. Ba shi da damuwa a shekarar fări ba ya taɓa fasa ba da ’ya’ya.” Zuciya ta fi kome ruɗu ta fi ƙarfin warkewa. Wa zai iya gane ta? “Ni Ubangiji nakan bincike zuciya in gwada tunani, don in sāka wa kowane mutum bisa ga halinsa, bisa ga ayyukansa.” Kamar makwarwar da ta kwanta a kan ƙwan da ba ita ta zuba ba haka yake da mutumin da ya sami arziki a hanyar da ba daidai ba. A tsakiyar rayuwarsa za su rabu da shi, a ƙarshe kuma zai zama wawa. Kursiyi mai daraja, da aka ɗaukaka tun daga farko, shi ne wuri mai tsarkinmu. Ya Ubangiji, sa zuciyar Isra’ila, duk waɗanda suka rabu da kai za su sha kunya. Waɗanda suka juya maka baya za a rubuta su a ƙura domin sun yashe Ubangiji, maɓulɓular ruwan rai. Ka warkar da ni, ya Ubangiji, zan kuwa warke; ka cece ni zan kuwa cetu, gama kai ne nake yabo. Sun riƙa ce mini, “Ina maganar Ubangiji take? Bari tă cika yanzu!” Ban gudu zaman mai yin maka kiwo ba; ka sani ban marmarin ranan nan ta masifa ba. Abin da ya fito daga leɓunana kuwa, a bayyane suke gare ka. Kada ka zama mini abin razana; kai ne mafakata a ranar masifa. Bari masu tsananta mini su sha kunya, amma ka kiyaye ni daga shan kunya; bari su tsorata, amma ka kiyaye ni da razana. Ka kawo musu ranar masifa; ka hallaka su da hallaka riɓi biyu. Ga abin da Ubangiji ya ce mini, “Ka je ka tsaya a ƙofar mutane, inda sarakunan Yahuda sukan shiga su fita; ka tsaya kuma a dukan sauran ƙofofin Urushalima. Ka ce musu, ‘Ku ji maganar Ubangiji, ku sarakunan Yahuda, da dukan mutanen Yahuda da dukan mazaunan Urushalima waɗanda suke bi ta waɗannan ƙofofi. Ga abin da Ubangiji yana cewa, ku yi hankali kada ku ɗauki kaya a ranar Asabbaci ko ku shigar da shi ta ƙofofin Urushalima. Kada ku fitar da kayan gidajenku ko ku yi wani aiki a ranar Asabbaci mai tsarki, yadda na umarci kakanni-kakanninku. Duk da haka ba su saurara ba, ba su kuwa mai da hankali ba; suka taurare ba su kuwa saurara ko su karɓi horo ba. Amma in kuka yi hankali kuka yi mini biyayya, in ji Ubangiji, ba ku kuwa shigar da kaya ta ƙofofi a ranar Asabbaci ba, amma kuka kiyaye ranar Asabbaci da tsarki ba tare da yin wani aiki a cikinta ba, sa’an nan sarakuna da suke zama a kursiyin Dawuda za su shiga ta ƙofofin wannan birni tare da fadawansu. Su da fadawansu za su shiga a kan kekunan yaƙi da kuma a kan dawakai, mutanen Yahuda suna musu rakiya tare da waɗanda suke zaune a Urushalima, wannan birni kuwa za tă kasance da mazauna har abada. Mutane za su zo daga garuruwan Yahuda da ƙauyukan kewaye da Urushalima, daga iyakar Benyamin da gindin tuddan yamma, daga ƙasar tudu da kuma Negeb, suna kawo hadayun ƙonawa da hadayun gari, sadakokin turare da na godiya zuwa gidan Ubangiji. Amma in ba ku yi mini biyayya ba, ba ku kiyaye ranar Asabbaci da tsarki ba, kuka ɗauki wani kaya yayinda kuke shiga ƙofofin Urushalima a ranar Asabbaci, to, sai in cinna wa ƙofofin Urushalima wutar da ba a iya kashewa, tă cinye kagaranta.’ ” Ga maganar da ta zo wa Irmiya daga wurin Ubangiji. “Ka gangara zuwa gidan mai ginin tukwane, a can zan ba ka saƙona.” Sai na gangara zuwa gidan mai ginin tukwane, na gan shi yana aiki a na’urar ginin tukwanen. Amma tukunyar da yake ginawa ta lalace a hannuwansa, sai mai ginin tukwanen ya sāke gina wata tukunya dabam, yana gyara ta yadda ya ga dama. Sai maganar Ubangiji ta zo mini cewa, “Ya gidan Isra’ila, ashe, ba zan yi da ku yadda mai ginin tukwanen nan yake yi ba?” In ji Ubangiji. “Kamar yumɓu a hannun mai ginin tukwane, haka kuke a hannuna, ya gidan Isra’ila. A duk lokacin da na yi shela cewa za a tumɓuke, a kakkarya a kuma hallaka wata al’umma ko mulki, in wannan al’ummar da na yi wa gargaɗi ta tuba daga muguntarta, sai in janye in kuma fasa kawo mata masifar da na yi niyya aukar mata. In kuma wani lokaci na yi shela cewa za a gina wata al’umma ko mulki a kuma kafa ta, in ta yi mugunta a gabana ba tă kuwa yi mini biyayya ba, sai in janye alherin da na yi niyya in yi mata. “Yanzu fa, sai ka faɗa wa mutanen Yahuda da waɗanda suke zaune a Urushalima, ‘Ga abin da Ubangiji yana cewa ga shi! Ina shirya muku masifa ina ƙirƙiro dabara a kanku. Saboda haka ku juya daga mugayen hanyoyinku, kowannenku, ku canja hanyoyinku da kuma ayyukanku.’ Amma za su amsa su ce, ‘Ba amfani. Za mu ci gaba da shirye-shiryenmu; kowannenmu zai bi taurin muguwar zuciyarsa.’ ” Saboda haka ga abin da Ubangiji yana cewa, “Ku tattambaya a cikin al’ummai. Wa ya taɓa jin irin wannan abu? Budurwa Isra’ila ta yi mugun abu mafi banƙyama. Dusar ƙanƙarar Lebanon ta taɓa rabuwa da kan duwatsun Lebanon? Ruwan mai sanyinsa daga rafuffukansa masu nesa sun taɓa daina gudu? Duk da haka mutanena sun manta da ni; sun ƙone turare wa gumaka marasa amfani, waɗanda suka sa su tuntuɓe a al’amuransu a hanyoyin dā. Sun sa suka yi tafiya a ɓarayin hanyoyi a hanyoyin da ba a gina ba. Ƙasarsu za tă zama kufai, abin reni har abada; dukan waɗanda suka wuce za su yi mamaki su kaɗa kai. Kamar iska daga gabas zan warwatsa su a gaban abokan gābansu; zan juya musu bayana, ba zan nuna musu fuskata ba a ranar masifarsu.” Suka ce, “Zo mu shirya wa Irmiya maƙarƙashiya; gama koyarwar doka da firist ya yi ba za tă ɓace ba, haka ma shawara daga mai hikima da kuma magana daga annabawa. Saboda haka ku zo, mu fāɗa masa da harsunanmu kada mu saurari wani abin da zai faɗa.” Ka saurare ni, ya Ubangiji ka ji abin da masu zargina suke cewa! Ya kamata a sāka wa alheri da mugunta? Duk da haka sun haƙa mini rami. Ka tuna cewa na tsaya a gabanka na kuma yi magana a madadinsu don ka janye fushinka daga gare su. Saboda haka ka kawo wa ’ya’yansu yunwa; ka miƙa su ga ikon takobi. Bari matansu su zama marasa ’ya’ya da gwauraye; bari a kashe mazansu, a kuma kashe samarinsu da takobi a yaƙi. Bari a ji kuka daga gidajensu sa’ad da ka kawo masu hari a kansu farat ɗaya, gama sun haƙa rami don su kama ni suka kuma kafa tarko wa ƙafafuna. Amma Ya Ubangiji, ka san duk maƙarƙashiyarsu, na neman su kashe ni. Kada ka gafarta musu laifofinsu ko ka shafe zunubansu daga gabanka. Bari a tumɓuke su a gabanka; ka yi da su sa’ad da kake fushi. Ga abin da Ubangiji yana cewa, “Tafi ka sayo tulu a wurin mai ginin tukwane. Ka ɗauki waɗansu dattawan jama’a da kuma na firistoci ku fita zuwa Kwarin Ben Hinnom, kusa da mashigin Ƙofar Kasko. A can ka furta maganganun da na faɗa maka, ka ce, ‘Ku ji maganar Ubangiji, ya sarakunan Yahuda da kuma mutanen Urushalima. Ga abin da Ubangiji Maɗaukaki, Allah na Isra’ila, yana cewa ku saurara! Zan kawo masifa a wannan wuri, wanda duk ya ji, kunnuwansa za su kaɗa. Gama sun yashe ni suka kuma mai da wannan wuri ya zama na baƙin alloli; sun ƙone hadayu a cikinsa wa allolin da ko su ko kakanninsu ko sarakunan Yahuda ba su taɓa sani ba, suka kuma cika wannan wuri da jini marasa laifi. Suka gina masujadai na kan tudu na Ba’al don su ƙona ’ya’yansu maza a cikin wuta a matsayin hadaya ga Ba’al abin da ban umarta ba, ban ambata ba, bai kuma zo mini ba. Saboda haka ku lura, kwanaki suna zuwa, in ji Ubangiji, sa’ad da mutane ba za su ƙara ce da wannan wuri Tofet ko Kwarin Ben Hinnom ba, amma za su ce da shi Kwarin Kisa. “ ‘A wannan wuri zan lalace dabarun Yahuda da na Urushalima. Zan sa a kashe su da takobi a gaban abokan gābansu, a hannuwan waɗanda suke neman ransu, zan kuma ba da gawawwakinsu su zama abinci ga tsuntsayen sararin sama da kuma namun jeji. Zan ragargazar da wannan birni in mai da shi abin reni, duk wanda ya wuce zai yi mamaki ya kuma yi tsaki saboda dukan masifunsa. Zan sa su ci naman ’ya’yansu maza da mata, za su kuma ci naman juna a lokacin damuwar ƙawanya da abokan gāban da suke neman ransu za su yi musu.’ “Sa’an nan ka fasa tulun yayinda waɗanda suka tafi tare da kai suna duba, ka kuma ce musu, ‘Ga abin da Ubangiji Maɗaukaki yana cewa zan farfasa wannan al’umma da wannan birni kamar yadda aka farfasa wannan tulu mai ginin tukwane ba kuwa zai gyaru ba. Za a binne matattu a Tofet har sai ba sauran wuri. Ga abin da zan yi wa wannan wuri da waɗanda suke zaune a nan, in ji Ubangiji. Zan mai da wannan birni kamar Tofet. Gidaje a Urushalima da waɗannan na sarakunan Yahuda za su ƙazantu kamar wannan wuri, Tofet, dukan gidajen da suke ƙone turare a kan rufi wa duk rundunan taurari suna kuma zuba hadayun sha ga sauran alloli.’ ” Sa’an nan Irmiya ya komo daga Tofet, inda Ubangiji ya aike shi don yă yi annabci, ya tsaya a filin haikalin Ubangiji ya ce wa mutane duka, “Ga abin da Ubangiji Maɗaukaki, Allah na Isra’ila, yana cewa, ‘Ku saurara! Zan kawo wa wannan birni da ƙauyukan da suke kewayensa kowace masifar da na furta a kansu, domin sun yi taurinkai, ba su kuwa saurari maganata ba.’ ” Da firist nan Fashhur ɗan Immer, babban ma’aikaci a cikin haikalin Ubangiji, ya ji Irmiya yana annabcin waɗannan abubuwa, sai ya sa aka yi wa Irmiya dūka aka kuma sa shi a turu a Ƙofar Bisa na Benyamin a haikalin Ubangiji. Kashegari, sa’ad da Fashhur ya fitar da shi daga turu, sai Irmiya ya ce masa, “ Ubangiji ba zai kira ka Fashhur ba, amma ya ba ka suna Magor-Missabib. Gama ga abin da Ubangiji yana cewa, ‘Zan maishe ka abin razana ga kanka da kuma ga dukan abokanka; da idanunka za ka gan takobin abokan gāba yana kashe su. Zan miƙa Yahuda duka ga sarkin Babilon, wanda zai kwashe su zuwa Babilon ya kuma kashe su da takobi. Zan ba wa abokan gābansu dukan dukiyar wannan birni dukan amfaninsa, dukan abubuwa masu daraja na sarakunan Yahuda. Za su kwashe su ganima su kai su Babilon. Kai kuma Fashhur, da dukan waɗanda suke a gidanka za ku tafi zaman bauta a Babilon. A can za ku mutu a kuma binne ku, da kai da dukan abokanka waɗanda ka yi musu annabce-annabcen ƙarya.’ ” Ya Ubangiji, ka ruɗe ni, na kuwa ruɗu; ka fi ni ƙarfi, ka kuwa yi nasara. Na zama abin dariya dukan yini; kowa yana yi mini ba’a. Duk sa’ad da na yi magana, nakan tā da murya ina furta hargitsi da hallaka. Haka maganar Ubangiji ta kawo mini zagi da reni dukan yini. Amma in na ce, “Ba zan ambace shi ba ba zan ƙara yin magana da sunansa ba,” sai in ji maganarsa a cikina kamar wuta, wutar da aka kulle a ƙasusuwana. Na gaji da danne ta a cikina; tabbatacce ba zan iya ba. Na ji mutane da yawa suna raɗa cewa, “Razana ta kowace fuska! Mu kai kararsa! Bari mu kai kararsa!” Dukan abokaina suna jira in yi tuntuɓe, suna cewa, “Mai yiwuwa a ruɗe shi; sai mu yi nasara a kansa mu ɗau fansa a kansa.” Amma Ubangiji yana tare da ni kamar babban jarumi; saboda haka masu tsananta mini za su yi tuntuɓe ba kuwa za su yi nasara ba. Za su fāɗi su kuma sha mummunar kunya; ba za a taɓa manta da rashin bangirmansu ba. Ya Ubangiji Maɗaukaki, kai da kake gwada adali kana bincika zuciya duk da tunani, bari in ga sakayyarka a kansu, gama a gare ka na miƙa damuwata. Ku rera ga Ubangiji! Ku yabi Ubangiji! Ya kuɓutar da ran mabukaci daga hannuwan mugaye. La’ananniya ce ranar da aka haife ni! Kada ranar da mahaifiyata ta haife ni ta zama mai albarka! La’ananne ne mutumin da ya kawo wa mahaifina labari, wanda ya sa shi ya yi murna cewa, “An haifa maka yaro, ɗa namiji!” Bari mutumin ya zama kamar garuruwan da Ubangiji ya tumɓuke ba tausayi. Bari yă ji kuka da safe kururuwan yaƙi kuma da tsakar rana. Gama bai kashe ni a cikin ciki ba, da ma ya sa cikin mahaifiyata ya zama kabarina, cikinta ya fadada har abada. Me ya sa na ma fito daga cikin ciki in ga wahala da baƙin ciki in kuma ƙare kwanakina da kunya? Magana ta zo wa Irmiya daga Ubangiji sa’ad da Sarki Zedekiya ya aiki Fashhur ɗan Malkiya da firist Zefaniya ɗan Ma’asehiya gare shi. Suka ce masa, “Yanzu ka roƙi mana Ubangiji saboda Nebukadnezzar sarkin Babilon yana kawo mana yaƙi. Wataƙila Ubangiji zai yi mana waɗansu abubuwa banmamaki kamar a lokacin baya don yă janye daga gare mu.” Amma Irmiya ya amsa musu ya ce, “Ku faɗa wa Zedekiya cewa, ‘Ga abin da Ubangiji, Allah na Isra’ila, yake cewa ina shirin juya kayan yaƙin da suke a hannuwanka a kanka, waɗanda kake amfani don ka yaƙi sarki Babilon da kuma Babiloniyawa waɗanda suka kewaye katangar birnin, zan kuwa tsiba kayan yaƙinka a tsakiyar birnin nan. Ni da kaina zan yi yaƙi da kai da miƙaƙƙen hannu mai ƙarfi cikin fushi da hasala mai girma. Zan kashe waɗanda suke zaune a wannan birni, mutane da dabbobi za su kuwa mutu da muguwar annoba. Bayan wannan, in ji Ubangiji, zan ba da Zedekiya sarkin Yahuda, fadawansa da kuma mutanen wannan birni waɗanda suka tsira daga annoba, takobi da kuma yunwa, ga Nebukadnezzar sarkin Babilon da kuma ga abokan gābansu waɗanda suke neman ransu. Zai kashe su da takobi; ba zai ji tausayinsu ko ya yi musu jinƙai ko ya yi juyayinsu ba.’ “Bugu da ƙari, ka faɗa wa mutanen cewa, ‘Ga abin da Ubangiji yana cewa, ga shi na sa a gabanku hanyar rai da hanyar mutuwa. Duk wanda ya zauna a wannan birni zai mutu ta takobi, yunwa ko annoba. Amma duk wanda ya fita ya miƙa kansa ga Babiloniyawa waɗanda suka kewaye ku zai rayu; zai kuɓutar da ransa. Na ƙudura in yi wa wannan birni lahani ba alheri ba, in ji Ubangiji. Za a ba da shi a hannuwan sarki Babilon, zai kuwa hallaka shi da wuta.’ “Ban haka ma, ka faɗa wa gidan sarauta na Yahuda cewa, ‘Ku saurari maganar Ubangiji; Ya gidan Dawuda ga abin da Ubangiji yana cewa, “ ‘Ku yi gaskiya kowace safiya; ku kuɓuta daga hannun mai danniya wannan da aka yi wa fashi in ba haka ba hasalata za tă sauka ta kuma ci kamar wuta saboda muguntar da kuka aikata za tă ci babu wanda zai kashe ta. Ina gāba da ku, mazaunan Urushalima, ku da kuke zama a bisa wannan kwari kan dutsen da yake a fili, in ji Ubangiji ku da kuke cewa, “Wa zai iya yaƙe mu? Wa zai iya shiga mafakarmu?” Zan hukunta ku gwargwadon ayyukanku, in ji Ubangiji. Zan sa wuta a kurminku da za tă cinye kome da yake kewaye da ku.’ ” Ga abin da Ubangiji yana cewa, “Ka gangara zuwa fadan sarkin Yahuda ka yi shelar wannan saƙo a can ka ce, ‘Ka ji maganar Ubangiji, ya sarkin Yahuda, kai da kake zaune kan gadon sarautar Dawuda, kai, da fadawanka da mutanenka waɗanda suke shiga ta waɗannan ƙofofi. Ga abin da Ubangiji yana cewa, ka yi abin da yake gaskiya da kuma daidai. Ka kuɓutar da wannan da aka yi masa ƙwace daga hannun mai zaluntarsa. Kada ka yi abin da ba daidai ba ko ka cuci baƙo, maraya ko gwauruwa, kuma kada ka zub da jini marar laifi a wannan wuri. Gama in ka lura da bin waɗannan umarnai, to, sarakunan da suke zaune a gadon sarautar Dawuda za su shiga ta ƙofofin wannan fada, suna hawan kekunan yaƙi da dawakai, fadawansu da mutanensu suna musu rakiya. Amma in ba ku kiyaye waɗannan umarnai ba, in ji Ubangiji, na rantse da kaina cewa wannan fada za tă zama kufai.’ ” Gama ga abin da Ubangiji yana cewa game da wannan fadar sarkin Yahuda, “Ko da yake kina kamar Gileyad a gare ni, kamar ƙwanƙolin Lebanon, tabbatacce zan maishe ki hamada, kamar garuruwan da ba mazauna. Zan aika da mai hallakarwa a kanki, kowane mutum da makamansa, za su kuma yayyanka gumaguman al’ul na ki masu kyau su jefa su cikin wuta. “Mutane daga al’ummai da yawa za su ratsa cikin wannan birni su kuma tambayi juna suna cewa, ‘Me ya sa Ubangiji ya yi haka da wannan babban birni?’ Amsar kuwa za tă zama, ‘Domin sun keta alkawarin Ubangiji Allahnsu, suka yi sujada suka kuma bauta wa waɗansu alloli.’ ” Kada ku yi kuka domin sarkin da ya mutu ko ku yi makoki saboda rashinsa; a maimako, ku yi kuka mai zafi saboda wanda aka kai zaman bauta, domin ba zai ƙara dawowa ba ko ya ƙara ganin ƙasarsa ta haihuwa. Gama ga abin da Ubangiji yana cewa game da Shallum ɗan Yosiya, wanda ya gāji mahaifinsa a matsayin sarkin Yahuda amma bai bar wurin nan ba, “Ba zai ƙara dawowa ba. Zai mutu a inda suka kai shi zaman bauta; ba zai ƙara ganin wannan ƙasa ba.” “Kaiton wanda ya gina gidansa ta hanyar rashin adalci, ɗakunansa na sama kuma ta hanyar rashin gaskiya, yana sa mutanen ƙasarsa suna aiki a banza ba ya biyansu wahalarsu. Yana cewa, ‘Zan gina wa kaina babban fada da manyan ɗakuna.’ Ta haka sai ya yi musu manyan tagogi ya manne musu al’ul ya yi musu ado kuma da ruwan ja. “Wannan zai mai da kai sarki ne in kana da al’ul a kai a kai? Mahaifinka bai kasance da abinci da abin sha ba? Ya yi abin da yake gaskiya da kuma daidai saboda haka kome ya kasance da lafiya da shi. Ya kāre muradin matalauta da mabukata, ta haka kome ya tafi masa daidai. Ba abin da ake nufi da ba san ni ke nan ba?” In ji Ubangiji. “Amma idanunka da zuciyarka sun kahu kawai a kan ƙazamar riba, da a kan zub da jinin marar laifi da kuma a kan danniya da zalunci.” Saboda haka ga abin da Ubangiji yana cewa game da Yehohiyakim ɗan Yosiya sarkin Yahuda, “Ba za su yi kuka dominsa ba, ‘Kaito, ɗan’uwana! Kaito, ’yar’uwata!’ Ba za su yi kuka dominsa ba, ‘Kaito, maigidana! Kaito, darajarsa!’ Za a binne shi kamar jaki za a ja shi a ƙasa a jefar a bayan ƙofofin Urushalima.” “Ka haura zuwa Lebanon ka yi kuka, bari a ji muryarka a Bashan, yi kuka daga Abarim, gama an murƙushe dukan abokanka. Na ja maka kunne sa’ad da kake zama lafiya, amma sai ka ce, ‘Ba zan saurara ba!’ Wannan halinka ne tun kana matashi; ba ka yi mini biyayya ba. Iska za tă koro dukan makiyayanka abokanka kuma za su tafi zaman bauta. Sa’an nan za ka sha kunya a kuma walaƙanta ka saboda dukan muguntarka. Kai da kake zama a ‘Lebanon,’ kai da kake sheƙa a gine-ginen al’ul za ka yi nishi sa’ad da zafi ya auka maka, zafi kamar na mace mai naƙuda! “Muddin ina raye,” in ji Ubangiji, “ko kai, Yehohiyacin ɗan Yehohiyakim sarkin Yahuda, ka zama zoben hatimin dama a hannuna na dama, zan kwaɓe ka. Zan ba da kai ga waɗanda suke neman ranka, waɗanda kake tsoro, ga Nebukadnezzar sarkin Babilon da kuma ga Babiloniyawa. Zan jefar da kai da mahaifiyar da ta haife ka zuwa wata ƙasa, inda babu ɗayanku da aka haifa a wurin, a can kuma za ka mutu. Ba za ka ƙara dawo ƙasar da kake marmarin dawowa ba.” Wannan mutum Yehohiyacin ne da aka rena, fasasshen tukunya, abin da babu wanda yake so? Me ya sa za a jefar da shi da ’ya’yansa a jefar da su a ƙasar da ba su sani ba? Ya ke ƙasa, ƙasa, ƙasa, ki ji maganar Ubangiji! Ga abin da Ubangiji yana cewa, “Ka rabu da wannan mutum sai ka ce marar ’ya’ya, mutumin da ba zai yi nasara a rayuwarsa ba, gama babu zuriyarsa da za tă yi nasara babu wani da zai zauna a kursiyin Dawuda ko ya ƙara yin mulkin Yahuda.” “Kaiton makiyayan da suka hallakar suka kuma warwatsar da tumakin makiyayanta!” In ji Ubangiji. Saboda haka ga abin da Ubangiji, Allah na Isra’ila yana ce wa makiyayan da suke lura da mutanena, “Domin kun watsar da garkena kuka kuma kore su ba ku kuma lura da su ba, zan kawo hukunci a kanku saboda muguntar da kuka yi,” in ji Ubangiji. “Ni kaina zan tattara raguwar garkena daga ƙasashen da na kore su zuwa zan kuma dawo da su ga makiyayansu, inda za su yi ta haihuwa su riɓaɓɓanya. Zan sa makiyaya a kansu waɗanda za su lura da su, ba za su ƙara jin tsoro ko razana ba, ba kuwa waninsu da zai ɓace,” in ji Ubangiji. “Kwanaki suna zuwa,” in ji Ubangiji, “sa’ad da zan tā da wa Dawuda Reshen adalci, Sarki wanda zai yi mulki da hikima ya kuma yi abin da yake gaskiya da kuma daidai a ƙasar. A cikin zamaninsa za a ceci Yahuda Isra’ila kuma zai zauna lafiya. Sunan da za a kira shi ke nan, Ubangiji Adalcinmu. “Saboda haka fa, kwanaki suna zuwa,” in ji Ubangiji, “sa’ad da mutanen ba za su ƙara cewa, ‘Muddin Ubangiji yana raye, wanda ya fito da Isra’ila daga Masar ba,’ amma za su ce, ‘Muddin Ubangiji yana raye, wanda ya fito da zuriyar Isra’ila daga ƙasar arewa da kuma daga dukan ƙasashen da ya yashe su.’ Sa’an nan za su zauna a ƙasarsu.” Game da annabawa kuwa, Zuciyata ta karai; dukan ƙasusuwana suna kaɗuwa. Na zama kamar wanda ya bugu, kamar mutumin da ruwan inabi ya sha kansa, saboda Ubangiji da kuma maganarsa mai tsarki. Ƙasar ta cika da mazinata; saboda la’ana ƙasar ta zama kango makiyaya a hamada ta bushe. Annabawa suna bin mugayen muradu suna kuma amfani da ƙarfinsu a hanyar marar kyau. “Annabi da firist dukansu biyu marasa sanin Allah ne; har ma a cikin haikalina na tarar da muguntarsu,” in ji Ubangiji. “Saboda haka hanyarsu za tă yi santsi; za a jefar da su cikin duhu a can kuwa za su fāɗi. Zan kawo musu masifa a shekarar da za a hukunta su,” in ji Ubangiji. “A cikin annabawan Samariya na ga wannan abin banƙyama. Suna annabci ta wurin Ba’al suna ɓad da mutanena Isra’ila. A cikin annabawan Urushalima kuma na ga wani abin bantsoro. Suna zina suna kuma rayuwar ƙarya. Sun ƙarfafa hannuwa masu aikata mugunta, domin kada wani ya juya daga muguntarsa. Dukansu sun yi kama da Sodom a gare ni; mutanen Urushalima sun yi kama da Gomorra.” Saboda haka, ga abin da Ubangiji Maɗaukaki yana cewa game da annabawa, “Zan sa su ci abinci mai ɗaci su kuma sha ruwa mai dafi, domin daga annabawan Urushalima rashin sani Allah ya bazu ko’ina a ƙasar.” Ga abin da Ubangiji Maɗaukaki yana cewa, “Kada ku saurari abin da annabawan suke muku annabci; suna cika ku da sa zuciyar ƙarya. Suna maganar wahayi daga tunaninsu, ba daga bakin Ubangiji ba. Suna cin gaba da ce wa waɗanda suka rena ni, ‘ Ubangiji ya ce za ku zauna lafiya.’ Ga duka waɗanda suke bin taurin zukatansu kuwa sukan ce, ‘Babu lahanin da zai same ku.’ Amma wane ne a cikinsu ya taɓa tsaya a majalisar Ubangiji yă ga ko ya ji maganarsa? Wa ya saurari ya kuma ji maganarsa? Ga shi, hadarin Ubangiji zai taso cikin hasala guguwa tana kaɗawa a kan kawunan mugaye. Fushin Ubangiji ba zai kau ba sai ya aikata nufin zuciyarsa. A kwanakin masu zuwa za ku gane sarai. Ban aiki waɗannan annabawa ba, duk da haka sun tafi da saƙonsu; ban yi musu magana ba, duk da haka sun yi annabci. Amma da a ce sun tsaya a majalisata, da sun yi shelar maganata ga mutanena sun kuma juyar da su daga mugayen hanyoyinsu da kuma daga mugayen ayyukansu. “Ni ɗin Allah na kusa ne kawai,” in ji Ubangiji, “ba Allah na nesa ba? Akwai wanda zai iya ɓuya a lungu har da ba zan iya ganinsa ba?” In ji Ubangiji “Ban cika sama da ƙasa ba?” In ji Ubangiji. “Na ji abin da annabawa suna cewa su da suke annabcin ƙarya a sunana. Suna cewa, ‘Na yi mafarki! Na yi mafarki!’ Har yaushe wannan zai ci gaba a cikin zukata annabawa masu ƙarya, waɗanda suke annabcin ruɗun tunaninsu? Suna tsammanin mafarkan da suke faɗa wa juna za su sa mutane su manta da sunana, kamar yadda kakanninsu suka manta da sunana ta wurin yin wa Ba’al sujada. Bari annabin da ya yi mafarki ya faɗa mafarkinsa, amma bari wanda yake da maganata ya yi ta da aminci. Gama me ya haɗa ciyawa da alkama?” In ji Ubangiji. “Maganata ba wuta ba ce,” in ji Ubangiji, “kuma kamar gudumar da kan ragargaza dutse? “Saboda haka,” in ji Ubangiji, “Ina gāba da annabawan da suke satar maganganuna daga juna. I,” in ji Ubangiji, “Ina gāba da annabawan da suke kaɗa harsunansu sa’an nan su ce, ‘ Ubangiji ne ya furta.’ Tabbatacce, ina gāba da waɗannan da suke annabci mafarkan karya,” in ji Ubangiji. “Suna faɗarsu suna ɓad da mutanena da ƙarairayinsu na rashin hankali, duk da haka ban aike su ba, ban kuwa umarce su ba. Ba su amfani wannan mutane ba ko kaɗan,” in ji Ubangiji. “Sa’ad da waɗannan mutane, ko annabi ko firist, ya tambaye ka, ‘Mece ce maganar Ubangiji?’ Ka ce musu, ‘Wace magana? Zan yashe ku, in ji Ubangiji.’ In annabi ko firist ko da wani dabam ya ce, ‘Wannan ne abin da Ubangiji yake cewa,’ zan hukunta wannan mutum da kuma gidansa. Ga abin da kowannenku yana cin gaba da ce wa abokinsa ko danginsa, ‘Mece ce amsar Ubangiji?’ Ko kuwa ‘mene ne Ubangiji ya faɗa?’ Amma kada ku ƙara ambatar ‘maganar Ubangiji ’ domin kowace maganar mutum kan zama maganarsa. Ta haka kukan lalace maganar Allah mai rai, Ubangiji Maɗaukaki, Allahnmu. Ga abin da za ku ci gaba da faɗa wa annabi, ‘Mece ce amsar Ubangiji gare ka?’ Ko kuwa ‘mene ne Ubangiji ya faɗa?’ Ko da yake kuna cewa, ‘Wannan ce maganar Ubangiji,’ ga abin da Ubangiji yana cewa kuna amfani da kalmomi, ‘Wannan ce maganar Ubangiji,’ ko da yake na ce muku kada ku ce, ‘Wannan ce maganar Ubangiji.’ Saboda haka, tabbatacce zan manta da ku in kuma jefar da ku daga gabana tare da birnin da na ba ku da kuma kakanninku. Zan kawo muku madawwamiyar kunya, kunya ta har abada wadda ba za a taɓa manta ba.” Bayan Nebukadnezzar ya kwashi Yekoniya ɗan Yehohiyakim sarkin Yahuda da fadawa, da masu sana’a da masu zane zanen Yahuda daga Urushalima zuwa Babilon zaman bauta, Ubangiji ya nuna mini kwanduna biyu na ’ya’yan ɓaure ajiye a gaban haikalin Ubangiji. Kwando guda yana da ’ya’yan ɓaure masu kyau sosai, kamar waɗanda suka nuna da wuri; ɗayan kwandon kuma yana da ’ya’yan ɓaure marasa kyau, sun yi muni har ba a iya ci. Sa’an nan Ubangiji ya tambaye ni ya ce, “Me ka gani, Irmiya?” Na ce, “’Ya’yan ɓaure. Masu kyau ɗin suna da kyau sosai, amma munanan sun yi muni har ba a iya ci.” Sai maganar Ubangiji ta zo mini cewa, “Ga abin da Ubangiji, Allah na Isra’ila, yana cewa, ‘Kamar ’ya’yan ɓauren nan masu kyau, haka zan kula da mutanen Yahuda waɗanda aka kwaso waɗanda na fisshe su daga wannan wuri zuwa ƙasar Babiloniyawa Idanuna za su kula da su don kyautatawarsu, zan kuma komo da su wannan ƙasa. Zan gina su ba zan rushe su ba; zan dasa su ba kuwa zan tumɓuke su ba. Zan ba su zuciya don su san ni, cewa ni ne Ubangiji. Za su zama mutanena, zan zama Allahnsu, gama za su komo gare ni da dukan zuciyarsu. “ ‘Amma kamar ’ya’yan ɓauren nan marasa kyau, waɗanda sun yi muni har ba a iya ci,’ in ji Ubangiji, ‘haka zan yi da Zedekiya sarkin Yahuda, fadawansa da sauran mutanen da suka tsira a Urushalima, ko suna a wannan ƙasa ko suna zama a Masar. Zan mai da su abin ƙyama da masifa ga dukan mulkokin duniya, abin zargi da abin karin magana, abin ba’a da abin la’ana a duk inda zan kore su zuwa. Zan aika da takobi, yunwa da annoba a kansu sai an hallaka su sarai daga ƙasar da na ba su da kuma kakanninsu.’ ” Magana ta zo wa Irmiya game da dukan mutanen Yahuda a shekara ta huɗu ta Yehohiyakim ɗan Yosiya sarkin Yahuda, wadda ta kasance shekara ta fari ta Nebukadnezzar sarkin Babilon. Saboda haka Irmiya annabi ya ce wa dukan mutanen Yahuda da dukan mazaunan Urushalima. Shekaru ashirin da uku, daga shekara ta goma sha uku ta Yosiya ɗan Amon sarkin Yahuda har zuwa wannan rana, maganar Ubangiji ta zo mini na kuma yi muku magana sau da sau, amma ba ku saurara ba. Ko da yake Ubangiji ya aika dukan bayinsa annabawa gare ku sau da sau, ba ku saurara ba, ba ku kuma kula ba. Sun ce, “Ku juye yanzu, kowannenku, daga mugayen hanyoyinku da mugayen ayyukanku, za ku kuwa iya zauna a ƙasar da Ubangiji ya ba ku da kuma kakanninku har abada abadin. Kada ku bi waɗansu alloli don ku bauta ku kuma yi musu sujada; kada ku tsokane ni in yi fushi da abin da hannuwanku suka yi. Sa’an nan ba zan kawo muku lahani ba.” “Amma ba ku saurare ni ba,” in ji Ubangiji, “kun tsokane ni da abin da kuka yi da hannuwanku, kuka kuma kawo lahani wa kanku.” Saboda haka Ubangiji Maɗaukaki ya ce, “Domin kun ƙi ku saurara ga maganata, zan kira dukan mutanen arewa da bawana Nebukadnezzar sarkin Babilon,” in ji Ubangiji, “zan kuma kawo su su yi gāba da wannan ƙasa da mazaunanta da kuma gāba da dukan al’ummai da suke kewaye. Zan hallaka su sarai in kuma mai da su abin bantsoro da abin dariya, za su kuma zama kufai har abada. Zan kawar da muryoyin farin ciki da murna daga gare su, muryoyin amarya da na ango, ƙarar dutsen niƙa da hasken fitila. Dukan wannan ƙasa za tă zama kango, kuma waɗannan al’ummai za su bauta wa sarkin Babilon shekaru saba’in. “Amma sa’ad da shekaru saba’in ɗin suka cika, zan hukunta sarkin Babilon da kuma al’ummarsa, ƙasar Babiloniyawa, saboda laifinsu,” in ji Ubangiji, “in kuma mai da ita kango har abada. Zan kawo wa wannan ƙasa dukan abubuwan na yi magana a kanta, dukan abubuwan da aka rubuta a wannan littafi, abubuwan da Irmiya kuma ya yi annabci a kan dukan al’ummai. Su kansu al’ummai da sarakuna masu yawa za su bautar da su; zan sāka musu bisa ga ayyukansu da aikin hannuwansu.” Ga abin da Ubangiji, Allah na Isra’ila, ya faɗa mini, “Ka karɓi kwaf ruwan inabin nan na fushina a wurina, ka sa dukan al’umman da na aike ka gare su, su sha. Sa’ad da suka sha, za su yi ta tangaɗi su kuma yi hauka saboda takobin da zan aika a cikinsu.” Saboda haka na karɓi kwaf daga hannun Ubangiji na sa dukan al’ummai waɗanda ya aiko ni wurinsu su sha. Urushalima da garuruwan Yahuda, sarakunan da fadawanta, don su mai da su kufai da kuma abin bantsoro da ba’a da la’ana, yadda suke a yau; Fir’auna sarkin Masar, ma’aikatansa, fadawansa da dukan mutanensa, da dukan baƙin da suke can; dukan sarakunan Uz; dukan sarakunan Filistiyawa (waɗannan na Ashkelon, Gaza, Ekron da mutanen da aka bari a Ashdod); Edom, Mowab da Ammon; dukan sarakunan Taya da Sidon; sarakunan bakin teku a ƙetaren teku; Dedan, Tema, Buz da dukan waɗanda suke a manisantan wurare; dukan sarakunan Arabiya da dukan sarakunan baƙin da suke zama a hamada; dukan sarakunan Zimri, Elam da Mediya; da kuma dukan sarakunan arewa, nesa da kuma kusa, bi da bi, dukan mulkokin duniya. Bayan dukansu kuma, sai sarkin Sheshak ma yă sha. “Sa’an nan na faɗa musu cewa, ‘Ga abin da Ubangiji Maɗaukaki, Allah na Isra’ila, yana cewa ku sha, ku bugu ku kuma yi amai, ku fāɗi, kada kuma ku ƙara tashi saboda takobin da zan aiko muku.’ Amma in suka ki su karɓi kwaf ɗin daga hannunka su sha, ka faɗa musu cewa, ‘Ga abin da Ubangiji Maɗaukaki yana cewa dole ku sha! Ga shi, na sa masifa tă yi aiki cikin birnin da ake kira da sunana, kuna gani za ku tafi ba hukunci? Ba za ku tafi ba hukunci ba, gama ina kawo wa dukan mazaunan duniya takobi, in ji Ubangiji Maɗaukaki.’ “Yanzu ka yi annabcin dukan waɗannan maganganu a kansu ka kuma ce musu, “ ‘ Ubangiji zai yi ruri daga bisa; zai yi tsawa daga mazauninsa mai tsarki ya kuma yi ruri da ƙarfi a kan ƙasarsa. Zai yi ihu kamar waɗanda suke matsin ’ya’yan inabi, yi ihu a kan dukan waɗanda suke zaune a duniya. Hayaniya za tă taso har iyakar duniya, gama Ubangiji zai kawo tuhume-tuhume a kan al’ummai; zai kawo shari’a a kan dukan ’yan adam ya kuma kashe mugaye da takobi,’ ” in ji Ubangiji. Ga abin da Ubangiji Maɗaukaki yana cewa, “Duba! Masifa tana yaɗuwa daga al’umma zuwa al’umma; hadari mai girma yana tasowa daga iyakar duniya.” A lokacin waɗanda Ubangiji ya kashe za su kasance a ko’ina, daga wannan bangon duniya zuwa wancan. Ba za a yi kuka dominsu, ba za a tattara su don a binne ba, amma za su zama kamar juji da an tsiba a ƙasa. Ku yi kuka ku kuma yi makoki, ku makiyaya; ku yi ta birgima a ƙura, ku shugabannin garke. Gama lokacin da za a yanka ku ya zo; za ku fāɗi ku kuma farfasa kamar tukunyar yumɓu mai kyau. Makiyaya ba za su sami wurin da za su gudu su tafi ba, shugabannin garke ba za su sami wurin kuɓuta ba. Ji kukan makiyaya, kururuwan shugabannin garke, gama Ubangiji yana hallaka wurin kiwo. Rafi mai gudu a hankali zai zama kango saboda zafin fushin Ubangiji. Kamar zaki zai bar wurin ɓuyarsa, ƙasarsu kuma za tă zama kufai saboda takobin masu danniya da kuma saboda zafin fushin Ubangiji. A farkon sarautar Yehohiyakim ɗan Yosiya sarkin Yahuda, wannan magana ta zo daga wurin Ubangiji, “Ga abin da Ubangiji yana cewa, ka tsaya a filin gidan Ubangiji ka kuma yi magana ga dukan mutanen garuruwan Yahuda waɗanda suka zo sujada a gidan Ubangiji. Ka faɗa musu kome da na umarce ka; kada ka bar wata magana. Wataƙila su saurara kowanne kuma ya juyo daga mugun hanyarsa. Sa’an nan in yi juyayi in kuma janye masifar da nake shirin kawo a kansu saboda muguntar da suka aikata. Ka faɗa musu, ‘Ga abin da Ubangiji yana cewa, in ba ku saurare ni, ku kuma bi dokata, wadda na sa a gabanku ba, in kuma ba ku saurari maganganun bayina annabawa, waɗanda na aika muku sau da sau ba (ko da yake ba ku saurara ba), to, sai in mai da gidan nan kamar Shilo, birnin nan kuma abin la’ana a cikin al’umman duniya.’ ” Firistoci, annabawa da dukan mutane suka ji Irmiya yana waɗannan maganganu a gidan Ubangiji. Amma da Irmiya ya gama faɗar wa dukan mutanen abin da Ubangiji ya umarce shi ya faɗa, sai firistoci, annabawa da dukan mutane suka kama shi suka ce, “Mutuwa za ka yi! Me ya sa ka yi annabci da sunan Ubangiji cewa wannan gida zai zama kamar Shilo, wannan birni kuma zai zama kango da hamada?” Sai duk mutane suka tattaru kewaye da Irmiya a cikin gidan Ubangiji. Da fadawan Yahuda suka ji haka, sai suka haura daga fada zuwa gidan Ubangiji suka zazzauna a wuraren zamansu a mashigin Sabuwar Ƙofar gidan Ubangiji. Sa’an nan firistoci da annabawa suka ce wa fadawan da dukan mutane, “Mutumin nan ya cancanci hukuncin kisa gama ya yi annabci gāba da wannan birni. Ku kun ji da kunnuwanku!” Sai Irmiya ya ce wa dukan fadawa da kuma dukan mutane, “ Ubangiji ya aiko ni in yi annabci gāba da wannan gida da wannan birni dukan abin da na faɗa. Yanzu sai ku gyara hanyoyinku da kuma ayyukanku ku yi biyayya da Ubangiji Allahnku. Sa’an nan Ubangiji zai yi juyayi ya kuma janye masifar da ya furta zai kawo a kanku. Game da ni dai, ina a hannuwanku; ku yi duk abin da kuka ga ya yi kyau, ya kuma dace a gare ku. Ku tabbata dai, cewa in kuka kashe ni, za ku jawo wa kanku alhakin jini marar laifi a kanku da a kan birnin nan da kuma a kan masu zama a cikinsa, gama a gaskiya Ubangiji ne ya aiko ni wurinku domin in faɗa muku dukan maganan nan a kunnuwanku.” Sai fadawa da dukan mutane suka ce wa firistoci da annabawa. “Wannan mutum bai yi abin da ya isa hukuncin kisa ba, gama ya yi magana da sunan Ubangiji Allahnmu.” Waɗansu daga cikin dattawan ƙasar suka zo gaba suka ce wa dukan taron jama’a, “Mika mutumin Moreshet, ya yi annabci a kwanakin Hezekiya sarkin Yahuda. Ya ce wa dukan mutanen Yahuda, ‘Ga abin da Ubangiji Maɗaukaki yana cewa, “ ‘Za a nome Sihiyona kamar gona, Urushalima kuwa za tă zama tsibin juji, ƙwanƙolin dutsen haikali kuwa zai zama kurmi.’ “Hezekiya sarkin Yahuda ko kuwa wani a Yahuda ya kashe shi? Ashe, Hezekiya bai ji tsoron Ubangiji ya nemi tagomashinsa ba? Ubangiji kuwa bai yi juyayi ya kuma janye masifar da ya furta zai kawo a kansu ba? Muna gab da jawo wa kanmu muguwar masifa!” (To, fa, Uriya ɗan Shemahiya daga Kiriyat Yeyarim wani mutum ne wanda ya yi annabci da sunan Ubangiji; ya yi annabci irin abu ɗaya gāba da wannan birni da wannan ƙasa yadda Irmiya ya yi. Da sarki Yehohiyakim da dukan fadawansa da ma’aikatansa suka ji wannan magana, sai sarki ya nemi a kashe shi. Amma Uriya ya ji wannan shiri sai ya gudu zuwa Masar don tsoro. Sarki Yehohiyakim ya aiki Elnatan ɗan Akbor zuwa Masar, tare da waɗansu mutane. Suka dawo da Uriya daga Masar suka kawo shi wurin Sarki Yehohiyakim, wanda ya kashe shi da takobi aka kuma jefar da gawarsa a makabartar talakawa.) Bugu da ƙari, Ahikam ɗan Shafan ya goyi bayan Irmiya, saboda haka ba a ba da shi ga mutane don su kashe shi ba. A farkon sarautar Zedekiya ɗan Yosiya sarkin Yahuda, wannan magana ta zo wa Irmiya daga Ubangiji. Ga abin da Ubangiji ya ce mini, “Ka yi karkiyar itace da maɗaurai ka ɗaura a wuyanka. Sa’an nan ka aika da saƙo zuwa wurin sarakunan Edom, Mowab, Ammon, Taya da Sidon ta bakin jakadu waɗanda suka zo Urushalima wurin Zedekiya sarkin Yahuda. Ka ba su saƙo wa iyayengijinsu su ce, ‘Ga abin da Ubangiji Maɗaukaki, Allah na Isra’ila, yana cewa, “Ku faɗa wa iyayengijinku wannan. Da ikon mai ƙarfi da kuma hannuna da na miƙa na yi duniya da mutanenta da kuma dabbobin da suke ciki, na ba da ita ga duk wanda na ga dama. Yanzu zan ba da dukan ƙasashenku ga bawana Nebukadnezzar sarkin Babilon; zan sa namun jeji ma su bauta masa. Dukan al’ummai za su bauta masa da ɗansa da kuma jikansa har sai har lokacin ƙasarsa ya kai; sa’an nan al’ummai masu yawa da kuma manyan sarakuna za su kasance a ƙarƙashinsa. “ ‘ “Amma fa, duk al’umma ko mulkin da bai bauta wa Nebukadnezzar sarkin Babilon ba bai kuwa rusunar da wuyarsa ga karkiyarsa ba, zan hukunta wannan al’umma da takobi, yunwa da annoba, in ji Ubangiji, har sai na hallaka ta ta wurin hannunsa. Saboda haka kada ku saurari annabawanku, masu dubanku, masu fassarar mafarkanku, bokayenku ko masu maitancinku waɗanda suke ce muku, ‘Ba za ku bauta wa sarkin Babilon ba.’ Suna muku annabcin ƙaryar ne kawai da za tă kau da ku daga ƙasarku; zan kore ku za ku kuwa hallaka. Amma duk al’ummar da ta rusuna da wuyarta a ƙarƙashin karkiyar sarkin Babilon ta kuma bauta masa, zan bar al’ummar ta zauna a ƙasarta ta noma ta, ta kuma zauna a can, in ji Ubangiji.” ’ ” Na ba da wannan saƙo guda ga Zedekiya sarkin Yahuda. Na ce, “Ka rusunar da wuyanka a ƙarƙashin sarkin Babilon; ka bauta masa da kuma mutanensa, za ka kuwa rayu. Me ya sa kai da mutanenka za ku mutu saboda takobi, yunwa da annoba waɗanda Ubangiji ya yi barazana wa duk al’ummar da ba za tă bauta wa sarkin Babilon ba? Kada ku saurari maganganun annabawa waɗanda suke ce muku, ‘Ba za ku bauta wa sarkin Babilon ba,’ gama annabcin ƙarya suke muku. ‘Ban aike su ba,’ in ji Ubangiji. ‘Suna annabcin ƙarya ne da sunana. Saboda haka, zan kore ku za ku kuwa hallaka, da ku da kuma annabawan da suke muku annabci.’ ” Sai na ce wa firistoci da dukan waɗannan mutane, “Ga abin da Ubangiji yana cewa, kada ku saurari annabawan da suke cewa, ‘Ba daɗewa ba za a komo da kayan gidan Ubangiji daga Babilon.’ Suna muku annabcin ƙarya ne. Kada ku saurare su. Ku bauta wa sarkin Babilon, za ku kuwa rayu. Don me wannan birni zai zama kufai? In su annabawa ne da gaske suna kuma da maganar Ubangiji, bari su roƙi Ubangiji Maɗaukaki ya sa kada a kwashe kayayyakin da suka ragu a gidan Ubangiji da kuma a cikin fadar sarkin Yahuda da kuma cikin Urushalima a kai Babilon. Gama ga abin da Ubangiji Maɗaukaki yana cewa game da ginshiƙai, kwatarniya, da dakalai, da sauran kayayyaki da aka bar su a birnin nan, waɗanda Nebukadnezzar sarkin Babilon ya kwashe sa’ad da ya kame Yekoniya ɗan Yehohiyakim sarkin Yahuda zuwa zaman bauta daga Urushalima zuwa Babilon tare da dukan manyan mutanen Yahuda da Urushalima, I, ga abin da Ubangiji Maɗaukaki, Allah na Isra’ila yana cewa game da abubuwan da aka bari a gidan Ubangiji da kuma a cikin fadar sarkin Yahuda da Urushalima, ‘Za a kwashe su zuwa Babilon a can kuwa za su kasance sai ranar da na neme su,’ in ji Ubangiji. ‘Sa’an nan zan komo da su in maido da su wannan wuri.’ ” A wata na biyar na wannan shekara, shekara ta huɗu, a farkon sarautar Zedekiya sarkin Yahuda, sai annabi Hananiya ɗan Azzur, wanda ya fito daga Gibeyon, ya zo wurina a gidan Ubangiji a gaban firistoci da kuma dukan mutane, “Ga abin da Ubangiji Maɗaukaki, Allah na Isra’ila ya ce, ‘Zan karya karkiyar sarkin Babilon. Cikin shekaru biyu zan komo da dukan kayayyakin gidan Ubangiji da Nebukadnezzar sarkin Babilon ya kwashe daga wannan wuri ya kai Babilon. Zan kuma komo da Yekoniya ɗan Yehohiyakim sarkin Yahuda da kuma dukan sauran masu zaman bauta daga Yahuda waɗanda suka tafi Babilon,’ in ji Ubangiji, ‘gama zan karya karkiyar sarkin Babilon.’ ” Sai annabi Irmiya ya amsa wa annabi Hananiya a gaban firistoci da kuma dukan mutane waɗanda suke tsaye a gidan Ubangiji. Ya ce, “Amin! Ubangiji yă sa yă zama haka! Ubangiji yă cika maganar da ka yi annabci ta wurin komo da kayayyakin gidan Ubangiji da kuma dukan masu zaman bauta zuwa wannan wuri daga Babilon. Duk da haka, ka saurari abin da zan faɗa a kunnenka da kuma a kunnen duka mutane, Daga farko fari annabawan da suka riga ka da ni sun yi annabcin yaƙi, masifa da annoba a kan ƙasashe masu yawa da kuma manyan mulkoki. Amma annabin da ya yi annabcin salama shi za a ɗauka a matsayin wanda Ubangiji ya aika in har abin da ya furta ya zama gaskiya.” Sai annabi Hananiya ya cire karkiya daga wuyar annabi Irmiya ya karya ta, ya ce a gaban dukan mutane, “Ga abin da Ubangiji yana cewa, ‘A haka zan karya karkiyar Nebukadnezzar sarkin Babilon daga wuyan dukan al’ummai a cikin shekaru biyu.’ ” Da wannan, annabi Irmiya ya yi tafiyarsa. Ba a daɗe ba bayan annabi Hananiya ya karya karkiya daga wuyan annabi Irmiya, sai maganar Ubangiji ta zo wa Irmiya cewa, “Je ka faɗa wa Hananiya cewa, ‘Ga abin da Ubangiji yana cewa, ka karya karkiyar katako, amma a wurinsa za ka sami karkiyar ƙarfe. Ga abin da Ubangiji Maɗaukaki, Allah na Isra’ila, yana cewa zan sa karkiyar ƙarfe a wuyan dukan waɗannan al’ummai don in sa su bauta wa Nebukadnezzar sarkin Babilon, za su kuwa bauta masa. Zan ma sa shi ya mallaki namun jeji.’ ” Sa’an nan annabi Irmiya ya ce wa annabi Hananiya, “Ka saurara, Hananiya! Ubangiji bai aike ka ba, duk da haka ka lallashe wannan al’umma su dogara ga ƙarya. Saboda haka, ga abin da Ubangiji yana cewa, ‘Ina shirin kawar da kai daga fuskar duniya. A wannan shekara za ka mutu, domin ka yi wa’azin tawaye a kan Ubangiji.’ ” A wata na bakwai na wannan shekara, annabi Hananiya ya mutu. Ga abin da yake cikin wasiƙar annabi Irmiya da ya aika daga Urushalima zuwa ga sauran dattawan da suka ragu a cikin masu zaman bauta da kuma zuwa ga firistoci, annabawa da kuma dukan sauran mutanen da Nebukadnezzar ya kwashe zuwa zaman bauta daga Urushalima zuwa Babilon. (Wannan ya faru bayan Sarki Yekoniya da mahaifiyar sarauniya, shugabannin fada da kuma dukan shugabannin Yahuda da Urushalima, gwanayen sana’a da masu sassaƙa suka tafi zaman bauta daga Urushalima.) Ya ba da wasiƙar ta hannun Eleyasa ɗan Shafan da Gemariya ɗan Hilkiya, waɗanda Zedekiya sarkin Yahuda ya aika wurin Sarki Nebukadnezzar a Babilon. Wasiƙar ta ce, Ga abin da Ubangiji Maɗaukaki, Allah na Isra’ila, yana cewa ga dukan waɗanda aka kwashe zuwa zaman bauta daga Urushalima zuwa Babilon. “Ku gina gidaje ku zauna; ku dasa gonaki ku kuma ci abin da suka haifar. Ku yi aure ku kuma haifi ’ya’ya maza da mata; ku nemi mata wa ’ya’yanku maza, ku kuma ba da ’ya’yanku mata ga aure, saboda su ma za su haifi ’ya’ya maza da mata. Ku riɓaɓɓanya a can, kada ku ragu. Haka kuma, ku nemi zaman salama da cin gaba a birnin da aka kai ku zaman bauta. Ku yi addu’a ga Ubangiji saboda birnin, domin in ya ci gaba, ku ma za ku ci gaba.” I, ga abin da Ubangiji Maɗaukaki, Allah na Isra’ila yana cewa, “Kada ku bar annabawa da masu sihiri a cikinku su ruɗe ku. Kada ku saurari mafarkan da dā kuke ƙarfafa su su yi. Suna muku annabcin ƙarya da sunana. Ban aike su ba,” in ji Ubangiji. Ga abin da Ubangiji yana cewa, “Sa’ad da shekaru saba’in suka cika a Babilon, zan zo muku in cika alkawarin alherina don in komo da ku zuwa wannan wuri. Gama na san shirye-shiryen da na yi muku,” in ji Ubangiji, “shirye-shiryen cin gaba ba na cutarwa ba, shirye-shiryen ba ku sa zuciya da kuma na nan gaba. Sa’an nan za ku kira gare ni ku zo ku kuma yi addu’a gare ni, zan kuwa ji ku. Za ku neme ni ku kuwa same ni sa’ad da kuka neme ni da dukan zuciyarku. Za ku same ni,” in ji Ubangiji, “zan kuma komo da ku daga bauta. Zan tattaro ku daga dukan al’ummai in sa ku inda na kore ku,” in ji Ubangiji, “zan kuma komo da ku zuwa wurin da na kwashe ku zuwa zaman bauta.” Za ku iya ce, “ Ubangiji ya tā da annabawa saboda mu a Babilon.” Amma ga abin da Ubangiji yana cewa game da sarki, wanda yake zaune a kursiyin Dawuda da kuma dukan mutanen da suka ragu a wannan birni, ’yan’uwanku waɗanda ba su tafi tare da ku zuwa zaman bauta ba. I, ga abin da Ubangiji Maɗaukaki yana cewa, “Zan aika da takobi, yunwa da annoba a kansu zan kuma sa su zama kamar ɓaure marar amfani da suka yi munin da ba a iya ci. Zan fafare su da takobi, yunwa da annoba zan kuma sa su zama abin ƙyama ga dukan mulkokin duniya da kuma abin la’ana da abin bantsoro, abin dariya da abin reni, a cikin dukan al’umman da aka kore su zuwa. Gama ba su saurari maganata ba,” in ji Ubangiji, “maganar da na aika gare su sau da sau ta bayina annabawa. Ku kuma masu zaman bauta ba ku saurara ba,” in ji Ubangiji. Saboda haka, ku ji maganar Ubangiji, dukanku masu zaman bauta waɗanda na aika daga Urushalima zuwa Babilon. Ga abin da Ubangiji Maɗaukaki, Allah na Isra’ila, yana cewa game da Ahab ɗan Kolahiya da Zedekiya ɗan Ma’asehiya, waɗanda suke muku annabcin ƙarya da sunana. “Zan ba da su ga Nebukadnezzar sarkin Babilon, zai kuwa kashe su a gaban idanunku. Saboda su, dukan masu zaman bauta daga Yahuda waɗanda suke a Babilon za su yi amfani da wannan la’ana cewa, ‘ Ubangiji ka yi da mu kamar Zedekiya da Ahab waɗanda sarkin Babilon ya ƙone da wuta.’ Gama sun aikata munanan abubuwa a Isra’ila; sun yi zina da matan maƙwabtansu kuma da sunana suka yi ƙarya, waɗanda ban faɗa musu su yi ba. Na san wannan kuma ni shaida ne ga haka,” in ji Ubangiji. Faɗa wa Shemahiya mutumin Nehelam, “Ga abin da Ubangiji Maɗaukaki, Allah na Isra’ila, yana cewa ka aika da wasiƙu da sunanka ga dukan mutane a Urushalima, zuwa ga Zefaniya ɗan Ma’asehiya firist da kuma ga sauran firistoci. Ka ce wa Zefaniya, ‘ Ubangiji ya naɗa ka firist a wurin Yehohiyada don ka lura da gidan Ubangiji; ya kamata ka sa kowane mahaukaci wanda yake yi kamar annabi cikin turu da kuma a kangi. To, me ya sa ba ka tsawata wa Irmiya daga Anatot, wanda yana ɗauka kansa annabi a cikinku ba? Ya aiko mana da saƙonsa a Babilon cewa zai ɗauki lokaci ƙwarai. Saboda haka ku gina gidaje ku zauna; ku dasa gonaki ku kuma ci abin da suka haifar.’ ” Zefaniya firist kuwa, ya karanta wasiƙar annabi Irmiya. Sa’an nan maganar Ubangiji ta zo wa Irmiya cewa, “Ka aika da wannan saƙo zuwa ga dukan masu zaman bauta cewa, ‘Ga abin da Ubangiji yana cewa game da Shemahiya, mutumin Nehelam. Domin Shemahiya ya yi muku annabci, ko da yake ban aike shi ba, ya kuma sa kuka gaskata ƙarya, ga abin da Ubangiji yana cewa, tabbatacce zan hukunta Shemahiya mutumin Nehelam da zuriyarsa. Ba zai kasance da wani da ya rage a cikin wannan mutane ba, ba kuwa zai ga abubuwa alherin da zan yi wa mutanena ba, in ji Ubangiji, domin ya yi wa’azin tawaye a kaina.’ ” Ga maganar da ta zo wa Irmiya daga Ubangiji. “Ga abin da Ubangiji, Allah na Isra’ila, yana cewa, ‘Ka rubuta a cikin littafi dukan maganganun da na yi maka. Kwanaki suna zuwa,’ in ji Ubangiji, ‘sa’ad da zan komo da mutanena Isra’ila da Yahuda daga bauta in kuma maido da su ga ƙasar da na ba wa kakanninsu mallaka,’ in ji Ubangiji.” Ga kalmomin Ubangiji da ya yi game da Isra’ila da Yahuda, “Ga abin da Ubangiji yana cewa, “ ‘Ana jin kukan tsoro, razana, ba salama ba. Ku tambaya ku ji. Namiji zai iya haifi ’ya’ya? To, me ya sa kuke ganin kowane mai ƙarfi da hannuwansa a kwankwaso kamar mace mai naƙuda, kowace fuska ta koma fari? Kaito, gama wannan rana za tă zama mai girma! Babu kamar ta. Zai zama lokacin wahala wa Yaƙub, amma za a cece shi daga cikinta. “ ‘A wannan rana,’ in ji Ubangiji Maɗaukaki, ‘Zan karya karkiya daga wuyansu zan kuma cire musu kangi; baƙi ba za su ƙara bautar da su ba. A maimakon haka, za su bauta wa Ubangiji Allahnsu Dawuda sarkinsu kuwa, wanda na tayar musu. “ ‘Saboda haka kada ka ji tsoro, ya Yaƙub bawana; kada ka karai, ya Isra’ila,’ in ji Ubangiji. ‘Tabbatacce zan cece ka daga wuri mai nesa, zuriyarka daga ƙasar zaman bautansu. Yaƙub zai sami salama da zaman lafiya, kuma ba wanda zai sa ya ji tsoro. Ina tare da kai zan kuma cece ka,’ in ji Ubangiji. ‘Ko da yake na hallakar da dukan al’umma gaba ɗaya a inda na warwatsa ku, ba zan hallaka ku gaba ɗaya ba. Zan hore ku amma da adalci kaɗai; ba zan ƙyale ku ku tafi gaba ɗaya ba hukunci ba.’ “Ga abin da Ubangiji yana cewa, “ ‘Mikinku marar warkewa ne, raunin da kuka ji ya sha ƙarfin warkarwa. Babu wanda zai yi roƙo saboda damuwarku, ba magani domin mikinku babu warkarwa dominku. Dukan abokanku sun manta da ku; ba su ƙara kulawa da ku. Na buge ku kamar yadda abokin gāba zai yi na kuma hukunta ku yadda mai mugunta zai yi, domin laifinku da girma yake zunubanku kuma da yawa suke. Me ya sa kuke kuka a kan mikinku, wahalarku da ba ta da magani? Domin laifinku da girma yake da kuma zunubanku masu yawa na yi muku waɗannan abubuwa. “ ‘Amma duk wanda ya cinye ku za a cinye shi; dukan abokan gābanku za su tafi zaman bauta. Waɗanda suka washe ku su ma za a washe su; dukan waɗanda suka mai da ku ganima su ma zan mai da su ganima. Amma zan mayar muku da lafiya in kuma warkar da mikinku,’ in ji Ubangiji, ‘domin ana ce da ku yasassu, Sihiyona wadda ba wanda ya kula da ita.’ “Ga abin da Ubangiji yana cewa, “ ‘Zan mayar da wadatar tentin Yaƙub in kuma ji tausayin wuraren zamansa; za a sāke gina birnin a kufansa, fadar kuwa za tă tsaya a wurin da ya dace da ita. Daga gare su waƙoƙi za su fito na godiya da kuma sowa ta farin ciki. Zan riɓaɓɓanya su, ba za su kuwa ragu ba; zan kawo musu ɗaukaka, ba kuwa za a ƙasƙanta su ba. ’Ya’yansu za su kasance kamar a kwanakin dā jama’arsu kuma za su kahu a gabana; zan hukunta duk wanda ya zalunce su. Shugabansu zai zama ɗaya daga cikinsu; mai mulkinsu zai taso daga cikinsu. Zan kawo shi kusa zai kuma zo kusa da ni, gama wane ne zai miƙa kansa don yă yi kusa da ni?’ In ji Ubangiji. ‘Saboda haka za ku zama mutanena, ni kuwa in zama Allahnku.’ ” Ga shi, hadarin Ubangiji zai fasu cikin hasala, iskar guguwa mai hurawa a kan kawunan mugaye. Fushi mai zafi na Ubangiji ba zai kawu ba sai ya cika manufofin zuciyarsa gaba ɗaya. A kwanaki masu zuwa za ku gane wannan. “A lokacin nan, zan zama Allah na dukan kabilan Isra’ila, za su kuma zama mutanena,” in ji Ubangiji. Ga abin da Ubangiji yana cewa, “Mutanen da suka tsere wa takobi za su sami tagomashi a hamada; zan zo don in ba da hutu ga Isra’ila.” Ubangiji ya bayyana mana a dā, yana cewa, “Na ƙaunace ku da madawwamiyar ƙauna; na janye ku da ƙauna marar iyaka. Zan sāke gina ki za ki kuwa sāke ginuwa, ya Budurwar Isra’ila. Za ki kuma ɗauki ganganki ki fita don ki yi rawa da masu farin ciki. Za ki sāke dasa gonakin inabi a kan tussan Samariya; manoma za su yi shuka a kansu su kuma ji daɗin amfaninsu. Za a yi ranar da matsara za su tā da murya a kan tuddan Efraim su ce, ‘Ku zo, bari mu haura Sihiyona, zuwa wurin Ubangiji Allahnmu.’ ” Ga abin da Ubangiji yana cewa, “Ku rera don farin ciki wa Yaƙub; ku yi sowa don al’ummai da suke nesa. Ka sa a ji yabanku, ku kuma ce, ‘Ya Ubangiji ka ceci mutanenka, raguwar Isra’ila.’ Ga shi, zan kawo su daga ƙasar arewa in tattara su daga iyakar duniya. A cikinsu makafi da guragu za su kasance, mata masu ciki da matan da suke naƙuda; jama’a mai yawan gaske za su komo. Za su zo da kuka; za su yi addu’a yayinda nake komo da su. Zan bishe su kusa da rafuffukan ruwa a miƙaƙƙiyar hanya inda ba za su yi tuntuɓe ba, domin ni ne mahaifin Isra’ila, Efraim kuma ɗan farina ne. “Ku ji maganar Ubangiji, ya al’ummai; ku yi shelarta a gaban teku masu nesa cewa, ‘Shi wanda ya watsar da Isra’ila zai tattara su zai kuma lura da garkensa kamar makiyayi.’ Gama Ubangiji zai fanshi Yaƙub zai cece su daga hannun waɗanda suka fi su ƙarfi. Za su zo su yi sowa don farin ciki a ƙwanƙolin Sihiyona; za su yi farin ciki cikin yalwar Ubangiji hatsi, sabon ruwan inabi da mai, ’ya’yan garken tumaki da na shanu. Za su zama kamar gonar da aka yi wa banruwa, ba za su ƙara yin baƙin ciki ba. ’Yan mata za su yi rawa su kuma yi murna, haka ma samari da tsofaffi. Zan mai da makokinsu farin ciki; zan ta’azantar da su in kuma sa su yi farin ciki a maimakon baƙin ciki. Zan ƙosar da firistoci da yalwa, mutanena kuma za su cika da yalwa,” in ji Ubangiji. Ga abin da Ubangiji yana cewa, “An ji murya daga Rama, makoki da kuka mai zafi, Rahila tana kuka domin ’ya’yanta ta kuma ƙi a ta’azantar da ita domin ’ya’yanta ba su.” Ga abin da Ubangiji yana cewa, “Hana muryarki kuka da kuma idanunki hawaye, gama za a sāka wa aikinki,” in ji Ubangiji. “Za su komo daga ƙasar abokin gāba. Saboda haka akwai sa zuciya domin nan gaba,” in ji Ubangiji. “’Ya’yanki za su komo ƙasarsu. “Tabbatacce na ji gurnanin Efraim yana cewa, ‘Ka hore ni kamar ɗan maraƙi mai ƙin ji, na kuwa horu. Ka mayar da ni, zan kuwa dawo, domin kai ne Ubangiji Allahna. Bayan na kauce, sai na tuba; bayan na gane, sai na sunkuyar da kaina. Na ji kunya da ƙasƙanci domin ina ɗauke da kunyar ƙuruciyata.’ Efraim ba ƙaunataccen ɗana ba ne, ɗan da nake jin daɗinsa? Ko da yake sau da dama ina maganar gāba a kansa, duk da haka nakan tuna da shi. Saboda haka zuciyata tana marmarinsa; ina da jinƙai mai girma dominsa,” in ji Ubangiji. “Ki kafa alamun hanya; ki sa shaidun bishewa. Ki lura da babbar hanya da kyau, hanyar da kika bi. Ki komo, ya Budurwar Isra’ila, ki komo zuwa garuruwanki. Har yaushe za ki yi ta yawo, Ya ’ya marar aminci? Ubangiji zai ƙirƙiro sabon abu a duniya mace za tă kewaye namiji.” Ga abin da Ubangiji Maɗaukaki, Allah na Isra’ila yana cewa, “Sa’ad da na komo da su daga bauta mutane a ƙasar Yahuda da cikin garuruwanta za su sāke yi amfani da waɗannan kalmomi. ‘ Ubangiji ya albarkace ka, ya mazauni mai adalci, ya tsarkakan dutse.’ Mutane za su zauna tare a Yahuda da dukan garuruwansa, manoma da waɗanda suke yawo da garkunansu. Zan wartsake waɗanda suka gaji in kuma ƙosar da waɗanda ransu ya yi yaushi.” A kan wannan na farka na duba kewaye. Barcina ya yi mini daɗi. “Kwanaki suna zuwa,” in ji Ubangiji, “sa’ad da zan kafa gidan Isra’ila da gidan Yahuda da ’ya’yan mutane da na dabbobi. Kamar yadda na lura da su don su tumɓuke su kuma rusar, su lalatar, su hallaka su kuma kawo masifa, haka zan lura da su don su gina su kuma dasa,” in ji Ubangiji. “A waɗannan kwanaki mutane ba za su ƙara ce, “ ‘Ubanni suka ci ’ya’yan inabi masu tsami, haƙoran ’ya’ya suka mutu ba.’ A maimako, kowa zai mutu saboda zunubinsa; duk wanda ya ci ’ya’yan inabi masu tsami, haƙoransa ne za su mutu. “Lokaci yana zuwa,” in ji Ubangiji, “sa’ad da zan yi sabon alkawari da gidan Isra’ila da kuma gidan Yahuda. Ba zai zama kamar alkawarin da na yi da kakanni kakanninsu ba sa’ad da na kama su da hannu na bishe su daga Masar, domin sun take alkawarina, ko da yake na zama miji a gare su,” in ji Ubangiji. “Ga alkawarin da zan yi da gidan Isra’ila bayan wannan lokaci,” in ji Ubangiji. “Zan sa dokata a tunaninsu in kuma rubuta ta a zukatansu. Zan zama Allahnsu, za su kuma zama mutanena. Mutum ba zai ƙara koya wa maƙwabci ba, ko ya koya wa ɗan’uwansa cewa, ‘Ka san Ubangiji,’ domin duk za su san ni, daga ƙaraminsu har zuwa babba,” in ji Ubangiji. “Gama zan gafarta muguntarsu ba zan kuwa ƙara tuna da zunubansu ba.” Ga abin da Ubangiji yana cewa, shi da ya kafa rana don tă yi haske a yini shi da ya sa wata da taurari su yi haske da dare, shi da yake dama teku don raƙuman ruwansa su yi ruri Ubangiji Maɗaukaki ne sunansa. “In dai wannan kafaffiyar ƙa’ida ta daina aiki a gabana,” in ji Ubangiji, “to, sai zuriyar Isra’ila ta daina zama al’umma a gabana.” Ga abin da Ubangiji yana cewa, “In a iya auna sammai a kuma bincike tushen duniya a ƙarƙas to, sai in ƙi dukan zuriyar Isra’ila ke nan saboda dukan abin da suka yi,” in ji Ubangiji. “Kwanaki suna zuwa,” in ji Ubangiji, “sa’ad da za a sāke gina wannan birni domina daga Hasumiyar Hananel zuwa Ƙofar Kusurwa. Ma’auni zai miƙe daga can ya nausa kai tsaye zuwa tudun Gareb sa’an nan ya juya zuwa Gowa. Dukan kwarin da ake zubar da toka da kuma gawawwaki, da dukan lambatun da suke can har zuwa Kwarin Kidron a gabas zuwa kusurwar Ƙofar Doki, za su zama mai tsarki ga Ubangiji. Ba za a ƙara tumɓuke birnin ko a rushe shi ba.” Ga maganar da ta zo wa Irmiya daga Ubangiji a shekara ta goma ta Zedekiya sarkin Yahuda, wanda ya kasance shekara ta goma sha takwas ta Nebukadnezzar. Sojojin sarkin Babilon a lokacin suna ƙawanya wa Urushalima annabi Irmiya kuwa yana a tsare a sansanin matsara a fadar Yahuda. Zedekiya sarkin Yahuda fa ya sa shi a kurkuku yana cewa, “Don me kake yin annabci? Ka ce, ‘Ga abin da Ubangiji yana cewa, ina gab da ba da wannan birni ga sarkin Babilon, zai kuwa cinye ta. Zedekiya sarkin Yahuda ba zai kuɓuta daga hannuwan Babiloniyawa ba amma tabbatacce za a ba da shi ga sarkin Babilon, zai kuwa yi masa magana fuska da fuska ya kuma gan shi da idanunsa. Zai kai Zedekiya Babilon, inda zai zauna har sai ya magance shi, in ji Ubangiji. In ka yi yaƙi da Babiloniyawa, ba za ka yi nasara ba.’ ” Irmiya ya ce, “Maganar Ubangiji ta zo mini cewa, Hananel ɗan Shallum ɗan’uwan mahaifinka zai zo wurinka ya ce, ‘Saya filina a Anatot, domin a matsayinka na dangi na kurkusa hakkinka ne kuma kai ya wajaba ka saye shi.’ “Sa’an nan, kamar dai yadda Ubangiji ya faɗa, sai ga Hananel yaron ɗan’uwan mahaifina ya zo wurina a sansanin matsara ya ce, ‘Saya filina a Anatot a yankin Benyamin. Da yake hakkinka ne ka fanshe shi ka kuma mallake shi, ka sayo shi wa kanka.’ “Sai na gane cewa wannan maganar Ubangiji ce; saboda haka sai na saye filin a Anatot daga hannun Hananel yaron ɗan’uwan mahaifina na kuma auna masa shekel goma sha bakwai na azurfa. Na sa hannu a takarda, na buga hatimi na liƙe, na sami shaidu na kuwa auna shekel a ma’auni. Na ɗauki takardar ciniki, takardar da aka rubuta sharuɗan a ciki, da kuma takardar da ba a liƙe ba, na kuma ba wa Baruk ɗan Neriya, ɗan Masehiya, wannan takarda a gaban Hananel yaron ɗan’uwan mahaifina da kuma a gaban shaidun da suka sa hannu a takardan ciniki da kuma a gaban dukan Yahudawan da suke zaune a sansanin matsaran. “A gabansu na yi wa Baruk waɗannan umarnai cewa, ‘Ga abin da Ubangiji Maɗaukaki, Allah na Isra’ila, yana cewa ka ɗauki waɗannan takardun ciniki, wanda aka liƙe da wanda ba a liƙe ba, ka sa su a cikin tulun yumɓu don kada su lalace. Gama ga abin da Ubangiji Maɗaukaki, Allah na Isra’ila, yana cewa za a sāke saye gidaje, filaye da gonakin inabi a wannan ƙasa.’ “Bayan na ba da takardun ciniki ga Baruk ɗan Neriya, sai na yi addu’a ga Ubangiji na ce, “A, Ubangiji Mai Iko Duka, ka yi sammai da duniya ta wurin ikonka mai girma da kuma hannunka mai iko. Ba abin da ya gagare ka. Kakan nuna ƙauna ga dubbai amma kakan hukunta ’ya’ya saboda laifin ubanninsu a bayansu. Ya mai girma da kuma Allah mai iko, wanda sunansa ne Ubangiji Maɗaukaki, manufofinka da girma suke, ayyukanka kuma masu girma ne. Idanunka suna a buɗe ga dukan hanyoyin mutane; kakan sāka wa kowa gwargwadon halinsa yadda ya dace. Ka aikata ayyukan banmamaki da kuma al’ajabai a Masar ka kuma ci gaba da su har yă zuwa yau, a Isra’ila da kuma a cikin dukan ’yan adam, ka kuma sami sunan da har yanzu yake naka. Ka fitar da mutanenka Isra’ila daga Masar da alamu da abubuwa banmamaki, ta wurin hannu mai iko da kuma hannu mai ƙarfi tare da banrazana mai girma. Ka ba su wannan ƙasa da ka rantse za ka ba wa kakanni kakanninsu, ƙasa mai zub da madara da zuma. Suka shiga suka mallake ta, amma ba su yi maka biyayya ba, ba su kuma bi dokarka ba; ba su yi abin da ka umarce su ba. Saboda haka ka kawo masifa a kansu. “Duba yadda aka gina mahaurai don a kame birni. Saboda takobi, yunwa da annoba, za a ba da birnin ga Babiloniyawa waɗanda suka kewaye shi da yaƙi. Abin da ka faɗa ya faru, yadda kake gani yanzu. Ko da yake za a ba da birnin ga Babiloniyawa, kai, ya Ubangiji Mai Iko Duka, ka ce mini, ‘Saye fili da azurfa ka kuma sa a shaida cinikin.’ ” Sa’an nan maganar Ubangiji ta zo wa Irmiya cewa, “Ni ne Ubangiji Allah na dukan ’yan adam. Akwai wani abin da ya gagare ni? Saboda haka, ga abin da Ubangiji yana cewa, ina gab da ba da wannan birni ga Babiloniyawa da kuma ga Nebukadnezzar sarkin Babilon, wanda zai yaƙe ta. Babiloniyawan da suke yaƙi da wannan birni za su zo ciki su cinna masa wuta; tare da gidaje inda mutane suka tsokane ni na yi fushi ta wurin ƙona turare a rufin ɗakuna wa Ba’al suka zub da hadayun sha wa waɗansu alloli. “Mutanen Isra’ila da na Yahuda ba abin da suka yi sai mugunta a gabana daga ƙuruciyarsu; tabbatacce, mutanen Isra’ila ba su yi kome ba sai dai tsokane ni da abin da hannuwansu suka yi, in ji Ubangiji. Daga ranar da aka gina ta har zuwa yanzu, wannan birni ta tā da fushina da hasalata da dole a kawar da ita daga gabana. Mutanen Isra’ila da na Yahuda sun tsokane ni ta wurin dukan muguntar da suka aikata su, sarakunansu da fadawansu, firistocinsu da annabawa, mutanen Yahuda da mutanen Urushalima. Sun juya mini bayansu ba fuskokinsu ba; ko da yake na koyar da su sau da sau, ba su saurara ko bi horo na ba. Sun kafa gumakansu na banƙyama a cikin haikalina wanda ake kira da sunana, sun kuwa ƙazantar da shi. Sun gina masujadai kan tudu wa Ba’al a Kwarin Ben Hinnom don su miƙa ’ya’yansu maza da mata hadaya ga Molek, ko da yake ban taɓa umarce su ba, bai kuma zo mini cewa su yi abin banƙyama irin wannan ba ta haka suka sa Yahuda ya yi zunubi. “Kana cewa game da wannan birni, ‘Ta wurin takobi, yunwa da annoba za a ba da shi ga sarkin Babilon’; amma ga abin da Ubangiji, Allah na Isra’ila yana cewa tabbatacce zan tattara su daga dukan ƙasashen da na kore su zuwa cikin fushina da hasalata mai girma; zan komo da su wurin nan in sa su zauna lafiya. Za su zama mutanena, ni kuwa in zama Allahnsu. Zan ba su zuciya ɗaya da aiki ɗaya, don kullum su ji tsorona domin amfaninsu da kuma amfanin ’ya’yansu a bayansu. Zan yi madawwamin alkawari da su. Ba zan taɓa barin aikata musu alheri ba, zan kuma iza su su ji tsorona, don kada su ƙara juya daga gare ni. Zan yi farin ciki a yin musu alheri, tabbatacce zan su dasa a wannan ƙasa da dukan zuciyata da dukan raina. “Ga abin da Ubangiji yana cewa, yadda na kawo dukan wannan masifa a kan wannan mutane, haka zan ba su wadatar da na yi musu alkawari. Za a sāke sayi filaye a wannan ƙasa da kuka ce, ‘Kango ce, ba mutane ko dabbobi, gama an ba da ita ga Babiloniyawa.’ Za a sayi filaye da azurfa, a kuma sa hannu a takardan ciniki, a liƙe a kuma shaida a yankin Benyamin, a ƙauyukan kewayen Urushalima, a garuruwan Yahuda da kuma a garuruwan ƙasar tudu, na yammancin gindin dutse da na Negeb, domin zan maido da wadatarsu, in ji Ubangiji.” Yayinda Irmiya yana a tsare a sansanin matsara, sai maganar Ubangiji ta zo masa sau na biyu cewa, “Ga abin da Ubangiji yana cewa, shi da ya halicci duniya, Ubangiji wanda ya siffanta ta ya kuma kafa ta, Ubangiji ne sunansa. ‘Kira gare ni zan kuwa amsa maka in kuma faɗa maka manyan abubuwan da ba a iya kaiwa, da ba ka sani ba.’ Gama ga abin da Ubangiji, Allah na Isra’ila yana cewa game da gidaje a wannan birni da fadodin Yahuda da aka rurrushe domin a yi amfani da su a kan mahaurai da kuma takobi a yaƙi da Babiloniyawa. ‘Za su cika da gawawwakin mutane waɗanda na kashe da fushina da hasalata. Zan ɓoye fuskata wa wannan birni saboda dukan muguntarsu. “ ‘Duk da haka, zan kawo lafiya da warkarwa gare ta; zan warkar da mutanena in kuma wadata su da salama da zama lafiya. Zan komo da Yahuda da Isra’ila daga bauta zan kuma sāke gina su kamar yadda suke a dā. Zan tsarkake su daga dukan zunubin da suka yi mini zan kuma gafarta musu dukan zunubansu na yin mini tawaye. Sa’an nan birnin nan za tă sa in zama sananne, farin ciki, yabo da girma a gaban dukan al’ummai a duniya da suka ji abubuwa masu kyau da na yi mata; za su kuma yi mamaki su kuma yi rawan jiki saboda yalwar wadata da salamar da na ba ta.’ “Ga abin da Ubangiji yana cewa, ‘Kuna cewa game da wannan wuri, “Kango ne, babu mutane ko dabbobi.” Duk da haka a cikin garuruwan Yahuda da titunan Urushalima da aka yashe, inda ba mutane ko dabbobi, za a sāke jin sowa ta farin ciki da murna, muryoyin amarya da na ango, da muryoyin waɗanda suka kawo hadayun salama a gidan Ubangiji suna cewa, “ ‘ “Ku yi godiya ga Ubangiji Maɗaukaki, gama Ubangiji mai alheri ne; ƙaunarsa za tă dawwama har abada.” Gama zan mayar da wadatar ƙasar kamar yadda suke a dā,’ in ji Ubangiji. “Ga abin da Ubangiji Maɗaukaki yana cewa, ‘A wannan wuri, kango da babu mutane ko dabbobi, cikin dukan garuruwansa za a sāke kasance da wurin kiwo don makiyaya su hutar da garkunansu. A cikin garuruwan ƙasar tudu, garuruwan yammancin gindin dutse da na Negeb, a yankin Benyamin, a cikin ƙauyuka kewayen Urushalima da kuma a cikin garuruwan Yahuda, garkuna za su sāke bi a ƙarƙashin hannun mai ƙidayawa,’ in ji Ubangiji. “ ‘Kwanaki suna zuwa,’ in ji Ubangiji, ‘sa’ad da zan cika alkawarin alheri da na yi wa gidan Isra’ila da kuma gidan Yahuda. “ ‘A waɗannan kwanaki da kuma a wannan lokaci zan tā da Reshe mai adalci daga zuriyar Dawuda; zai yi abin da yake daidai da kuma gaskiya a ƙasar. A kwanakin nan zan ceci Yahuda Urushalima kuma za tă zauna lafiya. Sunan da za a kira ta shi ne, Ubangiji Adalcinmu.’ Gama ga abin da Ubangiji yana cewa, ‘Dawuda ba zai taɓa rasa mutumin da zai zauna a gadon sarautar Isra’ila ba, ba kuwa firistoci waɗanda suke Lawiyawa za su rasa mutumin da zai ci gaba da tsaya a gabana don miƙa hadayun ƙonawa, ya ƙona hadayun hatsi ya kuma miƙa sadakoki ba.’ ” Sai maganar Ubangiji ta zo wa Irmiya cewa, “Ga abin da Ubangiji yana cewa, ‘In ka tā da alkawarina na rana da kuma alkawarina na dare, har dare da rana ba za su ƙara bayyana a ƙayyadaddun lokutansu ba, to, sai a tā da alkawarina da Dawuda bawana da alkawarina da Lawiyawan da suke firistoci masu hidima a gabana, Dawuda kuma ba zai ƙara kasance da zuriyar da za tă yi mulki. Zan sa zuriyar Dawuda bawana da kuma Lawiyawan da suke hidima a gabana su yi yawa kamar taurarin sararin sama da kuma yashin bakin tekun da ba a iya ƙidaya.’ ” Sai maganar Ubangiji ta zo wa Irmiya cewa, “Ba ka lura ba cewa waɗannan mutane suna cewa, ‘ Ubangiji ya ƙi masarautai biyu da ya zaɓa’? Saboda haka suka rena mutanena ba sa ƙara ɗaukansu a matsayin al’umma. Ga abin da Ubangiji yana cewa, ‘In ban kafa alkawarina game da rana da kuma game da dare ba in kuma gyara dokokin sama da duniya ba, to zan ƙi zuriyar Yaƙub da na Dawuda bawana ba zan kuma zaɓi ɗaya daga cikin ’ya’yansa maza ya yi mulki a kan zuriyar Ibrahim, Ishaku da Yaƙub ba. Gama zan mayar da wadatarsu in kuma yi musu jinƙai.’ ” Yayinda Nebukadnezzar sarkin Babilon da dukan sojojinsa da kuma dukan mulkokinsa da mutanen masarautar da yake mulki suna yaƙi da Urushalima da dukan garuruwan da suke kewaye, sai wannan magana ta zo wa Irmiya daga wurin Ubangiji cewa, “Ga abin da Ubangiji, Allah na Isra’ila, yana cewa ka tafi wurin Zedekiya sarkin Yahuda ka faɗa masa, ‘Ga abin da Ubangiji yana cewa, ina gab da ba da wannan birni ga sarkin Babilon, zai kuwa ƙone ta. Ba za ka tsere daga hannunsa ba amma tabbatacce za a kama ka a kuma ba da kai gare shi. Za ka ga sarkin Babilon da idanunka, zai kuwa yi magana da kai fuska da fuska. Za ka kuwa tafi Babilon. “ ‘Duk da haka ka ji alkawarin Ubangiji, ya Zedekiya sarkin Yahuda. Ga abin da Ubangiji yake cewa game da kai. Ba za ka mutu ta takobi ba; za ka mutu cikin salama. Yadda mutane suka ƙuna wutar jana’iza don girmama kakanninka, sarakunan da suka riga ka, haka za su ƙuna wuta don girmama da kuma makokinka suna cewa, “Kaito, ya maigida!” Ni kaina na yi wannan alkawari, in ji Ubangiji.’ ” Sa’an nan annabi Irmiya ya faɗi dukan wannan wa Zedekiya sarkin Yahuda, a Urushalima, yayinda sojojin sarkin Babilon suna yaƙi da Urushalima da sauran garuruwan Yahuda waɗanda suka ragu, Lakish da Azeka. Waɗannan su ne birane masu katanga kaɗai a Yahuda. Maganar ta zo wa Irmiya daga Ubangiji bayan Sarki Zedekiya ya yi yarjejjeniya da duka mutane a Urushalima ya yi shelar ’yanci wa bayi. Kowa ya ’yantar da bayinsa da suke Ibraniyawa, maza da mata; kada kowa ya riƙe bawa wanda yake mutumin Yahuda. Saboda haka dukan fadawa da mutane suka yi yarjejjeniyar cewa za su ’yantar da bayinsu maza da mata ba za su kuwa ƙara riƙe su bayi ba. Suka yarda, suka kuma sake su. Amma daga baya suka canja ra’ayoyinsu suka maido bayinsu suka kuma sāke bautar da su. Sai maganar Ubangiji ta zo wa Irmiya cewa, “Ga abin da Ubangiji, Allah na Isra’ila, yana cewa na yi alkawari da kakanni-kakanninku sa’ad da na fitar da su daga Masar, daga ƙasar bauta. Na ce, ‘A kowace shekara ta bakwai dole kowannenku yă ’yantar da duk wani ɗan’uwa mutumin Ibraniyawa wanda aka sayar masa. Bayan ya yi muku hidima shekaru shida, dole ku bar shi yă tafi ’yantacce.’ Amma kakanninku ba su saurare ni ba, ba su ji ni ba. Bai daɗe ba da kuka tuba, kuka kuma yi abin da yake mai kyau a idona. Kowannenku ya yi shelar ’yanci ga ɗan’uwansa. Kun ma yi yarjejjeniya a gabana a gidan da ake kira da Sunana. Amma yanzu kun juya kun kuma ɓata sunana; kowannenku ya mayar da bayi maza da matan da kuka ’yantar su tafi inda suka ga dama. Kun sāke tilasta su su zama bayinku. “Saboda haka, ga abin da Ubangiji yana cewa, kun yi mini rashin biyayya; ba ku yi shelar ’yanci don ’yan’uwanku ba. Saboda haka yanzu na yi muku shelar ’yanci in ji Ubangiji, ’yanci ga mutuwa ta takobi, annoba da kuma yunwa. Zan sa ku zama abin ƙyama ga sauran mulkokin duniya. Mutanen da suka keta alkawarina da ba su cika sharuɗan alkawarin da suka yi a gabana ba, zan yi da su kamar ɗan maraƙin da suka yanka biyu suka bi ta tsakiyarsa. Shugabannin Yahuda da Urushalima, fadawa, firistoci da kuma dukan mutanen ƙasar waɗanda suka bi tsakanin ɗan maraƙin da aka yanka, zan ba da su ga abokan gābansu waɗanda suke neman ransu. Gawawwakinsu za su zama abincin tsuntsayen sararin sama da na namun jeji. “Zan ba da Zedekiya sarkin Yahuda da fadawansa ga abokan gābansu waɗanda suke neman ransu, ga sojojin sarkin Babilon, waɗanda suke janye daga gare ku. Zan yi umarni, in ji Ubangiji, zan kuma komo da su wannan birni. Za su kuwa yi yaƙi da ita, su ƙwace ta su kuma ƙone ta. Zan kuma mai da garuruwan Yahuda kufai don kada wani ya zauna a can.” Ga maganar da ta zo wa Irmiya daga wurin Ubangiji a lokacin mulkin Yehohiyakim ɗan Yosiya sarkin Yahuda. “Ka tafi wurin iyalin Rekabawa ka gayyace su su zo a ɗaya daga cikin ɗakunan da suke gefe a gidan Ubangiji ka kuma ba su ruwan inabi su sha.” Sai na tafi don in kawo Ya’azaniya ɗan Irmiya, ɗan Habazziniya, da ’yan’uwansa da kuma dukan ’ya’yansa maza, dukan iyalin Rekabawa. Na kawo su cikin gidan Ubangiji, a cikin ɗakin ’ya’yan Hanan ɗan Igdaliya maza mutumin Allah. Ɗakin ne kusa da ɗakin fadawa, wanda yake bisa na Ma’asehiya ɗan Shallum mai tsaron ƙofa. Sai na ajiye ƙwarya cike da ruwan inabi da waɗansu kwaf a gaban iyalin Rekabawan na kuma ce musu, “Ku sha ruwan inabin.” Amma sai suka amsa suka ce, “Ba ma shan ruwan inabi, domin kakanmu Yehonadab ɗan Rekab ya umarce mu cewa, ‘Ko ku, ko zuriyarku kada ku sha ruwan inabi. Haka kuma ba za ku gina gidaje, ku dasa iri ko ku nome gonakin inabi ba; kada ku kasance da wani daga cikin waɗannan abubuwa, amma dole kullum ku zauna a tentuna. Ta haka za ku yi dogon rai a cikin ƙasar baƙuncinku.’ Mun yi biyayya da kome da kakanmu Yehonadab ɗan Rekab ya umarce mu. Mu ko matanmu ko ’ya’yanmu maza da mata ba mu taɓa shan ruwan inabi ba ba mu kuma gina gidaje mu zauna a ciki ba ko mu yi gonakin inabi, gonaki ko hatsi ba. Mun yi rayuwarmu a cikin tentuna mun kuma yi biyayya ƙwarai da kowane abin da kakanmu Yehonadab ya umarce mu. Amma da Nebukadnezzar sarkin Babilon ya kawo wa ƙasan nan hari, sai muka ce, ‘Ku zo, dole mu tafi Urushalima don mu tsira daga Babiloniyawa da kuma sojojin Arameyawa.’ Saboda haka ne muke a Urushalima.” Sai maganar Ubangiji ta zo wa Irmiya cewa, “Ga abin da Ubangiji, Maɗaukaki, Allah na Isra’ila, yana cewa ka tafi ka faɗa wa mutanen Yahuda da kuma mutanen Urushalima cewa, ‘Ba za ku koyi darasi ku kuma yi biyayya da maganata ba?’ In ji Ubangiji. ‘Yehonadab ɗan Rekab ya umarci ’ya’yansa maza kada su sha ruwan inabi sun kuma kiyaye wannan umarni. Har yă zuwa yau ba sa shan ruwan inabi, domin sun yi biyayya da umarnin kakansu. Amma na yi muku magana sau da sau, duk da haka ba ku yi biyayya ba. Sau da sau na aika dukan bayina annabawa gare ku. Suka ce, “Kowannenku ya juyo daga mugayen hanyoyinsa ya sabunta ayyukansa; kada yă bi waɗansu alloli don yă bauta musu. Ta haka za ku zauna a cikin ƙasar da na ba ku da kuma kakanninku.” Amma ba ku saurara ba, ba ku kuwa ji ni ba. Zuriyar Yehonadab ɗan Rekab sun yi biyayya da umarnin da kakansu ya ba su, amma waɗannan mutane ba su yi mini biyayya ba.’ “Saboda haka, ga abin da Ubangiji Allah Maɗaukaki, Allah na Isra’ila, yana cewa, ‘Ku saurara! Zan kawo wa Yahuda da kuma kowane mutumin da yake zama a Urushalima kowace masifar da na ambata a kansu. Na yi musu magana, amma ba su saurara ba; na kira su, amma ba su amsa ba.’ ” Sai Irmiya ya ce wa iyalin Rekabawa, “Ga abin da Ubangiji Maɗaukaki, Allah na Isra’ila, yana cewa, ‘Kun yi biyayya da umarnin kakanku Yehonadab kuka kuma kiyaye dukan umarnansa kuka yi kome bisa ga tsari.’ Saboda haka, ga abin da Ubangiji Maɗaukaki, Allah na Isra’ila, yana cewa, ‘Yehonadab ɗan Rekab ba zai taɓa rasa mutumin da zai yi mini hidima ba.’ ” A shekara ta huɗu ta Yehohiyakim ɗan Yosiya sarkin Yahuda, wannan magana ta zo wa Irmiya daga wurin Ubangiji cewa, “Ka ɗauki littafi ka rubuta dukan maganganun da na yi maka game da Isra’ila, Yahuda da kuma dukan sauran al’ummai daga lokacin da na fara maka magana a mulkin Yosiya har zuwa yanzu. Wataƙila sa’ad da mutanen Yahuda suka ji game da kowace masifar da na shirya in auka musu, kowa ya juya daga muguwar hanyarsa; sa’an nan in gafarta musu muguntarsu da kuma zunubinsu.” Saboda haka Irmiya ya kira Baruk ɗan Neriya, yayinda Irmiya yake fadar dukan waɗannan maganganun da Ubangiji ya faɗa masa, Baruk ya rubuta su a littafin. Sai Irmiya ya ce wa Baruk, “An hana ni, ba zan tafi haikalin Ubangiji ba. Saboda haka ka tafi gidan Ubangiji a ranar azumi ka karanta wa mutane daga littafin maganar Ubangiji da na shibta maka ka rubuta. Ka karanta su ga dukan mutanen Yahuda waɗanda suka zo daga garuruwansu. Wataƙila za su kawo kukansu a gaban Ubangiji, kowanne kuma ya juya daga muguwar hanyarsa, gama fushi da hasalar da Ubangiji ya furta a kan mutanen nan yana da girma.” Sai Baruk ɗan Neriya ya yi dukan abin da annabi Irmiya ya ce ya yi; a haikalin Ubangiji kuwa ya karanta maganar Ubangiji daga littafin A watan tara na shekara ta biyar ta Yehohiyakim ɗan Yosiya sarkin Yahuda, an yi shela a yi azumi a gaban Ubangiji ga dukan mutanen Urushalima da waɗanda suka zo daga garuruwan Yahuda. Daga ɗakin Gemariya ɗan Shafan magatakarda, wanda yake a fili na bisa a mashigin Sabuwar Ƙofar haikali, Baruk ya karanta wa dukan mutane a haikalin Ubangiji maganar Irmiya daga littafin. Sa’ad da Mikahiya ɗan Gemariya, ɗan Shafan, ya ji dukan maganar Ubangiji daga littafin, sai ya sauka zuwa ɗakin magatakarda a fada, inda dukan fadawa suke zaune, Elishama magatakarda, Delahiya ɗan Shemahiya, Elnatan ɗan Akbor, Gemariya ɗan Shafan, Zedekiya ɗan Hananiya, da dukan sauran fadawa. Bayan Mikahiya ya faɗa musu kome da ya ji Baruk ya karanta wa mutane daga littafin, sai dukan fadawan suka aiki Yehudi ɗan Netaniya, ɗan Shelemiya, ɗan Kushi, ya ce wa Baruk, “Ka zo tare da littafin da ka karanta wa mutane.” Saboda haka Baruk ɗan Neriya ya tafi wurinsu tare da littafin a hannunsa. Suka ce masa, “Zauna, ka karanta mana littafin.” Sai Baruk ya karanta musu littafin. Da suka ji dukan maganar, sai suka dubi juna a firgice suka ce wa Baruk, “Dole mu sanar da dukan maganan nan ga sarki.” Sa’an nan suka ce wa Baruk, “Faɗa mana yadda ka yi ka rubuta dukan wannan. Irmiya ne ya yi maka shibtar ta?” Baruk ya amsa ya ce, “I, shi ne ya faɗa mini dukan wannan magana, na kuwa rubuta su a takarda.” Sa’an nan fadawan suka ce wa Baruk, “Kai da Irmiya ku je ku ɓuya. Kada ku bari wani ya san inda kuke.” Bayan da suka ajiye littafin a ɗakin Elishama magatakarda, sai suka tafi wurin sarki a fili suka sanar da shi kome. Sai sarki ya aiki Yehudi ya kawo littafin daga ɗakin Elishama magatakarda ya kuma karanta wa sarki da kuma dukan fadawan da suke tsaye kusa da shi. A watan tara ne sarki kuwa yana zaune a gidansa na rani, wuta kuwa tana ci a kasko a gabansa. Duk sa’ad da Yehudi ya karanta sashi uku ko huɗu na littafin, sai sarkin ya sa wuƙa ya yanke su, ya zuba a wutar da take ci a kasko, da haka ya ƙone dukan littafin. Sai sarki da dukan masu yin masa hidima waɗanda suke jin maganan nan ba su firgita ba, balle su keta rigunansu. Ko da yake Elnatan, Delahiya da Gemariya sun roƙi sarki kada yă ƙone littafin, bai saurare su ba. A maimakon haka, sai sarki ya umarci Yerameyel ɗan sarki, Serahiya ɗan Azriyel da Shelemiya ɗan Abdeyel su kama Baruk marubuci da Irmiya annabi. Amma Ubangiji ya ɓoye su. Bayan sarki ya ƙone littafin da ya ƙunshi maganar da Baruk ya rubuta daga shibtar Irmiya, sai maganar Ubangiji ta zo wa Irmiya cewa, “Ka ɗauki wani littafi ka rubuta a kansa dukan maganar da littafi na farin ya ƙunsa, wanda Yehohiyakim sarkin Yahuda ya ƙone. Ka kuma faɗa wa Yehohiyakim sarkin Yahuda cewa, ‘Ga abin da Ubangiji yana cewa, ka ƙone wancan littafin ka kuma ce, “Don me ka rubuta a cikinsa, cewa lalle sarkin Babilon zai zo ya hallaka wannan ƙasa, zai kashe mutum duk da dabba?” Saboda haka, ga abin da Ubangiji yana cewa game da Yehohiyakim sarkin Yahuda. Ba zai kasance da wani wanda zai zauna a kan gadon sarautar Dawuda ba; za a jefar da gawarsa ta sha zafi da rana da dare kuma ta sha matsanancin sanyi. Zan hukunta shi da kuma ’ya’yansa da masu hidimarsa saboda muguntarsu; zan kawo kowace masifar da na furta a kansu da kuma waɗanda suke zama a Urushalima da na Yahuda, domin sun ƙi su saurara.’ ” Sai Irmiya ta ɗauko wani littafi ya ba wa Baruk ɗan Neriya marubuci, kuma yayinda Irmiya yake shibtawa, Baruk ya rubuta a littafin dukan maganar da take a littafin da Yehohiyakim sarkin Yahuda ya ƙone. Ya kuma ƙara ire-iren maganganun nan a kansu. Nebukadnezzar sarkin Babilon ya naɗa Zedekiya ɗan Yosiya sarkin Yahuda; ya yi mulki a madadin Yehohiyacin ɗan Yehohiyakim. Shi da masu yin masa hidima da mutanen ƙasar ba su kula da maganar da Ubangiji ya yi ta wurin Irmiya annabi ba. Sai sarki Zedekiya ya aiki Yehukal ɗan Shelemiya tare da firist nan Zefaniya ɗan Ma’asehiya da wannan saƙo cewa, “Ina roƙonka ka yi addu’a ga Ubangiji Allahnmu saboda mu.” To, fa, Irmiya ya sami ’yancin kai da kawowa a cikin mutane, gama ba a riga an sa shi a kurkuku ba. Sojojin Fir’auna suka fita daga Masar, sa’ad da Babiloniyawa waɗanda suke ƙawanya wa Urushalima suka ji labari game da su, sai suka janye daga Urushalima. Sai maganar Ubangiji ta zo wa Irmiya annabi cewa, “Ga abin da Ubangiji, Allah na Isra’ila, yana cewa ka faɗa wa sarkin Yahuda, wanda ya aika a neme ni cewa, ‘Sojojin Fir’aunan da suka fito su taimake ka, za su koma ƙasarsu, Masar. Sa’an nan Babiloniyawa za su koma su yaƙi wannan birni su ci ta su kuma ƙone shi.’ “Ga abin da Ubangiji yana cewa, kada ku ruɗe kanku, kuna tsammani, ‘Tabbatacce Babiloniyawa sun bar mu.’ Ba za su bari ba! Ko da a ce za ku ci dukan sojojin Babiloniyawan da suke yaƙi da ku har raunana ne kawai aka bari a tentunansu, za su fito su ƙone wannan birni.” Bayan sojojin Babiloniyawa suka janye daga Urushalima saboda sojojin Fir’auna, sai Irmiya ya bar birnin don yă je yankin Benyamin ya sami rabon mallaka a cikin mutane a can. Amma sa’ad da ya kai Ƙofar Benyamin, sai hafsa mai tsaro, wanda ake kira Iriya ɗan Shelemiya, ɗan Hananiya, ya kama shi ya kuma ce, “Kana gudu daga Babiloniyawa ne!” Sai Irmiya ya ce, “Ba gaskiya ba ce, ba na gudu daga Babiloniyawa.” Amma Iriya bai saurare shi ba; a maimako, ya kama Irmiya ya kawo shi wurin fadawa. Suka yi fushi da Irmiya suka sa aka yi masa dūka aka kuma jefa shi cikin kurkuku a gidan Yonatan magatakarda, gama an mai da gidansa ya zama kurkuku. Aka sa Irmiya a can cikin kurkuku, inda ya kasance kwanaki masu yawa. Sa’an nan Sarki Zedekiya ya aika a kawo shi aka kuma kawo shi fada, inda ya tambaye shi a kaɗaice ya ce, “Akwai wata magana daga Ubangiji?” Irmiya ya amsa ya ce, “I, za a ba da kai ga sarkin Babilon.” Sai Irmiya ya ce wa Sarki Zedekiya, “Wane laifi na yi maka ko fadawanka ko kuwa wannan mutane, da ka sa aka jefa ni cikin kurkuku? Ina annabawanka waɗanda suka yi maka annabci suna cewa, ‘Sarkin Babilon ba zai yaƙe ka ko wannan ƙasa ba’? Amma yanzu, ranka yă daɗe, sarkina, ka saurara. Bari in kawo kukata a gabanka. Kada ka mai da ni gidan Yonatan magatakarda, in ba haka zan mutu a can.” Sarki Zedekiya ya yi umarni a ajiye Irmiya a sansanin matsara a kuma ba shi burodi daga titin masu gashin burodi kowace rana sai duka burodi a birnin ya ƙare. Saboda haka Irmiya ya zauna a sansanin matsara. Shefatiya ɗan Mattan, Gedaliya ɗan Fashhur, Yukal ɗan Shelemiya da Fashhur ɗan Malkiya ya ji abin da Irmiya yana faɗa wa dukan mutane sa’ad da ya ce, “Ga abin da Ubangiji yana cewa, ‘Duk wanda ya zauna a wannan birni zai mutu ta takobi, yunwa ko annoba, amma duk wanda ya je wurin Babiloniyawa zai rayu. Zai tsira da ransa, ya rayu.’ Kuma ga abin da Ubangiji yana cewa, ‘Tabbatacce za a ba da wannan birni ga sojojin sarkin Babilon, wanda zai ci shi.’ ” Sai fadawa suka ce wa sarki, “Ya kamata a kashe wannan mutum. Yana karya zuciyar sojojin da suka ragu a birnin, da zuciyar sauran mutane, ta wurin abubuwan da yake faɗa musu. Wannan mutum ba ya neman jin daɗin zaman wannan sai dai wahala.” “Yana a hannuwanku” Sarki Zedekiya ya amsa. “Sarki ba zai iya yin kome ya hana ku ba.” Saboda haka suka kama Irmiya suka sa a rijiyar da ba ruwa a ciki ta Malkiya, ɗan sarki, wadda take a sansanin matsara. Suka saukar da Irmiya cikin rijiyar da ba ruwa da igiya; babu ruwa a cikinta, sai laka, Irmiya ya nutse cikin laka. Amma Ebed-Melek mutumin Kush, wani hafsa a fada, ya ji cewa sun sa Irmiya a rijiyar da ba ruwa. Yayinda sarki yana zama a Ƙofar Benyamin, Ebed-Melek ya fita daga fadar ya ce masa, “Ranka yă daɗe sarki, waɗannan mutane sun yi mugun abu a duk abin da suka yi wa Irmiya annabi. Sun jefa shi cikin rijiyar da ba ruwa, inda zai mutu da yunwa gama ba sauran wani burodi a birnin.” Sai sarki ya umarce Ebed-Melek mutumin Kush, “Ka ɗauko mutane talatin daga nan ku fid da Irmiya annabi daga rijiyar kafin ya mutu.” Saboda haka Ebed-Melek ya ɗauki mutane tare da shi suka shiga ɗaki a ƙarƙashin baitulmali a cikin fada. Ya ɗauko waɗansu tsofaffin tsummoki da tsofaffi riguna daga can ya kuma zurara su da igiya wa Irmiya a cikin rijiyar. Ebed-Melek mutumin Kush ya ce wa Irmiya, “Ka sa waɗannan tsummoki da tsofaffin rigunan a hammatarka, ya zarga igiya.” Irmiya ya yi haka, suka kuma ja shi sama da igiya suka fid da shi daga rijiyar. Irmiya kuwa ya zauna a sansanin matsara. Sai Sarki Zedekiya ya aika a kawo Irmiya annabi, ya sa aka kawo shi a ƙofa ta uku ta haikalin Ubangiji. Sai sarki ya ce wa Irmiya, “Zan tambaye ka wani abu, kada ka ɓoye mini wani abu.” Irmiya ya ce wa Zedekiya, “In na ba ka amsa, ba za ka kashe ni ba? Ko da na ba ka shawara, ba za ka saurare ni ba.” Amma Sarki Zedekiya ya yi wannan rantsuwa a kaɗaice ga Irmiya cewa, “Muddin Ubangiji yana a raye, wanda ya ba mu numfashi, ba zan kashe ka ko in ba da kai ga waɗanda suke neman ranka ba.” Sa’an nan Irmiya ya ce wa Zedekiya, “Ga abin da Ubangiji Allah Maɗaukaki, Allah na Isra’ila, yana cewa, ‘In ka miƙa wuya ga hafsoshin sarkin Babilon, za a bar ka da rai ba za a kuma ƙone wannan birni ba; da kai da iyalinka za ku rayu. Amma in ba ka miƙa wuya ga hafsoshin sarkin Babilon ba, za a ba da wannan birni ga Babiloniyawa za su kuma cinna mata wuta; kai kanka ba za ka tsira daga hannuwansu ba.’ ” Sarki Zedekiya ya ce wa Irmiya, “Ina jin tsoron Yahudawan da suka tafi wurin Babiloniyawa, gama Babiloniyawa mai yiwuwa su ba da ni gare su su kuma wulaƙanta ni.” Irmiya ya ce, “Ba za su ba da kai ba, ka yi biyayya ga Ubangiji ta wurin yin abin da na faɗa maka. Ta haka zai zama maka da amfani, za ka kuwa rayu. Amma in ka ƙi miƙa wuya, ga abin da Ubangiji ya bayyana mini. Za a fitar da dukan matan da suka ragu a fadan sarkin Yahuda wa hafsoshin sarkin Babilon. Waɗannan mata za su ce maka, “ ‘Sun ruɗe ka suka kuma rinjaye ka, waɗannan abokanka. Ƙafafunka sun nutse a cikin laka; abokanka sun yashe ka.’ “Za a kawo dukan matanka da ’ya’yanka wa Babiloniyawa. Kai kanka ba za ka tsira daga hannuwansu ba amma za su sa sarkin Babilon zai kama ka; za a kuma ƙone wannan birni. ” Sai Zedekiya ya ce wa Irmiya, “Kada ka bar wani ya san wannan zance, in ba haka ba za ka mutu. In fadawa suka ji cewa na yi magana da kai, suka kuma zo wurinka suka ce, ‘Faɗa mana abin da ka faɗa wa sarki da kuma abin da sarki ya faɗa maka; kada ka ɓoye mana, in ba haka za mu kashe ka,’ sai ka ce musu cewa, ‘Na roƙi sarki kada yă mai da ni gidan Yonatan in mutu a can.’ ” Dukan fadawa kuwa suka zo wurin Irmiya suka tambaye shi, ya kuma faɗa musu dukan abin da sarki ya umarce shi ya faɗa. Saboda haka ba su ƙara ce masa kome ba, gama ba wanda ya ji zance da suka yi da sarki. Irmiya kuwa ya zauna a sansanin masu gadi har ranar da aka ci Urushalima da yaƙi. Ga yadda aka ci Urushalima, A shekara ta tara ta Zedekiya sarkin Yahuda, a wata na goma, Nebukadnezzar sarkin Babilon ya fita yaƙi da Urushalima da dukan sojojinsa ya kuma yi mata ƙawanya. A rana ta tara ga watan huɗu a shekara ta goma sha ɗaya ta mulkin Zedekiya, sai aka huda katanga. Sa’an nan dukan fadawan sarkin Babilon suka shiga suka zazzauna a Ƙofar Tsakiya. Wato, Nergal-Sharezer na Samgar-Nebo, Sarsekim wani babban hafsa, Nergal-Sharezer bafade mai girma da dukan sauran fadawan sarkin Babilon. Sa’ad da Zedekiya sarkin Yahuda da dukan sojoji suka gan su, sai suka gudu; suka bar birnin da dare ta hanyar lambun sarki, ta ƙofar da take tsakanin katanga biyu, suka nufi waje Araba. Amma sojojin Babiloniyawa suka bi su, suka ci wa Zedekiya a filayen Yeriko. Suka kama shi suka kai shi wurin Nebukadnezzar a Ribla a ƙasar Hamat, inda aka yanke masa hukunci. A can Ribla sarkin Babilon ya kashe ’ya’yan Zedekiya a idanunsa aka kuma kashe dukan manyan mutanen Yahuda. Sa’an nan ya ƙwaƙule idanun Zedekiya ya kuma buga masa ƙuƙumi, ya kai shi Babilon. Sai Babiloniyawa suka cinna wa fadar da kuma gidajen mutane wuta suka farfasa katangar Urushalima. Nebuzaradan shugaban matsaran sarki ya kwashi mutanen da suka rage a birnin zuwa zaman bauta a Babilon, tare da waɗanda suka riga suka tafi wurinsa, da kuma sauran mutanen. Amma Nebuzaradan shugaban matsaran ya bar waɗansu matalauta a ƙasar Yahuda, su da ba su da kome; a lokacin kuwa ya ba su gonakin inabi da kuma filaye. To, fa, Nebukadnezzar sarkin Babilon ya ba da wannan umarnai game da Irmiya ta wurin Nebuzaradan shugaban matsaran sarki cewa, “Ka ɗauke shi ka lura da shi da kyau, kada ka yi masa wani mugun abu, amma ka yi masa dukan abin da yake so.” Saboda haka Nebuzaradan shugaban matsara, Nebushazban babban hafsa, Nergal-Sharezer bafade mai girma da sauran hafsoshin sarkin Babilon suka aika aka kawo Irmiya daga filin matsar. Suka miƙa shi ga Gedaliya ɗan Ahikam, ɗan Shafan, don yă kai shi gidansa. Saboda haka ya zauna a can a cikin mutanensa. Yayinda aka kulle Irmiya a sansanin matsara, maganar Ubangiji ta zo masa cewa, “Tafi ka faɗa wa Ebed-Melek mutumin Kush, ‘Ga abin da Ubangiji Maɗaukaki, Allah na Isra’ila, yana cewa ina gab da cika maganata a kan wannan birni ta wurin masifa, ba wadata ba. A lokacin za tă cika a idanunka. Amma zan kuɓutar da kai a wannan rana, in ji Ubangiji; ba zan ba da kai ga waɗanda kake tsoronsu ba. Zan cece ka; ba za ka mutu ta wurin takobi ba amma za ka tsira da ranka, domin ka dogara gare ni, in ji Ubangiji.’ ” Sai magana ta zo wa Irmiya daga Ubangiji bayan Nebuzaradan shugaban matsaran sarki ya sake shi a Rama. Ya sami Irmiya a daure da sarƙoƙi a cikin sauran kamammu daga Urushalima da kuma Yahuda waɗanda ake kaiwa zaman bauta a Babilon. Sa’ad da shugaban matsaran ya sami Irmiya sai ya ce masa, “ Ubangiji Allahnka ya sa wannan masifa saboda wannan wuri. Yanzu kuma Ubangiji ya cika shi; ya yi kamar yadda ya faɗa. Dukan wannan ya faru domin kun yi zunubi ga Ubangiji ba ku kuwa yi masa biyayya ba. Amma yau ina ’yantar da kai daga sarƙoƙin da suke a hannuwanka. Zo mu tafi Babilon, in kana so, zan kuwa lura da kai; amma in ba ka so, kada ka zo. Ga shi, dukan ƙasar tana a gabanka; ka tafi duk inda ka so.” Amma, kafin Irmiya yă juya yă tafi, Nebuzaradan ya ƙara da cewa, “Ka koma wurin Gedaliya ɗan Ahikam, ɗan Shafan, wanda sarkin Babilon ya naɗa a kan garuruwan Yahuda, ka zauna da shi a cikin mutane, ko kuwa ka tafi duk inda ka ga dama.” Sa’an nan shugaban ya ba shi abinci da kuma kyauta sai ya bar shi ya tafi. Saboda haka Irmiya ya tafi wurin Gedaliya ɗan Ahikam, a Mizfa ya zauna tare da shi a cikin mutanen da aka bari a ƙasar. Sa’ad da dukan shugabannin hafsoshin tare da mutanen da suke a karkara suka ji cewa sarkin Babilon ya naɗa Gedaliya ɗan Ahikam gwamna a kan ƙasar ya kuma sa shi ya lura da maza, mata da ’ya’yan da suke mafi talauci a ƙasar da waɗanda ba a kwashe zuwa zaman bauta a Babilon ba, sai suka zo wurin Gedaliya a Mizfa, Ishmayel ɗan Netaniya, Yohanan da Yonatan ’ya’yan Kareya, da Serahiya ɗan Tanhumet maza, ’ya’yan Efai maza, mutumin Netofa, da Yezaniya ɗan mutumin Ma’aka da mutanensu. Gedaliya ɗan Ahikam, ɗan Shafan, ya yi rantsuwa don yă tabbatar musu da mutanensu. Ya ce, “Kada ku ji tsoron bauta wa Babiloniyawa. Ku zauna a ƙasar ku bauta wa sarkin Babilon, zai kuma yi muku amfani. Ni kaina zan zauna a Mizfa in zama wakilinku a gaban Babiloniyawa waɗanda za su zo wurinmu, amma ku girbe ruwan inabi, ’ya’yan itatuwa na kaka, da mai, ku zuba su a tulunan ajiyarku, ku kuma zauna a garuruwan da kuka ci.” Sa’ad da dukan Yahudawan da suke a Mowab, Ammon, Edom da sauran ƙasashe suka ji cewa sarkin Babilon ya bar raguwa a Yahuda ya kuma naɗa Gedaliya ɗan Ahikam, ɗan Shafan gwamna a kansu, sai suka dawo ƙasar Yahuda, wurin Gedaliya a Mizfa, daga dukan ƙasashen da suke a warwatse. Suka girbe ruwan inabi a yalwace da ’ya’yan itatuwan kaka. Yohanan ɗan Kareya da dukan manyan sojoji da suke a karkara suka zo wurin Gedaliya a Mizfa suka ce masa, “Ba ka san cewa Ba’alis sarkin Ammonawa ya aiki Ishmayel ɗan Netaniya ya ɗauke ranka ba?” Amma Gedaliya ɗan Ahikam bai gaskata su ba. Sai Yohanan ɗan Kareya ya yi wa Gedaliya a Mizfa magana a asirce ya ce, “Bari in tafi in kashe Ishmayel ɗan Netaniya, ba kuwa wanda zai sani. Me zai sa ya ɗauke ranka ya watsar da dukan Yahudawan da suka taru kewaye da kai har waɗanda suka ragu na Yahuda su hallaka?” Amma Gedaliya ɗan Ahikam ya ce wa Yohanan ɗan Kareya, “Kada ka yi irin wannan abu! Abin da kake faɗa game da Ishmayel ba gaskiya ba ne.” A wata na goma sha bakwai sai Ishmayel ɗan Netaniya, ɗan Elishama, wanda yake mai jinin sarauta yake kuma ɗaya daga cikin hafsoshin sarki, ya zo tare da mutum goma wurin Gedaliya ɗan Ahikam a Mizfa. Yayinda suke ci tare a can, sai Ishmayel ɗan Netaniya da mutum goma waɗanda suke tare da shi suka kashe Gedaliya ɗan Ahikam, ɗan Shafan, da takobi, suka kashe wannan da sarkin Babilon ya naɗa a matsayin gwamna a kan ƙasar. Ishmayel ya kuma kashe dukan Yahudawan da suke tare da Gedaliya a Mizfa, haka ma ya yi da sojojin Babiloniyawan da suke can. Kashegari bayan an kashe Gedaliya, kafin wani ya san abin da ya faru, sai ga mutane tamanin daga Shekem, Shilo da Samariya suka zo da gemunsu a aske, da tufafinsu a kece, da jikunansu a tsage, suka kawo hadayun gari da turare tare da su a gidan Ubangiji. Ishmayel ɗan Netaniya ya fito daga Mizfa don yă sadu da su. Sa’ad da ya sadu da su, sai ya ce, “Ku zo wurin Gedaliya ɗan Ahikam.” Da suka shiga cikin birni, sai Ishmayel ɗan Netaniya da mutanen da suke tare da shi suka karkashe su suka zubar a rijiya. Amma goma daga cikinsu suka ce wa Ishmayel, “Kada ka kashe mu, muna da alkama da sha’ir, mai da kuma zuma, a ɓoye a gona.” Saboda haka ka bar mu kada ka kashe mu tare da sauran. To, rijiyar da ya zubar da gawawwakin mutanen da ya kashe tare da ta Gedaliya ita ce wadda Sarki Asa ya haƙa a matsayin kāriya saboda Ba’asha sarkin Isra’ila. Ishmayel ɗan Netaniya ya cika ta da gawawwaki. Ishmayel ya mai da dukan sauran mutanen da suke Mizfa bayi ’ya’yan sarki mata tare da dukan sauran da aka bari a can, waɗanda Nebuzaradan shugaban matsaran sarki ya bari a hannun Gedaliya ɗan Ahikam. Ishmayel ɗan Netaniya ya kwashe su ganima, ya tashi don yă haye zuwa wurin Ammonawa. Sa’ad da Yohanan ɗan Kareya da dukan shugabannin sojojin da suke tare da shi suka ji dukan laifofin da Ishmayel ɗan Netaniya ya aikata, sai suka kwashe dukan mutanensu suka tafi don su yaƙi Ishmayel ɗan Netaniya. Suka iske shi kusa da babban tafki a Gibeyon. Sa’ad da dukan mutanen da suke tare da Ishmayel suka ga Yohanan ɗan Kareya da shugabannin sojojin da suke tare da shi, sai suka yi farin ciki. Dukan mutanen da Ishmayel ya kame a Mizfa suka juya, suka tafi wurin Yohanan ɗan Kareya. Amma Ishmayel ɗan Netaniya da mutanensa takwas suka tsere daga Yohanan suka gudu zuwa wurin Ammonawa. Sai Yohanan ɗan Kareya da dukan shugabannin sojojin da suke tare da shi suka bi da dukan waɗanda suka tsira daga Mizfa waɗanda ya karɓe daga Ishmayel ɗan Netaniya bayan ya kashe Gedaliya ɗan Ahikam, wato, sojoji, mata, yara da fadawan da ya kawo daga Gibeyon Sai suka ci gaba, suka dakata a Gerut Kimham kusa da Betlehem a kan hanyarsu zuwa Masar don su kuɓuce wa Babiloniyawa. Sun ji tsoronsu domin Ishmayel ɗan Netaniya ya kashe Gedaliya ɗan Ahikam, wanda sarkin Babilon ya naɗa gwamna a kan ƙasar. Sa’an nan dukan shugabannin sojoji, haɗe da Yohanan ɗan Kareya da Yezaniya ɗan Hoshahiya, da dukan mutane daga ƙarami zuwa babba, suka zo wurin Irmiya annabi suka ce masa, “Muna roƙonka ka ji kukanmu ka kuma yi addu’a ga Ubangiji Allahnka saboda dukan wannan raguwar mutane. Gama kamar yadda kake gani yanzu, ko da yake dā muna da yawa, yanzu ɗan kaɗan muka rage. Ka yi addu’a cewa Ubangiji Allahnka zai faɗa mana inda za mu tafi da kuma abin da za mu yi.” Sai Irmiya ya amsa ya ce, “Na ji ku, tabbatacce zan yi addu’a ga Ubangiji Allahnku yadda kuka roƙa; zan faɗa muku duk abin da Ubangiji ya faɗa ba kuwa zan ɓoye muku kome ba.” Sa’an nan suka ce wa Irmiya, “ Ubangiji ya zama shaida na gaskiya da kuma aminci a kanmu in ba mu yi bisa da duk abin da Ubangiji Allahnka ya aike ka ka faɗa mana ba. Ko ya gamshe mu ko bai gamshe mu ba, za mu yi biyayya da Ubangiji Allahnmu, ga wanda muke aikan ka, saboda ya zama mana da amfani, gama za mu yi biyayya da Ubangiji Allahnmu.” Bayan kwana goma sai maganar Ubangiji ta zo wa Irmiya. Saboda haka ya kira Yohanan ɗan Kareya da dukan shugabannin sojoji waɗanda suke tare da shi da dukan jama’a daga ƙarami zuwa babba. Ya ce musu, “Ga abin da Ubangiji, Allah na Isra’ila, wanda kuka aike ni gare shi don in gabatar da kukanku, yana cewa, ‘In kuka zauna a wannan ƙasa, zan gina ku ba zan kuwa rushe ku ba; zan dasa ku ba kuwa zan tumɓuke ku ba, gama ina baƙin ciki a kan masifar da na aukar a kanku. Kada ku ji tsoron sarkin Babilon, wanda kuke tsoro a yanzu. Kada ku ji tsoronsa, in ji Ubangiji, gama ina tare da ku zan kuma cece ku daga hannuwansa. Zan nuna muku jinƙai don yă nuna muku jinƙai ya kuma maido da ku ƙasarku.’ “Amma fa, in kuka ce, ‘Ba za mu zauna a wannan ƙasa ba,’ ta haka kuka kuma nuna rashin biyayya ga Ubangiji Allahnku, in kuma kuka ce, ‘A’a, za mu tafi mu zauna a Masar, inda ba za mu ga yaƙi ko mu ji ƙarar ƙaho ko mu ji yunwa ba,’ to, ku ji maganar Ubangiji, ya raguwar Yahuda. Ga abin da Ubangiji Maɗaukaki, Allah na Isra’ila, yana cewa, ‘In kun ƙudura ku tafi Masar kuka kuma tafi kun zauna a can, takobin da kuke tsoro zai same ku a can, kuma yunwar da kuke tsoro za tă bi ku zuwa Masar, a can kuwa za ku mutu. Tabbatacce, duk waɗanda suka ƙudura suka tafi Masar su zauna a can za su mutu ta wurin takobi, yunwa da annoba; ba ko ɗayansu zai tsira ko ya kuɓuta wa masifar da zan aukar a kansu.’ Ga abin da Ubangiji Maɗaukaki, Allah na Isra’ila, yana cewa, ‘Kamar yadda na kwararo fushina da hasalata a kan mazaunan Urushalima, haka kuma zan kwararo fushina a kanku sa’ad da kuka tafi Masar. Za ku zama abin la’ana da abin tsoro, abin ƙyama da abin ba’a; ba za ku ƙara ganin wannan wuri ba.’ “Ya ku raguwar Yahuda, Ubangiji ya ce muku, ‘Kada ku je Masar.’ Ku tabbatar da wannan. Na gargaɗe ku yau cewa in kun yi kuskure sa’ad da kuka aike ni wurin Ubangiji Allahnku kuka kuma ce, ‘Yi mana addu’a ga Ubangiji Allahnmu; ka faɗa mana duk abin da ya faɗa za mu kuwa aikata.’ Na faɗa muku yau, amma har yanzu ba ku yi biyayya ga Ubangiji Allahnku cikin dukan abin da ya aiko ni in faɗa muku ba. Saboda haka yanzu, ku tabbatar da wannan. Za ku mutu ta wurin takobi, yunwa da annoba a wurin da kuke so ku tafi ku zauna.” Sa’ad da Irmiya ya gama faɗa wa mutane dukan maganar Ubangiji Allahnsu, duk abin da Ubangiji ya aike shi ya faɗa musu, Azariya ɗan Hoshahiya da Yohanan ɗan Kareya da dukan masu ɗaga kai suka ce wa Irmiya, “Kana ƙarya ne! Ubangiji Allahnmu bai aike ka ka ce, ‘Kada ku tafi Masar don ku zauna a can.’ Amma Baruk ɗan Neriya yana zuga ka a kanmu don ka ba da mu ga Babiloniyawa, don su kashe mu ko su kai mu zaman bauta a Babilon.” Saboda haka Yohanan ɗan Kareya da dukan shugabannin sojoji da dukan mutane suka yi rashin biyayya ga umarnin Ubangiji da su zauna a ƙasar Yahuda. A maimako, Yohanan ɗan Kareya da dukan shugabannin sojoji suka kwashe raguwar Yahuda waɗanda suka dawo su zauna a ƙasar Yahuda daga dukan al’umman inda aka kora su. Suka kuma kwashe dukan maza, mata da yara da ’ya’yan sarki mata waɗanda Nebuzaradan shugaban matsaran sarki ya bari tare da Gedaliya ɗan Ahikam, ɗan Shafan, da Irmiya annabi da kuma Baruk ɗan Neriya. Saboda haka suka shiga Masar cikin rashin biyayya ga Ubangiji suka tafi har can Tafanes. A Tafanes maganar Ubangiji ta zo wa Irmiya cewa, “Yayinda Yahudawa suna kallo, ka ɗauki waɗansu manyan duwatsu tare da kai ka kuma binne su cikin yumɓu a tubalin dakalin ƙofar shiga fadar Fir’auna a Tafanes. Sa’an nan ka faɗa musu cewa, ‘Ga abin da Ubangiji Maɗaukaki, Allah na Isra’ila, yana cewa, zan aika wa bawana Nebukadnezzar sarkin Babilon, zan kuma sa kursiyinsa a kan waɗannan duwatsun da na binne a nan; zai fadada bukkar mulkinsa a bisansu. Zai zo ya yaƙi Masar, ya kawo mutuwa ga waɗanda aka ƙaddara musu mutuwa, zaman bauta ga waɗanda aka ƙaddara musu zaman bauta, da kuma takobi ga waɗanda aka ƙaddara su mutu ta takobi. Zai sa wuta wa haikalan allolin Masar; zai ƙone haikalansu yă kuma kwashe allolinsu bayi. Kamar yadda makiyayi yakan yafa mayafinsa kewaye da shi, haka zai yafa Masar kewaye da kansa ya kuma tashi a wurin babu abin da ya same shi. A can cikin haikalin rana a Masar zai rushe al’amudan duwatsu yă kuma ƙone haikalan allolin Masar.’ ” Wannan maganata zo wa Irmiya game da dukan Yahudawa masu zama a Masar ta Ƙasa, a Migdol, Tafanes da Memfis, da kuma a Masar ta Bisa. “Ga abin da Ubangiji Maɗaukaki, Allah na Isra’ila yana cewa kun ga masifa mai girmar da na kawo a kan Urushalima da kuma a kan dukan garuruwan Yahuda. A yau sun zama hamada da kuma kango saboda muguntar da suka aikata. Sun tsokane ni na yi fushi ta wurin ƙone turare da kuma ta wurin bauta wa waɗansu allolin da su ko ku ko kakanninku ba su taɓa sani ba. Sau da sau na aiki bayina annabawa, waɗanda suka ce, ‘Kada ku yi wannan abin ƙyama da na ƙi!’ Amma ba su saurara ko su kasa kunne ba; ba su juye daga muguntarsu ko su daina ƙone turare wa waɗansu alloli ba. Saboda haka, fushina mai ƙuna ya fāɗo a kan garuruwan Yahuda da kuma titunan Urushalima na kuma mai da su kufai da suke a yau. “To, ga abin da Ubangiji Allah Maɗaukaki, Allah na Isra’ila, yana cewa don me kuka kawo irin masifa mai girma haka a kanku ta wurin warewa daga Yahuda maza da mata, yara da jarirai, kun kuma bar kanku babu raguwa? Me ya sa kuka tsokane ni in yi fushi saboda abin da hannuwanku suka yi, kuna ƙone turare wa waɗansu alloli a Masar, inda kuka zo don ku zauna? Za ku hallakar da kanku ku kuma mai da kanku abin la’ana da abin zargi da abin ba’a a cikin dukan al’umman duniya. Kun manta mugayen ayyukan kakanninku, da na sarakuna da sarauniyoyin Yahuda da mugayen ayyukanku, da na matanku a cikin Yahuda da kan titunan Urushalima? Har yă zuwa yau ba su ƙasƙantar da kansu ko su nuna bangirma, ko su kiyaye dokata da ƙa’idodin da na sa a gabanku da kakanninku ba. “Saboda haka ga abin da Ubangiji Maɗaukaki, Allah na Isra’ila, yana cewa na ƙudura in aukar muku da masifa in kuma hallaka dukan Yahuda. Zan ɗauke raguwar Yahuda waɗanda suka ƙudurta su je Masar su zauna a can. Duk za su hallaka a Masar; za su mutu ta wurin takobi ko su mutu da yunwa. Daga ƙarami zuwa babba, za su mutu ta wurin takobi ko yunwa. Za su zama abin zarge da abin tsoro, abin la’ana da abin ba’a. Zan hukunta waɗanda suke zama a Masar da takobi, yunwa da annoba, yadda na hukunta Urushalima. Babu wani daga raguwar Yahuda wanda ya tafi Masar da zai kuɓuta ko ya tsira har ya komo zuwa ƙasar Yahuda, wadda za su yi marmari su komo su zauna; babu wani da zai komo sai dai ’yan gudun hijira.” Sai dukan mazan da suka san cewa matansu suna ƙone turare wa waɗansu alloli, tare da dukan matan da suke a nan babban taro, da kuma dukan mutanen da suke zama a Masar ta Ƙasa da ta Bisa, suka ce wa Irmiya, “Ba za mu saurari saƙon da ka yi mana magana a sunan Ubangiji ba! Lalle za mu aikata duk abin da muka ce za mu yi. Za mu ƙone turare ga Sarauniyar Sama za mu kuma miƙa hadayun sha gare ta kamar dai yadda mu da kakanninmu, sarakunanmu da fadawanmu muka yi a garuruwan Yahuda da kuma kan titunan Urushalima. A lokacin muna da abinci a yalwace muna kuma da arziki ba mu kuma da wata damuwa. Amma tun da muka daina ƙone turare ga Sarauniyar Sama da kuma miƙa mata hadayun sha, muka rasa kome muna ta mutuwa ta wurin takobi da yunwa.” Matan suka ƙara da cewa, “Sa’ad da muka ƙone turare ga Sarauniyar Sama muka kuma miƙa mata hadayun sha, mazanmu ba su san muna yin waina kamar siffarta muna kuma miƙa mata hadayun sha ba?” Sai Irmiya ya ce wa dukan mutanen, maza da mata, waɗanda suke ba shi amsa, “ Ubangiji bai tuna ya kuma yi tunani game da turaren da aka ƙone a garuruwan Yahuda da kan titunan Urushalima wanda ku da kakanninku, sarakunanku da fadawanku da mutanen ƙasar ba ne? Sa’ad da Ubangiji bai iya jurewa da mugayen ayyukanku da kuma abubuwa banƙyama da kuka aikata ba, sai ƙasarku ta zama abin la’ana da kufai babu mazauna yadda yake a yau. Domin kun ƙone turare kuka kuma yi wa Ubangiji zunubi ba ku kuma yi masa biyayya ko ku kiyaye dokarsa ko ƙa’idodinsa ko farillansa ba, wannan masifa ta aukar muku, yadda yanzu kuka gani.” Sai Irmiya ya ce wa dukan mutane, har da mata, “Ku saurari maganar Ubangiji, dukanku mutanen Yahuda a Masar. Ga abin da Ubangiji Maɗaukaki, Allah na Isra’ila, yana cewa ku da matanku kun nuna ta wurin ayyukanku abin da kuka yi alkawari sa’ad da kuka ce, ‘Lalle za mu yi abin da muka yi alkawari na ƙone turare da kuma miƙa hadayun sha ga Sarauniyar Sama.’ “To, sai ku ci gaba, ku aikata abin da kuka yi alkawari! Ku cika alkawarinku! Amma ku ji maganar Ubangiji, dukan Yahudawan da suke zama a Masar, ‘Na rantse da sunana,’ in ji Ubangiji, ‘cewa babu wani daga Yahuda wanda yake zama a ko’ina a Masar zai ƙara kira bisa sunana ko ya rantse ya ce, “Muddin Ubangiji Mai Iko Duka yana raye.” Gama ina lura da su don lahani, ba alheri ba; mutanen Yahuda da suke a Masar za su hallaka ta wurin takobi da yunwa sai dukansu sun hallaka. Waɗanda suka kuɓuta wa takobi suka komo zuwa ƙasar Yahuda daga Masar za su zama kima kawai. Sa’an nan dukan raguwar Yahuda waɗanda suka zo don su yi zama a Masar za su san maganar wane ne za tă tabbata, tawa ko tasu. “ ‘Wannan zai zama alama a gare ku cewa zan hukunta ku a wannan wuri,’ in ji Ubangiji, ‘saboda ku san cewa barazanata ta lahani a kanku tabbatacce za tă cika.’ Ga abin da Ubangiji yana cewa, ‘Zan bayar da Fir’auna Hofra sarkin Masar ga abokan gābansa waɗanda suke neman ransa, kamar yadda na ba da Zedekiya sarkin Yahuda ga Nebukadnezzar sarkin Babilon, abokin gāban da ya nemi ransa.’ ” Ga abin da Irmiya annabi ya faɗa wa Baruk ɗan Neriya a shekara ta huɗu ta Yehohiyakim ɗan Yosiya sarkin Yahuda, bayan Baruk ya rubuta maganar da Irmiya ya shibta masa a kan littafi cewa, “Ga abin da Ubangiji, Allah na Isra’ila, yana ce maka, Baruk. Ka ce, ‘Kaitona! Ubangiji ya ƙara baƙin ciki da wahalata; na gaji da nishe-nishe ban kuma huta ba.’ ” Ubangiji ya ce, “Ka faɗa masa wannan, ‘Ga abin da Ubangiji yana cewa, zan rushe abin da na gina in kuma tumɓuke abin da na dasa, a duk fāɗin ƙasar. Ya kamata ka nemi manyan abubuwa wa kanka? Kada ka neme su. Gama zan aukar da masifa a kan dukan mutane, in ji Ubangiji, amma duk inda ka tafi zan bar ka ka kuɓutar da ranka.’ ” Ga maganar Ubangiji da ta zo wa Irmiya annabi game da al’ummai. Game da Masar. Ga saƙo game da sojojin Fir’auna Neko sarkin Masar, wanda Nebukadnezzar sarkin Babilon ya ci da yaƙi a Karkemish a Kogin Yuferites a shekara ta huɗu ta Yehohiyakim ɗan Yosiya sarkin Yahuda. “Ku shirya garkuwoyinku, manya da ƙanana, ku kuma fito don yaƙi! Ku shirya dawakai, ku sa musu sirdi! Ku tsaya a wurarenku saye da hulunan kwano a kai! Ku wasa māsunku, ku yafa kayan yaƙinku! Me nake gani? Sun tsorata, suna ja da baya, an ci jarumawansu. Suna gudu da sauri ba waiwayawa, akwai razana a kowane gefe,” in ji Ubangiji. “Masu saurin gudu ba sa iya gudu haka ma masu ƙarfi ba sa iya kuɓuta. A arewa ta Kogin Yuferites sun yi tuntuɓe sun fāɗi. “Wane ne wannan mai tashi kamar Nilu, kamar koguna masu tafasar ruwaye? Masar tana tashi kamar Nilu, kamar koguna masu tafasa. Tana cewa, ‘Zan tashi in rufe duniya; zan hallakar da birane da kuma mutanensu.’ Ku yi sukuwar hauka, ya dawakai! Ku tashi a guje, ya mahayan kekunan yaƙi! Ku yi ta fitowa, ya jarumawa, mutanen Kush da kuma Ludim masu riƙon garkuwoyi, mutanen Lidiya, masu iya jan baka. Amma wannan rana ta Ubangiji, Ubangiji Maɗaukaki ranar ɗaukar fansa, gama ɗaukar fansa a kan maƙiyansa. Takobi zai yi ta ci sai ya gamsu, sai ya kashe ƙishirwansa da jini. Gama Ubangiji, Ubangiji Maɗaukaki, zai miƙa hadaya a ƙasar arewa kusa da Kogin Yuferites. “Ki haura Gileyad ki samo magani, Ya Budurwa ’Yar Masar. Amma kin riɓanya magani a banza; ba magani dominki. Al’ummai za su ji game da kunyar da kika sha; kukanki zai cika duniya. Jarumi zai yi tuntuɓe a kan wani; dukansu biyu za su fāɗi tare.” Ga saƙon da Ubangiji ya yi wa Irmiya annabi game da zuwan Nebukadnezzar sarkin Babilon don yă yaƙi Masar. “Ka yi shelar wannan a Masar, ka kuma furta shi a Migdol; ka yi shelarsa kuma a Memfis da Tafanes. ‘Ku ɗauki matsayinku ku kuma shirya, gama takobi na cin waɗanda suke kewaye da ku.’ Me zai sa a wulaƙanta jarumawanka haka? Ba za su iya tsayawa ba, gama Ubangiji zai ture su ƙasa. Za su yi ta tuntuɓe; za su fāɗi akan juna. Za su ce, ‘Mu tashi, mu koma zuwa wurin mutanenmu da kuma ƙasashenmu, daga takobin masu danniya.’ A can za su tā da murya su ce, ‘Fir’auna sarkin Masar mai yawan surutu ne kawai; ya bar zarafi ya wuce masa.’ “Muddin ina raye,” in ji Sarki, wanda sunansa ne Ubangiji Maɗaukaki, “wani zai ɓullo wanda yake kamar Tabor a cikin duwatsu, kamar Karmel kusa da teku. Ku tattara kayanku don shirin zuwa zaman bauta, ku da kuke zama a Masar, gama Memfis za tă zama kufai ta zama kango, babu mazauna. “Masar kyakkyawar karsana ce, amma bobuwa tana zuwa a kanta daga arewa. Sojojin da ta yi hayarsu a cikinta suna kamar ’yan maruƙa masu kitse. Su ma za su juya su kuma gudu gaba ɗaya, ba za su iya tsayawa ba, gama ranar masifa tana zuwa a kansu, lokacin da za su sha hukunci. Masar za tă yi huci kamar macijin da yake gudu yayinda abokin gāba yana matsowa da ƙarfi; za su fāɗo mata gatura kamar mutanen da suke saran itatuwa. Za su sari kurminta,” in ji Ubangiji, “ko da yake yana maƙare da itatuwa. Sun fi fāra yawa, ba su ƙidayuwa. Za a kunyatar da Diyar Masar, da aka bashe ga mutanen arewa.” Ubangiji Maɗaukaki, Allah na Isra’ila, yana cewa, “Ina gab da kawo hukunci a kan allahn Amon na Tebes, a kan Fir’auna, a kan Masar da allolinta da sarakunanta, da kuma a kan waɗanda suka dogara ga Fir’auna. Zan ba da su ga waɗanda suke neman ransu, ga Nebukadnezzar sarkin Babilon da fadawansa. Amma daga baya, Masar za tă kasance da mazauna kamar dā,” in ji Ubangiji. “Kada ka ji tsoro, ya Yaƙub bawana; kada ka karai, ya Isra’ila. Tabbatacce zan cece ka daga wuri mai nisa, zuriyarka daga ƙasar bautarsu. Yaƙub zai sāke kasance cikin salama, rai kwance, babu kuma wanda zai sa ya ji tsoro. Kada ka ji tsoro, ya Yaƙub bawana, gama ina tare da kai,” in ji Ubangiji. “Ko da na hallaka dukan al’ummai sarai inda na kora ka, ba zan hallaka ka sarai ba. Zan hore ka amma da adalci kaɗai; ba zan bar ka ba hukunci ba.” Ga maganar Ubangiji da ta zo wa Irmiya annabi game da Filistiyawa kafin Fir’auna ya yaƙi Gaza. Ga abin da Ubangiji yana cewa, “Dubi yadda ruwaye suna tasowa a arewa; za su zama kogi mai rigyawa. Za su malala a ƙasa da kuma a kan kome da yake cikinta, garuruwa da waɗanda suke zaune a cikinsu. Mutane za su yi kuka; dukan mazaunan ƙasar za su yi kururuwa da jin motsin takawar kofatan dawakai, da jin surutun kekunan yaƙin abokin gāba da motsin ƙafafunsu. Ubanni ba za su juye don su taimaki ’ya’yansu ba; hannuwansu za su yi laƙwas. Gama rana ta zo da za a hallaka Filistiyawa a kuma datse dukan waɗanda suka ragu waɗanda za su iya taimakon Taya da Sidon. Ubangiji yana gab da hallaka Filistiyawa, raguwa daga bakin tekun Kaftor. Gaza za tă aske kanta cikin baƙin ciki; Ashkelon zai yi shiru. Ya raguwar da suke zama a fili, har yaushe za ku tsattsage kanku? “Za ku yi kuka kuna cewa, ‘Wayyo, takobin Ubangiji sai yaushe za ka huta? Ka koma kubenka; ka huta, ka yi shiru.’ Amma ta yaya zai huta sa’ad da Ubangiji ya umarta, sa’ad da ya umarta shi don yă faɗa wa Ashkelon da kuma bakin teku?” Game da Mowab. Ga abin da Ubangiji Maɗaukaki, Allah na Isra’ila, yana cewa, “Kaito ga Nebo, gama za tă lalace. Kiriyatayim za su kunyata a kuma kame ta; katagar za tă sha kunya ta kuma wargaje. Ba za a ƙara yabi Mowab ba; a Heshbon mutane za su shirya mata maƙarƙashiya. ‘Zo, mu tafi mu kawo ƙarshe ga wannan al’umma.’ Ke kuma, ya Madmen za ki yi shiru; takobi zai fafare ki. Saurari kuka daga Horonayim, kukan risɓewa mai girma da hallaka. Za a karye Mowab; ƙanananta za su yi kuka. Sun haura hanyar zuwa Luhit, suna kuka mai zafi yayinda suke tafiya; a hanyar da ta gangara zuwa Horonayim suna kuka a kan hallakar da aka ji. Ku gudu! Ku gudu don tserar da ranku; ku zama kamar kurmi a hamada. Da yake kun dogara ga ayyukanku da arzikinku, ku ma za a kwashe ku bayi, Kemosh zai tafi bauta, tare da firistocinsa da fadawansa. Mai hallakarwa zai aukar wa kowane gari, kuma ba wani garin da zai kuɓuta. Kwari zai lalace tudu kuma ya hallaka, domin Ubangiji ya faɗa. Ku sa gishiri a kan Mowab, gama za tă zama kango; garuruwanta za su zama kufai, ba mazauna a cikinsu. “La’ananne ne shi wanda yake sake a yin aikin Ubangiji! La’ananne ne wanda ya janye takobinsa daga zub da jini! “Mowab ta kasance cikin kwanciyar rai tun ƙuruciyarta, kamar ruwan inabin da aka bari lis, ba a juya daga tulu zuwa wani tulu ba ba tă tafi bauta ba. Saboda haka tana da ɗanɗanonta, kuma ƙanshinta bai canja ba. Kwanaki suna zuwa,” in ji Ubangiji, “sa’ad da zan aika da mutanen da za su tuntsurar da tuluna, su kuma zubar da ita waje. Za su bar tulunan ba kome a ciki su kuma farfashe tulunanta. Sa’an nan Mowab za tă ji kunyar Kemosh, yadda gidan Isra’ila ya ji kunya sa’ad da suka dogara ga Betel. “Yaya za ku ce, ‘Mu jarumawa ne, mutane masu ƙarfi a yaƙi?’ Mowab za tă hallaka a kuma kai wa garuruwanta hari; samarinta kyawawa za su gangara cikin mayanka,” in ji Sarki, wanda sunansa Ubangiji Maɗaukaki ne. “Fāɗuwar Mowab ta yi kusa; bala’inta zai auku nan da nan. Yi kuka saboda ita, dukanku mazaunan kewayenta, duk waɗanda suka san shahararta; ku ce, ‘Dubi yadda sandan sarauta mai iko ya karye, dubi yadda sanda mai daraja ya karye!’ “Sauko daga darajarku ku zauna a busasshiyar ƙasa, Ya mazaunan Diyar Dibon, gama shi mai hallaka Mowab zai haura a kanku zai kuma lalace biranenku masu kagarai. Ku tsaya a bakin hanya ku duba, ku da kuke zama a Arower. Ku tambayi mutumin da yake gudu da macen da take tserewa, tambaye su, ‘Me ya faru?’ An kunyata Mowab, gama ta wargaje. Ku yi kuka ku kuma tā da murya! Ku yi shela kusa da Arnon cewa an hallaka Mowab. Hukunci ya zo wa tudu, zuwa Holon, Yahza da Mefa’at, zuwa Dibon, Nebo da Bet-Dibilatayim, zuwa Kiriyatayim, Bet-Gamul da Bet-Meyon, zuwa Keriyot da Bozra zuwa dukan garuruwan Mowab, nesa da kusa. An karye ƙahon Mowab; an karye hannunta,” in ji Ubangiji. “Ku bugar da ita domin ta tayar wa Ubangiji. Bari Mowab tă yi ta birgima a cikin amanta; bari tă zama abin dariya. Isra’ila ma bai zama abin dariya a gare ki ba? Ba a kama shi cikin ɓarayi, har kaɗa kai na ba’a kike yi a duka sa’ad da kike magana game da shi? Ku bar garuruwanku ku zauna a cikin duwatsu, ku da kuke zama a Mowab. Ku zama kamar kurciyar da take sheƙarta a bakin kogo. “Mun ji labarin girman kan Mowab mun ji alfarma girmankanta da kumburinta girmankanta da fariyarta da renin zuciyarta. Na san alfarmanta amma a banza ne,” in ji Ubangiji, “kuma taƙamarta ba ya cimma kome. Saboda haka zan yi kuka a kan Mowab gama dukan Mowab zan yi kuka, Zan yi gurnani don mutanen Kir Hareset. Zan yi kuka saboda kai, yadda Yazer ya yi kuka Ya kuringar Sibma. Rassanki sun kai har teku; sun kai har tekun Yazer. Mai hallakarwa ya fāɗo a kan ’ya’yan itatuwanku da kuma inabinku da suka nuna. Farin ciki da murna su ɓace daga lambunan itatuwa da kuma gonakin Mowab. Na dakatar da malalar ruwan inabi daga wurin matsi; ba wanda zai matse su da ihun farin ciki. Ko da yake akwai sowa sowar ba ta farin ciki ba ce. “Muryar kukansu na tashi daga Heshbon zuwa Eleyale da Yahaz, daga Zowar har zuwa Horonayim da Eglat Shelishiya, gama har ruwan Nimrim ma sun bushe. A Mowab zan kawo ƙarshen waɗanda suke miƙa hadayu a masujadan kan tudu suna kuma ƙone turare ga allolinsu,” in ji Ubangiji. “Saboda haka zuciyata na makoki don Mowab kamar busa; tana makoki kamar busa saboda mutanen Kir Hareset. Arzikin da suka samu ta ƙare. An aske kowane kai aka kuma yanke kowane gemu aka kuma sa wa kowane kwankwaso rigar makoki. A kan dukan rufi a Mowab da kuma a dandalin jama’a babu wani abu sai kuka gama na karye Mowab kamar tulun da babu mai so,” in ji Ubangiji. “Duba yadda aka ragargazar ta ita! Duba yadda suke kuka! Duba yadda Mowab ta juya bayanta da kunya! Mowab ta zama abin ba’a abin tsoro ga dukan waɗanda suke kewaye da ita.” Ga abin da Ubangiji yana cewa, “Ga shi! Gaggafa tana firiya zuwa ƙasa, tana shimfiɗa fikafikanta a kan Mowab. Za a ci Keriyot a kuma kame kagarai. A wannan rana zukatan jarumawan Mowab za su zama kamar zuciyar macen da take naƙuda. Za a hallakar da Mowab a matsayin al’umma domin ta tayar wa Ubangiji. Razana da rami da tarko suna jiranku, Ya mutanen Mowab,” in ji Ubangiji. “Duk wanda ya gudu daga razana zai fāɗa cikin rami, duk wanda ya haura daga rami zai fāɗa cikin tarko; gama zan kawo wa Mowab shekarar hukuncinta,” in ji Ubangiji. “A ƙarƙashin Heshbon masu gudun hijira suna tsaye ba mai taimako, gama wuta ta mutu daga Heshbon, harshen wuta daga tsakiyar Sihon; ta ƙone goshin Mowab, ƙoƙon kai na ’yan tayarwa masu surutu. Kaitonki, ya Mowab! Mutanen Kemosh sun hallaka; an kai ’ya’yanki maza daurin talala ’ya’yanki mata zaman bauta. “Duk da haka zan maido da wadatar Mowab a kwanaki masu zuwa,” in ji Ubangiji. A nan hukuncin Mowab ya ƙare. Game da Ammonawa. Ga abin da Ubangiji yana cewa, “Isra’ila ba shi da ’ya’ya maza ne? Ba shi da magāda ne? To, me ya sa Molek ya mallaki Gad? Me ya sa mutanensa suka zama a garuruwansa? Amma kwanaki suna zuwa,” in ji Ubangiji, “sa’ad da zan yi kirarin yaƙi a kan Rabba ta Ammonawa; zai zama tarin juji, za a sa wuta a ƙauyukan da suke kewayenta. Sa’an nan Isra’ila zai kori waɗanda suka kore shi,” in ji Ubangiji. “Ki yi kuka, ya Heshbon, gama an hallaka Ai! Ku tā da murya ku yi kuka, ya mazaunan Rabba! Ku sa tufafin makoki; ku ruga nan da can a cikin katanga, gama Molek zai tafi bauta, tare da firistocinsa da kuma fadawansa. Me ya sa kuke taƙama da kwarurukanku, taƙama da kwarurukanku masu amfani? Ya ke diya marar aminci, kin dogara a wadatarki kika kuma ce, ‘Wa zai iya fāɗa mini?’ Zan kawo razana a kanki daga waɗanda suke kewaye da ke,” in ji Ubangiji Maɗaukaki. “Za a kore kowannenku, babu wani da zai tattara masu gudun hijira. “Duk da haka, daga baya, zan maido da wadatar Ammonawa,” in ji Ubangiji. Game da Edom. Ga abin da Ubangiji Maɗaukaki yana cewa, “Babu sauran hikima a Teman ne? Shawara ta ɓace daga masu basira ne? Hikimarsu ta ruɓe ne? Ku juya ku gudu, ku ɓuya a cikin kogwanni masu zurfi, ku da kuke zama a Dedan, gama zan kawo masifa a kan Isuwa a lokacin da zan hukunta shi. In masu tsinkar ’ya’yan inabi suka zo maka, ba za su rage ’ya’yan inabi kaɗan ba? In ɓarayi suka zo da dare, ba za su sata abin da kawai suke bukata ba? Amma zan washe Isuwa sarai; zan bubbuɗe wuraren ɓuyarsa, don kada yă ɓoye kansa. ’Ya’yansa, danginsa da maƙwabtansa za su hallaka, ba kuwa zai ƙara kasancewa ba. Ka bar marayunka; zan tsare ransu. Gwaurayenka kuma za su dogara a gare ni.” Ga abin da Ubangiji yana cewa, “In waɗanda ba su dace su sha kwaf ɗin ba suka sha shi, me ya sa za ka kuɓuta? Ba za ka kuɓuta ba, sai ka sha shi. Na rantse da kaina,” in ji Ubangiji, “cewa Bozra za tă zama kufai da kuma abin tsoro, abin dariya da abin la’ana; kuma dukan garuruwanta za su kasance kufai har abada.” Na ji saƙo daga Ubangiji cewa; an aiki jakada zuwa ga al’ummai ya ce, “Ku tattara kanku don ku fāɗa mata! Ku tashi don yaƙi!” “Yanzu zan mai da kai ƙanƙani a cikin al’ummai abin reni a cikin mutane. Tsoron da ka sa ake ji da kuma girman kan zuciyarka ya ruɗe ka, kai da kake zama a kogon dutse, kai da kake kan tudu. Ko da yake ka gina wa kanka sheƙa can bisa kamar na gaggafa, daga can zan sauko da kai ƙasa,” in ji Ubangiji. “Edom za tă zama abin tsoro; dukan wanda ya wuce zai giggice ya yi tsaki saboda dukan mikinta. Kamar yadda aka tumɓuke Sodom da Gomorra, tare da garuruwan da suke maƙwabtaka da su,” in ji Ubangiji, “haka ba wanda zai zauna a can; ba wani da zai zauna a cikinta. “Kamar zaki mai haurawa daga kurmin Urdun zuwa wurin kiwo mai kyau, zan kori Edom daga ƙasarta nan da nan. Wane ne zaɓaɓɓen da zan naɗa don wannan? Wane ne yake kama da ni kuma wa zai kalubalance ni? Kuma wane makiyayi ne zai yi gāba da ni?” Saboda haka, ku ji abin da Ubangiji ya shirya a kan Edom, abin da ya nufa wa waɗanda suke zama a Teman. Za a ja ƙanana na garken tumaki a tafi; zai hallaka wurin kiwonsu sarai saboda su. Amon fāɗuwarsu zai sa ƙasa ta girgiza; za a kuma ji muryar kukansu a Jan Teku. Duba! Gaggafa tana firiya tana kuma saukowa, tana buɗe fikafikanta a bisa Bozra. A wannan rana zukatan jarumawan Edom za su zama kamar macen da take naƙuda. Game da Damaskus. “Hamat da Arfad sun giggice, gama sun ji mummunar labari. Suna damuwa, sun damu kamar tekun da baya hutu. Damaskus ta karai ta juya don ta gudu tsoro kuma ya kama ta; wahala da zafi sun kama ta, zafi kamar na mace mai naƙuda. Me ya sa ba a tafi aka bar sanannen birnin nan ba, birnin da nake jin daɗi? Tabbatacce, samarinta za su fāɗi a tituna; dukan sojojinta za su yi shiru a wannan rana,” in ji Ubangiji Maɗaukaki. “Zan cinna wa katangar Damaskus wuta; za tă ci kagaran Ben-Hadad.” Game da Kedar da mulkokin Hazor, waɗanda Nebukadnezzar sarkin Babilon ya fāɗa wa. Ga abin da Ubangiji yana cewa, “Tashi, ku fāɗa wa Kedar ku kuma hallaka mutanen Gabas. Za a ƙwace tentunansu da garkunansu; za a tafi da mafakanta tare da dukan kayayyakinsu da raƙumansu. Mutane za su yi musu ihu, ‘Razana ko’ina!’ “Ku yi maza ku gudu! Ku zauna a kogo masu zurfi, ku da kuke zama a Hazor,” in ji Ubangiji. “Nebukadnezzar sarkin Babilon ya shirya muku maƙarƙashiya; ya ƙulla maƙarƙashiya a kanku. “Ku tashi ku kuma fāɗa wa al’umma da sauƙi wadda take zama da ƙarfin hali,” in ji Ubangiji, “al’ummar da ba ta da ƙofofi ko ƙyamare; mutanenta suna zama su kaɗai. Za a washe raƙumansu, garkunansu mai girma za su zama ganima. Zan watsar da waɗanda suke a wurare masu nesa a ko’ina zan kuma kawo musu masifa a kowane gefe,” in ji Ubangiji. “Hazor za tă zama mazaunin diloli, kufai har abada. Ba wanda zai zauna a can; ba wanda zai zauna a cikinta.” Ga maganar Ubangiji da ta zo wa Irmiya annabi game da Elam, a farkon mulkin Zedekiya sarkin Yahuda. Ga abin da Ubangiji Maɗaukaki yana cewa, “Ga shi, zan karye ƙarfin Elam, zaunannen ƙarfinsu. Zan kawo a kan Elam a kusurwoyi huɗu daga kusurwoyi huɗu na duniya; zan watsar da su zuwa kusurwoyi huɗu, kuma ba al’ummar da masu gudun hijirar Elam ba za su kai ba. Zan ragargaza Elam a gaban maƙiyansu, a gaban waɗanda suke neman ransu; zan kawo masifa a kansu, da zafin fushina,” in ji Ubangiji. “Zan runtume su da takobi sai na kawo ƙarshensu. Zan sa kursiyina a Elam in kuma hallaka sarkinta da fadawanta,” in ji Ubangiji. “Duk da haka zan maido da wadatar Elam a kwanaki masu zuwa,” in ji Ubangiji. Ga maganar Ubangiji da ya yi ta wurin Irmiya annabi game da Babilon da kuma ƙasar Babiloniyawa. “Ka yi shela ka kuma furta a cikin al’ummai, ka tā da tuta ka kuma furta; kada ku ɓoye kome, amma ku ce, ‘Za a ci Babilon da yaƙi; za a kunyata Bel, Marduk ya cika da tsoro. Siffofinta za su sha kunya gumakanta za su cika da tsoro.’ Al’umma daga arewa za tă fāɗa mata su mai da ƙasar kango. Ba wanda zai zauna a cikinta; mutane da dabbobi za su gudu. “A kwanakin nan, a wannan lokaci,” in ji Ubangiji, “mutanen Isra’ila da mutanen Yahuda gaba ɗaya za su tafi cikin hawaye su nemi Ubangiji Allahnsu. Za su tambayi hanyar zuwa Sihiyona su kuma juya fuskokinsu wajenta. Za su zo su haɗa kansu ga Ubangiji a madawwamin alkawari da ba za a manta da shi ba. “Mutanena sun zama ɓatattun tumaki; makiyayansu sun bauɗar da su suka sa suna ta yawo a cikin duwatsu. Sun yi ta yawo a bisa dutse da tudu suka manta wurin hutunsu. Duk wanda ya same su ya cinye su; abokan gābansu suka ce, ‘Ba mu da laifi, gama sun yi zunubi wa Ubangiji, wurin kiwonsu na gaske, Ubangiji, abin sa zuciyar kakanninsu.’ “Ku gudu daga Babilon; ku bar ƙasar Babiloniyawa, ku zama kamar awakin da suke bi da garke. Gama zan kuta in kuma kawo a kan Babilon haɗinkan manyan al’ummai na arewa. Za su ja dāgār gāba da ita, kuma daga arewa za a ci ta da yaƙi. Kibiyoyinsu za su zama kamar na gwanayen jarumawa waɗanda ba sa dawowa hannu wofi. Saboda haka za a washe Babiloniyawa; dukan waɗanda suka washe ta za su ƙoshi,” in ji Ubangiji. “Saboda kuna farin ciki kuna kuma murna, ku da kuka washe gādona, domin kuna tsalle kamar karsana mai sussuka hatsi kuna kuma haniniya kamar ingarmu. Mahaifiyarku za tă sha babbar kunya; ita da ta haife ku za tă sha kunya. Za tă zama mafi ƙanƙanta na al’ummai, jeji, busasshiyar ƙasa, hamada. Saboda fushin Ubangiji ba za tă zauna a cikinta ba amma za tă zama kufai gaba ɗaya. Duk waɗanda suka wuce Babilon za su ji tsoro su kuma yi tsaki saboda dukan mikinta. “Ku ja dāgā kewaye da Babilon, dukanku waɗanda kuke jan baka. Ku harbe ta! Kada ku rage kibiyoyi, gama ta yi zunubi ga Ubangiji. Ku yi kuwwa a kanta a kowane gefe! Ta miƙa wuya, hasumiyarta ta fāɗi, katangarta sun rushe. Da yake wannan sakayya ce ta Ubangiji, ku ɗauki fansa a kanta; yi mata yadda ta yi wa waɗansu. Ku datse wa Babilon mai shuka, da mai girbi lauje a lokacin girbi. Saboda takobin mai zalunci bari kowa ya koma ga mutanensa, bari kowa ya gudu zuwa ga ƙasarsa. “Isra’ila garke ne da ya watse da zakoki suka kora. Na farkon da ya cinye shi sarkin Assuriya ne; na ƙarshen da ya ragargaza ƙasusuwansa Nebukadnezzar sarkin Babilon ne.” Saboda haka ga abin da Ubangiji Maɗaukaki, Allah na Isra’ila, yana cewa, “Zan hukunta sarkin Babilon da ƙasarsa yadda na hukunta sarkin Assuriya. Amma zan komo da Isra’ila zuwa wurin kiwonsa zai kuwa yi kiwo a Karmel da Bashan; zai ƙosar da marmarinsa a tuddan Efraim da Gileyad. A kwanakin nan, da kuma a lokacin nan,” in ji Ubangiji, “za a yi bincike don laifin Isra’ila, amma ba za a samu ba, kuma don zunubin Yahuda, amma ba za a sami wani abu ba, gama zan gafarta wa raguwar da na rage. “Ku fāɗa wa ƙasar Meratayim da waɗanda suke zama a Fekod. Ku fafara, ku kashe kuma hallaka su sarai,” in ji Ubangiji. “Ku aikata dukan abin da na umarce ku. Hargowar yaƙi tana a ƙasar, hargowar babbar hallaka! Dubi yadda aka karya aka kuma ragargaza gudumar dukan duniya! Dubi yadda Babilon ta zama kufai a cikin al’ummai! Na sa miki tarko, Babilon, kika kuwa kamu kafin ki sani; aka same ki aka kuma kama ki domin kin tayar wa Ubangiji. Ubangiji ya buɗe taskar makamansa ya fitar da makaman fushinsa, gama Maɗaukaki Ubangiji Mai Iko Duka yana da aikin da zai yi a ƙasar Babiloniyawa. Ku zo ku yi gāba da ita daga nesa. Ku buɗe rumbunanta; ku jibga ta kamar tsibin hatsi. Ku hallaka ta sarai kada ku bar mata raguwa. Ku kashe dukan ’yan bijimanta bari su gangara zuwa mayanka! Kaitonsu! Gama ranansu ta zo, lokaci ya yi da za a hukunta su. Ku saurari masu gudun hijira da masu neman mafaka daga Babilon suna furtawa a Sihiyona yadda Ubangiji Allahnmu ya ɗauki fansa, fansa domin haikalinsa. “Ku kira ’yan baka a kan Babilon, dukan waɗanda suke jan baka. Ku yi sansani kewaye da ita duka; kada ku bar wani ya tsira. Ku sāka mata don ayyukanta; ku yi mata yadda ta yi. Gama ta tayar wa Ubangiji, Mai Tsarkin nan na Isra’ila. Saboda haka, samarinta za su fāɗi a tituna; za a kawar da dukan sojojinta a wannan rana,” in ji Ubangiji. “Ga shi, ina gāba da ke, ya ke mai girman kai,” in ji Ubangiji, Ubangiji Maɗaukaki, “gama ranarki ta zo, lokacin da za a hukunta ki. Mai ɗaga kai za tă yi tuntuɓe ta kuma fāɗi kuma ba wanda zai taimake ta tă tashi; zan hura wuta a garuruwanta da za tă cinye duk waɗanda suke kewaye da ita.” Ga abin da Ubangiji Maɗaukaki yana cewa, “An danne mutanen Isra’ila, haka ma mutanen Yahuda. Dukan waɗanda suka kama su suna riƙe su kankan, suna kin barinsu su tafi. Duk da haka Mai Fansarsu yana da ƙarfi; Ubangiji Maɗaukaki ne sunansa. Zai kāre muradunsu gabagadi don yă kawo hutu ga ƙasarsu, amma rashin hutu ga waɗanda suke zaune a Babilon. “Akwai takobi a kan Babiloniyawa!” In ji Ubangiji “a kan waɗanda suke zama a Babilon da kuma a kan fadawanta da masu hikimarta! Akwai takobi a kan annabawan ƙaryanta! Za su zama wawaye. Akwai takobi a kan jarumawanta! Za su cika da tsoro. Akwai takobi a kan dawakanta da kekunan yaƙinta da kuma dukan baƙin da suke cikin mayaƙanta! Za su zama mata. Akwai takobi a kan dukiyarta! Za a washe su. Fări a kan ruwanta! Za su bushe ƙaf. Gama ƙasa ce ta gumaka, gumakan da za su haukace da tsoro. “Saboda haka halittun hamada da kuraye za su zauna a can, a can kuma mujiya za tă zauna. Ba za a ƙara zauna ko a yi zama a cikinta ba daga tsara zuwa tsara. Yadda Allah ya tumɓuke Sodom da Gomorra tare da maƙwabtan garuruwansu,” in ji Ubangiji “haka ma ba wanda zai zauna a can; ba wani da zai zauna a cikinta. “Duba! Ga sojoji suna zuwa daga arewa; babbar al’umma da sarakuna masu yawa suna tahowa daga iyakokin duniya. Suna riƙe da baka da māshi; mugaye ne marasa tausayi. Amonsu ya yi kamar rurin teku yayinda suke hawan dawakansu; suna zuwa kamar mutane a dāgār yaƙi don su fāɗa miki, ya Diyar Babilon. Sarkin Babilon ya ji rahotanni game da su, hannunsa kuma ya yi laƙwas. Wahala ta kama shi, zafi kamar na mace mai naƙuda. Kamar zaki mai haurawa daga kurmin Urdun zuwa wurin kiwo mai dausayi, zan fafare Babilon daga ƙasan nan da nan. Wane ne zaɓaɓɓen da zan naɗa domin wannan? Wane ne kamar ni da zai kalubalance ni? Kuma wanda makiyayi zai iya tsaya gāba da ni?” Saboda haka, ku ji abin da Ubangiji ya shirya a kan Babilon, abin da ya nufa gāba da ƙasar Babiloniyawa. Za a kwashe ƙananan garkensu a tafi; zai hallaka wurin kiwonsu sarai saboda su. Da jin an ci Babilon da yaƙi sai duniya ta girgiza; za a ji kukanta cikin al’ummai. Ubangiji ya ce, “Ga shi, zan zuga ruhun mai hallakarwa a kan Babilon da mutanen Leb Kamai. Zan aika da baƙi zuwa Babilon su casa ta su kuma yi kaca-kaca da ƙasarta; za su yi hamayya da ita a kowane gefe a ranar masifarta. Kada ku bar maharbi yă ja bakansa, kada kuma ku bari yă sa kayan yaƙinsa. Kada ku rage samarinta, ku hallaka sojojinta ƙaf. Za su fāɗi matattu a ƙasar Babilon, da munanan raunuka a titunanta. Gama Ubangiji Maɗaukaki, Allah na Isra’ila da Yahuda bai yashe su ba, ko da yake ƙasarsu cike da take da laifi a gaban Mai Tsarki na Isra’ila. “Ku gudu daga cikin Babilon! Bari kowa yă ceci ransa! Kada a hallaka saboda zunubanta. Gama lokaci ne don ramuwar Ubangiji, zai sāka mata bisa ga alhakinta. Babilon ta zama ƙoƙon zinariya a hannun Ubangiji, ta sa dukan duniya ta yi maye. Ƙasashe sun sha ruwan inabinta, saboda haka yanzu sun haukace. Farat ɗaya Babilon za tă fāɗi ta farfashe. Ku yi kuka dominta! Ku samo mata magani saboda azabarta; wataƙila za a iya warkar da ita. “ ‘Da mun warkar da Babilon, amma ba za tă warke ba; mu ƙyale ta kowane yă koma garinsu, gama hukuncinta ya kai sammai, ya yi tsawo kamar gizagizai.’ “ ‘ Ubangiji ya baratar da mu; zo mu tafi mu yi shelarsa a Sihiyona mu faɗa abin da Ubangiji Allahnmu ya yi.’ “Ku wasa kibiyoyi, ku ɗauko garkuwoyi! Ubangiji ya zuga sarakunan Medes, domin niyyarsa ce yă hallaka Babilon. Ubangiji zai yi ramuwa, zai yi ramuwa saboda haikalinsa. Ku tā da tuta gāba da katangan Babilon! Ku ƙara matsara, ku kafa masu tsaro, ku shirya kwanto! Ga shi, Ubangiji zai aikata abin da ya faɗa umarninsa a kan mutanen Babilon. Ke da kike zama kusa da ruwaye da kike kuma wadatar dukiya, ƙarshenki ya zo, lokaci ya yi da za a kau da ke. Ubangiji Maɗaukaki ya rantse da zatinsa, ya ce Tabbatacce zan cika ka da mutane kamar fāra, za su kuwa yi sowa don nasara a kanka. “Ya halicci ƙasa ta wurin ikonsa; ya kafa duniya ta wurin hikimarsa, ya kuma shimfiɗa sammai ta wurin fahiminsa. Sa’ad da ya yi tsawa ruwan da suke sammai sukan yi ruri; yakan sa gizagizai su tashi daga ƙarshen duniya. Yakan tura walƙiya tare da ruwan sama yakan kuma saki iska daga cikin taskokinsa. “Kowane mutum marar azanci ne kuma ba shi da sani; kowane maƙerin zinariya yakan sha kunya daga wurin gumakansa. Siffofinsa na ƙarya ne; babu numfashi a cikinsu. Su marasa amfani ne, abubuwan ba’a ne kawai; sa’ad da lokacin hukuncinsu ya kai, za su hallaka. Wanda yake na wajen Yaƙub ba kamar waɗannan ba ne, gama shi ne Mahalicci dukan abu, har da kabilar abin gādonsa, Ubangiji Maɗaukaki ne sunansa. “Kai ne kulkin yaƙina, kayan yaƙina, da kai ne na ragargaza ƙasashe, da kai ne na hallaka mulkoki, da kai ne na ragargaza doki da mahayi, da kai ne na ragargaza keken yaƙin da matuƙi, da kai ne na ragargaza miji da mata, da kai ne na ragargaza tsoho da saurayi, da kai ne na ragargaza saurayi da budurwa, da kai ne na ragargaza makiyayi da garke, da kai ne na ragargaza manoma da dawakan noma, da kai ne na ragargaza masu mulki da shugabanni. “Zan sāka wa Babilon da dukan mazaunan Babilon a idanunku saboda dukan muguntar da suka aikata a Sihiyona,” in ji Ubangiji. “Ga shi, ina gāba da kai, ya ke dutse mai hallakarwa, wadda ta hallaka duniya duka,” in ji Ubangiji. “Zan miƙa hannuna gāba da ke, zan mirgina ƙasa daga ƙwanƙolin dutse, zan maishe ki ƙonannen dutse. Ba za a ɗauki dutsen yin kusurwa daga gare ki ba ko na kafa harsashen gini, gama za ki zama marar amfani har abada,” in ji Ubangiji. “Ku tā da tuta a ƙasa! Ku busa ƙahoni a cikin ƙasashe! Ku shirya ƙasashe don yaƙi da ita, ku kira waɗannan mulkokin gāba da ita. Ararat, Minni, da Ashkenaz. A naɗa shugaba gāba da ita; ku shirya dawakai kamar fāra. Ku shirya ƙasashe don yaƙi da ita, sarakunan Medes, gwamnoninsu da dukan masu shugabancinsu da kowace ƙasar da take ƙarƙashin mulkinsu. Ƙasa ta girgiza tana makyarkyata saboda nufin Ubangiji na gāba da Babilon ya tabbata, nufinsa na mai da ƙasar Babilon kufai don kada kowa yă zauna a can. Sojojin Babilon sun daina yaƙi, suna zaune a cikin kagaransu. Ƙarfinsu ya ƙare, sun zama mata. An sa wa wuraren zamanta wuta, an karya ƙyamaren ƙofofin garinta. Maguji yana biye da maguji a guje, jakada yana biye da jakada, don su faɗa wa sarkin Babilon, cewa an ci birninsa a kowane gefe. An ƙwace mashigai aka ƙone fadamu da wuta, sojoji kuma suka giggice.” Ni Ubangiji Maɗaukaki, Allah na Isra’ila na ce, “’Yar Babilon kamar daɓen masussuka a lokacin da ake sussuka, ba da daɗewa ba lokacin girbe ta zai zo.” “Nebukadnezzar sarkin Babilon ya cinye mu, ya sa muka rikice, ya maishe mu kamar tulun da babu kome a cikinsa. Ya cinye mu kamar yadda dodon ruwa yakan yi ya kuma cika cikinsa da kayan marmarinmu, sa’an nan kuma ya yi amanmu. Bari abin da aka yi wa jikinmu yă kasance a bisa Babilon,” in ji mazaunan Sihiyona. “Bari jininmu yă kasance a kan waɗanda suke zama a Babilon,” in ji Urushalima. Saboda haka ga abin da Ubangiji ya ce, “Duba, zan tsaya muku, zan ɗaukar muku fansa, zan sa tekunta kafe in kuma sa maɓulɓulanta su ƙafe. Babilon za tă zama tarin juji, wurin zaman diloli, abin ƙyama da abar ba’a, inda ba kowa. Mutanenta duk suna ruri kamar zakoki, suna gurnani kamar ’ya’yan zaki. Amma sa’ad da aka farkar da su, zan yi musu biki in sa su sha su bugu, domin yi sowa da dariya, sa’an nan su shiga barcin da ba za su farka ba,” in ji Ubangiji. “Zan sauko da su kamar tumaki zuwa mayanka, kamar raguna da bunsurai. “Yadda za a ci Sheshak, taƙamar duniya duka za tă daina! Babilon za tă zama abar ƙyama a cikin al’ummai! Teku zai malalo a kan Babilon, raƙumansa masu hauka za su rufe ta. Garuruwanta sun zama abin kufai, za tă zama hamada inda ba ruwa, ƙasar da ba mazauna, ba kuma mutumin da zai ratsa ta cikinta. Zan hukunta Bel a Babilon, in sa ya yi aman abin da ya haɗiye. Ƙasashe ba za su ƙara bumbuntowa wurinsa ba. Katangan Babilon kuwa za tă rushe! “Ku fito daga cikinta, jama’ata! Ku tsere da ranku! Ku tsere daga zafin fushin Ubangiji. Kada zuciyarku tă yi suwu ko ku ji tsoro sa’ad da aka ji labarin a ƙasar, labari guda a wannan shekara, wani kuma a ta biye, labarin hargitsi a ƙasar mai mulki ya tasar wa mai mulki. Gama kwanaki tabbatacce suna zuwa, sa’ad da zan hukunta gumakan Babilon, zan kunyatar da dukan ƙasar kuma matattunta duk za su kwanta a cikinta. Sa’an nan sama da ƙasa da dukan abin da yake cikinsu, za su yi sowa ta murna a kan Babilon, gama daga arewa masu hallakarwa su auko mata,” in ji Ubangiji. “Babilon za tă fāɗi saboda kisassun mutanen Isra’ila, kamar dai yadda kisassu dukan duniya suka fāɗi saboda Babilon. Ku waɗanda kuka tsere wa takobi, ku gudu kada ku tsaya! Ku tuna da Ubangiji a ƙasa mai nesa, ku kuma yi ta tunani a kan Urushalima.” “Mun sha kunya saboda zargin da ake yi mana kunya ta rufe mu, domin baƙi sun shiga tsarkakan wurare na gidan Ubangiji.” “Amma kwanaki suna zuwa,” in ji Ubangiji, “sa’ad da zan hukunta gumakanta, da kuma a dukan ƙasarta waɗanda aka yi wa rauni, za su yi nishi. Ko da Babilon za tă kai sararin sama ne, ta gina kagaranta mai ƙarfi, duk da haka zan aiki masu hallakarwa a kanta,” in ji Ubangiji. “Ku ji muryar kuka daga Babilon, Da hargowar babbar hallakarwa daga ƙasar Babiloniyawa! Gama Ubangiji zai rushe Babilon, zai sa ta ƙame bakinta na alfarma. Sojoji za su yi ta kutsawa kamar raƙuman ruwa; suna tā da muryoyinsu. Gama mai hallakarwa ya auka wa Babilon, a kama sojojinta, a kuma kakkarya bakkunansu. Gama Ubangiji shi Allah ne mai sakayya; zai yi sakayya sosai. Zan sa mahukuntanta da masu hikimarta, gwamnoninta, shugabanninta da sojojinta su sha su bugu; za su dinga yin barcin da ba za su farka ba,” in ji Sarkin, mai suna Ubangiji Maɗaukaki. Ni Ubangiji Maɗaukaki, na ce, “Za a baje katangan nan na Babilon mai kauri za a kuma ƙone dogayen ƙyamarenta da wuta; mutane sun wahalar da kansu a banza, al’umma sun yi wahala kawai domin wutar lalata.” Jawabin da annabi Irmiya ya ba Serahiya, ɗan Neriya, wato, jikan Ma’asehiya, lokacin da ya tafi tare da Zedekiya, Sarkin Yahuda, zuwa Babilon a shekara ta huɗu ta mulkinsa. Serahiya shi ne shugaba mai lura da gidajen saukar baƙi. Irmiya ya rubuta a littafi dukan masifun da za su auko wa Babilon, wato, dukan wannan magana da aka rubuta a kan Babilon. Irmiya kuwa ya ce wa Serahiya, “Lokacin da ka kai Babilon, sai ka karanta dukan maganan nan. Ka kuma ce, ‘Ya Ubangiji, kai ne ka yi magana a kan wannan wuri, cewa za ka lalatar da shi, har ba abin da zai zauna a ciki, mutum ko dabba. Wurin zai zama kufai har abada.’ Sa’ad da ka gama karanta wannan littafi, sai ka ɗaura wa littafin dutse, sa’an nan ka jefar da shi tsakiyar Kogin Yuferites. Sa’an nan ka ce, ‘Haka Babilon za tă nutse, ba za tă ƙara tashi ba saboda masifar da zan kawo mata. Mutanenta kuwa za su fāɗi.’ ” Wannan shi ne ƙarshen kalmomin Irmiya. Zedekiya yana da shekara ashirin da ɗaya sa’ad da ya ci sarauta. Ya yi mulki a Urushalima shekara goma sha ɗaya. Sunan uwarsa Hamutal, ’yar Irmiya, wanda yake zaune a Libna. Sarki Zedekiya ya aikata abin da yake mugu a gaban Ubangiji kamar yadda Sarki Yehohiyakim ya yi. Al’amarin ya zama da muni ƙwarai a cikin Isra’ila da Yahuda, don haka Ubangiji ya husata har ya sa aka kai mutanen bautar talala. Zedekiya kuwa ya tayar wa Sarkin Babilon. A kan rana ta goma ga watan goma, a shekara ta tara ta mulkin Zedekiya, Sarkin Yahuda, sai Nebukadnezzar, Sarkin Babilon, ya zo yaƙi da Urushalima tare da dukan sojojinsa. Suka kewaye ta da yaƙi, suka gina katanga kewaye da ita. An kewaye birnin da yaƙi har shekara ta goma sha ɗaya ta mulkin Zedekiya. A kan rana ta tara a watan huɗu na wannan shekara, yunwa ta tsananta ƙwarai a birnin. Mutane suka rasa abin da za su ci. Sai aka huda katangan birnin, sojojin kuwa suka gudu, suka fita daga cikin birnin da dare ta hanyar ƙofar da take tsakanin bango biyu, kusa da gonar sarki, sa’ad da Babiloniyawa suke kewaye da birnin. Sojojin suka nufi wajen Araba. Amma sojojin Babiloniyawa suka runtumi sarki Zedekiya, suka ci masa a filayen Yeriko. Dukan sojoji suka yashe shi. Da aka kama Zedekiya, sai aka kai shi wurin Sarkin Babilon a Ribla a ƙasar Hamat, a nan ne Sarkin Babilon ya yanke masa shari’a. Sarkin Babilon ya kashe ’ya’yan Zedekiya a idonsa. Ya kuma kashe dukan shugabannin Yahuda a Ribla. Sa’an nan ya ƙwaƙule idanun Zedekiya, ya kuma sa masa ƙuƙumi, aka kai shi Babilon inda aka sa shi a kurkuku har ran da ya mutu. A kan rana ta goma ga watan biyar a shekara ta goma sha tara ta sarautar Nebukadnezzar, Sarkin Babilon, sai Nebuzaradan shugaban matsara da kuma ɗan majalisar sarki, ya zo Urushalima. Sai ya ƙone haikalin Ubangiji, da gidan sarki, da dukan gine-gine masu alfarman da suke Urushalima. Sojojin Babiloniyawa da suke tare da shugaban matsara, suka rushe dukan katangan Urushalima. Sa’an nan Nebuzaradan shugaban matsara ya kwashe waɗansu matalauta, da sauran mutane da aka bari a birnin, da waɗanda suka gudu zuwa wurin Sarkin Babilon, da sauran masu sana’a, ya kai su bautar talala a Babilon. Amma ya bar waɗansu matalauta na gaske a ƙasar don su yi aiki a gonakin inabi, da sauran gonaki. Babiloniyawa kuwa suka farfasa ginshiƙan tagulla, da dakalai, da babbar kwatarniya, waɗanda suke a haikalin Ubangiji. Suka kwashe tagulla duka suka kai Babilon. Suka kwashe tukwanen ƙarfe, da manyan cokula, da hantsuka, da daruna, da tasoshin ƙona turare, da kayayyakin tagulla waɗanda ake amfani da su domin hidimar haikali. Suka kuma kwashe ƙananan kwanonin sha, da farantan wuta, da daruna, da tukwane, da alkukai, da tasoshin ƙona turare, da kwanonin miƙa hadayar sha. Duk abin da yake na zinariya da azurfa, shugaban matsara ya kwashe. Tagullar da sarki Solomon ya yi wa haikalin Ubangiji da ita, wato, ginshiƙai biyu, da ƙaton kwano mai suna Teku na tagulla, da bijimai goma sha biyu, waɗanda suke ɗauke da kwatarniya, da dakalai, ta fi ƙarfin a auna. Tsawon kowane ginshiƙi kamu goma sha takwas ne, kewayensa kuwa kamu goma sha biyu ne, kaurinsa kuma huɗu ne. Kowannensu yana da rami a ciki. A kan kowane ginshiƙi, an yi masa dajiyar tagulla, tsayinta kamu biyar. A bisa kan kowace dajiya akwai raga da siffofin rumman na tagulla kewaye da dajiyar. Ginshiƙi na biyu ma haka yake da siffofin rumman. Akwai siffofin rumman tasa’in da shida da ake gani a gefen. Dukan siffofin rumman da suke a kan ragar kewaye, guda ɗari ne. Shugaban matsara kuma ya ɗauki Serahiya babban firist, da Zefaniya wanda yake biye da babban firist, da mutum uku masu tsaron ƙofar, ya tafi da su. Daga cikin birnin kuma ya ɗauki shugaban sojojin, da mutum bakwai ’yan majalisar sarki, da magatakardan shugaban sojojin wanda yakan tara sojojin ƙasar, da mutane sittin na ƙasar, waɗanda aka same su a birnin, ya tafi da su. Nebuzaradan shugaban matsara ya tafi da waɗannan mutane wurin Sarkin Babilon a Ribla, Sarkin Babilon kuwa ya kashe su a Ribla a ƙasar Hamat. Haka aka tafi da mutanen Yahuda bautar talala, daga ƙasarta. Wannan shi ne yawan mutanen da Nebukadnezzar ya kai su bauta. A shekara ta bakwai ta sarautarsa, ya tafi da Yahudawa 3,023; a shekara ta goma sha takwas ta sarautar Nebukadnezzar, ya tafi da Yahudawa daga Urushalima 832; a shekara ta ashirin da uku ta sarautarsa, Nebuzaradan shugaban matsara ya tafi da Yahudawa 745. Jimillarsu duka 4,600 ne. A shekarar da Ewil-Merodak ya zama Sarkin Babilon, sai ya nuna wa Yehohiyacin Sarkin Yahuda alheri. Ya fisshe shi daga kurkuku. Wannan ya faru ran ashirin da biyar ga watan goma sha biyu a shekara ta talatin da bakwai bayan da aka kai Yehohiyacin bauta. Ewil-Merodak ya nuna wa Yehohiyacin alheri, ya ba shi matsayi na daraja fiye da waɗansu sarakunan da aka kai su bautar talala a Babilon tare da shi. Yehohiyacin ya tuɓe tufafin kurkuku, ya riƙa cin abinci kullum a teburin sarki, har dukan sauran kwanakin ransa. Kowace rana akan ba shi kyauta bisa ga umarnin sarkin Babilon, saboda bukatarsa. Haka aka yi masa har rasuwarsa. Yanzu birnin ya zama babu kowa a ciki, birnin da a dā yake cike da mutane! Yanzu birnin ya zama kamar gwauruwa, wadda a dā babba ce ita a cikin ƙasashe! Ita da take sarauniya a cikin larduna yanzu ta zama baiwa. Tana yin kuka mai zafi da dare, hawaye na gangara a kan kumatunta. A cikin masoyanta duka babu wanda ya yi mata ta’aziyya. Duk abokanta sun yashe ta; sun zama abokan gābanta. Bayan wahala da baƙin ciki, Yahuda ta tafi bauta. Ta zauna a cikin ƙasashe, ba tă samu wurin hutawa ba. Duk masu fafararta sun same ta sa’ad da take cikin matuƙar ɓacin rai. Hanyoyin zuwa Sihiyona suna makoki, gama ba wanda ya zo bikin da ta shirya. Ba kowa a hanyoyin shiganta. Firistocinta suna gurnani, ’yan matana kuma suna wahala, kuma tana cikin shan wahala ƙwarai. Maƙiyanta sun zama shugabanninta; Abokan gābanta suna da kwanciyar rai. Ubangiji ya kawo mata ɓacin rai domin yawan zunubanta. ’Ya’yanta sun tafi bauta, a ƙarƙashin maƙiyanta. Diyar Sihiyona ba ta da sauran daraja. ’Ya’yan sarakunanta sun zama kamar bareyi waɗanda suka rasa wurin kiwo; cikin rashin ƙarfi suka guje wa masu fafararsu. A cikin kwanakin da take shan wahala take kuma yawo Urushalima ta tuna da dukan dukiyar da take da ita a kwanakin dā can. Sa’ad da mutanenta suka faɗa cikin hannun abokan gābanta, ba wanda ya taimake ta. Maƙiyanta suka dube ta suka yi mata dariya don hallakar da ta auko mata. Urushalima ta yi zunubi ƙwarai saboda haka ta zama marar tsarki. Dukan masu martaba ta sun raina ta, gama sun ga tsiraicinta; ita ma da kanta tana nishi da ƙyar ta kuma juya baya. Ƙazantarta ta manne wa rigunanta; ba tă kula da nan gaba ba, fāɗuwarta kuwa babban abu ne; babu wanda zai yi mata ta’aziyya. “Duba, ya Ubangiji, ka ga wahalata, gama maƙiyi ya yi nasara.” Maƙiya ya kwashe dukiyarta duka; ta ga mutanen da ba su san Allah ba sun shiga wuri mai tsarkinta waɗanda ka hana su shiga taron jama’arka. Dukan mutanenta suna nishi da ƙyar suna neman burodi; sun sayar da dukiyarsu don su samu abinci don kada su mutu da yunwa. “ Ubangiji, ka duba ka gani, gama an yashe ni.” “Ko wannan ba wani abu ba ne a wurinku, dukanku masu wucewa? Ku duba ku gani. Ko akwai wata wahala kamar irin wadda nake sha, wadda Ubangiji ya auko mini a cikin zafin fushinsa? “Daga sama ya aiko da wuta, ya aiko ta cikin ƙasusuwana. Ya shimfiɗa raga a ƙafafuna ya juyo da ni. Ya bar ni ni kaɗai, sumamme dukan yini. “Ya ɗaura zunubaina a wuyana; aka naɗe su a hannuwansa. Aka rataye su a wuyana Ubangiji ya kwashe ƙarfina. Ya bashe ni ga waɗanda suka fi ni ƙarfi. “Ubangiji ya ƙi duk mayaƙan da suke tare da ni; ya sa wata runduna ta tayar mini ta kuma tattake samarina. Ubangiji ya tattake budurwa Diyar Yahuda kamar ’ya’yan inabi a wurin matsewa. “Dalilin da ya sa nake kuka ke nan idanuna kuma suna ta zubar da hawaye. Babu wani a kusa da zai yi mini ta’aziyya, ba wanda zai sabunta ruhuna. ’Ya’yana sun zama fakirai domin maƙiyina ya yi nasara.” Sihiyona ta miƙa hannunta, amma ba wani da zai yi mata ta’aziyya. Ubangiji ya umarta cewa maƙwabtansa za su zama maƙiyansa; Urushalima ta zama abar ƙyama a cikinsu. “ Ubangiji mai adalci ne, duk da haka na yi tawaye da umarninsa. Ku saurara, jama’a duka; ku dubi wahalar da nake sha. Samarina da ’yan matana duka sun tafi bauta. “Na kira abokaina amma sun yashe ni. Firistocina da dattawana sun hallaka a cikin birnin yayinda suke neman abinci don kada su mutu da yunwa. “Duba, Ubangiji, ka ga ƙuncin da nake ciki! Ina shan azaba a raina, ba ni da kwanciyar rai a cikin zuciyata, domin na yi tawaye sosai. A waje takobi na kisa; a ciki kuma akwai mutuwa. “Mutane suna ji ina nishi da ƙyar, amma ba wanda zai yi mini ta’aziyya. Dukan maƙiyana sun ji wahalar da nake ciki; suna farin ciki da abin da ka yi. Ka kawo ranan nan da ka sanar domin su ma su zama kamar ni. “Bari ka ga muguntarsu duka; ka yi musu yadda ka yi mini domin dukan zunubansu. Nishina da yawa kuma zuciyata ta gaji.” Yadda Ubangiji ya rufe Diyar Sihiyona da gizagizan fushi! Ya jefar da darajar Isra’ila daga sama zuwa ƙasa; bai tuna da wurin ɗora ƙafafunsa ba a ranar fushinsa. Ubangiji ya hallakar da wurin zaman Yaƙub ba tausayi; A cikin fushinsa kuma zai rurrushe kagaran Diyar Yahuda. Ya ƙasƙantar da mulki da masu mulki. A cikin zafin fushi ya fasa kowane ƙaho na Isra’ila. Ya janye hannun damansa sa’ad da maƙiyi ya zo. Ya yi ƙuna a cikin Yaƙub kamar wuta mai ƙone duk abin da yake kusa da ita. Kamar abokin gāba, ya ɗana bakansa; hannun damansa na shirye. Kamar maƙiyi, ya kashe duk wanda idonsa ya ji daɗin gani; ya zuba fushinsa kamar wuta a kan tenti na Diyar Sihiyona. Ubangiji kamar maƙiyi ne; ya hallaka Isra’ila. Ya hallaka wurarenta duka ya kuma hallaka kagaranta. Ya ƙara yawan makoki da baƙin ciki wa Diyar Yahuda. Ya rushe haikalinsa kamar lambu; ya hallaka wurin yi masa sujada. Ubangiji ya sa Sihiyona ta manta da bukukkuwanta da kuma ranakunta na Asabbaci; a cikin zafin fushinsa ya watsar da sarki da firist. Ubangiji ya ƙi bagadensa ya kuma yi wofi da haikalinsa. Ya ba maƙiyinta fadodinta; suka yi sowa a cikin gidan Ubangiji kamar a ranar da ake yin biki. Ubangiji ya ƙuduri niyya yă rushe bangon da yake kewaye da Diyar Sihiyona. Ya auna da igiyar awo bai fasa hallaka ta ba. Ya sa katanga da katanga duk suka lalace. Ƙofofinta sun nutse a cikin ƙasa; ya kakkarya ƙarafanta. Sarakunanta da ’ya’yan sarakunanta duk an kai su bauta cikin waɗansu ƙasashe, babu sauran doka, annabawa kuma ba su samun wahayi daga wurin Ubangiji. Dattawan Diyar Sihiyona sun zauna shiru a ƙasa; suka kuma sa rigar buhu. ’Yan matan Urushalima suka sunkuyar da kawunansu ƙasa. Idanuna sun dushe don yawan kuka, raina na cike da baƙin ciki; zuciyata ta karaya domin mutanena sun hallaka, domin yara da jarirai suna suma a kan hanyoyi a cikin birni. Suna ce wa uwayensu, “Ina burodi da ruwan inabi?” Yayinda suke suma kamar mutanen da aka ji masu ciwo a cikin birni, sa’ad da suke mutuwa a hannuwan uwayensu. Me zan ce miki? Da me zan kwatanta ki, ke Diyar Urushalima? Da me zan misalta ki, yadda zan iya yi miki ta’aziyya, Ke Budurwa Diyar Sihiyona? Ciwonki yana da zurfi kamar teku. Wane ne zai iya warkar da ke? Wahayin annabawanki ƙarya ne kuma marasa amfani; ba su tona zunubanki ba yadda za su iya ceto ki daga bauta ba. Sun yi miki annabcin ƙarya marar amfani. Duk masu wucewa suna yi miki tafi na reni; suna yi wa Diyar Urushalima tsaki suna kaɗa kai suna cewa, “Wannan ne birnin da aka ce kyakkyawa ne, mai farantawa dukan duniya rai?” Maƙiyanki duka suna ta surutu game da ke; suna tsaki suna cizon haƙora suna cewa, “Mun hallaka ta. Wannan ce ranar da muke jira; yau mun gan ta.” Ubangiji ya yi abin da ya shirya; ya cika maganarsa, wadda ya umarta tun daɗewa. Ya jefar da ke ba tausayi, ya bari maƙiya sun yi nasara da ke, ya ɗaukaka ƙahon maƙiyanki. Zuciyar mutane ta yi kuka ga Ubangiji. Ya bangon Diyar Urushalima, bar hawayenki su zuba kamar rafi dare da rana; kada ki huta, kada idanunki su huta. Ki tashi, ki yi kuka cikin dare, dare na yi sai ki fara kuka; kina buɗewa Ubangiji zuciyarki. Ki ɗaga hannuwanki gare shi domin rayukan ’ya’yanki, waɗanda suka suma don yunwa a kan kowane titi. “Ka duba, ka gani ya Ubangiji. Wane ne ka taɓa yi wa haka? Ko ya kamata uwaye su ci ’ya’yansu, ’ya’yan da suka yi reno? Ko ya kamata a kashe firistoci da annabawa a cikin haikalin Ubangiji? “Matasa da tsofaffi duk suna kwanciya a cikin ƙurar tituna; an karkashe matasa da ’yan matana da takobi. Ka kashe su a ranar fushinka; ka kashe su ba tausayi. “Kamar yadda kake yin gayyata a ranar biki, haka kake kawo mini tsoro a kowane gefe. A ranar fushin Ubangiji ba mai tserewa ba wanda zai tsira; maƙiyina ya kashe waɗanda na yi renonsu, na kuma lura da su.” Ni ne mutumin da ya ga azaba ta wurin bulalar fushin Ubangiji. Ya kore ni, ya sa na yi tafiya a cikin duhu maimakon a cikin haske; ba shakka, ya juya mini baya, yana gāba da ni sau da sau, dukan yini. Ya sa fatar jikina da naman jikina sun tsufa ya kuma karya ƙasusuwana. Ya yi mini kwanton ɓauna ya kuma kewaye ni da baƙin ciki da kuma wahala. Ya sa na zauna a cikin duhu kamar waɗanda suka mutu da jimawa. Ya kewaye ni yadda ba zan iya gudu ba; Ya daure ni da sarƙa mai nauyi. Ko lokacin da nake kira don neman taimako, ba ya jin addu’ata. Ya tare hanyata da tubula na duwatsu; ya sa hanyata ta karkace. Kamar beyar da take a laɓe tana jira, kamar zaki a ɓoye, ya janye ni daga kan hanya ya ɓatar da ni ya bar ni ba taimako. Ya ja kwarinsa ya sa in zama abin baratarsa. Ya harbi zuciyata da kibiyoyin kwarinsa. Na zama abin dariya ga mutanena duka; suna yi mini ba’a cikin waƙa dukan yini. Ya cika ni da kayan ɗaci ya gundure ni da abinci mai ɗaci. Ya kakkarya haƙorana da tsakuwa; ya tattake ni cikin ƙura. An hana ni salama; na manta da ko mene ne ake kira wadata. Saboda haka na ce, “Darajata ta ƙare da kuma duk abin da nake begen samu daga wurin Ubangiji.” Na tuna da azabata da kuma sintiri, da na yi ta yi da ɗacin rai. Na tuna su sosai, sai kuma na ji ba daɗi a raina. Duk da haka na tuna da wannan na kuma sa bege ga nan gaba. Domin ƙaunar Ubangiji ba mu hallaka ba; gama jiyejiyanƙansa ba su ƙarewa. Sababbi ne kowace safiya; amincinka kuwa mai girma ne. Na ce wa kaina, “ Ubangiji shi ne nawa; saboda haka zan jira shi.” Ubangiji mai alheri ne ga waɗanda suke da bege a cikinsa, ga kuma wanda yake neman shi; yana da kyau ka jira shiru domin samun ceton Ubangiji. Yana da kyau mutum yă sha wuya tun yana yaro. Bari yă zauna shiru shi kaɗai, gama haka Ubangiji ya sa yă yi. Bari yă ɓoye fuskarsa cikin ƙura kila akwai bege. Bari yă ba da kumatunsa a mare shi, yă kuma bari a ci masa mutunci. Gama Ubangiji ba ya yashe mutane har abada. Ko da ya kawo ɓacin rai, zai nuna tausayi sosai, ƙaunarsa tana da yawa. Gama ba haka kawai yake kawo wahala ko ɓacin rai ga ’yan adam ba. Bai yarda a tattake ’yan kurkuku a ƙasa ba, ko kuma a danne wa mutum hakkinsa a gaban Maɗaukaki, ko kuma a danne wa mutum shari’ar gaskiya ashe Ubangiji ba zai ga irin waɗannan abubuwa ba? Wane ne ya isa yă yi magana kuma ta cika in ba Ubangiji ne ya umarta ba? Ba daga bakin Maɗaukaki ne bala’i da abubuwa masu kyau suke fitowa ba? Don mene ne wani mai rai zai yi gunaguni sa’ad da aka ba shi horo domin zunubansa? Bari mu auna tafiyarmu mu gwada ta, sai mu kuma koma ga Ubangiji. Bari mu ɗaga zuciyarmu da hannuwanmu ga Allah na cikin sama, mu ce, “Mun yi zunubi mun yi tawaye ba ka kuwa gafarta ba. “Ka rufe kanka da fushi, ka fafare mu; ka karkashe mu ba tausayi. Ka rufe kanka da gajimare don kada addu’armu ta kai wurinka. Ka mai da mu tarkace da juji a cikin mutane. “Dukan maƙiyanmu suna ta yin mana magana marar daɗi. Muna cika da tsoro, da lalatarwa da hallakarwa.” Hawaye na kwararowa daga idanuna domin an hallaka mutanena. Idanuna za su ci gaba da kwararowa da hawaye, ba hutawa. Har sai in Ubangiji ya duba daga sama ya gani. Abin da nake gani yana kawo mini baƙin ciki domin dukan matan birnina. Maƙiyana suna farauta ta ba dalili kamar tsuntsu. Sun yi ƙoƙari su kashe ni a cikin rami suka kuma jajjefe ni da duwatsu; ruwaye suka rufe kaina, sai na yi tunani cewa na kusa mutuwa. Na yi kira ga sunanka, ya Ubangiji, daga rami mai zurfi. Ka ji roƙona, “Kada ka toshe kunnuwanka ka ƙi jin roƙona na neman taimako.” Ka zo kusa lokacin da na kira ka, kuma ka ce mini, “Kada ka ji tsoro.” Ya Ubangiji, ka goyi bayana; ka fanshi raina. Ya Ubangiji, ka ga inda aka yi mini ba daidai ba. Ka shari’anta, ka ba ni gaskiya! Ka ga zurfin ramakonsu, da duk mugun shirin da suke yi mini. Ya Ubangiji, ka ji zaginsu, da duka mugun shirin da suke yi mini Abin da maƙiyana suke yin raɗa a kai game da ni duk yini. Dube su! A zaune ko a tsaye, suna yi mini ba’a cikin waƙoƙinsu. Ka ba su abin da ya dace su samu, ya Ubangiji, domin abin da hannuwansu suka yi. Ka sa yana ta rufe zuciyarsu, kuma bari la’anarka ta bi su. Ka fafare su cikin fushi ka hallaka su daga cikin duniya ta Ubangiji. Zinariya ta rasa kyanta, hasken zinariya ya dushe! An warwatsar da tsarkakakkun duwatsu masu daraja a kan tituna. Dubi samarin Sihiyona masu daraja, waɗanda a dā darajarsu ta isa nauyin zinariya, yanzu ana ɗaukar su a matsayin tukwanen ƙasa, aikin maginin tukwane! Ko diloli suna ba ’ya’yansu nono su sha, amma mutanena sun zama marasa zuciya kamar jiminai a cikin jeji. Domin ƙishirwa harshen jarirai ya manne a rufin bakinsu; yaran suna roƙo a ba su burodi, amma ba wanda ya ba su. Waɗanda a dā sukan ci abinci mai daɗi yanzu su ne masu bara a tituna. Waɗanda a dā suke sa kaya masu kyau yanzu suna kwance a kan tarin toka. Horon mutanena ya fi na Sodom girma, wadda aka hallaka farat ɗaya ba wani hannu da ya juya ya taimake ta. ’Ya’yan sarakunansu sun fi ƙanƙara haske sun kuma fi madara fari, jikunansu sun fi murjani ja, kyansu kamar shuɗin yakutu. Amma yanzu sun fi dare duhu; ba a iya gane su a tituna. Fatar jikinsu ta manne da ƙasusuwansu; sun bushe kamar itace. Gara waɗanda aka kashe su da takobi da waɗanda suke mutuwa da yunwa; sun rame domin rashin abinci a gona. Da hannuwansu mata masu tausayi sun dafa yaransu, suka zama masu abinci sa’ad da aka hallaka mutanena. Ubangiji ya saki fushinsa; ya zuba zafin fushinsa. Ya hura wuta a Sihiyona ta kuma cinye harsashin gininta. Sarakunan duniya ba su gaskata ba, haka ma mutanen duniya, cewa magabta da maƙiya za su iya shiga ƙofofin Urushalima. Amma ya faru domin zunuban annabawanta da muguntar firistocinta, waɗanda suka zub da jinin masu adalci a cikinsu. Yanzu suna yawo barkatai a tituna kamar makafi. Sun ƙazantu da jini yadda ba wanda zai kuskura ya taɓa rigunansu. “Ku tafi! Ba ku da tsabta!” Haka mutane suke ihu suke ce musu. “Ku tashi daga nan! Ku tashi daga nan! Kada ku taɓa mu!” Sa’ad da suka gudu suna yawo, mutanen waɗansu ƙasashe suka ce, “Ba za su ci gaba da zama a nan ba.” Ubangiji kansa ya warwatsa su; ya daina duban su. Ba a ba firistoci girma, ba su ba dattawa gata. Idanunmu sun gaji, suna ta dubawa ko taimako zai zo; mu sa ido ko za mu ga ƙasar da za tă iya taimakon mu. Ana bin sawunmu, ba za mu iya tafiya kan tituna ba. Ƙarshenmu ya kusa, kwanakinmu sun ƙare, gama ƙarshenmu ya zo. Masu fafarar mu sun fi gaggafa mai firiya a sararin sama sauri; sun fafare mu a kan duwatsu suna fakon mu a jeji. Shafaffe na Ubangiji, numfashin ranmu, ya fāɗi cikin tarkonsu. Muna tunani cewa za mu iya rayuwa cikin sauran mutane a ƙarƙashin inuwarsa. Ku yi murna da farin ciki, ya Diyar Edom, ke mai zama a ƙasar Uz. Amma ke ma za a ba ki kwaf; za ki bugu ki zama tsirara. Ya Diyar Sihiyona, hukuncinki zai ƙare; ba zai sa zaman bautarki yă yi tsayi ba. Amma ya Diyar Edom, zai hukunta zunubinki yă tona tsiraicinki. Ka tuna, ya Ubangiji, abin da ya faru da mu; duba, ka ga kunyar da muka sha. An ba wa baƙi gādonmu, gidajenmu kuma aka ba bare. Mun zama marayu marasa ubanni, uwayenmu kamar gwauraye. Dole mu sayi ruwan da muke sha; sai mun biya mu sami itace. Masu fafararmu sun kusa kama mu; mun gaji kuma ba dama mu huta. Mun miƙa kanmu ga Masar da Assuriya don mu sami isashen abinci. Kakanninmu sun yi zunubi kuma ba sa nan yanzu, mu ne aka bari muna shan hukuncinsu. Bayi suna mulki a kanmu, kuma ba wanda zai ’yantar da mu daga hannuwansu. Muna samun burodi a bakin rayukanmu domin takobin da yake a jeji. Fatar jikinmu ta yi zafi kamar murhu, muna jin zazzaɓi domin yunwa. An yi wa mata fyaɗe a cikin Sihiyona, da kuma budurwai a cikin garuruwan Yahuda. An rataye ’ya’yan sarakuna da hannuwansu; ba a ba wa dattawa girma. Samari suna faman yin niƙa; yara kuma suna fama da ƙyar da nauyin kayan itace. Dattawan sun bar ƙofar birnin, samari sun daina rera waƙa. Farin ciki ya rabu da zuciyarmu; rayuwarmu ta zama makoki. Rawani ya fāɗi daga kanmu. Kaiton mu gama mun yi zunubi! Domin wannan zuciyarmu ta yi sanyi; domin waɗannan abubuwa idanunmu sun dushe gama Tudun Sihiyona ya zama kufai, sai diloli ke yawo a wurin. Ya Ubangiji, kai ne mai iko har abada; kursiyinka ya dawwama cikin dukan zamani. Don mene ne kake mantawa da mu koyaushe? Me ya sa ka yashe mu da jimawa? Ka sāke jawo mu gare ka, ya Ubangiji, don mu komo; ka sabunta kwanakinmu su zama kamar yadda suke a dā sai dai in ka ƙi mu gaba ɗaya kana fushi da mu fiye da yadda za a iya aunawa. A shekara ta talatin, a wata na huɗu a rana biyar, yayinda nake cikin ’yan zaman bauta kusa da Kogin Kebar, sai sammai suka buɗe na kuwa ga wahayoyin Allah. A rana biyar ga wata, a shekara ta biyar ne ta zaman bautan Sarki Yehohiyacin, maganar Ubangiji ta zo wa Ezekiyel firist, ɗan Buzi, kusa da Kogin Kebar a ƙasar Babiloniyawa. A can hannun Ubangiji yana a kansa. Na duba, sai na ga guguwa ta taso daga arewa babban hadari cike da walƙiya kewaye da haske mai haske sosai. Tsakiyar wutar ta yi kamar ƙarfe mai cin wuta balbal, a cikin wutar kuwa akwai abin da ya yi kamar halittu guda huɗu. A bayyane kamanninsu ya yi kamar siffar mutum, amma kowannensu yana da fuskoki huɗu da fikafikai guda huɗu. Ƙafafunsu miƙaƙƙu ne; kuma ƙafafunsu sun yi kamar na maraƙi suna kuma walƙiya kamar tagullar da aka goge. A ƙarƙashin fikafikansu huɗu suna da hannuwan mutum a kowane gefe. Dukansu huɗu suna da fuskoki da fikafikai, kuma fikafikansu suna taɓan juna. Kowanne ya miƙe gaba; ba sa juyawa sa’ad da suke tafiya. Fuskokinsu sun yi kamar haka. Kowanne a cikin huɗun yana da fuskar mutum, kuma a gefen dama kowanne yana da fuskar zaki, a hagu kuma fuskar maraƙi; kowanne yana kuma da fuskar gaggafa. Haka fuskokinsu suka kasance. Fikafikansu sun buɗu sama; kowanne yana da fikafikai biyu, ɗaya yana taɓa fikafikan ɗayan halittar a ɗayan gefe, fikafikai biyu kuma suna rufe jikinsa. Kowanne ya miƙe gaba sosai. Duk inda ruhu zai tafi, can za su, ba tare da juyawa ba yayinda suke tafiya. Kamannin halittun ya yi kamar garwashi mai cin wuta ko kuwa kamar fitilu. Wuta tana kai da kawowa a cikin halittun; ta yi haske ƙwarai, walƙiya kuma tana wulgawa daga cikinta. Halittun suna gaggauta kai da kawowa kamar walƙiya. Yayinda nake kallon rayayyun halittun nan, sai na ga da’ira a ƙasa kusa da kowace halitta da fuskokinsa huɗu. Ga kamanni da fasalin da’irorin. Suna ƙyalƙyali kamar kirisolit, kuma dukan huɗun sun yi kama da juna. Kowacce ta yi kamar da’ira a cikin da’ira. Yayinda suke tafiya, sukan nufi duk wani gefe guda cikin gefe huɗun da halittun suka nufa; da’irorin ba za su juya ba sa’ad da halittun suke tafiya. Ƙarafansu da suka yi kamar zobe sun yi tsayi suna kuma da bantsoro, dukan ƙarafan nan huɗu kuwa da suka yi kamar zobe suna cike da idanu a kewaye. Sa’ad da rayayyun halittun suke tafiya, da’irorin da suke kusa da su kan motsa; kuma sa’ad da rayayyun halittun sun tashi sama, da’irorin su ma sukan tashi sama. Duk inda ruhu za shi, su ma can za su, kuma da’irorin za su tashi tare da su, domin ruhun rayayyun halittun nan yana a cikin da’irorin. Sa’ad da halittun sun motsa, sai su ma su motsa; sa’ad da halittun sun tsaya cik, su ma sai su tsaya cik, sa’ad da kuma halittun sukan tashi sama, da’irorin suka tashi tare da su, domin ruhun rayayyun halittun nan yana a cikin da’irorin. A bisa kawunan rayayyun halittun nan akwai abin da ya yi kamar ƙanƙara, mai bantsoro. A ƙarƙashin al’arshin fikafikansu sun miƙe kyam ɗaura da juna, kuma kowanne yana da fikafikai biyu da suka rufe jikinsa. Sa’ad da halittun suke tafiya, sai na ji ƙarar fikafikansu, kamar rurin ruwaye masu gudu, kamar muryar Maɗaukaki, kamar hayaniyar rundunar mayaƙa. In sun tsaya cik, sukan sauko da fikafikansu. Sai aka ji murya daga al’arshi a kan kawunansu yayinda suke tsaye da fikafikansu a sauke. A bisa al’arshin a kan kawunansu akwai abin da ya yi kamar saffaya, kuma a can bisa a kan kursiyin akwai siffa kamar na mutum. Na ga daga abin da ya yi kamar kwankwasonsa zuwa bisa ya yi kamar ƙarfe mai walƙiya, sai ka ce wuta, kuma daga kwankwasonsa zuwa ƙasa ya yi kamar wuta; haske kuma mai walƙiya sosai kewaye da shi. Kamar kamannin bakan gizo a cikin gizagizai a ranar da aka yi ruwan sama, haka hasken da ya kewaye shi. Wannan shi ne kwatancin kamannin ɗaukakar Ubangiji. Sa’ad da na gani, sai na fāɗi rubda ciki, na kuma ji muryar wani tana magana. Ya ce mini, “Ɗan mutum, tashi ka tsaya a ƙafafunka zan kuma yi maka magana.” Yayinda yake magana, sai Ruhu ya sauko mini ya kuma tā da ni a ƙafafuna, na kuma ji shi yana mini magana. Ya ce, “Ɗan mutum, ina aikan ka zuwa ga Isra’ilawa, zuwa ga al’ummar ’yan tawayen nan da suka yi mini tayarwa; su da kakanninsu sun yi mini tawaye har yă zuwa yau. Mutanen da nake aikan ka masu ƙin ji ne da kuma taurinkai. Ka faɗa musu cewa, ‘Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka ya faɗa.’ Kuma ko su ji ko kada su ji, gama su gida ne mai tawaye, za su san cewa akwai annabi a cikinsu. Kai kuwa, ɗan mutum, kada ka ji tsoro, ko da sarƙaƙƙiya da ƙayayyuwa duk sun kewaye ka kana kuma zama a cikin kunamai. Kada ka ji tsoron abin da za ka faɗa ko ka firgita ta wurinsu, ko da yake su gida ne mai tawaye. Dole ka yi maganata gare su, ko su ji ko kada su ji, gama su ’yan tawaye ne. Amma kai, ɗan mutum, ka saurari abin da zan faɗa maka. Kada ka yi tawaye kamar wannan gidan ’yan tawaye; ka buɗe bakinka ka kuma ci abin da na ba ka.” Sai na duba, na kuma ga hannu ya miƙe zuwa wurina. A cikinsa akwai littafi, wanda ya nannaɗe a gabana. A kowane gefensa akwai rubutun kalmomin makoki da kuka da kuma kaito. Ya kuma ce mini, “Ɗan mutum, ka ci abin da yake a gabanka, ka ci wannan littafi; sa’an nan ka tafi ka yi magana wa gidan Isra’ila.” Saboda haka na buɗe bakina, ya kuma ba ni littafin in ci. Sai ya ce mini, “Ɗan mutum, ka ci wannan littafin da nake ba ka, ka kuma cika cikinka da shi.” Sai na ci shi, ya kuma yi zaki kamar zuma a bakina. Sa’an nan ya ce mini, “Ɗan mutum, yanzu ka tafi gidan Isra’ila ka faɗa kalmomina gare su. Ba ina aikan ka wurin mutanen da suke da baƙon harshe da kuma yare mai wuya ba ne, amma zuwa ga gidan Isra’ila ne, ba ga mutane da yawa na baƙon harshe da yare mai wuya, waɗanda ba ka san kalmominsu ba. Tabbatacce da na aike ka wurin irinsu, da sun saurare ka. Amma gidan Isra’ila ba sa niyya su saurare ka domin ba sa niyya su saurare ni, gama dukan gidan Isra’ila sun taurare suna kuma kin ji. Amma zan sa ka zama mai taurinkai da taurin zuciya kamar su. Zan sa goshinka ya zama da tauri kamar dutse, da tauri fiye da dutsen ƙanƙara ƙarfi. Kada ka ji tsoronsu ko ka firgita ta wurinsu, ko da yake su gidan ’yan tawaye ne.” Ya kuma ce mini, “Ɗan mutum, ka ji da kyau ka kuma lura da dukan kalmomin da nake maka magana. Ka tafi yanzu zuwa ga ’yan’uwanka waɗanda suke zaman bauta ka yi musu magana. Ka ce musu, ‘Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa,’ ko ku ji, ko kada ku ji.” Sa’an nan Ruhu ya ɗaga ni sama, a bayana na ji wata karar babban motsi na cewa, Bari a yabi ɗaukakar Ubangiji a wurin zamansa! Karar fikafikan rayayyun halittun nan ne suke goge junansu da kuma karar da’irorin nan da suke kusa da su, ƙarar babban motsi. Sa’an nan Ruhu ya ɗaga ni sama ya kuma tafi da ni, na kuwa tafi da ɓacin rai da kuma fushin ruhuna, tare da hannu mai ƙarfi na Ubangiji a bisa na. Na zo wurin masu zaman bautan da suke zama a Tel Abib kusa da Kogin Kebar, A can kuwa, inda suke zama, na zauna a cikinsu kwana bakwai, ina mamaki. A ƙarshen kwana bakwai ɗin maganar Ubangiji ta zo mini cewa, “Ɗan mutum, na mai da kai mai tsaro don gidan Isra’ila; saboda haka ka ji maganar da zan yi ka kuma yi musu kashedin nan da ya fito daga gare ni. In na ce wa mugu, ‘Lalle za ka mutu,’ ba ka kuwa yi masa kashedi ko ka tsawata masa a kan mugayen hanyoyinsa don yă ceci ransa ba, wannan mugun zai mutu saboda zunubinsa, zan kuwa nemi hakkin jininsa a hannunka. Amma in ka yi wa mugun kashedi bai kuwa juya daga mugayen hanyoyinsa ba, zai mutu saboda zunubinsa; amma kai kam za ka kuɓuta. “Har yanzu, in mai adalci ya juya daga adalcinsa ya aikata mugunta, na kuma sa abin tuntuɓe a gabansa, zai mutu. Da yake ba ka yi masa kashedi ba, zai mutu saboda zunubinsa. Ba za a tuna da abin adalcin da ya yi ba, zan kuwa nemi hakkin jininsa a hannunka. Amma in ka yi wa mai adalcin kashedi kada yă yi zunubi bai kuwa yi zunubi ba, tabbatacce zai rayu saboda ya ji kashedin, kuma kai kam za ka kuɓuta.” Hannun Ubangiji ya kasance a kaina a can, ya kuma ce mini, “Tashi ka fita zuwa fili, a can kuwa zan yi maka magana.” Saboda haka na tashi da tafi fili. Ɗaukakar Ubangiji kuwa ta tsaya a can, kamar ɗaukakar da na gani kusa da Kogin Kebar, sai na fāɗi rubda ciki. Sai Ruhu ya sauko a kaina ya kuma ɗaga ni na tsaya a ƙafafuna. Ya yi mini magana ya ce, “Ka fita, ka rufe kanka a cikin gida. Kuma kai, ɗan mutum, za su ɗaura ka da igiyoyi; za a daure ka yadda ba za ka iya fita a cikin mutane ba. Zan sa harshenka ya manne wa dasashinka don ka yi shiru ka kuma kāsa tsawata musu, ko da yake su gidan ’yan tawaye ne. Amma sa’ad da na yi maka magana, zan buɗe bakinka za ka kuwa faɗa musu cewa, ‘Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka ya faɗa.’ Duk mai ji ya ji, kuma duk wanda ya ƙi ji, ya ƙi ji; gama su gida ne na ’yan tawaye. “Yanzu, ɗan mutum, ka ɗauki tubalin yumɓu, ka ajiye shi a gabanka ka kuma zāna birnin Urushalima a kansa. Sa’an nan ka yi mata ƙawanya. Ka kafa mata katangar ƙawanya, ka gina katangar da ɗan tudu ka kewaye ta da dundurusai. Sa’an nan ka ɗauki kwanon ƙarfe, ka shirya shi kamar katangar ƙarfe tsakaninka da birnin ka kuma zuba mata ido. Za tă kasance a ƙarƙashin ƙawanya, kai kuwa za ka yi mata ƙawanya. Wannan zai zama alama ga gidan Isra’ila. “Sa’an nan ka kwanta a hagunka ka kuma sa zunubin gidan Isra’ila a kanka. Za ka ɗauki zunubinsu na waɗansu kwanakin da kake kwance a gefenka. Na ɗora maka kwanaki bisa ga shekarun zunubinsu. Saboda haka cikin kwana 390 za ka ɗauki zunubin gidan Isra’ila. “Bayan ka gama haka, ka sāke kwantawa, a wannan lokaci a gefen damarka, ka kuma ɗauki zunubin gidan Yahuda. Na ɗora maka kwanaki 40, kwana guda a madadin shekara guda. Ka juya fuskarka wajen ƙawanyar Urushalima da hannunka a buɗe ka yi annabci a kanta. Zan ɗaura ka da igiyoyi don kada ka juya daga wannan gefe zuwa wani gefe sai ka gama kwanakin ƙawanyarka. “Ka ɗauki alkama da sha’ir, wake da acca, gero da maiwa; ka sa su a tulun ajiya ka kuma yi amfani da su don yin burodi wa kanka. Za ka ci shi a kwanaki 390 da za ka kwanta a gefenka. Ka auna shekel ashirin na abinci don kowace rana ka kuma ci shi a ƙayyadadden lokaci. Haka ma ka auna kashi ɗaya bisa shida na garwan ruwa ka sha shi a ƙayyadadden lokaci. Ka ci abinci yadda za ka ci ƙosai sha’ir, ka gasa shi a gaban mutane, ka yi amfani da najasar mutane kamar itacen wuta.” Ubangiji ya ce, “Ta haka mutanen Isra’ila za su ci ƙazantaccen abinci a cikin al’ummai inda zan kore su in kai.” Sai na ce, “Ba haka ba ne, Ubangiji Mai Iko Duka! Ban taɓa ƙazantar da kaina ba. Daga ƙuruciyata har zuwa yanzu ban taɓa cin wani abin da aka samu ya mutu ko abin da namun jeji suka kashe ba. Ba nama marar tsabtan da ya taɓa shiga bakina.” Sai ya ce, “To da kyau, zan bari ka gasa burodin a kan kashin shanu a maimakon najasar mutane.” Sa’an nan ya ce mini, “Ɗan mutum, zan yanke tanadin abinci a Urushalima. Mutane za su auna abincin da za su ci da tsoro su kuma auna ruwan da za su sha cikin fargaba, domin abinci da ruwa za su kāsa. Za su damu da ganin juna za su kuma lalace saboda zunubinsu. “Yanzu, ɗan mutum, ka ɗauki takobi mai kaifi ka kuma yi amfani da shi kamar rezan mai aski don askin kanka da gemunka. Sa’an nan ka ɗauki ma’auni ka kuma raba gashin. Sa’ad da kwanakin ƙawanyarka sun ƙare, sai ka ƙone kashi ɗaya bisa uku na gashin da wuta a cikin birnin. Ka ɗauki kashi ɗaya bisa uku ka yayyanka shi da takobi kewaye da birnin. Ka kuma watsar da kashi ɗaya bisa uku a iska. Gama zan fafare su da takobin da aka zāre. Amma ka ɗibi gashi kaɗan ka daure a shafin rigarka. Har yanzu, ka ɗibi kaɗan na waɗannan ka zuba su cikin wuta su kuma ƙone. Wuta zai bazu daga nan zuwa dukan gidan Isra’ila. “Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka ya ce Urushalima ce wannan, wadda na kafa a tsakiyar al’ummai, da ƙasashe kewaye da ita a ko’ina. Duk da haka cikin muguntarta ta yi tayarwa a kan dokokina da ƙa’idodina fiye da al’ummai da ƙasashe kewaye da ita. Ta ƙi dokokina ba tă kuwa bi ƙa’idodina ba. “Saboda haka ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka ya ce kin yi ƙin ji fiye da al’umman da suke kewaye da ke ba ki kuma bi ƙa’idodina ko ki kiyaye dokokina ba. Ba ki ma dace da matsayin al’umman da suke kewaye da ke ba. “Saboda haka ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka ya ce Ni kaina ina gāba da ke, Urushalima, kuma zan hukunta ki a gaban al’ummai. Saboda dukan gumakan banƙyamarki, zan yi abin da ban taɓa yi ba, ba kuwa zan ƙara yinsa ba. Saboda haka a cikinki ubanni za su ci ’ya’yansu, ’ya’ya kuma za su ci ubanninsu. Zan hukunta ki zan kuma watsar da dukan waɗanda suke tsira da suke naki a iska. Saboda haka muddin ina a raye, in ji Ubangiji Mai Iko Duka, domin kin ƙazantar da wuri mai tsarkina da dukan mugayen siffofinki da kuma ayyukanki masu banƙyama, ni kaina zan janye alherina; ba zan ji tausayinki ko in haƙura da ke ba. Kashi ɗaya bisa uku na mutanenki za su mutu da annoba ko su mutu da yunwa a cikinki; kashi ɗaya bisa uku takobi ne zai kashe su a waje da katangarki; kashi ɗaya bisa uku kuma zan watsar a iska in kuma fafare su da takobin da aka zāre. “Sa’an nan ne fushina zai huce hasalata a kanki kuma ta lafa, in kuma wartsake. Kuma sa’ad da na zuba fushina a kansu, a sa’an nan ne za su san cewa Ni Ubangiji na yi magana a cikin fushin kishina a kansu. “Zan mai da ki kufai da kuma abin dariya a cikin al’ummai kewaye da ke, a gaban dukan waɗanda suke wucewa. Za ki zama abin dariya da abin ba’a, kashedi da abin banrazana ga al’ummai kewaye da ke sa’ad da na hukunta ki cikin fushi da cikin hasala da kuma tsawatawa mai zafi. Ni Ubangiji na faɗa. Sa’ad da na harbe ki da mugayen kibiyoyina da kuma kibiyoyi masu hallakarwa na yunwa, zan yi harbi don in kashe ki. Zan kawo ƙarin yunwa a kanki in kuma yanke tanadin abincinki. Zan aika da yunwa da namun jeji a kanki, za su kuma bar ku ba ’ya’ya. Annoba da zub da jini za su ratsa cikinki, zan kuma kawo takobi a kanki. Ni Ubangiji na faɗa.” Maganar Ubangiji ta zo mini cewa, “Ɗan mutum, ka kafa idonka a kan duwatsun Isra’ila; ka yi annabci a kansu ka ce, ‘Ya ku duwatsun Isra’ila, ku ji maganar Ubangiji Mai Iko Duka. Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka ya ce wa duwatsu da tuddai, ga rafuffuka da kuma kwaruruka. Ina shirin kawo takobi a kanku, kuma zan hallaka masujadanku. Za a ragargaza bagadanku a kuma farfasa bagadanku na ƙone turare; zan kuma kashe mutanenku a gaban gumakanku. Zan shimfiɗa gawawwakin Isra’ilawa a gaban gumakansu, in kuma watsar da ƙasusuwanku kewaye da bagadanku. Duk inda kuke zama, garuruwa za su zama kango, za a kuma ragargaza masujadai, saboda bagadanku su rurrushe su zama kango, a kuma farfasa gumakanku su lalace, za a rurrushe bagadan ƙone turarenku, a kuma shafe dukan abin da kuka yi. Za a kashe mutanenku a cikinku, za ku kuwa sani ni ne Ubangiji. “ ‘Amma zan bar waɗansu, gama waɗansunku za su tsere wa takobi sa’ad da aka watsar da ku a cikin ƙasashe da al’ummai. Sa’an nan a cikin al’ummai inda aka kai ku zaman bauta, waɗanda suka a tsere za su tuna da ni, yadda raina ya ɓaci ta wurin zukatansu marasa imani, waɗanda suka rabu da ni, da kuma ta wurin idanunsu, waɗanda suka yi sha’awace-sha’awacen gumakansu. Za su ji ƙyamar kansu saboda mugayen abubuwan da suka aikata. Za su kuwa san cewa ni ne Ubangiji; ba a banza na ce zan kawo musu wannan masifa ba. “ ‘Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka ya ce ku tafa hannuwanku tare ku kuma taka ƙafafunku ku yi ihu ku ce, “Kaito!” Saboda dukan mugaye da kuma abubuwan banƙyama na gidan Isra’ila, gama za su mutu ta wurin takobi, yunwa da annoba. Wanda yake da nisa zai mutu da annoba, shi da yake kusa kuma zai mutu ta takobi, wanda kuma ya tsira aka kuma bari zai mutu da yunwa. Ta haka zan aukar da fushina a kansu. Za su kuwa san cewa ni ne Ubangiji, sa’ad da gawawwakin mutanensu suna kwance a kusa da gumakansu da kewaye da bagadansu, a kowane kan tudu mai tsawo da kuma a kan dukan kan duwatsu, a ƙarƙashin kowane inuwar itace da kuma kowane oak mai ganye, wuraren da suke ƙone turare masu ƙanshi wa dukan gumakansu. Zan kuma miƙa hannuna a kansu in mai da ƙasarsu kango daga hamadan Dibila, a duk inda suke zama. Sa’an nan za su san cewa ni ne Ubangiji.’ ” Maganar Ubangiji ta zo gare ni cewa, “Ɗan mutum, ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yake cewa wa ƙasar Isra’ila, “ ‘Ƙarshe ya zo! Ƙarshe ya zo a kan kusurwoyi huɗu na ƙasar. Ƙarshe yanzu yana a kanki. Zan fashe fushina a kanki. Zan shari’anta ki bisa ga halinki in sāka miki kuma saboda dukan ayyukan banƙyamar da kika yi. Ba zan dube ki da tausayi; ko in ƙyale ki ba. Tabbatacce zan sāka miki saboda halinki da kuma ayyukanki masu banƙyama a cikinki. Sa’an nan za ki san cewa ni ne Ubangiji.’ “Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa, “ ‘Masifa! Masifar da ba a taɓa gani ba tana zuwa. Ƙarshe ya zo! Ƙarshe ya zo! Ya farka a kanki. Ga shi, ya zo! Ƙaddara ta auko miki, ya ke wadda ke zama cikin ƙasar. Lokaci ya yi, rana ta gabato; akwai fargaba, ba farin ciki ba, a kan duwatsu. Ina gab da fasa hasalata a kanki in kuma aukar da fushina a kanki; zan shari’anta ke bisa ga halinki in kuma sāka miki saboda dukan ayyukanki masu banƙyama. Ba zan dube ki da tausayi ko in ƙyale ke ba; zan sāka miki bisa ga halinki da kuma ayyukan masu banƙyama a cikinki. Sa’an nan za ki san cewa ni ne Ubangiji wanda yake bugunki. “ ‘Ga shi ranar ta zo! Ta iso! Ƙaddararki ta keto, sandar ta yi toho, girman kai ya yi fure! Rikici ya yi girma ya zama sandar da za a hukunta mugunta; babu wani daga cikin mutanen da za a bari, babu wani dukiyarsu da za a bari, babu wani abin amfani. Lokaci ya yi! Ranar ta gabato! Kada mai saya ya yi farin ciki ko kuwa mai sayarwa ya yi baƙin ciki, gama hasala tana a kan dukan jama’a. Mai sayarwa ba zai mayar da ƙasar da ya sayar tuntuni ba muddin dukansu suna da rai, gama ba za a sauya wahayin da ya shafi dukan jama’a ba. Saboda zunubansu, babu ɗayansu da zai adana ransa. “ ‘Ko da yake suna busa ƙaho suna kuma shirya kome, ba wanda zai tafi yaƙi, gama hasalata tana a kan dukan jama’a. A waje takobi ne, a ciki annoba ne da yunwa; waɗanda suke fili za su mutu ta wurin takobi, waɗanda kuma suke cikin birni yunwa da annoba za su cinye su. Duk waɗanda suka tsira suka tsere za su kasance a cikin duwatsu, suna kuka kamar kurciyoyin kwaruruka, kowanne saboda zunubansa. Kowane hannu zai raunana, kowace gwiwa kuma za tă zama marar ƙarfi kamar ruwa. Za su sa tufafin makoki su kuma rufu da fargaba. Fuskokinsu kuma za su rufu da kunya a kuma aske kawunansu. “ ‘Za su zubar da azurfarsu a tituna, zinariyarsu kuma za tă zama ƙazantacciyar aba. Azurfarsu da zinariyarsu ba za su iya cetonsu a ranar hasalar Ubangiji ba. Ba za su ƙosar da yunwansu ko su cika cikinsu da shi ba, gama su ne sanadin tuntuɓensu cikin zunubi. Sun yi fariya kyan kayan adonsu suka kuma yi amfani da su don su yi gumakansu masu banƙyama, da ƙazantattun abubuwa. Zan ba da su duka kamar ganima ga baƙi da kuma kamar abin da aka washe ga mugayen duniya, za su kuma ƙazantar da su. Zan juye fuskata daga gare su, za su kuwa ƙazantar da wurina mai daraja; ’yan fashi za su shiga su kuma ƙazantar da shi. “ ‘Ka shirya sarƙoƙi, domin ƙasar ta cika da alhakin jini, birnin kuma ya cika da rikici. Zan kawo al’ummai mafi mugunta su mallaki gidajenku; zan kawo ƙarshen fariyar masu ƙarfi, Wurare Masu Tsarkinsu za su ƙazantu. Sa’ad da wahala ta zo, za su nemi salama, amma ba za su same ta ba. Masifa a kan masifa za su zo, jita-jita kuma a kan jita-jita. Za su yi ƙoƙarin samun wahayi daga annabi; koyarwar doka ta wurin firist za tă ɓace, kamar yadda shawarar dattawa za tă ɓace. Sarki zai yi makoki, yerima zai fid da zuciya, hannuwan mutanen ƙasar kuma za su yi rawa. Zan sāka musu bisa ga ayyukansu, zan kuma hukunta su bisa ga ma’auninsu. Sa’an nan za su san cewa ni ne Ubangiji.’ ” A shekara ta shida, a wata shida a ranar ta biya, yayinda nake zaune a gidana dattawan Yahuda kuma suna zaune a gabana, hannun Ubangiji Mai Iko Duka ya zo a kaina a can. Na duba, sai na ga siffa kamar na mutum. Daga kwankwaso zuwa ƙasa ya yi kamar wuta, kuma daga kwankwaso zuwa sama kamanninsa ya yi haske yana ƙyalli kamar ƙarfe mai haske. Ya miƙa abin da ya yi kamar hannu ya kama a gashin kaina. Ruhu ya ɗaga ni tsakanin sama da ƙasa, a cikin wahayoyi kuma Allah ya ɗauke ni zuwa Urushalima, zuwa ƙofa zuwa gabas na cikin fili, inda gunki mai tsokanar kishi yake tsaye. A can gabana kuwa ga ɗaukakar Allah na Isra’ila, kamar a wahayin da na gani a fili. Sai ya ce mini, “Ɗan mutum, duba waje arewa.” Sai na duba, a mashigin arewa na ƙofar bagaden kuwa na ga wannan gunki na tsokanar kishi. Ya kuma ce mini, “Ɗan mutum, ka ga abin da suke yi, abubuwan banƙyamar da gidan Isra’ila ke yi a nan, abubuwan da za su kore ni daga wuri mai tsarkina? Amma za ka ga abubuwan da suka ma fi banƙyama.” Sa’an nan ya kawo ni mashigin filin. Na duba, na kuma ga rami a bango. Ya ce mini, “Ɗan mutum, yanzu ka haƙa cikin bangon.” Da na haƙa cikin bangon sai na ga ƙofar shiga a can. Sai ya ce mini, “Shiga ka ga mugaye da kuma abubuwa banƙyamar da suke yi a can.” Na kuwa shiga na duba, sai na ga zāne-zāne ko’ina a bangon na kowane irin abubuwa masu rarrafe da kuma dabbobi masu ƙazanta da dukan gumakan gidan Isra’ila. A gabansu ga dattawa saba’in na gidan Isra’ila tsaye a cikinsu, Ya’azaniya ɗan Shafan kuwa yana tsaye a cikinsu. Kowa yana da farantin ƙona turare a hannunsa, tulin hayaƙin turare mai ƙanshi ya tunnuƙe zuwa sama. Ya ce mini, “Ɗan mutum, ka ga abin da dattawan gidan Isra’ila suke yi a cikin duhu, kowa yana a ɗakin tsafin gunkinsa? Suna cewa, ‘ Ubangiji ba ya ganinmu; Ubangiji ya yashe ƙasar.’ ” Ya kuma ce, “Za ka gan su suna yin abubuwan da suka fi waɗannan banƙyama.” Sa’an nan ya kawo ni mashigin arewa na ƙofar gidan Ubangiji, sai na ga mata zaune a can, suna makokin Tammuz. Ya ce mini, “Ɗan mutum, ka ga wannan? Za ka ga abubuwan da suke masu banƙyama fiye da wannan.” Sa’an nan ya kawo ni cikin fili na cikin gidan Ubangiji, a can kuwa a ƙofar haikali, tsakanin shirayi da bagade, akwai kamar mutum ashirin da biyar. Suka ba haikalin Ubangiji baya suna fuskanta wajen gabas, suna rusuna wa rana a gabas. Ya ce mini, “Ka ga wannan, ɗan mutum? Ƙaramin abu ne gidan Yahuda su yi abubuwan banƙyamar da suke yi a nan? Dole ne su cika ƙasar da rikici su kuma ci gaba da tsokane ni in yi fushi? Dube su suna tsokanata! Saboda haka zan hukunta su cikin fushi; Ba zan dube su da tausayi ko kuwa in ƙyale su ba. Ko da yake suna ihu a kunnuwana, ba zan saurare su ba.” Sai na ji ya yi kira da babbar murya yana cewa, “Kawo matsaran birni a nan, kowanne da makami a hannunsa.” Na kuma ga mutane shida suna zuwa daga kowane gefen ƙofar ta bisa, wadda take fuskantar arewa, kowanne da makamin kisa a hannunsa. Tare da su akwai mutum saye da lilin yana rataye da jaka ƙunshe da kayan rubutu a gefensa. Suka shiga suka tsaya kusa da bagaden tagulla. To, fa, ɗaukakar Allah na Isra’ila ta haura daga bisa kerubobi, inda ta kasance, ta tashi zuwa bakin madogarar ƙofar haikali. Sai Ubangiji ya kira mutumin da yake saye da lilin wanda ya rataye jaka ƙunshe da kayan rubutu a gefensa ya ce masa, “Ka ratsa birnin Urushalima ka sa shaida a goshin waɗanda suke baƙin ciki da kuma makoki a kan dukan abubuwan banƙyamar da ake yi a cikinsa.” Yayinda nake saurara, sai ya ce wa waɗansu, “Ku bi shi ta birnin ku kuma kashe, babu tausayi ko kuwa jinƙai. Ku kashe tsofaffi da samari da ’yan mata, mata da yara, amma kada ku taɓa wani wanda yake da shaida. Ku fara a wuri mai tsarkina.” Saboda haka suka fara da dattawan da suke gaban haikali. Sa’an nan ya ce musu, “Ku ƙazantar da haikalin ku kuma cika filayen da kisassu. Ku tafi!” Saboda haka suka fita suka kuma fara kisa a duk birnin. Yayinda suke kisan sai aka bar ni kaɗai, na fāɗi rubda ciki, na yi kuka na ce, “Kash, Ubangiji Mai Iko Duka! Za ka hallaka dukan raguwar Isra’ila a wannan zafin fushinka a Urushalima?” Ya amsa mini ya ce, “Zunubin gidan Isra’ila da Yahuda ya yi girma ainun; ƙasar ta cika da rashin adalci. Suna cewa, ‘ Ubangiji ya yashe ƙasar; Ubangiji ba ya gani.’ Saboda haka ba zan dube su da tausayi ko kuwa in ƙyale su ba, amma zan kawo wa kansu abin da suka yi.” Sai mutumin da yana saye da lilin yake kuma rataye da jaka ƙunshe da kayan rubutu a gefensa ya mayar da magana, yana cewa, “Na yi yadda ka umarci ni.” Na duba, sai na ga kamannin kursiyin saffaya a kan sararin da yake a bisa kawunan kerubobi. Sai Ubangiji ya ce wa mutumin da yake saye da lilin, “Ka shiga cikin da’irorin da suke ƙarƙashin kerubobi. Ka cika hannuwanka da garwashin wuta wanda yake tsakanin kerubobin ka kuma watsar da su a kan birnin.” Yayinda nake dubawa, sai ya shiga. Kerubobin kuwa suna tsaye a gefen kudu na haikali sa’ad da mutumin ya shiga, sai girgije ya cika filin da yake can ciki. Sai ɗaukakar Ubangiji ya tashi daga bisa kerubobi ya tafi zuwa madogarar ƙofar haikali. Girgijen ya cika haikali, filin kuwa ya cika da hasken ɗaukakar Ubangiji. Sai aka ji ƙarar fikafikan kerubobin har a filin waje, kamar muryar Allah Maɗaukaki sa’ad da ya yi magana. Sa’ad da Ubangiji ya umarci mutumin da yake saye da lilin cewa, “Ka ɗibi wuta daga cikin tsakanin da’irorin, daga tsakanin kerubobin,” sai mutumin ya shiga ya tsaya kusa da da’irar. Sa’an nan ɗaya daga cikin kerubobin ya miƙa hannu zuwa wurin wutar da take tsakaninsu. Ya ɗebo wutar daga ciki ya zuba a hannuwan mutumin da yake saye da lilin, shi kuwa ya karɓa ya fita. (A ƙarƙashin fikafikan kerubobin ana iya ganin abin da ya yi kamar hannuwan mutum.) Na duba, sai na ga kusa da kerubobin akwai da’irori huɗu, kowanne kusa da kerub guda; da’irorin suna ƙyalli kamar wani dutse mai daraja. Game da kamanninsu kuwa, huɗu a cikinsu sun yi kama da juna; kowanne ya yi kamar da da’ira a cikin da’ira. Yayinda suke tafiya, sukan tafi kowane gefe huɗun da kerubobin suka nufa; da’irorin ba sa juyawa yayinda kerubobin suke tafiya. Kerubobin suka tafi kowane gefen da kan ya nufa, ba tare da juyawa ba sa’ad da suke tafiya. Jikunansu gaba ɗaya, har da bayansu, hannuwansu da fikafikansu, sun cika gaba ɗaya da idanu, kamar yadda suke a da’irori huɗun. Na ji ana kiran da’irorin “da’irorin guguwa.” Kowane daga kerubobin yana da fuskoki huɗu. Fuska ɗaya na kerub ne, na biyun fuskar mutum ne, na ukun fuskar zaki ne, na huɗun kuwa fuskar gaggafa ce. Sai kerubobin suka tashi sama. Waɗannan ne halittu masu ran da na gani kusa da Kogin Kebar. Sa’ad da kerubobin suka motsa, sai da’irorin da suke kusa da su su motsa; kuma sa’ad da kerubobin suka buɗe fikafikansu don su tashi daga ƙasa, da’irorin ba sa barin wurarensu. Sa’ad da kerubobin suka tsaya cik, su ma sukan tsaya cik; kuma sa’ad da kerubobin suka tashi, sai su ma su tashi tare da su, domin ruhun rayayyun halittun yana a cikinsu. Sai ɗaukakar Ubangiji ya tashi daga bisa madogarar ƙofar haikali ya kuma tsaya a bisa kerubobi. Yayinda nake duba, kerubobin suka buɗe fikafikansu suka kuma tashi daga ƙasa, yayinda suka tafi kuwa, da’irorin suka tafi tare da su. Suka tsaya a mashigin ƙofar gabas na gidan Ubangiji, ɗaukakar Allah na Isra’ila kuwa yana a kansu. Waɗannan ne rayayyun halittun da na gani a ƙarƙashin Allah na Isra’ila kusa da Kogin Kebar, na kuma gane cewa su kerubobi ne. Kowanne yana da fuskoki huɗu da fikafikai huɗu, a ƙarƙashin kuwa akwai wani abin da ya yi kamar hannuwan mutum. Fuskokinsu suna da kamanni ɗaya da waɗanda na gani kusa da Kogin Kebar. Kowanne ya tafi kai tsaye sosai. Sa’an nan Ruhu ya ɗaga ni sama ya kawo ni ƙofar gidan Ubangiji wadda take fuskantar gabas. Can a mashigi zuwa ƙofar akwai mutum ashirin da biyar, na kuma ga a cikinsu akwai Ya’azaniya ɗan Azzur da Felatiya ɗan Benahiya, shugabannin jama’a. Ubangiji ya ce mini, “Ɗan mutum, waɗannan su ne mutanen da suke ƙulla mugunta suna kuma ba da muguwa shawara a cikin wannan birni. Suna cewa, ‘Lokaci bai yi kusa da za a gina gidaje ba? Wannan birni yana tukunyar dahuwa, mu ne kuwa naman.’ Saboda haka yi annabci a kansu; yi annabci, ɗan mutum.” Sai Ruhun Ubangiji ya sauko a kaina, ya kuma faɗa mini in ce, “Ga abin da Ubangiji yana cewa, haka kuke cewa, ya gidan Isra’ila, amma na san abin da yake a zuciyarku. Kun kashe mutane da yawa a wannan birni kuka kuma cika titunanta da gawawwaki. “Saboda haka ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa gawawwakin da kuka zubar a can su ne naman, wannan birni kuwa ita ce tukunya, amma zan kore ku daga cikinta. Kuna jin tsoron takobi, kuma takobi ne zan kawo muku, in ji Ubangiji Mai Iko Duka. Zan kore ku daga birnin in miƙa ku a hannuwan baƙi in kuma azabtar da ku. Za ku mutu ta wurin takobi, zan kuma hukunta ku a iyakokin Isra’ila. Sa’an nan za ku san cewa ni ne Ubangiji. Wannan birni ba za tă zama muku tukunya ba, ba kuwa za ku zama nama a cikinta ba; zan hukunta ku a iyakokin Isra’ila. Za ku kuwa san cewa ni ne Ubangiji, gama ba ku bi ƙa’idodina ba balle ku kiyaye dokokina, amma kuka bi hanyoyin al’ummai kewaye da ku.” Yanzu yayinda nake yin annabci, sai Felatiya ɗan Benahiya ya mutu. Sai na fāɗi rubda ciki na kuma yi kuka da babbar murya na ce, “Kash, Ubangiji Mai Iko Duka! Za ka hallaka raguwar Isra’ila ƙaƙaf ne?” Sai maganar Ubangiji ta zo mini cewa, “Ɗan mutum, ’yan’uwanka, ’yan’uwanka waɗanda suke danginka na cikinka da kuma dukan gidan Isra’ila su ne waɗanda mutanen Urushalima suka ce, ‘Su ne da nisa daga Ubangiji; an ba mu wannan ƙasa ta zama mallakarmu.’ “Saboda haka ka ce, ‘Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa ko da yake na kore su zuwa cikin al’ummai na kuma warwatsa su cikin ƙasashe, duk da haka na zama wuri mai tsarki a gare su a ƙasashen da suka tafi.’ “Saboda haka, ka ce, ‘Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa zan tattaro ku daga al’ummai in kuma dawo da ku daga ƙasashen da aka warwatsa ku, zan kuwa sāke mayar muku da ƙasar Isra’ila.’ “Za su dawo gare ta su kawar da dukan mugayen siffofi da gumaka masu banƙyama. Zan ba su zuciya ɗaya in kuma sa sabon ruhu a cikinsu; zan fid da zuciyar dutse daga gare su in kuma ba su zuciya ta nama. Sa’an nan za su bi ƙa’idodina su kuma yi hankali ga kiyaye dokokina. Za su zama mutanena, ni kuwa zan zama Allahnsu. Amma game da waɗanda zukatansu suka karkata ga bin mugayen siffofi da gumakan banƙyama, zan sāka musu gwargwadon ayyukansu, in ji Ubangiji Mai Iko Duka.” Sa’an nan kerubobi, tare da da’irori kusa da su, suka buɗe fikafikansu, ɗaukakar Allah kuwa tana a bisansu. Ɗaukakar Ubangiji ta haura daga cikin birnin ta sauka a bisa dutse gabas da shi. Ruhu ya ɗaga ni sama ya kuma kawo ni ga masu zaman bauta a ƙasar Babilon cikin wahayin da Ruhun Allah ya bayar. Sa’an nan wahayin da na gani ya rabu da ni, na kuwa faɗa wa masu zaman bautan dukan abin da Ubangiji ya nuna mini. Maganar Ubangiji ta zo mini cewa ɗan mutum, kana zama a cikin mutane masu tawaye, Suna da idanun gani amma ba sa gani, suna da kunnuwan ji amma ba sa ji, gama ’yan tawaye ne. “Saboda haka ɗan mutum, ka tattara kayanka don zuwa zaman bauta, ka tashi da rana suna gani ka ƙaura a inda kake zuwa wani wuri. Mai yiwuwa za su gane, ko da yake su gidan ’yan tawaye ne. Da rana, yayinda suke kallo, ka fid da kayanka da ka tattara don zuwa zaman bauta. Sa’an nan da yamma, yayinda suke kallo, ka fita kamar yadda mutane masu tafiyar zaman bauta sukan yi. Yayinda suke kallo, ka huda katanga ka fitar da kayanka daga ciki. Ka sa su a kafaɗarka yayinda suke kallo ka kuma fitar da su da dare. Ka rufe fuskarka don kada ka ga ƙasar, gama na mai da kai alama ga gidan Isra’ila.” Sai na yi kamar yadda aka umarce ni. Da rana na fitar da kayana da na tattara don zuwa zaman bauta. Sa’an nan da yamma na huda katanga da hannuwana. Na kwashe kayana da dare, na ɗauke su a kafaɗuna yayinda suke kallo. Da safe maganar Ubangiji ta zo mini cewa, “Ɗan mutum, gidan ’yan tawayen nan na Isra’ila ba su tambaye ka, ‘Me kake yi ba?’ “Ka ce musu, ‘Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa wannan abin da Allah ya yi magana a kai ya shafi sarki a Urushalima da kuma dukan gidan Isra’ila waɗanda suke a can.’ Ka ce musu, ‘Ni alama ne a gare ku.’ “Kamar yadda na yi, haka za a yi da su. Za a kai su zaman bauta kamar kamammu. “Sarkin da yake a cikinsu zai ɗauki kayansa ya saɓa a kafaɗarsa da dare ya tafi, za a huda masa rami a katanga ya fita. Zai rufe fuskarsa don kada yă ga ƙasar. Zan shimfiɗa masa ragata, za a kuwa kama shi da tarkona; zan kawo shi Babiloniya, ƙasar Kaldiyawa, amma ba zai gan ta ba, a can kuwa zai mutu. Zan warwatsa dukan waɗanda suke kewaye da shi a dukan fuskokin iska, ma’aikatansa da dukan rundunoninsa, zan fafare su da takobin da aka zāre. “Za su san cewa ni ne Ubangiji sa’ad da na watsar da su a cikin al’ummai na kuma warwatsa su cikin ƙasashe. Amma zan bar kaɗan daga cikinsu su tsere wa takobi, yunwa da annoba, saboda a cikin al’umman da suka tafi su furta dukan ayyukansu masu banƙyama. Sa’an nan za su san cewa ni ne Ubangiji.” Maganar Ubangiji ta zo mini cewa, “Ɗan mutum, ka yi rawar jiki yayinda kake cin abincinka, ka kuma yi makyarkyata don tsoro yayinda kake shan ruwanka. Ka faɗa wa mutanen ƙasar cewa, ‘Ga abin Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa game da waɗanda suke zama a Urushalima da kuma cikin ƙasar Isra’ila. Za su ci abincinsu da razana, su sha ruwansu da tsoro, gama za a washe dukan abin da yake ƙasarsu saboda hargitsin dukan waɗanda suna zama a can. Garuruwan da mutane suna ciki za su zama kufai ƙasar kuma za tă zama kango. Sa’an nan za ku san cewa ni ne Ubangiji.’ ” Maganar Ubangiji ta zo mini cewa, “Ɗan mutum, mene ne wannan karin magana da kuke da shi a ƙasar Isra’ila mai cewa, ‘Kwanaki suna ta wucewa, wahayi bai gudana ba’? Ka ce musu, ‘Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa zan kawo ƙarshen wannan karin magana, ba za su ƙara faɗar wannan karin magana a Isra’ila ba.’ Ka ce musu, ‘Kwanaki sun gabato da za a tabbatar da kowane wahayi. Gama ba za a ƙara ganin wahayin ƙarya ko a yi duba na daɗin baki a cikin mutanen Isra’ila ba. Amma Ni Ubangiji zan yi magana abin da na nufa, za tă kuwa tabbata ba tare da jinkiri ba. Gama cikin kwanakinku, kai gidan ’yan tawaye, zan cika duk abin da na faɗa, in ji Ubangiji Mai Iko Duka.’ ” Maganar Ubangiji ta zo mini cewa, “Ɗan mutum, gidan Isra’ila suna cewa, ‘Wahayin da yake gani na shekaru masu yawa ne nan gaba, yana kuma annabce-annabce game da wani zamani ne can.’ “Saboda haka ka ce musu, ‘Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yake cewa ba wata maganata da za tă ƙara yin jinkiri; duk abin da na faɗa zai cika, in ji Ubangiji Mai Iko Duka.’ ” Maganar Ubangiji ta zo mini cewa, “Ɗan mutum, yi annabci a kan annabawan Isra’ila waɗanda suke annabci yanzu. Ka faɗa wa waɗanda suke annabci bisa ga ra’ayinsu cewa, ‘Ku ji maganar Ubangiji! Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yake faɗa, Kaiton wawaye annabawan da suke bin ruhunsu kuma ba su ga kome ba! Annabawanki, ya Isra’ila, suna kama da diloli a kufai. Ba ku haura don ku rushe katanga don ku gyara gidan Isra’ila saboda ya tsaya daram a yaƙi a ranar Ubangiji ba. Wahayoyinsu ƙarya ne suna yin dubansu na ƙarya ne. Sukan ce, Ubangiji ya furta, alhali kuwa Ubangiji bai aike su ba; duk da haka sukan sa zuciya ga cikawar maganarsu. Ba ku ga wahayin ƙarya kuka kuma faɗa yin duban ƙarya sa’ad da kuka ce, “ Ubangiji ya furta,” ko da yake bai yi magana ba? “ ‘Saboda haka ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa saboda maganganunku na ƙarya da wahayinku na ƙarya, ina gāba da ku, in ji Ubangiji Mai Iko Duka. Hannuna zai yi gāba da annabawan da suke ganin wahayin ƙarya suna kuma yin duban ƙarya. Ba za su kasance cikin taron mutanena ba, ba kuwa za a rubuta su a littafin gidan Isra’ila ba, ba za su shiga ƙasar Isra’ila ba. Ta haka za ku san cewa ni ne Ubangiji Mai Iko Duka. “ ‘Domin sun ɓad da mutanena, suna cewa, “Salama,” sa’ad da ba salama, kuma saboda, sa’ad da ana gina katanga marar ƙarfi, sukan shafe ta da farar ƙasa, saboda haka ka faɗa wa waɗanda suka shafe da farar ƙasa cewa za tă fāɗi. Ruwan sama zai sauko da rigyawa, zan kuma aika da ƙanƙara, kuma babbar iska za tă ɓarke. Sa’ad da katangar ta fāɗi, mutane ba za su tambaye ku ba cewa, “Ina shafen farar ƙasar da kuka yi mata?” “ ‘Saboda haka ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa a cikin hasalata zan saki babbar iska, kuma cikin fushina zan tura ƙanƙara kuma rigyawan ruwan sama zai sauko da fushin hallaka. Zan rushe katangar da kuka shafe da farar ƙasa zan baje ta har ƙasa saboda tushenta zai tsaya tsirara. Sa’ad da ta fāɗi, za a hallaka ku a cikinta; kuma za ku san cewa ni ne Ubangiji Mai Iko Duka. Ta haka zan aukar wa katangar da hasalata da kuma a kan waɗanda suka yi shafenta da farar ƙasa. Zan ce muku, “Katangar ta fāɗi haka kuma mutanen da suka shafe ta da farar ƙasa, waɗannan annabawan Isra’ila waɗanda suka yi annabci wa Urushalima suka kuma ga mata wahayin salama sa’ad da ba salama, in ji Ubangiji Mai Iko Duka.” ’ “To, ɗan mutum, ka kafa idonka a kan ’yan matan mutanenka waɗanda suke annabci bisa ga ra’ayinsu. Yi annabci a kansu ka kuma ce, ‘Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa kaiton matan da suke ɗinka kambuna a hannuwansu suna kuma yin gyale masu tsawo dabam-dabam wa kawunansu don su farauci mutane. Za ku farauci rayukan mutanena ku bar naku? Kun jawo mini kunya a cikin mutanena don a tafa muku sha’ir da ɗan dunƙulen burodi. Ta wurin yin ƙarya wa mutanena, waɗanda suke jin ƙarairayi, kuka kashe waɗanda bai kamata su mutu ba kuka bar waɗanda ya kamata su mutu. “ ‘Saboda haka ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa ina gāba da kambunanku waɗanda kuke farautar mutane da su kamar tsuntsaye don haka zan kuma tsintsinke su daga hannuwanku; zan ’yantar da mutanen da kuka farauto kamar tsuntsaye. Zan kyakketa gyalenku in ceci mutanena daga hannuwanku, ba za su kuma ƙara zama ganima a hannunku ba. Sa’an nan za ku san cewa ni ne Ubangiji Domin kun karya zuciyar masu adalci da ƙarairayinku, sa’ad da na fitar da su babu damuwa, kuma domin kun ƙarfafa mugaye kada su juye daga mugayen hanyoyinsu su ceci rayukansu, saboda haka ba za ku ƙara ganin wahayin ƙarya ba, ko ku yi duba. Zan ceci mutanena daga hannuwanku. A sa’an nan za ku san cewa ni ne Ubangiji.’ ” Waɗansu dattawan Isra’ila suka zo wurina suka zauna a ƙasa a gabana. Sai maganar Ubangiji ta zo mini cewa, “Ɗan mutum, waɗannan mutane sun kafa gumaka a cikin zukatansu suka sa mugayen abubuwan sa tuntuɓe a gabansu. Zan bar su, su taɓa nemi ni? Saboda haka ka yi musu magana ka faɗa musu cewa, ‘Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa sa’ad da wani mutumin Isra’ila ya kafa gumaka a cikin zuciyarsa ya kuma sa mugun abin tuntuɓe a gabansa sa’an nan ya tafi wurin annabi, Ni Ubangiji zan amsa masa da kaina game da babban bautar gumakarsa. Zan yi haka don in sāke ƙame zukatan mutanen Isra’ila, waɗanda duk suka yashe ni don gumakansu.’ “Saboda haka ka faɗa wa gidan Isra’ila cewa, ‘Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa ku tuba! Ku juyo daga gumakanku ku kuma furta dukan ayyukanku masu banƙyama! “ ‘Duk sa’ad da mutumin Isra’ila ko baƙo mai zama a Isra’ila ya rabu da ni ya kuma kafa gumaka a cikin zuciyarsa ya kuna sa mugun abin tuntuɓe a gabansa sa’an nan ya tafi wurin annabi don yă neme ni, Ni Ubangiji zan amsa masa da kaina. Zan yi gāba da mutumin in kuma sa ya zama misali da kuma abin karin magana. Zan ware shi daga mutanena. Sa’an nan za ku san cewa ni ne Ubangiji. “ ‘In kuma aka ruɗi annabin har ya yi annabci, Ni Ubangiji na rinjayi wannan annabi, zan kuma miƙa hannuna gāba da shi in hallaka shi daga cikin mutanena Isra’ila. Za su ɗauki hakkin laifinsu annabin zai zama mai laifi daidai da wanda ya zo neman shawararsa. Sa’an nan mutanen Isra’ila ba za su ƙara kauce daga gare ni ba, ba kuwa za su ƙara ƙazantar da kansu da dukan zunubansu ba. Za su zama mutanena, ni kuma zan zama Allahnsu, in ji Ubangiji Mai Iko Duka.’ ” Maganar Ubangiji ta zo mini cewa, “Ɗan mutum, in wata ƙasa ta yi mini zunubi ta wurin rashin aminci na kuma miƙa hannuna gāba da ita don in toshe hanyar samun abincinta na kuma aika da yunwa a kanta na kashe mutanenta da dabbobinta, ko da waɗannan mutum uku Nuhu, Daniyel da kuma Ayuba suna a cikinta, za su iya ceton kansu ne kawai ta wurin adalcinsu, in ji Ubangiji Mai Iko Duka. “Ko kuwa in na aika da namun jeji su ratsa cikin wannan ƙasa suka kuma bar ta babu yaro, ta kuma zama kufai har babu wanda zai ratsa cikinta saboda namun jeji, muddin ina raye, in ji Ubangiji Mai Iko Duka, ko da ma waɗannan mutum uku suna a cikinta, ba za su iya ceton ’ya’yansu maza ko mata ba. Su kaɗai za a iya ceto, amma ƙasar za tă zama kufai. “Ko kuma in na kawo takobi a kan wannan ƙasa na kuma ce, ‘Bari takobin ya ratsa cikin dukan ƙasar,’ na kuma kashe mutanenta da dabbobinsu, muddin ina raye, in ji Ubangiji Mai Iko Duka, ko da waɗannan mutum uku suna cikinta, ba za su iya ceton ’ya’yansu maza ko mata ba. Su kaɗai za a iya ceto. “Ko kuma in na aika da annoba a cikin wannan ƙasa na kuma yi fushi a kanta ta wurin kisa, ina kisan mutanenta da dabbobinsu, muddin ina raye, in ji Ubangiji Mai Iko Duka, ko da Nuhu, Daniyel da Ayuba suna a cikinta, ba za su iya ceton ɗansu ko ’yarsu ba. Za su iya ceton kansu ne kaɗai ta wurin adalcinsu. “Gama ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa balle fa sa’ad da na aika wa Urushalima da hukuntaina guda huɗu masu zafi takobi da yunwa da namun jeji da annoba don su kashe mutanenta da dabbobinsu! Duk da haka za a sami mutanen da za su ragu ’ya’ya maza da matan da za a fitar daga cikinta. Za su zo wurinka, kuma sa’ad da ka gan halinsu da ayyukansu, za ka ta’azantu game da bala’in da na kawo a kan Urushalima kowane bala’in da na kawo a kanta. Za ka ta’azantu sa’ad da ka ga halinsu da kuma ayyukansu, gama za ka san cewa ban aikata wani abu a cikinta ba dalili ba, in ji Ubangiji Mai Iko Duka.” Maganar Ubangiji ta zo mini cewa, “Ɗan mutum, da me itacen kuringa ya fi reshen waɗansu itatuwa kyau a cikin kurmi? An taɓa ɗaukan itacensa an yi wani abu mai amfani? Akan yi maratayi da ita da za a rataya wani abu a kai? Bayan kuma a jefa ta cikin wuta, wuta kuma ta cinye kowane gefe ta kuma babbaka tsakiyarta, tana da amfani don yin wani abu kuma? In ba ta da amfanin wani abu sa’ad da take cikakkiya, balle bayan da wuta ta babbake ta, za a iya yin amfani da ita? “Saboda haka ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa kamar yadda na ba da itacen kuringa a cikin itatuwan kurmi ya zama itacen wuta, haka zan sa mazaunan Urushalima su zama. Zan yi gāba da su. Ko da yake sun fito daga wuta, wuta za tă cinye su. Kuma sa’ad da na yi gāba da su, za ku san cewa ni ne Ubangiji. Zan mai da ƙasar kufai domin sun yi rashin aminci, in ji Ubangiji Mai Iko Duka.” Maganar Ubangiji ta zo mini cewa, “Ɗan mutum, ka sa Urushalima ta san ayyukanta masu banƙyama ka ce, ‘Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa wa Urushalima, Asalinki da haihuwarki daga ƙasar Kan’ana ne; mahaifinki mutumin Amoriyawa ne, mahaifiyarki kuma mutuniyar Hitti ce. A ranar da aka haife ki ba a yanke cibiyarki ba, ba a kuma yi miki wanka don a tsabtacce ki ba, ba a kuma goge ki da gishiri ba ko a naɗe ki cikin tsummoki. Ba wanda ya dube ki da tausayi ko ya nuna miki isashen jinƙai don yă yi miki ɗaya daga cikin waɗannan abubuwa. A maimako, sai aka jefar da ke a fili, gama a ranar da aka haife ki an ji ƙyamarki. “ ‘Sa’an nan na wuce na ga kina birgima cikin jininki, yayinda kike kwance can cikin jininki sai na ce miki, “Ki rayu!” Na sa kin yi girma kamar tsiro a fili. Kin yi girma kika kuma yi tsayi kika zama mafiya kyau na kayan ado. Nononki suka fito, gashinki kuwa suka yi girma, duk da haka tsirara kike tik. “ ‘Daga baya na wuce, da na dube ki sai na ga cewa kin yi girma sosai har kin kai a ƙaunace ki, na yafa gefen tufafina a kanki na kuma rufe tsiraincinki. Na rantse miki, na ƙulla alkawari da ke, kin kuwa zama tawa, in ji Ubangiji Mai Iko Duka. “ ‘Na yi miki wanka na wanke miki jini daga gare ki na kuma shafa miki mai. Na rufe ki da rigar da aka yi wa ado na kuma sa miki takalman fata. Na sa miki riga ta lilin mai kyau na kuma rufe ki da riguna masu tsada. Na yi miki ado da kayan ado masu daraja, na sa miki mundaye a hannuwanki da abin wuya a wuyanki, na kuma sa miki zobe a hancinki, abin kunne a kunnuwanki da rawani mai kyau a kanki. Haka kuwa aka caɓa miki zinariya da azurfa; tufafinki kuwa na lilin mai kyau da riguna masu tsada waɗanda aka yi musu ado. Abincinki na gari mai laushi ne, zuma da man zaitun. Kika zama kyakkyawa har kika kuma zama sarauniya. Sunanki ya yaɗu a cikin al’ummai saboda kyanki, domin darajar da na ba ki ya sa kyanki ya zama cikakke, in ji Ubangiji Mai Iko Duka. “ ‘Amma kika dogara ga kyanki kika kuma yi amfani da sunan da kika yi don ki zama karuwa. Kin yi ta jibga alherai a kan kowa da ya wuce, sai kyanki ya zama naki. Kin ɗauki waɗansu tufafinki don ki yi wa kanki masujadai masu ado, inda kike karuwancinki. Irin waɗannan abubuwa bai kamata su faru ba, bai kuma kamata su taɓa faruwa ba. Kika kuma ɗauki kayan ado masu kyau da na ba ki, kayan adon da aka yi da zinariya da azurfa, kika yi wa kanki gumakan maza kika kuma yi ta yin karuwanci da su. Kika ɗauki rigunanki masu ado don ki sa a kansu, kika kuma miƙa maina da turarena a gabansu. Haka ma abincin da na tanada miki, lallausan gari, man zaitun, da zuman da na ba ki ki ci, kin miƙa su kamar turare mai ƙanshi a gabansu, in ji Ubangiji Mai Iko Duka. “ ‘Kika kuma kwashe ’ya’yanki maza da mata waɗanda kin haifa mini kika miƙa su kamar abinci ga gumakanki. Karuwancinki bai isa ba ne? Kin kashe ’ya’yana kika kuma miƙa su ga gumaka. Cikin dukan ayyukan banƙyamarki da karuwancinki ba ki tuna da kwanakin ƙuruciyarki ba, sa’ad da kike tsirara tik, kina birgima cikin jininki. “ ‘Kaito! Kaitonki, in ji Ubangiji Mai Iko Duka. Bugu da ƙari a kan dukan waɗansu muguntarki, kin gina wa kanki ɗakunan sama da gidajen tsafi a kowane dandali. A kowane titi kin gina ɗakin tsafi kika kuma wulaƙanta kyanki, kina miƙa jikinki da ƙarin fasikanci ga duk mai wucewa. Kin yi karuwanci da Masarawa, maƙwabtanki masu kwaɗayi, kika tsokane ni har na yi fushi da ƙarin fasikancinki. Saboda haka na miƙa hannuna gāba da ke na kuma rage iyakarki; na ba da ke ga abokan gābanki masu haɗama, ’yan matan Filistiyawa, waɗanda suka sha mamaki saboda halinki na lalata. Kin kuma yi karuwanci da Assuriyawa, domin ba kya ƙoshi; kai ko bayan wannan, ba ki ƙoshi ba. Sai kika ƙara fasikancinki da ya haɗa da ƙasar cinikin Babilon, amma duk da haka ba ki ƙoshi ba. “ ‘Kina da rashin ƙarfi a zuci, in ji Ubangiji Mai Iko Duka, sa’ad da kika yi duk waɗannan abubuwa, kina yi kamar karuwar da aka watsa! Sa’ad da kika gina ɗakunan samanki a kowane gefen titi kika kuma gina ɗakunan tsafinki a kowane dandali, ba kamar karuwa kike ba, domin kin karɓi kuɗi. “ ‘Ke mazinaciyar mace! Kin gwammace baƙi a maimakon mijinki! Kowace karuwa kan karɓi kuɗi, amma kina ba da kyautai ga dukan kwartayenki, kina ba su cin hanci don su zo wurinki daga ko’ina don alherai marasa ƙa’ida. Saboda haka cikin karuwancinki kin sha bamban da saura; babu wanda yake binki saboda alheranki. Ke dai dabam ce, gama kikan biya kuma ba mai biyanki. “ ‘Saboda haka, ke karuwa, ki ji maganar Ubangiji! Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa domin kin zubar da dukiyarki kika bayyana tsiraicinki cikin fasikancinki da kwartayenki, kuma saboda dukan gumakan banƙyamarki, kuma saboda kin ba su jinin ’ya’yansu, saboda haka zan tattara dukan kwartayenki, waɗanda kike jin daɗinsu, waɗanda kike ƙauna da waɗanda kike ƙi. Zan tattara su gāba da ke daga dukan kewaye zan kuma tuɓe ki a gabansu, za su kuwa ga dukan tsiraicinki. Zan hukunta ki da hukuncin matan da suke zina da kuma waɗanda suke zub da jini; zan kawo hakkin jini na fushina da kuma fushin kishina. Sa’an nan zan miƙa ki ga kwartayenki, za su kuwa rurrushe ɗakunan samanki su kuma farfashe ɗakunan tsafinki. Za su tuɓe miki tufafinki su kuma kwashe kayan adonki masu kyau su bar ki tsirara tik. Za su kawo taron jama’a a kanki, waɗanda za su jajjefe ki da dutse su sassare ki gunduwa-gunduwa da takubansu. Za su ƙone gidajenki su kuma hukunta ki a idon mata masu yawa. Zan kawo ƙarshen karuwancinki, ba za ki kuma ƙara biyan kwartayenki ba. Sa’an nan fushina a kanki zai huce fushin kishina kuma ya kwanta; zan huce ba kuwa zan ƙara yin fushi ba. “ ‘Domin ba ki tuna da kwanakin ƙuruciyarki ba amma kika husatar da ni da waɗannan abubuwa, tabbatacce zan sāka miki alhakin ayyukanki, in ji Ubangiji Mai Iko Duka. Ba kin ƙara lalata ga dukan waɗansu ayyuka masu banƙyamarki ba? “ ‘Duk mai yin amfani da karin magana zai faɗi wannan karin magana a kanki cewa, “Kamar yadda mahaifiya take haka ’yar take.” Ke ’yar mahaifiyarki ce da gaske, wadda ta ƙi mijinta da ’ya’yanta; ke kuma ’yar’uwar ’yar’uwanki mata ce da gaske, waɗanda suka ƙi mazansu da ’ya’yansu. Mahaifiyarki mutuniyar Hitti ce, mahaifinki kuma mutumin Amoriyawa ne. Babbar ’yar’uwarki mutuniyar Samariya ce, wadda take zaune da ’ya’yanta mata wajen arewa da ke; ƙanuwarki ita ce Sodom wadda take zaune kudu da ke tare da ’ya’yanta mata. Ba ki bi hanyoyinsu da abubuwansu na banƙyama kaɗai ba, sai ka ce wannan ya yi miki kaɗan, amma kin lalace fiye da su. Muddin in raye, in ji Ubangiji Mai Iko Duka, ’yar’uwarki Sodom da ’ya’yanta mata ba su yi abin da ’ya’yanki mata suka yi ba. “ ‘To, fa, ga zunubin ’yar’uwarki Sodom. Ita da ’ya’yanta mata sun yi girman kai, sun ƙoshi fiye da kima kuma ba su kula da wani abu ba; ba su taimaki matalauta da kuma masu bukata ba. Su masu girman kai ne kuma suka aikata abubuwa masu banƙyama a gabana. Saboda haka na kau da su kamar yadda ka gani. Samariya ba tă aikata ko rabin zunubanki ba. Kin aikata abubuwa masu banƙyama fiye da su, suka kuma sa ’yan’uwanki mata suka zama kamar masu adalci ta wurin dukan waɗannan abubuwa da kika aikata. Ki sha kunyarki, gama kin yi rangwame wa ’yan’uwanki mata. Saboda zunubanki sun yi muni fiye da nasu, sai suka zama kamar sun fi ki adalci. Saboda haka, ki sha kunya ki kuma sha ƙasƙancinki, gama kin sa ’yan’uwanki mata suka zama kamar su masu adalci ne. “ ‘Amma fa, zan komo da nasarar Sodom da ’ya’yanta mata da ta Samariya da ’ya’yanta mata, nasararki kuma tare da su, domin ki sha ƙasƙancinki ki kuma sha kunyar dukan abin da kika aikata ta wurin ta’azantar da su. ’Yan’uwanki kuwa, Sodom da ’ya’yanta mata da Samariya tare da ’ya’yanta mata, za su koma kamar yadda suke a dā; ke kuma da ’ya’yanki mata za ku koma kamar yadda kike a dā. Ba za ki ma iya ambaci ’yar’uwarki Sodom a ranar fariyarki ba, kafin a tone muguntarki. Ko da ma haka, yanzu ’ya’yan Arameyawa mata da dukan maƙwabtanta da kuma ’ya’yan Filistiyawa mata suna miki dariyar, dukan waɗanda suke kewaye da ke da suka rena ki. Za ki ɗauki hakkin lalatarki da kuma ayyukanki masu banƙyama, in ji Ubangiji. “ ‘Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa zan hukunta kamar yadda ya dace da ke, domin kin ƙyale rantsuwana ta wurin karya alkawari. Duk da haka zan tuna da alkawarin da na yi da ke a kwanakin ƙuruciyarki, zan kuma kafa madawwamin alkawari da ke. Sa’an nan za ki tuna da hanyoyinki ki kuma ji kunya sa’ad da kika karɓi ’yan’uwanki mata, waɗanda suka girme ki da kuma waɗanda kika girme su. Zan ba da su kamar ’ya’ya mata gare ki, amma ba bisa alkawarina da ke ba. Ta haka zan kafa alkawarina da ke, za ki kuma san cewa ni ne Ubangiji. Sa’an nan, sa’ad da na yi kafara saboda ke domin dukan abin da kika aikata, za ki tuna ki kuma ji kunya har ki kāsa buɗe bakinki saboda kunya, in ji Ubangiji Mai Iko Duka.’ ” Maganar Ubangiji ta zo mini cewa, “Ɗan mutum, ka shirya kacici-kacici ka faɗa wa gidan Isra’ila misali. Ka ce musu, ‘Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa babbar gaggafa mai manyan fikafikai, dogayen gasusuwa da gasusuwa da yawa masu launi iri-iri ta zo Lebanon. Ta cire kan al’ul, ta karya kan tohonsa da yake can bisansa ta kai ƙasar ciniki, inda ta shuka shi a birnin ’yan kasuwa. “ ‘Ta ɗebi waɗansu irin ƙasarku ta sa a ƙasa mai taƙi. Ta shuka shi kamar itacen wardi kusa da ruwa mai yawa, ya kuwa yi toho ya zama kuringa gajeruwa mai yaɗuwa. Rassanta suka tanƙwasa wajen gaggafar, amma saiwoyinta suka zauna a ƙarƙashinta. Ta haka ta zama kuringa, ta yi rassa ta kuma fid da ganyaye. “ ‘Akwai kuma wata babbar gaggafa mai manyan fikafikai da gashi mai yawa. Kuringan nan ta tanƙwasa saiwoyinta zuwa wajen wannan gaggafa daga inda aka shuka ta, ta kuma miƙe rassanta wajenta don gaggafar ta yi mata banruwa. An shuka ta a ƙasa mai kyau kusa da ruwa mai yawa don tă yi rassa masu yawa, ta ba da ’ya’ya ta kuma zama kuringa mai daraja.’ “Ka gaya musu cewa, ‘Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa wannan za tă ci gaba? Ba za a tumɓuke ta a kuma kakkaɓe ’ya’yanta don ta bushe ba? Dukan sababbin tohonta za su bushe. Ba sai da hannu mai ƙarfi, ko kuwa da yawan mutane za a tumɓuke ta daga saiwoyinta ba. Ko da an sāke shuka ta, za tă yi amfani ne? Ba za tă bushe gaba ɗaya sa’ad da iskar gabas ta hura ba, tă bushe a ƙasar da ta yi girma?’ ” Sai maganar Ubangiji ta zo mini cewa, “Ka faɗa wa gidan ’yan tawayen nan, ‘Ba ka san abin da waɗannan abubuwa suke nufi ba?’ Ka faɗa musu cewa, ‘Sarkin Babilon ya tafi Urushalima ya tafi da sarkinta da kuma manyan garinta, ya dawo da su Babilon. Sa’an nan ya ɗauki wani daga iyalin sarauta ya yi yarjejjeniya da shi, ya sa shi ya yi rantsuwa. Ya kuma tafi da shugabannin ƙasar, don a raunana masarautar, kada tă ƙara tashi, amma ta tsaya dai kan cika yarjejjeniyarsa. Amma sarkin nan ya yi tawaye a kan sarkin Babilon ta wurin aika jakadunsa zuwa Masar don a ba shi dawakai da sojoji masu yawa. Zai ci nasara? Shi da ya yi wannan abu zai tsira? Zai iya taka yarjejjeniya har ya tsere? “ ‘Muddin in raye, in ji Ubangiji Mai Iko Duka, zai mutu a Babilon, a ƙasar sarkin nan da ya naɗa shi, domin bai cika rantsuwa da alkawarin da ya yi ba. Fir’auna da yawan sojojinsa da kuma yawan jama’arsa ba zai zama da taimako gare shi a yaƙi ba, sa’ad da sarkin Babilon zai gina mahaurai ya kuma yi ƙawanya don yă hallaka rayuka masu yawa. Bai cika rantsuwa ba ta wurin take alkawari. Domin sarkin Isra’ila ya ƙulla alkawari ya kuma aikata dukan waɗannan abubuwa, ba zai tsira ba. “ ‘Saboda haka ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka ya ce muddin ina raye, zan nemi hakkin rantsuwata da ya ƙi cikawa da kuma alkawarin da ya take. Zan kafa masa tarkona, zai kuma fāɗi a tarkona. Zan kawo shi a Babilon in kuma hukunta shi a can domin ya yi mini rashin aminci. Dukan sojojinsa zaɓaɓɓu za a kashe su da takobi, za a kuma watsar da waɗanda suka ragu ko’ina. Ta haka za ku san cewa Ni Ubangiji na faɗa. “ ‘Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa ni kaina zan cire toho a kan itacen al’ul da yake can bisa in shuka; zan kuma karya ƙanƙanin reshe daga can bisan tohon in shuka a dutse mai tsayi. A ƙwanƙolin dutsen Isra’ila zan shuka shi; zai yi rassa yă ba da ’ya’ya yă kuma zama al’ul mai daraja. Tsuntsaye iri-iri za su yi sheƙa a cikinsa; za su sami mafaka a inuwar rassansa. Dukan itatuwan jeji za su san cewa Ni Ubangiji ne mai sa manyan itatuwa su zama ƙanana in kuma sa ƙananan itatuwa su zama manya. Nakan sa ɗanyen itace ya bushe, busasshen itace kuma ya zama ɗanye. “ ‘Ni Ubangiji na faɗa, zan kuma aikata.’ ” Maganar Ubangiji ta zo mini cewa, “Me ku mutane kuke nufi da faɗar wannan karin magana a kan ƙasar Isra’ila cewa, “ ‘Ubanni sun ci ’ya’yan inabi masu tsami, haƙoran ’ya’ya kuwa sun mutu’? “Muddin ina raye, in ji Ubangiji Mai Iko Duka, ba za ku ƙara faɗar wannan karin magana a Isra’ila ba. Gama kowane mai rai nawa ne, mahaifi da ɗa, duk nawa ne. Mutumin da ya yi zunubi shi zai mutu. “A ce akwai mai adalci wanda yake aikata abin da yake daidai da kuma gaskiya; ba ya cin abinci a duwatsun tsafi ko ya dogara ga gumakan gidan Isra’ila. Ba ya ƙazantar da matar maƙwabcinsa ko ya kwana da mace lokacin al’adarta ba. Ba ya cin zalin wani, amma yakan mayar wa wanda ya ba shi jingina abin da ya jinginar masa. Ba ya yi fashi amma yakan ba wa mayunwata abinci ya kuma tanada wa marasa tufafi riga. Ba ya ba da bashi da ruwa ko ya karɓa ƙarin riba. Yakan janye hannunsa daga aikata mugunta yakan kuma yi shari’a cikin gaskiya tsakanin mutum da mutum. Yana bin ƙa’idodina yana kuma kiyaye dokokina da aminci. Wannan mutumin adali ne; tabbatacce zai rayu, in ji Ubangiji Mai Iko Duka. “A ce yana da ɗa wanda yana kisa ko yana yin ɗaya daga cikin waɗannan abubuwa (ko da yake mahaifin bai yi ko ɗaya daga cikinsu ba). “Yakan ci abinci a duwatsun tsafi. Yakan ƙazantar da matar maƙwabci. Yakan ci zalin matalauta da mabukata. Yakan yi fashi. Ba ya mayar da abin da aka jinginar masa. Ya dogara ga gumaka. Yana aikata ayyukan banƙyama. Yakan ba da bashi da ruwa ya kuma karɓi riba mai yawa. Irin wannan mutum zai rayu? Ba zai rayu ba! Domin ya aikata dukan waɗannan abubuwa masu banƙyama, tabbatacce za a kashe shi, kuma hakkin jininsa zai zauna a kansa. “Amma a ce wannan ɗa yana da ɗa wanda ya ga dukan zunuban da mahaifinsa yake aikata, kuma ko da yake ya gan su, bai yi ko ɗaya daga cikin irin abubuwan nan ba, wato, “Bai ci abinci a duwatsun tsafi ba ko ya dogara ga gumakan gidan Isra’ila. Bai ƙazantar da matar maƙwabcinsa ba. Bai ci zalin wani ko ya karɓi jingina ba. Ba ya fashi amma yakan ba da abincinsa ga mayunwata ya tanada tufafi wa marasa tufafi. Yakan janye hannunsa daga zunubi ba ya kuma ba da bashi da ruwa ko karɓan riba da yawa. Yakan kiyaye dokokina ya kuma bi ƙa’idodina. Ba zai mutu saboda zunubin mahaifinsa ba; tabbatacce zai rayu. Amma mahaifinsa zai mutu saboda zunubinsa, domin ya yi ƙwace, ya yi wa ɗan’uwansa fashi ya kuma yi abin da ba daidai ba a cikin mutanensa. “Duk da haka kukan yi tambaya, ‘Me ya sa ɗan ba zai sami rabo a laifin mahaifinsa ba?’ Da yake ɗan ya yi abin da yake daidai da kuma gaskiya, ya kuma kiyaye dukan ƙa’idodina, tabbatacce zai rayu. Mutumin da ya yi zunubi shi zai mutu. Ɗa ba zai sami rabo a laifin mahaifi ba, mahaifi ba zai sami rabo a laifi ɗa ba. Adalcin adali zai zama nasa, muguntar mugu za tă koma kansa. “Amma in mugun mutum ya juya daga dukan zunubin da ya aikata ya kuma kiyaye dukan ƙa’idodina ya kuwa yi abin da yake daidai da kuma gaskiya, tabbatacce zai rayu; ba zai mutu ba. Babu laifin da ya yi da za a tuna da su. Saboda abubuwan adalcin da ya aikata, zai rayu. Ina jin daɗin mutuwar mugu ne? In ji Ubangiji Mai Iko Duka. A maimako, ban fi jin daɗi sa’ad da suka juyo daga hanyoyinsu suka rayu ba? “Amma in mai adalci ya juya daga adalcinsa ya yi zunubi ya kuma aikata abubuwa masu banƙyamar da mugun mutum ke aikatawa, zai rayu? Babu abubuwan adalcin da ya aikata da za a tuna da su. Saboda rashin amincinsa da kuma saboda zunubai da ya yi, zai mutu. “Duk da haka kun ce, ‘Hanyar Ubangiji ba daidai ba ce.’ Ka ji, ya gidan Isra’ila. Hanyata ba daidai ba ce? In mai adalci ya juye daga adalcinsa ya yi zunubi, zai mutu saboda wannan; saboda zunubin da ya yi, zai mutu. Amma in mugun mutum ya juye daga muguntarsa ya kuma yi abin da yake daidai da kuma gaskiya, zai ceci ransa. Domin ya lura da dukan laifofin da ya yi ya kuma juye daga gare su, tabbatacce zai rayu; ba zai mutu ba. Duk da haka mutanen Isra’ila sun ce, ‘Hanyar Ubangiji ba daidai ba ce.’ Hanyoyina ba daidai ba ne, ya gidan Isra’ila? Ba hanyoyinku ne ba daidai ba? “Saboda haka, ya gidan Isra’ila, zan hukunta ku, kowa bisa ga hanyarsa, in ji Ubangiji Mai Iko Duka. Ku tuba! Ku juye daga dukan laifofinku; sa’an nan zunubi ba zai zama sanadin fāɗuwarku ba. Ku raba kanku da dukan laifofin da kuka yi, ku sami sabuwar zuciya da sabon ruhu. Don me za ku mutu, ya gidan Isra’ila? Gama ba na jin daɗin mutuwar wani, in ji Ubangiji Mai Iko Duka. Ku tuba don ku rayu! “Ka yi makoki game da sarakunan Isra’ila ka ce, “ ‘Mahaifiyarki zakanya ce cikin zakoki! Takan kwanta cikin ’yan zakoki ta kuma yi renon kwiyakwiyanta. Ta goyi ɗaya daga cikin kwiyakwiyanta, ya yi girma ya zama zaki mai ƙarfi. Ya koyi yayyage abin da ya yi farauta yakan kuma cinye mutane. Al’ummai suka ji labarinsa, aka kuma kama shi cikin raminsu. Suka ja shi da ƙugiyoyi zuwa ƙasar Masar. “ ‘Sa’ad da ta ga sa zuciyarta bai cika ba, abin da take fata gani ya tafi, sai ta ɗauki wani daga cikin kwiyakwiyanta ta mai da shi zaki mai ƙarfi. Ya yi ta yawo a cikin zakoki, gama yanzu shi zaki ne mai ƙarfi. Ya koyi yayyage abin da ya yi farauta yakan kuma cinye mutane. Ya rurrushe kagaransu ya kuma ragargaza biranensu. Ƙasar da dukan waɗanda suke cikinta sun tsorata da jin rurinsa. Sai al’ummai suka tayar masa, waɗannan daga yankunan da suke kewaye. Suka yafa raga dominsa ya kuwa fāɗa cikin raminsu. Da ƙugiyoyi suka ja shi cikin keji suka kawo shi wurin sarkin Babilon. Suka sa shi cikin kurkuku, saboda haka ba a ƙara jin rurinsa a kan duwatsun Isra’ila ba. “ ‘Mahaifiyarku kamar kuringa ce a cikin gonar inabi da aka shuka kusa da ruwa; ta ba da ’ya’ya da kuma cikakkun rassa saboda yalwan ruwa. Rassanta suka yi ƙarfi, suka dace da sandar mai mulki. Ta yi tsayi zuwa sama ana ganin ta saboda tsayinta da kuma saboda yawan rassanta. Amma aka tumɓuke ta cikin fushi aka jefar da ita a ƙasa. Iskar gabas ta sa ta yanƙwane, aka kakkaɓe ’ya’yanta; rassanta masu ƙarfi suka bushe wuta kuma ta cinye su. Yanzu an shuka ta a hamada, a busasshiyar ƙasa marar ruwa. Wuta ta fito daga jikin rassanta ta cinye ’ya’yanta. Babu sauran reshe mai ƙarfin da ya rage a kanta da ya dace da sandar mai mulki.’ Wannan waƙa ce kuma za a yi amfani da ita a matsayin makoki.” A shekara ta bakwai, a wata na biyar a rana ta goma, waɗansu dattawan Isra’ila suka zo don su nemi nufin Ubangiji, suka kuwa zauna a ƙasa a gabana. Sai maganar Ubangiji ta zo mini cewa, “Ɗan mutum, ka yi magana da dattawan Isra’ila ka ce musu, ‘Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa kun zo ne ku nemi shawarata? Muddin ina raye, ba zan bari ku nemi shawarata ba, in ji Ubangiji Mai Iko Duka.’ “Za ka hukunta su? Za ka hukunta su, ɗan mutum? To, sai ka kalubalance su da ayyukan banƙyamar kakanninsu ka ce musu, ‘Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa a ranar da na zaɓi Isra’ila, na ɗaga hannuna, na rantse wa zuriyar gidan Yaƙub na kuma bayyana kaina gare su a Masar da hannun da na ɗaga na ce musu, “Ni ne Ubangiji Allahnku.” A ranar na yi musu rantsuwa cewa zan fitar da su daga Masar zuwa ƙasar da na samo musu, ƙasa mai zub da madara da zuma, ƙasa mafi kyau cikin dukan ƙasashe. Na kuma ce musu, “Kowannenku ya zubar da mugayen siffofin da kuka kafa idanunku a kai, kuma kada ku ƙazantar da kanku da gumakan Masar. Ni ne Ubangiji Allahnku.” “ ‘Amma sai suka yi tawaye a kaina ba su kuwa saurare ni ba; ba su zubar da mugayen siffofin da suka kafa idanunsu a kai ba, balle su ƙi gumakan Masar. Saboda haka zan zubo hasalata a kansu in kuma aukar musu da fushina a Masar. Amma saboda sunana na yi abin da zai kiyaye shi daga ƙazantuwa a idanun al’umman da suka zauna a ciki da kuma a idanun al’ummai da na bayyana kaina ga Isra’ilawa ta wurin fitar da su daga Masar. Saboda haka na fisshe su daga Masar na kawo su cikin hamada. Na ba su ƙa’idodina na kuma sanar musu da dokokina, gama mutumin da ya yi biyayya da su zai rayu ta wurinsu. Na kuma ba su Asabbataina kamar alama tsakaninmu, domin su san cewa Ni Ubangiji ne yake tsarkake su. “ ‘Duk da haka mutanen Isra’ila suka yi mini tawaye a cikin hamada. Ba su bi ƙa’idodina ba amma suka ki dokokina, ko da yake mutumin da ya yi biyayya da su zai rayu ta wurinsu, suka ɓata Asabbataina ƙwarai. Saboda haka na ce zan zuba hasalata a kansu in kuma hallaka su a hamada. Amma saboda sunana na yi abin da zai kiyaye shi daga ƙazantuwa a idanun al’umman da a idonsu na fisshe su. Na kuma ɗaga hannu na rantse musu a hamada cewa ba zan kawo su ƙasar da na ba su ba, ƙasa mai zub da madara da zuma, ƙasa mafi kyau cikin dukan ƙasashe, domin sun ƙi dokokina ba su kuwa bi ƙa’idodina ba suka kuma ƙazantar da Asabbataina. Gama zukatansu sun fi so su bauta wa gumakansu. Duk da haka na dube su ta tausayi ba zan hallaka su ko in kawo ƙarshensu a hamada ba. Na faɗa wa ’ya’yansu a hamada, “Kada ku bi farillai kakanninku ko ku kiyaye dokokinsu ko ku ƙazantar da kanku da gumakansu. Ni ne Ubangiji Allahnku; ku bi ƙa’idodina ku kuma kula ku kiyaye dokokina. Ku kiyaye Asabbataina da tsarki, don su zama alama tsakaninmu. Ta haka za ku san cewa ni ne Ubangiji Allahnku.” “ ‘Amma ’ya’yan suka yi mini tawaye. Ba su bi ƙa’idodina ba, ba su kula su kiyaye dokokina ba, ko da yake mutumin da ya kiyaye su zai rayu ta wurinsu, suka kuma ƙazantar da Asabbataina. Saboda haka na ce zan zuba hasalata a kansu in kuma aukar musu da fushina a hamada. Amma na janye hannuna, kuma saboda sunana na yi abin da zai kiyaye shi daga ƙazantuwa a idanun al’umman da a idonsu na fisshe su. Na kuma ɗaga hannu na rantse musu cewa zan watsar da su cikin al’ummai in kuma warwatsa su cikin ƙasashe, domin ba su kiyaye dokokina ba amma suka ƙi ƙa’idodina suka kuma ƙazantar da Asabbataina, idanunsu suka yi sha’awar gumakan kakanninsu. Na kuma ba da su ga farillan da ba su da kyau da dokokin da ba za su rayu ta wurinsu ba; na bari suka ƙazantu ta wurin kyautai, hadayar kowane ɗan fari don in cika su da abin tsoro domin su san cewa ni ne Ubangiji.’ “Saboda haka, ɗan mutum, ka yi magana da mutanen Isra’ila ka faɗa musu cewa, ‘Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa a wannan kuma kakanninku suka saɓe ni ta wurin yashe ni. Sa’ad da na kawo su cikin ƙasar da na rantse zan ba su suka kuma ga tudu mai tsawo ko itace mai ganye, a can suka miƙa hadayunsu, suka yi sadakokin da suka tsokane ni na yi fushi, suka miƙa turaren ƙanshinsu suka kuma zuba sadakokinsu na sha. Sai na ce musu, Wane ɗakin tsafi kuke tafiya?’ ” (Ana ce da shi Bama har wa yau.) “Domin haka ka faɗa wa gidan Isra’ila, ‘Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa za ku ƙazantar da kanku yadda kakanninku suka yi ne ku yi sha’awar mugayen siffofinsu? Sa’ad da kuka miƙa kyautai naku, hadayar ’ya’yanku maza a wuta, kuna cin gaba da ƙazantar da kanku da duka gumakanku har wa yau. Zan bari ku nemi shawarata, ya gidan Isra’ila? Muddin ina raye, in ji Ubangiji Mai Iko Duka, ba zan bari ku nemi shawarata ba. “ ‘Kukan ce, “Kuna so ku zama kamar sauran al’ummai, kamar sauran mutanen duniya, waɗanda suke bauta wa itace da dutse.” Amma abin da kuke tunani ba zai taɓa faruwa ba. Muddin ina raye, in ji Ubangiji Mai Iko Duka, zan yi mulki a kanku da hannu mai iko da kuma hannu mai ƙarfi da kuma fushi. Zan fitar da ku daga al’ummai in tattara ku daga ƙasashe inda aka warwatsa ku, da hannu mai iko da kuma hannu mai ƙarfi da kuma fushi. Zan kawo ku cikin hamadar al’ummai a can kuwa, fuska da fuska, zan hukunta ku. Yadda na hukunta kakanninku a hamadar ƙasar Masar, haka zan hukunta ku, in ji Ubangiji Mai Iko Duka. Zan lura da ku yayinda kuke wucewa ƙarƙashin sanda, zan kuma kawo ku cikin daurin alkawari. Zan fitar da waɗanda suke mini tayarwa da kuma ’yan tawaye. Ko da yake zan fitar da su daga ƙasar da suke zama, duk da haka ba za su shiga ƙasar Isra’ila ba. Sa’an nan za ku san cewa ni ne Ubangiji. “ ‘Game da ku, ya gidan Isra’ila, ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa ku tafi ku bauta wa gumakanku, kowannenku! Amma daga baya tabbatacce za ku saurare ni ba kuwa za ku ƙara ɓata sunana mai tsarki da hadayunku da gumakanku ba. Gama a kan dutsena mai tsarki, dutse mai tsayi na Isra’ila, in ji Ubangiji Mai Iko Duka, a can a ƙasar gidan Isra’ila gaba ɗaya za su bauta mini, a can kuwa zan karɓe su. A can zan bukaci hadayunku da sadake sadakenku mafi kyau, tare da dukan tsarkakan hadayunku. Zan karɓe ku kamar turare mai ƙanshi sa’ad da na fitar da ku daga al’ummai na kuma tattara ku daga ƙasashe inda aka warwatsa ku, zan kuma nuna kaina mai tsarki a cikinku a idon al’ummai. Sa’an nan za ku san cewa ni ne Ubangiji sa’ad da na kawo ku cikin ƙasar Isra’ila, ƙasar da na ɗaga hannu na rantse zan ba wa kakanninku. A can za ku tuna da halinku da kuma dukan ayyukanku waɗanda kuka ɓata kanku da su, za ku kuwa ji ƙyamar kanku saboda mugayen abubuwan da kuka aikata. Za ku san cewa ni ne Ubangiji, sa’ad da na yi muku haka saboda sunana ba bisa ga mugayen hanyoyinku da ayyukanku marasa kyau ba, ya gidan Isra’ila, in ji Ubangiji Mai Iko Duka.’ ” Maganar Ubangiji ta zo mini cewa, “Ɗan mutum, ka kafa fuskarka wajen kudu; ka yi wa’azi a kan kudu ka kuma yi annabci a kan kurmin ƙasar kudu. Ka faɗa wa kurmin kudanci, ‘Ji maganar Ubangiji. Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa ina gab da sa maka wuta, za tă kuwa cinye dukan itatuwanki sarai, da ɗanye da busasshe. Ba za a kashe wutar da take ci ba, kuma kowace fuska a kudu zuwa arewa za tă ƙone. Kowa zai san cewa Ni Ubangiji ne ya ƙuna ta; ba za a kashe ta ba.’ ” Sai na ce, “Kash, Ubangiji Mai Iko Duka! Suna zance a kaina cewa, ‘Ba misalai kawai yake yi ba?’ ” Maganar Ubangiji ta zo mini cewa, “Ɗan mutum, ka kafa fuskarka gāba da Urushalima ka kuma yi wa’azi a kan wuri mai tsarki. Ka yi annabci gāba da ƙasar Isra’ila ka faɗa mata, ‘Ga abin da Ubangiji ya ce ina gāba da ke. Zan ja takobina daga kubensa in karkashe adalai da mugaye daga cikinki. Domin zan karkashe adalai da kuma mugaye, ba zan rufe takobina a kan kowa daga kudu zuwa arewa ba. Sa’an nan duka mutane za su san cewa Ni Ubangiji na ja takobina daga kubensa; ba zai sāke koma kuma ba.’ “Saboda ka yi nishi, ɗan mutum! Yi nishi a gabansu da ajiyar zuciya da ɓacin rai. Kuma sa’ad da suka tambaye ka, ‘Me ya sa kake nishi?’ Sai ka ce musu, ‘Domin labarun da suke fitowa. Kowace zuciya za tă narke kowane hannu kuma ya gurgunta; kowane ruhu zai sume kowane gwiwa kuma ta rasa ƙarfi kamar ruwa.’ Yana zuwa! Tabbatacce zai faru, in ji Ubangiji Mai Iko Duka.” Maganar Ubangiji ta zo mini cewa, “Ɗan mutum, yi annabci ka ce, ‘Ga abin da Ubangiji ya faɗa, “ ‘Takobi, takobi, wasasshe da kuma gogagge, wasasshe don kisa, gogagge har yana walwal kamar walƙiya! “ ‘Kada ku yi farin ciki, hukunci yana zuwa, domin kowa ya ƙi jin abin da na yi gargaɗi a kai. “ ‘An ba da wannan takobi don a goge, don a kama da hannu; an washe shi aka kuma goge, shiryayye don a yi kisa da shi. Ka yi kuka ka yi makoki, ɗan mutum, gama yana gāba da dukan sarakunan Isra’ila. An jefa su ga takobi tare da jama’ata. Saboda haka ku buga ƙirjinku. “ ‘Gwaji tabbatacce zai zo. Kuma a ce sandan Yahuda, wanda takobi ya ƙi, ya ci gaba? In ji Ubangiji Mai Iko Duka.’ “Saboda haka fa, ɗan mutum ka yi annabci ka kuma tafa hannuwanka. Bari takobi ya yi sara sau biyu, har sau uku ma. Takobin kisa ne, takobi ne don kisa mai girma, zai kewaye su a kowane gefe. Domin zukata su narke da yawa kuma su fāɗi, na tsai da takobin kisa a dukan ƙofofinsu. Kash! A sa ya haska kamar walƙiya, ana riƙe da shi don kisa. Ya takobi, yi sara zuwa dama ka yi kuma zuwa hagu, duk inda aka juya ka. Zan tafa hannuwana, fushina kuwa zai sauka. Ni Ubangiji na faɗa.” Sai maganar Ubangiji ta zo mini cewa, “Ɗan mutum, ka nuna hanyoyi biyu inda takobin sarkin Babilon zai bi, duka biyun su fara daga ƙasa guda. Ka kafa shaida inda hanyar za tă rabu zuwa cikin birni. Ka nuna hanya guda wadda takobi zai fāɗo wa Rabba ta Ammonawa ɗayan kuma da zai fāɗo a kan Yahuda da kuma Urushalima mai katanga. Gama sarkin Babilon zai tsaya a mararrabar hanya, a inda hanyar ta rabu biyu, don yă yi duba. Zai jefa ƙuri’a da kibiyoyinsa, zai nemi shawarar gumakansa, zai bincike hanta. A hannunsa na dama ƙuri’a don Urushalima za tă fito, inda zai kafa dundurusai, ya ba da umarni kisa, a yi kururuwar yaƙi, a kafa dundurusai a kan ƙofofi, a gina mahaurai a kuma yi ƙawanya. Zai zama kamar duban ƙarya ne ga waɗanda suka yi rantsuwar yin masa biyayya, amma zai tunashe su game da laifinsu ya kuma kama su. “Saboda haka ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa, ‘Domin ku mutanen nan kun tuna da laifinku ta wurin tawaye, kun kuma bayyana zunubanku cikin dukan abin da kuke yi, domin kun yi haka, za a kama ku. “ ‘Ya kai ƙazantaccen mugu, yerima Isra’ila, wanda kwanansa ta zo, wanda lokacin hukuncinsa ya cika fal, ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa ka kunce rawanin, ka ɗauke rawanin nan. Ba zai zama kamar yadda yake ba. Za a ɗaukaka ƙasƙantacce, amma a ƙasƙantar da mai girma. Hallaka! Hallaka! Zan hallaka shi! Ba za a maido da shi ba sai ya ga ainihin mai shi; gare shi zan bayar da shi.’ “Kai kuma, ɗan mutum, ka yi annabci ka ce, ‘Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa game da Ammonawa da kuma zarginsu. “ ‘Takobi, takobi, an ja don kisa, an goge don cinyewa yana haske kamar walƙiya! Duk da wahayin ƙarya game da kai, duban ƙarya game da kai, za a sa shi a wuyan mugaye waɗanda za a kashe, waɗanda kwanansu ta zo, waɗanda lokacin hukuncinsu ya cika fal. “ ‘Ka mai da takobi a kubensa. A inda aka halicce ka, a ƙasar kakanninka, zan hukunta ka. Zan zub da hasalata a kanka in hura maka wutar fushina; Zan ba da kai a hannun mugayen mutanen da suka gwanince a hallakarwa. Za ka zama itacen wuta, za a zub da jininka a ƙasarka, ba za a ƙara tuna da kai ba; gama Ni Ubangiji na faɗa.’ ” Maganar Ubangiji ta zo mini cewa, “Ɗan mutum, za ka shari’anta ta? Za ka shari’anta wannan birni mai kisankai? To, sai ka kalubalance ta da dukan ayyukanta na banƙyama ka kuma ce, ‘Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka ya ce ya birnin da take kawo wa kansa hallaka ta wurin kisankai a cikinta kina kuma ƙazantar da kanki ta wurin yin gumaka, kin zama mai laifi saboda jinin da kika zubar kika kuma zama ƙazantacciya ta wurin gumakan da kika yi. Kin kawo kwanakinki ga ƙarshe, kuma ƙarshen shekarunki sun zo. Saboda haka zan mai da ke abar ba’a ga al’ummai da abin dariya ga dukan ƙasashe. Waɗanda suke kusa da waɗanda suke nesa za su yi miki ba’a, ya ke birni marar kunya, cike da rigima. “ ‘Duba yadda kowane yerima Isra’ila waɗanda suke cikinki yake yin amfani da ikonsa yana kisankai. A cikinki sun rena mahaifi da mahaifiya; a cikinki sun zalunci baƙo suka wulaƙanta maraya da gwauruwa. Kin rena abubuwana masu tsarki kika kuma ƙazantar da Asabbataina. A cikinki akwai mutane waɗanda suka nace su yi kisankai; a cikinki akwai waɗanda suke ci a dutsen tsafi suna yin ayyukan lalata. A cikinki akwai waɗanda suke kwana da matan mahaifansu; a cikinki akwai waɗanda suke kwana da mata a lokacin da suke al’adarsu, sa’ad da suke da rashin tsarki. A cikinki mutum guda yakan yi laifi abin ƙyama da matar maƙwabcinsa, wani cikin rashin kunya ya ƙazantar da matar ɗansa, wani kuma ya kwana da ’yar’uwansa, ’yar mahaifinsa. A cikinki mutane suna karɓan cin hanci don su yi kisankai; kina ba da rance da ruwa da ƙari, kina kuma cin riba a kan maƙwabcinki ta wurin ƙwace. Kina kuma manta da ni, in ji Ubangiji Mai Iko Duka. “ ‘Tabbatacce zan tafa hannuwana a kan ƙazamar riba da kika ci da jinin da kin zubar a cikinki. Ƙarfin halinki zai jure ko kuwa hannuwanki za su yi ƙarfi a ranar da na gamu da ke? Ni Ubangiji na faɗa, zan kuma aikata. Zan watsar da ke cikin al’ummai in warwatsa ke cikin ƙasashe; zan kuma kawo ƙarshen rashin tsarkinki. Sa’ad da ki ƙazantu a idanun al’umma, za ki san cewa ni ne Ubangiji.’ ” Sai maganar Ubangiji ta zo mini cewa, “Ɗan mutum, gidan Isra’ila ta zama ƙwan maƙera a gare ni; dukansu tagulla ne, kuza, ƙarfe da darma da suka rage a tanderu. Su ƙwan maƙerar azurfa ne kawai. Saboda haka ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa, ‘Domin ku duka kun zama ƙwan maƙera, zan tattara ku a Urushalima. Kamar yadda mutane sukan tattara azurfa, tagulla, ƙarfe, darma da kuza a cikin tanderu don su narkar da su da wuta, haka zan tattara ku cikin fushina da kuma hasalata in sa ku cikin birnin in narkar da ku. Zan tattara ku zan kuma hura muku wutar hasalata, za ku kuma narke a cikinta. Kamar yadda azurfa kan narke a tanderu, haka za ku narke a cikinta, kuma za ku san cewa Ni Ubangiji na zubo muku da zafin fushina.’ ” Har yanzu maganar Ubangiji ta zo gare ni cewa, “Ɗan mutum, ka faɗa wa ƙasar, ‘Ke ƙasa ce marar ruwan sama ko yayyafi a ranar hasala.’ Akwai haɗin bakin sarakunanki a cikinki kamar rurin zaki mai yayyage ganimarsa; suna cin mutane, suna kwashe dukiya da abubuwa masu daraja suna mai da yawanci gwauraye a cikinki. Firistocinki suna karya dokokina, sun ƙazantar da tsarkakan abubuwana; ba sa bambanta tsakanin tsarki da marar tsarki; suna koyarwa cewa babu bambanci tsakanin marar tsarki da mai tsarki; suna kuma rufe idanunsu ga kiyaye Asabbataina, da haka suke saɓon sunana. Shugabanninki a cikinki suna kama da kyarketai masu yayyage ganimarsu; suna kisa suna kuma kashe mutane don samun ƙazamar riba. Annabawanki sun yi wa waɗannan ayyuka shafe da farar ƙasa ta wurin wahayin ƙarya da duban ƙarya. Suna cewa, ‘Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa’ alhali kuwa Ubangiji bai faɗa ba. Mutanen ƙasar na yin ƙwace suna yin fashi; suna cin zalin matalauta da mabukata suna wulaƙanta baƙo suna hana musu adalci. “Na nemi mutum guda a cikinsu wanda zai gina katanga ya tsaya a gabana a tsakani a madadin ƙasar don kada in hallaka ta, amma ban sami ko ɗaya ba. Saboda haka zan zuba hasalata a kansu in cinye su da wutar fushina, ina ɗora alhakin ayyukansu a bisa kawunansu, in ji Ubangiji Mai Iko Duka.” Maganar Ubangiji ta zo mini cewa, “Ɗan mutum, an yi mata biyu, ’yan matan mahaifiya guda. Suka zama karuwai a Masar, suka yi karuwanci tun daga ƙuruciyarsu. A wancan ƙasar an rungumi mamansu da ƙirjinsu na budurwanci. Sunan babbar Ohola, ƙanuwarta kuwa Oholiba. Sun zama nawa suka kuma haifi ’ya’ya maza da mata. Ohola ita ce Samariya, Oholiba kuwa ita ce Urushalima. “Ohola ta shiga karuwanci yayinda take zamana; ta kuwa yi ta kai da kawowa da kwartayenta, Assuriyawa, mayaƙa waɗanda suke saye da shunayya, gwamnoni da manyan sojoji, dukansu samari ne masu bansha’awa, suna bisa kan dawakai. Ta ba da kanta ga duk waɗanda suke masu ilimin Assuriya ta kuma ƙazantar da kanta da dukan gumaka na kowa da take kai da kawowa a cikinsu. Ba ta bar karuwancin da ta fara a Masar ba, sa’ad da take budurwa maza sun kwana da ita, suka rungumi ƙirjinta suka kuma biya kwaɗayinsu a kanta. “Saboda haka na bashe ta ga kwartayenta, Assuriyawa, waɗanda ta yi ta kai da kawowa a cikinsu. Suka tuɓe ta tsirara, suka kwashe ’ya’yanta maza da mata suka kuma kashe ta da takobi. Ta kuwa zama abin karin magana a cikin mata, aka kuma yi mata hukunci. “Ƙanuwarta Oholiba kuwa ta ga wannan, duk da haka cikin kai da kawowarta da karuwancinta ta fi ’yar’uwar lalacewa. Ita ma ta yi ta kai da kawowa cikin Assuriyawa, gwamnoni da manyan sojoji; mayaƙa masu saye da kayan yaƙi, suna bisa dawakai, dukansu samari ne masu bansha’awa. Na ga cewa ita ma ta ƙazantar da kanta; dukansu biyu sun bi hanya guda. “Amma karuwancinta ya zarce. Ta ga an zāna mutane a kan bango, siffofin sojojin Kaldiyawa suna cikin jajjayen riguna, da ɗamara a gindinsu da rawuna a kansu suna kaɗawa falfal; dukansu sun yi kamar jarumawan kekunan yaƙin Babiloniyawa ’yan Kaldiya. Nan da nan da ta gan su, sai ta yi sha’awarsu ta aika da ’yan aika zuwa wurinsu a Kaldiya. Sai Babiloniyawan suka zo wurinta, zuwa gadon soyayya, cikin kai da kawowarsu suka ƙazantar da ita. Bayan sun ƙazantar da ita, sai ta ji ƙyamarsu, ta rabu da su. Sa’ad da ta ci gaba da yin karuwancinta a fili ta kuma nuna tsiraicinta, sai na ji ƙyamarta, na rabu da ita, kamar dai yadda na rabu da ’yar’uwarta. Duk da haka sai ta yi ta ƙara fasikanci tana tuna da kwanakin budurcinta, sa’ad da take karuwa a Masar. A can ta yi ta kai da kawowa da kwartayenta, waɗanda al’auransu kamar na jakuna ne waɗanda maniyyinsu kuwa kamar na dawakai ne. Haka kika yi ta lalacin budurcinki, sa’ad da a Masar aka rungumi ƙirjinta aka tattaɓa nononta. “Saboda haka, Oholiba, ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa zan zuga kwartayenki su yi gāba da ke, su waɗanda kika ji ƙyamarsu, zan kuma kawo su su yi gāba da ke daga kowane gefe, Babiloniyawa da dukan Kaldiyawa, mutanen Fekod da Showa da Kowa, da dukan Assuriyawa, samari masu bansha’awa, dukan gwamnoni da manyan sojoji, hafsoshin keken yaƙin da mutane masu manyan matsayi, dukansu a bisa dawakai. Za su yi gāba da ke da kayan yaƙi, kekunan yaƙi da kekunan doki da mutane masu yawa; za su ja dāgā a kanki a kowane gefe da garkuwoyi manya da ƙanana da kuma hulunan kwano. Zan miƙa ke gare su don hukunci, za su kuma hukunta ki bisa ga shari’arsu. Zan nuna fushin kishina a kanki, za su kuwa wulaƙanta ki da fushi. Za su yanke hancinki da kunnuwanki, waɗanda suka rage miki kuma za a kashe su da takobi. Za su kama ’ya’yanki maza da mata, waɗanda suka rage miki kuwa za a ƙone su da wuta. Za su tuɓe tufafinki su kuma kwashe kayan adonki masu kyau. Ta haka zan tsai da marmari da kuma karuwancin da kika fara a Masar. Ba za ki dubi waɗannan abubuwa da marmari ko ki ƙara tuna da Masar ba. “Gama ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa ina shirin miƙa ki ga waɗanda suke ƙinki, ga waɗanda kika ji ƙyamarsu kika rabu da su. Za su hukunta ki da ƙiyayya su kuma kwashe kome da kika yi wahalarsa. Za su bar ki tsirara tik, kunyan karuwancinki kuma zai tonu. Marmarinki da fasikancinki sun jawo miki wannan, domin ki yi ta kai da kawowa cikin ƙasashe kina ƙazantar da kanki da gumakansu. Kin bi hanyar ’yar’uwarki; saboda haka zan sa kwaf nata a hannunki. “Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa, “Za ki sha kwaf na ’yar’uwarki, kwaf wanda yake da girma da kuma zurfi; zai jawo dariya da kuma reni gama yana ɗauke da abubuwa da yawa. Za ki cika da buguwa da baƙin ciki, kwaf lalaci da kaɗaici, kwaf na ’yar’uwarki Samariya. Za ki sha shi ki kuma lashe shi ƙaf; za ki buga shi da ƙasa ya yi rugu-rugu ki tsattsage nononki. Ni Ubangiji Mai Iko Duka na faɗa. “Saboda haka ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa da yake kin manta da ni kika tura ni bayanki, dole ki sha sakamakon marmarinki da karuwancinki.” Ubangiji ya ce mini, “Ɗan mutum, za ka shari’anta Ohola da Oholiba? To, sai ka kalubalance su da ayyukansu masu banƙyama, gama sun yi zina kuma jinin yana a hannuwansu. Sun yi zina da gumakansu; har suka miƙa ’ya’yansu da suka haifa mini, su zama musu abinci. Sun kuma yi mini wannan. A lokaci guda sun ƙazantar da wuri mai tsarkina suka ɓata Asabbataina. A ranar da suka miƙa ’ya’yansu ga gumakansu, sai suka shiga wuri mai tsarkina suka kuma ƙazantar da shi. Abin da suka yi a gidana ke nan. “Sun ma aiki manzanni wa mutanen da suka zo daga nesa, kuma da suka iso kun yi wanka dominsu, kuka yi shafe-shafen idanunku, kuka kuma sa kayan adonku. Kuka zauna a gado mai daraja, da tebur a shirye a gabanku wanda kun ajiye turare da maina. “Surutun taron mutane marasa kula suna kewaye da ita; aka kawo Sabenawa daga hamada tare da mutane daga mashaya, suka sa mundaye a hannuwan macen da kuma ’yar’uwarta suka kuma sa rawani masu kyau a kawunansu. Sai na yi magana a kan wadda ta ƙare ƙarfi ta wurin karuwanci na ce, ‘Yanzu bari su yi amfani da ita kamar karuwa, gama abin da take ke nan.’ Suka kuwa kwana da ita. Kamar yadda maza suke kwana ta karuwa, haka suka kwana da waɗannan lalatattun mata, Ohola da Oholiba. Amma masu adalci za su hukunta su irin da akan yi wa matan da suka yi zina suka kuma yi kisa, domin su mazinata ne kuma jini yana a hannuwansu. “Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa kawo taron mutane a kansu a kuma miƙa su don a firgitar da su a kuma washe su. Taron mutanen za su jajjefe su, su kuma sassare su da takuba; za su kashe ’ya’yansu maza da mata su kuma ƙone gidajensu. “Ta haka zan kawo ƙarshe ga lalaci a ƙasar, don dukan mata su ji gargaɗi kada kuma su kwaikwaye ku Za ku sha hukuncin lalacinku ku kuma ɗauki hakkin zunuban bautar gumaka. Sa’an nan za ku san cewa Ni ne Ubangiji Mai Iko Duka.” A shekara ta tara, a wata na goma, a rana ta goma, maganar Ubangiji ta zo mini cewa, “Ɗan mutum, ka rubuta wannan rana, wannan rana, domin sarkin Babilon ya yi ƙawanya wa Urushalima a wannan rana. Ka faɗa wa wannan gidan ’yan tawaye wani misali ka kuma faɗa musu cewa, ‘Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa, “ ‘Ka sa tukunyar dahuwa; ka sa ta a kan wuta ka kuma zuba ruwa a cikinta. Ka sa gunduwoyin nama a cikinta dukan gunduwoyi masu kyau, cinya da kafaɗa. Ka cika ta da waɗannan ƙasusuwa mafi kyau; ka kama mafi kyau daga cikin garken. Ka tara itace a ƙarƙashinta saboda ƙasusuwan; ka sa ta tafasa ka kuma dafa ƙasusuwan a cikinta. “ ‘Gama wannan shi ne abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa, “ ‘Kaito birnin nan mai zubar da jini, ga tukunya wadda take da tsatsa, wadda tsatsarta ba za tă fita ba! Ka fitar da shi gunduwa-gunduwa ba tare da jefa ƙuri’a a kansu ba. “ ‘Gama zubar da jini yana a tsakiyarta, ta zubar da shi a dutsen da yake a fili; ba tă zubar da shi a ƙasa ba, inda ƙura za tă rufe shi. Don a zuga hasala a kuma yi sakayya na sa jininta a dutsen da ba a rufe ba, saboda kada a rufe. “ ‘Saboda haka ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa, “ ‘Kaito birnin nan mai zubar da jini! Ni ma zan jibge itace da yawa. Ka tula gumagumai ka kuma ƙuna wuta. Ka dafa naman da kyau, kana haɗawa da yaji; ka kuma bar ƙasusuwan su ƙone. Sa’an nan ka sa tukunyan nan da babu kome a kan garwashi sai ta yi zafi har darmarta ta yi ja wur domin dattinta ya narke tsatsarta kuma ta ƙone. Ta gajiyar da dukan ƙoƙari; ba a fid da tsatsarta nan mai yawa ba, kai, ko a wuta ma. “ ‘Yanzu ƙazantarki ita ce lalaci. Domin na yi ƙoƙari in tsabtacce ke amma ba ki tsabtattu daga ƙazantarki ba, ba za ki ƙara yin tsabta ba sai hasalata a kanki ya kwanta. “ ‘Ni Ubangiji na faɗa. Lokaci ya zo da zan aikata. Ba zan janye ba; ba zan ji tausayi ba, ba kuwa zan bari ba. Za a hukunta ki bisa ga hali da ayyukanki, in ji Ubangiji Mai Iko Duka.’ ” Maganar Ubangiji ta zo mini cewa, “Ɗan mutum, da farat ɗaya ina gab da ɗauke abin da idanunka suke jin daɗin gani. Duk da haka kada ka yi makoki ko ka yi kuka ko ka zub da hawaye. Ka yi nishi shiru; kada ka yi makoki saboda matacciyar. Ka naɗa rawaninka ka kuma sa takalmanka a ƙafa; kada ka rufe sashen fuskarka daga ƙasa ko ka ci abincin da masu kuka sukan ci.” Da gari ya waye, sai na yi magana da mutane, da yamma kuwa matata ta rasu. Kashegari na yi yadda aka umarce ni. Sai mutane suka tambaye ni suka ce, “Ba za ka faɗa mana abin da waɗannan abubuwa suke nufi a gare mu ba?” Sai na ce musu, “Maganar Ubangiji ta zo mini cewa faɗa wa gidan Isra’ila, ‘Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa ina gab da ƙazantar da wuri mai tsarkina, kagarar da kuke taƙama, abin da idanunku suke jin daɗin gani, abin faranta zuciyarku. ’Ya’yanku maza da mata waɗanda kun bari a baya za su mutu ta wurin takobi. Za ku kuma yi yadda na yi. Ba za ku rufe sashe ƙasa na fuskarku ko ku ci abinci da masu kuka sukan ci ba. Za ku naɗa rawunanku a kai ku sa takalmanku a ƙafafunku. Ba za ku yi kuka ko makoki ba amma za ku lalace saboda zunubanku ku kuma yi ta yin nishi. Ezekiyel zai zama alama gare ku; za ku yi daidai yadda ya yi. Sa’ad da wannan ya faru, za ku san cewa ni ne Ubangiji Mai Iko Duka.’ “Kai kuma ɗan mutum, a ranar da zan ɗauke musu kagararsu, farin cikinsu da darajarsu, abin da idanunsu ke jin daɗin gani, abin da yake faranta musu zuciya, da kuka ’ya’yansu maza da mata, a ranan nan wanda ya tsere zai zo don yă ba ka labari. A lokacin bakinka zai buɗe, za ka yi magana da shi ba kuwa za ka ƙara yin shiru ba. Ta haka za ka zama alama gare su, za su kuwa san cewa ni ne Ubangiji.” Maganar Ubangiji ta zo mini cewa, “Ɗan mutum, ka fuskanci wajen Ammonawa ka kuma yi annabci a kansu. Ka ce musu, ‘Ku ji maganar Ubangiji Mai Iko Duka. Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa domin kun ce “Yauwa” a kan wuri mai tsarkina sa’ad da aka ƙazantar da shi da kuma a kan ƙasar Isra’ila sa’ad da aka mai da ita kufai da lokacin da aka kai mutanen Yahuda bautar talala, saboda haka zan ba da ku ga mutanen Gabas abin mallaka. Za su kafa sansanoninsu su yi tentunansu a cikinku; za su ci ’ya’yan itatuwanku su kuma sha madararku. Zan mai da Rabba wurin kiwo don raƙuma, Ammon kuma wurin hutu don tumaki. Sa’an nan za ku san cewa ni ne Ubangiji. Gama ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa domin kun tafa hannuwanku kuka kuma buga ƙafafunku, kuna farin ciki don nuna dukan ƙiyayyarku a kan ƙasar Isra’ila, saboda haka zan miƙa hannuna gāba da ku in kuma ba da ku ganima ga al’ummai. Zan datse ku daga al’ummai in kuma kore ku daga ƙasashe. Zan hallaka ku, za ku kuwa san cewa ni ne Ubangiji.’ ” “Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa, ‘Domin Mowab da Seyir sun ce, “Duba, gidan Yahuda ta zama sauran al’ummai,” saboda haka zan buɗe ƙofar shiga Mowab, farawa daga garuruwan da suke kan iyaka, Bet-Yeshimot, Ba’al-Meyon da Kiriyatayim, darajar ƙasar. Zan ba da Mowabawa tare da Ammonawa ga mutanen Gabas abin mallaka, don kada a ƙara tuna da Ammonawa a cikin al’ummai; zan hukunta Mowabawa. Ta haka za su san cewa ni ne Ubangiji.’ ” “Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa, ‘Domin Edom ya ɗauki wa kanta fansa a kan gida Yahuda, ta yi babban laifi ta wurin yin haka, saboda haka ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa zan miƙa hannuna a kan Edom in kashe mutanenta da dabbobinsu. Zan sa ta zama kufai, kuma tun daga Teman har zuwa Dedan za a kashe su da takobi. Zan ɗau fansa a kan Edom ta hannun mutanena Isra’ila, za su kuwa hukunta Edom bisa ga fushina da hasalata; za su san sakayyata, in ji Ubangiji Mai Iko Duka.’ ” “Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa, ‘Domin Filistiyawa sun yi sakayya, suka ɗauki fansa da mugunta a zukatansu, da kuma daɗaɗɗen ƙiyayya sun nemi su hallaka Yahuda, saboda haka ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa ina gab da miƙa hannuna a kan Filistiyawa, zan kuwa datse Keretawa in kuma hallaka waɗanda suka rage a bakin teku. Zan yi musu babbar sakayya da hukunci mai tsanani cikin hasalata. Sa’an nan za su san cewa ni ne Ubangiji, sa’ad da na ɗauki fansa a kansu.’ ” A shekara ta goma sha ɗaya, a rana ta fari ga wata, maganar Ubangiji ta zo mini cewa, “Ɗan mutum, domin Taya ta yi magana a kan Urushalima ta ce, ‘Yauwa! Ƙofar zuwa al’ummai ta karye, an kuma buɗe mini ƙofofinta; yanzu da take kufai zan wadace,’ saboda haka ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa ina gāba da ke, ya Taya, zan kuwa kawo al’ummai masu yawa su yi gāba da ke, kamar yadda teku takan kawo raƙuman ruwa. Za su hallaka katangar Taya su kuma rurrushe hasumiyoyinta; zan kankare tarkacenta, in maishe ta fā. Za tă zama wurin shanya abin kamun kifi a tsakiyar teku, gama na faɗa, in ji Ubangiji Mai Iko Duka. Za tă zama ganima ga sauran al’ummai, za a kashe mazaunan filin ƙasar da takobi. Ta haka za su san cewa ni ne Ubangiji. “Gama ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa daga arewa zan kawo wa Taya Nebukadnezzar sarkin Babilon, sarkin sarakuna, tare da dawakai da kekunan yaƙi, da mahayan dawakai da babbar rundunar soja. Zai kashe mazaunan filin ƙasar da takobi; zai yi miki ƙawanya, ya gina miki mahaurai, sa’an nan ya rufe ki da garkuwoyi. Zai rushe katangarki da dundurusai, ya rurrushe hasumiyoyinki da makamai. Dawakansa za su yi yawa har su rufe ke da ƙura. Katanga za su girgiza saboda motsin dawakan yaƙi, kekunan doki da keken yaƙin sa’ad da suka shiga birnin da aka rushe katangar. Kofatan dawakansa za su tattake dukan titunanki; zai kashe mutanenki da takobi, ginshiƙanki masu ƙarfi kuma za su fāɗi a ƙasa. Za su washe dukiyarki, kayan cinikinki kuma su zama ganima; za su rurrushe katangarki su ragargaza gidajenki masu kyau su kuma zubar da duwatsunki, katakanki da kuma tarkacenki a cikin teku. Zan kawo ƙarshen waƙoƙinki masu surutu, ba kuwa za a ƙara jin kaɗe-kaɗen garayunki ba. Zan maishe ki fā, za ki kuma zama wurin shanya abin kamun kifi. Ba za a sāke gina ki ba, gama Ni Ubangiji na faɗa, in ji Ubangiji Mai Iko Duka. “Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa wa Taya. Ƙasashen da suke a bakin teku ba za su girgiza saboda ƙarar fāɗuwarki, sa’ad da nishin waɗanda aka yi wa rauni da kashe-kashen da aka yi a cikinki suka faru ba? Sa’an nan sarakunan bakin teku za su sauka daga gadajen sarautarsu, su tuɓe rigunansu, da rigunansu waɗanda aka yi wa ado. Za su zauna a ƙasa suna rawar jiki a kowane lokaci suna razana saboda abin da ya same ki. Sa’an nan za su yi makoki game da ke su ce, “ ‘Yaya kika hallaka haka nan, ya birnin da ta yi suna, cike da mutanen teku! Ke da kika zama mai ƙarfi cikin tekuna, ke da mazauna cikinki; kin sa tsoronki a kan dukan waɗanda suka zauna a can. Yanzu tsibirai suna rawar jiki a ranar fāɗuwarki; tsibirai a cikin teku sun tsorata a ɓacewarki.’ “Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa sa’ad da na maishe ki kufai, kamar sauran biranen da ba a ƙara zama a ciki, sa’ad da kuma na kawo zurfafan teku a kanki da yawan ruwansa suka rufe ki, a sa’an nan zan sauko da ke ƙasa tare da waɗanda suke gangarawa zuwa rami, zuwa wurin mutanen dā. Zan sa ki zauna ƙarƙashin ƙasa, kamar a kufai na tun dā, tare da waɗanda suke gangarawa zuwa rami, ba kuwa za ki ƙara dawowa ba ko ki ɗauki matsayinki a ƙasar masu rai. Zan sa ki yi mummunan ƙarshe kuma ba za ki ƙara kasancewa ba. Za a neme ki, amma ba za a ƙara same ki ba, in ji Ubangiji Mai Iko Duka.” Maganar Ubangiji ta zo mini cewa, “Ɗan mutum, ka yi makoki domin Taya. Ka ce wa Taya, wadda take zaune a hanyar shiga zuwa teku, kasuwar masu yawa mutane a bakin teku, ‘Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa, “ ‘Kin ce, ya Taya, “Ni kyakkyawa ce cikakkiya.” Manyan tekuna ne wurin zamanki; maginanki sun sa kyanki ya zama cikakke. Sun yi dukan katakanki daga itatuwan fir daga Senir; sun kwaso itatuwan al’ul daga Lebanon don su yi miki jigon jirgin ruwa. Da oak daga Bashan suka yi sandunan tuƙan jirgin ruwa da itatuwan kasharina daga bakin tekun Saifurus suka yi daɓe jirgin ruwanki, suka kuma manne masa hauren giwa. Lilin mai kyau mai ado daga Masar ne filafilan jirgin ruwanki suka kuma zama tutarki; an yi tutarki da shuɗi da shunayya daga bakin tekun Elisha. Mutanen Sidon da Arfad su ne matuƙan jirgin ruwanki; gwanayenki, ya Taya, suna ciki a matsayi matuƙan jiragen ruwa. Masu hikima na Gebal suna ciki a matsayin masu tattoshe mahaɗan katakon jirginki. Dukan jiragen ruwa da matuƙansu sukan zo wurinki don kasuwanci. “ ‘Mutanen Farisa, Lidiya da Fut su ne suka zama sojoji a cikin mayaƙanki. Sun rataye garkuwoyinsu da hulunan kwano a katangarki, suna kawo miki daraja. Mutanen Arfad da Helek sun yi tsaron katangar a kowace gefe; mutanen Gammad su ne a hasumiyoyinki. Sun rataye garkuwoyinsu kewaye da katangarki; sun sa kyanki ya zama cikakke. “ ‘Tarshish ta yi ciniki da ke saboda yawan wadatar kayayyakinki; sun sayi kayan cinikinki da azurfa, ƙarfe, kuza da dalma. “ ‘Girka, Tubal da Meshek sun yi kasuwanci da ke; sun sayi kayanki suka biya da bayi da kuma abubuwan da aka yi da tagulla. “ ‘Mutanen Bet Togarma sun sayi kayan cinikinki da dawakai, dawakan yaƙi da alfadarai. “ ‘Mutanen Dedan sun yi kasuwanci da ke, bakin teku masu yawa abokan cinikinki ne; sun biya ki da hauren giwa da katakon kanya. “ ‘Mutanen Aram sun yi ciniki da ke saboda yawan kayanki; suka sayi kayan cinikinki da zumurrudu, da shunayya, da kayan ado, da lilin mai taushi, da murjani, da yakutu. “ ‘Yahuda da Isra’ila sun yi kasuwanci da ke; sun sayi kayanki da alkama da Minnit da alawa, da zuma, da mai, da ganyaye masu ƙanshi. “ ‘Mutanen Damaskus sun ga abin da za ki iya bayarwa sai suka yi ciniki da ke, ta sayi kayanki da ruwan inabi daga Helbon, da ulu daga Zahar. Wedan da Yaban kusa da Uzal, suka sayi kayanki; wato gyararren ƙarfe da kayan yaji. “ ‘Mutanen Dedan sun sayi kayanki da sirdin zama a kan dawakai. “ ‘Mutanen Arabiya da dukan sarakunan Kedar abokan cinikinki ne; sun yi ciniki da ke suka sayi kayanki da ’yan raguna, da raguna, da awaki. “ ‘’Yan kasuwan Sheba da Ra’ama sun yi ciniki da ke; suka sayi kayanki da kayan yaji mafi kyau iri-iri, da duwatsu masu daraja iri-iri, da zinariya. “ ‘Haran, Kanne da Eden da kuma ’yan kasuwan Sheba, Assuriya da Kilmad sun yi ciniki da ke. A kasuwarki sun yi ciniki da ke suka sayar miki tufafi masu tsada, da na shuɗi, da masu ado, da dardumai masu ƙyalƙyali da kirtani, da igiyoyi waɗanda aka tuƙa da kyau. “ ‘Jiragen ruwan Tarshish sun zama masu jigilar kayanki. Kin cika da kaya masu nauyi a tsakiyar teku. Matuƙan jiragenki sun kai ki can cikin manyan tekuna. Amma iskar gabas za tă farfasa ki kucu-kucu a tsakiyar teku. Dukiyarki, cinikinki da kayan kasuwarki, ma’aikatanki na jirgi, matuƙan jiragenki da masu tattoshe mahaɗan katakan jiragenki, ’yan kasuwarki da dukan sojojinki, da kuma kowa da yake cikin jirgi zai nutsa a tsakiyar teku a ranar da jirginki zai nutse. Ƙasashen bakin teku za su girgiza sa’ad da matuƙan jirginki suka yi kuka. Dukan waɗanda suke riƙe da matuƙi za su ƙyale jiragensu; ma’aikatan jirage da dukan matuƙan jirage za su tsaya a bakin teku. Za su tā da muryarsu su yi kuka mai zafi a kanki; za su yayyafa ƙura a kawunansu, su yi ta birgima a cikin toka. Za su aske kawunansu saboda ke za su kuma sa tufafin makoki. Za su yi kuka dominki su yi ɓacin rai da kuma kuka mai zafi. Yayinda suke kuka a kanki kuwa, za su yi makoki dominki suna cewa, “Wa ya taɓa yin shiru kamar Taya, kewaye da teku?” Sa’ad da kayan cinikinki suka tafi ƙasashen hayi, kin gamsar da al’ummai masu yawa; da dukiyarki masu yawa da kuma kayan cinikinki kin azurtar da sarakunan duniya. Yanzu teku ta farfashe ki cikin zurfafan ruwaye; kayan cinikinki da dukan kamfaninki sun nutse tare da ke. Dukan mazaunan bakin teku sun giggice saboda masifarki; sarakunansu sun tsorata ƙwarai fuskokinsu kuwa sun yamutse don tsoro. ’Yan kasuwa a cikin al’ummai suna yin miki tsaki; kin zo ga mummunar ƙarshe ba za ki ƙara kasancewa ba har abada.’ ” Maganar Ubangiji ta zo mini cewa, “Ɗan mutum, ka faɗa wa mai mulkin Taya cewa, ‘Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa, “ ‘Cikin alfarmar zuciyarka ka ce, “Ni allah ne; ina zama a kan kursiyin allah a tsakiyar tekuna.” Amma kai mutum ne ba allah ba, ko da yake ka ɗauka kana da hikima kamar allah. Ka fi Daniyel hikima ne? Ba asirin da yake ɓoye a gare ka? Ta wurin hikimarka da ganewarka ka sami dukiya wa kanka ka kuma tara zinariya da azurfa cikin wuraren ajiyarka. Ta wurin dabararka mai girma cikin kasuwanci ka ƙara dukiyarka, kuma saboda dukiyarka zuciyarka ta cika da alfarma. “ ‘Saboda haka ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa, “ ‘Domin ka ɗauka kai mai hikima ne, mai hikima kamar allah, zan kawo baƙi a kanka, waɗanda suka fi mugunta cikin sauran al’ummai; za su zāre takubansu a kan kyakkyawar hikimarka su kuma ɓarke darajarka mai walƙiya. Za su jefar da kai cikin rami, za ka kuwa yi muguwar mutuwa a tsakiyar tekuna. Za ka iya ce yanzu, “Ni allah ne,” a gaban waɗanda suka kashe ka? Za ka zama mutum kurum, ba allah ba, a hannuwan waɗanda suka kashe ka. Za ka yi mutuwar marar kaciya a hannuwan baƙi. Na faɗa, in ji Ubangiji Mai Iko Duka.’ ” Maganar Ubangiji ta zo mini cewa, “Ɗan mutum, ka yi makoki domin sarkin Taya ka kuma ce masa, ‘Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa, “ ‘Ka kasance hatimin cikakke, cike da hikima da cikakke a kyau. Ka kasance a Eden, a lambun Allah; aka yi maka ado da kowane dutse mai daraja, yakutu, tofaz, da zumurrudu, kirisolit, onis da yasfa, saffaya, turkuwoyis da beril. Tsare-tsare da shirye-shiryenka an yi su da zinariya ne; a ranar da aka halicce ka an shirya su. An shafe ka kamar kerub mai tsaro, gama haka na naɗa ka. Kana a tsattsarkan dutsen Allah; ka yi tafiya a tsakiyar duwatsun wuta. Ka kasance marar laifi cikin dukan hanyoyinka daga ranar da aka halicce ka sai da aka sami mugunta a cikinka. Ta wurin yawan kasuwancinka ka cika da rikici, ka kuma yi zunubi. Saboda haka na kore ka da kunya daga dutsen Allah, na kore ka, ya kerub mai tsaro, daga cikin duwatsun wuta. Zuciyarka ta cika da alfarma saboda kyanka, ka kuma lalace hikimarka saboda darajarka. Saboda haka na jefar da kai zuwa ƙasa; na sa ka zama abin kallo a gaban sarakuna. Ta wurin yawan zunubanka da kasuwancinka na cuta ka ƙazantar da wuri mai tsarkinka. Saboda haka na sa wuta ta fito daga cikinka, ta cinye ka, na maishe ka toka a bisa ƙasa a kan idon dukan waɗanda suke kallonka. Dukan al’umman da suka san ka sun giggice saboda masifar da ta auko maka; ka zo ga mummunar ƙarshe ba za ka ƙara kasancewa ba har abada.’ ” Maganar Ubangiji ta zo mini cewa, “Ɗan mutum, ka fuskanci Sidon; ka yi annabci a kanta ka ce, ‘Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa, “ ‘Ina gāba da ke, ya Sidon, zan sami ɗaukaka a cikinki. Za su san cewa ni ne Ubangiji, sa’ad da na zartar da hukunci a kanta na kuma nuna kaina mai tsarki a cikinta. Zan aika da annoba a kanta in kuma sa jini ya zuba a titunanta. Kisassu za su fāɗi a cikinta, da takobi yana gāba da ita a kowane gefe. Sa’an nan za su san cewa ni ne Ubangiji. “ ‘Mutanen Isra’ila ba za su ƙara kasance da mugayen maƙwabta waɗanda za su zama sarƙaƙƙiya masu zafi da ƙaya mai tsini ba. Sa’an nan za su san cewa ni ne Ubangiji Mai Iko Duka. “ ‘Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa sa’ad da na tattara mutanen Isra’ila daga al’ummai inda suke a warwatse, zan nuna kaina mai tsarki a cikinsu a idon al’ummai. Sa’an nan za su zauna a ƙasarsu, wadda na ba wa bawana Yaƙub. Za su zauna a can lafiya su kuma gina gidaje su nome gonakin inabi; za su zauna lafiya sa’ad da zan zartar da hukunci a kan dukan maƙwabtansu da suka wulaƙanta su. Sa’an nan za su san cewa ni ne Ubangiji Allahnsu.’ ” A shekara ta goma, a wata na goma, a rana ta goma sha biyu, maganar Ubangiji ta zo mini cewa, “Ɗan mutum, ka fuskanci Fir’auna sarkin Masar ka kuma yi annabci gāba da shi da dukan Masar. Yi masa magana ka ce, ‘Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa, “ ‘Ina gāba da kai, Fir’auna sarkin Masar, kai babban mugun dodon ruwa kwance cikin rafuffukanka. Ka ce, “Nilu nawa ne; na yi shi wa kaina.” Amma zan sa ƙugiyoyi a muƙamuƙanka in sa kifin rafuffukanka su manne wa kamɓorinka. Zan jawo ka daga cikin tsakiyar rafuffukanka, da dukan kifayen rafuffukanka, waɗanda suka manne a ƙamborinka, Zan bar ka a cikin hamada, kai da dukan kifin rafuffukanka. Za ka fāɗi a fili ba kuwa za a tattara ka ko a kwashe ba. Zan ba da kai kamar abinci ga namun jeji na duniya da tsuntsayen sararin sama. Ta haka dukan waɗanda suke zama a Masar za su san cewa ni ne Ubangiji. “ ‘Ka zama sandan iwa domin gidan Isra’ila. Sa’ad da suka kama ka da hannuwansu, ka tsattsage, ka kuma buɗu a kafaɗunsu; sa’ad da suka jingina a kanka, sai ka karye, bayansu kuwa ya firgita. “ ‘Saboda haka ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa zan kawo takobi a kanka in kashe mutane da dabbobi. Masar za tă zama kufai. Sa’an nan za su san cewa ni ne Ubangiji. “ ‘Domin ka ce, “Nilu nawa ne; ni na yi shi,” saboda haka ina gāba da kai da rafuffukanka, zan kuma maishe ƙasar Masar ta lalace ta kuma zama kango daga Migdol zuwa Aswan, har iyakar Kush. Ba ƙafar mutum ko ta dabbar da za tă ratsa ta; ba wanda zai zauna a can har shekaru arba’in. Zan mai da ƙasar Masar kufai a cikin ƙasashen da aka ragargaza, biranenta kuma za su zama kango har shekaru arba’in a cikin biranen da aka lalace. Zan watsar da Masarawa a cikin al’ummai in warwatsa su cikin ƙasashe. “ ‘Duk da haka ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa a ƙarshen shekaru arba’in ɗin zan tattara Masarawa daga al’ummai inda aka warwatsa su. Zan komo da su daga zaman bauta in mai da su zuwa Masar ta Bisa, ƙasarsu ta ainihi. A can za su zama masarauta marar ƙarfi. Za tă zama masarauta mafi rarrauna cikin masarautai, ba kuwa za tă ƙara ɗaga kanta a kan sauran al’ummai ba. Zan sa tă zama marar ƙarfi ƙwarai, har da ba za tă ƙara yin mulkin a kan al’ummai ba. Masar ba za tă ƙara zama abin dogara ga mutanen Isra’ila ba amma za tă zama abin tunin zunubinsu na juyawa gare ta don taimako. Sa’an nan za su san cewa ni ne Ubangiji Mai Iko Duka.’ ” A shekara ta ashirin da bakwai, a wata na fari a rana ta farko, maganar Ubangiji ta zo mini cewa, “Ɗan mutum, Nebukadnezzar sarkin Babilon ya sa sojojinsa su matsa wa Taya; kowane kai ya koɗe, kowace kafaɗa kuma ta goge. Duk da haka shi da sojojinsa ba su sami wani lada daga matsin da suka yi a kan Taya ba. Saboda haka ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa zan ba da Masar ga Nebukadnezzar sarkin Babilon, zai washe dukiyarta. Zai kwashe ya washe ƙasar ganima a matsayin abin biyan sojojinsa. Saboda haka na ba shi Masar a matsayin lada don ƙoƙarinsa domin shi da sojojinsa sun yi wannan domina ne, in ji Ubangiji Mai Iko Duka. “A wannan rana zan sa ƙaho ya tsiro wa gidan Isra’ila, zan kuma buɗe bakinka a cikinsu. Sa’an nan za su san cewa ni ne Ubangiji.” Maganar Ubangiji ta zo mini cewa, “Ɗan mutum, ka yi annabci ka ce, ‘Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa, “ ‘Yi kuka kana cewa, “Kaito saboda wannan rana!” Gama ranar ta yi kusa, ranar Ubangiji ta gabato, ranar gizagizai, lokacin hallaka wa al’ummai. Takobi zai zo a kan Masar, azaba za tă zo a kan Kush. Sa’ad da kisassu za su fāɗi a Masar, za a kwashe dukiyarta a tafi a rushe harsashinta. Kush da Fut, Lidiya da dukan Arabiya, Libiya da kuma mutanen ƙasar alkawari za su mutu ta wurin takobi tare da Masar. “ ‘Ga abin da Ubangiji ya faɗa, “ ‘Waɗanda suke goyon bayan Masar za su fāɗi ƙarfinta da take fariya da shi zai ƙare. Daga Migdol zuwa Aswan za su mutu ta wurin takobi a cikinta, in ji Ubangiji Mai Iko Duka. Za su zama kango a cikin ƙasashen da suke kango, biranensu kuwa za su zama kufai a cikin biranen da suka lalace. Sa’an nan za su san cewa ni ne Ubangiji, sa’ad da suka ga na sa wuta wa Masar aka kuma ragargaza masu taimakonta. “ ‘A wannan rana manzanni za su fito daga wurina a jiragen ruwa don su tsorata Kush daga sake jikinta. Azaba za tă kama su a ranar hallakar Masar, gama tabbatacce za tă zo. “ ‘Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa, “ ‘Zan kawo ƙarshen mutanen Masar ta hannun Nebukadnezzar sarkin Babilon. Shi da sojojinsa, mafi bantsoro cikin al’ummai, za a kawo don su hallaka ƙasar. Za su zāre takuba a kan Masar su kuma cika ƙasar da kisassu. Zan kafe rafuffukan Nilu in sayar da ƙasar ga mugayen mutane; ta hannun baƙi zan sa ƙasar ta lalace da kome da yake cikinta. Ni Ubangiji na faɗa. “ ‘Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa, “ ‘Zan hallaka gumaka in kuma kawo ƙarshen siffofi a Memfis. Ba za a ƙara samun yerima a ƙasar Masar ba, zan kuma baza tsoro a duk fāɗin ƙasar. Zan lalace Masar ta Bisa in ƙuna wuta wa Zowan in zartar da hukunci a kan Tebes. Zan kwarara hasalata a kan Felusiyum, kagarar Masar, in kuma datse mutanen Tebes. Zan ƙuna wuta wa Masar; Felusiyum za tă sha azaba mai zafi. Za a tayar wa Tebes da hankali; Memfis za tă riƙa kasance cikin ɓacin rai. Samarin Heliyofolis da Bubastis za su mutu ta wurin takobi, biranen kansu za su tafi bauta. Duhu ne zai zama rana a Tafanes sa’ad da na karye ikon Masar; a can ƙarfin da take fariya zai ƙare. Za a rufe ta da gizagizai ƙauyukanta kuma za su tafi bauta. Ta haka zan zartar da hukunci a kan Masar, za su kuwa san cewa ni ne Ubangiji.’ ” A shekara ta goma sha ɗaya, a wata na fari a rana ta goma sha bakwai, maganar Ubangiji ta zo mini cewa, “Ɗan mutum, na karye hannun Fir’auna sarkin Masar. Ba a daure shi don warkarwa ba ko a sa tsinke saboda kada yă zama da ƙarfi har ya riƙe takobi. Saboda haka ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa ina gāba da Fir’auna sarkin Masar. Zan karye hannuwansa biyu, hannun da yake da kyau da kuma wanda an riga an karya, in kuma sa takobi ya fāɗi daga hannunsa. Zan watsar da Masarawa a cikin al’ummai in warwatsa su cikin ƙasashe. Zan ƙarfafa hannuwan sarkin Babilon in kuma sa takobina a hannunsa, amma zan karya hannuwan Fir’auna, zai kuwa yi nishi a gabansa kamar mutumin da aka yi wa raunin mutuwa. Zan ƙarfafa hannuwan sarkin Babilon, amma hannuwan Fir’auna za su shanye. Sa’an nan za su san cewa ni ne Ubangiji, sa’ad da na sa takobi a hannun sarkin Babilon na kuma miƙa shi a kan Masar. Zan watsar da Masarawa a cikin al’ummai in warwatsa su cikin ƙasashe. Sa’an nan za su san cewa ni ne Ubangiji.” A shekara ta goma sha ɗaya, a wata na uku a rana ta farko, maganar Ubangiji ta zo mini cewa, “Ɗan mutum, faɗa wa Fir’auna sarkin Masar da jama’arsa cewa, “ ‘Da wa za a kwatanta girmanka? Ka dubi Assuriya, ta taɓa zama kamar al’ul a Lebanon da rassa masu kyau suna inuwartar da kurmi; ya yi tsayi ainun kansa ya kai cikin gizagizai. Ruwa ya sa ya yi girma, zurfafan maɓulɓulai sun sa ya yi tsayi; rafuffuka suna gudu kewaye da tushensa yana aika da rafuffukansa zuwa dukan itatuwan kurmi. Saboda haka ya yi tsayi fiye da sauran itatuwan kurmi; rassansa suka ƙaru suka yi tsayi, suka bazu saboda yalwar ruwaye. Dukan tsuntsayen sararin sama suka yi sheƙa a rassansa, dukan namun jeji suka haihu a ƙarƙashin rassansa; dukan al’ummai suka zauna a inuwarsa. Yana da girma a kyau, da dogayen rassansa da ya baza, gama saiwoyinsa sun nutse can ƙasa har cikin yalwar ruwaye. Al’ul a cikin lambun Allah ba su kai shi ba, balle itatuwan kasharina su kai rassansa, ko itatuwan durumi su kai rassansa, ko itace a lambun Allah ya kai kyansa. Na sa ya yi kyau da yalwar rassa, abin ƙyashi na dukan itatuwan Eden a lambun Allah. “ ‘Saboda haka ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa domin ya yi tsayi, kansa kuma ya kai cikin gizagizai, kuma domin ya yi fariya saboda tsayinsa, na miƙa shi ga mai mulkin al’ummai, don yă sāka masa gwargwadon muguntarsa. Na jefar da shi a gefe, kuma baƙi mafi mugunta na al’ummai suka sare shi suka bar shi. Rassansa sun fāɗi a kan duwatsun da suke cikin dukan kwaruruka; rassansa kuma sun kakkarye, sun fāɗi a cikin dukan magudanan ruwa na ƙasa. Dukan al’umman duniya suka fito daga ƙarƙashin inuwarsa suka bar shi. Dukan tsuntsaye sararin sama suka zauna a itacen da ya fāɗi, dukan namun jeji kuma suna cikin rassansa. Saboda haka ba wani daga cikin itatuwan da suke kusa da ruwan da zai taɓa yin fariyar tsawonsa, har kawunansu su kai cikin gizagizai. Ba wani daga cikin itatuwan da ya sha ruwa sosai da zai taɓa yi wannan tsayi; duk an bashe su ga mutuwa, zuwa can ƙasa, a cikin matattu, tare da waɗanda suka gangara zuwa rami. “ ‘Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa a ranar da aka yi ƙasa da shi zuwa kabari na rufe zurfafa maɓulɓulai da makoki dominsa; na janye rafuffukansa, aka kuma hana yalwan ruwansa. Saboda shi na rufe Lebanon da baƙin ciki, dukan itatuwan kurmi suka bushe. Na sa al’ummai suka yi rawar jiki da jin ƙarar fāɗuwarsa sa’ad da na yi ƙasa da shi zuwa kabari tare da waɗanda suka gangara rami. Sai dukan itatuwan Eden, zaɓaɓɓu da kuma mafi kyau na Lebanon, dukan itatuwan da aka yi musu banruwa, sun ta’azantu a ƙarƙashin ƙasa. Waɗanda suka zauna a inuwarsa, dukan masu tarayyarsa a cikin al’ummai, su ma sun gangara zuwa kabari tare da shi, sun haɗu da waɗanda aka kashe da takobi. “ ‘Da wa cikin itatuwan Eden za a kwatanta da kai cikin girma da daraja? Duk da haka kai ma, za a yi ƙasa da kai tare da itatuwan Eden zuwa ƙarƙashin ƙasa; za ka kwanta a cikin marasa kaciya, tare da waɗanda aka kashe da takobi. “ ‘Fir’auna ke nan da dukan jama’arsa, in ji Ubangiji Mai Iko Duka.’ ” A shekara ta goma sha biyu, a wata na goma sha biyu a rana ta fari, maganar Ubangiji ta zo mini cewa, “Ɗan mutum, ka yi makoki a kan Fir’auna sarkin Masar ka faɗa masa. “ ‘Kai kamar zaki ne a cikin al’ummai; kai kamar dodon ruwa a cikin tekuna kana ɓullowa cikin rafuffukanka, kana gurɓata ruwa da ƙafafunka kana kuma dama rafuffuka. “ ‘Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa, “ ‘Da taron jama’a masu yawa zan jefa abin kamun kifi a kanka, za su kuwa jawo ka da abin kamun kifi. Zan jefar da kai a ƙasa zan jefa ka a fili. Zan sa dukan tsuntsayen sararin sama su zauna a kanka dukan namun jeji na duniya kuma za su ƙosar da kansu a kanka. Zan baza namanka a kan duwatsu in kuma cika kwaruruka da gawarka. Zan jiƙa ƙasar da jininka mai gudu har zuwa duwatsu, magudanan ruwa za su cika da namanka. Sa’ad da na shafe ka, zan rufe sammai in duhunta taurarinsu; zan rufe rana da girgije, wata kuwa ba zai ba da haskensa ba. Dukan haskokin sammai za su zama duhu a kanka; zan kawo duhu a kan ƙasarka, in ji Ubangiji Mai Iko Duka. Zan dami zukatan mutane masu yawa sa’ad da na kawo maka hallaka a cikin al’ummai, a cikin ƙasashen da ba ka taɓa sani ba. Zan sa mutane da yawa su giggice saboda abin da ya same ka, sarakunansu kuma za su yi rawar jiki saboda kai sa’ad da na kaɗa takobina a gabansu. A ranar fāɗuwarka kowannensu zai yi rawar jiki a kowane lokaci saboda ransa. “ ‘Gama ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa, “ ‘Takobin sarkin Babilon zai auko maka. Zan sa jama’arka su mutu ta wurin takuban ƙarfafan mutane, masu bantsoro na dukan al’ummai. Za su lalatar da girman kan Masar, su kuma tumɓuke dukan jama’arta. Zan hallaka dukan dabbobinta da suke kusa da ruwaye masu yawa ƙafar mutum ba zai ƙara damunsa ko kofaton dabba ya gurɓata shi. Sa’an nan zan sa ruwanta su kwanta in sa rafuffukanta su gudu kamar mai, in ji Ubangiji Mai Iko Duka. Sa’ad da na mai da Masar kufai na kuma raba ƙasar da abin da take cike da shi, sa’ad da na bugi dukan waɗanda suke cikinta, a sa’an nan ne za su san cewa ni ne Ubangiji.’ “Wannan ne makokin da za a yi mata. ’Yan matan al’ummai za su rera shi; gama Masar da dukan jama’arta za su rera shi, in ji Ubangiji Mai Iko Duka.” A shekara ta goma sha biyu, a rana ta goma sha biyar ga wata, maganar Ubangiji ta zo mini cewa, “Ɗan mutum, yi kuka saboda jama’ar Masar ka kuma tura ta da ’yan matan manyan al’ummai zuwa ƙarƙashin ƙasa, tare da waɗanda suka gangara zuwa rami. Ka ce, ‘Kin fi sauran tagomashi ne? Ki gangara, ki kwanta cikin marasa kaciya.’ Za su fāɗi cikin waɗanda aka kashe da takobi. Takobin da an zāre; bari a ja ta a tafi tare da dukan jama’arta. Daga cikin kabari manyan shugabanni za su yi maganar Masar da abokanta su ce, ‘Sun gangara sun kuma kwanta da marasa kaciya, tare da waɗanda aka kashe da takobi.’ “Assuriya tana can tare da dukan sojojinta; an kewaye ta da kaburburan dukan waɗanda aka kashe, dukan waɗanda suka mutu ta wurin takobi. Kaburburansu suna cikin zurfafan rami kuma sojojinta suna kwance kewaye da kabarinta. Dukan waɗanda suka haddasa tsoro a ƙasar masu rai sun mutu, an kashe su da takobi. “Elam tana can, tare da dukan jama’arta kewaye da kabarinta. Dukansu sun mutu, an kashe su da takobi. Dukan waɗanda suka haddasa tsoro a ƙasar masu rai sun gangara wurin marasa kaciya a duniyar da take ƙarƙashi. Suna shan kunya tare da waɗanda suka gangara zuwa rami. An yi mata gado a cikin matattu, tare da dukan jama’arta kewaye da kabarinta. Dukansu marasa kaciya ne, da aka kashe da takobi. Domin tsoronsu ya bazu cikin ƙasar masu rai, suna shan kunya tare da waɗanda suka gangara zuwa rami; an kwantar da su tare da waɗanda aka kashe. “Meshek da Tubal suna can, tare da dukan jama’arsu kewaye da kaburburansu. Dukansu marasa kaciya ne, da aka kashe da takobi domin sun haddasa tsoronsu a ƙasar masu rai. Ba sun kwanta tare da sauran jarumawa marasa kaciyan da aka kashe, waɗanda suka gangara kabari tare da makaman yaƙinsu, waɗanda aka yi musu matashin kai da takubansu ba? Hukuncin zunubansu yana a bisa ƙasusuwansu, ko da yake tsoron waɗannan jarumawa ya manne cikin ƙasar masu rai. “Kai kuma, ya Fir’auna, za a kakkarye ka za ka kuma kwanta a cikin marasa kaciya, tare da waɗanda aka kashe da takobi. “Edom tana can, sarakunanta da dukan yerimanta; duk da ikonsu, sun kwanta tare da waɗanda aka kashe da takobi. Suna kwance tare da marasa kaciya, tare da waɗanda suka gangara zuwa rami. “Dukan yerima arewa da dukan Sidoniyawa suna can; sun gangara tare da waɗanda aka kashe cikin kunya duk da tsoron da suka haddasa ta wurin ikonsu. Sun kwanta tare da marasa kaciya tare da waɗanda aka kashe da takobi suna kuma shan kunya tare da waɗanda suka gangara zuwa rami. “Fir’auna, shi da dukan sojojinsa, za su gan su zai kuma ta’azantu domin dukan jama’arsa da aka kashe da takobi, in ji Ubangiji Mai Iko Duka. Ko da yake na sa ta haddasa tsoro a ƙasar masu rai, Fir’auna da dukan jama’arsa za su kwanta a cikin marasa kaciya, tare da waɗanda aka kashe da takobi, in ji Ubangiji Mai Iko Duka.” Maganar Ubangiji ta zo mini cewa, “Ɗan mutum, yi magana da mutanen ƙasarka ka faɗa musu cewa, ‘Sa’ad da na kawo takobi a kan ƙasar, mutanen ƙasar kuwa suka zaɓi ɗaya daga cikin mutanensu suka mai da shi mai tsaro, ya kuma ga takobi yana zuwa a kan ƙasar ya kuwa busa ƙaho don yă faɗakar da mutane, in wani ya ji busar amma bai kula ba, takobin zai zo ya ɗauki ransa, jininsa kuwa zai zauna a kansa. Da yake ya ji ƙarar busar amma bai kula ba, jininsa zai zauna a kansa. Da a ce ya kula, da ya ceci kansa. Amma a ce mai tsaron ya ga takobi yana zuwa bai kuwa busa ƙaho don yă faɗakar da mutane ba sai takobi ya zo ya ɗauki ran waninsu, za a kawar da wannan mutum saboda zunubinsa, amma zan nemi hakkin jinin mutumin a kan mai tsaron.’ “Ɗan mutum, na mai da kai mai tsaro bisa gidan Isra’ila; saboda haka ka ji abin da zan faɗa ka kuma gargaɗe su. Sa’ad da na ce wa mugu, ‘Ya mugun mutum, tabbatacce za ka mutu,’ kai kuma ba ka yi magana don ka juyar da shi daga hanyoyinsa ba, wannan mugun mutum zai mutu domin zunubinsa, zan kuma nemi hakkin jininsa a kanka. Amma in ka faɗakar da mugun mutumin don yă juye daga hanyoyinsa bai kuwa yi haka ba, zai mutu saboda zunubinsa, amma kai za ka kuɓutar da kanka. “Ɗan mutum, faɗa wa gidan Isra’ila, ‘Ga abin da kuke cewa, “Laifofinmu da zunubanmu suna nawaita mana, muna kuma lalacewa saboda su. Ta ƙaƙa za mu rayu?” ’ Ka faɗa musu, ‘Muddin ina raye, in ji Ubangiji Mai Iko Duka, ba na jin daɗin mutuwar mugu, amma a maimako haka ya fi su juye daga hanyoyinsu su rayu. Ku juye! Ku juye daga mugayen hanyoyinku! Don me za ku mutu, ya gidan Isra’ila?’ “Saboda haka, ɗan mutum, ka faɗa wa mutanen ƙasarka, ‘Adalcin adali ba zai cece shi sa’ad da ya ƙi yin biyayya ba, kuma muguntar mugu ba za tă sa ya fāɗi sa’ad da ya juya daga gare ta ba. Adali, in ya yi zunubi, ba za a bari yă rayu saboda adalcinsa na dā ba.’ In na faɗa wa adali cewa tabbatacce zai rayu, amma sai ya dogara ga adalcinsa ya kuma aikata mugunta, babu ayyukan adalcinsa da za a tuna; zai mutu saboda muguntar da ya aikata. Kuma in na ce wa mugu, ‘Tabbatacce za ka mutu,’ amma sai ya juye daga zunubinsa ya kuma yi abin da yake gaskiya da kuma daidai, in ya mayar da jingina, ya mayar da abin da ya sata, ya kiyaye ƙa’idodin da suke ba da rai, ya daina yin mugunta, tabbatacce zai rayu; ba zai mutu ba. Babu wani zunubin da ya aikata da za a tuna da shi. Ya yi abin da yake gaskiya da kuma daidai; tabbatacce zai rayu. “Duk da haka mutanen ƙasarka sun ce, ‘Hanyar Ubangiji ba daidai ba ce.’ Alhali kuwa tasu ce ba daidai ba. In adali ya juye daga adalcinsa ya yi mugunta, zai mutu saboda haka. Kuma in mugu ya juye daga muguntarsa ya aikata abin da yake gaskiya da kuma daidai, zai rayu ta yin haka. Duk da haka, ya gidan Isra’ila kun ce, ‘Hanyar Ubangiji ba daidai ba ce.’ Amma zan hukunta kowane ɗayanku gwargwadon ayyukansa.” A shekara ta goma sha biyu ta zaman bautanmu, a wata na goma a rana ta biyar, wani mutumin da ya gudu daga Urushalima ya zo wurina ya ce, “Birnin ya fāɗi!” To a yamman da ya wuce kafin mutumin ya iso, hannun Ubangiji yana a kaina, ya kuma buɗe bakina kafin mutumin ya iso wurina da safe. Sai bakina ya buɗu ban kuma yi shiru ba. Sai maganar Ubangiji ta zo mini cewa, “Ɗan mutum, mutanen da suke zama a waɗannan kufai a ƙasar Isra’ila suna cewa, ‘Ibrahim mutum ɗaya ne kaɗai, duk da haka Ibrahim ya mallaki ƙasar. Amma mu da muke da yawa; lalle an ba mu ƙasar ta zama mallakarmu.’ Saboda haka ka faɗa musu, ‘Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa da yake kun ci nama da jini a cikinsa kuka kuma bauta wa gumakanku kuka zub da jini, kuna gani za ku mallaki ƙasar? Kun dogara ga takobinku, kuka aikata abubuwan banƙyama, kowannenku kuma ya ƙazantar da matar maƙwabcinsa. Kuna gani za ku mallaki ƙasar?’ “Ka faɗa musu wannan, ‘Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa muddin ina raye, waɗanda aka rage a kufai za su fāɗi ga takobi, waɗanda suke bayan gari kuwa namun jeji za su cinye su, waɗanda suke a mafaka da kogwannin duwatsu annoba za tă kashe su. Zan mai da ƙasar kango, kuma fariyar ƙarfinta zai ƙare, duwatsun Isra’ila za su zama kufai don kada wani ya ratsa su. Sa’an nan za su san cewa ni ne Ubangiji, sa’ad da na mai da ƙasar kango saboda dukan abubuwan banƙyamar da suka yi.’ “Game da kai kuma, ɗan mutum, mutanen ƙasarka suna magana da juna game da kai a katanga da kuma ƙofofin gidaje, suna ce wa juna, ‘Ku zo mu tafi mu ji maganar da ta zo daga wurin Ubangiji.’ Mutanena sukan zo wurinka, yadda suka saba su zauna a gabanka don su saurari maganarka, amma ba sa aiki da abin da suka ji. Da bakunansu suna nuna ƙauna, amma zukatansu cike da haɗama suke don ƙazamar riba. Tabbatacce, gare su ba ka fi mai waƙar ƙauna da murya mai daɗi kana kuma yin kiɗa sosai ba, gama sukan ji maganarka amma ba sa amfani da ita. “Sa’ad da dukan wannan ya cika kuma zai cika ɗin, sa’an nan za su sani akwai annabi a tsakiyarsu.” Maganar Ubangiji ta zo mini cewa, “Ɗan mutum, ka yi annabci a kan makiyayan Isra’ila; ka yi annabci ka ce musu, ‘Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa kaiton makiyayan Isra’ila waɗanda suke kula da kansu ne kawai! Ashe, bai kamata makiyaya ne su lura da tumaki ba? Kuna cin kitsensu, kuna yi wa kanku tufafi da gashinsu, kukan yanka turkakkun, amma ba ku yi kiwon tumakin ba. Ba ku ƙarfafa marasa ƙarfi ba, ko ku warkar da marasa lafiya ko ku ɗaura waɗanda suka ji rauni. Ba ku dawo da waɗanda suka yi makuwa ko ku nemi waɗanda suka ɓace ba. Amma sai kuka mallake su ƙarfi da yaji. Saboda haka suka warwatse domin babu makiyayi, kuma da suka warwatsu sai suka zama abincin namun jeji. Tumakina suna ta yawo a kan dukan duwatsu da kuma kowane tudu. Sun watsu a dukan duniya, kuma ba wanda ya neme su. “ ‘Saboda haka, ku makiyaya, ku ji maganar Ubangiji, Muddin ina raye, in ji Ubangiji Mai Iko Duka, domin tumaki sun rasa makiyayi ta haka aka washe su suka kuma zama abincin dukan namun jeji, kuma domin makiyayana ba su nemi tumakina ba amma suka kula da kansu a maimakon tumakina, saboda haka, ya ku makiyaya, ku ji maganar Ubangiji, Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa ina gāba da makiyaya kuma zan nemi hakkin tumakina daga gare su. Zan hana su yin kiwon tumakin don kada makiyayan su ƙara yin kiwon kansu. Zan ƙwace tumakina daga bakunansu, ba kuwa za su ƙara zama abincinsu. “ ‘Gama ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa ni kaina zan nemi tumakina. Kamar yadda makiyayi yakan lura da tumakinsa da suka watse sa’ad da yake tare da su, haka zan lura da tumakina. Zan cece su daga dukan wuraren da aka watsar da su a ranar gizagizai da baƙin duhu. Zan dawo da su daga al’ummai in kuma tattara su daga ƙasashe, zan kuma kawo su cikin ƙasarsu. Zan yi kiwonsu a kan duwatsun Isra’ila, a maɓulɓulai da kuma cikin wuraren zamansu a ƙasar. Zan kula da su a wurin kiwo mai kyau, kuma ƙwanƙolin duwatsun Isra’ila ne zai zama wurin kiwonsu. Za su kwanta a wurin kiwo mai kyau, a can kuma za su yi kiwo a wurin kiwo mai kyau a kan duwatsun Isra’ila. Ni kaina zan lura da tumakina in kuma sa su kwanta, in ji Ubangiji Mai Iko Duka. Zan nemi ɓatattuna in kuma dawo da waɗanda suka yi makuwa. Zan ɗaura raunin waɗanda suka ji ciwo in kuma ƙarfafa marasa ƙarfi, amma zan hallaka ƙarfafa da kuma masu ƙiba. Zan yi kiwo tumaki da adalci. “ ‘Game da ku, tumakina, ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa zan hukunta tsakanin tunkiya da tunkiya, da tsakanin raguna da awaki. Bai isa ba a ce kun yi kiwo a wuri mai kyau? Sai kun tattake sauran wurin kiwonku da ƙafafunku tukuna? Bai isa ba a ce kun sha ruwa mai tsabta? Sai kun kuma gurɓata sauran da ƙafafunku? Dole ne tumakina su ci abin da kuka tattake su kuma sha abin da kuka gurɓata da ƙafafunku? “ ‘Saboda haka ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka ya ce musu, duba, ni kaina zan hukunta tsakanin turkakkun tumaki da ramammun tumaki. Domin kun tunkuɗe marasa ƙarfi da kafaɗunku, kun kuma tunkuye su da ƙahoninku sai da suka gudu, zan cece tumakina ba za su ƙara zama ganima ba. Zan hukunta tsakanin tunkiya da tunkiya. Zan sa musu makiyaya guda, bawana Dawuda, zai kuwa lura da su; zai kula da su ya kuma zama makiyayinsu. Ni Ubangiji zan zama Allahnsu, bawana kuma Dawuda zai zama yerima a cikinsu. Ni Ubangiji na faɗa. “ ‘Zan yi alkawarin salama da su in kuma kawar wa ƙasar da namun jeji domin su zauna a hamada su kuma kwana a kurmi lafiya lau. Zan albarkace su in kuma sa tuduna kewaye da su. Zan zubo yayyafi a lokacinsa; za a kasance da yayyafin albarka. Itatuwan gona za su ba da ’ya’yansu, ƙasa kuma za tă ba da amfaninta; mutane za su zauna lafiya a ƙasarsu. Za su san cewa ni ne Ubangiji, sa’ad da na karya karkiyarsu, na cece su daga hannun waɗanda suka bautar da su. Ba za su ƙara zama ganimar al’ummai ba, ba kuwa namun jeji za su cinye su ba. Za su zauna lafiya, kuma babu wani da zai sa su ji tsoro. Zan tanada musu ƙasar da aka sani don hatsinta, ba za su kuma ƙara zama abin da yunwa za tă fara musu a ƙasa ba ko su sha zargin sauran al’ummai. Sa’an nan za su san cewa ni, Ubangiji Allahnsu, ina tare da su kuma cewa su, gidan Isra’ila, mutanena ne, in ji Ubangiji Mai Iko Duka. Ku tumakina, tumakin wurin kiwona, mutanena ne, ni kuwa Allahnku ne, in ji Ubangiji Mai Iko Duka.’ ” Maganar Ubangiji ta zo mini cewa, “Ɗan mutum, ka fuskanci Dutsen Seyir; ka yi annabci a kansa ka ce, ‘Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa ina gāba da kai, Dutsen Seyir, zan kuma miƙa hannuna gāba da kai in mai da kai kango. Zan mai da garuruwanka kufai za ka kuma zama kango. Sa’an nan za ka san cewa ni ne Ubangiji. “ ‘Domin ka riƙe ƙiyayya ta tun dā, ka kuma ba da mutanen Isra’ila domin a kashe su da takobi a lokacin masifarsu, lokacin da adadin horonsu ya cika, saboda haka muddin ina raye, in ji Ubangiji Mai Iko Duka, zan sa a zub da jininka zan kuwa fafare ka. Da yake ba ka ƙi zub da jini ba, zub da jini zai fafare ka. Zan mai da Dutsen Seyir kango in kuma yanke dukan waɗanda suke shiga da fita a cikinka. Zan cika duwatsunka da matattu; waɗanda aka kashe da takobi za su fāɗi a kan tuddanka, da cikin kwarurukanka, da cikin dukan kwazazzabanka. Zan mai da kai kango har abada; ba za a zauna a cikin garuruwanka ba. Sa’an nan za ka san cewa ni ne Ubangiji. “ ‘Domin kun ce, “Waɗannan al’ummai biyu da ƙasashe za su zama namu za mu kuma mallake su,” ko da yake Ni Ubangiji ina a can, saboda haka muddin ina raye, in ji Ubangiji Mai Iko Duka, zan sāka maka gwargwadon fushi da kuma kishin da ka nuna a ƙiyayyarsu da ka yi zan kuma sanar da kaina a cikinsu sa’ad da na hukunta ka. Sa’an nan za ka san cewa Ni Ubangiji na ji duk abubuwan banzan da ka faɗa a kan duwatsun Isra’ila. Ka ce, “An mai da su kango an kuma ba mu su mu cinye.” Ka yi fariya a kaina, ka kuma yi magana a kaina ba gaggautawa, na ji shi sarai. Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa yayinda dukan duniya take farin ciki, zan mai da kai kango. Domin ka yi farin ciki sa’ad da gādon gidan Isra’ila ya zama kufai, haka zan yi da kai, ya Dutsen Seyir, kai da dukan Edom. Sa’an nan za ka san cewa ni ne Ubangiji.’ ” “Ɗan mutum, ka yi annabci wa duwatsun Isra’ila ka ce, ‘Ya duwatsun Isra’ila, ku ji maganar Ubangiji. Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa abokin gāba yana magana game da ku cewa, “Yauwa! Tsofaffin tuddai sun zama mallakarmu yanzu.” ’ Saboda haka ka yi annabci ka ce, ‘Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa domin sun lalace ku suka kuma maishe ku kufai marar amfani a kowane gefe saboda ku zama mallakar sauran al’ummai da kuma abin magana da tsegumi ga mutane, saboda haka, ya duwatsun Isra’ila, ku ji maganar Ubangiji Mai Iko Duka, ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana faɗa wa duwatsu da tuddai, wa kwazazzabai da kwaruruka, wa kufai da garuruwan da suka zama kango waɗanda aka washe aka wulaƙanta suka zama ganimar sauran al’ummai da suke kewaye da ku, ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa cikin kishina mai ƙuna na yi magana gāba da sauran al’ummai, da kuma gāba da Edom, gama da farin ciki da reni a zukatansu suka mai da ƙasata mallakarsu don su washe wuraren kiwonta.’ Saboda haka ka yi annabci game da ƙasar Isra’ila ka kuma ce wa duwatsu da tuddai, wa kwazazzabai da kwaruruka, ‘Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa ga shi, na yi magana da kishina da hasalata saboda sun sha zargi wurin al’ummai. Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa na ɗaga hannuna sama na rantse cewa al’ummai da suke kewaye da ku za su sha ba’a. “ ‘Amma ku, ya duwatsun Isra’ila, za ku miƙa rassanku ku ba da amfani ga mutanena Isra’ila, gama ba da daɗewa ba za su komo gida. Na damu da ku kuma zan dube ku da tausayi; za ku nome ku kuma shuka, zan kuma riɓaɓɓanya mutane a kanku, dukan gidan Isra’ila ke nan. Za a zauna a birane a kuma sāke gina rusassun wurare. Zan sa mutane da dabbobi su yi yawa a kanku, za su kuma ba da ’ya’ya su kuma yi yawa. Zan zaunar da mutane a kanku kamar dā zan kuma sa ku wadaita fiye da dā. Sa’an nan za ku san cewa ni ne Ubangiji. Zan sa mutanena Isra’ila su yi tafiya a kanku. Za su mallake ku, za ku kuma zama gādonsu; ba za ku ƙara sa su rasa ’ya’yansu ba. “ ‘Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa domin mutane suna magana game da ku cewa, “Kun cinye mutane kuka kuma sa al’ummarku ta rasa ’ya’yanta,” saboda haka ba za ku ƙara cinye mutane ko ku sa al’ummarku ta rasa ’ya’ya ba, in ji Ubangiji Mai Iko Duka. Ba zan ƙara bari ku ji maganar banza ta al’ummai ba, ba kuwa za ku ƙara shan ba’ar mutane ko in sa al’ummarku ta fāɗi ba, in ji Ubangiji Mai Iko Duka.’ ” Maganar Ubangiji ta sāke zuwa mini cewa, “Ɗan mutum, sa’ad da mutanen Isra’ila suke zama a ƙasarsu, sun ƙazantar da ita ta wurin halinsu da kuma ayyukansu. Halinsu ya yi kamar rashin tsarkin mace a lokacin al’adarta a gabana. Saboda haka na husata da su domin sun yi kisankai a ƙasar kuma domin sun ƙazantar da ita da gumakansu. Na warwatsa su cikin al’ummai, suka kuwa warwatsu cikin dukan ƙasashe; na hukunta su gwargwadon halinsu da ayyukansu. Kuma ko’ina da suka tafi a cikin al’ummai sun ɓata sunana mai tsarki, gama an yi magana a kansu cewa, ‘Waɗannan mutanen Ubangiji ne, duk da haka dole su bar ƙasarsa.’ Na damu saboda sunana mai tsarki, wanda gidan Isra’ila ya ɓata a cikin al’ummai inda suka tafi. “Saboda haka ka faɗa musu cewa, ‘Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa ba dominku ba ne, ya gidan Isra’ila da nake yin waɗannan abubuwa, amma saboda sunana ne mai tsarki, wanda kuka ɓata a cikin al’ummai inda kuka tafi. Zan nuna tsarkin girman sunana, wanda aka ɓata a cikin al’umma, sunana da kuka ɓata a cikinsu. Sa’an nan al’ummai za su san cewa ni ne Ubangiji, in ji Ubangiji Mai Iko Duka, sa’ad da na nuna kaina mai tsarki ta wurinku a idanunsu. “ ‘Gama zan fitar da ku daga al’ummai; zan tattara ku daga dukan ƙasashe in komo da ku zuwa ƙasarku. Zan yayyafa muku ruwa mai tsabta, zan kuwa tsarkake ku daga dukan ƙazantarku daga kuma dukan gumakanku. Zan ba ku sabuwa zuciya in kuma sa sabon ruhu a cikinku; zan fid da zuciyar dutse in kuma ba ku zuciyar nama. Zan kuma sa Ruhuna a cikinku in kuma motsa ku ku bi ƙa’idodina ku kuma kiyaye dokokina. Za ku zauna a ƙasar da na ba wa kakanninku; za ku zama mutanena, ni kuwa zan zama Allahnku. Zan cece ku daga dukan rashin tsabtarku. Zan sa hatsi ya yi yalwa ba zan kawo yunwa a kanku ba. Zan ƙara ’ya’yan itatuwa da amfanin gona, saboda kada ku ƙara shan kunya a cikin al’ummai saboda yunwa. Sa’an nan za ku tuna mugayen hanyoyinku da mugayen ayyukanku, za ku kuwa ji ƙyamar kanku saboda zunubanku da kuma ayyukanku na banƙyama. Ina so ku san cewa ba na yi wannan saboda ku, in ji Ubangiji Mai Iko Duka. Ku ji kunya ku kuma giggita saboda halinku, ya gidan Isra’ila! “ ‘Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa a ranar da na tsarkake ku daga dukan zunubanku, zan sāke zaunar da ku a garuruwanku, a kuma sāke gina kufai. Ƙasar da take kango a dā za ku nome ta a maimakon zama kango a idon dukan masu ratsawa a cikinta. Za su ce, “Wannan ƙasar da take kango a dā ta zama kamar lambu Eden; biranen da dā suke kufai, kango da kuma aka lalata, yanzu suna da katanga ana kuma zama a ciki.” Sa’an nan al’ummai kewaye da ku da suka rage za su san cewa Ni Ubangiji na sāke gina abin da aka lalace na kuma sāke shuka abin da yake kango. Ni Ubangiji na faɗa, kuma zan aikata.’ “Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa har yanzu zan ji roƙon gidan Isra’ila in kuma yi musu wannan. Zan sa mutanensu su yi yawa kamar tumaki, yawansu ya yi kamar garken tumaki don hadaya a Urushalima a ƙayyadaddun lokuta bukukkuwarta. Haka biranen da suke kufai za su cika da ɗumbun mutane. Sa’an nan za su san cewa ni ne Ubangiji.” Hannun Ubangiji yana a kaina, ya kuma fitar da ni ta wurin Ruhun Ubangiji ya sa ni a tsakiyar kwarin; yana cike da ƙasusuwa. Ya sa na kai na komo a ciki, na kuma ga ƙasusuwa masu girma da yawa a ƙasar kwarin, ƙasusuwan da suka bushe ƙwarai. Sai ya tambaye ni cewa, “Ɗan mutum, waɗannan ƙasusuwa za su iya rayu?” Ni kuwa na ce, “Ya Ubangiji Mai Iko Duka, kai kaɗai ka sani.” Sai ya ce mini, “Ka yi wa waɗannan ƙasusuwa annabci ka ce musu, ‘Busassun ƙasusuwa, ku ji maganar Ubangiji! Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka ya ce wa waɗannan ƙasusuwa. Zan sa numfashi ya shiga muku, za ku kuwa rayu. Zan harhaɗa muku jijiyoyi in sa muku tsoka in kuma rufe ku da fata; zan sa numfashi a cikinku, za ku kuwa rayu. Sa’an nan za ku san cewa ni ne Ubangiji.’ ” Saboda haka sai na yi annabci yadda aka umarce ni. Da nake annabcin, sai aka ji motsi, ƙarar girgiza, sai ƙasusuwan suka harhaɗu, ƙashi ya haɗu da ƙashi. Na duba, sai ga jijiyoyi da nama suka bayyana a kansu fata kuma ta rufe su, amma ba numfashi a cikinsu. Sa’an nan ya ce mini, “Ka yi annabci wa numfashi; ka yi annabci, ɗan mutum, ka ce masa, ‘Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa ka fito daga kusurwoyi huɗu, ya numfashi, ka kuma numfasa cikin waɗannan matattu, don su rayu.’ ” Saboda haka na yi annabci yadda aka umarce ni, sai numfashi ya shiga musu; suka rayu suka kuma miƙe tsaye a ƙafafunsu babbar runduna ce ƙwarai. Sa’an nan ya ce mini, “Ɗan mutum, waɗannan ƙasusuwa su ne dukan gidan Isra’ila. Suna cewa, ‘Ƙasusuwanmu sun bushe, sa zuciyarmu duk ya tafi; an share mu ƙaf.’ Saboda haka yi annabci ka ce musu, ‘Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa ya mutanena, zan buɗe kaburburanku in fitar da ku daga cikinsu; zan mai da ku ƙasar Isra’ila. Sa’an nan ku, mutanena, za ku san cewa ni ne Ubangiji, sa’ad da na buɗe kaburburanku na fitar da ku daga cikinsu. Zan sa Ruhuna a cikinku za ku kuwa rayu, zan kuma zaunar da ku a ƙasarku. Sa’an nan za ku san cewa Ni Ubangiji na faɗa, zan kuma aikata, in ji Ubangiji.’ ” Maganar Ubangiji ta zo mini cewa, “Ɗan mutum, ka ɗauki sanda ka rubuta a kansa, ‘Na Yahuda da Isra’ilawan da suke tare da shi.’ Sa’an nan ka ɗauki wani sanda, ka rubuta a kansa, ‘Sandan Efraim, na Yusuf da dukan gidan Isra’ilan da suke tare da shi.’ Ka haɗa su su zama sanda guda saboda su kasance ɗaya a hannunka. “In mutanen ƙasarka suka tambaye ka cewa, ‘Ba za ka faɗa mana abin da kake nufi da wannan ba?’ Ka ce musu, ‘Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa, Zan ɗauki sandan Yusuf, wanda yake a hannun Efraim, da na kabilan Isra’ilawan da suke tare da shi, in haɗa shi da sandan Yahuda, in mai da su sanda guda, za su kuwa zama ɗaya a hannuna.’ Ka riƙe sandunan da ka yi rubutun a gabansu ka ce musu, ‘Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa zan fitar da Isra’ilawa daga al’ummai inda suka tafi. Zan tattara su daga dukan kewaye in komo da su ƙasarsu. Zan mai da su al’umma ɗaya a cikin ƙasar, a kan duwatsun Isra’ila. Za a kasance da sarki guda a kan dukansu ba za su ƙara zama al’ummai biyu ko su rabu su zama masarautai biyu ba. Ba za su ƙara ƙazantar da kansu da gumaka da mugayen siffofi ko kuma da wani daga laifofinsu ba, gama zan cece su daga dukan zunubinsu na ridda, zan kuma tsarkake su. Za su zama mutanena, ni kuma zan zama Allahnsu. “ ‘Bawana Dawuda zai zama sarki a kansu, dukansu kuwa za su kasance da makiyayi guda. Za su bi dokokina su kuma kiyaye ƙa’idodina. Za su zauna a ƙasar da na ba wa bawana Yaƙub, ƙasar da kakanninsu suka zauna. Su da ’ya’yansu da ’ya’ya ’ya’yansu za su zauna a can har abada, kuma Dawuda bawana zai zama sarkinsu har abada. Zan yi alkawarin salama da su; zai zama madawwamin alkawari. Zan kafa su in ƙara yawansu, zan kuma sa wuri mai tsarkina a cikinsu har abada. Mazaunina zai kasance da su; zan kuwa zama Allahnsu, za su kuma zama mutanena. Sa’an nan al’ummai za su san cewa Ni Ubangiji na mai da Isra’ila mai tsarki, sa’ad da wuri mai tsarkina yana a cikinsu har abada.’ ” Maganar Ubangiji ta zo mini cewa, “Ɗan mutum, ka fuskanci Gog, na ƙasar Magog, babban sarkin Meshek da Tubal; ka yi annabci a kansa ka ce, ‘Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa ina gāba da kai, ya Gog, babban sarkin Meshek da Tubal. Zan juyar da kai, in sa ƙugiyoyi a muƙamuƙanka in fitar da kai tare da dukan sojojinka, dawakanka, mahayan dawakanka saye da makamai, da kuma jama’a mai girma masu riƙe da garkuwoyi manya da ƙanana, dukansu da takuba a zāre. Farisa, Kush da Fut za su kasance tare da su, duka riƙe da garkuwoyi da hulunan kwano, haka ma Gomer da dukan sojojinsa, da Bet Togarma daga can arewa tare da dukan sojojinsa, al’ummai masu yawa tare da kai. “ ‘Ka shirya; ka kintsa, kai da dukan jama’arka da suka taru kewaye da kai, ka kuma zama mai ba su umarni. Bayan kwanaki masu yawa za a kira ka. A shekaru masu zuwa za ka kai hari a ƙasar da ta farfaɗo daga yaƙi, wadda aka tattara mutanenta daga al’ummai masu yawa zuwa duwatsun Isra’ila, dā kango ne sosai. An fitar da su daga al’ummai, yanzu kuwa dukansu suna zama lafiya. Kai da dukan sojojinka da kuma al’ummai masu yawa da suke tare da kai za ku haura, kuna cin gaba kamar hadari; za ku zama kamar girgijen da yake rufewa ƙasa. “ ‘Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa a ranar, tunani zai shiga cikin zuciyarka za ka kuma ƙirƙiro muguwar dabara. Za ka ce, “Zan kai hari wa ƙasar da ƙauyukanta ba su da katanga; zan fāɗa wa mutanen da suke zamansu kurum cikin salama, dukansu suna zama babu katanga babu ƙofofi ko ƙyamare. Zan washe in kwashe ganima in kuma juye hannuna gāba da kufai da aka sāke zaunar da mutanen da aka tattara daga al’ummai, masu yawan shanu da kayayyaki, masu zama a tsakiyar ƙasa.” Sheba da Dedan da ’yan kasuwar Tarshish da dukan ƙauyukanta za su ce maka, “Ka zo ka kwashe ganima ne? Ka tattara jama’arka don ka yi waso, ka kuma kwashe azurfa da zinariya, ka kwashe shanu da kayayyaki ka kuma ƙwace ganima mai yawa?” ’ “Saboda haka ɗan mutum, ka yi annabci ka ce wa Gog, ‘Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa a ranar, sa’ad da mutanena Isra’ila suna zaman lafiya, ba za ka sani ba? Za ka zo daga wurinka a can arewa, kai da al’ummai masu yawa tare da kai, dukansu suna hawan dawakai, jama’a mai yawa, babbar runduna. Za ka ci gaba a kan mutanena Isra’ila kamar yadda girgijen yakan rufe ƙasa. A kwanaki masu zuwa, ya Gog, zan kawo ka, ka yi yaƙi da ƙasata, domin al’ummai su san ni sa’ad da na nuna kaina mai tsarki ta wurinka a gabansu. “ ‘Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa ba kai ba ne na yi magana da kai a kwanakin dā ta wurin bayina annabawan Isra’ila? A lokacin sun yi annabci shekaru masu yawa cewa zan kawo ka, ka yaƙe su. Ga abin da zai faru a ranar. Sa’ad da Gog ya fāɗa wa ƙasar Isra’ila, fushina mai zafi zai ƙuna, in ji Ubangiji Mai Iko Duka. Cikin kishina da hasalata mai zafi zan furta cewa a wannan lokaci za a yi babbar girgizar ƙasa a ƙasar Isra’ila. Kifin teku, tsuntsayen sarari, namun jeji, kowace halitta mai rarrafe da kuma dukan mutane a duniya za su yi rawar jiki a gabana. Za a tumɓuke duwatsu, a ragargaza tsaunuka, kuma kowane bango zai fāɗi ƙasa. Zan kira takobi a kan Gog a dukan duwatsuna, in ji Ubangiji Mai Iko Duka. Kowane takobin mutum zai yi gāba da ɗan’uwansa. Zan yi hukunci a kansa da annoba da kuma zub da jini; zan yi ruwa mai yawa da ƙanƙara da kibiritu mai cin wuta a kansa da a kan sojojinsa da kuma a kan al’ummai masu yawa da suke tare da shi. Ta haka zan nuna girmana da kuma tsarkina, zan sanar da kaina a gaban al’ummai masu yawa. Sa’an nan za su san cewa ni ne Ubangiji.’ “Ɗan mutum, ka yi annabci a kan Gog ka ce, ‘Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa ina gāba da kai, ya Gog, babban sarkin Meshek da Tubal. Zan juya ka in kuma ja ka. Zan kawo ka daga can arewa in aike ka don ka fāɗa wa duwatsun Isra’ila. Sa’an nan zan karya bakan da take a hannun hagunka, in sa kibiyoyin da suke a hannun damanka su fāɗi. A kan duwatsun Isra’ila za ka fāɗi, kai da sojojinka da kuma al’ummai da suke tare da kai. Zan bayar da kai ka zama abinci ga tsuntsaye da namun jeji masu cin nama. Za ka mutu a fili, gama haka ni na faɗa, in ji Ubangiji Mai Iko Duka. Zan aika da wuta a kan Magog da kuma a kan waɗanda suke zama lafiya a bakin teku, za su kuwa san cewa ni ne Ubangiji. “ ‘Zan sanar da sunana mai tsarki a cikin mutanena Isra’ila. Ba zan ƙara bari a ɓata sunana mai tsarki ba, kuma al’ummai za su san cewa Ni Ubangiji Mai Tsarki ne a cikin Isra’ila. Yana zuwa! Tabbatacce zai faru, in ji Ubangiji Mai Iko Duka. Ranar da na yi magana ke nan. “ ‘Sa’an nan waɗanda suke zama a garuruwan Isra’ila za su fita su tattara makamai su hura wuta da su su kuma ƙone su, manya da ƙanana garkuwoyi, bakkuna da kibiyoyi, kulake da māsu. Shekara bakwai za su yi amfani da su don hura wuta. Ba za su yi wahalar zuwa jeji don neman itacen hura wuta ba, domin za su yi amfani da makamai don hura wuta. Za su kuma washe waɗanda suka washe su ganima, in ji Ubangiji Mai Iko Duka. “ ‘A ranar zan yi wa Gog makabarta a cikin Isra’ila, a kwarin waɗanda suke tafiya wajen gabashin Teku. Za tă tare hanyar matafiya, domin za a binne Gog da dukan mutanensa a can. Ta haka za a kira wurin Kwarin Haman Gog. “ ‘Watanni bakwai gidan Isra’ila zai yi ta binne su don a tsarkake ƙasar. Dukan mutanen ƙasar za su binne su, kuma ranar da za a ɗaukaka ni za tă zama ranar tuni a gare su, in ji Ubangiji Mai Iko Duka. “ ‘Za a ɗauki mutane kullum don tsabtacce ƙasar. Waɗansu za su ratsa ƙasar, ƙari da waɗannan, waɗansu za su binne gawawwakin da suka ragu a ƙasar. A ƙarshen watanni bakwai ɗin za su fara bincikensu. Yayinda suke ratsa ƙasar, in waninsu ya ga ƙashin mutum, zai kafa shi kamar alama a gefe sai masu haƙa kabari sun binne shi a Kwarin Haman Gog. Akwai wani garin da ake kira Hamona zai kasance a can. Ta haka za su tsabtacce ƙasar.’ “Ɗan mutum, ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa, ka gayyato kowane irin tsuntsu da dukan namun jeji, ‘Ku taru ku kuma zo wuri ɗaya daga ko’ina don hadayar da nake shirya muku, babbar hadaya a kan duwatsun Isra’ila. A can za ku ci nama ku kuma sha jini. Za ku ci naman manyan mutane ku kuma sha jinin sarakunan duniya sai ka ce an yanka raguna da ’yan tumaki, awaki da bijimai, dukansu turkakkun dabbobi daga Bashan. A hadayar da nake shirya muku, za ku ci kitse sai kun ƙoshi ku kuma sha jini sai kun bugu. A teburina za ku ci iya ƙoshiyarku da naman jama’a da kuma mahaya, manyan mutane da sojoji na kowane iri,’ in ji Ubangiji Mai Iko Duka. “Zan nuna ɗaukakata a cikin al’ummai, kuma dukan al’ummai za su ga hukuncin da zan yi da kuma hannu mai nauyin da zan ɗora a kansu. Daga wannan rana zuwa gaba gidan Isra’ila zai san cewa ni ne Ubangiji Allahnsu. Al’ummai kuma za su san cewa mutanen Isra’ila sun tafi zaman bauta saboda zunubinsu, domin sun yi rashin aminci gare ni. Saboda haka na kawar da fuskata daga gare su na miƙa su ga abokan gābansu, suka kuwa mutu ta takobi. Na yi da su gwargwadon rashin tsabtarsu da laifofinsu, na kuma kawar da fuskata daga gare su. “Saboda haka ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa zan komo da Yaƙub daga zaman bauta zan kuma yi wa dukan Isra’ila jinƙai, zan kuma yi kishi saboda sunana mai tsarki. Za su manta da kunyar da suka sha da dukan rashin amincin da suka nuna mini sa’ad da suke zama lafiya a ƙasarsu inda ba wanda zai tsorata su. Sa’ad da na komo da su daga al’ummai na kuma tattara su daga ƙasashen abokan gābansu, zan nuna kaina mai tsarki ta wurinsu a gaban al’ummai masu yawa. Sa’an nan za su san cewa ni ne Ubangiji Allahnsu, gama ko da yake na tura su zaman bauta a cikin al’ummai, zan tattara su zuwa ƙasarsu, ba tare da barin wani a baya ba. Ba zan ƙara kawar da fuskata daga gare su, gama zan zuba Ruhuna a kan gidan Isra’ila, in ji Ubangiji Mai Iko Duka.” A shekara ta ashirin da biyar ta zaman bauta, a farkon shekara, a rana ta goma ga wata, a shekara ta goma sha huɗu bayan fāɗuwar birnin Urushalima, a wannan rana ikon Ubangiji ya sauko a kaina ya kuma iza ni. Cikin wahayin, Allah ya kai ni ƙasar Isra’ila ya sa ni a kan wani dutse mai tsayi ƙwarai, inda a gefen kudunsa akwai gine-ginen da suka yi kamar birni. A cikin wahayin ya kai ni can, na kuma ga mutum wanda kamanninsa ya yi kamar tagulla; yana tsaye a hanyar shiga yana riƙe da igiyar lilin da kuma karan awo a hannunsa. Mutumin ya ce mini, “Ɗan mutum, duba da idanunka, ka ji da kunnuwanka ka kuma lura da kowane abin da zan nuna maka, gama abin da ya sa na kawo ka nan ke nan. Ka faɗa wa gidan Isra’ila duk abin da ka gani.” Na ga katanga da ya kewaye filin haikali gaba ɗaya. Tsawon karan awon da yake a hannun mutumin kamu shida ne, sai ya auna kaurin katangar ya sami kamu shida, tsayinta kuma kamu shida. Sa’an nan ya tafi ƙofar da take fuskantar gabas. Ya hau matakanta ya auna madogarar ƙofa; zurfinta kamu shida ne. Tsawon kowane ɗakin matsara kamu shida ne, fāɗinsa kuma kamu shida, kaurin bangayen da suka raba ɗaki da ɗaki kamu biyar ne. Zurfin madogarar ƙofar da yake dab da shirayin da yake fuskantar haikalin kamu shida ne. Sa’an nan ya auna shirayin hanyar shiga; zurfinsa kamu takwas ne, kaurin kowane madogarar ƙofarsa kuwa kamu biyu ne. Shirayi hanyar shiga yana fuskantar haikalin. A cikin ƙofar gabas akwai ɗakuna uku a kowane gefe na hanyar shiga; dukan ukun girmansu ɗaya, bangayen da suke tsakani a kowane gefe girmansu ɗaya ne. Sa’an nan ya auna bakin hanyar shiga ya sami fāɗinsa kamu goma, tsawonsa kuma kamu goma sha uku. A gaban kowane ɗakin akwai bango mai tsayi kamu ɗaya, ɗakunan kuma kamu shida-shida ne a kowane gefe. Sa’an nan ya auna hanyar shiga daga saman bangon ɗaki a baya zuwa saman ɗakin da yake ɗaura da shi; nisansu kamu ashirin da biyar ne daga bango zuwa bango. Ya auna ɗakin bakin ƙofa na can ƙarshen hanyar shiga ya sami kamu sittin. Awon ya kai har zuwa shirayin da yake fuskantar filin. Nisan da take daga mashigin hanyar shiga zuwa can ƙarshen shirayin, kamu hamsin ne. Akwai ƙananan tagogi a ɗakunan da kuma a bangayen hanyar shiga, yadda suke a shirayin; tagogi a kewaye duka suna fuskantar ciki. An yi wa bangayen da suke waje ƙofar shiga ado da zāne-zāne siffofin itatuwan dabino. Sai mutumin ya bi da ni ta hanyar shiga zuwa filin waje, inda na ga ɗakuna talatin da aka gina kewaye a filin waje na filin. An gina waɗannan ɗakunan gefe a jikin bangon waje, a gabansu kuwa akwai daɓe kewaye da filin. Daɓen ya bi ta daidai gefen hanyoyin shiga, kuma faɗinsa ya yi daidai da tsawon ƙofofin shiga; wannan shi ne daɓen da yake ƙasa-ƙasa. Sa’an nan ya auna nisan da take daga hanyar shiga da take ƙasa-ƙasa daga ciki zuwa waje na filin ciki; ya kai kamu ɗari a gefen gabas haka ma yake a gefen arewa. Sa’an nan mutumin ya auna tsawo da fāɗin ƙofar da take fuskantar arewa, wadda take bi zuwa filin waje. Ƙofar shigar ma tana da ɗakuna uku-uku a kowane gefe. Girman bangayen da suka miƙe, da kuma shirayinta daidai suke da na ƙofa ta fari. Tsawonta kamu hamsin, fāɗinta kuwa kamu ashirin da biyar. Tagoginta, shirayinta da siffofin itatuwan dabinon da aka yi zāne-zānen adonta duk girmansu ɗaya ne da na ƙofar da take fuskantar gabas. Ɗakin shiga shi ma ya fuskanci filin yana kuma da matakai bakwai waɗanda suka bi zuwa ƙofar shiga, da shirayinta ɗaura da su. Akwai ƙofa zuwa filin ciki wadda take fuskantar ƙofar arewa, kamar dai yadda take a gabas. Ya auna daga ƙofa zuwa ƙofar da take ɗaura ta ita; ya sami kamu ɗari. Sa’an nan ya kai ni gefen kudu, na kuma ga ƙofa tana fuskantar kudu. Ya auna madogaranta da shirayinta, dukansu girmansu ɗaya ne kamar sauran ƙofofi biyun. Hanyar shiga da shirayinta suna da tagogi duk a kewaye, kamar tagogin sauran. Tsawonta kamu hamsin ne fāɗinta kuma kamu ashirin da biyar ne. Matakai bakwai sun haura zuwa ƙofar, da shirayi ɗaura da matakan; tana da zāne-zānen adon itatuwan dabino a bangayen a kowane gefe. Filin cikin ma yana da ƙofar da ta fuskanci kudu, sai ya auna daga wannan ƙofa zuwa ƙofar waje a gefen kudu; ya sami kamu ɗari. Sai ya kawo ni cikin filin ciki ta ƙofar kudu, ya kuma auna ƙofar kudu; ita ma tana da girma ɗaya da sauran ƙofofin shiga. Ɗakunanta na matsara, bangayenta duk suna da girma ɗaya da sauran. Hanyar shiga da shirayinta suna da tagogi duk a kewaye. Tsawonta kamu hamsin ne, fāɗinta kuma kamu ashirin da biyar ne. (Fāɗin shirayun hanyoyin shiga kewaye da filin ciki kamu ashirin da biyar ne, fāɗinsu kuma kamu biyar.) Shirayin ƙofar yana fuskantar filin waje; an yi zāne-zānen adon itatuwan dabino a madogarar bangayen hanyar shiga. Yana kuma da matakai takwas. Sai ya kai ni filin da yake ciki a gefen gabas, ya kuma auna hanyar shiga; girmanta iri ɗaya ne kamar sauran. Ɗakunanta, bangayenta da shirayinta duk girmansu iri ɗaya ne kamar sauran. Hanyar shiga da shirayinta suna da tagogi duk a kewaye. Tsawon hanyar shiga kamu hamsin ne, fāɗinta kuma kamu ashirin da biyar. Shirayinta yana fuskantar filin da yake waje; tana da zāne-zānen adon itatuwan dabino a madogararta. Tana kuma da matakai takwas. Sa’an nan ya kawo ni ƙofar arewa ya kuma auna ta. Girmanta ɗaya ne da sauran, Haka ma ɗakunanta, bangayenta da shirayinta, ƙofar tana da tagogi duk a kewaye. Tsawonta kamu hamsin, fāɗinta kuma kamu ashirin da biyar. Shirayin ƙofar ta fuskanci filin waje; tana da zāne-zānen adon itatuwan dabino a madogaranta, matakai takwas kuwa sun haura zuwa wajenta. Ɗakin da hanya ta ratsa ciki yana kusa da shirayin a kowane hanyoyin shiga na ciki, inda a kan wanke hadayun ƙonawa. A shirayin hanyar shiga akwai tebur biyu a kowane gefe, inda ake yankan hadayun ƙonawa, hadayun zunubi da kuma hadayun laifi. Ta bangon waje na shirayin hanyar shiga, kusa da matakai a mashigin zuwa hanyar shiga da take arewa akwai tebur biyu, akwai kuma tebur biyu a gefe ɗaya na matakan. Duka dai akwai tebur huɗu a gefe ɗaya na hanyar shiga, huɗu kuma a ɗaya gefen, tebur takwas ke nan gaba ɗaya, inda a kan yanka hadayu a kai. Akwai kuma tebur huɗu da aka yi da sassaƙaƙƙun duwatsu don hadayun ƙonawa, tsawon kowanne kuwa kamu ɗaya da rabi ne, fāɗinsa kamu ɗaya da rabi, tsayinsa kuma kamu ɗaya. A kansu ne a kan ajiye kayan yanka hadayun ƙonawa da kuma sauran hadayu. Aka kakkafa ƙugiyoyi kewaye a bangon, tsawon kowanne ya yi fāɗin tafin hannu. An yi amfani da teburin don a riƙa ajiye naman hadayu. Waje da ƙofar ciki, a cikin filin ciki, akwai ɗakuna biyu, ɗaya a gefen ƙofar arewa yana kuma fuskantar kudu, wani kuma a gefen ƙofar kudu yana fuskantar arewa. Sai mutumin ya ce mini, “Ɗakin da yake fuskantar kudu ne na firistocin da suke lura da haikali, ɗaya ɗakin kuma da yake fuskantar arewa ne na firistocin da suke lura da bagade. Waɗannan su ne ’ya’yan Zadok maza, waɗanda su ne kaɗai Lawiyawan da za su iya yin kusa da Ubangiji don su yi hidima a gabansa.” Sa’an nan ya auna filin, murabba’i ne, tsawonsa kamu ɗari, fāɗinsa kuma kamu ɗari. Bagaden kuwa yana a gaba a cikin haikalin. Sai ya kawo ni shirayin haikalin ya kuma auna madogaran shirayin; fāɗinsu a kowane gefe kamu biyar-biyar ne. Fāɗin mashigin kamu goma sha huɗu ne, bangayenta kuma kamu uku-uku ne a kowane gefe. Fāɗin shirayin kamu ashirin ne, kamu goma sha biyu kuma daga gaba zuwa baya. A kan kai samansa ta wurin hawan matakai, akwai kuma ginshiƙai a kowane gefe na madogaran. Sai mutumin ya kawo ni wuri mai tsarki da yake waje ya kuma auna madogaransa; fāɗin gefe-gefen kamu shida ne a kowane gefe. Faɗin ƙofar shiga kamu goma ne, fāɗin bangaye a kowane madogararta kamu biyar-biyar ne. Ya kuma auna wuri mai tsarkin da yake waje; tsawonsa kamu arba’in fāɗinsa kuma kamu ashirin. Sa’an nan ya shiga wuri mai tsarki da yake can ciki ya auna madogarar ƙofar shigar; fāɗin kowanne kamu biyu ne. Faɗin ƙofar shigan kamu shida ne, fāɗin bangayen a kowane gefenta kamu bakwai-bakwai ne. Ya kuma auna tsawon wuri mai tsarki da yake can ciki; tsawon kamu ashirin ne, fāɗinsa kuma kamu ashirin daga ƙurewa wuri mai tsarki da yake waje. Ya ce mini, “Wannan shi ne Wuri Mafi Tsarki.” Sa’an nan ya auna bangon haikalin; kaurinsa kamu shida ne, kuma kowane ɗakin da yake a gefe kewaye da haikalin fāɗinsa kamu huɗu ne. Ɗakunan da suke gefe masu hawa uku ne, wani bisa wani, guda talatin a kowane hawa. Akwai katanga kewaye da bangayen haikalin don ta tokare ɗakunan, domin ba a so ɗakunan su jingina da bangon haikalin. Faɗin ɗakunan da suke gefe kewaye da haikalin ya yi ta ƙaruwa daga hawa zuwa hawa. Ginin da aka yi kewaye da haikalin ya yi ta ƙaruwa daga hawa zuwa hawa, don haka ɗakunan suka yi ta ƙara fāɗi yayinda suka ƙara bisa. Akwai mataki daga ɗaki na ƙasa zuwa ɗaki na bisa ta hanya hawa ɗaki na tsakiya. Na ga cewa haikalin yana da ɗagaggen tushe kewaye da shi, wanda ya zama harsashin ɗakunan da suke gefe. Tsawonsa kara guda ne mai tsawon kamu shida. Kaurin bangon waje na ɗakunan da suke gefe kamu biyar ne. Faɗin filin da yake tsakanin ɗakunan da suke gefen haikalin da ɗakunan firistoci kamu ashirin ne kewaye da haikalin. Akwai ƙofofin shiga daga fili, ɗaya a arewa ɗaya kuma a kudu; fāɗin tushen da ya yi kusa da filin kamu biyar ne kewaye. Faɗin ginin da yake fuskantar filin haikali a wajen yamma kamu saba’in ne. Kaurin bangon ginin kamu biyar ne kewaye, tsawonsa kuma kamu tasa’in ne. Sa’an nan ya auna haikalin; tsawonsa kamu ɗari ne, tsawon filin haikalin da ginin tare da bangayensa su ma kamu ɗari ne. Faɗin filin haikalin a wajen gabas, haɗe da gaban haikalin, kamu ɗari ne. Sa’an nan ya auna tsawon ginin da yake fuskantar filin a bayan haikalin, haɗe da rumfunansa a kowane gefe, kamu ɗari. Wuri mai tsarki da yake waje, wuri mai tsarki da yake can ciki da shirayin da yake fuskantar filin, da madogaran ƙofa da matsattsun tagogi da rumfuna kewaye da su ukun, har da kome da yake gaba haɗe da madogarar ƙofa, an rufe su da katako. An rufe bangon haikalin daga ƙasa har zuwa tagogi, tagogin kuwa an rufe su. A filin da yake bisan ƙofar shiga na waje zuwa wuri mai tsarki na can ciki da kuma a bangayen da aka daidaita tsakani kewaye da wuri mai tsarki na can ciki da kuma na can waje an zāna siffofin kerubobi da na itatuwan dabino. Zānen siffar itacen dabino yana a tsakanin kerub da kerub. Kowane kerub yana da fuska biyu, fuskar ɗaya kamar ta mutum tana fuskantar zānen siffar itacen dabino a wannan gefe, ɗaya fuskar kamar ta zaki tana fuskantar zānen siffar itacen dabino na wancan gefe. Haka aka zāna su dukan a jikin bangon haikalin kewaye. Daga ƙasa zuwa daurin ƙofa, an zāna siffofin kerubobi da na itatuwan dabino a waje na wuri mai tsarki. Wuri mai tsarki da yake waje yana da madogarar ƙofa murabba’i, haka ma wadda take a gaban Wuri Mafi Tsarki. Akwai bagaden katako mai tsayi kamu uku, fāɗinsa kamu biyu da kuma tsawonsa kamu biyu; kusurwansa, tushensa da kuma gefe-gefensa duk katako ne. Sai mutumin ya ce mini, “Wannan shi ne tebur da yake a gaban Ubangiji.” A wuri mai tsarki da yake waje da kuma Wuri Mafi Tsarki suna da ƙofa biyu a haɗe. Kowace ƙofa tana da murfi biyu masu buɗewa ciki da waje. A ƙofofin wuri mai tsarki da yake waje an zāna siffofin kerubobi da na itatuwan dabino kamar yadda aka zāna a bangayen, akwai kuma rumfar da aka yi da itace a gaban shirayin. A bangayen da suke gefen shirayin akwai matsattsun tagogi da aka zāna siffar itatuwan dabino a kowane gefe. Gefe-gefen ɗakunan haikalin ma suna da rumfuna. Sai mutumin ya kai ni wajen arewa zuwa cikin filin da yake waje ya kuma kawo ni ɗakunan da suke ɗaura da filin haikalin da yake a gefen arewa. Tsawon ginin da yake fuskantar arewa kamu ɗari ne fāɗinsa kuma kamu hamsin. A gaban kamu ashirin na filin da yake can ciki da kuma a gaban daɓen filin da yake waje, akwai rumfuna a jere waɗanda suke fuskantar juna hawa uku-uku. A gaban ɗakunan akwai hanya a can ciki mai fāɗin kamu goma, tsawonta kuma kamu ɗari. Ƙofofinsu suna wajen arewa. Ɗakunan da suke bisa ba su da fāɗi, gama mataki hawan benen ya cinye wuri fiye da a ɗakunan da suke a hawa na ƙasa da na tsakiya. Ɗakunan da suke a hawa na uku ba su da ginshiƙai, yadda filayen suka kasance da su, saboda haka suka matsu fiye da waɗanda suke a hawa na ƙasa da na tsakiya. Akwai katanga wadda take waje, wadda ta yi hannun riga da ɗakunan filin waje; ta miƙe a gaban ɗakunan, tsawonta kamu hamsin ne. Yayinda tsawon jerin ɗakunan da suke a gefe kusa da filin da yake waje kamu hamsin ne, tsawon jerin ɗakunan da suke a gefen da yake kurkusa da wuri mai tsarki kamu ɗari ne. Ɗakunan da suke can ƙasa suna da ƙofar shiga a wajen gabas in za a shiga cikinsu daga filin da yake waje. A wajen kudu a ta katangar filin da yake waje, kusa da filin haikali da yake ɗaura da katangar waje, akwai ɗakuna da hanya a gabansu. Waɗannan sun yi kama da ɗakunan da suke wajen arewa; tsawonsu da fāɗinsu duk iri ɗaya ne, da irin mafita ɗaya da kuma yadda aka shirya su. Sun yi kama da ƙofofin da suke wajen arewa haka ma ƙofofin ɗakunan a wajen kudu. Akwai ƙofa a farkon hanyar da ta yi hannun riga da ɗayan katangar da ta miƙe wajen gabas, inda za a iya shiga ɗakunan. Sai ya ce mini, “Ɗakunan arewa da na kudu waɗanda suke fuskantar filin haikali ɗakunan firistoci ne, inda firistocin da suke kusaci Ubangiji za su ci hadayu mafi tsarki. A can za su ajiye hadayu mafi tsarki, hadayu na gari, hadayu na zunubi da hadayu na laifi, gama wuri mai tsarki ne. Da zarar firistoci suka shiga wuri mai tsarki, ba za su fita zuwa filin da yake waje ba sai sun tuɓe rigunan da suka yi hidima da su, gama waɗannan masu tsarki ne. Za su sa waɗansu riguna kafin su kusaci wuraren da mutane suke.” Da ya gama auna filin da yake cikin haikali, sai ya fitar da ni ta ƙofar gabas ya auna dukan filin kewaye. Ya auna gefen gabas da karan awo; ya samu kamu ɗari biyar. Ya auna gefen arewa da karan awon; ya samu kamu ɗari biyar. Ya auna gefen kudu da karan awon; ya samu kamu ɗari biyar. Sa’an nan ya juya zuwa gefen yamma ya auna shi da karan awon, ya samu kamu ɗari biya. Ta haka ya auna dukan kusurwoyi huɗu. Filin yana da katanga kewaye da shi, tsawon kamu ɗari biyar, fāɗin kuma kamu ɗari biyar don yă raba wuri mai tsarki daga wuri marar tsarki. Sai mutumin ya kawo ni ƙofar da take fuskantar gabas, sai na ga ɗaukakar Allah na Isra’ila tana tahowa daga gabas. Muryarsa ta yi kamar rurin ruwaye masu gudu, ƙasa kuma ta haskaka da ɗaukakarsa. Wahayin da na gani ya yi kamar wahayin da na gani sa’ad da ya zo don yă hallaka birnin, kamar kuma wahayin da na gani kusa da Kogin Kebar, na kuwa fāɗi rubda ciki. Ɗaukakar Ubangiji ta shiga haikali ta ƙofar da take fuskantar gabas. Sa’an nan Ruhu ya ɗaga ni sama ya kawo ni cikin fili na can ciki, ɗaukakar Ubangiji kuwa ta cika haikalin. Yayinda mutumin yana tsaye kusa da ni, na ji wani yana magana da ni daga cikin haikalin. Ya ce, “Ɗan mutum, wannan shi ne kursiyina da wurin tafin ƙafafuna. A nan ne zan zauna a cikin Isra’ilawa har abada. Gidan Isra’ila ba zai ƙara ɓata sunana mai tsarki ba, ko su ko sarakunansu, ta wurin karuwanci da gumakan da ba su da rai, sarakunansu a masujadan kan tudu. Sa’ad da suka sa madogarar ƙofarsu kusa da madogarar ƙofata, da katanga kawai a tsakanina da su, sun ɓata sunana mai tsarki ta wurin ayyukansu masu banƙyama. Saboda haka na hallaka su cikin fushina. Yanzu bari su kawar da karuwancinsu da gumakansu waɗanda ba su da rai na sarakunansu daga gabana, zan kuwa zauna a cikinsu har abada. “Ɗan mutum, ka bayyana haikalin ga mutanen Isra’ila, don su ji kunya saboda zunubansu. Bari su yi la’akari da fasalin, kuma in suka ji kunyar abubuwan da suka aikata, sai ka sanar musu fasalin haikalin da shirye-shiryensa, ƙofofinsa na shiga da fita, dukan fasalinsa da dukan ƙa’idodinsa da dokokinsa. Ka rubuta waɗannan a gabansu saboda su yi aminci da fasalinsa su kuma kiyaye dukan ƙa’idodinsa. “Wannan ita ce dokar haikalin. Dukan filin da yake kewaye a kan dutsen, zai zama wuri mafi tsarki. Dokar haikalin ke nan. “Waɗannan su ne aune-aunen bagade a tsawon kamu, wannan kamu shi ne kamun tafin hannu. Zurfin magudanar ruwansa kamu ɗaya ne fāɗinsa kuma kamu ɗaya, tare da da’ira kamun tafi ɗaya kewaye da gefensa. Wannan kuma shi ne tsayin bagaden. Daga lambatun da yake a ƙasa har zuwa ƙaramin mahaɗin da yake ƙasa wanda ya kewaye bagade, tsayinsa kamu biyu ne, fāɗinsa kuma kamu guda. Daga ƙaramin mahaɗi zuwa babban mahaɗin wanda ya kewaye bagade, zai zama kamu huɗu, fāɗinsa kuwa kamu ɗaya. Murhun bagaden kamu huɗu ne, akwai ƙahoni guda huɗu sun miƙe sama daga murhun. Murhun bagaden murabba’i ne, tsawonsa kamu goma sha biyu, fāɗinsa kuma kamu goma sha biyu. Gefen bisa ma murabba’i ne, tsawonsa kamu goma sha huɗu fāɗinsa kuma kamu goma huɗu, da da’ira da yake da fāɗin rabin kamu da magudanan ruwa kamu guda kewaye. Matakan bagaden suna fuskantar gabas.” Sai ya ce mini, “Ɗan mutum, ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa waɗannan su ne za su zama ƙa’idodi don yin hadaya ta ƙonawa da yayyafawar jini a kan bagaden sa’ad da aka gina shi. Za ka ba da ɗan bijimi a matsayin hadaya ta ƙonawa ga firistoci, waɗanda suke Lawiyawa, na iyalin Zadok, waɗanda suke zuwa kusa don hidima a gabana, in ji Ubangiji Mai Iko Duka. Za ka ɗibi jininsa ka zuba shi a ƙahoni huɗu na bagaden a gefen bisa da kuma kewaye da da’irar, ta haka za ka tsarkake bagaden ka kuma yi kafara dominsa. Za ka ɗauki bijimi na hadaya don zunubi ka ƙone shi a sashen da aka shirya na haikalin a wani wuri waje da wuri mai tsarki. “A rana ta biyu za ka miƙa bunsuru marar lahani domin hadaya don zunubi, za a kuma tsarkake bagaden yadda aka yi da bijimin. Sa’ad da ka gama tsarkake shi, sai ka miƙa ɗan bijimi da kuma rago daga cikin garke, dukansu marasa lahani. Za ka miƙa su a gaban Ubangiji, firistoci kuma za su barbaɗe gishiri a kansu su kuma miƙa su kamar hadaya ta ƙonawa ga Ubangiji. “Kwana bakwai za ka tanada bunsuru kullum domin hadaya don zunubi; za ka kuma tanada ɗan bijimi da rago daga garke, dukansu marasa lahani. Kwana bakwai za su yi kafara saboda bagaden su kuma tsarkake shi; ta haka za su keɓe shi. A ƙarshen waɗannan kwanaki, daga rana ta takwas zuwa gaba, firistoci za su miƙa hadayu na ƙonawa da hadayu na salama a kan bagade. Sa’an nan zan karɓe ku, in ji Ubangiji Mai Iko Duka.” Sai mutumin ya komo da ni zuwa ƙofar waje na wuri mai tsarki, wadda take fuskantar gabas, tana kuwa a rufe. Ubangiji ya ce mini, “Wannan ƙofar za tă kasance a rufe. Ba za a buɗe ta ba; ba wanda zai shiga ta wurinta. Za tă kasance a rufe domin Ubangiji, Allah na Isra’ila, ya shiga ta wurinta. Sarki kansa ne kaɗai zai zauna a hanyar shiga don yă ci a gaban Ubangiji. Zai shiga ta hanyar shirayin hanyar shiga yă kuma fita a wannan hanya.” Sa’an nan mutumin ya kawo ni ta hanyar ƙofar arewa zuwa gaban haikali. Na duba na kuma ga ɗaukakar Ubangiji tana cika haikalin Ubangiji, sai na fāɗi rubda ciki. Ubangiji ya ce mini, “Ɗan mutum, ka lura sosai, ka saurara sosai ka kuma mai da hankali ga kome da na faɗa maka game da dukan ƙa’idodi game da haikalin Ubangiji. Ka lura sosai da ƙofar shigar haikali da kuma dukan ƙofofin wuri mai tsarki. Faɗa wa ’yan tawayen gidan Isra’ila, ‘Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa ayyukan banƙyamarku sun isa haka, ya gidan Isra’ila! Ban da dukan sauran ayyukanku na banƙyama, kun kawo baƙi marasa kaciya a zuciya da jiki a wurina mai tsarki, kun kuma ƙazantar da haikalina yayinda kuke miƙa mini abinci, kitse da kuma jini, kun kuma karya alkawarina. A maimakon yin ayyukanku bisa ga abubuwana masu tsarki, kun sa waɗansu su lura da wurina mai tsarki. Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa ba baƙo marar kaciya a zuciya da jiki da zai shiga wurina mai tsarki, kai, har ma da baƙin da suke zama a cikin Isra’ila. “ ‘Lawiyawan da suka yi nesa da ni sa’ad da Isra’ila suka kauce da kuma waɗanda suka karkata daga gare ni suka bi gumakansu, dole su ɗauki alhakin zunubinsu. Za su iya yin hidima a wurina mai tsarki, suna lura da ƙofofin haikali suna kuma hidima a cikinsu; za su iya yankan hadayun ƙonawa da sadaka don mutane su kuma tsaya a gaban mutane su yi musu hidima. Amma domin sun yi musu hidima a gaban gumakansu suka sa gidan Isra’ila ya yi zunubi, saboda haka na ɗaga hannu na rantse cewa dole su ɗauki alhakin zunubinsu, in ji Ubangiji Mai Iko Duka. Ba za su yi kusa don su yi hidima kamar firistoci ko su zo kusa da abubuwana masu tsarki ko hadayuna mafi tsarki ba; dole su sha kunya saboda ayyukansu na banƙyama. Duk da haka zan sa su su lura da ayyukan haikali da kuma dukan ayyukan da za a yi a cikinsa. “ ‘Amma firistoci, waɗanda suke Lawiyawa kuma zuriyar Zadok waɗanda suka yi aminci ta wurin yin ayyukansu a wurina mai tsarki sa’ad da Isra’ilawa suka kauce daga gare ni, su ne za su zo kusa don hidima a gabana; za su tsaya a gabana don miƙa hadayun kitse da jini, in ji Ubangiji Mai Iko Duka. Su ne kaɗai za su shiga wurina mai tsarki; su ne kaɗai za su zo kusa da teburina don yin hidima a gabana su kuma yi hidimata. “ ‘Sa’ad da suka shiga ƙofofin fili na can ciki, dole su sa tufafin lilin; kada su sa wani rigar da aka yi da ulu yayinda suke hidima a ƙofofin fili na can ciki da cikin haikali. Za su naɗa rawunan lilin a kawunansu, su kuma sa wandunan lilin. Kada su sa wani abin da zai sa su yi zuffa. Sa’ad da suka fita daga haikali zuwa fili na waje inda mutane suke, sai su tuɓe rigunan da suka yi hidima da su su bar su a tsarkakan ɗakuna, su sa waɗansu riguna, don kada su tsarkake mutane ta wurin rigunansu. “ ‘Ba za su aske kawunansu ko su bar gashin kansu ya yi tsayi ba, amma sai su sausaye gashin kansu. Kada firist ya sha ruwan inabi sa’ad da zai shiga fili na can ciki. Kada su auri gwauruwa ko macen da aka sāke; za su auri budurwai ne kaɗai na Isra’ilawa ko gwaurayen firistoci. Za su koyar da mutanena bambanci tsakanin tsarki da rashin tsarki su kuma nuna musu yadda za su bambanta marar tsarki da mai tsarki. “ ‘A duk wani rashin jituwa, firistoci za su zama alƙalai su kuma yanke magana bisa ga farillaina. Za su kiyaye dokokina da ƙa’idodina a dukan ƙayyadaddun bukukkuwana, su kuma kiyaye Asabbataina da tsarki. “ ‘Firist ba zai ƙazantar da kansa ta wurin zuwa kusa da gawa ba; amma, in gawar mahaifinsa ko mahaifiyarsa, ko ɗansa ko ’yarsa, ko ɗan’uwansa ko ’yar’uwarsa ce, to, ba zai ƙazantar da kansa ba. Bayan ya tsarkaka, dole yă jira har kwana bakwai. A ranar da ya shiga fili na can ciki na wuri mai tsarki don hidima a wuri mai tsarki, zai miƙa hadaya don zunubi saboda kansa, in ji Ubangiji Mai Iko Duka. “ ‘Ni ne kaɗai zan zama abin gādon da firistoci za su kasance da shi. Kada ka ba su wani mallaka a Isra’ila; zan zama mallakarsu. Za su ci hadaya ta gari, hadaya don zunubi da hadaya don laifi; da kuma kowane keɓaɓɓen abu a Isra’ila da za a ba wa Ubangiji zai zama nasu. Mafi kyau na nunan farinku da kuma dukan kyautanku na musamman za su zama na firistoci. Za ku ba su rabo na fari na ɓarzajjen hatsinku saboda albarka ta kasance a gidanku. Firistoci ba za su ci mushen tsuntsu ko na dabba ba, ba kuwa za su ci waɗanda namun jeji suka kashe ba. “ ‘Sa’ad da kuka rarraba ƙasar gādo, ku miƙa wa Ubangiji rabon ƙasar ya zama yanki mai tsarki, tsawonsa ya zama kamu 25,000 fāɗinsa kuma ya zama 20,000, dukan ƙasar za tă zama mai tsarki. Daga cikin wannan, sashe guda da yake murabba’i mai tsawo kamu 500 zai zama don wuri mai tsarki, kamu 50 kewaye da shi zai zama fili. A cikin yanki mai tsarki, ka auna tsawo kamu 25,000 da kuma fāɗi kamu 10,000. A cikinsa wuri mai tsarki zai kasance, Wuri Mafi Tsarki. Zai zama tsattsarkan rabo na ƙasa domin firistoci, waɗanda za su yi hidima a cikin wuri mai tsarki da kuma waɗanda za su zo kusa don su yi hidima a gaban Ubangiji. Zai zama wuri don gidajensu ya kuma zama tsattsarkan wuri saboda wuri mai tsarki. Wani sashi kuma mai tsawo kamu 25,000 da fāɗi 10,000 zai zama na Lawiyawa, waɗanda suke hidima a cikin haikali, zai zama mallakarsu don su zauna a ciki. “ ‘Za ka ba wa birnin fāɗin mallakarsa kamu 5,000, tsawonsa kuma 25,000, haɗe da tsattsarkan rabo; zai kasance na gidan Isra’ila duka. “ ‘Sarki zai kasance da fili da ya yi iyaka da kowane gefe na yankin wuri mai tsarki da kuma mallakar birnin. Zai miƙe ya yi wajen yamma daga gefen yamma ya kuma yi wajen gabas daga gefen gabas, yana miƙewa a tsawo daga wajen yamma zuwa wajen gabashin iyaka don yă yi hannun riga da rabon kabilan. Wannan fili zai zama mallakarsa a Isra’ila. Kuma sarakunana ba za su ƙara zaluntar mutanena ba amma za su bar gidan Isra’ila ya mallaki ƙasar bisa ga kabilansu. “ ‘Ga abin da Ubangiji Mai Iko na ce ku sarakunan Isra’ila, danniya da zaluncin da kuke yi sun isa! Ku yi shari’a bisa ga gaskiya da adalci, ku bar korar mutanena, in ji Ubangiji Mai Iko Duka. Ku yi amfani da garwan da yake daidai, efa da yake daidai da kuma garwa da yake daidai. Efa da garwan su kasance girmansu ɗaya, garwan ya zama kashi ɗaya bisa goma na ganga efa kuma ya zama kashi ɗaya bisa goma na ganga; ganga fitaccen ma’auni na duka biyu. Shekel zai kasance da gera ashirin. Shekel ashirin a haɗa da shekel ashirin da biyar a haɗa da shekel goma sha biyar zai zama mina guda. “ ‘Wannan ita ce bayarwa ta musamman da za ku miƙa, kashi ɗaya bisa shida na efa daga kowace gangan alkama da kashi ɗaya bisa shida na efa daga kowace gangan sha’ir. Sashe na man da aka ƙayyade, da aka auna da garwa, kashi ɗaya bisa goma ne na garwa daga ganga (wanda yakan ci garwa goma, gama garwa goma suna daidai da ganga guda). A kuma ba da tunkiya daga kowane garke mai tumaki ɗari biyu daga makiyaya da aka yi masa banruwa sosai na Isra’ila. Za a yi amfani da waɗannan don hadayun gari, hadayun ƙonawa da hadayun salama don yin kafara saboda mutane, in ji Ubangiji Mai Iko Duka. Dukan mutanen ƙasar za su yi wannan bayarwa ta musamman saboda amfanin sarki a Isra’ila. Zai zama hakkin sarki ne ya tanada hadayu na ƙonawa, hadayu na gari da hadayu na sha a bukukkuwa, Sabuwar Wata da Asabbatai, a duk ƙayyadaddun bukukkuwa na gidan Isra’ila. Zai tanada hadayu don zunubi, hadayu na gari, hadayu na ƙonawa da hadayu na salama don yin kafara saboda gidan Isra’ila. “ ‘Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa a farkon wata a rana ta fari za ku ba da ɗan bijimi marar lahani a kuma tsarkake wuri mai tsarki. Firist zai ɗibi jinin hadaya don zunubi ya shafa a madogaran ƙofar haikali, a kusurwoyi huɗu na gefen bisa na bagade da kuma a kan madogaran ƙofar shiga na fili na can ciki. Za ku yi haka kuma a rana ta bakwai ga watan domin duk wanda ya yi zunubai ba da gangan ba ko ta wurin rashin sani; saboda haka sai ku yi kafara domin haikalin. “ ‘A wata na fari a rana ta goma sha huɗu za ku kiyaye Bikin Ƙetarewa, bikin da yakan ɗauki kwana bakwai, a lokacin ne za ku riƙa cin burodi marar yisti. A wannan rana sarki zai tanada bijimi a matsayin hadaya don zunubi domin kansa da kuma domin dukan mutanen ƙasar. Kowace rana a kwanaki bakwai na Bikin zai tanada bijimai guda bakwai da raguna bakwai marar lahani a matsayi hadaya ta ƙonawa ga Ubangiji, da kuma bunsuru saboda hadaya don zunubi. Zai tanada efa na gari don kowane bijimi da kuma efa don kowane rago, tare da kwalabar mai don kowane efa guda. “ ‘A lokacin kwana bakwai na Bikin, waɗanda za su fara a wata na bakwai a rana ta goma sha biyar, zai ba da abubuwan nan saboda hadayu don zunubi, hadayu na ƙonawa, hadayu na gari da kuma mai. “ ‘Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa a rufe ƙofa ta fili na can cikin da take fuskantar gabas ranaku shida na aiki, amma a ranar Asabbaci da kuma a ranar ganin Sabuwar Wata a buɗe ta. Sarki zai shiga daga waje ta shirayin hanyar shiga yă tsaya a madogarar ƙofa. Firistoci za su miƙa hadayarsa ta ƙonawa da hadayunsa na salama. Zai yi sujada a madogarar ƙofar hanyar shiga sa’an nan ya fita, amma ba za a rufe ƙofar ba sai da yamma. A Asabbatai da kuma a Sabuwar Wata mutanen ƙasar za su yi sujada a gaban Ubangiji a mashigin wannan hanyar shiga. Hadaya ta ƙonawar da sarki ya kawo wa Ubangiji a ranar Asabbaci ’yan raguna shida ne da rago guda, dukansu marasa lahani. Hadayar garin da aka bayar tare da ragon efa guda ne, hadayar garin da ’yan ragunan yadda ya ga dama, tare da kwalabar mai don kowace efa. A ranar Sabuwar Wata zai miƙa ɗan bijimi, ’yan raguna guda shida da kuma rago guda, dukansu marasa lahani. Zai tanada a matsayin hadaya ta gari, efa guda tare da bijimi, efa guda tare da ’yan raguna, da kuma ’yan raguna yadda ya ga dama, tare da kwalabar mai don kowace efa. Sa’ad da sarki zai shiga, zai shiga ta shirayin hanyar shiga, zai kuma fita ta nan. “ ‘Sa’ad da mutanen ƙasar suka zo gaban Ubangiji a ƙayyadaddun bukukkuwa, duk wanda ya shiga ta ƙofar arewa don yă yi sujada sai ya fita ta ƙofar kudu; kuma duk wanda ya shiga ta ƙofar kudu sai ya fita ta ƙofar arewa. Ba wanda zai koma ta ƙofar da ya shiga, amma kowa zai fita a ƙofar ɗaura da wadda ya shiga. Sarki zai kasance a cikinsu, zai shiga sa’ad da suke shiga ya kuma fita sa’ad da suka fita. “ ‘A bukukkuwa da ƙayyadaddun bukukkuwa, hadaya ta gari zai zama efa tare da bijimi, efa da rago, da kuma ’yan raguna da ya ga dama, haɗe da kwalabar mai. Sa’ad da sarki ya ba da hadaya ta yardar rai ga Ubangiji, ko hadaya ta ƙonawa ce ko hadayun salama ne, sai a buɗe masa ƙofar da take fuskantar gabas. Zai miƙa hadayarsa ta ƙonawa ko hadayarsa ta salama yadda yakan yi a ranar Asabbaci. Sa’an nan ya fita, bayan kuma ya fita, sai a rufe ƙofar. “ ‘Kullum za ku tanada ɗan rago bana ɗaya marar lahani don hadaya ta ƙonawa ga Ubangiji; kowace safiya za ku tanada shi. Tare da shi za ku tanada hadaya ta gari kowace safiya, da ya haɗa da kashi ɗaya bisa shida na efa tare da kashi ɗaya bisa uku na mai ga garin da aka cuɗa. Miƙawar wannan hadaya ta gari ga Ubangiji dawwammamiyar farilla ce. Saboda haka za a tanada ɗan rago da hadaya ta gari da kuma mai kowace safiya don hadaya ta ƙonawa ta kullum. “ ‘Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa in sarkin ya ba wa ɗaya daga cikin ’ya’yansa kyauta daga gādonsa, zai kuwa zama na zuriyar; zai kuwa zama mallakarsu ta wurin gādo. In kuma ya ba wa ɗaya daga cikin bayinsa kyauta daga gadonsa, bawan zai iya riƙe shi sai shekarar ’yantarwa; sa’an nan ya mayar wa sarkin. Gādon sarki na ’ya’yansa maza ne kaɗai; na su ne. Kada sarki ya ƙwace gādon mutane, yana korinsu daga mallakarsu. Zai ba wa ’ya’yansa maza gādonsu daga cikin mallakarsa, don kada a raba wani daga mutanena da mallakarsa.’ ” Sa’an nan mutumin ya fitar da ni ta ƙofar shiga a gefen ƙofar zuwa tsarkakakkun ɗakuna waɗanda suke fuskantar arewa, waɗanda suke na firistoci, ya kuma nuna mini wani wuri daga can ƙurewar yamma. Ya ce mini, “Wannan shi ne wurin da firistoci za su dafa hadaya don laifi, da hadaya don zunubi, a nan ne kuma za su toya hadaya ta gari, domin kada su kai su a filin da yake waje, su tsarkake mutane.” Sa’an nan ya kawo ni filin da yake waje ya kuma bi da ni kewaye da kusurwoyi huɗunsa, na kuma ga kowace kusurwa na wani fili. A kusurwoyi huɗu na filin da yake waje akwai waɗansu filaye a haɗe, tsawonsu kamu arba’in fāɗinsu kuwa kamu talatin; kowane fili a kusurwoyi huɗun nan girmansu ɗaya ne. Kewaye da cikin kowane filin huɗun nan akwai ginin dutse, da murhu da aka gina a kewaye a ƙarƙashin ginin. Sai ya ce mini, “Waɗannan su ne ɗakunan dahuwa inda masu hidima a haikali za su dafa hadayun da jama’a.” Mutumin ya komo da ni zuwa mashigin haikalin, sai na kuwa ga ruwa yana malalowa daga ƙarƙashin madogarar ƙofar haikalin wajen gabas (gama haikalin yana fuskantar gabas). Ruwan yana malalowa daga ƙarƙashin gefen kudun haikalin, kudu da bagaden. Sai ya fitar da ni ta ƙofar arewa ya kewaye da ni ta waje zuwa ƙofar da take waje mai fuskantar gabas, ruwan kuwa yana malalowa daga wajen kudu. Yayinda mutumin ya yi wajen gabas da karan awo a hannunsa, sai ya auna kamu dubu ya kuma bi da ni ta ruwan da zurfinsa ya kama ni a idon ƙafa. Ya auna wani kamu dubu ya kuma bi da ni a ruwan da zurfinsa ya kai ni gwiwa. Ya sāke auna kamu dubu ya kuma bi da ni a ruwan da zurfinsa kama ni a gindi. Ya auna wani kamu dubu, amma a yanzu ruwan ya zama kogin da ban iya hayewa ba, domin ruwan ya taso ya kuma yi zurfin da ya isa a yi iyo a ciki, kogin da ba za a iya hayewa ba. Sai ya ce mini, “Ɗan mutum, ka ga wannan?” Sa’an nan ya komo da ni zuwa bakin kogin. Sa’ad da na iso can, sai na ga itatuwa masu yawa a kowane gefen kogin. Sai ya ce mini, “Wannan ruwa yana malalowa zuwa yankin gabas ya kuma gangaro zuwa cikin Araba, inda zai shiga Teku. Sa’ad da ya shiga cikin Tekun sai ruwan a can ya zama mai daɗi. Tarin halittu masu rai za su rayu a duk inda ruwan ya malalo. Za a kasance da kifi masu yawa, domin wannan ruwa yana malalowa a can yana kuma mai da ruwan gishiri yă zama ruwa mai daɗi; saboda haka duk inda ruwan ya malalo, kome zai rayu. Masunta za su tsaya a gaɓar; daga En Gedi zuwa En Eglayim, za a kasance da wuraren jefa abin kamun kifi. Za a sami kifayen iri-iri, kamar kifaye Bahar Rum. Amma fadamun da tafkunan ba za su zama masu daɗi ba; za a bar su a gishirinsu. ’Ya’yan itatuwa na kowane iri za su yi girma a kowane gefen kogin. Ganyayensu ba su bushe ba, ba kuwa za su fasa yin ’ya’ya ba. Kowane wata za su ba da ’ya’ya domin ruwa daga wuri mai tsarki yana malalo musu. ’Ya’yansu za su zama abinci, ganyayensu kuma za su zama magani.” Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa, “Waɗannan su ne iyakokin da za ku raba ƙasar gādo cikin kabilan Isra’ila goma sha biyu, da rabo biyu don Yusuf. Za ku raba ta daidai a cikinsu. Gama na ɗaga hannu na rantse zan ba da ita ga kakanninku, wannan ƙasa za tă zama gādonku. “Wannan ce za tă zama iyakar ƙasa. “A wajen arewa za tă fara daga Bahar Rum ta hanyar Hetlon ta wuce Lebo Hamat zuwa Zedad, Berota da Sibrayim (wadda take a iyaka tsakanin Damaskus da Hamat), har zuwa Hazer-Hattikon, wadda take a iyakar Hauran. Iyakar za tă miƙe daga teku zuwa Hazar-Enon, ta iyakar Damaskus, da iyakar Hamat a arewa. Wannan ita ce iyakar a wajen arewa. A wajen gabas iyakar za tă kama tsakanin Hauran da Damaskus, ta bi ta Urdun tsakanin Gileyad da ƙasar Isra’ila, zuwa tekun gabas har zuwa Tamar. Wannan ita ce iyakar a wajen gabas. A wajen kudu za tă fara daga Tamar har zuwa ruwan Meriba Kadesh, sa’an nan ta bi Rafin Masar zuwa Bahar Rum. Wannan ita ce iyakar a wajen kudu. A wajen yamma, Bahar Rum ne zai zama iyakar zuwa wani wuri ɗaura da Lebo Hamat. Wannan ita ce iyakar a wajen yamma. “Za ku rarraba wannan ƙasa a tsakaninku bisa ga kabilan Isra’ila. Za ku raba ta kamar gādo wa kanku da kuma wa baƙin da suka zauna a cikinku waɗanda suke da ’ya’ya. Za ku ɗauka su kamar ’yan ƙasa haifaffun Isra’ilawa; za su yi gādo tare da ku a cikin kabilan Isra’ila. A duk kabilar da baƙon yake zama, a can za ku ba shi gādonsa,” in ji Ubangiji Mai Iko Duka. “Ga kabilan, a jere bisa ga sunayensu. “A iyaka ta arewa, Dan zai sami rabo; zai bi hanyar Hetlon zuwa Lebo Hamat. Hazar-Enan da iyakar arewancin Damaskus kusa da Hamat za tă zama sashen iyakarsa a wajen gabas zuwa wajen yamma. Asher zai sami rabo; zai yi iyaka da yankin Dan daga gabas zuwa yamma. Naftali zai sami rabo; zai yi iyaka da yankin Asher daga gabas zuwa yamma. Manasse zai sami rabo; zai yi iyaka da yankin Naftali daga gabas zuwa yamma. Efraim zai sami rabo; zai yi iyaka da yankin Manasse daga gabas zuwa yamma. Ruben zai sami rabo; zai yi iyaka da Efraim daga gabas zuwa yamma. Yahuda zai sami rabo; zai yi iyaka da yankin Ruben daga gabas zuwa yamma. “Kusa da yankin Yahuda daga gabas zuwa yamma zai zama rabon da za ku bayar a matsayin kyauta ta musamman. Faɗinsa zai zama kamu 25,000, tsawonsa kuma zai zama daidai da tsawon yankunan kabilu daga gabas zuwa yamma; wuri mai tsarki zai kasance a tsakiyar wannan yanki. “Tsawon rabo na musamman da za ku bayar ga Ubangiji zai zama kamu 25,000, fāɗinsa kuma kamu 10,000. Wannan ne zai zama tsattsarkan rabo domin firistoci. Tsawon zai zama kamu 25,000 a wajen arewa, fāɗin kuma kamu 10,000 wajen yamma, kamu 10,000 zai zama fāɗinsa a wajen gabas, tsawonsa a wajen kudu zai zama kamu 25,000. A tsakiyarsa ne wuri mai tsarki na Ubangiji zai kasance. Wannan zai zama na keɓaɓɓun firistoci, zuriyar Zadok, waɗanda suka yi aminci cikin hidimata ba su kuwa karkata kamar yadda Lawiyawa suka yi sa’ad da Isra’ilawa suka karkace ba. Zai zama kyauta ta musamman a gare su daga tsattsarkan rabon ƙasar, kusa da yankin Lawiyawa. “Dab da yankin firistoci, Lawiyawa za su sami rabo mai tsawon kamu 25,000, fāɗin kuma kamu 10,000. Tsawonsa gaba ɗaya zai zama kamu 25,000, fāɗinsa kuma kamu 10,000. Ba za su sayar da shi ko su musayar da wani sashensa ba. Wannan shi ne mafi kyau na ƙasar ba kuma za a jinginar da ita ga wani ba, gama mai tsarki ce ga Ubangiji. “Sauran wurin da ya rage mai fāɗin kamu 5,000 da tsawon kamu 25,000 zai zama don amfanin kowa a birnin, don gidaje da wurin kiwo. Birnin zai kasance a tsakiyar wurin da ya ragen nan zai kuwa kasance da wannan awon, a wajen arewa kamu 45,000, wajen kudu kamu 45,000, wajen gabas kamu 45,000, wajen kudu kuma kamu 45,000. Wurin kiwo don birnin zai zama kamu 250 a wajen arewa, kamu 250 a wajen kudu, kamu 250 a wajen gabas da kuma kamu 250 a wajen yamma. Tsawon abin da ya rage a wurin, dab da tsattsarkan rabo, zai zama kamu 10,000 wajen gabas, kamu 10,000 kuma wajen yamma. Amfanin da zai bayar zai tanada abinci don ma’aikatan birnin. Masu aiki daga birnin waɗanda suka nome ta za su fito daga dukan kabilan Isra’ila. Dukan rabon zai zama murabba’i, kamu 25,000 kowane gefe. A matsayin kyauta ta musamman za ku keɓe tsattsarkan rabo, haka ma za ku yi da mallakar birnin. “Abin da ya rage a kowane gefe na wurin zai zama tsattsarkan rabo kuma mallakar birnin za tă zama ta sarki. Zai miƙe wajen gabas daga kamu 25,000 na tsattsarkan rabo zuwa iyakar da take wajen gabashin iyaka, da kuma a wajen yamma kamu 25,000 zuwa iyakar da take a wajen yamma. Dukan wuraren nan da suke hannun riga da rabon kabilan zai zama na sarki, tsattsarkan rabon tare da wuri mai tsarkin za su kasance a tsakiyarsu. Ta haka mallakar Lawiyawa da mallakar birnin za su kasance a tsakiyar wurin da yake na sarki. Wurin da yake na sarki zai kasance tsakanin iyakar Yahuda da iyakar Benyamin. “Game da sauran kabilun kuwa, “Benyamin zai sami rabo; zai miƙe daga wajen gabas zuwa wajen yamma. Simeyon zai sami rabo; zai yi iyaka da yankin Benyamin daga gabas zuwa yamma. Issakar zai sami rabo; zai yi iyaka da yankin Simeyon daga gabas zuwa yamma. Zebulun zai sami rabo; zai yi iyaka da yankin Issakar daga gabas zuwa yamma. Gad zai sami rabo; zai yi iyaka da yankin Zebulun daga gabas zuwa yamma. Iyakar kudu ta Gad za tă miƙe kudu daga Tamar zuwa ruwan Meriba Kadesh, sa’an nan ta bi Rafin Masar zuwa Bahar Rum. “Wannan ce ƙasar da za ku raba gādo ga kabilan Isra’ila, kuma wannan ne zai zama rabonsu,” in ji Ubangiji Mai Iko Duka. “Waɗannan za su zama ƙofofin birnin. “Farawa da gefen arewa, wanda yake da tsawon kamu 4,500 za a ba wa ƙofofin birnin sunaye kabilan Isra’ila. Ƙofofi uku a gefen arewa za su zama ƙofar Ruben, ƙofar Yahuda da ƙofar Lawi. A gefen gabas, wanda yake da tsawon kamu 4,500 zai kasance da ƙofofi uku, ƙofar Yusuf, ƙofar Benyamin da ƙofar Dan. A gefen kudu, wanda yake da tsawon kamu 4,500, zai kasance da ƙofofi uku, ƙofar Simeyon, ƙofar Issakar da ƙofar Zebulun. A gefen yamma, wanda yake da tsawon kamun 4,500, zai kasance da ƙofofi uku, ƙofar Gad, ƙofar Asher da kuma ƙofar Naftali. “Duk nisan wurare kewaye da birnin zai zama kamu 18,000 ne. “Sunan birnin kuwa daga wannan lokaci zai zama, ‘ Ubangiji yana a nan.’ ” A Shekara ta uku ta mulki Yehohiyakim sarkin Yahuda, Nebukadnezzar sarkin Babilon ya zo Urushalima ya kuma yi mata ƙawanya. Sai Ubangiji ya bashe Yehohiyakim sarkin Yahuda a hannunsa, tare da waɗansu kayayyakin haikalin Allah. Ya ɗauki waɗannan kayan zuwa cikin haikalin allahnsa a Babilon cikin ma’ajin gidan allahnsa. Sa’an nan sarkin ya umarci Ashfenaz, shugaban fadarsa yă kawo waɗansu daga cikin Isra’ilawan da suka fito daga gidan sarauta da kuma na fitattun mutane. Matasa maza waɗanda ba su da wata naƙasa kuma kyawawa, hazikai ta kowace hanyar koyo, sanannu, masu saurin fahimtar abu, da kuma waɗanda suka cancanci su yi aiki a fadar sarki. Zai koya musu harshen Babiloniyawa da kuma littattafansu. Sarki kuma ya sa a ba su abinci da ruwan inabi kowace rana daga cikin abincin sarki. Za a koyar da su har shekaru uku, bayan haka kuma su shiga yin wa sarki hidima. Daga cikin waɗannan da aka zaɓa akwai waɗansu daga Yahuda, Daniyel, Hananiya, Mishayel da kuma Azariya. Sai sarkin fada ya raɗa musu sababbin sunaye, ga Daniyel ya raɗa masa Belteshazar; ga Hananiya ya raɗa masa Shadrak; ga Mishayel ya raɗa masa Meshak; ga Azariya kuma ya raɗa masa Abednego. Amma Daniyel ya ƙudura a zuciyarsa ba zai ƙazantar da kansa da abinci da ruwan inabin sarki ba, sai ya tambayi sarkin fada don a ba shi izinin kada yă ƙazantar da kansa ta wannan hanya. Sai Allah ya sa sarkin fada ya nuna masa tagomashi ya kuma ƙaunaci Daniyel, amma sai sarkin fada ya ce wa Daniyel, “Ina jin tsoron ranka yă daɗe, sarkina wanda ya sa a ba ku abinci da ruwan inabi. Me zai sa yă ga kuna ramewa fiye da sauran samari, tsaranku? Sarki zai sa a fille mini kai saboda ku.” Sai Daniyel ya ce wa mai gadi wanda sarkin fada ya sa yă kula da Daniyel, Hananiya, Mishayel da Azariya, “Ina roƙonka ka gwada bayinka kwana goma. Kada ka ba mu kome sai kayan lambu mu ci da kuma baƙin ruwa mu sha. Sa’an nan sai ka dubi fuskokinmu da na sauran samarin da suke ci daga abincin sarki; sa’an nan ka yi da bayinka bisa ga abin da ka gani.” Sai ya amince da haka ya kuma gwada su har kwana goma. A ƙarshen kwana goma sai aka ga fuskokinsu suna sheƙi, sun kuma yi ƙiba fiye da samarin da suke cin abinci irin na sarki. Sai mai gadinsu ya janye abinci da ruwan inabi irin na sarki, ya ci gaba da ba su kayan lambu. Ga samarin nan guda huɗu Allah ya ba su sani da ganewar dukan irin littattafai da kuma koyarwa. Daniyel kuma ya iya gane wahayi da kowane irin mafarki. A ƙarshen lokacin da sarki ya sa da za a kawo su ciki, sai sarkin fada ya gabatar da su ga Nebukadnezzar. Sarki kuwa ya yi magana da su, sai ya gano cewa babu wani kamar Daniyel, Hananiya, Mishayel da kuma Azariya; don haka sai suka shiga yi wa sarki hidima. A dukan al’amuran hikima da na fahimta wanda sarki ya tambaye su, ya tarar sun fi dukan masu sihiri da bokaye waɗanda suke cikin mulkinsa sau goma. Daniyel kuwa ya kasance a nan har shekara ta farko ta mulkin sarki Sairus. A shekara ta biyu ta mulkinsa, Nebukadnezzar ya yi mafarkai; hankalinsa ya tashi har ya kāsa barci. Sai sarki ya sa aka tattara masa masu sihiri da masu dabo da bokaye da masanan taurari domin su faɗi abin da ya yi mafarki a kai. Da suka shigo suka tsaya a gaban sarki, sai ya ce musu, “Na yi mafarkin da ya dame ni kuma ina so in san me yake nufi.” Sai masanan taurarin suka amsa wa sarki da Arameyanci “Ran sarki yă daɗe! Ka faɗa wa bayinka mafarkin, mu kuma sai mu fassara.” Sai sarki ya amsa wa masanan taurarin ya ce, “Na mance da abin, idan ba ku tuno mini mafarkin, duk da fassararsa ba, to, za a daddatse ku gunduwa-gunduwa, a mai da gidajenku juji. Amma in har kuka faɗa mini mafarkina kuka kuma bayyana fassararsa, za ku sami lada mai girma. Saboda haka ku faɗa mini mafarkin da kuma fassararsa.” Sai suka sāke amsa masa suka ce, “Ran sarki yă daɗe, faɗa wa bayinka mafarkin, mu kuma za mu fassara shi.” Sai sarki ya amsa ya ce, “Na gane cewa kuna ƙoƙari ku ɓata lokaci ne kawai domin ku ga na manta da abin. In ba ku faɗa mini mafarkin ba, akwai hukunci guda ɗaya kurum dominku. Kun haɗa baki domin ku faɗa mini munanan al’amura domin ku ruɗe ni har lokaci yă wuce. Sai ku faɗa mini mafarkin, ta haka kuwa zan sani za ku iya yi mini fassararsa.” Sai masanan taurarin suka amsa wa sarki suka ce, “Babu wani mutum a duniyan nan da zai iya yin abin da sarki yake nema! Babu wani sarki mai daraja da girma wanda ya taɓa yin irin wannan tambaya ga masu sihiri ko masu dabo ko masanan taurari. Abin da sarki yake nema yana da wuya matuƙa. Babu wani da zai iya bayyana wannan ga sarki sai dai alloli; kuma ba su zama tare da ’yan adam.” Wannan ya sa sarki ya fusata ƙwarai, ya ba da umarni a tafi da dukan masu hikima na Babilon a kashe su. Sai aka ba da dokar da za a kashe masu hikima, sa’an nan aka aika mutane su je su nemo Daniyel da abokansa domin a kashe su. Sa’ad da Ariyok, shugaban ƙungiyar matsaran sarki, ya fita domin yă kashe masu hikima na Babilon, sai Daniyel ya yi masa magana cikin hikima da dabara. Ya tambayi mai tsaro na sarki, “Me ya sa sarki ya fitar da wannan doka haka da fushi?” Sai Ariyok ya yi wa Daniyel bayanin batun. Da jin haka sai Daniyel ya tafi wurin sarki ya nemi ƙarin lokaci, domin yă bayyana wa sarki mafarkin da kuma fassararsa. Sa’an nan Daniyel ya komo gida ya kuma sanar wa abokansa Hananiya, Mishayel da Azariya, batun nan duka. Ya roƙe su su roƙi jinƙan Allah na sama domin wannan mafarki, saboda kada a kashe shi da abokansa tare da sauran masu hikima na Babilon. A wannan dare sai aka bayyana wa Daniyel mafarkin cikin wahayi. Daniyel kuwa ya ɗaukaka Allah na sama. Ya ce, “Yabo ya tabbata ga sunan Allah har abada abadin; hikima da iko nasa ne. Yana sāke lokuta, yana tuɓe sarakuna yana kuma naɗa waɗansu. Yana ba da hikima ga masu hikima kuma ilimi ga masu basira. Yakan bayyana zurfafa da ɓoyayyun abubuwa; ya san abin da yake cikin dare, haske kuwa yana zaune tare da shi. Na gode maka ina yabonka, Allah na kakannina. Kai ka san hikima da iko, ka sanar da ni abin da muka tambaye ka, ka kuma sanar da mu mafarkin sarki.” Sai Daniyel ya tafi wurin Ariyok, wanda sarki ya sa yă kashe masu hikiman Babilon, ya kuma ce masa, “Kada ka kashe masu hikiman Babilon ka kai ni wurin sarki, ni kuma zan fassara masa mafarkinsa.” Sai Ariyok ya kai Daniyel wurin sarki nan take ya ce masa, “Na gano wani mutum daga cikin kamammun kabilar Yahuda wanda zai faɗa wa sarki abin da mafarkin yake nufi.” Sarki ya tambayi Daniyel (wanda ake kira Belteshazar), za ka iya faɗa mini mafarkin da na yi ka kuma fassara shi? Daniyel ya amsa, “Babu wani mai hikima, ko mai sihiri, ko mai dabo ko mai duban da zai iya warware wa sarki wannan matsala da ta dame shi, amma akwai Allahn da yake a sama wanda yake bayyana asirai, ya nuna wa sarki Nebukadnezzar abin da zai faru a kwanaki masu zuwa. Mafarkinka da wahayin da ya wuce cikin tunaninka a sa’ad da kake kwance a gadonka su ne, “A sa’ad da kake kwance, ya sarki, tunaninka ya ga al’amuran da suke zuwa, kuma shi mai bayyana al’amuran ya bayyana maka asiran abubuwan da za su faru. Amma ba a bayyana mini wannan asiri saboda ina da wata hikima fiye da sauran mutane ba, sai dai domin a sanar wa sarki da fassarar, ka kuma san tunanin da ya shiga zuciyarka. “Ya sarki, ka ga wata babbar siffa, mai girma, siffa ce mai haske, abar bantsoro tana tsaye a gabanka. An yi kan wannan siffa da zinariya zalla, ƙirjinta da kuma hannuwanta an yi su da azurfa, cikinta da kuma cinyarta da tagulla ne. An yi ƙafafun da ƙarfe, tafin ƙafafunta kuma an yi rabi da ƙarfe rabi kuma da yumɓu. A lokacin da kake dubawa, sai aka yanko wani dutse, amma ba da hannun mutum ba. Ya fāɗa a kan ƙafafun siffar na ƙarfen da aka haɗa da yumɓu aka kuma ragargaje su. Sai ƙarfen da yambun da tagulla da azurfan da kuma zinariyan suka ragargaje a lokaci ɗaya ya zama kamar ƙaiƙayi a masussuka a lokacin kaka. Sai iska ta kwashe su ta tafi, har ba a iya ganin ko alamarsu. Amma dutsen da ya fāɗo a siffar ya girke ya zama tsauni ya kuma cika dukan duniya. “Wannan shi ne mafarkin, yanzu kuma za mu fassara ta wa sarki. Ya, sarki, kai ne sarkin sarakuna. Allah na sama ya ba ka iko da girma da suna; a cikin hannunka ya sanya ɗan adam, da namun jeji da tsuntsayen sama. A duk inda suke zaune, ya maishe ka ka yi mulki a bisansu kai ne kan zinariyan nan na siffar. “A bayanka, za a yi wani mulki, wanda bai kai naka ba. A gaba kuma, za a yi mulki na uku wanda yake na tagulla, zai yi mulkin dukan duniya. A ƙarshe, za a yi mulki na huɗu, mai ƙarfi kamar ƙarfe, Da yake baƙin ƙarfe yakan kakkarya, ya ragargaje abubuwa, haka nan wannan mulki zai ragargaje sauran mulkoki Ka kuma ga an yi ƙafafun da yatsotsin da baƙin ƙarfe gauraye da yumɓu, wato, mulkin zai rabu, amma zai kasance da ƙarfi kamar na baƙin ƙarfe da yake gauraye da yumɓu. Kamar yadda yatsotsin rabi na ƙarfe rabi kuma na yumɓu ne, haka wannan mulki zai zama rabi mai ƙarfi rabi kuma marar ƙarfi. Kamar dai yadda ka ga ƙarfen ya gauraye da yumɓu, haka mutanen za su zama a gauraye amma ba za su haɗu da juna ba, kamar yadda baƙin ƙarfe da yumɓu ba su haɗuwa. “A lokacin mulkin waɗannan sarakunan, Allah na sama zai kafa mulki da ba zai taɓa rushewa ba, ba kuma za a ba ma waɗansu mutane ba. Zai ragargaje waɗannan mulkokin da kuma kawo su ga ƙarshe, amma shi wannan mulki zai dawwama har abada. Wannan shi ne ma’anar wannan wahayin da ka gani na dutsen da aka yanko daga jikin tsaunin, amma ba da hannun ɗan adam ba, dutsen da ya ragargaza ƙarfen, da tagullar, da yumɓun da azurfar da kuma zinariyar. “Allah mai girma ya nuna wa sarki abin da zai faru nan gaba. Mafarkin gaskiya ne, fassararsa kuma abin dogara ne.” Sai sarki Nebukadnezzar ya fāɗi da fuskarsa har ƙasa a gaban Daniyel domin ya girmama shi ya kuma umarta a miƙa hadaya da kuma hadayar ƙonawa ta turare ga Daniyel. Sarki ya kuma ce wa Daniyel, “Tabbatacce Allahnka shi ne Allahn alloli da kuma Sarkin sarakuna da mai bayyana asirai, gama ka iya bayyana wannan asiri.” Sai sarki ya ɗora Daniyel a babban matsayi ya kuma sanya shi mai mulki a kan dukan yankin ƙasar Babilon; ya kuma ɗora shi yă zama mai kula da duk masu hikima. Bugu da ƙari, bisa ga bukatar Daniyel sai sarki yă naɗa Shadrak da Meshak da Abednego su zama masu kula da harkokin lardin Babilon, amma Daniyel kuma ya tsaya a fadar sarki. Sarki Nebukadnezzar ya yi gunkin zinariya, tsawonsa kamu tasa’in, fāɗinsa kuma kamu tara ne, ya kafa shi a filin Dura a yankin Babilon. Sa’an nan ya aika a kira hakimai da wakilai da gwamnoni da mashawarta, da ma’aji, da alƙalai, da marubutan kotu, da dukan sauran ma’aikatan yankunan, suka hallara domin a rusuna wa wannan siffar da ya kafa. Saboda haka sai hakimai, da wakilai da gwamnoni, mashawarta da ma’aji da alƙalai, da marubutan alƙalai, da kuma dukan ma’aikatan yankunan suka tattaru domin kaddamar da siffar da Nebukadnezzar ya kafa, suka kuma tsaya a gabansa. Sai mai shela ya daga murya da ƙarfi ya ce, “Wannan shi ne abin da aka umarce ku ku yi, ya ku mutane da al’umma da kowane yare. Da zarar kuka ji karar ƙaho, da sarewa, da garaya da goge da molo da algaita da kowane irin kaɗe-kaɗe da bushe-bushe ku rusuna ku yi sujada ga wannan gunkin da sarki Nebukadnezzar ya kafa. Duk wanda bai rusuna ya yi sujada ba, nan take za a jefa shi a cikin tendarun wuta.” Saboda haka, da zarar suka ji karar ƙaho, da sarewa, garaya da goge da kowane irin kaɗe-kaɗe da bushe-bushe da kowane irin kaɗe-kaɗe kowane mutum da ko wace al’umma da kowane irin yare suka sunkuya suka yi sujada ga wannan siffa ta zinariya da sarki Nebukadnezzar ya kafa. A wannan lokaci sai waɗansu masanan taurari suka zo gaba suka yi karar Yahudawa. Suka ce wa sarki Nebukadnezzar, “Ran sarki yă daɗe, Ya sarki, ka fitar da doka, cewa duk wanda ya ji karar ƙaho, da sarewa, da garayu da goge, da molo da algaita da kowane irin kayan kaɗe-kaɗe da bushe-bushe sai yă rusuna yă yi sujada ga siffar zinariya, kuma cewa duk wanda bai rusuna ya yi sujadar ba za a jefa shi cikin tanderun wuta. Amma sai ga waɗansu Yahudawa waɗanda ka ɗora su a kan harkokin yankin Babilon, wato, Shadrak, Meshak da Abednego waɗanda ba su kula da umarninka ba, ya sarki. Ba su bauta wa allolin ba balle su yi sujada ga gunkin zinariya da ka kafa.” Cikin fushi da hasala, Nebukadnezzar ya aika a kira Shadrak, Meshak da Abednego. Aka kawo waɗannan mutane a gaban sarki, sai Nebukadnezzar ya ce musu, “Gaskiya ne Shadrak, Meshak da Abednego, cewa kun ƙi ku bauta wa alloli kuka kuma ƙi yi sujada ga gunkin da na kafa? Yanzu sa’ad da kuka ji karar ƙaho, da sarewa, da garaya, da goge, da molo da algaita da kowane irin kaɗe-kaɗe da bushe-bushe, in kuna a shirye ku rusuna ƙasa ku yi wa wannan gunkin da na yi sujada, to, da kyau. Amma in ba ku yi sujada ba, za a je fa ku yanzu a cikin tanderun wutar nan. In ga kowane ne allahn nan da zai kuɓutar da ku daga hannuna?” Sai Shadrak, Meshak da Abednego suka amsa wa sarki suka ce, “Ya Nebukadnezzar, ba mu bukata mu kāre kanmu a gabanka a kan wannan batu. In an jefa mu cikin tanderun wutar nan, Allahn da muke bauta wa zai iya cetonmu daga ita, kuma ya sarki, zai cece mu daga hannunka. Amma ko da bai cece mu ba, muna so ka sani, ya sarki; cewa ba za mu bauta wa allolinka ba ko kuma mu yi sujada ga gunkin zinariyar da ka kafa ba.” Sai Nebukadnezzar ya husata da Shadrak, Meshak da Abednego, sai al’amuransa a kansu ya canja. Sai ya umarta a ƙara zuga wutar har sau bakwai domin tă yi zafi fiye da yadda take a dā. Kuma ya umarci waɗansu ƙarfafan sojoji a cikin rundunarsa su daure Shadrak, Meshak da Abednego su jefa su cikin tanderun wutar. Waɗannan mutanen suna sanye da riguna, da wanduna, da rawani da waɗansu kayan sawa, aka daure su, aka jefa su cikin tanderun wuta. Sarki ya ba da umarnin da gaggawa kuma wutar ta yi zafi ƙwarai har harshen wutar ya kashe sojojin nan da suka ɗauki Shadrak, Meshak da Abednego, waɗannan mutane uku kuma a daure, suka fāɗa cikin tanderun wutar. Sai Sarki Nebukadnezzar ya miƙe tsaye, cike da mamaki ya tambayi mashawartansa, “Shin ba mutum uku ba ne muka daure muka jefa cikin wutar?” Suka amsa, “Tabbatacce haka yake ya sarki.” Sai ya ce, “Ku duba ina ganin mutum huɗu suna tafiya suna yawo a cikin wutar, a sake kuma babu abin da ya same su, na huɗun sai ka ce ɗan alloli.” Sai Nebukadnezzar ya matsa kusa da ƙofar tanderun wutar ya yi kira da ƙarfi, “Shedrak, Meshak da Abednego, bayin Allah Mafi Ɗaukaka ku fito! Ku zo nan!” Sai Shadrak, Meshak da Abednego suka fita daga cikin wutar, Sa’an nan hakimai, da wakilai, da gwamnoni da masu ba wa sarki shawara suka kewaya su. Suka ga wutar ba tă yi musu wani lahani a jikinsu ba, babu ko gashin kansu da ya ƙuna; ko warin wuta ma ba su yi ba. Sa’an nan Nebukadnezzar ya ce, “Yabo ya tabbata ga Allahn Shadrak, Meshak da Abednego wanda ya aiko da mala’ikansa ya ceci bayinsa da suka dogara matuƙa a gare shi, suka ki bin umarnin sarki kuma su na a shirye domin su ba da ransu da suka ƙi bauta ko su yi sujada ga wani allah sai dai Allahnsu. Domin haka ina ba da doka cewa duk mutane da kowace al’umma ko kowane yaren da ya ce wani abu mummuna a kan Allahn Shadrak, Meshak da Abednego za a yanka shi gunduwa-gunduwa kuma gidansu zai zama wurin zuba shara, domin babu wani allahn da zai iya ceto ta irin wannan hanya.” Sa’an nan sarki ya ƙara wa su Shadrak, Meshak da Abednego girma a yankin Babilon. Daga sarki Nebukadnezzar. Zuwa ga mutane da al’ummai da kuma kowane yare, da suke zama a duniya. Salama mai yawa ta tabbata a gare ku! Ina murna in shaida muku game da alamu da al’ajabai waɗanda Allah Mafi Ɗaukaka ya yi ta wurina. Alamunsa da girma suke, ayyukansa da girma suke! Mulkinsa mulki ne na har abada; sarautarsa kuma za tă dawwama daga zamani zuwa zamani. Ni, Nebukadnezzar, ina zaune a gidana cikin fadata, ina jin daɗi ina bunkasa. Na yi mafarkin da ya ba ni tsoro. A sa’ad da nake kwance a gadona, siffofi da wahayoyi da suka bi ta cikin tunanina sun firgita ni. Don haka na ba da umarni a tattaro dukan masu hikima na Babilon su bayyana a gabana domin su fassara mini mafarkin. Sa’ad da masu sihiri, da masu dabo, da masanan taurari da masu duba suka zo, na faɗa musu mafarkin, amma ba su iya fassarta mini mafarkin ba. A ƙarshe, sai Daniyel ya zo gabana na kuma faɗa masa mafarkin. (Ana ce da shi Belteshazar, wanda aka ba shi sunan allahna kuma ruhun alloli masu tsarki suna a bisansa.) Na ce, “Belteshazar, shugaban masu sihiri, na san ruhun alloli suna a kanka, babu wani asirin da zai fi ƙarfin ganewarka. Ga dai mafarkin da na yi, sai ka fassara mini. Waɗannan su ne wahayin da na gani a lokacin da nake kwance a gadona, na duba, a gabana kuwa ga wani itace a kafe a tsakiyar duniya, yana da tsawo ƙwarai. Itacen ya yi girma ya kuma yi ƙarfi, har tsayinsa ya taɓa sarari sama; ana iya ganinsa a ko’ina a duniya. Ganyayensa suna da kyau, yana da ’ya’ya jingim, abinci kuma domin kowa da kowa. A ƙarƙashinsa namun jeji suke samun wurin hutawa, kuma tsuntsayen sama suna zaune a bisa rassansa; daga cikinsa kowace halitta take cin abinci. “A cikin wahayin da gani sa’ad da nake kwance a kan gadona, Na duba, a gabana kuwa ga wani ɗan saƙo, mai tsarki, yana saukowa daga sama. Sai ya yi kira da babbar murya ya ce, ‘A sare itacen a kuma yayyanka rassansa; a karkaɗe ganyensa a kuma warwatsar da ’ya’yansa. Bari dabbobi su tashi daga ƙarƙashinsa da kuma tsuntsayen da suke a rassansa. Amma a bar kututturen da kuma saiwoyinsa, a daure shi da ƙarfe da kuma tagulla, a bar shi a cikin ƙasa, a cikin ciyayin filaye. “ ‘Bari yă jiƙu da raɓar, bari yă zauna cikin dabbobi tare da tsire-tsiren duniya. Bari a canja tunaninsa irin na mutane a ba shi tunani irin na dabbobi, har sau bakwai su wuce a kansa. “ ‘An sanar da wannan matsayi ne ta bakin ’yan saƙo, masu tsarki ne kuwa suka sanar da hukuncin, domin masu rai su sani Mafi Ɗaukaka ne mai iko duka a bisa kowane mulkin mutane, yakan kuma ba wa duk wanda ya ga dama, yakan sanya talaka yă zama sarki.’ “Wannan shi ne mafarkin da ni, Nebukadnezzar, na yi. Yanzu Belteshazar, sai ka faɗa mini abin da yake nufi, domin babu wani a cikin masu hikima a mulkina da ya iya fassara mini shi. Amma za ka iya, domin ruhun alloli masu tsarki yana a bisanka.” Sai Daniyel (wanda ake kira Belteshazar) ya tsaya zugum na ɗan lokaci, tunaninsa ya ba shi tsoro. Saboda haka sarki ya ce, “Belteshazar, kada ka bar mafarkin ko ma’anarsa ta tayar maka da hankali.” Belteshazar ya amsa ya ce, “Ranka yă daɗe, in dai har mafarkin zai tsaya a kan abokan gābanka da ma’anarsa kuma ta faɗa kan maƙiyan! Itacen da ka gani; wanda ya yi girma da ƙarfe, da tsayinsa ya taɓa sararin sama, wanda ana ganinsa ko’ina a duniya, wanda ganyayensa masu kyau ne yana da ’ya’yan itace da yawa, wanda yake ba da abinci ga duka, yana ba da wurin hutu ga namun jeji, kuma rassansa suna ɗauke da sheƙar tsuntsayen sama. Ya sarki kai ne itacen nan! Ka yi girma da ƙarfi; girmanka kuma ta kai har sama, mulkinka kuma ya kai ko’ina a duniya. “Ya sarki ka ga ɗan saƙon mai tsarkin nan, yana saukowa daga sama yana cewa, ‘A sare itacen a hallaka shi, amma a bar kututturensa daure da ƙarfe da tagulla, a bar shi can a ɗanyar ciyawar filaye, ya jiƙe da raɓa, ya zauna tare da namun jeji har shekara bakwai.’ “Ga fassarar, ya sarki, wannan ita ce doka wadda Mafi Ɗaukaka ya bayar a kan ranka yă daɗe, sarkina. Za a kore ka daga cikin mutane, za ka kuma zauna cikin namun jeji; za ka ci ciyawa kamar shanu, za ka jiƙe da raɓa har shekara bakwai cif sa’an nan za ka sani cewa Mafi Ɗaukaka ne mai iko duka a kan dukan mulkoki a duniya, yake kuma ba da mulki ga duk wanda ya ga dama. Umarni na barin kututturen itacen da saiwoyinsa yana nufin cewa za a maido maka da mulkinka a lokacin da ka gane cewa Mai sama ne yake mulki. Saboda haka, ya sarki, ina roƙonka ka karɓi shawarar da zan ba ka; ka furta zunubanka ta wurin yin abin da yake daidai. Ka bar muguntarka, ka aikata alheri ga waɗanda ake wulaƙantawa, wataƙila za a ƙara tsawon kwanakinka da salama.” Duk wannan kuwa ya faru da sarki Nebukadnezzar. Bayan wata goma sha biyu, a sa’ad da sarki yake takawa a bisan saman ɗakin fadar Babilon, sai ya ce, “Ba wannan ita ce Babilon babba da na gina domin wurin zaman sarautar Babilon, da ikona kuma domin ɗaukakar darajata ba?” Tun kalmomin suna cikin bakinsa sai ya ji murya daga sama tana cewa, “Wannan shi ne abin da aka zartar a kanka, Sarki Nebukadnezzar. An karɓe ikon mulkinka. Za a kore ka daga cikin mutane za ka kuma yi rayuwa tare da namun jeji. Za ka ci ciyawa kamar sa har shekara bakwai cif, sa’an nan za ka gane Mafi Ɗaukaka ne mai iko duka a kan dukan mulkoki a duniya, yake kuma ba da mulki ga duk wanda ya ga dama.” Nan da nan abin da aka faɗa a kan Nebukadnezzar tabbatarsa ya cika. Aka kore shi daga cikin mutane ya kuma shiga cin ciyawa kamar shanu. Jikinsa ya jiƙe da raɓa, har gashinsa ya yi tsawo kamar fikafikan gaggafa, kumbarsa kuma suka yi tsawo kamar na tsuntsu. A ƙarshen waɗannan kwanaki, ni, Nebukadnezzar, na ɗaga idanuna sama, sai hankalina ya komo mini. Na kuwa yabi Maɗaukaki, na girmama shi, na ɗaukaka shi wanda yake rayayye har abada. Mulkinsa dawwammamen mulki ne; sarautarsa ta dawwama daga zamani zuwa zamani. Dukan mutanen duniya ba a bakin kome suke ba. Yakan yi abin da ya gamshe shi da ikokin sama da kuma na mutanen duniya. Babu mai hana shi ko yă ce masa; “Me ka yi?” A lokacin nan hankalina ya komo mini, sai aka mayar mini da masarautata mai daraja, da martabata, da girmana. ’Yan majalisata da fadawana suka nemo ni. Aka maido ni kan gadon sarautata da daraja fiye da ta dā. Yanzu ni, Nebukadnezzar, ina yabon Sarkin sama, ina waƙa ina kuma darjanta shi, saboda dukan abin da ya yi mini, mai kyau ne kuma dukan hanyoyinsa gaskiya ne. Kuma duk masu tafiya da girman kai zai ƙasƙantar da su. Sarki Belshazar ya yi babban biki domin dubban hakimansa ya kuma sha ruwan inabi tare da su. Yayinda Belshazar yake shan ruwan inabi, sai ya umarta a kawo zinariya da azurfan da Nebukadnezzar mahaifinsa ya kwaso daga haikali a Urushalima, saboda sarki da hakimansa, da matansa da ƙwarƙwaransa su sha da su. Sai suka kawo kayan zinariyan nan da aka kwaso daga haikalin Allah a Urushalima, sarki kuwa da hakimansa, da matansa, da ƙwarƙwaransa suka yi ta sha da su. Yayinda suke shan ruwan inabin, sai suka yabi allolin zinariya da azurfa, da na tagulla, da na ƙarfe, da na itace da kuma na dutse. Nan da nan sai ga yatsotsin hannun mutum sun bayyana, suna yin rubutu a kan shafen bangon, kusa da wurin da ake ajiye fitilar fadar sarki. Sarki kuwa yana ganin hannun yayinda yake rubutu. Sai fuskarsa ta ruɗe, ya kuma ji tsoro ƙwarai har gwiwoyinsa suka yi ta bugun juna, ƙafafunsa kuma suka rasa ƙarfi. Sai sarki ya kira masu dabo, masanan taurari da masu duba, a kawo su, ya kuma ce wa masu hikima na Babilon, “Duk wanda ya karanta wannan rubutu ya kuma faɗa mini abin da yake nufi, za a sa masa rigar shunayya, a kuma sa masa sarƙar zinariya a wuyansa, zai zama na uku a cikin masu mulkin ƙasar.” Sa’an nan sai dukan masu hikima suka zo ciki, amma ba su iya karanta rubutun ba ko su faɗa wa sarki abin da yake nufi. Saboda haka Sarki Belshazar ya firgita ƙwarai kuma fuskarsa ta ƙara ruɗewa. Hakimansa kuma suka rikice. Sai sarauniya, da jin muryoyi na sarki da na hakimansa, ta shiga babban ɗakin liyafar. Ta ce, “Ya sarki, ranka yă daɗe! Kada ka firgita! Kada fuskarka ta ruɗe! Akwai wani mutum a masarautarka wanda yake da ruhun alloli masu tsarki a cikinsa. A zamanin mahaifinka an gane cewa yana da basira da hazaka da hikima kamar na alloli. Sarki Nebukadnezzar mahaifinka, mahaifinka sarki, na ce, ya naɗa shugaban masu dabo, da masu sihiri, masanan taurari da kuma masu duba. Wannan mutum Daniyel, wanda sarki ya kira Belteshazar, an gane yana da ruhu nagari, da ilimi, da ganewa don yin fassarar mafarkai, da bayyana ma’anar kacici-kacici, da warware al’amura masu wuya. Ka kira Daniyel shi kuwa zai faɗa maka abin da rubutun nan yake nufi.” Saboda haka aka kawo Daniyel a gaban sarki, sai sarki ya ce masa, “Kai ne Daniyel ɗin nan, ɗaya daga cikin kamammu waɗanda mahaifina sarki ya kawo daga Yahuda? Na sami labari cewa kana da ruhun alloli a cikinka da kuma basira, da hazaka da kuma fitacciyar hikima. An kawo masu hikima da masu dabo a gabana domin su karanta wannan rubutu su kuma faɗa mini abin da yake nufi, amma ba su iya ba. Na sami labari cewa kana iya ba da fassara da kuma warware matsaloli masu wuya. In har ka iya karanta wannan rubutun ka kuma faɗa mini abin da yake nufi, za a sa maka riga shunayya, a kuma sa sarƙar zinariya a wuyanka. Za ka zama na uku a cikin masu mulkin ƙasar.” Sai Daniyel ya amsa wa sarki ya ce, “Za ka iya ajiye kyautar wa kanka ko kuma ka ba wa wani. Duk da haka, zan karanta wa sarki rubutun, in kuma faɗa abin da yake nufi. “Ya sarki, Allah Mafi Ɗaukaka ya ba mahaifinka Nebukadnezzar sarauta, da girma, da ɗaukaka, da martaba. Saboda irin matsayin da ya ba shi, dukan mutane da al’ummai da kuma dukan harsuna suka ji tsoronsa suka yi rawar jiki a gabansa. Bisa ga ganin damarsa yakan kashe wani, ya bar wani da rai, haka kuma yakan ɗaukaka wani, ya ƙasƙantar da wani. Amma da lokacin da zuciyarsa ta cika da girman kai ta kuma taurare, sai aka kore shi daga gadon sarautarsa, aka raba shi kuma da darajarsa. Aka kore shi daga cikin mutane aka kuma ba shi tunani irin na dabba; ya yi zama tare da jakunan jeji, ya kuma ci ciyawa kamar shanu; jikinsa kuma ya jiƙe da raɓa, har zuwa lokacin da ya gane, ashe, Allah Maɗaukaki ne mai iko duka a kan dukan mulkoki a duniya, yake kuma ba da mulki ga duk wanda ya ga dama. “Amma kai ɗansa, Ya Belshazar, ba ka ƙasƙantar da kanka ba, ko da yake ka san wannan duka. A maimakon, sai ka nuna wa Ubangiji na sama girman kai. Ka sa aka kawo maka su kwaf na zinariya daga haikalinsa, da kai da hakimanka, da matanka da ƙwarƙwaranka kuka sha ruwan inabi da su. Kuka yabi allolin zinariya da na azurfa, da na tagulla, da na baƙin ƙarfe, da na itace, da na dutse waɗanda ba sa ji, ba sa gani, ba sa da gane kome. Amma ba ka girmama Allah ba, wanda ranka da dukan harkokinka suna a hannunsa. Saboda haka ya aiko da hannun da ya yi rubutun nan. “Wannan shi ne rubutun da aka yi, Mene, mene, tekel, farsin “Abin da kalmomin nan suke nufi shi ne, “Mene, Allah ya ƙayyade yawan kwanakin mulkinka ya kuma kawo su ga ƙarshe. “Tekel, An kuma auna ka a ma’auni aka tarar ka kāsa. “Feres, An raba mulkinka aka ba wa Medes da Farisa.” Sai Belshazar ya umarta, aka sa wa Daniyel riga mai shunayya, aka sa sarƙar zinariya a wuyansa, aka kuma yi shela, cewa yanzu shi ne na uku a cikin masu mulkin ƙasar. A wannan dare aka kashe Belshazar, sarkin Babiloniyawa, Dariyus mutumin Medes kuwa ya karɓi mulkin, yana da shekara sittin da biyu. Ya gamshi Dariyus ya naɗa muƙaddasai 120 su yi shugabanci a duk fāɗin masarautar, ya naɗa mutum uku a bisa waɗannan muƙaddasan, Daniyel yana ɗaya daga cikin mutum ukun nan. Sai aka sa muƙaddasan nan a ƙarƙashin waɗannan uku ɗin domin kada sarki ya yi hasarar kome. To, Daniyel dai ya yi ficce a cikin shugabannin nan uku har da muƙaddasan ma, saboda waɗansu halaye nagari da yake da su, wanda ya sa sarki ya yi shiri ya ɗora shi a kan dukan mulkinsa. A kan haka, shugabannin nan uku da muƙaddasan nan suka yi ƙoƙari su sami wani laifi a kan Daniyel a yadda yake tafiyar da aikin shugabancinsa, amma ba su samu ba. Ba su same shi da wani laifin cin hanci ba, domin shi amintacce ne kuma babu wani aibi a kansa ko rashin kula. A ƙarshe waɗannan mutane suka ce; “Ba za mu taɓa samun wani laifin da za mu kama Daniyel da shi ba, sai dai ko abin ya shafi dokar Allahnsa.” Saboda haka shugabannin nan suka haɗu da muƙaddasan nan suka tafi wurin sarki a ƙungiyance suka ce, “Ya Sarki Dariyus, ranka yă daɗe! Shugabannin masarauta, da masu mulki, da muƙaddasai, da mashawarta da gwamnoni duk sun amince cewa sarki yă kafa doka yă kuma yi umarni cewa a cikin kwana talatin nan gaba duk wanda ya yi addu’a ga wani allah ko mutum, in ba a gare ka ba, ya sarki, jefa shi cikin kogon zakoki. Yanzu, ya sarki, sai ka yi umarni ka kuma yi shi a rubuce saboda kada a canja shi, bisa ga dokar Medes da Farisa, waɗanda ba a iya sokewa.” Sai Sarki Dariyus ya ba da umarnin a rubuce. To, da Daniyel ya ji labarin cewa an fitar da doka, sai ya tafi gidansa a ɗakinsa na sama inda tagogin ɗakin suke duban wajen Urushalima. Sau uku yakan durƙusa yă yi addu’a yana yin godiya ga Allahnsa, kamar yadda ya saba yi. Sai waɗannan mutane suka tafi a ƙungiyance suka kuma iske Daniyel yana addu’a yana roƙon Allah yă taimake shi. Sai suka tafi wurin sarki suka yi masa magana game da dokar mulkinsa, suka ce, “Ashe, ba ka yi doka cewa a cikin kwana talatin nan gaba duk wanda aka tarar yana addu’a ga wani allah ko mutum in ba kai ba, ya sarki, za ka jefa shi a cikin ramin zakoki ba?” Sarki ya amsa ya ce, “Dokar tana nan daram bisa ga dokar Medes da Farisa, waɗanda ba a iya sokewa.” Sai suka ce wa sarki, “Daniyel ɗin nan, wanda yake ɗaya daga cikin waɗanda aka kwaso daga Yahuda, bai kula da kai ba, ya sarki, balle fa dokar da ka yi. Har yanzu yana addu’a sau uku a rana.” Da sarki ya ji haka, sai ya damu sosai, ya ƙudura yă ceci Daniyel, ya yi ta fama har fāɗuwar rana yadda zai yi yă kuɓutar da shi. Sai mutanen nan suka je wurin sarki a ƙungiyance suka ce masa, “Ka tuna, ya sarki; cewa bisa ga dokar Medes da Farisa, babu umarni ko dokar da sarki ya yi da za a iya sokewa.” Saboda haka sai sarki ya ba da umarni suka kuma kawo Daniyel suka jefa shi cikin ramin zakoki. Sarki ya ce wa Daniyel, “Bari Allahn nan wanda kake bauta masa kullum, yă cece ka!” Aka kawo dutsen aka rufe bakin ramin, sa’an nan sarki ya hatimce shi da zobensa da kuma zoban manyan mutanensa, don kada wani yă canja yanayin Daniyel. Sa’an nan sarki ya koma fadarsa ya kwana bai ci ba, kuma babu wata liyafar da aka kawo masa. Ya kuma kāsa barci. Gari yana wayewa, sai sarki ya tashi ya hanzarta zuwa ramin zakoki. Da ya yi kusa da ramin zakokin, sai ya kira Daniyel da muryar mai cike da damuwa ya ce, “Daniyel bawan Allah mai rai, ko Allahn nan naka wanda kake bauta wa kullum, ya iya cetonka daga zakoki?” Sai Daniyel ya amsa ya ce, “Ran sarki, yă daɗe! Allahna ya aiko da mala’ikansa, ya kuwa rufe bakunan zakoki. Ba su yi mini rauni ba, gama an same ni marar laifi ne a gabansa. Ban kuwa taɓa yin wani abu marar kyau a gabanka ba, ya sarki.” Sai sarki ya cika da murna ƙwarai, ya kuma yi umarni a ciro Daniyel daga ramin zakoki. Kuma da aka fito da Daniyel daga ramin, ba a sami wani rauni a jikinsa ba, domin ya dogara ga Allahnsa. Sai sarki ya umarta, a kawo mutanen nan da suka yi wa Daniyel maƙarƙashiya, a tura su, da ’ya’yansu, da matansu cikin ramin zakoki. Kafin ma su kai ƙurewar ramin, sai zakoki suka hallaka su suka yayyage su, suka yi kaca-kaca da su. Sa’an nan Sarki Dariyus ya rubuta wa dukan mutane, da al’ummai da kuma mutanen dukan harsunan a duk fāɗin ƙasar. “Bari yă yi nasara sosai! “Na fitar da doka cewa a cikin dukan iyakar ƙasar mulkina, dole mutane su ji tsoro su kuma girmama Allah na Daniyel. “Gama shi ne Allah mai rai kuma madawwami ne har abada; ba za a taɓa lalace masarautarsa ba, mulkinsa kuma ba za tă taɓa ƙarewa ba Yakan kuɓutar ya kuma ceci; yana yin alamu da al’ajabai a sama da kuma a duniya. Shi ya ceci Daniyel daga ikon zakoki.” Daniyel kuwa ya bunkasa a lokacin mulkin Dariyus da kuma mulkin Sairus na Farisa. A shekara ta fari ta mulkin Belshazar sarkin Babilon, Daniyel ya yi mafarki, wahayoyi kuma suka ratsa tunaninsa a sa’ad da yake a kwance a gadonsa. Sai ya rubuta abin da mafarkin ya ƙunsa. Daniyel ya ce, “A cikin wahayina da dare na duba, a gabana kuwa ga kusurwoyi huɗu na sama suna gurɓata babban teku. Sai ga dabbobi huɗu, kowannensu ya yi dabam da sauran, suna fitowa daga teku. “Na farkon ya yi kamar zaki kuma yana da fikafikai kamar gaggafa. Ina kallo, sai aka fizge fikafikanta, aka ɗaga ta sama, aka sa ta tsaya a kan ƙafafu biyu kamar mutum, aka ba ta tunani irin na mutum. “A gabana kuma ga dabba ta biyu, wadda ta yi kamar beyar. Aka ɗaga ta a gefenta guda, tana kuwa da haƙarƙarai uku a bakinta a tsakanin haƙoranta. Aka faɗa mata, ‘Tashi ki cika cikinki da ɗanyen nama!’ “Bayan haka, na duba, a gabana kuwa ga wata dabba wadda ta yi kamar Damisa, a bayanta kuma tana da fikafikai huɗu irin na tsuntsu. Wannan dabbar tana da kawuna huɗu, aka kuma ba ta iko tă yi mulki. “Bayan haka, a cikin wahayina da dare na duba, a gabana kuwa ga dabba ta huɗu, wadda take da bantsoro da banrazana da kuma iko ƙwarai. Tana da manyan haƙoran ƙarfe; ta ragargaje ta cinye abin da ta kama, ta kuma tattaka duk abin da ya rage a ƙarƙashin ƙafafunta. Ta bambanta da dukan sauran dabbobin da suka riga ta, tana kuma da ƙahoni goma. “Yayinda nake cikin tunani game da ƙahonin nan, a gabana kuwa ga wani ƙaho, ɗan ƙanƙani, wanda ya fito daga cikinsu; kuma an tumɓuke uku daga cikin ƙahonin farko kafin wannan. Wannan ƙaho yana da idanu kamar na mutum da kuma bakin da yake maganganun fariya. “Ina cikin dubawa, “sai aka ajiye kursiyoyi, sai ga wani wanda yake tun fil azal ya zauna a mazauninsa. Rigarsa ta yi fari fat kamar ƙanƙara; gashin kansa sun yi fari kamar ulu. Kursiyinsa kuma harshen wuta, dukan ƙafafun kursiyin masu kama da keken yaƙin, wuta ne. Kogin wuta yana gudu, yana fitowa daga gabansa. Dubun dubbai sun yi masa hidima; dubu goma sau dubu goma sun tsaya a gabansa. Aka zauna don shari’a, aka kuma buɗe littattafai. “Sa’an nan na ci gaba da kallo saboda kalmomin fariyar da wannan ƙaho yake furtawa. Na yi ta kallo har sai da aka yanke dabbar, aka kuma hallaka jikinta a cikin wuta. (An tuɓe sauran dabbobin daga mulkinsu, amma aka bar su su rayu na wani lokaci.) “A wahayina na dare, na ga a gabana wani kamar ɗan mutum yana saukowa tare da gizagizan sama. Ya kusaci Wannan wanda yake Tun fil azal aka kuma kai shi gabansa. Aka ba shi mulki, daraja da kuma mafificin iko; dukan mutane, da al’ummai, da mutane daga kowane harshe suka yi masa sujada. Mulkinsa kuwa dawwammamen mulki ne da ba zai ƙare ba, sarautarsa kuma ba ta taɓa lalacewa. “Ni, Daniyel, ruhuna ya damu ƙwarai, kuma wahayin da ya ratsa tunanina ya dame ni. Sai na matsa kusa da ɗaya daga cikin waɗanda suke tsaye a can, na tambaye shi gaskiya ma’anar waɗannan al’amura. “Don haka sai ya faɗa mini, ya kuma ba ni fassarar waɗannan al’amura. ‘Waɗannan manyan dabbobi huɗu, Masarautai ne huɗu waɗanda za su taso a duniya. Amma tsarkaka na Mafi Ɗaukaka za su karɓi wannan sarauta, za su kuwa mallake ta har abada, I, har abada abadin.’ “Sa’an nan kuma sai na so in san ma’anar wannan dabba ta huɗu, wadda ta yi dabam da sauran dabbobin da suke da matuƙar bantsoro, da take da haƙoran ƙarfe da kuma farcen tagulla, dabbar ta ragargaje ta cinye abin da ta kama, ta kuma tattaka duk abin da ya rage a ƙarƙashin ƙafafunta. Na kuma so in gane game da ƙahonin nan guda goma da suke a kanta da kuma game da ƙahon nan da ya fito, wanda aka tumɓuke ƙahoni uku a gabansa, ƙahon nan da yake da idanu da bakin da yake furta manyan maganganun fariya, wanda ya yi kamar ya fi sauran girma. Ina cikin dubawa, sai ga wannan ƙaho yana yaƙi da tsarkaka yana kuma cin nasara a kansu, sai da Wannan wanda yake tun fil azal ya zo ya furta hukunci, aka kuma ba tsarkaka na Mafi Ɗaukaka gaskiya, lokaci kuwa ya cika sai suka karɓi mulki. “Sai ya ba ni wannan bayani, ‘Dabbar nan ta huɗu, ita ce mulki na huɗu da zai bayyana a duniya. Zai bambanta da dukan sauran mulkoki, zai kuma cinye dukan duniya, yă tattake ta, yă kuma ragargaje ta. Ƙahonin nan goma, sarakuna ne goma waɗanda za su taso daga wannan mulki. Bayansu kuma, wani sarki zai taso, wanda ya sha dabam da waɗanda suka riga shi. Zai rinjayi sarakunan nan uku. Zai yi maganar saɓo a kan Mafi Ɗaukaka, zai kuma tsananta wa tsarkaka yă kuma yi ƙoƙarin sāke lokuta da shari’u. Za a miƙa tsarkaka a hannunsa na wani lokaci, lokuta da kuma rabin lokaci. “ ‘Amma majalisa za tă yi zama, za a karɓe ikonsa, a kuma hallaka shi gaba ɗaya har abada. Sa’an nan za a ba da mulki, iko da girma na mulkokin da suke a ƙarƙashin dukan sammai ga tsarkaka, mutane na Mafi Ɗaukaka. Mulkinsa kuwa mulki ne marar matuƙa, kuma dukan masu mulki za su yabe shi, su kuma yi masa biyayya.’ “Wannan shi ne ƙarshen batun. Ni, Daniyel na damu ƙwarai da irin tunanina, kuma fuskata ta rikice, amma na riƙe batun a zuciyata.” A shekara ta uku ta mulkin sarki Belshazar, ni, Daniyel, na ga wahayi, bayan wancan da na riga gani. A cikin wahayin, na ga kaina a mafakar Shusha a yankin Elam; a wahayin na ga ina a bakin Kogin Ulai. Na ɗaga ido, a gabana kuwa sai ga rago mai ƙahoni biyu, yana tsaye a gefen mashigin kogin, ƙahonin kuma suna da tsawo. Ɗaya daga cikin ƙahonin ya fi ɗayan tsawo. Wanda ya fi tsawon shi ne ya tsiro daga baya. Na lura da ragon sa’ad da ya kai karo wajen yamma da arewa da kudu. Babu wata dabbar da ta iya ƙarawa da shi, babu kuma wanda ya iya kuɓuta daga ikonsa. Ya yi yadda ya ga dama, ya kuma zama mai girma. Yayinda nake tunani game da wannan, farat ɗaya sai ga bunsurun da yake da sanannen ƙaho tsakanin idanunsa ya ɓullo daga wajen yamma, yana ratsa dukan duniya ba ya ko taɓa ƙasa. Ya zo wajen rago mai ƙahoni biyu ɗin nan da na riga na gani tsaye a gefen mashigin kogin nan ya tasar masa da fushi mai zafi. Na ga ya zo kusa da ragon, ya husata da shi ƙwarai, ya kai wa ragon hari. Ya kakkarya ƙahoninsa nan biyu. Ƙarfin ragon ya kāsa, bai iya kāre kansa daga bunsurun ba. Bunsurun ya buge shi ƙasa ya tattake shi. Ba wanda ya iya ceton ragon daga bunsurun. Bunsurun kuwa ya ƙasaita, amma a ƙwanƙolin ikonsa sai aka karye babban ƙahonsa, kuma a wurin da ƙahon nan ya kasance waɗansu sanannun ƙahoni huɗu suka tsiro suna fuskantar kusurwoyin nan huɗu. Daga cikin ɗayansu kuma wani ƙaramin ƙaho ya fito, ya yi girma ya ƙasaita ƙwarai zuwa kudu da kuma gabas da wajen Kyakkyawar Ƙasa. Ya yi girma sai da ya kai rundunar sammai, ya kuma fid da waɗansu rundunar taurari zuwa ƙasa ya kuma tattake su. Sai ya ɗora kansa ya zama mai girma kamar Sarkin runduna; sai aka ɗauke hadaya ta kullayaumi daga gare shi, aka kuma saukar da wurin masujadarsa ƙasa. Saboda tawaye, sai aka ba da rundunar tsarkaka da kuma hadayar ƙonawa ta kowace rana ga ƙahon. Sai ya yi watsi da gaskiya, ya yi abin da ya ga dama, ya kuwa yi nasara. Sa’an nan na ji mai tsarkin nan yana magana, wani mai tsarki kuma ya ce da wancan, “Har yaushe wannan wahayi zai tabbata, wahayi game da hadaya ta kullayaumi, da tawayen da yake kawo lalacewa, da kuma miƙa wuri mai tsarki da kuma na rundunar da za a tattake a ƙarƙashin sawu?” Sai ya ce mini, “Zai ɗauki safiya da yamma 2,300; sa’an nan za a sāke tsarkake wuri mai tsarki.” Yayinda ni, Daniyel, nake duban wahayi ina ƙoƙari in fahimce shi, sai ga wani a gabana wanda ya yi kama da mutum. Sai na ji muryar wani mutum daga Ulai tana cewa, “Jibra’ilu, faɗa wa wannan mutum ma’anar wahayin.” Da ya zo kusa da inda nake tsaye, na firgita na kuma fāɗi rubda ciki. Ya ce da ni “Ɗan mutum, ka gane da cewa wannan wahayi yana magana ne a kan kwanakin ƙarshe.” Yayinda yake magana da ni, barci mai nauyi ya kwashe ni, da nake kwance rubda ciki. Sai ya taɓa ni ya kuma tashe ni tsaye. Sai ya ce, “Zan faɗa maka abin da zai faru a lokacin fushi, saboda wahayin yana magana ne a kan lokacin da aka ƙayyade na ƙarshe. Rago mai ƙahoni biyu da ka gani, yana a madadin sarakunan Medes da Farisa ne. Bunsurun kuwa sarkin Girka ne, kuma babban ƙahon da yake tsakanin idanunsa, sarki na farko ne. Ƙahoni huɗu da suka maya wannan da ya karye yana a madadin masarautu huɗu da za su tashi daga cikin al’ummarsa amma ba za su sami irin ikonsa ba. “Can wajen ƙarshe mulkinsu, sa’ad da muguntarsu ta kai intaha, wani mugun sarki mai rashin hankali, uban makirci, zai fito. Zai yi ƙarfi ƙwarai da gaske, amma ba da ikonsa ba. Zai jawo mummunar hallakarwa kuma zai yi nasara a duk abin da ya sa gaba. Zai hallakar da majiya ƙarfi da kuma tsarkaka. Zai sa yaudara ta ƙara yin yawa, zai ɗaukaka kansa. Sa’ad da suke ji sun sami mafaka, zai hallaka mutane da yawa sa’an nan kuma yă fara gāba da Sarkin sarakuna. Duk da haka za a hallaka shi, amma ba da ikon mutum ba. “Wahayin nan na safiya da yamma da aka nuna maka gaskiya ne, amma ka ɓoye wahayin, gama ya shafi nan gaba mai tsawo ne.” Ni, Daniyel, na gaji matuƙa na kuma yi rashin lafiya na kwanaki masu yawa. Sa’an nan sai na tashi na ci gaba da hidimar sarki. Wahayin ya shige mini duhu, ya fi ƙarfin fahimtata. A shekara ta fari da mulkin Dariyus ɗan Zerzes (wanda yake Bamediye), wanda aka mai da shi sarki a masarautar Babiloniyawa a shekara ta farko ta mulkinsa, ni, Daniyel na gane daga cikin littattafai, bisa ga maganar Ubangiji da aka faɗa wa annabi Irmiya, cewa zaman Urushalima kango zai kai shekara saba’in. Sai na juya wurin Ubangiji Allah na roƙe shi ta wurin addu’a da koke-koke, cikin azumi, ina saye da tsummoki, na kuma zauna a cikin toka. Na yi addu’a ga Ubangiji Allahna na furta laifina. “Ya Ubangiji, mai alfarma da kuma Allah mai banrazana, wanda yake cika alkawarinsa na ƙauna ga duk wanda ya ƙaunace shi ya kuma kiyaye dokokinsa, mun yi zunubi muka kuma yi ba daidai ba. Mu mugaye ne da kuma ’yan tawaye; mun juya wa umarninka da shari’unka baya. Ba mu saurari bayinka annabawa ba, waɗanda suka yi magana a sunanka ga sarakunanmu da masu mulkinmu da iyayenmu, da kuma dukan mutanen ƙasa. “Ubangiji, kai mai adalci ne, amma a yau kunya ta rufe mu, mutanen Yahuda da mutanen Urushalima da na dukan Isra’ila, waɗanda suke kusa da kuma nesa, a dukan ƙasashen da ka warwatsa mu saboda rashin amincinmu a gare ka. Ya Ubangiji, mu da sarakunanmu, da masu mulkinmu da iyayenmu kunya ta rufe mu saboda mun yi maka zunubi. Ubangiji Allahnmu mai jinƙai ne, mai gafartawa ne kuma, ko da yake mun yi masa tawaye; ba mu yi biyayya ga Ubangiji Allahnmu ba, ba mu kuma kiyaye shari’unsa da ya ba mu ta wuri bayinsa annabawa ba. Dukan Isra’ila sun karya dokokinka suka kuma juya maka baya, sun ƙi yi maka biyayya. “Saboda haka la’anoni da rantsuwar hukunce-hukuncen da suke a rubuce a cikin Dokar Musa, bawan Allah, sun kama mu domin mun yi maka zunubi. Ka cika kalmomin da ka yi a kanmu da kuma a kan masu mulkinmu ta wurin kawo mana babban bala’i. A duniya duka ba a taɓa yin wani abu kamar yadda aka yi wa Urushalima ba. Kamar yadda yake a rubuce cikin Dokar Musa, dukan wannan bala’i ya sauko a kanmu, duk da haka ba mu nemi tagomashin Ubangiji Allahnmu ta wurin barin aikatawa zunubanmu, mu kuma mai da hankali a kan gaskiyarka ba. Ubangiji bai yi wata-wata wajen kawo mana bala’i ba, domin Ubangiji Allahnmu mai adalci ne a cikin dukan abin da yake yi; duk da haka ba mu yi masa biyayya ba. “Yanzu, ya Ubangiji Allahnmu, wanda ya fito da mutanensa daga Masar ta hannu mai ƙarfi wanda kuma ya yi wa kansa sunan da ya dawwama har yă zuwa yau, mun yi zunubi, mun yi abin da ba daidai ba. Ya Ubangiji, ta wurin kiyaye dukan ayyukanka na adalci, ka huce daga fushinka da hukuncinka da ka yi a kan Urushalima, birninka, tudunka mai tsarki. Zunubinmu da laifofin iyayenmu sun mai da Urushalima da kuma mutanenka abin ba’a ga dukan waɗanda suke kewaye da mu. “Yanzu, ya Allahnmu, ka ji addu’o’i da koke-koken bayinka. Saboda sunanka, ya Ubangiji, ka duba da rahama wurinka mai tsarki da ya zama kango. Ka kasa kunne, ya Allah, ka kuma ji; ka buɗe idanunka ka kuma ga yadda birninka ya zama kango, birnin da yake ɗauke da Sunanka. Ba cewa muna roƙonka saboda mu masu adalci ba ne, amma saboda girman jinƙanka. Ya Ubangiji, ka saurara! Ya Ubangiji ka gafarta! Ya Ubangiji, ka ji ka kuma yi wani abu! Saboda sunanka, ya Allahna, kada ka yi jinkiri, domin da sunanka ake kiran birninka da jama’arka.” Yayinda da nake magana da addu’a, ina furta zunubina da zunubin mutanena Isra’ila ina miƙa koke-kokena ga Ubangiji Allahna saboda tudunsa mai tsarki, yayinda nake cikin addu’a, sai Jibra’ilu, mutumin nan da na gani a wahayin da ya wuce, ya zo wurina gaggauce wajen lokacin yin hadaya ta yamma. Ya umarce ni ya kuma ce mini, “Daniyel, yanzu na zo domin in ba ka hikima da ganewa. Da zarar ka fara addu’a, an amsa, wadda na zo in faɗa maka, gama ana ƙaunar ka sosai. Saboda haka, ka yi lura da saƙon ka kuma fahimci wahayin. “An ƙayyade wa jama’arka da tsattsarkan birninka shekara ɗari huɗu da tasa’in domin a kawo ƙarshen laifi da zunubi, domin a yi kafarar laifi, sa’an nan a shigo da adalci madawwami, a rufe wahayi da annabci, a tsarkake haikali. “Sai ka sani ka kuma fahimci wannan; Tun daga sa’ad da aka kafa doka don a maido a kuma sāke gina Urushalima har sai Shafaffen nan, mai mulki, ya zo, za a yi shekara arba’in da tara, da shekara ɗari huɗu da talatin da huɗu. Za a sāke gina ta a yi mata tituna da mafaka. Bayan shekara ɗari huɗu da talatin da huɗu, za a datse Shafaffen nan zai kuma kasance ba shi da kome. Mutanen mai mulkin za su zo su hallaka birnin da kuma wuri mai tsarki. Ƙarshen zai zo kamar rigyawa. Yaƙi zai ci gaba har ƙarshe, a kuma hallakar kamar yadda aka ƙaddara. Zai tabbatar da alkawari da mutane masu yawa har na shekara bakwai. A tsakiyar bakwai ɗin nan ɗaya zai kawo ƙarshen duk wata hadaya da baiko. Kuma a kusurwar haikali zai sa abin ƙyama mai kawo hallaka, har sai ƙarshen da aka ƙaddara ya auko wa wanda ya sa abin ƙyama.” A shekara ta uku ta Sairus sarkin Farisa, sai aka ba wa Daniyel (wanda ake kira Belteshazar) wahayi. Saƙon kuwa gaskiya ce wadda take tattare da babban yaƙi. Fahimtar saƙon ya zo masa a cikin wahayi. A wannan lokaci ni Daniyel na yi makoki har na sati uku. Ban ci abinci mai kyau ba; ba nama ko ruwa inabin da ya shiga bakina; kuma ba na amfani da man shafawa gaba ɗaya har sai da sati nan uku suka wuce. A rana ta ashirin da huɗu ga watan farko, a sa’ad da nake tsaye a bakin babban kogi, Tigris, na ɗaga kaina na duba sai ga wani mutum tsaye sanye da rigar lilin, ya yi ɗamara da zinariya zalla daga Ufaz kewaye da ƙugunsa. Jikinsa kamar lu’ulu’u yake, fuskarsa kuma kamar walƙiya, idanunsa kamar harshen wuta, hannuwansa da ƙafafunsa kamar gogaggiyar tagulla, muryarsa kuma kamar amon babban taron jama’a. Ni, Daniyel, kaɗai ne na ga wahayin; mutanen da suke tare da ni ba su gani ba, amma wata irin babbar razana ta auko musu har suka gudu suka ɓuya. Sai aka bar ni ni kaɗai, ina juyayi wannan babban wahayi, ba ni da sauran ƙarfi, fuskata ta yamutse kuma ba ni da sauran ƙarfi. Sai na ji yana magana, da ina sauraronsa, sai na shiga barci mai nauyi, na kuwa fāɗi rubda ciki. Sai hannu ya taɓa ni ya sa makyarkyata a hannuna da ƙafafuna. Sai ya ce, “Daniyel, kai ne wanda ake ƙauna sosai, ka yi lura da kyau game da kalmomin da zan yi maka magana a kansu, ka tashi yanzu, gama an aiko ni a gare ka.” Sa’ad da ya faɗa mini haka, sai na tashi a tsaye ina rawan jiki. Sai ya ci gaba da cewa, “Kada ka ji tsoro, Daniyel. Gama tun daga ran da ka fara sa zuciya ga neman ganewa, ka kuma ƙasƙantar da kanka a gaban Allahnka, an ji addu’arka, amsar addu’arka ce ta kawo ni. Amma mai mulkin masarautar Farisa ya tsare ni har kwana ashirin da ɗaya. Sai da Mika’ilu, ɗaya daga cikin manya shugabanni, ya zo ya taimake ni, saboda an tsare ni a can tare da sarkin Farisa. Yanzu na zo domin in bayyana maka abin da zai faru da mutanenka nan gaba, gama wahayin ya shafi lokacin da bai riga ya zo ba ne.” Yayinda yake faɗin mini haka, sai na sunkuyar da kaina ƙasa shiru, ba magana. Sai wani wanda ya yi kama da mutum ya taɓa leɓunana, na kuma buɗe bakina sai na fara magana. Na ce wa wannan da yake tsaye a gabana, “Na cika da azaba saboda wannan wahayi, ranka yă daɗe, ina kuma neman taimako. Yaya ni bawanka zan iya magana da kai, ranka yă daɗe? Ƙarfina ya ƙare kuma ina numfashi da ƙyar.” Har yanzu wannan wanda yana kama da mutum ya taɓa ni ya kuma ba ni ƙarfi. Ya kuma ce, “Kada ka ji tsoro, ya kai mutumin da ake fahariya, salama a gare ka! Ka ƙarfafa yanzu; ka yi ƙarfin hali.” Sa’ad da ya yi magana da ni, sai na samu ƙarfi na ce, “Ka yi magana ranka yă daɗe, tun da yake ka sa na sami ƙarfi.” Sai ya ce mini, “Ka san abin da ya kawo ni gare ka? Ba da jimawa ba zan koma in yi yaƙi da mai mulkin Farisa, kuma idan na tafi, mai mulkin Hellenawa zai taso; amma da farko zan faɗa maka abin da aka rubuta a cikin Littafin Gaskiya (Babu wanda ya taimake ni yaƙi da waɗannan sai dai Mika’ilu, sarkinku. A shekara ta fari ta Dariyus mutumin Mede, na ɗauki matsayina domin in goyi baya in kuma kāre shi.) “Yanzu dai, zan faɗa maka gaskiya. Sarakuna uku za su taso a Farisa, sa’an nan kuma na huɗu, wanda zai fi dukansu dukiya. Sa’ad da zai sami iko saboda dukiyarsa, zai zuga dukan kowane mutum yă yi gāba da masarautar Girka. Sa’an nan wani babban sarki zai bayyana, wanda zai yi mulki da babban iko yă kuma yi abin da ya ga dama. Bayan da ya bayyana, daularsa za tă wargaje za a rarraba ta zuwa kusurwoyi huɗu na duniya, a ba waɗansu waɗanda ba zuriyarsa ba, ba kuwa za su yi mulki da iko kamar yadda ya yi ba, gama za a tumɓuki daularsa a kuma ba wa waɗansu. “Sai sarki Kudu zai yi ƙarfi ƙwarai, amma ɗaya daga cikin komandodinsa zai yi ƙarfi fiye da shi, zai kuma yi mulki masarautarsa da iko mai girma. Bayan ’yan shekaru, za su haɗa kai. Diyar sarkin Kudu za tă je wurin sarkin Arewa ta sada zumunci, amma ba za tă riƙe iko ba, shi kuwa da ikonsa ba za su daɗe ba. A waɗannan kwanaki za a bashe ta, da ita da masu rakiyarta da kuma mahaifinta da kuma wanda ya goyi bayanta. “Wani daga cikin zuriyarta zai taso yă ɗauki matsayinta. Zai kai wa sojojin sarkin Arewa hari yă kuma shiga kagararsa; zai yi yaƙi da su yă kuma yi nasara. Zai ƙwace allolinsu, siffofinsu na ƙarfe da kuma kaya masu daraja na azurfa da na zinariya a kuma kai su Masar. Zai yi ’yan shekaru bai kai wa sarkin Arewa yaƙi ba. Sa’an nan sarkin Arewa zai kai wa sarkin Kudu hari, amma zai janye, yă koma ƙasarsa. ’Ya’yansa maza za su yi shirin yaƙi za su kuma tattara babbar rundunar sojoji, waɗanda za su yi ta mamayewa kamar rigyawar da ba iya tarewa, kuma za su kai yaƙin har kagararsa. “Sa’an nan sai sarkin Kudu zai kama hanya da fushi zuwa yaƙi da sarkin Arewa, wanda zai tattara babbar rundunar yaƙi, amma za a ci shi da yaƙi. Sa’ad da zai kawar da rundunar, sarkin Kudu zai cika da girman kai zai kuma kashe mutane dubbai, duk da haka ba zai kasance mai nasara ba. Sarki Arewa kuma zai ƙara tara babbar rundunar soja, wadda ta fi ta dā girma; bayan waɗansu shekaru kuma, zai tafi yaƙi da babbar rundunar mayaƙa cike da kayan yaƙi. “A waɗannan lokutan mutane da yawa za su tashi gāba da sarkin Kudu. Amma waɗansu ’yan kama-karya za su taso daga jama’arka da niyya su cika abin da wahayin ya ce, amma za a fatattake su. Sa’an nan sarkin arewa zai zo ya gina mahaurai a jikin katagar birni don yă ci birnin da yaƙi. Sojojin nan na Kudu kuwa ba za su iya tsayawa ba, ko zaɓaɓɓun jarumawansu ma, gama za su rasa ƙarfin tsayawa. Wanda ya kai harin zai yi yadda ya ga dama, ba wanda zai iya ja da shi. Zai kafa kansa a Kyakkyawar Ƙasa zai kuma sami ikon da zai hallaka ta. Zai yunƙura yă zo da ƙarfin dukan masarautarsa zai kuma nemi haɗinkan sarkin Kudu. Zai kuma ba shi diyarsa yă aura don yă lalatar da mulkin, amma shirinsa ba zai yi nasara ba ko yă taimake shi ba. Sa’an nan zai mai da hankalinsa zuwa ƙasashe a bakin kogi, zai kuma kama da yawansu, amma wani komanda zai kawo ƙarshen faɗin ransa, zai kuma sa faɗin ransa yă koma masa. Bayan wannan, zai juya ga kagarar ƙasarsa, amma zai yi tuntuɓe yă fāɗi, ba kuwa za a ƙara ganinsa ba. “Magājinsa zai aiki mai karɓar haraji don darajar masarautarsa. Amma ba da daɗewa ba za a hallaka shi, duk da haka ba da fushi ko cikin yaƙi ba. “Magājin wannan sarki zai zama wani mutumin banza wanda ma bai fito daga gidan sarauta ba. Zai taso ba zato ba tsammani, yă ƙwace sarautar ta hanyar zamba. Sa’an nan zai shafe mayaƙa masu yawa a gabansa; zai hallaka har da waɗanda suke mulki na alkawari. Bayan ƙulla yarjejjeniya da shi, zai yi zamba cikin aminci, kuma zai sami damar hawan mulki da goyon baya mutane kaɗan. Sa’ad da yankuna mafi arziki suke ji kome lafiya yake, zai kai musu hari kuma Zai aikata abin da kakanninsa ba su taɓa yi ba. Zai rarraba abin da aka kwaso daga yaƙi, da ganima, da dukiya ga dukan mabiyansa. Zai kuma yi shiri yă kai wa mafaka hari, amma na ɗan lokaci ne kawai. “Tare da babbar rundunar mayaƙa zai yi ƙarfin hali yă far wa sarkin Kudu da yaƙi. Sarkin kudu zai haɗa babbar rundunar soja mai ƙarfi don yaƙin, amma ba zai iya karo da shi ba, domin za a shirya masa maƙarƙashiya. Waɗanda suke ci daga tanadin sarki za su yi ƙoƙari su hallaka shi; za a share mayaƙansa, kuma za a kashe mutane masu yawa a yaƙin. Sarakunan nan biyu sun sa mugunta a ransu. Za su zauna a tebur guda su yi ta shara wa juna ƙarya, amma a banza, gama lokacin da aka ƙayyade bai yi ba tukuna. “Sarkin Arewa zai koma ƙasarsa da dukiya mai girma, amma zuciyarsa za tă yi gāba da tsattsarkan alkawari. Zai ɗauki mataki a kan wannan abu sa’an nan yă koma ƙasarsa. “A ƙayyadadden lokaci zai sāke kai wa Kudu hari, amma a wannan karo abin da zai faru zai sha bamban daga abin da ya faru can baya. Jiragen ruwa yammancin bakin teku za su yi gāba da shi, zuciyarsa kuwa za tă yi sanyi. Sa’an nan zai juya ya huce haushinsa a kan tsattsarkan alkawari. Zai komo yă nuna jinƙai ga waɗanda suka juya wa tsattsarkan alkawari baya. “Mayaƙansa za su taso su ƙazantar da kagarar haikali za su kuma kawar da hadaya ta kullum. Sa’an nan za su kafa abin banƙyama da yake lalatarwa. Ta wurin daɗin baki zai gurɓata waɗannan da suka karya alkawari, amma mutanen da suka san Allahnsu za su yi tsayin daka su yi jayayya da shi. “Waɗanda suke da hikima za su wayar da kan mutane da yawa, duk da haka za a kashe su da takobi, waɗansu da wuta, a washe waɗansu a kai su bauta. Sa’ad da suka fāɗi, za su sami ɗan taimako, mutane da yawa za su haɗa kai da su, amma da munafunci. Waɗansu masu hikima za su yi tuntuɓe, don a tsabtacce su, a tsarkake su, su yi tsab, har matuƙar da aka ƙayyade ta yi. “Sarkin zai yi abin da ya ga dama. Zai ɗaukaka yă kuma girmama kansa gaba da kowane allah zai kuma faɗa munanan abubuwa a kan Allahn alloli. Zai yi nasara har sai lokacin hukunci ya cika, gama abin da aka ƙaddara zai cika. Ba zai kula da alloli iyayensa ba ko wanda mata suke sha’awa, balle ma yă ga darajar wani allah, amma zai ɗaukaka kansa gaba da su duka. A maimakonsu, zai ɗaukaka allahn kagarai; allahn da kakanninsa ba su ko sani ba, shi ne zai miƙa masa zinariya, da azurfa, da duwatsu masu daraja, da abubuwa masu tsada. Zai kai wa kagarai mafi ƙarfi hari da taimakon baƙon allah zai kuma girmama waɗanda suka yarda da shi zai ba su girma, ya kuma shugabantar da su a kan mutane da yawa, zai raba musu ƙasa ta zama ladansu. “A lokaci ƙarshe sarkin Kudu zai tasar masa da yaƙi, sarkin Arewa kuwa zai tunzura, yă tasar masa da kekunan yaƙi da mahayan dawakai, da jiragen ruwa da yawa. Zai ratsa ƙasashe, yă ci su da yaƙi, yă wuce. Zai kuma mamaye Kyakkyawa Ƙasa. Ƙasashe masu yawa za su fāɗi, amma Edom, Mowab da kuma shugabannin Ammon za su kuɓuta daga hannunsa. Zai fadada mulkinsa har zuwa ƙasashe masu yawa; Masar ma ba za tă tsira ba. Zai mallaki dukiyoyi na zinariya, da na azurfa, da dukan abubuwa masu tsada na Masar. Zai kuma ci Libiyawa da Kush da yaƙi. Amma labari daga gabas da arewa za su firgita shi, shi kuwa zai ci gaba da yin yaƙi da zafi, yă karkashe mutane da yawa, yă shafe su. Zai kafa tentin mulkinsa tsakanin tekunan da suke a kyakkyawan tsauni mai tsarki. Duk da haka zai zo ga ƙarshensa, kuma babu wanda zai taimake shi. “A wannan lokaci Mika’ilu, babban mai mulki wanda yake kāre mutanenka, zai tashi. Za a yi lokacin matsananciyar wahala wanda ba a taɓa yi tun farkon ƙasashe har zuwa yanzu. Amma a lokacin da mutanenka, kowane mutum wanda aka sami sunansa a rubuce a cikin littafin, za a cece shi. Ɗumbun mutanen da suka yi barci cikin turɓayar duniya za su farka, waɗansu zuwa ga rai madawwami, waɗansu zuwa ga madawwamiyar kunya da kuma madawwamin ƙasƙanci. Waɗanda suke da hikima za su haskaka kamar hasken samaniya, waɗanda kuma suka jagoranci waɗansu da yawa zuwa adalci, za su zama kamar taurari har abada abadin. Amma kai, Daniyel, ka rufe zancen nan ka kuma liƙe kalmomin littafin nan har sai ƙarshe. Mutane da yawa za su yi ta kai komo don neman sani.” Sa’an nan ni, Daniyel, na duba, a gabana kuwa ga waɗansu mutum biyu tsaye, ɗaya a wannan hayen kogi ɗaya kuma a ƙetaren kogin. Ɗayansu ya ce wa mutumin da yake sanye da tufafin lilin, wanda yake a saman ruwan kogin, “Har yaushe waɗannan abubuwan banmamakin za su cika?” Mutumin da yake sanye da tufafin lilin, wanda yake a saman ruwan kogin, ya ɗaga hannun damansa da kuma na hagunsa sama, sai na ji yana rantsuwa da wannan da yake raye har abada, yana cewa, “Zai kasance na ɗan lokaci, lokuta da rabin lokaci. Za a kammala waɗannan abubuwa, sa’ad da aka gama ragargaje ikon tsarkakan mutane.” Na kuma ji, amma ban fahimta ba. Don haka sai na yi tambaya, “Ranka yă daɗe, mene ne ƙarshen waɗannan abubuwa?” Sai ya amsa ya ce, “Ka kama hanyarka, Daniyel, domin a rufe kalmomin aka kuma liƙe su har sai ƙarshen lokaci. Za a tsarkake mutane da yawa, za a maishe su marasa aibi a kuma tace su; amma mugaye za su ci gaba da mugunta. Babu wani mugun da zai fahimta, amma waɗanda za su zama masu hikima za su fahimta. “Daga lokacin da za a hana miƙa hadayar ƙonawa ta yau da kullum, a kuma kafa abin banƙyama, wanda yake lalatarwa, za a yi kwana 1,290. Mai albarka ne wanda ya jira har yă zuwa ƙarshen kwanakin nan 1,335. “Gare ka dai, ka yi tafiyarka har zuwa ƙarshe. Za ka huta, sa’an nan a ƙarshen kwanaki za ka tashi don karɓi sashen gadon da aka ba ka.” Maganar Ubangiji da ta zo wa Hosiya ɗan Beyeri a zamanin mulkin Uzziya, Yotam, Ahaz da Hezekiya, sarakunan Yahuda, da zamanin mulkin Yerobowam ɗan Yowash sarkin Isra’ila. Sa’ad da Ubangiji ya fara magana ta wurin Hosiya, Ubangiji ya ce masa, “Ka tafi, ka auro wa kanka mazinaciya da ’ya’yan da aka haifa ta hanyar rashin aminci, domin ƙasar tana da laifin mummunan zina ta wurin rabuwa da Ubangiji.” Saboda haka sai ya auri Gomer ’yar Dibilayim, ta kuwa yi ciki ta haifi ɗa namiji. Sai Ubangiji ya ce wa Hosiya, “Ka ba shi suna Yezireyel, domin ba da daɗewa ba zan hukunta gidan Yehu saboda kisan da aka yi a Yezireyel, zan kuma kawo ƙarshen mulkin Isra’ila. A wannan rana zan karye ƙarfin Isra’ila a Kwarin Yezireyel.” Gomer ta sāke ɗauki ciki ta kuma haifi ’ya mace. Sai Ubangiji ya ce wa Hosiya, “Ka ba ta suna, Lo-Ruhama, gama ba zan ƙara nuna wa gidan Isra’ila ƙauna ba, har da zan gafarta musu. Duk da haka zan nuna ƙauna ga gidan Yahuda; zan kuma cece su, ba da baka, takobi ko yaƙi ba, ko ta wurin dawakai, ko masu hawan dawakai ba, sai ko ta wurin Ubangiji Allahnsu.” Bayan ta yaye Lo-Ruhama, sai Gomer ta sāke haifi wani ɗa namiji. Sai Ubangiji ya ce, “Ka ba shi suna Lo-Ammi, gama ku ba mutanena ba ne, ni kuma ba Allahnku ba ne. “Duk da haka Isra’ilawa za su zama kamar yashi a bakin teku, da ba za a iya aunawa ko a ƙirga ba. A inda aka ce musu, ‘Ku ba mutanena ba ne,’ za a kira su ‘’ya’yan Allah mai rai.’ Mutanen Yahuda da mutanen Isra’ila za su sāke haɗu su zama ɗaya, za su kuma naɗa shugaba guda su kuma fita daga ƙasar, gama ranar za tă zama mai girma wa Yezireyel. “Ka ce da ’yan’uwanka maza, ‘Mutanena,’ ka kuma ce da ’yan’uwanka mata, ‘Ƙaunatacciyata.’ “Ka tsawata wa mahaifiyarka, ka tsawata mata, gama ita ba matata ba ce, ni kuma ba mijinta ba ne. Ku roƙe ta tă daina karuwancinta da kuma rashin aminci a tsakanin nononta. In ba haka ba zai tuɓe ta tsirara in bar ta kamar yadda take a ranar da aka haife ta; zan sa ta zama kamar hamada, in mayar da ita busasshiyar ƙasar, in kashe ta da ƙishirwa. Ba zan nuna wa ’ya’yanta ƙaunata ba, domin su ’ya’yan zina ne. Mahaifiyarsu ta yi rashin aminci ta kuma ɗauki cikinsu ta wurin yi abin kunya. Ta ce, ‘Zan bi kwartayena, waɗanda suke ba ni abinci da ruwa, ulu nawa da lilina, mai nawa da kuma abin sha na.’ Saboda haka zai tare hanyarta da ƙaya; zan yi mata katanga don kada tă sami hanya. Za tă bi kwartayenta amma ba za tă kama su ba; za tă neme su amma ba za tă same su ba. Sa’an nan za tă ce, ‘Zan koma ga mijina na fari, gama dā ya fi mini yadda nake a yanzu.’ Ba ta yarda cewa ni ne wanda ya ba ta hatsi, sabon ruwan inabi da mai ba, wanda ya jibge mata azurfa da zinariya, waɗanda suka yi amfani wa Ba’al ba. “Saboda haka zan ƙwace hatsina sa’ad da ya nuna, da sabon ruwan inabina sa’ad da ya ƙosa. Zan karɓe ulu nawa da lilina, da take niyya ta rufe tsiraicinta. Saboda haka yanzu zan buɗe tsiraicinta a idanun kwartayenta; ba wani da zai ƙwace ta daga hannuwana. Zan tsayar da dukan bukukkuwarta, bukukkuwarta na shekara-shekara, da kuma kiyaye bikin Sababbin Wata nata, kwanakin Asabbacinta, dukan ƙayyadaddun bukukkuwarta. Zan lalatar da inabinta da kuma itatuwan ɓaurenta, waɗanda take cewa su ne abin da kwartayenta suka biya; zan mayar da su kurmi, namun jeji kuwa za su ci su. Zan hukunta ta saboda kwanakin da ta ƙone turare wa Ba’al; ta yi wa kanta ado da zobai da duwatsu masu daraja, ta bi kwartayenta, amma ta manta da ni,” in ji Ubangiji. “Saboda haka yanzu zan rarrashe ta; zan bishe ta zuwa hamada in kuma yi mata magana a hankali. A can zan mayar mata da gonakin inabinta, zan kuma sa Kwarin Akor yă zama ƙofar bege. A can za tă rera kamar a kwanakin ƙuruciyarta, kamar a lokacin da ta fita daga Masar. “A waccan rana,” in ji Ubangiji, “za ki ce da ni ‘mijina’; ba za ki ƙara ce ni ‘maigidana’ ba. Zan cire sunayen Ba’al daga leɓunanta; ba za a ƙara kira sunayensu ba. A waccan rana zan yi alkawari dominsu da namun jeji da kuma tsuntsayen sararin sama da dukan halittu masu rarrafe a ƙasa. Baka da takobi da yaƙi zan sa su ƙare a ƙasar, domin duk su zauna lafiya. Zan ɗaura aure da ke har abada; zan ɗaura aure da yake cikin adalci da gaskiya, cikin ƙauna da jinƙai. Zan ɗaura aure da yake cikin aminci za ki kuwa yarda cewa ni ne Ubangiji. “A waccan rana zan amsa,” in ji Ubangiji, “zan amsa wa sararin sama, za su kuwa amsa wa ƙasa; ƙasa kuma za tă amsa wa hatsi, sabon ruwan inabi da kuma mai, su kuma za su amsa wa Yezireyel. Zan dasa ta wa kaina a ƙasar; zan shuka ƙaunata ga wanda na ce ‘Ba ƙaunatacciyata ba.’ Zan faɗa wa waɗanda a ce ‘Ba mutanena ba, ’ ‘Ku mutanena ne’; za su kuwa ce, ‘Kai ne Allahna.’ ” Ubangiji ya ce mini, “Ka tafi, ka sāke nuna wa matarka ƙauna, ko da yake wani yana son ta, ita kuma mazinaciya ce. Ka ƙaunace ta yadda Ubangiji yake ƙaunar Isra’ilawa, ko da yake sun juya ga waɗansu alloli suna kuma ƙauna wainar zabibi mai tsarki.” Ta haka na saye ta da shekel goma sha biyar na azurfa da kuma wajen buhu na sha’ir. Sai na faɗa mata, “Za ki zauna tare da ni kwanaki masu yawa; kada ki yi karuwanci ko ki yi abuta da wani namiji, ni kuwa zan zauna tare da ke.” Gama Isra’ilawa za su yi kwanaki masu yawa ba tare da sarki ko shugaba ba, babu hadaya ko keɓaɓɓun duwatsu, babu efod ko gunki. Daga baya Isra’ilawa za su dawo su nemi Ubangiji Allahnsu da kuma Dawuda sarkinsu. Za su je da rawan jiki wajen Ubangiji da kuma ga albarkunsa a kwanakin ƙarshe. Ku ji maganar Ubangiji, ku Isra’ilawa, gama Ubangiji yana da tuhumar da zai kawo a kan ku waɗanda suke zama a ƙasar. “Babu aminci, babu ƙauna, babu yarda da Allah a cikin ƙasar. Akwai la’ana ce kawai, yin ƙarya da kisa, yin sata da zina; sun wuce gona da iri, kisankai a kan kisankai. Saboda wannan ƙasar tana makoki, kuma dukan waɗanda suke zama a cikinta sun lalace; namun jeji da tsuntsayen sararin sama da kuma kifin teku suna mutuwa. “Amma kada wani mutum yă kawo tuhuma, kada wani mutum yă zargi wani, gama mutanenka suna kama da waɗanda suke kawo tuhume-tuhume a kan firist ne. Kuna tuntuɓe dare da rana, annabawa ma suna tuntuɓe tare da ku. Saboda haka zan hallaka mahaifiyarku, mutanena suna hallaka saboda jahilci. “Domin kun ƙi neman sani, ni ma na ƙi ku a matsayin firistocina; domin kun ƙyale dokar Allahnku, ni ma zan ƙyale ’ya’yanku. Yawan ƙaruwar firistoci, haka suke yawan zunubi a kaina; sun yi musaya Ɗaukakarsu da wani abin kunya. Suna ciyar da kansu a kan zunuban mutanena suna kuma haɗamar muguntarsu. Zai kuwa zama, kamar yadda mutane suke, haka firistoci suke. Zan hukunta dukansu saboda al’amuransu in kuma sāka musu saboda ayyukansu. “Za su ci amma ba za su ƙoshi ba; za su shiga karuwanci amma ba za su ƙaru ba, gama sun rabu da Ubangiji don su ba da kansu ga karuwanci, ga tsoho da kuma sabon ruwan inabi, waɗanda suka ɗauke ganewar mutanena. Sun nemi shawarar gunkin da aka yi da itace suka kuwa sami amsa daga sanda. Halin karuwanci yakan ɓad da su; sun yi rashin aminci ga Allahnsu. Suna miƙa hadaya a kan ƙwanƙolin duwatsu suna kuma ƙone hadayu a kan tuddai, a ƙarƙashin itatuwa oak, aduruku da katambiri, inda inuwa take da daɗi. Saboda haka ’ya’yanku mata suka juya wa karuwanci surukanku mata kuma suka shiga yin zina. “Ba zan hukunta ’ya’yanku mata sa’ad da suka juya ga yin karuwanci ba, balle surukanku mata, sa’ad da suka yi zina, gama mazan da kansu suna ma’amala da karuwai suna kuma miƙa hadaya tare da karuwai na masujada, mutane marasa ganewa za su lalace! “Ko da yake kun yi zina, ya Isra’ila, kada Yahuda ya yi laifi. “Kada ku tafi Gilgal; kada ku haura zuwa Bet-Awen. Kuma kada ku rantse cewa, ‘Muddin Ubangiji yana a raye!’ Isra’ilawa masu taurinkai ne, kamar karsana mai taurinkai. Yaya Ubangiji zai iya kiwonsu kamar tumaki a makiyaya mai ɗanyar ciyawa? Efraim ya haɗa kai da gumaka; ku ƙyale shi kurum! Ko ma sa’ad da abin shansu ya ƙare, sai suka ci gaba da karuwancinsu; masu mulkinsu suna ƙaunar abin kunya. Guguwa za tă share su, hadayunsu kuma za su jawo musu abin kunya. “Ku ji wannan, ku firistoci! Ku kasa kunne, ku Isra’ilawa! Ku saurara, ya ku gidan sarauta! Wannan hukunci yana a kanku, kun zama tarko a Mizfa, ragar da aka shimfiɗa a kan Tabor. ’Yan tawaye sun yi zurfi cikin kisan gilla. Zan hore su duka. Na san Efraim ƙaf; Isra’ila ba a ɓoye take a gare ni ba. Efraim, yanzu ka juya ka shiga karuwanci; Isra’ila ta lalace. “Ayyukansu ba su ba su dama su koma ga Allahnsu ba. Halin karuwanci yana cikin zuciyarsu; ba su yarda da Ubangiji ba. Girmankan Isra’ila yana ba da shaida a kansu; Isra’ilawa, har ma Efraim, sun yi tuntuɓe a cikin zunubinsu; Yahuda ma ya yi tuntuɓe tare da su. Sa’ad da suka tafi tare da garkunan shanu, tumaki da awakinsu don su nemi Ubangiji, ba za su same shi ba; ya janye kansa daga gare su. Su marasa aminci ne ga Ubangiji; suna haihuwar shegu. Yanzu bukukkuwar Sabon Watansu za su cinye su da gonakinsu. “Amon kakaki a Gibeya, ƙaho a Rama. Ku yi kirarin yaƙi a Bet-Awen; ku ja gaba, ya Benyamin. Efraim za tă zama kango a ranar hukunci. A cikin kabilan Isra’ila na yi shelar abin da yake tabbatacce. Shugabannin Yahuda suna kamar waɗanda suke matsar da duwatsun shaidar da aka sa a kan iyaka ne. Zan zubo musu da fushina a kansu kamar rigyawar ruwa. An danne Efraim, an murƙushe ta a shari’a ta ƙudura ga bin gumaka. Na zama kamar asu ga Efraim, kamar ruɓa ga mutanen Yahuda. “Sa’ad da Efraim ya ga ciwonsa, Yahuda kuwa miyakunta, sai Efraim ya juya ga Assuriya, ya aika wurin babban sarki don neman taimako. Amma bai iya warkar da kai ba, bai iya warkar da miyakunka ba. Gama zan zama kamar zaki ga Efraim, kamar babban zaki ga Yahuda. Zan yage su kucu-kucu in tafi; zan kwashe su, ba wanda zai kuɓutar da su. Sa’an nan zan koma wurina sai sun yarda da laifinsu. Za su kuma nemi fuskata; cikin azabansu za su nace da nemana.” “Ku zo, mu koma ga Ubangiji. Ya yayyage mu kucu-kucu amma zai warkar da mu; ya ji mana ciwo amma zai daure mana miyakunmu. Bayan kwana biyu zai rayar da mu, a rana ta uku zai tashe mu, don mu rayu a gabansa. Bari mu yarda da Ubangiji; bari mu nace gaba don mu yarda da shi. Muddin rana tana fitowa, zai bayyana; zai zo mana kamar ruwan bazara, kamar ruwan saman farko da yake jiƙe ƙasa.” “Me zan yi da kai Efraim? Me zan yi da kai Yahuda? Ƙaunarku tana kamar hazon safiya, kamar raɓar safiya da takan ɓace. Saboda haka na yayyaga ku kucu-kucu tare da annabawana, na kashe ku da kalmomin bakina; hukuntaina sun haskaka kamar walƙiya a kanku. Gama jinƙai nake bukata, ba hadaya ba, ku kuma san Allah a maimakon hadayun ƙonawa. Kamar Adamu, sun tā da alkawari, sun yi mini rashin aminci a can. Gileyad birni ce ta mugayen mutane, da tabon alamun jini. Kamar yadda mafasa sukan yi fakon mutum, haka ƙungiyoyin firistoci suke; suna kisa a hanya zuwa Shekem, suna aikata laifofi bankunya. Na ga wani abu mai bantsoro a gidan Isra’ila. A can Efraim ya miƙa wuya ga karuwanci Isra’ila kuma ta ƙazantu. “Ku kuma, ya mutanen Yahuda, na shirya muku ranar girbi. “A duk sa’ad da zan mayar da dukiya wa mutanena, a duka sa’ad da zan warkar da Isra’ila, zunuban Efraim za su tonu za a kuma bayyana laifofin Samariya. Suna ruɗu, ɓarayi sukan fasa su shiga gidaje, ’yan fashi sukan yi fashi a tituna; amma ba su gane cewa na tuna da dukan ayyukan muguntarsu ba. Zunubansu sun kewaye su; kullum suna a gabana. “Suna faranta wa sarki zuciya da muguntarsu, shugabanni kuma da ƙarairayinsu. Dukansu mazinata ne suna ƙuna kamar matoya wadda mai gashin burodi ba ya bukata yă tura mata wuta daga cuɗe kullu har kumburinsa. A ranar bikin sarkinmu shugabanni sukan bugu da ruwan inabi, yă yi cuɗanya da masu ba’a. Zukatansu suna kamar matoya; sukan kusace shi da wayo. Muguwar aniyarsu takan yi ta ci dukan dare; da safe sai ta ƙuna kamar harshen wuta. Dukansu suna da zafi kamar matoya; suna kashe masu mulkinsu. Dukan sarakunansu sukan fāɗi, kuma babu waninsu da yake kira gare ni. “Efraim yana cuɗanya da al’ummai; Efraim waina ne mai fāɗi da ba a juye ba. Baƙi sun tsotse ƙarfinsa, amma bai gane ba. Gashi kansa ya cika da furfura, amma bai lura ba. Girmankan Isra’ila ya ba da shaida a kansa, amma duk da haka bai dawo ga Ubangiji Allahnsa ko yă neme shi ba. “Efraim yana kama da kurciya, marar wayo, marar hankali, yanzu yana kira ga Masar, yanzu yana juyewa ga Assuriya. Sa’ad da suka tafi, zan jefa ragata a kansu; zai janye su ƙasa kamar tsuntsayen sararin sama. Sa’ad da na ji suna tafiya tare, zan kama su. Kaitonsu, domin sun kauce daga gare ni! Hallaka za tă aukar musu, domin sun tayar mini! Na ƙudura in cece su amma suna faɗar ƙarya a kaina. Ba sa yin mini kuka da zuciyarsu amma suna ihu a kan gadajensu. Sukan taru wurin ɗaya don hatsi da ruwan inabi amma su juya mini baya. Na horar da su na kuma ƙarfafa su, amma sun ƙulla mini maƙarƙashiya. Ba sa juya ga Mafi Ɗaukaka; suna kama da tanƙwararren baka. Za a kashe shugabanninsu da takobi saboda banzan maganganunsu. Saboda wannan za a wulaƙanta su a ƙasar Masar. “Ka sa kakaki a leɓunanka! Gaggafa tana a bisan gidan Ubangiji domin mutane sun tā da alkawarina suka kuma tayar wa dokata. Isra’ila ta yi mini kuka, ‘Ya Allahnmu, mun yarda da kai!’ Amma Isra’ila sun ƙi abin da yake mai kyau; abokin gāba zai fafare su. Suna naɗa sarakuna, ba da izinina ba; sun zaɓa shugabanni ba da yardanta ba. Da azurfa da zinariya sun ƙera gumaka wa kansu wanda zai kai zuwa ga hallakarsu. Ku zubar da gunkin maraƙinku, ya Samariya! Fushina yana ƙuna a kansu. Sai yaushe za su rabu da gumaka? Su daga Isra’ila ne! Wannan maraƙi, mai aikin hannu ne ya yi shi; gunki ne ba Allah ba. Za a farfashe shi kucu-kucu, waccan maraƙin Samariya. “Gama sun shuka iska don haka za su girbe guguwa. Hatsin da yake tsaye ba shi da kai, ba zai yi tsaba ba. Ko da ya yi tsaba ma, baƙi ne za su ci. An haɗiye Isra’ila; yanzu tana cikin al’ummai kamar abin da ba shi da amfani. Gama sun haura zuwa Assuriya kamar jakin jejin da yake yawo shi kaɗai. Efraim ya sayar da kansa ga maza. Ko da yake sun sayar da kansu a cikin al’ummai, yanzu zan tattara su wuri ɗaya. Za su fara lalacewa a ƙarƙashi danniyar babban sarki. “Ko da yake Efraim ya gina bagadai masu yawa don hadayun zunubi, waɗannan sun zama bagade don yin zunubi. Na rubuta musu abubuwa masu yawa na dokata, amma suka ɗauke su tamƙar wani baƙon abu ne. Suna miƙa hadayun da aka ba ni su kuma ci nama, amma Ubangiji ba ya jin daɗinsu. Yanzu zai tuna da muguntarsu yă kuma hukunta zunubansu. Za su koma Masar. Isra’ila ya manta da Mahaliccinsa ya kuma gina fadodi; Yahuda ya gina katanga a yawancin garuruwansa. Amma zan aiko da wuta a bisa biranensu da zai cinye kagaransu.” Kada ku yi farin ciki, ya Isra’ila; kada ku yi murna kamar waɗansu al’ummai. Gama kun yi rashin aminci ga Allahnku; kuna son hakkokin karuwa a kowace masussuka. Masussukai da wuraren matsin inabi ba za su ciyar da mutane ba; sabon ruwan inabi zai kāsa musu. Ba za su ci gaba da zama a ƙasar Ubangiji ba; Efraim zai koma Masar yă kuma ci abinci marar tsarki a Assuriya. Ba za su zuba hadayun ruwan inabi ga Ubangiji ba, ba kuwa hadayunsu za su gamshe shi ba. Irin hadayun nan za su zama musu kamar burodin masu makoki; duk wanda ya ci su zai ƙazantu. Wannan abincin zai zama na kansu ne; ba zai zo cikin haikalin Ubangiji ba. Me za ku yi a ƙayyadaddiyar ranar bukukkuwarku, a ranakun bikin Ubangiji? Ko da sun kuɓuta daga hallaka, Masar za tă tattara su, Memfis kuma za tă binne su. Sarƙaƙƙiya za tă mamaye kayan azurfansu, ƙayayyuwa su tsiro a cikin tentunansu. Kwanakin hukunci suna zuwa, kwanakin ba da lissafi suna a kusa. Bari Isra’ila su san da wannan. Saboda zunubanku sun yi yawa ƙiyayyarku kuma ta yi yawa, har ake ɗauka annabi wawa ne, mutumin da aka iza kuwa mahaukaci. Annabi, tare da Allahna, su ne masu tsaro a bisa Efraim, duk da haka tarko na jiransa a dukan hanyoyi, da kuma ƙiyayya a cikin gidan Allahnsa. Sun nutse da zurfi cikin lalaci, kamar a kwanakin Gibeya. Allah zai tuna da muguntarsu yă kuma hukunta su saboda zunubansu. “Sa’ad da na sami Isra’ila, ya zama kamar samun inabi a hamada; sa’ad da na ga kakanninku, ya zama kamar ganin ’ya’yan itace na farko a itacen ɓaure. Amma sa’ad da suka zo Ba’al-Feyor, suka keɓe kansu wa gumaka bankunya sai suka zama abubuwan banƙyama kamar abubuwan da suke ƙauna. Darajar Efraim za tă yi firiya tă tafi kamar tsuntsu, ba haihuwa, ba juna biyu, ba ɗaukar ciki. Ko da sun yi renon ’ya’ya, zan sa su yi baƙin cikin kowannensu. Kaitonsu sa’ad da na juya musu baya! Na ga Efraim, kamar birnin Taya, da aka kafa a wuri mai daɗi. Amma Efraim zai fitar da ’ya’yansu ga masu yanka.” Ka ba su, ya Ubangiji Me za ka ba su? Ka ba su mahaifar da za su yi ɓarin ciki da busassun nono. “Saboda dukan muguntarsu a Gilgal, na ƙi su a can. Saboda ayyukansu na zunubi, zan kore su daga gidana. Ba zan ƙara ƙaunace su ba; dukan shugabanninsu ’yan tawaye ne. An ka da Efraim, saiwarsu ta bushe, ba sa ba da amfani. Ko da sun haifi ’ya’ya zan kashe waɗanda suka fi ƙauna.” Allahna zai ƙi su saboda ba su yi masa biyayya ba; za su zama masu yawo a cikin al’ummai. Isra’ila kuringa ce mai yaɗuwa; ya fitar da ’ya’ya wa kansa. Yayinda ’ya’yan suka ƙaru, ya gina ƙarin bagadai; da ƙasarsa ta wadata, ya yi wa keɓaɓɓun duwatsu ado. Zuciyarsu masu ruɗu ne, yanzu kuwa dole su ɗauki laifinsu. Ubangiji zai rushe bagadansu yă kuma hallaka keɓaɓɓun duwatsunsu. Sa’an nan za su ce, “Ba mu da sarki domin ba mu girmama Ubangiji ba. Amma ko da ma muna da sarki, me zai yi mana?” Sun yi alkawura masu yawa, suka yi rantsuwar ƙarya da kuma yarjejjeniyoyi; saboda haka ƙararraki suka taso kamar ciyayi masu dafi da aka nome a gona. Mutanen da suke zama a Samariya suna tsoro saboda gunki maraƙin Bet-Awen. Mutanensa za su yi makokinsa, haka ma firistocinsa matsafa, waɗanda suka yi farin ciki a kan darajarsa, don an ɗauke ta daga gare su aka kai ta zaman bauta. Za a ɗauke shi a kai Assuriya kamar gandu wa babban sarki. Efraim zai sha kunya; Isra’ila zai sha kunya saboda gumakan itacensa. Samariya da sarkinta za su ɓace kamar kumfa a bisa ruwaye. Za a hallaka masujadai kan tudu na mugunta zunubin Isra’ila ne. Ƙayayuwa da sarƙaƙƙiya za su yi girma su rufe bagadansu. Sa’an nan za su ce wa duwatsu, “Ku rufe mu!” Ga tuddai kuma, “Ku fāɗo a kanmu!” “Tun daga kwanakin Gibeya, kun yi zunubi, ya Isra’ila, a can kuwa kuka ci gaba. Yaƙi bai cimma masu aikata mugunta a Gibeya ba? Sa’ad da na ga dama, zan hukunta su; al’ummai za su taru su yi gāba da su don su daure su saboda zunubansu da suka riɓanya. Efraim horarriyar karsana ce mai son sussuka; saboda haka zan sa karkiya a kyakkyawan wuyanta. Zan bi da Efraim, Dole Yahuda yă yi noma, dole kuma Yaƙub yă ja garman noma. Ku shuka wa kanku adalci, ku girbe ’ya’yan jinƙai marar ƙarewa, ku kuma nome ƙasar da ba a nome ba; gama lokaci ne na neman Ubangiji, sai ya zo ya zubo adalci a kanku. Amma kun shuka mugunta, kuka girbe mugu kuka ci ’ya’yan ruɗu. Domin kun dogara da ƙarfinku da kuma a jarumawanku masu yawa, hayaniyar yaƙi za tă tashi gāba da mutanenku, saboda a ragargaza kagaranku, kamar yadda Shalman ya ragargaza Bet-Arbel a ranar yaƙi, sa’ad da aka fyaɗa uwaye tare da ’ya’yansu da ƙasa. Haka zai faru da kai, ya Betel, domin muguntarka ta yi yawa. Sa’ad da wannan rana ta zo, za a hallaka sarkin Isra’ila ƙaƙaf. “Sa’ad da Isra’ila yake yaro, na ƙaunace shi, daga Masar kuma na kira ɗana. Amma yawan kiran da na yi wa Isra’ila haka nesa da ni da suke ta yi. Suka miƙa hadaya ga Ba’al suka kuma ƙona turare ga siffofi. Ni ne na koya wa Efraim tafiya ina kama su da hannu; amma ba su gane cewa ni ne na warkar da su ba. Na bishe su da linzamin alheri da tausayi, da ragamar ƙauna; Na cire karkiya daga wuyansu na kuma rusuna na ciyar da su. “Ba za su koma Masar ba Assuriya kuma ba za tă yi mulki a bisansu ba saboda sun ƙi su tuba ba? Takuba za su yi ta wulgawa a biranensu, za su hallaka sandunan ƙarafan ƙofofinsu su kuma kawo ƙarshen ƙulle-ƙullensu. Mutanena sun ƙudura su juye daga gare ni. Ko da ma suka yi kira ga Mafi Ɗaukaka, ta ko ƙaƙa ba zai girmama su ba. “Yaya zan ba da kai, Efraim? Yaya zan miƙa ka, Isra’ila? Yaya zan yi da kai kamar Adma? Yaya zan yi da kai kamar Zeboyim? Zuciyata ta canja a cikina; dukan tausayina ya huru. Ba zan zartar da fushina mai zafi ba, ba kuwa zan juya in ragargaza Efraim ba. Gama ni Allah ne, ba mutum ba, Mai Tsarki a cikinku. Ba zan zo cikin fushi ba. Za su bi Ubangiji; zai yi ruri kamar zaki. Sa’ad da ya yi ruri, ’ya’yansa za su zo da rawan jiki daga yamma. Za su zo da rawan jiki kamar tsuntsaye daga Masar, kamar kurciyoyi daga Assuriya. Zan zaunar da su a cikin gidajensu,” in ji Ubangiji. Mutanen Efraim sun kewaye ni da ƙarairayi, gidan Isra’ila da ruɗu. Mutanen Yahuda kuma suna yi wa Allah ƙin ji, har ma a kan Mai Tsarkin nan mai aminci. Efraim yana kiwo a kan iska; yana fafarar iskar gabas dukan yini yana riɓaɓɓanya ƙarairayi da rikici. Ya yi yarjejjeniya da Assuriya ya kuma aika wa Masar man zaitun. Ubangiji yana da ƙarar da zai kawo a kan Yahuda; zai hukunta Yaƙub bisa ga hanyoyinsa zai sāka masa bisa ga ayyukansa. A cikin mahaifa ya cafke ɗiɗɗigen ɗan’uwansa; a matsayin mutum ya yi kokawa da Allah. Ya yi kokawa da mala’ika ya kuma rinjaye shi; ya yi kuka ya kuma yi roƙo don tagomashi. Ya same shi a Betel ya kuma yi magana da shi a can, Ubangiji Allah Maɗaukaki, Ubangiji ne sunansa sananne! Amma dole ku koma ga Allahnku; ku ci gaba da ƙauna da yin gaskiya, ku kuma saurari Allahnku kullum. Ɗan kasuwa yana amfani da mudu marar gaskiya; yana jin daɗin cuta. Efraim yana fariya yana cewa, “Ni mai arziki ne ƙwarai; na azurta. Da dukan wadatata ba za a sami wani laifi ko zunubi a gare ni ba.” “Ni ne Ubangiji Allahnku, wanda ya fitar da ku daga Masar; zan sa ku sāke zauna a tentuna, kamar a kwanakin ƙayyadaddun bukukkuwanku. Na yi magana da annabawa, na ba su wahayi da yawa na kuma ba da misalai ta wurinsu.” Gileyad mugu ne? Mutanensa mutanen banza ne! Suna miƙa bijimai a Gilgal? Bagadansu za su zama tsibin duwatsu. A gonar da aka nome. Yaƙub ya gudu zuwa ƙasar Aram; Isra’ila ya yi bauta don yă sami mata, domin kuma yă biya, sai da ya yi kiwon tumaki. Ubangiji ya yi amfani da annabi don yă fitar da Isra’ila daga Masar ta wurin annabi ya lura da shi. Amma Efraim ya yi muguwar tsokana da ta sa ya yi fushi; shugabansa zai ɗora musu hakkin jini a kansa kuma zai sāka masa saboda wulaƙancinsa. Sa’ad da Efraim ya yi magana, mutane sun yi rawan jiki; an girmama shi a cikin Isra’ila. Amma sai ya zama mai laifi na yin wa Ba’al sujada, ya kuwa mutu. Yanzu sai yin zunubi a kai a kai suke; suna yin gumaka wa kansu daga azurfansu, da wayo suna sarrafa siffofi, dukansu aikin masu aikin hannu ne. Ana magana waɗannan mutane cewa, “Suna miƙa hadayar mutum su kuma sumbaci gumakan maruƙa.” Saboda haka za su zama kamar hazon safiya, kamar raɓar safen da yakan kakkaɓe, kamar ƙaiƙayin da ake tankaɗe daga masussuka, kamar hayaƙin da yake fita daga taga. “Amma ni ne Ubangiji Allahnku, wanda ya fitar da ku daga Masar. Ba za ku yarda da wani Allah ba sai ni, ba wani Mai Ceto in ban da ni. Na lura da ku a hamada, cikin ƙasar mai ƙunar zafi. Sa’ad da na ciyar da su sun ƙoshi; sa’ad da suka ƙoshi, sai suka fara taƙama; sai suka manta da ni. Saboda haka zan hau kansu kamar zaki, zan ɓuya a bakin hanya kamar damisa. Kamar beyar da aka ƙwace mata ’ya’yanta, zan fāɗa musu in ɓarke su. Kamar zaki zan cinye su; kamar naman jeji zan yayyage su. “An hallaka ku, ya Isra’ila, domin kun tayar mini, kun tayar wa mai taimakonku. Ina sarkinku, da zai cece ku? Ina masu mulkinku cikin dukan garuruwanku, waɗanda kuka ce, ‘Ba mu sarki da shugabanni’? Saboda haka cikin fushina na ba ku sarki, kuma cikin hasalata na ɗauke shi. An yi ajiyar laifin Efraim, aka lissafta zunubansa. Naƙuda ta zo masa kamar a mace mai haihuwa, amma shi yaro ne marar hikima; sa’ad da lokaci ya kai, ba ya zuwa inda mahaifa ta buɗe. “Zan fanshe su daga ikon kabari; zan cece su daga mutuwa. Ina annobanki, ya mutuwa? Ina hallakarka, ya kabari? “Ba zan ji tausayi ba, ko da ma ya ci gaba cikin ’yan’uwansa. Iskar gabas daga Ubangiji za tă zo, tana hurawa daga hamada; maɓulɓularsa za tă kafe rijiyarsa kuma ta bushe. Za a kwashi kaya masu daraja na ɗakin ajiyarsa ganima. Dole mutanen Samariya su ɗauki laifinsu, domin sun tayar wa Allahnsu. Za a kashe su da takobi; za a fyaɗa ƙananansu da ƙasa, za a ɓarke matansu masu ciki.” Ku dawo, ya Isra’ila, ga Ubangiji Allahnku. Zunubanku ne sun zama sanadin fāɗuwarku! Ku ɗauki magana tare da ku ku komo wurin Ubangiji. Ku ce masa, “Ka gafarta mana dukan zunubanmu ka kuma karɓe mu da alheri, don mu iya yabe ka da leɓunanmu. Assuriya ba za su iya cece mu ba; ba za mu hau dawakan yaƙi ba. Ba za mu ƙara ce, ‘Allolinmu’ wa abin da hannuwanmu suka yi ba, gama a gare ka ne maraya yakan sami jinƙai.” “Zan gyara ɓatancinsu in kuma ƙaunace su a sake, gama fushina ya juya daga gare su. Zan zama kamar raɓa ga Isra’ila zai yi fure kamar lili. Kamar al’ul na Lebanon zai sa saiwarsa zuwa ƙasa; tohonsa za su yi girma. Darajarsa za tă zama kamar itacen zaitun, ƙanshinsa kamar al’ul na Lebanon. Mutane za su sāke zauna a inuwarsa. Zai haɓaka kamar ƙwayar hatsi. Zai yi fure kamar kuringa, zai zama sananne kamar ruwan inabi daga Lebanon. Efraim zai ce, me kuma zai haɗa ni da gumaka? Zan amsa masa in kuma lura da shi. Ni kamar koren itacen fir ne; amincinka yana fitowa daga gare ni ne.” Wane ne yake da hikima? Zai gane waɗannan abubuwa. Hanyoyin Ubangiji daidai ne; masu adalci sukan yi tafiya a kansu, amma ’yan tawaye sukan yi tuntuɓe a kansu. Maganar Ubangiji wadda ta zo wurin Yowel ɗan Fetuwel. Ku ji wannan, ku dattawa, ku kasa kunne, dukan waɗanda suke zaune a ƙasar. Ko wani abu makamancin haka ya taɓa faruwa a kwanakinku ko a kwanakin kakanninku? Ku faɗa wa ’ya’yanku, bari kuma ’ya’yanku su faɗa wa ’ya’yansu, ’ya’yansu kuma su faɗa wa tsara ta gaba. Abin da ɗango ya bari fāri masu girma sun cinye; abin da fāri masu girma suka bari, burduduwa ta cinye; abin da burduduwa ta bari sauran kwari sun cinye. Ku farka, ku bugaggu, ku yi kuka! Ku yi kuka da ƙarfi, ku dukan mashayan ruwan inabi; ku yi kuka mai ƙarfi saboda sabon ruwan inabi, gama an riga an ƙwace ta daga leɓunanku. Wata al’umma ta mamaye ƙasata, tana da ƙarfi ba ta kuma ƙidayuwa; tana da haƙoran zaki, da zagar zakanya. Ta mayar da kuringar inabina kango ta kuma lalatar da itatuwan ɓaurena. Ta ɓamɓare bayansu duka ta kuma jefar da su ta bar rassansu fari fat. Ku yi makoki kamar budurwa a cikin tsummoki tana baƙin ciki domin mijinta na ƙuruciyarta. Hadayun hatsi da hadayun sha an yanke su daga gidan Ubangiji. Firistoci suna makoki, su waɗanda suke yi wa Ubangiji hidima. Filaye sun zama marasa amfani, ƙasa ta bushe; an lalatar da hatsi, sabon ruwan inabin ya bushe, mai kuma ba amfani. Ku fid da zuciya, ku manoma, ku yi ihu, ku masu noma inabi; ku yi baƙin ciki saboda alkama da sha’ir, saboda an lalata girbin filaye. Kuringar inabin ta bushe itacen ɓaure kuma ya yi yaushi, ’ya’yan rumman, itacen dabino da itacen gawasa, dukan itatuwan filaye, sun bushe. Tabbatacce farin cikin ’yan adam ya bushe. Ku sa tsummoki, ya firistoci, ku yi makoki; ku yi ihu, ku da kuke yin hidima a gaban bagade. Zo, ku kwana saye da tsummoki, ku waɗanda kuke yi wa Allahna hidima, gama an yanke hadayun hatsi da hadayun sha daga gidan Allahnku. Ku yi shelar azumi mai tsarki; ku kira tsarkakan taro. Ku kira dattawa da kuma dukan mazaunan ƙasar zuwa gidan Ubangiji Allahnku, ku kuma yi kuka ga Ubangiji. Kaito saboda wannan rana! Gama ranar Ubangiji ta kusa, za tă zo kamar hallaka daga wurin Maɗaukaki. Ba a yanke abinci a idanunmu, farin ciki da kuma murna daga gidan Allahnmu ba? Iri suna ta yanƙwanewa a busasshiyar ƙasa Ɗakunan ajiya sun lalace, an rurrushe rumbunan hatsin, gama hatsi ya ƙare. Ji yadda dabbobi suke nishi! Garkunan shanu sun ruɗe saboda ba su da ciyawa, har garkunan tumaki ma suna shan wahala. A gare ka, ya Ubangiji, nake kira, gama wuta ta cinye wurin kiwo harshen wuta kuma ya ƙone dukan itatuwan jeji. Har ma namun jeji suna haki gare ka; rafuffuka sun bushe wuta kuma ta cinye wurin kiwo a jeji. Ku busa ƙaho a cikin Sihiyona; ku yi karar amo a tsaunina mai tsarki. Bari dukan mazaunan ƙasar su yi rawan jiki, gama ranar Ubangiji tana zuwa. Tana gab da faruwa rana ce ta baƙin duhu ƙirin, ranar gizagizai ce baƙi ƙirin. Babbar rundunar mayaƙa mai ƙarfi tana zuwa kamar ketowar alfijir a kan duwatsu yadda ba a taɓa ganin irinta ba, ba kuwa za a ƙara ganin irinta ba har tsararraki masu zuwa. A gabansu wuta tana ci, a bayansu ga harshen wuta yana ci, A gabansu ƙasa ta yi kamar gonar Eden, a bayansu kuma jeji ne wofi, babu abin da ya kuɓuce musu. Suna da kamannin dawakai; suna gudu kamar dokin yaƙi. Da motsi kamar na kekunan yaƙi sun tsallake ƙwanƙolin duwatsu, kamar ƙarar harshen wuta mai cin tattaka, kamar runduna mai ƙarfi wadda ta ja dāgār yaƙi. Da ganinsu, al’ummai sun kamu da azaba; kowace fuska ta yanƙwane. Sukan auka kamar jarumawa; sukan hau katanga kamar sojoji. Kowa yana takawa bisa ga tsari, ba mai kaucewa. Ba sa turin juna, kowane yakan miƙe gaba. Sukan kutsa cikin abokan gāba ba mai tsai da su. Sukan ruga cikin birni, suna gudu a kan katanga. Sukan hau gidaje, sukan shiga ta tagogi kamar ɓarayi. A gabansu duniya takan girgiza, sararin sama kuma yakan jijjigu, rana da wata su yi duhu, taurari kuma ba sa ba da haske. Ubangiji ya yi tsawa wa shugaban mayaƙansa; sojojinsa sun fi a ƙirge masu ƙarfi ne kuma su waɗanda suke biyayya da umarninsa. Ranar Ubangiji da girma take; mai banrazana. Wa zai iya jure mata? “Ko yanzu”, in ji Ubangiji, “Ku juyo gare ni da dukan zuciyarku, da azumi da kuka da makoki.” Ku kyakkece zuciyarku ba rigunanku ba. Ku juyo ga Ubangiji Allahnku, gama shi mai alheri ne mai tausayi kuma mai jinkirin fushi da yawan ƙauna, yakan kuma janye daga aika da bala’i. Wa ya sani? Ko zai juya yă kuma ji tausayi yă sa mana albarka ta wurin hadaya ta gari da hadaya ta sha wa Ubangiji Allahnku. A busa ƙaho a Sihiyona, a yi shelar azumi mai tsarki, a kira tsarkakan taro. A tattara mutane; ku tsarkake taron; ku kawo dattawa wuri ɗaya; ku kuma tara yara, da waɗanda suke shan mama. Bari ango yă bar ɗakinsa amarya kuma lolokinta. Bari firistocin da suke yin hidima a gaban Ubangiji, su yi kuka tsakanin filin haikali da bagade. Bari su ce, “Ka cece mutanenka, ya Ubangiji. Kada ka bar gādonka yă zama abin dariya, da abin ba’a a cikin al’ummai. Me zai sa a ce a cikin mutane, ‘Ina Allahnsu yake?’ ” Ta haka Ubangiji zai yi kishin ƙasarsa yă kuma ji tausayin mutanensa. Ubangiji zai amsa musu ya ce, “Ina aika da hatsi, sabon ruwan inabi, da mai, isashe da zai ƙosar da ku sosai; ba kuma zan ƙara maishe ku abin dariya ga al’ummai ba. “Zan kori sojojin arewa nesa da ku, in tura su cikin busasshiyar ƙasa marar amfani kuma, kuma da sawunsu na gaba zan tura su zuwa gabashin teku da kuma sawunsu na baya tura su zuwa yammanci a Bahar Rum. Warinsu kuma zai bazu; ɗoyinsu zai tashi.” Tabbatacce ya yi al’amura masu girma. Kada ki ji tsoro, ya ƙasa; ki yi murna ki kuma yi farin ciki. Tabbatacce Ubangiji ya yi abubuwa masu girma. Kada ku ji tsoro, ya ku namun jeji, gama wuraren kiwo sun yi kore shar. Itatuwa suna ba da ’ya’yansu; itacen ɓaure da na inabi suna ba da amfaninsu. Ku yi murna, ya ku mutanen Sihiyona, ku yi farin ciki cikin Ubangiji Allahnku, gama ya ba ku ruwan bazara cikin adalci. Yakan aika muku yayyafi a yalwace, na bazara da na kaka, kamar dā. Masussukai za su cika da hatsi; randuna za su cika da sabon ruwan inabi da mai suna zuba. “Zan mayar muku da abin da fāra suka ci a waɗannan shekaru waɗanda ɗango da fāra masu gaigayewa, da kuma sauran fāra da tarin fāra babban mayaƙan da na aika don su fāɗa muku. Za ku sami a wadace ku ci, har sai kun ƙoshi, za ku kuma yabi sunan Ubangiji Allahnku, wanda ya yi muku ayyukan banmamaki; mutanena ba za su ƙara shan kunya ba. Sa’an nan za ku sani ina cikin Isra’ila, cewa ni ne Ubangiji Allahnku, babu wani kuma; mutanena ba za su ƙara shan kunya ba. “Daga baya kuma, zan zuba Ruhuna a bisan dukan mutane. ’Ya’yanku maza da mata za su yi annabci, tsofaffinku za su yi mafarkai, matasanku za su ga wahayoyi. Har ma a bisan bayina, maza da mata, zan zuba Ruhuna a kwanakin nan. Zan nuna abubuwan banmamaki a cikin sammai da kuma a kan duniya, za a ga jini da wuta da murtukewar hayaƙi. Rana za tă duhunta wata kuma yă zama jini kafin isowar babbar ranan nan mai banrazana ta Ubangiji. Amma dukan waɗanda suka nemi Ubangiji za su tsira. Kamar yadda Ubangiji ya ce, gama a Dutsen Sihiyona da Urushalima akwai ceto, a cikin waɗannan da Ubangiji ya kira. “A waɗancan kwanaki da kuma a wancan lokaci, sa’ad da zan maido da arzikin Yahuda da Urushalima, zan tattara dukan al’ummai in kuma kawo su Kwarin Yehoshafat Can zan yi musu shari’a game da gādona, mutanena Isra’ila, gama sun warwatsar da mutanena a cikin al’ummai sun kuma raba ƙasata. Sun jefa ƙuri’a a kan mutanena suna kuma sayar da yara maza don karuwanci, sun sayar da ’yan matan domin ruwan inabi wanda za su sha. “Yanzu mene ne damuwarku da ni, ya Taya da Sidon da kuma dukan mazaunan yankunan Filistiya? Kuna ƙoƙari ku sāka mini don abin da na yi ne? In kuna sāka mini ne, to, da gaggawa zan mayar muku da sakayya a kanku. Gama kun kwashe azurfata da zinariyata kun kuma washe dukiyata mafi kyau kun kai cikin haikalinku. Kun sayar da mutanen Yahuda da na Urushalima ga mutanen Hellenawa, don ku aika da su nesa da ƙasarsu. “Duba, zan dawo da su daga wuraren da kuka sayar da su, in kuma yi muku abin da kuka yi musu. Zan sayar da ’ya’yanku maza da mata ga mutanen Yahuda, su kuma za su sayar da su ga mutanen Sabenawa, al’umma da take nesa da ku.” Ubangiji ya faɗa. Ku yi shelar wannan ga al’ummai. Ku yi shirin yaƙi! Ku tā da jarumawa! Bari mayaƙa su ja kusa su kai hari. Ku bubbuge garemaninku su zama takuba da kuma laujenku su zama māsu. Bari raunana su ce, “Ni mai ƙarfi ne!” Ku gaggauta, dukanku al’ummai daga kowane ɓangare, ku tattaru a can. Ka sauko da mayaƙanka, ya Ubangiji! “Bari a tā da dukan al’ummai; bari su kutsa zuwa Kwarin Yehoshafat gama a can zan zauna in shari’anta dukan al’ummai daga kowane ɓangare. Ku fito da lauje, gama girbi ya nuna. Ku zo, ku tattaka inabin, gama wurin matsewar ruwan inabi ya cika randunan tarawa kuma sun cika har suna zuba, muguntarsu da girma take!” Dubun dubbai suna a cikin kwarin yanke shawara! Gama ranar Ubangiji ta yi kusa a cikin kwarin yanke shawara. Za a duhunta rana da wata, taurari kuma ba za su ba da haske ba. Ubangiji zai yi ruri daga Sihiyona tsawa kuma daga Urushalima; duniya da sararin sama za su yi rawan jiki. Amma Ubangiji zai zama mafakar mutanensa, mafaka ga mutanensa Isra’ila. “Sa’an nan za ku san cewa ni, Ubangiji Allahnku, ina zaune a Sihiyona, dutsena mai tsarki. Urushalima za tă zama mai tsarki; baƙi ba za su ƙara mamaye ta ba. “A wannan rana duwatsu za su ɗiga da sabon ruwan inabi, tuddai kuma za su malmalo madara; dukan rafuffukan Yahuda za su yi ta gudano da ruwa. Maɓulɓula kuma za tă fito daga gidan Ubangiji haka ma ruwa a kwarin itatuwan ƙirya. Amma Masar za tă zama kango, Edom kuma hamada marar amfani, saboda kama-karyar da aka yi wa mutanen Yahuda, a ƙasar da aka zub da jinin marasa laifi. Za a zauna a Yahuda har abada Urushalima kuma daga tsara zuwa tsara. Alhakin jininsu, wanda ban gafarta ba, zan gafarta.” Ubangiji yana zama a Sihiyona! Kalmomin Amos, ɗaya daga cikin makiyayan Tekowa, abubuwan da ya gani game da Isra’ila shekaru biyu kafin a yi girgizar ƙasa, a lokacin da Uzziya yake sarkin Yahuda, Yerobowam ɗan Yowash kuma yake sarkin Isra’ila. Ya ce, “ Ubangiji ya yi ruri daga Sihiyona ya kuma yi tsawa daga Urushalima; wuraren kiwo duk sun bushe, dutsen Karmel kuma ya yi yaushi.” Ga abin da Ubangiji ya ce, “Saboda zunubai uku na Damaskus, har guda huɗu ma, ba zan fasa hukunta su ba. Domin sun ci zalunci Gileyad zalunci mai tsanani, zan sa wuta a gidan Hazayel, da za tă ƙona kagarun Ben-Hadad. Zan kakkarye ƙofofin Bet-Damaskus; zan hallaka sarkin da yake cikin Kwarin Awen da kuma mai riƙe da sandar mulkin Bet-Eden. Mutanen Aram za su je bauta a ƙasar Kir,” in ji Ubangiji. Ga abin da Ubangiji ya ce, “Saboda zunubai uku na Gaza, har guda huɗu ma, ba zan fasa hukunta su ba. Don sun kwashe al’umma gaba ɗaya sun sayar wa Edom, Zan aika da wuta a katangar Gaza ta ƙone duk kagarunta. Zan hallaka sarkin Ashdod da kuma mai riƙe da sandar mulki na Ashkelon. Zan hukunta Ekron, har sai dukan Filistiyawa sun mutu,” in ji Ubangiji Mai Iko Duka. Ga abin da Ubangiji ya ce, “Saboda zunubai uku na Taya, har guda huɗu ma, ba zan fasa hukunta su ba. Don sun kwashe al’umma gaba ɗaya sun kai su bauta a Edom, ba su kula da yarjejjeniyar da aka yi ta zama kamar ’yan’uwa ba, zan aika da wuta a Taya, da za tă ƙone kagarunta.” Ga abin da Ubangiji ya ce, “Saboda zunubai uku na Edom, har guda huɗu ma, ba zan fasa hukunta shi ba. Don ya fafari ɗan’uwansa da takobi, babu tausayi, domin ya ci gaba da fusata bai yarda yă huce daga fushinsa ba. Zan aika wuta a Teman da za tă ƙone kagarun Bozra.” Ga abin da Ubangiji ya ce, “Saboda zunubai uku na Ammon, har guda huɗu ma, ba zan fasa hukunta shi ba. Don ya tsaga cikin matan Gileyad masu juna biyu don kawai yă ƙwace ƙasar. Zan sa wuta a katangar Rabba da za tă ƙone kagarunta za a yi kururuwa a ranar yaƙi, faɗan kuwa zai yi rugugi kamar hadiri. Sarkinta zai je bauta, shi da ma’aikatansa,” in ji Ubangiji. Ga abin da Ubangiji ya ce, “Saboda zunubai uku na Mowab, har guda huɗu ma, ba zan fasa hukunta su ba. Gama ya ƙone ƙasusuwan sarkin Edom suka zama sai ka ce toka. Zan sa wuta a Mowab da za tă ƙone kagarun Keriyot Mowab za tă gangara cikin hayaniya mai girma cikin kururuwar yaƙi da kuma ƙarar ƙaho. Zan hallaka mai mulkinta zan kuma kashe shugabanninta.” Ga abin da Ubangiji ya ce, “Saboda zunubai uku na Yahuda, har guda huɗu ma, ba zan fasa hukunta su ba. Gama sun ƙi bin dokar Ubangiji ba su kuma yi biyayya da ƙa’idodinsa ba, domin allolin ƙarya sun ruɗe su, allolin da kakanninsu suka bauta. Zan sa wuta a Yahuda da za tă ƙone kagarun Urushalima.” Ga abin da Ubangiji ya ce, “Saboda zunubai uku na Isra’ila, har guda huɗu ma, ba zan fasa hukunta su ba. Don sun sayar da adalai waɗanda suka kāsa biyan bashinsu. Sun kuma sayar da matalauta waɗanda bashinsu bai ma kai ko kuɗin bi-labi ba. Sun tattake kawunan matalauta kamar yadda suke taka laka suka kuma danne wa marasa galihu gaskiya. Uba da ɗa su na kwana da yarinya guda, suna kuma ɓata sunana mai tsarki. Suna kwanciya kurkusa da kowane bagade a kan tufafin da suka karɓe jingina. A gidajen allolinsu sukan sha ruwan inabin da suka karɓo daga wurin waɗanda suka ci wa tara. “Na hallaka mutumin Amoriyawa a gabansu, ko da yake ya yi dogo kamar itacen al’ul kuma mai ƙarfi kamar itacen oak. Na hallaka ’ya’yan itatuwansa daga sama, da kuma jijiyoyinsa daga ƙasa. Na fitar da ku daga ƙasar Masar, na kuma bishe ku tsawon shekaru arba’in a cikin hamada don in ba ku ƙasar Amoriyawa. “Na kuma tā da annabawa daga cikin ’ya’yanku maza waɗansu kuma su zama keɓaɓɓu daga cikin samarinku. Ba haka ba ne, mutanen Isra’ila?” In ji Ubangiji. “Amma kuka sa keɓaɓɓun suka sha ruwan inabi kuka kuma umarci annabawa kada su yi annabci. “Saboda haka, yanzu zan murƙushe ku kamar yadda amalanke yakan murƙushe sa’ad da aka yi masa labtun hatsi. Masu gudu da sauri ba za su tsira ba, masu ƙarfi ba za su iya yin amfani da ƙarfinsu ba, jarumi kuma ba zai iya ceton ransa ba. ’Yan baka ba za su iya dāgewa ba, masu saurin gudu ba za su tsira ba mahayin dawakai kuma ba zai tsere da ransa ba. Ko jarumawa mafi jaruntaka za su gudu tsirara a ranan nan,” in ji Ubangiji. Ku ji wannan maganar da Ubangiji ya yi game da ku, ya ku jama’ar Isra’ila, a kan dukan iyalin da na fitar daga Masar. “Ku ne kaɗai na zaɓa cikin dukan al’umman duniya; saboda haka zan hukunta ku saboda dukan zunubanku.” Mutum biyu za su iya yin tafiya tare in ba su yarda su yi haka ba? Zaki yakan yi ruri a jeji in bai sami kama nama ba? Zai yi gurnani a cikin kogonsa in bai kama kome ba? Tsuntsu yakan fāɗa a tarko a ƙasa inda ba a sa tarko ba, ko tarko yakan zargu daga ƙasa in ba abin da ya taɓa shi? Idan aka busa ƙaho a ciki birni mutane ba sa yin rawar jiki? Sa’ad da bala’i ya auko wa birni, ba Ubangiji ne ya sa a kawo shi ba? Ba shakka, Ubangiji Mai Iko Duka ba ya yin wani abu ba tare da ya sanar wa bayinsa annabawa ba. Zaki ya yi ruri, wa ba zai tsorata ba? Ubangiji Mai Iko Duka ya yi magana, wa ba zai yi annabci ba? Ku yi shela ga kagarun Ashdod da kuma ga kagarun Masar. “Ku tara kanku a tuddan Samariya; ku ga rashin jituwar da take a cikinta, da kuma zaluncin da ake yi a cikin mutanenta.” “Ba su ma san yadda za su yi abin da yake daidai ba,” in ji Ubangiji, “sun ɓoye ganima da abubuwan da suka washe a cikin kagarunsu.” Saboda haka ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka ya ce, “Abokin gāba zai ƙwace ƙasar, zai saukar da mafakarku, zai washe kagarunku.” Ga abin da Ubangiji ya ce, “Kamar yadda makiyayi yakan ceci daga bakin zaki ƙasusuwa ƙafafu biyu kawai ko kunne ɗaya, haka za a ceci Isra’ilawa, masu zama a Samariya da kan gado kawai da kuma a ɗan ƙyalle a kan dogayen kujerunsu. ” “Ku ji wannan ku kuma yi wa gidan Yaƙub gargaɗi,” in ji Ubangiji, Ubangiji Allah Maɗaukaki. “A ranar da zan hukunta Isra’ila saboda zunubanta, zan hallaka bagadan Betel; za a yayyanka ƙahonin bagadan za su fāɗa ƙasa Zan rushe gidan rani da na damina; gidajen da aka yi musu ado da hauren giwa za a rushe su haka ma duk za a rurrushe manyan gidaje,” in ji Ubangiji. Ku kasa kunne ga wannan, ya ku shanun Bashan a kan Dutsen Samariya, ku matan da kuke cin zalin matalauta, kuke kuma danne matalauta, kuna kuma ce wa mazanku, “Ku kawo mana abin sha!” Ubangiji Mai Iko Duka ya rantse da tsarkinsa. “Tabbatacce lokaci yana zuwa da za a jawo ku da ƙugiyoyi, na ƙarshenku za a kama da ƙugiyar kifi. Dukanku za ku wuce ta kai tsaye ta inda katangar ta tsage, za a jefar da ku a Harmon,” in ji Ubangiji. “Ku tafi Betel ku yi ta aikata zunubi; ku je Gilgal ku ƙara yin zunubi. Ku kawo hadayunku kowace safiya, zakkarku kowace shekara uku. Ku ƙona burodinku mai yisti kamar hadaya ta godiya, ku yi fariya game da hadayunku na yarda rai, ku yi taƙama game da su, ya ku Isra’ilawa, gama abin da kuke jin daɗin aikata ke nan,” in ji Ubangiji Mai Iko Duka. “Na bar ku da yunwa a kowace birni, da kuma rashin abinci a kowane gari, duk da haka ba ku juyo gare ni ba,” in ji Ubangiji. “Na kuma hana muku ruwan sama tun shuke-shuken suna wata uku kafin lokacin girbi. Na sa aka yi ruwan sama a wani gari, sai na hana a yi a wani gari. Wata gona ta sami ruwan sama; wata gona kuma ta bushe. Mutane suna tangaɗi daga gari zuwa gari suna neman ruwa amma ba su sami isashen ruwan sha ba, duk da haka ba ku juyo gare ni ba,” in ji Ubangiji. “Sau da yawa na ɓata gonakinku da fumfuna da kuma cuta. Fāri suka cinye itatuwanku na inabi da na ɓaure, da na zaitun duk da haka ba ku juyo gare ni ba,” in ji Ubangiji. “Na aiko muku annoba yadda na yi a Masar. Na karkashe samarinku da takobi, tare da kamammun dawakanku. Na cika hancinku da warin sansaninku, duk da haka ba ku juyo gare ni ba” in ji Ubangiji. “Na hallaka waɗansunku kamar yadda na hallaka Sodom da Gomorra. Kuna kama da itace mai cin wutar da na cire daga cikin wuta, duk da haka ba ku juyo gare ni ba,” in ji Ubangiji. “Saboda haka ga abin da zan yi da ku, ya Isra’ila, don kuwa zan yi muku haka, sai ku yi shirin gamuwa da Allahnku, ya Isra’ila.” Shi wanda ya yi duwatsu, ya halicci iska, ya kuma bayyana wa mutum tunaninsa, shi wanda ya juya safiya ta zama duhu yana takawa a wurare masu tsawo na duniya, Ubangiji Allah Maɗaukaki ne sunansa. Ku ji wannan magana, ya gidan Isra’ila, ina makokin nan dominku. “Budurwa Isra’ila ta fāɗi, ba za tă ƙara tashi ba, an yashe ta a ƙasarta, ba wanda zai ɗaga ta.” Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka ya ce, “Birnin da ta fitar da masu ƙarfi dubbai don Isra’ila guda ɗari kaɗai za su dawo; garin da ya fitar da masu ƙarfi ɗari kuwa goma kaɗai za su dawo.” Ga abin da Ubangiji ya ce wa gidan Isra’ila. “Ku neme ni ku rayu; kada ku nemi Betel, kada ku je Gilgal, kada ku yi tafiya zuwa Beyersheba. Gama ba shakka Gilgal za tă tafi bauta, za a kuwa mai da Betel ba kome ba.” Ku nemi Ubangiji ku kuma rayu, ko kuwa zai ratsa yă share gidan Yusuf kamar wuta; zai cinye Betel kuwa ba zai sami wanda zai kashe ta ba. Ku ne masu mai da gaskiya ta koma ɗaci ku kuma zubar da adalci. (Shi wanda ya yi Taurarin nan da ake ce Kaza da ’Ya’yanta da kuma Mai Farauta da Kare, wanda ya mai da duhu ya zama haske ya kuma baƙanta rana ta zama dare, yakan kwashe ruwan teku ya zubar a ƙasa, Ubangiji ne sunansa, yakan kawo hallaka a mafaka mai ƙarfi yakan kuma mai da birnin mai katanga ya zama kufai). Ba ku son mai yin gaskiya a ɗakin shari’a kuna ƙin mai faɗar gaskiya. Kuna matsa wa matalauta kuna sa su dole su ba ku hatsi. Saboda haka, ko da yake kun gina gidajen duwatsu, ba za ku zauna a cikinsu ba; ko da yake kun nome gonaki masu kyau, ba za ku sha ruwan inabinsu ba. Gama na san yawan laifofinku da kuma girman zunubanku. Kuna danne masu adalci kuna kuma cin hanci kuna kuma hana a yi wa matalauta shari’ar adalci a majalisa. Saboda haka mai hankali yakan yi shiru a lokuta kamar haka, gama lokutan mugaye ne. Ku yi nagarta, ba mugunta ba; don ku rayu sa’an nan Ubangiji Allah Maɗaukaki zai kasance da ku, kamar yadda kuka ce zai yi. Ku ƙi mugunta, ku ƙaunaci nagarta; ku dinga yin shari’ar gaskiya a ɗakunan shari’a. Mai yiwuwa Ubangiji Allah Maɗaukaki zai ji tausayin raguwar Yusuf. Saboda haka ga abin da Ubangiji, Ubangiji Allah Maɗaukaki yana cewa, “Za a yi kururuwa a dukan tituna a kuma yi kuka don azaba a dukan wuraren da jama’a sukan taru. Za a yi kira ga manoma su yi kuka masu makoki kuma su yi kuka. Za a yi kuka a dukan gonakin inabi, gama zan ratsa a cikinku,” in ji Ubangiji. Kaitonku masu son ganin ranar Ubangiji! Don me kuke son ganin ranar Ubangiji? Za a duhunta ranan nan, ba haske ba. Za ku zama kamar mutanen da suka guje wa zaki sai suka fāɗa a hannun beyar, ko kuma kamar wanda ya shiga gida ya dāfa hannu a bango sai maciji ya sare shi. Ashe, ranar Ubangiji ba duhu ba ce, a maimakon haske, duhu wuluk, ba tare da ko ɗan haske ba. “Na ƙi, ina kuma ƙyamar bukukkuwanku na addini; ba na son ganin tarurrukanku. Ko da kun kawo mini hadayu na ƙonawa da kuma hadayu na hatsi, ba zan karɓa ba. Ko da kun kawo zaɓaɓɓun hadayu na zumunta, ba zan ɗauke su a bakin kome ba. Ku tashi daga nan da surutan waƙoƙinku! Ba zan saurari kaɗe-kaɗe da bushe bushenku ba. Amma bari gaskiya ta kwararo kamar kogi, adalci kuma kamar rafin da ba ya taɓa bushewa! “Kun kawo mini hadayu da sadakoki shekaru arba’in a cikin jeji, ya ku gidan Isra’ila? Kun ɗaga masujadar sarkinku, siffofin gumakanku, tauraron allahnku, wanda kuka yi wa kanku. Saboda haka zan tura ku zaman bauta gaba da Damaskus,” in ji Ubangiji, wanda sunansa ne Allah Mai Iko. Taku ta ƙare, ku da kuke zaman sakewa a Sihiyona, da ku waɗanda kuke ji zama a Dutsen Samariya lafiya ne, ku manyan mutanen ƙasar da take sananniya, waɗanda mutanen Isra’ila suke zuwa! Ku je Kalne ku dube ta; ku wuce daga can zuwa Hamat-rabba, sa’an nan ku gangara zuwa Gat a Filistiya. Sun fi masarautunku biyu ne? Ƙasarsu ta fi taku girma? Kuna ƙoƙari ku kauce wa wannan muguwar rana kuna kuma jawo mulkin tashin hankali kusa. Kuna kwanciya a kan gadajen da aka yi musu shimfiɗar hauren giwa kuna mimmiƙe a kan kujerunku. Kuna cin naman ƙibabbun raguna da na ƙosassun ’yan maruƙa. Kuna kaɗa molayenku yadda Dawuda ya yi kuna ƙirƙiro waƙoƙi a kan kayan kaɗe-kaɗe. Da manyan kwanoni kuke shan ruwan inabi kuna kuma shafa mai mafi kyau, amma ba kwa baƙin ciki game da kangon da Yusuf ya zama. Saboda haka za ku zama na farkon da za su tafi zaman bauta; bukukkuwanku da shagulgulanku za su ƙare. Ubangiji Mai Iko Duka da kansa ya rantse, Ubangiji Allah Maɗaukaki ya furta, “Ina ƙyamar girman kan Yaƙub, ba na kuma son kagarunsa; zan ba da birnin da duk abin da yake cikinta.” Ko da mutum goma ne suka ragu a gida guda, su ma za su mutu. In kuma wani dangi ya shiga don yă fitar da gawawwakin yă ƙone ya kuwa tambayi wani wanda yake ɓoye a can, yana cewa, “Akwai wani tare da kai?” Ya kuwa ce, “Babu,” sai yă ce, “Kul! Kada mu ambaci sunan Ubangiji.” Gama Ubangiji ya ba da umarni, zai kuma ragargaza babban gidan nan kucu-kucu ƙaramin gidan kuwa zai yi rugu-rugu da shi. Dawakai sukan yi gudu a kan duwatsu? Wani yana iya yin noma a teku da shanun noma? Amma ga shi kun mai da gaskiya ta zama dafi amfanin adalci kuma ya zama ɗaci, ku da kuke murna saboda an ci Lo Debar da yaƙi kuka kuma ce, “Ba da ƙarfinmu ne muka ƙwace Karnayim ba?” Gama Ubangiji Allah Maɗaukaki ya ce, “Zan sa wata ƙasa ta tayar muku, ya ku gidan Isra’ila, wadda za tă matsa muku tun daga Lebo Hamat zuwa kwarin Araba.” Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka ya nuna mini. Ubangiji yana shirya cincirindon fāri bayan da aka ƙarasa yankan rabon hatsin da yake na sarki, hatsi na biyu kuma yake tohuwa. Sa’ad da suka cinye kome, sai na yi kira, na ce, “ Ubangiji Mai Iko Duka, ka gafarta! Ta yaya Yaƙub zai tsira? Ga shi ɗan ƙarami ne!” Saboda haka sai Ubangiji ya dakatar da nufinsa. “Wannan ba zai faru ba,” in ji Ubangiji. Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka ya nuna mini. Ubangiji Mai Iko Duka yana shirin hukunta da wuta; wutar ta ƙone teku ta kuma ƙone ƙasa. Sai na yi kira, na ce, “ Ubangiji Mai Iko Duka, ina roƙonka ka dakata! Ta yaya Yaƙub zai tsira? Ga shi ɗan ƙarami ne!” Saboda haka sai Ubangiji ya dakatar da nufinsa. “Wannan ma ba zai faru ba,” in ji Ubangiji Mai Iko Duka. Ga abin da ya nuna mini. Ubangiji yana tsaye kusa da bangon da aka gina, bisa ga awon igiyar gwada gini, da kuma magwaji a hannunsa. Sai Ubangiji ya tambaye ni, “Me kake gani, Amos?” Sai na amsa, “Igiyar gwada gini.” Sa’an nan Ubangiji ya ce, “Duba, zan sa igiyan nan a cikin mutanena Isra’ila; ba zan ƙara barinsu ba. “Za a hallakar da wuraren sujada na Ishaku kuma tsarkakan wurare na Isra’ila za su zama kango; da takobina zan tayar wa gidan Yerobowam.” Sai Amaziya firist na Betel ya aika da saƙo zuwa wurin Yerobowam sarkin Isra’ila. “Amos yana shirya maka maƙarƙashiya a tsakiyar Isra’ila. Ƙasar ba za tă iya ɗauka abubuwan da yake faɗi ba. Gama ga abin da Amos yake cewa, “ ‘Yerobowam zai mutu ta wurin takobi, kuma tabbatacce Isra’ila za su tafi zaman bauta, nesa da ainihin ƙasarsu.’ ” Sai Amaziya ya ce wa Amos, “Tafi daga nan, mai duba kawai! Koma ƙasar Yahuda. Ka nemi abin zaman garinka a can ka kuma yi annabcinka a can. Kada ka ƙara yin annabci a Betel, gama nan wuri mai tsarki ne na sarki da kuma haikalin ƙasar.” Amos ya amsa wa Amaziya, “Ni ba annabi ba ne ko ɗan annabi, amma ni makiyayi ne, kuma ina lura da itatuwan al’ul. Amma Ubangiji ya ɗauke ni daga kiwon dabbobi ya ce mini, ‘Je ka, ka yi wa mutanena Isra’ila annabci.’ Yanzu fa, sai ka ji maganar Ubangiji. Ka ce, “ ‘Kada in yi annabci a kan Isra’ila, kuma in daina yin wa’azi a kan gidan Ishaku.’ “Saboda haka ga abin da Ubangiji ya ce, “ ‘Matarka za tă zama karuwa a cikin birni, kuma da takobi za a kashe ’ya’yanka maza da mata. Za a auna ƙasarka a kuma raba ta, kai kuma za ka mutu a ƙasar arna. Ba shakka Isra’ila za su tafi zaman bauta, nesa da ainihin ƙasarsu.’ ” Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka ya nuna mini. Ubangiji ya nuna mini kwandon nunannun ’ya’yan itace. Ya yi tambaya ya ce, “Me ka gani Amos?” Sai na amsa na ce, “Kwandon nunannun ’ya’yan itace.” Sai Ubangiji ya ce mini, “Lokaci ya yi wa mutanena Isra’ila da ba zan ƙara barinsu ba. “A ranan nan,” in ji Ubangiji Mai Iko Duka, “Waƙoƙin a haikali za su koma makoki. Za a ga gawawwaki a ko’ina! Shiru!” Ku ji wannan, ku da kuke tattake masu bukata kuka kori matalautan ƙasar. Kuna cewa, “Yaushe Sabon Wata zai wuce don mu sayar da hatsi, Asabbaci ta wuce, don mu sayar da alkama?” Mu yi awo da ma’aunin zalunci mu ƙara kuɗin kaya mu kuma cutar da mai saya, mu sayi matalauta da azurfa masu bukata kuma da takalmi, mu sayar da alkamar haɗe da yayi. Ubangiji ya rantse da Girman Yaƙub, “Ba zan taɓa mantawa da duk wani abin da suka yi ba. “Shin, ƙasar ba za tă yi rawan jiki saboda wannan ba, kuma duk masu zama a cikinta ba za su yi makoki ba? Ƙasar duka za tă hau ta sauka kamar Nilu; za a dama ta sa’an nan ta nutse kamar kogin Masar. “A wannan rana,” in ji Ubangiji Mai Iko Duka, “Zan sa rana ta fāɗi da tsakar rana in kuma duhunta duniya da rana tsaka. Zan mai da bukukkuwanku na addini su zama makoki kuma dukan waƙoƙinku su zama kuka. Zan sa dukanku ku sa rigunan makoki za ku kuma aske kawunanku. Zan sa wannan lokaci yă zama kamar lokacin da ake makokin ɗan tilon da ake da shi kuma ƙarshenta kamar rana mai ɗaci. “Ranakun suna zuwa,” in ji Ubangiji Mai Iko Duka, “sa’ad da zan aika da yunwa cikin ƙasar, ba yunwar abinci ko ta ƙishirwa ba, sai dai yunwa ta jin maganar Ubangiji. Mutane za su yi ta tangaɗi daga teku zuwa teku suna yawo daga arewa zuwa kudu, suna neman maganar Ubangiji, amma ba za su samu ba. “A wannan rana “kyawawan ’yan mata da kuma samari masu ji da ƙarfi za su suma don ƙishirwa. Waɗanda suka yi rantsuwa da abin kunya na Samariya, ko kuma su ce, ‘Muddin allahnku yana a raye, ya Dan,’ ko kuwa, ‘Muddin allahn Beyersheba yana a raye,’ za su fāɗi, ba kuwa za su ƙara tashi ba.” Na ga Ubangiji yana tsaye a gaban bagade, ya kuma ce, “Bugi kan ginshiƙan don madogaran ƙofa su girgiza. Saukar da su a kan dukan mutane; waɗanda ba su mutu ba zan kashe su da takobi. Ba mutum guda da zai tsere, babu wani da zai tsira. Ko da sun tona rami kamar zurfin kabari, daga can hannuna zai fitar da su. Ko da sun hau can sama daga can zan sauko da su. Ko da sun ɓuya a bisa Karmel, a can zan farauce su in cafko. Ko da sun ɓuya can ƙarƙashin teku, a can zan umarci maciji yă sare su. Ko da abokan gābansu sun kore su zuwa zaman bauta, a can zan umarci takobi yă kashe su. “Zan sa musu ido don mugunta ba don alheri ba.” Ubangiji, Ubangiji Maɗaukaki, shi da yakan taɓa ƙasa sai ta narke, kuma dukan mazauna cikinta suna makoki, ƙasar gaba ɗaya takan hau ta kuma sauka kamar Nilu, sa’an nan ta nutse kamar kogin Masar, shi da ya gina kyakkyawar fadarsa a cikin sammai ya kuma kafa harsashenta a duniya, shi da yakan kira ruwan teku yă kuma kwarara su a bisa duniya, Ubangiji ne sunansa. “Ku ba Isra’ilawa ba ne, daidai gare ni kamar yadda Kushawa suke?” In ji Ubangiji. “Ban fito da Isra’ila daga Masar ba, Filistiyawa kuma daga Kaftor Arameyawa kuma daga Kir ba? “Tabbatacce idanun Ubangiji Mai Iko Duka suna a kan mulkin nan mai zunubi. Zan hallaka shi daga fuskar duniya, duk da haka ba zan hallaka gidan Yaƙub ƙaƙaf ba,” in ji Ubangiji. “Gama zan ba da umarni, zan kuma tankaɗe gidan Isra’ila a cikin dukan ƙasashe kamar yadda ake tankaɗe hatsi a cikin matankaɗi kuma ko ƙwaya ɗaya ba za tă fāɗi a ƙasa ba. Dukan masu zunubi a cikin mutanena za su mutu ta wurin takobi, wato, su masu cewa, ‘Masifa ba za tă fāɗo ko ta same mu ba.’ “A wannan rana zan maido da tentin Dawuda da ya fāɗi. Zan gyaggyara wuraren da suka yayyage, in kuma maido da kufansa in gina shi kamar yadda yake a dā, domin su mallaki raguwar Edom da duk al’ummai da suke amsa sunana,” in ji Ubangiji shi wanda zai yi waɗannan abubuwa. “Ranaku suna zuwa, in ji Ubangiji, “sa’ad da mai huɗa zai sha gaban mai girbi mai shuki kuma yă bi bayan mai matsin inabi. Sabon ruwan inabi zai ɗiga daga duwatsu yă kuma kwararo daga tuddai. Zan dawo da waɗanda aka kai zaman bauta mutanena Isra’ila. “Za su sāke gina biranen da suke kango su kuma zauna a cikinsu. Za su shuka gonakin inabi su kuma sha ruwan inabinsu; za su yi lambuna su kuma ci amfaninsu. Zan dasa Isra’ila a ƙasarsu, ba kuwa za a ƙara tumɓuke su daga ƙasar da na ba su ba,” in ji Ubangiji Allahnku. Wahayin Obadiya. Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka ya ce a kan Edom. Mun ji saƙo daga wurin Ubangiji cewa, An aiki jakada zuwa ga al’ummai yă faɗa musu cewa, “Ku tashi, mu tafi mu yi yaƙi da ita.” “Duba, zan maishe ki ƙarama a cikin al’ummai; za a rena ki ƙwarai. Fariyar zuciyarki ta yaudare ki, ke da kike zama can bisa duwatsu kika kuma yi gidanki a kan ƙwanƙoli, ke da kike ce wa kanki, ‘Wa zai iya saukar da ni ƙasa?’ Ko da yake kina firiya kamar gaggafa kin kuma yi sheƙarki a can cikin taurari, daga can zan saukar da ke,” in ji Ubangiji. “In ɓarayi suka zo miki, in kuma ’yan fashi suka shigo gidan da dare, kash, bala’i zai jira ki ba abin da suke so ne kawai za su sata ba? In kuma masu tsinka ’ya’yan inabi suka zo miki, ba sukan bar ’ya’yan inabi kaɗan ba? Amma za a washe Isuwa ƙaƙaf, a kuma yaye ɓoyayyiyar dukiyarsa! Dukan waɗanda kike tarayya da su, za su kore ki zuwa iyaka; abokanki kuma za su yaudare ki, su kuma sha ƙarfinki; waɗanda suke cin abincinki, za su sa miki tarko, amma ba za ki gane ba. “A wannan rana,” in jin Ubangiji, “zan hallaka masu hikimar Edom, zan shafe mutane masu fahima a duwatsun Isuwa. Jarumawanki, ya Teman, za su razana, za a kashe kowane mutum a duwatsun Isuwa. Saboda halin kama-karyar da kika yi wa ɗan’uwanka Yaƙub, za ki sha kunya; za a hallaka ki har abada. A ranan nan kin tsaya kawai kina zuba ido yayinda baƙi suke washe dukiyar ɗan’uwanki, baƙi kuma suka shiga ta ƙofofinsa suka jefa ƙuri’a don a rarraba Urushalima, kin tsaya kina kallo kamar ɗaya daga cikin abokan gābansa. Bai kamata ki rena ɗan’uwanki a ranar masifarsa ba, ko ki yi farin ciki a kan mutanen Yahuda a ranar hallakarsu, ko ki yi fariya sosai a ranar wahalarsu. Bai kamata ki bi ta ƙofofin mutanena a ranar bala’insu ba, ko ki rena su a cikin masifarsu a ranar bala’insu, ko ki ƙwace dukiyarsu a ranar bala’insu ba. Bai kamata ki tsaya a mararraba don ki kashe waɗanda suke ƙoƙarin tserewa ba, ko ki ba da waɗanda suka tsere ga hannun maƙiyansu a ranar wahalarsu ba. “Ranar Ubangiji ta yi kusa don dukan al’ummai. Kamar yadda kuka yi, haka za a yi muku; ayyukanku za su koma a kanku. Kamar yadda kuka sha a kan tuduna mai tsarki, haka dukan al’ummai za su yi ta sha, za su sha, su kuma sha su zama sai ka ce ba su taɓa kasancewa ba. Amma a kan Dutsen Sihiyona za a sami ceto; Dutsen zai zama mai tsarki, gidan Yaƙub kuma zai mallaki gādonsa. Gidan Yaƙub zai zama kamar wuta, gidan Yusuf kuma kamar harshen wuta; gidan Isuwa zai zama kamar tattaka, za a kuma sa masa wuta yă ƙone. Babu wanda zai tsira daga gidan Isuwa.” Ni Ubangiji na faɗa. Mutane daga Negeb za su mamaye duwatsun Isuwa, mutane kuma daga gindin tuddai za su mallaki ƙasar Filistiyawa. Za su mamaye filayen Efraim da Samariya, Benyamin kuwa zai mallaki Gileyad. Wannan ƙungiyar Isra’ilawan da aka kwashe zuwa bauta da suke a Kan’ana za su mallaki ƙasar har zuwa Zarefat; waɗannan da aka kwashe zuwa bauta daga Urushalima da suke a Sefarad za su mallaki garuruwan Negeb. Masu kawo ceto za su haura zuwa Dutsen Sihiyona don su yi mulkin duwatsun Isuwa. Ubangiji ne zai yi mulki. Maganar Ubangiji ta zo wa Yunana ɗan Amittai cewa, “Tafi babban birnin nan Ninebe ka yi mata wa’azi, saboda muguntarta ta haura zuwa gabana.” Amma Yunana ya gudu daga Ubangiji ya nufi Tarshish. Ya gangara zuwa Yaffa, inda ya sami jirgin ruwa mai shirin tashi daga tashar. Bayan ya biya kuɗin tafiya, sai ya shiga jirgi ya kama hanya zuwa Tarshish don yă tsere wa Ubangiji. Sai Ubangiji ya aika da babban iska a bisan teku, hadiri ya tsananta ƙwarai har jirgin ya yi barazanar farfashewa. Dukan matuƙan jirgin suka tsorata, kowannensu kuma ya yi kuka ga allahnsa, suka kuma jefar da kayan jirgi a cikin teku domin su rage nauyin jirgin. Ana cikin haka, ashe, Yunana ya sauka can ƙarƙashin jirgi ya je ya kwanta, yana ta sharar barcinsa. Sai kyaftin ɗin ya je wajensa ya ce masa, “Don me kake barci? Tashi ka kira bisa ga allahnka! Mai yiwuwa yă ji mu, yă cece mu don kada mu hallaka.” Matuƙan jirgin suka ce wa juna, “Ku zo, mu jefa ƙuri’a mu ga wa ke da alhakin wannan masifa.” Sai suka jefa ƙuri’a, ƙuri’ar kuwa ta fāɗa a kan Yunana. Saboda haka suka tambaye shi suka ce, “Yanzu, gaya mana, dalilin da ya sa wannan masifa ta zo mana? Mene ne aikinka? Daga ina ka fito? Ina ne ƙasarka? Daga wacce kabila ce ka fito?” Sai ya amsa, “Ni mutumin Ibraniyawa ne, ina kuma bauta wa Ubangiji Allah na sama, wanda ya yi teku da tuddai.” Sai matuƙan jirgin suka tsorata ƙwarai, suka ce masa, “Wane irin mugun abu ne ka aikata haka?” (Sun gane cewa yana gudu ne daga wurin Ubangiji, domin ya riga ya faɗa musu.) Sai tekun ya daɗa rikicewa. Sai suka tambaye shi, “Me za mu yi da kai domin tekun yă daina hauka?” Ya amsa musu ya ce, “Ku ɗauke ni ku jefa a cikin teku, tekun zai kwanta. Na san cewa laifina ne ya jawo wannan babban hadirin da ya auka muku.” Maimakon mutanen su yi haka, sai suka yi ƙoƙari su tura jirgin ruwan zuwa bakin teku. Amma ba su iya ba, saboda iskar ta sa tekun ya yi ta ƙara hauka. Sai suka yi kuka ga Ubangiji suka ce, “Ya Ubangiji, in ka yarda kada ka bar mu mu mutu saboda ran mutumin nan. Kada ka yi mana hukuncin masu kisankai, gama kai ne, ya Ubangiji, ka ga ya gamshe ka.” Sa’an nan suka ɗauki Yunana suka jefar da shi daga jirgin, sai tekun ya kwanta. Ganin haka sai mutanen suka cika da tsoron Ubangiji, suka kuma miƙa wa Ubangiji hadaya, suka yi wa’adi da shi. Amma Ubangiji ya tanada wani babban kifi da zai haɗiye Yunana, Yunana kuwa ya yi yini uku da dare uku a ciki cikin kifin. Daga ciki cikin kifi, Yunana ya yi addu’a ga Ubangiji Allahnsa. Ya ce, “A cikin damuwata na yi kira ga Ubangiji, ya kuwa amsa mini. Daga cikin zurfi kabari na yi kiran neman taimako, ka kuwa saurari kukata. Cikin tashin hankali, ka jefa ni cikin zurfafa, a tsakiyar teku, ka kuma jujjuya ni a cikin ruwa; dukan raƙuman ruwanka da ambaliyarka sun bi ta kaina. Sai na ce, ‘An kore ni daga fuskarka; duk da haka zan sāke duba wajen haikalinka mai tsarki.’ Ruwayen da suke kewaye da ni sun yi mini barazana, zurfi kuma ya kewaye ni, ciyayin ruwa suna nannaɗe kewaye da ni. Na nutsa har ƙarƙashin tuddai; a ƙarƙashin duniya, ka rufe ni har abada. Amma ka dawo da raina daga rami, Ya Ubangiji Allahna. “Sa’ad da na ji raina yana rabuwa da ni, na tuna da kai ya Ubangiji, addu’ata kuma ta kai gare ka, a haikalinka mai tsarki. “Waɗanda suka maƙale wa gumaka marasa amfani, sukan ƙyale alherin da zai kasance nasu. Amma ni, da waƙar godiya, zan miƙa tawa hadaya gare ka. Abin da na yi alkawari, shi ne zan yi. Ceto yakan zo ne kawai daga wurin Ubangiji.” Sai Ubangiji ya umarci kifin, kifin kuwa ya amayar da Yunana a gaɓan teku. Sa’an nan sai maganar Ubangiji ta zo wa Yunana sau na biyu. “Tafi babban birnin nan Ninebe, ka yi masa shelar saƙon da na ba ka.” Sai Yunana ya yi biyayya da maganar Ubangiji, ya tafi Ninebe. Ninebe birni ne da yake da muhimmanci, wanda sai an ɗauki kwana uku kafin a iya zaga shi. A rana ta fari, Yunana ya kama tafiya yana ratsa birnin. Sai ya yi shela cewa, “Nan da kwana arba’in za a hallaka Ninebe?” Mutanen Ninebe kuwa suka gaskata Allah. Aka yi shela a yi azumi, sai dukansu daga babba har zuwa ƙaraminsu, suka sa tufafin makoki. Da saƙon Yunana ya kai kunnen sarkin Ninebe, sai ya tashi daga kujerar mulkinsa, ya tuɓe alkyabbarsa, ya sa rigar makoki, ya zauna cikin toka. Sai ya yi umarni a Ninebe cewa, “Bisa ga umarnin sarki da fadawansa. “Kada a bar wani mutum ko dabba, garke ko shannu, su ɗanɗana wani abu; kada a bari su ci ko su sha. Bari kowane mutum da dabba yă yafa rigunan makoki. Kowa yă roƙi Allah da gaske, kowa kuma yă bar mugayen ayyukan da yake yi. Wa ya sani? Ko Allah zai ji tausayinmu da kuma juyayinmu yă janye zafin fushinsa don kada mu hallaka.” Da Allah ya ga abin da suka yi, da kuma yadda suka juya daga mugayen hanyoyinsu sai ya ji tausayinsu, bai kawo hallaka a kansu yadda ya yi shirin yi ba. Sai abin ya ɓata wa Yunana rai ƙwarai har ya yi fushi. Sai ya yi addu’a ga Ubangiji ya ce, “Ya Ubangiji, ba irin abin da na faɗa ke nan ba tun ina gida? Wannan ne ya sa na yi ƙoƙarin tserewa zuwa Tarshish. Ai, na sani kai Allah ne mai alheri da tausayi, mai jinkirin fushi da cikakkiyar ƙauna, kai Allah ne mai dakatar da nufinka na yin hukunci. Yanzu, ya Ubangiji, ka ɗauki raina, domin ya fi sauƙi a gare ni in mutu da in rayu.” Amma Ubangiji ya amsa, ya ce; “Daidai ne ka yi fushi?” Sai Yunana ya fita daga birnin ya yi wajen gabas, ya zauna. A nan ya yi wa kansa rumfa, ya zauna cikin inuwarta yana jira yă ga abin da zai sami birnin. Sai Ubangiji Allah ya sa wata ’yar kuringa ta tsiro, ta yi girma a inda Yunana yake, don ta inuwantar da shi, yă ji daɗi. Yunana kuwa ya yi murna matuƙa da wannan kuringa. Amma kashegari da safe sai Allah ya sa tsutsa ta cinye ’yar kuringar har ta mutu. Sa’ad da rana ta yi sama, sai Allah ya sa iskar gabas mai zafi ta huro, zafin ranar kuma ya buga kan Yunana, har ya ji sai ka ce zai suma. Ya so a ce ya mutu ma, sai ya ce, “Gara in mutu da a ce ina zaune da rai.” Amma Allah ya ce wa Yunana, “Daidai ne ka yi fushi saboda wannan kuringa?” Sai Yunana ya ce, “I, daidai ne, ina fushi matuƙa, har ina so da na mutu ma.” Sai Ubangiji ya ce, “Ai, wannan kuringa ta tsira dare ɗaya ta kuma ɓace kafin dare na biyu, ba ka yi wata wahala dominta ba, ba kai ne ka sa ta yi girma ba, duk da haka ranka ya ɓace saboda ita. Ashe, ba dole ne in ji tausayin babban birnin nan Ninebe mai mutum sama da dubu ɗari da ashirin (120,000) marasa alhaki, da kuma dabbobi masu yawa ba?” Maganar Ubangiji ta zo wa Mika mutumin Moreshet a zamanin Yotam, da na Ahaz, da kuma na Hezekiya, sarakunan Yahuda, Mika ya ga wahayi a kan Samariya da kuma a kan Urushalima. Ga abin da ya ce. Ku ji, ya ku mutane duka, ki saurara, ya ke duniya da dukan mazauna cikinki, bari Ubangiji Mai Iko Duka yă zama shaida a kanku, daga haikalinsa mai tsarki. Duba! Ubangiji yana zuwa daga wurin zamansa; zai sauko yă taka maɗaukakan wuraren duniya. Duwatsu za su narke a ƙarƙashin ƙafafunsa, kamar kaki a gaban wuta, kwaruruka kuma za su ɓace, kamar ruwan da yake gangarowa daga tsauni. Duk wannan zai faru saboda laifin Yaƙub, da kuma zunuban gidan Isra’ila ne. Mene ne laifin Yaƙub? Shin, ba Samariya ba ce? Ina ne maɗaukakan wuraren Yahuda? Shin, ba Urushalima ba ce? “Saboda haka zan mai da Samariya tarin juji, wurin noman inabi. Zan zubar da duwatsunta a cikin kwari in kuma bar harsashin gininta a bayyane. Za a ragargaje dukan allolinta; za a ƙone dukan baye-bayenta na haikali da wuta; zan lalatar da dukan gumakanta. Tun da ta wurin karuwanci ne ta tattara su, ga karuwanci kuma za su koma.” Saboda wannan zan yi baƙin ciki, in yi kuka; zan yi tafiya ba takalmi, zan tuɓe, in kuma yi tafiya tsirara. Zan yi kuka kamar dila, in yi baƙin ciki kamar mujiya. Gama raunin Samariya ba mai warkewa ba ne; ya bazu har Yahuda. Ya ma kai bakin ƙofar mutanena, har ma Urushalima da kanta. Kada a faɗe shi a Gat; kada ma a yi kuka. A maimako haka, a yi birgima a cikin ƙura a Bet-Leyafra. Ku wuce tsirara da kuma kunya, ku mazaunan Shafir. Bet-Ezel tana makoki domin babu wani daga Za’anan da ya fito don yă taimaka. Mazaunan Marot sun ƙosa su ga alheri, amma Ubangiji ya sauko da azaba, har zuwa ƙofar Urushalima. Ku da kuke zama a Lakish, ku ɗaura wa dawakai kekunan yaƙi. Gama ku kuka fara yin zunubi a Sihiyona, gama an sami laifofin Isra’ila a cikinku. Saboda haka za ku ba da kyautan bankwana ga Moreshet Gat. Garin Akzib zai zama abin yaudara ga sarakunan Isra’ila. Ku mazaunan Maresha Ubangiji zai kawo wanda zai ci ku da yaƙi. Sarakunan Isra’ila za su gudu zuwa Adullam. Ku aske kanku ƙwal don makoki, ku yi wa kanku ƙwalƙwal kamar ungulu. Gama za a ja ’ya’yan da kuke farin ciki a kai su bauta. Taku ta ƙare, ku da kuke shirya makirci, ku da kuke ƙulle-ƙullen mugunta a kan gadonku! Da gari ya waye sai ku fita ku aikata mugunta domin ikon aikatawa yana hannunku. Kukan yi ƙyashin gonaki ku kuma ƙwace su, ku yi ƙyashin gidaje ku kuma ƙwace. Kukan zalunci mutum, ku ƙwace masa gidansa, har ku ƙwace masa gādonsa. Saboda haka, Ubangiji ya ce, “Ina shirya wa waɗannan mutane bala’i, yadda ba za ku iya ceton kanku ba. Ba za ku ƙara tafiya kuna taƙama ba, gama zai zama lokacin bala’i ne. A wannan rana mutane za su yi muku ba’a za su yi muku gwalo da wannan waƙar makoki, ‘An lalatar da mu sarai; an rarraba mallakar mutanena. Ya ɗauke shi daga gare ni! Ya miƙa filayenmu ga maciyan amanarmu.’ ” Saboda haka ba za ku kasance da wani a taron jama’ar Ubangiji da zai raba ƙasar ta wurin jefa ƙuri’a ba. “Kada ku yi annabci” in ji annabawansu. “Kada ku yi annabci game da waɗannan abubuwa; abin kunya ba zai same mu ba.” Daidai ne a ce, ya gidan Yaƙub, “Ruhun Ubangiji yana fushi ne? Yana yin irin waɗannan abubuwa?” “Ashe, maganata ba tă amfane wanda ayyukansa suke daidai ba? Ba da daɗewa ba mutanena sun tashi kamar magabci. Kun tuɓe riga mai tsada daga waɗanda suke wucewa ba tare da kun damu ba, sai ka ce mutanen da suke komowa daga yaƙi. Kun kori matan mutanena daga gidajensu masu daɗi. Kuka kawar da albarkata har abada daga wurin ’ya’yansu. Ku tafi, ku ba ni wuri! Gama wannan ba wurin hutunku ba ne, gama ya ƙazantu, ya zama kangon da ya wuce gyara. In maƙaryaci da mazambaci ya zo ya ce, ‘Zan yi muku annabci ku sami wadataccen ruwan inabi da barasa,’ zai dai zama annabin da ya dace da wannan mutane ne! “Tabbatacce zan tattara ku duka, ya gidan Yaƙub; zan tattara ku raguwar Isra’ila. Zan kawo su wuri ɗaya kamar tumaki a cikin garke, kamar garke a wajen kiwonsa; wurin zai cika da mutane. Wanda ya fasa ƙofa ya buɗe, shi zai haura yă yi musu jagora, za su fashe bangon su fita. Sarkinsu zai wuce gabansu, Ubangiji kuma zai kasance a gaba.” Sa’an nan na ce, “Ku kasa kunne, ku shugabannin Yaƙub, ku masu mulkin gidan Isra’ila. Ya kamata ku san shari’a, ku da kuke ƙin abu mai kyau kuke ƙaunar mugunta, ku da kuke feɗe mutanena kuke tuge nama daga ƙasusuwansu; ku da kuke cin naman mutanena, ku feɗe fatar jikinsu kuke kakkarya ƙasusuwansu, kuke yayyanka su gunduwa-gunduwa kamar naman da za a toya, kamar naman da za a sa a dafa.” Sa’an nan za su kira ga Ubangiji, amma ba zai amsa musu ba. A wannan lokaci zai ɓoye fuskarsa daga gare su saboda irin muguntar da suka yi. Ga abin da Ubangiji ya faɗa, “Game da annabawa masu ɓad da mutanena, in wani ya ciyar da su, sai su ce akwai ‘salama’ amma in bai ciyar da su ba, a shirye suke su kai masa hari. Saboda haka dare yana zuwa a bisanku, ba tare da wahayi ba, kuma duhu, ba tare da duba ba. Rana za tă fāɗi wa annabawa, yini kuma zai zama musu duhu. Masu gani za su ji kunya, masu duba kuma za su ji taƙaici. Dukansu za su rufe fuskokinsu gama ba amsa daga Allah.” Amma game da ni, ina cike da iko ta wurin Ruhun Ubangiji da kuma adalci da ƙarfi, don a sanar da Yaƙub laifofinsa, ga Isra’ila kuma zunubinsa. Ku ji wannan, ku shugabannin gidan Yaƙub, ku masu mulkin gidan Isra’ila, ku da kuke ƙyamar gaskiya, kuka karkatar duk abin da yake na gaskiya; kuka gina Sihiyona ta wurin zub da jini, Urushalima kuma ta wurin mugunta. Hukunce-hukuncen shugabannin ƙasar na cin hanci ne, firistocinta kuma suna koyarwa don a biya su, annabawanta kuwa suna yin annabci don neman kuɗi. Duk da haka suna jingina a kan Ubangiji suna cewa, “Ba Ubangiji yana tare da mu ba? Ba bala’in da zai zo mana.” Don haka, saboda ku, za a nome Sihiyona kamar gona, Urushalima kuma ta zama tarin juji, tudun haikali kuwa zai zama kurmin ƙayayyuwa. A kwanakin ƙarshe za a kafa dutsen haikalin Ubangiji yă zama babba a cikin duwatsu. Za a ɗaga shi sama da tuddai, mutane kuma za su riƙa ɗunguma zuwa gare shi. Al’ummai da yawa za su zo su ce, “Ku zo, bari mu haura zuwa dutsen Ubangiji, zuwa gidan Allah na Yaƙub. Zai koya mana hanyoyinsa, don mu yi tafiya cikin hanyoyinsa.” Doka za tă fita daga Sihiyona, maganar Ubangiji kuma daga Urushalima. Zai shari’anta tsakanin mutane yă kuma sulhunta tsakanin manyan al’ummai nesa da kuma kusa. Har su mai da takubansu su zama garemani, māsunsu kuma su zama wuƙaƙen askin itace. Al’umma ba za tă ɗauki takobi gāba da wata al’umma ba, ko a yi horarwa don yaƙi. Kowa zai zauna a tushen kuringar inabinsa da tushen ɓaurensa, kuma ba wanda zai tsoratar da su, gama Ubangiji Maɗaukaki ne ya faɗa. Dukan al’ummai za su iya tafiya a cikin sunan allolinsu; mu dai za mu yi tafiya a cikin sunan Ubangiji Allahnmu har abada abadin. “A wannan rana,” in ji Ubangiji, “zan tattara guragu; zan kuma tara masu zaman bauta, da waɗanda na sa suka damu. Zan mai da guragu su zama raguwa, waɗanda aka kora, su zama al’umma mai ƙarfi. Ubangiji zai yi mulkinsu a Dutsen Sihiyona daga wannan rana da kuma har abada. Game da ke, ya hasumiyar tsaron garke, Ya mafaka Diyar Sihiyona, za a maido miki da mulkinki na dā, sarauta kuma za tă zo wa Diyar Urushalima.” Don me yanzu kike kuka da ƙarfi, ba ki da sarki ne? Masu shawararki sun hallaka ne, da zafi ya cika ki kamar mace mai naƙuda? Ki yi birgima cikin zafin azaba, ya Diyar Sihiyona, kamar macen da take naƙuda, don yanzu dole ki bar birni ki kafa sansani a filin Allah. Za ki tafi Babilon; a can za a kuɓutar da ki. A can ne Ubangiji zai fanshe ki daga hannun maƙiyanki. Amma yanzu al’ummai da yawa suna gāba da ke. Suna cewa, “Bari a ƙazantar da ita, bari mu zuba wa Sihiyona ido.” Amma ba su san tunanin Ubangiji ba; ba su fahimci shirinsa ba, shi da ya tattara su kamar dammuna a masussuka. “Ki tashi ki yi sussuka, ya Diyar Sihiyona, gama zan ba ki ƙahonin ƙarfe; zan ba ki kofatan tagulla domin ki ragargaje al’ummai masu yawa.” Za ki ba Ubangiji dukan dukiyarsu da suka tara ta hanyar zamba, wadatarsu kuma ga Ubangiji dukan duniya. Ki tattara sojojinki, ya ke birnin mayaƙa, gama an kewaye mu da yaƙi. Za su bugi kumatun mai mulkin Isra’ila da sandar ƙarfe. “Amma ke, Betlehem ta Efrata, ko da yake ke ƙarama ce daga cikin zuriyarki a Yahuda, daga cikinki wani zai zo domina wanda zai yi mulkin Isra’ila, wanda asalinsa tun fil azal ne.” Saboda haka za a yashe Isra’ila har sai wadda take naƙuda ta haihu sauran ’yan’uwansa kuma sun dawo su haɗu da Isra’ilawa. Zai tsaya yă yi kiwon garkensa da ƙarfin Ubangiji, cikin girman sunan Ubangiji Allahnsa. Za su kuma zauna lafiya, gama girmansa za tă kai har ƙarshen duniya. Zai kuma zama salamarsu. Sa’ad da Assuriyawa suka kawo wa ƙasarmu hari suka tattake kagarunmu, za mu tā da makiyaya bakwai, har ma shugabannin mutane takwas su yi gāba da su. Za su yi mulkin ƙasar Assuriya da takobi, ƙasar Nimrod kuma da zaran takobi. Zai cece mu daga hannun Assuriyawa sa’ad da suka kawo wa ƙasarmu hari suka kuma tattake zuwa cikin iyakokinmu. Raguwar Yaƙub za tă kasance a tsakiyar mutane masu yawa kamar raɓa daga Ubangiji, kamar yayyafi a kan ciyawa, wanda ba ya jiran mutum ko kuma yă dakata wa ɗan adam. Raguwar Yaƙub za tă kasance tare da al’ummai, a cikin mutane masu yawa, kamar zaki a cikin sauran namun jeji, kamar ɗan zaki cikin garken tumaki, wanda yake tattaka yă kuma yi kaca-kaca da su sa’ad da yake ratsa a cikinsu, ba kuwa wanda zai cece su. Za a ɗaga hannunka cikin nasara a kan abokan gābanka, za a hallaka maƙiyanka duka. “A wannan rana,” in ji Ubangiji “Zan hallaka dawakanku daga cikinku, in kuma rurrushe kekunan yaƙinku. Zan hallaka biranen ƙasarku in yi rugu-rugu da dukan katangunku. Zan kawar da maitarku, ba za a ƙara yin sihiri ba. Zan sassare dukan gumakan da kuka sassaƙa da keɓaɓɓun duwatsunku a cikinku, nan gaba ba za ku ƙara rusuna wa aikin hannuwanku ba. Zan tumɓuke daga gare ku ginshiƙan Asheranku in kuma rurrushe biranenku. Zan yi ramuwa cikin fushi da hasala a kan al’umman da ba su yi mini biyayya ba.” Ku saurari abin da Ubangiji ya ce, “Tashi ku gabatar da ƙararku a gaban duwatsu; bari tuddai su ji abin da kuke so ku faɗa. “Ku saurara, ya ku duwatsu game da tuhumar da Ubangiji yake muku, ku ji, ku daɗaɗɗun tushin duniya. Gama Ubangiji yana da ƙara a kan mutanensa; yana tuhumar Isra’ila. “Ya ku mutanena, me na yi muku? Ta yaya na nawaita muku? Ku amsa mini. Na fito da ku daga ƙasar Masar na kuma ’yantar da ku daga ƙasar bauta. Na aika da Musa yă jagorance ku, haka ma Haruna da Miriyam. Ya ku mutanena, ku tuna abin da Balak sarkin Mowab ya ƙulla da kuma amsar da Bala’am ɗan Beyor ya bayar. Ku tuna da tafiyarku daga Shittim zuwa Gilgal, don ku san ayyukan adalcin Ubangiji.” Da me zan zo a gaban Ubangiji in rusuna a gaban Maɗaukaki Allah? Shin, zan zo ne a gabansa da hadaya ta ƙonawa, da ɗan maraƙi bana ɗaya? Ubangiji zai ji daɗin hadayar raguna dubbai da kuma rafuffukan mai dubbai goma? Zan ba da ɗan farina ne don laifina, ko ’ya’yan jikina domin zunubin raina? Ya nuna maka, ya mutum, abin da yake mai kyau. Me Ubangiji yake bukata daga gare ka kuwa shi ne ka yi gaskiya ka so aikata jinƙai ka kuma yi tafiya da tawali’u a gaban Allah. Ku saurara! Ubangiji yana kira ga birni, a ji tsoron sunana kuwa hikima ce, “Ku kasa kunne ga sandan nan da kuma wannan wanda ya naɗa. Har yanzu zan manta, ya muguwar gida da dukiyarki da kika samu a muguwar hanya zan kuma manta da bugaggen mudun awo wanda ake zargi? Zan kuɓutar da mutumin da yake da ma’auni na rashin gaskiya, da kuma buhun ma’aunan ƙarya? Attajiranta masu fitina ne; mutanenta kuma maƙaryata ne harsunansu kuwa suna yaudara. Saboda haka, zan hallaka ku in lalace ku saboda zunubanku. Za ku ci amma ba za ku ƙoshi ba, cikinku zai zama babu kome Za ku tattara amma ba za ku yi ajiyar kome ba, gama abin da kuka yi ajiya zan ba wa takobi. Za ku yi shuki amma ba za ku girba ba; za ku matse zaitun amma ba za ku yi amfani da mai wa kanku ba, za ku tattaka ’ya’yan inabi amma ba za ku sha ruwan inabin ba. Kuna kiyaye ƙa’idodin Omri da dukan ayyukan gidan Ahab kun kuma bi al’adunsu. Saboda haka, zan maishe ku kufai in mai da ku abin dariya a cikin mutane, za ku sha reni a wurin al’ummai.” Tawa ta ƙare! Ina kama da wanda yake tattara ’ya’yan itatuwa a lokacin kalar ’ya’yan inabi; babu sauran nonon inabin da za a tsinka a ci, babu kuma ’ya’yan ɓaure na farko-farkon da raina yake marmari. An kawar da masu tsoron Allah daga ƙasar; babu sauran mai adalcin da ya rage. Dukan mutane suna kwanto don su zub da jini; kowa yana farautar ɗan’uwansa da tarko. Dukan hannuwansu sun gwaninta wajen yin mugunta; shugabanni suna nema a ba su kyautai, alƙalai suna nema a ba su cin hanci, masu iko suna faɗar son zuciyarsu, duk suna ƙulla makirci tare. Mafi kyau a cikinsu yana kama da ƙaya, mafi gaskiyarsu ya fi shingen ƙaya muni. Ranar da Allah zai ziyarce ku ta zo, ranar da masu gadinku za su hura ƙaho. Yanzu ne lokacin ruɗewarku. Kada ka yarda da maƙwabci; kada ka sa begenka ga abokai. Ko ma wadda take kwance a ƙirjinka, ka yi hankali da kalmominka. Gama ɗa yakan ce wannan ba mahaifinsa ba ne, diya kuma takan tayar wa mahaifiyarta, matar ɗa takan yi gāba da uwar mijinta, abokan gāban mutum su ne iyalin cikin gidansa. Amma game da ni, zan sa bege ga Ubangiji, ina sauraron Allah Mai Cetona; Allahna kuwa zai ji ni. Kada ku yi farin ciki, ku maƙiyana! Ko da yake na fāɗi, zan tashi. Ko da yake na zauna a cikin duhu, Ubangiji zai zama haskena. Domin na yi masa zunubi, zan fuskanci fushin Ubangiji, har sai ya dubi batuna ya kuma tabbatar da ’yancina. Zai kawo ni zuwa wurin haske; zan ga adalcinsa. Sa’an nan maƙiyina zai gani yă kuma sha kunya, shi da yake ce da ni “Ina Ubangiji Allahnka?” Zai gani, yă kuma ji kunya. Ko yanzu ma za a tattake shi kamar taɓo a tituna. Ranar gina katangarka tana zuwa, a ranar za a fadada iyakokinka. A wannan rana mutane za su zo gare ka daga Assuriya da kuma biranen Masar, daga Masar ma har zuwa Yuferites daga teku zuwa teku, kuma daga dutse zuwa dutse. Duniya za tă zama kufai saboda mazaunanta, saboda ayyukansu. Ka yi kiwon mutanenka da sandarka, garken gādonka, wanda yake zaune shi kaɗai a kurmi, a ƙasa mai kyau ta kiwo, bari su yi kiwo a Bashan da Gileyad kamar a kwanakin dā. “Kamar a kwanakin da kuka fito daga Masar, zan nuna musu al’ajabaina.” Al’ummai za su gani su kuma ji kunya, za a kuma ƙwace musu dukan ikonsu. Za su kama bakinsu kunnuwansu kuma za su zama kurame. Za su lashi ƙura kamar maciji, kamar dabbobi masu rarrafe a ƙasa. Za su fito daga maɓuyarsu da rawan jiki, za su juya cikin tsoro ga Ubangiji Allahnmu su kuma ji tsoronku. Wane ne Allah kamar ka, wanda yake yafe zunubi yă kuma gafarta laifofin mutanensa da suka ragu? Ba ka zama mai fushi har abada amma kana marmari ka nuna jinƙai. Za ka sāke jin tausayinmu; za ka tattake zunubanmu a ƙarƙashin sawunka ka kuma tura dukan kurakuranmu zuwa cikin zurfafan teku. Za ka yi wa Yaƙub aminci, ka kuma nuna jinƙai ga Ibrahim, kamar yadda ka yi alkawari da rantsuwa ga kakanninmu tun a kwanankin dā. Jawabi game da Ninebe a littafin wahayin Nahum, mutumin Elkosh. Ubangiji Allah mai kishi ne, mai sakayya kuma. Ubangiji Allah mai kishi ne, mai ɗaukar fansa kuma. Ubangiji yakan ɗauki fansa a kan maƙiyansa, yakan ci gaba da fushi a kan abokan gābansa. Ubangiji mai jinkirin fushi ne, mai iko duka kuma. Ubangiji ba zai bar masu zunubi babu horo ba. Hanyarsa tana cikin guguwa da kuma hadari, gizagizai kuwa su ne ƙurar ƙafafunsa. Yakan tsawata wa teku yă kuma busar da shi; yakan sa dukan koguna su kafe. Bashan da Karmel sun yi yaushi tohon Lebanon kuma ya koɗe. Duwatsu suna rawan jiki a gabansa tuddai kuma sun narke. Duniya da dukan abin da yake cikinta suna rawan jiki a gabansa. Wa zai iya tsaya wa fushinsa? Wa yake da ikon jimre wa zafin hasalarsa? Ana zuba fushinsa kamar wuta; aka kuma ragargaza duwatsu a gabansa. Ubangiji nagari ne, mafaka kuma a lokacin wahala. Yana kula da waɗanda suka dogara gare shi, amma da ambaliyar ruwa zai kawo Ninebe ga ƙarshe; zai fafari maƙiyansa zuwa cikin duhu. Dukan abin da suke ƙullawa game da Ubangiji zai kawo ga ƙarshe; wahala ba za tă sāke komowa ƙaro na biyu ba. Za su sarƙafe a ƙaya, za su kuma bugu da ruwan inabinsu; za a laƙume su kamar busasshiyar ciyawa. Daga cikinki, ya Ninebe wani ya fito wanda ya ƙulla wa Ubangiji makirci yana ba da mugayen shawarwari. Ga abin da Ubangiji ya ce, “Ko da yake sun yi tarayya, suna kuma da yawa, za a yanke su, a kawar a su. Ko da yake na ba ki azaba, ya Yahuda, ba zan ƙara ba ki azaba ba. Yanzu zan karya karkiyarsu daga wuyanki in kuma tsittsinke sarƙar da suka ɗaura ki.” Ubangiji ya ba da umarni game da ke Ninebe, “Ba za ki sami zuriyar da za tă ci gaba da sunanki ba. Zan rurrushe siffofin da kuka sassaƙa da kuma gumakan da kuka ƙera gumakan da suke a cikin haikalin allolinku. Zan shirya kabarinki, domin ke muguwa ce.” Duba, can a bisa duwatsu, ga ƙafafu mai kawo labari mai daɗi, wanda yake shelar salama! Ki yi bukukkuwanki, ya Yahuda, ki kuma cika wa’adodinki. Mugaye ba za su ƙara mamaye ki ba; domin za a hallaka su ƙaƙaf. Mai hari yana matsowa a kanki, Ninebe. Ki tsare mafaka, ki yi gadin hanya ki sha ɗamara ki tattaro dukan ƙarfinki! Ubangiji zai maido da darajar Yaƙub, kamar ta Isra’ila, ko da yake masu washewa sun washe su suka kuma lalatar da inabinsu. Garkuwoyin sojojinsa ja wur ne; jarumawansa suna sanye da kaya masu ruwan jan garura. Ƙarafan kekunan yaƙi suna walƙiya a ranar da aka shirya su; ana kaɗa māsu da bantsoro. Kekunan yaƙi sun zabura a tituna, suna kai da kawowa a dandali. Suna walƙiya kamar tocila suna sheƙawa a guje kamar walƙiya. Ninebe ta tattara rundunarta, duk da haka sun yi ta tuntuɓe a kan hanyarsu. Sun ruga zuwa katangan birnin, sun sanya garkuwar kāriya a inda ya kamata. An buɗe ƙofofin rafuffukan sai wurin ya rurrushe. An umarta cewa birnin za tă tafi bauta, za a kuma yi gaba da su. Bayi ’yan mata suna kuka kamar tattabaru suna buga ƙirjinsu. Ninebe tana kama da tafki, wanda ruwanta yana yoyo. Suna kuka suna cewa, “Ku tsaya! Ku tsaya,” amma ba wanda ya waiga. A washe azurfa; a washe zinariya; dukiyarsu ba ta da iyaka, arzikinsu kuma ba ya ƙarewa. Ta zama wofi, an washe ta, an tuɓe ta! Zukata sun narke, gwiwoyi suna kaɗuwa, jikuna suna rawa, fuskoki duk sun kwantsare! Ina kogon zakokin nan yake yanzu, inda suka ciyar da ’ya’yansu, inda zaki da zakanya sukan shiga, da ’ya’yansu, ba mai damunsu Zaki ya kashe abin da ya ishe ’ya’yansa ya kuma murɗe wuyan dabbobi ya cika wurin zamansa da abin da ya kama ya cika kogwanninsa da abin da ya kashe. “Ina gāba da ke,” in ji Ubangiji Maɗaukaki. “Zan ƙone kekunan yaƙinki, takobi kuma zai fafare ’ya’yan zakokinki. Ba kuma zan bar miki namun jejin da za ki kashe a duniya ba. Ba kuwa za a ƙara jin muryar ’yan saƙonki ba.” Kaiton birni mai zub da jini, wadda take cike da ƙarairayi, cike da ganima, wadda ba a rasa masu fāɗawa cikin wahala! Ku ji karar bulala da kwaramniyar ƙafafu, da sukuwar dawakai da girgizar kekunan yaƙi! Mahaya dawakai sun kunno kai, takuba suna walƙiya, māsu kuma suna ƙyali; ga ɗumbun da aka kashe ga tsibin matattu, gawawwaki ba iyaka, mutane suna tuntuɓe da gawawwaki, duk saboda yawan sha’awace-sha’awacen karuwa, mai daɗin baki, uwargidan maita, wadda ta ɓad da al’ummai ta wurin karuwancinta ta kuma ɓad da mutane ta wurin maitancinta. “Ina gāba da ke,” in ji Ubangiji Maɗaukaki. “Zan kware fatarinki a idonki. Zan nuna wa al’ummai tsiraicinki, masarautai kuma kunyarki. Zan watsa miki ƙazanta, in yi miki wulaƙanci in kuma mai da ke abin reni. Duk wanda ya gan ki zai gudu daga gare ki yana cewa, ‘Ninebe ta lalace, wa zai yi makoki domin ta?’ Ina zan sami wani wanda zai yi miki ta’aziyya?” Kin fi Tebes ne da take a bakin Nilu, da ruwa yake kewaye da ita? Rafi shi ne kāriyarta, ruwanta kuma katanga. Kush da kuma Masar su ne ƙarfinta marar iyaka; Fut da Libiya suna cikin mataimakanta. Duk da haka an tafi da ita ta kuma tafi bauta. Aka fyaɗa ƙanananta da ƙasa aka yayyanka su gunduwa-gunduwa a kan kowane titi. Aka jefa ƙuri’a a kan manyan mutanenta, aka daure manyan mutanenta da sarƙoƙi. Ke ma za ki bugu, za ki ɓuya. Ki kuma nemi mafaka daga wurin abokin gāba. Dukan kagarunki suna kama da itatuwan ɓaure da ’ya’yansu da suka nuna. Da an girgiza, sai ɓaure su zuba a bakin mai sha. Dubi mayaƙanki, duk mata ne! Ƙofofin ƙasarki a buɗe suke ga abokan gābanki, wuta ta cinye madogaransu. Ki ja ruwa gama za a kewaye ki da yaƙi. Ki ƙara ƙarfin kagaranki! Ki kwaɓa laka, ki sassaƙa turmi ki gyara abin yin tubali! A can wuta za tă cinye ki; takobi zai sare ki, kuma kamar fāra, za a cinye ki. Ki riɓaɓɓanya kamar fāra, ki riɓaɓɓanya kamar fārin ɗango! Kin ƙara yawan masu kasuwancinki har sai da suka fi taurarin sama. Amma kamar fāra sun cinye ƙasar sa’an nan suka tashi, suka tafi. Masu tsaronki suna kama da fāri ɗango, shugabanninki sun yi cincirindo kamar fārin ɗango da suka sauka a kan bango a rana mai sanyi, amma da rana ta fito, duk za su tashi su tafi, ba kuma wanda ya san inda suka nufa. Ya sarkin Assuriya, makiyayanka sun yi barci; manyan mutanenka sun kwanta su huta. An watsar da mutanenka a cikin duwatsu, ba wanda zai tattaro su. Ba abin da zai warkar da rauninka; rauninka ya yi muni. Duk wanda ya ji labarinka zai tafa hannuwansa saboda farin cikin fāɗuwarka, gama wane ne bai ji jiki a hannunka ba? Saƙon da annabi Habakkuk ya karɓa. Har yaushe, ya Ubangiji, zan yi kukan neman taimako, amma ka ƙi ji? Ina kuka a gare ka saboda zalunci amma ba ka ce ufam ba. Me ya sa ka bari ina ta kallon rashin gaskiya? Me ya sa kake barin abin da ba daidai ba? Hallaka da tashin hankali suna a gabana; ga rashin jituwa da faɗa ko’ina. Saboda haka ba a bin doka, shari’a kuma ba ta aiki. Mugaye sun kewaye masu adalci don a hana gaskiya tă yi aiki. “Ka dubi al’ummai, ka gani, ka sha mamaki. Ga shi zan yi wani abu a kwanakinka, wanda ko ma an faɗa maka ba za ka gaskata ba. Zan tā da Babiloniyawa, waɗannan marasa hankali da kuma marasa tausayi; masu gajeren haƙuri, waɗanda suke ratsa ko’ina a duniya don su ƙwace wuraren zaman da ba nasu ba. Suna da bantsoro da firgitarwa; dokoki da ƙa’idodinsu ne kawai suka sani. Dawakansu sun fi damisoshi sauri, sun fi kyarketan yamma zafin rai. Mahayansu suna zuwa a guje; mahayansu daga nesa suka fito. Suna firiya kamar ungulu mai sauka da gaggawa don yă ci mushe; duk sukan zo da nufin tā-da-na-zaune-tsaye. Ana jin tsoronsu tun ma kafin su iso suna tattara bayi kamar yashi. Sukan yi wa sarakuna ba’a su kuma rena masu mulki. Sukan yi wa dukan birane masu mafaka dariya; sukan tara ƙasa su hau, su cinye abokan gābansu da yaƙi. Sa’an nan su wuce da sauri kamar iska, mutane ne masu laifi, waɗanda ƙarfinsu shi ne allahnsu.” Ya Ubangiji, ba tun fil azal kake ba? Ya Allahna, Mai Tsarkina, ba za mu mutu ba. Ya Ubangiji ka sanya su su tabbatar da hukunci; Ya Dutse, ka naɗa su don su yi hukunci. Idanunka masu tsarki ne da suka fi gaban duban mugunta; ba ka amince da abin da ke ba daidai ba. To, don me ka ƙyale munafukai suna cin karensu ba babbaka? Me ya sa kake shiru sa’ad da mugaye suke haɗiye adalai da suka fi su adalci? Ka mai da maza kamar kifin teku, kamar halittun tekun da ba su da shugaba. Mugu abokin gāba yakan kama su duka da ƙugiya, yă jawo su waje da abin kamun kifinsa, yă tattara su cikin ragarsa, ta haka yakan yi murna da farin ciki. Saboda haka yakan yi hadaya wa abin kamun kifinsa yă kuma ƙona turare wa ragarsa, domin ta wurin abin kamun kifinsa ne yake yin rayuwar jin daɗi yă kuma zaɓi irin abincin da yake so. Zai ci gaba da juye abin kamun kifinsu ke nan, suna hallaka al’ummai ba tausayi? Zan tsaya wurin tsarona in kuma zauna a kan katanga; zan jira in ga abin da zai ce mini, da kuma wace amsa zan bayar ga wannan kuka. Sa’an nan Ubangiji ya amsa ya ce, “Ka rubuta wannan ru’uya ka bayyana ta a fili a kan alluna don mai shela yă ruga da ita, yă kai. Gama ru’uyar tana jiran ƙayyadadden lokaci; tana zancen ƙarshe kuma ba za tă zama ƙarya ba. Ko da ka ga kamar tana jinkiri, ka jira ta; lalle za tă zo, ba za tă makara ba. “Duba, abokin gāba ya cika da ɗaga kai; sha’awarsa ba daidai ba ce, amma mai adalci zai rayu ta wurin bangaskiyarsa, ba shakka, ruwan inabi ya yaudare shi; yana fariya kuma ba ya hutu. Domin shi mai haɗama ne kamar kabari kuma kamar mutuwa, ba ya ƙoshi; yakan tattara dukan al’ummai wa kansa yana kuma kama dukan mutane su zama kamammu. “Dukansu ba za su yi masa tsiya, suna yin masa ba’a da dariya ba, suna cewa, “ ‘Kaito ga wannan wanda ya tara wa kansa kayan sata ya kuma wadatar da kansa da kayan ƙwace! Har yaushe wannan abu zai ci gaba?’ Masu binka bashi ba za su taso maka nan da nan ba? Ba za su farka su sa ka fargaba ba? Ta haka ka zama ganima a gare su. Domin ka washe al’ummai masu yawa, mutanen da suka rage za su washe ka. Domin ka zub da jinin mutane; ka hallaka ƙasashe, da birane, da kuma kowa da yake cikinsu. “Kaito ga wanda ya gina masarautarsa da ƙazamar riba don yă kafa sheƙarsa can bisa, don yă tsere wa zama kango! Ka ƙulla lalacin mutane masu yawa, ta haka ka kunyatar da gidanka ka kuma hallaka ranka. Duwatsun katanga za su yi kuka, ginshiƙan katako kuma za su amsa. “Kaiton mutumin da ya gina birni da jinin da ya zubar ya kuma kafa gari ta wurin mugun aiki! Ba Ubangiji Maɗaukaki ne ya ƙudura cewa wahalar mutane ta zama mai kawai don wuta ba, cewa al’ummai su gajiyar da kansu a banza ba? Gama duniya za tă cika da sanin ɗaukakar Ubangiji, yadda ruwaye suka rufe teku. “Kaito wanda ya ba wa maƙwabtansa abin sha, yana ta zubawa daga salkan ruwan inabi har sai sun bugu, don dai yă ga tsiraicinsu. Za ka cika da kunya a maimakon ɗaukaka. Yanzu lokacinka ne! Kai ma ka sha, a kuma tone asirinka! Gama kwaf na hannun daman Ubangiji yana zuwa kewaye da kai, abin kunya kuma zai rufe darajarka. Ɓarnar da ka yi wa Lebanon zai komo kanka, kuma hallakar dabbobin da ka yi zai sa dabbobi su tsorata ka. Gama ka zub da jinin mutum; ka hallaka ƙasashe, da birane, da kuma kowa da yake cikinsu. “Ina amfanin gunki da mutum ne ya sassaƙa? Ko siffar da take koyar da ƙarya? Gama wanda ya yi shi yana dogara ne ga halittarsa; ya yi gumakan da ba sa magana. Kaito wanda ya ce da katako, ‘Rayu!’ Ko kuwa dutse marar rai, ‘Farka!’ Zai iya bishewa ne? An dalaye shi da zinariya da azurfa; ba numfashi a cikinsa.” Amma Ubangiji yana a cikin haikalinsa mai tsarki; bari dukan duniya tă yi shiru a gabansa. Addu’ar annabi Habakkuk. A kan shigiyont. Ya Ubangiji, na ji irin shaharar da ka yi; na yi al’ajabi game da ayyukanka, ya Ubangiji. Ka maimaita su a kwanakinmu, ka sanar da su a lokacinmu; ka yi jinƙai ko a lokacin da kake fushi. Allah ya zo daga Teman, Mai Tsarkin nan daga Dutsen Faran. Ɗaukakarsa ta rufe sammai yabonsa kuma ya cika duniya. Darajarsa ta yi kamar fitowar rana; ƙyalƙyali ya wulga daga hannunsa, inda ikonsa yake a ɓoye. Annoba ta sha gabansa; cuta kuma tana bin bayansa. Ya tsaya, ya kuwa girgiza duniya; ya duba, sai ya sa al’ummai suka yi rawan jiki. Tsofaffin duwatsu sun wargaje daɗaɗɗun tuddai kuma suka rurrushe. Hanyoyinsa dawwammamu ne. Na ga tentin Kushan cikin azaba; wuraren zaman Midiyan cikin damuwa. Ka ji haushin koguna ne, ya Ubangiji? Ko kuwa ka hasala da rafuffuka ne? Ko ka yi fushi da teku ne sa’ad da ka hau dawakanka da kuma kekunan yaƙinka masu nasara? Ka ja bakanka, ka nemi a ba ka kibiyoyi masu yawa. Ka raba duniya da koguna; duwatsu sun gan ka sai suka ƙame. Ruwaye masu hauka sun yi ta fantsamawa; zurfafa suka yi ruri suka tā da raƙuman ruwansu sama. Rana da wata suka tsaya cik a sammai da ganin kibiyoyinka masu wucewa fyu, da ganin hasken māshinka mai walƙiya. Cikin hasala ka ratsa duniya cikin fushi kuma ka tattake ƙasashe. Ka fito don ka fanshi mutanenka, don ceci shafaffenka. Ka ragargaza shugaban ƙasar mugaye, ka tuɓe shi daga kai har ƙafa. Da māshinsa ka soki kansa sa’ad da jarumawansa suka fito don su tarwatse mu, suna farin ciki sai ka ce masu shirin cinye matalautan da suke a ɓoye. Ka tattake teku da dawakanka, kana kaɗa manyan ruwaye. Na ji sai zuciyata ta buga, leɓunana sun yi rawa da jin murya; ƙasusuwana suka ruɓe, ƙafafuna kuma sun yi rawa. Duk da haka zan jira da haƙuri ga ranar bala’i ta zo a kan al’umman nan mai kawo mana hari. Ko da yake itace ɓaure bai tohu ba, ba kuma ’ya’ya a kuringar inabi, ko da yake zaitun bai ba da amfani ba, gonaki kuma ba su ba da abinci ba, ko da yake babu tumaki a garke, ba kuma shanu a turaku, duk da haka zan yi farin ciki da Ubangiji, zan yi murna da Allah Mai Cetona. Ubangiji Mai Iko Duka shi ne ƙarfina; yakan mai da ƙafafuna kamar na barewa, yakan sa in yi tafiya a wurare masu tsayi. Domin mai bi da kaɗe-kaɗe. A kan kayan kiɗi masu tsirkiyata. Maganar Ubangiji da ta zo wa Zefaniya ɗan Kushi, ɗan Gedaliya, ɗan Amariya, ɗan Hezekiya, a zamanin Yosiya ɗan Amon sarkin Yahuda. “Zan hallaka kome a fuskar duniya,” in ji Ubangiji. “Zan hallaka mutane da dabbobi; zan kuma hallaka tsuntsayen sama da kifayen teku, da gumakan da suke sa mugaye su yi tuntuɓe.” “Sa’ad da zan kawar da mutum daga fuskar duniya,” in ji Ubangiji. “Zan miƙa hannuna gāba da Yahuda da kuma dukan mazaunan Urushalima. Zan datse raguwar Ba’al daga wannan wuri, da sunayen firistocin gumaka da na marasa sanin Allah, waɗanda suka rusuna a kan rufin ɗaki don su yi sujada ga rundunar taurari. Waɗanda suka rusuna suka kuma yi rantsuwa da sunan Ubangiji suke kuma rantsuwa da sunan Molek. Waɗanda suka juya daga bin Ubangiji, ba sa kuma neman Ubangiji ko su nemi nufinsa.” Ku yi shiru a gaban Ubangiji Mai Iko Duka, gama ranar Ubangiji ta yi kusa. Ubangiji ya shirya hadaya; ya kuma tsarkake waɗanda ya gayyato. “A ranar hadayar Ubangiji zan hukunta sarakuna da kuma ’ya’yan sarakuna da duk waɗanda suke sanye da rigunan ƙasashen waje. A wannan rana zan hukunta dukan waɗanda suke kauce taka madogarar ƙofa, waɗanda suke cika haikalin allolinsu da rikici da ruɗu. “A wannan rana,” in ji Ubangiji, “Za a ji kuka daga Ƙofar Kifi, kururuwa daga Sabon Mazauni, da kuma amo mai ƙarfi daga tuddai. Ku yi kururuwa, ku da kuke zaune a yankin kasuwa; za a hallaka dukan ’yan kasuwanku, dukan waɗanda suke kasuwanci da azurfa za su lalace. A wannan lokaci zan bincike Urushalima da fitilu in kuma hukunta waɗanda ba su kula ba, waɗanda suke kamar ruwan inabin da aka bar a ƙasan tukunya, waɗanda suke tsammani, ‘ Ubangiji ba zai yi kome ba nagari ko mummuna.’ Za a washe dukiyarsu, a rurrushe gidajensu. Za su gina gidaje amma ba za su zauna a ciki ba; za su shuka inabi amma ba za su sha ruwansa ba.” Babbar ranar Ubangiji ta yi kusa, ta yi kusa kuma tana zuwa da sauri. Ku saurara! Kukan ranar Ubangiji za tă yi zafi, za a ji kururuwan jarumi a can. Ranan nan za tă zama ranar fushi, rana ce ta baƙin ciki da azaba, rana ce ta tashin hankali da lalacewa, ranar duhu baƙi ƙirin, ranar gizagizai da baƙin duhu, rana ce ta busa ƙaho da kururuwar yaƙi gāba da birane masu mafaka, da kuma kusurwar hasumiyoyi. “Zan kawo baƙin ciki a kan mutane za su kuma yi tafiya kamar makafi, domin sun yi wa Ubangiji zunubi. Za a zubar da jininsu kamar ƙura kayan cikinsu kuma kamar najasa. Azurfarsu ko zinariyarsu ba za su iya cetonsu ba a ranar fushin Ubangiji.” A cikin zafin kishinsa za a hallaka dukan duniya gama zai kawo ƙarshen dukan mazaunan duniya nan da nan. Ku tattaru, ku tattaru, Ya ku al’umma marar kunya, kafin ƙayyadadden lokacin nan yă zo ranan nan kuma ta share ku kamar ƙaiƙayi kuma kafin fushi mai tsanani na Ubangiji yă auko muku, kafin ranar fushin Ubangiji ta auko muku. Ku nemi Ubangiji, dukanku ƙasashe masu tawali’u, ku da kuke yin abin da ya umarta. Ku nemi adalci da tawali’u; mai yiwuwa ku sami mafaka a ranar fushin Ubangiji. Za a yashe Gaza a kuma bar Ashkelon kango. Da tsakar rana Ashdod za tă zama babu kowa a kuma tumɓuke Ekron. Taku ta ƙare ku da kuke zama a bakin teku, Ya ku mutanen Keretawa; maganar Ubangiji tana gāba da ke, Ya ke Kan’ana, ƙasar Filistiyawa. “Zan hallaka ki kuma babu abin da zai rage.” Ƙasar da take a bakin teku, inda Keretawa suke zaune, za tă zama wurin da makiyaya da ta garken tumaki. Za tă zama mallakar raguwar gidan Yahuda; a can za su sami wurin kiwo. Da yamma za su kwanta a gidajen Ashkelon. Ubangiji Allahnsu zai lura da su; zai maido musu da martabarsu. “Na ji irin zagin da Mowab take yi, da kuma ba’ar Ammonawa, waɗanda suka zagi mutanena suna kuma yi barazana a kan ƙasarsu. Saboda haka, muddin ina raye,” in ji Ubangiji Maɗaukaki, Allah na Isra’ila, “tabbatacce Mowab za tă zama kamar Sodom, Ammonawa kuma kamar Gomorra, ƙasa mai ciyayi da rammukan gishiri, ƙasa marar amfani har abada. Raguwar mutanena za su washe su; waɗanda suka rage na al’ummata za su gāda ƙasarsu.” Wannan ne zai zama sakamakon girmankansu, saboda zagi da kuma ba’ar da suka yi wa mutanen Ubangiji Maɗaukaki. Ubangiji zai zama abin tsoro a gare su sa’ad da ya hallaka allolin ƙasar. Al’ummai a kowane bakin teku za su yi masa sujada, kowa a ƙasarsa. “Ku ma, ya Kushawa, za a kashe ku da takobina.” Zai kuma miƙa hannunsa gāba da arewa yă kuma hallaka Assuriya, zai mai da Ninebe kango gaba ɗaya ta kuma zama busasshiya kamar hamada. Garkuna za su kwanta a can, da kowace irin halitta, Mujiyar hamada da bushiya za su zauna a kan ginshiƙanta. Kukansu za tă ratsa tagogi, ɓuraguzai za su tare ƙofofin shiga, za a kware ginshiƙan al’ul. Birnin da yake harka ke nan da take zaune lafiya. Ta ce wa kanta, “Ni ce, kuma babu kamata.” Dubi irin kangon da ta zama mana, mazaunin namun jeji! Duk wanda ya wuce ta sai ya yi mata tsaki yana kaɗa kai. Taki ta ƙare, ke birnin mai danniya, mai ’yan tawaye da kuma masu ƙazanta! Ba kya yi wa kowa biyayya, ba kya kuma yarda da kuskurenki. Ba kya dogara ga Ubangiji, ba kya kuma kusatowa kusa da Allahnki. Sarakunanki ruri ne na zakoki, shugabanninki kyarketan dare ne, waɗanda ba sa rage kome don safe. Annabawanki mahaukata ne mutanenki masu cin amana ne. Firistocinki suna ƙazantar da Wurin Mai Tsarki suna kuma keta dokoki. Ubangiji da yake cikinki mai adalci ne; ba ya yin abin da ba daidai ba. Kowace safiya yakan bayyana dokokinsa a fili, kowace sabuwar rana kuma ba ya kāsawa, duk da haka marasa adalci ba sa jin kunya. “Na daddatse al’ummai; an kuma rurrushe kagararsu. Na bar titunansu ba kowa, ba mai ratsawa a ciki. An ragargaza biranensu; ba wanda za a bari, babu ko ɗaya. Na ce wa birnin, ‘Tabbatacce za ki ji tsorona ki kuma yarda da gyara!’ Ta haka ba za a datse wurin zamanki ba, ba kuwa dukan hukuncena za su hau bisa kansu ba. Amma har yanzu suna marmari su yi rashin gaskiya a duk abin da suke yi. Saboda haka ku jira ni,” in ji Ubangiji; “a ranar da zan tsaya in ba da shaida, Na yanke shawara in tattara dukan al’ummai, in tattara mulkoki in kuma zuba fushina a kansu, da dukan zafin haushina. Za a mamaye dukan duniya da zafin fushina. “Sa’an nan zan tsarkake leɓunan mutanen, don dukansu su kira bisa ga sunan Ubangiji su kuma yi masa hidima kafaɗa da kafaɗa. Tun daga ƙetaren rafuffukan Kush masu yi mini sujada, mutanena da suke a warwatse, za su kawo mini hadayu. A wannan rana ba za ku sha kunya saboda laifofin da kuka yi mini, gama zan ɗauke wa wannan birni waɗanda suke farin ciki cikin girmankansu. Ba kuma za ka ƙara yin kallon reni a tuduna mai tsarki ba. Amma zan zauna a cikinki masu tawali’u da masu ƙasƙantar da kai, waɗanda suke dogara ga sunan Ubangiji. Raguwar Isra’ila ba za su ƙara aikata abin da ba daidai ba, ba za su faɗa ƙarya ba, ba kuwa za a sami ruɗu a bakunansu ba. Za su ci su kuma kwanta kuma babu wanda zai ba su tsoro.” Ki rera, ya Diyar Sihiyona; ki tā da murya, ya Isra’ila! Ki yi murna ki kuma yi farin ciki da dukan zuciyarki, Ya Diyar Urushalima! Ubangiji ya ɗauke hukuncinki, ya mai da abokan gābanki baya. Ubangiji, Sarkin Isra’ila, yana tare da ke; ba kuma za ki ƙara jin tsoron wani lahani ba. A wannan rana za su cewa Urushalima, “Kada ki ji tsoro, ya Sihiyona; kada ki bar hannuwanki su raunana. Ubangiji Allahnki yana tare da ke, mai iko ne don ceto. Zai yi matuƙar farin ciki da ke, zai rufe ki da ƙaunarsa, zai yi farin ciki da ke ta wurin rerawa.” “Zan cire taƙaici daga gare ki a ƙayyadaddun bukukkuwa; su kaya ne da kuma zargi a gare ki. A wannan lokaci zan jijji wa waɗanda suka danne ku; zan kuɓutar da guragu in kuma tattara waɗanda suke a warwatse. Zan sa a yabe su a kuma girmama su a kowace ƙasar da aka kunyatar da su. A wannan lokaci zan tattara ku; a wannan lokaci zan kawo ku gida, zan sa a yabe ku a kuma girmama ku a cikin dukan mutanen duniya a sa’ad da na maido da arzikinku a idanunku,” in ji Ubangiji. A shekara ta biyu ta mulkin Sarki Dariyus, a rana ta fari ga watan shida, maganar Ubangiji ta zo ta wurin annabi Haggai zuwa ga Zerubbabel ɗan Sheyaltiyel, gwamnan Yahuda, da kuma Yoshuwa ɗan Yehozadak, babban firist. Ga abin da Ubangiji Maɗaukaki ya ce, “Waɗannan mutane sun ce, ‘Lokaci bai yi ba tukuna da za a gina gidan Ubangiji.’ ” Sa’an nan maganar Ubangiji ta zo ta wurin annabi Haggai cewa, “Ashe, lokaci ya yi da za ku zauna a ɗakunan da kuka yi da rufin katako, amma haikalin nan yana zaman kufai?” To, ga abin da Ubangiji Maɗaukaki ya ce, “Ku lura da al’amuranku. Kun shuka da yawa, amma kun girbe kaɗan. Kun ci, amma ba ku ƙoshi ba. Kun sha, amma ba ku kashe ƙishirwa ba. Kun sa tufafi, amma ba ku ji ɗumi ba. Kuna karɓar albashi, ya zama sai ka ce kuna zuba a hudajjen aljihu.” Ga abin da Ubangiji Maɗaukaki ya ce, “Ku lura da al’amuranku. Ku haura zuwa kan duwatsu ku sauko da katakai don ku gina gidan, don ni ma in ji daɗinsa, in kuma sami ɗaukaka,” in ji Ubangiji. “Ga shi, kukan sa rai za ku sami da yawa, amma sai ku ga kun sami kaɗan. Ɗan kaɗan ɗin ma da kukan kawo gida, nakan hura shi yă tafi. Me ya sa yake faruwa haka?” In ji Ubangiji Maɗaukaki. “Saboda gidana da yake zaman kango, yayinda kowannenku yana faman gina gidansa. Shi ya sa, saboda ku sammai sun ƙi saukar da raɓa, ƙasa kuma ta ƙi ba da amfani. Na kawo fări a ƙasar, da a kan duwatsu, da a kan hatsi, da a kan dukan abin da yake tsirowa daga ƙasa, da a kan mutane, da a kan dabbobi da kuma a kan wahalar hannuwanku.” Sa’an nan sai Zerubbabel ɗan Sheyaltiyel, da Yoshuwa ɗan Yehozadak, wanda yake babban firist, da kuma dukan raguwar jama’ar suka yi biyayya da muryar Ubangiji Allahnsu da kuma saƙon annabi Haggai, domin Ubangiji Allahnsu ne ya aiko shi. Mutane kuwa suka ji tsoron Ubangiji. Sai Haggai, ɗan saƙon Ubangiji, ya ba da wannan saƙo na Ubangiji ga mutane cewa, “Ina tare da ku” in ji Ubangiji. Saboda haka Ubangiji ya motsa zuciyar Zerubbabel ɗan Sheyaltiyel, wanda yake gwamna a Yahuda, da kuma zuciyar Yoshuwa ɗan Yehozadak, babban firist, da kuma zukatan dukan raguwar jama’ar. Suka zo suka fara aiki a gidan Ubangiji Maɗaukaki, Allahnsu, a ranar ashirin da huɗu ga watan shida. A shekara ta biyu ta mulkin Sarki Dariyus, a ranar ashirin da ɗaya ga watan bakwai, maganar Ubangiji ta zo ta wurin annabi Haggai cewa, “Ka yi magana da Zerubbabel ɗan Sheyaltiyel wanda yake gwamna a Yahuda, da Yoshuwa ɗan Yehozadak, babban firist, da kuma dukan raguwar mutane. Ka tambaye su ka ce, ‘Wane ne a cikinku ya ragu da ya ga wannan gida a darajarsa ta dā? Yaya yake a gare ku a yanzu? Bai yi kamar a bakin kome ba, ko ba haka ba? Amma yanzu ka ƙarfafa, ya Zerubbabel,’ in ji Ubangiji. ‘Ka ƙarfafa, ya Yoshuwa ɗan Yehozadak, babban firist. Ku ƙarfafa, dukanku mutanen ƙasar,’ in ji Ubangiji, ‘ku yi aiki. Gama ina tare da ku,’ in ji Ubangiji Maɗaukaki. ‘Wannan shi ne alkawarin da na yi da ku a lokacin da kuka fito daga Masar. Ruhuna kuwa yana tare da ku. Kada ku ji tsoro.’ “Ga abin da Ubangiji Maɗaukaki ya ce, ‘Ba da jimawa ba zan sāke girgiza sammai da kuma ƙasa, teku da busasshiyar ƙasa. Zan girgiza dukan al’ummai, marmarin kowace al’umma kuma zai taso, sa’an nan zan cika gidan nan da ɗaukaka,’ in ji Ubangiji Maɗaukaki. ‘Da zinariya da azurfa duka nawa ne,’ in ji Ubangiji Maɗaukaki. ‘Ɗaukakar gidan nan na yanzu za tă fi ɗaukakar gidan nan na dā,’ in ji Ubangiji Maɗaukaki. ‘A wannan wuri kuma zan ba da salama,’ in ji Ubangiji Maɗaukaki.” A ranar ashirin da huɗu ga watan tara, a shekara ta biyu ta mulkin Dariyus, maganar Ubangiji ta zo wa annabi Haggai cewa, “Ga abin da Ubangiji Maɗaukaki ya ce, ‘Ku tambayi firist abin da doka ta ce. Idan mutum yana riƙe da naman da aka keɓe a rigarsa, sa’an nan kuma wannan rigar ta taɓa burodi, ko dafaffen abinci, ko ruwan inabi, ko mai, ko kowane irin abinci, wannan zai sa abin yă zama tsarkake?’ ” Firistoci suka amsa, suka ce, “A’a.” Sa’an nan Haggai ya ce, “In mutumin da ya ƙazantar da kansa ta wurin taɓa gawa, ya taɓa wani daga cikin waɗannan abubuwa, za su ƙazantu?” Firistoci suka amsa, suka ce, “I, zai ƙazantu.” Sai annabi Haggai ya ce, “ ‘Haka yake da wannan mutane da kuma wannan al’umma a gabana,’ in ji Ubangiji. ‘Duk abin da suke yi da kuma dukan abin da suke miƙawa ƙazantattu ne. “ ‘Yanzu kuwa sai ku yi la’akari da wannan daga wannan rana zuwa gaba, ku tuna yadda al’amura suke kafin a ɗora wani dutse bisa wani a haikalin Ubangiji. A lokacin, idan wani ya tafi wurin tsibin da zai auna mudu ashirin, sai yă iske mudu goma kawai. Idan kuma wani ya tafi wurin matse ruwan inabi don yă ɗebo lita hamsin, sai yă tarar da lita ashirin kawai. Na mai da aikin da kuka sha wahala kuka yi ya zama banza ta wurin saukar da burtuntuna, da fumfuna, da ƙanƙara, duk da haka ba ku juyo gare ni ba,’ in ji Ubangiji. ‘Daga wannan rana zuwa gaba, wato, rana ta ashirin da huɗu ga watan tara, ku lura da ranar da aka kafa harsashin haikalin Ubangiji. Ku lura da kyau. Akwai sauran irin da ya rage a rumbu? Har yanzu, kuringar inabi da itacen ɓaure, rumman da itacen zaitun ba su ba da ’ya’ya ba tukuna. “ ‘Amma daga wannan rana zuwa gaba zan sa muku albarka.’ ” Maganar Ubangiji ta zo wa annabi Haggai sau na biyu a rana ta ashirin da huɗu ga wata cewa, “Ka faɗa wa Zerubbabel gwamnan Yahuda cewa zan girgiza sammai da ƙasa. Zan hamɓarar da gadajen mulki in kuma ragargaza ƙarfin ƙasashen al’ummai. Zan tumɓuke kekunan yaƙi da mahayansu; dawakai da mahayansu za su mutu, kowane ta wurin takobin ɗan’uwansu. “ ‘A wannan rana,’ in ji Ubangiji Maɗaukaki, ‘Zan ɗauke ka, bawana Zerubbabel ɗan Sheyaltiyel,’ in ji Ubangiji, ‘in kuma maishe ka kamar zoben hatimi, gama na zaɓe ka,’ in ji Ubangiji Maɗaukaki.” A wata na bakwai na shekara ta biyu ta mulkin Dariyus, maganar Ubangiji ta zo wa annabi Zakariya ɗan Berekiya ɗan Iddo. “ Ubangiji ya yi fushi sosai da kakanninku. Saboda haka ka gaya wa mutanen, ga abin da Ubangiji Maɗaukaki ya ce, ‘Ku komo gare ni,’ in ji Ubangiji Maɗaukaki, ‘ni kuma zan komo gare ku,’ in ji Ubangiji Maɗaukaki. Kada ku zama kamar kakanninku, waɗanda annabawa na dā suka ce musu, ga abin da Ubangiji Maɗaukaki ya ce, ‘Ku juya daga mugayen hanyoyinku da mugayen abubuwan da kuke yi.’ Amma ba su saurara ba, ko ma su kula da ni, in ji Ubangiji. Yanzu ina kakanninku suke? Annabawan kuma fa, sun rayu har abada ne? Amma maganata da dokokina da na umarta ta wurin bayina annabawa fa, ashe, ba su tabbata ba a kan kakanninku? “Sa’an nan suka tuba suka ce, ‘ Ubangiji Maɗaukaki ya yi mana daidai abin da hanyoyinmu suka cancanci mu samu, kamar dai yadda ya yi niyya yi.’ ” 7-8 A rana ta ashirin da huɗu ga watan goma sha ɗaya, wato, watan Shebat, a shekara ta biyu ta Dariyus, maganar Ubangiji ta zo wa annabi Zakariya ɗan Berekiya ɗan Iddo. Da dare, na ga wahayi, a gabana kuwa ga mutum a kan jan doki! Yana tsaye a cikin itatuwa masu furanni, a bayansa a cikin itatuwan ci-zaƙi, a bayansa kuwa akwai dawakai masu ruwan ja, ruwan ƙasa-ƙasa da kuma ruwan fari. Sai na yi tambaya na ce, “Mene ne waɗannan ranka yă daɗe?” Mala’ikan da yake magana da ni ya amsa ya ce, “Zan nuna maka mene ne su.” Sai mutumin da yake tsaye cikin itatuwan ci-zaƙin ya yi bayani cewa, “Su ne waɗanda Ubangiji ya aika ko’ina a duniya.” Sai suka ce wa mala’ikan da yake tsaye cikin itatuwan ci-zaƙin, “Mun ratsa ko’ina a duniya, sai muka ga duniya duka tana zaman lafiya.” Sa’an nan mala’ikan Ubangiji ya ce, “Ya Ubangiji Maɗaukaki, har yaushe za ka ci gaba da ƙi nuna wa Urushalima da kuma garuruwan Yahuda jinƙai, waɗanda kake fushi da su shekarun nan saba’in?” Sai Ubangiji ya yi wa mala’ikan da ya yi magana da ni magana da kalmomi masu daɗi da kuma masu ta’azantarwa. Sai mala’ikan da yake magana da ni ya ce, “Ka yi shelar maganan nan, ga abin da Ubangiji Maɗaukaki ya ce, ‘Ina kishi domin Urushalima da Sihiyona, amma ina fushi da ƙasashen da suke ji suna zaman lafiya, na ɗan yi fushina kawai, amma sai suka ƙara musu masifar.’ “Saboda haka, ga abin da Ubangiji ya ce, ‘Zan komo Urushalima da jinƙai, a can ne za a sāke gina gidana. Za a kuma miƙe ma’auni a bisa Urushalima,’ in ji Ubangiji Maɗaukaki. “Ci gaba da yin shela, ga abin da Ubangiji Maɗaukaki ya ce, ‘Garuruwana za su sāke kwarara da wadata, Ubangiji kuma zai sāke yi wa Sihiyona ta’aziyya, yă kuma zaɓi Urushalima.’ ” Sa’an nan na dubi sama a gabana kuwa sai ga ƙahoni huɗu! Na tambayi mala’ikan da yake mini magana, na ce, “Mene ne waɗannan?” Ya amsa mini ya ce, “Waɗannan su ne ƙahonin da suka watsar da Yahuda, Isra’ila da kuma Urushalima.” Sa’an nan Ubangiji ya nuna mini maƙera guda huɗu. Na yi tambaya na ce, “Mene ne waɗannan suke zuwa yi?” Ya amsa ya ce, “Waɗannan ne ƙahonin da suka watsar da Yahuda har ba wanda yake iya ɗaga kansa, amma maƙeran sun zo don su tsorata su su kuma saukar da ƙahonin ƙasashen nan waɗanda suka ɗaga ƙahoninsu gāba da ƙasar Yahuda don su warwatsa ta.” Sa’an nan na ɗaga kai sai na ga mutum a tsaye riƙe da ma’auni a hannunsa! Sai na yi tambaya, na ce, “Ina za ka?” Ya amsa mini ya ce, “Zan je in auna Urushalima, in ga yadda fāɗinta da tsawonta suke.” Sai mala’ikan da yake yi mini magana ya tafi, sai wani mala’ika ya zo ya same shi ya ce masa, “Yi gudu, gaya wa saurayin can cewa, ‘Urushalima za tă zama birni marar katanga domin mutane da dabbobi masu yawa ƙwarai za su kasance a cikinta. Ni da kaina ne zan zama katangar wuta kewaye da birnin, in kuma zama darajarta,’ in ji Ubangiji. “Zo! Zo! Ku gudu daga ƙasar arewa,” in ji Ubangiji, “gama na warwatsa ku a kusurwoyi huɗu na sama,” in ji Ubangiji. “Zo, ya ke Sihiyona! Ku tsere, ku masu zama a cikin Diyar Babilon!” Gama ga abin da Ubangiji Maɗaukaki ya ce, “Bayan ya ɗaukaka ni, ya kuma aiko ni ga ƙasashen da suka washe ku gama duk wanda ya taɓa ku ya taɓa ƙwayar idonsa ne. Ba shakka zan tā da hannuna a kansu domin bayinsu su washe su. Sa’an nan za ku san cewa Ubangiji Maɗaukaki ne ya aiko ni. “Ki yi sowa ki yi murna, ya ke Diyar Sihiyona. Gama ina zuwa, zan zauna a cikinki,” in ji Ubangiji. “Ƙasashe da yawa za su haɗa kai da Ubangiji a ranan nan, za su kuma zama mutanena. Zan zauna a cikinku, za ku kuma san cewa Ubangiji Maɗaukaki ne ya aiko ni gare ku. Ubangiji zai gāji Yahuda a matsayin rabonsa a cikin ƙasa mai tsarki zai kuma sāke zaɓi Urushalima. Ku yi tsit a gaban Ubangiji, dukanku ’yan adam, gama ya taso daga wurin zamansa mai tsarki.” Sa’an nan ya nuna mini Yoshuwa babban firist a tsaye a gaban mala’ikan Ubangiji, Shaiɗan kuma yana tsaye a damansa don yă tuhume shi. Ubangiji ya ce wa Shaiɗan, “ Ubangiji ya tsawata maka, Shaiɗan! Ubangiji wanda ya zaɓi Urushalima, ya tsawata maka! Ashe, mutumin nan ba shi ne sandar da take ƙonewa da aka ciro daga cikin wuta ba?” Yanzu an sa wa Yoshuwa tufafi masu dauda sa’ad da yake tsaye a gaban mala’ikan. Mala’ikan ya ce wa waɗanda suke tsaye a gabansa, “Ku cire masa tufafinsa masu dauda.” Sai ya ce wa Yoshuwa, “Duba, na ɗauke zunubanka, zan sa maka tufafi masu tsada.” Sai na ce, “Sa masa rawani mai tsabta a kansa.” Aka sa masa rawani mai tsabta a kansa aka kuma sa masa tufafi yayinda mala’ikan Ubangiji yake tsaye a wurin. Mala’ikan Ubangiji ya yi wa Yoshuwa wannan gargaɗi. “Ga abin da Ubangiji Maɗaukaki ya ce, ‘In za ka yi tafiya a hanyoyina ka kuma kiyaye abubuwan da nake so, za ka zama shugaban haikalina, ka kuma lura da ɗakunan shari’ata, zan kuma ba ka wuri cikin waɗannan da suke tsaye a nan. “ ‘Ka saurara, ya babban firist Yoshuwa, kai da abokanka da suke zaune a gabanka, ku da kuke alamun abubuwan da za su zo. Zan kawo bawana, wanda yake Reshe. Dubi dutsen da na ajiye a gaban Yoshuwa! Akwai idanu bakwai a kan wannan dutse guda, zan kuma yi rubutu a kansa,’ in ji Ubangiji Maɗaukaki, ‘zan kuma kawar da zunubin ƙasan nan a rana ɗaya. “ ‘A wannan rana kowannenku zai gayyaci maƙwabcinsa yă zauna a ƙarƙashin itacen inabi da kuma na ɓaure,’ in ji Ubangiji Maɗaukaki.” Sai mala’ikan da ya yi magana da ni ya komo ya farkar da ni, kamar yadda ake farkar da mutum daga barcinsa. Ya tambaye ni ya ce, “Me ka gani?” Na amsa, na ce, “Na ga wurin ajiye fitilan zinariya da kwano a kai, da kuma fitilu bakwai a kansa, da butocin kai wa fitilu mai guda bakwai. Akwai kuma itatuwan zaitun guda biyu a gefensa, ɗaya a gefen dama na kwanon ɗaya kuma a gefen hagunsa.” Na tambayi mala’ikan da ya yi magana da ni na ce, “Mene ne waɗannan, ranka yă daɗe?” Sai ya amsa ya ce, “Ba ka san mene ne waɗannan ba?” Na amsa, na ce, “A’a, ranka yă daɗe.” Sai ya ce mini, “Wannan ce maganar Ubangiji ga Zerubbabel. ‘Ba ta wurin ƙarfi ba, ko ta wurin iko, sai dai ta wurin Ruhuna,’ in ji Ubangiji Maɗaukaki. “Kai mene ne, ya babban dutse? A gaban Zerubbabel za a rushe ka ka zama fili. Sa’an nan Zerubbabel yă kawo dutsen da ya fi kyau, a kuma yi ta sowa ana cewa, ‘Allah yă yi masa albarka! Allah yă yi masa albarka!’ ” Sai maganar Ubangiji ta zo mini, “Hannuwan Zerubbabel sun kafa harsashin haikalin nan; hannuwansa ne kuma za su gama ginin. Sa’an nan ne za ka san cewa Ubangiji Maɗaukaki ne ya aiko ni zuwa wurinka. “Wa ya rena ranar ƙananan abubuwa? Mutane za su yi murna sa’ad da suka ga igiyar gwaji a hannun Zerubbabel. “Waɗannan guda bakwai ɗin su ne idanun Ubangiji, masu jujjuyawa cikin dukan duniya.” Sai na tambaye shi na ce, “Mene ne waɗannan itatuwan zaitun guda biyu tsaye a hagu da kuma daman wurin ajiye fitilan fitilu?” Na sāke tambaye shi na ce, “Mene ne waɗannan rassa biyun nan na zaitun a gefen bututu biyu na zinariya da suke zuba man zinariya?” Ya amsa ya ce, “Ba ka san mene ne waɗannan ba?” Na ce, “A’a, ranka yă daɗe.” Sai ya ce, “Waɗannan su ne biyun da aka shafe don su yi wa Ubangiji dukan duniya hidima.” Na sāke dubawa sai ga naɗaɗɗen littafi mai firiya a gabana! Sai ya tambaye ni ya ce, “Me ka gani?” Sai na amsa na ce, “Na ga naɗaɗɗen littafi mai firiya, tsawonsa ƙafa talatin da fāɗinsa kuma ƙafa goma sha biyar.” Sai ya ce mini, “Wannan ce la’anar da za tă ratsa dukan ƙasar; gama bisa ga abin da ya ce a gefe ɗaya, za a kawar da kowane ɓarawo, kuma bisa ga abin da ya ce a ɗaya gefen za a kawar da duk mai rantsuwar ƙarya. Ubangiji Maɗaukaki ya ce, ‘Zan aika shi, zai shiga gidan ɓarawo, da gidan mai rantsuwar ƙarya da sunana. Zai kasance a gidansa yă hallaka gidan da katakon da duwatsun.’ ” Sai mala’ikan da yake mini magana ya zo gaba ya ce mini, “Duba ka gani ko mene ne wannan da yake fitowa.” Na tambaya na ce, “Mene ne?” Ya amsa ya ce, “Kwando ne na awo.” Ya ƙara da cewa, “Wannan shi ne laifin mutanen a duk fāɗin ƙasar.” Sa’an nan aka ɗaga murfin dalman, a ciki kuwa ga mace zaune! Ya ce, “Wannan mugunta ce,” ya kuma tura ta cikin kwandon ya rufe da murfin dalman, ya kuma danna da dutse. Na ɗaga idona sama, sai ga mata biyu a gabana, iska tana hura fikafikansu! Suna da fikafikai kamar na shamuwa, suka kuma ɗaga kwandon sama. Na tambayi mala’ikan da yake magana da ni na ce, “Ina za ku kai kwandon?” Ya amsa ya ce, “Zuwa ƙasar Babiloniya don a gina masa haikali. Sa’ad da aka gama ginin, za a ajiye shi a ciki.” Na sāke ɗaga kai sama, sai ga kekunan yaƙi guda huɗu a gabana suna fitowa tsakanin duwatsu guda biyu, duwatsun tagulla! Karusa ta farko tana da jajjayen dawakai, ta biyu kuma baƙaƙen dawakai, ta ukun farare dawakai, ta huɗu kuma dawakai masu ɗigo-ɗigo a dukan jikinsu, dukansu kuwa ƙarfafa. Sai na tambayi mala’ikan da yake magana da ni na ce, “Mene ne waɗannan, ranka yă daɗe?” Mala’ikan ya amsa mini ya ce, “Waɗannan su ne ruhohi huɗu na sama, waɗanda suka fito daga wurin Ubangiji na dukan duniya. Wannan mai baƙaƙen dawakai zai nufi wajen ƙasar arewa, mai fararen dawakai zai nufi wajen yamma, sai kuma mai dawakai masu ɗigo-ɗigo a jiki zai nufi wajen kudu.” Da ƙarfafa dawakan suka fito, sai suka yi marmari su ratsa dukan duniya. Sai ya ce, “Ku ratsa dukan duniya!” Saboda haka suka ratsa dukan duniya. Sai ya kira ni ya ce, “Duba, waɗanda suka nufi wajen ƙasar arewa sun ba wa Ruhuna hutu a ƙasar arewa.” Maganar Ubangiji ta zo mini, ta ce, “Ka karɓi azurfa da zinariya daga masu zaman bauta Heldai, Tobiya, Yedahiya, waɗanda suka iso daga Babilon. A ranar kuma ka je gidan Yosiya ɗan Zefaniya. Ka ɗauki azurfar da zinariyar ka yi rawani, ka ɗora shi a kan babban firist, Yoshuwa ɗan Yehozadak. Ka ce masa ga abin da Ubangiji Maɗaukaki ya ce, ‘Ga mutumin da sunansa ne Reshe, zai kuma ratse daga inda yake yă gina haikalin Ubangiji. Shi ne zai gina haikalin Ubangiji, za a kuma martaba shi da daraja, zai kuma zauna yă yi mulki a kan kursiyinsa. Zai zama firist a kan kursiyinsa. Kuma a tsakanin biyun za a sami zaman lafiya.’ Za a ba Heldai, Tobiya, Yedahiya da kuma Hen ɗan Zefaniya kamar abin tunawa a cikin haikalin Ubangiji. Waɗanda suke nesa za su zo su taimaka gina haikalin Ubangiji, za ku kuma san cewa Ubangiji Maɗaukaki ne ya aiko ni gare ku. Wannan zai faru in kuka yi biyayya sosai ga Ubangiji Allahnku.” A shekara ta huɗu ta Sarki Dariyus, maganar Ubangiji ta zo wa Zakariya a rana ta huɗu ta watan tara, wato, watan Kisleb. Mutanen Betel sun aika Sharezer da Regem-Melek, tare da mutanensu su nemi tagomashin Ubangiji ta wurin tambayar firistocin da kuma annabawan gidan Ubangiji Maɗaukaki, “Ko ya kamata in yi makoki da azumi a wata na biyar, yadda na yi a shekaru masu yawa?” Sai maganar Ubangiji Maɗaukaki ta zo mini ta ce, “Ka tambayi dukan mutanen ƙasar da firistoci cewa, ‘Sa’ad da kuka yi makoki da azumi a wata na biyar da na bakwai dukan shekaru saba’in nan, a ainihi saboda ni kuka yi azumi? Kuma sa’ad da kuke ci kuke sha, ba kanku kuke yi wa shagali ba? Ashe, ba kalmomin da Ubangiji ya faɗi ke nan ta bakin annabawan farko ba sa’ad da Urushalima da garuruwan da suke kewaye da ita suke hutawa, suke cikin wadata, akwai kuma mutane a Negeb da yammancin gindin tuddai?’ ” Sai maganar Ubangiji ta sāke zuwa wa Zakariya cewa, “Ga abin da Ubangiji Maɗaukaki ya ce, ‘Ku yi shari’ar gaskiya; ku nuna jinƙai da tausayi ga juna. Kada ku danne gwauruwa ko maraya, baƙo ko talaka. A cikin zuciyarku kada ku yi mugun tunani game da juna.’ “Amma suka ƙi su saurara; da taurinkai suka juya bayansu suka kuma toshe kunnuwansu. Suka taurare zukatansu kamar dutse, suka ƙi jin abin da doka ko kuma maganar Ubangiji Maɗaukaki take faɗi wadda ya aika ta wurin Ruhunsa ta wurin annabawan farko. Saboda haka Ubangiji Maɗaukaki ya ji fushi ƙwarai. “ ‘Sa’ad da na yi kira, ba su saurara ba; saboda haka sa’ad da suka kira, ba zan saurara ba,’ in ji Ubangiji Maɗaukaki. ‘Na warwatsar da su da guguwa a cikin dukan ƙasashe, inda suka zama baƙi. Aka bar ƙasar ta zama kango bayansu, da har ba mai shiga ko fita. Haka suka sa ƙasan nan mai daɗi ta zama kango.’ ” Maganar Ubangiji Maɗaukaki ta sāke zuwa gare ni. Ga abin da Ubangiji Maɗaukaki ya ce, “Ina kishin Sihiyona ƙwarai; ina kuma cike da kishi dominta.” Ga abin da Ubangiji ya ce, “Zan koma Sihiyona in zauna a Urushalima. Sa’an nan za a kira Urushalima Birnin Gaskiya, a kuma kira dutsen Ubangiji Maɗaukaki Dutse Mai Tsarki.” Ga abin da Ubangiji Maɗaukaki ya ce, “Tsofaffi maza da mata za su sāke zauna a titunan Urushalima, kowanne da sanda a hannu saboda tsufa. Titunan birnin za su cika da samari da ’yan mata suna wasa.” Ga abin da Ubangiji Maɗaukaki ya ce, “Mai yiwuwa ya zama da mamaki ga raguwar wannan mutanen da suke nan a lokacin, amma zai zama abin mamaki gare ni ne?” In ji Ubangiji Maɗaukaki. Ga abin da Ubangiji Maɗaukaki ya ce, “Zan ceci mutanena daga ƙasashen gabas da yamma. Zan komo da su su zauna a Urushalima; za su zama mutanena, ni kuwa zan zama amintaccen Allahnsu mai adalci.” Ga abin da Ubangiji Maɗaukaki ya ce, “Ku da yanzu kuke jin maganan nan da annabawa suka faɗi, waɗanda suke a nan lokacin da aka kafa harsashin haikalin Ubangiji Maɗaukaki, bari hannuwanku su zama da ƙarfi don a gama gina haikalin. Kafin wannan lokaci babu albashi domin mutum ko dabba. Ba wanda yake iya sakewa yă yi hidimominsa saboda maƙiya, domin na sa kowa yă zama maƙiyi maƙwabcinsa. Amma yanzu ba zan yi da waɗanda raguwar mutane yadda na yi da na dā ba,” in ji Ubangiji Maɗaukaki. “Iri zai yi girma da kyau, kuringa za tă ba da ’ya’yanta, ƙasa za tă ba da hatsi, sama kuma za tă ba da raɓa. Zan ba da duk waɗannan abubuwa su zama gādo ga raguwar mutanen nan. Kamar yadda kuka zama abin la’ana a ƙasashe, ya Yahuda da Isra’ila, haka zan cece ku, za ku kuma zama albarka. Kada ku ji tsoro, sai dai ku bar hannuwanku su zama da ƙarfi.” Ga abin da Ubangiji Maɗaukaki ya ce, “Kamar dai yadda na yi niyyar kawo muku bala’i, in kuma ƙi jin tausayi sa’ad da kakanninku suka ba ni haushi,” in ji Ubangiji Maɗaukaki, kada ku ji tsoro “saboda a yanzu na yi niyya in sāke yi wa Urushalima da Yahuda abu mai kyau. Abubuwan da za ku yi ke nan. Ku gaya wa juna gaskiya, ku kuma dinga yin shari’ar gaskiya a ɗakunanku na shari’arku; kada ku ƙulla wa maƙwabtanku mugunta, kuma kada ku so yin rantsuwa ta ƙarya. Ina ƙyamar waɗannan duka,” in ji Ubangiji Maɗaukaki. Maganar Ubangiji Maɗaukaki ta sāke zuwa wurina. Ga abin da Ubangiji Maɗaukaki ya ce, “Azumin wata na huɗu, da na watan biyar, da na watan bakwai da na watan goma za su zama lokutan farin ciki da murna da kuma bukukkuwa na murna ga Yahuda. Saboda haka sai ku ƙaunaci gaskiya da salama.” Ga abin da Ubangiji Maɗaukaki ya ce, “Mutane da yawa da kuma mazaunan birane da yawa har yanzu za su zo, mazaunan wani birni za su je wurin mazaunan wani birni su ce, ‘Bari mu je nan da nan mu roƙi Ubangiji mu kuma nemi Ubangiji Maɗaukaki. Ni kaina zan je.’ Mutane da yawa kuma da al’ummai masu ƙarfi za su zo Urushalima su nemi Ubangiji Maɗaukaki su kuma roƙe shi.” Ga abin da Ubangiji Maɗaukaki ya ce, “A kwanakin nan, mutane goma daga kabilu da al’ummai za su riƙe rigar mutumin Yahuda guda su ce, ‘Bari mu tafi tare da kai, domin mun ji cewa Allah yana tare da ku.’ ” Annabci. Maganar Ubangiji tana gāba da ƙasar Hadrak za tă kuma sauko a kan Damaskus, gama idanun dukan mutane da na kabilan Isra’ila suna a kan Ubangiji, da kuma a kan Hamat ita ma, wadda ta yi iyaka da ita, da kuma a kan Taya da Sidon, ko da yake suna da hikima ƙwarai. Taya ta gina wa kanta mafaka mai ƙarfi; ta tara azurfa kamar ƙasa, zinariya kuma kamar tarin shara a tituna. Amma Ubangiji zai karɓe mallakarta, zai hallaka ikonta da take da shi a kan teku, wuta kuma za tă cinye ta. Ashkelon za tă ga haka ta ji tsoro; Gaza za tă yi birgima cikin azaba, haka Ekron ma, gama za tă fid da zuciya. Gaza za tă rasa sarkinta za a kuma gudu a bar Ashkelon. Baƙi za su mallaki Ashdod, kuma zan kawar da girman kan Filistiyawa. Zan kawar da jini daga bakinsu, zan kuma cire abincin da aka haramta daga tsakanin haƙoransu. Waɗanda za a bari za su zama na Allahnmu, su kuma zama shugabanni a Yahuda, Ekron kuma za tă zama kamar Yebusiyawa. Amma zan kāre gidana daga sojoji masu kai da kawowa. Azzalumi ba zai ƙara cin mutanena da yaƙi ba, gama yanzu ina tsaro. Ki yi murna ƙwarai, ya Diyar Urushalima! Ki yi sowa, Diyar Urushalima! Duba, ga sarkinki yana zuwa wurinki, mai adalci yana kuma da ceto, mai tawali’u yana kuma hawan jaki, yana a kan ɗan aholaki, a kan ’yar jaka. Zan ƙwace kekunan yaƙi daga Efraim, da kuma dawakan yaƙi daga Urushalima, za a kuma karya bakan yaƙi. Zai yi shelar salama ga al’ummai. Mulkinsa zai yaɗu daga teku zuwa teku, daga Kogi kuma zuwa ƙarshen duniya. Ke kuma, saboda jinin alkawarina da ke, zan ’yantar da ’yan kurkukunki daga rami marar ruwa. Ku koma maɓuya, ya ku ’yan kurkuku masu sa zuciya; ko yanzu ma na sanar cewa zan mayar muku ninki biyu. Zan lanƙwasa Yahuda yadda nake lanƙwasa bakana, in kuma cika ta da Efraim kamar kibiya. Zan tā da ’ya’yanki maza, ya Sihiyona, gāba da ’ya’yanki, ya Girka, in kuma mai da ke kamar takobin jarumin yaƙi. Sa’an nan Ubangiji zai bayyana a bisansu; kibiyarsa za tă wulga kamar walƙiya. Ubangiji Mai Iko Duka zai busa ƙaho; zai taho ta cikin guguwa daga kudu, Ubangiji Maɗaukaki kuma zai tsare su. Za su hallakar su kuma yi nasara da duwatsun majajjawa. Za su sha su yi kururuwa kamar sun sha ruwan inabi; za su cika kamar kwanon da ake amfani don a yayyafa jini a kusurwoyin bagade. Ubangiji Allahnsu zai cece su a wannan rana gama su mutanensa ne da kuma garkensa. Za su haska a cikin ƙasarsa kamar lu’ulu’u a rawani. Za su yi kyan gani da kuma bansha’awa! Hatsi zai sa samari su yi murna, sabon ruwan inabi kuma zai sa ’yan mata su yi farin ciki. Ku roƙi Ubangiji yă ba ku ruwa a lokacin bazara; Ubangiji ne yake yin gizagizan hadari. Shi ne yake ba wa mutane yayyafin ruwan sama yana kuma ba da tsire-tsire na fili ga kowa. Gumaka suna maganganun ruɗu, masu duba suna ganin wahayoyin ƙarya, suna faɗa mafarkan ƙarya suna ba da ta’aziyyar banza. Saboda haka mutane suna yawo kamar tumaki waɗanda suke shan wahala saboda rashin makiyayi. “Ina fushi da makiyayan, zan kuma hukunta shugabannin; gama Ubangiji Maɗaukaki zai lura da garkensa, wato, gidan Yahuda, zai kuma sa su zama kamar doki mai fariya cikin yaƙi. Daga Yahuda dutsen kusurwa zai fito, daga gare shi za a samu abin kafa tenti, daga gare shi za a sami bakan yaƙi, daga gare shi za a sami kowane mai mulki. Tare za su zama kamar mutane masu ƙarfi suna tattake lakar tituna a cikin yaƙi. Domin Ubangiji yana tare da su, za su yi faɗa su kuma yi nasara a kan masu yaƙi a kan dawakai. “Zan ƙarfafa gidan Yahuda in kuma ceci gidan Yusuf. Zan maido da su domin ina jin tausayinsu. Za su zama kamar ban taɓa ƙinsu ba, gama ni ne Ubangiji Allahnsu zan kuma amsa musu. Mutanen Efraim za su zama kamar mutane masu ƙarfi, zukatansu kuwa za su yi murna kamar sun sha ruwan inabi. ’Ya’yansu za su gani su yi murna; zuciyarsu za tă yi farin ciki a cikin Ubangiji. Zan ba da alama in kuma tattara su. Ba shakka zan fanshe su; za su yi yawa kamar yadda suke a dā. Ko da yake na warwatsa su cikin mutane, duk da haka a can ƙasashe masu nisa za su tuna da ni. Su da ’ya’yansu za su rayu, za su kuwa komo. Zan komo da su daga Masar in kuma tattara su daga Assuriya. Zan kawo su Gileyad da Lebanon, har wuri yă kāsa musu. Za su ratsa cikin tekun wahala; zan kwantar da raƙuman teku dukan zurfafan Nilu kuma za su bushe. Za a ƙasƙantar da Assuriya, sandar sarautar Masar kuma za tă rabu da ita. Zan ƙarfafa su a cikin Ubangiji kuma a cikin sunansa za su yi tafiya,” in ji Ubangiji. Buɗe ƙofofinki, ya Lebanon, don wuta ta cinye itatuwan al’ul naki. Yi kuka, ya itacen fir, gama itacen al’ul ya fāɗi; itatuwa masu daraja sun lalace! Ku yi kuka, ku itatuwan oak na Bashan; an sassare itatuwan babban kurmi! Ku ji kukan makiyaya; an ɓata musu wuraren kiwonsu masu ciyayi! Ku ji rurin zakoki; an lalatar da jejin Urdun! Ga abin da Ubangiji Allahna ya ce, “Yi kiwon garken tumakin da za a yanka. Masu sayensu sun yanyanka su, suka kuwa tafi ba hukunci. Masu sayar da su sun ce, ‘Yabi Ubangiji, na yi arziki!’ Makiyayansu ma ba su ji tausayinsu ba. Gama ba zan ƙara jin tausayin mutanen ƙasar ba,” in ji Ubangiji. “Zan ba da kowa ga maƙwabcinsa da kuma sarkinsa. Za su zalunci ƙasar, ba zan kuma cece su daga hannuwansu ba.” Saboda haka na yi kiwon garken da za a yanka, musamman garken da ake zalunta. Sai na ɗauki sanduna biyu na kira ɗaya Tagomashi, ɗaya kuma Haɗinkai, sai na yi kiwon garken. Cikin wata guda na kawar da makiyayan nan uku. Garken suka ƙi ni, na kuwa gaji da su na ce, “Ba zan zama makiyayinku ba. Bari masu mutuwa su mutu, masu hallaka kuma su hallaka. Bari waɗanda suka ragu su ci naman juna.” Sai na ɗauki sandana mai suna Tagomashi na karya shi, na janye alkawarin da na yi da dukan al’ummai. An janye shi a ranan nan, saboda haka garken da yake cikin wahala masu kallona sun san cewa maganar Ubangiji ce. Na faɗa musu cewa, “In kun ga ya fi kyau, ku biya ni; in kuwa ba haka ba, ku riƙe.” Saboda haka suka biya ni azurfa talatin. Sai Ubangiji ya ce mini, “Jefar da shi cikin ma’aji,” Lada mai kyau da aka yi cinikina ne! Saboda haka sai na ɗauki azurfa talatin ɗin na jefa su cikin gidan Ubangiji don a sa cikin ma’aji. Sai na karya sandana na biyu mai suna Haɗinkai, ta haka na karya ’yan’uwantakar da take tsakanin Yahuda da Isra’ila. Sai Ubangiji ya ce mini, “Ka sāke ɗaukar kayan aiki na wawan makiyayi. Gama zan tā da makiyayi a ƙasar wanda ba zai kula da ɓatattu, ko yă nemi ƙanana, ko yă warkar da waɗanda suka ji ciwo, ko kuma ciyar da masu lafiya ba, sai dai zai ci naman keɓaɓɓun tumaki, yă farfasa kofatonsu. “Kaito ga banzan makiyayin nan, wanda ya bar garken! Bari takobi yă sare hannunsa da idonsa na dama! Bari hannunsa yă shanye gaba ƙaf, idonsa na dama kuma yă makance sarai!” Annabci, maganar Ubangiji game da Isra’ila. Ubangiji, wanda ya shimfiɗa sammai, wanda ya kafa harsashin duniya, wanda kuma ya yi ruhun mutum a cikinsa ya ce, “Zan sa Urushalima ta zama kwaf mai sa mutanen da suke a dukan kewayenta, jiri. Yaƙi zai kewaye Urushalima har yă shafi Yahuda ma. A ranan nan, sa’ad da duk al’umman duniya za su tayar mata, zan sa Urushalima ta zama dutsen da ba a iya matsarwa ga dukan al’ummai. Duk waɗanda suka yi ƙoƙari su matsar da shi za su ji ciwo. A ranan nan zan sa kowane doki yă tsorata, mai hawan dokin kuma yă haukace,” in ji Ubangiji. “Zan sa idanuna in tsare gidan Yahuda, amma zan makantar da dukan dawakan al’ummai. Sa’an nan shugabannin Yahuda za su ce a cikin zukatansu, ‘Mutanen Urushalima suna da ƙarfi domin Ubangiji Maɗaukaki shi ne Allahnsu.’ “A ranan nan zan sa shugabannin Yahuda su zama kamar tukunyar wuta a tarin itacen wuta; kamar harshen wuta a dammunan hatsi. Za su ƙone dukan mutanen da suke kewaye da su hagu da dama, amma babu abin da zai taɓa mutanen Urushalima. “ Ubangiji zai ceci wuraren zaman Yahuda da farko, don kada darajar gidan Dawuda da mazaunan Urushalima su fi na Yahuda daraja. A ranan nan Ubangiji zai kiyaye waɗanda suke zama a Urushalima, domin marasa ƙarfi a cikinsu su zama kamar Dawuda, gidan Dawuda kuma zai zama kamar Allah, kamar mala’ikan Ubangiji da yake tafiya a gabansu. A ranan nan zan fito don in hallaka dukan al’umman da suka yaƙi Urushalima. “Zan kuma zubo wa gidan Dawuda da mazaunan Urushalima ruhun alheri da na addu’a. Za su dube ni, wannan da suka soke shi, za su kuma yi makoki dominsa kamar yadda mutum yakan yi makokin mutuwar ɗansa tilo, su kuma yi baƙin ciki ƙwarai kamar yadda mutum yakan yi baƙin ciki don ɗan fari. A ranan nan kuka a Urushalima zai yi yawa kamar kukan Hadad Rimmon a filin Megiddo. Ƙasar za tă yi makoki, kowane iyali zai yi makoki a ware, tare da matansu su ma a ware, iyalin gidan Dawuda da matansu, iyalin gidan Natan da matansu, iyalin gidan Lawi da matansu, iyalin gidan Shimeyi da matansu, dukan sauran iyalan kuma da matansu. “A ranan nan za a buɗe maɓulɓulan ruwa zuwa gidan Dawuda da mazaunan Urushalima, don a tsarkake su daga zunubi da rashin tsabta. “A ranan nan, zan kawar da sunayen gumaka daga ƙasar, ba kuwa za a ƙara tunawa da su ba,” in ji Ubangiji Maɗaukaki. “Zan kawar da annabawa da kuma ruhu marar tsabta daga ƙasar. In kuma wani ya yi annabci, sai mahaifinsa da mahaifiyarsa su ce masa, ‘Ba za ka rayu ba, gama kana faɗar ƙarya da sunan Ubangiji.’ Sa’ad da yake yin annabci, iyayensa za su soke shi da takobi. “A ranan nan kowane annabi zai ji kunyar annabcin wahayinsa. Ba zai sa rigar annabci mai gashi ba don yă yi ruɗu. Zai ce, ‘Ni ba annabi ba ne. Ni manomi ne; ƙasa ce nake samun abin zaman gari tun ina matashi.’ In wani ya tambaye shi, ‘Waɗanne miyaku ne haka a jikinka?’ Zai amsa yă ce, ‘Miyakun da aka yi mini a gidan abokaina ne.’ “Tashi, ya takobi, gāba da makiyayina, mutumin da yake kusa da ni sosai!” In ji Ubangiji Maɗaukaki. “Kashe makiyayin, sai tumakin su watse, in kuma tayar wa ƙananan. A cikin ƙasar duka,” in ji Ubangiji, “kashi biyu bisa uku za a buge su su hallaka; duk da haka za a bar kashi ɗaya bisa uku a cikinta. Wannan kashi ɗaya bisa ukun zan kawo in sa a cikin wuta; zan tace su kamar azurfa in gwada su kamar zinariya. Za su kira bisa sunana zan kuwa amsa musu; zan ce, ‘Su mutanena ne,’ za su kuma ce, ‘ Ubangiji ne Allahnmu.’ ” Ranar Ubangiji tana zuwa sa’ad da za a raba muku ganimar da aka washe daga gare ku. Zan tara dukan al’ummai su yaƙi Urushalima; za a ci birnin da yaƙi, za a washe gidaje, a kuma yi wa mata fyaɗe. Rabin birnin zai je bauta, amma ba za a kwashe sauran mutanen daga birnin ba. Sa’an nan Ubangiji zai fita yă yi yaƙi da waɗannan al’ummai, kamar yadda yake yaƙi a ranar yaƙi. A ranan nan ƙafafunsa za su tsaya a kan Dutsen Zaitun, gabas da Urushalima, za a kuma tsage Dutsen Zaitun kashi biyu daga gabas zuwa yamma, yă zama babban kwari, rabin dutsen zai matsa zuwa wajen arewa, rabi kuma zai matsa zuwa wajen kudu. Za ku gudu ta wajen kwarin dutsena, gama zai miƙe har zuwa Azel. Za ku gudu kamar yadda kuka guje wa girgizar ƙasa a kwanakin Uzziya sarkin Yahuda. Sa’an nan Ubangiji Allahna zai zo, tare da duk masu tsarki. A ranan nan ba za a kasance da haske ko sanyi ba, ko hazo mai duhu ba. Za tă zama rana ce ta musamman, ba yini ko dare, rana da take sananne ga Ubangiji. Sa’ad da yamma ta yi, za a yi haske. A ranan nan ruwan rai zai kwararo daga Urushalima, rabi zai gangara gabas zuwa teku rabi kuma zai gangara yamma zuwa Bahar Rum, a damina da rani. Ubangiji zai sama sarki bisa dukan duniya. A ranan nan za a kasance da Ubangiji ɗaya, ba wani suna kuma sai nasa. Ƙasar gaba ɗaya daga Geba zuwa Rimmon, kudu da Urushalima, za tă zama kamar Araba. Amma Urushalima za tă kasance a wurinta, daga Ƙofar Benyamin zuwa sashen Ƙofa ta Farko, zuwa Ƙofar Kusurwa, daga kuma Hasumiyar Hananel zuwa wurin matsin ruwan inabin sarki. Za a zauna a cikinka; ba za a ƙara hallaka ta ba. Urushalima za tă zauna lafiya. Ga bala’in da Ubangiji zai bugi dukan al’umman da suka yi yaƙi da Urushalima. Fatar jikinsu za tă ruɓe tun suna tsaye a ƙafafunsu, idanunsu za su ruɓe a cikin kwarminsu, harsunansu kuma zai ruɓe a cikin bakunansu. A ranan nan Ubangiji zai sa maza su cika da tsoro ƙwarai. Kowane mutum zai kama hannun ɗan’uwansa, za su kai wa juna hari. Yahuda ma za tă yi yaƙi a Urushalima. Za a tattara dukiyar al’umman da suke kewaye, za a tara zinariya da azurfa masu yawan gaske tare da tufafi. Irin wannan bala’i zai auko wa dawakai da alfadarai, raƙuma da jakuna, da kuma dukan dabbobi a wannan sansani. Sa’an nan waɗanda suka tsira daga cikin al’umman da suka yaƙe Urushalima za su haura shekara-shekara su yi wa Sarki, Ubangiji Maɗaukaki sujada, su kuma yi Bikin Tabanakul. In waɗansu mutanen da suke duniya ba su haura Urushalima suka yi wa Sarki, Ubangiji Maɗaukaki sujada ba, ba za su sami ruwan sama ba. In mutanen Masar ba su haura sun yi sujada ba, ba za su sami ruwan sama ba. Ubangiji zai kawo masu bala’in da ya aika wa al’umman da ba su haura sun yi Bikin Tabanakul ba. Wannan ne zai zama hukuncin Masar da kuma na dukan al’umman da ba su haura sun yi Bikin Tabanakul ba. A ranan nan za a rubuta TSARKI GA Ubangiji a jikin ƙararrawar dawakai, kuma tukwanen dahuwa a gidan Ubangiji za su zama kamar kwanoni masu tsarki a gaban bagade. Kowace tukunya a Urushalima da Yahuda za tă zama mai tsarki ga Ubangiji Maɗaukaki, kuma duk wanda ya zo don miƙa hadaya zai ɗauki waɗansu tukwane yă yi dahuwa da su. A ranan nan kuwa, ba Bakan’ane da zai ƙara kasance a gidan Ubangiji Maɗaukaki. Annabci, wannan ita ce maganar Ubangiji ga Isra’ila ta wurin Malaki. “Na ƙaunace ku, in ji Ubangiji. “Amma sai kuka ce, ‘Yaya ka ƙaunace mu?’ “Isuwa ba ɗan’uwan Yaƙub ba ne?” In ji Ubangiji. “Duk da haka na ƙaunaci Yaƙub, amma na ƙi Isuwa, na kuma mai da ƙasarsa da take kan duwatsu kango, na ba da gādonsa ga dilolin hamada.” Edom zai iya cewa, “Ko da yake an ragargaza mu, ai, za mu sāke gina kufanmu.” Amma ga abin da Ubangiji Maɗaukaki ya ce, “Za su iya gini, amma zan rushe. Za a ce da su Muguwar Ƙasa, mutane da kullum suke a ƙarƙashi fushin Ubangiji. Za ku ga wannan da idanunku ku kuma ce, ‘ Ubangiji da girma yake, har gaba da iyakokin Isra’ila ma!’ “Ɗa yakan girmama mahaifinsa, bawa kuma yakan girmama maigidansa. In ni mahaifi ne, ina girman da ya dace da ni? In ni maigida ne, ina girman da ya dace da ni?” In ji Ubangiji Maɗaukaki. “Ku firistoci, ku ne kuka rena sunana. “Amma sai kuka ce, ‘Yaya muka rena sunanka?’ “Kun ajiye abinci mai ƙazanta a kan bagadena. “Sai kuka ce, ‘Yaya muka ƙazantar da kai?’ “Ta wurin cewa teburin Ubangiji abin reni ne. Sa’ad da kuka kawo makauniyar dabba don ku miƙa mini hadaya, wannan daidai ne? Sa’ad da kuka miƙa gurguwar dabba ko marar lafiya, wannan daidai ne? Ku gwada ba wa gwamnanku irin wannan ku gani! Kuna gani zai ji daɗinku? Zai karɓe ku ne?” In ji Ubangiji Maɗaukaki. “To, firistoci yanzu ku gwada ku roƙi Allah yă yi mana alheri. Da irin hadayun nan a hannuwanku ne zai ji ku?” In ji Ubangiji Maɗaukaki. “Kash, da ma wani daga cikinku ya rufe ƙofofin haikali don kada ku shiga, ku hura wuta marar amfani a bisa bagadena! Ba na jin daɗinku, ba zan kuwa karɓi hadaya daga hannuwanku ba” in ji Ubangiji Maɗaukaki. Sunana zai zama mai girma a cikin al’ummai, daga fitowar rana har zuwa fāɗuwarta. A kowane wuri za a miƙa wa sunana turare da tsabtacciyar hadaya domin sunana zai zama mai girma a cikin al’ummai, in ji Ubangiji Maɗaukaki. “Amma kun ƙazantar da sunana ta wurin cewa ‘Teburin Ubangiji ya ƙazantu,’ kuka kuma yi magana a kan abincinsa kuna cewa, ‘Abin reni ne.’ Kun kuma ce, ‘Mun gaji da irin wannan wahala!’ Kuna hura mini hancin reni,” in ji Ubangiji Maɗaukaki. “Sa’ad da kuka kawo raunannu, gurguntattun dabbobi, ko kuma dabbobi masu fama da cuta, kuka kuma miƙa su hadaya, kuna gani zan karɓi wannan daga gare ku?” In ji Ubangiji. “La’ananne ne macucin da yake da lafiyayyiyar dabba namiji a garkensa wadda ya yi alkawari zai bayar, amma sai ya miƙa hadayar dabba mai aibi ga Ubangiji. Gama ni babban sarki ne, za a kuma ji tsoron sunana a cikin al’ummai,” in ji Ubangiji Maɗaukaki. “Yanzu fa wannan gargaɗi dominku ne, ku firistoci. In ba ku saurara ba, in kuma ba ku sa zuciyarku ga girmama sunana ba, zan aukar muku da la’ana, zan kuma la’antar da albarkunku. I, na riga na la’anta su, domin ba ku sa zuciyarku ga girmama ni ba, in ji Ubangiji Maɗaukaki. “Saboda ku zan tsawata wa zuriyarku; zan watsa kashin dabbobin hadayunku a fuskokinku, a kuma kwashe ku tare da shi. Za ku kuwa san cewa ni ne na aika muku da wannan gargaɗi domin alkawarina da Lawi yă ci gaba,” in ji Ubangiji Maɗaukaki. “Alkawarina da shi, alkawari ne na rai da salama, wanda na ba shi; domin yă girmama ni, ya kuwa girmama ni, ya kuma ji tsoron sunana ƙwarai. Umarnin gaskiya yana a bakinsa, ba a kuma sami wani ƙarya a leɓunansa ba. Ya yi tafiya tare da ni cikin salama da adalci, ya kuwa juyo da mutane masu yawa daga zunubi. “Gama ya kamata leɓunan firist su kiyaye ilimi, ya kamata kuma mutane su nemi umarni daga bakinsa, domin shi ne manzon Ubangiji Maɗaukaki. Amma sai kuka kauce hanya, ta wurin koyarwarku kuma kuka sa mutane da yawa suka yi tuntuɓe; kun keta alkawarin da na yi da Lawi,” in ji Ubangiji Maɗaukaki. “Saboda haka na sa a rena ku, a kuma wulaƙanta ku a gaban dukan mutane, domin ba ku bi hanyoyina ba amma kuka nuna sonkai a al’amuran shari’a.” Ashe, ba Mahaifi guda dukanmu muke da shi ba? Ba Allah ɗaya ne ya halicce mu ba? Don me muka keta alkawarin kakanninmu ta wurin cin amanar juna? Yahuda ya ci amana. An yi abin kunya a Isra’ila da kuma a Urushalima. Yahuda ya ƙazantar da wuri mai tsarkin da Ubangiji yake ƙauna, ta wurin auren ’yar wani baƙon allah. Game da mutumin da ya aikata wannan, ko wane ne shi, bari Ubangiji yă yanke shi daga tentunan Yaƙub, ko da ma ya kawo hadayu ga Ubangiji Maɗaukaki. Ga kuma wani abin da kuke yi. Kukan cika bagaden Ubangiji da hawaye. Kukan yi kuka kuna ihu gama Ubangiji ba ya mai da hankali ga hadayunku ko yă karɓe su da farin ciki. Kukan ce, “Don me ba ya karɓan hadayunmu?” Ai, domin Ubangiji ya zama shaida tsakaninka da matar ƙuruciyarka, gama ka keta amanar da ka yi mata, ko da yake ita abokiyar zamanka ce, matar aurenka ta alkawari. Ashe, Ubangiji bai maishe su ɗaya ba? Cikin jiki da ruhu, su nasa ne. Me ya sa suke ɗaya? Domin yana neman ’ya’ya masu tsoron Allah. Saboda haka sai ka lura da kanka, kada kuma ka ci amanar matar ƙuruciyarka. “Na ƙi kisan aure,” in ji Ubangiji, Allah na Isra’ila. “Na kuma ƙi mutumin da ya rufe kansa da tashin hankali kamar riga,” in ji Ubangiji Maɗaukaki. Saboda haka sai ka lura da kanka, kada kuma ka ci amana. Kun sa Ubangiji Maɗaukaki ya gaji da maganganunku. Sai kuka ce, “Yaya muka sa ya gaji?” Kun yi haka ta wurin cewa, “Duk waɗanda suke aikata mugunta, mutanen kirki ne a gaban Ubangiji, yana kuwa jin daɗinsu,” kuna kuma cewa, “Ina Allah mai adalci yake?” “Duba, zan aika manzona, wanda zai shirya hanya a gabana. Sa’an nan a farat ɗaya Ubangiji wanda kuke nema zai zo haikalinsa. Manzon alkawari, wanda kuke sa zuciya kuwa zai zo,” in ji Ubangiji Maɗaukaki. Amma wa zai jure wa ranar zuwansa? Wa zai iya tsaya sa’ad da ya bayyana? Gama zai zama kamar wuta mai tace ƙarfe, ko sabulu mai wanki. Zai zama kamar mai tace azurfa da mai tsarkaketa; zai tsabtacce Lawiyawa, yă kuma tace su kamar zinariya da azurfa. Sa’an nan Ubangiji zai sami mutanen da za su kawo hadayu a cikin adalci. Hadayun Yahuda da na Urushalima za su zama yardajje ga Ubangiji, za su zama kamar a kwanakin da suka wuce, kamar a shekarun baya. “Ta haka zan zo kusa da ku don in yi hukunci. Zan hanzarta ba da shaida a kan masu yin sihiri, da mazinata da masu shaidar zur. Zan ba da shaida a kan waɗanda suke zaluntar ma’aikata a kan albashinsu, da waɗanda suke ƙwarar gwauraye da marayu, suna kuma hana baƙi samun adalci, ba sa ma tsorona,” in ji Ubangiji Maɗaukaki. “Ni Ubangiji ba na canjawa. Shi ya sa ku zuriyar Yaƙub, ba a hallaka ku ƙaƙaf ba. Tun zamanin kakanninku, kun juye wa ƙa’idodina baya, ba ku kuma kiyaye su ba. Ku komo gare ni, ni kuma zan koma gare ku,” in ji Ubangiji Maɗaukaki. “Amma sai kuka ce, ‘Yaya za mu koma gare ka?’ “Mutum zai iya yi wa Allah fashi ne? Duk da haka kun yi mini fashi. “Amma sai kuka ce, ‘Yaya muka yi maka fashi?’ “A wajen zakka da hadayu. Kuna ƙarƙashin la’ana, dukan al’ummarku, domin kuna yin mini fashi. Ku kawo dukan zakka cikin gidan ajiya, don a kasance da abinci a gidana. Ku gwada ni a wannan ku ga, ko ba zan buɗe taskokin sama in zubo muku albarka mai yawa, wadda har ba za ku rasa wurin sa ta ba, in ji Ubangiji Maɗaukaki. Zan hana ƙwari su cinye hatsinku. Kuringar inabi a gonakinku kuma ba za su zubar da ’ya’yansu kafin su nuna ba,” in ji Ubangiji Maɗaukaki. “Sa’an nan dukan al’ummai za su ce da ku masu albarka, gama ƙasarku za tă yi daɗin zama,” in ji Ubangiji Maɗaukaki. “Kun faɗi mugayen abubuwa a kaina,” in ji Ubangiji. “Duk da haka kuka ce, ‘Me muka faɗa a kanka?’ “Kun ce, ‘Ba amfani a bauta wa Allah. Wanda amfani muka samu ta wurin kiyaye umarnansa muna yawo kamar masu makoki a gaban Ubangiji Maɗaukaki? A ganinmu, masu girman kai suna jin daɗi. Masu aikata mugunta kuwa ba arziki kaɗai suka yi ba, amma sukan gwada Allah da mugayen ayyukansu, su kuwa zauna lafiya.’ ” Sa’an nan waɗanda suke tsoron Ubangiji suka yi magana da juna, Ubangiji kuwa ya kasa kunne ya kuma ji. A gabansa aka rubuta a littafin tarihi waɗanda suke tsoron Ubangiji, suna kuma girmama sunansa. “A ranar da na shirya ajiyayyen mallakata, za su zama nawa,” in ji Ubangiji Maɗaukaki. “Zan ji kansu kamar yadda mahaifi cikin tausayi yakan ji kan ɗansa wanda yake masa hidima. Za ku kuma ga bambanci tsakanin masu adalci da mugaye, tsakanin waɗanda suke wa Allah hidima da kuma waɗanda ba sa yi. “Tabbatacce rana tana zuwa; za tă yi ƙuna kamar wutar maƙera. Dukan masu girman kai da kowane mai aikata mugunta zai zama ciyawa, wannan rana mai zuwa za tă ƙone su. Babu saiwa ko reshen da za a bar musu,” in ji Ubangiji Maɗaukaki. Amma ku da kuke girmama sunana, ranar adalci za tă fito tare da warkarwa a fikafikanta. Za ku kuwa fita kuna tsalle kamar ’yan maruƙan da aka sake daga garke. Sa’an nan za ku tattake mugaye; za su zama toka a ƙarƙashin tafin ƙafafunku a ranar da zan aikata waɗannan abubuwa, in ji Ubangiji Maɗaukaki. “Ku tuna da dokar bawana Musa, ƙa’idodi da dokokin da na ba shi a Horeb domin dukan Isra’ila. “Ga shi, zan aika muku da annabi Iliya kafin babbar ranan nan mai banrazana ta Ubangiji tă zo. Zai juye zukatan iyaye ga ’ya’yansu, zukatan ’ya’ya kuma ga iyayensu; in ba haka ba zan bugi ƙasar da hallaka gaba ɗaya.” Tarihin da aka rubuta game da asalin Yesu Kiristi ɗan Dawuda, ɗan Ibrahim. Ibrahim ya haifi Ishaku, Ishaku ya haifi Yaƙub, Yaƙub ya haifi Yahuda da ’yan’uwansa, Yahuda ya haifi Ferez da Zera, waɗanda Tamar ce mahaifiyarsu; Ferez ya haifi Hezron, Hezron ya haifi Ram, Ram ya haifi Amminadab, Amminadab ya haifi Nashon, Nashon ya haifi Salmon, Salmon ya haifi Bowaz, wanda Rahab ce mahaifiyarsa, Bowaz ya haifi Obed, wanda Rut ce mahaifiyarsa, Obed ya haifi Yesse, Yesse kuwa ya haifi Sarki Dawuda. Dawuda ya haifi Solomon, wanda matar Uriya ce mahaifiyarsa. Solomon ya haifi Rehobowam, Rehobowam ya haifi Abiya, Abiya ya haifi Asa, Asa ya haifi Yehoshafat, Yehoshafat ya haifi Yehoram, Yehoram ya haifi Azariya, Azariya ya haifi Yotam, Yotam ya haifi Ahaz, Ahaz ya haifi Hezekiya, Hezekiya ya haifi Manasse, Manasse ya haifi Amon, Amon ya haifi Yosiya, Yosiya kuma ya haifi Yekoniya da ’yan’uwansa a lokacin da aka kwashe su zuwa bauta a Babilon. Bayan an kwashe su zuwa bauta a Babilon. Yekoniya ya haifi Sheyaltiyel, Sheyaltiyel ya haifi Zerubbabel, Zerubbabel ya haifi Abiyud, Abiyud ya haifi Eliyakim, Eliyakim ya haifi Azor, Azor ya haifi Zadok, Zadok ya haifi Akim, Akim kuma ya haifi Eliyud, Eliyud ya haifi Eleyazar, Eleyazar ya haifi Mattan, Mattan ya haifi Yaƙub, Yaƙub ya haifi Yusuf, mijin Maryamu, wadda ta haifi Yesu, wanda ake kira Kiristi. Ta haka akwai zuriya goma sha huɗu ke nan duka-duka daga lokacin Ibrahim zuwa lokacin Dawuda, goma sha huɗu kuma daga Dawuda zuwa bauta a Babilon, goma sha huɗu kuma daga bauta a Babilon zuwa Kiristi. Ga yadda haihuwar Yesu Kiristi ta kasance. An yi alkawarin auren mahaifiyarsa Maryamu, ga Yusuf. Amma tun kafin su zama miji da mata, sai aka tarar Maryamu tana da ciki, ta wurin Ruhu Mai Tsarki. Yusuf mijinta, da yake shi mai adalci ne, bai so yă ba ta kunya, yă tone mata asiri a fili ba, sai ya yi tunani yă sake ta a ɓoye. Amma yana cikin wannan tunani, sai wani mala’ikan Ubangiji ya bayyana masa cikin mafarki ya ce, “Yusuf ɗan Dawuda, kada ka ji tsoron ɗaukan Maryamu zuwa gidanka a matsayin matarka, gama cikin nan nata, daga wurin Ruhu Mai Tsarki ne. Za tă haifi ɗa, za ka kuma sa masa suna Yesu, gama shi ne zai ceci mutanensa daga zunubansu.” Duk wannan ya faru ne, don a cika abin da Ubangiji ya faɗi ta bakin annabin cewa, “Ga shi budurwa za tă yi ciki, za tă haifi ɗa, kuma za a kira shi Immanuwel” (wanda yake nufin “Allah tare da mu”). Da Yusuf ya farka daga barci, sai ya bi umarnin mala’ikan Ubangiji, ya ɗauki Maryamu zuwa gida a matsayin matarsa. Amma bai kwana da ita ba, sai bayan da ta haifi ɗan. Ya kuwa sa masa suna Yesu. Bayan an haifi Yesu a Betlehem, a Yahudiya, a zamanin Sarki Hiridus, sai waɗansu Masana, daga gabas suka zo Urushalima suka yi tambaya suka ce, “Ina shi wanda aka haifa sarkin Yahudawa? Gama mun ga tauraronsa a gabas mun kuwa zo ne domin mu yi masa sujada.” Da Sarki Hiridus ya ji wannan, sai hankalinsa ya tashi haka ma na dukan Urushalima. Bayan ya kira dukan manyan firistoci da malaman dokoki na mutane wuri ɗaya, sai ya tambaye su inda za a haifi Kiristi. Suka amsa suka ce, “A Betlehem ne, cikin Yahudiya, gama haka annabin ya rubuta. “ ‘Amma ke Betlehem, a cikin ƙasar Yahuda, ba ke ce mafi ƙanƙanta a cikin masu mulki a Yahuda ba, gama daga cikinki mai mulki zai zo, wanda zai zama makiyayin mutanena Isra’ila.’ ” Sai Hiridus ya kira Masanan nan a ɓoye, yă gano daga wurinsu daidai lokacin da tauraron ya bayyana. Sai ya aike su Betlehem ya ce, “Ku je ku binciko a hankali game da yaron nan. Da kun same shi, sai ku kawo mini labari nan da nan, domin ni ma in je in yi masa sujada.” Bayan sun saurari sarki, sai suka kama hanyarsu, tauraron da suka gani a gabas kuwa yana tafe a gabansu, sai da ya kai inda yaron yake. Da suka ga tauraron, sai suka yi farin ciki ƙwarai. Suka shiga gidan, suka kuwa ga yaron tare da mahaifiyarsa Maryamu. Suka durƙusa har ƙasa, suka yi masa sujada. Sa’an nan suka kunce dukiyarsu, suka miƙa masa kyautai na zinariya da na turare da na mur. Bayan an gargaɗe su cikin mafarki kada su koma wurin Hiridus, sai suka koma ƙasarsu ta wata hanya dabam. Bayan sun tafi, sai mala’ikan Ubangiji ya bayyana ga Yusuf a mafarki ya ce, “Tashi, ka ɗauki yaron da mahaifiyarsa, ku gudu zuwa Masar. Ku zauna a can sai na gaya muku, gama Hiridus zai nemi yaron don yă kashe.” Sai Yusuf ya tashi, ya ɗauki yaron da mahaifiyarsa da dad dare suka tafi Masar, inda ya zauna har sai da Hiridus ya mutu. Ta haka kuwa aka cika abin da Ubangiji ya faɗa ta bakin annabin cewa, “Daga Masar na kira ɗana.” Da Hiridus ya gane cewa Masanan nan sun yi masa wayo, sai ya husata ƙwarai, ya yi umarni cewa a karkashe dukan ’yan yara maza da suke a Betlehem da kewayenta, daga masu shekara biyu zuwa ƙasa, bisa ga lokacin da ya sami labarin daga Masanan nan. Sai abin da aka faɗa ta bakin annabi Irmiya ya cika, cewa, “An ji murya a Rama, tana kuka da makoki mai tsanani, Rahila ce take kuka domin ’ya’yanta, an kāsa ta’azantar da ita, don ba su.” Bayan Hiridus ya mutu, sai mala’ikan Ubangiji ya bayyana ga Yusuf a mafarki a Masar, ya ce, “Tashi, ka ɗauki yaron da mahaifiyarsa ku tafi ƙasar Isra’ila, domin waɗanda suke neman ran yaron sun mutu.” Sai ya tashi, ya ɗauki yaron da mahaifiyarsa suka tafi ƙasar Isra’ila. Amma da ya ji Arkelawus ne yake mulki a Yahudiya a matsayin wanda ya gāji mahaifinsa Hiridus, sai ya ji tsoron zuwa can. Bayan an gargaɗe shi a mafarki, sai ya ratse zuwa gundumar Galili, ya je ya zauna a wani garin da ake kira Nazaret. Ta haka aka cika abin da aka faɗa ta bakin annabawa cewa, “Za a ce da shi Banazare.” A waɗancan kwanaki, Yohanna Mai Baftisma ya zo, yana wa’azi a Hamadan Yahudiya yana cewa, “Ku tuba, gama mulkin sama ya yi kusa.” Wannan shi ne wanda aka yi maganarsa ta wurin annabi Ishaya cewa, “Ga murya mai kira a hamada tana cewa, ‘Ku shirya wa Ubangiji hanya, ku miƙe hanyoyi dominsa.’ ” Tufafin Yohanna kuwa an yi su da gashin raƙumi ne, yana kuma daure da ɗamara ta fata. Abincinsa kuwa fāri ne da zumar jeji. Mutane suka zo wurinsa daga Urushalima da dukan Yahudiya da kuma dukan yankin Urdun. Suna furta zunubansu, ya kuma yi musu baftisma a Kogin Urdun. Amma da Yohanna ya ga Farisiyawa da Sadukiyawa da yawa suna zuwa inda yake yin baftisma, sai ya ce musu, “Ku macizai! Wa ya gargaɗe ku ku guje wa fushin nan mai zuwa? Ku yi ayyukan da suka dace da tuba. Kada ma ku yi tunani a ranku cewa, ‘Ai, Ibrahim ne mahaifinmu.’ Ina gaya muku cewa Allah zai iya tā da ’ya’ya wa Ibrahim daga cikin duwatsun nan. An riga an sa bakin gatari a gindin itatuwa, kuma duk itacen da bai ba da ’ya’ya masu kyau ba, za a sare shi a jefa cikin wuta. “Ina muku baftisma da ruwa domin tuba. Amma wani yana zuwa a bayana wanda ya fi ni iko, wanda ko takalmansa ma ban isa in ɗauka ba. Zai yi muku baftisma da Ruhu Mai Tsarki da kuma wuta. Yana riƙe da matankaɗinsa, zai tankaɗe hatsinsa, yă kuma tattara alkamarsa a cikin rumbu, amma zai ƙone yayin da wutar da ba a iya kashewa.” Sai Yesu ya zo daga Galili, ya je Urdun don Yohanna yă yi masa baftisma. Amma Yohanna ya so yă hana shi, yana cewa, “Ina bukata ka yi mini baftisma, yaya kake zuwa wurina?” Yesu ya amsa ya ce, “Bari yă zama haka yanzu; ya dace mu yi haka don mu cika dukan adalci.” Sa’an nan Yohanna ya yarda. Nan da nan da aka yi wa Yesu baftisma, sai ya fito daga ruwa. A wannan lokaci sama ya buɗe, sai ya ga Ruhun Allah yana saukowa kamar kurciya ya kuwa sauka a kansa. Sai murya daga sama ta ce, “Wannan shi ne Ɗana wanda nake ƙauna; wanda kuma nake jin daɗinsa ƙwarai.” Sa’an nan Ruhu ya kai Yesu cikin hamada don Iblis yă gwada shi. Bayan ya yi azumi yini arba’in da kuma dare arba’in, sai ya ji yunwa. Sai mai gwajin ya zo wurinsa ya ce, “In kai Ɗan Allah ne, ka ce wa duwatsun nan su zama burodi.” Yesu ya amsa ya ce, “A rubuce yake cewa, ‘Ba da abinci kaɗai mutum yake rayuwa ba, sai dai da kowace kalmar da take fitowa daga bakin Allah.’ ” Sai Iblis ya kai shi birni mai tsarki, ya kai shi can wuri mafi tsayi duka na haikali. Ya ce, “In kai Ɗan Allah ne, yi tsalle ka sauka ƙasa. Gama a rubuce yake, “ ‘Zai umarci mala’ikunsa game da kai, za su tallafe ka da hannuwansu, don kada ka buga ƙafarka a kan dutse.’ ” Yesu ya amsa masa ya ce, “A rubuce yake kuma cewa, ‘Kada ka gwada Ubangiji Allahnka.’ ” Har wa yau, Iblis ya kai shi bisa wani dutse mai tsawo sosai, ya nunnuna masa dukan mulkokin duniya da darajarsu. Ya ce, “Zan ba ka dukan wannan, in za ka durƙusa ka yi mini sujada.” Sai Yesu ya ce masa, “Rabu da ni, Shaiɗan! Gama a rubuce yake, ‘Yi wa Ubangiji Allahnka sujada, shi kaɗai kuma za ka bauta wa.’ ” Sa’an nan Iblis ya bar shi, mala’iku kuwa suka zo suka yi masa hidima. Da Yesu ya ji labari cewa an kulle Yohanna a kurkuku, sai ya koma zuwa Galili. Ya bar Nazaret, ya je ya zauna a Kafarnahum, wadda take a bakin tafki wajen Zebulun da Naftali don a cika abin da aka faɗa ta bakin annabi Ishaya cewa, “Ƙasar Zebulun da ƙasar Naftali, da kuke a hanyar zuwa tekun Galili, a ƙetaren Urdun, wannan yankin Galili ta Al’ummai, mutanen da suke zama cikin duhu sun ga babban haske; haske kuma ya haskaka a kan waɗanda suke zama a inuwar mutuwa.” Tun daga wannan lokaci, Yesu ya fara wa’azi yana cewa, “Ku tuba, gama mulkin sama ya yi kusa.” Da Yesu yana kan tafiya a bakin Tekun Galili, sai ya ga waɗansu ’yan’uwa guda biyu, Siman wanda ake kira Bitrus da ɗan’uwansa Andarawus. Suna jefa abin kamun kifi a tafki, gama su masunta ne. Sai Yesu ya ce, “Zo, ku bi ni, ni kuwa zan mai da ku masu jan mutane zuwa wurina.” Nan da nan suka bar abin kamun kifinsu suka bi shi. Da ya ci gaba daga nan, sai ya ga waɗansu ’yan’uwa guda biyu, Yaƙub ɗan Zebedi da ɗan’uwansa Yohanna. Suna cikin jirgin ruwa tare da mahaifinsu Zebedi, suna shirya abin kamun kifinsu. Yesu ya kira su, nan take suka bar jirgin ruwan da mahaifinsu suka kuwa bi Yesu. Yesu ya zazzaga dukan Galili, yana koyarwa a cikin majami’unsu, yana wa’azin labari mai daɗi na mulkin sama, yana kuma warkar da kowace cuta da rashin lafiyar mutane. Labarinsa ya bazu ko’ina a Suriya, mutane kuwa suka kawo masa dukan waɗanda suke fama da cututtuka iri-iri, da waɗanda suke da zafin ciwo, da masu aljanu, da waɗanda suke masu farfaɗiya, da shanyayyu, ya kuwa warkar da su. Taron mutane mai yawa daga Galili, Dekafolis, Urushalima, Yahudiya da kuma yankin hayin Urdun suka bi shi. Ganin taron mutane, sai ya hau kan gefen dutse ya zauna. Almajiransa kuwa suka zo wurinsa, sai ya fara koya musu. Yana cewa, “Masu albarka ne waɗanda suke matalauta a ruhu, gama mulkin sama nasu ne. Masu albarka ne waɗanda suke makoki, gama za a yi musu ta’aziyya. Masu albarka ne waɗanda suke masu tawali’u, gama za su gāji duniya. Masu albarka ne waɗanda suke jin yunwa da ƙishirwa don gani an yi adalci, gama za a ƙosar da su. Masu albarka ne waɗanda suke masu jinƙai, gama za a nuna musu jinƙai. Masu albarka ne waɗanda suke masu tsabtar zuciya, gama za su ga Allah. Masu albarka ne waɗanda suke masu ƙulla zumunci, gama za a kira su ’ya’yan Allah. Masu albarka ne waɗanda ake tsananta musu don gani an yi adalci, gama mulkin sama nasu ne. “Masu albarka ne ku, sa’ad da mutane suke zaginku, suna tsananta muku, suna kuma faɗin kowace irin muguwar magana a kanku saboda ni. Ku yi murna ku kuma yi farin ciki, domin ladarku mai yawa ne a sama, gama haka suka tsananta wa annabawan da suka riga ku. “Ku ne gishirin duniya, amma in gishiri ya rabu da daɗin ɗanɗanonsa, yaya za a sāke mai da daɗin ɗanɗanonsa? Ba shi da sauran amfani, sai dai a zubar da shi mutane kuma su tattaka. “Ku ne hasken duniya. Birnin da yake a bisan tudu ba ya ɓoyuwa. Mutane ba sa ƙuna fitila su rufe ta da murfi. A maimako, sukan ajiye ta a kan wurin ajiye fitila, takan kuma ba da haske ga kowa a cikin gida. Haka ma, bari haskenku yă haskaka a gaban mutane, domin su ga ayyukanku masu kyau, su kuwa yabi Ubanku da yake cikin sama. “Kada ku yi tsammani na zo ne domin in kawar da Doka ko kuma Annabawa; ban zo domin in kawar da su ba ne, sai dai domin in ciccika su. Gaskiya nake gaya muku, kafin sama da ƙasa sun shuɗe, babu ko ɗan wasali, babu wani ɗigo ta kowace hanya da zai ɓace daga Dokar, sai an cika kome. Duk wanda ya karya ɗaya daga cikin mafi ƙanƙanta na umarnan nan, ya kuma koya wa waɗansu su yi haka, za a ce da shi mafi ƙanƙanta a mulkin sama. Amma duk wanda ya aikata, ya kuma koyar da waɗannan umarnai, za a kira shi mai girma a cikin mulkin sama. Gama ina faɗa muku cewa in dai adalcinku bai fi na Farisiyawa da na malaman dokoki ba, faufau, ba za ku shiga mulkin sama ba. “Kun dai ji an faɗa wa mutanen dā cewa, ‘Kada ka yi kisankai; kuma duk wanda ya yi kisankai za a hukunta shi.’ Amma ina gaya muku, duk wanda ya yi fushi da ɗan’uwansa, za a hukunta shi. Kuma duk wanda ya ce wa ɗan’uwansa ‘ Raka,’ za a kai shi gaban Majalisa. Amma duk wanda ya ce, ‘Kai wawa!’ Zai kasance a hatsarin shiga jahannama ta wuta. “Saboda haka, in kana cikin ba da baikonka a kan bagade, a can kuwa ka tuna cewa ɗan’uwanka yana riƙe da kai a zuci, sai ka bar baikonka a can gaban bagade. Ka je ka shirya tukuna da ɗan’uwanka; sa’an nan ka zo ka ba da baikonka. “Ka yi hanzari ka shirya al’amura da maƙiyinka wanda yake ƙararka a kotu. Ka yi haka, tun kana tare da shi a kan hanya, in ba haka ba, zai miƙa ka ga alƙali, alƙali kuma yă miƙa ka ga ɗan sanda, mai yiwuwa kuwa a jefa ka a kurkuku. Gaskiya nake gaya maka, ba za ka fita ba, sai ka biya kobo na ƙarshe. “Kun dai ji an faɗa, ‘Kada ka yi zina.’ Amma ina gaya muku, duk wanda ya dubi mace, sa’an nan ya yi sha’awarta a zuci, ya riga ya yi zina ke nan da ita a zuciyarsa. In idonka na dama yana sa ka yin zunubi, ƙwaƙule shi ka yar. Zai fiye maka ka rasa ɗaya daga cikin gaɓoɓin jikinka, da a jefa jikinka ɗungum a cikin jahannama ta wuta. In kuma hannunka na dama yana sa ka yin zunubi, yanke shi ka yar. Zai fiye maka ka rasa ɗaya daga cikin gaɓoɓin jikinka, da a jefa jikinka ɗungum a cikin jahannama ta wuta. “An kuma faɗa, ‘Duk wanda ya saki matarsa, dole yă ba ta takardar saki.’ Amma ina gaya muku, duk wanda ya saki matarsa in ba a kan laifin zina ba, ya sa ta zama mazinaciya ke nan, kuma duk wanda ya auri macen da mijinta ya sake, shi ma yana zina ne. “Har wa yau dai kun ji an faɗa wa mutane a dā, ‘Kada ka karya alkawarinka, sai dai ka cika alkawaran da ka yi wa Ubangiji.’ Amma ina gaya muku, Kada ku yi rantsuwa sam, ko da sama, domin kursiyin Allah ne; ko da ƙasa, domin matashin ƙafafunsa ne; ko kuma da Urushalima, domin birnin Babban Sarki ne. Kada kuma ka rantse da kanka, domin ba za ka iya mai da ko gashi ɗaya yă zama fari ko baƙi ba. Abin da ya kamata ku ce kawai, shi ne, I, ko A’a. Abin da ya wuce haka kuwa daga wurin Mugun nan yake. “Kun dai ji an faɗa, ‘Ido domin ido, haƙori kuma domin haƙori.’ Amma ina gaya muku, Kada ku yi tsayayya da mugun mutum. In wani ya mare ka a kumatun dama, juya masa ɗayan ma. In kuma wani yana so yă yi ƙararka yă ƙwace rigarka, to, ba shi mayafinka ma. In wani ya tilasta ka yin tafiya mil ɗaya, to, tafi tare da shi mil biyu. Ka ba wa duk wanda ya roƙe ka abu, kada kuma ka hana wa wanda yake neman bashi daga gare ka. “Kun dai ji an faɗa, ‘Ka ƙaunaci maƙwabcinka, ka kuma ƙi abokin gābanka.’ Amma ina gaya muku, ku ƙaunaci abokan gābanku kuma ku yi wa waɗanda suke tsananta muku addu’a, don ku zama ’ya’yan Ubanku na sama. Shi yakan sa ranarsa ta haskaka a kan mugaye da masu kirki; yakan kuma sako ruwan sama a bisa masu adalci da marasa adalci. In masoyarku kawai kuke ƙauna, wace lada ce gare ku? Ko masu karɓar haraji ma ba haka suke yi ba? In kuwa kuna gai da ’yan’uwanku ne kaɗai, me kuke yi fiye da waɗansu? Marasa bin Allah ma ba haka suke yi ba? Saboda haka sai ku zama cikakku, yadda Ubanku na sama yake cikakke. “Ku yi hankali kada ku nuna ‘ayyukanku na adalci’ a gaban mutane, don su gani. In kuka yi haka, ba za ku sami lada daga wurin Ubanku da yake cikin sama ba. “Saboda haka sa’ad da kake ba wa masu bukata taimako, kada ka yi shelarsa, yadda munafukai suke yi a majami’u da kuma kan tituna, don mutane su yabe su. Gaskiya nake gaya muku, sun riga sun sami ladarsu cikakke. Amma sa’ad da kake ba wa masu bukata taimako, kada ka yarda hannun hagunka yă ma san abin da hannun damarka yake yi, don bayarwarka ta zama a ɓoye. Ubanka kuwa mai ganin abin da ake yi a ɓoye, zai sāka maka. “Sa’ad da kuma kuke addu’a, kada ku zama kamar munafukai, gama sun cika son yin addu’a a tsaye a cikin majami’u da kuma a bakin titi, don mutane su gan su. Gaskiya nake gaya muku, sun riga sun sami ladarsu cikakke. Amma sa’ad da kake addu’a, sai ka shiga ɗakinka, ka rufe ƙofa, ka yi addu’a ga Ubanka wanda ba a gani. Ubanka kuwa mai ganin abin da ake yi a ɓoye, zai sāka maka. Sa’ad da kuma kuke addu’a, kada ku yi ta maimaita magana, kamar marasa sanin Allah, domin suna tsammani za a ji su saboda yawan maganarsu. Kada ku zama kamar su, gama Ubanku ya san abin da kuke bukata kafin ma ku roƙe shi. “To, ga yadda ya kamata ku yi addu’a. “ ‘Ubanmu wanda yake cikin sama, a tsarkake sunanka, mulkinka yă zo a aikata nufinka a duniya kamar yadda ake yi a sama. Ka ba mu yau abincin yininmu. Ka gafarta mana laifofinmu, kamar yadda mu ma muke gafarta wa masu yin mana laifi. Kada ka bari a kai mu cikin jarraba, amma ka cece mu daga mugun nan. ’ Gama in kuna yafe wa mutane sa’ad da suka yi muku laifi, Ubanku da yake cikin sama ma zai gafarta muku. Amma in ba kwa yafe wa mutane laifofinsu, Ubanku ma ba zai gafarta muku zunubanku ba. “Sa’ad da kuma kuna azumi, kada ku ɓata fuska, yadda munafukai suke yi. Sukan ɓata fuskokinsu domin su nuna wa mutane cewa suna azumi. Gaskiya nake gaya muku, sun riga sun sami ladarsu cikakke. Amma sa’ad da kana azumi, ka shafa wa kanka mai, ka wanke fuskarka, domin kada mutane su ga alama cewa kana azumi, sai dai Ubanka kaɗai wanda ba a gani; Ubanka kuwa mai ganin abin da ake yi a ɓoye, zai sāka maka. “Kada ku yi wa kanku ajiyar dukiya a duniya, inda asu da tsatsa suke ɓatawa, inda kuma ɓarayi sukan fasa, su yi sata. Amma ku yi wa kanku ajiyar dukiya a sama, inda ba tsatsa da asu da za su ɓata su, inda kuma ba ɓarayin da za su fasa, su yi sata. Gama inda dukiyarka take, a nan ne fa zuciyarka za tă kasance. “Ido shi ne fitilar jiki. In idanunka suna da kyau, dukan jikinka zai cika da haske. Amma in idanunka suna da lahani, dukan jikinka ma zai cika da duhu. To, in hasken da yake a cikinka duhu ne, duhun ya wuce misali ke nan! “Ba mai iya bauta wa iyayengiji biyu. Ko dai yă ƙi ɗaya, yă ƙaunaci ɗaya, ko kuwa yă yi aminci ga ɗaya, sa’an nan yă rena ɗayan. Ba dama ku bauta wa Allah, ku kuma bauta wa kuɗi gaba ɗaya.” “Saboda haka, ina gaya muku, kada ku damu game da rayuwarku, game da abin da za ku ci, ko abin da za ku sha; ko kuma game da jikinku, game da abin da za ku sa. Ashe, rai bai fi abinci ba, jiki kuma bai fi tufafi ba? Ku dubi tsuntsayen sararin sama mana; ba sa shuki ko girbi ko ajiya a rumbuna, duk da haka, Ubanku na sama yana ciyar da su. Ashe, ba ku fi su daraja nesa ba? Wane ne a cikinku ta wurin damuwa zai iya ƙara wa rayuwarsa ko sa’a ɗaya? “Me ya sa kuke damuwa a kan riguna? Ku dubi yadda furannin jeji suke girma mana. Ba sa aiki ko saƙa. Duk da haka ina gaya muku ko Solomon cikin dukan darajarsa bai sa kayan adon da ya kai na ko ɗaya a cikinsu ba. In haka Allah yake yi wa ciyawar jeji sutura, wadda yau tana nan, gobe kuwa a jefa a cikin wuta, ba zai ma fi yi muku sutura ba, ya ku masu ƙarancin bangaskiya? Don haka, kada ku damu, kuna cewa, ‘Me za mu ci?’ Ko, ‘Me za mu sha?’ Ko kuma, ‘Me za mu sa?’ Gama marasa sanin Allah suna fama neman dukan waɗannan abubuwa, Ubanku na sama kuwa ya san kuna bukatarsu. Da farko dai, ku nemi mulkin Allah da kuma adalcinsa, za a kuwa ba ku dukan waɗannan abubuwa. Saboda haka kada ku damu game da gobe, gama gobe zai damu da kansa. Damuwar yau ma ta isa wahala. “Kada ku ba wa kowa laifi, don kada a ba ku laifi ku ma. Gama da irin shari’ar da kuka yi wa waɗansu, da ita za a shari’anta ku. Mudun da kuka yi awo da shi, da shi za a yi muku. “Don me kake duban ɗan tsinken da yake idon ɗan’uwanka, alhali kuwa ga gungume a naka ido? Yaya za ka ce wa ɗan’uwanka, ‘Bari in cire maka ɗan tsinken nan daga idonka,’ alhali kuwa a kowane lokaci akwai gungume a naka ido? Kai munafuki, fara cire gungumen da yake idonka, a sa’an nan ne za ka iya gani sosai yadda za ka cire ɗan tsinken da yake a idon ɗan’uwanka. “Kada ku ba karnuka abin da yake mai tsarki; kada kuma ku jefa wa aladu lu’ulu’anku. In kuka yi haka za su tattake su, sa’an nan su juyo su jijji muku ciwo. “Ku roƙa za a ba ku; ku nema za ku samu; ku ƙwanƙwasa za a kuwa buɗe muku ƙofa. Gama duk wanda ya roƙa, akan ba shi; wanda ya nema kuwa, yakan samu, wanda kuma ya ƙwanƙwasa, za a buɗe masa ƙofa. “Wane ne a cikinku in ɗansa ya roƙe shi burodi, sai yă ba shi dutse? Ko kuwa in ya roƙe shi kifi, sai yă ba shi maciji? In ku da kuke mugaye kun san yadda za ku ba da kyautai masu kyau ga ’ya’yanku, balle Ubanku na sama, ba zai fi ku iya ba da abubuwa masu kyau, ga su waɗanda suka roƙe shi ba! Saboda haka, duk abin da kuke so mutane su yi muku, ku ma sai ku yi musu, domin wannan shi ne Doka da koyarwar Annabawa sun ƙunsa. “Ku shiga ta matsattsiyar ƙofa. Gama ƙofar zuwa hallaka faɗaɗɗiya ce mai sauƙin bi kuma, masu shiga ta cikinta kuwa suna da yawa. Amma ƙofar zuwa rai, ƙarama ce matsattsiya kuma, masu samunta kuwa kaɗan ne. “Ku yi hankali da annabawan ƙarya. Sukan zo muku da kamannin tumaki, amma daga ciki mugayen kyarketai ne. Ta wurin aikinsu za ku gane su. Mutane suna iya tsinkan inabi a jikin ƙaya, ko kuwa ɓaure a jikin sarƙaƙƙiya? Haka ma kowane itace mai kyau yakan ba da ’ya’ya masu kyau, kuma mummunan itace ba ya ba da ’ya’ya masu kyau. Itace mai kyau ba ya ba da munanan ’ya’ya, haka kuma mummunan itace ba ya ba da ’ya’ya masu kyau. Duk itacen da ba ya ba da ’ya’ya masu kyau sai a sare shi a jefa cikin wuta. Ta haka, ta wurin aikinsu za ku gane su.” “Ba duk mai ce mini, ‘Ubangiji, Ubangiji,’ ne zai shiga mulkin sama ba, sai dai wanda yake aikata nufin Ubana da yake sama. Da yawa za su ce mini a wannan rana, ‘Ubangiji, Ubangiji, ashe, ba mu yi annabci a cikin sunanka ba, ba kuma a cikin sunanka ne muka fitar da aljanu, muka yi abubuwan banmamaki da yawa ba?’ Sa’an nan zan ce musu a fili, ‘Ban taɓa saninku ba. Ku rabu da ni, ku masu aikata mugunta!’ “Saboda haka duk wanda yake jin kalmomin nan nawa yake kuma aikata su, yana kama da mutum mai hikima wanda ya gina gidansa a kan dutse. Ruwan sama ya sauko, rafuffuka suka cika, iska kuma ta hura ta bugi gidan; duk da haka bai fāɗi ba, gama yana da harsashinsa a kan dutse. Amma duk wanda yake jin kalmomin nan nawa bai kuwa aikata su ba, yana kama da wani wawa wanda ya gina gidansa a kan yashi. Ruwan sama ya sauko, rafuffuka suka cika, iska kuwa ta hura ta bugi gidan, sai ya fāɗi da mummunar ragargajewa kuwa.” Sa’ad da Yesu ya gama faɗin waɗannan abubuwa, sai taron mutanen suka yi mamakin koyarwarsa, domin ya koyar kamar wani wanda yake da iko, ba kamar malamansu na dokoki ba. Da ya sauko daga dutsen, sai taron mutane mai yawan gaske suka bi shi. Wani mutum mai kuturta ya zo ya durƙusa a gabansa ya ce, “Ubangiji, in kana so, kana iya tsabtacce ni.” Yesu ya miƙa hannunsa ya taɓa mutumin. Ya ce, “Ina so, ka tsabtacce!” Nan da nan aka warkar da shi daga kuturtarsa. Sai Yesu ya ce masa, “Ka lura kada ka gaya wa kowa. Sai dai ka tafi, ka nuna kanka ga firist ka kuma yi bayarwar da Musa ya umarta, a matsayin shaida gare su.” Da Yesu ya shiga Kafarnahum, sai wani jarumi ya zo wurinsa, yana neman taimako. Ya ce, “Ubangiji, bawana yana kwance a gida shanyayye, yana kuma shan azaba ƙwarai.” Yesu ya ce masa, “Zan je in warkar da shi.” Jarumin ya amsa, “Ubangiji, ban cancanci in sa ka zo gidana ba, ka dai yi magana kawai, bawana zai warke. Gama ni kaina mutum ne a ƙarƙashin iko, da kuma sojoji a ƙarƙashina. Nakan ce wa wannan, ‘Je ka,’ sai yă tafi; wancan kuma, ‘Zo nan,’ sai yă zo. Nakan ce wa bawana, ‘Yi wannan,’ sai kuwa yă yi.” Da Yesu ya ji wannan, sai ya yi mamaki ya kuma ce wa waɗanda suke binsa, “Gaskiya nake gaya muku, ban taɓa samun wani a Isra’ila da bangaskiya mai girma haka ba. Ina kuma gaya muku da yawa za su zo daga gabas da kuma yamma, su ɗauki wuraren zamansu a biki tare da Ibrahim, Ishaku, da Yaƙub a cikin mulkin sama. Amma za a jefar da ’ya’yan mulki waje, zuwa cikin baƙin duhu, inda za a yi kuka da cizon haƙora.” Sa’an nan Yesu ya ce wa jarumin, “Je ka! Za a yi bisa ga bangaskiyarka.” A daidai wannan lokaci bawansa kuwa ya warke. Da Yesu ya zo cikin gidan Bitrus, sai ya ga surukar Bitrus tana kwance a gado tana da zazzaɓi. Ya taɓa hannunta sai zazzaɓin ya sake ta, ta kuwa tashi ta fara yin masa hidima. Da yamma ta yi, aka kawo masa masu aljanu da yawa, ya kuwa fitar da ruhohin ta wurin magana, ya kuma warkar da dukan marasa lafiya. Wannan ya faru ne domin a cika abin da aka faɗa ta bakin annabi Ishaya cewa, “Ya ɗebi rashin lafiyarmu, ya kuma ɗauki cututtukanmu.” Da Yesu ya ga taron mutane kewaye da shi, sai ya ba da umarni a ƙetare zuwa ɗayan hayin tafkin. Sai wani malamin dokoki ya zo wurinsa ya ce, “Malam, zan bi ka duk inda za ka.” Sai Yesu ya amsa ya ce, “Yanyawa suna da ramummuka, tsuntsayen sararin sama suna da sheƙuna, amma Ɗan Mutum ba shi da wurin da zai sa kansa.” Sai wani almajiri ya ce masa, “Ubangiji, da farko bari in je in binne mahaifina.” Amma Yesu ya ce masa, “Ka bi ni, ka bar matattu su binne matattunsu.” Sai ya shiga jirgin ruwa, almajiransa kuwa suka bi shi. Ba zato ba tsammani, sai wani babban hadari ya taso a tafkin, har raƙuman ruwan suka sha kan jirgin. Amma Yesu yana barci. Almajiran suka je suka tashe shi, suna cewa, “Ubangiji, ka cece mu! Za mu nutse!” Ya amsa ya ce, “Ku masu ƙarancin bangaskiya, me ya sa kuke tsoro haka?” Sa’an nan ya tashi ya tsawata wa iskar da kuma raƙuman ruwan, sai wuri ya yi tsit gaba ɗaya. Mutanen suka yi mamaki suka ce, “Wane irin mutum ne wannan? Har iska da raƙuman ruwa suna masa biyayya!” Da ya isa ɗayan gefen a yankin Gadarenawa (ko kuwa Gerasenawa), sai ga mutum biyu masu aljanu suna fitowa daga kaburbura suka tarye shi. Su abin tsoro ne ƙwarai, har ba mai iya bin wannan hanya. Suka yi ihu suka ce, “Me ya haɗa ka da mu, Ɗan Allah?” Ka zo ne nan don ka ji mana kafin lokaci yă yi? Nesa kaɗan da su kuwa akwai babban garken aladu da yake kiwo. Aljanun suka roƙi Yesu suka ce, “In ka fitar da mu, tura mu cikin garken aladun nan.” Ya ce musu, “Ku tafi!” Sai suka fita suka shiga cikin aladun, dukan garken kuwa ya gangara a guje daga kan tudun zuwa cikin tafkin aladun kuma suka mutu a cikin ruwa. Masu kiwon aladun suka ruga, suka je cikin gari suka ba da labarin dukan wannan, haɗe da abin da ya faru da mutanen nan masu aljanu. Sai dukan garin suka fito don su taryi Yesu. Da suka kuwa gan shi, sai suka roƙe shi yă bar musu yanki. Yesu ya shiga jirgin ruwa, ya ƙetare ya zo garinsa. Waɗansu mutane suka kawo masa wani shanyayye, kwance a tabarma. Da Yesu ya ga bangaskiyarsu, sai ya ce wa shanyayyen, “Kada ka damu saurayi, an gafarta maka zunubanka.” Da jin wannan, waɗansu malaman dokoki suka ce wa juna, “Wannan mutum yana yin saɓo!” Sane da tunaninsu, Yesu ya ce, “Me ya sa kuke da mugun tunani a zuciyarku? Wanne ya fi sauƙi, a ce, ‘An gafarta maka zunubanka,’ ko kuwa a ce, ‘Tashi ka yi tafiya?’ Amma don ku san cewa Ɗan Mutum yana da iko a duniya yă gafarta zunubai.” Sai ya ce wa shanyayyen, “Tashi, ɗauki tabarmarka ka tafi gida.” Mutumin kuwa ya tashi ya tafi gida. Da taron suka ga haka, sai suka cika da tsoro, suka yabi Allah wanda ya ba wa mutane irin ikon nan. Da Yesu ya yi gaba daga wurin, sai ya ga wani mutum mai suna Mattiyu zaune a inda ake karɓar haraji. Ya ce masa, “Bi ni.” Mattiyu kuwa ya tashi ya bi shi. Yayinda Yesu yake cin abinci a gidan Mattiyu, masu karɓar haraji da yawa da kuma masu zunubi suka zo suka kuwa ci tare da shi da kuma almajiransa. Sa’ad da Farisiyawa suka ga haka, sai suka tambayi almajiransa suka ce, “Don me malaminku yake ci tare da masu karɓar haraji, da masu zunubi?” Da jin wannan, Yesu ya ce, “Ai, ba masu lafiya ba ne su bukatar likita, sai dai marasa lafiya. Amma ku je ku koyi abin da wannan yake nufi, ‘Jinƙai nake bukata, ba hadaya ba.’ Gama ban zo domin in kira masu adalci ba, sai dai masu zunubi.” Sai almajiran Yohanna suka zo suka tambaye shi suka ce, “Me ya sa mu da Farisiyawa muke azumi, amma almajiranka ba sa yi?” Yesu ya amsa ya ce, “Yaya baƙin ango za su yi makoki yayinda yake tare da su? Lokaci yana zuwa da za a ɗauke ango daga gare su, sa’an nan za su yi azumi. “Ba mai yin faci da sabon ƙyalle a kan tsohuwar riga, gama facin zai kece rigar yă sa kecewar ma ta fi ta dā muni. Mutane kuma ba sa zuba sabon ruwan inabi a cikin tsofaffin salkuna. In suka yi haka, salkunan za su farfashe, ruwan inabin kuwa yă zube salkunan kuma su lalace. A’a, ai, sukan zuba sabon ruwan inabi ne a cikin sababbin salkuna, don a kiyaye dukan biyun.” Yayinda yake faɗin wannan, sai wani mai mulki ya zo ya durƙusa a gabansa ya ce, “Yanzu-yanzu diyata ta rasu. Amma ka zo ka ɗibiya hannunka a kanta, za tă kuwa rayu.” Yesu ya tashi ya tafi tare da shi, haka ma almajiransa. A daidai wannan lokaci sai ga wata mace wadda ta yi shekaru goma sha biyu tana zub da jini ta raɓo ta bayansa ta taɓa gefen rigarsa. Ta ce a ranta, “Ko da rigarsa ce kawai na taɓo, zan warke.” Yesu ya juya ya gan ta. Sai ya ce, “Kada ki damu diyata, bangaskiyarki ta warkar da ke.” Nan take macen ta warke. Da Yesu ya shiga gidan mai mulkin ya ga masu busan sarewa da taro mai hayaniya, sai ya ce, “Ku ba da wuri. Ai, yarinyar ba tă mutu ba, tana barci ne.” Amma suka yi masa dariya. Bayan an fitar da taron waje, sai ya shiga ciki ya kama yarinyar a hannu, ta kuwa tashi. Labarin wannan kuwa ya bazu ko’ina a yankin. Da Yesu ya fita daga can, sai waɗansu makafi biyu suka bi shi, suna kira, suna cewa, “Ka yi mana jinƙai, Ɗan Dawuda!” Da ya shiga cikin gida, sai makafin nan suka zo wurinsa, ya kuma tambaye su, “Kun gaskata cewa ina iya yin wannan?” Suka amsa suka ce, “I, Ubangiji.” Sa’an nan ya taɓa idanunsu ya ce, “Bisa ga bangaskiyarku a yi muku haka”; sai idanunsu suka buɗe. Yesu ya gargaɗe su sosai ya ce, “Ku lura kada wani yă san wani abu game da wannan.” Amma suka fita suka yi ta baza labari game da shi ko’ina a wannan yankin. Yayinda suke fitowa, sai aka kawo wa Yesu wani mutum mai aljani, da ba ya iya magana. Sa’ad da aka fitar da aljanin kuwa, sai beben ya yi magana. Taron suka yi mamaki suka ce, “Ba a taɓa ganin irin wannan abu a Isra’ila ba.” Amma Farisiyawa suka ce, “Ai, da ikon sarkin aljanu yake fitar da aljanu.” Yesu ya zazzaga dukan garuruwa da ƙauyuka, yana koyarwa a majami’unsu, yana wa’azin labari mai daɗi na mulkin yana kuma warkar da kowace irin cuta da rashin lafiya. Da ya ga taron mutane, sai ya ji tausayinsu, domin an wulaƙanta su ba su kuma da mai taimako, kamar tumaki marasa makiyayi. Sai ya ce wa almajiransa, “Girbi yana da yawa, amma ma’aikata kaɗan ne. Saboda haka ku roƙi Ubangijin girbi, yă aiko da ma’aikata cikin gonarsa na girbi.” Sai ya kira almajiransa goma sha biyu wurinsa ya kuma ba su iko su fitar aljanu, su kuma warkar da kowace irin cuta da rashin lafiya. Ga sunayen manzannin nan goma sha biyu, da fari, Siman (wanda ake kira Bitrus) da ɗan’uwansa Andarawus; Yaƙub ɗan Zebedi da ɗan’uwansa Yohanna; Filibus da Bartolomeyu; Toma da Mattiyu mai karɓar haraji; Yaƙub ɗan Alfayus da Taddayus; Siman Zilot da kuma Yahuda Iskariyot wanda ya bashe Yesu. Waɗannan sha biyun ne Yesu ya aika da umarni cewa, “Kada ku je cikin Al’ummai, ko kuwa ku shiga wani garin Samariyawa. A maimakon haka ku je wajen ɓatattun tumakin Isra’ila. Sa’ad da kuke tafiya, ku yi wa’azi, kuna cewa, ‘Mulkin sama ya kusato.’ Ku warkar da marasa lafiya, ku tā da matattu, ku tsabtacce kutare, ku kuma fitar da aljanu. A kyauta kuka samu, ku kuma bayar a kyauta. “Kada ku riƙe wata zinariya ko azurfa ko jan ƙarfe a aljihunanku, kada ku ɗauki jaka don tafiya, ko ƙarin riga, ko takalma ko sanda; domin ma’aikaci ya cancanci hakkinsa. Kowane gari ko ƙauyen da kuka shiga, ku nemi mai mutunci a wurin, ku kuma zauna a gidansa har sai kun tashi. Da shigarku gidan, ku yi gaisuwa. In gidan na kirki ne, bari salamarku ta zauna a kansa; in kuwa ba mai kirki ba, salamarku ta komo muku. Duk wanda ya ƙi marabtarku ko ya ƙi sauraron kalmominku, sai ku karkaɗe ƙurar ƙafafunku sa’ad da kuka fita gidan ko garin. Gaskiya nake gaya muku, za a fi jin tausayin Sodom da Gomorra a ranar shari’a fiye da wannan gari. “Ina aikan ku kamar tumaki a cikin kyarketai. Saboda haka ku zama masu wayo kamar macizai, kuma marasa ɓarna kamar kurciyoyi. Ku yi hankali da mutane; za su miƙa ku ga majalisa su kuma yi muku bulala a majami’unsu. Saboda ni, za a ja ku zuwa gaban gwamnoni da gaban sarakuna domin ku ba da shaida a gabansu, da kuma ga Al’ummai. Amma sa’ad da suka kama ku, kada ku damu game da abin da za ku faɗa ko kuwa yadda za ku faɗe shi. A lokacin za a ba ku abin da za ku faɗa, gama ba ku ba ne kuke magana, amma Ruhun Ubanku ne yake magana ta wurinku. “Ɗan’uwa zai ci amanar ɗan’uwansa, a kuma kashe shi, Uba ma zai yi haka da ɗansa; ’ya’ya za su tayar wa iyayensu, su kuma sa a kashe su. Dukan mutane za su ƙi ku saboda ni, amma wanda ya jure har ƙarshe zai sami ceto. Sa’ad da aka tsananta muku a wannan wuri, ku gudu zuwa wancan. Gaskiya nake gaya muku, kafin ku gama zazzaga dukan biranen Isra’ila, Ɗan Mutum zai zo. “Ɗalibi ba ya fin malaminsa, haka ma, bawa ba ya fin maigidansa. Ya isa wa ɗalibi yă zama kamar malaminsa, haka ma bawa kamar maigidansa. In har an kira wanda yake kan gida Be’elzebub, me za su ce game da mutanen gidansa? “Saboda haka kada ku ji tsoronsu. Ba abin da yake a rufe da ba za a tone ba, ko kuwa a ɓoye da ba za a bayyana ba. Abin da na faɗa muku a asirce, ku faɗe shi a sarari; abin da aka faɗa muku a kunne, ku yi shelarsa daga kan rufin ɗaki. Kada ku ji tsoron masu kashe jiki amma ba sa iya kashe rai. A maimakon haka, ku ji tsoron Wannan wanda yake da iko yă hallaka rai duk da jiki a jahannama ta wuta. Ba akan sayar da kanari biyu kobo ɗaya ba? Duk da haka ba ɗayansu da zai fāɗi ƙasa ba da yardar Ubanku. Kai, ko gashin kanku ma duk an ƙidaya su. Saboda haka kada ku ji tsoro; kun fi kanari masu yawa, daraja nesa. “Duk wanda ya bayyana yarda a gare ni a gaban mutane, ni ma zan bayyana yarda a gare shi a gaban Ubana da yake cikin sama. Amma duk wanda ya yi mūsun sani na a gaban mutane, ni ma zan yi mūsun saninsa a gaban Ubana da yake cikin sama. “Kada fa ku ɗauka na zo ne don in kawo salama a duniya. A’a, ban zo don in kawo salama ba, sai dai takobi. Gama na zo ne in sa, “ ‘gāba tsakanin mutum da mahaifinsa, ’ya da mahaifiyarta, matar ɗa da surukarta, abokan gāban mutum, za su zama mutanen gidansa ne.’ “Duk wanda ya fi ƙaunar mahaifinsa ko mahaifiyarsa fiye da ni, bai dace yă zama nawa ba; duk kuwa wanda yake ƙaunar ɗansa ko diyarsa fiye da ni, bai dace yă zama nawa ba; duk wanda kuma bai ɗauki gicciyensa ya bi ni ba, bai dace yă zama nawa ba. Duk mai son adana ransa zai rasa shi, duk wanda kuwa ya rasa ransa saboda ni zai same shi. “Wanda ya karɓe ku, ya karɓe ni ne, wanda kuma ya karɓe ni, ya karɓi wanda ya aiko ni ne. Duk wanda ya karɓi annabi don shi annabi ne, zai sami ladar annabi, duk kuwa wanda ya karɓi mutum mai adalci don shi mai adalci ne, zai sami ladar mai adalci. In kuma wani ya ba wa ɗaya daga cikin ƙananan nan ko da kwaf ruwan sanyi ne kan shi almajirina ne, gaskiya nake gaya muku, ba shakka ba zai rasa ladarsa ba.” Bayan Yesu ya gama yi wa almajiransa sha biyun nan umarni, sai ya yi gaba daga can don yă koyar yă kuma yi wa’azi a garuruwan Galili. Sa’ad da Yohanna Mai Baftisma ya ji a kurkuku abin da Kiristi yake yi, sai ya aiki almajiransa su tambaye shi, “Kai ne wanda zai zo, ko kuwa mu sa ido ga wani?” Yesu ya amsa ya ce, “Ku koma ku gaya wa Yohanna abin da kuka ji, kuka kuma gani. Makafi suna gani, guragu suna tafiya, ana warkar da waɗanda suke da kuturta, kurame suna ji, ana tā da matattu, ana kuma yi wa matalauta wa’azin labari mai daɗi. Mai albarka ne mutumin da bai yi tuntuɓe ba saboda ni.” Sa’ad da almajiran Yohanna suke barin wurin, sai Yesu ya fara yi wa taron magana game da Yohanna. “Me kuka je kallo a hamada? Ciyawar da iska take kaɗawa ne? In ba haka ba, to, me kuka je kallo? Mutum mai sanye da riguna masu kyau ne? A’a, masu sa riguna masu kyau, ai, a fadan sarakuna suke. To, me kuka je kallo ne? Annabi? I, ina gaya muku, ya ma fi annabi. Wannan shi ne wanda aka rubuta game da shi cewa, “ ‘Zan aiki ɗan saƙona yă sha gabanka, wanda zai shirya hanyarka a gabanka.’ Gaskiya nake gaya muku. A cikin dukan waɗanda mata suka haifa, ba wani da ya taso da ya fi Yohanna Mai Baftisma girma; duk da haka mafi ƙanƙanta a mulkin sama ya fi shi girma. Tun daga kwanakin Yohanna Mai Baftisma har yă zuwa yanzu, mulkin sama yana sha da ƙyar, fitanannu kuma sun kama mulkin sama sun riƙe gam. Gama dukan Annabawa da kuma Doka sun yi ta annabci har yă zuwa kan Yohanna. In kuna niyya ku yarda da wannan, to, shi ne Iliya da dā ma zai zo. Duk mai kunnen ji, yă ji. “Da me zan kwatanta wannan zamani? Suna kama da yara da suke zaune a kasuwa, suna kiran juna, suna cewa, “ ‘Mun yi muku busa, ba ku kuwa yi rawa ba, mun rera waƙar makoki, ba ku kuwa yi makoki ba.’ Gama Yohanna Mai Baftisma ya zo ba ya ciye-ciye, ba ya shaye-shaye, sai suka ce, ‘Ai, yana da aljani.’ Ɗan Mutum ya zo yana ciye-ciye, yana shaye-shaye, sai suka ce, ‘Ga mai haɗama da kuma mashayi, abokin masu karɓar haraji da masu zunubi.’ Amma akan tabbatar da hikima ta wurin ayyukanta.” Sai Yesu ya fara yin tir da biranen da aka yi yawancin ayyukansa na banmamaki, don ba su tuba ba. “Kaitonki, Korazin! Kaitonki, Betsaida! Da a ce ayyukan banmamakin da aka yi a cikinki ne aka yi a Taya da Sidon, da tuni sun tuba sanye da rigar makoki da toka. Amma ina gaya muku, za a fi jin tausayin Taya da Sidon a ranar shari’a, fiye da ku. Ke kuma Kafarnahum, za a ɗaga ki sama ne? A’a, za ki gangara zuwa zurfafa ne. Da a ce ayyukan banmamakin da aka yi a cikinki ne a aka yi a Sodom, da tana nan har yă zuwa yau. Amma ina gaya miki, za a fi jin tausayin Sodom fiye da ke a ranar shari’a.” A wannan lokaci sai Yesu ya ce, “Ina yabonka, Uba, Ubangijin sama da ƙasa, gama ka ɓoye waɗannan abubuwa ga masu hikima da masu ilimi, ka kuma bayyana su ga ƙananan yara. I, Uba, gama wannan shi ne abin da ka ji daɗin yi. “Dukan kome Ubana ya danƙa mini. Ba wanda ya san Ɗan sai dai Uban, ba kuma wanda ya san Uban, sai dai Ɗan da kuma waɗanda Ɗan ya so yă bayyana musu shi. “Ku zo gare ni, dukanku da kuka gaji kuke kuma fama da kaya, zan kuwa ba ku hutu. Ku ɗauki karkiyata a kanku, ku kuma yi koyi da ni, gama ni mai tawali’u ne marar girman kai, za ku kuwa sami hutu don rayukanku. Gama karkiyata mai sauƙi ce, kayana kuma marasa nauyi ne.” A lokacin nan Yesu ya bi ta gonakin hatsi a ranar Asabbaci. Almajiransa kuwa suna jin yunwa, sai suka fara kakkarya kan hatsi suna ci. Sa’ad da Farisiyawa suka ga wannan, sai suka ce masa, “Duba! Almajiranka suna yin abin da doka ta hana a yi a ranar Asabbaci.” Sai ya amsa ya ce, “Ba ku karanta abin da Dawuda ya yi ba ne sa’ad da shi da abokan tafiyarsa suka ji yunwa? Ya shiga gidan Allah, da shi da abokan tafiyarsa suka ci keɓaɓɓen burodin, wanda doka ta hana su yi, sai firistoci kaɗai. Ko kuwa ba ku karanta a Doka cewa a ranar Asabbaci firistoci sukan karya dokar Asabbaci duk da haka ba da yin wani laifi ba? Ina faɗa muku cewa wani wanda ya fi haikali yana a nan. Da a ce kun san abin da waɗannan kalmomi suke nufi, ‘Jinƙai nake bukata, ba hadaya ba,’ da ba ku zargi marar laifi ba. Gama Ɗan Mutum shi ne Ubangijin Asabbaci.” Da ya ci gaba daga wurin, sai ya shiga majami’arsu, a nan kuwa akwai wani mutum mai shanyayyen hannu. Don neman dalili su zargi Yesu, sai suka tambaye shi suka ce, “Ya dace a warkar a ranar Asabbaci?” Ya ce musu, “In waninku yana da tunkiya, ta kuma fāɗa a rami ran Asabbaci, ba zai cire ta daga ramin ba? Sau nawa mutum ya fi tunkiya daraja! Saboda haka ya dace a aikata alheri ran Asabbaci.” Sa’an nan ya ce wa mutumin, “Miƙa hannunka.” Sai ya miƙa, hannunsa kuwa ya koma lafiyayye, kamar dai ɗayan. Amma Farisiyawa suka fita suka ƙulla shawara yadda za su kashe Yesu. Da ya gane wannan, sai Yesu ya janye daga wurin. Da yawa suka bi shi, ya kuwa warkar da dukan masu ciwonsu, yana jan musu kunne kada su faɗa wa kowa akan ko shi wane ne. Wannan kuwa domin a cika abin da aka faɗa ta bakin annabi Ishaya ne cewa, “Ga bawana da na zaɓa, ƙaunataccena, wanda nake farin ciki da shi; zan sa Ruhuna a kansa, zai kuma yi shelar adalci ga al’ummai. Ba zai yi faɗa ko yă ɗaga murya ba, ba kuwa wanda zai ji muryarsa a kan tituna. Kyauron da ya tanƙwasa ba zai karye shi ba. Fitilar da ta yi kusan mutuwa ba zai kashe ta ba, sai ya jagoranci adalci zuwa ga nasara. Cikin sunansa al’ummai za su dogara.” Sai aka kawo masa wani bebe kuma makaho mai aljani, Yesu kuwa ya warkar da shi, har ya iya magana ya kuma sami ganin gari. Dukan mutane suka yi mamaki, suka ce, “Wannan Ɗan Dawuda ne kuwa?” Amma da Farisiyawa suka ji haka, sai suka ce, “Ahab, da Be’elzebub sarkin aljanu ne kaɗai, wannan mutum yake fitar da aljanu.” Yesu kuwa ya san tunaninsu sai ya ce musu, “Duk mulkin da yake gāba da kansa zai lalace, kuma duk birni ko gidan da yake rabe gāba da kansa ba zai ɗore ba. In Shaiɗan yana fitar da Shaiɗan, ai, ya rabu yana gāba da kansa ke nan. Yaya kuwa mulkinsa zai ɗore? In kuwa ta wurin Be’elzebub nake fitar da aljanu, to, ta wa mutanenku suke fitar da su? Saboda haka, su ne za su zama alƙalanku. Amma in ina fitar da aljanu ta wurin Ruhun Allah ne, to, fa, mulkin Allah ya zo muku ke nan. “Ko kuwa, yaya wani zai iya shiga gidan mai ƙarfi yă ƙwace masa kaya ba tare da ya fara daure mai ƙarfin nan tukuna ba? Sa’an nan zai iya washe gidansa. “Wanda ba ya tare da ni, yana gāba da ni ne, kuma wanda ba ya taya ni tarawa, watsarwa yake yi. Saboda haka ina gaya muku, za a gafarta wa mutane kowane zunubi da kuma saɓo, amma saɓo game da Ruhu, ba za a gafarta ba. Duk wanda ya zargi Ɗan Mutum, za a gafarta masa, amma duk wanda ya zargi Ruhu Mai Tsarki, ba za a gafarta masa ba, ko a wannan zamani ko a zamani mai zuwa. “Itace mai kyau, yakan ba da ’ya’ya masu kyau. Itace marar kyau kuma, yakan ba da ’ya’ya marasa kyau. Itace dai, da irin ’ya’yansa ne ake gane shi. Ku macizai, ta yaya ku da kuke mugaye za ku iya magana kirki? Gama daga baki, mutum yakan faɗi abin da yake cikin zuciya. Mutumin kirki yakan fito da abubuwa masu kyau daga ajiyar da aka a yi cikinsa, mugun mutum kuwa yakan fito da mugayen abubuwa daga cikin muguntar da aka yi ajiya a cikinsa. Amma ina gaya muku cewa mutane za su ba da lissafi a ranar shari’a a kan kowace kalmar banza da suka faɗa. Gama ta wurin kalmominka za a kuɓutar da kai, kuma ta wurin kalmominka za a hukunta ka.” Sa’an nan waɗansu Farisiyawa da malaman dokoki suka ce masa, “Malam, muna so mu ga wata alama mai banmamaki daga gare ka.” Sai ya amsa ya ce, “Mugaye da masu zinan zamanin nan suna neman wata alama mai banmamaki! Amma babu wadda za a nuna musu, sai dai alama ta annabi Yunana. Gama kamar yadda Yunana ya yi yini uku da kuma dare uku a cikin wani babban kifi, haka Ɗan Mutum zai yi yini uku da kuma dare uku a cikin ƙasa. Mutanen Ninebe za su tashi a ranar shari’a tare da wannan zamani, su kuwa hukunta shi; don sun tuba saboda wa’azin Yunana, yanzu kuwa ga wanda ya fi Yunana girma a nan. Sarauniyar Sheba za tă tashi a ranar shari’a tare da wannan zamani, tă kuwa hukunta shi; don ta zo daga ƙarshen duniya, ta saurari hikimar Solomon, yanzu kuwa ga wanda ya fi Solomon girma a nan. “Sa’ad da mugun ruhu ya fita daga mutum, yakan bi wuraren da ba ruwa yana neman hutu, ba ya kuwa samu. Sa’an nan yakan ce, ‘Zan koma gidan da na bari.’ Sa’ad da ya iso, ya tarar da gidan ba kowa a ciki, shararre, kuma a kintse. Sai yă je yă ɗebo waɗansu ruhohi bakwai da suka fi shi mugunta, su kuwa zo su shiga su zauna a can. Ƙarshen mutumin nan fa zai fi farkonsa muni. Haka zai zama ga wannan mugun zamani.” Yayinda Yesu yake cikin magana da taron, sai ga mahaifiyarsa da ’yan’uwansa tsaye a waje, suna so su yi magana da shi. Wani ya ce masa, “Mahaifiyarka da ’yan’uwanka suna tsaye a waje, suna so su yi magana da kai.” Ya amsa masa ya ce, “Wace ce mahaifiyata, su wane ne kuma ’yan’uwana?” Sai ya miƙa hannu wajen almajiransa ya ce, “Ga mahaifiyata da kuma ’yan’uwana. Ai, duk wanda yake aikata nufin Ubana wanda yake cikin sama, shi ne ɗan’uwana da ’yar’uwata da kuma mahaifiyata.” A ranan nan sai Yesu ya fita daga gida ya je ya zauna a bakin tafkin. Taron mutane mai yawan gaske suka taru kewaye da shi har ya kai sai da ya shiga jirgin ruwa ya zauna, yayinda dukan mutane suka tsaya a gaci. Sa’an nan ya faɗa musu abubuwa da yawa cikin misalai, yana cewa, “Wani manomi ya fita don yă shuka irinsa. Da yana yafa irin, waɗansu suka fāffāɗi a kan hanya, tsuntsaye kuwa suka zo suka cinye su. Waɗansu suka fāɗi a wurare mai duwatsu, inda babu ƙasa sosai, nan da nan kuwa suka tsira, da yake ƙasar ba zurfi. Sai dai da rana ta ɗaga, sai tsire-tsiren suka ƙone, suka kuma yanƙwane domin ba su da saiwa sosai. Waɗansu irin suka fāɗi a cikin ƙaya, ƙayan kuwa ta yi girma ta shaƙe su. Har yanzu, waɗansu irin suka fāffāɗi a ƙasa mai kyau, inda suka ba da amfani riɓi ɗari, sittin ko kuma talatin na abin da aka shuka. Duk mai kunnen ji, yă ji.” Almajiran suka zo wurinsa suka tambaye shi, “Me ya sa kake wa mutane magana da misalai?” Ya amsa ya ce, “Sanin asirin mulkin sama kam, ku aka ba wa, amma su ba a ba su ba. Duk wanda yake da shi, za a ƙara masa, zai kuwa samu a yalwace. Duk wanda kuma ba shi da shi, ko ɗan abin da yake da shi ma, za a karɓe. Abin da ya sa nake musu magana da misalai ke nan. “Ko da yake suna kallo, ba sa gani; ko da yake suna saurara, ba sa ji ko su gane. A kansu ne aka cika annabcin Ishaya cewa, “ ‘Za ku yi ta ji amma ba za ku taɓa ganewa ba; za ku yi ta kallo amma ba za ku taɓa gani ba. Gama zuciyar mutanen nan ta taurare; da ƙyar suke ji da kunnuwansu, sun kuma rufe idanunsu. Da ba haka ba, mai yiwuwa su gani da idanunsu, su kuma ji da kunnuwansu, su gane a zuciyarsu, su kuwa juya, in kuma warkar da su.’ Amma idanunku masu albarka ne domin suna gani, haka ma kunnuwanku domin suna ji. Gama gaskiya nake gaya muku, annabawa da mutane masu adalci da yawa sun yi marmarin ganin abin da kuke gani amma ba su gani ba, su kuma ji abin da kuke ji amma ba su ji ba. “To, ku saurari ma’anar misali na mai shukan nan. Duk sa’ad da wani ya ji saƙo game da mulkin bai kuwa fahimce shi ba, mugun nan yakan zo yă ƙwace abin da aka shuka a zuciyarsa. Wannan shi ne irin da ya fāɗi a kan hanya. Wanda ya karɓi irin da ya fāɗi a wuraren duwatsu kuwa, shi ne mutumin da yakan ji maganar, nan da nan kuwa yă karɓe ta da murna. Sai dai da yake ba shi da saiwa, yakan ɗan jima kaɗan kawai. Da wata wahala ko tsanani ya auko masa saboda maganar, nan da nan sai yă ja da baya. Wanda ya karɓi irin da ya fāɗi cikin ƙaya kuwa, shi ne mutumin da yakan ji maganar, sai dai damuwoyin rayuwan nan da jarrabar arzikin duniya sukan shaƙe shi, yă sa maganar ta kāsa amfani. Amma wanda ya karɓi irin da ya fāɗi a ƙasa mai kyau, shi ne mutumin da yakan ji maganar yă kuwa fahimce ta. Yakan ba da amfani wani riɓi ɗari, sittin, ko talatin na abin da aka shuka.” Yesu ya ba su wani misali. “Mulkin sama yana kama da wani da ya shuka iri mai kyau a cikin gonarsa. Amma yayinda kowa yake barci, abokin gābansa ya zo ya yafa ciyayi a cikin alkamar, ya tafi abinsa. Sa’ad da alkamar ta tashi ta yi kawuna, sai ciyayin ma suka bayyana. “Bayin mai gonar suka zo wurinsa suka ce, ‘Ranka yă daɗe, ashe, ba iri mai kyau ka shuka a gonarka ba? To, ina ciyayin nan suka fito?’ “Sai ya ce, ‘Abokin gāba ne ya yi wannan.’ “Bayin suka tambaye shi suka ce, ‘Kana so mu je mu tuttumɓuke su?’ “Ya amsa ya ce, ‘A’a, don kada garin tuttumɓuke ciyayi, ku cire har da alkamar. Ku ƙyale su su yi girma tare sai lokacin girbi. A lokacin zan gaya wa masu girbi, da fari ku tara ciyayin ku kuma daure su dami-dami don a ƙone; sa’an nan ku tara alkamar ku kuma kawo su cikin rumbuna.’ ” Ya ba su wani misali ya ce, “Mulkin sama yana kama da ƙwayar mustad, wadda mutum ya ɗauka ya shuka a gonarsa. Ko da yake ita ce mafi ƙanƙanta cikin ƙwayoyinku, duk da haka sa’ad da ta yi girma, takan zama mafi girma cikin tsire-tsiren lambu ta kuma zama itace, har tsuntsayen sararin sama su zo su yi sheƙa a rassansa.” Har yanzu ya ba su wani misali ya ce, “Mulkin sama yana kama da yisti wanda mace ta ɗauka ta kwaɓa garin alkama mai yawa, har sai da yistin ya gauraye yistin duka.” Yesu ya faɗa wa taron dukan waɗannan abubuwa cikin misalai; bai faɗa musu kome ba, sai tare da yin amfani da misalai. Ta haka aka cika abin da aka faɗa ta wurin annabi cewa, “Zan buɗe bakina da misalai, zan faɗi abubuwan da suke ɓoye tun halittar duniya.” Sa’an nan ya bar taron ya shiga gida. Almajiransa kuwa suka zo wurinsa suka ce, “Bayyana mana misalin ciyayin nan a gona.” Ya amsa ya ce, “Mai yafa irin mai kyan nan, shi ne Ɗan Mutum. Gonar kuwa ita ce duniya, irin nan mai kyau kuwa suna a matsayin ’ya’yan mulkin. Ciyayin nan kuma su ne ’ya’yan mugun nan, abokin gāban da yake shuka su kuwa, Iblis ne. Lokacin girbi kuma shi ne ƙarshen zamani, masu girbin kuwa su ne mala’iku. “Kamar yadda aka tattara ciyayin aka kuma ƙone a wuta, haka zai zama a ƙarshen zamani. Ɗan Mutum zai aiki mala’ikunsa, su kuwa cire daga mulkinsa kome da yake jawo zunubi da kuma duk masu aikata mugunta. Za su jefa su cikin wuta mai zafi, inda za a yi kuka da cizon haƙora. Sa’an nan masu adalci za su haskaka kamar rana a mulkin Ubansu. Duk mai kunnen ji, yă ji.” “Mulkin sama yana kama da dukiyar da aka ɓoye a gona. Da wani ya same ta, sai yă sāke ɓoye ta, sa’an nan cikin farin cikinsa yă je yă sayar da duk abin da yake da shi yă sayi gonar. “Har wa yau dai, mulkin sama yana kama da ɗan kasuwa mai neman lu’ulu’ai masu kyau. Da ya sami dutse guda mai daraja sosai, sai ya tafi ya sayar da dukan abin da yake da shi ya saye shi. “Har yanzu, mulkin sama yana kama da abin kamun kifin da aka jefa cikin tafki yă kamo kifi iri-iri. Da abin kamun kifi ya cika, masuntan suka jawo shi gaci. Sai suka zauna suka tattara kifi masu kyau a kwanduna, amma suka zubar da marasa kyau. Haka zai kasance a ƙarshen zamani. Mala’iku za su zo su ware masu mugunta daga masu adalci su kuma jefa su cikin wuta mai zafi, inda za a yi kuka da cizon haƙora.” Yesu ya tambaye su ya ce, “Kun gane dukan waɗannan abubuwa?” Suka amsa, “I.” Sa’an nan ya ce musu, “Saboda haka duk malamin dokokin da ya horu game da koyarwar mulkin sama, yana kama da maigida wanda yakan fitar daga ɗakin ajiyarsa sababbin dukiya da kuma tsofaffi.” Sa’ad da Yesu ya gama ba da waɗannan misalai, sai ya ci gaba daga can. Yana isowa garinsa, sai ya fara koya wa mutane a cikin majami’arsu, suka kuwa yi mamaki. Suka yi ta tambaya suna cewa, “Ina wannan mutum ya sami irin wannan hikima da kuma ayyukan banmamaki haka? Wannan ba shi ne ɗan kafinta nan ba? Ba mahaifiyarsa ba ce Maryamu, ’yan’uwansa kuma Yaƙub, Yusuf, Siman da Yahuda ba? Duk ’yan’uwansa mata kuma ba tare da mu suke ba? To, a ina wannan mutum ya sami dukan waɗannan abubuwa?” Sai suka ji haushinsa. Amma Yesu ya ce musu, “Sai a garinsa da kuma a gidansa na kaɗai annabi ba ya samun girma.” Bai kuwa yi abubuwan banmamaki da yawa a can ba saboda rashin bangaskiyarsu. A lokacin nan sarki Hiridus ya ji labarin Yesu, sai ya ce wa fadawansa, “Wannan Yohanna Mai Baftisma ne; ya tashi daga matattu! Shi ya sa abubuwan banmamakin nan suke faruwa ta wurinsa.” To, dā Hiridus ya kama Yohanna ya daure, ya kuma sa shi cikin kurkuku saboda Hiridiyas, matar ɗan’uwansa Filibus, gama Yohanna ya dinga ce masa, “Ba daidai ba ne ka aure ta.” Hiridus ya so yă kashe Yohanna, amma yana jin tsoron mutane, don sun ɗauka shi annabi ne. A bikin tuna da ranar haihuwar Hiridus, diyar Hiridiyas ta yi musu rawa ta kuma gamsar da Hiridus ƙwarai, har ya yi alkawari da rantsuwa cewa zai ba ta duk abin da ta roƙa. Da mahaifiyarta ta zuga ta, sai ta ce, “Ba ni a cikin kwanon nan, kan Yohanna Mai Baftisma.” Sarki ya yi baƙin ciki, amma saboda rantsuwarsa da kuma baƙinsa, sai ya ba da umarni a ba ta abin da ta roƙa ya kuma sa aka yanke kan Yohanna a kurkuku. Aka kawo kansa cikin kwano aka ba yarinyar, ita kuma ta kai wa mahaifiyarta. Almajiran Yohanna suka zo suka ɗauki gawarsa suka binne. Sa’an nan suka je suka gaya wa Yesu. Sa’ad da Yesu ya ji abin da ya faru, sai ya shiga jirgin ruwa ya janye shi kaɗai zuwa wani wuri inda ba kowa. Da jin haka, taron mutane suka bi shi da ƙafa daga garuruwa. Da Yesu ya sauka ya kuma ga taro mai yawa, sai ya ji tausayinsu ya kuma warkar da marasa lafiyarsu. Da yamma ta yi, sai almajiransa suka zo wurinsa suka ce, “Wurin nan fa ba kowa, ga shi kuma rana ta kusa fāɗuwa. Ka sallami taron don su shiga ƙauyuka su nemi wa kansu abinci.” Yesu ya amsa, “Ba su bukata su tafi. Ku ku ba su wani abu su ci.” Suka ce, “Burodi biyar da kifi biyu ne kawai muke da su a nan.” Ya ce, “Ku kawo mini su a nan.” Sai ya umarci mutanen su zazzauna a kan ciyawa. Da ya ɗauki burodi biyar da kifin biyun nan ya dubi sama, ya yi godiya ya kuma kakkarya burodin. Sa’an nan ya ba wa almajiransa, almajiran kuwa suka ba wa mutane. Duk suka ci suka ƙoshi, almajiran kuwa suka kwashe ragowar gutsattsarin cike da kwanduna goma sha biyu. Yawan waɗanda suka ci, sun yi wajen maza dubu biyar, ban da mata da yara. Nan da nan Yesu ya sa almajiran su shiga jirgin ruwa su sha gabansa, su haye zuwa ɗayan hayin, yayinda shi kuma yă sallami taron. Bayan ya sallame su, sai ya haura bisan gefen dutse shi kaɗai don yă yi addu’a. Da yamma ta yi, yana can shi kaɗai, jirgin ruwan kuwa ya riga ya yi nesa da gaci, yana fama da raƙuman ruwa domin iska tana gāba da shi. Wajen tsaro na huɗu na dare, sai Yesu ya nufe su, yana takawa a kan tafkin. Sa’ad da almajiran suka gan shi yana takawa a kan tafkin, sai tsoro ya kama su. Suka yi ihu don tsoro suka ce, “Fatalwa ce.” Amma nan da nan Yesu ya ce musu, “Ku yi ƙarfin hali! Ni ne. Kada ku ji tsoro.” Sai Bitrus ya amsa ya ce, “Ubangiji in kai ne ka ce mini in zo wurinka a kan ruwan.” Ya ce, “Zo.” Sai Bitrus ya fita daga jirgin ruwan, ya taka a kan ruwan ya nufe wajen Yesu. Amma da ya ga haukar iskar, sai ya ji tsoro, ya kuma fara nutsewa, sai ya yi ihu ya ce, “Ubangiji, ka cece ni!” Nan da nan Yesu ya miƙa hannu ya kamo shi ya ce, “Kai mai ƙarancin bangaskiya, don me ka yi shakka?” Da suka hau jirgin ruwan, sai iskar ta kwanta. Waɗanda suke cikin jirgin ruwan kuwa suka yi masa sujada, suna cewa, “Gaskiya kai Ɗan Allah ne.” Sa’ad da suka haye, sai suka sauka a Gennesaret. Da mutanen wurin suka gane da Yesu, sai suka kai labari a ko’ina a ƙauyukan da suke kewaye. Mutane suka kawo masa dukan marasa lafiyarsu suka kuwa roƙe shi yă bar marasa lafiya su taɓa ko da gefen rigarsa kawai, duk waɗanda suka taɓa shi kuwa suka warke. Sa’an nan waɗansu Farisiyawa da malaman dokoki suka zo wurin Yesu daga Urushalima suka yi tambaya suka ce, “Me ya sa almajiranka suke karya al’adun dattawa? Ba sa wanke hannuwansu kafin su ci abinci!” Yesu ya amsa ya ce, “Ku ma me ya sa kuke karya dokar Allah saboda al’adarku? Gama Allah ya ce, ‘Ka girmama mahaifinka da mahaifiyarka, kuma duk wanda ya zagi mahaifinsa ko mahaifiyarsa dole a kashe shi.’ Amma ku kukan ce, in wani ya ce wa mahaifinsa ko mahaifiyarsa, ‘Duk taimakon da dā ya kamata za ku samu daga gare ni an ba wa Allah,’ ba zai ‘girmama mahaifinsa’ da shi ba. Ta haka kun yi banza da maganar Allah saboda al’adarku. Ku munafukai! Daidai ne Ishaya ya yi annabci a kanku da ya ce, “ ‘Waɗannan mutane da baki kawai suke girmama ni, amma zukatansu suna nesa da ni. A banza suke mini sujada, koyarwarsu, dokoki ne kawai da mutane suke koyarwa.’ ” Sai Yesu ya kira taron wurinsa ya ce, “Ku saurara ku kuma gane. Abin da yake shiga bakin mutum ba ya ƙazantar da shi, sai dai abin da yake fitowa daga bakinsa, shi ne yake ƙazantar da shi.” Sai almajiran suka zo wurinsa suka ce, “Ka san cewa Farisiyawa ba su ji daɗi sa’ad da suka ji wannan ba?” Ya amsa ya ce, “Duk tsiron da Ubana na sama bai shuka ba, za a tumɓuke shi daga saiwoyi. Ku ƙyale su, ai, makafin jagorai ne. In makaho ya yi wa makaho jagora, dukansu za su fāɗa a rami.” Bitrus ya ce, “Ka bayyana mana wannan misali.” Yesu ya tambaye su ya ce, “Har yanzu ba ku gane ba ne? Ba ku gane cewa duk abin da ya shiga baki yakan wuce ciki ne daga nan kuma yă fita daga jiki ba? Amma abubuwan da suke fitowa ta baki suna fitowa ne daga zuciya, su ne kuma suke ƙazantar da mutum. Gama daga zuciya ne mugayen tunani, kisankai, zina, fasikanci, sata, shaidar ƙarya, ɓatan suna, suka fitowa. Waɗannan su ne suke ƙazantar da mutum; amma cin abinci ba tare da wanke hannuwa ba, ba ya ƙazantar da mutum.” Barin wurin ke nan, sai Yesu ya janye zuwa yankin Taya da Sidon. Wata mutuniyar Kan’ana daga wajajen ta zo wurinsa, tana ihu tana cewa, “Ubangiji, Ɗan Dawuda, ka yi mini jinƙai! ’Yata tana shan wahala ƙwarai daga aljanin da yake cikinta.” Yesu bai ce mata uffam ba. Saboda haka almajiransa suka zo wurinsa suka roƙe shi suka ce, “Ka kore ta tă tafi, tana ta binmu tana damunmu da ihu.” Ya amsa ya ce, “An aiko ni wurin ɓatattun tumakin Isra’ila ne kaɗai.” Sai macen ta zo ta durƙusa a gabansa ta ce, “Ubangiji, ka taimake ni!” Ya amsa ya ce, “Ba daidai ba ne a ɗauki abincin yara a jefa wa karnukansu.” Ta amsa, ta ce, “I, Ubangiji, amma karnuka ma sukan ci gutsattsarin da sukan fāɗi daga teburin maigidansu.” Sa’an nan Yesu ya amsa ya ce, “Mace, kina da bangaskiya mai yawa! An biya miki bukatarki.” ’Yarta kuwa ta warke nan take. Yesu ya tashi daga nan ya bi ta gefen Tekun Galili. Sa’an nan ya haura gefen wani dutse ya zauna. Taron mutane mai girma kuwa suka zo wurinsa, suna kawo masa guragu, makafi, shanyayyu, kurame da dai waɗansu da yawa, suka kuwa kwantar da su a gabansa; ya kuma warkar da su. Mutanen kuwa suka yi mamaki sa’ad da suka ga kurame suna magana, shanyayyu suna samun lafiya, guragu suna takawa, makafi kuma suna ganin gari. Sai suka yabi Allah na Isra’ila. Yesu ya kira almajiransa wurinsa ya ce, “Ina jin tausayin mutanen nan; gama kwana uku ke nan suke tare da ni ba abin da za su ci. Ba na so in sallame su da yunwa, don kada su kāsa a hanya.” Sai almajiransa suka amsa suka ce, “Ina za mu sami isashen burodi a wannan wurin da babu kowa mu ciyar da irin taron nan?” Yesu ya tambaye su, “Burodi guda nawa kuke da shi?” Suka amsa suka ce, “Guda bakwai da ’yan ƙananan kifaye.” Ya sa taron su zazzauna a ƙasa. Sa’an nan ya ɗauki burodi guda bakwai da kuma kifayen nan, da ya yi godiya, sai ya kakkarya su ya ba wa almajiran, su kuma suka ba wa mutane. Duk kuwa suka ci, suka ƙoshi. Daga baya almajiran suka kwashe ragowar gutsattsarin cike da kwanduna bakwai. Yawan waɗanda suka ci kuwa, maza dubu huɗu ne, ban da mata da yara. Bayan Yesu ya sallami taron, sai ya shiga jirgin ruwa ya tafi wajajen Magadan. Farisiyawa da Sadukiyawa suka zo don su gwada Yesu ta wurin neman yă nuna musu wata alama daga sama. Ya amsa ya ce, “Sa’ad da yamma ta yi, kukan ce, ‘Yanayi zai yi kyau, gama sararin sama ya yi ja,’ da safe kuma, ku ce, ‘Yau kam za a yi hadari, gama sararin sama ya yi ja, ya kuma ɓata fuska.’ Kun san yadda za ku fassara yanayin sararin sama, amma ba kwa iya fassarar alamun lokuta. Wannan mugu da mazinacin zamani yana neman wani abin banmamaki, amma ba wata alamar da za a nuna wa wannan zamani sai dai ta Yunana.” Sai Yesu ya bar su ya tafi abinsa. Da suka ƙetare tafkin, almajiran sun manta su riƙe burodi. Yesu ya ce musu, “Ku yi hankali, ku yi taka zallan da yistin Farisiyawa da Sadukiyawa.” Sai suka fara tattaunawa da junansu suna cewa, “Ko don ba mu kawo burodi ba ne.” Sane da abin da suke zance, sai Yesu ya ce, “Ku masu ƙarancin bangaskiya, don me kuke magana da junanku a kan ba ku zo da burodi ba? Har yanzu ba ku gane ba ne? Ba ku tuna da gurasa biyar ɗin nan na mutum dubu biyar ba? Kwando nawa kuka tattara cike? Ko kuma burodi bakwai nan na mutum dubu huɗu, cikakku manyan kwanduna nawa kuka ɗauka? Yaya kuka kāsa gane cewa ba zancen burodi nake yi ba? Sai dai ku yi hankali da yistin Farisiyawa da Sadukiyawa.” Sa’an nan suka gane ba cewa yake musu su yi hankali da yistin da ake amfani da shi a burodi ba ne, sai dai su yi hankali da koyarwar Farisiyawa da Sadukiyawa ne. Sa’ad da Yesu ya zo yankin Kaisariya Filibbi, sai ya tambayi almajiransa ya ce, “Wa mutane suke ce da Ɗan Mutum?” Suka amsa, “Waɗansu suna ce Yohanna Mai Baftisma; waɗansu kuma suna ce annabi Iliya; har wa yau waɗansu suna ce Irmiya ne ko kuma ɗaya daga cikin annabawa.” Ya tambaye su, “Amma ku fa, wane ne ni a ganinku?” Siman Bitrus ya amsa ya ce, “Kai ne Kiristi, Ɗan Allah mai rai.” Yesu ya amsa ya ce, “Mai albarka ne kai Siman ɗan Yunana, gama ba mutum ne ya bayyana maka wannan ba, sai dai Ubana da yake cikin sama. Ina kuwa gaya maka, kai ne Bitrus, a kan wannan dutse zan gina ikkilisiyata, kuma ƙofofin Hades ba za su rinjaye ta ba. Zan ba ka mabuɗan mulkin sama; kome ka daure a duniya zai zama a daure a sama, kome kuma ka kunce a duniya zai zama a kunce a sama.” Sa’an nan ya gargaɗe almajiransa cewa kada su faɗa wa kowa shi ne Kiristi. Tun daga wannan lokaci Yesu ya fara bayyana wa almajiransa cewa dole yă tafi Urushalima yă sha wahaloli da yawa a hannun dattawa, manyan firistoci da kuma malaman dokoki, dole a kashe shi, a rana ta uku kuma a tashe shi. Bitrus ya ja shi gefe ya fara tsawata masa yana cewa, “Sam, Ubangiji! Wannan ba zai taɓa faruwa da kai ba!” Yesu ya juya ya ce wa Bitrus, “Rabu da ni, Shaiɗan! Kai abin sa tuntuɓe ne a gare ni; ba ka tunanin al’amuran Allah, sai dai al’amuran mutane.” Sa’an nan Yesu ya ce wa almajiransa, “Duk mai son bina, dole yă ƙi kansa, yă ɗauki gicciyensa, yă bi ni. Gama duk mai son ceton ransa zai rasa shi, amma duk wanda ya rasa ransa saboda ni, zai same shi. Me mutum zai amfana in ya sami duniya duka, amma ya rasa ransa? Ko kuwa me mutum zai bayar a bakin ransa? Gama Ɗan Mutum zai zo cikin ɗaukakar Ubansa, tare da mala’ikunsa, sa’an nan zai ba wa kowane mutum lada gwargwadon abin da ya yi. “Gaskiya nake gaya muku, akwai waɗansu da suke tsaitsaye a nan da ba za su mutu ba sai sun ga Ɗan Mutum yana zuwa cikin mulkinsa.” Bayan kwana shida, sai Yesu ya ɗauki Bitrus, Yaƙub da Yohanna ɗan’uwan Yaƙub, ya kai su kan wani dutse mai tsawo, su kaɗai. A can aka sāke kamanninsa a gabansu. Fuskarsa ta haskaka kamar rana, tufafinsa kuwa suka zama fari fat suna walƙiya. Nan take sai ga Musa da Iliya suka bayyana a gabansu, suna magana da Yesu. Sai Bitrus ya ce wa Yesu, “Ubangiji, ya yi kyau da muke nan. In kana so, sai in kafa bukkoki uku, ɗaya dominka, ɗaya domin Musa, ɗaya kuma domin Iliya.” Yayinda yake cikin magana, sai wani girgije mai haske ya rufe su, sai wata murya daga cikin girgijen ta ce, “Wannan Ɗana ne, wanda nake ƙauna; wanda kuma nake jin daɗinsa ƙwarai. Ku saurare shi!” Sa’ad da almajiran suka ji haka, sai suka fāɗi ƙasa rubda ciki, a firgice. Amma Yesu ya zo ya taɓa su ya ce, “Ku tashi, kada ku ji tsoro.” Da suka ɗaga kai, ba su ga kowa ba sai Yesu kaɗai. Suna cikin gangarowa daga dutsen ke nan, sai Yesu ya umarce su cewa, “Kada ku faɗa wa kowa abin da kuka gani, sai bayan an tā da Ɗan Mutum daga matattu.” Almajiran suka tambaye shi suka ce, “To, me ya sa malaman dokoki suke cewa, dole sai Iliya ya fara zuwa?” Yesu ya amsa ya ce, “Tabbatacce, Iliya zai zo, zai kuma gyara dukan abubuwa. Amma ina faɗa muku, Iliya ya riga ya zo, ba su kuwa gane shi ba, amma suka yi masa duk abin da suka ga dama. Haka ma Ɗan Mutum zai sha wahala a hannunsu.” Sa’an nan almajiran suka gane cewa yana musu zancen Yohanna Mai Baftisma ne. Da suka isa wajen taron, sai wani mutum ya zo ya durƙusa a gabansa. Ya ce, “Ubangiji, ka yi wa ɗana jinƙai. Yana da farfaɗiya yana kuma shan wahala ƙwarai. Ya sha fāɗuwa cikin wuta ko ruwa. Na kuma kawo shi wurin almajiranka, amma ba su iya warkar da shi ba.” Yesu ya amsa ya ce, “Ya ku zamani marasa bangaskiya da kuma masu taurinkai, har yaushe zan kasance tare da ku? Har yaushe kuma zan yi haƙuri da ku? Kawo mini yaron a nan.” Yesu ya tsawata wa aljanin, ya kuwa rabu da yaron, nan take yaron ya warke. Sa’an nan almajiran suka zo wurin Yesu a ɓoye suka tambaye shi suka ce, “Me ya sa ba mu iya fitar da aljanin ba?” Ya amsa ya ce, “Saboda kuna da ƙarancin bangaskiya sosai. Gaskiya nake gaya muku, in kuna da bangaskiyar da take ƙanƙanuwa kamar ƙwayar mustad, za ku iya ce wa wannan dutse, ‘Matsa daga nan zuwa can,’ zai kuwa matsa. Babu abin da zai gagare ku.” Da suka taru a Galili, sai ya ce musu, “Za a bashe Ɗan Mutum, a hannun mutane. Za su kashe shi, a rana ta uku kuma za a tashe shi.” Almajiran kuwa suka cika da baƙin ciki. Bayan Yesu da almajiransa suka isa Kafarnahum, sai masu karɓan harajin rabin shekel suka zo wurin Bitrus suka ce, “Malaminku ba ya biyan harajin haikali ne?” Ya amsa ya ce “I, yana biya.” Da Bitrus ya shiga gida, Yesu ne ya fara magana. Ya ce masa, “Me ka gani, Siman? Daga wurin wane ne sarakunan duniya suke karɓar kuɗin shiga da kuma haraji, daga wurin ’ya’yansu ne ko kuwa daga wurin waɗansu?” Bitrus ya amsa ya ce, “Daga wurin waɗansu.” Yesu ya ce masa, “Wato, an ɗauke wa ’ya’yan ke nan. Amma don kada mu ɓata musu rai, ka je tafki ka jefa ƙugiyarka. Ka ɗauki kifin da ka fara kama; ka buɗe bakinsa, za ka sami shekel guda. Ka kawo ka ba su, harajina da naka ke nan.” A lokacin nan sai almajirai suka zo wurin Yesu suka yi tambaya suka ce, “Wane ne mafi girma a mulkin sama?” Sai ya kira ƙaramin yaro ya sa shi yă tsaya a tsakiyarsu. Sai ya ce, “Gaskiya nake gaya muku, in ba kun canja kuka zama kamar ƙananan yara ba, labudda, ba za ku shiga mulkin sama ba. Saboda haka, duk wanda ya ƙasƙantar da kansa kamar wannan yaro, shi ne mafi girma a mulkin sama. Duk kuma wanda ya karɓi ƙaramin yaro kamar wannan a cikin sunana ya karɓe ni ne. “Amma duk wanda ya sa ɗaya daga cikin ƙananan nan da suka gaskata da ni ya yi zunubi, zai fiye masa a rataya babban dutsen niƙa a wuyarsa, a kuma nutsar da shi a zurfin teku. Kaiton duniya saboda abubuwan da suke sa mutane su yi zunubi! Dole irin waɗannan abubuwa su zo, sai dai kaiton mutumin da ya zama sanadin kawo su! In hannunka ko ƙafarka yana sa ka zunubi, yanke shi ka yar. Zai fiye maka ka shiga rai da hannu ko ƙafa ɗaya da hannuwa biyu ko ƙafafu biyu da a jefar da kai cikin madawwamiyar wuta da hannuwa biyu ko ƙafafu biyu. In kuma idonka yana sa ka zunubi, ƙwaƙule shi ka yar. Zai fiye maka ka shiga rai da ido ɗaya, da ka shiga jahannama ta wuta da idanunka biyu. “Ku lura, kada ku rena ɗaya daga cikin waɗannan ƙanana. Gama ina faɗa muku mala’ikunsu a sama kullum suna duban fuskar Ubana da yake cikin sama. “Me kuka gani? In wani yana da tumaki ɗari, sai ɗaya daga cikinsu ta ɓace, ba sai yă bar tasa’in da taran a kan tuddai yă je neman guda ɗayan da ta ɓace ba? In kuwa ya same ta, ina gaya muku gaskiya, zai yi murna saboda ɗayan fiye da tasa’in da taran da ba su ɓace ba. Haka ma Ubanku da yake cikin sama ba ya so ko ɗaya daga cikin ƙananan nan yă ɓace. “In ɗan’uwanka ya yi maka laifi, ka je ka nuna masa laifinsa, tsakaninku biyu kaɗai. In ya saurare ka, ka maido da ɗan’uwanka ke nan. Amma in bai saurare ka ba, ka je tare da mutum ɗaya ko biyu, domin ‘a tabbatar da kowace magana a bakin shaidu biyu ko uku.’ In kuwa ya ƙi yă saurare su, sai ka gaya wa ikkilisiya; in kuma ya ƙi yă saurari ikkilisiya ma, ka yi da shi kamar marar sanin Allah ko mai karɓar haraji. “Gaskiya nake gaya muku, duk abin da kuka daure a duniya, za a daure a sama, duk kuma abin da kuka kunce a duniya, za a kunce shi a sama. “Har wa yau, ina gaya muku cewa in mutum biyu a cikinku a duniya suka yarda su roƙi wani abu, Ubana da yake cikin sama zai yi muku. Gama inda mutum biyu ko uku suka taru cikin sunana, a can ma ina tare da su.” Sai Bitrus ya zo wurin Yesu ya yi masa tambaya ya ce, “Ubangiji, sau nawa zan yafe wa ɗan’uwana sa’ad da ya yi mini zunubi? Har sau bakwai?” Yesu amsa ya ce, “Ina gaya maka, ba sau bakwai ba, amma sau saba’in da bakwai. “Saboda haka, mulkin sama yana kama da wani sarki wanda ya so yă yi ƙididdigar dukiyarsa da take a hannun bayinsa. Da ya fara ƙididdigar, sai aka kawo masa wani wanda yake bin bashin talenti dubu goma. Da yake bai iya biya ba, sai maigida ya umarta a sayar da shi da matarsa da yaransa da kuma duk abin da yake da shi, a biya bashin. “Bawan ya durƙusa a gabansa. Ya yi roƙo ya ce, ‘Ka yi mini haƙuri, zan biya ka ƙaf.’ Maigidan bawan ya ji tausayinsa, ya yafe masa bashin, ya kuma sake shi. “Amma da wannan bawa ya fita, sai ya gamu da wani abokin bautarsa wanda yake binsa bashin dinari ɗari. Sai ya cafke shi, ya shaƙe shi a wuya yana cewa, ‘Biya ni abin da nake binka!’ “Wannan abokin bautarsa ya durƙusa ya roƙe shi, ‘Ka yi mini haƙuri, zan biya ka.’ “Amma ya ƙi. A maimako, sai ya je ya sa aka jefa shi a kurkuku, har yă biya bashin. Sa’ad da sauran bayin suka ga abin da ya faru, abin ya ɓata musu rai ƙwarai, sai suka tafi suka faɗa wa maigidansu dukan abin da ya faru. “Sai maigidan ya kira wannan bawa. Ya ce, ‘Kai mugun bawa, na yafe duk bashin da nake binka domin ka roƙe ni. Ashe, bai kamata kai ma ka ji tausayin abokin bautarka yadda na yi maka ba?’ Cikin fushi, maigidan ya miƙa shi ga ma’aikatan kurkuku su gwada masa azaba, har yă biya dukan bashin da ake binsa. “Haka Ubana da yake cikin sama zai yi da kowannenku, in ba ku yafe wa ’yan’uwanku daga zuciyarku ba.” Sa’ad da Yesu ya gama faɗin waɗannan abubuwa, sai ya bar Galili, ya tafi yankin Yahudiya a ɗaya gefen Urdun. Taron mutane mai yawa suka bi shi, ya kuwa warkar da su a can. Waɗansu Farisiyawa suka zo wurinsa don su gwada shi. Suka yi tambaya suka ce, “Daidai ne mutum yă saki matarsa saboda wani dalili da kuma a kan kowane dalili?” Ya amsa ya ce, “Ba ku taɓa karantawa ba ne cewa, a farkon halitta, Mahalicci ‘ya yi su namiji da ta mace,’ ya kuma ce, ‘Saboda wannan dalili, namiji zai bar mahaifinsa da mahaifiyarsa yă manne wa matarsa, biyun kuwa su zama jiki guda’? Ta haka, ba sa ƙara zama biyu, sai dai ɗaya. Saboda haka abin da Allah ya haɗa fa, kada mutum yă raba.” Suka yi tambaya, suka ce, “To, me ya sa Musa ya umarta cewa mutum yă ba wa matarsa takardar saki, yă kuma kore ta?” Yesu ya amsa ya ce, “Musa ya ba ku izini ku saki matanku saboda taurin zuciyarku ne. Amma ba haka yake ba daga farko. Ina faɗa muku cewa duk wanda ya saki matarsa, sai dai a kan rashin aminci a cikin aure, ya kuwa auri wata, ya yi zina ke nan.” Almajiran suka ce masa, “In haka yake tsakanin miji da mata, ashe, ya ma fi kyau kada a yi aure.” Yesu ya ce, “Ba kowa ba ne zai yarda da wannan magana, sai dai waɗanda aka yarda musu. Gama waɗansu bābānni ne domin haka aka haife su; waɗansu kuwa mutane ne suka mai da su haka; waɗansu kuma sun ƙi aure ne saboda mulkin sama. Duk mai iya ɗaukar wannan yă ɗauka.” Sa’an nan aka kawo yara ƙanana wurin Yesu don yă ɗibiya musu hannuwansa, yă kuma yi musu addu’a. Amma almajirai suka tsawata wa waɗanda suka kawo su. Yesu ya ce, “Ku bar yara ƙanana su zo wurina, kada ku hana su, gama mulkin sama na irin waɗannan ne.” Sa’ad da ya ɗibiya musu hannuwansa, sai ya tafi abinsa. To, fa, sai ga wani ya zo wurin Yesu ya tambaye shi ya ce, “Malam, wane abu mai kyau ne ya zama mini dole in yi don in sami rai madawwami?” Yesu ya amsa ya ce, “Don me kake tambayata game da abin da yake mai kyau? Akwai Mai kyau Ɗaya kaɗai. In kana so ka sami rai madawwami, ka kiyaye dokokin nan.” Mutumin ya yi tambaya ya ce, “Waɗanne?” Yesu ya amsa ya ce, “ ‘Kada ka yi kisankai, kada ka yi zina, kada ka yi sata, kada ka yi shaidar ƙarya, ka girmama mahaifinka da mahaifiyarka,’ ka kuma ‘ƙaunaci maƙwabcinka kamar kanka.’ ” Saurayin ya ce, “Duk waɗannan na kiyaye. Me kuma ya rage mini?” Yesu ya amsa ya ce, “In kana so ka zama cikakke, ka je, ka sayar da dukan dukiyarka ka kuma ba matalauta, za ka kuwa sami dukiya a sama. Sa’an nan ka zo, ka bi ni.” Da saurayin ya ji haka, sai ya tafi rai a ɓace, don yana da arziki sosai. Sa’an nan Yesu ya ce wa almajiransa, “Gaskiya nake gaya muku, yana da wuya mai arziki yă shiga mulkin sama. Har wa yau ina gaya muku, zai fi sauƙi raƙumi yă shiga ta kafar allura, da mai arziki yă shiga mulkin Allah.” Sa’ad da almajiran suka ji wannan, sai suka yi mamaki ƙwarai. Suka yi tambaya suka ce, “To, wa zai sami ceto ke nan?” Yesu ya kalle su ya ce, “Ga mutum kam, wannan ba ya yiwuwa, amma ga Allah kuwa, dukan abubuwa masu yiwuwa ne.” Sai Bitrus ya amsa masa, “Ga shi mun bar kome don mu bi ka! Me za mu samu ke nan?” Yesu ya ce musu, “Gaskiya nake gaya muku, a lokacin sabunta dukan kome, sa’ad da Ɗan Mutum ya zauna a kan kursiyinsa mai daraja, ku da kuka bi ni, ku ma za ku zauna a kan kursiyoyi goma sha biyu, kuna yi wa kabilu goma sha biyu na Isra’ila shari’a. Duk kuma wanda ya bar gidaje ko ’yan’uwa maza ko ’yan’uwa mata ko mahaifi ko mahaifiya ko yara ko gonaki, saboda ni, zai sami abin da ya fi haka riɓi ɗari, yă kuma gāji rai madawwami. Amma da yawa da suke na farko, za su zama na ƙarshe, da yawa kuma da suke na ƙarshe, za su zama na farko. “Mulkin sama yana kama da wani mai gona, wanda ya fita da sassafe don yă yi hayar mutane su yi aiki a gonar inabinsa. Ya yarda yă biya su dinari guda a yini, sai ya tura su gonar inabinsa. “Wajen sa’a ta uku, ya fita sai ya ga waɗansu suna tsattsaye a bakin kasuwa ba sa kome. Ya ce musu, ‘Ku ma ku tafi gonar inabina ku yi aiki, zan kuwa biya ku abin da ya dace.’ Saboda haka suka tafi. “Ya sāke fita a sa’a ta shida da kuma sa’a ta tara, ya sāke yin haka. Wajen sa’a ta goma sha ɗaya, ya sāke fita, ya tarar da waɗansu har yanzu suna tsattsaye. Ya tambaye su, ‘Don me kuke yini tsattsaye a nan ba kwa kome?’ “Suka amsa, ‘Don ba wanda ya ɗauke mu aiki.’ “Ya ce musu, ‘Ku ma ku je ku yi aiki a gonar inabina.’ “Sa’ad da yamma ta yi, sai mai gonar inabin ya ce wa wakilinsa, ‘Kira ma’aikatan, ka biya su hakkin aikinsu, fara daga waɗanda aka ɗauke su a ƙarshe har zuwa na farko.’ “Ma’aikatan da ka ɗauka wajen sa’a ta goma sha ɗaya suka zo, kowannensu kuwa ya karɓi dinari guda. Saboda haka da waɗanda aka ɗauka da fari suka zo, sun zaci za su sami fiye da haka. Amma kowannensu ma ya karɓi dinari guda. Sa’ad da suka karɓa, sai suka fara yin gunaguni a kan mai gonar. Suna cewa, ‘Waɗannan mutanen da aka ɗauka a ƙarshe sun yi aikin sa’a ɗaya ne kawai, ka kuma mai da su daidai da mu da muka yini muna faman aiki, muka kuma sha zafin rana.’ “Amma ya amsa wa ɗayansu ya ce, ‘Aboki, ban cuce ka ba. Ba ka yarda ka yi aiki a kan dinari guda ba? Ka karɓi hakkinka ka tafi. Ni na ga damar ba waɗannan na ƙarshe daidai da yadda na ba ka. Ba ni da ikon yin abin da na ga dama da kuɗina ne? Ko kana kishi saboda ni mai kyauta ne?’ “Saboda haka fa, na ƙarshe za su zama na farko, na farko kuma su zama na ƙarshe.” To, da Yesu yana haurawa zuwa Urushalima, sai ya ja almajiran nan goma sha biyu gefe, ya ce musu, “Za mu haura zuwa Urushalima, za a kuma bashe Ɗan Mutum ga manyan firistoci da malaman dokoki. Za su yi masa hukuncin kisa za su kuma bashe shi ga Al’ummai su yi masa ba’a, su yi masa bulala, su kuma gicciye shi. A rana ta uku kuma a tashe shi!” Sai mahaifiyar ’ya’yan Zebedin nan ta zo wurin Yesu tare da ’ya’yanta, da ta durƙusa a ƙasa, sai ta roƙe shi yă yi mata wani abu. Ya yi tambaya ya ce, “Mene ne kike so?” Ta ce, “Ka sa daga cikin ’ya’yan nan nawa biyu, ɗaya yă zauna a damarka, ɗaya kuma a hagunka, a mulkinka.” Yesu ya ce musu, “Ba ku san abin da kuke roƙo ba. Za ku iya sha daga kwaf da zan sha?” Suka amsa, “Za mu iya.” Yesu ya ce musu, “Tabbatacce za ku sha daga kwaf na, sai dai zama a damana, ko haguna, ba ni nake da izinin bayarwa ba. Waɗannan wurare na waɗanda Ubana ya shirya wa ne.” Da goman suka ji haka, sai suka yi fushi da ’yan’uwan nan biyu. Yesu ya kira su wuri ɗaya ya ce, “Kun san cewa masu mulkin Al’ummai sukan nuna musu iko, hakimansu kuma sukan gasa musu iko. Ba haka zai kasance da ku ba. Maimakon haka, duk mai son zama babba a cikinku, dole yă zama bawanku, kuma duk mai son zama shugaba, dole yă zama bawanku, kamar yadda Ɗan Mutum bai zo don a bauta masa ba, sai dai don yă yi bauta, yă kuma ba da ransa fansa saboda mutane da yawa.” Sa’ad da Yesu da almajiransa suke barin Yeriko, sai wani babban taro ya bi shi. Makafi biyu kuwa suna zaune a bakin hanya, da suka ji cewa Yesu yana wucewa, sai suka ɗaga murya suka ce, “Ubangiji, Ɗan Dawuda, ka ji tausayinmu!” Mutane suka tsawata musu, suka ce musu su yi shiru. Sai suka ƙara ɗaga murya suna cewa, “Ubangiji, Ɗan Dawuda, ka ji tausayinmu!” Yesu ya tsaya ya kira su. Ya tambaye su, “Me kuke so in yi muku?” Suka amsa suka ce, “Ubangiji, muna so mu sami ganin gari.” Sai Yesu ya ji tausayinsu, ya taɓa idanunsu. Nan da nan kuwa suka sami ganin gari, suka kuma bi shi. Da suka yi kusa da Urushalima suka kuma kai Betfaji da yake kan Dutsen Zaitun, sai Yesu ya aiki almajirai biyu, yana ce musu, “Ku je ƙauyen da yake gabanku, nan take za ku ga wata jaka a daure tare da ɗanta kusa da ita, a can. Ku kunce su ku kawo mini. In wani ya yi muku wata magana, ku ce masa Ubangiji yana bukatarsu, zai kuwa mai da su nan da nan.” Wannan ya faru ne don a cika abin da aka faɗa ta bakin annabin cewa, “Ku ce wa Diyar Sihiyona, ‘Duba, sarkinki yana zuwa gare ki, mai tawali’u yana a kan jaki, a kan aholaki, ɗan jaki.’ ” Almajiran suka tafi suka yi kamar yadda Yesu ya umarce su. Suka kawo jakar da ɗanta, suka shimfiɗa mayafansu a kansu, Yesu kuma ya zauna a kansu. Wani babban taron mutane suka shimfiɗa mayafansu a kan hanya, yayinda waɗansu suka sassari rassan itatuwa suka shisshimfiɗa a kan hanya. Taron mutanen da suke gabansa da kuma waɗanda suke binsa a baya suka yi ihu suna cewa, “Hosanna ga Ɗan Dawuda!” “Mai albarka ne wanda yake zuwa cikin sunan Ubangiji!” “Hosanna a cikin sama!” Sa’ad da Yesu ya shiga Urushalima, dukan birnin ya ruɗe, ana ta tambaya, “Wane ne wannan?” Taron mutane suka amsa, “Wannan shi ne Yesu, annabin nan daga Nazaret a Galili.” Yesu ya shiga filin haikali, ya kuma kori duk masu saya da sayarwa a can. Ya tutture tebur masu canjin kuɗi da kuma kujerun masu sayar da tattabarai. Ya ce musu, “A rubuce yake, ‘Za a ce da gidana, gidan addu’a,’ amma kuna mai da shi ‘kogon ’yan fashi.’ ” Makafi da guragu suka zo wurinsa a haikali, ya kuwa warkar da su. Amma da manyan firistoci da malaman dokoki suka ga abubuwan banmamakin da ya yi, yara kuma suna ihu a filin haikali suna cewa, “Hosanna ga Ɗan Dawuda,” sai fushi ya kama su. Suka tambaye shi suka ce, “Kana jin abin da waɗannan suke faɗa?” Yesu ya amsa ya ce, “I, ba ku taɓa karanta ba cewa, “ ‘Daga leɓunan yara da jarirai kai, Ubangiji, ka shirya wa kanka yabo’?” Sai ya bar su, ya fita daga birnin ya tafi Betani, inda ya kwana. Kashegari da sassafe, yayinda yake kan hanyarsa ta komawa cikin birni, sai ya ji yunwa. Ganin itacen ɓaure kusa da hanya, sai ya je wajensa amma bai sami kome a kansa ba sai ganye. Sai ya ce masa, “Kada ka ƙara yin ’ya’ya!” Nan da nan itacen ya yanƙwane. Sa’ad da almajiran suka ga haka, sai suka yi mamaki suna tambaya, “Yaya itacen ɓauren ya yanƙwane nan da nan haka?” Yesu ya amsa ya ce, “Gaskiya nake gaya muku, in kuna da bangaskiya, ba kuwa da wata shakka ba, ba kawai za ku iya yin abin da aka yi wa itacen ɓauren nan ba, amma za ku ma iya ce wa dutsen nan, ‘Je ka, ka jefa kanka cikin teku,’ sai yă faru. In kun gaskata, za ku karɓi duk abin da kuka roƙa a cikin addu’a.” Sai Yesu ya shiga filin haikali, yayinda yake koyarwa, sai manyan firistoci da dattawan mutane suka zo wurinsa suka yi tambaya, “Da wane iko kake yin waɗannan abubuwa? Kuma wa ya ba ka wannan iko?” Yesu ya amsa ya ce, “Ni ma zan yi muku tambaya guda. In kuka ba ni amsa, ni ma zan gaya muku ko da wane iko nake yin waɗannan abubuwa. Baftismar Yohanna, daga ina ta fito? Daga sama ce, ko daga mutane?” Sai suka tattauna a junansu suka ce, “In muka ce, ‘Daga sama,’ zai ce, ‘To, me ya sa ba mu gaskata shi ba?’ In kuma muka ce, ‘Daga mutane,’ muna tsoron mutane, gama duk sun ɗauka Yohanna annabi ne.” Saboda haka suka amsa wa Yesu suka ce, “Ba mu sani ba.” Sai ya ce, “Ni ma ba zan gaya muku ko da wane iko nake yin waɗannan abubuwa ba.” “Me kuka gani? An yi wani mutum wanda yake da ’ya’ya biyu maza. Sai ya je wajen ɗan farin ya ce, ‘Ɗana, yau tafi gonar inabi ka yi aiki.’ “Ya amsa ya ce, ‘Ba zan tafi ba,’ amma daga baya ya sāke tunani, ya tafi. “Sai mahaifin ya tafi waje na biyun ya faɗa masa iri magana guda. Sai ya amsa ya ce, ‘Zan tafi, ranka yă daɗe,’ amma bai tafi ba. “Wanne cikin yaran nan biyu ya yi abin da mahaifinsa yake so?” Suka amsa, “Na farin.” Yesu ya ce musu, “Gaskiya nake gaya muku, masu karɓar haraji da karuwai suna riga ku shiga mulkin Allah. Gama Yohanna Mai Baftisma ya zo wurinku don yă nuna muku hanyar adalci, ba ku gaskata shi ba, amma masu karɓar haraji da karuwai sun gaskata. Har ma bayan kun ga wannan, ba ku tuba kun gaskata shi ba.” “Ku saurari wani misali. An yi wani mai gona wanda ya yi gonar inabi. Ya kewaye ta da katanga, ya haƙa wurin matsin inabi a ciki, ya kuma gina hasumiyar gadi. Sa’an nan ya ba wa waɗansu manoma hayar gonar inabin, ya kuma yi tafiya. Da lokacin girbi ya yi kusa, sai ya aiki bayinsa wajen ’yan hayan, su karɓo masa ’ya’yan inabi. “Amma ’yan hayan suka kama bayinsa; suka dūke ɗaya, suka kashe ɗaya, suka kuma jajjefi na ukun. Sai ya sāke aiken waɗansu bayi wurinsu, fiye da na dā yawa, amma ’yan hayan suka yi musu kamar yadda suka yi wa na farin. A ƙarshe, sai ya aiki ɗansa a wurinsu. Ya ce, ‘Za su girmama ɗana.’ “Amma da ’yan hayan suka hangi ɗan, sai suka ce wa juna, ‘Wannan shi ne magājin. Ku zo, mu kashe shi, mu ci gādonsa.’ Saboda haka suka kama shi, suka jefar da shi bayan katangar gonar inabin, suka kashe shi. “To, idan mai gonar inabin ya zo, me zai yi da ’yan hayan nan?” Suka amsa suka ce, “Zai yi wa banzan mutanen nan mugun kisa, yă ba da hayar gonar inabin ga waɗansu ’yan haya, waɗanda za su ba shi rabonsa na amfanin gona a lokacin girbi.” Yesu ya ce musu, “Ashe, ba ku taɓa karanta a cikin Nassi cewa, “ ‘Dutsen da magina suka ƙi shi ne ya zama dutsen kusurwar gini. Ubangiji ne ya aikata wannan, kuma abin mamaki ne a idanunmu’? “Saboda haka, ina gaya muku cewa za a karɓe mulkin Allah daga gare ku, a ba wa mutanen da za su ba da amfani. Duk wanda ya fāɗi a kan dutsen nan, zai kakkarye. Amma duk wanda dutsen nan ya fāɗi a kansa, za a murƙushe shi.” Da manyan firistoci da Farisiyawa suka ji misalan Yesu, sai suka gane cewa da su yake. Suka nemi hanyar kama shi, amma suka ji tsoron taron, don mutane sun ɗauka shi annabi ne. Yesu ya sāke yin musu magana da misalai, yana cewa, “Mulkin sama yana kama da wani sarki wanda ya shirya bikin auren ɗansa. Sai ya aiki bayinsa su kira waɗanda aka gayyata zuwa bikin, amma waɗanda aka ce su zo bikin, suka ƙi zuwa. “Sai ya sāke aiken waɗansu bayi ya ce, ‘Ku ce wa waɗanda aka gayyata cewa na shirya abinci. An yanka bijimai da shanun da aka yi kiwo, kome a shirye yake. Ku zo bikin auren mana.’ “Amma ba su kula ba, suka kama gabansu, ɗaya ya tafi gonarsa, ɗaya kuma ya tafi kasuwancinsa. Sauran suka kama bayinsa suka wulaƙanta su, suka kuma kashe su. Sai sarkin ya yi fushi. Ya aiki mayaƙansa suka karkashe masu kisankan nan, aka kuma ƙone birninsu. “Sa’an nan ya ce wa bayinsa, ‘Bikin aure fa ya shiryu, sai dai mutanen da na gayyata ba su dace ba. Ku bi titi-titi ku gayyato duk waɗanda kuka gani, su zo bikin.’ Saboda haka bayin suka bi titi-titi, suka tattaro duk mutanen da suka samu, masu kirki da marasa kirki, zauren bikin ya cika makil da baƙi. “Amma da sarkin ya shigo don yă ga baƙin, sai ya ga wani can da ba ya sanye da kayan auren. Ya yi tambaya ya ce, ‘Aboki, yaya ka shigo nan ba tare da rigar aure ba?’ Mutumin ya rasa ta cewa. “Sai sarkin ya ce wa fadawa, ‘Ku daure shi hannu da ƙafa, ku jefar da shi waje, cikin duhu, inda za a yi kuka da cizon haƙora.’ “Gama kirayayu da yawa, amma zaɓaɓɓu kaɗan ne zaɓaɓɓu.” Sai Farisiyawa suka yi waje, suka ƙulla yadda za su yi masa tarko cikin maganarsa. Suka aiki almajiransu tare da mutanen Hiridus wurinsa. Suka ce, “Malam, mun san kai mutum ne mai mutunci, kuma kana koyar da maganar Allah bisa gaskiya. Mutane ba sa ɗaukan hankalinka, domin ba ka kula ko su wane ne ba. To, ka gaya mana, a ra’ayinka? Ya dace a biya Kaisar haraji ko a’a?” Amma Yesu da yake ya san mugun nufinsu, sai ya ce, “Ku munafukai, don me kuke ƙoƙarin sa mini tarko? Ku nuna mini kuɗin da ake biyan haraji da shi.” Sai suka kawo masa dinari, sai ya tambaye su ya ce, “Hoton wane ne wannan? Kuma rubutun wane ne?” Suka amsa, “Na Kaisar ne.” Sai ya ce musu, “Ku ba wa Kaisar abin da yake na Kaisar, ku kuma ba wa Allah abin da yake na Allah.” Da suka ji haka, sai suka yi mamaki. Saboda haka suka ƙyale shi, suka yi tafiyarsu. A ranan nan Sadukiyawa, waɗanda suke cewa babu tashin matattu, suka zo wurinsa da tambaya. Suka ce “Malam, Musa ya faɗa mana cewa in mutum ya mutu ba shi da ’ya’ya, dole ɗan’uwansa yă auri gwauruwar yă kuma haifar wa ɗan’uwan ’ya’ya. A cikinmu an yi ’yan’uwa guda bakwai. Na fari ya yi aure, ya mutu, da yake bai sami ’ya’ya ba, sai ya bar matarsa wa ɗan’uwansa. Haka ya faru da ɗan’uwa na biyu da na uku, har zuwa na bakwai. A ƙarshe, macen ta mutu. To, a tashin matattu, matar wa a cikinsu bakwai ɗin nan za tă zama, da yake dukansu sun aure ta?” Yesu ya amsa ya ce, “Kun ɓata, domin ba ku san Nassi ko ikon Allah ba. Ai, a tashin matattu, mutane ba za su yi aure ko su ba da aure ba; za su zama kamar mala’iku a sama. Amma game da tashi daga matattu na waɗanda suka mutu ba ku karanta abin da Allah ya ce muku ba ne, ‘Ni ne Allah na Ibrahim, Allah na Ishaku da kuma Allah na Yaƙub’? Ai, shi ba Allah na matattu ba ne, shi Allah na masu rai ne.” Da taro suka ji haka, sai suka yi mamakin koyarwarsa. Da jin Yesu ya ƙure Sadukiyawa, sai Farisiyawa suka tattaru. Ɗaya daga cikinsu, wani masanin Doka, ya gwada shi da wannan tambaya. “Malam, wace doka ce mafi girma a cikin dokoki?” Yesu ya amsa ya ce, “ ‘Ka ƙaunaci Ubangiji Allahnka da dukan zuciyarka da dukan ranka da kuma dukan hankalinka.’ Wannan, ita ce doka ta fari da kuma mafi girma. Ta biye kuma kamar ta farkon take. ‘Ka ƙaunaci maƙwabcinka kamar kanka.’ Dukan Doka da Annabawa suna rataya ne a kan waɗannan dokoki biyu.” Yayinda Farisiyawa suke a tattare wuri ɗaya, sai Yesu ya tambaye su, “Me kuke tsammani game da Kiristi? Ɗan wane ne shi?” Suka amsa suka ce, “Ɗan Dawuda.” Ya ce musu, “To, ta yaya Dawuda ya yi magana ta wurin Ruhu Mai Tsarki, ya kira shi ‘Ubangiji’? Gama ya ce, “ ‘Ubangiji ya ce wa Ubangijina, “Zauna a hannun damana, sai na sa abokan gābanka su zama matashin sawunka.” ’ To, in Dawuda ya kira shi ‘Ubangiji,’ yaya zai zama ɗansa?” Ba wanda ya iya tanka masa, daga wannan rana kuwa ba wanda ya sāke yin karambanin yin masa wata tambaya. Sa’an nan Yesu ya ce wa taron mutane da kuma almajiransa, “Malaman dokoki da Farisiyawa suke zama a kujerar Musa. Saboda haka dole ku yi musu biyayya, ku kuma yi duk abin da suka faɗa muku. Sai dai kada ku yi abin da suke yi, gama ba sa yin abin da suke wa’azi. Sukan ɗaura kaya masu nauyi, su sa wa mutane a kafaɗa. Amma su kansu, ba sa ko sa yatsa su taimaka. “Kome suke yi, suna yi ne don mutane su gani. Sukan yi layunsu fantam-fantam bakin rigunarsu kuma sukan kai har ƙasa; suna son wurin zaman manya a wurin biki, da kuma wuraren zama gaba-gaba a majami’u; suna so a yi ta gaisuwarsu a kasuwa, ana kuma riƙa ce musu, ‘Rabbi.’ “Amma kada a kira ku ‘Rabbi,’ gama kuna da Maigida ɗaya ne, ku duka kuwa, ’yan’uwa ne. Kada kuma ku kira wani a duniya ‘uba,’ gama kuna da Uba ɗaya ne, yana kuwa a sama. Ba kuwa za a kira ku ‘malam’ ba, gama kuna da Malami ɗaya ne, Kiristi. Mafi girma a cikinku, zai zama bawanku. Gama duk wanda ya ɗaukaka kansa, za a ƙasƙantar da shi, duk kuma wanda ya ƙasƙantar da kansa, za a ɗaukaka shi. “Kaitonku, malaman dokoki da Farisiyawa, ku munafukai! Kun rufe ƙofar mulkin sama a gaban mutane. Ku kanku ba ku shiga ba, ba kuwa bar waɗanda suke ƙoƙarin shiga su shiga ba. “Kaitonku, malaman dokoki da Farisiyawa, munafukai! Kukan yi tafiye-tafiye zuwa ƙasashe, ku ƙetare teku don ku sami mai tuba ɗaya, sa’ad da ya tuba kuwa, sai ku mai da shi ɗan wuta fiye da ku, har sau biyu. “Kaitonku, makafi jagora! Kukan ce, ‘In wani ya rantse da haikali, ba damuwa; amma in ya rantse da zinariyar haikali, sai rantsuwar ta kama shi.’ Wawaye makafi! Wanne ya fi girma, zinariyar, ko haikalin da yake tsarkake zinariyar? Kukan kuma ce, ‘In wani ya rantse da bagade, ba damuwa; amma in ya rantse da bayarwar da take bisansa, sai rantsuwar ta kama shi.’ Makafi kawai! Wanne ya fi girma, bayarwar, ko kuwa bagaden da yake tsarkake bayarwar? Saboda haka, duk wanda ya rantse da bagade, ya rantse ne da bagaden tare da abin da yake bisansa. Kuma duk wanda ya rantse da haikali, ya rantse ne da shi da kuma wanda yake zaune a cikinsa. Duk kuma wanda ya rantse da sama, ya rantse ne da kursiyin Allah da kuma wanda yake zaune a kansa. “Kaitonku, malaman dokoki da Farisiyawa, munafukai! Kukan ba da kashi ɗaya bisa goma na kayan yajinku, na’ana’a, anise, da lafsur. Amma kun ƙyale abubuwan da suka fi girma na dokoki, adalci, jinƙai da aminci. Waɗannan ne ya kamata da kun kiyaye ba tare da kun ƙyale sauran ba. Makafi jagora! Kukan tace ƙwaro ɗan mitsil amma sai ku haɗiye raƙumi. “Kaitonku, malaman dokoki da Farisiyawa, munafukai! Kukan wanke bayan kwaf da kwano, amma a ciki, cike suke da zalunci da sonkai. Kai makaho Bafarisiye! Ka fara wanke cikin kwaf da kwano, sa’an nan bayan ma zai zama da tsabta. “Kaitonku, malaman dokoki da Farisiyawa, munafukai! Kuna kama da kaburburan da aka shafa musu farin fenti, waɗanda suna da kyan gani a waje, amma a ciki, cike suke da ƙasusuwan matattu da kuma kowane irin abu mai ƙazanta. Haka ku ma, a waje, a idon mutane, ku masu adalci ne, amma a ciki, cike kuke da munafunci da mugunta. “Kaitonku, malaman dokoki da Farisiyawa, munafukai! Kukan gina kaburbura don annabawa, ku kuma yi wa kaburburan mutane masu adalci ado. Kuna cewa, ‘Da mun kasance a zamanin kakanninmu, ai, da ba mu haɗa hannu da su muka karkashe annabawa ba.’ Ta haka kuna ba da shaida a kanku cewa ku zuriyar waɗanda suka karkashe annabawa ne. To, sai ku ci gaba ku cikasa ayyukan da kakanninku suka fara! “Ku macizai! ’Ya’yan macizai! Ta yaya za ku tsere wa hukuncin jahannama ta wuta? Saboda haka ina aika muku da annabawa, da masu hikima da malamai. Waɗansunsu za ku kashe ku kuma gicciye; waɗansu kuma za ku yi musu bulala a majami’unku kuna kuma binsu gari-gari. Ta haka alhakin jinin masu adalcin da aka zubar a duniya, tun daga jinin Habila mai adalci, zuwa jinin Zakariya ɗan Berekiya, wanda kuka kashe tsakanin haikali da bagade zai koma kanku. Gaskiya nake gaya muku, duk wannan zai auko wa wannan zamani. “Urushalima, ayya Urushalima, ke da kike kashe annabawa, kike kuma jifan waɗanda aka aiko gare ki, sau da sau na so in tattara ’ya’yanki wuri ɗaya, yadda kaza takan tattara ’ya’yanta cikin fikafikanta, amma kuka ƙi. Ga shi, an bar muku gidanku a yashe. Gama ina gaya muku, ba za ku sāke ganina ba sai kun ce, ‘Mai albarka ne wanda yake zuwa cikin sunan Ubangiji.’ ” Yesu ya bar haikali ke nan, yana cikin tafiya sai almajiransa suka zo wurinsa don su ja hankalinsa ga gine-ginen haikali. Sai Yesu ya ce, “Kun ga duk waɗannan abubuwa? Gaskiya nake gaya muku, ba wani dutse a nan da za a bari a kan wani; duk za a rushe.” Da Yesu yana zaune a Dutsen Zaitun, almajiran suka zo wurinsa a ɓoye. Suka ce, “Gaya mana, yaushe ne wannan zai faru, mece ce alamar zuwanka da kuma ta ƙarshen zamani?” Yesu ya amsa, “Ku lura fa, kada wani yă ruɗe ku. Gama mutane da yawa za su zo cikin sunana, suna cewa, ‘Ni ne Kiristi,’ za su kuwa ruɗi mutane da yawa. Za ku ji labarin yaƙe-yaƙe da kuma jita-jitarsu, sai dai ku lura kada hankalinku yă tashi. Dole irin waɗannan abubuwa su faru, amma ƙarshen tukuna. Al’umma za tă tasar wa al’umma, mulki yă tasar wa mulki. Za a yi yunwa da girgizar ƙasa a wurare dabam-dabam. Dukan waɗannan fa, mafarin azabar naƙudar haihuwa ne. “Sa’an nan za a bashe ku don a tsananta muku a kuma kashe ku, dukan al’ummai za su ƙi ku saboda ni. A wannan lokaci, da yawa za su juya daga bangaskiya, su ci amana su kuma ƙi juna, annabawan ƙarya da yawa za su firfito su kuma ruɗi mutane da yawa. Saboda ƙaruwar mugunta, ƙaunar yawanci za tă yi sanyi, amma duk wanda ya tsaya da ƙarfi har ƙarshe, zai sami ceto. Za a kuma yi wa’azin wannan bisharar mulki a cikin dukan duniya, yă zama shaida ga dukan al’ummai, sa’an nan ƙarshen yă zo. “Saboda haka sa’ad da kuka ga ‘abin ƙyama mai kawo hallaka,’ wanda annabi Daniyel ya yi magana a kai, yana tsaye a tsattsarkan wuri (mai karatu yă gane), to, sai waɗanda suke cikin Yahudiya, su gudu zuwa cikin duwatsu. Kada wani da yake a kan rufin gidansa, yă sauko don ɗaukar wani abu a gida. Kada wani da yake gona kuma yă komo don ɗaukar rigarsa. Kaiton mata masu ciki da mata masu renon ’ya’ya a waɗancan kwanakin! Ku yi addu’a, kada gudunku yă zama a lokacin sanyi ko a ranar Asabbaci. Gama a lokacin za a yi wata matsananciyar wahala, wadda ba a taɓa yi ba tun farkon duniya har ya zuwa yanzu ba kuwa za a ƙara yi ba. “Da ba don an taƙaita kwanakin nan ba, da babu wani da zai tsira, amma saboda zaɓaɓɓun nan, za a taƙaita kwanakin. A lokacin in wani ya ce muku, ‘Duba, ga Kiristi nan!’ Ko, ‘Ga shi can!’ Kada ku gaskata. Gama Kiristi masu yawa na ƙarya, da annabawan ƙarya za su firfito, su kuma aikata manyan alamu da ayyukan banmamaki don su ruɗi har da zaɓaɓɓu ma in zai yiwu. Ga shi, na faɗa muku tun da wuri. “Saboda haka in wani ya ce muku, ‘Ga shi can a hamada,’ kada ku fita; ko, ‘Ga shi nan a ɗakunan ciki,’ kada ku gaskata. Gama kamar yadda walƙiya take wulgawa walai daga gabas zuwa yamma, haka dawowar Ɗan Mutum zai kasance. Duk inda mushe yake, can ungulai za su taru. “Nan da nan bayan tsabar wahalan nan “ ‘sai a duhunta rana, wata kuma ba zai ba da haskensa ba; taurari kuma za su fāffāɗi daga sararin sama, za a kuma girgiza abubuwan sararin sama.’ “A sa’an nan ne alamar dawowar Ɗan Mutum zai bayyana a sararin sama, dukan al’umman duniya kuwa za su yi kuka. Za su ga Ɗan Mutum yana zuwa kan gizagizan sararin sama, da iko da kuma ɗaukaka mai girma. Zai kuwa aiki mala’ikunsa su busa ƙaho mai ƙara sosai, za su kuwa tattaro zaɓaɓɓunsa daga kusurwoyi huɗun nan, daga wannan bangon duniya zuwa wancan. “Yanzu fa, sai ku koyi wannan darasi daga itacen ɓaure. Da zarar rassansa suka yi taushi ganyayensa kuma suka toho, kun san damina ta kusa. Haka kuma, sa’ad da kun ga dukan waɗannan abubuwa, ku sani ya yi kusan zuwa, yana ma dab da bakin ƙofa. Gaskiya nake gaya muku, wannan zamani ba zai shuɗe ba sai dukan abubuwan nan sun faru. Sama da ƙasa za su shuɗe, amma maganata ba za tă taɓa shuɗe ba. “Babu wanda ya san wannan rana ko sa’a, ko mala’ikun da suke sama ma, ko Ɗan, sai dai Uban kaɗai. Kamar yadda ya faru a zamanin Nuhu, haka zai zama a dawowar Ɗan Mutum. Gama a kwanaki kafin ruwan tsufana, mutane sun yi ta ci, sun kuma yi ta sha, suna aure, suna kuma aurarwa, har zuwa ranar da Nuhu ya shiga jirgi; ba su kuwa san abin da yake faruwa ba sai da ruwan tsufana ya zo ya share su tas. Haka zai zama a dawowar Ɗan Mutum. Maza biyu za su kasance a gona; za a ɗau ɗaya a bar ɗaya. Mata biyu za su kasance suna niƙa; za a ɗau ɗaya a bar ɗaya. “Saboda haka sai ku zauna a faɗake, gama ba ku san a wace rana ce Ubangijinku zai zo ba. Ku dai gane wannan, da maigida ya san ko a wane lokaci ne da dare, ɓarawo zai zo, da sai yă zauna a faɗake yă kuma hana a shiga masa gida. Saboda haka ku ma, sai ku zauna a faɗake, domin Ɗan Mutum zai zo a sa’ar da ba ku za tă ba. “Wane ne bawan nan mai aminci da kuma mai hikima, wanda maigida ya sa yă lura da bayi a cikin gidansa, yă riƙa ba su abinci a daidai lokaci? Zai zama wa bawan nan da kyau in maigidan ya dawo ya same shi yana yin haka. Gaskiya nake gaya muku, zai sa shi yă lura da dukan dukiyarsa. Amma in wannan bawa mugu ne, ya kuma ce a ransa, ‘Maigidana ba zai dawo da wuri ba.’ Sa’an nan yă fara dūkan ’yan’uwansa bayi, yana ci yana kuma sha tare da mashaya. Maigidan wannan bawa zai dawo a ranar da bai yi tsammani ba, a sa’ar kuma da bai sani ba. Maigidan zai farfasa masa jiki da bulala, yă kuma ba shi wuri tare da munafukai, inda za a yi kuka da cizon haƙora. “A lokacin mulkin sama zai zama kamar budurwai goma waɗanda suka ɗauki fitilunsu suka fita don su taryi ango. Biyar daga cikinsu wawaye ne, biyar kuma masu hikima. Wawayen sun ɗauki fitilunsu, sai dai ba su riƙe mai ba. Masu hikimar kuwa suka riƙo tulunan mai da fitilunsu. Ango ya yi jinkirin zuwa, sai duk suka shiga gyangyaɗi har barci ya kwashe su. “Can tsakar dare, sai aka ji kira, ana cewa, ‘Ga ango nan! Ku fito, ku tarye shi!’ “Sai dukan budurwan nan suka farka suka kuna fitilunsu. Sai wawayen suka ce wa masu hikimar, ‘Ku ɗan sassam mana manku; fitilunmu suna mutuwa.’ “Su kuwa suka amsa, suka ce, ‘A’a, wataƙila ba zai ishe mu da ku ba. Gara ku je wurin masu sayarwa ku sayo.’ “Amma yayinda suke kan tafiya garin sayen mai, sai ango ya iso. Budurwai da suke a shirye, suka shiga wajen bikin auren tare da shi. Aka kuma kulle ƙofa. “An jima can, sai ga sauran sun iso. Suka ce, ‘Ranka yă daɗe! Ranka yă daɗe! Ka buɗe mana ƙofa!’ “Amma ya amsa ya ce, ‘Gaskiya nake gaya muku, ban san ku ba.’ “Saboda haka sai ku zauna a faɗake, don ba ku san ranar ko sa’ar ba. “Har wa yau, za a kwatanta shi da mutumin da zai yi tafiya, wanda ya kira bayinsa ya kuma danƙa musu mallakarsa. Ga guda, ya ba shi talenti biyar na kuɗi, ga wani talenti biyu, ga wani kuma talenti ɗaya, kowa bisa ga azancinsa. Sa’an nan ya yi tafiyarsa. Mutumin da ya karɓi talenti biyar, nan da nan ya tafi ya yi kasuwanci da su har ya sami ribar talenti biyar. Haka ma, wannan mai talenti biyu, shi ma ya yi riba biyu. Amma mutumin da ya karɓi talenti ɗaya ɗin, ya tafi, ya tona rami, ya ɓoye kuɗin maigidansa. “Bayan an daɗe, sai maigidan bayin nan ya dawo, ya kuma daidaita lissafi da su. Mutumin da ya karɓi talenti biyar, ya kawo ƙarin talenti biyar. Ya ce, ‘Maigida, ka danƙa mini talenti biyar. Ga shi, na yi ribar biyar.’ “Maigidansa ya amsa ya ce, ‘Madalla, bawan kirki mai aminci! Ka yi aminci a kan abubuwa kaɗan, zan sa ka lura da abubuwa masu yawa. Zo ka yi farin ciki tare da maigidanka!’ “Mutumin da yake da talenti biyu, shi ma ya zo ya ce, ‘Maigida, ka danƙa mini talenti biyu; ga shi, na yi ribar biyu.’ “Maigidansa ya amsa ya ce, ‘Madalla, bawan kirki mai aminci! Ka yi aminci a kan abubuwa kaɗan, zan sa ka lura da abubuwa masu yawa. Zo ka yi farin ciki tare da maigidanka!’ “Sa’an nan mutumin da ya karɓi talenti ɗaya ya zo. Ya ce, ‘Maigida, na san cewa kai mutum ne mai wuyan sha’ani, kana girbi inda ba ka shuka ba, kana kuma tara inda ba ka yafa iri ba. Saboda haka na ji tsoro, na je na ɓoye talentinka a ƙasa. Ga abinka.’ “Maigidansa ya amsa ya ce, ‘Kai mugun bawa, mai ƙyuya! Ashe, ka san cewa ina girbi inda ban yi shuka ba, ina kuma tarawa inda ban yafa iri ba? To, in haka ne, ai, da ka sa kuɗina a banki, don sa’ad da na dawo da na karɓi abina da riba. “ ‘Karɓi talentin daga hannunsa ku ba wanda yake da talenti goma. Gama duk mai abu za a ƙara masa, zai kuma same shi a yawalce. Duk wanda ba shi da shi kuwa, ko ɗan abin da yake da shi ma, sai an karɓe masa. Ku jefar da banzan bawan nan waje, cikin duhu, inda za a yi kuka da cizon haƙora.’ “Sa’ad da Ɗan Mutum ya zo cikin ɗaukakarsa, tare da dukan mala’iku, zai zauna a kursiyinsa cikin ɗaukakar sama. Za a tara dukan al’ummai a gabansa, zai kuma raba mutane dabam-dabam yadda makiyayi yakan ware tumaki daga awaki. Zai sa tumaki a damansa, awaki kuma a hagunsa. “Sa’an nan Sarki zai ce wa waɗanda suke damansa, ‘Ku zo, ku da Ubana ya yi wa albarka; ku karɓi gādonku, mulkin da aka shirya muku tun halittar duniya. Gama da nake jin yunwa, kun ciyar da ni, da nake jin ƙishirwa, kun ba ni abin sha, da nake baƙunci, kun karɓe ni, da nake bukatar tufafi, kun yi mini sutura, da na yi rashin lafiya, kun lura da ni, da nake kurkuku, kun ziyarce ni.’ “Sa’an nan masu adalci za su amsa masa, su ce, ‘Ubangiji, yaushe muka gan ka da yunwa muka ciyar da kai, ko da ƙishirwa muka ba ka abin sha? Yaushe kuma muka gan ka baƙo muka karɓe ka, ko cikin bukatar tufafi muka yi maka sutura? Yaushe kuma muka gan ka cikin rashin lafiya ko a kurkuku muka ziyarce ka?’ “Sarkin zai amsa ya ce, ‘Gaskiya nake gaya muku, duk abin da kuka yi wa ɗaya daga cikin waɗannan ’yan’uwana mafi ƙanƙanta, ni kuka yi wa.’ “Sa’an nan zai ce wa waɗanda suke a hagunsa, ‘Ku rabu da ni, la’anannu, zuwa cikin madawwamiyar wutar da aka shirya don Iblis da mala’ikunsa. Gama da nake jin yunwa, ba ku ba ni abinci ba, da nake jin ƙishirwa, ba ku ba ni abin sha ba, da na yi baƙunci, ba ku karɓe ni ba, da nake bukatar tufafi, ba ku yi mini sutura ba, da na yi rashin lafiya kuma ina a kurkuku, ba ku lura da ni ba.’ “Su ma za su amsa, su ce, ‘Ubangiji, yaushe muka gan ka cikin yunwa ko ƙishirwa ko baƙo ko cikin bukatar tufafi ko cikin rashin lafiya ko cikin kurkuku, ba mu taimake ka ba?’ “Zai amsa, yă ce, ‘Gaskiya nake gaya muku, duk abin da ba ku yi wa ɗaya daga cikin waɗannan mafi ƙanƙanta ba, ba ku yi mini ba ke nan.’ “Sa’an nan za su tafi cikin madawwamiyar hukunci, amma masu adalci kuwa za su shiga rai madawwami.” Sa’ad da Yesu ya gama faɗin dukan waɗannan abubuwa, sai ya ce wa almajiransa, “Kamar yadda kuka sani, Bikin Ƙetarewa sauran kwana biyu, za a kuma ba da Ɗan Mutum don a gicciye shi.” Sai manyan firistoci da dattawan mutane, suka taru a fadan babban firist, mai suna Kayifas, suka ƙulla shawara su kama Yesu da makirci, su kuma kashe shi. Suka ce, “Amma ba a lokacin Biki ba, don kada mutane su tā da rikici.” Yayinda Yesu yake a Betani, a gidan wani mutumin da ake kira Siman Kuturu, wata mace ta zo wurinsa da wani ɗan tulun alabasta na turaren mai tsada sosai, wanda ta zuba a kansa a lokacin da yake cin abinci. Sa’ad da almajiransa suka ga wannan, sai suka yi fushi. Suka ce, “Wannan almubazzaranci fa! Wannan turare ai, da an sayar da shi da kuɗi mai yawa a ba matalauta kuɗin.” Sane da wannan, Yesu ya ce musu, “Me ya sa kuke damun macen nan? Ta yi mini abu mai kyau ne. Matalauta za su kasance tare da ku kullum, amma ni ba zan kasance tare da ku kullum ba. Sa’ad da ta zuba turaren nan a jikina, ta shirya ni ne don jana’izata. Gaskiya nake gaya muku, duk inda aka yi wa’azin bisharan nan a duniya duka, abin da matan nan ta yi, za a riƙa faɗarsa don tunawa da ita.” Sai ɗaya daga cikin Sha Biyun nan, wanda ake kira Yahuda Iskariyot, ya je wurin manyan firistoci ya ce, “Me za ku ba ni, in na bashe shi gare ku?” Sai suka ƙirga masa kuɗi azurfa talatin. Daga wannan lokaci, Yahuda ya yi ta neman zarafin da zai miƙa shi. A rana ta fari ta Bikin Burodi Marar Yisti, sai almajiran suka zo wurin Yesu suka yi tambaya suka ce, “Ina kake so mu je mu shirya maka wurin da za ka ci Bikin Ƙetarewa?” Ya amsa ya ce, “Ku shiga gari wurin wāne, ku ce masa, ‘Malam ya ce, lokacina ya yi kusa. Zan ci Bikin Ƙetarewa tare da almajiraina a gidanka.’ ” Saboda haka almajiran suka yi yadda Yesu ya umarce su, suka kuwa shirya Bikin Ƙetarewa. Da yamma ta yi, sai Yesu ya zauna don cin abinci tare da Sha Biyun. Yayinda suke cin abinci, sai ya ce, “Gaskiya nake gaya muku, ɗayanku zai bashe ni.” Suka yi baƙin ciki ƙwarai, suka fara ce masa da ɗaya-ɗaya, “Gaskiya nake gaya muku, ɗayanku zai bashe ni.” Yesu ya amsa ya ce, “Wanda ya sa hannunsa a kwano tare da ni ne, zai bashe ni. Ɗan Mutum zai tafi kamar yadda aka rubuta game da shi. Amma kaiton mutumin da zai bashe Ɗan Mutum! Da ma ba a haifi mutumin nan ba, da ya fi masa.” Sa’an nan Yahuda, wanda zai bashe shi ya ce, “Tabbatacce ba ni ba ne, ko, Rabbi?” Yesu ya amsa ya ce, “I, kai ma ka fada.” Yayinda suke cikin cin abinci, Yesu ya ɗauki burodi, ya yi godiya ya kuma kakkarya, ya ba wa almajiransa yana cewa, “Ku karɓa ku ci; wannan jikina ne.” Sa’an nan ya ɗauki kwaf, ya yi godiya, ya kuma ba su, yana cewa, “Ku shassha daga cikinsa, dukanku. Wannan jinina ne na sabon alkawari, wanda aka zubar saboda mutane da yawa, don gafarar zunubai. Ina gaya muku, ba zan ƙara shan ruwan inabin nan ba har sai ranar da zan sha shi sabo tare da ku a mulkin Ubana.” Da suka rera waƙa, sai suka fita, suka tafi Dutsen Zaitun. Sai Yesu ya ce musu, “A wannan dare, dukanku za ku ja da baya saboda ni, gama a rubuce yake cewa, “ ‘Zan bugi makiyayin, tumakin garken kuwa za su fasu.’ Amma bayan na tashi, zan sha gabanku zuwa Galili.” Bitrus ya amsa ya ce, “Ko da duka sun ja da baya saboda kai, ba zan taɓa ja da baya ba.” Yesu ya amsa ya ce, “Gaskiya nake gaya maka, a daren nan, kafin zakara yă yi cara, za ka yi mūsun sanina sau uku.” Bitrus ya furta, “Ko da ma zan mutu ne tare da kai, ba zan taɓa yin mūsun saninka ba.” Dukan sauran almajiran ma suka faɗa haka. Sa’an nan Yesu ya tafi da almajiransa zuwa wani wurin da ake kira Getsemane, ya ce musu, “Ku zauna nan, in je can in yi addu’a.” Ya ɗauki Bitrus da ’ya’ya biyun nan na Zebedi tare da shi, sai ya fara baƙin ciki, ya kuma damu. Sai ya ce musu, “Raina yana cike da baƙin ciki har kamar zan mutu. Ku dakata a nan, ku kuma yi tsaro tare da ni.” Da ya yi gaba kaɗan, sai ya fāɗi a ƙasa, ya yi addu’a ya ce, “Ubana, in mai yiwuwa ne, a ɗauke mini wannan kwaf. Amma ba nufina ba, sai naka.” Sa’an nan ya komo wurin almajiransa, ya tarar suna barci. Ya tambayi Bitrus ya ce, “Ashe, ba za ku iya yin tsaro tare da ni ko na sa’a guda ba? Ku yi tsaro, ku kuma yi addu’a, don kada ku fāɗi cikin jarraba. Ruhu yana so, sai dai jiki raunana ne.” Ya sāke tafiya sau na biyu, ya yi addu’a ya ce, “Ubana, in ba zai yiwu a ɗauke wannan kwaf ba sai na sha shi, to, bari a aikata nufinka.” Da ya dawo, har yanzu ya tarar suna barci, domin idanunsu sun yi nauyi da barci. Saboda haka ya sāke barinsu, ya yi addu’a sau na uku, yana maimaita iri abu guda. Sa’an nan ya komo wurin almajiransa, ya ce musu, “Har yanzu kuna barci kuna hutawa ba? Ga shi, sa’a ta yi kusa, an kuma bashe Ɗan Mutum a hannuwan masu zunubi. Ku tashi, mu tafi! Ga mai bashe ni nan yana zuwa!” Yayinda yana cikin magana, sai Yahuda, ɗaya daga cikin Sha Biyun nan, ya iso. Tare da shi kuwa ga taro mai yawa riƙe da takuba da sanduna, manyan firistoci da dattawan mutane ne suka turo su. To, mai bashe shi ɗin, ya riga ya shirya alama da su, “Wanda na yi masa sumba, shi ne mutumin; ku kama shi.” Da zuwansa, sai ya miƙe zuwa wurin Yesu ya ce, “Gaisuwa, Rabbi!” Sa’an nan ya yi masa sumba. Yesu ya amsa ya ce, “Aboki, yi abin da ya kawo ka.” Sa’an nan mutanen suka matso, suka kama Yesu suka riƙe shi. Ganin haka, sai ɗaya daga cikin waɗanda suke tare da Yesu, ya zaro takobinsa ya kai wa bawan babban firist sara, ya fille masa kunne. Sai Yesu ya ce, masa, “Mai da takobinka kube, gama duk masu zare takobi, a takobi za su mutu. Kuna tsammani ba zan iya kira Ubana, nan take kuwa yă aiko mini fiye da rundunar mala’iku goma sha biyu ba? Amma ta yaya za a cika Nassin da ya ce dole haka yă faru?” A wannan lokaci sai Yesu ya ce wa taron, “Ina jagoran wani tawaye ne, da kuka fito da takuba da kuma sanduna domin ku kama ni? Kowace rana ina zama a filin haikali ina koyarwa, ba ku kuwa kama ni ba. Amma wannan duka ya faru ne don a cika rubuce-rubucen annabawa.” Sa’an nan dukan almajiran suka yashe shi suka gudu. Waɗanda suka kama Yesu kuwa suka kai shi wurin Kayifas, babban firist, inda malaman dokoki da dattawa suka taru. Amma Bitrus ya bi daga nesa, har zuwa cikin filin gidan babban firist. Ya shiga, ya zauna tare da masu gadi, don yă ga ƙarshen abin. Sai manyan firistoci da ’yan majalisa duka suka yi ta neman shaidar ƙarya a kan Yesu, don su sami dama su kashe shi. Amma ba su sami ko ɗaya ba, ko da yake masu shaidar ƙarya da yawa sun firfito. A ƙarshe, biyu suka zo gaba, suka furta cewa, “Wannan mutum ya ce, ‘Ina iya rushe haikalin Allah, in sāke gina shi cikin kwana uku.’ ” Sa’an nan babban firist ya miƙe tsaye, ya ce wa Yesu, “Ba ka da wata amsa? Shaidar da mutanen nan suke yi a kanka fa?” Amma Yesu ya yi shiru. Sai babban firist ya ce masa, “Na haɗa ka da Allah mai rai. Faɗa mana in kai ne Kiristi, Ɗan Allah.” Sai Yesu ya amsa ya ce, “I, haka yake yadda ka faɗa. Sai dai ina gaya muku duka, nan gaba, za ku ga Ɗan Mutum zaune a hannun dama na Mai Iko, yana kuma zuwa a kan gizagizan sama.” Sa’an nan babban firist ya yage tufafinsa ya ce, “Ya yi saɓo! Don me muke bukatar ƙarin shaidu? Ga shi, yanzu kun dai ji saɓon. Me kuka gani?” Suka amsa, suka ce, “Ya cancanci mutuwa.” Sai suka tottofa masa miyau a fuskarsa, suka kuma bubbuge shi da hannuwansu. Waɗansu kuma suka mammare shi suka ce, “Yi mana annabci, Kiristi. Wa ya buge ka?” To, Bitrus yana nan zaune a filin, sai wata yarinya baiwa, ta zo wurinsa. Ta ce, “Kai ma kana tare da Yesu mutumin Galili.” Amma ya yi mūsu a gabansu duka. Ya ce, “Ban san abin da kike magana ba.” Sa’an nan ya fito zuwa hanyar shiga, inda wata yarinya kuma ta gan shi, ta ce wa mutanen da suke can, “Wannan mutum ma yana tare da Yesu Banazare.” Ya sāke mūsu har da rantsuwa, yana cewa, “Ban ma san mutumin nan ba!” Bayan ɗan lokaci, sai na tsattsaye a wurin, suka hauro wurin Bitrus, suka ce, “Tabbatacce, kai ɗayansu ne, don harshen maganarka, ya tone ka.” Sai ya fara la’antar kansa, yana ta rantsuwa yana ce musu, “Ban ma san mutumin nan ba!” Nan da take, sai zakara ya yi cara. Sai Bitrus ya tuna da maganar da Yesu ya yi cewa, “Kafin zakara yă yi cara, za ka yi mūsun sani na sau uku.” Sai ya fita waje, ya yi ta kuka. Da wayewar gari, sai dukan manyan firistoci da dattawan mutane suka yanke shawara su kashe Yesu. Suka daure shi, suka tafi da shi, suka ba da shi ga gwamna Bilatus. Sa’ad da Yahuda, wanda ya bashe Yesu, ya ga an yanke wa Yesu hukuncin kisa, sai ya yi “da na sani.” Ya je mayar wa manyan firistoci da dattawan kuɗin azurfa talatin ɗin. Ya ce, “Na yi zunubi da na ci amanar marar laifi.” Suka ce masa, “Ina ruwanmu da wannan? Wannan dai ruwanka ne.” Sai Yahuda ya zubar da kuɗin a cikin haikalin ya tafi. Sa’an nan ya je ya rataye kansa. Manyan firistoci suka ɗauki kuɗin, suka ce, “Doka ta hana a sa kuɗin a cikin ma’aji, da yake kuɗin jini ne.” Saboda haka, sai suka yanke shawara su yi amfani da kuɗin suka sayi filin mai yin tukwane, saboda binne baƙi. Shi ya sa ake kiran filin, Filin Jini har yă zuwa yau. Sai abin da aka faɗa ta bakin annabi Irmiya ya cika cewa, “Suka ɗauki azurfa talatin, kuɗin da mutanen Isra’ila suka sa a kansa, suka kuma yi amfani da su, suka sayi filin mai yin tukwane, kamar yadda Ubangiji ya umarce ni.” Ana cikin haka, Yesu kuwa yana tsaye a gaban gwamna, sai gwamnan ya tambaye shi, “Kai ne Sarkin Yahudawa?” Yesu ya ce, “I, haka ne, kamar yadda ka faɗa.” Da manyan firistoci da dattawa suka zarge shi, bai ba da amsa ba. Sai Bilatus ya tambaye shi ya ce, “Ba ka jin shaidar da suke kawowa a kanka?” Amma Yesu bai ce uffam game da ko ɗaya daga cikin zargin da suka yi masa ba. Har gwamna ya yi mamaki ƙwarai. A wannan irin Biki, gwamna yana da wata al’ada, ta sakin ɗan kurkuku guda wanda taron suka zaɓa. To, a wannan lokaci kuwa suna da wani shahararren ɗan kurkuku da ake kira Barabbas. Saboda haka da taron suka taru, sai Bilatus ya tambaye su ya ce, “Wane ne a cikinsu kuke so in sakar muku. Barabbas ko Yesu wanda ake kira Kiristi?” Don ya san saboda sonkai ne suka ba da Yesu a gare shi. Yayinda Bilatus yake zaune a kan kujerar shari’a, sai matarsa ta aika masa da wannan saƙo cewa, “Kada ka sa hannunka a kan marar laifin nan, domin na sha wahala ƙwarai, a cikin mafarki yau game da shi.” Amma manyan firistoci da dattawa suka shawo kan taron, su ce, a ba su Barabbas, amma a kashe Yesu. Gwamna ya yi tambaya ya ce, “Wane ne cikin biyun nan, kuke so in sakar muku?” Suka ce, “Barabbas.” Bilatus ya yi tambaya, “To, me zan yi da Yesu wanda ake kira Kiristi?” Duka suka ce, “A gicciye shi!” Bilatus ya ce, “Don me? Wane laifi ya yi?” Amma suka ƙara tā da ihu, suna cewa, “A gicciye shi!” Da Bilatus ya ga cewa ba ya kaiwa ko’ina, sai ma hargitsi ne yake so yă tashi, sai ya ɗibi ruwa, ya wanke hannuwansa a gaban taron ya ce, “Ni kam, ba ruwana da alhakin jinin mutumin nan. Wannan ruwanku ne!” Sai dukan mutane suka amsa, suka ce, “Bari alhakin jininsa yă zauna a kanmu da ’ya’yanmu!” Sai ya sakar musu Barabbas. Amma ya sa aka yi wa Yesu bulala, sa’an nan ya ba da shi a gicciye. Sai sojojin gwamna suka ɗauki Yesu suka kai shi Fadar mai mulki, sa’an nan suka tara dukan kamfanin sojoji kewaye da shi. Suka tuɓe shi, suka yafa masa wata jar riga. Suka kuma tuƙa wani rawanin ƙaya, suka sa masa a kā. Suka sa sanda a hannun damansa. Suka durƙusa a gabansa, suka yi masa ba’a, suna cewa, “Ranka yă daɗe sarkin Yahudawa!” Suka tattofa masa miyau, suka karɓe sandan, suka yi ta ƙwala masa shi a kai. Bayan sun yi masa ba’a, sai suka tuɓe masa rigar, suka sa masa nasa tufafin. Sai suka tafi da shi, domin su gicciye shi. Suna fitowa ke nan, sai suka sadu da wani mutumin Sairin, mai suna Siman. Sai suka tilasta shi ya ɗauki gicciyen. Sai suka iso wani wurin da ake kira Golgota (wanda yake nufin Wurin Ƙoƙon Kai). A can, suka ba shi ruwan inabi gauraye da wani abu mai ɗaci yă sha. Amma da ya ɗanɗana, sai ya ƙi sha. Bayan da suka gicciye shi, sai suka raba tufafinsa a tsakaninsu ta wurin jefa ƙuri’a. Sa’an nan suka zauna suna tsaronsa. Bisa da kansa kuwa, an kafa rubutun zargin da aka yi masa, da ya ce, Wannan shi ne Yesu Sarkin Yahudawa. An gicciye ’yan fashi biyu tare da shi, ɗaya a damansa, ɗaya kuma a hagunsa. Masu wucewa, suka zazzage shi, suna kaɗa kai, suna cewa, “Kai da za ka rushe haikali, ka kuma gina shi cikin kwana uku, ceci kanka mana! In kai Ɗan Allah ne, ka sauka daga gicciyen!” Haka ma, manyan firistoci da malaman dokoki da kuma dattawa, suka yi ta yin masa ba’a, suna cewa, “Ya ceci waɗansu, amma ya kāsa ceton kansa! In shi ne Sarkin Isra’ila! To, yă sauko daga kan gicciyen nan, mu kuwa mu gaskata shi. Ya dogara ga Allah. Bari Allah yă cece shi yanzu, in yana sonsa, domin ya ce, ‘Ni Ɗan Allah ne.’ ” Haka ma, ’yan fashin da aka gicciye tare da shi, suka zazzage shi. Daga sa’a ta shida, har zuwa sa’a ta tara, duhu ya rufe ƙasa duka. Wajen sa’a ta tara, Yesu ya ɗaga murya da ƙarfi ya ce, “Eloi, Eloi, lama sabaktani?” (Wato, “Ya Allahna, ya Allahna, don me ka yashe ni?” ). Sa’ad da waɗanda suke tsattsaye a wurin suka ji haka, sai suka ce, “Yana kiran Iliya.” Nan da nan, ɗaya daga cikinsu ya ruga, ya sami soso, ya jiƙa shi da ruwan tsami, ya sa a sanda, ya miƙa wa Yesu, yă sha. Sauran kuwa suka ce, “Ƙyale shi mu ga, ko Iliya zai zo yă cece shi.” Da Yesu ya sāke ɗaga murya da ƙarfi, sai ya saki ruhunsa. A daidai wannan lokaci, sai labulen haikali ya tsage gida biyu, daga sama har ƙasa. Ƙasa ta jijjiga, duwatsu kuma suka farfashe. Kaburbura suka bubbuɗe, jikunan tsarkaka da yawa kuwa cikin waɗanda da suka mutu, suka tashi. Suka firfito daga kaburbura, sa’an nan bayan tashin Yesu daga matattu, suka shiga birni mai tsarki, suka bayyana ga mutane da yawa. Da jarumin nan tare da waɗanda suke tsaron Yesu, suka ga girgizar ƙasa, da kuma abin da ya faru, sai tsoro ya kama su, suka kuma ce, “Gaskiya, wannan Ɗan Allah ne!” Akwai mata da yawa a can, suna kallo daga nesa. Sun bi Yesu tun daga Galili, suna masa hidima. A cikinsu, akwai Maryamu Magdalin, da Maryamu uwar Yaƙub da Yoses, da kuma uwar ’ya’yan Zebedi. Da yamma ta yi, sai ga wani mutum mai arziki daga Arimateya, sunansa Yusuf, wanda shi da kansa almajirin Yesu ne. Ya je wurin Bilatus, ya roƙe shi yă ba shi jikin Yesu. Sai Bilatus ya umarta a ba shi. Yusuf ya ɗauki jikin ya nannaɗe shi da zanen lilin mai tsabta. Sa’an nan ya sa shi a sabon kabarinsa, wanda ya haƙa a dutse. Bayan ya gungura wani babban dutse ya rufe bakin kabarin, sai ya tafi abinsa. Maryamu Magdalin da ɗayan Maryamun, suna zaune a wurin, ɗaura da kabarin. Kashegari, wato, bayan Ranar Shirye-shirye, sai manyan firistoci da Farisiyawa, suka je wurin Bilatus. Suka ce, “Ranka yă daɗe, mun tuna, mai ruɗin nan tun yana da rai ya ce, ‘Bayan kwana uku, zan tashi daga matattu.’ Saboda haka, ka ba da umarni, a tsare kabarin sai rana ta uku ɗin. In ba haka ba, almajiransa za su iya zuwa su sace jikin, sa’an nan su faɗa wa mutane cewa, an tashe shi daga matattu. Ruɗin ƙarshen nan fa, sai yă fi na farkon muni.” Sai Bilatus ya ce, “Shi ke nan, ku ɗebi soja, ku je ku tsare kabarin iya ƙoƙarinku.” Sai suka je suka tsare kabarin ta wurin buga masa hatimi, suka kuma sa masu gadi. Bayan ranar Asabbaci, da sassafe, a ranar farko ta mako, Maryamu Magdalin tare da ɗaya Maryamun, suka je don su ga kabarin. Sai aka yi wata babbar girgizar ƙasa. Don wani mala’ikan Ubangiji ya sauka daga sama, ya je kabarin, ya gungurar da dutsen, ya kuma zauna a kai. Kamanninsa yana kama da walƙiya, tufafinsa kuma fari fat kamar dusan ƙanƙara. Masu gadin kabarin kuma suka ji tsoro ƙwarai, suka yi rawan jiki, suka zama kamar matattu. Mala’ikan ya ce wa matan, “Kada ku ji tsoro, domin na san cewa kuna neman Yesu wanda aka gicciye ne. Ai, ba ya nan, ya tashi kamar yadda ya faɗa. Ku zo ku ga inda ya kwanta. Sai ku tafi da sauri ku gaya wa almajiransa cewa, ‘Ya tashi daga matattu, ya kuma ya sha gabanku zuwa Galili. Can za ku gan shi.’ Ga shi na faɗa muku.” Sai matan suka bar kabarin da hanzari, da tsoro, sai dai cike da farin ciki, suka tafi a guje don su gaya wa almajiransa. Kwaram, sai ga Yesu ya gamu da su ya ce, “Gaisuwa.” Sai suka zo kusa da shi, suka rungumi ƙafafunsa, suka yi masa sujada. Sai Yesu ya ce musu, “Kada ku ji tsoro, ku tafi ku gaya wa ’yan’uwana, su tafi Galili. A can za su gan ni.” Yayinda matan nan suna cikin tafiya, sai waɗansu daga cikin masu gadin suka shiga gari, suka ba wa manyan firistoci labarin duk abin da ya faru. Da manyan firistoci da dattawa suka taru, sai suka ƙulla wata dabara, suka ba wa sojojin kuɗi mai yawa. Suka ce musu, “Ku, za ku ce, ‘Almajiransa ne sun zo da dare suka sace shi, lokacin da muke barci.’ In wannan labari ya kai kunnen gwamna, za mu lallashe shi, mu kuma kāre ku daga duk wata wahala.” Sai sojojin suka karɓi kuɗin, suka kuma yi kamar yadda aka umarce su. Wannan labarin kuwa shi ne ake bazawa ko’ina a cikin Yahudawa, har yă zuwa yau. Sa’an nan almajiransa goma sha ɗaya, suka tafi Galili, suka je dutsen da Yesu ya gaya musu. Da suka gan shi, sai suka yi masa sujada, amma waɗansu suka yi shakka. Sai Yesu ya zo wurinsu ya ce, “An ba ni dukan iko a sama da kuma ƙasa. Saboda haka ku tafi, ku mai da dukan al’umman duniya su zama almajiraina, kuna yi musu baftisma a cikin sunan Uba, da na Ɗa, da na Ruhu Mai Tsarki, kuna kuma koya musu, su yi biyayya da duk abin da na umarce ku, kuma tabbatacce, ina tare da ku kullum, har ƙarshen zamani.” Farkon bishara game da Yesu Kiristi, Ɗan Allah. An rubuta a cikin littafin annabi Ishaya cewa, “Zan aika da ɗan aikena yă sha gabanka, wanda zai shirya hanyarka,” “muryar mai kira a hamada tana cewa, ‘Ku shirya wa Ubangiji hanya, ku miƙe hanyoyi dominsa.’ ” Ta haka Yohanna ya zo, yana baftisma a yankin hamada, yana kuma wa’azin baftismar tuba don gafarar zunubai. Dukan ƙauyukan Yahudiya da dukan mutanen Urushalima suka fiffito zuwa wurinsa. Suna furta zunubansu, ya kuwa yi musu baftisma a Kogin Urdun. Yohanna ya sa tufafin gashin raƙumi, ya kuma yi ɗamara da fata. Abincinsa fāri ne da kuma zumar jeji. Wannan kuwa shi ne saƙonsa, “A bayana, wanda ya fi ni iko yana zuwa, ban kuwa isa in sunkuya in kunce igiyar takalmansa ba. Ina muku baftisma da ruwa, amma shi zai yi muku baftisma da Ruhu Mai Tsarki.” A lokacin, Yesu ya zo daga Nazaret na Galili, Yohanna kuwa ya yi masa baftisma a Urdun. Da Yesu yana fitowa daga ruwan, sai ya ga sama ya buɗe, Ruhu kuma yana saukowa a kansa kamar kurciya. Sai murya ta fito daga sama ta ce, “Kai ne Ɗana, wanda nake ƙauna, da kai kuma nake fari ciki ƙwarai.” Nan da nan, sai Ruhu ya kai shi cikin hamada, ya kuma kasance a hamada kwana arba’in, Shaiɗan yana gwada shi. Yana tare da namomin jeji, mala’iku kuma suka yi masa hidima. Bayan da aka sa Yohanna a kurkuku, sai Yesu ya shigo cikin Galili, yana shelar bisharar Allah. Yana cewa, “Lokaci ya yi. Mulkin Allah ya yi kusa. Ku tuba, ku gaskata bishara!” Yayinda Yesu yake tafiya a gaɓar Tekun Galili, sai ya ga Siman da ɗan’uwansa Andarawus, suna jefa abin kamun kifi a cikin tafkin, domin su masunta ne. Yesu ya ce, “Ku zo, ku bi ni, ni kuwa zan mai da ku masuntan mutane.” Nan da nan, suka bar abin kamun kifinsu, suka bi shi. Da ya yi gaba kaɗan, sai ya ga Yaƙub ɗan Zebedi, da ɗan’uwansa Yohanna a cikin jirgin ruwa, suna gyaran abin kamun kifinsu. Ba da ɓata lokaci ba, ya kira su, sai suka bar mahaifinsu Zebedi a cikin jirgin ruwan, tare da ’yan haya, suka kuwa bi shi. Suka tafi Kafarnahum. Da ranar Asabbaci ta kewayo, sai Yesu ya shiga majami’a ya fara koyarwa. Mutane suka yi mamakin koyarwarsa, domin ya koyar da su kamar wanda yake da iko, ba kamar malaman dokoki ba. Nan take, sai wani mutum mai mugun ruhu a majami’arsu, ya ɗaga murya ya ce, “Ina ruwanka da mu, Yesu Banazare? Ka zo ne don ka hallaka mu? Na san wane ne kai, Mai Tsarki nan na Allah!” Yesu ya tsawata masa ya ce, “Yi shiru! Fita daga cikinsa!” Sai mugun ruhun ya jijjiga mutumin da ƙarfi, ya fita daga jikinsa da ihu. Dukan mutane suka yi mamaki, suna tambayar juna suna cewa, “Mene ne haka? Tabɗi! Yau ga sabuwar koyarwa kuma da iko! Yana ma ba wa mugayen ruhohi umarni, suna kuma yin masa biyayya.” Labari game da shi ya bazu nan da nan ko’ina a dukan yankin Galili. Da suka bar majami’ar, sai suka tafi gidan su Siman da Andarawus, tare da Yaƙub da Yohanna. Surukar Siman tana kwance da zazzaɓi, sai suka gaya wa Yesu game da ita. Sai ya je wajenta, ya kama hannunta, ya ɗaga ta. Zazzaɓin kuwa ya sāke ta, ta kuma yi musu hidima. A wannan yamma, bayan fāɗuwar rana, mutane suka kawo wa Yesu dukan marasa lafiya, da masu aljanu. Duk garin ya taru a ƙofar gidan. Yesu kuwa ya warkar da marasa lafiya da yawa da suke da cututtuka iri-iri. Ya kuma fitar da aljanu da yawa, amma bai yarda aljanun suka yi magana ba, don sun san wane ne shi. Da sassafe, tun da sauran duhu, Yesu ya tashi, ya bar gida, ya tafi wani wurin da ba kowa, a can ya yi addu’a. Siman da abokansa suka fita nemansa. Da suka same shi, sai suka ce, “Kowa yana nemanka!” Yesu ya amsa ya ce, “Mu je wani wuri dabam, zuwa ƙauyukan da suke kusa, don in yi wa’azi a can ma. Wannan shi ne dalilin zuwana.” Sai ya tafi ko’ina a Galili, yana wa’azi a majami’unsu, yana kuma fitar da aljanu. Wani mutum mai kuturta ya zo wurinsa, ya durƙusa ya roƙe shi ya ce, “In kana so, za ka iya tsabtacce ni.” Cike da tausayi, sai Yesu ya miƙa hannunsa ya taɓa mutumin ya ce, “Na yarda, ka tsabtacce!” Nan da nan, sai kuturtar ta rabu da shi, ya kuma warke. Yesu ya sallame shi nan take, da gargaɗi mai ƙarfi cewa, “Ka lura kada ka gaya wa kowa wannan. Amma ka tafi ka nuna kanka ga firist, ka kuma miƙa hadayun da Musa ya umarta saboda tsarkakewarka, don yă zama shaida gare su.” A maimakon haka, sai ya fita, ya fara magana a sake, yana baza labarin. Saboda haka, Yesu bai ƙara iya shiga cikin gari a fili ba, sai dai ya kasance a wuraren da ba kowa. Duk da haka, mutane suka yi ta zuwa wurinsa daga ko’ina. Bayan ’yan kwanaki, da Yesu ya sāke shiga Kafarnahum, sai mutane suka ji labarin zuwansa gida. Mutane suka taru da yawa har ma babu wuri, ko a bakin ƙofa ma, sai ya yi musu wa’azin bishara. Waɗansu mutum huɗu suka zo wajensa ɗauke da wani shanyayye. Da ba su iya kai shi wurin Yesu ba, saboda taron, sai suka buɗe rufin gidan saman, bisa daidai inda Yesu yake. Bayan da suka huda rami, sai suka saukar da shanyayyen, kwance a kan tabarmarsa. Da Yesu ya ga bangaskiyarsu, sai ya ce wa shanyayyen, “Saurayi, an gafarta zunubanka.” To, waɗansu malaman dokoki da suke zaune a wurin, suka yi tunani a zuciyarsu, suna cewa, “Me ya sa mutumin nan yake magana haka? Yana saɓo! Wane ne zai iya gafarta zunubai, in ba Allah kaɗai ba?” Nan da nan, Yesu ya gane a ruhunsa abin da suke tunani a zuciyarsu, sai ya ce musu, “Me ya sa kuke tunanin waɗannan abubuwa? Wanne ya fi sauƙi, a ce wa shanyayyen, ‘An gafarta zunubanka,’ ko a ce, ‘Tashi, ɗauki tabarmarka ka yi tafiya’? Amma don ku san cewa, Ɗan Mutum yana da iko a duniya yă gafarta zunubai.” Sai ya ce wa shanyayyen, “Ina ce maka, tashi, ɗauki tabarmarka, ka tafi gida.” Sai ya tashi, ya ɗauki tabarmarsa, ya yi tafiyarsa a gabansu duka. Wannan ya ba wa kowa mamaki, suka kuma ɗaukaka Allah suna cewa, “Ba mu taɓa ganin abu haka ba!” Yesu ya sāke tafiya bakin tafkin. Taro mai yawa ya zo wurinsa, sai ya fara koya musu. Yana cikin tafiya, sai ya ga Lawi, ɗan Alfayus zaune a inda ake karɓar haraji. Yesu ya ce masa, “Bi ni.” Sai Lawi ya tashi, ya bi shi. Yayinda Yesu yake cin abinci a gidan Lawi, sai masu karɓar haraji da “masu zunubi” da yawa, suka zo suka ci tare da shi da almajiransa, gama akwai mutane da yawa da suka bi shi. Da malaman dokoki, waɗanda su ma Farisiyawa ne, suka ga yana ci tare da masu “zunubi” da masu karɓar haraji, sai suka tambayi almajiransa, suka ce, “Me ya sa yake ci tare da masu karɓar haraji da masu zunubi?” Da jin wannan, Yesu ya ce musu, “Ai, masu lafiya ba sa bukatar likita, sai dai marasa lafiya. Ban zo domin in kira masu adalci ba, sai dai masu zunubi.” To, almajiran Yohanna da na Farisiyawa suna azumi, sai waɗansu mutane suka zo suka tambayi Yesu, suka ce, “Yaya almajiran Yohanna da na Farisiyawa suna azumi, amma almajiranka ba sa yi?” Yesu ya amsa ya ce, “Yaya abokan ango za su yi azumi, sa’ad da yana tare da su? Ai, ba za su yi ba, muddin yana tare da su. Ai, lokaci yana zuwa da za a ɗauke musu angon. A sa’an nan ne fa za su yi azumi. “Ba mai facin sabon ƙyalle a tsohuwar riga. In ya yi haka, sabon ƙyallen zai yage daga tsohuwar, yagewar kuwa za tă zama da muni. Ba wanda yakan zuba sabon ruwan inabi a tsofaffin salkuna. In ya yi haka, ruwan inabin zai farfashe salkunan, yă yi hasarar ruwan inabin, salkunan kuma su lalace. A’a, yakan zuba sabon ruwan inabin a sababbin salkuna.” Wata ranar Asabbaci, Yesu yana ratsa gonakin hatsi, sai almajiransa da suke tafiya tare da shi, suka fara kakkarya waɗansu kan hatsi. Farisiyawa suka ce masa, “Duba, me ya sa suke yin abin da doka ta hana a yi, a ranar Asabbaci?” Ya amsa ya ce, “Ashe, ba ku taɓa karanta abin da Dawuda ya yi ba, sa’ad da shi da abokan tafiyarsa suka ji yunwa, suna kuma cikin bukata? Ya shiga gidan Allah a zamanin Abiyatar babban firist, ya ci keɓaɓɓen burodin nan, ya kuma ba wa abokan tafiyarsa abin da firistoci kaɗai sukan ci bisa ga doka?” Sai ya ce musu, “An yi Asabbaci saboda mutum ne, ba mutum saboda Asabbaci ba. Don haka, Ɗan Mutum Ubangiji ne, har ma da na Asabbaci.” Wani lokaci, da ya sāke shiga majami’a, sai ga wani mutum mai shanyayyen hannu. Waɗansu daga cikin mutane suna neman dalilin zargin Yesu, sai suka zuba masa ido, su ga ko zai warkar da shi a ranar Asabbaci. Yesu ya ce wa mutumin mai shanyayyen hannun, “Tashi ka tsaya a gaban kowa.” Sai Yesu ya tambaye su ya ce, “Me ya kamata a yi bisa ga doka, a ranar Asabbaci, a aikata alheri, ko a aikata mugunta, a ceci rai, ko a yi kisa?” Amma suka yi shiru. Sai ya kalle su da fushi, don taurin zuciyarsu ya ɓata masa rai sosai. Sai ya ce wa mutumin, “Miƙo hannunka.” Sai ya miƙa, hannunsa kuwa ya koma lafiyayye. Sai Farisiyawa suka fita, suka fara ƙulla shawara da mutanen Hiridus yadda za su kashe Yesu. Yesu da almajiransa suka janye zuwa tafkin, taro mai yawa kuwa daga Galili ya bi shi. Mutane da yawa daga Yahudiya, da Urushalima, da Edom, da kuma yankunan da suke ƙetaren Urdun, da kewayen Taya, da Sidon suka zo wurinsa, don sun ji dukan abubuwan da yake yi. Saboda taron, sai ya ce wa almajiransa su shirya masa ƙaramin jirgin ruwa, don kada mutane su matse shi. Gama ya warkar da mutane da yawa, masu cututtuka suka yi ta ƙoƙarin zuwa gaba, don su taɓa shi. Duk sa’ad da mugayen ruhohi suka gan shi, sai fāɗi a gabansa, su ɗaga murya, su ce, “Kai Ɗan Allah ne.” Amma yakan tsawata musu, kada su shaida ko wane ne shi. Yesu ya hau gefen wani dutse, ya kira waɗanda yake so, suka kuma zo wurinsa. Ya naɗa sha biyu, ya kira su manzanni don su kasance tare da shi, domin kuma yă aike su yin wa’azi, don kuma su sami ikon fitar da aljanu. Ga sha biyun da ya naɗa. Siman (wanda ya ba shi suna Bitrus); Yaƙub ɗan Zebedi da kuma ɗan’uwansa Yohanna (ga waɗannan kuwa ya sa musu suna Buwarnajis, wato, “’ya’yan tsawa”); Andarawus, Filibus, Bartolomeyu, Mattiyu, Toma, Yaƙub ɗan Alfayus, Taddayus, Siman wanda ake kira Zilot, da kuma Yahuda Iskariyot, wanda ya bashe Yesu. Sai Yesu ya shiga wani gida, taro kuma ya sāke haɗuwa, har shi da almajiransa ma ba su sami damar cin abinci ba. Da ’yan’uwansa suka sami wannan labari, sai suka tafi don su dawo da shi, suna cewa, “Ai, ya haukace.” Malaman dokokin da suka zo daga Urushalima suka ce, “Ai, yana da Be’elzebub! Da ikon sarkin aljanu yake fitar da aljanu.” Sai Yesu ya kira su, ya yi musu magana da misalai ya ce, “Yaya Shaiɗan zai fitar da Shaiɗan? In mulki yana gāba da kansa, wannan mulki ba zai tsaya ba. In gida yana gāba da kansa, wannan gida ba zai tsaya ba. In kuwa Shaiɗan yana gāba da kansa, ya kuma rabu biyu, ba zai tsaya ba, ƙarshensa ya zo ke nan. Tabbatacce, ba mai shiga gidan mai ƙarfi yă kwashe dukiyarsa, sai bayan ya daure mai ƙarfin, sa’an nan zai iya yin fashin gidansa. Gaskiya nake gaya muku, za a gafarta duk zunubai da kuma saɓon mutane suka yi. Amma duk wanda ya saɓi Ruhu Mai Tsarki, ba za a taɓa gafara masa ba. Ya aikata madawwamin zunubi ke nan.” Ya faɗi haka domin suna cewa, “Yana da mugun ruhu.” Sai mahaifiyar Yesu tare da ’yan’uwansa suka iso. Suna tsaye a waje, sai suka aiki wani ciki yă kira shi. Taron yana zaune kewaye da shi, sai suka ce masa, “Mahaifiyarka da ’yan’uwanka suna waje, suna nemanka.” Ya yi tambaya ya ce, “Su wane ne mahaifiyata, da ’yan’uwana?” Sai ya dubi waɗanda suke zaune kewaye da shi ya ce, “Ga mahaifiyata da ’yan’uwana! Duk wanda yake aikata nufin Allah, shi ne ɗan’uwana, da ’yar’uwata, da kuma mahaifiyata.” Har wa yau, Yesu ya fara koyarwa a bakin tafki. Domin taron da yake kewaye da shi mai girma ne sosai, sai ya shiga cikin jirgin ruwa, ya zauna a ciki a tafkin, dukan mutanen kuwa suna a gaɓar ruwan. Ya koya musu abubuwa da yawa da misalai. A koyarwarsa kuwa ya ce, “Ku saurara! Wani manomi ya fita don yă shuka irinsa. Da yana yafa irin, sai waɗansu suka fāɗi a kan hanya, tsuntsaye suka zo suka cinye su. Waɗansu suka fāɗi a wuri mai duwatsu inda babu ƙasa sosai. Nan da nan, suka tsira domin ƙasar ba zurfi. Amma da rana ta taso, sai tsire-tsiren suka ƙone, suka yanƙwane, domin ba su da saiwa. Waɗansu irin suka fāɗi a cikin ƙaya. Da suka yi girma sai ƙaya suka shaƙe su, har ya sa ba su yi ƙwaya ba. Har yanzu, waɗansu irin suka fāɗi a ƙasa mai kyau. Suka tsira, suka yi girma, suka ba da amfani, suka yi riɓi talatin-talatin, waɗansu sittin-sittin, waɗansu kuma ɗari-ɗari.” Sai Yesu ya ce, “Duk mai kunnen ji, yă ji.” Lokacin da yake shi kaɗai, Sha Biyun, da kuma waɗanda suke kewaye da shi, suka tambaye shi game da misalan. Sai ya ce musu, “An ba ku sanin asirin mulkin Allah. Amma ga waɗanda suke waje kuwa, kome sai da misalai. Saboda, “ ‘ko sun dinga duba, ba za su taɓa gane ba, kuma ko su dinga ji, ba za su taɓa fahimta ba, in ba haka ba, mai yiwuwa, su tuba, a gafarta musu!’ ” Sai Yesu ya ce musu, “Ba ku fahimci wannan misali ba? Yaya za ku fahimci wani misali ke nan? Manomi yakan shuka maganar Allah. Waɗansu mutane suna kama da irin da ya fāɗi a kan hanya, inda akan shuka maganar Allah. Da jin maganar, nan da nan sai Shaiɗan yă zo yă ɗauke maganar da aka shuka a zuciyarsu. Waɗansu suna kama da irin da aka shuka a wurare masu duwatsu, sukan ji maganar Allah, sukan kuma karɓe ta nan da nan da farin ciki. Amma da yake ba su da saiwa, ba sa daɗewa. Da wahala ko tsanani ya tashi saboda maganar, nan da nan, sai su ja da baya. Har yanzu, waɗansu kamar irin da aka shuka cikin ƙaya, sukan ji maganar, amma damuwar wannan duniya, da son dukiya, da kuma kwaɗayin waɗansu abubuwa, sukan shiga, su shaƙe maganar, har su mai da ita marar amfani. Waɗansu mutane kuwa suna kama da irin da aka shuka a ƙasa mai kyau, sukan ji maganar Allah, su kuma karɓa, sa’an nan kuma su fid da amfani riɓi talatin-talatin, ko sittin-sittin, ko ɗari-ɗari.” Sai ya ce musu, “Ko kukan kawo fitila ku rufe ta da murfi ko kuma ku sa ta a ƙarƙashin gado ne? Ba kukan sa ta a kan wurin ajiye fitila ba? Duk abin da yake a ɓoye, dole za a fallasa shi. Duk abin da kuma yake a rufe, dole za a fitar da shi a fili. Duk mai kunnen ji, bari yă ji.” Ya ci gaba da cewa, “Ku lura da abin da kuke ji da kyau. Mudun da ka auna da shi, da shi za a auna maka, har ma a ƙara. Duk wanda yake da shi, za a ƙara masa, duk wanda kuma ba shi da shi, ko abin da yake da shi ma, za a karɓe daga gare shi.” Ya sāke cewa, “Mulkin Allah yana kama da haka. Wani mutum ya yafa iri a gona. A kwana a tashi har irin yă tsiro, yă yi girma, bai kuwa santa yadda aka yi ba. Ƙasar da kanta takan ba da ƙwaya, da farko takan fid da ƙara, sa’an nan ta fid da kai, sa’an nan kan yă fid da ƙwaya. Da ƙwayan ya nuna, sai yă sa lauje yă yanka, domin lokacin girbi ya yi.” Ya kuma ce, “Da me za mu kwatanta mulkin Allah, ko kuwa da wane misali za mu bayyana shi? Yana kama da ƙwayar mustad, wadda ita ce ƙwaya mafi ƙanƙanta da akan shuka a gona. Duk da haka, in aka shuka ƙwayar, sai tă yi girma, tă zama mafi girma a itatuwan lambu. Har itacen yă kasance da manyan rassa, inda tsuntsayen sararin sama sukan iya huta a inuwarsa.” Da misalai da yawa irin waɗannan, Yesu ya yi magana da su, daidai yadda za su iya fahimta. Ba abin da ya faɗa musu, da ba da misali ba. Amma lokacin da yake shi kaɗai tare da almajiransa, sai yă bayyana kome. A wannan rana, da yamma, sai ya ce wa almajiransa, “Mu ƙetare zuwa wancan hayi.” Da suka bar taron, sai suka tafi tare da shi yadda yake, a cikin jirgin ruwa. Akwai waɗansu jiragen ruwa kuma tare da shi. Sai babban hadari mai iska ya tashi, raƙuman ruwa suna ta bugun jirgin ruwan, har jirgin ruwan ya kusa yă cika da ruwa. Yesu kuwa yana can baya, yana barci a kan katifa. Sai almajiran suka tashe shi suka ce masa, “Malam, ba ka kula ba ko mu nutse?” Sai ya farka ya tsawata wa iskar, ya ce wa raƙuman ruwan, “Shiru! Ku natsu!” Sai iskar ta kwanta, kome kuma ya yi tsit. Sai ya ce wa almajiransa, “Don me kuke tsoro haka? Har yanzu ba ku da bangaskiya ne?” Suka tsorata, suka ce wa juna, “Wane ne wannan? Har iska da raƙuman ruwa ma suna masa biyayya!” Suka ƙetare tafkin suka je yankin Gerasenawa. Da Yesu ya sauka daga jirgin ruwa, sai wani mutum mai mugun ruhu ya fito daga kaburbura, ya tarye shi. Wannan mutumin ya mai da kaburbura gidansa. Kuma ba wanda ya iya daure shi, ko da sarƙa ma. Gama an sha daure shi hannu da ƙafa da sarƙa, amma yakan tsintsinke sarƙar, yă kuma karye ƙarafan da suke ƙafafunsa. Ba wanda yake da ƙarfin da zai iya yă riƙe shi. Dare da rana, sai yă dinga kuka yana ƙuƙƙuje jikinsa da duwatsu a cikin kaburbura da kan tuddai. Da ya hangi Yesu daga nesa, sai ya ruga da gudu, ya zo ya durƙusa a gabansa. Ya yi ihu da babbar murya ya ce, “Ina ruwanka da ni Yesu, Ɗan Allah Mafi Ɗaukaka? Ka rantse da Allah cewa ba za ka ba ni azaba ba!” Gama Yesu ya riga ya ce masa, “Ka fita daga jikin mutumin nan, kai mugun ruhu!” Sai Yesu ya tambaye shi ya ce, “Mene ne sunanka?” Sai ya amsa ya ce, “Sunana Lejiyon, wato, ‘Tuli,’ domin muna da yawa.” Sai ya yi ta roƙon Yesu, kada yă kore su daga wurin. A kan tudun da yake nan kusa kuwa, akwai wani babban garken aladu, suna kiwo. Sai aljanun suka roƙi Yesu, suka ce, “Tura mu cikin aladun nan, ka bari mu shiga cikinsu.” Ya kuwa yarda musu, sai mugayen ruhohin suka fita suka shiga cikin aladun. Garken kuwa, yana da kusan aladu dubu biyu, suka gangara daga kan tudun zuwa cikin tafkin, suka nutse. Masu kiwon aladun kuwa suka ruga da gudu zuwa cikin gari da ƙauyuka, suka ba da wannan labari. Sai mutanen suka fito, domin su ga abin da ya faru. Da suka kai wajen Yesu, sai suka ga mutumin da dā yake da tulin aljanun yana zaune a wurin, sanye da tufafi kuma cikin hankalinsa, sai suka ji tsoro. Waɗanda suka ga abin da ya faru, suka ba da labarin abin da ya faru da mai aljanun, da kuma aladun. Sai mutane suka fara roƙon Yesu yă bar yankinsu. Yesu yana kan shiga cikin jirgin ruwa ke nan, sai mutumin da dā yake da aljanun ya roƙa yă bi shi. Yesu bai yardar masa ba, amma ya ce, “Ka tafi gida wurin iyalinka, ka gaya musu babban alherin da Ubangiji ya yi maka, da yadda ya yi maka jinƙai.” Sai mutumin ya tafi, ya yi ta ba da labari a cikin Dekafolis a kan babban alherin da Yesu ya yi masa. Dukan mutane kuwa suka yi mamaki. Da Yesu ya sāke ƙetarewa cikin jirgin ruwa zuwa ɗaya hayen tafkin, sai taro mai yawa ya taru kewaye da shi yayinda yake a bakin tafkin. Sai ɗaya a cikin masu mulkin majami’a, wanda ake kira Yayirus ya zo wurin. Da ganin Yesu, sai ya durƙusa a gabansa, ya roƙe shi da gaske ya ce, “Ƙaramar diyata tana bakin mutuwa. In ka yarda, ka zo ka ɗibiya hannunka a kanta, domin ta warke, ta kuma rayu.” Sai Yesu ya tafi tare da shi. Babban taron kuma ya bi shi, suna ta matsinsa a kowane gefe. A can kuwa akwai wata mace, wadda ta yi shekaru goma sha biyu tana zub da jini. Ta kuma sha wahala ƙwarai a hannun likitoci da yawa, har ta kashe duk abin da take da shi, amma maimakon samun sauƙi, sai ciwon ya ƙara muni. Da ta ji labarin Yesu, sai ta zo ta bayansa, a cikin taron, ta taɓa rigarsa, domin ta yi tunani cewa, “Ko da rigunarsa ma na taɓa, zan warke.” Nan da take, zub da jininta ya tsaya, sai ta ji a jikinta ta rabu da shan wahalarta. Nan da nan Yesu ya gane cewa, iko ya fita daga gare shi. Sai ya juya a cikin taron ya yi tambaya, “Wa ya taɓa rigata?” Sai almajiransa suka ce, “Kana ganin mutane suna matsinka, duk da haka kana tambaya, ‘Wa ya taɓa ni?’  ” Amma Yesu ya ci gaba da dubawa don yă ga wa ya taɓa shi. Matar, da yake ta san abin da ya faru da ita, sai ta zo ta durƙusa a gabansa, da tsoro da rawan jiki, ta kuma gaya masa dukan abin da ya faru. Sai ya ce mata, “Diyata, bangaskiyarki ta warkar da ke. Ki sauka lafiya, kin kuma rabu da dukan wahalarki.” Yayinda Yesu yana cikin magana, sai waɗansu mutane daga gidan Yayirus, mai mulkin majami’a, suka zo suka ce, “Diyarka ta rasu. Kada ma ka wahal da Malam.” Yesu bai kula da abin da suka faɗa ba, sai ya ce wa mai mulkin majami’ar, “Kada ka ji tsoro, ka gaskata kawai.” Bai bar kowa ya bi shi ba, sai Bitrus, Yaƙub da Yohanna ɗan’uwan Yaƙub. Da suka iso gidan mai mulkin majami’ar, sai Yesu ya ga ana hayaniya, mutane suna kuka da kururuwa. Sai ya shiga ciki, ya ce musu, “Mene ne dalilin wannan hayaniya da kuka? Yarinyar ba mutuwa ne ta yi ba, barci take yi.” Sai suka yi masa dariya. Bayan ya fitar da su duk waje, sai ya ɗauki mahaifin da mahaifiyar yarinyar tare da almajiran da suke tare da shi, suka shiga inda yarinyar take. Sai ya kama hannunta ya ce mata, “Talita kum!” (Wato, “Ƙaramar yarinya, na ce miki, tashi!” ). Nan da nan, sai yarinyar ta tashi ta yi tafiya (shekarunta goma sha biyu ne). Saboda wannan, suka yi mamaki ƙwarai. Sai ya ba da umarni mai tsanani, kada kowa yă san kome game da wannan. Sai ya ce musu, su ba ta wani abu tă ci. Yesu ya tashi daga can ya tafi garinsa, tare da almajiransa. Da Asabbaci ya kewayo, sai ya fara koyarwa a cikin majami’a, mutane da yawa da suka saurare shi, suka yi mamaki. Suna tambaya, “Ina mutumin nan ya sami waɗannan abubuwa? Wace hikima ce wannan da aka ba shi, har da yana yin ayyukan banmamaki haka! Ashe, wannan ba shi ne kafinta nan ba? Shin, ba shi ne ɗan Maryamu ba, ba shi ne ɗan’uwan su Yaƙub, Yusuf, Yahuda da kuma Siman ba? Ashe, ’yan’uwansa mata kuma ba suna nan tare da mu ba?” Sai suka ji haushinsa. Yesu ya ce musu, “Sai a garinsa kaɗai, da kuma cikin ’yan’uwansa, da cikin gidansa ne, annabi ba shi da daraja.” Bai iya yin ayyukan banmamaki a wurin ba, sai dai ɗibiya hannuwansa da ya yi a kan mutane kima da suke da cututtuka, ya kuwa warkar da su. Ya kuwa yi mamaki ƙwarai don rashin bangaskiyarsu. Sai ya Yesu zazzaga ƙauyuka yana koyarwa. Ya kira Sha Biyun nan wurinsa, ya aike su biyu-biyu, ya kuma ba su iko bisa mugayen ruhohi. Ga dai umarnansa, “Kada ku ɗauki kome don tafiyar, sai dai sanda ba burodi, ba jaka, ba kuɗi a ɗamararku. Ku sa takalma, amma ban da riga fiye da waɗanda kuka sa. Duk sa’ad da kuka shiga wani gida, ku zauna nan sai kun bar garin. In kuwa a wani wuri ba a karɓe ku, ba a kuwa saurare ku ba, sai ku karkaɗe ƙurar ƙafafunku sa’ad da kuka fita, a matsayin shaida a kansu.” Suka fita, suna yi wa’azi, suna ce wa mutane su tuba. Suka fitar da aljanu da yawa, suka shafa wa marasa lafiya da yawa mai, suka kuwa warkar da su. Sarki Hiridus ya ji wannan labari, gama sunan Yesu ya bazu a ko’ina. Waɗansu suna cewa, “An tashe Yohanna Mai Baftisma daga matattu ne, shi ya sa yana da ikon yin ayyukan banmamakin nan.” Waɗansu suka ce, “Ai, Iliya ne.” Har wa yau waɗansu suka ce, “Ai, annabi ne, kamar ɗaya daga cikin annabawan dā.” Amma da Hiridus ya ji haka, sai ya ce, “Ai, Yohanna ne, mutumin da na yanke masa kai, shi ne ya tashi daga matattu!” Gama Hiridus da kansa ya ba da umarni a kama Yohanna, ya kuma sa aka daure shi, aka sa shi a kurkuku. Ya yi haka saboda Hiridiyas, matar ɗan’uwansa Filibus, wadda ya aura. Gama Yohanna ya yi ta ce wa Hiridus, “Ba daidai ba ne bisa ga doka, ka ɗauki matar ɗan’uwanka.” Saboda haka, Hiridiyas ta ƙulla munafunci game da Yohanna, ta kuma so ta kashe shi. Amma ba tă iya ba, domin Hiridus yana jin tsoron Yohanna, ya kuma kāre shi sosai, da sanin cewa shi mutum ne mai adalci da kuma mai tsarki. Duk sa’ad da Hiridus ya saurari Yohanna, yakan damu ƙwarai, duk da haka, yakan so yă ji shi. A ƙarshe, ta sami zarafi. A ranar murnar haihuwar Hiridus, ya yi biki domin hakimansa, da shugabannin sojojinsa, da kuma manyan mutanen Galili. Sa’ad da diyar Hiridiyas ta shigo, ta kuma yi rawa, sai ta gamshi Hiridus tare da baƙinsa. Sai Sarkin ya ce wa yarinyar, “Ki tambaye ni kome da kike so, ni kuwa zan ba ki.” Ya yi mata alkawari da rantsuwa cewa, “Duk abin da kika roƙa, zan ba ki, ko da rabin mulkina ne.” Sai ta fita ta ce wa mahaifiyarta, “Me zan roƙa?” Ta ce, “Kan Yohanna Mai Baftisma.” Nan da nan, sai yarinyar ta yi hanzari zuwa wajen sarki da roƙon, “Ina so ka ba ni kan Yohanna Mai Baftisma a cikin tasa, yanzu-yanzu nan.” Sai sarki ya yi baƙin ciki ƙwarai, amma saboda rantsuwar da kuma baƙinsa, bai so yă hana ta ba. Nan take, sai ya aiki mai aiwatar da kisa da umarni ya kawo kan Yohanna. Mutumin ya je ya yanke kan Yohanna a kurkuku. Ya kuma kawo kan a tasa ya ba yarinyar. Ita kuma ta ba wa mahaifiyarta. Da almajiran Yohanna suka sami labari, sai suka zo suka ɗauki jikinsa suka binne a kabari. Manzannin suka taru kewaye da Yesu, suka ba shi rahoton duk abin da suka yi, da kuma suka koyar. To, saboda mutane da yawa suna kai da kawowa, har ma ba su sami damar cin abinci ba, sai ya ce musu, “Ku zo mu kaɗaita inda ba kowa don ku ɗan huta.” Sai suka tafi a jirgin ruwa su kaɗai, inda ba kowa. Amma mutane da yawa waɗanda suka ga tashinsu, sun gane su, sai suka ruga da gudu a ƙafa daga dukan birane, suka riga su kaiwa can. Da Yesu ya sauka, ya ga taro mai yawa, sai ya ji tausayinsu, gama kamar tumaki suke waɗanda ba su da makiyayi. Sai ya fara koya musu abubuwa da yawa. A lokacin nan yamma ta yi, sai almajiransa suka zo wurinsa suka ce masa, “Wurin nan ƙauye ne, ga shi kuma lokaci ya ƙure. Ka sallami mutanen su shiga ƙauyukan da suke kurkusa, su sayi wa kansu wani abu, su ci.” Sai ya amsa ya ce, “Ku, ku ba su wani abu su ci.” Suka ce masa, “Ai, wannan zai ɗauki albashin wata takwas na mutum! Mu je mu kashe yawan kuɗin nan a burodi mu ba su su ci?” Sai ya yi tambaya ya ce, “Burodi nawa kuke da su? Je ku duba.” Da suka duba, sai suka ce, “Biyar da kifi biyu.” Sa’an nan Yesu ya umarce su su sa dukan mutanen su zazzauna ƙungiya-ƙungiya a kan ɗanyar ciyawa. Haka suka zazzauna a ƙungiyar ɗari-ɗari, da kuma hamsin-hamsin. Ya ɗauki burodi guda biyar da kifin nan biyu, ya ɗaga kai sama, ya yi godiya, ya kakkarya burodin. Sai ya ba wa almajiransa su rarraba wa mutane. Ya kuma rarraba kifi biyun a tsakaninsu duka. Kowa ya ci, ya ƙoshi, almajiran suka kwashe gutsattsarin burodin da na kifin cike da kwanduna goma sha biyu. Yawan mutanen da suka ci kuwa maza dubu biyar ne. Nan da nan Yesu ya sa almajiransa su shiga jirgin ruwa, su sha gabansa zuwa Betsaida, shi kuma yă sallami taron. Bayan ya bar su, sai ya hau kan dutse don yă yi addu’a. Da yamma ta yi, jirgin ruwan yana tsakiyar tafkin, Yesu kuma yana can a ƙasa shi kaɗai. Ya ga almajiran suna fama da tuƙi saboda iska tana gāba da su. Wajen tsara ta huɗu na dare, sai ya tafi wurinsu, yana takawa a kan tafkin. Ya yi kamar zai wuce su, amma da suka gan shi yana takawa a kan tafkin, sai suka yi tsammani fatalwa ce. Sai suka yi ihu, domin dukansu sun gan shi, suka kuma tsorata. Nan da nan ya yi magana da su ya ce, “Ku yi ƙarfin hali! Ni ne. Kada ku ji tsoro.” Sai ya shiga jirgin ruwan tare da su, iskar kuma ta kwanta. Dukansu suka yi mamaki, gama ba su fahimci al’amarin burodin nan ba, don zuciyarsu ta taurare. Da suka haye, sai suka sauka a Gennesaret, suka daure jirgin a ƙugiya. Da fitowarsu daga jirgin, sai mutane suka gane Yesu. Suka gama yankin da gudu, suna ɗaukan marasa lafiya a kan tabarmai zuwa duk inda suka ji yake. Duk inda ya shiga, cikin ƙauyuka, birane ko karkara, sai su kwantar da marasa lafiya a bakin kasuwa. Suka roƙe shi yă bari su taɓa gefen rigarsa kawai, kuma duk waɗanda suka taɓa shi kuwa, suka warke. Farisiyawa da waɗansu malaman dokoki waɗanda suka zo daga Urushalima, suka taru kewaye da Yesu. Sai suka ga waɗansu daga cikin almajiransa suna cin abinci da hannuwa marasa tsabta, wato, da ba a wanke ba. (Farisiyawa da dukan Yahudawa ba sa cin abinci, sai sun wanke hannuwa sarai tukuna, yadda al’adun dattawa suka ce. Sa’ad da suka dawo daga wurin kasuwanci, dole su wanke hannu kafin su ci abinci. Sukan kuma kiyaye waɗansu al’adu da yawa, kamar wanken kwafuna, tuluna da butoci. ) Saboda haka, Farisiyawa da malaman dokoki suka tambayi Yesu, suka ce, “Don me almajiranka ba sa bin al’adun dattawa, a maimakon haka suna cin abinci da hannuwa marasa tsabta?” Ya amsa ya ce, “Daidai ne Ishaya ya yi annabci game da ku munafukai; kamar yadda yake a rubuce cewa, “ ‘Waɗannan mutane da baki suke girmama ni, amma zukatansu sun yi nesa da ni. A banza suke mini sujada, koyarwarsu, dokokin mutane ne kawai.’ Kun yar da umarnan Allah, kuna bin al’adun mutane.” Ya kuma ce musu, “Kuna da hanya mai sauƙi na ajiye umarnan Allah a gefe ɗaya, don ku kiyaye al’adunku! Gama Musa ya ce, ‘Ka girmama mahaifinka da mahaifiyarka,’ kuma, ‘Duk wanda ya zagi mahaifinsa ko mahaifiyarsa, dole a kashe shi.’ Amma ku, kukan ce, in mutum ya ce wa mahaifinsa, ko mahaifiyarsa, ‘Duk taimakon da ya kamata ku samu daga wurina, Korban ne,’ (wato, abin da aka keɓe wa Allah), sa’an nan haka ba kwa ƙara barinsa yă yi wa mahaifinsa ko mahaifiyarsa wani abu. Ta haka kuke rushe maganar Allah ta wurin al’adun da kuke miƙa wa ’ya’yanku. Haka kuma kuke yin abubuwa da yawa.” Sai Yesu ya sāke kiran taron wurinsa ya ce, “Ku saurare ni dukanku, ku kuma fahimci wannan. Ba abin da yake shiga mutum daga waje ba ne yake ƙazantar da shi. Sai dai abin da ya fita daga cikin mutum ne, yake ƙazantar da shi.” Bayan ya bar taron, ya shiga gida, sai almajiransa suka tambaye shi ma’anar wannan misali. Ya ce, “Ashe, ba ku da saurin ganewa? Ba ku gane cewa ba abin da yake shiga mutum daga waje ba ne yake ƙazantar da shi. Gama ba ya shiga cikin zuciyarsa, sai dai cikin tumbinsa, sa’an nan kuma yă fita daga jikinsa.” (Da faɗin haka, Yesu ya nuna tsabtar kowane irin abinci.) Ya ci gaba, “Abin da yake fitowa daga mutum ne yake ƙazantar da shi. Gama daga ciki, daga zuciyar mutane, mugayen tunani suke fitowa, fasikanci, sata, kisankai, zina, kwaɗayi, ƙeta, ruɗu, ƙazantaccen sha’awa, kishi, ɓata suna, girman kai da kuma wauta. Duk waɗannan mugayen abubuwa daga cikin suke fitowa, suna kuma ƙazantar da mutum.” Sai Yesu ya bar wurin, ya kuma tafi wajajen Taya. Ya shiga wani gida, bai kuwa so kowa yă sani ba. Duk da haka, bai iya ɓoye kasancewarsa ba. Da jin labarinsa, sai wata mace wadda ƙaramar diyarta tana da mugun ruhu, ta zo ta durƙusa a gabansa. Macen kuwa mutuniyar Hellenawa ce, an haife ta a Funisiya a Suriya. Ta roƙi Yesu yă fitar da aljani da yake jikin diyarta. Yesu ya ce mata, “Da farko, bari ’ya’ya su ci su ƙoshi tukuna, gama ba daidai ba ne, a ɗauki burodin yara a jefa wa karnukansu.” Ta amsa, ta ce, “I, Ubangiji, ko karnuka ma da suke ƙarƙashin tebur, sukan ci burbuɗin da suke fāɗuwa daga abincin yara.” Sai ya ce mata, “Saboda irin wannan amsa, ki tafi, aljanin ya rabu da diyarki.” Ta tafi gida, ta tarar da diyarta kwance a gado, aljanin kuwa ya fita. Sai Yesu ya bar wajajen Taya, ya bi ta Sidon har zuwa Tekun Galili da kuma cikin yankin Dekafolis. A can ne waɗansu mutane suka kawo masa wani kurma, wanda da ƙyar yake magana. Sai suka roƙe shi yă ɗibiya hannunsa a kan mutumin. Bayan da ya jawo shi gefe, sai Yesu ya sa yatsotsinsa a kunnuwan mutumin, ya tofa miyau ya kuma taɓa harshen mutumin. Ya ɗaga kai sama, ya ja numfashi mai zurfi, sa’an nan ya ce masa, “Effata!” (Wato, “Buɗe!” ). Bayan ya faɗa haka, sai kunnuwan mutumin suka buɗe, harshensa kuma ya kunce, sai ya fara magana sarai. Yesu ya umarce su, kada su gaya wa kowa. Amma ƙara yawan kwaɓarsu ƙara yawan yaɗa labarin suke ta yi. Mutane suka cika da mamaki, suka ce, “Kai, ya yi kome daidai. Har ma yana sa kurame su ji, bebaye kuma su yi magana.” A kwanakin nan wani taro mai girma ya taru. Tun da yake ba su da abin da za su ci, sai Yesu ya kira almajiransa ya ce, “Ina jin tausayin mutanen nan, kwanansu uku ke nan tare da ni, kuma ba su da abin da za su ci. In na sallame su gida da yunwa, za su kāsa a hanya, don waɗansu daga cikinsu sun zo daga nesa.” Almajiransa suka amsa suka ce, “Amma a ina, a wannan wurin da ba kowa, wani zai iya samun isashen burodi, don a ciyar da su?” Sai Yesu ya yi tambaya ya ce, “Burodi guda nawa kuke da su?” Suka ce, “Bakwai.” Sai ya gaya wa taron su zazzauna a ƙasa. Bayan ya ɗauki burodin nan bakwai, ya yi godiya, sai ya kakkarya, ya ba wa almajiransa su rarraba wa mutanen, suka kuwa yi haka. Suna kuma da ƙananan kifaye kaɗan, ya ba da godiya dominsu, ya kuma ce wa almajiran su rarraba musu. Mutanen suka ci, suka ƙoshi. Daga baya, almajiran suka tattara gutsattsarin da suka rage cike da kwanduna bakwai. Wajen maza dubu huɗu ne suka kasance. Da ya sallame su, sai ya shiga jirgin ruwa tare da almajiransa, suka tafi yankin Dalmanuta. Farisiyawa suka zo suka fara yin wa Yesu tambayoyi. Don su gwada shi, sai suka nemi yă nuna musu wata alama daga sama. Sai ya ja numfashi mai zurfi ya ce, “Don me wannan zamani yake neman ganin abin banmamaki? Gaskiya nake gaya muku, ba wata alamar da za a ba su.” Sai ya bar su, ya koma cikin jirgin ruwan, suka ƙetare zuwa ɗaya hayin. Almajiran suka manta su riƙe burodi, sai dai guda ɗaya da suke da shi a cikin jirgin ruwan. Yesu ya gargaɗe su ya ce, “Ku yi hankali, ku kuma lura da yistin Farisiyawa da na Hiridus.” Suka tattauna wannan da juna, suna cewa, “Don ba mu da burodi ne.” Da ya gane abin da suke tattaunawa, sai Yesu ya tambaye su ya ce, “Don me kuke zancen rashin burodi? Har yanzu ba ku gane ko fahimta ba? Zukatanku sun taurare ne? Kuna da idanu, amma kun kāsa gani, kuna da kunnuwa, amma kun kāsa ji? Ba ku tuna ba? Da na kakkarya burodi guda biyar wa mutane dubu biyar, kwanduna nawa kuka kwashe cike da gutsattsarin?” Suka amsa, “Sha biyu.” “Da na kuma kakkarya burodin nan bakwai wa mutum dubu huɗu, kwanduna nawa kuka kwashe cike da gutsattsarin?” Suka ce, “Bakwai.” Ya ce musu, “Har yanzu ba ku fahimta ba?” Suka iso Betsaida, sai waɗansu mutane suka kawo wani makaho, suka roƙi Yesu yă taɓa shi. Yesu ya kama hannun makahon ya kai shi bayan ƙauyen. Bayan ya tofa miyau a idanun mutumin, ya kuma ɗibiya masa hannuwansa, sai ya tambaye shi ya ce, “Kana iya ganin wani abu?” Sai ya ɗaga kai ya ce, “Ina ganin mutane, suna kama da itatuwa da suke tafiya.” Yesu ya sāke ɗibiya hannuwansa a idanun mutumin, sai idanunsa suka buɗe, ya sami gani, ya kuma ga kome sarai. Yesu ya sallame shi gida ya ce, “Kada ka shiga cikin ƙauyen.” Yesu da almajiransa suka tafi ƙauyukan da suke kewaye da Kaisariya Filibbi. A hanya ya tambaye su ya ce, “Wa, mutane suke ce da ni?” Suka amsa, suka ce, “Waɗansu suna cewa, Yohanna Mai Baftisma, waɗansu Iliya, waɗansu kuma har wa yau sun ce, ɗaya daga cikin annabawa.” Sai ya yi tambaya ya ce, “Amma ku fa, wa kuke ce da ni?” Bitrus ya amsa ya ce, “Kai ne Kiristi. ” Yesu ya gargaɗe su kada su gaya wa kowa kome a kansa. Sai ya fara koya musu cewa, dole Ɗan Mutum yă sha wahaloli da yawa, dattawa, manyan firistoci da malaman dokoki kuma su ƙi shi. Dole kuma a kashe shi, bayan kwana uku kuma, yă tashi. Ya yi wannan zance a sarari. Sai Bitrus ya jawo shi gefe, ya fara tsawata masa. Amma da Yesu ya juya ya dubi almajiransa, sai ya tsawata wa Bitrus ya ce, “Tashi daga nan Shaiɗan! Ba ka da al’amuran Allah a zuciyarka, sai na mutane.” Sai ya kira taron wurinsa tare da almajiransa ya ce, “Duk wanda zai bi ni, dole yă ƙi kansa, yă ɗauki gicciyensa yă bi ni. Domin duk mai son ceton ransa zai rasa shi, amma duk wanda ya rasa ransa saboda ni, da kuma bishara, zai same shi. Me mutum zai amfana, in ya ribato duniya duka a bakin ransa? Ko kuma, me mutum zai bayar a musayar ransa? Duk wanda ya ji kunyata, da na kalmomina a wannan zamani na fasikanci da zunubi, Ɗan Mutum ma zai ji kunyarsa lokacin da ya shiga cikin ɗaukakar Ubansa, tare da tsarkakan mala’iku.” Ya kuma ce musu, “Gaskiya nake gaya muku, waɗansu da suke tsattsaye a nan ba za su mutu ba, sai sun ga mulkin Allah ya bayyana da iko.” Bayan kwana shida, sai Yesu ya ɗauki Bitrus, Yaƙub da Yohanna tare da shi, ya kai su kan wani dutse mai tsawo, suka kasance su kaɗai a wurin. A can aka sāke kamanninsa a gabansu. Tufafinsa suka zama fari suna ƙyalli, fiye da yadda wani a duniya zai iya yi su. Iliya da Musa suka bayyana a gabansu, suna magana da Yesu. Bitrus ya ce wa Yesu, “Rabbi, ya yi kyau da muke nan. Bari mu kafa bukkoki guda uku, ɗaya dominka, ɗaya domin Musa, ɗaya kuma domin Iliya.” (Bai san abin da zai faɗa ba ne, gama sun tsorata ƙwarai.) Sai wani girgije ya bayyana, ya rufe su, wata murya kuma ta fito daga girgijen, ta ce, “Wannan Ɗana ne, wanda nake ƙauna, ku saurare shi!” Farat ɗaya, da suka waiwaya, ba su ƙara ganin kowa tare da su ba, sai dai Yesu. Da suna saukowa daga dutsen, Yesu ya umarce su kada su gaya wa kowa abin da suka gani, sai bayan Ɗan Mutum ya tashi daga matattu. Suka riƙe wannan zance a ɓoye tsakaninsu, suna tattaunawa ko mece ce ma’anar “tashi daga matattu.” Suka tambaye shi, suka ce, “Don me malaman dokoki suke cewa, sai Iliya ya fara zuwa?” Yesu ya amsa ya ce, “Gaskiya ne, Iliya zai zo da fari, yă kuma mayar da dukan abubuwa. Don me kuma aka rubuta cewa, dole Ɗan Mutum yă sha wahala sosai, kuma a ƙi shi? Amma ina faɗa muku, Iliya ya riga ya zo, kuma suka yi duk abin da suka ga dama da shi, kamar yadda aka rubuta game da shi.” Da suka dawo wurin sauran almajiran, sai suka ga babban taro kewaye da su, malaman dokoki suna gardama da su. Nan take da dukan mutanen suka ga Yesu, sai suka cika da mamaki, suka ruga da gudu don su gai da shi. Ya tambaye su ya ce, “Gardamar me kuke yi da su?” Wani mutum a cikin taron ya amsa ya ce, “Malam, na kawo maka ɗana mai wani ruhun da yake hana shi magana. Duk lokacin da mugun ruhun ya kama shi, yakan jefa shi a ƙasa. Bakinsa yakan yi kumfa, yă cije haƙorarsa, yakan sa jikinsa ya sandare, yă zama da ƙarfi. Na roƙi almajiranka su fitar da ruhun, amma ba su iya ba.” Yesu ya ce, “Ya ku zamani marar bangaskiya, har yaushe zan kasance tare da ku? Har yaushe zan yi haƙuri da ku? Kawo mini yaron.” Sai suka kawo shi. Da ruhun ya ga Yesu, nan da nan sai ya buge yaron da farfaɗiya. Ya fāɗi a ƙasa, yana birgima, bakinsa yana kumfa. Yesu ya tambayi mahaifin yaron ya ce, “Tun yaushe yake haka?” Ya ce, “Tun yana ƙarami. Ya sha jefa shi cikin wuta, ko ruwa don yă kashe shi. Amma in za ka iya yin wani abu, ka ji tausayinmu ka taimake mu.” Yesu ya ce, “ ‘In za ka iya’? Ai, kome mai yiwuwa ne ga wanda ya gaskata.” Nan da nan mahaifin yaron ya faɗa da ƙarfi ya ce, “Na gaskata, ka taimake ni in sha kan rashin bangaskiyata!” Da Yesu ya ga taron suna zuwa can a guje, sai ya tsawata wa mugun ruhun ya ce, “Kai ruhun kurma, da na bebe, na umarce ka, ka fita daga cikinsa, kada kuma ka ƙara shigarsa.” Sai ruhun ya yi ihu, ya buge shi da ƙarfi da farfaɗiya, ya fita. Yaron ya kwanta kamar matacce, har mutane da yawa suka ce, “Ai, ya mutu.” Amma Yesu ya kama shi a hannu ya ɗaga, ya kuwa tashi tsaye. Da Yesu ya shiga gida, almajiransa suka tambaye shi a ɓoye, suka ce, “Me ya sa ba mu iya fitar da shi ba?” Ya amsa ya ce, “Sai da addu’a kaɗai irin wannan yakan fita.” Suka bar wurin suka bi ta Galili. Yesu bai so wani yă san inda suke ba, gama yana koya wa almajiransa. Ya ce musu, “Za a ci amanar Ɗan Mutum, a ba da shi ga hannun mutane. Za su kashe shi, bayan kwana uku kuma zai tashi.” Amma ba su fahimci abin da yake nufi ba, suka kuma ji tsoro su tambaye shi game da wannan. Suka iso Kafarnahum. Da yana cikin gida, sai ya tambaye su ya ce, “Gardamar me kuke yi a hanya?” Amma suka yi shiru, don a hanya suna gardama ne, a kan ko wane ne a cikinsu ya fi girma? Da Yesu ya zauna, sai ya kira Sha Biyun ya ce, “In wani yana so yă zama na fari, dole yă zama na ƙarshe duka, da kuma bawan kowa.” Ya ɗauki wani ƙaramin yaro ya sa yă tsaya a tsakiyarsu. Ya ɗauke shi a hannunsa, ya ce musu, “Duk wanda ya karɓi ɗaya daga cikin waɗannan ƙananan yara a cikin sunana, ni ya karɓa. Duk wanda kuma ya karɓe ni, ba ni ya karɓa ba, amma wanda ya aiko ni ne ya karɓa.” Yohanna ya ce, “Malam mun ga wani mutum yana fitar da aljanu a cikin sunanka, sai muka ce yă daina, domin shi ba ɗaya daga cikinmu ba ne.” Yesu ya ce, “Kada ku hana shi. Ba wanda yake yin ayyukan banmamaki a cikin sunana, nan take yă faɗi wani abu mummuna game da ni. Gama duk wanda ba ya gāba da mu, namu ne. Gaskiya nake gaya muku, duk wanda ya ba ku ruwan sha a sunana, saboda ku na Kiristi ne, lalle, ba zai rasa ladarsa ba. “Idan kuma wani yă sa ɗaya daga cikin waɗannan ’yan yara masu gaskatawa da ni yă yi laifi, zai fiye masa a rataya wani babban dutsen niƙa a wuyarsa, a jefa shi cikin teku. In hannunka yana sa ka yin zunubi, yanke shi. Ai, gwamma ka shiga rai da hannu ɗaya, da ka shiga jahannama ta wuta, inda ba a iya kashe wutar ba, da hannuwanka biyu. In kuma ƙafarka tana sa ka yin zunubi, yanke ta. Ai, gwamma ka shiga rai da ƙafa ɗaya, da a jefa ka cikin jahannama ta wuta, da ƙafafunka biyu. In kuma idonka yana sa ka zunubi, ƙwaƙule shi. Ai, gwamma ka shiga mulkin Allah da ido ɗaya, da a jefa ka cikin jahannama ta wuta, da idanu biyu, inda “ ‘tsutsotsinsu ba sa mutuwa, wutar kuma ba a iya kashewa.’ Za a tsarkake kowa da wuta. “Gishiri yana da daɗi, amma in ya rabu da ɗanɗanonsa, ta yaya za a sāke mai da ɗanɗanonsa? Ku kasance da gishiri a cikinku, ku kuma yi zauna lafiya da juna.” Sai Yesu ya tashi daga nan ya tafi yankin Yahudiya, da kuma ƙetaren Urdun. Taron mutane suka sāke zuwa wurinsa, ya kuma koya musu kamar yadda ya saba. Waɗansu Farisiyawa suka zo suka gwada shi, ta wurin yin masa tambaya cewa, “Daidai ne bisa ga doka, mutum yă saki matarsa?” Ya amsa ya ce, “Me Musa ya umarce ku?” Suka ce, “Musa ya ba da izini mutum yă rubuta takardar saki, yă kuma kore ta.” Yesu ya ce, “Saboda taurin kanku ne, Musa ya rubuta muku wannan doka. Amma a farkon halitta, Allah ya ‘halicce su miji da mace.’ ‘Saboda wannan dalili, mutum zai bar mahaifinsa da mahaifiyarsa, yă manne wa matarsa, su biyun kuma za su zama jiki ɗaya.’ Saboda haka, su ba mutum biyu ba ne, amma mutum ɗaya. Domin haka, abin da Allah ya haɗa, kada mutum yă raba.” Da suna cikin gida kuma, sai almajiran suka tambayi Yesu game da wannan. Ya amsa ya ce, “Duk wanda ya saki matarsa, ya auri wata, yana da laifin aikata zina a kan matar da ya saki. In kuma ta saki mijinta ta auri wani, ta yi zina ke nan.” Mutane suka kawo ƙananan yara wurin Yesu don yă taɓa su, amma almajiran suka kwaɓe su. Da Yesu ya ga haka, sai ya yi fushi, ya ce musu, “Ku bar yara ƙanana su zo wurina, kada ku hana su, gama mulkin Allah na irin waɗannan ne. Gaskiya nake gaya muku, duk wanda bai karɓi mulkin Allah kamar ƙaramin yaro ba, ba zai taɓa shiga mulkin ba.” Sai ya ɗauki yaran a hannuwansa, ya ɗibiya musu hannuwansa, ya kuma albarkace su. Da Yesu ya kama hanya, sai wani mutum ya ruga da gudu ya zo wajensa, ya durƙusa a gabansa ya ce, “Malam nagari, me zan yi domin in gāji rai madawwami?” Yesu ya amsa ya ce, “Don me kake ce da ni mai nagarta? Ai, ba wani nagari, sai Allah kaɗai. Ka san dokokin da suka ce, ‘Kada ka yi kisankai, kada ka yi zina, kada ka yi sata, kada ka ba da shaida ta ƙarya, kada ka cuci wani, ka girmama mahaifinka da mahaifiyarka.’ ” Mutumin ya ce, “Malam, ai, tun ina yaro na kiyaye duk waɗannan.” Yesu ya kalle shi da ƙauna ya ce, “Abu ɗaya ka rasa, ka tafi ka sayar da duk abin da kake da shi, ka ba wa matalauta, za ka kuwa sami dukiya a sama. Sa’an nan ka zo ka bi ni.” Da jin wannan, sai mutumin ya ɓata fuskarsa, ya tafi da baƙin ciki, gama yana da arziki sosai. Yesu ya dudduba, sai ya ce wa almajiransa, “Yana da wuya fa masu arziki su shiga mulkin Allah!” Almajiransa suka yi mamakin kalmominsa. Amma Yesu ya sāke ce musu, “’Ya’yana, yana da wuya fa a shiga mulkin Allah! Ya fi sauƙi raƙumi yă shiga ta kafar allura, da mai arziki yă shiga mulkin Allah.” Almajiran suka yi mamaki ƙwarai, suka ce wa juna, “To, wa zai sami ceto ke nan?” Yesu ya kalle su ya ce, “Ga mutum kam, wannan ba mai yiwuwa ba ne, amma ga Allah, wannan mai yiwuwa ne; dukan abubuwa masu yiwuwa ne ga Allah.” Bitrus ya ce, “Mun bar kome domin mu bi ka!” Yesu ya amsa ya ce, “Gaskiya nake gaya muku, babu wanda zai bar gida, ko ’yan’uwa maza da mata, ko mahaifiya, ko mahaifi, ko ’ya’ya, ko gonaki saboda ni, da kuma bishara, sa’an nan yă kāsa samun ninkinsu ɗari a zamanin yanzu (na gidaje, da ’yan’uwa mata, da ’yan’uwa maza, da uwaye, da ’ya’ya, da gonaki amma tare da tsanani) a lahira kuma yă sami rai madawwami. Amma da yawa da suke na farko, za su zama na ƙarshe, na ƙarshe kuma, za su zama na farko.” Suna haurawa a hanyarsu zuwa Urushalima ke nan, Yesu yana a gaba, almajiran suna bin sa suna mamaki, waɗanda suke bi kuma suna ji tsoro. Ya sāke kai Sha Biyun nan gefe, ya gaya musu abin da zai faru da shi. Ya ce, “Za mu haura zuwa Urushalima, za a bashe Ɗan Mutum, ga manyan firistoci da malaman dokoki. Za su yi masa hukuncin kisa, a kuma ba da shi ga Al’ummai, waɗanda za su yi masa ba’a, su tofa masa miyau, su yi masa bulala, su kuma kashe shi. Bayan kwana uku kuma yă tashi.” Sai Yaƙub da Yohanna, ’ya’yan Zebedi maza suka zo wurinsa suka ce, “Malam, muna so ka yi mana duk abin da muka roƙa.” Ya tambaye su ya ce, “Me kuke so in yi muku?” Suka amsa suka ce, “Ka bar ɗayanmu yă zauna a damarka, ɗayan kuma a hagunka, a cikin ɗaukakarka.” Yesu ya ce, “Ba ku san abin da kuke roƙo ba. Za ku iya shan kwaf da zan sha, ko a yi muku baftisma da baftismar da aka yi mini?” Suka ce, “Za mu iya.” Yesu ya ce musu, “Za ku sha kwaf da zan sha, a kuma yi muku baftisma da aka yi mini, amma zama a damana ko haguna, ba ni nake ba da izinin ba. Waɗannan wurare na waɗanda aka riga aka shirya musu ne.” Da sauran goman suka ji wannan, sai suka yi fushi da Yaƙub da Yohanna. Yesu ya kira su ya ce musu, “Kun sani waɗanda aka san su da mulkin al’ummai sukan nuna musu iko, hakimansu ma sukan gasa musu iko. Ba haka ya kamata yă zama da ku ba. A maimakon, duk wanda yake so yă zama babba a cikinku, dole yă zama bawanku. Duk wanda kuma yake so yă zama na farko, dole yă zama bawan kowa. Gama ko Ɗan Mutum ma, bai zo domin a bauta masa ba, amma don yă yi bauta, yă kuma ba da ransa fansa saboda mutane da yawa.” Sai suka iso Yeriko. Sa’ad da Yesu da almajiransa tare da taro mai yawa suke barin birnin, wani makaho da ake kira Bartimawus kuwa (wato, “ɗan Timawus”), yana zaune a gefen hanya yana bara. Da ya ji cewa Yesu Banazare ne, sai ya ɗaga murya, yana cewa, “Yesu Ɗan Dawuda, ka yi mini jinƙai!” Mutane da yawa suka kwaɓe shi, suka ce yă yi shiru, amma ya ƙara ɗaga murya yana cewa, “Ɗan Dawuda, ka yi mini jinƙai!” Yesu ya tsaya ya ce, “Ku kira shi.” Sai suka kira makahon suka ce, “Ka yi farin ciki! Tashi tsaye! Yana kiranka.” Ya jefar da mayafinsa waje ɗaya, ya yi wuf, ya zo wurin Yesu. Yesu ya tambaye shi ya ce, “Me kake so in yi maka?” Makahon ya ce, “Rabbi, ina so in sami ganin gari.” Yesu ya ce, “Je ka, bangaskiyarka ta warkar da kai.” Nan da nan, ya sami ganin gari, ya kuma bi Yesu suka tafi. Sa’ad da suka yi kusa da Urushalima, suka zo Betfaji da Betani wajen Dutsen Zaitun, sai Yesu ya aiki biyu daga cikin almajiransa, ya ce musu, “Ku je ƙauyen da yake gaba da ku, da shigarku, za ku tarar da wani ɗan jaki a daure a can, wanda ba wanda ya taɓa hawa. Ku kunce shi ku kawo nan. In wani ya tambaye ku, ‘Don me kuke yin haka?’ Ku gaya masa cewa, ‘Ubangiji yana bukatarsa, zai kuma dawo da shi ba da jimawa ba.’ ” Suka tafi, suka kuwa tarar da wani ɗan jaki a waje, a titi, daure a ƙofar gida. Suna cikin kunce shi ke nan, sai waɗansu mutane da suke tsattsaye a wurin suka ce musu, “Me kuke yi da kuke kunce ɗan jakin nan?” Suka amsa kamar yadda Yesu ya ce su yi. Mutanen kuwa suka ƙyale su. Da suka kawo shi wajen Yesu, sai suka shimfiɗa rigunarsu a bayansa. Yesu kuwa ya hau ya zauna bisansa. Mutane da yawa suka shimfiɗa rigunarsu a kan hanya, waɗansu kuma suka baza rassan itatuwan da suka sara daga gonaki. Waɗanda suka yi gaba, da kuma waɗanda suke biye, duk suka ɗaga murya, suna cewa, “Hosanna! ” “Mai albarka ne wanda yake zuwa a cikin sunan Ubangiji!” “Mai albarka ne mulkin nan mai zuwa na mahaifinmu Dawuda!” “Hosanna a can cikin samaniya!” Yesu ya shiga Urushalima ya kuma tafi filin haikali. Ya dudduba kome duka, amma da yake yamma ta yi, sai ya tafi Betani tare da Sha Biyun. Kashegari, da suke barin Betani, Yesu kuwa ya ji yunwa. Da ya hangi wani itacen ɓaure mai ganye, sai ya je domin yă ga ko yana da ’ya’ya. Amma da ya kai can, bai tarar da kome ba sai ganye, domin ba lokacin ’ya’yan ɓaure ba ne. Sai ya ce wa itacen, “Kada kowa yă ƙara cin ’ya’yanka.” Almajiransa kuwa suka ji ya faɗi haka. Da suka kai Urushalima, sai Yesu ya shiga filin haikalin, ya fara korar waɗanda suke saya da sayarwa a can. Ya tutture tebur na masu musayar kuɗi, da kujerun masu sayar da tattabaru, ya kuma hana kowa yă ratsa da a filin haikali ɗauke da kayan ciniki. Da yake koya musu, sai ya ce, “Ashe, ba a rubuce yake ba cewa, ‘Za a kira gidana, gidan addu’a na dukan al’ummai ba’? Amma ga shi kun mai da shi ‘kogon ’yan fashi.’ ” Manyan firistoci da malaman dokoki suka ji wannan, sai suka fara neman hanyar da za su kashe shi, gama suna jin tsoronsa, saboda dukan taron suna mamakin koyarwarsa. Da yamma ta yi, sai Yesu da almajiransa suka bar garin. Da safe, da suke wucewa, sai suka ga itacen ɓauren nan ya yanƙwane tun daga saiwarsa. Bitrus ya tuna, sai ya ce wa Yesu, “Rabbi, duba! Itacen ɓauren nan da ka la’anta, ya yanƙwane!” Yesu ya amsa ya ce, “Ku gaskata da Allah. Gaskiya nake gaya muku, in wani ya ce wa dutsen nan, ‘Je ka, ka fāɗa cikin teku,’ bai kuwa yi shakka a zuciyarsa ba, amma ya gaskata cewa, abin da ya faɗa zai faru, haka kuwa za a yi masa. Saboda haka, ina faɗa muku, duk abin da kuka roƙa cikin addu’a, ku gaskata kun riga kun karɓa, zai kuwa zama naku. A duk lokacin da kuke tsaye cikin addu’a, in kuna riƙe da wani mutum a zuciyarku, ku gafarta masa, domin Ubanku da yake sama shi ma yă gafarta muku zunubanku.” Suka sāke dawowa cikin Urushalima. Da Yesu yana tafiya a filin haikali, sai manyan firistoci, malaman dokoki da kuma dattawa suka zo wurinsa. Suka tambaye, shi suka ce, “Da wane iko kake yin waɗannan abubuwa? Wa kuma ya ba ka ikon yin wannan?” Yesu ya ce, “Zan yi muku tambaya guda. Ku ba ni amsa, ni kuma zan gaya muku, ko da wane iko nake yin waɗannan abubuwa. Baftismar Yohanna, daga sama ce, ko daga mutane? Ku faɗa mini!” Sai suka tattauna a junansu, suka ce, “In muka ce, ‘Daga sama ne,’ zai ce, ‘To, don me ba ku gaskata shi ba?’ In kuma muka ce, ‘Daga wurin mutane ne’; suna jin tsoron mutane, don kowa ya ɗauka cewa, Yohanna, annabi ne na gaskiya.” Saboda haka, suka amsa wa Yesu suka ce, “Ba mu sani ba.” Yesu ya ce, “To, ni ma ba zan gaya muku ko da wane iko nake yin waɗannan abubuwa ba.” Sa’an nan ya fara yi musu magana da misalai ya ce, “Wani mutum ya shuka gonar inabi. Ya kewaye ta da katanga, ya haƙa rami domin matsin inabin, ya kuma gina ɗakin gadi. Sai ya ba wa waɗansu manoma hayar gonar inabin, sa’an nan ya yi tafiya. Da lokacin girbi ya yi, sai ya aiki wani bawa wajen ’yan hayan, don yă karɓo masa ’ya’yan inabin daga wurinsu. Amma suka kama shi, suka yi masa dūka, suka kore shi hannun wofi. Sai ya sāke aikan wani bawa wurinsu, amma suka bugi wannan mutum a kai, suka wulaƙanta shi. Har yanzu ya sāke aikan wani. Wannan kuwa suka kashe. Ya aika waɗansu da yawa; suka bubbuge waɗansu, sauran kuwa suka kashe. “Sauran mutum ɗaya da ya rage ya aika, ɗa, da yake ƙauna. Daga ƙarshe sai ya aike shi, yana cewa, ‘Za su girmama ɗana.’ “Amma ’yan hayan suka ce wa juna, ‘Aha! Wannan shi ne magājin. Ku zo mu kashe shi, gādon kuma yă zama namu.’ Sai suka kama shi suka kashe, suka jefa shi bayan gonar inabin. “To, me, mai gonar inabin zai yi ke nan? Zai zo yă karkashe dukan ’yan hayan nan, ya kuma ba wa waɗansu gonar inabin. Ba ku taɓa karanta wannan Nassi ba, “ ‘Dutsen da magina suka ƙi, shi ne kuwa ya zama dutsen kusurwan gini. Ubangiji ya yi wannan, ya kuma yi kyau a idanunmu’?” Sai manyan Firistoci da malaman dokoki da shugabanni suka nemi hanyar da za su kama shi, domin sun gane ya yi misalin a kansu ne. Amma suka ji tsoron taron, saboda haka suka bar shi suka yi tafiyarsu. Daga baya, sai suka tura waɗansu Farisiyawa da mutanen Hiridus zuwa wurin Yesu, domin su sa masa tarko a cikin maganarsa. Suka zo wurinsa suka ce, “Malam, mun san kai mutum ne mai mutunci. Ba ka bin ra’ayin mutane, don ba ka nuna bambanci. Amma kana koyar da hanyar Allah bisa ga gaskiya. Daidai ne a biya wa Kaisar haraji, ko babu? Mu biya ko kada mu biya?” Amma Yesu ya san munafuncinsu, sai ya yi tambaya ya ce, “Don me kuke ƙoƙarin sa mini tarko? Ku kawo mini dinari in ga.” Suka kawo masa kuɗin, sai ya tambaye, su ya ce, “Hoton wane ne wannan? Kuma rubutun wane ne wannan?” Suka ce, “Na Kaisar.” Sai Yesu ya ce musu, “Ku ba wa Kaisar abin da yake na Kaisar, ku ba wa Allah kuma abin da yake na Allah.” Suka yi mamakinsa ƙwarai. Sa’an nan Sadukiyawa da suke cewa, babu tashin matattu, suka zo masa da tambaya. Suka ce, “Malam, Musa ya rubuta mana cewa, in ɗan’uwan wani mutum ya mutu, ya bar mata babu ’ya’ya, dole mutumin ya auri gwauruwar, yă kuma samo wa ɗan’uwansa ’ya’ya. To, an yi waɗansu ’yan’uwa guda bakwai. Na fari ya yi aure, ya mutu babu ’ya’ya. Na biyun ya auri gwauruwar, sai shi ma ya mutu, babu ’ya’ya. Haka kuma na ukun. A gaskiya, ba ko ɗaya daga cikin bakwai ɗin da ya bar ’ya’ya. Daga ƙarshe, macen ta mutu. To, a tashin matattu, matar wa za tă zama, don duk su bakwai nan sun aure ta?” Yesu ya ce, “Ashe, ba a cikin kuskure kuke ba saboda rashin sanin Nassi, ko ikon Allah? Sa’ad da matattu suka tashi, ba za su yi aure ba, ba kuwa za a ba da su ga aure ba. Za su zama kamar yadda mala’iku suke a cikin sama. Game da tashin matattu kuwa, ashe, ba ku karanta a cikin littafin Musa ba, game da labarin ɗan kurmin nan mai cin wuta da Musa ya gani a jeji, yadda Allah ya yi magana da shi ya ce, ‘Ni ne Allah na Ibrahim, Allah na Ishaku da kuma Allah na Yaƙub’? Shi ba Allah na matattu ba ne, shi Allah na masu rai ne. Kun yi mummunan kuskure!” Wani daga cikin malaman dokoki ya zo ya ji suna muhawwara. Da ya lura cewa Yesu ya amsa musu daidai, sai ya tambaye shi ya ce, “A cikin dukan dokoki, wacce ta fi girma duka?” Yesu ya ce, “Wadda ta fi girma duka, ita ce wannan. ‘Ku saurara, ya Isra’ila, Ubangiji Allahnmu, Ubangiji ɗaya ne. Ka ƙaunaci Ubangiji Allahnka da dukan zuciyarka, da dukan ranka, da dukan hankalinka, da kuma dukan ƙarfinka.’ Na biyun ita ce, ‘Ka ƙaunaci maƙwabcinka kamar kanka.’ Ba wata doka da ta fi waɗannan.” Mutumin ya ce, “Malam, ka faɗi daidai. Daidai ne da ka ce, Allah ɗaya ne, babu kuma wani sai shi. Nuna ƙauna ga Allah da dukan zuciyarka, da dukan ganewarka, da dukan ƙarfinka, da kuma nuna ƙauna ga maƙwabcinka kamar kanka, ya fi dukan hadayun ƙonawa da sadakoki.” Da Yesu ya ga ya amsa da hikima, sai ya ce masa, “Ba ka da nisa da mulkin Allah.” Daga lokacin, ba wanda ya yi karambani yin masa wata tambaya. Yayinda Yesu yake koyarwa a filin haikalin, sai ya yi tambaya ya ce, “Yaya malaman dokoki suke cewa Kiristi ɗan Dawuda ne? Dawuda da kansa ya yi magana ta wurin Ruhu Mai Tsarki ya ce, “ ‘Ubangiji ya ce wa Ubangijina, “Zauna a hannun damana sai na sa abokan gābanka a ƙarƙashin sawunka.” ’ Dawuda da kansa ya kira shi ‘Ubangiji.’ To, ta yaya zai zama ɗansa?” Taro mai yawa suka saurare shi da murna. Sa’ad da Yesu yake koyarwa ya ce, “Ku lura da malaman dokoki. Sukan so yin tafiya a manyan riguna, a kuma dinga gaishe su a wuraren kasuwanci. Sukan kuma nemi wuraren zama mafi daraja a majami’u, da kuma wuraren zaman manya a bukukkuwa. Suna ƙwace gidajen gwauraye, kuma don nuna iyawa, sukan yi dogayen addu’o’i. Irin mutanen nan, za su sha hukunci mai tsanani sosai.” Yesu ya zauna ɗaura da inda ake bayarwa, ya kuma dubi yadda taron suke sa kuɗinsu a cikin ɗakunan ajiya haikali. Masu arziki da yawa suka zuba kuɗaɗe masu yawa. Amma wata matalauciya gwauruwa, ta zo ta saka anini biyu, da suka yi daidai da rabin kobo. Yesu ya kira almajiransa wurinsa ya ce, “Gaskiya nake gaya muku, abin da matalauciya gwauruwan nan ta zuba cikin ɗakunan ajiya nan ya fi na sauran dukan. Dukansu sun bayar ne daga cikin arzikinsu; ita kuwa, daga cikin talaucinta, ta ba da kome, duk abin da take da shi na rayuwa.” Da yake barin haikalin, sai ɗaya daga cikin almajiransa ya ce masa, “Malam! Dubi irin manya-manyan duwatsun nan! Ka ga irin gine-ginen nan masu kyau mana!” Yesu ya amsa ya ce, “Ka ga dukan manyan gine-ginen nan? Ba wani dutse a nan, da za a bari kan wani da ba za a rushe ba.” Da Yesu yana zaune a kan Dutsen Zaitun da yake ɗaura da haikali, sai Bitrus, Yaƙub, Yohanna da kuma Andarawus, suka tambaye shi a ɓoye, suka ce, “Ka gaya mana, yaushe waɗannan abubuwa za su faru? Wace alama ce kuma za tă nuna cewa, duk waɗannan suna dab da cikawa?” Sai Yesu ya ce musu, “Ku lura fa kada wani yă ruɗe ku. Da yawa za su zo a cikin sunana, suna cewa, ‘Ni ne shi.’ Za su kuwa ruɗi mutane da yawa. Sa’ad da kuka ji labarun yaƙe-yaƙe da jita-jitar yaƙe-yaƙe, kada hankalinku yă tashi. Dole irin waɗannan abubuwa su faru. Amma ƙarshen tukuna. Al’umma za tă tasar wa al’umma, mulki kuma yă tasar wa mulki. Za a yi girgizar ƙasa a wurare dabam-dabam, a kuma yi yunwa. Waɗannan dai mafarin azabar naƙuda. “Dole ku yi zaman tsaro. Za a ba da ku ga hukuma, a kuma bulale ku a majami’u. Saboda ni kuma, za ku tsaya a gaban gwamnoni da sarakuna, domin ku ba da shaida a gabansu. Dole sai an fara yin wa’azin bishara ga dukan al’ummai. Sa’ad da aka kama ku, aka kuma kai ku don a yi muku shari’a, kada ku damu da abin da za ku faɗa. Sai dai ku faɗi abin da aka ba ku a lokacin. Gama ba ku kuke magana ba, Ruhu Mai Tsarki ne. “Ɗan’uwa zai ba da ɗan’uwa a kashe. Mahaifi zai ba da ɗansa. ’Ya’ya za su tayar wa iyayensu, su kuma sa a kashe su. Dukan mutane za su ƙi ku saboda ni, amma wanda ya tsaya da ƙarfi har ƙarshe, zai sami ceto. “Sa’ad da kuka ga ‘abin ƙyama, mai kawo hallaka’ tsaye inda bai kamata ba (mai karatu ya gane), to, sai waɗanda suke a Yahudiya su gudu zuwa duwatsu. Kada wani da yake kan rufin gidansa yă sauka, ko yă shiga gida don yă ɗauki wani abu. Kada wani da yake gona kuma yă koma don ɗaukar rigarsa. Kaiton mata masu ciki, da mata masu renon ’ya’ya a waɗancan kwanakin! Ku yi addu’a, kada wannan yă faru a lokacin sanyi. Domin waɗancan kwanakin za su zama kwanaki na baƙin ciki, waɗanda ba a taɓa yin irinsa ba tun farkon halitta, har yă zuwa yanzu, ba kuwa za a sāke yin irinsa ba. “Da ba don Ubangiji ya rage kwanakin nan ba, da ba wani da zai tsira. Amma saboda zaɓaɓɓu waɗanda ya zaɓa, sai ya rage kwanakin. A lokacin nan, in wani ya ce muku, ‘Duba, ga Kiristi nan!’ Ko kuwa, ‘Duba, ga shi can!’ Kada ku gaskata. Gama Kiristi masu yawa na ƙarya, da annabawan ƙarya za su firfito, su kuma aikata manyan alamu da ayyukan banmamaki don su ruɗi har da zaɓaɓɓu ma in zai yiwu. Amma ku kula! Na dai gaya muku kome tun da wuri. “Amma waɗancan kwanaki, bayan baƙin azaban nan, “ ‘rana za tă yi duhu, wata kuma ba zai ba da haskensa ba; taurari za su fāffāɗo daga sararin sama. Za a kuma girgiza manyan abubuwan da suke a sararin sama.’ “Sa’an nan, mutane za su ga Ɗan Mutum yana zuwa cikin gizagizai da iko, da ɗaukaka mai girma. Zai kuma aiko mala’ikunsa su tattaro zaɓaɓɓunsa daga kusurwoyi huɗun nan, daga iyakar duniya har yă zuwa iyakar sama. “To, sai ku yi koyi da itacen ɓaure. Da zarar rassansa suka yi taushi, ganyayensa kuma suka toho, kun san cewa damina ta yi kusa ke nan. Haka ma, in kuka ga waɗannan abubuwa suna faruwa, ku san cewa ya yi kusan zuwa, yana ma dab da bakin ƙofa. Gaskiya nake gaya muku, zamanin nan ba zai shuɗe ba sai duk abubuwan nan sun faru. Sama da ƙasa za su shuɗe, amma kalmomina ba za su taɓa shuɗewa ba. “Game da wannan rana ko sa’a kuwa, ba wanda ya sani, ko mala’ikun da suke sama, ko Ɗan, sai Uban kaɗai. Ku lura fa! Ku zauna a shirye! Don ba ku san lokacin da shi zai zo ba. Yana kama da mutumin da zai yi tafiya. Yakan bar gidansa a hannun bayinsa, kowa da nasa aikin da aka sa shi, yă kuma ce wa wanda yake gadin ƙofa, yă yi tsaro. “Saboda haka, sai ku zauna a shirye, domin ba ku san lokacin da maigidan zai dawo ba, ko da yamma ne, ko da tsakar dare ne, ko lokacin da zakara na cara ne, ko kuma da safe ne. In ya zo kwaram, kada ka bari yă tarar da kai kana barci. Abin da na faɗa muku, na faɗa wa kowa. ‘Ku yi tsaro!’ ” To, saura kwana biyu ne kaɗai a yi Bikin Ƙetarewa da Bikin Burodi Marar Yisti, sai manyan firistoci da malaman dokoki, suka nemi wani dalili su kama Yesu a ɓoye, su kashe. Suka ce, “Ba a lokacin Biki ba, don kada mutane su yi tawaye.” Yayinda yake a Betani, a gidan wani mutumin da ake kira Siman Kuturu, yana cin abinci, sai wata mace ta zo da wani ɗan tulu na turaren alabasta da aka yi da nardi zalla, mai tsadan gaske. Ta fasa tulun, ta kuma zuba turaren a kansa. Waɗansu daga cikin waɗanda suke wurin, suka ji haushi, suka ce wa juna, “Me ya sa za a ɓata turaren nan haka? Da an sayar da shi, ai, da an sami kuɗi fiye da albashi ma’aikaci na shekara guda, a ba wa matalauta. Sai suka tsawata mata da zafi.” Yesu ya ce, “Ku ƙyale ta mana. Don me kuke damunta? Ta yi abu mai kyau a gare ni. Matalauta dai suna tare da ku kullum, za ku kuma iya taimakonsu a duk lokacin da kuke so. Amma ni ba zan kasance da ku kullum ba. Ta yi abin da ta iya yi. Ta zuba turare a jikina kafin lokaci, don shirin jana’izata. Gaskiya nake gaya muku, duk inda aka yi wa’azin bishara ko’ina a duniya, za a faɗi abin da ta yi, domin tunawa da ita.” Sai Yahuda Iskariyot, ɗaya daga cikin Sha Biyun nan, ya je wajen manyan firistoci don yă bashe Yesu a gare su. Suka yi murna da jin haka, suka yi alkawari za su ba shi kuɗi. Don haka, ya fara neman zarafi yă ba da shi. A rana ta fari ta Bikin Burodi Marar Yisti, lokacin da akan yanka ɗan ragon hadayar kafara, bisa ga al’ada ta tunawa da Bikin Ƙetarewa, sai almajiran Yesu suka tambaye shi, suka ce, “Ina kake so mu je mu shirya maka wurin da za ka ci Bikin Ƙetarewa?” Sai ya aiki biyu daga cikin almajiransa ya ce, “Ku shiga cikin birni, za ku sadu da wani ɗauke da tulun ruwa. Ku bi shi. Gidan da ya shiga, ku gaya wa maigidan cewa, ‘Malam yana tambaya, ina ɗakin baƙina, inda zan ci Bikin Ƙetarewa tare da almajiraina?’ Zai nuna muku wani babban ɗakin sama da aka shirya domin baƙi. Ku yi mana shirin a can.” Almajiran suka tafi, suka shiga cikin birnin, suka kuwa tarar da kome kamar yadda Yesu ya faɗa musu. Sai suka shirya Bikin Ƙetarewa. Da yamma ta yi, sai Yesu ya zo tare da Sha Biyun. Yayinda suke cin abinci a tebur, sai ya ce, “Gaskiya nake gaya muku, ɗaya daga cikinku zai bashe ni, wani wanda yake ci tare da ni.” Suka cika da baƙin ciki, da ɗaya-ɗaya suka ce masa, “Tabbatacce, ba ni ba ne, ko?” Ya ce, “Ɗaya daga cikin Sha Biyun ne, wanda yake ci tare da ni a kwano. Ɗan Mutum zai tafi kamar yadda yake a rubuce game da shi, amma kaiton mutumin da ya bashe Ɗan Mutum! Zai fi masa, da ba a haife shi ba.” Yayinda suke cin abinci, sai Yesu ya ɗauki burodi, ya yi godiya, ya kakkarya, ya ba wa almajiransa, yana cewa, “Ku karɓa, wannan jikina ne.” Sai kuma ya ɗauki kwaf ruwan inabi, ya yi godiya, ya kuma miƙa musu, dukansu suka sha daga ciki. Sai ya ce musu, “Wannan jinina ne na alkawari, wanda aka zubar da shi saboda mutane da yawa. Gaskiya nake gaya muku, ‘Ba zan ƙara sha daga ’ya’yan inabi ba, sai ranan nan, da zan sha shi sabo a mulkin Allah.’ ” Da suka rera waƙa, sai suka fita, suka tafi Dutsen Zaitun. Yesu ya ce musu, “Dukanku za ku ja da baya ku bar ni, gama yana a rubuce cewa, “ ‘Zan bugi makiyayin tumaki, tumakin kuwa za su warwatse.’ Amma bayan na tashi, zan sha gabanku zuwa Galili.” Bitrus ya ce, “Ko da duka sun ja da baya suka bar ka, ba zan bar ka ba.” Yesu ya ce, “Gaskiya nake faɗa maka, yau, tabbatacce, a daren nan, kafin zakara yă yi cara sau biyu kai da kanka za ka yi mūsun sanina sau uku.” Amma Bitrus ya yi ta nanatawa da ƙarfi ya ce, “Ko da zan mutu tare da kai, ba zan taɓa yin mūsun saninka ba.” Duk sauran ma suka ce haka. Suka tafi wani wurin da ake kira Getsemane, Yesu ya kuma ce wa almajiransa, “Ku zauna a nan, yayinda ni kuwa in yi addu’a.” Ya tafi tare da Bitrus, Yaƙub da kuma Yohanna. Sai ya fara baƙin ciki da damuwa ƙwarai. Sai ya ce musu, “Raina yana cike da baƙin ciki har ma kamar zan mutu. Ku dakata a nan ku yi tsaro.” Sai ya yi gaba kaɗan, ya fāɗi a ƙasa, ya yi addu’a, ya ce in mai yiwuwa ne, a ɗauke masa wannan sa’a. Ya ce, “Ya Abba, Uba, kome mai yiwuwa ne a gare ka. Ka ɗauke mini wannan kwaf. Amma ba abin da nake so ba, sai dai abin da kake so.” Sai ya koma wajen almajiransa, ya same su suna barci. Ya ce wa Bitrus, “Siman, kana barci ne? Ka kāsa yin tsaro na sa’a ɗaya? Ku yi tsaro, ku kuma yi addu’a, domin kada ku fāɗi cikin jarraba. Ruhu yana so, sai dai jiki raunana ne.” Ya sāke komawa, ya maimaita addu’ar da ya yi. Da ya dawo, ya sāke tarar da su suna barci, domin barci ya cika musu ido. Suka rasa abin da za su ce masa. Da ya koma sau na uku, sai ya ce musu, “Har yanzu kuna barci, kuna hutawa ba? Ya isa! Lokaci ya yi. Duba an ba da Ɗan Mutum a hannun masu zunubi. Ku tashi! Mu tafi! Ga mai bashe ni ɗin yana zuwa!” Yana cikin magana ke nan, sai Yahuda, ɗaya daga cikin Sha Biyun ya bayyana. Ya zo tare da taro da suke riƙe da takuba da sanduna. Manyan firistoci da malaman dokoki, da kuma dattawa ne suka turo taron. Mai bashe shi ɗin ya riga ya shirya alama da su cewa, “Wanda na yi wa sumba, shi ne mutumin, ku kama shi, ku riƙe sosai.” Nan da nan Yahuda ya je wurin Yesu ya ce, “Rabbi!” Ya kuma yi masa sumba. Mutanen kuwa suka kama Yesu, suka riƙe shi. Sai wani cikin waɗanda suke tsattsaye kusa ya zāre takobinsa, ya sare kunnen bawan babban firist. Yesu ya ce, “Ina jagoran wani tawaye ne da kuka fito da takuba da kuma sanduna domin ku kama ni? Kowace rana ina tare da ku, ina koyarwa a filin haikali, ba ku kama ni ba. Amma dole a cika Nassi.” Sai kowa ya yashe shi ya gudu. Wani saurayin da ba ya sanye da kome sai rigar lilin, yana bin Yesu. Da suka yi ƙoƙarin kama shi, sai ya gudu ya bar rigarsa, ya gudu tsirara. Suka kai Yesu wajen babban firist, sai dukan manyan firistoci, dattawa da kuma malaman dokoki suka taru. Bitrus ya bi shi daga nesa, har cikin filin gidan babban firist. A can, ya zauna tare da masu gadi, yana jin ɗumin wuta. Manyan firistoci da dukan ’yan Majalisa, suka shiga neman shaidar laifin da za a tabbatar a kan Yesu, domin su kashe shi. Amma ba su sami ko ɗaya ba. Da yawa suka ba da shaidar ƙarya a kansa, amma shaidarsu ba tă zo ɗaya ba. Sai waɗansu suka miƙe tsaye, suka ba da wannan shaida ƙarya a kansa, suka ce, “Mun ji shi ya ce, ‘Zan rushe wannan haikali da mutum ya gina, cikin kwana uku, in sāke gina wani wanda ba ginin mutum ba.’ ” Duk da haka ma, shaidarsu ba tă zo ɗaya ba. Sai babban firist ya tashi a gabansu, ya tambayi Yesu ya ce, “Ba za ka amsa ba? Wane shaida ke nan waɗannan mutane suke kawowa a kanka?” Amma Yesu ya yi shiru, bai kuwa amsa ba. Babban firist ya sāke tambayarsa ya ce, “Kai ne Kiristi, Ɗan Mai Albarka?” Yesu ya ce, “Ni ne. Za ku kuwa ga Ɗan Mutum yana zaune a hannun dama na Mai Iko, yana kuma zuwa a cikin gizagizan sama.” Babban firist ya yage tufafinsa, ya yi ce, “Ina dalilin neman waɗansu shaidu kuma? Kun dai ji saɓon. Me kuka gani?” Duka suka yanke masa hukuncin kisa. Sai waɗansu suka fara tattofa masa miyau, suka rufe masa idanu, suka bubbuge shi da hannuwansu, suka ce, “Yi annabci!” Masu gadin kuma suka ɗauke shi, suka yi masa duka. Yayinda Bitrus yake ƙasa a filin gidan, sai wata yarinya, baiwa, ɗaya daga cikin ma’aikatan babban firist, ta zo can. Da ta ga Bitrus yana jin ɗumi, sai ta dube shi da kyau. Ta ce, “Kai ma kana tare da Yesu, Banazare.” Amma ya yi mūsu ya ce, “Ban san abin da kike magana ba, balle ma in fahimce ki.” Sai ya fita zuwa zaure. Da baiwar ta gan shi a can, sai ta sāke gaya wa waɗanda suke tsattsaye a wurin, ta ce, “Wannan mutum yana ɗaya daga cikinsu.” Sai ya sāke yin musu. Bayan ɗan lokaci kaɗan, sai waɗanda suke tsattsaye kusa suka ce wa Bitrus, “Lalle, kana ɗaya daga cikinsu, gama kai mutumin Galili ne.” Sai ya fara la’antar kansa, yana rantsuwa musu, yana cewa, “Ban san wannan mutumin da kuke magana a kai ba.” Nan da nan zakara ya yi cara sau na biyu. Sai Bitrus ya tuna da maganar da Yesu ya yi masa cewa, “Kafin zakara yă yi cara sau biyu, za ka yi mūsun sanina sau uku.” Sai ya fashe da kuka. Da sassafe, sai manyan firistoci da dattawa, da malaman dokoki, da dukan Majalisa, suka yanke shawara. Suka daure Yesu, suka kai shi, suka miƙa shi ga Bilatus. Bilatus ya yi tambaya ya ce, “Kai ne Sarkin Yahudawa?” Yesu ya amsa ya ce, “I, haka yake, kamar yadda ka faɗa.” Manyan firistoci suka zarge shi a kan abubuwa da yawa. Don haka Bilatus ya sāke tambayarsa ya ce, “Ba za ka amsa ba? Dubi abubuwa da yawa da suke zarginka da su.” Amma har yanzu, Yesu bai ba da amsa ba, Bilatus ya yi mamaki. Yanzu fa, al’ada ce a lokacin Bikin, a saki ɗan kurkuku guda wanda mutane suka roƙa. Wani mutumin da ake kira Barabbas, yana a kurkuku, tare da waɗansu ’yan tawaye da suka yi kisankai a lokacin wani hargitsi. Taron suka matso, suka ce roƙi Bilatus yă yi musu abin da ya saba yi. Bilatus ya yi tambaya ya ce, “Kuna so in sakar muku Sarkin Yahudawa?” Don ya san saboda sonkai ne manyan firistoci suka ba da Yesu a gare shi. Amma manyan firistoci suka zuga taron su sa a saki Barabbas, a maimakon Yesu. Bilatus ya tambaye su ya ce, “To, me zan yi da wanda kuke ce da shi, sarkin Yahudawa?” Suka yi ihu, suka ce, “A gicciye shi!” Bilatus ya yi tambaya ya ce, “Don me? Wane laifi ya yi?” Amma suka ƙara yin ihu suna cewa, “A gicciye shi!” Don son yă faranta wa taron rai, sai Bilatus ya sakar musu Barabbas. Ya sa aka yi wa Yesu bulala, sa’an nan ya ba da shi a gicciye. Sojojin suka tafi da Yesu cikin fadar gwamna (wato, Firetoriyum), suka kira dukan kamfanin sojoji wuri ɗaya. Suka sa masa wata riga mai ruwan shunayya, suka kuma tuƙa rawanin ƙaya suka sa masa. Sai suka fara ce masa, “Ranka yă daɗe sarkin Yahudawa!” Suka dinga bugunsa a kā da sanda, suka tattofa masa miyau. Suka durƙusa suka yi masa bangirma na ba’a. Bayan da suka gama yin masa ba’a, suka tuɓe rigar mai ruwan shunayyar, suka sa masa nasa tufafi. Sai suka tafi da shi don a gicciye shi. Sai ga wani mutum daga Sairin da ake kira Siman, mahaifin Alekzanda da Rufus, yana wucewa kan hanyarsa daga ƙauye. Sai suka tilasta shi yă ɗauki gicciyen. Suka kawo Yesu a wurin da ake kira Golgota (wanda yake nufin Wurin Ƙoƙon Kai). Sai suka miƙa masa ruwan inabi gauraye da mur, don yă rage zafi, amma bai sha ba. Sai suka gicciye shi. Suka rarraba tufafinsa, suka jefa ƙuri’a a kansu don su ga abin da kowa zai samu. Sa’a ta uku na safe ce kuwa aka gicciye shi. Akwai rubutu na zarginsa, da ya ce, Sarkin Yahudawa. Suka gicciye ’yan fashi biyu tare da shi, ɗaya a damansa, ɗayan kuma a hagunsa. Masu wucewa suka zazzage shi. Suka kaɗa kai suna cewa, “To, kai da za ka rushe haikali ka kuma gina shi a kwana uku, sai ka sauko daga gicciyen, ka ceci kanka!” Haka kuma, manyan firistoci da malaman dokoki suka yi masa ba’a a junansu, suna cewa, “Ya ceci waɗansu, amma ya kāsa ceton kansa! Bari wannan Kiristi, wannan Sarkin Isra’ila, yă sauko yanzu daga gicciye, don mu ga mu kuma gaskata.” Waɗanda aka gicciye tare da shi ma suka zazzage shi. Daga sa’a ta shida har zuwa sa’a ta tara na rana, duhu ya rufe dukan ƙasar. A daidai sa’a ta tara na rana, sai Yesu ya ɗaga murya da ƙarfi ya ce, “Eloi, Eloi, lama sabaktani?” (Wato, “Ya Allahna, ya Allahna, don me ka yashe ni?” ). Da waɗansu cikin waɗanda suke tsattsaye kusa da wurin suka ji haka, suka ce, “Ku saurara, yana kiran Iliya.” Wani mutum ya ruga ya je ya jiƙo soso da ruwan tsami, ya soka a sanda ya miƙa wa Yesu yă sha. Ya ce, “Ku ƙyale shi. Bari mu ga ko Iliya zai zo yă saukar da shi.” Da murya mai ƙarfi, Yesu ya ja numfashinsa na ƙarshe. Labulen haikali kuwa ya yage kashi biyu, daga sama har ƙasa. Da jarumin da yake tsaye a gaban Yesu ya ji muryarsa, ya kuma ga yadda ya mutu, sai ya ce, “Gaskiya, wannan mutum Ɗan Allah ne!” Waɗansu mata suna kallo daga nesa. A cikinsu kuwa akwai Maryamu Magdalin, Maryamu mahaifiyar Yaƙub ƙarami da Yusuf, da kuma Salome. A Galili waɗannan mata ne suka riƙa bin sa suna yin masa hidima. Waɗansu mata da yawa da suka zo tare da shi daga Urushalima, su ma suna nan a can. Ranar kuwa ita ce ranar Shirye-shirye (wato, ana kashegari Asabbaci). Saboda haka, da yamma ta yi, sai Yusuf daga Arimateya, wani sanannen ɗan Majalisa, wanda dā ma yake jiran zuwan mulkin Allah, ya je wajen Bilatus ba tsoro, ya roƙa a ba shi jikin Yesu. Bilatus ya yi mamaki da ya ji cewa Yesu ya riga ya mutu. Sai ya kira jarumin ya tambaye shi ko Yesu ya riga ya mutu. Da ya ji ta bakin jarumin cewa haka ne, sai ya ba wa Yusuf jikin. Sai Yusuf ya kawo zanen lilin, ya saukar da jikin, ya nannaɗe shi da lilin ɗin, sa’an nan ya sa shi a kabarin da aka fafe a cikin dutse. Sai ya gungura wani dutse ya rufe bakin kabarin. Maryamu Magdalin da Maryamu uwar Yusuf sun ga inda aka kwantar da shi. Da Asabbaci ya wuce, sai Maryamu Magdalin, Maryamu mahaifiyar Yaƙub, da kuma Salome suka sayi kayan ƙanshi domin su je su shafa wa jikin Yesu. A ranar farko ta mako, da sassafe, bayan fitowar rana, suna kan hanyarsu zuwa kabarin ke nan, sai suka tambaye juna suka ce, “Wane ne zai gungura mana dutsen daga bakin kabarin?” Amma da suka ɗaga kai, sai suka ga cewa, an riga an gungura dutsen. Dutsen kuwa babba ne. Da suna shiga cikin kabarin, sai suka ga wani saurayi sanye da farar riga, yana zaune a hannun dama, sai suka firgita. Ya ce, “Kada ku firgita. Kuna neman Yesu Banazare wanda aka gicciye ne. Ya tashi! Ba ya nan. Ku dubi inda aka kwantar da shi. Amma ku tafi ku gaya wa almajiransa da kuma Bitrus cewa, ‘Ya sha gabanku zuwa Galili. Can za ku gan shi, kamar yadda ya faɗa muku.’ ” Da rawan jiki da kuma ruɗewa, matan suka fita a guje daga kabarin. Ba su kuwa gaya wa kowa ba, don suna tsoro. [Waɗansu rubuce-rubucen hannu na farko-farko da waɗansu shaidu na dā ba su da ayoyi 9-20.] Da Yesu ya tashi daga matattu da safe, a ranar farko ta mako, ya fara bayyana ga Maryamu Magdalin, wadda ya fitar da aljanu bakwai daga cikinta. Ta je ta gaya wa waɗanda dā suke tare da shi, waɗanda kuma suke makoki da kuka. Da suka ji cewa Yesu yana da rai, har ma ta gan shi, ba su gaskata ba. Daga baya Yesu ya bayyana a wani kamanni dabam ga biyunsu, yayinda suke tafiya ƙauye. Waɗannan kuwa suka koma suka shaida wa sauran, amma su ma ba su gaskata ba. Bayan haka, Yesu ya bayyana ga Sha Ɗayan, yayinda suke cin abinci. Ya tsawata musu a kan rashin bangaskiyarsu, da yadda suka ƙi gaskata waɗanda suka gan shi bayan ya tashi. Ya ce, musu, “Ku tafi cikin dukan duniya, ku yi wa’azin bishara ga dukan halitta. Duk wanda ya gaskata, aka kuma yi masa baftisma, zai sami ceto. Amma duk wanda bai gaskata ba kuwa, zai hallaka. Waɗannan alamu za su kasance tare da waɗanda suka gaskata. A cikin sunana za su fitar da aljanu, za su yi magana da sababbin harsuna. Za su ɗauki macizai da hannuwansu. In kuwa suka sha mugun dafi, ba zai cuce su ba ko kaɗan. Za su ɗibiya hannuwansu a kan marasa lafiya, su kuwa warke.” Bayan Ubangiji Yesu ya yi musu magana, sai aka ɗauke shi zuwa sama, ya kuma zauna a hannun dama na Allah. Sai almajiran suka fita, suka yi wa’azi ko’ina. Ubangiji kuwa ya yi aiki tare da su, ya tabbatar da maganarsa ta wurin alamu da suke biye da maganar. Mutane da yawa sun ɗau niyyar rubuta labarin abubuwan da aka cika a cikinmu, kamar yadda muka karɓe su daga waɗanda tun farko shaidu ne da kuma masu hidimar bishara. Saboda haka, da yake ni da kaina na binciko kome a hankali daga farko, na ga ya yi kyau in rubuta maka labarin dalla-dalla, ya mafifici Tiyofilus, don ka san tabbacin abubuwan da aka koyar da kai. A lokacin da Hiridus ne yake sarautar Yahudiya, an yi wani firist mai suna Zakariya, na sashin firistoci gidan Abiya. Matarsa Elizabet ma ’yar zuriyar Haruna ce. Dukansu biyu kuwa masu adalci ne a gaban Allah, suna kuma bin umarnan Ubangiji da farillansa duka da halin rashin zargi. Sai dai ba su da ’ya’ya, domin Elizabet bakararriya ce; kuma dukansu biyu sun tsufa. Wata rana da lokacin aikin firistoci na sashen Zakariya na yin hidima ya kewayo, yana kuma cikin hidimarsa ta firist a gaban Allah, sai aka zaɓe shi ta wurin ƙuri’a, bisa ga al’adar aikin firist, yă shiga haikalin Ubangiji yă ƙone turare. Da lokacin ƙone turare ya yi, duk taron masu sujada suna a waje suna addu’a. Sai mala’ikan Ubangiji ya bayyana gare shi, tsaye a dama da bagaden turare. Da Zakariya ya gan shi sai ya firgita, tsoro kuma ya kama shi. Amma mala’ikan ya ce masa, “Kada ka ji tsoro, Zakariya; an ji addu’arka. Matarka Elizabet za tă haifa maka ɗa, za ka kuma ba shi suna Yohanna. Zai zama abin murna da farin ciki a gare ka, mutane da yawa kuwa za su yi murna don haihuwarsa, gama zai zama mai girma a gaban Ubangiji. Ba kuwa zai taɓa shan ruwan inabi ko wani abu mai sa maye ba. Zai cika da Ruhu Mai Tsarki tun haihuwa. Shi ne zai juye mutanen Isra’ila da yawa zuwa wurin Ubangiji Allahnsu. Zai sha gaban Ubangiji, a ruhu da kuma iko irin na Iliya, domin yă juye zukatan iyaye ga ’ya’yansu, marasa biyayya kuma ga zama masu biyayya don yă kintsa mutane su zama shiryayyu domin Ubangiji.” Sai Zakariya ya tambayi mala’ikan ya ce, “Yaya zan tabbatar da wannan? Ga ni tsoho, matana kuma ta kwana biyu.” Mala’ikan ya ce, “Ni ne Jibra’ilu. Ina tsaya a gaban Allah, an kuma aiko ni in yi maka magana, in kuma faɗa maka wannan labari mai daɗi. Yanzu za ka zama bebe, ba za ka ƙara iya magana ba sai ranar da wannan magana ta cika, saboda ba ka gaskata da kalmomina waɗanda za su zama gaskiya a daidai lokacinsu ba.” Ana cikin haka, mutane suna jiran Zakariya, suna kuma mamaki me ya sa ya daɗe haka a cikin haikali. Da ya fito, bai iya yin musu magana ba. Sai suka gane, ya ga wahayi ne a haikali, domin ya dinga yin musu alamu, amma ya kāsa yin magana. Da lokacin hidimarsa ya cika, sai ya koma gida. Bayan wannan, matarsa Elizabet ta yi ciki, ta kuma riƙa ɓuya har wata biyar. Sai ta ce, “Ubangiji ne ya yi mini wannan. A waɗannan kwanaki ya nuna tagomashinsa ya kuma kawar mini da kunya a cikin mutane.” A wata na shida, sai Allah ya aiki mala’ika Jibra’ilu zuwa Nazaret, wani gari a Galili, gun wata budurwar da aka yi alkawarin aurenta ga wani mutum mai suna Yusuf daga zuriyar Dawuda. Sunan budurwar Maryamu. Mala’ikan ya je wurinta ya ce, “A gaishe ki, ya ke da kika sami tagomashi ƙwarai! Ubangiji yana tare da ke.” Maryamu ta damu ƙwarai da kalmominsa, tana tunani wace irin gaisuwa ce haka? Amma mala’ikan ya ce mata, “Kada ki ji tsoro, Maryamu, kin sami tagomashi a wurin Allah. Ga shi za ki yi ciki ki kuma haifi ɗa, za ki kuma ba shi suna Yesu. Zai zama mai girma, za a kuma kira shi Ɗan Maɗaukaki. Ubangiji Allah zai ba shi gadon sarautar kakansa Dawuda, zai yi mulkin gidan Yaƙub har abada, mulkinsa kuma ba zai taɓa ƙare ba.” Maryamu ta tambayi mala’ikan ta ce, “Yaya wannan zai yiwu, da yake ni budurwa ce?” Mala’ikan ya amsa ya ce, “Ruhu Mai Tsarki zai sauko miki, ikon Maɗaukaki kuma zai rufe ke. Saboda haka, Mai Tsarkin nan da za a haifa, za a kira shi Ɗan Allah. ’Yar’uwarki Elizabet ma za tă haifi ɗa a tsufanta, ita da aka ce bakararriya, ga shi tana a watanta na shida. Gama ba abin da zai gagari Allah.” Maryamu ta amsa ta ce, “To, ni baiwar Allah ce, bari yă zama mini kamar yadda ka faɗa.” Sai mala’ikan ya tafi abinsa. A lokacin sai Maryamu ta shirya ta gaggauta zuwa wani gari a ƙasar tudu ta Yahudiya, inda ta shiga gidan Zakariya ta kuma gai da Elizabet. Da Elizabet ta ji gaisuwar Maryamu, sai jaririn da yake a cikinta ya yi motsi. Elizabet kuma ta cika da Ruhu Mai Tsarki. Sai ta ɗaga murya da ƙarfi ta ce, “Ke mai albarka ce a cikin mata. Mai albarka ne kuma ɗan da za ki haifa! Me ya sa na sami wannan tagomashi har da mahaifiyar Ubangijina za tă zo wurina? Da jin gaisuwarki, sai jaririn da yake cikina ya yi motsi don murna. Mai albarka ce wadda ta gaskata cewa abin da Ubangiji ya faɗa mata zai cika!” Sai Maryamu ta ce, “Raina yana ɗaukaka Ubangiji ruhuna kuma yana farin ciki da Allah Mai Cetona, gama ya lura da ƙasƙancin baiwarsa. Daga yanzu nan gaba dukan zamanai za su ce da ni mai albarka, gama Mai Iko Duka ya yi mini manyan abubuwa, sunansa labudda Mai Tsarki ne. Jinƙansa ya kai ga masu tsoronsa, daga zamani zuwa zamani. Ya aikata manyan ayyuka da hannunsa; ya watsar da waɗanda suke masu girman kai a zurfin tunaninsu. Ya saukar da masu mulki daga gadajen sarautarsu amma ya ɗaukaka ƙasƙantattu. Ya ƙosar da masu yunwa da kyawawan abubuwa amma ya sallami mawadata hannu wofi. Ya taimaki bawansa Isra’ila, yana tunawa yă nuna jinƙai ga Ibrahim da zuriyarsa har abada, kamar yadda ya faɗa wa kakanninmu.” Maryamu ta zauna da Elizabet kusan wata uku sa’an nan ta koma gida. Sa’ad da kwanaki suka yi don Elizabet ta haihu, sai ta haifi ɗa. Maƙwabtanta da ’yan’uwanta suka ji cewa Ubangiji ya nuna mata jinƙai mai yawa, suka kuma taya ta farin ciki. A rana ta takwas, sai suka zo don a yi wa yaron kaciya, dā za su sa masa sunan mahaifinsa Zakariya ne, amma mahaifiyar yaron ta ce, “A’a! Za a ce da shi Yohanna.” Sai suka ce mata, “Ba wani a cikin danginku mai wannan suna.” Sai suka yi alamu wa mahaifinsa, don su san sunan da zai su a kira yaron. Ya yi alama a kawo masa allo, a gaban kowa sai ya rubuta, “Sunansa Yohanna.” Dukan mutane kuwa suka yi mamaki. Nan da nan bakinsa ya buɗe harshensa kuma ya saku, sai ya fara magana yana yabon Allah. Maƙwabta duk suka cika da tsoro, mutane kuwa suka yi ta yin magana game da dukan waɗannan abubuwa a ko’ina a cikin ƙasar tudu ta Yahudiya. Duk waɗanda suka ji wannan kuwa sun yi mamaki suna cewa, “To, me yaron nan zai zama?” Gama hannun Ubangiji yana tare da shi. Mahaifinsa Zakariya ya cika da Ruhu Mai Tsarki sai ya yi annabci ya ce, “Yabo ya tabbata ga Ubangiji, Allah na Isra’ila, domin ya zo ya kuma fanshe mutanensa. Ya tā mana ƙahon ceto a gidan bawansa Dawuda (yadda ya yi magana tun tuni ta wurin annabawansa masu tsarki), cewa zai cece mu daga abokan gābanmu daga kuma hannun dukan waɗanda suke ƙinmu don yă nuna jinƙai ga kakanninmu, yă kuma tuna da alkawarinsa mai tsarki, rantsuwar da ya yi wa mahaifinmu Ibrahim, don yă kuɓutar da mu daga hannun abokan gābanmu, yă kuma sa mu iya yin masa hidima babu tsoro, cikin tsarki da adalci a gabansa dukan kwanakinmu. “Kai kuma, ɗana, za a ce da kai annabin Maɗaukaki; gama za ka sha gaban Ubangiji don ka shirya masa hanya, don ka sanar da mutanensa ceto, ta wurin gafarar zunubansu, saboda jinƙai na Allahnmu mai ƙauna, hasken nan na ceto zai ɓullo mana daga sama, don yă haskaka a kan waɗanda suke zama cikin duhu, da kuma cikin inuwar mutuwa, don yă bi da ƙafafunmu a hanyar salama.” Yaron kuwa ya yi girma ya kuma ƙarfafa a ruhu; ya zauna a hamada sai lokacin da ya fito a fili ga mutanen Isra’ila. A waɗancan kwanaki, Kaisar Augustus ya ba da doka cewa ya kamata a yi ƙidaya a dukan masarautar Roma. (Wannan ce ƙidaya ta fari da aka yi a lokacin da Kwiriniyus yake gwamnar Suriya.) Sai kowa ya koma garinsa don a rubuta shi. Saboda haka Yusuf ma ya haura daga Nazaret a Galili zuwa Yahudiya, ya tafi Betlehem garin Dawuda, don shi daga gida da kuma zuriyar Dawuda ne. Ya tafi can don a rubuta shi tare da Maryamu, wadda aka yi masa alkawari zai aura, tana kuwa da ciki. Yayinda suke can, sai lokacin haihuwar jaririn ya yi, ta kuwa haifi ɗanta na fari. Ta nannaɗe shi a zane ta kuma kwantar da shi cikin wani kwami, don ba su sami ɗaki a masauƙi ba. Akwai makiyaya masu zama a fili kusa da wurin, suna tsaron garkunan tumakinsu da dare. Sai wani mala’ikan Ubangiji ya bayyana gare su, ɗaukakar Ubangiji kuma ta haskaka kewaye da su, suka kuwa tsorata ƙwarai. Amma mala’ikan ya ce musu, “Kada ku ji tsoro. Na kawo muku labari mai daɗi na farin ciki mai yawa ne wanda zai zama domin dukan mutane. Yau a birnin Dawuda an haifa muku Mai Ceto; shi ne Kiristi Ubangiji. Wannan zai zama alama a gare ku. Za ku tarar da jariri a nannaɗe a zane kwance a kwami.” Ba labari sai ga taron rundunar sama suka bayyana tare da mala’ikan, suna yabon Allah suna cewa, “Ɗaukaka ga Allah a can cikin sama, a duniya kuma salama ga mutane waɗanda tagomashinsa yake bisansu.” Da mala’ikun suka bar su, su suka koma sama, sai makiyayan suka ce wa juna, “Mu je Betlehem mu ga wannan abin da ya faru, wanda Ubangiji ya sanar mana.” Sai suka tafi da sauri, suka tarar da Maryamu da Yusuf, da kuma jaririn kwance a kwami. Sa’ad da suka gan shi, sai suka baza maganar da aka gaya musu game da yaron, duk kuwa waɗanda suka ji wannan, suka yi mamaki a kan abin da makiyayan suka faɗa. Amma Maryamu ta riƙe dukan waɗannan abubuwa ta kuma yi ta tunaninsu a zuciyarta. Makiyayan kuwa suka koma, suna ɗaukaka suna kuma yabon Allah saboda dukan abubuwan da suka ji, suka kuma gani, yadda aka gaya musu. A rana ta takwas, da lokaci ya yi da za a yi masa kaciya, sai aka ba shi suna Yesu, sunan da mala’ika ya ba shi kafin a yi cikinsa. Da lokacin tsarkakewarsu bisa ga Dokar Musa ya cika, sai Yusuf da Maryamu suka ɗauke shi suka haura zuwa Urushalima don su miƙa shi ga Ubangiji (yadda yake a rubuce a Dokar Ubangiji cewa, “Kowane ɗan fari, za a keɓe shi ga Ubangiji” ), don kuma su miƙa hadaya bisa ga abin da aka faɗa a Dokar Ubangiji cewa, “kurciyoyi biyu ko ’yan tattabarai biyu.” To, akwai wani mutum a Urushalima mai suna Siman, shi mai adalci da kuma mai ibada. Yana jiran fansar Isra’ila, Ruhu Mai Tsarki kuwa yana tare da shi. An bayyana masa ta wurin Ruhu Mai Tsarki cewa ba zai mutu ba sai ya ga Kiristi na Ubangiji. Da Ruhu ya iza shi, sai ya shiga cikin filin haikali. Sa’ad da iyayen suka kawo jaririn nan Yesu don su yi masa abin da al’adar Doka ta bukaci, sai Siman ya karɓi yaron a hannuwansa ya yabi Allah, yana cewa, “Ya Ubangiji Mai Iko Duka, kamar yadda ka yi alkawari, yanzu ka sallami bawanka lafiya. Gama idanuna sun ga cetonka, wanda ka shirya a gaban dukan mutane, haske don bayyanawa ga Al’ummai da kuma ɗaukaka ga mutanenka Isra’ila.” Mahaifin yaron da kuma mahaifiyarsa suka yi mamaki abin da aka faɗa game da shi. Sa’an nan Siman ya sa musu albarka ya ce wa Maryamu mahaifiyarsa, “An ƙaddara yaron nan yă zama sanadin fāɗuwa da tashin mutane da yawa a Isra’ila, zai kuma zama alamar da mutane ba za su so ba, ta haka za a fallasa tunanin zukatan mutane da yawa. Ke ma, takobi zai soki zuciyarki.” Akwai wata annabiya ma, mai suna Anna, diyar Fanuwel, na kabilar Asher. Ta tsufa kutuf; ta yi zama da mijinta shekaru bakwai bayan sun yi aure, ta kuwa zama gwauruwa sai da ta kai shekaru tamanin da huɗu. Ba ta taɓa barin haikali ba, tana sujada dare da rana, tana kuma azumi da addu’a. Tana haurawa wurinsu ke nan a wannan lokaci, sai ta yi wa Allah godiya ta kuma yi magana game da yaron nan ga dukan waɗanda suke sauraron fansar Urushalima. Bayan da Yusuf da Maryamu suka gama yin dukan abubuwan da Dokar Ubangiji ta bukaci, sai suka koma Galili suka tafi Nazaret garinsu. Yaron kuwa ya yi girma ya yi ƙarfi; ya cika da hikima, alherin Allah kuwa yana bisansa. Kowace shekara, iyayen Yesu sukan je Urushalima don Bikin Ƙetarewa. Da Yesu ya cika shekaru goma sha biyu, sai suka tafi Bikin bisa ga al’ada. Bayan Bikin, da iyayen suka kama hanya don su koma gida, sai Yesu, yaron nan, ya tsaya a Urushalima, ba da saninsu ba. Su kuwa sun ɗauka yana tare da su, saboda haka, suka yi ta tafiya har na yini guda. Sa’an nan suka fara nemansa cikin ’yan’uwansu da abokansu. Da ba su gan shi ba, sai suka koma Urushalima nemansa. Bayan kwana uku, sai suka same shi a filin haikali zaune a tsakiyar malamai, yana sauraronsu yana kuma yi musu tambayoyi. Dukan waɗanda suka ji shi, suka yi mamakin fahimtarsa, da amsoshinsa. Da iyayensa suka gan shi sai suka yi mamaki. Mahaifiyarsa ta ce masa, “Ɗana, don me ka yi mana haka? Ni da mahaifinka duk mun damu muna nemanka.” Sai ya ce, “Don me kuke nemana? Ba ku san cewa, dole in kasance a gidan Ubana ba?” Amma ba su fahimci abin da yake faɗin musu ba. Sai ya koma Nazaret tare da su, yana yi musu biyayya. Mahaifiyarsa kuma ta riƙe dukan waɗannan abubuwa a zuciyarta. Yesu kuwa ya yi girma, ya kuma ƙaru cikin hikima, ya kuma sami tagomashi a wurin Allah da mutane. A shekara ta goma sha biyar ta mulkin Kaisar Tiberiyus, a lokacin Buntus Bilatus ne gwamnar Yahudiya, Hiridus kuma yana sarautar Galili, ɗan’uwansa Filibus yana sarautar Ituriya da Tarakunitis, Lisaniyas kuma yana sarautar Abiline.  A lokacin ne Annas da Kayifas suke manyan firistoci. Sai maganar Allah ta zo wa Yohanna, ɗan Zakariya a hamada. Ya zaga dukan ƙasar da take kewaye da Urdun, yana wa’azin baftismar tuba don gafarar zunubai. Kamar yadda yake a rubuce a littafin annabi Ishaya. “Muryar mai kira a hamada, ‘Ku shirya wa Ubangiji hanya, ku miƙe hanyoyi dominsa. Za a cike kowane kwari, a farfashe kowane dutse da kowane tudu. Za a miƙe hanyoyin da suka karkace, a gyaggyara hanyoyi masu gargaɗa su zama sumul. Dukan ’yan Adam kuwa za su ga ceton Allah!’ ” Yohanna ya ce wa taron da suke zuwa domin yă yi musu baftisma, “Ku macizai! Wa ya gargaɗe ku, ku guje wa fushin nan mai zuwa? Ku yi ayyukan da suka dace da tuba. Kada ma ku yi tunani za ku iya ce wa kanku, ‘Ai, muna da mahaifinmu Ibrahim.’ Ina gaya muku cewa daga cikin duwatsun nan Allah zai iya tā da ’ya’ya wa Ibrahim. An riga an sa bakin gatari a gindin itatuwa, kuma duk itacen da bai ba da ’ya’ya masu kyau ba, za a sare shi a jefa cikin wuta.” Sai taron suka tambaye shi, suka ce “Me za mu yi ke nan?” Ya amsa ya ce, “Ya kamata, mutumin da yake da riguna biyu, yă raba da wanda ba shi da riga, mai abinci kuma yă yi haka.” Masu karɓar haraji ma suka zo, domin a yi musu baftisma. Suka yi tambaya, suka ce “Malam, me ya kamata mu yi?” Ya ce musu, “Kada ku karɓa fiye da abin da aka ce a karɓa.” Sai waɗansu sojoji suka tambaye shi, “Mu fa? Me ya kamata mu yi?” Sai ya amsa ya ce, “Kada ku ƙwace kuɗin mutane, kada kuma ku yi shaidar ƙarya. Ku yi haƙuri da abin da ake biyanku.” Mutane suka zuba ido, suna kuma tunani a zuciyarsu, ko Yohanna ne Kiristi wanda ake sauraron zuwansa. Yohanna ya amsa musu duka ya ce, “Ina muku baftisma da ruwa. Amma wani wanda ya fi ni iko yana zuwa, ban ma isa in kunce igiyar takalmansa ba. Shi zai yi muku baftisma da Ruhu Mai Tsarki da wuta kuma. Matankaɗinsa yana a hannunsa don yă tankaɗe sussukarsa ya kuma tattara alkama cikin rumbunsa, amma zai ƙone yayin da wutar da ba a iya kashewa.” Da kalmomi masu yawa Yohanna ya yi wa mutane gargaɗi, ya kuma yi musu wa’azin bishara. Amma da Yohanna ya tsawata wa Hiridus mai mulki saboda Hiridiyas, matar ɗan’uwansa, da kuma dukan sauran mugayen abubuwan da ya yi, Hiridus dai ya ƙara ɓata al’amarin. Ya sa a kulle Yohanna a kurkuku. Sa’ad da ake wa dukan mutane baftisma, sai aka yi wa Yesu shi ma. Da yana cikin addu’a, sai sama ya buɗe, Ruhu Mai Tsarki kuma ya sauko masa a wata siffa, kamar kurciya. Sai murya ta fito daga sama, ta ce, “Kai ne Ɗana, wanda nake ƙauna, kai ne kuma kana faranta mini zuciya ƙwarai.” To, Yesu kansa yana da shekaru kusan talatin da haihuwa sa’ad da ya fara aikinsa. An ɗauka shi ɗan Yusuf ne, ɗan Heli, ɗan Mattat, ɗan Lawi, ɗan Melki, ɗan Yannai, ɗan Yusuf, ɗan Mattatiyas, ɗan Amos, ɗan Nahum, ɗan Esli, ɗan Naggai, ɗan Ma’at, ɗan Mattatiyas, ɗan Semeyin, ɗan Yosek, ɗan Yoda, ɗan Yowanan, ɗan Resa, ɗan Zerubbabel, ɗan Sheyaltiyel, ɗan Neri, ɗan Melki, ɗan Addi, ɗan Kosam, ɗan Elmadam, ɗan Er, ɗan Yoshuwa, ɗan Eliyezer, ɗan Yorim, ɗan Mattat, ɗan Lawi, ɗan Simeyon, ɗan Yahuda, ɗan Yusuf, ɗan Yonam, ɗan Eliyakim, ɗan Meleya, ɗan Menna, ɗan Mattata, ɗan Natan, ɗan Dawuda, ɗan Yesse, ɗan Obed, ɗan Bowaz, ɗan Salmon, ɗan Nashon, ɗan Amminadab, ɗan Ram, ɗan Hezron, ɗan Ferez, ɗan Yahuda, ɗan Yaƙub, ɗan Ishaku, ɗan Ibrahim, ɗan Tera, ɗan Nahor, ɗan Serug, ɗan Reyu, ɗan Feleg, ɗan Eber, ɗan Sala, ɗan Kainan, ɗan Arfakshad, ɗan Shem, ɗan Nuhu, ɗan Lamek, ɗan Metusela, ɗan Enok, ɗan Yared, ɗan Mahalalel, ɗan Kainan, ɗan Enosh, ɗan Shitu, ɗan Adamu, ɗan Allah. Yesu kuwa cike da Ruhu Mai Tsarki, ya dawo daga Urdun, Ruhu kuma ya kai shi cikin hamada, inda kwana arba’in, Iblis ya gwada shi. Bai ci kome ba a cikin kwanakin nan, a ƙarshensu kuwa ya ji yunwa. Iblis ya ce masa, “In kai Ɗan Allah ne, ka faɗa wa wannan dutse yă zama burodi.” Yesu ya amsa ya ce, “A rubuce yake, ‘Ba da abinci kaɗai mutum zai rayu ba.’ ” Iblis ya kai shi can kan wani wuri mai tsawo, ya nunnuna masa a ƙyiftawar ido dukan mulkokin duniya. Ya ce masa, “Zan ba ka dukan ikonsu da darajarsu, gama ni aka danƙa wa, kuma zan bai wa duk wanda na ga dama. Saboda haka in ka yi mini sujada, dukan wannan zai zama naka.” Yesu ya amsa ya ce, “A rubuce yake, ‘Ka yi wa Ubangiji Allahnka sujada, kuma shi kaɗai za ka bauta wa.’ ” Sai Iblis, ya kai shi Urushalima ya sa ya tsaya a kan wuri mafi tsayi na haikali ya ce, “In kai Ɗan Allah ne, ka yi tsalle daga nan zuwa ƙasa. Gama a rubuce yake, “ ‘Zai umarci mala’ikunsa game da kai, su kiyaye ka da kyau; za su tallafe ka da hannuwansu, don kada ka buga ƙafarka a kan dutse.’ ” Yesu ya amsa ya ce, “An ce, ‘Kada ka gwada Ubangiji Allahnka.’ ” Da Iblis ya gama dukan wannan gwajin, ya bar shi sai lokacin da wata dama ta samu. Yesu ya koma Galili cikin ikon Ruhu. Labarinsa kuwa ya bazu ko’ina a ƙauyuka. Ya yi ta koyarwa a majami’unsu, kowa kuwa ya yabe shi. Ya tafi Nazaret, inda aka yi renonsa. A ranar Asabbaci kuma, ya shiga majami’a kamar yadda ya saba. Sai ya miƙe don yă yi karatu. Aka kuwa ba shi naɗaɗɗen littafin annabi Ishaya. Da ya buɗe, sai ya sami wurin da aka rubuta, “Ruhun Ubangiji yana kaina, domin ya shafe ni, in yi wa matalauta wa’azin bishara. Ya aiko ni in yi shelar ’yanci ga ’yan kurkuku, in kuma buɗe idanun makafi, in ba da ’yanci ga waɗanda aka danne. In yi shelar shekarar tagomashin Ubangiji.” Sai ya naɗe naɗaɗɗen littafin ya mayar wa mai hidimar, ya kuma zauna. Dukan idanun waɗanda suke a majami’ar, suka koma a kansa. Sai ya fara ce musu, “A yau, Nassin nan, ya cika a kunnenku.” Duk suka yabe shi, suka yi mamakin kalmomin alheri da suke fitowa daga bakinsa. Suka yi tambaya, suna cewa, “Anya, wannan ba ɗan Yusuf ba ne?” Yesu ya ce musu, “Tabbatacce, na san za ku faɗa mini karin maganan nan, ‘Likita, warkar da kanka! Ka kuma yi abin da muka ji ka yi a Kafarnahum, a nan garinka.’ ” Ya ci gaba, da ce musu, “Gaskiya nake gaya muku, babu annabin da ake yarda da shi a garinsa. Ina tabbatar muku a zamanin Iliya, akwai gwauraye da yawa a Isra’ila, sa’ad da aka rufe sararin sama har shekara uku da rabi, aka kuma yi yunwa mai tsanani ko’ina a ƙasar. Duk da haka, ba a aiki Iliya ga ko ɗaya a cikinsu ba. Sai dai zuwa ga wata gwauruwa da take a Zarefat, a yankin Sidon. Akwai kuma mutane da yawa a Isra’ila masu kuturta a zamanin annabi Elisha, amma ba ko ɗayansu da aka tsarkake sai Na’aman mutumin Suriyan nan kaɗai.” Dukan mutanen da suke cikin majami’a suka fusata ƙwarai da jin wannan. Suka tashi, suka fitar da Yesu bayan gari, suka kai shi goshin tudun da aka gina garin, don su ture shi ƙasa, amma sai ya bi ta tsakiyar taron ya yi tafiyarsa. Sai ya tafi Kafarnahum, wani gari a Galili, a ranar Asabbaci kuma, ya fara koya wa mutane. Suka yi ta mamakin koyarwarsa, domin saƙonsa yana da iko. A cikin majami’ar, akwai wani mutum mai aljani, wani mugun ruhu. Mutumin ya ɗaga murya da ƙarfi ya ce, “Wayyo! Ina ruwanka da mu, Yesu Banazare? Ka zo ne don ka hallaka mu? Na san wane ne kai, Mai Tsarki na Allah!” Yesu ya tsawata masa da ƙarfin cewa, “Yi shiru! Ka fita daga cikinsa!” Sai aljanin ya fyaɗa mutumin da ƙasa a gabansu duka, sa’an nan ya fita, ya bar shi ba wani rauni. Dukan mutanen suka yi mamaki, suka ce wa junansu, “Wace irin koyarwa ce haka? Da ƙarfi da iko, yana ba wa mugayen ruhohin umarni suna kuma fita!” Labarinsa kuwa ya bazu ko’ina a cikin ƙasar. Yesu ya fita daga majami’ar, ya tafi gidan Siman. Surukar Siman kuwa tana fama da zazzaɓi mai tsanani, sai suka roƙi Yesu yă taimake ta. Sai ya sunkuya kusa da ita, ya kuma tsawata wa zazzaɓin, sai zazzaɓin ya sāke ta. Nan take ta tashi, ta yi musu hidima. Rana tana fāɗuwa, sai mutane suka yi ta kawo wa Yesu dukan waɗanda suke da cuta iri-iri, sai ya ɗibiya wa kowannensu hannuwansa, ya warkar da su. Bugu da ƙari, aljanu suka fiffita daga cikin mutane da yawa suna ihu suna cewa, “Kai Ɗan Allah ne!” Amma ya kwaɓe su, ya hana su magana, don sun san cewa shi ne Kiristi. Da gari yana wayewa, sai Yesu ya je inda ba kowa. Mutane suka yi ta nemansa, da suka zo inda yake, sai suka yi ƙoƙari su hana shi barinsu. Amma ya ce, “Dole in yi wa’azin bisharar mulkin Allah ga sauran garuruwa, saboda wannan ne aka aiko ni.” Sai ya dinga yin wa’azi a majami’un Yahudiya. Wata rana, Yesu yana tsaye a bakin Tafkin Gennesaret, mutane kuma suna ta matsawa kewaye da shi, domin su ji maganar Allah, sai ya hangi jiragen ruwa biyu a bakin tafkin, waɗanda masu kamun kifi suka bari suna wankin abin kamun kifinsu. Sai ya shiga ɗaya jirgin ruwan da yake na Siman, ya kuma roƙe shi yă tura shi kaɗan daga gaci. Sai ya zauna a jirgin ruwan, ya koyar da mutane daga ciki. Da ya gama magana, sai ya ce wa Siman, “Ka tuƙa jirgin zuwa inda akwai zurfi, ka saukar da abin kamun kifinka ka kama kifi.” Siman ya amsa ya ce, “Ranka yă daɗe, duk dare mun yi ta fama ba mu kama kome ba, amma tun da ka ce haka, zan saki abin kamun kifin.” Da suka yi haka, sai suka kama kifi da yawa, har abin kamun kifinsu suka fara tsintsinkewa. Sai suka kira abokansu a ɗaya jirgin, su zo su taimake su, suka kuwa zo. Suka cika jiragen biyu da kifi cif, har jiragen suka fara nutsewa. Da Siman Bitrus ya ga wannan, sai ya fāɗi a gaban Yesu ya ce, “Rabu da ni, Ubangiji. Ni mai zunubi ne!” Gama mamaki ya kama shi da abokansa duka, saboda yawan kifin da suka kama. Yaƙub da Yohanna, ’ya’yan Zebedi, abokan aikin Siman su ma suka yi mamaki. Sai Yesu ya ce wa Siman, “Kada ka ji tsoro, daga yanzu za ka riƙa kama mutane ne.” Sai suka jawo jiragen ruwansu zuwa gaci, suka bar kome da kome, suka bi shi. Yayinda Yesu yake ɗaya daga cikin garuruwan nan, sai ga wani mutum wanda kuturta ta ci ƙarfinsa. Da ganin Yesu, sai ya fāɗi da fuskarsa a ƙasa, ya roƙe shi ya ce, “Ubangiji, in ka yarda, kana iya ka tsabtacce ni.” Yesu ya miƙa hannunsa ya taɓa mutumin ya ce, “Na yarda, ka zama da tsabta!” Nan da nan, sai kuturtar ta rabu da shi. Sai Yesu ya umarce shi ya ce, “Kada ka gaya wa kowa, amma ka tafi ka nuna kanka ga firist, ka kuma miƙa hadayu da Musa ya umarta, saboda tsarkakewarka ta zama shaida a gare su.” Duk da haka, labarinsa ya ƙara bazuwa sosai, har taron mutane suka dinga zuwa don jinsa, da kuma neman warkarwa daga cututtukansu. Amma Yesu sau da yawa, yakan keɓe kansa zuwa wuraren da ba kowa, yă yi addu’a. Wata rana, da yake cikin koyarwa, waɗansu Farisiyawa da malaman dokoki waɗanda suka zo daga kowane ƙauye a Galili, Yahudiya da Urushalima kuwa suna zaune. Ikon Ubangiji yana nan don yă warkar da masu ciwo. Sai ga waɗansu mutane suka kawo wani shanyayye a kan tabarma. Suka yi ƙoƙari su shigar da shi cikin gidan, domin su kwantar da shi a gaban Yesu. Da suka ga babu hanyar da za su bi saboda taron, sai suka haura rufin, suka saukar da shi a kan tabarmarsa, ta bakin ramin da suka huda a rufin, suka ajiye shi a tsakiyar taron, a gaban Yesu. Da Yesu ya ga bangaskiyarsu, sai ya ce, “Saurayi, an gafarta maka zunubanka.” Farisiyawa da malaman dokoki suka fara yin tunani a zukatansu, “Wane ne wannan mutum da yake saɓo haka? Wa zai iya gafarta zunubai, in ba Allah kaɗai ba?” Yesu ya san abin da suke tunani, sai ya yi tambaya ya ce, “Don me kuke tunanin waɗannan abubuwa a zukatanku? Wanne ya fi sauƙi, a ce, ‘An gafarta maka zunubanka,’ ko kuma a ce, ‘Tashi, ka yi tafiya’? Amma domin ku san cewa Ɗan Mutum yana da iko a duniya ya gafarta zunubai.” Sai ya ce wa shanyayyen, “Na ce maka, tashi, ɗauki tabarmarka ka tafi gida.” Nan da nan, ya tashi tsaye a gabansu, ya ɗauki tabarmar da yake kwance a kai, ya tafi gida, yana yabon Allah. Kowa ya yi mamaki, ya kuma yabi Allah. Suka cika da tsoro, suna cewa, “Mun ga abubuwan banmamaki yau.” Bayan wannan, sai Yesu ya fita, ya ga wani mai karɓar haraji, mai suna Lawi, yana zaune a wurin da ake karɓar haraji. Yesu ya ce masa, “Bi ni.” Sai Lawi ya tashi, ya bar kome da kome, ya bi shi. Sai Lawi ya shirya wa Yesu wani babban liyafa a gidansa. Wani babban taron na masu karɓar haraji, tare da waɗansu suna cin abinci tare da su. Amma Farisiyawa da malaman dokokin da suke a ƙungiyarsu, suka yi wa almajiransa gunaguni, suna cewa, “Don me kuke ci, kuke sha tare da masu karɓar haraji da masu zunubi?” Yesu ya amsa musu ya ce, “Ai, masu lafiya ba sa bukatar likita, sai dai marasa lafiya. Ban zo don in kira masu adalci ba, sai dai masu zunubi zuwa ga tuba.” Suka ce masa, “Almajiran Yohanna sukan yi azumi da addu’a, haka ma almajiran Farisiyawa, amma naka sai ci da sha.” Yesu ya amsa ya ce, “Za ku iya sa abokan ango yin azumi yayinda yake tare da su? Amma lokaci yana zuwa, da za a ɗauke ango daga gare su. A waɗancan kwanakin ne za su yi azumi.” Sai ya faɗa musu wannan misali ya ce, “Ba wanda yakan yage ƙyalle daga sabuwar riga ya yi wa tsohuwar riga faci. In ya yi haka, zai yage sabuwar rigar, kuma facin daga sabuwar ba zai dace da tsohuwar rigar ba. Kuma ba wanda yakan zuba sabon ruwan inabi a cikin tsofaffin salkuna. In ya yi haka, sabon ruwan inabi zai farfashe salkunan, ruwan inabin yă zube, salkunan kuma su lalace. A’a, sai dai a zuba sabon ruwan inabi a sababbin salkuna. Kuma ba wanda yakan so shan sabon ruwan inabi bayan ya sha tsohon, don yakan ce, ‘Ai, tsohon ya fi kyau.’ ” A wata ranar Asabbaci, Yesu yana bi ta gonakin hatsi, sai almajiran suka fara kakkarya kan hatsi suna murjewa a hannuwansu suna ci. Sai waɗansu Farisiyawa suka ce, “Me ya sa kuke yin abin da doka ta hana yi a ranar Asabbaci?” Yesu ya amsa musu ya ce, “Ashe, ba ku taɓa karanta abin da Dawuda ya yi, sa’ad da shi da abokan tafiyarsa suka ji yunwa ba? Ya shiga gidan Allah, ya ɗauki keɓaɓɓen burodi, sa’an nan ya ci abin da firistoci kaɗai sukan ci bisa ga doka. Ya kuma ba wa abokan tafiyarsa?” Sai Yesu ya ce musu, “Ai, Ɗan Mutum ne Ubangijin Asabbaci.” A wata ranar Asabbaci kuma, Yesu ya shiga majami’a yana koyarwa. To, a nan kuwa akwai wani mutumin da hannun damansa ya shanye. Farisiyawa da malaman dokoki suka zuba wa Yesu ido, su ga ko zai warkar a ranar Asabbaci, don su sami dalilin zarginsa. Amma Yesu ya san abin da suke tunani. Sai ya ce wa mutumin mai shanyayyen hannun, “Tashi ka tsaya a gaban kowa.” Sai ya tashi ya tsaya. Yesu ya ce musu, “Ina tambayarku, me ya kamata a yi bisa ga doka, a ranar Asabbaci, a aikata alheri ko a aikata mugunta, a ceci rai, ko a hallaka shi?” Sai ya kalle su duka, sa’an nan ya ce wa mutumin, “Miƙo hannunka.” Sai ya miƙe, hannunsa kuwa ya koma lafiyayye. Amma Farisiyawa da malaman Doka suka fusata, suka fara tattauna da junansu a kan abin da za su yi wa Yesu. Wata rana, a cikin kwanakin nan, Yesu ya je wani dutse domin yă yi addu’a, ya kuma kwana yana addu’a ga Allah. Da gari ya waye, sai ya kira almajiransa zuwa wurinsa, ya zaɓi guda goma sha biyu daga cikinsu, waɗanda ya kira su, Manzanni. Siman (wanda ya kira Bitrus), ɗan’uwansa Andarawus, Yaƙub, Yohanna, Filibus, Bartolomeyu, Mattiyu, Toma, Yaƙub ɗan Alfayus, Siman wanda ake kira Zilot, Yahuda ɗan Yaƙub, da kuma Yahuda Iskariyot, wanda ya bashe Yesu. Sai ya sauko tare da su, ya tsaya a wani fili. A can, akwai taro mai yawa na almajiransa, da kuma mutane masu yawan gaske daga ko’ina a Yahudiya, Urushalima da kuma Taya da Sidon da suke bakin teku, waɗanda suka zo domin su ji shi, a kuma warkar da cututtukansu. Waɗanda suke fama da mugayen ruhohi kuwa aka warkar da su. Kuma dukan mutane suka yi ƙoƙari su taɓa shi, domin iko yana fitowa daga gare shi, ya kuwa warkar da su duka. Da ya dubi almajiransa, sai ya ce, “Masu albarka ne ku da kuke matalauta, gama mulkin Allah naku ne. Masu albarka ne ku da kuke jin yunwa yanzu, gama za ku ƙoshi. Masu albarka ne ku da kuke kuka yanzu, gama za ku yi dariya. Masu albarka ne sa’ad da mutane suka ƙi ku, suka ware ku, suka zage ku, suna ce da ku mugaye, saboda Ɗan Mutum. “Ku yi farin ciki a wannan rana, ku kuma yi tsalle don murna, saboda ladarku yana da yawa a sama. Gama haka kakanninsu suka yi wa annabawa. “Amma kaitonku da kuke da arziki, gama kun riga kun sami ta’aziyyarku. Kaitonku da kuke ƙosassu yanzu, gama za ku zauna da yunwa. Kaitonku da kuke dariya yanzu, gama za ku yi makoki da kuka. Kaitonku sa’ad da dukan mutane suna magana mai kyau a kanku, gama haka kakanninsu suka yi da annabawan ƙarya. “Amma ina faɗa muku, ku da kuke ji na, ku ƙaunaci abokan gābanku, ku yi wa masu ƙinku alheri. Ku albarkaci waɗanda suke la’anta ku, ku kuma yi wa waɗanda suke wulaƙanta ku addu’a. In wani ya mare ka a wannan kumatu, juya masa ɗayan ma, in wani ya ƙwace maka babban riga, kada ma ka hana masa ’yar cikin ma. Duk wanda ya roƙe ka abu, ka ba shi. In kuma wani ya yi maka ƙwace, kada ka nema yă mayar maka. Ka yi wa waɗansu abin da kai kake so su yi maka. “In kana ƙaunar masu ƙaunarka ne kawai, ina ribar wannan? Ko masu zunubi ma suna ƙaunar waɗanda suke ƙaunarsu. In kuma kana yin alheri ga masu yi maka ne kaɗai, ina ribar wannan? Ko masu zunubi ma suna yin haka. In kana ba da bashi ga mutanen da za su iya biyan ka ne kawai, ina ribar wannan? Ko masu zunubi ma, suna ba da bashi ga masu zunubi, da fata za a biya su tsab. Amma, ku ƙaunaci abokan gābanku, ku kuma yi musu alheri, ku ba su bashi, ba da sa zuciya sai an biya ku ba. Ta yin haka ne kawai, za ku sami lada mai yawa, ku kuma zama ’ya’yan Mafi Ɗaukaka, gama shi mai alheri ne ga marasa godiya da mugaye. Ku zama masu jinƙai, kamar yadda Ubanku mai jinƙai ne. “Kada ku ɗora wa wani, ku ma ba za a ɗora muku ba. Kada ku yanke wa wani hukunci, ku ma ba za a yanke muku ba. Ku gafarta, ku ma za a gafarta muku. Ku bayar, ku ma sai a ba ku mudu a cike, a danƙare, har yă yi tozo, yana zuba, za a juye muku a hannun riga. Mudun da kuka auna da shi, da shi za a auna muku.” Ya kuma faɗa musu wannan misali cewa, “Makaho yana iya jagoran makaho ne? Ba sai dukansu biyu su fāɗa a rami ba? Ɗalibi bai fi malaminsa ba, sai dai kowane ɗalibi wanda ya sami cikakkiyar koyarwa, zai zama kamar malaminsa. “Don me kake duban ɗan tsinke da yake idon ɗan’uwanka, amma ba ka kula da gungumen da yake a naka ido ba? Yaya za ka ce wa ɗan’uwanka, ‘Ɗan’uwa, bari in cire maka ɗan tsinke da yake idonka,’ alhali kuwa, kai kanka ka kāsa ganin gungumen da yake a naka ido? Kai munafuki! Ka fara cire gungumen daga idonka, sa’an nan za ka iya gani sosai, ka kuma cire ɗan tsinken da yake a idon ɗan’uwanka.” “Ba itace mai kyau da yake ba da munanan ’ya’ya. Mummunan itace kuma ba ya ba da ’ya’ya masu kyau. Kowane itace da irin ’ya’yansa ne ake saninsa. Mutane ba sa tsinke ’ya’yan ɓaure daga ƙaya, ko kuwa ’ya’yan inabi daga sarƙaƙƙiya. Mutumin nagari yakan nuna abubuwa nagari daga cikin nagarta da yake a ɓoye a zuciyarsa, mugun mutum kuwa yakan nuna mugayen abubuwa daga muguntar da take a ɓoye a zuciyarsa. Gama baki yakan faɗa abin da ya cika zuciya ne.” “Don me kuke ce da ni, ‘Ubangiji, Ubangiji,’ amma ba kwa yin abin da na faɗa? Zan nuna muku kwatancin mutumin da yakan zo wurina, yă ji kalmomina, yă kuma aikata. Yana kama da mutumin da ya gina gida, wanda ya haƙa ƙasa da zurfi, sa’an nan ya kafa tushen ginin a kan dutse. Da ambaliyar ruwa ta taso, ƙarfin ruwa kuwa ya buga gidan, wannan bai jijjiga shi ba, domin an yi masa tushen gini na ainihi. Amma wanda yakan ji kalmomina, ba ya kuma aikata su, yana kama da mutumin da ya gina gida a ƙasa, ba tare da ya kafa tushen gini ba. A sa’ad da ƙarfin ruwa ya buga gidan, sai gidan yă rushe, mummunar rushewa kuwa.” Bayan Yesu ya gama gaya wa mutanen dukan waɗannan abubuwa, sai ya shiga Kafarnahum. A can, akwai wani bawan wani jarumin yana ciwo, yana kuma a bakin mutuwa. Maigidansa kuwa yana sonsa sosai. Jarumin sojan ya ji labarin Yesu, sai ya aiki waɗansu dattawan Yahudawa wajensa, yana roƙonsa yă zo yă warkar da bawansa. Da suka isa wurin Yesu, sai suka roƙe shi sosai, suka ce, “Wannan mutum, ai, ya dace a yi masa haka, gama yana ƙaunar al’ummarmu ta Yahudawa, har ya gina majami’armu.” Sai Yesu ya tafi tare da su. Da ya yi kusa da gidan, sai jarumin nan, ya aiki abokai su ce masa, “Ubangiji, kada ka dami kanka, gama ban isa ka shiga gidana ba. Shi ya sa ban ma ga na isa in zo wurinka ba. Amma ka yi magana kawai, bawana zai warke. Gama ni kaina, mutum ne a ƙarƙashin iko, akwai kuma sojoji a ƙarƙashin ikona. Nakan ce wa wannan, ‘Je ka,’ sai yă tafi, ga wani kuma in ce, ‘Zo nan,’ sai yă zo. Nakan kuma ce wa bawana, ‘Yi abu kaza,’ sai yă yi.” Da Yesu ya ji haka, sai ya yi mamaki sosai. Ya juya ya wa taron da yake bin sa, “Ina faɗa muku, ban taɓa samun irin bangaskiya mai girma haka ko cikin Isra’ila ba.” Sai mutanen da aka aika, suka koma gida, suka tarar bawan ya warke. Ba a daɗe ba, sai Yesu ya tafi wani garin da ake kira Nayin. Almajiransa da taro mai yawa suka tafi tare da shi. Da ya yi kusa da ƙofar garin, sai ga wata gawa ana fitowa da ita. Shi ne ɗa kaɗai ga mahaifiyarsa, ita kuma gwauruwa ce. Taro mai yawa daga garin yana tare da ita. Da Ubangiji ya gan ta, sai ya ji tausayinta ya ce, “Kada ki yi kuka.” Yesu ya je ya taɓa akwatin gawar, sai masu ɗaukarsa suka tsaya cik. Sai ya ce, “Saurayi, na ce maka, tashi!” Sai mamacin ya tashi zaune, ya fara magana. Yesu kuma ya ba da shi ga mahaifiyarsa. Sai tsoro ya kama su duka, suka yabi Allah, suna cewa, “Babban annabi ya bayyana a cikinmu. Allah ya zo domin yă taimaki mutanensa.” Wannan labarin game da Yesu, ya bazu ko’ina a Yahudiya da kewayenta. Almajiran Yohanna suka gaya masa dukan waɗannan abubuwa. Sai ya kira biyu daga cikinsu, ya aike su wurin Ubangiji, su tambaya su ce, “Kai ne wanda zai zo, ko kuma mu saurari wani dabam?” Da mutanen suka iso wurin Yesu, sai suka ce, “Yohanna Mai Baftisma ne ya aike mu wurinka, mu yi tambaya, ‘Ko kai ne wanda zai zo, ko kuma mu saurari wani dabam?’ ” A daidai lokacin nan, Yesu ya warkar da mutane da yawa masu ciwo, masu cututtuka, da kuma masu mugayen ruhohi. Ya kuma ba makafi da yawa ganin gari. Sai ya amsa wa almajiran Yohanna ya ce, “Ku koma ku faɗa wa Yohanna abin da kuka ji, da abin da kuka gani. Makafi suna ganin gari, guragu suna tafiya, ana warkar da waɗanda suke da kuturta, kurame suna ji, ana tā da matattu, ana kuma yi wa matalauta wa’azin bishara. Mai albarka ne mutumin da bai yi shakkar bangaskiyar da yake da ita a kaina ba.” Bayan almajiran Yohanna suka tafi, sai Yesu ya fara yi wa taron magana game da Yohanna ya ce, “Me kuka je kallo a hamada? Ciyawar da iska take kaɗawa ne? In ba haka ba, to, me kuka je kallo? Mutum mai sanye da tufafi masu kyau ne? A’a, masu sa kayan tsada da suke cikin annashuwa, ai, a fada suke. Amma me kuka je kallo? Annabi? I, ina kuma faɗa muku, ya ma fi annabi. Wannan shi ne wanda aka rubuta game da shi cewa, “ ‘Zan aiko da ɗan saƙona yă sha gabanka, wanda zai shirya hanya, a gabanka.’ Ina faɗa muku, a cikin duk waɗanda mata suka haifa, ba wanda ya fi Yohanna girma. Duk da haka wanda ya fi ƙasƙanta a Mulkin Allah ya fi shi.” (Dukan mutane, har da masu karɓar haraji, da suka ji kalmomin Yesu, sai suka yarda cewa hanyar Allah gaskiya ce, domin Yohanna ne ya yi musu baftisma. Amma Farisiyawa da masanan dokoki, suka ƙi nufin Allah game da su, domin Yohanna bai yi musu baftisma ba.) Yesu ya ci gaba da cewa, “To, da me zan kwatanta mutanen zamanin nan? Kamar me suke? Suna kama da yaran da suke zama a bakin kasuwa, suna kiran juna, suna cewa, “ ‘Mun busa muku sarewa, amma ba ku yi rawa ba, Mun kuma yi muku waƙar makoki, ba ku kuma yi kuka ba.’ Gama Yohanna Mai Baftisma ya zo, ba ya cin burodi, ba ya shan ruwan inabi, sai kuka ce, ‘Ai, yana da aljani.’ Ɗan Mutum ya zo yana ci, yana sha, sai kuka ce, ‘Ga mai yawan ci, mashayi, da kuma abokin masu karɓar haraji da masu zunubi.’ Amma akan tabbatar da hikima ta gaskiya bisa ga dukan ’ya’yanta.” To, ana nan, sai ɗaya daga cikin Farisiyawa ya gayyaci Yesu cin abincin yamma a gidansa, ya kuwa tafi gidan Bafarisiyen, ya zauna a tebur. Da wata mace wadda ta yi rayuwar zunubi a wannan gari ta ji Yesu yana cin abinci a gidan Bafarisiyen, sai ta kawo ɗan tulun turaren alabasta, ta kuma tsaya daga bayansa, wajen ƙafafunsa tana kuka, sai hawayenta sun fara zuba a ƙafafunsa. Sai ta goge su da gashin kanta, ta sumbace su, sa’an nan ta shafa musu turare. Da Bafarisiyen da ya gayyace shi, ya ga wannan, sai ya ce a ransa, “Da mutumin nan annabi ne, da ya san ko wace ce take taɓansa, da kuma irin macen da take, cewa mai zunubi ce.” Sai Yesu ya ce masa, “Siman, ina da abin da zan faɗa maka.” Shi kuwa ya ce, “Malam sai ka faɗa.” Yesu ya ce, “An yi waɗansu mutum biyu da suke riƙe bashin mai ba da rance. Ana bin guda dinari ɗari biyar, ɗayan kuma hamsin. Dukan biyun suka gagara biyansa, sai ya yafe musu. To, a ganinka, wa zai fi ƙaunar mutumin nan?” Siman ya amsa ya ce, “A ganina, wanda aka yafe wa mai yawa ne.” Sai Yesu ya ce, “Ka faɗa daidai.” Sai ya juya wajen macen, ya ce wa Siman, “Ka ga macen nan? Na shigo gidanka, ba ka ba ni ruwa don ƙafafuna ba, amma ta wanke ƙafafuna da hawayenta, ta kuma goge su da gashin kanta. Ba ka yi mini sumba ba, amma tun shigowata a nan, macen nan ba tă daina sumbar ƙafafuna ba. Ba ka shafa mai a kaina ba, amma ta zubo turare a ƙafafuna. “Saboda haka ina gaya maka, zunubanta masu yawa, an gafarta mata, gama ƙaunarta mai yawa ce. Amma wanda aka gafarta wa kaɗan kuwa, yakan nuna ƙauna kaɗan.” Sai Yesu ya ce mata, “An gafarta miki zunubanki.” Sauran baƙin suka fara ce wa juna, “Wane ne wannan, wanda har yake gafarta zunubai?” Yesu ya ce wa macen, “Bangaskiyarki ta cece ki, ki sauka lafiya.” Bayan wannan sai Yesu ya zazzaga gari da ƙauye, yana wa’azin bisharar mulkin Allah. Sha Biyun nan kuwa suna tare da shi, da kuma waɗansu mata waɗanda aka warkar da su daga cututtukansu, da kuma mugayen ruhohi. Cikinsu akwai Maryamu (wadda ake kira Magdalin) wadda aljanu bakwai suka fito daga cikinta. Da Yowanna matar Kuza, manajan iyalin Hiridus; da Suzana; da waɗansu mata da yawa. Waɗannan mata suna taimaka musu cikin hidima, daga cikin abin da suke da shi na zaman gari. Yayinda taron mai girma na taruwa, mutane kuma daga garuruwa dabam-dabam suna zuwa wurin Yesu, sai ya ba da wannan misali ya ce, “Wani manomi ya fita domin ya shuka irinsa. Da yana watsa irin, sai waɗansu suka fāɗi a kan hanya, aka tattaka su, tsuntsayen sararin sama kuma suka cinye su. Waɗansu suka fāɗi a kan dutse, da suka tsira sai suka yanƙwane don babu ruwa a wurin. Waɗansu kuma suka fāɗi a cikin ƙaya. Da suka yi girma tare, sai ƙayan suka shaƙe su. Waɗansu kuma har yanzu, suka fāɗi a ƙasa mai kyau, suka yi girma, suka ba da amfani riɓi ɗari-ɗari, fiye da abin da aka shuka.” Da faɗin haka sai ya ce, “Duk mai kunnen ji, yă ji.” Almajiransa suka tambaye shi ma’anar wannan misali. Sai ya ce, “Ku ne aka ba sanin asirin mulkin Allah, amma ga sauran mutane kam, ina magana da misalai, saboda, “ ‘ko da yake suna kallo, ba za su gani ba, ko da yake suna ji, ba za su gane ba.’ “Ga ma’anar misalin, irin, shi ne maganar Allah. Waɗanda suka fāɗi a kan hanya su ne mutanen da suka ji, amma Iblis, yakan zo ya ɗauke maganar daga zuciyarsu, don kada su gaskata, su sami ceto. Na kan dutse kuwa, su ne da jin maganar, sukan karɓa da murna, amma ba su da saiwa. Sukan gaskata na ɗan lokaci, amma lokacin gwaji, sai su ja da baya. Irin da suka fāɗi a cikin ƙaya kuwa, su ne mutanen da suka ji, amma a kwana a tashi, tunanin kayan duniya, da neman arziki, da son jin daɗi, sukan hana su ba da ’ya’ya. Amma irin da suka fāɗi a ƙasa mai kyau kuwa, su ne mutane masu kyakkyawar zuciya, mai kyau, da suka ji, suka riƙe, suka kuma jimre har suka ba da ’ya’ya.” “Ba mai ƙuna fitila sa’an nan ya ɓoye ta a cikin tulu, ko kuma ya sa ta a ƙarƙashin gado ba. A maimakon haka, yakan sa ta a kan wurin ajiye fitila, saboda mutane masu shigowa su ga haske. Ba abin da yake ɓoye da ba za a fallasa ba. Kuma ba abin da yake rufe, da ba za a sani ba, ko a fitar da shi a fili ba. Saboda haka, ku yi tunani da kyau yadda kuke saurara. Duk wanda yake da shi, za a ƙara masa, duk wanda ba shi da shi kuma, abin da yake tsammani yana da shi ma, za a karɓe daga gare shi.” Sai uwar Yesu da ’yan’uwansa suka zo, domin su gan shi, amma ba su iya zuwa kusa da shi ba, saboda taron. Sai wani ya faɗa masa cewa, “Ga uwarka da ’yan’uwanka suna tsaye a waje suna so su gan ka.” Ya amsa ya ce, “Mahaifiyata da ’yan’uwana, su ne waɗanda suke jin maganar Allah, suna kuma aikata ta.” Wata rana Yesu ya ce wa almajiransa, “Mu haye zuwa wancan gefen tafkin.” Sai suka shiga jirgin ruwa suka fara tafiya. Da suna cikin tafiya, sai barci ya kwashe shi. Sai wata babban iska ta taso kan tafkin, har ruwa ya fara shiga cikin jirgin. Suka shiga babban hatsari. Almajiran suka je suka tashe shi daga barci, suka ce, “Ubangiji, Ubangiji, za mu nutse!” Ya tashi ya kwaɓe iskar da kuma haukar ruwan. Sai ruwan da iskar suka natsu. Kome ya yi tsit. Sai ya tambayi almajiransa, “Ina bangaskiyarku?” A cikin tsoro da mamaki, suka ce wa junansu, “Wane ne wannan? Yana ba da umarni ga iska da ruwa ma, kuma suna biyayya da shi?” Suka shiga jirgin ruwa zuwa yankin Gerasenawa da yake a hayin tafkin, daga wajen Galili. Da Yesu ya sauka daga jirgin, sai ga wani mutum mai aljanu daga garin. Mutumin ya daɗe bai sa tufafi ba, kuma ba ya zama a gida. Yana zama a cikin kaburbura. Da ya ga Yesu, sai mutumin ya ɗaga murya da ƙarfi, ya fāɗi a gabansa, yana ihu cewa, “Ina ruwanka da ni, Yesu, Ɗan Allah Mafi Ɗaukaka? Ina roƙonka, kada ka ba ni wahala!” Gama Yesu ya riga ya umarci mugun ruhun ya fita daga mutumin. Sau da yawa mugun ruhun ya sha kamunsa. Ko da yake akan daure shi hannu da ƙafa, da sarƙa, a kuma yi gadinsa, amma yakan tsinke sarƙoƙinsa, aljanun kuma su kore shi zuwa wuraren kaɗaici, inda ba kowa. Yesu ya tambaye shi, “Mene ne sunanka?” Sai ya amsa, “Tuli,” gama aljanu masu ɗumbun yawa ne suna cikinsa. Suka yi ta roƙonsa kada yă umarce su su shiga ramin Abis. A wurin kuwa, akwai babban garken aladu da suke kiwo a gefen tudu. Aljanun suka roƙi Yesu ya bar su, su shiga cikin aladun, ya kuwa yardar musu. Da aljanun suka fita daga cikin mutumin, sai suka shiga cikin aladun. Garken kuma ya gangara daga kan tudun zuwa cikin tafkin, kuma suka nutse. Da masu kiwon aladun suka ga abin da ya faru, sai suka ruga da gudu zuwa garin da kewaye suka kai labari. Mutanen kuma suka fito don su ga abin da ya faru. Da suka iso wurin Yesu, sai suka tarar da mutumin da aljanun suka fita daga cikinsa, yana zaune kusa da Yesu sanye da tufafi, kuma cikin hankalinsa, sai tsoro ya kama su. Waɗanda suka ga abin da faru, suka gaya wa mutanen yadda aka warkar da mai aljanun. Sai dukan mutanen yankin Gerasenawa suka roƙi Yesu ya bar su, don sun tsorata sosai. Sai Yesu ya shiga jirgin ruwa ya tafi. Mutumin da aka fitar da aljanun daga cikinsa, ya roƙi Yesu don yă tafi tare da shi, amma Yesu ya sallame shi ya ce, “Koma gida, ka shaida babban alherin da Allah ya yi maka.” Sai mutumin ya tafi yana faɗin abin da Yesu ya yi masa a duk garin. Da Yesu ya koma, taron suka marabce shi, don dā ma duk suna jiransa. Sai wani mutum mai suna Yayirus, wani mai mulkin majami’a, ya zo ya fāɗi a gaban Yesu, yana roƙonsa ya zo gidansa, domin diyarsa ɗaya tak, wadda ta kai shekara goma sha biyu, tana bakin mutuwa. Da Yesu yake kan hanyarsa, taron mutane masu yawa suka yi ta matsa shi a kowane gefe. A wurin kuwa, akwai wata mace wadda tana da ciwon zubar da jini, har na shekara goma sha biyu, amma babu wanda ya iya warkar da ita. Sai ta zo ta bayansa, ta taɓa bakin rigarsa. Nan da nan, zubar da jininta ya tsaya. Yesu ya yi tambaya, “Wa ya taɓa ni?” Bayan kowa ya yi musu, sai Bitrus ya ce, “Ubangiji, ai, mutane da yawa suna matsinka ta kowane gefe.” Amma Yesu ya ce, “Wani ya taɓa ni, na san cewa iko ya fita daga wurina.” Sai macen, da ta ga ba halin ɓoyewa, sai ta fita, jikinta na rawa, ta fāɗi a gabansa. A gaban dukan mutanen, ta faɗi dalilin da ya sa ta taɓa shi, da yadda ta warke nan take. Sai Yesu ya ce mata, “Diyata, bangaskiyarki ta warkar da ke. Ki sauka lafiya.” Yayinda Yesu na cikin magana har yanzu, sai ga wani daga gidan Yayirus, mai mulkin majami’ar ya ce, “Kada ka ƙara damun malam, diyarka ta rasu.” Da Yesu ya ji wannan, sai ya ce wa Yayirus, “Kada ka ji tsoro, ka gaskata, za a kuma warkar da ita.” Da ya iso gidan Yayirus, sai ya hana kowa yă bi shi cikin ɗakin, sai dai Bitrus, da Yohanna, da Yaƙub, da kuma mahaifin da mahaifiyar. Ana cikin haka, dukan mutanen kuma sai kuka da makoki suke ta yi, domin yarinyar. Sai Yesu ya ce, “Ka daina yin kuka, ba tă mutu ba, tana barci ne.” Sai suka yi masa dariya, da yake sun san cewa, ta mutu. Amma Yesu ya kama ta a hannu ya ce, “Diyata, tashi.” Ruhunta ya dawo, kuma ta tashi, nan take. Yesu ya ce musu, su ba ta wani abu tă ci. Iyayenta suka yi mamaki, amma ya ba su umarni kada su faɗa wa kowa abin da ya faru. Bayan da Yesu ya tara Sha Biyun wuri ɗaya, sai ya ba su iko da izini na fitar da dukan aljanu, da na warkar da cututtuka. Ya kuma aike su, su yi wa’azin mulkin Allah, su kuma warkar da marasa lafiya. Ya ce musu, “Kada ku ɗauki kome don tafiyar, wato, ba sanda, ba jaka, ba burodi, ba kuɗi, ba riga na biyu. Duk gidan da kuka sauka, ku zauna nan sai kun bar garin. In mutane ba su karɓe ku ba, sa’ad da kun bar garinsu, ku karkaɗe ƙurar ƙafafunku don shaida a kansu.” Sai suka tashi suka shiga ƙauye zuwa ƙauye suna wa’azin bishara, suna warkar da marasa lafiya a ko’ina. Yanzu fa, Hiridus mai sarauta ya ji labarin dukan abubuwan da suke faruwa. Sai ya rikice, don waɗansu mutane suna cewa, Yohanna Mai Baftisma ne ya tashi daga matattu, waɗansu kuma suna cewa, annabi Iliya ne ya sāke bayyana. Waɗansu kuma har wa yau, suna cewa, ɗaya daga cikin annabawa na dā ne, ya tashi. Amma Hiridus ya ce, “Yohanna dai na yanke kansa, amma wanne mutum ne nake jin labarin abubuwan nan a kansa?” Sai ya yi ƙoƙari ya ga Yesu. Da manzannin suka dawo, sai suka faɗa wa Yesu abin da suka yi. Sai ya ɗauke su, suka keɓe kansu su kaɗai, zuwa wani gari da ake kira Betsaida. Amma taron mutane suka ji labari, sai suka bi shi. Ya marabce su, kuma ya yi musu magana a kan mulkin Allah, ya kuma warkar da masu bukatar warkarwa. Da rana ta kusa fāɗuwa, sai Sha Biyun suka zo wurinsa, suka ce, “Ka sallami taron domin su shiga ƙauyuka na kewaye, su nemi abin da za su ci, da wurin kwana, don inda muke, ba kowa.” Yesu ya ce, “Ku, ku ba su wani abu su ci.” Sai suka ce masa, “Muna da burodi biyar da kifi biyu kaɗai. Sai dai, in mun je mu sayi abinci domin dukan wannan taron.” Maza kaɗai sun kai kusan dubu biyar. Amma ya ce wa almajiransa, “Ku sa su su zauna a ƙungiya hamsin-hamsin.” Haka almajiran suka yi, kowa kuwa ya zauna. Sai Yesu ya ɗauki burodin biyar da kifin biyun, ya ɗaga kansa sama, ya yi godiya, ya kuma kakkarya su. Ya ba wa almajiransa, domin su rarraba wa mutanen. Duka kuwa suka ci suka ƙoshi. Almajiran suka kwashe ragowar gutsattsarin cike da kwanduna goma sha biyu. Wata rana sa’ad da Yesu yana addu’a a ɓoye, almajiransa kuma suna tare da shi, sai ya tambaye, su ya ce, “Wa, taron mutane ke ce da ni?” Suka amsa, suka ce, “Waɗansu suna cewa, Yohanna Mai Baftisma, waɗansu kuma annabi Iliya, har wa yau waɗansu suna cewa, kai ɗaya daga cikin annabawan da ne, da ya tashi da rai.” “Amma ku fa, wa, kuke ce da ni?” Bitrus ya amsa ya ce, “Kiristi na Allah.” Yesu ya gargaɗe su da ƙarfi, kada su gaya wa kowa wannan magana. Ya sāke cewa, “Dole ne Ɗan mutum ya sha wahaloli da yawa, dattawa, da manyan firistoci, da malaman dokoki kuma su ƙi shi, kuma dole a kashe shi, a rana ta uku kuma a tā da shi da rai.” Sai ya ce wa dukansu, “In wani zai bi ni, dole yă mūsanta kansa, ya ɗauki gicciyensa kowace rana, ya bi ni. Gama duk mai son ceton ransa zai rasa shi, amma duk wanda ya rasa ransa saboda ni zai same shi. Ina amfani, in mutum ya ribato duniya duka, amma ya rasa ransa, ko kuma ya yi hasarar ransa. Duk wanda yake jin kunyana da na kalmomina, Ɗan Mutum ma zai ji kunyarsa sa’ad da zai zo a cikin ɗaukakarsa, da ɗaukakar Uban, da kuma ta tsarkaka mala’ikun. “Gaskiya nake gaya muku, waɗansu da suke tsattsaye a nan ba za su ga mutuwa ba, sai sun ga mulkin Allah.” Bayan kamar kwana takwas da yin wannan magana, sai Yesu ya ɗauki Bitrus, da Yohanna, da kuma Yaƙub, suka hau kan dutse tare don yin addu’a. Yana cikin addu’a, sai kamannin fuskarsa ta sāke, tufafinsa kuma suka zama da haske kamar hasken walƙiya. Sai ga mutum biyu, Musa da Iliya, suka bayyana cikin kyakkyawar daraja, suna magana da Yesu. Suka yi zance a kan tashinsa, wanda shi ya kusan ya kawo ga cikarsa a Urushalima. Barci kuwa ya kama Bitrus da abokan tafiyarsa sosai. Da idanunsu suka warware, sai suka ga ɗaukakarsa da kuma mutum biyun tsaye tare da shi. Da mutanen na barin Yesu, sai Bitrus ya ce masa, “Ubangiji, ya yi kyau da muke nan. Bari mu kafa bukkoki guda uku, wato, ɗaya dominka, ɗaya domin Musa, ɗaya kuma domin Iliya.” (Bai ma san abin da yake faɗi ba.) Yayinda yake cikin magana, sai wani girgije ya bayyana ya rufe su, sai suka ji tsoro, yayinda suke shiga cikin girgijen. Wata murya ta fito daga cikin girgijen, tana cewa, “Wannan Ɗana ne, zaɓaɓɓena, ku saurare shi.” Da muryar ta gama magana, sai suka tarar Yesu shi kaɗai ne. Almajiran kuwa suka riƙe wannan al’amari a zukatansu. A lokacin nan, ba su gaya wa kowa abin da suka gani ba. Kashegari, sa’ad da Yesu tare da almajiran nan uku suka sauka daga kan dutsen, sai taro mai yawa ya haɗu da shi. Sai wani mutum daga cikin taron ya yi kira da ƙarfi ya ce, “Malam, ina roƙonka, ka dubi ɗan nan nawa, gama shi ne kaɗai nake da shi. Wani ruhu yakan kama shi, sai ya yi ihu farar ɗaya. Yakan sa shi farfaɗiya, har bakinsa ya yi kumfa. Da ƙyar yake barinsa, yana kuwa kan hallakar da shi. Na roƙi almajiranka su fitar da shi, amma ba su iya ba.” Yesu ya amsa ya ce, “Ya karkataccen zamani marar bangaskiya, har yaushe ne zan kasance tare da ku, ina kuma haƙuri da ku? Kawo yaronka nan.” Yaron yana kan zuwa ke nan, sai aljanin ya buga shi ƙasa, cikin farfaɗiya. Amma Yesu ya kwaɓe mugun ruhun, ya warkar da yaron, sai ya miƙa shi ga mahaifinsa. Duk suka yi mamakin girman Allah. Yayinda kowa yana cikin mamakin dukan abubuwan da Yesu ya yi, sai ya ce wa almajiransa, “Ku kasa kunne da kyau ga abin da zan faɗa muku. Za a bashe Ɗan Mutum ga hannun mutane.” Amma ba su fahimci abin da yake nufi da wannan magana ba. Ba su gane ba, don an ɓoye musu shi. Su kuwa sun ji tsoro su tambaye shi. Wata gardama ta tashi a tsakanin almajiran, a kan ko wane ne a cikinsu zai zama mafi girma Da yake Yesu ya san tunaninsu, sai ya ɗauki wani ƙaramin yaro, ya sa ya tsaya kusa da shi. Sai ya ce musu, “Duk wanda ya karɓi wannan ƙaramin yaron a cikin sunana, ni ya karɓa, kuma duk wanda ya karɓe ni, ya karɓi wanda ya aiko ni ne. Gama mafi ƙanƙanta duka a cikinku, shi ne kuma mafi girma.” Sai Yohanna ya ce, “Ubangiji, mun ga wani mutum yana fitar da aljanu a cikin sunanka, muka yi ƙoƙarin hana shi, don shi ba ɗaya ba ne daga cikinmu.” Yesu ya ce, “Kada ku hana shi, gama duk wanda ba ya gāba da ku, naku ne.” Da lokaci ya yi kusa da za a ɗauki Yesu zuwa sama, sai ya ɗaura niyyar tafiya Urushalima. Sai ya aiki ’yan saƙo, su yi gaba. Su kuwa, suka shiga cikin wani ƙauyen Samariyawa, don su shirya masa abubuwa. Amma mutanen ƙauyen ba su karɓe shi ba, don yana kan hanyar zuwa Urushalima ne. Da almajiransa, Yaƙub da Yohanna suka ga haka, sai suka yi tambaya suka ce, “Ubangiji, kana so mu kira wuta ta sauka daga sama ta hallaka su?” Amma Yesu ya juya, ya kwaɓe su. Sai shi da almajiransa suka tafi wani ƙauye. Suna kan tafiya a hanya, sai wani mutum ya ce masa, “Zan bi ka, duk inda za ka.” Yesu ya ce, “Yanyawa suna da ramummuka, tsuntsayen sararin sama suna da sheƙuna, amma Ɗan Mutum ba shi da wurin da zai sa kansa.” Ya kuma ce wa wani mutum, “Ka bi ni.” Amma mutumin ya amsa ya ce, “Ubangiji, bari in je in binne mahaifina tukuna.” Yesu ya ce masa, “Ka bar matattu su binne matattunsu, amma kai, ka je ka yi shelar mulkin Allah.” Har wa yau, wani ya ce, “Zan bi ka, Ubangiji, amma ka bar ni in je in yi bankwana da iyalina tukuna.” Yesu ya amsa ya ce, “Babu wani da yakan sa hannunsa a garman shanu, sa’an nan ya waiwaya baya, da ya isa ya shiga hidima a cikin mulkin Allah ba.” Bayan haka, Ubangiji ya naɗa waɗansu mutum saba’in da biyu, ya aike su biyu-biyu, su riga shi yin gaba zuwa kowane gari da kowane wuri da zai shiga. Ya ce musu, “Girbi na da yawa, amma ma’aikata kaɗan ne. Saboda haka, ku roƙi Ubangijin girbi ya aikar da ma’aikata zuwa gonarsa. Ku tafi! Ina aikan ku kamar tumaki cikin kyarketai. Kada ku ɗauki jakar kuɗi, ko jaka, ko takalma. Kada ma ku gai da kowa a kan hanya. “Sa’ad da kuka shiga wani gida, ku fara da cewa, ‘Salama a gare ku mutanen gida.’ In akwai mutum mai salama a gidan, salamarku za tă kasance tare da shi, in kuwa babu, salamarku za tă koma muku. Ku zauna a wannan gidan, kuna ci kuna shan duk abin da suka ba ku, gama ma’aikaci ya cancanci albashinsa. Kada ku yi yawan sāke masauƙi, daga gida zuwa gida. “Sa’ad da kuka shiga garin, kuma aka karɓe ku, ku ci ko mene ne da aka ajiye a gabanku. Ku warkar da marasa lafiya da suke wurin. Ku kuma faɗa musu cewa, ‘Mulkin Allah yana kusa da ku.’ Amma sa’ad da kuka shiga garin, kuma ba a karɓe ku ba, ku bi titi-titi ku ce, ‘Ko ƙurar garinku da kuke manne a ƙafafunmu, mun karkaɗe muku. Duk da haka, ku tabbatar da wannan, “Mulkin Allah yana kusa.” ’ Ina dai faɗa muku, a ranan nan, za a fi jin tausayin Sodom fiye da wannan garin. “ ‘Kaitonki, Korazin! Kaitonki, Betsaida!’ Ai, da a ce a Taya da Sidon ne aka yi ayyukan banmamaki da aka yi a cikinku, da tuni sun tuba, suna zama cikin rigar makoki da toka. A ranar shari’a, za a fi jin tausayin Taya da Sidon fiye da ku. Ke kuma Kafarnahum, kina tsammani za ki sami ɗaukaka ne? A’a, za a hallaka ki. “Wanda ya saurare ku, ni yake saurara. Wanda ya ƙi ku, ni yake ƙi. Amma wanda ya ƙi ni kuwa, ya ƙi wanda ya aiko ni ne.” Mutum saba’in da biyun nan suka dawo da murna, suka ce, “Ubangiji, har mun sha ƙarfin aljanu ma a cikin sunanka.” Sai ya amsa ya ce, “Na ga Shaiɗan ya fāɗi daga sama kamar walƙiya. Na ba ku iko da za ku tattaka macizai, da kunamai, ku kuma shawo kan dukan ikon abokin gāba, kuma ba wani lahani da zai same ku. Duk da haka, kada ku yi farin ciki da cewa, kun sha ƙarfin ruhohi, amma ku yi farin ciki, domin an rubuta sunayenku a sama.” A wannan lokaci, Yesu, cike da murna ta wurin Ruhu Mai Tsarki ya ce, “Na yabe ka, ya Uba, Ubangijin sama da ƙasa, domin ka ɓoye waɗannan abubuwa ga masu hikima, da masu ilimi, ka kuma bayyana su ga ƙananan yara. I, ya Uba, gama wannan shi ne nufinka mai kyau. “Ubana ya danƙa mini dukan kome. Ba wanda ya san Ɗan sai Uban, kuma ba wanda ya san Uban, sai Ɗan, da kuma waɗanda Ɗan ya zaɓa ya bayyana musu shi.” Sai ya juya wajen almajiransa, ya ce musu a ɓoye, “Albarka ga idanun da suka ga abin da kuke gani. Ina faɗa muku, annabawa da sarakuna da yawa sun so su ga abin nan da kuke gani, amma ba su gani ba. Sun so su ji abin da kuke ji, amma ba su ji ba.” Wata rana, sai wani masanin dokoki ya miƙe tsaye don yă gwada Yesu. Ya tambaya ya ce, “Malam, me zan yi don in gāji rai madawwami?” Yesu ya amsa ya ce, “Me aka rubuta a cikin Doka? Yaya kake karanta ta?” Sai ya amsa ya ce, “ ‘Ka ƙaunaci Ubangiji Allahnka da dukan zuciyarka, da dukan ranka, da dukan ƙarfinka, da kuma dukan hankalinka’; kuma, ‘Ka ƙaunaci maƙwabcinka kamar kanka.’ ” Yesu ya ce, “Ka amsa daidai. Ka yi haka, kuma za ka rayu.” Amma domin ya kāre kansa, sai ya tambayi Yesu ya ce, “Shin, wane ne maƙwabcina?” Yesu ya amsa ya ce, “Wani mutum ya tashi daga Urushalima za shi Yeriko, sai ya fāɗi a hannun mafasa, wato, ’yan fashi. Suka ƙwace tufafinsa, suka yi masa dūka, suka bar shi nan bakin rai da mutuwa. Ya zamana wani firist ya bi kan wannan hanya. Da ya ga mutumin, sai ya bi gefe ya wuce abinsa. Haka ma wani daga kabilar Lawi, mai hidima cikin haikali, da ya zo wurin, ya gan shi, sai shi ma ya bi gefe ɗaya, ya wuce abinsa. Amma wani mutumin Samariya da yake kan tafiya, da ya kai inda mutumin yake, ya gan shi, sai ya ji tausayinsa. Ya je wurinsa, ya daddaure masa raunukansa, sa’an nan ya zuba mai, da ruwan inabi. Ya ɗauki mutumin ya sa a kan jakinsa, ya kai shi wani masauƙi, ya yi jinyarsa. Kashegari, sai ya ɗauki dinari biyu, ya ba wa mai masauƙin ya ce, ‘Ka lura da shi, bayan na dawo, zan biya ka duk abin da ka ƙara kashewa a kansa.’ “A ganinka, a cikin waɗannan mutane uku, wane ne maƙwabcin mutumin da ya fāɗi a hannun mafasa?” Masanin dokoki ya amsa ya ce, “Wanda ya nuna masa jinƙai.” Yesu ya ce masa, “Je ka, ka yi haka nan.” Yayinda Yesu da almajiransa suna cikin tafiya, sai ya kai wani ƙauye inda wata mace mai suna Marta ta marabce shi a gidanta. Tana da ’yar’uwa mai suna Maryamu, wadda ta zauna a gaban Ubangiji tana jin maganarsa. Marta kuwa, aikin hidima da ya kamata a yi, ya ɗauke mata hankali, sai ta zo wurin Yesu, ta ce, “Ubangiji, ba ka damu da yadda ’yar’uwata ta bar mini aiki ni kaɗai ba? Gaya mata ta taimake ni!” Amma Ubangiji ya amsa ya ce, “Marta, Marta, hankalinki ya tashi, kuma kina damuwa a kan abubuwa da yawa. Amma abu ɗaya tak ake bukata, Maryamu ta zaɓi abin da ya fi kyau, kuma ba za a raba ta da shi ba.” Wata rana Yesu yana addu’a a wani wuri. Da ya gama, sai ɗaya daga cikin almajiransa ya ce masa, “Ubangiji, ka koya mana yin addu’a, kamar yadda Yohanna ya koya wa almajiransa.” Sai ya ce musu, “Sa’ad da kuke yin addu’a ku ce, “ ‘Ya Uba, sunanka mai tsarki ne mulkinka ya zo. Ka ba mu kowace rana abincin yini. Ka gafarta mana zunubanmu, kamar yadda mu ma ke gafarta wa duk wanda ya yi mana laifi. Kada ka bari a kai mu cikin jarraba.’ ” Sa’an nan ya ce musu, “Da a ce ɗayanku yana da aboki, sa’an nan ya je wurinsa da tsakar dare ya ce, ‘Aboki, ranta mini burodi guda uku, domin wani abokina da yake tafiya ya sauka a wurina. Ga shi, ba ni da abinci da zan ba shi.’ Sai wanda yake cikin ɗaki ya amsa ya ce, ‘Kada ka dame ni. An riga an kulle ƙofa, da ni da yarana kuwa mun kwanta, ba zan iya tashi in ba ka kome ba.’ Ina gaya muku, ko da yake ba zai so ya tashi ya ba shi burodin don shi abokinsa ne ba, duk da haka, zai tashi ya ba shi yawan abin da yake bukata, saboda nacewarsa. “Don haka ina faɗa muku, ku roƙa, za a ba ku, ku nema za ku samu, ku ƙwanƙwasa za a kuwa buɗe muku ƙofa. Gama duk wanda ya roƙa, yana karɓa, mai nema yana samu, wanda ya ƙwanƙwasa kuma, za a buɗe masa ƙofa. “Wane mahaifi ne a cikinku, in ɗansa ya roƙe shi kifi, zai ba shi maciji a maimakon, ko kuma in ya roƙi ƙwai, ya ba shi kunama? In fa haka ne, ko da yake ku mugaye ne, kun san ba ’ya’yanku kyautai masu kyau, balle fa Ubanku na sama, zai yi fiye da haka, ta wurin ba da Ruhu Mai Tsarki, ga masu roƙonsa!” Sa’ad da Yesu yake fitar da wani beben aljani daga wani mutum, da aljanin ya fita, sai mutumin wanda da bebe ne, ya yi magana, taron kuwa suka yi mamaki. Amma waɗansunsu suka ce, “Ai, da ikon Be’elzebub, sarkin aljanu ne, yake fitar da aljanu.” Waɗansu kuma suka gwada shi, ta wurin neman yă nuna musu wata alama daga sama. Yesu kuwa ya san tunaninsu, sai ya ce musu, “Duk mulkin da yake gāba da kansa, zai lalace, kuma gidan da yake gaba da kansa zai rushe. In Shaiɗan yana gāba da kansa, yaya mulkinsa zai tsaya? Ina faɗin haka domin kun ce, da ikon Be’elzebub nake fitar da aljanu. In da ikon Be’elzebub nake fitar da su, to, da ikon wa masu binku suke fitar da su? Saboda haka, za su zama alƙalanku ke nan. Amma in da ikon Allah ne ni nake fitar da aljanu, ashe, mulkin Allah ya zo muku ke nan. “Sa’ad da mutum mai ƙarfi, wanda yake da makamai yana gadin gidan kansa, an tsare lafiyar dukiyarsa ke nan. Amma in wani wanda ya fi shi ƙarfi, ya faɗa masa ya kuma sha ƙarfinsa, yakan ƙwace makaman da mutumin ke dogara da su, ya kuma rarraba ganima. “Wanda ba ya tare da ni, yana gāba da ni, wanda kuma ba ya tarawa da ni, watsarwa yake yi. “Lokacin da mugun ruhu ya fita daga mutum, sai ya bi ta wuraren da ba mutane, yana neman hutu, amma ya kāsa samu, sai ya ce, ‘Zan koma gidan da na bari.’ Sa’ad da ya koma, ya tarar da gidan a share da tsabta, kuma a shirye. Sai ya je ya ɗebo waɗansu ruhohi bakwai da suka fi shi mugunta, sai su shiga su zauna a wurin. Ƙarshen wannan mutum kuwa zai fi farkonsa muni.” Da Yesu yake cikin faɗin waɗannan abubuwa, sai wata mace daga cikin taron ta ɗaga murya ta ce masa, “Mai albarka ce uwar da ta haife ka, wadda ka sha mamanta.” Yesu ya amsa ya ce, “A maimakon, masu albarka ne waɗanda suke jin maganar Allah, suna kuma biyayya da ita.” Da taron mutane suka ƙaru, sai Yesu ya ce, “Wannan mugun zamani ne. Tana neman wani abin banmamaki, amma ba ko ɗaya da za a ba ta, sai dai ta Yunana. Kamar yadda Yunana ya zama alama ga mutanen Ninebe, haka ma Ɗan Mutum zai zama ga zamanin nan. A ranar shari’a, Sarauniyar Kudu za tă tashi tsaye tare da wannan zamani, ta yanke wa wannan zamani hukunci, domin ta zo daga ƙarshen duniya ta saurari hikimar Solomon, ga shi kuwa, shi wanda ya fi Solomon girma, na nan. A ranar shari’a, mutanen Ninebe za su tashi tsaye tare da wannan zamani, su yanke wa wannan zamani hukunci. Gama sun tuba sa’ad da Yunana ya yi musu wa’azi. Ga shi yanzu, shi wanda ya fi Yunana girma, na nan. “Babu wanda yakan ƙuna fitila sa’an nan ya ɓoye ta, ko ya rufe ta da murfi ba. A maimako, yakan ajiye ta a kan wurin ajiye fitila, don masu shiga su ga haske. Idonka shi ne fitilar jikinka. Sa’ad da idanunka suna da lafiya, dukan jikinka ma na cike da haske, amma sa’ad da idanunka suna da lahani, dukan jikinka ma na cike da duhu. Ka lura fa, kada hasken da yake cikinka ya zamana duhu ne. Saboda haka, in dukan jikinka yana cike da haske, ba inda ke da duhu, jikinka kuwa zai kasance da haske gaba ɗaya, kamar yadda hasken fitila yake haskaka ka.” Da Yesu ya gama magana, sai wani Bafarisiye ya gayyace shi cin abinci tare da shi. Sai kuwa ya shiga ya zauna a tebur. Amma Bafarisiyen ya lura cewa, Yesu bai wanke hannu kafin ya ci abinci ba, sai mamaki ya kama shi. Sai Ubangiji ya ce masa, “Ku Farisiyawa, kukan wanke bayan kwano da kwaf, amma a ciki kuna cike da kwaɗayi da mugunta. Ku wawayen mutane! Ashe, wanda ya yi bayan, ba shi ne kuma ya yi cikin ba? Ku ba matalauta abin da yake cikin kwano, kuma kome zai zama muku da tsabta. “Kaitonku, Farisiyawa, domin kuna ba wa Allah zakka na na’ana’arku, da ƙarƙashinku, da kuma sauran ganyen lambunku iri-iri, amma kun ƙyale adalci da ƙaunar Allah. Ya kamata da kun kiyaye na ƙarshen, ban ba barin na farkon. “Kaitonku, Farisiyawa, domin kun cika son wuraren zama masu daraja a majami’u, da kuma yawan gaisuwa a wuraren kasuwanci. “Kaitonku, domin ku kamar kaburbura ne da ba a sa musu alama ba, waɗanda mutane suke takawa don rashin sani.” Sai ɗaya daga cikin masanan dokoki ya ce wa Yesu, “Malam, in ka faɗi waɗannan abubuwa haka, kai kuma ka zage mu ke nan.” Yesu ya amsa ya ce, “Ku masanan dokoki ma, kaitonku, domin kun ɗora wa mutane kaya masu nauyi waɗanda da ƙyar suke ɗaukawa, amma ku da kanku ba za ku sa ko yatsa ɗaya, don ku taimake su ba. “Kaitonku, domin kun gina kaburbura saboda annabawa, nan kuwa kakannin-kakanninku ne suka kashe su. Wannan ya shaida cewa kun amince da abin da kakannin-kakanninku suka yi. Sun karkashe annabawa, ku kuma kun gina kaburburansu. Saboda haka, Allah a cikin hikimarsa ya ce, ‘Zan aika musu da annabawa da manzanni. Za su kashe waɗansu, su kuma tsananta wa waɗansu.’ Saboda haka, alhakin jinin dukan annabawa da aka kashe, tun farkon duniya, yana kan wannan zamani, wato, tun daga jinin Habila, har zuwa jinin Zakariya, wanda aka kashe tsakanin bagade da mazauni. I, ina gaya muku, alhakinsu duka yana kan wannan zamani. “Kaitonku, masanan dokoki, domin kun ɗauke mabuɗin ilimi. Ku kanku ba ku shiga ba, kuma kun hana wa waɗanda suke shiga, su shiga.” Da Yesu ya bar wurin, sai Farisiyawa da malaman dokoki suka fara gaba mai tsanani da shi, kuma suna tsokanansa da tambayoyi. Suna fakonsa, don su kama shi a kan wata magana da zai faɗa. Ana nan sa’ad da taron dubban mutane suka taru har suna tattaka juna, Yesu fara yin magana, da farko da almajiransa ya ce, “Ku yi hankali da yistin Farisiyawa, wato, munafunci. Ba abin da yake rufe da ba za a fallasa ba, ko kuma abin da yake ɓoye da ba za a bayyana ba. Abin da kuka faɗa a cikin duhu, za a ji shi a hasken rana. Kuma abin da kuka faɗa a kunne, a cikin ɗakunan ciki-ciki, za a yi shelarsa daga kan rufin ɗakuna. “Ina dai gaya muku abokaina, kada ku ji tsoron masu kashe jiki, amma bayan haka, ba sauran abin da za su iya yi. Amma zan nuna muku wanda za ku ji tsoronsa. Ku ji tsoron wanda, bayan da ya kashe jikin, yana da iko ya jefa ku cikin jahannama ta wuta. I, ina gaya muku, ku ji tsoronsa. Ba ana sayar da kanari biyar a kan kobo biyu ba? Duk da haka, Allah bai manta da ko ɗayansu ba. Tabbatacce, gashin kanku ɗin nan ma, an ƙidaya su duka. Kada ku ji tsoro. Darajarku ta fi na kanari masu yawa girma. “Ina gaya muku, duk wanda ya shaida ni a gaban mutane, Ɗan Mutum ma zai shaida shi a gaban mala’ikun Allah. Amma wanda ya yi mūsun sanina a gaban mutane, shi ma za a yi mūsunsa a gaban mala’ikun Allah. Kuma duk wanda ya faɗi kalmar zagi a kan Ɗan Mutum, za a gafarta masa, amma duk wanda ya saɓa wa Ruhu Mai Tsarki, ba za a gafarta masa ba. “Sa’ad da an kai ku a gaban majami’u, da gaban masu mulki, da kuma gaban masu iko, kada ku damu da yadda za ku kāre kanku, ko kuma abin da za ku faɗa, gama Ruhu Mai Tsarki zai koya muku abin da ya dace ku faɗa a lokacin.” Sai wani mutum daga cikin taron ya ce masa, “Malam, ka ce wa ɗan’uwana ya raba gādon da ni.” Yesu ya amsa masa ya ce, “Kai, wa ya naɗa ni alƙali, ko mai sulhu a tsakaninku?” Sai ya ce musu, “Ku lura fa! Ku tsare kanku daga dukan kowane irin kwaɗayi. Ran mutum ba ya danganta a kan yawan dukiyarsa ba.” Sai ya gaya musu wannan misali ya ce, “Gonar wani mai arziki ta ba da amfani sosai. Ya yi tunani a ransa ya ce, ‘Ba ni da inda zan ajiye amfanin gonana. Me zan yi ke nan?’ “Sai ya ce, ‘Ga abin da zan yi. Zan rushe rumbunana, in gina manya, in zuba dukan hatsina da kayana a ciki. Ni kuma zan ce wa raina, “Kana da kaya da yawa masu kyau, da aka yi ajiyarsu domin shekaru da dama masu zuwa. Yi hutunka, ka ci, ka sha, ka yi annashuwa.” ’ “Amma Allah ya ce masa, ‘Kai wawa! A wannan dare za a nemi ranka. Bayan haka, wa zai gāji abin da ka tara wa kanka?’ “Haka zai zama ga duk wanda ya tara wa kansa dukiya, amma ba shi da arziki a gaban Allah.” Sai Yesu ya ce wa almajiransa, “Saboda haka, ina faɗa muku, kada ku damu game da rayuwarku, abin da za ku ci, ko kuma game da jikinku, abin da za ku yafa. Rai ya fi abinci, jiki kuma ya fi tufafi. Ku dubi hankaki. Ba sa shuki ko girbi, kuma ba su da ɗakin ajiya ko rumbu ba, duk da haka, duk da haka, Allah na ciyar da su. Darajarku ta fi na tsuntsaye sau da yawa! Wane ne a cikinku ta wurin damuwarsa, zai iya ƙara ko sa’a ɗaya ga rayuwarsa? Tun da ba za ku iya yin wannan ƙanƙanin abu ba, me ya sa kuke damuwa a kan sauran? “Ku dubi yadda furanni suke girma. Ba sukan yi aiki, ko saƙa ba, duk da haka, ina faɗa muku cewa, ko Solomon cikin kyakkyawan darajarsa duka, bai yafa kayan ado da ya kai kamar na ko ɗaya a cikinsu ba. In haka ne Allah yake yi wa ciyayin jeji sutura, wadda yau suna nan, sa’an nan gobe kuma a jefa cikin wuta, Allah ba zai yi muku sutura fiye da ciyayin jeji ba, ya ku masu ƙarancin bangaskiya! Kada ku sa zuciyarku a kan abin da za ku ci, ko abin da za ku sha, kada ku damu a kan su. Gama duniya da ba tă san Allah ba, tana faman neman dukan waɗannan abubuwa, Ubanku na sama kuwa, ya san kuna bukatarsu. Amma ku nemi mulkinsa, za a kuwa ƙara muku waɗannan abubuwa. “Ya ƙaramin garke, kada ku ji tsoro, gama ya gamshi Ubanku ya ba ku mulkin. Ku sayar da dukiyarku, ku ba wa matalauta. Ku yi wa kanku jakar kuɗin da ba za su lalace ba. Ku yi wa kanku ajiyar dukiyar da ba za tă kare ba a sama, inda ɓarawo ba zai yi kusa ba, asu kuma ba za su iya su lalatar ba. Gama inda dukiyarku take, nan ne zuciyarku ma take. “Ku shirya ɗamara don hidima. Ku bar fitilunku suna ci, kamar maza da suke jiran maigidansu ya dawo daga bikin aure. Saboda duk lokacin da ya dawo ya ƙwanƙwasa ƙofa, a shirye suke su buɗe masa nan da nan. Zai zama da albarka in maigida ya dawo, ya tarar da bayinsa suna zaman tsaro. Gaskiya ni faɗa muku, zai sa kayan hidima da kansa, ya sa bayinsa su zauna kan tebur, sa’an nan ya yi musu hidimar abinci. Zai zama da albarka ga bayin da maigidansu ya iske su, suna zaman tsaro, a duk lokacin da ya dawo, ko da ya dawo a sa’a ta biyu, ko ta uku na tsakar dare ne. Amma ku fahimci wannan. Da maigida ya san sa’ar da ɓarawo zai zo, ai, da ba zai bari a shiga, a fasa masa gida ba. Ku ma, sai ku zauna da shiri, domin Ɗan Mutum zai zo a sa’ar da ba ku yi tsammani ba.” Bitrus ya yi tambaya ya ce, “Ya Ubangiji, mu ne kake faɗa wa wannan misali, ko kuwa ga kowa da kowa ne?” Ubangiji ya amsa ya ce, “To, wane ne manaja mai aminci da hikima, wanda maigida ya ba shi riƙon bayinsa, domin ya ba su abincinsu a daidai lokaci? Zai zama da albarka ga bawan nan wanda maigidan ya dawo, ya same shi yana yin haka. Gaskiya nake gaya muku, maigidan zai ba shi riƙon dukan dukiyarsa. Amma da a ce bawan ya yi tunani a zuciyarsa ya ce, ‘Ai, maigidana ya yi jinkirin dawowa,’ sa’an nan ya fara dūkan bayin, maza da mata, ya kuma shiga ci, da sha, har da buguwa. Maigidan bawan nan zai dawo a ranar da wannan bawan bai yi tsammaninsa ba, kuma a sa’ar da bai sani ba. Maigidan zai yayyanka shi, ya kuma ba shi rabonsa tare da marasa bangaskiya. “Bawan da ya san nufin maigidansa, kuma bai yi shiri ba, ko kuma bai yi abin da maigidansa yake so ba, zai sha mummunan duka. Amma wanda bai sani ba, ya kuwa yi abin da ya isa horo, za a dūke shi kaɗan. Duk wanda aka ba shi mai yawa, mai yawan ne za a bida daga gare shi. Duk wanda kuma aka ba shi riƙon amana mai yawa, fiye da haka kuma za a bida daga gare shi. “Na zo ne domin in kawo wuta a duniya. Ina so da ta riga ta ƙunu! Amma ina da baftismar da za a yi mini, na kuwa damu sosai, sai na kammala ta! Kuna tsammani na zo domin in kawo salama a duniya ne? A’a! Ina gaya muku, rabuwa ne. Daga yanzu, za a iske mutum biyar a gida ɗaya sun rabu, suna gāba da juna, uku suna gāba da biyu, biyun suna gāba da ukun. Za su rarrabu. Mahaifi yana gāba da ɗan, ɗan kuma yana gāba da mahaifin. Mahaifiya tana gāba da diyar, diyar kuma tana gāba da mahaifiyar. Suruka tana gāba da matar ɗa, matar ɗa kuma tana gāba da suruka.” Ya ce wa taron, “Sa’ad da kuka ga hadari ya fito daga yamma, nan da nan kukan ce, ‘Za a yi ruwan sama,’ sai a kuwa yi. Sa’ad da kuma iska ta taso daga kudu, kukan ce, ‘Za a yi zafi,’ sai kuwa a yi. Munafukai! Kuna san yadda za ku fassara yanayin ƙasa da na sararin sama. Ta yaya ba ku san yadda za ku yi fassarar wannan zamani ba? “Don me ba ku iya auna wa kanku, abin da yake daidai ba? Yayinda kake kan hanyar zuwa kotu da maƙiyinka, ka yi matuƙar ƙoƙari ku shirya tun kuna kan hanya. In ba haka ba, zai kai ka gaban alƙali, alƙali kuma ya miƙa ka ga ɗan sanda, ɗan sanda kuma ya jefa ka a kurkuku. Ina gaya maka, ba za ka fita ba, sai ka biya kobo na ƙarshe.” A yanzun fa, akwai waɗansu da suka kasance a lokacin can, suka ba Yesu labarin Galiliyawa da Bilatus ya gauraye jininsu tare da jinin hadayunsu. Yesu ya amsa ya ce, “Kuna tsammani waɗannan Galiliyawan sun fi dukan sauran Galiliyawa zunubi ne, shi ya sa suka sha irin wannan wahala? Ina gaya muku, a’a! Amma in ba ku tuba ba, ku ma duka za ku hallaka. Ko kuwa kuna tsammani, sha takwas ɗin nan da suka mutu lokacin da hasumiya a Silowam ya fāɗi a kansu, sun fi dukan sauran mutanen Urushalima laifi ne? Ina gaya muku, a’a! Amma in ba ku tuba ba, ku ma duka za ku hallaka.” Sai ya ba su wannan misali ya ce, “Wani mutum yana da itacen ɓaure, da aka shuka a gonar inabinsa. Da ya je cire ’ya’yan itacen, sai ya tarar ba tă yi ’ya’ya ba. Sai ya ce wa mai lura da gonar inabin, ‘Yau shekara uku ke nan ina zuwa neman ’ya’yan ɓaure daga itacen nan, amma ba na samun kome. Sare shi! Don me za a bar shi ya tare wuri.’ “Mutumin ya amsa ya ce, ‘Ranka yă daɗe, ka bar shi, in yi masa banƙasa, in kuma zuba masa taki har na shekara ɗaya. In kuwa ya ba da ’ya’ya shekara mai zuwa, yana da kyau! In kuwa ba haka ba, sai ka sare shi.’ ” Wata ranar Asabbaci, Yesu yana koyarwa a wata majami’a, a wurin kuwa, akwai wata mace wadda aljani ya gurgunta, har na shekaru goma sha takwas. Duk ta tanƙware, ba ta ma iya miƙewa ko kaɗan. Da Yesu ya gan ta, sai ya kirata gaba, ya ce mata, “Mace, an ’yantar da ke daga rashin lafiyarki.” Sai ya ɗibiya hannuwansa a kanta, nan da nan sai ta miƙe, ta yabi Allah. Amma mai mulkin majami’ar ya ji haushi da Yesu ya yi warkarwa a ranar Asabbaci. Sai ya ce wa mutanen, “Akwai ranaku shida da ya kamata a yi aiki. Saboda haka, ku zo a ranakun nan a warkar da ku, ba ranar Asabbaci ba.” Ubangiji ya amsa masa ya ce, “Ku munafukai! Ashe, kowannenku ba yakan kunce bijiminsa ko jakinsa, yă kai shi waje yă ba shi ruwa, a ranar Asabbaci ba? Ashe, bai kamata a ’yantar da macen nan, diyar zuriyar Ibrahim, wadda Shaiɗan ya daure, har shekara goma sha takwas, a ranar Asabbaci, daga abin da ya daure ta ba?” Sa’ad da ya faɗi wannan, sai duka masu gāba da shi suka kunyata. Amma mutane kuwa suka yi murna saboda dukan abubuwan banmamaki da yake yi. Sai Yesu ya yi tambaya ya ce, “Yaya mulkin Allah yake? Da me zan kwatanta shi? Yana kama da ƙwayar mustad, wadda wani mutum ya ɗauka, kuma ya shuka a gonarsa. Ta yi girma, ta zama itace, kuma tsuntsayen sararin sama suka huta a rassansa.” Ya sāke tambaya, “Da me zan kwatanta mulkin Allah? Yana kama da yisti wadda mace ta ɗauka, ta kwaɓa garin alkama mai yawa da shi, har sai da yistin ya gauraye kullun duka.” Sa’ad da Yesu yana kan hanyarsa zuwa Urushalima, sai ya bi ta cikin garuruwan da ƙauyukan, yana koyarwa. Sai wani ya tambaye shi ya ce, “Ya Ubangiji, shin, wai mutane kima ne kawai za su sami ceto?” Ya ce musu, “Ku yi matuƙar ƙoƙari ku shiga ta matsattsiyar ƙofa, domin ina faɗa muku, mutane da yawa za su yi ƙoƙarin shiga, amma ba za su iya ba. Da zaran maigidan ya tashi ya rufe ƙofar, za ku tsaya a waje kuna ƙwanƙwasawa, kuna roƙo cewa, ‘Ranka yă daɗe, buɗe mana ƙofa.’ “Amma shi zai amma ya ce, ‘Ni ban san ku, ko inda kuka fito ba.’ “Sa’an nan za ku ce, ‘Haba, mu da muka ci, muka sha tare da kai, har ka yi koyarwa a cikin titi-titi namu.’ “Amma shi zai amma ya ce, ‘Ban san ku, ko inda kuka fito ba. Ku rabu da ni, dukan ku masu aikata mugunta!’ “Za a yi kuka a can, da cizon haƙora, sa’ad da kuka ga Ibrahim, da Ishaku, da Yaƙub, da dukan annabawa a mulkin Allah, amma ku kuwa, za a jefar da ku a waje. Mutane za su zo daga gabas, da yamma, da kudu, da arewa, su ɗauki wuraren zamansu a bikin, a cikin mulkin Allah. Tabbatacce, akwai waɗansu da suke na ƙarshe, da za su zama na farko, na farko kuma, da za su zama na ƙarshe.” A wannan lokaci, waɗansu Farisiyawa suka zo suka ce wa Yesu, “Ka bar nan ka tafi wani wuri dabam. Hiridus yana so ya kashe ka.” Ya amsa ya ce, “Ku je ku gaya wa dilan nan, wato, mai makirci cewa, ‘Da yau da kuma gobe, zan fitar da aljanu, in kuma warkar da mutane, sa’an nan a rana ta uku in cika burin aikina. Duk da haka, dole in ci gaba da aikin a yau, da kuma gobe, sa’an nan in ci gaba da yin haka kashegari kuma, gama tabbatacce, ba annabi da yakan mutu a bayan birnin Urushalima!’ “Urushalima, ayya Urushalima, ke da kika kashe annabawa, kuma kika jefa wa waɗanda aka aika gare ki da duwatsu. Sau da yawa na yi kewan in tattara ’ya’yanki wuri ɗaya, kamar yadda kaza takan tattara ’ya’yanta cikin fikafikanta, amma ba ki yarda ba! Duba, an bar muku gidanku fanko. Ina kuwa faɗa muku, ba za ku sāke ganina ba, sai kun ce, ‘Mai albarka ne shi wanda yake zuwa cikin sunan Ubangiji.’ ” Wata ranar Asabbaci, da Yesu ya shiga gidan wani sanannen Bafarisiye don cin abinci, sai mutane suka zuba masa ido da kyau. A nan a gabansa kuwa akwai wani mutum mai ciwon kumburin ƙafa da hannu. Sai Yesu ya tambayi masanan dokoki da Farisiyawa ya ce, “Daidai ne bisa ga doka, a yi warkarwa a ranar Asabbaci, ko babu?” Amma ba su ce kome ba. Sai ya riƙe mutumin, ya warkar da shi, sa’an nan ya sallame shi. Sai ya tambaye, su ya ce, “In wani a cikinku yana da ɗa, ko bijimi da ya faɗa a rijiya a ranar Asabbaci, ba za ku cire shi nan da nan ba?” Suka rasa abin faɗi. Da ya lura da yadda baƙi suna zaɓan wuraren zama masu bangirma a tebur, sai ya faɗa musu wannan misali, ya ce; “In wani ya gayyace ka bikin aure, kada ka zaɓi wurin zama mai bangirma, don wataƙila akwai wani da ya fi ka girma, da aka gayyata. In kuwa haka ne, wanda ya gayyace duk biyunku, zai zo ya ce maka, ‘Ka ba wa mutumin nan wurin zamanka.’ Ka ga, an ƙasƙantar da kai, kuma dole ka ɗauki wuri mafi ƙasƙanci. Amma in an gayyace ka, ɗauki wuri mafi ƙasƙanci, don in wanda ya gayyace ka ya zo, zai ce maka, ‘Ka hawo nan aboki a wuri mafi girma.’ Wannan zai ɗaukaka ka a gaban dukan ’yan’uwanka baƙi. Gama duk wanda ya ɗaukaka kansa, za a ƙasƙantar da shi. Shi wanda kuma ya ƙasƙantar da kansa, za a ɗaukaka shi.” Sai Yesu ya ce wa wanda ya gayyace shi, “Lokacin da ka shirya biki ko liyafa, kada ka gayyaci abokanka, ko ’yan’uwanka, ko danginka, ko kuma maƙwabtanka masu arziki, gama in ka yi haka, suna iya gayyatarka, su biya maka alherin da ka yi musu. Amma lokacin da ka kira biki, ka gayyaci matalauta, da guragu, da shanyayyu, da makafi. Ta haka, za ka sami albarka. Ko da yake ba za su iya biyan ka ba, za a biya ka a ranar tashin masu adalci daga matattu.” Da jin haka, sai wani da yake tare da shi a tebur ɗin, ya ce wa Yesu, “Mai albarka ne wanda zai ci abinci a bikin nan a mulkin Allah.” Yesu ya amsa ya ce, “Wani mutum yana shirya wani babban biki, ya kuma gayyaci baƙi da yawa. Da lokacin bikin ya yi, sai ya aiki bawansa ya je ya ce wa waɗanda aka gayyata, ‘Ku zo, don an shirya kome.’ “Amma sai dukansu suka fara ba da hujjoji. Na farkon ya ce, ‘Na sayi gona yanzun nan, dole in je in ga yadda take, ina roƙonka ka yi mini haƙuri.’ “Wani ya ce, ‘Na sayi shanun noma guda goma yanzun nan, ina kan hanyata ke nan in gwada su, ina roƙonka, ka yi mini haƙuri.’ “Har yanzu wani ya ce, ‘Na yi aure yanzun nan, don haka ni ba zan iya zuwa ba.’ “Bawansa ya dawo ya gaya wa maigidansa wannan. Sai maigidan ya yi fushi, ya ba da umarni ga bawansa ya ce, ‘Ka fita da sauri, ka bi titi-titi da lungu-lungu na garin, ka kawo matalauta, da guragu, da makafi, da shanyayyu.’ “Bawan ya dawo ya ce, ‘Ranka yă daɗe, an yi abin da ka umarta, amma har yanzu da sauran wuri.’ “Maigidan ya ce wa bawansa, ‘Ka je kan hanyoyin da layi-layi na karkara, ka sa su shigo, don gidana ya cika.’ Ina gaya muku, babu ko ɗaya daga cikin mutanen nan da aka gayyata da zai ɗanɗana bikina.” Taron mutane mai yawa suna tafiya tare da Yesu, sai ya juya ya ce musu, “Duk wanda yakan zo wurina, amma bai ƙi mahaifinsa da mahaifiyarsa, da matarsa da ’ya’yansa, da ’yan’uwansa mata da maza, kai, har ma ransa ba, ba zai iya zama almajirina ba. Kuma duk wanda ba yakan ɗauki gicciyensa ya bi ni ba, ba zai iya zama almajirina ba. “In wani daga cikinku yana so ya gina gidan sama, ai, yakan fara zama ne, ya yi lissafin abin da ginin zai ci tukuna, don yă ga ko yana da isashen kuɗi da zai gama ginin. Gama in ya sa tushen gini, amma bai iya gamawa ba, duk wanda ya gani zai yi masa ba’a, yana cewa, ‘Wannan mutum ya fara gini, amma bai iya gamawa ba.’ “Ko kuma, wane sarki ne, in zai je yaƙi da wani sarki, ai, yakan fara zama ne, ya duba ya ga, ko da mutane dubu goma, shi zai iya ƙarawa da mai zuwa da dubu ashirin? In ba zai iya ba, to, tun suna nesa, zai aika da wakilai, su je neman sharuɗan salama. Haka nan fa, kowane ne a cikinku, da ba ya rabu da abin da yake da shi ba, ba zai iya zama almajirina ba. “Gishiri fa yana da kyau, amma in gishiri ya rabu da daɗin ɗanɗanonsa, ta yaya za a sāke mai da daɗin ɗanɗanonsa? Ba shi da wani amfani, ko ga ƙasa, ko ga juji, sai dai a zubar da shi. “Duk mai kunnen ji, yă ji.” Yanzu fa, masu karɓar haraji da “masu zunubi” duka suna taruwa don jin koyarwar Yesu. Amma Farisiyawa da malaman dokoki suka yi gunaguni, suna cewa, “Wannan mutum yana karɓan ‘masu zunubi,’ kuma yana ci tare da su.” Sai Yesu ya faɗa musu wannan misali ya ce, “In ɗayanku yana da tumaki ɗari, sa’an nan ɗayansu ta ɓace. Ashe, ba zai bar tasa’in da tara a fili ya je neman wadda ta ɓace, har sai ya same ta ba? In ya same ta, zai sa ta a kafaɗa da murna, ya dawo gida. Sa’an nan zai kira abokansa da maƙwabtansa wuri ɗaya ya ce, ‘Ku taya ni murna, na sami tunkiyana da ta ɓata.’ Ina gaya muku, haka za a yi murna sosai a sama, a kan mai zunubi guda ɗaya da ya tuba, fiye da masu adalci tasa’in da tara, waɗanda ba su bukatan tuba. “Ko kuwa in wata mace tana da kuɗi na azurfa guda goma, sa’an nan ɗaya ya ɓata, ashe, ba za tă ƙuna fitila, ta share gidan, ta nema a hankali, har sai ta samu ba? In ta same shi, sai ta kira ƙawayenta da maƙwabtanta wuri ɗaya, ta ce musu, ‘Ku taya ni murna, na sami kuɗina da ya ɓata.’ Haka, ina gaya muku, akwai murna a gaban mala’ikun Allah a kan mai zunubi guda ɗaya, da ya tuba.” Yesu ya ci gaba da cewa, “Akwai wani mutum wanda yake da ’ya’ya biyu maza. Ƙaramin ya ce wa mahaifinsu, ‘Baba, ba ni rabon gādona.’ Sai mahaifin ya raba musu dukiyarsa. “Bayan ’yan kwanaki, sai ƙaramin ɗan ya tattara kayansa duk, ya tashi ya tafi wata ƙasa mai nisa. A can, ya ɓatar da dukiyarsa duka a rayuwar banza. Bayan ya ɓatar da kome, sai ga muguwar yunwa a dukan ƙasar, har ya shiga rashi. Sai ya je ya sami aiki a wurin wani mutumin ƙasar, wanda ya aike shi a gonakinsa, ya yi kiwon aladu. Ya yi marmarin cin dusan da aladun suke ci, amma ba wanda ya ba shi wani abu. “Da hankalinsa ya dawo, sai ya ce, ‘Kai, bayin mahaifina guda nawa ne, da suke da abinci fiye da isashe, ni kuma ina nan, zan mutu don yunwa! Zan tashi in koma wurin mahaifina, in ce masa, “Baba, na yi wa sama, na kuma yi maka zunubi. Ni ban isa a ƙara kira na ɗanka ba. Ka mai da ni kamar ɗaya daga cikin bayinka.” ’ Sai ya tashi ya kama hanya ya koma wurin mahaifinsa. “Amma tun yana nesa, mahaifinsa ya hange shi. Tausayi kuma ya kama shi, sai ya tashi ya ruga da gudu wurinsa, ya rungume shi, ya yi masa sumba. “Sai ɗan ya ce masa, ‘Baba, na yi wa sama, na kuma yi maka zunubi. Ni ban isa a ƙara kira na ɗanka ba.’ “Amma mahaifin ya ce wa bayinsa, ‘Maza! Ku kawo riga mafi kyau ku sa masa. Ku sa zobe a yatsarsa, da takalma kuma a ƙafafunsa. Ku kawo ɗan saniya mai ƙiba ku yanka. Bari mu yi biki mu yi shagali. Gama ɗan nan nawa, da ya mutu, amma yanzu yana da rai kuma. Da ya ɓata, amma yanzu an same shi.’ Sai suka fara shagali. “Yayinda ake haka, babban ɗan yana gona. Da ya zo kusa da gida, sai ya ji ana kiɗi ana rawa. Sai ya kira ɗaya daga cikin bayin, ya tambaye shi abin da yake faruwa. Bawan ya ce, ‘Ai, ɗan’uwanka ne ya dawo, shi ne mahaifinka ya yanka ɗan saniya mai ƙiba, gama ya yi murna ya karɓi ɗansa da ya dawo gida lafiyayye, ba abin da ya same shi.’ “Sai yayan ya yi fushi, ya ƙi shiga gida. Sai mahaifinsa ya fita ya roƙe shi. Amma ya amsa wa mahaifinsa ya ce, ‘Duba! Duk waɗannan shekaru, ina yin maka aiki kamar bawa, ban taɓa maka rashin biyayya ba. Duk da haka, ba ka taɓa ba ni ko ɗan akuya domin in yi shagali da abokaina ba. Amma da wannan ɗan naka, wanda ya ɓatar da dukiyarka a kan karuwai ya dawo, ka yanka masa ɗan saniya mai ƙiba!’ “Sai mahaifin ya ce masa, ‘Ɗana, kullum kana nan tare da ni, kuma duk abin da nake da shi, naka ne. Amma ya zama mana dole, mu yi shagali, mu yi murna, domin ɗan’uwan nan naka, da ya mutu, yanzu kuwa yana da rai, da ya ɓata, amma yanzu an same shi.’ ” Yesu ya ce wa almajiransa, “An yi wani mai arziki wanda aka yi wa manajansa zargin yin banza da dukiyarsa. Sai ya kira manajan, ya tambaye shi, ‘Me nake ji haka a kanka? Ka kawo lissafin aikinka, domin ba za ka iya cin gaba da aikinka ba.’ “Sai manajan ya ce cikin tunaninsa, ‘Maigidana zai kore ni daga aiki, me zan yi? Ba ni da ƙarfin noma, kuma ina jin kunyan yin bara. Na san abin da zan yi, don mutane su karɓe ni a gidajensu, bayan an kore ni daga aiki a nan.’ “Sai ya kira kowane ɗaya da maigidansa yake bin bashi. Ya tambayi na farkon ya ce, ‘Nawa ne maigidana yake bin ka?’ “Ya amsa ya ce, ‘Garwar mai na zaitun guda ɗari tara.’ “Manajan ya ce, ‘Ga takardarka, ka zauna maza ka mai da shi ɗari huɗu.’ “Ya kuma tambayi na biyun, ‘Kai fa, nawa ne ake bin ka?’ “Sai ya amsa ya ce, ‘Buhunan alkama dubu.’ “Ya ce, ‘Ga takardarka, ka mai da shi ɗari takwas.’ “Maigidan kuwa ya yabi manajan nan marar gaskiya saboda wayonsa. Gama ’yan duniyan nan suna da wayon yin hulɗa da junansu fiye da ’yan haske. Ina gaya muku, ku yi amfani da dukiya na wannan duniya, domin ku sami wa kanku abokai. Saboda bayan dukiyar ta ƙare, za a karɓe ku a wuraren zama da sun dawwama. “Duk wanda ana amincewa da shi cikin ƙaramin abu, ana kuma amincewa da shi cikin babba. Kuma duk marar gaskiya cikin ƙaramin abu, zai zama marar gaskiya cikin babba. In fa ku ba amintattu ne cikin tafiyar da dukiya ta wannan duniya ba, wa zai amince muku da dukiya ta gaskiya? In fa ku ba amintattu ne cikin tafiyar da dukiyar wani ba, wa zai ba ku dukiya naku, na kanku? “Babu wani bawa mai iya bauta wa iyayengiji biyu ba. Ko dai ya ƙi ɗaya, ya so ɗayan, ko kuwa ya dāge ga yi wa ɗaya bauta, sa’an nan ya rena ɗayan. Ba za ku iya ku bauta wa Allah tare da bauta wa Mammon (wato, Kuɗi) a lokaci ɗaya ba.” Da Farisiyawa masu son kuɗi suka ji wannan duka, sai suka yi wa Yesu tsaki. Ya ce musu, “Ku ne masu mai da kanku marasa laifi a gaban mutane, amma Allah ya san zuciyarku. Abu mai daraja a gaban mutane, abin ƙyama ne a gaban Allah. “An yi shelar Doka da Annabawa har zuwa lokacin Yohanna. Tun daga lokacin nan, bisharar mulkin Allah ne ake wa’azinta, kowa kuma yana ƙoƙarin kutsa kai ya shiga. Gama ta fi sauƙi sama da ƙasa su shuɗe, da a ce ɗigo guda ɗaya na rubutun, ya fita ya fāɗi daga cikin Doka. “Duk wanda ya saki matarsa ya auri wata mace, zina ne yake yi. Kuma mutumin da ya auri macen da aka sake, zina ne yake yi. “An yi wani mutum mai arziki wanda yakan sa tufafi masu ruwan shunayya, da kuma na lallausan lilin, yana kuma cikin rayuwar jin daɗi kullum. A ƙofar gidansa kuma akan ajiye wani mai bara, mai suna Lazarus, wanda jikinsa duk gyambuna ne. Shi kuwa yakan yi marmarin cin abin da yakan fāɗi daga tebur na mai arzikin nan. Har karnuka ma sukan zo su lashe gyambunansa. “Ana nan, sai mai baran ya mutu, kuma mala’iku suka ɗauke shi zuwa gefen Ibrahim. Mai arzikin ma ya mutu, aka kuma binne shi. A cikin jahannama ta wuta, inda yana shan azaba, ya ɗaga kai ya hangi Ibrahim can nesa, da kuma Lazarus a gefensa. Sai ya yi masa kira ya ce, ‘Baba, Ibrahim, ka ji tausayina, ka aiki Lazarus ya sa ɗan yatsarsa a ruwa, ya ɗiga mini a harshe saboda in ji sanyi, domin ina shan azaba cikin wannan wuta.’ “Amma Ibrahim ya ce, ‘Ka tuna fa ɗana, a lokacin da kake duniya, ka sami abubuwa masu kyau naka, Lazarus kuwa ya sami munanan abubuwa. Amma yanzu ya sami ta’aziyya a nan, kai kuwa kana shan azaba. Ban da wannan duka ma, tsakaninmu da kai, akwai wani babban rami da aka yi, yadda waɗanda suke son ƙetarewa daga nan zuwa wurinku, ba za su iya ba, kuma ba mai iya ƙetarewa daga wurinku zuwa wurinmu.’ “Ya amsa ya ce, ‘To, ina roƙonka, ya uba, ka aiki Lazarus zuwa gidan mahaifina, gama ina da ’yan’uwana biyar maza. Bari yă ba su gargaɗi, don kada su ma su zo wurin nan mai azaba.’ “Ibrahim ya amsa ya ce, ‘Suna da Musa da Annabawa, ai, sai su saurare su.’ “Sai ya ce, ‘A’a, ya uba, Ibrahim, in dai wani ya tashi daga matattu ya je wurinsu, za su tuba.’ “Amma ya ce masa, ‘In ba su saurari Musa da Annabawa ba, kai, ko da wani ya tashi daga matattu ma, ba za su saurare shi ba.’ ” Yesu ya ce wa almajiransa, “Dole ne a sami abubuwan da suke sa mutane su yi zunubi, amma kaiton mutumin nan wanda suke zuwa ta wurinsa. Gwamma a ɗaura dutsen niƙa a wuyansa, a jefa shi cikin teku, da ya sa ɗaya daga cikin ƙananan yaran nan ya yi zunubi. Saboda haka, ku lura da kanku. “In ɗan’uwanka ya yi zunubi, ka kwaɓe shi. In ya tuba, ka gafarta masa. In ya yi maka laifi sau bakwai a rana ɗaya, ya kuma dawo sau bakwai ɗin a wurinka, yana cewa, ‘Na tuba,’ sai ka gafarta masa.” Sai manzannin suka ce wa Ubangiji, “Ka ƙara mana bangaskiya!” Ya amsa musu ya ce, “In kuna da bangaskiya da take ƙanƙani kamar ƙwayar mustad, kuna iya ce wa wannan itacen durumi, ‘Ka tumɓuke daga nan, ka dasu a cikin teku.’ Zai kuwa yi muku biyayya. “In ɗaya a cikinku yana da bawa, wanda yake masa noma, ko kiwon tumaki, da dawowar bawan daga gonar, ai, ba zai ce masa, ‘Ka zo nan, ka zauna, ka ci abinci ba’? Ashe, ba zai ce masa, ‘Ka shirya mini abincin yamma, ka shirya ka yi mini hidima domin in ci in sha, bayan haka kana iya ci, ka kuma sha ba’? Shin, zai gode wa bawan don yă yi aikin da aka ce ya yi ne? Haka ku ma, bayan kun yi duk abin da aka ce muku ku yi, ya kamata ku ce, ‘Mu bayi ne marasa cancanta, mun dai yi aikinmu ne kaɗai.’ ” Yesu yana kan hanyarsa zuwa Urushalima, sai ya bi takan iyakar Samariya da Galili. Da zai shiga wani ƙauye, sai maza goma da suke da kuturta suka sadu da shi. Suka tsaya da nesa, suka yi kira da babbar murya, suka ce, “Yesu, Ubangiji, ka ji tausayinmu!” Da ya gan su sai ya ce, “Ku je ku nuna kanku ga firistoci.” Suna kan hanyar tafiya sai suka tsabtacce. Da ɗayansu ya ga ya warke, sai ya koma, yana yabon Allah da babbar murya. Ya zo ya fāɗi a gaban Yesu, ya gode masa. Shi kuwa mutumin Samariya ne. Yesu ya yi tambaya ya ce, “Ba duka goma ne aka tsabtacce ba? Ina sauran taran? Ba wanda ya dawo don yă yabi Allah, sai dai wannan baƙon?” Sai ya ce masa, “Tashi, ka yi tafiyarka, bangaskiyarka ta warkar da kai.” Wata rana, Farisiyawa suka tambaye shi lokacin da mulkin Allah zai zo, Yesu ya amsa ya ce, “Ai, mulkin Allah ba takan zo ta wurin yin kallon ku ba. Mutane kuma ba za su ce, ‘Ga shi nan,’ ko kuma, ‘Ga shi can’ ba, domin mulkin Allah yana cikinku ne.” Sai ya ce wa almajiransa, “Lokaci yana zuwa da za ku yi marmarin ganin rana ɗaya cikin ranakun Ɗan Mutum, amma ba za ku gani ba. Mutane za su ce muku, ‘Ga shi can!’ Ko kuma, ‘Ga shi nan!’ Kada ku yi hanzarin binsu. Gama Ɗan Mutum, a cikin ranarsa, zai zama kamar walƙiya da take walƙawa, da take kuma haskaka sararin sama, daga wannan kusurwa zuwa wancan kusurwa. Amma da fari, dole yă sha wahaloli masu yawa, kuma mutanen zamanin nan su ƙi shi. “Daidai kamar yadda ya faru a zamanin Nuhu, haka zai zama a zamanin Ɗan Mutum. Mutane suna ci, suna sha, suna aurayya, ana kuma ba da su ga aure, har ranar da Nuhu ya shiga jirgin. Sa’an nan ambaliyar ruwan ya sauka, ya hallaka su duka. “Haka ma aka yi a zamanin Lot. Mutane suna ci, suna sha, suna saya, suna sayarwa, suna shuki, suna kuma gine-gine. Amma a ranar da Lot ya bar Sodom, sai aka yi ruwan wuta da farar wuta daga sama, aka hallaka su duka. “Daidai haka zai zama, a ranar da Ɗan Mutum zai bayyana. A ranan nan, kada wanda yake kan rufin gidansa ya sauka don yă kwashe dukiyarsa da take cikin gidan. Haka ma duk wanda yake gona, kada yă koma don wani abu. Ku tuna fa da matar Lot! Duk wanda yake so ya ceci ransa, zai rasa shi, amma duk wanda ya rasa ransa, zai cece shi. Ina gaya muku, a daren nan, mutane biyu za su kasance a gado ɗaya, za a ɗauki ɗaya, a bar ɗayan. Mata biyu za su kasance suna niƙan hatsi tare, za a ɗauki ɗaya, a bar ɗayan.” Suka tambaya, suka ce, “A ina ne, ya Ubangiji?” Ya ce musu, “Ai, inda gawa take, nan ne ungulai za su taru.” Yesu ya ba wa almajiransa wani misali, don yă koya musu yadda ya kamata su dinga yin addu’a kullum, ban da fasawa. Ya ce, “A wani gari, an yi wani alƙali wanda ba ya tsoron Allah, bai kuma kula da mutane ba. A garin nan kuma, akwai wata gwauruwa, wadda ta dinga zuwa wurin alƙalin nan, da roƙo cewa, ‘Ka yi mini adalci tsakanina da maƙiyina.’ “An daɗe yana ƙi, amma a ƙarshe ya ce cikin tunaninsa, ‘Ko da yake ba na tsoron Allah, ba na kuma kula da mutane ba, amma don gwauruwan nan ta dame ni, zan tabbatar cewa ta sami adalci, domin kada tă gajiyar da ni, da yawan zuwanta.’ ” Sai Ubangiji ya ce, “Ku ji fa abin da alƙalin nan, marar gaskiya, ya ce. Ashe, Allah ba zai biya wa zaɓaɓɓunsa da suke masa kuka, dare da rana adalci ba? Zai ci gaba da ƙin sauraronsu ne? Ina gaya muku, zai tabbatar sun sami adalci, ban da ɓatan lokaci. Amma sa’ad da Ɗan Mutum ya dawo, zai sami bangaskiya a duniya ke nan?” Yesu ya kuma faɗi wannan misali ga waɗansu masu taƙama da adalcinsu, kuma suna rena sauran mutane ya ce, “Waɗansu mutane biyu sun tafi haikali don yin addu’a. Ɗaya Bafarisiye ne, ɗayan kuma mai karɓar haraji. Sai Bafarisiyen ya tashi tsaye, ya yi addu’a game da kansa yana cewa, ‘Allah, na gode maka, saboda ni ba kamar sauran mutane ba ne, wato, mafasa, masu aikata mugunta, masu zina, ko kuma kamar mai karɓar harajin nan. Ina azumi sau biyu a mako, ina ba da zakka daga kowane abin da na samu.’ “Amma mai karɓar harajin ya tsaya daga nesa. Bai ma iya ɗaga kansa sama ba, sai ya buga ƙirjinsa, yana cewa, ‘Allah, ka yi mini jinƙai, ni mai zunubi ne.’ “Ina gaya muku, wannan mutum ne, ba ɗayan ba, ya koma gida baratacce, babu laifi a gaban Allah. Gama duk wanda ya ɗaukaka kansa, za a ƙasƙantar da shi. Wanda kuma ya ƙasƙantar da kansa, za a ɗaukaka shi.” Mutane suna kawo jarirai wurin Yesu don yă taɓa su. Da almajiransa suka ga haka, sai suka kwaɓe su. Amma Yesu ya kira yaran a wurinsa ya ce, “Ku bar yara ƙanana su zo wurina. Kada ku hana su, gama mulkin Allah na irin waɗannan ne. Gaskiya nake gaya muku, duk wanda ba zai karɓi mulkin Allah kamar ƙaramin yaro ba, ba zai taɓa shiga mulkin ba.” Wani mai mulki ya tambayi Yesu ya ce, “Malam managarci, me zan yi don in gāji rai madawwami?” Yesu ya amsa ya ce, “Don me kake kira na managarci? Ai, ba wani nagari, sai Allah kaɗai. Ka san dokokin da suka ce, ‘Kada ka yi zina, kada ka yi kisankai, kada ka yi sata, kada ka ba da shaida ta ƙarya, ka girmama mahaifinka da mahaifiyarka.’ ” Mutumin ya ce, “Ai, tun ina ƙarami, na kiyaye duka waɗannan.” Da Yesu ya ji haka, sai ya ce masa, “Akwai abu ɗaya har yanzu da ya rage maka. Ka sayar da duk abin da kake da shi, ka ba wa matalauta, sa’an nan za ka sami dukiya a sama. Bayan haka, ka zo ka bi ni.” Da jin haka, sai ya ɓata rai, domin shi mai arziki ne sosai. Yesu ya kalle shi ya ce, “Yana da wuya fa, masu arziki su shiga mulkin Allah! Tabbatacce, zai fi sauƙi raƙumi ya shiga ta kafar allura, da mai arziki ya shiga mulkin Allah.” Waɗanda suka ji wannan suka yi tambaya suka ce, “To, wa zai iya samun ceto?” Yesu ya amsa ya ce, “Abin da ba ya yiwuwa ga mutane, mai yiwuwa ne ga Allah.” Sai Bitrus ya ce, masa, “To, ga shi mun bar kome da muke da shi, don mu bi ka!” Yesu ya ce musu, “Gaskiya nake gaya muku, ba wanda ya bar gida, ko mata, ko ’yan’uwa maza, ko iyaye, ko yara, saboda mulkin Allah, da zai kāsa samun riɓi mai yawa, a wannan zamani, ya kuma sami rai madawwami a zamani mai zuwa.” Sai ya kai Sha Biyun gefe ɗaya, ya ce musu, “Za mu Urushalima, kuma dukan abin da annabawa suka rubuta a kan Ɗan Mutum zai cika. Za a ba da shi ga Al’ummai, za su yi masa ba’a, su zage shi, su tofa masa miyau, za su yi masa bulala, su kuma kashe shi. A rana ta uku kuma zai tashi.” Almajiran ba su gane da ko ɗaya daga cikin wannan ba. An ɓoye musu ma’anarsa, kuma ba su gane da abin da yake magana a kai ba. Da Yesu ya yi kusa da Yeriko, akwai wani makaho da yake zaune a gefen hanya, yana bara. Da ya ji taron suna wucewa, sai ya yi tambaya ko mene ne ke faruwa. Suka ce masa, “Ai, Yesu Banazare ne ke wucewa.” Sai ya yi kira ya ce, “Yesu, Ɗan Dawuda, ka yi mini jinƙai!” Mutane da suke gaba suka kwaɓe shi, suka ce masa ya yi shiru. Amma sai ya ƙara ɗaga murya, yana cewa, “Ɗan Dawuda, ka yi mini jinƙai!” Sai Yesu ya tsaya, ya ba da umarni a kawo mutumin wurinsa. Da ya zo kusa, Yesu ya tambaye shi ya ce, “Me kake so in yi maka?” Sai ya amsa ya ce, “Ubangiji, ina so in sami ganin gari.” Yesu ya ce masa, “Ka sami ganin garinka; bangaskiyarka ta warkar da kai.” Nan da nan, ya sami ganin garinsa, kuma ya bi Yesu, yana yabon Allah. Da dukan mutane suka ga wannan, sai su ma suka yabi Allah. Yesu ya shiga Yeriko, yana ratsa ta cikinta. Akwai wani mutum a garin, mai suna Zakka. Shi shugaban masu karɓar haraji ne, mai arziki kuma. Ya so yă ga ko wane ne Yesu, amma saboda taron, bai iya ba, domin shi gajere ne. Saboda haka, ya yi gaba da gudu, kuma ya hau itacen sikamo, don yă gan shi, tun da Yesu zai bi wannan hanyar ne. Da Yesu ya iso wurin, sai ya ɗaga ido sama, ya ce masa, “Zakka, ka yi maza ka sauka. Ni kam, dole in sauka a gidanka yau.” Sai ya sauka nan da nan, ya karɓe shi da murna. Dukan mutane suka ga haka, kuma suka fara gunaguni, suka ce, “Ya je don yă zama baƙon ‘mai zunubi.’ ” Amma Zakka ya tashi a tsaye, ya ce wa Ubangiji, “Duba, Ubangiji! Nan take, rabin dukiyar da nake da shi, na ba wa matalauta. In kuma na taɓa cutan wani, a kan wani abu, zan mayar da shi ninki huɗu.” Sai Yesu ya ce masa, “Yau, ceto ya zo gidan nan, domin wannan mutum shi ma ɗan Ibrahim ne. Saboda Ɗan Mutum ya zo ne, domin yă nemi abin da ya ɓata, yă cece shi kuma.” Yayinda suna cikin sauraron wannan, sai ya ci gaba da gaya musu wani misali, domin ya yi kusa da Urushalima, kuma mutanen suna tsammani mulkin Allah zai bayyana, nan da nan. Ya ce, “Wani mutum mai martaba ya tafi wata ƙasa mai nisa don a naɗa shi sarki sa’an nan ya dawo. Saboda haka ya kira bayinsa goma ya ba su mina goma. Ya ce, ‘Ku yi kasuwanci da kuɗin nan, sai na dawo.’ “Amma talakawansa suka ƙi shi, sai suka aikar da wakilai bayansa, domin su ce, ‘Ba mu son wannan mutum ya zama sarkinmu.’ “Duk da haka, aka naɗa shi sarki, sa’an nan ya dawo gida. Sai ya aika aka kira bayin da ya ba su kuɗin, don yă san ribar da suka samu. “Na fari ya zo ya ce, ‘Ranka yă daɗe, minarka ya sami ribar goma.’ “Maigidan ya amsa ya ce, ‘Madalla, bawana mai kirki! Tun da ka yi aminci a kan abu ƙanƙani, ka yi riƙon birane goma.’ “Na biyun ya zo ya ce, ‘Ranka yă daɗe, minarka ya sami ribar biyar.’ “Maigidansa ya ce, ‘Kai ka yi riƙon birane biyar.’ “Sai wani bawan ya zo ya ce, ‘Ranka yă daɗe, ga minarka. Na ɓoye shi a wani ɗan tsumma. Na ji tsoronka, don kai mai wuyan sha’ani ne. Kakan ɗauki abin da ba ka ajiye ba, kakan kuma yi girbin abin da ba ka shuka ba.’ “Sai maigidansa, ya amsa ya ce, ‘Zan hukunta ka a kan kalmominka, kai mugun bawa! Ashe, ka san cewa ni mai wuyan sha’ani ne, nakan ɗauka abin da ban ajiye ba, ina kuma girbin abin da ban shuka ba? Don me ba ka sa kuɗina a wajen ajiya, don in na dawo, in sami riba a kai ba?’ “Sai ya ce wa waɗanda suke tsaye a wajen, ‘Ku karɓi minarsa ku ba wa wanda yake da mina goma.’ “Suka ce, ‘Ranka yă daɗe, ai, yana da guda goma ko!’ “Ya amsa ya ce, ‘Ina gaya muku, duk wanda yake da abu, za a ƙara masa. Amma wanda ba shi da shi kuwa, ko abin da yake da shi ma, za a karɓe. Amma waɗannan abokan gābana, waɗanda ba su so in zama sarkinsu ba, ku kawo su nan, ku karkashe su, a gabana.’ ” Bayan Yesu ya yi wannan magana, sai ya yi gaba zuwa Urushalima. Da ya kai kusa da Betfaji da Betani, a tudun da ake kira Dutsen Zaitun, sai ya aiki almajiransa guda biyu, ya ce musu, “Ku je ƙauyen da yake gaba da ku. Da kuna shiga, za ku tarar da wani ɗan jaki, wadda ba wanda ya taɓa hawa, a daure a wurin. Ku kunce shi ku kawo nan. In wani ya tambaye ku, ‘Don me kuke kunce shi?’ Ku ce masa, ‘Ubangiji yana bukatarsa.’ ” Waɗanda aka aika su yi gaba suka tafi, suka kuwa tarar kamar yadda ya gaya musu. Suna cikin kunce ɗan jakin, sai masu ɗan jakin suka ce musu, “Don me kuke kunce shi?” Suka amsa suka ce, “Ubangiji ne na bukatarsa.” Suka kawo shi wurin Yesu. Suka sa rigunarsu a kan ɗan jakin, sa’an nan suka sa Yesu a kai. Yana cikin tafiya, sai mutane suka shimfiɗa rigunarsu a kan hanya. Da ya yi kusa da wurin da hanyar ta gangara zuwa Dutsen Zaitun, sai dukan taron almajirai suka fara yabon Allah, da muryoyi masu ƙarfi, da murna, saboda dukan ayyukan banmamaki da suka gani. Suna cewa, “Mai albarka ne sarki wanda yake zuwa cikin sunan Ubangiji!” “Salama ta kasance a sama, da ɗaukaka kuma a can cikin sama!” Sai waɗansu Farisiyawa a cikin taron suka ce wa Yesu, “Malam, ka kwaɓi almajiranka!” Ya amsa ya ce, “Ina gaya muku, ko da sun yi shiru, duwatsu za su fara kirari.” Da ya yi kusa da Urushalima, ya kuma ga birnin, sai ya yi kuka a kanta, kuma ya ce, “In ke, ko ke ɗin ma, dā ma kin san abin da zai kawo miki salama a wannan rana, amma yanzu an ɓoye shi daga idanunki. Ranakun za su auko miki, a lokacin da abokan gābanki za su gina bango gāba da ke, su kuma kewaye inda kike, za su kuma tsare kowane gefenki, su sa ke a tsakiya. Za su fyaɗa ke a ƙasa, ke da ’ya’yan da suke cikin katanganki. Ba za su bar wani dutse a kan wani ba, saboda ba ki gane da lokacin da Allah zai ziyarce ki ba.” Sai ya shiga filin haikali, ya fara korar masu sayar da kaya. Ya ce musu, “A rubuce, yake cewa, ‘Gidana, zai zama gidan addu’a,’ amma ga shi kun mai da shi ‘kogon ’yan fashi.’ ” Kowace rana, ya yi ta koyarwa a haikalin. Amma manyan firistoci, da malaman dokoki, da shugabannin mutane, suna ƙoƙarin kashe shi. Amma ba su sami hanyar yin haka ba, domin kalmominsa sun kama hankalin dukan mutanen. Wata rana da Yesu yana koyar da mutane, yana musu wa’azin bishara a filin haikalin, sai manyan firistoci da malaman dokoki, tare da dattawan suka zo wurinsa. Suka ce masa, “Gaya mana, da wane iko kake yin waɗannan abubuwa. Wa ya ba ka wannan ikon?” Ya amsa ya ce, “Ni ma zan yi muku wata tambaya. Ku faɗa mini, baftismar Yohanna, daga sama ne ta fito, ko kuwa daga wurin mutane ne?” Sai suka yi shawara da junansu, suka ce, “In muka ce, ‘Daga sama ne,’ zai tambaya, ‘To, don me ba ku gaskata shi ba?’ Amma in kuma muka ce, ‘Daga mutane ne,’ dukan mutanen za su jajjefe mu da duwatsu, domin sun tabbata cewa, Yohanna annabi ne.” Don haka, sai suka amsa cewa, “Ba mu san inda ta fito ba.” Yesu ya ce, “To, ni ma ba zan gaya muku, ko da wane iko ne, nake yin waɗannan abubuwa ba.” Sai ya ci gaba da gaya wa mutanen wannan misali ya ce, “Wani mutum ya yi gonar inabi, sai ya ba da hayarta ga waɗansu manoma, sa’an nan ya yi wata doguwar tafiya. A lokacin girbi, sai ya aiki bawa zuwa wurin masu hayan, don su ba shi daga cikin ’ya’yan inabin. Amma ’yan hayan suka yi wa bawan nan dūka, suka kore shi hannu wofi. Ya sāke aikan wani bawa, shi ma suka yi masa dūka, suka kunyata shi, suka kuma kore shi hannu wofi. Har yanzu, ya sāke aikan na uku, amma suka ji masa rauni, suka jefar da shi waje. “Sai mai gonar inabin ya ce, ‘Me zan yi? Zan aiki ɗana da nake ƙauna, wataƙila za su girmama shi.’ “Amma da ’yan hayan suka gan shi, sai suka tattauna zancen, suka ce, ‘Wannan shi ne magājin, mu kashe shi sa’an nan gādon zai zama namu!’ Sai suka fitar da shi waje, suka kashe shi. “To, me mai gonar inabin zai yi da su? Zai zo ya karkashe masu hayan nan, ya ba wa waɗansu gonar inabin.” Da mutanen suka ji wannan, sai suka ce, “Allah ya sawwaƙa!” Yesu ya zura musu ido ya ce, “To, mene ne ma’anar abin da aka rubuta cewa, “ ‘Dutsen da magina suka ƙi, shi ne kuwa ya zama dutsen kan ginin’ Duk wanda ya fāɗi a kan dutsen nan, zai kakkarye. Kuma in dutsen nan ya fāɗi a kan wani, zai murƙushe shi.” Malaman dokoki da manyan firistoci, suka nemi hanyar kama shi nan da nan, domin sun san cewa, ya yi wannan misali a kansu ne, amma suna jin tsoron mutane. Sai suka sa masa ido, suka aiki ’yan leƙen asiri, waɗanda suka nuna kamar su masu gaskiya ne, suna nufin su kama shi game da abin da zai faɗa, domin su ba da shi ga gwamna mai mulki, da mai iko. Sai ’yan leƙen asirin suka tambaye shi, suka ce, “Malam, mun sani kana faɗin, kuma kana koyar da abin da yake daidai, ba ka kuma nuna bambanci, amma kana koyar da hanyar Allah bisa ga gaskiya. Daidai ne mu biya haraji ga Kaisar, ko babu?” Ya gane makircinsu, sai ya ce musu, “Nuna mini dinari. Hoton wane ne, kuma rubutun wane ne a kai?” Suka amsa, “Na Kaisar.” Sai ya ce musu, “Ku ba wa Kaisar abin da yake na Kaisar, ku kuma ba wa Allah abin da yake na Allah.” Ba su iya kama shi a kan abin da ya faɗa a fili ba. Amsarsa ya ba su mamaki, shi ya sa suka yi shiru. Waɗansu Sadukiyawa da suke cewa, ba tashin matattu, suka zo wurin Yesu da tambaya cewa, “Malam, Musa ya rubuta mana cewa, ‘In ɗan’uwan wani mutum ya mutu, ya bar mata amma ba ’ya’ya, dole mutumin ya aure gwauruwar, ya samo wa ɗan’uwansa ’ya’ya.’ To, an yi waɗansu ’yan’uwa bakwai. Na fari ya auri wata mace, ya mutu ba ’ya’ya. Na biyun, da na ukun suka aure ta. Haka nan dukansu bakwai suka mutu babu ’ya’ya. A ƙarshe, ita macen ma ta mutu. Shin, a tashin matattu, matar wa za tă zama? Tun da su bakwan nan, sun aure ta.” Yesu ya amsa ya ce, “Mutanen zamanin nan suna aure, suna kuma ba da aure, amma su waɗanda aka ga sun cancantar kasancewa a zamanin can, da kuma na tashin matattu, ba za su yi aure, ko su ba da aure ba. Kuma ba za su sāke mutuwa ba, gama su kamar mala’iku ne. Su ’ya’yan Allah ne, tun da su ’ya’yan tashin matattu ne. Amma bisa ga labari na bishiya nan, mai cin wuta da Musa ya gani a jeji, ko Musa ma, ya nuna cewa, matattu suna tashi. Gama ya kira Ubangiji, ‘Allah na Ibrahim, da Allah na Ishaku, da kuma Allah na Yaƙub.’ Shi ba Allah na matattu ba ne, amma na masu rai ne, gama a gare shi, duka na da rai.” Sai waɗansu malaman dokoki suka amsa suka ce, “Ka faɗi daidai, malam!” Kuma ba wanda ya sami ƙarfin halin yin masa waɗansu tambayoyi. Sai Yesu ya ce musu, “Yaya suke cewa, ‘Kiristi ɗan Dawuda ne?’ Dawuda da kansa ya faɗa a cikin Zabura, “ ‘Ubangiji ya ce wa Ubangijina, “Zauna a hannun damana, sai na sa abokan gābanka su zama matashin sawunka.” ’ Dawuda ya kira shi ‘Ubangiji.’ Ta, yaya zai zama ɗansa?” Yayinda dukan mutane suna cikin sauraronsa, sai Yesu ya ce wa almajiransa, “Ku yi hankali da malaman dokoki. Sukan so sa manyan riguna suna zaga, suna sha’awan karɓan gaisuwa a wuraren kasuwanci, da kuma wuraren zama mafi daraja a majami’u, da wuraren bangirma a bukukkuwa. Suna mamaye gidajen gwauraye, kuma don burga, suna dogayen addu’o’i. Ga irin waɗannan mutane, za a yi musu hukunci mai tsanani sosai.” Da Yesu ya ɗaga ido, sai ya ga waɗansu masu arziki suna sa baikonsu a ma’ajin haikalin. Ya kuma ga wata gwauruwa matalauciya, ta saka anini biyu. Sai ya ce, “Gaskiya ina faɗa muku, wacce nan gwauruwa matalauciya ta sa fiye da dukan sauran. Dukan mutanen nan sun ba da baikonsu daga cikin arzikinsu ne, amma ita daga cikin talaucinta, ta saka duk abin da take da shi na rayuwa.” Waɗansu daga cikin almajiransa, suka fara magana a kan yadda aka yi wa haikalin ado da duwatsu masu kyau, da kuma kyautai da aka keɓe wa Allah. Amma Yesu ya ce, “Wannan abin da kuke kallo a nan, lokaci yana zuwa da ba za a bar wani dutse a kan wani dutse ba. Kowannensu, za a rushe shi.” Suka tambaye shi suka ce, “Malam, yaushe waɗannan za su faru? Kuma wace alama za tă nuna cewa suna dab da faruwa?” Ya amsa ya ce, “Ku lura, kada ku kuma a ruɗe ku. Gama da yawa za su zo a cikin sunana, suna cewa, ‘Ai, ni ne shi,’ da kuma, ‘Lokaci ya yi kusa.’ Kada ku bi su. Sa’ad da kuka ji labarin yaƙe-yaƙe, da juye juyen mulki, kada ku tsorota. Dole ne waɗannan abubuwa su fara faruwa, amma ƙarshen ba zai zo nan da nan ba.” Sai ya ce musu, “Al’umma za tă tasar wa al’umma, mulki zai tasar wa mulki. Za a yi manyan girgizar ƙasa, da yunwa, da annoba a wurare dabam-dabam, da kuma abubuwa masu bantsoro, da manyan alamu daga sama. “Amma kafin duk abubuwa nan, za a kama ku a tsananta muku. Za a kai ku majami’u, da kurkuku. Za a kuma kai ku gaban sarakuna da gwamnoni, kuma dukan waɗannan saboda sunana. Wannan zai sa ku zama shaidu a gare su. Amma ku yi ƙuduri, wato, ku shirya zuciyarku, a kan ba za ku damu ba kafin lokacin, game da yadda za ku kāre kanku. Gama zan ba ku kalmomi, da hikima waɗanda ba ko ɗaya daga cikin maƙiyanku, za su iya tsayayya da ku, ko su ƙaryata. Har iyayenku, da ’yan’uwanku maza, da danginku, da abokanku ma, duk za su bashe ku, su kuma kashe waɗansunku. Duk mutane za su ƙi ku saboda ni. Amma ko gashi ɗaya na kanku, ba zai hallaka ba. Ta wurin tsayawa da ƙarfi, za ku sami rai. “In kuka ga mayaƙa sun kewaye Urushalima, za ku sani rushewarta ya yi kusa. A lokacin nan, bari waɗanda suke Yahudiya, su gudu zuwa cikin duwatsu. Bari waɗanda suke cikin birnin kuma su fita, bari kuma waɗanda suke ƙauye kada su shiga birnin. Gama wannan shi ne lokacin hukunci, saboda a cika duk abin da aka rubuta. Zai zama abin kaito ga mata masu ciki, da mata masu renon ’ya’ya, a waɗancan kwanakin! Za a yi baƙin ciki mai tsanani a ƙasar, da kuma fushi mai tsanani a kan mutanen nan. Za a kashe su da takobi, a kuma ɗauke su ’yan kurkuku, zuwa dukan al’ummai. Al’ummai za su tattaka Urushalima, har sai lokacin Al’ummai ya cika. “Za a yi alamu a cikin rana, da cikin wata, da cikin taurari. A duniya, al’ummai za su yi baƙin ciki, su kuma rikice don tsoro, saboda ruri da kuma tafasar teku. Mutane za su suma don tsoro, za su kuma yi fargaba, a kan abin da yake zuwa a bisan duniya, gama za a girgiza duniyar taurarin sararin sama. A lokacin ne za su ga Ɗan Mutum yana zuwa cikin girgije, da iko, da ɗaukaka mai girma. Sa’ad da waɗannan abubuwa sun fara faruwa, ku tashi tsaye, ku ɗaga kawunanku, domin fansarku yana matsowa kusa.” Sai ya gaya musu wannan misali ya ce, “Ku dubi itacen ɓaure da dukan itatuwa. A duk lokacin da sun fara fitar da ganye, za ku gani da kanku, ku san cewa, damina ta yi kusa. Haka ma, in kuka ga waɗannan abubuwa suna faruwa, ku sani mulkin Allah ya yi kusa. “Gaskiya nake gaya muku, ba shakka, wannan zamani ba zai shuɗe ba, sai dukan waɗannan abubuwa sun cika. Sama da ƙasa za su shuɗe, amma kalmomina ba za su taɓa shuɗewa ba. “Ku lura fa don kada son jin daɗi na banza, da shaye-shaye, da damuwa na rayuwa su rinjayi zuciyarku, har ranar ta auko muku ba tsammani kamar tarko. Gama za tă zo a kan kowa da yake kan dukan duniya. Ku yi tsaro kullum, ku yi addu’a don ku iya kuɓuta daga dukan waɗannan abubuwa da suke kusan faruwa, don ku iya tsayawa a gaban Ɗan Mutum.” Kowace rana, Yesu yakan je haikalin ya yi koyarwa, da kowace yamma kuma, ya je ya kwana a kan tudun da ake kira Dutsen Zaitun. Da sassafe kuma, dukan mutanen suka zo haikalin, don su saurare shi. Yanzu fa, Bikin Burodi Marar Yistin da ake kira Bikin Ƙetarewa ya yi kusa, manyan firistoci da malaman dokoki kuma suna neman yadda za su kashe Yesu a ɓoye, don suna tsoron mutane. Shaiɗan kuwa ya shiga Yahuda, wanda ake kira Iskariyot, ɗaya daga cikin Sha Biyun. Sai Yahuda ya je ya tattauna da manyan firistoci, da ma’aikatan ’yan gadin haikali, a kan yadda zai ba da Yesu a gare su. Suka kuwa yi murna, suka yarda su ba shi kuɗi. Ya ko yarda, ya fara neman zarafin da zai ba da Yesu a gare su, sa’ad da taro ba sa nan tare da shi. Sai ranar Bikin Burodi Marar Yisti ta kewayo, wato, ranar hadayar ɗan ragon kafara na Bikin Ƙetarewa. Sai Yesu ya aiki Bitrus da Yohanna, ya ce musu, “Ku je ku yi shirye-shiryen Bikin Ƙetarewar da za mu ci.” Suka tambaye shi suka ce, “Ina kake so mu je mu yi shirin?” Ya amsa ya ce, “Sa’ad da kuka shiga cikin gari, za ku sadu da wani mutum yana ɗauke da tulun ruwa. Ku bi shi zuwa gidan da zai shiga. Ku ce wa maigidan, Malam ya aike mu mu ce maka, ‘Ina ɗakin baƙi, inda ni da almajiraina za mu ci abincin Bikin Ƙetarewa?’ Zai nuna muku wani babban ɗakin sama a shirye. Nan za ku yi shirin.” Sai suka tafi, suka kuma iske kome kamar yadda Yesu ya faɗa musu. Sai suka shirya Bikin Ƙetarewa. Da lokaci ya yi, sai Yesu ya zauna tare da manzanninsa don cin abinci. Sai ya ce musu, “Na yi marmari ƙwarai don in ci wannan Bikin Ƙetarewa tare da ku, kafin in sha wahala. Ina dai gaya muku, ba zan ƙara cinsa ba, sai ya sami cika a mulkin Allah.” Bayan ya ɗauki kwaf ruwan inabi, ya yi godiya, sai ya ce, “Ku karɓa, ku rarraba wa junanku. Ina dai gaya muku, ba zan ƙara sha daga ’ya’yan inabi ba, sai mulkin Allah ya zo.” Sai ya ɗauki burodi ya yi godiya, ya kakkarya ya ba su, da cewa, “Wannan jikina ne, da aka bayar dominku. Ku riƙa yin haka don tunawa da ni.” Haka kuma, bayan abincin, ya ɗauki kwaf ruwan inabi ya ce, “Wannan kwaf ruwan inabi shi ne, na sabon alkawari cikin jinina, da aka zubar dominku. Amma hannun wanda zai ci amanata, yana cin abincin tare da ni. Ɗan Mutum zai mutu kamar yadda aka ƙaddara, amma kaiton mutumin da zai bashe shi.” Sai suka fara tambayar junansu, ko wane ne a cikinsu zai yi wannan. Gardama ta tashi a tsakaninsu, a kan ko wane ne a cikinsu ya fi girma. Yesu ya ce musu, “Sarakunan Al’ummai suna nuna iko a kan mutanensu, kuma waɗanda suke nuna iko a kansu, suna kiran kansu Masu Taimakon mutane. Amma ku, kada ku zama haka. A maimakon haka, sai dai wanda ya fi girma a cikinku, ya zama kamar wanda ya fi ƙanƙanta, wanda kuma ke mulki, ya zama kamar mai hidima. Wane ne ya fi girma? Wanda yake zaune a tebur ne, ko kuma shi da yake yin hidima? Ashe, ba wanda yake zaune a tebur ba ne? Amma ga ni, ni mai yin hidima ne a cikinku. Ku ne kuka tsaya tare da ni a gwaje-gwajen da na sha. Daidai kamar yadda Ubana ya ba ni mulki, haka ni ma nake ba ku. Saboda ku ci, ku sha a teburina a cikin mulkina. Kuma ku zauna a kan gadon sarauta, ku yi wa kabilu goma sha biyu na Isra’ila shari’a. “Siman, Siman, Shaiɗan ya nemi izini ya sheƙe ka kamar alkama. Amma na yi maka addu’a, Siman, domin kada bangaskiyarka ta kāsa. Bayan ka juyo, ka ƙarfafa ’yan’uwanka.” Amma ya amsa ya ce, “Ubangiji, ina a shirye in tafi tare da kai har kurkuku, ko mutuwa ma.” Yesu ya ce, “Ina gaya maka Bitrus, kafin zakara ya yi cara yau, za ka yi mūsun sanina sau uku.” Sai Yesu ya tambaye, su ya ce, “Lokacin da na aike ku ba tare da jakar kuɗi, ko jaka, ko takalma ba, kun rasa wani abu?” Suka amsa, “Babu.” Ya ce musu, “Amma yanzu, in kuna da jakar kuɗi, ko jaka, ku ɗauka. In kuma ba ku da takobi, ku sayar da rigarku, ku saya. A rubuce yake cewa, ‘An lissafta shi tare da masu zunubi.’ Ina kuwa gaya muku, dole wannan ya cika a kaina. I, abin da aka rubuta a kaina yana kusan cikawa.” Almajiran suka ce, “Duba Ubangiji, ga takuba biyu.” Yesu ya ce, “Ya isa.” Yesu ya fita zuwa Dutsen Zaitun kamar yadda ya saba, almajiransa kuma suka bi shi. Da ya kai wurin, sai ya ce musu, “Ku yi addu’a don kada ku fāɗi cikin jarraba.” Sai ya janye daga wurinsu, misalin nisan jifa, ya durƙusa a ƙasa ya yi addu’a, “Uba, in ka yarda, ka ɗauke mini wannan kwaf, amma ba nufina ba, sai dai naka.” Wani mala’ika daga sama ya bayyana gare shi, ya ƙarfafa shi. Domin tsananin azaba, sai ya ƙara himma cikin addu’a, zuffansa kuma na ɗigowa ƙasa kamar jini. Da ya tashi daga addu’a, ya koma inda almajiransa suke, sai ya iske su suna barci, daga gajiyar baƙin ciki. Ya tambaye su, “Don me kuke barci? Ku tashi ku yi addu’a, don kada ku fāɗi cikin jarraba.” Yana cikin magana sai ga taro sun zo. Mutumin nan da ake kira Yahuda, ɗaya daga cikin Sha Biyun, shi ya bi da su. Sai ya matso kusa da Yesu don yă yi masa sumba. Amma Yesu ya tambaye shi ya ce, “Yahuda, ashe, da sumba za ka bashe Ɗan Mutum?” Da masu bin Yesu suka ga abin da zai faru, sai suka ce, “Ubangiji, mu yi sara da takubanmu ne?” Sai ɗayansu ya kai sara ga bawan babban firist, ya sare kunnen damansa. Amma Yesu ya amsa ya ce, “Kada a ƙara yin wannan!” Sai ya taɓa kunnen mutumin da aka sara, ya warkar da shi. Sai Yesu ya ce wa manyan firistoci, da ma’aikatan ’yan gadin haikali, da dattawa, waɗanda suka zo don su kama shi, “Ina jagoran wani tawaye ne, da za ku zo da takuba da sanduna? Kullum ina tare da ku a filin haikali, amma ba ku kama ni ba. Amma wannan ne sa’a naku, lokacin da duhu yake mulki.” Sai suka kama shi suka kai shi gidan babban firist. Bitrus ya bi su daga nesa. Amma da suka hura wuta a tsakiyar harabar gidan, kowa ya zauna, sai Bitrus ya zo ya zauna tare da su. Wata baiwa ta gan shi zaune kusa da wutar. Ta dube shi sosai sa’an nan, ta ce, “Ai, wannan mutum ma yana tare da shi.” Amma ya yi mūsu ya ce, “Mace, ban san shi ba!” Bayan ɗan lokaci kaɗan, wani dabam ya gan shi ya ce, “Kai ma ɗayansu ne.” Bitrus ya amsa ya ce, “Kai, ba na cikinsu!” Bayan kamar sa’a ɗaya, sai wani mutum ya ce, “Ba shakka, mutumin nan ma yana tare da shi, don shi mutumin Galili ne.” Bitrus ya amsa ya ce, “Kai, ban ma san abin da kake magana a kai ba!” Yana cikin magana, sai zakara ya yi cara. Ubangiji kuma ya juya ya kafa wa Bitrus ido. Sai Bitrus ya tuna da maganar da Ubangiji ya ce masa, “Kafin zakara ya yi cara yau, za ka yi mūsun sanina sau uku.” Sai ya fita waje, ya yi kuka mai zafi. Mutanen da suke gadin Yesu suka fara masa ba’a da dūka. Suka rufe masa idanu suna tambaya cewa, “Ka yi annabci! Wa ya mare ka?” Suka kuma yi masa waɗansu baƙaƙen maganganu masu yawa. Da gari ya waye, sai majalisar dattawa na mutane, da manyan firistoci, da malaman dokoki, suka taru wuri ɗaya. Sai aka kawo Yesu a gabansu. Suka ce, “Ka faɗa mana, ko kai ne Kiristi?” Yesu ya amsa ya ce, “Ko na gaya muku, ba za ku gaskata ni ba, in kuma na yi muku tambaya ba za ku iya ba ni amsa ba. Amma daga yanzu, Ɗan Mutum zai zauna a hannun dama na Allah Mai Iko.” Sai dukansu suka yi tambaya suka ce, “Wato, kai Ɗan Allah ke nan?” Ya amsa ya ce, “Kun faɗa daidai, ni ne.” Sai suka ce, “Wace shaida kuma muke nema? Ai, mun ji abin da ya ce da bakinsa.” Sai dukan majalisa suka tashi, suka kai shi gaban Bilatus. Suka fara zarginsa suna cewa, “Mun sami wannan mutum yana rikitar da al’ummarmu. Yana hana a biya haraji ga Kaisar. Yana kuma cewa, shi Kiristi ne, sarki kuma.” Sai Bilatus ya tambayi Yesu ya ce, “Kai ne sarkin Yahudawa?” Yesu ya amsa ya ce, “I, haka yake, kamar yadda ka faɗa.” Sai Bilatus ya sanar wa manyan firistoci da taron ya ce, “Ni fa, ban sami wani ainihin abin zargi game wannan mutum nan ba.” Amma suka nace, suna cewa, “Yana tā da hankulan mutane, ko’ina a Yahudiya da koyarwarsa. Ya fara daga Galili, ga shi har ya kai nan.” Da Bilatus ya ji haka, sai ya yi tambaya, “Ko shi mutumin Galili ne?” Da ya ji cewa, Yesu yana ƙarƙashin mulkin Hiridus ne, sai ya aika da shi zuwa wurin Hiridus, don a lokacin Hiridus yana Urushalima. Da Hiridus ya ga Yesu, sai ya yi murna ƙwarai, don tun dā ma yana marmari ya gan shi a kan abin da ya ji game da shi. Ya yi fata ya ga Yesu, yă kuma yi waɗansu ayyukan banmamaki. Ya yi masa tambayoyi masu yawa, amma Yesu bai ba shi ko amsa ba. Manyan firistoci da malaman dokoki suna tsaye a wurin, suna kawo zargi masu ƙarfi a kansa. Sai Hiridus da sojojinsa suka wulaƙanta shi, suka yi masa ba’a. Sa’an nan, suka sa masa babban riga, suka mai da shi wurin Bilatus. A ranar, Hiridus da Bilatus suka zama abokan juna, don tun dā ma, su abokan gāba ne. Bilatus ya tara manyan firistoci, da masu mulki, da mutane, ya ce musu, “Kun kawo mini wannan mutum, a matsayin wanda yana zuga mutane su yi tawaye. Na bincike shi a gabanku, ban ga a kan me kuka kawo kararsa ba. Haka ma Hiridus, shi ya sa ya dawo da shi nan wurinmu. Kamar yadda ku ma kun gani, ba abin da mutumin nan ya yi, da ya isa mutuwa. Saboda haka, zan yi masa bulala, in sāke shi.” Suka yi ihu gaba ɗaya suka ce, “A yi gaba da wannan mutum! A sake mana Barabbas!” (Barabbas yana kurkuku saboda laifin tā da hankali a birnin, da kuma don kisankai.) Sai Bilatus ya sāke yin musu magana don yana so ya saki Yesu. Amma sai suka ci gaba da ihu, suna cewa, “A gicciye shi! A gicciye shi!” Ya sāke ce musu, sau na uku, “Don me? Wane laifi wannan mutum ya yi? Ni dai ban same shi da wani dalilin da ya isa a kashe shi ba. Saboda haka, zan sa a hore shi, sa’an nan in sāke shi.” Amma suna ihu, suna nacewa, suna cewa, dole a gicciye shi, har ihunsu ya rinjaye shi. Sai Bilatus ya biya bukatarsu da ya ji roƙonsu. Ya saki mutumin da aka jefa a kurkuku saboda tā da hankali, da kisankai, shi wanda suka roƙa. Sa’an nan ya ba da Yesu ga nufinsu. Sa’ad da suna tafiya da Yesu, sai wani da ake kira Siman, mutumin Sairin, yana zuwa daga ƙauye. Suka kama shi, suka aza masa gicciyen, suka tilasta shi ya ɗauki gicciyen, ya bi Yesu a baya. Mutane da yawa sosai suka bi shi, a cikinsu ma da mata waɗanda suka yi makoki da kuka dominsa. Yesu ya juya, ya ce musu, “’Yan matan Urushalima, kada ku yi kuka saboda ni, amma ku yi kuka saboda kanku, da kuma saboda ’ya’yanku. Gama lokaci yana zuwa da za ku ce, ‘Masu albarka ne bakararru, wato, mata marasa haihuwa, da mahaihuwar da ba su taɓa haihuwa ba, da kuma mama da ba su taɓa shayar da nono ba!’ Sa’an nan “ ‘za su ce wa duwatsu, “Ku fāɗi a kanmu!” Za su ce wa tuddai kuma, “Ku rufe mu!” ’ Gama in mutane suna yin waɗannan abubuwa a lokacin da itace na ɗanye, me zai faru in ya bushe?” Tare da shi akwai mutum biyu masu laifi, da aka tafi da su don a gicciye. Da suka isa wurin da ake kira “Ƙoƙon Kai,” nan suka gicciye shi, tare da masu laifin nan, ɗaya a hannun damansa, ɗayan kuma a hagunsa. Yesu ya ce, “Ya Uba ka yi musu gafara, don ba su san abin da suke yi ba.” Suka rarraba tufafinsa ta wurin jefa ƙuri’a. Mutanen suka tsaya suna kallo. Har masu mulki ma suka yi masa ba’a, suna cewa, “Ya ceci waɗansu, to, ya ceci kansa in shi ne Kiristi na Allah, Zaɓaɓɓe.” Sojoji su ma, suka zo suka yi masa ba’a. Suka miƙa masa ruwan tsami. Suka ce, “In kai ne sarkin Yahudawa, ka ceci kanka mana.” Bisa da shi kuma akwai rubutun da ya ce, Wannan shi ne Sarkin Yahudawa. Ɗaya daga cikin masu laifin da aka gicciye a wurin ya zazzage shi ya ce, “Shin, ba kai ne Kiristi ba? To, ka ceci kanka, ka kuma cece mu mana!” Amma ɗayan mai laifi ya kwaɓe shi ya ce, “Ba ka da tsoron Allah ne, wai saboda kana ƙarƙashin hukunci ɗaya tare da shi? Horonmu, daidai aka yi mana, sakamakon abin da muka yi ne. Amma wannan mutum, bai yi wani laifi ba.” Sai ya ce, “Yesu, ka tuna da ni sa’ad da ka shiga mulkinka.” Yesu ya amsa, ya ce masa, “Gaskiya nake faɗa maka, yau ɗin nan, za ka kasance tare da ni, a mulkina a sama.” Yanzu kuwa wajen sa’a ta shida ne, kuma duhu ya rufe ko’ina a ƙasar, har zuwa sa’a ta tara, domin rana ta daina haskakawa. Labulen da yake cikin haikali kuma ya yage kashi biyu. Yesu ya yi kira da babbar murya ya ce, “Ya Uba, na danƙa ruhuna a hannunka.” Da ya faɗi haka, sai ya ja numfashi na ƙarshe. Da jarumin ya ga abin da ya faru, sai ya yabi Allah ya ce, “Gaskiya, wannan mutum mai adalci ne.” Da dukan mutanen da suka taru, domin shaidar waɗannan abubuwa, suka ga abin da ya faru, sai suka buga ƙirjinsu suka tafi. Amma dukan mutanen da suka san Yesu, tare da mata da suka bi shi daga Galili, suka tsaya daga nesa suna kallon abubuwan nan. Akwai wani mutum mai suna Yusuf, ɗan Majalisa, wanda shi nagari ne, mai adalci, shi dā ma bai yarda da shawararsu, da kuma abin da suka yi ba. Shi daga Arimateya ne wani garin Yahudiya. Yana kuma jiran zuwa mulkin Allah. Sai ya je wurin Bilatus ya roƙa a ba shi jikin Yesu. Sai ya saukar da jikin, ya nannaɗe shi a cikin zanen lilin, ya sa shi a wani kabari da aka fafe a cikin dutse, wadda ba a taɓa sa kowa ba. An yi haka ne a Ranar Shirye-shirye, ranar Asabbaci kuma yana dab da farawa. Matan da suka zo tare da Yesu, daga Galili suka bi Yusuf suka ga kabarin, da kuma yadda aka ajiye jikin. Sa’an nan, suka koma gida, suka shirya kayan ƙanshi da turare. Amma suka huta a ranar Asabbaci don kiyaye doka. Da sassafe a ranar farko ta mako, matan suka je kabarin, da kayan ƙanshin da suka shirya. Suka iske an riga an gungurar da dutsen daga bakin kabarin. Amma da suka shiga ciki, ba su iske jikin Ubangiji Yesu ba. Yayinda suna cikin tunani a kan wannan, nan take, ga waɗansu mutum biyu tsaye kusa da su, sanye da kaya masu ƙyalli, kamar walƙiya. A cikin tsoro, matan suka fāɗi da fuskokinsu a ƙasa, amma mutanen suka ce musu, “Me ya sa kuke neman mai rai a cikin matattu? Ba ya nan, ya tashi! Ku tuna yadda ya gaya muku tun yana tare da ku a Galili cewa, ‘Dole a ba da Ɗan Mutum ga hannun masu zunubi, a kuma gicciye shi, a rana ta uku kuma a tashe shi.’  ” Sai suka tuna da maganarsa. Da suka dawo daga kabarin, sai suka faɗa wa Sha Ɗayan nan da sauransu, dukan waɗannan abubuwa. Matan da suka gaya wa manzannin waɗannan abubuwa su ne, Maryamu Magdalin, da Yowanna, da Maryamu uwar Yaƙub, da waɗansu da suke tare da su. Amma ba su gaskata matan ba, domin sun ɗauki kalmominsu wani zancen banza ne. Duk da haka, Bitrus ya tashi a guje zuwa kabarin. Da ya sunkuya, sai ya ga ƙyallayen lilin kaɗai a kwance. Sai ya koma yana tunani a ransa, a kan abin da ya faru. A wannan rana kuma, biyu daga cikinsu suna tafiya zuwa wani ƙauye, da ake kira Emmawus, da suke kusan mil bakwai daga Urushalima. Suna magana da juna a kan dukan abubuwan da suka faru. Da suna magana, kuma suna tattauna waɗannan abubuwa da junansu, sai Yesu da kansa ya zo yana tafiya tare da su. Amma ba a ba su ikon gane shi ba. Sai ya tambaye, su ya ce, “Mene ne kuke tattaunawa da juna a cikin tafiyarku?” Suka tsaya shiru, da damuwa a fuskarsu. Ɗaya daga cikinsu, mai suna Kiliyobas, ya tambaye shi ya ce, “Ashe, kai baƙo ne a Urushalima, da ba ka san abubuwan da suka faru a can, a cikin kwanakin nan ba?” Sai ya yi tambaya, “Waɗanne abubuwa?” Suka amsa suka ce, “Game da Yesu Banazare. Shi annabi ne, mai iko ne kuma cikin ayyukansa da maganarsa, a gaban Allah da kuma dukan mutane. Manyan firistoci da masu mulkinmu sun ba da shi a yi masa hukuncin mutuwa, suka kuwa gicciye shi. Amma da, muna sa zuciya cewa, shi ne wanda zai fanshi Isra’ila. Bugu da ƙari kuma yau kwana uku ke nan tun da wannan abin ya faru. Har wa yau, waɗansu daga cikin matanmu sun ba mu mamaki. Sun je kabarin da sassafen nan, amma ba su sami jikinsa ba. Sun dawo sun faɗa mana cewa, sun ga wahayi na mala’iku, da suka ce yana da rai. Sa’an nan, waɗansu abokanmu suka je kabarin, suka kuma tarar da kome kamar yadda matan suka faɗa, amma shi, ba su gan shi ba.” Sai ya ce musu, “Ashe, ku marasa azanci ne, masu nauyin zuciyar gaskata, da dukan abin da annabawa suka faɗa! Ai, dole Kiristi yă sha waɗannan wahalolin, kafin yă shiga ɗaukakarsa. Sai ya fara bayyana musu daga Musa da dukan Annabawa, abin da dukan Nassi ya faɗa a kansa.” Da suka yi kusa da ƙauyen da za su, sai Yesu ya yi kamar zai ci gaba. Amma suka matsa masa suka ce, “Sauka wurinmu, don dare ya kusa, rana ta kusa fāɗuwa.” Sai ya sauka wurinsu. Da ya zauna a tebur tare da su, sai ya ɗauki burodi, ya yi godiya, ya kakkarya ya fara ba su. Sa’an nan idanunsu suka buɗe, suka gane shi. Sai ya ɓace musu. Suka tambayi juna, “Ashe, shi ya sa zukatanmu suka kuna a cikinmu, sa’ad da yake magana da mu a hanya, yana bayyana mana Nassi.” Suka tashi nan da nan suka koma Urushalima. A can suka sami Sha Ɗayan nan da waɗanda suke tare da su a wuri ɗaya, suna cewa, “Gaskiya ne! Ubangiji ya tashi, ya kuma bayyana ga Siman” Sai su biyun nan suka ba da labarin abin da ya faru a hanya, da kuma yadda suka gane Yesu yayinda ya kakkarya burodin. Suna cikin wannan zance, sai ga Yesu da kansa tsaye a tsakiyarsu. Sai ya ce musu, “Salama a gare ku!” Suka firgita, suka tsorota, suna tsammani fatalwa ce suka gani. Sai ya ce musu, “Don me kuke damuwa, kuke kuma shakka a zuciyarku? Ku duba hannuwana da ƙafafuna. Ai, ni ne da kaina! Ku taɓa ni ku ji, ai, fatalwa ba ta da nama da ƙashi, yadda kuke gani nake da su.” Da ya faɗi haka, sai ya nuna musu hannuwansa da ƙafafunsa. Kuma har yanzu, suna cikin rashin gaskatawa, saboda murna da mamaki, sai ya tambaye su, “Kuna da abinci a nan?” Suka ba shi ɗan gasasshen kifi, ya karɓa ya ci a gabansu. Ya ce musu, “Wannan shi ne abin da na gaya muku tun ina tare da ku cewa, dole a cika kome da aka rubuta game da ni, a cikin Dokar Musa, da Annabawa, da kuma Zabura.” Sai ya wayar da tunaninsu don su fahimci Nassi. Ya ce musu, “Wannan shi ne abin da aka rubuta, cewa dole Kiristi yă sha wahala, a rana ta uku kuma yă tashi daga matattu. Kuma a cikin sunansa za a yi wa’azin tuba da gafarar zunubai, ga dukan ƙasashe. Za a kuwa fara daga Urushalima. Ku ne shaidun waɗannan abubuwa. Zan aika muku da abin da Ubana ya yi alkawari. Amma ku dakata a birnin tukuna, sai an rufe ku da iko daga sama.” Bayan ya kai su waje kusa da Betani, sai ya ɗaga hannuwansa ya sa musu albarka. Yana cikin sa musu albarka, sai ya rabu da su. Aka ɗauke shi zuwa cikin sama. Sai suka yi masa sujada, suka koma Urushalima cike da murna sosai. Sai suka ci gaba da zama a cikin haikalin, suna yabon Allah. Tun farar farawa akwai Kalma, Kalman kuwa yana nan tare da Allah, Kalman kuwa Allah ne. Yana nan tare da Allah tun farar farawa. Ta wurin Kalman ne aka halicci dukan abubuwa. In ba tare da shi ba, babu abin da aka yi wanda aka yi. A cikinsa rai ya kasance, wannan rai kuwa shi ne hasken mutane. Hasken yana haskakawa cikin duhu, amma duhun bai rinjaye shi ba. Akwai wani mutumin da aka aiko daga Allah; mai suna Yohanna. Ya zo a matsayin mai shaida domin yă ba da shaida game da wannan haske, don ta wurinsa dukan mutane su ba da gaskiya. Shi kansa ba shi ne hasken ba; sai dai ya zo a matsayin shaida ne kaɗai ga hasken. Haske na gaskiya da yake ba da haske ga kowane mutum mai shigowa duniya. Yana a duniya, kuma ko da yake an yi duniya ta wurinsa ne, duniya ba tă gane shi ba. Ya zo wurin abin da yake nasa, amma nasa ɗin ba su karɓe shi ba. Duk da haka dukan waɗanda suka karɓe shi, ga waɗanda suka gaskata a sunansa, ya ba su iko su zama ’ya’yan Allah ’ya’yan da aka haifa ba bisa hanyar ’yan adam, ko shawarar mutum ko nufin namiji ba, sai dai haifaffu bisa ga nufin Allah. Kalman ya zama mutum, ya kuwa zauna a cikinmu. Muka ga ɗaukakarsa, ɗaukaka ta wanda yake Ɗaya kuma Makaɗaici, wanda ya zo daga wurin Uba, cike da alheri da gaskiya. (Yohanna ya ba da shaida game da shi. Ya ɗaga murya yana cewa, “Wannan shi ne wanda na ce, ‘Mai zuwa bayana ya fi ni girma domin yana nan kafin ni.’ ”) Daga yalwar alherinsa dukanmu muka sami albarka bisa albarka. Gama an ba da doka ta wurin Musa; alheri da gaskiya kuwa sun zo ne ta wurin Yesu Kiristi. Ba wanda ya taɓa ganin Allah, sai dai Allah da yake Ɗaya da kuma Makaɗaici wanda yake a gefen Uba, shi ne ya bayyana shi. To, ga shaidar Yohanna sa’ad da Yahudawan Urushalima suka aiki firistoci da Lawiyawa su tambaye shi ko shi wane ne. Bai yi mūsu ba, amma ya shaida a fili cewa, “Ba ni ne Kiristi ba.” Sai suka tambaye shi suka ce, “To, wane ne kai? Kai ne Iliya?” Ya ce, “A’a, ni ba shi ba ne.” “Kai ne Annabin nan?” Ya amsa ya ce, “A’a.” A ƙarshe suka ce, “Wane ne kai? Ka ba mu amsa don mu mayar wa waɗanda suka aike mu. Me kake ce da kanka?” Yohanna ya amsa da kalmomin annabi Ishaya, “Ni murya ne mai kira a hamada, ‘Ku miƙe hanya domin Ubangiji.’ ” To, waɗansu Farisiyawan da aka aika suka tambaye shi suka ce, “Don me kake yin baftisma in kai ba Kiristi ba ne, ba kuwa Iliya ba, ba kuma annabin nan ba?” Yohanna ya amsa ya ce, “Ni dai ina baftisma da ruwa ne, amma a cikinku akwai wani tsaye da ba ku sani ba. Shi ne mai zuwa bayana, wanda ko igiyar takalmansa ma ban isa in kunce ba.” Wannan duk ya faru ne a Betani a ƙetaren Urdun, inda Yohanna yake yin baftisma. Kashegari Yohanna ya ga Yesu yana zuwa wajensa sai ya ce, “Ku ga, ga Ɗan Rago na Allah mai ɗauke zunubin duniya! Wannan shi ne wanda nake nufi sa’ad da na ce, ‘Mutum mai zuwa bayana ya fi ni girma, domin yana nan kafin ni.’ Ko ni ma dā ban san shi ba, sai dai abin da ya sa na zo ina baftisma da ruwa shi ne domin a bayyana shi ga Isra’ila.” Sai Yohanna ya ba da wannan shaida, “Na ga Ruhu ya sauko kamar kurciya daga sama ya zauna a kansa. Dā ban san shi ba, sai dai wanda ya aiko ni in yi baftisma da ruwa ya gaya mini cewa, ‘Mutumin da ka ga Ruhu ya sauko ya kuma zauna a kansa shi ne wanda zai yi baftisma da Ruhu Mai Tsarki.’ Na gani na kuma shaida cewa wannan Ɗan Allah ne.” Kashegari kuma Yohanna yana can tare da biyu daga cikin almajiransa. Da ya ga Yesu yana wucewa, sai ya ce, “Ku ga, ga Ɗan Rago na Allah!” Da almajiran nan biyu suka ji ya faɗi haka, sai suka bi Yesu. Da juyewa, sai Yesu ya ga suna bin sa, sai ya tambaye, su ya ce, “Me kuke nema?” Suka ce, “Rabbi” (wato, “Malam”), “ina kake da zama?” Ya amsa musu ya ce, “Ku zo, za ku kuma gani.” Saboda haka suka je suka ga inda yake da zama, suka kuma zauna a can tare da shi. Wajen sa’a ta goma ce kuwa. Andarawus ɗan’uwan Siman Bitrus, yana ɗaya daga cikin biyun nan da suka bi Yesu bayan da suka ji maganar Yohanna a kan Yesu. Abu na fari da Andarawus ya yi shi ne ya sami ɗan’uwansa Siman ya gaya masa cewa, “Mun sami Almasihu” (wato, Kiristi). Ya kuma kawo shi wurin Yesu. Yesu ya dube shi ya ce, “Kai ne Siman ɗan Yohanna. Za a ce da kai Kefas” (in an fassara, Bitrus ke nan ). Kashegari Yesu ya yanke shawara yă tafi Galili. Da ya sami Filibus sai ya ce masa, “Bi ni.” Filibus, kamar Andarawus da Bitrus shi ma daga garin Betsaida ne. Filibus ya sami Natanayel ya kuma gaya masa, “Mun sami wanda Musa ya rubuta game da shi a cikin Doka, kuma wanda annabawa suka rubuta a kansa, Yesu Banazare, ɗan Yusuf.” Natanayel ya ce, “A Nazaret! Wani abin kirki zai iya fito daga can?” Filibus ya ce, “Zo ka gani.” Da Yesu ya ga Natanayel yana zuwa, sai ya yi magana game da shi cewa, “Ga mutumin Isra’ila na gaske wanda ba shi da ha’inci.” Natanayel ya yi tambaya ya ce, “A ina ka san ni?” Yesu ya amsa ya ce, “Na gan ka yayinda kake a gindin itacen ɓaure, kafin Filibus yă kira ka.” Sai Natanayel ya ce, “Rabbi, kai Ɗan Allah ne. Kai ne Sarkin Isra’ila.” Yesu ya ce, “Ka gaskata domin na ce maka na gan ka a gindin itacen ɓaure. Za ka ga abubuwan da suka fi haka.” Sai ya ƙara da cewa, “Gaskiya nake gaya muku, za ku ga sama a buɗe, mala’ikun Allah kuma suna hawa suna kuma sauka a kan Ɗan Mutum.” A rana ta uku sai aka yi bikin aure a Kana ta Galili. Mahaifiyar Yesu kuwa tana can, aka gayyaci Yesu da almajiransa su ma a auren. Da ruwan inabi ya ƙare, sai mahaifiyar Yesu ta ce masa, “Ba su da sauran ruwan inabi.” Yesu ya ce, “Mace, me ya sa kike haɗa ni a wannan? Lokacina bai yi ba tukuna.” Sai mahaifiyarsa ta ce wa bayin, “Ku yi duk abin da ya faɗa.” Nan kusa kuwa akwai tulunan ruwa shida na dutse a ajiye, irin da Yahudawa suke amfani da su don tsarkakewa bisa ga al’ada, kowace kan ci gallon kusan ashirin zuwa talatin. Sai Yesu ya ce wa bayin, “Ku ciccika tulunan da ruwa.” Suka kuwa ciccika su fal. Sa’an nan ya ce musu, “Yanzu ku ɗiba ku kai wa uban bikin.” Suka yi haka. Uban bikin kuwa ya ɗanɗana ruwan da aka juya ya zama ruwan inabi. Bai san daga ina ya fito ba, ko da yake bayin da suka ɗiba ruwan sun sani. Sai ya kira angon waje ɗaya ya ce, “Kowa yakan kawo ruwan inabi mafi kyau da fari, sa’an nan marar kyan bayan baƙin sun sha da yawa; amma ka ajiye ruwan inabi mafi kyau sai yanzu.” Wannan shi ne na fari cikin abubuwan banmamakin da Yesu ya yi a Kana ta Galili. Ta haka ya bayyana ɗaukakarsa, almajiransa kuwa suka ba da gaskiya gare shi. Bayan wannan sai ya tafi Kafarnahum tare da mahaifiyarsa da ’yan’uwansa da kuma almajiransa. A can suka zauna ’yan kwanaki. Da lokacin Bikin Ƙetarewa na Yahudawa ya yi kusa, sai Yesu ya haura zuwa Urushalima. A filin haikali ya sami mutane suna sayar da shanu, tumaki da tattabaru, waɗansu kuma zaune a tebur suna canjin kuɗi. Saboda haka ya tuƙa bulala ta igiyoyi, ya kori duka daga filin haikali, har da tumaki da shanu; ya watsar da kuɗin masu canjin, ya birkice teburansu. Ga masu sayar da tattabaru kuwa ya ce, “Ku kwashe waɗannan daga nan! Don me za ku mai da gidan Ubana kasuwa!” Sai almajiransa suka tuna cewa a rubuce yake, “Himma saboda gidanka zai cinye ni.” Sai Yahudawa suka tambaye shi, “Wace abar banmamaki za ka nuna mana ka tabbatar mana ikonka na yin duk waɗannan?” Yesu ya amsa musu ya ce, “Ku rushe wannan haikali, zan kuwa sāke tā da shi cikin kwana uku.” Yahudawa suka ce, “Sai fa da aka shekara arba’in da shida ana ginin haikalin nan, kai kuwa a cikin kwana uku za ka tā da shi?” Amma haikalin da ya yi magana jikinsa ne. Bayan da ya tashi daga matattu, sai almajiransa suka tuna da abin da ya faɗa. Sa’an nan suka gaskata Nassi da kuma kalmomin da Yesu ya yi. To, yayinda yake a Urushalima a Bikin Ƙetarewa, mutane da yawa suka ga abubuwan banmamakin da yake aikata suka kuma gaskata da sunansa. Sai dai Yesu bai amince da su ba, don ya san dukan mutane. Ba ya bukatar shaidar mutum game da mutum, don yă san abin da yake cikin zuciyar mutum. Akwai wani Bafarisiye mai suna Nikodimus, wani ɗan majalisar Yahudawa. Ya zo wurin Yesu da dad dare ya ce, “Rabbi, mun sani kai malami ne daga Allah. Gama ba wanda zai iya yin waɗannan abubuwan banmamaki da kake yi in Allah ba ya tare da shi.” Yesu ya amsa ya ce, “Gaskiya nake faɗa maka, ba wanda zai iya ganin mulkin Allah sai an sāke haihuwarsa.” Nikodimus ya yi tambaya ya ce, “Yaya za a haifi mutum sa’ad da ya tsufa? Tabbatacce ba zai sāke koma sau na biyu a cikin mahaifiyarsa don a haife shi kuma ba!” Yesu ya amsa ya ce, “Gaskiya nake faɗa maka, ba wanda zai iya ganin mulkin Allah sai an haife shi ta wurin ruwa da kuma Ruhu. Jiki yakan haifi jiki, amma Ruhu yana haifi ruhu. Kada ka yi mamaki da na ce, ‘Dole ne a sāke haifarku.’ Iska takan hura zuwa inda take so. Kai kakan ji motsinta, sai dai ba ka iya sanin inda take fitowa ko kuwa inda za ta. Haka yake ga duk wanda aka haifa ta wurin Ruhu.” Nikodimus ya yi tambaya ya ce, “Yaya wannan zai yiwu?” Yesu ya ce, “Kai ma da kake malami na Isra’ila, ba ka fahimci waɗannan abubuwa ba? Gaskiya nake faɗa maka, muna magana a kan abin da muka sani, muka kuma shaida abin da muka gani ne, amma har yanzu kun ƙi ku karɓi shaidarmu. Na yi muku magana a kan abubuwan duniya amma ba ku gaskata ba; to, yaya za ku gaskata in na yi magana a kan abubuwan sama? Ba wanda ya taɓa hawa zuwa sama sai wanda ya sauka daga sama, wato, Ɗan Mutum. Kamar dai yadda Musa ya ɗaga maciji a hamada, haka dole ne a ɗaga Ɗan Mutum, don duk mai gaskata da shi ya sami rai madawwami.” Gama Allah ya ƙaunaci duniya sosai har ya ba da wanda yake Ɗaya kuma Makaɗaicin Ɗansa domin duk wanda ya gaskata da shi kada yă hallaka sai dai yă sami rai madawwami. Gama Allah bai aiki Ɗansa duniya don yă yi wa duniya hukunci ba, sai dai domin yă ceci duniya ta wurinsa. Duk wanda ya gaskata da shi ba za a yi masa hukunci ba, amma duk wanda bai gaskata ba an riga an yi masa hukunci domin bai gaskata da sunan wanda yake Ɗaya kuma Makaɗaicin Ɗan Allah ba. Hukuncin shi ne, Haske ya zo cikin duniya, amma mutane suka so duhu a maimakon haske domin ayyukansu mugaye ne. Duk mai aikata mugunta yana ƙin haske, ba zai kuwa zo cikin haske ba don yana tsoro kada ayyukansa su tonu. Amma duk mai rayuwa bisa ga gaskiya yakan zo cikin haske, domin a gani a sarari cewa ayyukan da ya yi an yi su ne ta wurin Allah. Bayan wannan, Yesu da almajiransa suka tafi ƙauyukan Yahudiya, inda ya ɗan jima da su, ya kuma yi baftisma. To, Yohanna ma yana yin baftisma a Ainon kusa da Salim, saboda akwai ruwa da yawa a can, mutane kuwa suka yi ta zuwa don a yi musu baftisma. (Wannan kuwa kafin a sa Yohanna a kurkuku.) Sai gardama ta tashi tsakanin waɗansu almajiran Yohanna da wani mutumin Yahuda a kan zancen al’adar tsarkakewa. Sai suka zo wurin Yohanna suka ce masa, “Rabbi, wancan mutumin da yake tare da kai a ƙetaren Urdun, wannan da ka ba da shaida a kansa sosai nan, yana baftisma, kuma kowa yana zuwa wurinsa.” Ga wannan zancen Yohanna ya amsa ya ce, “Mutum yakan karɓi kawai abin da aka ba shi ne daga sama. Ku kanku za ku shaida cewa na ce, ‘Ba ni ne Kiristi ba, sai dai an aiko ni ne in sha gabansa.’ Ango ne mai amarya. Abokin da yake masa hidima yakan jira ya kuma saurara masa, yakan kuma cika da farin ciki sa’ad da ya ji muryar ango. Wannan farin cikin kuwa nawa ne, ya kuma cika a yanzu. Dole ne yă yi ta ƙaruwa, ni kuma in yi ta raguwa. “Wannan da ya zo daga sama ya fi kowa; wannan da ya zo daga ƙasa na ƙasa ne, yana kuma magana kamar wanda ya zo daga ƙasa ne. Wannan da ya zo daga sama ya fi kowa. Yana ba da shaidar abin da ya gani da kuma ya ji, duk da haka ba wanda ya yarda da shaidarsa. Mutumin da ya yarda da ita ya tabbatar da cewa Allah mai gaskiya ne. Gama wannan da Allah ya aiko yakan faɗi kalmomin Allah ne, gama Allah yana ba da Ruhu babu iyaka. Uban yana ƙaunar Ɗan ya kuma danƙa kome a hannuwansa. Duk wanda ya gaskata da Ɗan yana da rai madawwami, amma duk wanda ya ƙi Ɗan ba zai sami rai ba, gama fushin Allah yana nan a bisansa.” Yesu ya ji labari cewa Yahudawa sun ji cewa ya wuce Yohanna samun masu bi, yana kuma yin musu baftisma, ko da yake ba Yesu ne yake baftismar ba, almajiransa ne. Da ya sami wannan labari, sai ya bar Yahudiya ya sāke koma Galili. To, ya zama dole yă bi ta Samariya. Sai ya zo wani gari a Samariya da ake ce da shi Saikar, kurkusa da filin da Yaƙub ya ba wa ɗansa Yusuf. Rijiyar Yaƙub kuwa tana can, Yesu kuwa, saboda gajiyar tafiya, sai ya zauna a bakin rijiyar. Wajen sa’a ta shida ne. Sa’ad da wata mutuniyar Samariya ta zo ɗiban ruwa, sai Yesu ya ce mata, “Ba ni ruwa in sha?” (Almajiransa kuwa sun shiga gari don sayi abinci.) Sai mutuniyar Samariyar ta ce masa, “Kai mutumin Yahuda ne, ni kuwa mutuniyar Samariya ce. Yaya za ka roƙe ni ruwan sha?” (Don Yahudawa ba sa hulɗa da Samariyawa.) Yesu ya amsa mata ya ce, “Da kin san kyautar Allah, da kuma wanda yake roƙonki ruwan sha, da kin roƙe shi, shi kuwa da ya ba ki ruwan rai.” Sai macen ta ce, “Ranka yă daɗe, ba ka da guga rijiyar kuwa tana da zurfi. Ina za ka sami wannan ruwan rai? Ka fi mahaifinmu Yaƙub ne, wanda ya ba mu rijiyar ya kuma sha daga ciki da kansa, haka ma ’ya’yansa da kuma garkunan shanunsa da tumakinsa?” Yesu ya amsa ya ce, “Kowa ya sha wannan ruwa, zai sāke jin ƙishirwa, amma duk wanda ya sha ruwan da zan ba shi, ba zai ƙara jin ƙishirwa ba. Tabbatacce, ruwan da zan ba shi, zai zama masa maɓuɓɓugan ruwa da yake ɓuɓɓugowa har yă zuwa rai madawwami.” Sai macen ta ce masa, “Ranka yă daɗe, ka ba ni ruwan nan, don kada in ƙara jin ƙishirwa, in yi ta zuwa nan ɗiban ruwa.” Sai ya ce mata, “Je ki zo da mijinki.” Sai ta amsa ta ce, “Ai, ba ni da miji.” Yesu ya ce mata, “Gaskiyarki da kika ce ba ki da miji. Gaskiyar ita ce, kin auri maza biyar, wanda kuke tare yanzu kuwa ba mijinki ba ne. A nan kam kin yi gaskiya.” Sai macen ta ce, “Ranka yă daɗe, ina gani kai annabi ne. Kakanninmu sun yi sujada a dutsen nan, amma ku Yahudawa kun ce a Urushalima ne ya kamata a yi sujada.” Sai Yesu ya ce, “Uwargida, ina tabbatar miki, lokaci yana zuwa da ba za ku yi wa Uba sujada ko a dutsen nan, ko kuwa a Urushalima ba. Ku Samariyawa ba ku san abin da kuke yi wa sujada ba; mu kuwa mun san abin da muke yi wa sujada, gama ceto daga Yahudawa yake. Duk da haka, lokaci yana zuwa har ma ya riga ya yi, da masu sujada na gaskiya za su yi wa Uba sujada a Ruhu da kuma gaskiya, gama irin waɗannan masu sujada ne Uba yake nema. Allah ruhu ne, masu yi masa sujada kuwa dole su yi masa sujada a ruhu, da gaskiya kuma.” Macen ta ce, “Na san cewa Almasihu” (da ake ce da shi Kiristi) “yana zuwa. Sa’ad da ya zo kuwa, zai bayyana mana kome.” Sai Yesu ya ce, “Ni mai maganan nan da ke, Ni ne shi.” Suna gama magana ke nan sai almajiransa suka iso, suka yi mamakin ganin yana magana da mace. Amma ba wanda ya ce, “Me kake so?” Ko “Me ya sa kake magana da ita?” Sai macen ta bar tulunta na ruwa, ta koma cikin gari ta ce wa mutane, “Ku zo, ku ga mutumin da ya gaya mini duk abin da na taɓa yi. Shin, ko shi ne Kiristi?” Sai suka fita daga garin suka nufa inda yake. Ana cikin haka, sai almajiransa suka roƙe shi suka ce, “Rabbi, ci abinci mana.” Amma ya ce musu, “Ina da abincin da ba ku san kome a kai ba.” Sai almajiran suka ce wa juna, “Shin, ko wani ya kawo masa abinci ne?” Yesu ya ce, “Abincina shi ne, in aikata nufin wannan da ya aiko ni, in kuma gama aikinsa. Ba kukan ce, ‘Sauran wata huɗu a yi girbi ba?’ Ina gaya muku, ku ɗaga idanu ku dubi gonaki! Sun isa girbi. Mai girbi na samun lada, yana kuma tara amfani zuwa rai madawwami, domin mai shuka da mai girbi su yi farin ciki tare. Karin maganan nan gaskiya ne cewa, ‘Wani da shuka, wani kuma da girbi.’ Na aike ku girbin abin da ba ku yi aikinsa ba. Waɗansu sun yi aikin nan mai wahala, ku kuwa kun sami ladan aikinsu.” Samariyawa da yawa daga wannan gari suka gaskata da shi saboda shaidar macen da ta ce, “Ya gaya mini duk abin da na taɓa yi.” To, da Samariyawa suka zo wurinsa, sai suka roƙe shi yă zauna da su, ya kuwa zauna kwana biyu. Saboda kalmominsa kuwa da yawa suka gaskata. Sai suka ce wa macen, “Yanzu kam mun gaskata, ba don abin da kika faɗa kawai ba; yanzu mun ji da kanmu, mun kuwa san cewa wannan mutum tabbatacce shi ne Mai Ceton duniya.” Bayan kwana biyun nan sai ya bar can zuwa Galili. (To, Yesu kansa ya taɓa faɗa cewa annabi ba shi da daraja a ƙasarsa.) Da ya isa Galili, sai mutanen Galili suka marabce shi. Sun ga duk abin da ya yi a Urushalima a lokacin Bikin Ƙetarewa, gama su ma sun kasance a can. Sai ya sāke ziyarci Kana ta Galili inda ya juya ruwa ya zama ruwan inabi. Akwai wani ma’aikacin hukuma a can wanda ɗansa yake kwance da rashin lafiya a Kafarnahum. Da mutumin nan ya ji cewa Yesu ya isa Galili daga Yahudiya, sai ya je wurinsa ya roƙe shi yă zo yă warkar da ɗansa da yake bakin mutuwa. Yesu ya ce masa, “Ku mutane, in ba kun ga alamu da abubuwan banmamaki ba, ba yadda za a yi ku ba da gaskiya.” Ma’aikacin hukuman ya ce, “Ranka yă daɗe, ka zo kafin ɗana yă mutu.” Sai Yesu ya amsa ya ce, “Ka tafi. Ɗanka zai rayu.” Mutumin kuwa ya amince da maganar da Yesu ya yi ya kuwa tafi. Tun yana kan hanya, bayinsa suka tarye shi da labari cewa yaron yana warkewa. Da ya tambayi lokacin da ɗansa ya sami sauƙi, sai suka ce masa, “Zazzaɓin ya sake shi jiya a sa’a ta bakwai.” Sai mahaifin ya gane a daidai wannan lokaci ne Yesu ya ce masa, “Ɗanka zai rayu.” Saboda haka shi da dukan iyalinsa suka gaskata. Wannan ce abin banmamaki ta biyu da Yesu ya yi, bayan zuwansa daga Yahudiya zuwa Galili. Bayan an ɗan jima, sai Yesu ya haura zuwa Urushalima don wani bikin Yahudawa. To, a Urushalima akwai wani tafki kusa da Ƙofar Tumaki, wanda a yaren Arameyik ake kira Betesda an kuma kewaye shi da shirayi biyar. A nan naƙasassu da yawa sukan kwanta, makafi, guragu, shanyayyu. Akwai wani da yake nan ba shi da amfani shekara talatin da takwas. Da Yesu ya gan shi kwance a can ya kuma sami labari cewa ya daɗe a wannan hali, sai ya tambaye shi, “Kana so ka warke?” Marar amfanin nan ya ce, “Ranka yă daɗe, ba ni da wanda zai taimaka yă sa ni a cikin tafkin sa’ad da aka motsa ruwan. Yayinda nake ƙoƙarin shiga, sai wani yă riga ni.” Sai Yesu ya ce masa, “Tashi! Ɗauki tabarmarka ka yi tafiya.” Nan take mutumin ya warke; ya ɗauki tabarmarsa ya yi tafiya. A ranar da wannan ya faru ranar Asabbaci ce, saboda haka kuwa Yahudawa suka ce wa mutumin da aka warkar, “Yau Asabbaci ne; doka ta hana ka ɗauki tabarmarka.” Amma ya amsa ya ce, “Mutumin da ya warkar da ni shi ya ce mini, ‘Ɗauki tabarmarka ka yi tafiya.’  ” Sai suka tambaye shi suka ce, “Wane ne wannan da ya ce maka ka ɗauke ta ka yi tafiya?” Mutumin da aka warkar kuwa bai ma san ko wane ne ba ne, gama Yesu ya ɓace cikin taron da yake can. Daga baya Yesu ya same shi a haikali ya ce masa, “Ga shi, ka warke. Ka daina yin zunubi, in ba haka ba wani abin da ya fi wannan muni zai iya samunka.” Sai mutumin ya je ya gaya wa Yahudawa cewa Yesu ne ya warkar da shi. To, domin Yesu yana yin waɗannan abubuwa a ranar Asabbaci, sai Yahudawa suka tsananta masa. Yesu ya ce musu, “Ubana yana cikin aikinsa kullum har yă zuwa wannan rana, haka ni ma, ina kan aiki.” Don haka Yahudawa suka ƙara nema su kashe shi; ba don yă karya Asabbaci kawai ba, har ma yana ce Allah Ubansa ne, yana mai da kansa daidai da Allah. Sai Yesu ya ba su wannan amsa cewa, “Gaskiya nake gaya muku, Ɗan ba ya iya yin kome da kansa; yana yin abin da ya ga Ubansa yake yi ne kawai, gama duk abin da Uban yake yi shi ne Ɗan ma yake yi. Gama Uban yana ƙaunar Ɗan yana kuma nuna masa duk abin da yake yi. I, za ku kuwa yi mamaki, gama zai nuna masa abubuwan da suka fi waɗannan girma. Gama kamar yadda Uban yake tā da matattu yake kuma ba su rai, haka ma Ɗan yake ba da rai ga wanda ya ga dama. Bugu da ƙari, Uban ba ya hukunta kowa, sai dai ya danƙa dukan hukunci a hannun Ɗan, don kowa yă girmama Ɗan kamar yadda yake girmama Uban. Wanda ba ya girmama Ɗan ba ya girmama Uban, da ya aiko shi ke nan. “Gaskiya nake gaya muku, duk wanda ya ji maganata ya kuma gaskata da wanda ya aiko ni yana da rai madawwami ba za a kuma hukunta shi ba; ya riga ya ƙetare daga mutuwa zuwa rai. Gaskiya nake gaya muku, lokaci yana zuwa har ma ya riga ya zo sa’ad da matattu za su ji muryar Ɗan Allah waɗanda kuwa suka ji za su rayu. Gama kamar yadda Uban yana da rai a cikinsa, haka ya sa Ɗan yă kasance da rai a cikin kansa. Ya kuma ba shi iko yă hukunta domin shi Ɗan Mutum ne. “Kada ku yi mamakin wannan, gama lokaci yana zuwa da duk waɗanda suke cikin kaburbura za su ji muryarsa su kuma fito, waɗanda suka aikata nagarta za su tashi zuwa ga rai, waɗanda kuma suka aikata mugunta za su tashi zuwa ga hukunci. Ni kaɗai dai ba na iya yin kome, ina shari’a ne bisa ga abin da na ji. Shari’ata kuwa mai adalci ce. Gama ba na neman gamsar da kaina, sai dai in gamshi shi wanda ya aiko ni. “In na ba da shaida a kaina, shaidata ba gaskiya ba ce. Akwai wani mai ba da shaida mai kyau a kaina, na kuma san cewa shaidarsa game da ni gaskiya ce. “Kun aika wajen Yohanna ya kuma yi shaida a kan gaskiya. Ba cewa ina neman shaidar mutum ba ne; sai dai na faɗi haka ne domin ku sami ceto. Yohanna fitila ne da ya ci ya kuma ba da haske, kun kuwa zaɓa ku ji daɗin haskensa na ɗan lokaci. “Ina da shaidar da ta fi ta Yohanna ƙarfi. Gama aikin nan da Uba ya ba ni in kammala, wanda kuwa nake yi, yana ba da shaida cewa Uba ne ya aiko ni. Uba da ya aiko ni kuwa kansa ya yi shaida game da ni. Ba ku taɓa jin muryarsa ko ganin siffarsa ba, maganarsa kuwa ba ta zama a cikinku, gama ba ku gaskata da wanda ya aiko ni ba. Kuna ta nazarin Nassosi da himma don kuna tsammani ta wurinsu ne kuna samun rai madawwami. Nassosin nan ne suke ba da shaida a kaina, duk da haka kun ƙi zuwa wurina domin ku sami rai. “Ni ba na neman yabon mutane, na fa san ku. Na san cewa ba ku da ƙaunar Allah a cikin zukatanku. Na zo a cikin sunan Ubana, ba ku kuwa karɓe ni ba; amma a ce wani dabam ya zo a cikin sunan kansa, za ku karɓe shi. Ta yaya za ku gaskata in kuna neman yabon junanku, ba kwa kuwa yin ƙoƙarin neman yabon da yake zuwa daga Allah Makaɗaici? “Kada fa ku yi tsammani zan yi ƙararku wurin Uba. Akwai mai yin ƙararku, shi ne Musa, wanda kuke dogara da shi. Da a ce kun gaskata da Musa, da kun gaskata ni, domin ya rubuta game da ni. Amma da yake ba ku gaskata abin da ya rubuta ba, yaya za ku gaskata maganata?” Ɗan lokaci bayan wannan, sai Yesu ya ƙetare zuwa gaɓar mai nesa na Tekun Galili (wato, Tekun Tibariya), sai taro mai yawa na mutane suka bi shi domin sun ga abubuwan banmamakin da ya yi ga marasa lafiya. Sa’an nan Yesu ya hau gefen dutse ya zauna tare da almajiransa. Bikin Ƙetarewan Yahudawa ya yi kusa. Sa’ad da Yesu ya ɗaga kai ya ga taro mai yawa suna zuwa wajensa, sai ya ce wa Filibus, “Ina za mu sayi burodi saboda mutanen nan su ci?” Ya yi wannan tambayar don yă gwada shi ne kawai, gama ya riga ya san abin da zai yi. Sai Filibus ya amsa ya ce, “Kai, ko albashin wata takwas ba zai iya sayan isashen burodin da kowa zai ɗan samu kaɗan ba!” Sai wani daga cikin almajiransa Andarawus, ɗan’uwan Bitrus, ya yi magana, “Ga wani yaro da ƙananan burodin sha’ir guda biyar da ƙananan kifi biyu, amma me wannan zai yi wa yawan mutanen nan.” Yesu ya ce, “Ku sa mutanen su zauna.” Wurin kuwa akwai ciyawa da sosai, sai maza suka zazzauna, sun kai wajen dubu biyar. Sa’an nan Yesu ya ɗauki burodin, ya yi godiya, ya kuma rarraba wa waɗanda suke zaune gwargwadon abin da ya ishe su. Haka kuma ya yi da kifin. Sa’ad da duk suka ci suka ƙoshi, sai ya ce wa almajiransa, “Ku tattara gutsattsarin da suka rage. Kada kome yă lalace.” Saboda haka suka tattara su suka kuma cika kwanduna goma sha biyu na gutsattsarin burodin sha’ir biyar nan da suka ragu bayan kowa ya ci. Bayan mutanen suka ga abin banmamakin da Yesu ya yi, sai suka fara cewa, “Lalle, wannan shi ne Annabin nan mai zuwa duniya.” Da Yesu ya gane suna shirin su ɗauke shi ƙarfi da yaji su naɗa shi sarki, sai ya sāke komawa kan dutsen shi kaɗai. Da yamma ta yi, sai almajiransa suka gangara zuwa tafki, inda suka shiga jirgin ruwa suka tasar wa haye tafkin zuwa Kafarnahum. A lokacin kuwa duhu ya yi, Yesu kuma bai riga ya zo wurinsu ba tukuna. Iska mai ƙarfi kuwa tana bugowa, ruwaye kuma suka fara hauka. Bayan sun yi tuƙi wajen mil uku ko uku da rabi, sai suka ga Yesu ya kusato jirgin ruwan, yana takawa a kan ruwan; sai suka tsorata. Amma ya ce musu, “Ni ne; kada ku ji tsoro.” Sa’an nan suka yarda suka karɓe shi a cikin jirgin ruwan, nan da nan kuwa jirgin ya kai gaɓar da za su. Kashegari taron da suka tsaya a wancan ƙetaren tafkin suka lura cewa jirgin ruwa ɗaya ne yake a can dā ma, kuma sun lura cewa Yesu bai shiga ciki tare da almajiransa ba, gama sun tashi su kaɗai. Sai ga waɗansu jiragen ruwa daga Tibariya suka iso kusa da wurin da mutanen suka ci burodi bayan Ubangiji ya yi godiya. Da taron suka lura cewa Yesu da almajiransa ba sa can, sai suka shiga jiragen ruwa suka tafi Kafarnahum neman Yesu. Da suka same shi a wancan ƙetaren tafkin, sai suka tambaye shi suka ce, “Rabbi, yaushe ka kai nan?” Yesu ya amsa ya ce, “Gaskiya nake gaya muku, kuna nemana ne ba don kun ga abubuwan banmamaki ba, sai dai domin kun ci burodi kun ƙoshi. Kada ku yi aiki saboda abincin da yake lalacewa, sai dai saboda abinci mai dawwama har yă zuwa rai madawwami, wanda Ɗan Mutum zai ba ku. A kansa ne Allah Uba ya sa hatimin amincewarsa.” Sai suka tambaye shi suka ce, “Me za mu yi don mu aikata ayyukan da Allah yake so?” Yesu ya amsa, “Aikin Allah shi ne, a gaskata da wanda ya aiko.” Sai suka tambaye shi, “Wace abin banmamaki ce za ka yi don mu gani mu kuwa gaskata ka? Me za ka yi? Kakannin-kakanninmu sun ci Manna a hamada; kamar yadda yake a rubuce, ‘Ya ba su burodi daga sama su ci.’ ” Yesu ya ce musu, “Gaskiya nake gaya muku, ba Musa ne ya ba ku burodi daga sama ba, sai dai Ubana ne yake ba ku burodi na gaskiya daga sama. Gama burodin Allah shi ne wanda yake saukowa daga sama, yana kuma ba wa duniya rai.” Sai suka ce, “Ranka yă daɗe, daga yanzu ka dinga ba mu wannan burodi.” Sa’an nan Yesu ya furta cewa, “Ni ne burodin rai. Wanda ya zo wurina ba zai taɓa jin yunwa ba, wanda kuma ya gaskata da ni ba zai taɓa jin ƙishirwa ba. Amma kamar yadda na faɗa muku, kun gan ni duk da haka ba ku gaskata ba. Duk waɗanda Uba ya ba ni za su zo wurina, kuma duk wanda ya zo wurina ba zan kore shi ba ko kaɗan. Gama na sauko daga sama ba don in cika nufin kaina ba sai dai don in cika nufin shi wanda ya aiko ni. Nufin wanda ya aiko ni kuwa shi ne, kada in yar da ko ɗaya daga cikin duk waɗanda ya ba ni, sai dai in tashe su a rana ta ƙarshe. Gama nufin Ubana shi ne, duk wanda yake duban Ɗan, ya kuma gaskata shi zai sami rai madawwami, ni kuwa zan tashe shi a rana ta ƙarshe.” Da jin haka, Yahudawa suka fara gunaguni a kansa, domin ya ce, “Ni ne burodin da ya sauka daga sama.” Suka ce, “Kai, wannan ba Yesu ba ne, ɗan Yusuf, wanda mahaifinsa da mahaifiyarsa duk mun san su? Yaya yanzu zai ce, ‘Na sauko daga sama?’ ” Sai Yesu ya amsa ya ce, “Ku daina gunaguni a junanku. Ba mai iya zuwa wurina, sai dai in Uban da ya aiko ni ya jawo shi, ni kuwa zan tashe shi a rana ta ƙarshe. A rubuce yake a cikin Annabawa cewa, ‘Allah zai koyar da dukansu.’ Duk wanda ya saurari Uba, ya kuma koyi daga wurinsa, zai zo wurina. Ba wanda ya taɓa ganin Uban, sai shi wanda ya zo daga Allah; shi ne kaɗai ya taɓa ganin Uban. Gaskiya nake gaya muku, wanda ya gaskata yana da rai madawwami. Ni ne burodin rai. Kakannin-kakanninku sun ci Manna a hamada, duk da haka suka mutu. Amma ga burodin da ya sauko daga sama, wanda mutum zai iya ci, ba zai kuma mutu ba. Ni ne burodin rai mai saukowa daga sama. Duk wanda ya ci wannan burodi, zai rayu har abada. Wannan burodin shi ne jikina, da zan bayar don duniya ta sami rai.” Sai Yahudawa suka fara gardama mai tsanani a junansu suna cewa, “Yaya wannan mutum zai ba mu naman jikinsa mu ci?” Sai Yesu ya ce musu, “Gaskiya nake gaya muku, sai kun ci naman jikin Ɗan Mutum kuka kuma sha jininsa, ba za ku kasance da rai a cikinku ba. Duk wanda ya ci naman jikina ya kuma sha jinina, yana da rai madawwami. Ni kuwa zan tashe shi a rana ta ƙarshe. Gama naman jikina abinci ne na gaskiya jinina kuma abin sha ne na gaskiya. Duk wanda ya ci naman jikina ya kuma sha jinina, yana cikina, ni kuma ina cikinsa. Kamar dai yadda Uba mai rai ya aiko ni, ina kuma rayuwa ta saboda shi, haka ma wanda yake ni ne abincinsa zai rayu saboda ni. Wannan shi ne burodin da ya sauko daga sama. Kakannin-kakanninku sun ci Manna suka kuma mutu, amma duk wanda yake cin wannan burodi zai rayu har abada.” Ya faɗi wannan ne lokacin da yake koyarwa a cikin majami’a a Kafarnahum. Da jin haka, da yawa daga cikin almajiransa suka ce, “Wannan koyarwa tana da wuya. Wa zai iya yarda da ita?” Da yake ya san almajiransa suna gunaguni game da wannan, sai Yesu ya ce musu, “Wannan ya ɓata muku rai ne? Me za ku ce ke nan, in kuka gan Ɗan Mutum yana hawa zuwa inda yake dā! Ruhu ne yake ba da rai; jikin kam, ba ya amfana kome. Kalmomin da na faɗa muku, Ruhu ne, da kuma rai. Duk da haka akwai waɗansunku da ba su gaskata ba.” Gama Yesu ya sani tun farko, waɗanda ba su gaskata ba, da kuma wanda zai bashe shi. Ya ci gaba da cewa, “Shi ya sa na faɗa muku cewa ba mai iya zuwa wurina, sai dai Uba ya yardar masa.” Daga wannan lokaci da yawa daga cikin almajiransa suka ja da baya, suka daina bin sa. Sai Yesu ya tambayi Sha Biyun, “Ku ma za ku tafi ne?” Sai Siman Bitrus ya amsa ya ce, “Ubangiji wajen wa za mu tafi? Kai ne da kalmomin rai madawwami. Mun gaskata mun kuma san cewa kai ne Mai Tsarkin nan na Allah.” Sai Yesu ya amsa ya ce, “Ba ni na zaɓe ku Sha Biyu ba? Amma ɗayanku Iblis ne!” (Yana nufin Yahuda, ɗan Siman Iskariyot, wanda, ko da yake ɗaya ne cikin Sha Biyun, zai bashe shi daga baya.) Bayan wannan, sai Yesu ya yi ta zagawa a cikin Galili, da ganga bai yarda yă je Yahudiya ba domin Yahudawa a can suna nema su kashe shi. Amma sa’ad da Bikin Tabanakul na Yahudawa ya yi kusa, sai ’yan’uwan Yesu suka ce masa, “Ya kamata ka bar nan ka tafi Yahudiya, don almajiranka su ga ayyukan banmamaki da kake yi. Ba wanda yake so a san shi da zai yi abu a ɓoye. Da yake kana yin waɗannan abubuwa, sai ka nuna kanka ga duniya.” Domin ko ’yan’uwansa ma ba su gaskata da shi ba. Saboda haka Yesu ya ce musu, “Lokacina bai yi ba tukuna; amma a gare ku kowane lokaci daidai ne. Duniya ba za tă iya ƙinku ba, amma ni take ƙi domin ina shaida cewa ayyukanta mugaye ne. Ku ku tafi Bikin, ba zan haura zuwa wannan Bikin ba yanzu, domin lokacina bai yi ba tukuna.” Da ya faɗa haka, sai ya dakata a Galili. Amma fa, bayan ’yan’uwansa suka tafi Bikin, shi ma ya tafi, ba a fili ba, amma a ɓoye. A Bikin kuwa, Yahudawa suka yi ta nemansa, suna cewa, “Ina mutumin yake?” A cikin taron kuwa aka yi ta raɗe-raɗe game da shi. Waɗansu suka ce, “Shi mutumin kirki ne.” Waɗansu kuwa suka ce, “A’a, ai, ruɗin mutane yake.” Amma ba wanda ya ce kome a fili game da shi don tsoron Yahudawa. Sai bayan da aka kai tsakiyar Bikin, sa’an nan Yesu ya haura zuwa filin haikali ya fara koyarwa. Yahudawa suka yi mamaki suna tambaya, “Yaya wannan mutum ya sami wannan sani haka ba tare da ya yi wani karatu ba?” Yesu ya amsa ya ce, “Koyarwata ba tawa ba ce, ta fito ne daga wurin wanda ya aiko ni. Duk wanda ya zaɓi yin nufin Allah, zai gane ko koyarwata daga Allah ce, ko kuwa don kaina ne nake magana. Mai magana don kansa, neman ɗaukakar kansa yake yi. Amma mai neman ɗaukakar wanda ya aiko shi, shi ne mai gaskiya, ba kuwa rashin gaskiya a gare shi. Ashe, ba Musa ba ne ya ba ku Doka? Duk da haka ba ko ɗayanku da yake kiyaye Dokar. Me ya sa kuke nema ku kashe ni?” Taron suka amsa suka ce, “Kana da aljani, wane ne yake so yă kashe ka?” Yesu ya ce musu, “Na yi abin banmamaki ɗaya, dukanku kuwa kuka yi mamaki. Duk da haka, domin Musa ya bar muku kaciya (ko da yake a gaskiya, ba daga wurin Musa ne ya fito ba, sai dai daga wurin kakannin kakanninku), ga shi kuna yin wa yaro kaciya a ranar Asabbaci. To, in za a iya yin wa yaro kaciya a ranar Asabbaci don kada a karya dokar Musa, don me kuke fushi da ni saboda na warkar da mutum a ranar Asabbaci? Ku daina yin shari’a bisa ga ganin ido, sai dai ku yi shari’a bisa ga adalci.” A nan ne fa waɗansu mutane daga Urushalima suka fara tambaya suna cewa, “Ashe, ba wannan mutum ne suke nema su kashe ba? Ga shi nan yana magana a fili, su kuma ba su ce masa uffam ba. Ko hukumomi sun yarda cewa shi ne Kiristi? Mun dai san inda mutumin nan ya fito; amma sa’ad da Kiristi ya zo ba wanda zai san inda ya fito.” Yesu yana cikin koyarwa a filin haikali ke nan, sai ya ɗaga murya ya ce, “I, kun san ni, kun kuma san inda na fito. Ban zo don kaina ba, sai dai shi da ya aiko ni mai gaskiya ne. Ba ku san shi ba, amma na san shi, domin ni daga wurinsa ne, kuma shi ya aiko ni.” Da jin haka, sai suka yi ƙoƙari su kama shi, sai dai ba wanda ya taɓa shi, don lokacinsa bai yi ba tukuna. Duk da haka, da yawa a cikin taron suka ba da gaskiya gare shi. Suka ce, “Sa’ad da Kiristi ya zo, zai yi abubuwan banmamaki fiye da na wannan mutum ne?” Farisiyawa suka ji taron suna raɗe-raɗen waɗannan abubuwa game da shi. Sai manyan firistoci da Farisiyawa suka aiki masu gadin haikalin su kama shi. Sai Yesu ya ce, “Ina tare da ku na ɗan ƙanƙanin lokaci ne kawai, sa’an nan zan koma wurin wanda ya aiko ni. Za ku neme ni, amma ba za ku same ni ba; inda nake kuwa, ba za ku iya zuwa ba.” Sai Yahudawa suka ce wa juna, “Ina mutumin nan yake niyyar tafiya da ba za mu iya samunsa ba? Zai je wurin mutanenmu da suke zaune warwatse a cikin Hellenawa, yă kuma koya wa Hellenawa ne? Me yake nufi da ya ce, ‘Za ku neme ni, amma ba za ku same ni ba,’ da kuma ‘Inda nake, ba za ku iya zuwa ba’?” A rana ta ƙarshe kuma mafi girma ta Bikin, Yesu ya tsaya ya yi magana da babbar murya ya ce, “Duk mai jin ƙishirwa, yă zo wurina yă sha. Duk wanda ya gaskata da ni, kamar yadda Nassi ya ce, kogunan ruwa masu rai za su gudana daga cikinsa.” Da wannan yana nufin Ruhu ke nan, wanda waɗanda suka gaskata da shi za su karɓa daga baya. Har yă zuwa wannan lokaci ba a ba da Ruhu ba tukuna, da yake ba a riga an ɗaukaka Yesu ba. Da jin kalmominsa, waɗansu mutane suka ce, “Ba shakka, mutumin nan shi ne Annabin.” Waɗansu suka ce, “Shi ne Kiristi.” Waɗansu har wa yau suka ce, “Yaya Kiristi zai fito daga Galili? Nassi bai ce Kiristi zai fito daga zuriyar Dawuda, daga kuma Betlehem garin da Dawuda ya zauna ba?” Sai mutanen suka rabu saboda Yesu. Waɗansu suka so su kama shi, sai dai ba wanda ya taɓa shi. A ƙarshe masu gadin haikali suka koma wurin manyan firistocin da Farisiyawa, waɗanda suka tambaye su cewa, “Don me ba ku kawo shi nan ba?” Sai masu gadin suka ce, “Kai, babu wanda ya taɓa magana kamar wannan mutum.” Sai Farisiyawa suka amsa cikin fushi suka ce, “Af, kuna nufi har da ku ma ya ruɗe ku ke nan? Akwai wani daga cikin masu mulki ko cikin Farisiyawan da ya gaskata da shi? A’a! Sai dai wannan taron da ba su san kome game da Doka ba, la’anannu ne.” Nikodimus, wanda ya je wurin Yesu dā, wanda kuma yake ɗayansu ya ce, “Ashe, dokarmu takan hukunta mutum ba tare da an fara ji daga bakinsa game da abin da yake yi ba?” Sai suka amsa suka ce, “Kai ma daga Galili ne? Bincika ka gani, za ka iske cewa ba annabin da zai fito daga Galili.” [Rubuce-rubucen farko-farko da kuma mafi ingancin da aka fi dogara da su tare da waɗansu shaidu na dā ba su da Yoh 7.53–8.11. Kaɗan daga cikin rubuce-rubucen hannu na dā sun ƙunshi waɗannan ayoyi, ko gaba ɗayansu ko kuma sashensu kawai bayan Yoh 7.36, Yoh 21.25, Luk 21.38 ko kuwa Luk 24.53.] Sai kowannensu ya koma gidansa. Amma Yesu ya tafi Dutsen Zaitun. Da sassafe ya sāke bayyana a filin haikali, inda dukan mutane suka taru kewaye da shi, sai ya zauna don yă koya musu. Sai malaman dokoki da Farisiyawa suka kawo wata macen da aka kama a zina. Suka sa ta tsaya a gaban taron suka kuma ce wa Yesu, “Malam, an kama wannan mace tana zina. A cikin Doka Musa ya umarce mu, mu jajjefe irin waɗannan mata. To, me ka ce?” Sun yi wannan tambaya ce don su sa masa tarko, don su sami hanyar zarge shi. Amma Yesu ya sunkuya ya fara rubutu a ƙasa da yatsarsa. Da suka ci gaba da yin masa tambayoyi, sai ya miƙe tsaye ya ce musu, “In da wani a cikinku da ba shi da zunubi, sai yă fara jifanta da dutse.” Sai ya sāke sunkuyawa ya kuma yi rubutu a ƙasa. Da jin haka, waɗanda suka ji sai suka fara tashi daga wurin ɗaya-ɗaya, tun daga babbansu har ya zuwa ƙaraminsu, sai da aka bar Yesu kaɗai, tare da macen tsaye a wurin. Sai Yesu ya miƙe tsaye ya tambaye ta ya ce, “Mace, ina suke? Ba wanda ya hukunta ki?” Ta ce, “Ba kowa, ranka yă daɗe.” Sai Yesu ya ce, “Haka ni ma ban hukunta ki ba. Ki tafi, ki daina rayuwar zunubi.” Sa’ad da Yesu ya sāke magana da mutanen, sai ya ce, “Ni ne hasken duniya. Duk wanda ya bi ni ba zai yi tafiya cikin duhu ba, sai dai yă sami hasken rayuwa.” Sai Farisiyawa suka tambaye shi suka ce, “Ga kai dai, kana yi wa kanka shaida, shaidarka kuwa ba tabbatacciya ba ce.” Sai Yesu ya amsa ya ce, “Ko na shaidi kaina, ai, shaidata tabbatacciya ce, gama na san inda na fito da kuma inda za ni. Amma ku ba ku san inda na fito ko inda za ni ba. Kuna shari’a bisa ga ma’aunin mutane; ni kuwa ba na yin wa kowa shari’a. Amma ko da zan yi shari’a, shari’ata daidai ce, don ba ni kaɗai ba ne. Ina tare da Uba da ya aiko ni. A cikin Dokarku a rubuce yake cewa shaidar mutum biyu tabbatacciya ce. Ni ne nake shaidar kaina, Uba da ya aiko ni kuma yana shaidata.” Suka tambaye shi suka ce, “Ina Uban nan naka?” Sai Yesu ya ce, “Ba ku san ni ko Ubana ba. Da kun san ni, da za ku san Ubana ma.” Ya faɗi waɗannan kalmomi ne yayinda yake koyarwa a filin haikali, kusa da inda ake ajiye baye-baye. Duk da haka ba wanda ya kama shi, domin lokacinsa bai yi ba tukuna. Har wa yau Yesu ya sāke ce musu, “Zan tafi, za ku kuwa neme ni, za ku kuma mutu cikin zunubinku. Inda za ni, ba za ku iya zuwa ba.” Wannan ya sa Yahudawa suka yi tambaya suka ce, “Zai kashe kansa ne? Shi ya sa yake cewa, ‘Inda za ni, ba za ku iya zuwa ba’?” Amma ya ci gaba da cewa, “Ku daga ƙasa kuke; ni kuwa daga bisa ne. Ku na duniyan nan ne; ni kuwa ba na duniyan nan ba ne. Na gaya muku cewa za ku mutu cikin zunubanku; in ba ku gaskata cewa ni ne wanda na ce nake ba, lalle za ku mutu cikin zunubanku.” Suka ce, “Wane ne kai?” Sai Yesu ya amsa ya ce, “Ni ne wannan da na sha faɗi muku. Ina da abubuwa masu yawa da zan faɗa game ku in kuma yi muku shari’a. Amma wanda ya aiko ni mai aminci ne, abin da kuma na ji daga gare shi, shi nake gaya wa duniya.” Ba su gane cewa yana yin musu magana game da Ubansa ba ne. Saboda haka Yesu ya ce, “Sa’ad da kuka ɗaga Ɗan Mutum, a sa’an nan ne za ku san cewa ni ne wannan da na ce nake. Ni kuwa ba na yin kome ni kaɗai, sai in dai faɗi abin da Uba ya koya mini. Wanda kuwa ya aiko ni yana tare da ni; bai bar ni ni kaɗai ba, domin kullum ina aikata abin da ya gamshe shi.” Sa’ad da yake cikin magana, da yawa suka ba da gaskiya gare shi. Sai Yesu ya ce wa Yahudawan da suka gaskata da shi, “In dai kun riƙe koyarwata, ku almajiraina ne da gaske. Sa’an nan za ku san gaskiya, gaskiyar kuwa za tă ’yantar da ku.” Sai suka amsa masa suka ce, “Ai, mu zuriyar Ibrahim ne kuma ba mu taɓa bauta wa kowa ba. Yaya za ka ce za a ’yantar da mu?” Yesu ya amsa ya ce, “Gaskiya nake gaya muku, duk mai yin zunubi bawan zunubi ne. Bawa dai ba shi da wurin zama na ɗinɗinɗin a cikin iyali, amma ɗa na gida ne har abada. Saboda haka in Ɗan ya ’yantar da ku, za ku ’yantu da gaske. Na dai san ku zuriyar Ibrahim ne. Duk da haka kuna shiri ku kashe ni, don maganata ba ta da wurin zama a cikinku. Ina faɗi muku abin da na gani a wurin Ubana, ku kuwa kuna yin abin da kuka ji daga wurin ubanku.” Suka ce, “To, ai, Ibrahim ne mahaifinmu.” Yesu ya ce, “Da ku ’ya’yan Ibrahim ne, da za ku aikata abubuwan da Ibrahim ya yi. Ga shi kun ƙudura, sai kun kashe ni, ni mutumin da ya faɗa muku gaskiyar da na ji daga Allah. Ibrahim bai yi irin waɗannan abubuwa ba. Kuna yin abubuwan da ubanku yake yi ne.” Suka ce, “Mu fa ba shegu ba ne. Uba guda kaɗai da muke da shi, shi ne Allah kansa.” Yesu ya ce musu, “Da Allah ne Ubanku, da kun ƙaunace ni, gama daga Allah na fito yanzu kuma ga ni nan. Ban zo saboda kaina ba, amma shi ne ya aiko ni. Me ya sa ba kwa gane da maganata? Don ba kwa iya jin abin da nake faɗi. Ku na ubanku ne, Iblis, kuna kuwa so ku aikata abin da ubanku yake so. Shi mai kisankai ne tun farko. Ba ruwansa da gaskiya, gama gaskiya ba ta cikinsa. Yayinda yake ƙarya, yana yin halinsa ne, gama shi maƙaryaci ne, uban ƙarairayi kuma. Amma domin ina faɗin gaskiya, ba kwa gaskata! Akwai waninku da zai iya haƙaƙƙewa na taɓa yin zunubi? In kuwa gaskiya na faɗa, me ya sa ba kwa gaskata ni? Wanda yake na Allah, yakan ji abin da Allah yake faɗi. Abin da ya sa ba kwa jin sa kuwa shi ne don ku ba na Allah ba ne.” Yahudawa suka amsa masa suka ce, “Aha, ai, gaskiyarmu da muka ce kai mutumin Samariya ne, kana kuma da aljani.” Yesu ya ce, “Ni ba mai aljani ba ne, ni dai ina girmama Ubana, ku kuwa ba kwa girmama ni. Ba na nema wa kaina ɗaukaka, amma akwai wani wanda yake neman mini, shi ne kuma alƙali. Gaskiya nake gaya muku, duk wanda ya kiyaye maganata, ba zai ɗanɗana mutuwa ba sam.” Da jin haka Yahudawa suka ce, “Tabɗi, yanzu kam mun san kana da aljani! Ibrahim ya mutu haka ma annabawa, ga shi kana cewa duk wanda ya kiyaye maganarka ba zai ɗanɗana mutuwa ba sam. Ka fi Ibrahim mahaifinmu ne? Ya mutu, haka ma annabawa. Wa kake ɗauka kanka ne?” Yesu ya amsa ya ce, “In ma na ɗaukaka kaina, ɗaukakata ba kome ba ce. Ubana, wanda kuke cewa shi ne Allahnku, shi ne wanda yake ɗaukaka ni. Ko da yake ba ku san shi ba, ni dai na san shi. In kuwa na ce ban san shi ba, na zama maƙaryaci kamar ku ke nan, amma na san shi, kuma ina kiyaye maganarsa. Mahaifinku Ibrahim ya yi farin ciki sosai yă sami ganin ranata; ya kuwa gan ta, ya yi murna.” Sai Yahudawa suka ce masa, “Kai, shekarunka har yanzu ba su kai hamsin tukuna ba fa, har ka ga Ibrahim!” Yesu ya amsa ya ce, “Gaskiya nake gaya muku, tun ba a haifi Ibrahim ba, ni ne!” Da jin haka sai suka ɗebo duwatsu don su jajjefe shi, amma Yesu ya ɓuya, ya fita daga filin haikali. Da Yesu yana tafiya, sai ya ga wani mutum wanda aka haifa makaho. Sai almajiransa suka tambaye shi suka ce, “Rabbi, wane ne ya yi zunubi, mutumin ne, ko iyayensa, da ya sa aka haife shi makaho?” Sai Yesu ya ce, “Ba don mutumin ko iyayensa sun yi zunubi ne ba, sai dai don a bayyana aikin Allah ne a rayuwarsa. Muddin da sauran rana, dole mu yi aikin wanda ya aiko ni. Dare yana zuwa, sa’ad da ba wanda zai iya yin aiki. Yayinda ina a cikin duniya, ni ne hasken duniya.” Bayan ya faɗi haka, sai ya tofa miyau a ƙasa, ya kwaɓa laka da miyau ɗin, ya kuma shafa a idanun mutumin. Ya ce masa, “Je ka, ka wanke a Tafkin Silowam” (kalman nan tana nufin “Aikakke”). Saboda haka mutumin ya tafi ya wanke, ya kuma dawo gida yana gani. Maƙwabta da waɗanda suka saba ganinsa dā yana bara, suka ce, “Kai, ba wannan mutum ne ya saba zama yana bara ba?” Waɗansu suka ce shi mana. Waɗansu kuwa suka ce, “A’a, ya dai yi kama da shi.” Amma shi ɗin ya ce, “Ƙwarai kuwa ni ne.” Sai suka ce, “To, yaya aka yi idanunka suka buɗe?” Ya amsa ya ce, “Mutumin da ake kira Yesu ne ya kwaɓa laka ya shafa mini a idanu. Ya ce mini in je Silowam in wanke. Na kuwa tafi, na wanke, sai na sami ganin gari.” Suka tambaye shi suka ce, “Ina mutumin yake?” Ya ce, “Ban sani ba.” Sai suka kawo mutumin da dā yake makaho wurin Farisiyawa. To, a ranar da Yesu ya kwaɓa laka ya buɗe idanun mutumin ranar Asabbaci ce. Saboda haka Farisiyawa suka tambaye shi yadda ya sami ganin gari. Mutumin ya amsa, “Ya shafa laka a idanuna, sai na wanke, ina kuwa gani.” Sai waɗansu daga cikin Farisiyawa suka ce, “Mutumin nan ba daga Allah yake ba, don ba ya kiyaye ranar Asabbaci.” Amma waɗansu suka yi tambaya suka ce, “Yaya mutum mai zunubi zai yi irin abubuwan banmamaki haka?” Sai ra’ayinsu ya sha bamban. A ƙarshe suka sāke koma ga makahon suka ce, “Kai fa, me ka gani game da shi? Idanunka ne fa ya buɗe.” Sai mutumin ya ce, “Tab, ai, shi annabi ne.” Yahudawa dai ba su yarda cewa dā shi makaho ne ya kuma sami ganin gari ba, sai da suka kira iyayen mutumin. Suka tambaye su, “Wannan ɗanku ne? Shi ne wanda kuka ce an haife shi makaho? To, ta yaya yake gani yanzu?” Iyayen suka amsa suka ce, “Mun dai san shi ɗanmu ne, mun kuma san cewa an haife shi makaho. Sai dai yadda yake gani yanzu, ko kuma wa ya buɗe idanunsa, ba mu sani ba. Ku tambaye shi. Ai, shi ba yaro ba ne, zai faɗa da bakinsa.” Iyayensa sun faɗa haka ne saboda suna tsoron Yahudawa, gama Yahudawa sun riga sun yanke shawara cewa duk wanda ya yarda cewa Yesu shi ne Kiristi, za a kore shi daga majami’a. Shi ya sa iyayensa suka ce, “Ai, shi ba yaro ba ne, ku tambaye shi.” Sai suka sāke kiran mutumin nan da yake makaho a dā, suka ce masa, “Ka ɗaukaka Allah, mu kam, mun san mutumin nan mai zunubi ne.” Sai ya amsa ya ce, “Ko shi mai zunubi ne ko babu, ni dai ban sani ba. Abu ɗaya fa na sani, dā ni makaho ne, amma yanzu ina gani!” Sai suka tambaye suka ce, “Shin, me ya yi maka? Ta yaya ya buɗe idanunka?” Ya amsa ya ce, “Na riga na gaya muku ba ku kuwa saurara ba. Don me kuke so ku sāke ji? Ko ku ma kuna so ku zama almajiransa ne?” Sai suka hau shi da zagi suna cewa, “Kai ne dai almajirin mutumin! Mu almajiran Musa ne! Mun dai san cewa Allah ya yi magana da Musa, amma wannan mutum ba mu san inda ya fito ba.” Sai mutumin ya ce, “Cabɗi, yau ga abin mamaki! Ba ku san inda ya fito ba, ga shi kuwa ya buɗe idanuna. Mun san cewa Allah ba ya sauraron masu zunubi. Yakan saurari mai tsoronsa mai aikata nufinsa. Ba wanda ya taɓa ji cewa an buɗe idanun wanda aka haifa makaho. Da mutumin nan ba daga Allah ba ne, da ba abin da zai iya yi.” Sai suka amsa suka ce, “Kai da aka haifa cike da zunubi; za ka yi karambanin koyarwar da mu!” Sai suka kore shi. Yesu ya ji labari cewa sun kore shi, da ya same shi kuwa, sai ya ce, “Ka gaskata da Ɗan Mutum?” Sai mutumin ya amsa ya ce, “Ranka yă daɗe, wane ne shi? Gaya mini, don in gaskata da shi.” Yesu ya ce, “Yanzu ka gan shi; tabbatacce ma, shi ne yake magana da kai.” Sai mutumin ya ce, “Ubangiji, na gaskata,” ya kuma yi masa sujada. Yesu ya ce, “Saboda shari’a ce na zo duniya nan, saboda makafi su sami ganin gari, waɗanda suke gani kuma su makance.” Da Farisiyawan da suke tare da shi suka ji ya faɗi haka sai suka yi tambaya suka ce, “Mene? Mu ma makafi ne?” Yesu ya ce, “Ai, da ku makafi ne ma, da ba ku da zunubi, amma da yake kun ce, kuna gani, zunubanku suna nan daram. “Gaskiya nake gaya muku, mutumin da bai shiga inda ake ajiye garken tumaki ta ƙofa ba, amma ya hau ta katanga, ɓarawo ne, ɗan fashi kuma. Mutumin da ya shiga ta ƙofa makiyayin tumakinsa ne. Mai gadin yakan buɗe wa makiyayin ƙofa, tumakin kuma sukan saurari muryarsa. Yakan kira tumakinsa da suna, yă kuma fid da su waje. Sa’ad da ya fitar da dukan nasa waje, sai ya ja gabansu, tumakinsa kuma sukan bi shi domin sun san muryarsa. Amma ba za su taɓa bin baƙo ba; sai dai ma su guje masa don ba su san muryar baƙo ba.” Yesu ya yi musu wannan misali, amma ba su fahimci abin da yake faɗa musu ba. Saboda haka Yesu ya sāke cewa, “Gaskiya nake gaya muku, ni ne ƙofar tumakin. Duk waɗanda suka riga ni zuwa ɓarayi ne, ’yan fashi kuma, amma tumakin ba su saurare su ba. Ni ne ƙofar; duk wanda ya shiga ta wurina zai sami ceto. Zai riƙa shiga yă fita yă kuwa sami wurin kiwo. Ɓarawo yakan zo don yă yi sata ne kawai da kisa da kuma ɓarna. Ni kuwa na zo ne don su sami rai, su kuma same shi a yalwace. “Ni ne makiyayi mai kyau. Makiyayi mai kyau yakan ba da ransa domin tumakin. Wanda aka ɗauko haya ba shi ne makiyayi mai tumakin ba. Saboda haka sa’ad da ya ga kyarkeci yana zuwa, sai yă sheƙa da gudu yă bar tumakin. Sai kyarkecin yă kai wa garken hari, yă kuma watsar da su. Mutumin yakan gudu don shi ɗan haya ne kawai, bai kuwa damu da tumakin ba. “Ni ne makiyayi mai kyau; na san tumakina, tumakina kuma sun san ni, kamar yadda Uba ya san ni, ni kuma na san Uba, ina kuwa ba da raina domin tumakin. Ina da waɗansu tumaki da ba na wannan garken ba ne. Dole ne in kawo su su ma. Za su saurari muryata, za su kasance garke guda ɗaya, makiyayi guda kuma. Abin da ya sa Ubana yake ƙaunata ke nan, domin ina ba da raina, in ɗauko shi kuma. Ba mai karɓe mini rai, ina dai ba da shi. Ina da iko in ba da shi, ina da iko in ɗauko shi kuma. Wannan umarni kuwa daga wurin Ubana na karɓo shi.” Saboda waɗannan kalmomi fa, sai ɓaraka ta sāke shiga cikin Yahudawa. Da yawa daga cikinsu suka ce, “Yana da aljani, yana kuma hauka. Don me za ku saurare shi?” Amma waɗansu suka ce, “Kai, waɗannan kalmomi ba na mai aljani ba ne. Anya, aljani yana iya buɗe idanun makaho?” Bikin Miƙawa a Urushalima ya kewayo, lokacin sanyin hunturu ne kuwa. Sai ga Yesu a filin haikali yana zagawa a Shirayin Solomon, sai Yahudawa suka taru kewaye da shi, suka ce masa, “Har yaushe za ka bar mu da shakka? In kai ne Kiristin, ka faɗa mana a fili mana.” Yesu ya amsa ya ce, “Na faɗa muku, amma ba ku gaskata ba. Ayyukan da nake yi cikin sunan Ubana su suke nuna ko wane ne ni. Amma ba ku gaskata ba domin ku ba tumakina ba ne. Tumakina sukan saurari muryata; na sansu, suna kuma bi na. Ina ba su rai madawwami, ba za su taɓa hallaka ba; ba kuma mai ƙwace su daga hannuna. Ubana, wanda ya ba ni su, ya fi duka girma, ba mai ƙwace su daga hannun Ubana. Da ni da Uba ɗaya ne.” Sai Yahudawa suka sāke ɗebo duwatsu don su jajjefe shi, amma Yesu ya ce musu, “Na nuna muku ayyukan alheri masu yawa da Uba ya aiko ni in yi, a kan wanne kuke so ku jajjefe ni?” Yahudawa suka amsa suka ce, “Ai, ba don wani daga cikin waɗannan ayyukan alheri ne muke so mu jajjefe ka ba, amma don saɓon da kake yi, kai da kake mutum kawai, kana mai da kanka Allah.” Yesu ya amsa musu ya ce, “Ba a rubuce yake a cikin Dokarku ba cewa, ‘Na ce ku alloli ne’? Mun dai san Nassi ba ya ƙarya, In har ya kira su waɗanda maganar Allah ta zo musu, ‘alloli,’ to, game da wanda Uba ya keɓe a matsayin nasa ne ya kuma aiko shi duniya. Don me kuke ce saɓo nake, domin na ce, ‘Ni Ɗan Allah ne?’ In ba ayyukan da Ubana yake yi ne nake yi ba, to, kada ku gaskata ni. Amma in su nake yi, ko ba ku gaskata ni ba, to, ku gaskata ayyukan, don ku sani, ku kuma gane, Uban yana cikina, ni kuma ina cikin Uban.” Sai suka sāke yin ƙoƙari su kama shi, amma ya kuɓuce musu. Sa’an nan Yesu ya sāke koma ƙetaren Urdun inda dā Yohanna yake baftisma. A can ya zauna mutane da yawa suka zo wurinsa. Suka ce, “Ko da yake Yohanna bai yi wani abin banmamaki ba, duk abubuwan da Yohanna ya faɗa game da mutumin nan gaskiya ne.” A nan kuwa mutane da yawa suka gaskata da Yesu. To, an yi wani mutum mai suna Lazarus wanda ya yi rashin lafiya. Shi daga Betani ne, ƙauyen su Maryamu da ’yar’uwarta Marta. Maryamun nan kuwa, wadda ɗan’uwanta Lazarus yake rashin lafiya, ita ce ta zuba wa Ubangiji turare ta kuma goge ƙafafunsa da gashin kanta. Saboda haka ’yan’uwansa mata suka aika da saƙo wa Yesu cewa, “Ubangiji, wannan da kake ƙauna yana rashin lafiya.” Sa’ad da ya ji haka, sai Yesu ya ce, “Wannan rashin lafiya ba zai kai ga mutuwa ba. A’a, sai dai don a ɗaukaka Allah a kuma ɗaukaka Ɗan Allah ta wurin wannan.” Yesu kuwa yana ƙaunar Marta da ’yar’uwarta da kuma Lazarus. Duk da haka sa’ad da ya ji Lazarus ba shi da lafiya, sai ya ƙara kwana biyu a inda yake. Sai ya ce wa almajiransa, “Mu koma Yahudiya.” Sai suka ce, “Rabbi, ba da daɗewa ba ne Yahudawa suka nemi su jajjefe ka, duk da haka za ka koma can?” Yesu ya amsa ya ce, “Ba sa’a goma sha biyu ce yini guda ba? Mutumin da yake tafiya da rana ba zai yi tuntuɓe ba gama yana ganin hasken duniyan nan. Sai a sa’ad da yake tafiya da dare ne zai yi tuntuɓe, don ba shi da haske.” Bayan ya faɗa haka, sai ya ƙara ce musu, “Abokinmu Lazarus ya yi barci, amma za ni in tashe shi.” Almajiransa suka ce, “Ubangiji, in barci ne yake, to, ai, zai sami sauƙi.” Yesu kuwa yana magana mutuwarsa ce, amma almajiransa suka ɗauka yana nufin barcin gaskiya ne. Saboda haka sai ya gaya musu a fili cewa, “Lazarus ya mutu, amma saboda ku na yi farin ciki da ba na can, domin ku gaskata. Amma mu dai je wurinsa.” Sai Toma (wanda ake kira Didaimus) ya ce wa sauran almajiran, “Mu ma mu je, mu mutu tare da shi.” Da isowarsa, Yesu ya tarar Lazarus ya riga ya yi kwana huɗu a kabari. Betani bai kai mil biyu ba daga Urushalima, Yahudawa da yawa kuwa suka zo wurin Marta da Maryamu don su yi musu ta’aziyya, saboda rasuwar ɗan’uwansu. Sa’ad da Marta ta ji cewa Yesu yana zuwa, sai ta fita don ta tarye shi, amma Maryamu ta zauna a gida. Sai Marta ta ce wa Yesu, “Ubangiji, da kana nan da ɗan’uwana bai mutu ba. Amma na san cewa ko yanzu ma Allah zai ba ka duk abin da ka roƙa.” Yesu ya ce mata, “Ɗan’uwanki zai sāke tashi.” Marta ta amsa ta ce, “Na sani zai sāke tashi a tashin matattu a rana ta ƙarshe.” Yesu ya ce mata, “Ni ne tashin matattu da kuma rai. Duk wanda ya gaskata da ni zai rayu, ko ya mutu; kuma duk wanda yake raye ya kuma gaskata da ni ba zai taɓa mutuwa ba. Kin gaskata wannan?” Sai ta ce masa, “I, Ubangiji, na gaskata kai ne Kiristi, Ɗan Allah, mai zuwa cikin duniya.” Bayan ta faɗa haka kuwa, sai ta koma ta je ta kira ’yar’uwarta Maryamu a gefe. Ta ce, “Ga Malam ya zo, kuma yana kiranki.” Sa’ad da Maryamu ta ji haka sai ta yi wuf ta tafi wurinsa. Yesu dai bai riga ya shiga ƙauyen ba tukuna, har yanzu yana inda Marta ta tarye shi. Da Yahudawan da suke tare da Maryamu a cikin gida, suke mata ta’aziyya, suka ga ta yi wuf ta fita, sai suka bi ta, suna tsammani za tă kabarin ne tă yi kuka a can. Sa’ad da Maryamu ta kai inda Yesu yake, ta kuma gan shi, sai ta fāɗi a gabansa ta ce, “Ubangiji, da kana nan, da ɗan’uwana bai mutu ba.” Da Yesu ya ga tana kuka, Yahudawan da suka zo tare da ita ma suna kuka, sai ya yi juyayi ƙwarai a ruhu ya kuma damu. Sai ya yi tambaya ya ce, “Ina kuka sa shi?” Suka amsa suka ce, “Ubangiji zo ka gani.” Yesu ya yi kuka. Sai Yahudawa suka ce, “Dubi yadda yake ƙaunarsa!” Amma waɗansunsu suka ce, “Anya, wanda ya buɗe wa makahon nan idanu, ba zai iya yin wani abu yă hana wannan mutum mutuwa ba?” Yesu, har yanzu cike da juyayi, ya zo kabarin. Kogo ne da aka rufe bakin da dutse. Sai Yesu ya ce, “Ku kawar da dutsen.” Marta, ’yar’uwan mamacin ta ce, “Ubangiji, yanzu, ai, zai yi wari, don yau kwanansa huɗu ke nan a can.” Sai Yesu ya ce, “Ban gaya miki cewa in kin gaskata za ki ga ɗaukakar Allah ba?” Saboda haka suka kawar da dutsen. Sa’an nan Yesu ya dubi sama ya ce, “Uba, na gode maka da ka saurare ni. Na san kullum kakan saurare ni, na dai faɗa haka ne saboda amfanin mutanen nan da suke tsaitsaye, don su gaskata cewa kai ka aiko ni.” Sa’ad da ya faɗa haka, sai Yesu ya yi kira da babbar murya ya ce, “Lazarus, ka fito!” Sai mamacin ya fito, hannuwansa da ƙafafunsa a daure da ƙyallayen lilin, fuskarsa kuwa an naɗe da mayafi. Yesu ya ce musu, “Ku tuɓe kayan bizo, ku bar shi yă tafi.” Saboda haka Yahudawa da yawa da suka zo don su ziyarci Maryamu, suka kuma ga abin da Yesu ya yi, suka ba da gaskiya gare shi. Amma waɗansunsu suka je wurin Farisiyawa suka gaya musu abin da Yesu ya yi. Sai manyan firistoci da Farisiyawa suka kira taron Majalisa. Suka yi tambaya suna cewa, “Me muke yi ne? Ga mutumin nan yana yin abubuwan banmamaki masu yawa. In fa muka ƙyale shi ya ci gaba da haka, kowa zai gaskata da shi, Romawa kuma su zo su karɓe wurinmu su kuma ƙwace ƙasarmu.” Sai waninsu, mai suna Kayifas, wanda ya kasance babban firist a shekarar ya ce, “Ku dai ba ku san kome ba! Ba ku gane ba, ai, gwamma mutum ɗaya yă mutu saboda mutane da duk ƙasar ta hallaka.” Bai faɗa haka bisa nufinsa ba, sai dai a matsayinsa na babban firist a shekarar, ya yi annabci ne cewa Yesu zai mutu saboda ƙasar Yahudawa, ba don ƙasan nan kaɗai ba amma don yă tattaro ’ya’yan Allah da suke warwatse ma, su zama ɗaya. Saboda haka, daga wannan rana suka ƙulla su ɗauke ransa. Saboda haka Yesu bai ƙara tafiya a cikin Yahudawa a sarari ba. A maimako haka sai ya janye zuwa yankin kusa da hamada, a wani ƙauye da ake kira Efraim, inda ya zauna da almajiransa. Sa’ad da lokaci ya yi kusa a yi Bikin Ƙetarewa na Yahudawa, da yawa suka haura daga ƙauyuka zuwa Urushalima, don su tsarkake kansu kafin Bikin Ƙetarewa. Suka yi ta neman Yesu, da suke a tsaitsaye a filin haikali kuwa suka dinga tambayar juna, suna cewa, “Me kuka gani? Anya, zai zo Bikin kuwa?” Manyan firistoci da Farisiyawa tuni sun riga sun yi umarni cewa duk wanda ya san inda Yesu yake, yă faɗa don su kama shi. Kwana shida kafin Bikin Ƙetarewa, sai Yesu ya iso Betani, inda Lazarus yake, wanda Yesu ya tā da daga matattu. A nan aka shirya abincin yamma don girmama Yesu. Marta ta ce yi hidima, Lazarus kuma yana ɗaya cikin waɗanda suke ci tare shi. Sai Maryamu ta ɗauki wajen awo guda na nardi zalla, turare mai tsada; ta zuba a ƙafafun Yesu ta kuma goge ƙafafunsa da gashinta. Gidan duk ya cika da ƙanshin turaren. Amma ɗaya daga cikin almajiransa, Yahuda Iskariyot, wanda daga baya zai bashe shi, bai amince ba ya ce, “Don me ba a sayar da turaren nan aka kuma ba da kuɗin ga matalauta ba? Ai, kuɗin ya kai albashin shekara guda.” Ya yi wannan magana ba don ya kula da matalauta ba ne, sai dai don shi ɓarawo ne. Da yake shi ne mai ajiya jakar kuɗin, yakan taimaki kansa da abin da aka sa a ciki. Yesu ya ce, “Ku ƙyale ta, an nufa ta ajiye wannan turaren don ranar jana’izata. Kullum za ku kasance da matalauta, amma ba kullum za ku kasance tare da ni ba.” Ana cikin haka sai babban taron Yahudawa suka sami labari Yesu yana can suka kuwa zo, ba kawai don shi ba amma don su kuma ga Lazarus, wanda ya tā da daga matattu. Saboda haka manyan firistoci suka ƙulla su kashe Lazarus shi ma, gama dalilinsa Yahudawa da yawa suna komawa ga Yesu suna kuma ba da gaskiya gare shi. Kashegari babban taron da suka zo Bikin suka sami labari cewa Yesu yana kan hanyarsa zuwa Urushalima. Sai suka ɗaɗɗauko rassan dabino suka fiffita taryensa, suna ɗaga murya suna cewa, “Hosanna!” “Mai albarka ne wanda yake zuwa cikin sunan Ubangiji!” “Mai albarka ne Sarkin Isra’ila!” Yesu ya sami ɗan jaki, ya hau, kamar yadda yake a rubuce cewa, “Kada ki ji tsoro, ya Diyar Sihiyona; duba, ga sarkinki yana zuwa, zaune a kan aholaki jaki.” Da fari almajiransa ba su gane dukan wannan ba. Sai bayan da aka ɗaukaka Yesu, sa’an nan suka gane cewa an rubuta waɗannan abubuwa game da shi ne, har ma suka yi masa waɗannan abubuwa. Taron da suke tare da shi a sa’ad da ya kira Lazarus daga kabari ya kuma tā da shi daga matattu suka yi ta baza labarin. Mutane da yawa kuwa suka fita taryensa, saboda sun ji labarin abin banmamakin da ya yi. Saboda haka Farisiyawa suka ce wa juna, “Duba, wannan ba ya kai mu ko’ina. Ga shi, duk duniya tana bin sa!” To, akwai waɗansu Hellenawa a cikin waɗanda suka haura don su yi sujada a Bikin. Suka zo wurin Filibus, wanda yake daga Betsaida ta Galili, da roƙo. Suka ce, “Ranka yă daɗe, muna so mu ga Yesu.” Sai Filibus ya je ya gaya wa Andarawus, Andarawus da kuma Filibus suka gaya wa Yesu. Yesu ya amsa ya ce, “Lokaci ya yi da za a ɗaukaka Ɗan Mutum. Gaskiya nake gaya muku, sai ƙwayar alkama ta fāɗi ƙasa ta mutu, in ba haka ba za tă kasance ƙwaya ɗaya tak. Amma in ta mutu, za tă ba da ’ya’ya da yawa. Duk mai ƙaunar ransa, zai rasa shi, duk mai ƙin ransa a wannan duniya, zai kiyaye shi har yă zuwa rai madawwami. Duk wanda zai bauta mini dole yă bi ni, inda kuma nake, a can bawana zai kasance. Ubana zai girmama wanda yake bauta mini. “Yanzu kuwa na damu, amma me zan ce? ‘Uba, ka cece ni daga wannan sa’a’? A’a, ai, saboda wannan dalili ne musamman na zo. Uba, ka ɗaukaka sunanka!” Sai wata murya ta fito daga sama ta ce, “Na riga na ɗaukaka shi, zan kuma ƙara ɗaukaka shi.” Taron da suke a wurin suka ji, suka ce an yi tsawa; waɗansu kuwa suka ce mala’ika ne ya yi masa magana. Yesu ya ce, “An yi wannan muryar saboda amfaninku ne, ba don nawa ba. Yanzu ne za a yi wa duniyan nan shari’a, yanzu ne za a tumɓuke mai mulkin duniyan nan. Amma ni, sa’ad da aka ɗaga ni daga ƙasa, zan ja dukan mutane gare ni.” Ya faɗa haka ne don yă nuna irin mutuwar da zai yi. Sai taron suka ce, “Ahab, Dokarmu ta gaya mana cewa, Kiristi zai kasance har abada, to, yaya za ka ce, ‘Dole ne a ɗaga Ɗan Mutum?’ Wane ne wannan ‘Ɗan Mutum’?” Sai Yesu ya ce musu, “Haske zai kasance da ku na ɗan lokaci. Ku yi tafiya yayinda hasken yana nan tare da ku, kada duhu yă cim muku. Mai tafiya a cikin duhu bai san inda za shi ba. Ku dogara ga hasken yayinda kuke da shi, don ku zama ’ya’yan haske.” Da Yesu ya gama magana, sai ya tafi ya ɓuya daga gare su. Ko bayan Yesu ya yi dukan waɗannan abubuwan banmamaki a gabansu, duk da haka ba su gaskata da shi ba. Wannan ya faru ne, don a cika maganar annabi Ishaya cewa, “Ubangiji, wa ya gaskata saƙonmu, ga wa kuma aka bayyana hannun ikon Ubangiji?” Saboda haka ba su iya gaskatawa ba, domin, kamar yadda Ishaya ya faɗa a wani wuri cewa, “Ya makantar da idanunsu ya kuma taurare zukatansu, don kada su gani da idanunsu, ko su fahimta a zukatansu, ko kuwa su juyo, har in warkar da su.” Ishaya ya faɗi haka ne, saboda ya hangi ɗaukakar Yesu, ya kuwa yi magana a kansa. Duk da haka, da yawa har daga cikin shugabanni ma suka gaskata da shi. Amma saboda Farisiyawa ba su furta bangaskiyarsu ba, don tsoron kada a kore su daga majami’a; gama sun fi son yabon mutane, fiye da yabon Allah. Sa’an nan Yesu ya ɗaga murya ya ce, “Duk wanda ya gaskata da ni, ba ni yake gaskatawa ba, amma ga wanda ya aiko ni ne. Duk mai dubana, yana duban wanda ya aiko ni ne. Na zo cikin duniya a kan ni haske ne, don duk wanda ya gaskata da ni, kada yă zauna a cikin duhu. “Duk mai jin kalmomina bai kuwa kiyaye su ba, ba ni ba ne nake shari’anta shi. Gama ban zo domin in yi wa duniya shari’a ba, sai dai domin in cece ta. Akwai mai hukunci saboda wanda ya ƙi ni, bai kuma karɓi kalmomina ba; wannan maganar da na faɗa ita ce za tă hukunta shi a rana ta ƙarshe. Gama ba don kaina na yi magana ba, Uban da ya aiko ni shi kansa ne ya ba ni umarni a kan abin da zan faɗa da kuma yadda zan faɗe shi. Na san cewa umarninsa yana kai ga rai madawwami. Saboda haka duk abin da na faɗa na faɗe shi ne kamar dai yadda Uba ya ce in faɗa.” Ana gab da Bikin Ƙetarewa. Yesu kuwa ya san cewa lokaci ya yi da zai bar wannan duniya, yă koma wurin Uba. Da yake ya ƙaunaci waɗanda suke nasa a duniya, yanzu kuwa ya nuna musu cikakkiyar ƙaunarsa. Ana cikin cin abincin yamma, Iblis kuwa ya riga ya zuga Yahuda Iskariyot, ɗan Siman yă bashe Yesu. Yesu kuwa ya san cewa, Uba ya sa dukan abubuwa a ƙarƙashin ikonsa, ya kuma san cewa daga Allah ya zo, zai kuma koma wurin Allah; saboda haka ya tashi daga cin abincin, ya tuɓe rigarsa ta waje, ya ɗaura tawul a ƙugunsa. Bayan haka, sai ya zuba ruwa a cikin kwano, sa’an nan ya fara wanke ƙafafun almajiransa, yana sharewa da tawul wanda ya ɗaura. Ya zo kan Siman Bitrus, wanda ya ce masa, “Ubangiji, kai za ka wanke ƙafafuna?” Yesu ya amsa ya ce, “Yanzu ba ka fahimci abin da nake yi ba, amma nan gaba za ka gane.” Sai Bitrus ya ce, “Faufau, ba za ka taɓa wanke ƙafafuna ba.” Yesu ya amsa ya ce, “Sai na wanke ka, in ba haka ba, ba ka da rabo a gare ni.” Sai Siman Bitrus ya ce, “To, Ubangiji, ba ƙafafuna kaɗai ba har ma da hannuwana da kaina kuma!” Yesu ya amsa ya ce, “Wanda ya riga ya yi wanka yana bukata yă wanke ƙafafunsa ne kawai; dukan jikinsa yana da tsabta. Ku kuwa kuna da tsabta, ko da yake ba kowannenku ba.” Gama ya san wanda zai bashe shi, shi ya sa ya ce, “Ba kowa ba ne yake da tsabta.” Da ya gama wanke ƙafafunsu, sai ya sa tufafinsa ya koma wurin zamansa. Ya tambaye su ya ce, “Kun fahimci abin da na yi muku? Kuna ce da ni ‘Malam’ da kuma ‘Ubangiji,’ daidai ne kuwa, gama haka nake. Da yake ni da nake Ubangijinku da kuma Malaminku, na wanke ƙafafunku, haka ku ma ya kamata ku wanke ƙafafun juna. Na ba ku misali domin ku yi yadda na yi muku. Gaskiya nake gaya muku, ba bawan da ya fi maigidansa, ko ɗan saƙon da ya fi wanda ya aike shi. Yanzu da kuka san waɗannan abubuwa, ku masu albarka ne, in kuka yi su. “Ba dukanku nake nufi ba; na san waɗanda na zaɓa. Wannan kuwa don a cika Nassi ne da ya ce, ‘Wanda ya ci burodina tare da ni ya tasar mini.’ “Ina faɗa muku yanzu tun kafin yă faru, domin in ya faru, ku gaskata cewa ni ne Shi. Gaskiya nake gaya muku, ‘Duk wanda ya karɓi wani da na aiko, ni ne ya karɓa ke nan. Kuma duk wanda ya karɓe ni, ya karɓi wanda ya aiko ni ne.’ ” Bayan Yesu ya faɗi haka, sai ya yi juyayi a ruhu, ya kuma furta cewa, “Gaskiya nake gaya muku, ɗayanku zai bashe ni.” Almajiransa suka dubi juna, suka rasa ko da wa yake. Ɗaya daga cikin almajiran Yesu wanda yake ƙauna kuwa, yana zaune kusa da shi. Sai Siman Bitrus ya taɓa wannan almajirin ya ce, “Tambaye shi, wa yake nufi?” Shi kuwa da yake jingine kusa da Yesu, ya ce, “Ubangiji, wane ne?” Yesu ya amsa ya ce, “Shi ne wanda zan ba shi gutsurin burodin nan sa’ad da na tsoma cikin kwanon.” Da ya tsoma gutsurin burodin, sai ya ba wa Yahuda Iskariyot, ɗan Siman. Nan take bayan Yahuda ya karɓi burodin, sai Shaiɗan ya shige shi. Sai Yesu ya ce masa, “Abin nan da kake niyyar yi, ka yi shi maza.” Amma ba wani a wurin cin abincin da ya fahimci dalilin da ya sa Yesu ya faɗa masa haka. Da yake Yahuda ne ma’aji, waɗansunsu suka ɗauka Yesu yana ce masa yă sayi abin da ake bukata don Bikin ne, ko kuwa yă ba wa matalauta wani abu. Nan da nan da Yahuda ya karɓi burodin, sai ya fita. A lokacin kuwa dare ya yi. Da ya tafi, sai Yesu ya ce, “Yanzu ne aka ɗaukaka Ɗan Mutum aka kuma ɗaukaka Allah a cikinsa. In kuwa Allah ya sami ɗaukaka a cikin Ɗan, Allah kuwa zai ɗaukaka Ɗan zuwa ga zatinsa, zai kuma ɗaukaka shi nan take. “’Ya’yana, zan kasance da ku na ɗan ƙanƙani lokaci ne. Za ku neme ni. Kuma kamar yadda na gaya wa Yahudawa, haka nake gaya muku yanzu. Inda zan tafi, ba za ku iya zuwa ba. “Sabon umarni nake ba ku. Ku ƙaunaci juna. Kamar yadda na ƙaunace ku, ku ma ku ƙaunaci juna. Ta haka kowa zai san cewa ku almajiraina ne, in kuna ƙaunar juna.” Siman Bitrus ya tambaye shi ya ce, “Ubangiji ina za ka?” Yesu ya amsa ya ce, “Wurin da za ni, ba za ka iya zuwa yanzu ba, amma za ka bi ni daga baya.” Bitrus ya ce masa, “Ubangiji, don me ba zan binka yanzu ba? Zan ba da raina saboda kai.” Sai Yesu ya amsa ya ce, “Anya, za ka iya ba da ranka saboda ni? Gaskiya nake faɗa maka, kafin zakara yă yi cara, za ka yi mūsun sanina sau uku! “Kada zuciyarku ta ɓaci. Ku gaskata da Allah, ku kuma gaskata da ni. A cikin gidan Ubana akwai wurin zama da yawa; da a ce ba haka ba ne, da na gaya muku. Za ni can don in shirya muku wuri. In kuwa na tafi na shirya muku wuri, sai in dawo in ɗauke ku ku kasance tare da ni don ku kasance inda nake. Ai, kun san hanyar zuwa inda za ni.” Sai Toma ya ce masa, “Ubangiji, ba mu san inda za ka ba, to, ta yaya za mu san hanyar?” Yesu ya amsa ya ce, “Ni ne hanya, ni ne gaskiya, ni ne kuma rai. Ba mai zuwa wurin Uba sai dai ta wurina. Da kun san ni, da za ku san Ubana ma. Daga yanzu, kun san shi kun kuma gan shi.” Filibus ya ce, “Ubangiji, ka nuna mana Uban, wannan kuwa zai biya bukatarmu.” Yesu ya amsa ya ce, “Ba san ni ba, Filibus, duk da daɗewan nan da na yi tare da ku? Duk wanda ya gan ni, ai, ya ga Uban. Yaya za ka ce, ‘Ka nuna mana Uban’? Ba ka gaskata cewa ina cikin Uba, Uba kuma yana cikina ba? Kalmomin da nake gaya muku ba na kaina ba ne. Ai, Uban da yake raye a cikina ne yake aikinsa. Ku gaskata ni sa’ad da na ce ina cikin Uba, Uba kuma yana cikina. Ko kuwa ku gaskata ni saboda ayyukan banmamakin su kansu. Gaskiya nake gaya muku, duk wanda yake da bangaskiya gare ni, zai yi abubuwan da ni nake yi. Zai ma yi abubuwa masu girma fiye da waɗannan, don zan tafi wurin Uba. Kuma zan yi duk abin da kuka roƙa cikin sunana, don Ɗan ya kawo ɗaukaka ga Uban. Za ku iya roƙe ni kome a cikin sunana, zan kuwa yi. “In kuna ƙaunata za ku yi biyayya da umarnina. Zan kuwa roƙi Uba, zai kuwa ba ku wani Mai Taimakon da zai kasance tare da ku har abada, Ruhun gaskiya. Duniya ba ta iya karɓarsa, don ba ta ganinsa ba ta kuma san shi ba. Amma kun san shi, saboda yana zama tare da ku zai kuma kasance a cikinku. Ba zan bar ku marayu ba; zan zo wurinku. Ba da daɗewa ba, duniya ba za tă ƙara ganina ba, amma za ku gan ni. Don ina raye, ku ma za ku rayu. A ranan nan za ku sani ina cikin Uba, ku kuma kuna cikina, ni kuma ina cikinku. Duk wanda yake da umarnaina yana kuma yin biyayya da su, shi ne wanda yake ƙaunata. Wanda yake ƙaunata kuwa Ubana zai ƙaunace shi, ni ma zan ƙaunace shi, in kuma bayyana kaina gare shi.” Sai Yahuda (ba Yahuda Iskariyot ba) ya ce, “Ubangiji, me ya sa za ka bayyana kanka gare mu amma ba ga duniya ba?” Yesu ya amsa ya ce, “Duk mai ƙaunata, zai yi biyayya da koyarwata. Ubana zai ƙaunace shi, za mu kuwa zo wurinsa mu zauna tare da shi. Wanda ba ya ƙaunata ba zai yi biyayya da koyarwata ba. Waɗannan kalmomin da kuke ji ba nawa ba ne; na Uba ne da ya aiko ni. “Duk wannan na faɗa ne yayinda ina tare da ku. Amma Mai Taimako, Ruhu Mai Tsarki, wanda Uba zai aiko cikin sunana, zai koya muku kome, zai kuma tuna muku duk abin da na faɗa muku. Salama na bari tare da ku; salamata nake ba ku. Ba kamar yadda duniya take bayarwa nake ba ku ba. Kada zuciyarku ta ɓaci kada kuma ku ji tsoro. “Kun dai ji na ce, ‘Zan tafi in kuma sāke dawo wurinku.’ In har kuna ƙaunata, za ku yi farin ciki cewa za ni wurin Uba, domin kuwa Uban ya fi ni. Na faɗa muku tun kafin yă faru, domin in ya faru, ku gaskata. Ba zan ƙara yi muku magana ba, gama mai mulkin duniyan nan yana zuwa. Ba shi da iko a kaina, amma dole duniya ta koya cewa ina ƙaunar Uba, ina kuma yin yadda Ubana ya umarce ni. “Ku zo, mu bar nan. “Ni ne kuringar inabi na gaskiya, Ubana kuwa shi ne manomin. Yakan sare kowane reshe a cikina da ba ya ’ya’ya, amma yakan ƙundume kowane reshe da yake ba da ’ya’ya, domin yă ƙara ba da ’ya’ya. Kun riga kun zama masu tsabta saboda maganar da na yi muku. Ku kasance a cikina, ni kuma zan kasance a cikinku. Babu reshen da zai iya yin ’ya’ya da kansa, dole yă kasance a jikin kuringar inabin. Haka ku ma, ba za ku iya ba da ’ya’ya ba sai kun kasance a cikina. “Ni ne kuringar inabin; ku ne kuma rassan. In mutum ya kasance a cikina ni kuma a cikinsa, zai ba da ’ya’ya da yawa; in ba tare da ni ba, ba za ku iya yin kome ba. Duk wanda bai kasance a cikina ba, yana kamar reshen da aka jefar yă bushe; irin waɗannan rassan ne akan tattara, a jefa cikin wuta a ƙone. In kun kasance a cikina kalmomina kuma suka kasance a cikinku, ku roƙi kome da kuke so, za a kuwa ba ku. Wannan ne yakan kawo ɗaukaka ga Ubana, ku ba da ’ya’ya da yawa, kuna kuma nuna kanku ku almajiraina ne. “Kamar yadda Uba ya ƙaunace ni, haka ni ma na ƙaunace ku. To, fa, ku kasance cikin ƙaunata. In kuka yi biyayya da umarnaina, za ku kasance a cikin ƙaunata, kamar dai yadda na yi biyayya da umarnan Ubana na kuma kasance a cikin ƙaunarsa. Na gaya muku wannan domin murnata ta kasance a cikinku, murnanku kuma ta zama cikakkiya. Umarnina shi ne, Ku ƙaunaci juna kamar yadda na ƙaunace ku. Babu ƙaunar da ta fi wannan, a ce mutum ya ba da ransa saboda abokansa. Ku abokaina ne, in kun yi abin da na umarta. Ba zan ƙara ce da ku bayi ba, don bawa bai san abin da maigidansa yake yi ba. A maimako in ce da ku abokai, domin na sanar da ku duk abin da na ji daga wurin Ubana. Ba ku kuka zaɓe ni ba, a’a, ni ne na zaɓe ku na kuma naɗa ku ku je ku ba da ’ya’ya-’ya’yan da za su dawwama. Uba kuwa zai ba ku duk abin da kuka roƙa cikin sunana. Umarnina ke nan. Ku ƙaunaci juna. “In duniya ta ƙi ku, ku san cewa ta fara ƙin na ne. Da ku na duniya ne, da ta ƙaunaci abinta. Kamar yadda yake, ku ba na duniya ba ne, na zaɓe ku daga duniya, shi ya sa duniya take ƙinku. Ku tuna da kalmomin da na yi muku cewa, ‘Ba bawan da ya fi maigidansa,’ In sun tsananta mini, ku ma za su tsananta muku. Da sun yi biyayya da koyarwata, da za su yi biyayya da taku ma. Za su yi muku haka saboda sunana, gama ba su san Wannan da ya aiko ni ba. Da a ce ban zo na yi musu magana ba, da ba su da zunubi. Yanzu kam, ba su da wata hujja a kan zunubinsu. Wanda ya ƙi ni ya ƙi ya ƙi Ubana ma. Da a ce ban yi ayyuka a cikinsu waɗanda babu wani da ya taɓa yi ba, da ba su da zunubi. Amma yanzu sun ga waɗannan ayyukan banmamaki, duk da haka sun ƙi ni sun kuma ƙi Ubana. Amma wannan ya faru ne domin a cika abin da yake a rubuce cikin Dokarsu cewa, ‘Sun ƙi ni ba dalili.’ “Sa’ad da Mai Taimako ya zo, wanda zan aiko muku daga wurin Uba, Ruhun gaskiya wanda yake fitowa daga wurin Uba, zai ba da shaida game da ni. Ku ma dole ku ba da shaida, domin kun kasance tare da ni tun daga farko. “Na faɗa muku wannan duka, domin kada ku bauɗe. Za su kore ku daga majami’a; lalle, lokaci yana zuwa da duk wanda ya kashe ku, zai ɗauka yana yin wa Allah hidima ne. Za su yi waɗannan abubuwa ne domin ba su san Uba ko ni ba. Na faɗa muku wannan, domin in lokacin ya yi, ku tuna na gargaɗe ku. Ban faɗa muku wannan tun da fari ba domin ina tare da ku. “Yanzu zan tafi wurin wanda ya aiko ni, duk da haka ba waninku da ya tambaye ni, ‘Ina za ka?’ Saboda na faɗa waɗannan abubuwa ga shi kun cika da baƙin ciki. Amma gaskiya nake gaya muku. Don amfaninku ne zan tafi. Sai ko na tafi, in ba haka ba Mai Taimakon nan ba zai zo muku ba. Amma in na tafi, zan aiko shi gare ku. Sa’ad da ya zo kuwa, zai kā da duniya a kan zunubi da adalci da kuma hukunci, a kan zunubi, domin mutane ba su gaskata da ni ba; a kan adalci, domin zan tafi wurin Uba, inda ba za ku ƙara ganina ba; a kan hukunci kuma, domin an yanke hukunci a kan mai mulkin duniyan nan. “Ina da sauran abubuwa da yawa da zan faɗa muku, amma ba za ku iya ɗauka a yanzu ba. Amma sa’ad da shi, Ruhun gaskiya ya zo, zai bi da ku zuwa ga dukan gaskiya. Ba zai yi magana don kansa ba; zai faɗi abin da ya ji ne kaɗai, zai kuma faɗa muku abin da bai faru ba tukuna. Zai kawo ɗaukaka gare ni ta wurin ɗaukan abin da yake nawa, ya bayyana muku. Duk abin da yake na Uba nawa ne. Shi ya sa na ce, ‘Ruhun zai ɗauko daga abin da yake nawa, yă bayyana muku.’ ” Yesu ya ci gaba da cewa, “Jim kaɗan, ba za ku ƙara ganina ba, sa’an nan bayan an jima kaɗan kuma, za ku gan ni.” A nan fa sai waɗansu almajiransa suka ce wa juna, “Me yake nufi da cewa, ‘Jim kaɗan ba za ku ƙara ganina ba, kuma bayan an jima kaɗan, za ku gan ni,’ da kuma, ‘Domin zan tafi wurin Uba’?” Suka yi ta tambaya, “Me yake nufi da ‘jim kaɗan’? Ba mu fahimci abin da yake faɗi ba.” Yesu ya gane suna so su tambaye shi game da wannan, sai ya ce musu, “Kuna tambayar juna game da abin da nake nufi da na ce, ‘Jim kaɗan ba za ku ƙara ganina ba, da kuma bayan an jima kaɗan, za ku gan ni’? Gaskiya nake gaya muku, za ku yi kuka da kuma gunji, yayinda duniya take murna. Za ku yi baƙin ciki, amma baƙin cikinku zai koma farin ciki. Macen da za tă haihu takan yi naƙuda domin lokacinta ya yi; amma sa’ad da ta haihu, sai ta manta da wahalar domin farin ciki an haifi jariri a duniya. Haka ku ma, yanzu ne lokacin baƙin cikinku, amma zan sāke ganinku za ku kuma yi farin ciki, ba kuwa wanda zai ɗauke muku farin cikinku. A ranan nan, ba za ku sāke tambaya ta kome ba. Gaskiya nake gaya muku, Ubana zai ba ku kome da kuka roƙa cikin sunana. Har yanzu dai ba ku roƙi kome cikin sunana ba. Ku roƙa za ku kuwa samu, farin cikinku kuwa zai zama cikakke. “Ko da yake ina magana da misalai, lokaci yana zuwa da ba zan ƙara yin magana da misalai ba, sai dai in faɗa muku a fili game da Ubana. A ranan nan, za ku roƙa a cikin sunana. Ban ce zan roƙi Uba a madadinku ba. Ai, shi Uban kansa yana ƙaunarku domin kun ƙaunace ni kun kuma gaskata cewa daga Allah na fito. Na fito daga wurin Uba, na kuma shigo duniya, yanzu kuwa zan bar duniya in koma wurin Uba.” Sai almajiran Yesu suka ce, “Haba, yanzu ne fa kake magana a sarari ba tare da misalai ba. Yanzu mun gane cewa ka san kome ba sai wani ya tambaye ka ba. Wannan ya sa muka gaskata ka fito daga Allah.” Yesu ya amsa ya ce, “A ƙarshe kun gaskata! Amma lokaci na zuwa, har ma ya yi, da za a warwatsa ku, kowa yă koma gidansa. Za ku bar ni ni kaɗai. Duk da haka ba ni kaɗai ba ne, gama Ubana yana tare da ni. “Na faɗa muku waɗannan abubuwa ne, domin a cikina ku sami salama. A duniyan nan za ku sha wahala. Amma ku yi ƙarfin hali! Na yi nasara a kan duniya.” Bayan da Yesu ya faɗi wannan, sai ya dubi sama ya yi addu’a ya ce, “Uba, lokaci ya yi. Ka ɗaukaka Ɗanka, don Ɗanka yă ɗaukaka ka. Gama ka ba shi iko bisa dukan mutane domin yă ba da rai madawwami ga duk waɗanda ka ba shi. Rai madawwami kuwa shi ne, su san ka, Allah makaɗaici mai gaskiya, da kuma Yesu Kiristi, wanda ka aiko. Na ɗaukaka ka a duniya ta wurin gama aikin da ka ba ni. Yanzu ya Uba, ka ɗaukaka ni a gabanka da ɗaukakar da dā nake da ita tun kafin a kafa duniya. “Na bayyana ka ga waɗanda ka ba ni a duniya. Su naka ne; kai ka ba ni su sun kuma yi biyayya da maganarka. Yanzu sun san cewa duk abin da ka ba ni daga gare ka ya fito. Na ba su kalmomin da ka ba ni sun kuwa karɓa. Sun san tabbatacce daga wurinka na fito. Sun kuma gaskata kai ka aiko ni. Ina addu’a dominsu. Ba domin duniya nake addu’a ba, amma domin waɗanda ka ba ni, gama su naka ne. Duk abin da nake da shi naka ne, kuma duk abin da kake da shi nawa ne. Na kuwa sami ɗaukaka ta wurinsu. Ba sauran zamana a duniya, amma waɗannan a duniya suke, ni kuwa ina zuwa wurinka. Ya Uba Mai Tsarki, ka kiyaye su ta wurin ikon sunanka, sunan da ka ba ni, don su zama ɗaya kamar yadda muke ɗaya. Yayinda nake tare da su, na kāre su na kuma kiyaye su ta wurin sunan nan da ka ba ni. Ba ko ɗayan da ya ɓace, sai dai wannan da aka ƙaddara zuwa ga hallaka don Nassi yă cika. “Yanzu ina zuwa wurinka, sai dai na faɗi waɗannan abubuwa ne tun ina a duniya domin farin ciki yă zama cikakke a cikinsu. Na gaya musu maganarka duniya kuwa ta ƙi su, don su ba na duniya ba ne yadda ni ma ba na duniya ba ne. Ba addu’ata ba ce ka ɗauke su daga duniya ba, sai dai ka kāre su daga mugun nan. Su ba na duniya ba ne, kamar yadda ni ma ba na duniya ba ne. Ka tsarkake su ta wurin gaskiya; maganarka ce gaskiya. Kamar yadda ka aiko ni cikin duniya, haka ni ma na aike su cikin duniya. Saboda su ne na tsarkake kaina, domin su ma a tsarkake su da gaske. “Addu’ata ba saboda masu bina kaɗai ba ne. Ina addu’a kuma saboda waɗanda za su gaskata da ni ta wurin maganarsu. Ina so dukansu su zama ɗaya, ya Uba, kamar yadda kake a cikina, ni kuwa a cikinka. Haka su ma bari su zauna cikinmu, domin duniya ta gaskata cewa kai ka aiko ni. Na ba su ɗaukakar da ka ba ni, don su zama ɗaya kamar yadda muke ɗaya. Ni a cikinsu kai kuma a cikina. Bari su kasance da cikakken haɗinkai, domin duniya ta san cewa kai ka aiko ni. Ka kuwa ƙaunace su yadda ka ƙaunace ni. “Uba, ina so waɗanda ka ba ni su kasance tare da ni a inda nake, su kuma ga ɗaukakata, ɗaukakar da ka ba ni domin kana ƙaunata kafin halittar duniya. “Ya Uba Mai Adalci, ko da yake duniya ba tă san ka ba, ni na san ka, sun kuma san kai ka aiko ni. Na bayyana ka a gare su, zan kuma ci gaba da bayyana ka domin ƙaunar da ka yi mini ta kasance a cikinsu ni ma in kasance a cikinsu.” Da ya gama addu’a, sai Yesu ya fita tare da almajiransa suka haye Kwarin Kidron. A wancan ƙetaren kuwa akwai lambun zaitun, da shi da almajiransa suka shiga ciki. To, Yahuda, wanda ya bashe shi, ya san wurin, domin Yesu ya sha zuwa wurin da almajiransa. Saboda haka Yahuda ya zo cikin lambun, yana jagoranta ƙungiyar sojoji da waɗansu ma’aikata daga wurin manyan firistoci da Farisiyawa. Suna riƙe da toci, fitilu da kuma makamai. Yesu kuwa, sane da duk abin da zai same shi, ya fito ya tambaye, su ya ce, “Wa kuke nema?” Suka amsa suka ce, “Yesu Banazare.” Yesu ya ce, “Ni ne shi.” (Yahuda kuwa wanda ya bashe shi yana nan tsaye tare da su.) Da Yesu ya ce, “Ni ne shi,” sai suka ja da baya suka fāɗi a ƙasa. Sai ya sāke tambayar su ya ce, “Wa kuke nema?” Suka ce, “Yesu Banazare.” Yesu ya amsa ya ce, “Ai, na gaya muku ni ne shi. In kuma ni ne kuke nema, to, sai ku bar waɗannan su tafi.” Wannan ya faru ne don a cika kalmomin da ya yi cewa, “Ban yar da ko ɗaya daga cikin waɗanda ka ba ni ba.” Sai Siman Bitrus, wanda yake da takobi, ya zāre, ya kai wa bawan babban firist sara, ya ɗauke masa kunnensa na dama (Sunan bawan kuwa Malkus ne.) Sai Yesu ya umarce Bitrus ya ce, “Mai da takobinka kube! Ba zan sha kwaf da Uba ya ba ni ba?” Sai ƙungiyar soja tare da shugaban sojanta da kuma ma’aikatan Yahudawa suka kama Yesu. Suka daure shi sa’an nan suka kawo shi da farko wurin Annas, wanda yake surukin Kayifas, babban firist a shekaran nan. Kayifas ne wanda ya shawarci Yahudawa cewa zai fi kyau mutum ɗaya yă mutu saboda mutane. Siman Bitrus da kuma wani almajiri suna bin Yesu. Domin almajirin nan sananne ne ga babban firist, sai ya shiga tare da Yesu a filin gidan babban firist ɗin, Bitrus kuwa ya dakata a waje a bakin ƙofa. Almajirin nan da yake sananne ga babban firist, ya dawo ya yi magana da yarinyar mai aiki a can, ya kuma shigo da Bitrus. Yarinyar da take bakin ƙofar ta ce wa Bitrus, “Kai ba ɗaya ne daga cikin almajiran mutumin nan ba ne?” Bitrus ya amsa ya ce, “A’a, ba na ciki.” To, ana sanyi, bayi da ma’aikatan suna tsattsaye kewaye da wutar da suka hura don su ji ɗumi. Bitrus ma yana tsaye tare da su, yana jin ɗumi. Ana cikin haka, sai babban firist ya tuhumi Yesu game da almajiransa da kuma koyarwarsa. Yesu ya amsa ya ce, “Ai, na yi wa duniya magana a fili. Na kuma sha yin koyarwa a majami’u ko kuma a haikali inda Yahudawa duka sukan taru. Ban taɓa faɗin kome a ɓoye ba. Don me kake tuhumata? Ka tambayi waɗanda suka ji ni. Ba shakka, sun san abin da na faɗa.” Da Yesu ya faɗa haka, sai ɗaya daga cikin ma’aikatan da yake tsaye kusa ya mare shi a fuska ya ce, “Haka za ka amsa wa babban firist?” Yesu ya amsa ya ce, “In na faɗi abin da ba daidai ba, ka nuna abin da ba daidai ba. Amma in gaskiya na faɗa, don me ka mare ni?” Sai Annas ya aika da shi, a daure, wurin Kayifas babban firist. Da Siman Bitrus yana nan tsaye yana jin ɗumin wuta, sai aka tambaye shi, “Kai, kai ma ba ɗaya daga cikin almajiransa ba ne?” Sai ya yi mūsu, yana cewa, “Sam, ba na ciki.” Sai wani daga cikin bayin babban firist dangin wanda Bitrus ya sare wa kunne, ya tambaya shi ya ce, “Kana tsammani ban gan ka tare da shi a gonar zaitun ba?” Bitrus ya sāke yin mūsu, nan take kuwa zakara ya yi cara. Sa’an nan Yahudawa suka fitar da Yesu daga wurin Kayifas zuwa fadar gwamnar Roma. A yanzu dai, safiya ta yi, don gudu kada su ƙazantar da kansu Yahudawa ba su shiga cikin fadar ba; sun so su iya ci Bikin Ƙetarewa. Saboda haka Bilatus ya fito wajensu ya ce, “Wace ƙara kuke kawowa game da mutumin nan?” Suka amsa suka ce, “Da a ce shi ba mai laifi ba ne, ai, da ba mu bashe shi gare ka ba.” Bilatus ya ce, “Ku tafi da shi da kanku mana, ku hukunta shi bisa ga dokarku.” Sai Yahudawa suka ƙi suka ce, “Ba mu da ikon yanke wa wani hukuncin kisa.” Wannan kuwa ya faru ne don a cika kalmomin da Yesu ya yi da suka nuna irin mutuwar da zai yi. Sai Bilatus ya koma cikin fada, ya kira Yesu ya tambaye shi, “Shin, kai ne sarkin Yahudawa?” Yesu ya yi tambaya ya ce, “Wannan ra’ayin kanka ne, ko waɗansu ne suka yi maka magana game da ni?” Bilatus ya amsa ya ce, “Ni mutumin Yahuda ne? Ai, mutanenka ne da kuma manyan firistoci suka bashe ka gare ni. Me ka yi?” Yesu ya ce, “Mulkina ba na duniyan nan ba ne. Da na duniyan nan ne da bayina sun yi yaƙi su hana Yahudawa kama ni. Amma fa mulkina daga wani waje ne.” Sai Bilatus ya ce, “To, wato, kai sarki ne!” Yesu ya amsa ya ce, “Haka yake, ni sarki ne yadda ka faɗa. Tabbatacce, saboda wannan dalili ne aka haife ni, kuma don wannan ne na zo duniya, domin in shaidi gaskiya. Duk wanda yake gefen gaskiya yakan saurare ni.” Bilatus ya tambaye shi ya ce, “Mece ce gaskiya?” Da ya faɗi haka, sai ya sāke fitowa wurin Yahudawa ya ce, “Ni fa ban sami wani abin zargi game da shi ba. Amma fa kuna da wata al’ada in lokacin Bikin Ƙetarewa ya yi, nakan sakar muku da ɗan kurkuku ɗaya. To, kuna so in sakar muku ‘sarkin Yahudawa’?” Sai suka ɗau kururuwa suna cewa, “Kai, ba shi ba! A ba mu Barabbas!” To, Barabbas ɗin nan yana da hannu dumu-dumu a wani tawaye. Sa’an nan Bilatus ya tafi da Yesu ya kuma sa aka yi masa bulala. Sai sojojin suka tuƙa rawanin ƙaya suka sa masa a kā, suka kuma yafa masa wata riga mai ruwan shunayya. Suka yi ta zuwa wurinsa suna cewa, “Ranka yă daɗe, sarkin Yahudawa!” Suna ta marinsa a fuska. Bilatus kuwa ya sāke fitowa ya ce wa Yahudawa, “Ga shi, zan fito muku da shi don ku san cewa ban same shi da wani abin zargi ba.” Sa’ad da Yesu ya fito sanye da rawanin ƙayar da kuma riga mai ruwan shunayya, sai Bilatus ya ce musu, “Ga mutumin!” Nan da nan da manyan firistoci da ma’aikatansu suka gan shi, sai suka yi ihu suka ce, “A gicciye! A gicciye!” Amma Bilatus ya amsa ya ce, “Ku, ku ɗauke shi ku gicciye. Ni dai ban same shi da wani abin zargi ba.” Yahudawa dai suka nace suna cewa, “Mu fa muna da doka, kuma bisa ga dokar dole yă mutu domin ya mai da kansa Ɗan Allah.” Da Bilatus ya ji haka, sai tsoro ya ƙara kama shi, sai ya sāke koma cikin fada. Ya tambayi Yesu, “Daga ina ka fito?” Amma Yesu bai amsa masa ba. Bilatus ya ce, “Ba za ka yi mini magana ba? Ba ka san cewa ina da ikon sakinka, ko gicciye ka ba?” Yesu ya amsa ya ce, “Ba ka da wani iko a kaina, in ba a ba ka daga sama ba. Saboda haka wanda ya bashe ni gare ka, ya fi na zunubi.” Daga nan fa, Bilatus ya yi nemi yă saki Yesu, sai dai Yahudawa suka yi ta ihu suna cewa, “In ka saki wannan mutum, kai ba abokin Kaisar ba ne. Duk wanda ya ɗauka kansa a matsayin sarki, ai, yana gāba da Kaisar ne.” Da Bilatus ya ji haka, sai ya fito da Yesu, ya kuma zauna a kujerar shari’ar da ake ce da shi Daɓen Dutse (wanda a harshen Arameyik ana ce da shi Gabbata). Ranar Shirye-shiryen Makon Bikin Ƙetarewa ce kuwa, wajen sa’a ta shida. Sai Bilatus ya ce wa Yahudawa, “Ga sarkinku.” Amma suka yi ihu suka ce, “A yi da shi! A yi da shi! A gicciye shi!” Bilatus ya ce, “A! In gicciye sarkinku?” Sai manyan firistoci suka amsa suka ce, “Mu dai, ba mu da wani sarki sai Kaisar.” A ƙarshe Bilatus ya ba da shi gare su a gicciye shi. Saboda haka sojoji suka tafi da Yesu. Ɗauke da gicciyensa, ya kuwa fita zuwa wurin Ƙoƙon Kai (wanda a harshen Arameya ana ce da shi Golgota). Nan suka gicciye shi tare da waɗansu mutum biyu, ɗaya a kowane gefe da Yesu a tsakiya. Bilatus ya sa aka rubuta wata sanarwa aka kafa a kan gicciyen. Abin da aka rubuta kuwa shi ne, Yesu Banazare, Sarkin Yahudawa. Yahudawa da yawa suka karanta wannan sanarwa, gama inda aka gicciye Yesu yana kusa da birni. An kuwa rubuta sanarwar da Arameyanci, Romanci da kuma Girik. Sai manyan firistocin Yahudawa suka ce, “A’a! Kada ka rubuta, ‘Sarkin Yahudawa,’ ka dai rubuta, wannan mutum ya ce shi sarkin Yahudawa ne.” Bilatus ya amsa ya ce, “Abin da na rubuta, na rubuta.” Da sojojin suka gicciye Yesu, sai suka ɗibi tufafinsa suka kasa kashi huɗu, kowanne ya ɗauki kashi ɗaya. Suka kuma ɗauki taguwarsa, taguwar kuwa ba ɗinki, saƙa ɗaya ce gudanta daga sama har ƙasa. Sai suka ce wa juna, “Kada mu yage ta, sai dai mu jefa ƙuri’a a kanta mu ga wanda zai ci.” Wannan ya faru ne don a cika nassin da ya ce, “Suka rarraba tufafina a junansu, suka kuma jefa ƙuri’a a kan rigata.” Abin da sojojin suka yi ke nan. To, tsaye kusa da gicciyen Yesu kuwa akwai mahaifiyarsa, tare da ’yar’uwar mahaifiyarsa, Maryamu matar Kilofas, da kuma Maryamu Magdalin. Sa’ad da Yesu ya ga mahaifiyarsa a can, da kuma almajirin nan da yake ƙauna tsaye kusa, sai ya ce wa mahaifiyarsa, “Mace, ga ɗanki,” ga almajirin kuwa ya ce, “Ga mahaifiyarka.” Tun daga wannan lokaci fa almajirin nan ya kai ta gidansa. Bayan haka, sanin cewa an cika kome, kuma domin a cika Nassi, sai Yesu ya ce, “Ina jin ƙishirwa.” To, akwai wani tulun ruwan tsami ajiye a can, saboda haka suka jiƙa soso da shi, suka soka soson a sandan itacen hizzob, suka kai bakin Yesu. Da ya tsotsi abin sha ɗin, sai Yesu ya ce, “An gama.” Da wannan fa, ya sunkuyar da kansa ya saki ruhunsa. To, ranan nan fa, ranar Shirye-shirye ce, kashegari kuma muhimmin Asabbaci ne. Domin Yahudawa ba sa so a bar jikunan a kan gicciyoyi a Asabbaci, sai suka roƙi Bilatus a kakkarye ƙafafunsu kuma sauko da jikunan. Sai sojoji suka zo suka karya ƙafafun mutum na farko da aka gicciye tare da Yesu, da kuma na ɗayan. Amma sa’ad da suka zo kan Yesu suka tarar ya riga ya mutu, ba su karya ƙafafunsa ba. A maimako, sai ɗaya daga cikin sojojin ya soki Yesu a gefe da māshi, nan take jini da ruwa suka fito. Mutumin da ya gani ɗin shi ya ba da shaida, shaidarsa kuwa gaskiya ce. Ya san gaskiya yake faɗa, yana kuma ba da shaidar domin ku ma ku gaskata. Waɗannan abubuwa sun faru don a cika Nassi ne cewa, “Ba ko ɗaya daga cikin ƙasusuwansa da za a karya,” kuma kamar yadda wani Nassi ya ce, “Za su dubi wanda suka soka.” Bayan haka, Yusuf mutumin Arimateya ya roƙi Bilatus a ba shi jikin Yesu. Yusuf dai almajirin Yesu ne, amma a ɓoye domin yana tsoron Yahudawa. Da izinin Bilatus, ya zo ya ɗauki jikin. Yana tare da Nikodimus, wannan da ya taɓa zuwa wurin Yesu da dare. Nikodimus ya zo da mur da aloyes a gauraye, wajen awo ɗari. Da ɗaukowar jikin Yesu, sai su biyun suka nannaɗe shi tare da kayan ƙanshi a cikin ƙyallayen lilin bisa ga al’adar Yahudawa ta jana’iza. A inda aka gicciye Yesu, akwai wani lambu, a cikin lambun kuwa akwai sabon kabari, wanda ba a taɓa sa kowa ba. Da yake ranan nan, ranar Shirye-shirye ce ta Yahudawa, kabarin kuma yana kusa, sai suka binne Yesu a can. Da sassafe a ranar farko ta mako, tun da sauran duhu, Maryamu Magdalin ta tafi kabarin ta kuwa tarar an kawar da dutsen daga bakin kabarin. Sai ta zo da gudu wajen Siman Bitrus da ɗayan almajirin, wanda Yesu yake ƙauna, ta ce, “Sun ɗauke Ubangiji daga kabarin, ba mu kuma san inda suka sa shi ba!” Sai Bitrus da almajirin nan suka nufi kabarin. Dukansu biyu suna gudu, amma ɗayan almajirin ya tsere wa Bitrus ya kuma fara kai kabarin. Ya sunkuya ya duba ciki ya ga ƙyallayen lilin ne kwance a can amma bai shiga ba. Sa’an nan Siman Bitrus, wanda yake bayansa, ya iso ya kuwa wuce cikin kabarin. Ya ga ƙyallayen lilin kwance a can, haka ma zanen binnewar da aka naɗe kan Yesu da shi. Zanen a naɗe yake shi kaɗai, a keɓe da lilin ɗin. A ƙarshe sai almajirin nan, wanda ya kai kabarin da farko, shi ma ya shiga. Ya gani ya kuma gaskata. (Har yanzu ba su fahimci Nassin nan da ya ce lalle ne Yesu yă tashi daga matattu ba.) Sai almajiran suka koma zuwa inda suke zama. Maryamu kuwa ta tsaya a bakin kabarin daga waje tana kuka. Da tana cikin kuka, sai ta sunkuya ta leƙa cikin kabarin, sai ta ga waɗansu mala’iku biyu saye da fararen tufafi, zaune a inda dā gawar Yesu take, ɗaya wajen kai ɗayan kuma wajen ƙafafu. Suka tambaye ta cewa, “Mace, don me kike kuka?” Ta ce, “Sun ɗauke Ubangijina, ban kuma san inda suka ajiye shi ba.” Da ta faɗin haka, sai ta juya ta ga Yesu tsaye, sai dai ba tă gane cewa Yesu ne ba. Sai ya ce, “Mace, don me kike kuka? Wa kike nema?” Ta yi tsammani shi ne mai aikin lambun, sai ta ce, “Ranka yă daɗe, in kai ne ka ɗauke shi, gaya mini inda ka ajiye shi, in je in ɗauke shi.” Yesu ya ce mata, “Maryamu.” Sai ta juya wajensa ta ɗaga murya ta ce da Arameyanci, “ Rabboni!” (Wanda yake nufin “Malam”). Yesu ya ce, “Kada ki riƙe ni, gama ban riga na koma wajen Uba tukuna ba. A maimako, ki tafi wajen ’yan’uwana ki gaya musu, ‘Ina komawa wajen Ubana da Ubanku, wajen Allahna da kuma Allahnku.’ ” Sai Maryamu Magdalin ta wajen almajiran da labari cewa, “Na ga Ubangiji!” Ta kuma gaya musu cewa ya faɗa mata waɗannan abubuwa. Da Yamman ranar farko ta mako, sa’ad da almajiran suna tare, ƙofofi kuma suna a kulle saboda tsoron Yahudawa, sai ga Yesu ya zo ya tsaya a tsakiyarsu ya ce, “Salama tă kasance tare da ku!” Bayan ya faɗa haka, sai ya nuna musu hannuwansa da gefensa. Sai almajiran suka yi farin ciki ƙwarai da suka ga Ubangiji. Sai Yesu ya sāke ce musu, “Salama tă kasance tare da ku! Kamar yadda Uba ya aiko ni, haka ni ma ina aikan ku.” Da wannan sai ya hura musu numfashinsa ya ce, “Ku karɓi Ruhu Mai Tsarki. Duk wanda kuka gafarta wa zunubansa, an gafarta masa ke nan. Duk wanda ba ku gafarta wa ba kuwa, ba a gafarta masa ba ke nan.” Toma kuwa (wanda ake kira Didaimus), ɗaya daga cikin Sha Biyun, ba ya tare da almajiran sa’ad da Yesu ya zo. Saboda haka sauran almajiran suka ce masa, “Ai, mun ga Ubangiji!” Amma ya ce musu, “Ina, ai, sai na ga ramin ƙusa a hannuwansa na sa yatsata a inda ƙusoshi suka kasance, na kuma sa hannuna a gefensa, in ba haka ba, ba zan gaskata ba.” Bayan mako guda, har wa yau almajiransa suna cikin gidan, Toma kuwa yana tare da su. Ko da yake ƙofofi suna kulle, sai ga Yesu ya zo ya tsaya a tsakiyarsu ya ce, “Salama tă kasance tare da ku!” Sa’an nan ya ce wa Toma, “Sa yatsarka nan; dubi hannuwana. Miƙa hannunka ka sa a gefena. Ka daina shakka ka gaskata.” Toma ya ce masa, “Ya Ubangijina da Allahna!” Sai Yesu ya ce masa, “Wato ka gaskata saboda ka gan ni ne, masu albarka ne waɗanda ba su gan ni ba, amma suka gaskata.” Yesu ya yi waɗansu abubuwan banmamaki da yawa a gaban almajiransa da ba a rubuta a wannan littafi ba. An dai rubuta waɗannan ne don ku gaskata Yesu ne Kiristi, Ɗan Allah kuma ta wurin gaskatawa ku sami rai a cikin sunansa. Daga baya Yesu ya sāke bayyana kansa ga almajiransa, a bakin Tekun Tibariya. Ga yadda ya faru. Siman Bitrus, Toma (wanda ake kira Didaimus), Natanayel daga Kana ta Galili, ’ya’yan Zebedi maza, da kuma waɗansu almajirai guda biyu suna tare. Sai Siman Bitrus ya ce musu, “Za ni kamun kifi,” suka ce, “Za mu tafi tare da kai.” Saboda haka suka fita suka shiga jirgin ruwa, amma a daren nan ba su kama kome ba. Da sassafe, sai ga Yesu tsaye a gaci, amma almajiran ba su gane cewa Yesu ne ba. Sai ya ce musu, “Abokai, kuna da kifi kuwa?” Suka amsa suka ce, “A’a.” Ya ce musu, “Ku jefa abin kamun kifinku dama da jirgin ruwan, za ku samu.” Da suka yi haka, sai suka kāsa jawo abin kamun kifin saboda yawan kifi. Sai almajirin da Yesu yake ƙauna ya ce wa Bitrus, “Ai, Ubangiji ne!” Nan da nan da Siman Bitrus ya ji ya ce, “Ai, Ubangiji ne,” sai ya yafa mayafinsa (don dā ma ya tuɓe shi), ya fāɗa cikin ruwan. Sauran almajiran kuwa suka bi shi cikin jirgin ruwan, janye da abin kamun kifin cike da kifi, don ba su da nisa daga gaci, wajen yadi ɗari ne. Da suka sauka, sai suka ga garwashin wuta a can da kifi a kai, da kuma ’yan burodi. Yesu ya ce musu, “Ku kawo waɗansu kifin da kuka kama yanzu.” Sai Siman Bitrus ya hau ya jawo abin kamun kifin gaci. Ya cika da manyan kifi, 153, amma duk da yawansun nan abin kamun kifin bai tsintsinke ba. Yesu ya ce musu, “Ku zo ku karya kumallo.” Ba wani daga cikin almajiran da ya yi karambanin tambayarsa, “Wane ne kai?” Sun san cewa Ubangiji ne. Yesu ya zo, ya ɗauki burodin ya ba su, haka kuma kifin. Wannan fa shi ne sau na uku da Yesu ya bayyana kansa ga almajiransa bayan an tashe shi daga matattu. Da suka gama ci, sai Yesu ya ce wa Siman Bitrus, “Siman ɗan Yohanna, kana ƙaunata da gaske fiye da waɗannan?” Ya ce, “I, Ubangiji, ka san cewa ina sonka.” Yesu ya ce, “Ciyar da ’ya’yan tumakina.” Har wa yau Yesu ya ce, “Siman ɗan Yohanna, kana ƙaunata da gaske?” Ya amsa ya ce, “I, Ubangiji, ka san cewa ina sonka.” Yesu ya ce, “Lura da tumakina.” Sau na uku ya ce masa, “Siman ɗan Yohanna, kana ƙaunata?” Sai Bitrus ya ɓata rai saboda Yesu ya tambaye shi sau na uku, “Kana ƙaunata?” Ya ce, “Ubangiji ka san kome duka; ka san cewa, ina ƙaunarka.” Yesu ya ce, “Ciyar da tumakina. Gaskiya nake faɗa maka, sa’ad da kake saurayi kakan yi wa kanka sutura ka tafi inda ka so; amma sa’ad da ka tsufa za ka miƙa hannuwanka, wani dabam yă yi maka sutura yă kai ka inda ba ka so.” Yesu ya faɗi wannan ne, don yă nuna irin mutuwar da Bitrus zai yi yă ɗaukaka Allah. Sa’an nan ya ce masa, “Bi ni!” Bitrus ya juya ya ga cewa almajirin nan da Yesu yake ƙauna yana binsu. (Wannan ne ya jingina a jikin Yesu sa’ad da suke cin abincin yamman nan da ya ce, “Ubangiji wane ne zai bashe ka?”) Da Bitrus ya gan shi sai ya ce, “Ubangiji, wannan fa?” Yesu ya amsa ya ce, “Idan na so yă kasance da rai har in dawo, mene ne naka a ciki? Kai dai bi ni.” Saboda wannan, jita-jita ta bazu a cikin ’yan’uwa cewa wannan almajirin ba zai mutu ba. Amma fa Yesu bai ce ba zai mutu ba; shi dai ya ce, “In na so yă kasance da rai har in dawo, mene ne naka a ciki?” Wannan shi ne almajirin da ya ba da shaida a kan waɗannan abubuwa ya kuma rubuta su. Mun san cewa shaidarsa gaskiya ce. Yesu ya yi waɗansu abubuwa da yawa kuma. Da a ce an rubuta kowannensu, na tabbata ko duniya duka ba za tă sami wuri saboda littattafan da za a rubuta ba. A littafina na farko, Tiyofilus, na rubuta game da dukan abin da Yesu ya fara yi, da abin da ya koyar har zuwa ranar da aka ɗauke shi zuwa sama, bayan ya ba da umarnai ta wurin Ruhu Mai Tsarki ga manzannin da ya zaɓa. Bayan wahalarsa, ya bayyana kansa ga waɗannan mutane ya kuma ba da tabbatattun alamu masu yawa cewa yana da rai. Ya bayyana a gare su har kwana arba’in ya kuma yi musu magana game da mulkin Allah. A wani lokaci, yayinda yake ci tare da su, ya ba su wannan umarni, “Kada ku bar Urushalima, amma ku jira kyautar da Ubana ya yi alkawari, wadda kuka ji na yi magana a kai. Gama Yohanna ya yi baftisma da ruwa, amma a cikin ’yan kwanaki za a yi muku baftisma da Ruhu Mai Tsarki.” Saboda haka, sa’ad da suka taru, sai suka tambaye shi, “Ubangiji, a wannan lokaci za ka mayar da mulki ga Isra’ila?” Ya ce musu, “Ba naku ba ne ku san lokuta ko ranakun da Uban ya shirya cikin ikonsa. Amma ku za ku karɓi iko sa’ad da Ruhu Mai Tsarki ya sauka a kanku; za ku kuma zama shaiduna cikin Urushalima, da kuma cikin dukan Yahudiya da Samariya, zuwa kuma iyakar duniya.” Bayan ya faɗi wannan, sai aka ɗauke shi sama a idanunsu sai wani girgije ya rufe shi daga ganinsu. Suna zuba ido a bisa, zuwa cikin sararin sama yayinda yake tafiya, nan da nan, sai ga mutane biyu saye da fararen riguna tsaye kusa da su. Sai suka ce, “Mutanen Galili, don me kuke tsaye a nan kuna duban sararin sama? Wannan Yesu, wanda aka ɗauke daga gare ku zuwa sama, zai komo daidai yadda kuka ga ya tafi sama.” Sai suka koma Urushalima daga tudun da ake kira Dutsen Zaitun, tafiyar ranar Asabbaci guda daga birnin. Da suka iso, sai suka hau gidan sama, zuwa ɗakin da suke zama. Waɗanda suka kasance kuwa su ne, Bitrus, Yohanna, Yaƙub da Andarawus; Filibus da Toma; Bartolomeyu da Mattiyu; Yaƙub ɗan Alfayus da Siman Zilot, da kuma Yahuda ɗan Yaƙub. Waɗannan duka suka duƙufa cikin addu’a, tare da waɗansu mata da Maryamu mahaifiyar Yesu, da kuma tare da ’yan’uwansa. A waɗancan kwanakin Bitrus ya miƙe tsaye cikin ’yan’uwa masu bi (taron da ya yi kusan mutum ɗari da ashirin) ya ce, “’Yan’uwana, dole a cika Nassin nan da Ruhu Mai Tsarki ya yi magana tun da daɗewa ta bakin Dawuda game da Yahuda, wanda ya zama jagora ga waɗanda suka kama Yesu dā shi ɗaya ne cikinmu, ya kuma yi hidima a cikin aikin nan.” (Da ladar da ya samu saboda muguntarsa Yahuda ya sayi wani fili; a can ya fāɗi da kā, jikinsa ya fashe, hanjinsa kuma duk suka zubo. Kowa a Urushalima ya ji game da wannan, saboda haka suka kira wannan filin Akeldama, da yarensu, wato, Filin Jini.) Bitrus ya ce, “Gama yana a rubuce a cikin Littafin Zabura cewa, “ ‘Bari wurinsa yă zama babu kowa; kada kowa ya zauna a cikinsa,’ kuma, “ ‘Bari wani ya ɗauki matsayinsa na shugabanci.’ Saboda haka dole a zaɓi ɗaya daga cikin mutanen da suke tare da mu duk lokacin da Ubangiji Yesu yake shiga da fita a cikinmu, farawa daga baftisma ta Yohanna har zuwa sa’ad da aka ɗauke Yesu daga gare mu. Gama dole ɗaya daga waɗannan ya zama shaidar tashinsa daga matattu tare da mu.” Saboda haka suka gabatar da mutane biyu. Yusuf mai suna Barsabbas (da aka kuma sani da Yustus) da kuma Mattiyas. Sai suka yi addu’a suka ce, “Ubangiji, ka san zuciyar kowa. Nuna mana wanne a cikin waɗannan biyu da ka zaɓa ya karɓi wannan aikin manzanci, wanda Yahuda ya bari don yă tafi wurin da yake nasa.” Sa’an nan suka jefa ƙuri’u, ƙuri’ar kuwa ta fāɗo a kan Mattiyas; sai aka sa shi cikin manzannin nan goma sha ɗaya. Da ranar Fentekos ta yi, dukansu suna tare wuri ɗaya. Ba zato ba tsammani sai aka ji motsi kamar ta babbar iska tana hurowa daga sama ta kuma cika dukan gidan da suke zaune. Suka ga wani abin da ya yi kama da harsunan wuta, suka rarrabu suna kuma sassauka a kan kowannensu. Dukansu kuwa suka cika da Ruhu Mai Tsarki suka kuma fara magana da waɗansu harsuna yadda Ruhu ya sa suka iya. To, a Urushalima akwai Yahudawa masu tsoron Allah, daga kowace ƙasa a duniya. Da suka ji wannan motsi, taro ya haɗu wuri ɗaya a ruɗe, domin kowannensu ya ji suna magana da yarensa. Cike da mamaki, suka yi tambaya suna cewa, “Ashe, duk waɗannan mutane masu magana ba Galiliyawa ba ne? To, yaya kowannenmu yana ji suna yarensa? Fartiyawa, Medes da Elamawa; mazaunan Mesofotamiya, Yahudiya da Kaffadokiya, Fontus da Asiya, Firjiya da Famfiliya, Masar da sassa Libiya kusa da Sairin; baƙi daga Roma (Yahudawa da kuma waɗanda suka tuba suka shiga Yahudanci); Kiretawa da Larabawa, mun ji su suna shelar abubuwan banmamaki na Allah da yarenmu!” A ruɗe kuma cike da mamaki, suka tambayi junansu cewa, “Mene ne wannan yake nufi?” Duk da haka waɗansu suka yi musu ba’a suka ce, “Sun yi tatil da ruwan inabi ne.” Sai Bitrus ya miƙe tsaye tare da Sha Ɗayan nan, ya ɗaga muryarsa ya yi wa taron jawabi ya ce, “’Yan’uwana Yahudawa da dukanku da kuke zama cikin Urushalima, bari in bayyana muku wannan, ku saurara da kyau ga abin da zan faɗa. Waɗannan mutane ba su bugu ba, kamar yadda kuka ɗauka. Yanzu ƙarfe tara na safe ne kawai! A’a, ai, abin da aka yi magana ta bakin annabi Yowel ke nan cewa, “Allah ya ce, ‘A kwanakin ƙarshe, zan zubo Ruhuna bisa dukan mutane. ’Ya’yanku maza da mata za su yi annabci, samarinku za su ga wahayoyi, dattawanku kuma za su yi mafarkai. Kai, har ma a kan bayina, maza da mata, zan zubo Ruhuna a waɗancan kwanaki, za su kuwa yi annabci. Zan nuna abubuwan banmamaki a sararin sama da alamu a nan ƙasa, jini da wuta da kuma hauhawan hayaƙi. Za a mai da rana duhu, wata kuma ya zama jini, kafin zuwa rana mai girma da kuma ta ɗaukaka ta Ubangiji. Kuma duk wanda ya kira bisa sunan Ubangiji zai sami ceto.’ “Mutanen Isra’ila, ku saurari wannan. Yesu Banazare shi ne mutumin da Allah ya tabbatar muku ta wurin mu’ujizai, ayyukan banmamaki, da kuma alamu, waɗanda Allah ya yi a cikinku ta wurinsa, kamar yadda ku kanku kuka sani. An ba da wannan mutum gare ku bisa ga nufin Allah da kuma rigyasaninsa, ku kuma tare da taimakon mugayen mutane, kuka kashe shi ta wurin kafa shi a kan gicciye. Amma Allah ya tashe shi daga matattu, ya ’yantar da shi daga azabar mutuwa, don ba ya yiwuwa mutuwa ta riƙe shi. Dawuda ya yi faɗi game da shi cewa, “ ‘Kullum ina ganin Ubangiji a gabana. Gama yana a hannuna na dama, ba zan jijjigu ba. Saboda haka, zuciyata na farin ciki, harshena kuma na murna, jikina kuma zai kasance da bege, gama ba za ka bar ni cikin kabari ba, ba kuwa za ka yarda Mai Tsarkinka yă ruɓa ba. Ka sanar da ni hanyoyin rai, za ka cika ni da farin ciki a gabanka.’ “’Yan’uwa, zan iya tabbatar muku gabagadi cewa kakanmu Dawuda ya mutu aka kuma binne shi, kabarinsa kuwa yana a nan har yă zuwa yau. Amma shi annabi ne ya kuma san abin da Allah ya yi masa alkawari da rantsuwa cewa zai ɗora ɗaya daga cikin zuriyarsa a kan gadon sarautarsa. Ganin abin da yake gaba, ya yi magana a kan tashin Kiristi daga matattu cewa, ba a bar shi a kabari ba, jikinsa kuma bai ruɓa ba. Allah ya tashe wannan Yesu zuwa rai, mu kuwa duk shaidu ne ga wannan. An ɗaukaka shi zuwa ga hannun dama na Allah, ya karɓi alkawarin Ruhu Mai Tsarki daga Uba, ya kuma zubo abin da yanzu kuke gani kuke kuma ji. Gama Dawuda bai hau zuwa sama ba, duk da haka ya ce, “ ‘Ubangiji ya ce wa Ubangijina, “Zauna a hannun damana, sai na sa abokan gābanka su zama matashin sawunka.” ’ “Saboda haka bari dukan Isra’ila su tabbatar da wannan. Allah ya mai da wannan Yesu, da kuka gicciye, Ubangiji da kuma Kiristi.” Sa’ad da mutane suka ji wannan, sai suka soku a zuci sai suka ce wa Bitrus da sauran manzanni, “’Yan’uwa, me za mu yi?” Bitrus ya amsa, “Ku tuba a kuma yi muku baftisma, kowannenku a cikin sunan Yesu Kiristi domin gafarar zunubanku. Za ku kuwa karɓi kyautar Ruhu Mai Tsarki. Alkawarin dominku ne da ’ya’yanku da kuma dukan waɗanda suke da nesa, domin dukan waɗanda Ubangiji Allahnmu zai kira.” Da waɗansu kalmomi masu yawa ya gargaɗe su; ya kuma roƙe su cewa, “Ku ceci kanku daga wannan lalataccen zamani.” Waɗanda suka yarda da saƙonsa kuwa aka yi musu baftisma, a ranar kuwa yawansu ya ƙaru da mutum kusan dubu uku. Suka ba da kansu ga koyarwar manzanni da kuma ga zumunci, ga gutsuttsura burodin da kuma ga addu’a. Kowa ya cika da tsoro, manzannin kuwa suka aikata abubuwan banmamaki da alamu masu yawa. Dukan masu bi suna tare, suna kuma mallakar kome tare. Suka dinga sayar da ƙaddarorinsu da kayayyakinsu, suka ba wa kowa gwargwadon bukatarsa. Kowace rana suka ci gaba da taruwa a filin haikali. Suka gutsuttsura burodi a gidajensu suna cin abinci tare da farin ciki da zuciya ɗaya, suna yabon Allah suna kuma samun tagomashin dukan mutane. Ubangiji kuwa ya ƙara yawansu kowace rana na waɗanda suke samun ceto. Wata rana, Bitrus da Yohanna suna haurawa zuwa haikali a lokacin addu’a da ƙarfe uku na rana. To, sai ga wani da aka haifa gurgu ana ɗauke da shi zuwa ƙofar haikalin da ake kira Kyakkyawa, inda akan ajiye kowace rana, don yă yi bara daga masu shigowa cikin filayen haikali. Da ya ga Bitrus da Yohanna suna gab da shiga, sai ya roƙe su kuɗi. Bitrus kuwa ya kafa masa ido, haka ma Yohanna. Sai Bitrus ya ce, “Dube mu!” Saboda haka mutumin ya mai da hankalinsa a kansu, yana fata samun wani abu daga gare su. Sai Bitrus ya ce, “Azurfa ko zinariya ba ni da su, amma abin da nake da shi, shi zan ba ka. A cikin sunan Yesu Kiristi Banazare, ka yi tafiya.” Ta wurin kama hannunsa na dama, ya taimake shi ya miƙe, nan take ƙafafu da idon sawun mutumin suka yi ƙarfi. Sai ya yi wuf da ƙafafunsa ya fara tafiya. Ya tafi tare da su ya shiga cikin filin haikali yana tafiya yana tsalle, yana kuma yabon Allah. Sa’ad da dukan mutane suka gan shi yana tafiya yana yabon Allah, sai suka gane cewa shi ne mutumin nan wanda dā yake zama yana bara a bakin ƙofar haikalin da ake kira Kyakkyawa, suka kuwa cika da mamaki da tsoro a kan abin da ya faru gare shi. Tun mai bawan yana riƙe da Bitrus da Yohanna, dukan mutanen suka yi mamaki, suka zo wurinsu a guje a inda ake kira Shirayin Solomon. Da Bitrus ya ga haka, sai ya ce musu, “Mutanen Isra’ila, don me wannan ya ba ku mamaki? Don me kuke kallonmu sai ka ce da ikon kanmu ne ko kuwa don ibadarmu ne muka sa wannan mutum ya yi tafiya? Allah na Ibrahim, Ishaku, da Yaƙub, Allah na kakanninmu, ya ɗaukaka bawansa Yesu. Ku kuka ba da shi domin a kashe, kuka yi mūsun saninsa a gaban Bilatus, ko da yake ya yi niyya ya sake shi. Kuka yi mūsun sanin Mai Tsarki da Mai Adalci kuka roƙa a sakar muku mai kisankai. Kuka kashe tushen rai, amma Allah ya tashe shi daga matattu. Mu shaidu ne ga wannan. Ta wurin bangaskiya cikin sunan Yesu ne wannan mutum da kuke gani kuka kuma sani ya sami ƙarfi. Da sunan Yesu, da kuma bangaskiyar da take samuwa ta wurinsa ne ya ba shi cikakkiyar warkarwa, yadda dukanku kuke gani. “To, ’yan’uwa, na san cewa, kun aikata wannan cikin jahilci ne, yadda shugabanninku suka yi. Amma ta haka ne Allah ya cika abin da ya rigyafaɗi ta bakin dukan annabawa cewa, Kiristinsa zai sha wahala. Saboda haka ku tuba, ku juyo ga Allah, don a shafe zunubanku, don lokutan wartsakewa su zo daga wurin Ubangiji, don kuma ya iya aika da Kiristi, wanda aka naɗa tun dā saboda ku, Yesu ke nan. Dole yă kasance a sama, sai lokaci ya yi da Allah zai mai da kome sabo, yadda ya yi alkawari tun dā ta wurin annabawansa masu tsarki. Gama Musa ya ce, ‘Ubangiji Allahnku zai tasar muku wani annabi kamar ni daga cikin mutanenku; dole ku saurari duk abin da ya faɗa muku. Duk wanda bai saurare shi ba za a ware shi gaba ɗaya daga mutanensa.’ “Tabbatacce, dukan annabawa daga Sama’ila zuwa gaba, dukansu da suka yi magana, sun rigya faɗin waɗannan kwanaki. Ku kuwa magādan annabawan ne da kuma na alkawarin da Allah ya yi da kakanninku. Ya ce wa Ibrahim, ‘Ta wurin zuriyarka, dukan kabilan duniya za su sami albarka.’ Da Allah ya tashe bawansa, ya aike shi da fari zuwa gare ku don yă albarkace ku ta wurin juye kowannenku daga mugayen hanyoyinku.” Sai firistoci da shugaban masu gadin haikalin da kuma Sadukiyawa suka hauro wurin Bitrus da Yohanna yayinda suke cikin magana da mutane. Sun damu ƙwarai da gaske domin manzannin suna koya wa mutane suna kuma shela a cikin Yesu cewa akwai tashin matattu. Sai suka kama Bitrus da Yohanna, amma da yake yamma ta riga ta yi sai suka sa su cikin kurkuku sai kashegari. Amma da yawa da suka ji saƙon suka gaskata, yawan mutanen kuwa ya ƙaru ya kai wajen dubu biyar. Kashegari, sai masu mulki, dattawa da kuma malaman dokoki suka taru a Urushalima. Annas babban firist yana nan, haka ma Kayifas Yohanna, Alekzanda da kuma sauran mutanen da suke iyalin babban firist. Suka sa aka kawo Bitrus da Yohanna a gabansu suka kuma fara yin musu tambayoyi cewa, “Da wane iko ko da wane suna kuka yi wannan?” Sai Bitrus, cike da Ruhu Mai Tsarki ya ce musu, “Masu mulki da dattawan mutane! In ana tuhumarmu ne yau saboda alherin da aka yi wa gurgun nan da kuma yadda aka warkar da shi, to, sai ku san wannan, ku da dukan mutanen Isra’ila cewa da sunan Yesu Kiristi Banazare, wanda kuka gicciye amma wanda Allah ya tasar daga matattu ne, wannan mutum yake tsaye a gabanku lafiyayye. Shi ne, “ ‘dutsen da ku magina kuka ƙi, wanda kuwa ya zama dutsen kusurwar gini.’ Ba a samun ceto ta wurin wani dabam, gama babu wani suna a ƙarƙashin sama da aka ba wa mutane wanda ta wurinsa dole mu sami ceto.” Da suka ga ƙarfin halin Bitrus da Yohanna suka kuma gane cewa su marasa ilimi ne, talakawa kuma, sai suka yi mamaki suka kuma lura cewa waɗannan mutane sun kasance tare da Yesu. Amma da yake sun ga mutumin da aka warkar yana tsaye a wurin tare da su, sai suka rasa abin faɗi. Saboda haka suka umarta a fitar da su daga Majalisar, sa’an nan suka yi shawara da juna. Suka ce, “Me za mu yi da waɗannan mutane? Kowa da yake zama a Urushalima ya san sun yi abin banmamaki, kuma ba za mu iya yin mūsu wannan ba. Amma don a hana wannan abu daga ƙara bazuwa cikin mutane, dole mu kwaɓe mutanen nan kada su ƙara yi wa kowa magana cikin wannan suna.” Sai suka sāke kiransu ciki suka kuma umarce su kada su kuskura su yi magana ko su ƙara koyarwa a cikin sunan Yesu. Amma Bitrus da Yohanna suka amsa, “Ku shari’anta da kanku ko daidai ne a gaban Allah mu yi muku biyayya maimakon Allah. Gama ba za mu iya daina yin magana game da abin da muka gani muka kuma ji ba.” Bayan ƙarin barazana sai suka bar su su tafi. Ba su iya yanke shawara yadda za a hore su ba, domin dukan mutane suna yabon Allah saboda abin da ya faru. Gama mutumin da ya sami warkarwar banmamaki, shekarunsa sun fi arba’in. Da aka sake su, Bitrus da Yohanna suka koma wajen mutanensu suka ba da labarin duk abin da manyan firistoci da dattawa suka faɗa musu. Sa’ad da suka ji wannan, sai suka ɗaga muryoyinsu gaba ɗaya cikin addu’a ga Allah, suka ce, “Ya Ubangiji Mai Iko Duka, kai ka halicci sama da ƙasa da kuma teku, da kome da yake cikinsu. Ka yi magana ta wurin Ruhu Mai Tsarki ta bakin bawanka, kakanmu Dawuda cewa, “ ‘Don me ƙasashe suke fushi, mutane kuma suke ƙulla shawara a banza? Sarakunan duniya sun ja dāgā, masu mulki kuma sun taru gaba ɗaya, suna gāba da Ubangiji da kuma Shafaffensa.’ Tabbatacce Hiridus da Buntus Bilatus suka haɗu tare da Al’ummai da kuma mutanen Isra’ila a wannan birni ce don su ƙulla gāba da bawanka mai tsarki Yesu, wanda ka shafe. Sun aikata abin da ikonka da kuma nufinka ya riga ya shirya tuntuni zai faru. Yanzu, Ubangiji, ka dubi barazanansu ka kuma sa bayinka su furta maganarka da iyakar ƙarfin hali. Ka miƙa hannunka don ka warkar ka kuma yi ayyukan banmamaki da alamu masu banmamaki ta wurin sunan bawanka mai tsarki Yesu.” Bayan suka yi addu’a, sai inda suka taru ya jijjigu. Dukansu kuwa suka cika da Ruhu Mai Tsarki, suka yi ta shaidar maganar Allah babu tsoro. Dukan masu bi kuwa zuciyarsu ɗaya ne, nufinsu kuwa ɗaya. Babu wani da ya ce abin da ya mallaka nasa ne, amma sun raba kome da suke da shi. Da iko mai ƙarfi manzanni suka ci gaba da shaidar tashin matattu na Ubangiji Yesu, alheri mai yawa kuwa yana bisansu duka. Babu mabukata a cikinsu. Lokaci-lokaci waɗanda suke da gonaki ko gidaje sukan sayar da su, su kawo kuɗi daga abin da suka sayar, su ajiye a sawun manzannin, a kuma raba wa kowa gwargwadon bukatarsa. Yusuf, wani Balawe daga Saifurus, wanda manzanni suke kira Barnabas (wanda yake nufin Ɗan Ƙarfafawa) ya sayar da wata gonar da ya mallaki ya kuma kawo kuɗin ya ajiye a sawun manzanni. To wani mutum mai suna Ananiyas tare da matarsa Saffiratu, shi ma ya sayar da wata mallakarsa. Da cikakken sanin matarsa ya ajiye sashi daga cikin kuɗin don kansa, ya kuma kawo sauran ya ajiye a sawun manzanni. Sai Bitrus ya ce, “Ananiyas, ta yaya Shaiɗan ya cika zuciyarka haka da ka yi wa Ruhu Mai Tsarki ƙarya ka kuma ajiye wa kanka sauran kuɗin da ka karɓa na filin? Ba naka ba ne kafin ka sayar da shi? Bayan da ka sayar da shi kuma, kuɗin ba naka ba ne? Me ya sa ka yi tunanin yin irin wannan abu? Ba mutum ne ka yi wa ƙarya ba, Allah ne ka yi masa.” Da Ananiyas ya ji wannan, sai ya fāɗi ya mutu. Sai babban tsoro kuwa ya kama duk waɗanda suka ji abin da ya faru. Sai samari suka zo gaba, suka naɗe gawarsa, suka fitar da shi suka je suka binne. Bayan kusan awa uku, sai matarsa ta shigo, ba da sanin abin da ya faru ba. Bitrus ya tambaye ta ya ce, “Gaya mini, kuɗin da yake da Ananiyas kuka sayar da filin ke nan?” Ta ce, “I, haka ne muka sayar.” Bitrus ya ce mata, “Ta yaya kuka yarda ku gwada Ruhun Ubangiji? Duba! Sawun mutanen da suka binne mijinki suna bakin ƙofa, za su kuwa ɗauke ki zuwa waje ke ma.” Nan take ta fāɗi a ƙafafunsa ta mutu. Sai samarin suka shigo ciki, suka kuwa same ta matacciya, suka ɗauke ta suka kai ta waje suka binne ta kusa da mijinta. Babban tsoro ya kama dukan ikkilisiya da kuma duk wanda ya ji game da abubuwan nan. Manzannin suka yi ayyukan da alamu masu banmamaki masu yawa a cikin mutanen. Dukan masu bi kuwa sukan taru a Shirayin Solomon. Ba wanda ya yi karambanin shiga cikinsu, duk da haka mutane suna girmama su ƙwarai. Duk da haka, maza da matan da suke gaskata ga Ubangiji sai ƙaruwa suke, suka kuma ƙaru a yawa. A sakamakon haka, mutane suka kawo marasa lafiya a tituna suka kwantar da su a kan gadaje da tabarmai domin aƙalla inuwar Bitrus za tă bi kan waɗansunsu yayinda yake wucewa. Jama’a ma suka tattaru daga garuruwa kewaye da Urushalima suna kawo marasa lafiyarsu da kuma waɗanda mugayen ruhohi suke damun su, dukansu kuwa suka warke. Sai babban firist da dukan abokan aikinsa, waɗanda suke na ƙungiyar Sadukiyawa suka cika da kishi. Suka kama manzannin suka sa su a kurkukun da ake sa kowa da kowa. Amma da dare wani mala’ikan Ubangiji ya buɗe ƙofofin kurkukun ya fitar da su. Ya ce, “Ku je ku tsaya a filin haikali ku sanar wa mutane cikakken saƙon wannan sabon rai.” Da gari ya waye, sai suka shiga filin haikali, yadda aka faɗa musu, suka kuwa fara koyar da mutane. Sa’ad da babban firist da abokan aikinsa suka iso, sai suka kira Majalisa gaba ɗaya dukan dattawan Isra’ila, suka kuma aika kurkuku a zo da manzannin. Amma da dogarawan suka iso kurkukun, ba su same su a can ba. Saboda haka suka dawo suka ba da labari, suka ce, “Mun iske kurkukun a kulle sosai, da masu gadi suna tsaye a bakin ƙofofin; amma da muka buɗe su, sai muka tarar ba kowa a ciki.” Da jin wannan labari, sai shugaban masu gadin haikali da manyan firistocin suka ruɗe, suna tunanin abin da wannan al’amari zai zama. Sai wani ya zo ya ce, “Ga shi! Mutanen da kuka sa a kurkuku suna tsaye a filin haikali suna koya wa mutane.” Da wannan, shugaban ya tafi tare da dogarawansa suka kawo manzannin. Sun kawo su amma fa ba ƙarfi da yaji ba, don suna tsoro kada mutane su jajjefe su da duwatsu. Da suka kawo manzannin, sai suka sa su suka bayyana a gaban Majalisar don babban firist ya tuhume su. Ya ce, “Mun kwaɓe ku da gaske kada ku ƙara koyarwa cikin wannan suna, duk da haka kun cika Urushalima da koyarwarku, har ma kuna so ku ɗora mana laifin jinin mutumin nan.” Bitrus da sauran manzannin suka amsa suka ce, “Dole ne mu yi wa Allah biyayya a maimakon mutane! Allahn kakanninmu ya tā da Yesu daga matattu, wanda kuka kashe ta wurin ratayewa a bisan itace. Allah ya ɗaukaka shi zuwa hannun damansa a matsayin Yerima da Mai Ceto don yă kawo tuba da gafarar zunubai ga Isra’ila. Mu shaidu ne ga waɗannan abubuwa, haka kuma Ruhu Mai Tsarki, wanda Allah ya ba wa waɗanda suke yin masa biyayya.” Da suka ji haka, sai suka yi fushi suka so su kashe su. Amma wani Bafarisiyen da ake kira Gamaliyel, wani malamin doka, wanda dukan mutane ke girmamawa, ya miƙe tsaye a Majalisar ya umarta a fitar da mutanen waje na ɗan lokaci. Sa’an nan ya yi musu jawabi ya ce, “Mutanen Isra’ila, ku yi kula da kyau da abin da kuke niyyar yi wa mutanen nan. Kwanan baya, Teyudas ya ɓullo, yana cewa wai shi wani mutum ne, kuma wajen mutane ɗari huɗu suka bi shi. Aka kuwa kashe shi, dukan masu binsa kuwa suka watse, kome ya wargaje. Bayansa, Yahuda mutumin Galili ya ɓullo a kwanakin ƙidaya, ya jagoranci mutane cikin tawaye. Shi ma aka kashe shi, dukan mabiyansa kuma aka watsar da su. Saboda haka, a wannan batu na yanzu, ina ba ku shawara. Ku ƙyale mutanen nan! Ku bar su su tafi! Gama in manufarsu ko ayyukansu na mutum ne, ai, zai rushe. Amma in daga Allah ne, ba za ku iya hana waɗannan mutane ba, za ku dai sami kanku kuna gāba da Allah ne.” Jawabinsa ya rinjaye su. Suka kira manzannin suka sa aka yi musu bulala. Sa’an nan suka kwaɓe su kada su ƙara magana a cikin sunan Yesu, suka kuma bar su suka tafi. Manzannin suka bar Majalisar, suna farin ciki domin an ga sun cancanta a kunyata su saboda Sunan nan. Kowace rana, a filin haikali da kuma gida-gida, ba su fasa koyarwa da kuma shelar labari mai daɗi cewa Yesu shi ne Kiristi ba. A waɗannan kwanaki, sa’ad da yawan almajirai suke ƙaruwa, sai Yahudawan masu jin Hellenanci a cikinsu suka yi gunaguni a kan Yahudawan da suke Ibraniyawa domin ba a kula da gwaurayensu a wajen raba abinci na yau da kullum. Saboda haka Sha Biyun nan suka tara dukan almajirai wuri ɗaya, suka ce, “Bai zai yi kyau mu bar hidimar maganar Allah don mu shiga hidimar abinci ba. ’Yan’uwa, ku zaɓi mutum bakwai daga cikinku waɗanda aka sani suna cike da Ruhu da kuma hikima. Mu kuwa za mu danƙa musu wannan aiki mu kuwa mu mai da halinmu ga yin addu’a da kuma hidimar maganar Allah.” Wannan shawarar kuwa ta gamshi dukan ƙungiyar. Sai suka zaɓi Istifanus, mutumin da yake cike da bangaskiya da kuma Ruhu Mai Tsarki; da Filibus, Burokorus, Nikano, Timon, Farmenas, da Nikolas daga Antiyok, wanda ya tuba zuwa Yahudanci. Suka gabatar da waɗannan mutane wa manzanni, waɗanda kuwa suka yi addu’a, suka ɗibiya hannuwansu a kansu. Saboda haka maganar Allah ta yaɗu. Yawan almajirai a Urushalima kuwa ya yi saurin ƙaruwa, firistoci masu yawa kuma suka zama masu biyayya ga wannan bangaskiya. To, Istifanus, mutum cike da alheri da ikon Allah, ya aikata manyan ayyukan da alamu masu banmamaki a cikin mutane. Sai hamayya ta taso daga ’yan ƙungiyar Majami’a na ’Yantattu (kamar yadda ake kiransu), Yahudawan Sairin da Alekzandariya da kuma lardunan Silisiya da Asiya. Mutanen nan suka fara muhawwara da Istifanus, amma ba su iya cin nasara kan hikimarsa ko kuma a kan Ruhu wanda ta wurinsa ne ya magana ba. Sa’an nan a asirce suka zuga waɗansu mutane su ce, “Mun ji Istifanus ya faɗa kalmomin saɓo game da Musa da kuma Allah.” Ta haka suka tā da hankalin mutane da dattawa da kuma malaman dokoki. Suka kama Istifanus suka kawo shi a gaban Majalisa. Suka kawo masu ba da shaidar ƙarya, waɗanda suka ba da shaida cewa, “Wannan mutum ba ya rabuwa da maganar banza a kan wurin nan mai tsarki da kuma doka. Gama mun ji shi yana cewa wannan Yesu Banazare zai rushe wurin nan ya kuma canja al’adun da Musa ya ba mu.” Dukan waɗanda suke zaune a Majalisar suka kafa wa Istifanus ido, suka kuma ga fuskarsa ta yi kama da ta mala’ika. Sai babban firist ya tambaye shi ya ce, “Waɗannan zargen gaskiya ne?” Game da wannan ya amsa ya ce, “’Yan’uwa da ubanni, ku saurare ni! Allah mai ɗaukaka ya bayyana ga kakanmu Ibrahim yayinda yake a ƙasar Mesofotamiya tukuna, kafin ya yi zama a Haran. Allah ya ce, ‘Ka bar ƙasarka da kuma mutanenka, ka tafi ƙasar da zan nuna maka.’ “Saboda haka ya bar ƙasar Kaldiyawa ya kuma yi zama a Haran. Bayan mutuwar mahaifinsa, Allah ya aika da shi wannan ƙasar da yanzu kuke zama. Bai ba shi gādo a nan ba, ko taki ɗaya na ƙasa. Amma Allah ya yi masa alkawari cewa shi da zuriyarsa masu zuwa bayansa za su mallaki ƙasar, ko da yake a lokacin Ibrahim ba shi da yaro. Allah ya yi magana da shi ta haka, ‘Shekara ɗari huɗu, zuriyarka za tă yi baƙunci a wata ƙasar da ba tasu ba, za su yi bauta su kuma sha wulaƙanci. Amma zan hore ƙasar da suka bauta wa.’ Allah ya ce, ‘Kuma daga baya za su fita daga wannan ƙasa su kuma yi mini sujada a wannan wuri.’ Sa’an nan ya yi wa Ibrahim alkawari game da kaciya. Ibrahim kuwa ya zama mahaifin Ishaku ya kuma yi masa kaciya kwana takwas bayan haihuwarsa. Daga baya Ishaku ya zama mahaifin Yaƙub, Yaƙub kuma ya zama mahaifin kakanninmu sha biyun nan. “Domin kakanninmu sun ji kishin Yusuf, sai suka sayar da shi bawa zuwa Masar. Amma Allah ya kasance tare da shi ya kuma cece shi daga dukan wahalolinsa. Ya ba wa Yusuf hikima ya kuma sa ya sami farin jini a wurin Fir’auna, sarkin Masar; saboda haka ya mai da shi mai mulki a kan Masar da kuma dukan fadarsa. “Sai yunwa ta auko wa dukan Masar da Kan’ana, ta kawo wahala mai tsanani, kakanninmu ba su iya samun abinci ba. Sa’ad da Yaƙub ya ji cewa akwai hatsi a Masar, sai ya aiki kakanninmu ziyararsu ta farko. A ziyararsu ta biyu, Yusuf ya faɗa wa ’yan’uwansa wane ne shi, Fir’auna kuwa ya sami sani game da iyalin Yusuf. Bayan wannan, Yusuf ya aika a zo da mahaifinsa Yaƙub da dukan iyalinsa, gaba ɗaya dai mutum saba’in da biyar ne. Sai Yaƙub ya gangara zuwa Masar, inda shi da kuma kakanninmu suka mutu. Aka dawo da gawawwakinsu Shekem aka binne su a kabarin da Ibrahim ya saya daga wurin ’ya’yan Hamor da waɗansu kuɗi a Shekem. “Da lokaci ya yi kusa da Allah zai cika alkawarin da ya yi wa Ibrahim, sai yawan mutanenmu da suke a Masar ya ƙaru ƙwarai. Sa’an nan wani sarki, wanda bai san kome game da Yusuf ba, ya zama mai mulkin Masar. Ya kuwa wulaƙanta mutanenmu sosai, ya kuma gwada wa kakanni-kakanninmu azaba ta wurin tilasta su su zubar da sababbin jariransu, don su mutu. “A lokacin nan aka haifi Musa, shi kuwa ba kamar sauran jarirai ba ne. Wata uku aka yi renonsa a gidan mahaifinsa. Sa’ad da aka ajiye shi a waje, diyar Fir’auna ta ɗauke shi ta kuma rene shi kamar ɗanta. Musa ya sami ilimi cikin dukan hikimar Masarawa ya kuma zama mai iko cikin magana da ayyuka. “Da Musa ya cika shekara arba’in da haihuwa, sai ya yanke shawara yă ziyarci ’yan’uwansa Isra’ilawa. Ya ga ɗayansu yana shan wulaƙanci a hannun wani mutumin Masar, sai ya je ya kāre shi, ya rama masa ta wurin kashe mutumin Masar ɗin. Musa ya yi tsammani mutanensa za su gane cewa, Allah yana amfani da shi don yă cece su, amma ba su gane ba. Kashegari, Musa ya sadu da Isra’ilawa biyu suna faɗa. Ya yi ƙoƙari ya sasanta su, yana cewa, ‘Ku mutane, ku ’yan’uwa ne, don me kuke so ku cutar da juna?’ “Amma mutumin da yake wulaƙanta ɗayan, ya tura Musa a gefe ya ce, ‘Wa ya mai da kai mai mulki, da alƙali a kanmu? Kana so ka kashe ni kamar yadda ka kashe mutumin Masar nan na jiya?’ Sa’ad da Musa ya ji haka, sai ya gudu zuwa ƙasar Midiyan, inda ya yi baƙunci, ya kuma haifi ’ya’ya biyu maza. “Bayan shekaru arba’in suka wuce, sai mala’ika ya bayyana ga Musa cikin harshen wuta a ɗan itace a hamada kusa da Dutsen Sinai. Sa’ad da ya ga haka, ya yi mamakin abin da ya gani. Da ya yi kusa domin ya duba sosai, sai ya ji muryar Ubangiji ta ce, ‘Ni ne Allahn kakanninka, Allah na Ibrahim, Ishaku, da kuma Yaƙub.’ Sai Musa ya yi rawan jiki don tsoro, bai kuwa yi karambanin dubawa ba. “Sa’an nan Ubangiji ya ce masa, ‘Ka cire takalmanka; wurin da kake tsayen nan mai tsarki ne. Tabbatacce na ga wulaƙancin da ake yi wa mutanena a Masar. Na ji nishinsu na kuma sauka domin in ’yantar da su. Yanzu ka zo, zan aike ka ka koma Masar.’ “Wannan Musa ɗin da suka ƙi suna cewa, ‘Wa ya mai da kai mai mulki da kuma alƙali?’ Allah da kansa ya aike shi, ta wurin mala’ikan da ya bayyana a gare shi a ɗan itace, yă zama mai mulkinsu, da kuma mai cetonsu. Ya fitar da su daga Masar ya kuma yi ayyukan da abubuwan banmamaki a Masar, a Jan Teku, da kuma cikin hamada har shekara arba’in. “Wannan Musa ne ya ce Isra’ilawa, ‘Allah zai aika muku wani annabi kamar ni daga cikin mutanenku.’ Ya kasance a cikin taron nan a hamada, tare da mala’ikan da ya yi magana da shi a Dutsen Sinai, da kuma tare da kakanninmu; ya kuma karɓi kalmomi masu rai don yă miƙa mana. “Amma kakanninmu suka ƙi yin masa biyayya. A maimakon haka, sai suka ƙi shi a cikin zuciyarsu kuwa suka koma Masar. Suka ce wa Haruna, ‘Ka yi mana allolin da za su yi mana jagora. Game da wannan Musa ɗin wanda ya fitar da mu daga Masar, ba mu san abin da ya faru da shi ba!’ A lokacin ne suka ƙera gunki mai siffar ɗan maraƙi. Suka kawo masa hadayu suka kuma yi bikin girmama abin da suka ƙera da hannuwansu. Sai Amma Allah ya juya musu baya ya kuma ba da su ga bautar abubuwan da suke a sararin sama. Wannan ya yi daidai da abin da yake a rubuce a cikin littafin annabawa cewa, “ ‘Kun kawo mini hadayu da sadakoki shekaru arba’in cikin, hamada, ya gidan Isra’ila? Kun ɗaukaka gidan tsafin Molek, da tauraron allahnku Refan, gumakan da kuka ƙera don ku yi musu sujada. Saboda haka zan aike ku zuwa bauta’ gaba da Babilon. “Kakanni-kakanninmu suna da tabanakul na Shaida tare da su a hamada. An yi shi bisa ga yadda Allah ya umarci Musa, bisa ga zānen da ya gani. Bayan sun gāji tabanakul nan, kakanninmu a ƙarƙashin jagorancin Yoshuwa suka kawo shi tare da su, lokacin da suka ƙwace ƙasar daga al’umman da Allah ya kora a idanunsu. Tabanakul ɗin ya kasance a ƙasar har zamanin Dawuda, wanda ya sami tagomashi daga Allah, ya kuma nemi yă yi wa Allah na Yaƙub wurin zama. Amma Solomon ne ya gina masa gida. “Duk da haka, Mafi Ɗaukaka ba ya zama a gidajen da mutane suka gina. Kamar yadda annabi ya faɗi cewa, “ ‘Sama ne kursiyina, duniya kuma wurin ajiye tafin ƙafata. Wane irin gida za ka gina mini? Ko kuwa ina wurin hutuna zai kasance? In ji Ubangiji. Ba hannuna ne ya yi dukan waɗannan abubuwa ba?’ “Ku mutane masu taurinkai, da zukata da kuma kunnuwa marasa kaciya! Kuna kama da kakanninku. Kullum kuna tsayayya da Ruhu Mai Tsarki! An yi wani annabin da kakanninku ba su tsananta wa ba? Sun ma kashe waɗanda suka yi maganar zuwan Mai Adalcin nan. Yanzu kuwa kun bashe shi kuka kuma kashe shi ku da kuka karɓi dokar da aka sa a aiki ta wurin mala’iku amma ba ku yi biyayya da ita ba.” Da membobin Sanhedrin suka ji haka, sai suka yi fushi suka ciji haƙoransu. Amma Istifanus, cike da Ruhu Mai Tsarki, ya dubi sama ya kuma ga ɗaukakar Allah, da Yesu kuma tsaye a hannun dama na Allah. Ya ce, “Ga shi, na ga sama a buɗe da kuma Ɗan Mutum tsaye a hannun dama na Allah.” Da jin haka sai suka tattoshe kunnuwansu, suka kuma yi ihu da ƙarfi sosai, suka aukar masa gaba ɗaya. Suka ja shi zuwa bayan birnin suka kuma yi ta jifansa da duwatsu. Ana cikin haka, shaidun suka ajiye tufafinsu a wurin wani saurayi mai suna Shawulu. Yayinda suke cikin jifansa, sai Istifanus ya yi addu’a ya ce, “Ubangiji Yesu, ka karɓi ruhuna.” Sa’an nan ya durƙusa ya ɗaga murya ya ce, “Ubangiji, kada ka riƙe wannan zunubi a kansu.” Da ya faɗi haka, sai ya yi barci. Shawulu kuwa yana can, yana tabbatar da mutuwarsa. A wannan rana wani babban tsanani ya auka wa ikkilisiyar da take a Urushalima, sai duka suka warwatsu ko’ina a Yahudiya da Samariya, manzanni kaɗai ne suka rage. Mutane masu tsoron Allah suka binne Istifanus suka kuma yi makoki ƙwarai dominsa. Amma Shawulu ya fara hallaka ikkilisiya. Yana shiga gida-gida, yana jan maza da mata yana jefa su cikin kurkuku. Waɗanda aka wartsar suka yi ta wa’azin maganar a duk inda suka tafi. Filibus ya gangara zuwa wani birni a Samariya ya kuma yi shelar Kiristi a can. Sa’ad da taron mutane suka ji Filibus suka kuma ga abubuwan banmamakin da ya yi, sai duk suka mai da hankali sosai ga abin da ya faɗa. Mugayen ruhohi suka fiffito suna kururuwa daga cikin mutane da yawa, shanyayyu da guragu masu yawa suka sami warkarwa. Saboda haka aka yi farin ciki ƙwarai a birnin. To, akwai wani mutum mai suna Siman wanda ya kwana biyu yana yin sihiri a birnin har ya ba wa duk mutanen Samariya mamaki. Ya kuma yi taƙama cewa shi wani mai girma ne, dukan mutane kuwa, manyan da ƙanana, suka mai da hankali gare shi suka kuma ce, “Mutumin nan shi ne ikon Allah da aka sani a matsayin Iko Mai Girma” Suka bi shi domin ya daɗe yana ba su mamaki da sihirinsa. Amma da suka gaskata da Filibus sa’ad da yake wa’azin labari mai daɗi na mulkin Allah da kuma sunan Yesu Kiristi, sai aka yi musu baftisma, maza da mata. Siman kansa ya gaskata aka kuma yi masa baftisma. Ya kuma bi Filibus ko’ina, yana mamakin manyan alamu da ayyukan banmamakin da ya gani. Sa’ad da manzannin da suke a Urushalima suka ji cewa Samariya ta karɓi maganar Allah, sai suka aika musu da Bitrus da Yohanna. Da suka iso, sai suka yi musu addu’a domin su karɓi Ruhu Mai Tsarki, domin Ruhu Mai Tsarki bai riga ya sauka wa waninsu ba tukuna, an dai yi musu baftisma ne kawai a cikin sunan Ubangiji Yesu. Sa’an nan Bitrus da Yohanna suka ɗibiya hannuwansu a kansu, suka kuwa karɓi Ruhu Mai Tsarki. Sa’ad da Siman ya ga cewa ana ba da Ruhu ta wurin ɗibiya hannuwan manzannin, sai ya miƙa musu kuɗi, ya ce, “Ni ma ku ba ni wannan iyawa don kowa na ɗibiya wa hannuwana yă karɓi Ruhu Mai Tsarki.” Bitrus ya amsa ya ce, “Bari kuɗinka ya hallaka tare da kai, domin ka yi tsammani za ka iya saya kyautar Allah da kuɗi! Ba ruwanka da wannan hidimar, domin zuciyarka ba daidai take a gaban Allah ba. Ka tuba daga wannan mugunta ka kuma yi addu’a ga Ubangiji. Wataƙila zai gafarta maka don irin tunanin da yake a zuciyarka. Gama na lura kana cike da ɗacin rai kana kuma daure cikin zunubi.” Sai Siman ya amsa ya ce, “Ku yi addu’a ga Ubangiji saboda ni don kada ko ɗaya daga cikin abin da ka faɗa ya same ni.” Sa’ad da suka yi shaidar suka kuma yi shelar maganar Ubangiji, sai Bitrus da Yohanna suka koma Urushalima, suna wa’azin bishara a ƙauyukan Samariya masu yawa. To wani mala’ikan Ubangiji ya ce wa Filibus, “Ka yi kudu zuwa hanyar, hanyar hamada, da ta gangara daga Urushalima zuwa Gaza.” Saboda haka ya kama hanya, a kan hanyarsa kuwa sai ya sadu da wani mutumin Itiyofiya, wanda yake bābā, hafsa mai muhimmanci wanda yake lura da dukan ma’ajin Kandas (wanda yake nufin “sarauniyar mutanen Itiyofiya”). Mutumin nan ya tafi Urushalima ne domin yin sujada, a kan hanyarsa ta komawa gida kuwa yana zaune bisan keken yaƙinsa yana karatun littafin annabin Ishaya. Sai Ruhu ya ce wa Filibus, “Matsa wurin kekunan yaƙin nan ka yi kusa da ita.” Sai Filibus ya ruga zuwa wajen keken yaƙin ya kuma ji mutumin yana karatun littafin annabin Ishaya. Filibus ya yi tambaya ya ce, “Ka fahimci abin da kake karantawa?” Sai ya ce, “Ina fa zan iya, in ba dai wani ya fassara mini ba?” Saboda haka sai ya gayyaci Filibus yă hau yă zauna tare da shi. Bābān yana karanta wannan Nassin, “An ja shi kamar tunkiya zuwa mayanka, kuma kamar ɗan rago a hannun mai askin gashinsa yake shiru, haka kuwa bai buɗe bakinsa ba. A cikin wulaƙacinsa aka hana masa gaskiya. Wa zai iya yin zancen zuriyarsa? Gama an ɗauke ransa daga duniya.” Sai bābān ya tambayi Filibus ya ce, “Ka gaya mini, ina roƙonka, annabin yana magana a kan wane ne, kansa ne, ko kuwa wani dabam?” Sa’an nan Filibus ya fara da wannan Nassi ɗin ya kuma faɗa masa labari mai daɗi game da Yesu. Yayinda suke cikin tafiya a kan hanya, sai suka iso wani wurin ruwa bābān nan ya ce, “Duba, ga ruwa. Me zai hana a yi mini baftisma?” Ya kuwa ba da umarni a tsai da keken yaƙin. Sa’an nan da Filibus da bābān suka gangara zuwa cikin ruwan Filibus kuwa ya yi masa baftisma. Sa’ad da suka fita daga cikin ruwan, sai Ruhun Ubangiji ya fyauce Filibus, bābān kuwa bai ƙara ganinsa ba, amma ya ci gaba da tafiyarsa yana farin ciki. Filibus kuwa ya fito a Azotus, ya yi ta zagawa, yana wa’azin bishara a dukan garuruwan sai da ya kai Kaisariya. Ana cikin haka, Shawulu ya ɗage yana barazana yin kisa da tsananta wa almajiran Ubangiji. Sai ya je wurin babban firist ya roƙe shi ya ba shi wasiƙu zuwa majami’un Damaskus, don in ya sami wani a wurin wanda yake bin wannan Hanya, ko maza ko mata, yă kama su a matsayin ’yan kurkuku yă kai Urushalima. Da ya yi kusa da Damaskus a kan hanyarsa, ba zato ba tsammani sai wani haske daga sama ya haskaka kewaye da shi. Sai ya fāɗi a ƙasa ya kuma ji wata murya ta ce masa, “Shawulu, Shawulu, don me kake tsananta mini?” Shawulu ya yi tambaya ya ce, “Wane ne kai, ya Ubangiji?” Ya amsa ya ce, “Ni ne Yesu wanda kake tsananta wa. Yanzu ka tashi ka shiga cikin birnin, za a kuma gaya maka abin da dole za ka yi.” Mutanen da suke tafiya tare da Shawulu suka rasa bakin magana; sun ji muryar amma ba su ga kowa ba. Shawulu ya tashi daga ƙasa, amma sa’ad da ya buɗe idanunsa bai iya ganin wani abu ba. Saboda haka aka kama hannunsa aka yi masa jagora zuwa cikin Damaskus. Kwana uku yana a makance, bai ci ba bai kuma sha kome ba. A Damaskus kuwa akwai wani almajiri mai suna Ananiyas. Ubangiji ya kira shi a cikin wahayi ya ce, “Ananiyas!” Ananiyas ya amsa, “Ga ni, ya Ubangiji.” Ubangiji ya ce masa, “Je gidan Yahuda da yake a Miƙaƙƙen Titi ka yi tambaya ko akwai wani mutum daga Tarshish mai suna Shawulu, gama ga shi yana addu’a. Cikin wahayi ya ga wani mutum mai suna Ananiyas ya zo ya sa hannuwansa a kansa don yă sāke samun ganin gari.” Ananiyas ya amsa ya ce, “Ubangiji, na ji labarin mutumin nan sosai da kuma duk lahanin da ya yi wa tsarkakanka a Urushalima. Ga shi kuma ya zo nan da izinin manyan firistoci, don yă kama duk wanda yake kiran bisa sunanka.” Amma Ubangiji ya ce wa Ananiyas, “Je ka! Wannan mutum zaɓaɓɓen kayan aikina ne don yă kai sunana a gaban Al’ummai da sarakunansu da kuma a gaban mutanen Isra’ila. Zan nuna masa wahalar da dole zai sha saboda sunana.” Sa’an nan Ananiyas ya tafi gidan ya kuma shiga ciki. Da ya sa hannuwansa a kan Shawulu, sai ya ce, “Ɗan’uwana Shawulu, Ubangiji, Yesu, wanda ya bayyana gare ka a kan hanya yayinda kake zuwa nan, ya aiko ni domin ka sāke gani a kuma cika ka da Ruhu Mai Tsarki.” Nan da nan, sai wani abu kamar ɓawo ya fāɗo daga idanun Shawulu, ya kuma sāke iya ganin gari. Sai ya tashi aka kuma yi masa baftisma, bayan ya ci abinci, sai sāke samun ƙarfi. Shawulu ya yi kwanaki masu yawa tare da almajiran da suke a Damaskus. Nan take ya fara wa’azi cikin majami’u cewa Yesu Ɗan Allah ne. Dukan waɗanda suka ji shi suka yi mamaki suka ce, “Ba shi ne mutumin da ya tā-da-na-zaune-tsaye a kan masu kira bisa ga wannan sunan a Urushalima ba? Ba ya zo nan ne don yă kai su a matsayin ’yan kurkuku ga manyan firistoci ba?” Duk da haka Shawulu ya yi ta ƙara ƙarfi, ya kuma rikitar da Yahudawan da suke zaune a Damaskus, ta wurin tabbatar musu cewa, Yesu shi ne Kiristi. Bayan kwanaki masu yawa, sai Yahudawa suka haɗa baki su kashe shi, amma Shawulu ya sami labarin shirinsu. Dare da rana suka yi fakonsa a ƙofofin birnin don su kashe shi. Amma almajiransa suka ɗauke shi da dare suka saukar da shi a cikin kwando ta taga a katanga. Da ya zo Urushalima, ya yi ƙoƙarin shiga cikin almajiran amma dukansu suka ji tsoronsa, ba su gaskata cewa tabbatacce shi almajiri ba ne. Amma Barnabas ya ɗauke shi ya kawo shi wurin manzanni. Ya gaya musu yadda Shawulu a kan hanyarsa ya ga Ubangiji kuma cewa Ubangiji ya yi magana da shi, da yadda a Damaskus ya yi wa’azi ba tsoro a cikin sunan Yesu. Saboda haka Shawulu ya zauna tare da su yana kai da kawowa a sake a cikin Urushalima, yana magana gabagadi a cikin sunan Ubangiji. Ya yi magana ya kuma yi muhawwara da Yahudawa masu jin Hellenanci, amma suka yi ƙoƙarin kashe shi. Sa’ad da ’yan’uwa suka sami labarin wannan, sai suka ɗauke shi zuwa Kaisariya suka aika da shi Tarshish. Sa’an nan ikkilisiya ko’ina a Yahudiya, Galili da kuma Samariya ta sami salama. Ta yi ƙarfi; ta kuma ƙarfafa ta wurin Ruhu Mai Tsarki, ta ƙaru sosai tana rayuwa cikin tsoron Ubangiji. Da Bitrus yake zazzaga ƙasar, sai ya je ya ziyarci tsarkakan da suke a Lidda. A can ya tarar da wani mutum mai suna Eniyas, shanyayye wanda yake kwance kan gado shekara takwas. Sai Bitrus ya ce masa, “Eniyas, Yesu Kiristi ya warkar da kai. Tashi ka naɗe tabarmarka.” Nan da nan Eniyas ya tashi. Duk waɗanda suke zama a Lidda da Sharon suka gan shi suka kuma juyo ga Ubangiji. A Yoffa akwai wata almajira mai suna Tabita (a harshen Girik sunanta shi ne Dokas ); ita mai aikin alheri ce kullum, tana kuma taimakon matalauta. A lokacin nan ta yi rashin lafiya ta mutu, aka kuma yi wa gawarta wanka aka ajiye a wani ɗaki a gidan sama. Lidda yana kusa da Yoffa; saboda haka sa’ad da almajirai suka ji cewa Bitrus yana a Lidda, sai suka aiki mutum biyu wurinsa su roƙe shi cewa, “In ka yarda ka zo nan da nan!” Sai Bitrus ya tafi tare da su, sa’ad da ya iso sai aka kai shi ɗakin saman. Duka gwauraye suka tsaya kewaye da shi, suna kuka suna nunnuna masa riguna da kuma waɗansu tufafin da Dokas ta yi yayinda take tare da su. Bitrus ya fitar da su duka daga ɗakin; sa’an nan ya durƙusa ya yi addu’a. Da ya juya wajen matacciyar, sai ya ce, “Tabita, tashi.” Ta buɗe idanunta, ta ga Bitrus sai ta tashi zaune. Ya kama ta a hannu ya taimake ta ta tsaya a ƙafafunta. Sa’an nan ya kira masu bi da kuma gwaurayen ya miƙa musu ita da rai. Wannan ya zama sananne ko’ina a Yoffa, mutane da yawa kuma suka gaskata da Ubangiji. Bitrus ya zauna a Yoffa na ɗan lokaci tare da wani mai aikin fatu mai suna Siman. A Kaisariya akwai wani mutum mai suna Korneliyus, wani jarumin Roma ne, a ƙungiyar soja da ake kira Bataliyar Italiya. Shi da dukan iyalinsa masu ibada ne masu tsoron Allah kuma; yakan ba da kyauta hannu sake ga masu bukata yana kuma addu’a ga Allah ba fasawa. Wata rana wajen ƙarfe uku na yamma ya ga wahayi. A sarari ya ga wani mala’ikan Allah, wanda ya zo wajensa ya ce, “Korneliyus!” Korneliyus kuwa ya zura masa ido a tsorace ya ce, “Mene ne, ya Ubangiji?” Mala’ikan ya ce, “Addu’o’inka da kyautanka ga matalauta sun kai har sama, hadayar tunawa ce a gaban Allah. Yanzu sai ka aiki mutane zuwa Yoffa su dawo da wani mutum mai suna Siman wanda ake kira Bitrus. Yana zama tare da Siman, mai aikin fatu, wanda gidansa ke bakin teku.” Sa’ad da mala’ikan da ya yi masa magana ya tafi, sai Korneliyus ya kira biyu daga cikin bayinsa da kuma wani soja mai ibada wanda yake ɗaya a cikin masu yin masa hidima. Ya fada musu duk abin da ya faru sa’an nan ya aike su Yoffa. Wajen tsakar rana kashegari yayinda suke cikin tafiyarsu suna kuma dab da birnin, sai Bitrus ya hau bisan rufin gida yă yi addu’a. Yunwa ta kama shi ya kuwa so yă ci wani abu, yayinda ake shirya abinci, sai wahayi ya zo masa. Ya ga sama ya buɗe ana kuwa saukowa wani abu ƙasa kamar babban mayafi zuwa duniya ta kusurwansa huɗu. Cikinsa kuwa akwai kowace irin dabba mai ƙafa huɗu da masu ja da ciki na duniya da kuma tsuntsayen sararin sama. Sa’an nan wata murya ta ce masa, “Bitrus, ka tashi. Ka yanka ka ci.” Bitrus ya ce, “Sam, Ubangiji! Ban taɓa cin wani abu marar tsarki ko marar tsabta ba.” Muryar ta yi magana da shi sau na biyu ta ce, “Kada ka ce da abin da Allah ya tsarkake marar tsarki.” Wannan ya faru har sau uku, sai nan da nan aka ɗauke mayafin zuwa sama. Tun Bitrus yana cikin tunani game da ma’anar wahayin nan, sai ga mutanen da Korneliyus ya aika sun sami gidan Siman suna kuma tsaye a ƙofar. Suka yi sallama, suna tambaya ko Siman wanda aka sani da suna Bitrus yana zama a can. Yayinda Bitrus yana cikin tunani game da wahayin, sai Ruhu ya ce masa, “Siman, ga mutum uku suna nemanka. Saboda haka ka tashi ka sauka. Kada ka yi wata-wata, gama ni ne na aiko su.” Sai Bitrus ya sauka ya ce wa mutanen, “Ni ne kuke nema. Me ya kawo ku?” Mutanen suka amsa, “Mun zo ne daga wurin Korneliyus wani jarumin. Shi mutum ne mai adalci mai tsoron Allah kuma, wanda dukan Yahudawa ke girmamawa. Wani mala’ika mai tsarki ya faɗa masa, yă sa ka zo gidansa don yă ji abin da za ka faɗa.” Sai Bitrus ya gayyaci mutanen cikin gida su zama baƙinsa. Kashegari Bitrus ya tafi tare da su, waɗansu ’yan’uwa daga Yoffa kuwa suka tafi tare da shi. Kashegari sai ya iso Kaisariya. Korneliyus kuwa yana nan yana jiransu, ya kuma gayyaci ’yan’uwansa da abokansa na kusa. Da Bitrus ya shiga gidan, Korneliyus ya sadu da shi ya kuma fāɗi a gabansa cikin bangirma. Amma Bitrus ya sa shi ya tashi. Ya ce, “Tashi, ni mutum ne kawai.” Yana magana da shi, sai Bitrus ya shiga ciki ya kuma tarar da taron mutane da yawa. Sai ya ce musu, “Ku da kanku kun san cewa dokarmu ta hana mutumin Yahuda yin cuɗanya, ko ya ziyarci Ba’al’umme. Amma Allah ya nuna mini cewa kada in kira wani mutum marar tsarki ko marar tsabta. Don haka sa’ad da aka aika in zo, na zo ba wata faɗa. To, ko zan san abin da ya sa ka aika in zo?” Korneliyus ya amsa ya ce, “Kwana huɗu da suka wuce ina a gidana ina addu’a a wannan lokaci, wajen ƙarfe uku na yamma. Ba zato ba tsammani sai ga wani mutum cikin tufafi masu walƙiya ya tsaya a gabana ya ce, ‘Korneliyus, Allah ya ji addu’arka, ya kuma tuna da kyautanka ga matalauta. Ka aika zuwa Yoffa don a kira Siman wanda ake ce da shi Bitrus. Shi baƙo ne a gidan Siman mai aikin fatu, wanda yake zama a bakin teku.’ Saboda haka na aika a zo da kai nan da nan, ya kuma yi kyau da ka zo. To ga mu duka a nan a gaban Allah don mu saurari dukan abin da Ubangiji ya umarce ka ka faɗa mana.” Sa’an nan Bitrus ya fara magana ya ce, “Yanzu na gane yadda gaskiya ne cewa Allah ba ya sonkai amma yana karɓan mutane daga kowace al’ummar da take tsoronsa suke kuma aikata abin da yake daidai. Kun san saƙon da Allah ya aika wa mutanen Isra’ila, yana shelar labari mai daɗi na salama ta wurin Yesu Kiristi, shi ne kuwa Ubangijin kowa. Kun san abin da ya faru a dukan Yahudiya, farawa daga Galili bayan baftismar da Yohanna ya yi wa’azi, yadda Allah ya shafe Yesu Banazare da Ruhu Mai Tsarki da kuma iko, da kuma yadda ya zaga ko’ina yana aikata alheri yana kuma warkar da dukan waɗanda suke ƙarƙashin ikon Iblis, domin Allah yana tare da shi. “Mu kuwa shaidu ne na dukan abin da ya yi a ƙasar Yahudawa da kuma a Urushalima. Suka kashe shi ta wurin rataye shi a kan itace, amma Allah ya tashe shi daga matattu a rana ta uku, ya sa kuma aka gan shi. Ba dukan mutane ne suka gan shi ba, amma ta wurin shaidun da Allah ya riga ya zaɓa, ta wurinmu da muka ci muka kuma sha tare da shi bayan tashinsa daga matattu. Ya umarce mu mu yi wa’azi ga mutane mu kuma shaida cewa shi ne wanda Allah ya naɗa yă zama mai shari’a na masu rai da na matattu. Duk annabawa sun yi shaida game da shi cewa duk wanda ya ba da gaskiya gare shi zai sami gafarar zunubai ta wurin sunansa.” Tun Bitrus yana cikin faɗin waɗannan kalmomi, sai Ruhu Mai Tsarki ya sauka wa duk waɗanda suka ji saƙon. Masu bin da suke da kaciya waɗanda suka zo tare da Bitrus suka yi mamaki cewa an ba da kyautar Ruhu Mai Tsarki har ma a kan Al’ummai. Gama sun ji su suna magana da waɗansu harsuna suna kuma yabon Allah. Sai Bitrus ya ce, “Wani zai iya hana a yi wa waɗannan mutane baftisma da ruwa? Sun karɓi Ruhu Mai Tsarki kamar yadda muka karɓa.” Saboda haka ya ba da umarni a yi musu baftisma cikin sunan Yesu Kiristi. Sa’an nan suka roƙi Bitrus yă zauna da su na ’yan kwanaki. Manzanni da ’yan’uwa ko’ina a Yahudiya suka ji cewa Al’ummai ma sun karɓi maganar Allah. Saboda haka sa’ad da Bitrus ya haura zuwa Urushalima, masu bin da suke da kaciya suka zarge shi suka ce, “Ka je gidan mutanen da suke marasa kaciya ka kuwa ci tare da su.” Bitrus ya fara yin musu bayani dalla-dalla yadda ya faru cewa, “Ina a birnin Yoffa ina addu’a, sai ga wahayi ya zo mini. Na ga ana sauko da wani abu kamar babban mayafi daga sama ta kusurwansa huɗu, ya kuma sauko inda nake. Na duba cikinsa na ga dabbobi masu ƙafa huɗu na duniya, da namun jeji, da masu ja da ciki, da kuma tsuntsayen sararin sama. Sa’an nan na ji wata murya tana ce mini, ‘Bitrus, ka tashi. Ka yanka ka ci.’ “Na amsa na ce, ‘Sam, Ubangiji! Ban taɓa cin wani abu marar tsarki ko marar tsabta ba.’ “Sai muryar daga sama ta yi magana sau na biyu, ta ce, ‘Kada ka ce da abin da Allah ya tsarkake marar tsarki.’ Wannan ya faru har sau uku, sa’an nan duk aka sāke ɗauke shi zuwa sama. “Nan take sai ga mutum uku da aka aika wurina daga Kaisariya a tsaye a ƙofar gidan da nake. Ruhu ya ce mini kada in yi wata-wata game da tafiya tare da su. Waɗannan ’yan’uwa guda shida su ma suka rako ni, muka kuwa shiga gidan mutumin. Ya kuma gaya mana yadda wani mala’ika ya bayyana a gidansa ya ce masa, ‘Ka aika zuwa Yoffa a kira Siman wanda ake ce da shi Bitrus. Zai kawo maka saƙo wanda ta wurinsa kai da dukan iyalinka za ku sami ceto.’ “Na fara magana ke nan, sai Ruhu Mai Tsarki ya sauko musu yadda ya sauko mana a farko. Sa’an nan na tuna da abin da Ubangiji ya ce, ‘Yohanna ya yi baftisma da ruwa, amma za a yi muku baftisma da Ruhu Mai Tsarki.’ To, in Allah ya ba su kyauta yadda ya ba mu, mu da muka gaskata da Ubangiji Yesu Kiristi, wane ni da zan yi hamayya da Allah?” Sa’ad da suka ji haka, ba su ƙara yin faɗa ba, suka kuma ɗaukaka Allah, suna cewa, “To, fa, har Al’ummai ma Allah ya sa suka tuba zuwa rai.” To, waɗanda suka warwatsu saboda tsananin da ya tashi a kan batun Istifanus suka tafi har Funisiya, Saifurus da kuma Antiyok, suna ba da saƙon ga Yahudawa kaɗai. Amma waɗansunsu kuwa, mutane daga Saifurus da Sairin, suka je Antiyok suka fara yi wa Hellenawa magana su ma, suna ba da labari mai daɗi game da Ubangiji Yesu. Hannun Ubangiji kuwa yana tare da su, mutane da yawan gaske kuwa suka gaskata suka juya ga Ubangiji. Labari wannan abu ya kai kunnuwan ikkilisiya a Urushalima, sai suka aiki Barnabas zuwa Antiyok. Da ya iso ya kuma ga tabbacin alherin Allah, sai ya yi farin ciki ya kuma ƙarfafa su duka su tsaya da gaskiya cikin Ubangiji da dukan zukatansu. Mutum ne nagari, cike da Ruhu Mai Tsarki da bangaskiya, mutane masu yawan gaske kuwa suka juya ga Ubangiji. Sa’an nan Barnabas ya tafi Tarshish don yă nemi Shawulu, sa’ad da ya same shi kuwa, sai ya kawo shi Antiyok. Ta haka shekara guda cur Barnabas da Shawulu suka yi suna taruwa da ikkilisiya, suka kuma koya wa mutane masu yawan gaske. A Antiyok ne aka fara kiran almajirai da suna Kirista. A wannan lokaci waɗansu annabawa sun zo Antiyok daga Urushalima. Ɗaya daga cikinsu mai suna Agabus, ya miƙe tsaye ya yi annabci ta wurin Ruhu cewa za a yi yunwa mai tsanani wadda za tă bazu a dukan duniyar Romawa (Wannan ya faru a zamanin mulkin Kalaudiyus.) Kowanne a cikin almajiran, gwargwadon azancinsa, ya yanke shawara ya ba da gudummawa ga ’yan’uwan da suke zama a Yahudiya. Haka kuwa suka yi, suka aika da kyautarsa wa dattawan ikkilisiyar ta hannu Barnabas da Shawulu. Kusan a wannan lokaci ne Sarki Hiridus ya kama waɗansu da suke na ikkilisiya, da niyya ya tsananta musu. Ya sa aka kashe Yaƙub, ɗan’uwan Yohanna, da takobi. Sa’ad da ya ga wannan ya faranta wa Yahudawa rai, sai ya kama Bitrus shi ma. Wannan ya faru kwanakin Bikin Burodi Marar Yisti. Bayan ya kama shi, sai ya sa shi a kurkuku, ya danƙa shi a hannun soja hurhuɗu kashi huɗu, don su yi gadinsa. Hiridus ya yi niyyar ya yi masa shari’a a gaban mutane bayan Bikin Ƙetarewa. Saboda haka aka tsare Bitrus a kurkuku, amma ikkilisiya ta nace da addu’a ga Allah dominsa. A daren da in gari ya waye da Hiridus yake niyyar kawo shi domin a yi masa shari’a, Bitrus yana barci tsakanin sojoji biyu, daure da sarƙoƙi biyu, masu gadi kuma suna bakin ƙofa. Ba zato ba tsammani sai mala’ikan Ubangiji ya bayyana haske kuma ya haskaka a ɗakin. Ya bugi Bitrus a gefe ya kuma tashe shi ya ce, “Maza, ka tashi!” Sarƙoƙin kuwa suka zube daga hannuwansa. Sa’an nan mala’ikan ya ce masa, “Ka sa rigunarka da takalmanka.” Bitrus kuwa ya sa. Mala’ikan ya faɗa masa cewa, “Ka yafa mayafinka ka bi ni.” Bitrus ya bi shi suka fita kurkukun, amma bai ma san cewa abin da mala’ikan yake yi tabbatacce ne ba; yana tsammani wahayi yake gani. Suka wuce masu gadi na fari da na biyu, suka kuma isa ƙofar ƙarfe ta shiga birni. Ƙofar kuwa ta buɗe musu da kanta, suka kuma wuce. Sa’ad da suka yi tafiya tsawon wani titi, nan take mala’ikan ya bar shi. Sai Bitrus ya dawo hankalinsa ya ce, “Yanzu na sani ba shakka Ubangiji ne ya aiki mala’ikansa yă cece ni daga hannun Hiridus da kuma dukan mugun fatan Yahudawa.” Da ya gane haka, sai ya tafi gidan Maryamu uwar Yohanna, wanda ake kuma kira Markus, inda mutane da yawa suka taru suna addu’a. Bitrus ya ƙwanƙwasa ƙofar waje, sai wata mai aiki a gidan da ake kira Roda ta zo tă ji ko wane ne. Da ta gane muryar Bitrus, ta cika da murna ta gudu ta koma ba tare da ta buɗe ƙofar ba, sai ta koma a guje ta ce da ƙarfi, “Ga Bitrus a bakin ƙofa!” Sai suka ce mata, “Kina hauka.” Da ta nace cewa shi ne, sai suka ce, “To, lalle, mala’ikansa ne.” Amma Bitrus ya yi ta ƙwanƙwasawa. Da suka buɗe ƙofar suka kuma gan shi, sai suka yi mamaki. Bitrus ya yi musu alama da hannunsa su yi shiru sai ya bayyana yadda Ubangiji ya fitar da shi daga kurkuku. Ya ce, “Ku gaya wa Yaƙub da kuma ’yan’uwa game da wannan,” sa’an nan ya tashi ya tafi wani wuri. Da safe, hargitsin da ya tashi tsakanin sojojin ba ƙarami ba ne, a kan abin da ya sami Bitrus. Bayan Hiridus ya neme shi bai same shi ba, sai ya tuhumi masu gadin, ya kuma ba da umarni a kashe su. Sa’an nan Hiridus ya tashi daga Yahudiya ya tafi Kaisariya ya kuma yi ’yan kwanaki a can. Yana da rashin jituwa da mutanen Taya da na Sidon; sai suka haɗa kai suka nemi ganawa da shi. Bayan suka sami goyon bayan Bilastus, amintaccen bawan sarki, sai suka nemi salama, domin sun dogara ga ƙasar sarkin don samun abincinsu. A ranar da aka shirya Hiridus, sanye da kayan sarautarsa, ya zauna a gadon sarautarsa ya kuma ya wa mutanen jawabi. Suka tā da murya suka ce, “Wannan muryar wani allah ne, ba ta mutum ba.” Nan take, domin Hiridus bai yi wa Allah yabo ba, wani mala’ikan Ubangiji ya buge shi, tsutsotsi kuwa suka cinye shi ya kuma mutu. Amma maganar Allah ta ci gaba da ƙaruwa ta kuma bazu. Sa’ad da Barnabas da Shawulu suka kammala aikinsu, sai suka komo daga Urushalima, tare da Yohanna, wanda ake kira Markus. A ikkilisiyar da take a Antiyok akwai waɗansu annabawa da malamai. Barnabas, Siman wanda ake kira Baƙi, Lusiyus mutumin Sairin, Manayen (wanda aka goya tare da Hiridus mai mulki), da kuma Shawulu. Yayinda suna cikin sujada da azumi ga Ubangiji, Ruhu Mai Tsarki ya ce, “Ku keɓe mini Barnabas da Shawulu domin aikin da na kira su.” Saboda haka bayan suka yi azumi da addu’a, sai suka ɗibiya musu hannuwansu a kansu suka sallame su. Sai su biyu da Ruhu Mai Tsarki ya aika suka gangara zuwa Selusiya suka shiga jirgin ruwa daga can zuwa Saifurus. Da suka isa Salamis, sai suka yi shelar maganar Allah a majami’un Yahudawa. Yohanna yana tare da su a matsayin mai taimakonsu. Suka zaga dukan tsibirin har sai da suka kai Bafos. A can suka sadu da wani mutumin Yahuda mai sihiri, annabin ƙarya, mai suna Bar-Yesu, wanda yake ma’aikacin muƙaddas Sergiyus Bulus ne. Muƙaddas ɗin kuwa mai azanci ne ƙwarai, ya sa aka kira Barnabas da Shawulu don yana so ya ji maganar Allah. Amma Elimas mai sihirin nan (domin ma’anar sunansa ke nan) ya yi hamayya da maganarsu ya kuma yi ƙoƙari ya juyar da muƙaddas ɗin daga bangaskiya. Sai Shawulu, wanda kuma ake kira Bulus, cike da Ruhu Mai Tsarki, ya kafa wa Elimas ido ya ce, “Kai ɗan Iblis ne abokin gāban dukan abin da yake daidai! Kana cike da kowane irin ruɗi da munafunci. Ba za ka daina karkata hanyoyin da suke daidai na Ubangiji ba? Ga shi hannun Ubangiji yana gāba da kai. Za ka makance, kuma ba za ka ga rana ba har na wani lokaci.” Nan take, hazo da duhu suka sauko a kansa, ya yi ta lallubawa, yana neman wanda zai yi masa jagora. Sa’ad da muƙaddas ɗin ya ga abin da ya faru, sai ya ba da gaskiya, gama ya yi mamaki a kan da koyarwa game Ubangiji. Bulus da abokan tafiyarsa suka tashi daga Bafos a jirgin ruwa zuwa Ferga a Famfiliya inda Yohanna ya bar su ya koma Urushalima. Daga Ferga kuwa suka ci gaba zuwa Antiyok na Fisidiya. A ranar Asabbaci sai suka shiga majami’a suka zauna. Bayan an yi karatu daga cikin Doka, da kuma Annabawa, sai shugabannin majami’ar suka aika musu suka ce, “’Yan’uwa, in kuna da wani saƙon ƙarfafawa domin jama’a, sai ku yi.” Yana miƙewa tsaye, sai Bulus ya yi musu alama da hannu ya ce, “Mutanen Isra’ila da kuma ku Al’ummai da kuke wa Allah sujada, ku saurare ni! Allahn mutanen Isra’ila ya zaɓi kakanninmu; ya kuma sa mutanen suka yi bunkasa yayinda suke zama a ƙasar Masar, da iko mai girma ya fitar da su daga ƙasar, ya kuma jure da halinsu har shekara arba’in a cikin hamada, ya tumɓuke ƙasashe bakwai a Kan’ana ya kuma ba da ƙasarsu gādo ga mutanensa. Dukan wannan ya ɗauki kusan shekaru 450. “Bayan wannan, Allah ya ba su alƙalai har zuwa zamanin annabi Sama’ila. Sa’an nan mutanen suka nemi a ba su sarki, Allah kuwa ya ba su Shawulu ɗan Kish, na kabilar Benyamin, wanda ya yi mulki shekaru arba’in. Bayan an kau da Shawulu, sai ya naɗa Dawuda ya zama sarkinsu. Ya kuma yi shaida game da shi cewa, ‘Na sami Dawuda ɗan Yesse, mutum ne da nake so a zuciyata; shi zai aikata dukan abin da nake so.’ “Daga zuriyar mutumin nan ne Allah ya kawo wa Isra’ila Mai Ceto Yesu, kamar yadda ya yi alkawari. Kafin zuwan Yesu, Yohanna ya yi wa’azin tuba da baftisma ga dukan mutanen Isra’ila. Yayinda Yohanna yake kammala aikinsa ya ce, ‘Wa kuke tsammani ni nake? Ba ni ne shi ba. A’a, amma yana zuwa bayana, wanda ko takalmansa ma ban isa in kunce ba.’ “Ya ku ’yan’uwa, ’ya’yan Ibrahim, da ku kuma Al’ummai masu tsoron Allah, a gare mu ne fa aka aiko wannan saƙon ceto. Mutanen Urushalima da masu mulkinsu ba su gane da Yesu ba, duk da haka cikin hukunta shi suka cika kalmomin annabawan da ake karantawa kowane Asabbaci. Ko da yake ba su same shi da wani dalilin da ya kai ga hukuncin kisa ba, suka roƙi Bilatus yă sa a kashe shi. Sa’ad da suka aikata duk abin da aka rubuta game da shi, sai suka saukar da shi daga itacen suka kuma sa shi a kabari. Amma Allah ya tashe shi daga matattu, kuma kwanaki da yawa waɗanda suka yi tafiya tare da shi daga Galili zuwa Urushalima suka gan shi. Su ne yanzu shaidu ga mutanenmu. “Muna gaya muku labari mai daɗi cewa abin da Allah ya yi wa kakanninmu alkawari, ya cika mana, mu zuriyarsu, ta wurin tā da Yesu daga matattu. Kamar yadda yake a rubuce a cikin Zabura ta biyu cewa, “ ‘Kai Ɗana ne, yau na zama Uba a gare ka.’ Gaskiyar cewa Allah ya tā da shi daga matattu, a kan ba zai taɓa ruɓewa ba, an faɗe shi a cikin waɗannan kalmomi. “ ‘Zan ba ku tsarki da kuma tabbatattun albarkun da na yi wa Dawuda alkawari.’ Haka kuma aka faɗa a wani wuri. “ ‘Ba za ka yarda Mai Tsarkinka ya ruɓa ba.’ “Gama sa’ad da Dawuda ya gama hidimar nufin Allah a zamaninsa, sai ya yi barci; aka binne shi tare da kakanninsa jikinsa kuwa ya ruɓe. Amma wanda Allah ya tā da daga matattu bai ruɓa ba. “Saboda haka, ’yan’uwana, ina so ku san cewa ta wurin Yesu ana sanar muku da gafarar zunubi. Ta wurinsa kowa da ya gaskata an kuɓutar da shi daga dukan abin da Dokar Musa ba tă iya kuɓutar ba. Ku lura kada abubuwan da annabawa suka faɗa su faru muku. “ ‘Ku duba, ku masu ba’a, ku yi mamaki, ku hallaka, gama zan yi wani abu a zamaninku da ba za ku taɓa gaskatawa ba ko da wani ya gaya muku.’ ” Bulus da Barnabas suna fita daga majami’ar ke nan, sai mutane suka gayyace su su ƙara yin maganan nan a kan waɗannan abubuwa a ranar Asabbaci mai zuwa. Da aka sallami jama’a, Yahudawa da yawa da kuma waɗanda suka tuba suka shiga Yahudanci masu ibada suka bi Bulus da Barnabas, waɗanda suka yi magana musu suka kuma ƙarfafa su su ci gaba a cikin alherin Allah. A ranar Asabbaci na biye kusan dukan birnin suka taru don su ji maganar Ubangiji. Sa’ad da Yahudawa suka ga taron mutanen, sai suka cika da kishi suka yi ta munanan maganganu a kan abin da Bulus yake faɗi. Sai Bulus da Barnabas suka amsa musu gabagadi, suka ce, “Ya zama mana dole mu yi muku maganar Allah da farko. Da yake kun ƙi ta ba ku kuma ga kun cancanci rai madawwami ba, to, za mu juya ga Al’ummai. Gama abin da Allah ya umarce mu ke nan cewa, “ ‘Na sa ka zama haske ga Al’ummai, don ka kawo cetona zuwa iyakokin duniya.’ ” Sa’ad da Al’ummai suka ji haka, sai suka yi farin ciki suka ɗaukaka maganar Ubangiji; kuma duk waɗanda aka zaɓa don samun rai madawwami, suka gaskata. Maganar Ubangiji kuwa ta bazu a dukan yankin. Amma Yahudawa suka zuga waɗansu mata masu tsoron Allah masu martaba da kuma waɗansu maza masu matsayi a gari. Suka tā da tsanani ga Bulus da Barnabas, suka kore su daga yankinsu. Saboda haka suka karkaɗe ƙurar ƙafafunsu don shaidar a kansu suka kuwa tafi Ikoniyum. Masu bi kuwa suka cika da farin ciki da kuma Ruhu Mai Tsarki. A Ikoniyum Bulus da Barnabas suka shiga majami’ar Yahudawa yadda suka saba. A can suka yi magana gabagadi har Yahudawa da Al’ummai masu yawa suka gaskata. Amma Yahudawan da suka ƙi ba da gaskata, suka zuga Al’ummai suka sa ɓata tsakaninsu da ’yan’uwa. Bulus da Barnabas kuwa suka daɗe sosai a can, suna magana gabagadi saboda Ubangiji, wanda kuwa ya tabbatar da saƙon alherinsa ta wurinsa su su aikata ayyuka da alamu masu banmamaki. Mutanen birnin suka rarrabu, waɗansu suka goyi bayan Yahudawa, waɗansu kuma suka goyi bayan manzannin. Yahudawa da Al’ummai tare da shugabanninsu suka ƙulla shawara a tsakaninsu, domin su wulaƙanta su su kuma jajjefe su da duwatsu. Amma suka sami labari suka kuma gudu zuwa biranen Ikoniyum na Listira da Derbe da kuma ƙauyukan kewaye, inda suka ci gaba da wa’azin labari mai daɗi. A Listira kuwa akwai wani gurgu zaune a ƙafafunsa, wanda gurgu ne tun haihuwa, kuma bai taɓa tafiya ba. Ya kasa kunne yayinda Bulus yake magana. Bulus kuma ya kafa masa ido, ya lura cewa yana da bangaskiyar da za tă warkar da shi sai ya ɗaga murya ya ce, “Tashi ka tsaya kan ƙafafunka!” Da jin haka, sai mutumin ya yi wuf ya kuma fara tafiya. Sa’ad da taron suka ga abin da Bulus ya yi, sai suka ihu da harshen Likayoniyawa, suna cewa, “Alloli sun sauka mana da siffar mutane!” Sai suka ba wa Barnabas, sunan Zeyus, Bulus kuma suka kira Hermes domin shi ne shugaban magana. Firist na Zeyus, wanda haikalinsa ke bayan birni, ya kawo bijimai da furanni a ƙofofin birni domin shi da taron mutanen sun so su miƙa musu hadayu. Amma da manzannin nan Barnabas da Bulus suka ji haka, sai suka yayyage tufafinsu suka ruga cikin taron, suna ihu suna cewa, “Ya ku mutane, don me kuke yin haka? Ai, mu ma mutane ne kawai, ’yan adam ne kamar ku. Mun kawo muku labari mai daɗi ne, muna gaya muku ku juya daga waɗannan abubuwa banza, ku juyo ga Allah mai rai, wanda ya yi sama da ƙasa da teku da kuma dukan abin da yake cikinsu. A zamanin dā, ya bar dukan ƙasashe su yi yadda suka ga dama. Duk da haka bai bar kansa babu shaida ba. Ya nuna alheri ta wurin ba ku ruwan sama da kuma amfanin gona a lokutansu; ya ba ku abinci mai yawa ya kuma cika zukatanku da farin ciki.” Ko da waɗannan kalmomi ma, da ƙyar suka hana jama’an nan yin musu hadaya. Sai waɗansu Yahudawa suka zo daga Antiyok da Ikoniyum suka sha kan taron. Suka jajjefi Bulus da duwatsu suka kuma ja shi bayan birni, suna tsammani ya mutu. Amma bayan da almajiran suka taru kewaye da shi, sai ya tashi ya koma cikin birni. Kashegari shi da Barnabas suka tashi zuwa Derbe. Suka yi wa’azin Labari mai daɗi a wannan birni, suka kuma sami almajirai da yawa. Sai suka koma Listira, Ikoniyum da kuma Antiyok, suna gina almajirai suna kuma ƙarfafa su su tsaya da gaske cikin bangaskiya. Suka ce, “Sai da shan wahaloli masu yawa za mu shiga mulkin Allah.” Bulus da Barnabas suka naɗa musu dattawa a kowace ikkilisiya, tare da addu’a da azumi, suka miƙa su ga Ubangiji, wanda suka dogara da shi. Bayan sun bi ta Fisidiya, sai suka zo cikin Famfiliya, kuma sa’ad da suka yi wa’azi a Ferga, sai suka gangara zuwa Attaliya. Daga Attaliya kuma suka shiga jirgin ruwa suka koma Antiyok, inda dā aka danƙa su ga alherin Allah saboda aikin da suka kammala yanzu. Da isarsu a can, sai suka tara ikkilisiya wuri ɗaya suka ba da rahoton duk abin da Allah ya aikata ta wurinsu da kuma yadda ya buɗe ƙofar bangaskiya domin Al’ummai. Suka kuma jima a can tare da almajirai. Waɗansu mutane suka gangara daga Yahudiya zuwa Antiyok suna kuma koya wa ’yan’uwa cewa, “Sai ko an yi muku kaciya bisa ga al’ada da Musa ya koyar, in ba haka ba, ba za ku sami ceto ba.” Wannan ya kai Bulus da Barnabas suka shiga babban gardama da muhawwara da su. Saboda haka aka naɗa Bulus da Barnabas tare da waɗansu masu bi, su haura zuwa Urushalima don su ga manzanni da dattawa a kan wannan magana. Ikkilisiya ta raka su suka tafi, yayinda suke ratsawa ta Funisiya da Samariya, suka ba da labari yadda Al’ummai suka tuba. Wannan labarin ya sa dukan ’yan’uwa suka yi murna ƙwarai. Sa’ad da suka isa Urushalima, sai ikkilisiya da manzanni da kuma dattawa suka marabce su, sai suka ba su rahoton dukan abin da Allah ya aikata ta wurinsu. Sai waɗansu daga cikin masu bin da suke na ƙungiyar Farisiyawa suka miƙe tsaye suka ce, “Dole ne a yi wa Al’ummai kaciya a kuma bukace su su yi biyayya da dokokin Musa.” Sai manzanni da dattawa suka taru don su duba maganar. Bayan aka yi muhawwara da sosai, sai Bitrus ya miƙe tsaye ya yi musu jawabi ya ce, “’Yan’uwa, kun san cewa a kwanakin baya Allah ya yi zaɓe a cikinku don Al’ummai su ji daga leɓunana saƙon bishara su kuma gaskata. Allah, wanda ya san zuciya, ya nuna cewa ya karɓe su ta wurin ba su Ruhu Mai Tsarki, kamar yadda ya ba mu. Bai nuna bambanci tsakaninmu da su ba, gama ya tsarkake zukatansu ta wurin bangaskiya. To, fa, don me kuke ƙoƙari ku gwada Allah ta wurin ɗora wa almajiran nan kayan da mu ko kakanninmu ba mu iya ɗauka ba? A’a! Mun gaskata cewa ta wurin alherin Ubangiji Yesu ne muka sami ceto, kamar yadda su ma suka samu.” Sai duk taron suka yi tsit yayinda suke sauraron Barnabas da Bulus suna ba da labari game da ayyuka da kuma abubuwan banmamakin da Allah ya yi a cikin Al’ummai ta wurinsu. Da suka gama, sai Yaƙub ya yi magana ya ce, “’Yan’uwa, ku saurare ni. Siman ya bayyana mana yadda Allah da farko ya nuna damuwarsa ta wurin ɗaukan mutane daga cikin Al’ummai su zama nasa. Kalmomin annabawa sun yi daidai da wannan, kamar yadda yake a rubuce cewa, “ ‘Bayan wannan zan koma in kuma sāke gina tentin Dawuda da ya rushe. Kufansa zan sāke gina, in kuma mai da shi, don ragowar mutane su nemi Ubangiji, kuma duk Al’umman da suke kira bisa sunana, in ji Ubangiji, wanda yake yin waɗannan abubuwa’ da aka sani tun zamanai. “Saboda haka, a ganina, kada mu matsa wa Al’ummai waɗanda suke juyowa ga Allah. A maimakon haka, ya kamata mu rubuta musu cewa, su guji abincin da alloli suka ƙazantar, da fasikanci, da naman dabbar da aka murɗe da kuma jini. Gama Musa ya yi wa’azi a kowace birni tun zamanin dā, ana kuma karanta shi a majami’u kowane Asabbaci.” Sai manzanni da dattawa, tare da dukan ikkilisiya, suka yanke shawara su zaɓi waɗansu daga cikin mutanensu su kuma aike su zuwa Antiyok tare da Bulus da Barnabas. Sai suka zaɓi Yahuda (wanda ake kira Barsabbas) da kuma Sila, mutum biyu da suke shugabanni cikin ’yan’uwa. Tare da su suka aika da wannan wasiƙa. Daga manzanni da dattawa, ’yan’uwanku. Zuwa ga Al’ummai masu bi a Antiyok, Suriya da Silisiya. Gaisuwa. Mun ji cewa, waɗansu da sun fita daga cikinmu ba tare da izininmu ba suka kuma dame ku, suna tā da hankalinku ta wurin abin da suka ce. Saboda haka dukanmu mun yarda mu zaɓi waɗansu mutane mu kuma aike su wurinku tare da ƙaunatattun abokanmu Barnabas da Bulus  mutanen da suka sa rayukansu cikin hatsari saboda sunan Ubangijinmu Yesu Kiristi. Saboda haka muna aika Yahuda da Sila don su tabbatar muku da baki abin da muka rubuta. Ya gamshe Ruhu Mai Tsarki da mu ma kada a ɗora muku nauyi fiye da na waɗannan abubuwa. Ku guji abincin da aka yi wa alloli hadaya, da jini, da naman dabbar da aka murɗe da kuma fasikanci. Za ku kyauta in kun kiyaye waɗannan abubuwa. Ku huta lafiya. Aka sallami mutanen sai suka gangara zuwa Antiyok, inda suka tara ikkilisiya wuri ɗaya suka ba da wasiƙar. Mutanen suka karantata suka kuma yi farin ciki saboda saƙonta mai ƙarfafawa. Yahuda da Sila, waɗanda su kansu annabawa ne, suka yi magana sosai don su gina su kuma ƙarfafa ’yan’uwa. Bayan suka yi ’yan kwanaki a can, sai ’yan’uwa suka sallame su da albarkar salama su dawo wurin waɗanda suka aike su. Amma Bulus da Barnabas kuwa suka dakata a Antiyok, inda su da waɗansu da yawa suka yi koyarwa suka kuma yi wa’azin maganar Ubangiji. Bayan ’yan kwanaki sai Bulus ya ce wa Barnabas, “Mu koma mu ziyarci ’yan’uwa a duk garuruwan da muka yi wa’azin bisharar Ubangiji mu ga yadda suke.” Barnabas ya so Yohanna, wanda ake kira Markus ya tafi tare da su, amma Bulus bai ga ya kyautu ya tafi da shi ba, domin ya yashe su a Famfiliya bai kuwa ci gaba tare da su a aikin ba. Suka sami saɓanin ra’ayi tsakaninsu har suka rabu. Barnabas ya ɗauki Markus suka shiga jirgin ruwa zuwa Saifurus, amma Bulus ya zaɓi Sila suka kuwa tashi, bayan ’yan’uwa suka danƙa su ga alherin Ubangiji. Ya ratsa ta Suriya da Silisiya, yana ƙarfafa ikkilisiyoyi. Bulus ya kai Derbe sa’an nan kuma zuwa Listira, inda wani almajiri mai suna Timoti yake da zama, wanda mahaifiyarsa mutuniyar Yahuda ce kuma mai bi ce, amma mahaifinsa mutumin Hellenawa ne. ’Yan’uwa a Listira da Ikoniyum sun yi magana mai kyau ƙwarai a kansa. Bulus ya so ya ɗauke shi a tafiyar, saboda haka ya yi masa kaciya, domin Yahudawan da suke da zama a wurin, don duk sun san cewa mahaifinsa mutumin Hellenawa ne. Yayinda suke tafiya daga gari zuwa gari, suka dinga ba da shawarwarin da manzanni da dattawa a Urushalima suka zartar domin mutane su kiyaye. Saboda haka ikkilisiyoyi suka ginu cikin bangaskiya suka kuma yi girma suka yi ta ƙaruwa kowace rana. Bulus da abokan tafiyarsa suka zazzaga dukan yankin Firjiya da Galatiya, don Ruhu Mai Tsarki ya hana su yin wa’azi a lardin Asiya. Da suka isa kan iyakar Misiya, suka yi ƙoƙari su shiga Bitiniya, amma Ruhun Yesu bai yarda musu ba. Saboda haka suka ratsa Misiya suka zo Toruwas. Da dare Bulus ya ga wahayin wani mutumin Makidoniya yana tsaye yana roƙonsa cewa, “Ka zo Makidoniya ka taimake mu.” Bayan Bulus ya ga wahayin, muka shirya nan take mu tashi zuwa Makidoniya, mun tabbata cewa, Allah ya kira mu mu yi musu wa’azin bishara. Daga Toruwas muka tashi zuwa teku muka kuma shiga jirgin ruwa muka miƙe kai tsaye zuwa Samotiras, kashegari kuma muka nufi Neyafolis. Daga can muka tafi Filibbi, wata babbar alkaryar Roma wadda kuma take babban birni a gundumar Makidoniya. Muka zauna a can kwanaki masu yawa. A Asabbaci, muka fita ƙofar birnin zuwa bakin kogi, inda muke tsammani za mu sami wurin yin addu’a. Muka zauna muka fara yin wa matan da suka taru a can magana. Ɗaya daga cikin waɗanda suka saurare mu mace ce mai suna Lidiya, mai sayar da yadunan jan garura masu tsada daga birnin Tiyatira, mai yi wa Allah sujada. Ubangiji ya buɗe zuciyarta har ta karɓi saƙon Bulus. Da aka yi mata baftisma tare da iyalin gidanta, sai ta gayyace mu zuwa gidanta. Ta ce, “In kun amince ni mai bi ce cikin Ubangiji, sai ku zo ku sauka a gidana.” Sai ta kuwa rinjaye mu. Wata rana muna tafiya zuwa wurin yin addu’a, sai muka sadu da wata baranya mai ruhun aljani mai duba. Takan samo wa mutanenta kuɗi da yawa, duban da take yi. Wannan yarinya kuwa ta bi Bulus da kuma sauranmu, tana ihu tana cewa, “Waɗannan mutane bayin Allah Mafi Ɗaukaka ne, suna sanar da ku hanyar ceto.” Ta yi ta faɗin haka har kwanaki masu yawa. A ƙarshe Bulus ya damu ƙwarai sai ya juya ya ce wa aljanin, “A cikin sunan Yesu Kiristi na umarce ka, ka rabu da ita!” Nan take aljanin ya rabu da ita. Da iyayengijin baranyar suka ga hanyar samun kuɗinsu ta toshe, sai suka kama Bulus da Sila suka ja su zuwa cikin kasuwa don su fuskanci hukuma. Sai suka kawo su a gaban alƙalai suka ce, “Waɗannan Yahudawa ne, suna kuma birkitar mana da gari, ta wurin koyar da al’adun da ba daidai ba ne mu Romawa mu karɓa ko mu aikata.” Sai taron suka fāɗa wa Bulus da Sila gaba ɗaya, alƙalan kuwa suka yi umarni a tuɓe su a kuma yi musu dūka. Bayan an yi musu bulala sosai, sai aka jefa su cikin kurkuku, aka umarci mai gadin kurkukun yă tsare su da kyau. Da karɓan irin umarnan nan, sai ya sa su can cikin ɗakin kurkuku na ciki-ciki, kuma ya ɗaura ƙafafunsu a turu. Wajen tsakar dare Bulus da Sila suna addu’a suna rera waƙoƙi ga Allah, sauran ’yan kurkuku kuwa suna sauraronsu. Ba zato ba tsammani sai aka yi wata babbar girgizar ƙasa har tushen ginin kurkukun ya jijjiga. Nan da nan sai duk ƙofofin kurkukun suka bubbuɗe, sarƙoƙin kowa kuma suka ɓaɓɓalle. Mai gadin kurkukun ya farka daga barci, sa’ad da ya ga ƙofofin kurkukun a buɗe, sai ya zāre takobinsa yana shirin kashe kansa domin ya ɗauka ’yan kurkukun sun gudu. Amma Bulus ya yi ihu ya ce, “Kada ka yi wa kanka lahani! Dukanmu muna nan!” Mai gadin kurkukun ya kira a kawo fitilu, ya ruga ciki ya fāɗi yana rawan jiki a gaban Bulus da Sila. Sai ya fito da su waje ya kuma tambaye su ya ce, “Ranku yă daɗe, me zan yi domin in sami ceto?” Suka amsa suka ce, “Ka gaskata da Ubangiji Yesu, za ka sami ceto, kai da iyalinka.” Sa’an nan suka yi masa maganar Ubangiji shi da kuma dukan sauran da suke a gidansa. A wannan sa’a na daren, mai gadin kurkukun ya ɗauke su ya wanke musu raunukansu; nan take aka yi masa baftisma da dukan iyalinsa. Sai mai gadin kurkukun ya kawo su cikin gidansa ya ba su abinci; ya kuwa cika da murna don yă gaskata da Allah, shi da dukan iyalinsa. Da gari ya waye, sai alƙalan suka aika ma’aikatansu wajen mai gadin kurkukun da umarni cewa, “Ka saki mutanen nan.” Sai mai gadin kurkukun ya gaya wa Bulus cewa, “Alƙalai sun ba da umarni a sake ku kai da Sila. Yanzu sai ku tafi. Ku sauka lafiya.” Amma Bulus ya ce wa ma’aikatan, “Sun yi mana dūka a fili ba tare da shari’a ba, ko da yake mu ’yan ƙasar Roma ne, suka kuma jefa mu cikin kurkuku. Yanzu suna so su fitar da mu a ɓoye? A’a! Sai dai su zo da kansu su rako mu waje.” Sai ma’aikatan suka faɗa wa alƙalan wannan, da suka ji cewa Bulus da Sila Romawa ne, sai suka ji tsoro. Sai suka zo don su roƙe su, suka yi musu rakiya daga kurkukun, suna roƙonsu su bar birnin. Bayan Bulus da Sila suka fita daga kurkukun, sai suka tafi gidan Lidiya, inda suka sadu da ’yan’uwa suka kuma ƙarfafa su. Sa’an nan suka tafi. Da suka bi ta Amfifolis da Afolloniya, sai suka isa Tessalonika, inda akwai majami’ar Yahudawa. Kamar yadda ya saba, Bulus ya shiga majami’ar, ranakun Asabbaci uku ya yi ta yin muhawwara da su daga cikin Nassosi, yana musu bayani da tabbatarwa cewa dole Kiristi ya sha wahala ya kuma tashi daga matattu. Ya kuma ce, “Wannan Yesu da nake sanar muku shi ne Kiristi.” Waɗansu Yahudawa suka amince suka kuma bi Bulus da Sila, haka ma Hellenawa da yawa masu tsoron Allah da kuma manyan mata ba kaɗan ba. Amma Yahudawa suka yi kishi; saboda haka suka tattara ’yan iska daga kasuwa, suka shirya wata ƙungiya, suka tā da tarzoma a birni. Suka ruga zuwa gidan Yason suna neman Bulus da Sila don su kawo su a gaban taron. Amma da ba su same su ba, sai suka ja Yason da waɗansu ’yan’uwa zuwa gaban mahukuntan birnin, suna ihu suna cewa, “Waɗannan mutanen da suke tā da fitina ko’ina a duniya sun iso nan, Yason kuwa ya karɓe su a gidansa. Dukansu suna karya dokokin Kaisar, suna cewa akwai wani sarki, wanda ake kira Yesu.” Da suka ji haka, sai hankalin taron da na mahukuntan birnin ya tashi. Sai suka sa Yason da sauran su biya kuɗin saki sa’an nan suka sallame su. Da dare ya yi, sai ’yan’uwa suka sallami Bulus da Sila su tafi Bereya. Da suka isa can, sai suka shiga majami’ar Yahudawa. Bereyawa kuwa sun fi Tessalonikawa hankali, gama sun karɓi saƙon da marmari ƙwarai, suka kuma yi ta yin bincike Nassosi kowace rana su ga ko abin da Bulus ya faɗa gaskiya ne. Yahudawa da yawa suka gaskata, haka ma waɗansu manyan matan Hellenawa da kuma mazan Hellenawa da yawa. Da Yahudawan da suke a Tessalonika suka ji cewa Bulus yana wa’azin maganar Allah a Bereya, sai suka je can ma, suna zuga taro suna kuma tā da hankalinsu. Nan da nan ’yan’uwa suka sa Bulus yă tafi bakin teku, amma Sila da Timoti suka dakata a Bereya. Mutanen da suka raka Bulus kuwa suka kawo shi Atens sa’an nan suka dawo da umarnai wa Sila da Timoti cewa su zo wurinsa da gaggawa. Yayinda Bulus yake jiransu a Atens, ya damu ƙwarai da ya ga birnin cike da gumaka. Saboda haka ya yi ta muhawwara a majami’a da Yahudawa da kuma Hellenawa masu tsoron Allah, haka kuma da waɗanda yake tararwa a bakin kasuwa. Wata ƙungiyar Afikuriya da kuma masu bin ussan ilimin Sitoyik suka fara gardama da shi. Waɗansunsu suka ce, “Mene ne mai surutun nan yake ƙoƙarin faɗi?” Waɗansu suka ce, “Kamar yana wa’azin baƙin alloli ne.” Sun faɗa haka ne domin Bulus yana wa’azin labari mai daɗi game da Yesu da kuma tashin matattu. Sai suka ɗauke shi suka kawo shi wurin taron Areyofagus, inda suka ce masa, “Ko za mu san mene ne sabon koyarwan nan ya ƙunsa da kake yi? Kana kawo mana ra’ayoyin da suke baƙo a gare mu, kuma muna so mu san mene ne suke nufi.” (Duk Atenawa da baƙin da suke zama a can suna zaman kashe wando ne kawai kuma ba abin da suke yi sai dai taɗi da kuma jin sababbin ra’ayoyi.) Sai Bulus ya miƙe tsaye a tsakiyar taron Areyofagus ya ce, “Ya ku mutanen Atens! Na dai lura cewa ta kowace hanya ku masu addini ne ƙwarai. Gama sa’ad da nake zagawa, na lura da kyau da abubuwan da kuke bauta wa, har ma na tarar da wani bagade da wannan rubutu, Ga Allahn da ba a sani ba. To, abin nan da kuke yi wa sujada a matsayin abin da ba ku sani nan ba shi ne zan sanar da ku. “Allahn da ya halicci duniya da kome da yake cikinta shi ne Ubangijin sama da ƙasa, ba ya kuma zama a haikalin da aka gina da hannuwa. Ba a kuma yin masa hidima da hannun mutum, sai ka ce mai bukatan wani abu, domin shi kansa ne ke ba wa dukan mutane rai da numfashi da kuma kome. Daga mutum ɗaya, ya halicci kowace al’ummar mutane, don su zauna a duk duniya; shi ne kuma ya ƙaddara lokuta bisa ga tsarinsu da kuma inda za su kasance. Allah ya yi wannan domin mutane su neme shi mai yiwuwa kuma su lalluba su same shi, ko da yake ba shi da nisa daga kowannenmu. ‘Gama a cikinsa ne muke rayuwa muke motsi muka kuma kasance.’ Yadda waɗansu mawaƙanku suka ce, ‘Mu zuriyarsa ce.’ “Saboda haka da yake mu zuriyar Allah ce, kada mu yi tsammani cewa kamannin Allah yana kama da zinariya ko azurfa ko dutse, siffar da mutum ya ƙago ta wurin dabararsa. A dā Allah ya kawar da Allah ya kawar da kai ga zamanin jahilci, amma yanzu ya umarci dukan mutane a ko’ina su tuba. Gama ya sa ranar da zai yi wa duniya shari’a da adalci ta wurin mutumin da ya naɗa. Ya riga ya ba da tabbacin wannan ga dukan mutane ta wurin tā da shi daga matattu.” Sa’ad da suka ji maganar tashin matattu, waɗansunsu suka yi tsaki, amma waɗansu suka ce, “Muna so mu ƙara jin ka a kan wannan batu.” Da wannan, Bulus ya bar Majalisar. Waɗansu mutane kima suka zama mabiyan Bulus suka kuwa gaskata. A cikinsu kuwa akwai Diyonasiyus ɗan Majalisar Areyofagus, haka kuma wata mace mai suna Damaris, da waɗansu dai haka. Bayan haka, Bulus ya bar Atens ya tafi Korint. A can ya sadu da wani mutumin Yahuda mai suna Akwila, ɗan garin Fontus, wanda ya je can ba da daɗewa ba daga Italiya tare da matarsa Firiskila, gama Kalaudiyus ya umarci dukan Yahudawa su bar Roma. Sai Bulus ya tafi yă gan su, da yake shi ma mai ɗinkin tenti ne kamar su, sai ya zauna ya yi aiki tare da su. Kowace Asabbaci kuwa yakan yi muhawwara a majami’a, yana ƙoƙari yă rinjayi Yahudawa da Hellenawa. Sa’ad da Sila da Timoti suka iso daga Makidoniya, sai Bulus ya ba da kansa ga yin wa’azi kaɗai, yana tabbatar wa Yahudawa cewa Yesu shi ne Kiristi. Amma sa’ad da Yahudawa suka yi hamayya da Bulus suka kuma shiga zaginsa, sai ya karkaɗe tufafinsa a cikin rashin yarda, ya ce musu, “Alhakinku yana a kanku! Ba ni da wani laifi. Daga yanzu zan tafi wajen Al’ummai.” Sai Bulus ya bar majami’ar ya kuma tafi ƙofar da take kusa da gidan Titus Yustus, mai yi wa Allah sujada. Kirisbus, shugaban majami’a, da dukan iyalinsa suka gaskata Ubangiji; Korintiyawa masu yawa kuwa da suka ji shi suka gaskata, aka kuwa yi musu baftisma. Wata rana da dad dare, Ubangiji ya yi magana da Bulus a cikin wahayi ya ce, “Kada ka ji tsoro; ka ci gaba da yin magana, kada ka yi shiru. Gama ina tare da kai, ba kuma wanda zai fāɗa maka ya cuce ka, domin ina da mutane da yawa a wannan birni.” Saboda haka Bulus ya zauna a nan har shekara ɗaya da rabi, yana koya musu maganar Allah. Yayinda Galliyo yake muƙaddas Akayya, Yahudawa suka haɗa kai suka tasar wa Bulus, suka kuwa kawo shi cikin kotu. Suka yi zarge cewa, “Wannan mutum yana rarrashin mutane su yi wa Allah sujada a hanyoyin da suka saɓa wa doka.” A daidai sa’ad da Bulus yana shirin yin magana, sai Galliyo ya ce wa Yahudawan, “Da a ce ku Yahudawa kuna gunaguni game da munafunci, ko kuma wani babban laifi, da sai in iya sauraronku. Amma da yake ya shafi gardama ce game da kalmomi da sunaye da kuma dokarku, sai ku ji da ita da kanku. Ni ba zan zama mai shari’a kan irin waɗannan abubuwa ba.” Saboda haka ya kore su. Sai duk suka juya kan Sostenes shugaban majami’a suka yi masa dūka a gaban kotun. Amma Galliyo ko yă kula. Bulus kuwa ya ci gaba da zama a Korint na ’yan kwanaki. Sa’an nan ya bar ’yan’uwa ya shiga jirgin ruwa zuwa Suriya tare da Firiskila da Akwila. Kafin ya tashi, ya aske kansa a Kenkireya saboda alkawarin da ya yi. Suka isa Afisa, inda Bulus ya bar Firiskila da Akwila. Shi kansa ya shiga majami’a ya kuma yi muhawwara da Yahudawa. Sa’ad da suka roƙe shi ya ƙara ’yan kwanaki da su, bai yarda ba. Amma da yake barin wurin, ya yi alkawari cewa, “Zan dawo in Allah ya yarda.” Sa’an nan ya tashi daga Afisa a jirgin ruwa. Sa’ad da ya sauka a Kaisariya, sai ya haura ya gai da ikkilisiya sa’an nan ya gangara zuwa Antiyok. Bayan ya yi ’yan kwanaki a Antiyok, Bulus ya tashi daga can ya zaga ko’ina a yankin Galatiya da Firjiya, yana ƙarfafa dukan almajirai. Ana cikin haka sai wani mutumin Yahuda mai suna Afollos, ɗan ƙasar Alekzandariya, ya zo Afisa. Shi masani ne, yana da cikakken sani na Nassosi. An horar da shi a hanyar Ubangiji, ya kuma himma ƙwarai a magana, ya kuma yi koyarwa game da Yesu, daidai, ko da yake baftismar Yohanna ce kaɗai ya sani. Sai ya fara magana gabagadi a majami’a. Sa’ad da Firiskila da Akwila suka ji shi, sai suka gayyace shi gidansu suka ƙara bayyana masa hanyar Allah sosai. Sa’ad da Afollos ya so ya tafi Akayya, sai ’yan’uwa suka ƙarfafa shi suka kuma rubuta wa almajiran da suke can da su marabce shi. Da isowarsa, ya zama da taimako ƙwarai ga waɗanda ta wurin alheri suka gaskata. Gama da ƙwazo ya ƙaryata Yahudawa a muhawwara a fili, yana tabbatar daga Nassosi cewa Yesu shi ne Kiristi. Lokacin da Afollos yake a Korint, Bulus ya bi hanyar da ta ratsa ta Asiya ya zo Afisa. A can ya sadu da waɗansu almajirai, sai ya tambaye, su ya ce, “Kun karɓi Ruhu Mai Tsarki sa’ad da kuka gaskata?” Suka amsa suka ce, “A’a, ba mu ma san akwai Ruhu Mai Tsarki ba.” Saboda haka Bulus ya yi tambaya ya ce, “To, wace baftisma aka yi muku?” Suka ce, “Baftismar Yohanna.” Bulus ya ce, “Ai, baftismar Yohanna, baftisma ce ta tuba. Ya ce wa mutane su gaskata a wani wanda yake zuwa bayansa, wato, Yesu.” Da ji wannan, sai aka yi musu baftisma a cikin sunan Ubangiji Yesu. Da Bulus ya ɗibiya musu hannuwansa, sai Ruhu Mai Tsarki ya sauka musu, suka kuwa yi magana da harsuna, suka kuma yi annabci. Mutane kuwa su wajen mutum goma sha biyu ne. Bulus ya shiga majami’a ya yi magana gabagadi a can na watanni uku, yana muhawwara yana kuma rinjayarsu game da mulkin Allah. Amma waɗansunsu suka taurara; suka ƙi su gaskata kuma a gaban jama’a suka yi baƙar magana game da Hanyar. Bulus kuwa ya bar su. Ya tafi tare da almajirai ya dinga tattaunawa da su kullum a babban ɗakin jawabi na Tirannus. Wannan ya ci gaba har shekara biyu, sai da ya sa dukan Yahudawa da Hellenawa da suke zaune a lardin Asiya suka ji maganar Ubangiji. Allah ya yi ayyukan banmamakin da suka wuce misali ta hannu Bulus, har ma ana kai hankicif da adikan da suka taɓa jikinsa wa marasa lafiya, suka kuwa warke daga cututtukansu mugayen ruhohi kuma suka rabu da su. Waɗansu Yahudawa masu yawo gari-gari suna fitar da mugayen ruhohi suka yi ƙoƙari su yi amfani da sunan Ubangiji Yesu a kan waɗanda suke da aljanu. Suna cewa, “A cikin sunan Yesu wanda Bulus yake wa’azi, na umarce ku, ku fito.” ’Ya’ya bakwai maza na Sikeba, wani babban firist na Yahudawa, suna yin haka. Wata rana mugun ruhu ya amsa musu ya ce, “Yesu kam na sani, Bulus kuma na sani, amma ku kuma su wane ne?” Sai mutumin da yake da mugun ruhun ya fāɗa musu ya sha ƙarfinsu duka. Ya yi musu dūkan tsiya har suka fita a guje daga gidan tsirara jini yana zuba. Da Yahudawa da Hellenawan da suke zama a Afisa suka ji wannan labari sai duk tsoro ya kama su, aka kuwa darjanta sunan Ubangiji Yesu ƙwarai. Da yawa cikin waɗanda suka gaskata yanzu suka zo a fili suka furta mugayen ayyukansu. Waɗansu masu yin sihiri suka kawo naɗaɗɗun littattafansu wuri ɗaya suka kuwa ƙone su a gaban jama’a. Sa’ad da aka lissafta yawan kuɗin naɗaɗɗun littattafan nan, sai jimillar ta kai darik dubu hamsin. Ta haka maganar Ubangiji ta bazu ko’ina ta kuma yi ƙarfi. Bayan dukan wannan ya faru, sai Bulus ya yanke shawara ya ratsa Makidoniya da Akayya in za shi Urushalima. Ya kuma ce, “Bayan na tafi can, dole in ziyarci Roma ita ma.” Sai ya aiki biyu daga cikin masu taimakonsa, Timoti da Erastus, zuwa Makidoniya, yayinda shi kuwa ya ɗan dakata a lardin Asiya. Kusan wannan lokaci sai aka yi wani babban hargitsi game da wannan Hanyar. Wani maƙerin azurfa, mai suna Demetiriyus wanda yake ƙera siffar ɗakunan tsafin Artemis da azurfa, ba ƙaramin ciniki yake kawo wa mutane masu sana’an nan ba. Sai ya tara su wuri ɗaya, tare da masu irin wannan sana’ar ya ce, “Ku jama’a, kun san muna samun kuɗin shiga sosai daga wannan sana’a. Kuma kuna ji kuna gani yadda Bulus ɗin nan ya shawo kan mutane da yawa ya kuma sa suka bauɗe a nan a Afisa da dukan lardin Asiya. Yana cewa alloli da mutum ya ƙera ba alloli ba ne ko kaɗan. Akwai hatsari, ba kawai cewa sana’armu za tă rasa sunanta mai daraja ba, amma za a yi banza da ɗakin tsafin Artemis alliyarmu mai girma, alliyar kanta wadda ake bauta a ko’ina a yankin Asiya da kuma duniya, za a raba ta da darajarta.” Da suka ji haka, sai suka yi fushi ƙwarai suka fara ihu suna cewa, “Girma ta tabbata ga Artemis ta Afisawa!” Jim kaɗan sai hayaniya ta tashi a dukan birnin. Sai mutane suka cafke Gayus da Aristarkus, abokan tafiyar Bulus daga Makidoniya, suka ruga da zuwa fili da nufi ɗaya. Bulus ya so ya bayyana a gaban taron, amma almajirai ba su bar shi ba. Har waɗansu shugabannin lardin ma, abokan Bulus, suka aika masa suna roƙonsa kada yă kuskura ya shiga filin nan. Taron kuwa ya ruɗe. Waɗansu suna ihu suna ce abu kaza, waɗansu kuma wani abu dabam. Yawancin mutane kuma ba su ma san abin da ya sa suke a wurin ba. Yahudawa suka tura Alekzanda gaba, sai waɗansu a taron suka riƙa yin masa ihu. Sai ya ɗaga hannu don a yi shiru don yă kāre kansa a gaban mutane. Amma sa’ad da suka gane shi mutumin Yahuda ne, sai duk suka yi ihu gaba ɗaya na kusa sa’a biyu, suna cewa, “Girma ta tabbata ga Artemis ta Afisawa!” Sai magatakardar birnin ya sa taron su yi shiru, sa’an nan ya ce, “Mutanen Afisa, ashe duk duniya ba tă san cewa birnin Afisa ce mai lura da haikalin Artemis mai girma da kuma siffarta da ya fāɗi daga sama ba? Saboda haka, da yake ba dama a yi mūsun wannan gaskiya, ya kamata ku natsu kada ku yi kome da garaje. Kun kawo mutanen nan a nan, gashi kuwa ba su yi fashin haikali ba, ba su kuwa saɓa wa alliyarmu ba. To, in haka ne, in Demetiriyus da abokan sana’arsa suna da wata magana game da wani ai, kotuna suna nan a buɗe, akwai kuma muƙaddasai. Suna iya kai ƙara. In kuma akwai wani abu har yanzu da kuke so ku kawo, dole a daidaita shi a majalisa. Yadda yake a yanzu, muna a hatsarin amsa zargin ta da hargitsi saboda abin da ya faru yau. Da yake ba za mu iya ba da dalilin da ya sa aka yi wannan hargitsi ba.” Bayan da ya faɗi haka, sai ya sallami taron. Sa’ad da hayaniyar ta kwanta, sai Bulus ya aika a kira almajiran, kuma bayan ya ƙarfafa su, sai ya yi bankwana ya tafi Makidoniya. Ya ratsa wurin yana ƙarfafa mutanen da kalmomi masu yawa, a ƙarshe kuma ya kai Giris, inda ya zauna wata uku. Da yake Yahudawa sun ƙulla masa makirci, a lokacin da yake shirin tashi cikin jirgin ruwa zuwa Suriya, sai ya yanka shawara yă koma ta Makidoniya. Sai Sofater ɗan Fairrus daga Bereya, Aristarkus da Sekundus daga Tessalonika, Gayus daga Derbe, Timoti ma, da Tikikus da Turofimus daga lardin Asiya suka tafi tare da shi. Waɗannan mutane suka sha gaba suka kuma jira mu a Toruwas. Amma muka tashi daga Filibbi a jirgin ruwa bayan Bikin Burodi Marar Yisti bayan kuma kwana biyar muka sadu da sauran a Toruwas, inda muka zauna kwana bakwai. A ranar farko ta mako muka taru wuri ɗaya don gutsuttsura burodi. Bulus ya yi wa mutane magana, don yana niyyar tashi kashegari, sai ya yi ta yin magana har tsakar dare. Akwai fitilu da yawa a ɗakin gidan saman da muka taru. Akwai wani saurayi zaune a taga mai suna Yitikus, wanda barci mai nauyi ya ɗauke shi yayinda Bulus yake ta tsawaita magana. Sa’ad da yake barci, sai ya fāɗi daga gidan sama a hawa ta uku aka kuma ɗauke shi matacce. Sai Bulus ya sauka, ya miƙe a kan saurayin ya rungume shi ya ce, “Kada ku damu, yana da rai!” Sai ya koma ɗakin da yake a gidan sama, ya gutsuttsura burodi ya kuma ci. Bayan ya yi magana har gari ya waye, sai ya tafi. Mutanen suka ɗauki saurayin da rai zuwa gida suka kuma ta’azantu ƙwarai da gaske. Mu kuwa muka ci gaba zuwa jirgin ruwan muka tashi muka nufi Assos inda za mu ɗauki Bulus. Ya yi wannan shirin don zai tafi can da ƙafa. Da ya same mu a Assos, sai muka ɗauke shi a jirgin ruwan muka zo Mitilen. Kashegari muka tashi cikin jirgin ruwa daga can muka zo gefen Kiyos. Kwana ɗaya bayan wannan, sai muka ƙetare zuwa Samos, kashegari kuma muka iso Miletus. Bulus ya yanke shawara yă wuce Afisa a jirgin ruwa don kada yă ɓata lokaci a lardin Asiya, gama yana sauri yă kai Urushalima, in ya yiwu ma, a ranar Fentekos. Daga Miletus, Bulus ya aika zuwa Afisa a kira dattawan ikkilisiya. Da suka iso, sai ya ce musu, “Kun san irin zaman da na yi tun lokacin da na zauna da ku, daga ranar farkon da na zo cikin lardin Asiya. Na bauta wa Ubangiji da matuƙar tawali’u har da hawaye, da gwagwarmaya iri-irin da na sha game da makircin Yahudawa. Kun san cewa ban yi wata-wata yin muku wa’azi game da duk abin da zai amfane ku ba amma na koyar da ku a fili da kuma gida-gida. Na yi shela ga Yahudawa da Hellenawa cewa dole su juye ga Allah cikin tuba su kuma amince da Ubangijinmu Yesu. “Yanzu kuma Ruhu ya tilasta ni, za ni Urushalima, ba tare da sanin abin da zai faru da ni a can ba. Na dai san cewa a kowace birni Ruhu Mai Tsarki yakan gargaɗe ni cewa kurkuku da shan wuya suna jirana. Amma ni ban ɗauki raina a bakin kome ba, in dai zan iya gama tserena in kuma kammala aikin da Ubangiji Yesu ya ba ni aikin shaida bisharar alherin Allah. “Yanzu na san cewa ba ko ɗaya daga cikinku wanda na zazzaga ina muku wa’azin mulkin Allah da zai sāke ganina. Saboda haka, ina muku shela a yau cewa ba ni da alhakin kowa a kaina. Gama ban yi wata-wata a sanar muku dukan nufin Allah ba. Ku lura da kanku da dukan garken da Ruhu Mai Tsarki ya sa ku ku zama masu kula da shi. Ku zama masu kiwon ikkilisiyar Allah, wadda ya saya da jininsa. Na san cewa bayan na tafi, mugayen kyarketai za su shigo cikinku ba za su kuwa ƙyale garken ba. Ko cikinku ma mutane za su taso su karkatar da gaskiya don su jawo wa kansu almajirai. Saboda haka ku zauna a faɗake! Ku tuna cewa shekara uku, dare da rana ban taɓa fasa yin wa kowannenku gargaɗi ba, har da hawaye. “To, yanzu na danƙa ku ga Allah da kuma ga maganar alherinsa, wadda za tă iya gina ku ta kuma ba ku gādo a cikin dukan waɗanda aka tsarkake. Ban yi ƙyashin azurfa ko zinariya ko tufafin kowa ba. Ku kanku kun san cewa hannuwan nan nawa sun biya mini bukatuna da kuma na abokan aikina. Cikin kowane abin da na yi, na nuna muku cewa da irin wannan aiki tuƙuru don mu taimaki marasa ƙarfi, muna tunawa da kalmomin da Ubangiji Yesu kansa ya ce, ‘Bayarwa ta fi karɓa albarka.’  ” Da ya faɗi haka, ya durƙusa tare da dukansu ya yi addu’a. Sai dukansu suka yi kuka suka rungume shi, suka kuma yi masa sumba. Abin da ya fi sa su baƙin ciki shi ne maganarsa da ya ce, ba za su ƙara ganin fuskarsa ba. Sai suka raka shi zuwa wajen jirgin ruwa. Bayan muka rabu da su da ƙyar, sai muka shiga jirgin ruwa, muka miƙe zuwa Kos. Kashegari muka tafi Rods daga can kuma muka je Fatara. Sai muka sami wani jirgin ruwa da zai ƙetare zuwa Funisiya, sai muka shiga muka kama tafiya. Bayan muka hangi Saifurus muka wuce shi ta kudu, sai muka ci gaba zuwa Suriya. Muka sauka a Taya, inda jirgin ruwanmu zai sauke kayansa. Da muka sami almajirai a can, sai muka zauna da su kwana bakwai. Ta wurin Ruhu, suka yi ƙoƙari su hana Bulus wucewa zuwa Urushalima. Amma da lokacin tashinmu ya yi, sai muka tashi muka ci gaba da tafiyarmu. Dukan almajirai da matansu da ’ya’yansu suka raka mu har bayan birni, a can kuwa a bakin teku muka durƙusa muka yi addu’a. Bayan mun yi bankwana da juna, sai muka shiga jirgin ruwa, su kuwa suka koma gida. Muka ci gaba da tafiyarmu daga Taya muka sauka a Tolemayis, inda muka gai da ’yan’uwa muka yi kwana ɗaya tare da su. Da muka tashi kashegari, sai muka isa Kaisariya muka kuma sauka a gidan Filibus mai bishara, ɗaya daga cikin Bakwai ɗin nan. Yana da ’ya’ya huɗu ’yan mata da ba su yi aure ba, waɗanda suka yi annabci. Bayan muka yi ’yan kwanaki da dama a can, sai wani annabin da ake kira Agabus ya gangaro daga Yahudiya. Da ya zo wurinmu, sai ya ɗauki ɗamarar Bulus, ya ɗaura hannuwansa da ƙafafunsa da ita sa’an nan ya ce, “Ruhu Mai Tsarki ya ce, ‘Haka Yahudawan Urushalima za su daure mai wannan ɗamara su kuma ba da shi ga Al’ummai.’ ” Sa’ad da muka ji haka, sai mu da mutanen da suke can muka roƙi Bulus kada yă je Urushalima. Sai Bulus ya amsa ya ce, “Don me kuke kuka kuna kuma ɓata mini zuciya? A shirye nake ba ma a daure ni kawai ba, amma har ma in mutu a Urushalima saboda sunan Ubangiji Yesu.” Da dai ya ƙi rarrasuwa, muka yi shiru, muka ce, “Bari Ubangiji yă yi nufinsa.” Bayan haka, sai muka shirya muka kuma haura zuwa Urushalima. Waɗansu almajirai daga Kaisariya suka raka mu suka kawo mu gidan Minason, inda za mu sauka. Shi mutumin Saifurus ne kuma ɗaya daga cikin almajirai na farko. Sa’ad da muka zo Urushalima, ’yan’uwa suka karɓe mu da murna. Kashegari Bulus da sauranmu muka tafi domin mu ga Yaƙub, dukan dattawan kuwa suna nan. Bulus ya gaishe su ya kuma ba su rahoto dalla-dalla a kan abin da Allah ya yi a cikin Al’ummai ta wurin aikinsa. Da suka ji haka, sai suka yabi Allah. Sa’an nan suka ce wa Bulus, “Ka gani ɗan’uwa, yawan dubban Yahudawan da suka gaskata, kuma dukansu masu himma ne a wajen bin doka. An sanar da su cewa kana koya wa dukan Yahudawan da suke zama a cikin Al’ummai cewa su juye daga Musa, kana kuma faɗa musu kada su yi wa ’ya’yansu kaciya ko su yi rayuwa bisa ga al’adunmu. To, me za mu yi ke nan? Lalle za su ji cewa ka iso, saboda haka, ka yi abin da muka faɗa maka. Akwai mutum huɗu tare da mu da suka yi alkawari. Ka ɗauki waɗannan mutane, ka tafi da su ku tsarkaka gaba ɗaya, ka kuma biya musu kome don su samu su yi aski. Ta haka kowa zai sani babu gaskiya a waɗannan rahotanni game da kai, za a kuma ga cewa kai kanka kana kiyaye dokar. Game da Al’ummai masu bi kuwa, mun yi musu wasiƙa a kan shawararmu cewa su guji abincin da aka miƙa wa gumaka, da jini, da naman dabbar da aka maƙure da kuma fasikanci.” Kashegari, sai Bulus ya ɗauki mutanen ya kuma tsarkake kansa tare da su. Sa’an nan ya tafi haikali domin yă sanar da ranar cikar tsarkakewarsu da kuma ranar da za a ba da sadaka domin kowannensu. Da kwana bakwai ɗin suka yi kusan cika, waɗansu Yahudawa daga lardin Asiya suka ga Bulus a haikali. Sai suka zuga taron duka, suka kama shi, suna ihu suna cewa “Mutanen Isra’ila ku taimake mu! Ga mutumin da yake koya wa dukan mutane ko’ina cewa su ƙi mutanenmu da dokarmu da kuma wannan wuri. Ban da haka ma, ya kawo Hellenawa a cikin filin haikali ya ƙazantar da wurin nan mai tsarki.” (Dā ma can sun ga Turofimus mutumin Afisa a birni tare da Bulus suka yi tsammani Bulus ya kawo shi filin haikali.) Duk birnin ya ruɗe, mutane suka zaburo da gudu daga kowane gefe. Suka kama Bulus, suka ja shi daga haikali, nan da nan aka rurrufe ƙofofi. Yayinda suke ƙoƙari su kashe shi, sai labari ya kai ga shugaban ƙungiyar sojan Roma cewa birnin Urushalima duk ta hargitse. Nan da nan ya ɗibi waɗansu hafsoshi da sojoji suka gangara a guje wurin taron. Da masu hargitsin suka ga shugaban ƙungiyar sojan da sojojinsa, sai suka daina dūkan Bulus. Shugaban ƙungiyar sojan ya zo ya kama shi ya ba da umarni a daure shi da sarƙoƙi biyu. Sa’an nan ya yi tambaya ko shi wane ne, da kuma abin da ya yi. Waɗansu daga cikin taron suka ɗau kururuwa suna ce abu kaza, waɗansu kuma suna ce abu kaza, da yake shugaban ƙungiyar sojan ya kāsa samun ainihin tushen maganar saboda yawan hayaniyar, sai ya yi umarni a kai Bulus barikin soja. Sa’ad da Bulus ya kai bakin matakala, sai da sojoji suka ɗaga shi sama saboda tsananin haukan taron. Taron da suka bi suka dinga kururuwa, suna cewa, “A yi da shi!” Da sojoji suka kai gab da shigar da Bulus cikin bariki, sai ya ce wa shugaban ƙungiyar sojan, “Ko ka yarda in yi magana da kai?” Sai ya amsa ya ce, “Ka iya Girik ne? Ba kai ba ne mutumin Masar nan da ya haddasa tawaye har ya yi jagorar ’yan ta’ada dubu huɗu zuwa hamada a shekarun baya?” Bulus ya amsa ya ce, “Ni mutumin Yahuda ne, daga Tarshish a Silisiya shahararren birnin nan. In ka yarda bari in yi wa mutane magana.” Da ya sami izini daga shugaban ƙungiyar sojan, sai Bulus ya tsaya a matakala, ya ɗaga wa taron hannu. Da dukan suka yi shiru, sai ya ce musu da Arameyanci, “’Yan’uwa da iyaye, ku saurari kāriyata yanzu.” Da suka ji ya yi musu magana da Arameyik, sai suka yi tsit. Sai Bulus ya ce, “Ni mutumin Yahuda ne haifaffen Tarshish na Silisiya, amma a nan birnin ne aka rene ni. Aka horar da ni sosai cikin dokokin kakanninmu a ƙarƙashin Gamaliyel ni ma dā mai himma ne cikin bauta wa Allah kamar yadda kowannenku yake a yau. Na tsananta wa masu bin wannan Hanyar har ga mutuwarsu, ina kama maza da mata ina kuma jefa su cikin kurkuku, kamar yadda babban firist da dukan Majalisa za su iya shaida. Na ma karɓi wasiƙu daga gare su zuwa ga ’yan’uwansu a Damaskus, na kuma tafi can don in kawo waɗannan mutane a daure zuwa Urushalima don a hukunta su. “Wajen tsakar rana da na yi kusa da Damaskus, ba zato ba tsammani sai wani babban haske daga sama ya haskaka kewaye da ni. Sai na fāɗi a ƙasa na kuma ji wata murya ta ce mini, ‘Shawulu! Shawulu! Don me kake tsananta mini?’ “Sai na yi tambaya na ce, ‘Wane ne kai, ya Ubangiji?’ “Ya amsa ya ce, ‘Ni ne Yesu Banazare, wanda kake tsanantawa.’ Abokan tafiyata suka ga hasken, amma ba su fahimci muryar mai magana da ni ba. “Sai na yi tambaya, na ce, ‘Me zan yi, ya Ubangiji?’ “Ubangiji ya ce, ‘Tashi, ka tafi cikin Damaskus. A can za a faɗa maka duk abin da aka shirya za ka yi.’ Abokan tafiyata suka ja ni a hannu zuwa cikin Damaskus, saboda ƙarfin hasken ya makanta ni. “Wani mutumin da ake kira Ananiyas ya zo ya gan ni. Shi mai ibada ne wajen kiyaye dokoki wanda dukan Yahudawan da suke zama a can suna girmama shi ƙwarai. Ya tsaya kusa da ni ya ce, ‘Ɗan’uwa Shawulu, ka sami ganin garinka!’ A daidai lokacin kuwa na iya ganinsa. “Sa’an nan ya ce, ‘Allah na kakanninmu ya zaɓe ka ka san nufinsa ka kuma ga Mai Adalcin nan ka kuma ji kalmomi daga bakinsa. Za ka zama mai shaidarsa ga dukan mutane game da abin da ka gani ka kuma ji. Yanzu me kake jira? Ka tashi, a yi maka baftisma, a wanke zunubanka, ta wurin kira bisa ga sunansa.’ “Sa’ad da na dawo Urushalima ina cikin addu’a a haikali, sai na ga wahayi na ga Ubangiji yana magana. Ya ce mini, ‘Maza! Ka bar Urushalima, gama ba za su yarda da shaidarka game da ni ba.’ “Na amsa na ce, ‘Ubangiji, waɗannan mutane sun san cewa na bi majami’a-majami’a na jefa waɗanda suka gaskata da kai a cikin kurkuku, in kuma yin musu dūka. Sa’ad da kuma aka zub da jinin Istifanus mashaidinka, na tsaya can ina ba da goyon bayana ina kuma tsaron tufafin masu kisansa.’ “Sa’an nan Ubangiji ya ce mini, ‘Je ka; zan aike ka can nesa a wurin Al’ummai.’  ” Taron suka saurari Bulus sai da ya yi wannan magana. Sa’an nan suka ɗaga muryoyinsu suka yi ihu suka ce, “A raba duniya da wannan mutum! Bai cancanci yă rayu ba!” Da suna ihu suna kaɗa mayafansu suna da tā da ƙura sama, sai shugaban ƙungiyar sojan ya umarta a kai Bulus a barikin soja. Ya ba da umarni a yi masa bulala a kuma tambaye shi abin da ya sa mutane suke masa ihu haka. Suna kwantar da shi ke nan domin a yi masa bulala, sai Bulus ya ce wa jarumin da yake tsaye a nan, “Ashe, daidai ne bisa ga doka a yi wa ɗan ƙasar Roma bulala wanda ba a ma tabbatar da laifi a kansa ba?” Da jarumin ya ji haka sai ya je wurin shugaban ƙungiyar sojan ya ce masa, “Me kake so yi ne? Wannan mutum ɗan ƙasar Roma ne.” Sai shugaban ƙungiyar sojan ya je ya tambayi Bulus ya ce, “Faɗa mini, kai ɗan ƙasar Roma ne?” Bulus ya ce, “I.” Sai shugaban ƙungiyar sojan ya ce, “Sai da na biya kuɗi mai yawa kafin in zama ɗan ƙasa.” Bulus ya ce, “Ni kuwa an haife ni ɗan ƙasa.” Waɗanda dā suke shirin yin masa tambayoyi suka ja da baya nan da nan. Shugaban ƙungiyar sojan kansa ya tsorata da ya fahimci cewa ya sa wa Bulus, ɗan ƙasar Roma sarƙa. Kashegari da yake shugaban ƙungiyar sojan ya so yă tabbatar da ainihin abin da ya sa Yahudawa suke zargin Bulus, sai ya sake shi ya kuwa umarci manyan firistoci da dukan Majalisar su taru. Sa’an nan ya kawo Bulus ya sa ya tsaya a gabansu. Bulus ya zuba wa Majalisar ido ya ce, “’Yan’uwana, na cika aikina ga Allah cikin lamiri mai kyau har yă zuwa yau.” Da jin wannan Ananiyas babban firist ya umarci waɗanda suke tsaye kusa da Bulus su buge bakinsa. Sai Bulus ya ce masa, “Allah zai buge ka, kai farin bango! Ka zauna a can kana hukunta ni bisa ga doka, ga shi kai kanka kana ƙetare dokar ta wurin ba da umarni a buge ni!” Waɗanda suke tsaye kusa da Bulus kuwa suka ce masa, “Babban firist na Allah za ka zaga?” Bulus ya amsa ya ce, “’Yan’uwa, ai, ban san cewa shi ne babban firist ba; gama yana a rubuce cewa, ‘Kada ka yi mugun magana game da mai mulkin mutanenka.’ ” Bulus, da ya gane cewa waɗansu daga cikinsu Sadukiyawa ne sauran kuma Farisiyawa ne, sai ya ɗaga murya a Majalisar ya ce, “’Yan’uwana, ni Bafarisiye ne, ɗan Farisiyawa. Ana mini shari’a saboda begen da nake da shi a kan tashin matattu.” Da ya faɗi haka, sai gardama ta tashi tsakanin Farisiyawa da Sadukiyawa, taron kuwa ya rabu biyu. (Sadukiyawa suna cewa babu tashin matattu, babu mala’iku ko ruhohi. Amma Farisiyawa kuwa sun tsaya a kan cewa duk akwai.) Aka yi babbar hayaniya. Waɗansu daga cikin malaman dokokin da suke Farisiyawa suka miƙe tsaye suka yi gardama mai ƙarfi suna cewa, “Ba mu sami wani laifi a wurin mutumin nan ba. A ce wani ruhu ko mala’ika ne ya yi masa magana fa?” Gardamar kuwa ta yi tsanani har shugaban ƙungiyar sojan ya ji tsoro za su yayyage Bulus. Ya umarci sojoji su tafi su ƙwace shi ƙarfi da yaji daga wurinsu su kawo shi cikin barikin soja. Kashegari da dare Ubangiji ya tsaya kusa da Bulus ya ce, “Ka yi ƙarfin hali! Don kamar yadda ka yi shaida game da ni a Urushalima, haka kuma lalle, za ka yi shaidata a Roma.” Kashegari, Yahudawa suka ƙulla makirci suka kuma yi rantsuwa cewa ba za su ci ko sha ba sai sun kashe Bulus. Fiye da mutane arba’in ne suka ƙulla wannan makirci. Suka je wajen manyan firistoci da dattawa suka ce, “Mun yi babbar rantsuwa cewa ba za mu ci kome ba sai mun kashe Bulus. Saboda haka, sai ku da Majalisa sai ku roƙi shugaban ƙungiyar sojan yă kawo shi a gabanku kamar kuna so ku ƙara samun cikakken bayani game da zancensa. Mu kuwa muna a shirye mu kashe shi kafin yă iso nan.” Amma da ɗan ’yar’uwar Bulus ya ji wannan makirci, sai ya tafi cikin barikin soja ya gaya wa Bulus. Sai Bulus ya kira ɗaya daga cikin jarumawan ya ce, “Ka kai wannan saurayi wurin shugaban ƙungiyar soja; yana da wani abin da zai faɗa masa.” Saboda haka ya ɗauke shi ya kai wajen shugaban ƙungiyar sojan. Jarumin ya ce, “Bulus, ɗan kurkukun nan ya kira ni, ya roƙe ni in kawo wannan saurayi a wurinka domin yana da wani abin da zai faɗa maka.” Sai shugaban ƙungiyar sojan ya kama hannun saurayin ya ja shi gefe, ya tambaye shi cewa, “Mene ne kake so ka gaya mini?” Saurayin ya ce, “Yahudawa sun ƙulla za su roƙe ka ka kawo Bulus a gaban Majalisa gobe kamar suna neman ƙarin cikakken bayani game da Bulus. Kada ka yarda da su, domin fiye da mutum arba’in daga cikinsu suna fakonsa. Sun yi rantsuwa ba za su ci ko sha ba sai sun kashe shi. Suna nan a shirye yanzu, suna jira ka amince da roƙonsu.” Sai shugaban ƙungiyar sojan ya sallami saurayin ya kwaɓe shi ya ce, “Kada ka gaya wa kowa cewa ka faɗa mini wannan.” Sai ya kira biyu daga cikin jarumawansa, ya umarce su cewa, “Ku shirya sojoji ɗari biyu, da masu hawan dawakai saba’in da kuma masu māsu ɗari biyu su tafi Kaisariya da ƙarfe tara na daren nan. Ku shirya wa Bulus dawakai da zai hau don a kai shi wurin Gwamna Felis lafiya.” Ya kuma rubuta wasiƙa kamar haka, Kalaudiyus Lisiyas. Zuwa ga Mai Girma, Gwamna Felis. Gaisuwa. Yahudawa sun kama wannan mutum suna kuma dab da kashe shi, amma na zo da sojojina na ƙwato shi, saboda na ji shi ɗan ƙasar Roma ne. Na so in san abin da ya sa suke zarginsa, saboda haka na kawo shi a gaban Majalisarsu. Na tarar cewa zargin da ake masa ya shafi waɗansu abubuwan da suka shafi dokarsu ne, amma ba wani zargi a kansa da ya isa kisa ko a daure shi. Sa’ad da na sami labari cewa akwai wani makircin da aka ƙulla masa, sai na aika shi wurinka nan da nan. Na kuma umarci masu zarginsa su kai ƙararsu gare ka. Saboda haka sojojin, don cika umarni, suka ɗauki Bulus da dad dare suka kawo shi har Antifatiris. Kashegari suka bar masu hawan dawakai suka ci gaba da shi, yayinda sojojin suka koma barikin soja. Sa’ad da masu hawan dawakai suka isa Kaisariya, sai suka ba wa gwamna wasiƙar suka kuma miƙa masa Bulus. Gwamna ya karanta wasiƙar ya kuma tambaya ko daga wanda lardi ne ya fito. Da ya ji cewa shi daga Silisiya ne, sai ya ce, “Zan ji batunka lokacin da masu zarginka suka iso.” Sa’an nan ya ba da umarni a kai Bulus a tsare shi a fadar Hiridus. Bayan kwana biyar sai Ananiyas babban firist ya tafi Kaisariya tare da waɗansu daga cikin dattawa da kuma wani lauya mai suna Tertullus, suka kawo ƙararsu game da Bulus a gaban gwamna. Sa’ad da aka shigo da Bulus, sai Tertullus ya shiga kai ƙararsa a gaban Felis yana cewa, “Mun daɗe muna zaman lafiya a ƙarƙashinka, hangen nesanka kuma ya kawo gyare-gyare a wannan ƙasa. Ko’ina da kuma a kowace hanya, ya mafifici Felis, mun amince da wannan da godiya marar iyaka. Amma don kada in ƙara gajiyar da kai, ina roƙonka ka yi haƙuri ka saurari ɗan taƙaitaccen jawabinmu. “Mun tarar da wannan mutum fitinanne ne, yana tā-da-na-zaune-tsaye a tsakanin Yahudawa ko’ina a duniya. Shi shugaban ɗarikar Nazarawa har ma ya yi ƙoƙari ya ƙazantar da haikali; shi ya sa muka kama shi. Ta wurin bincika shi da kanka za ka gane gaskiyar game da dukan waɗannan zargin da muke kawo a kansa.” Yahudawa ma suka goyi bayan zargin, suna tabbatar cewa waɗannan abubuwa haka suke. Da gwamna ya yi masa alama yă yi magana, sai Bulus ya amsa ya ce, “Na san cewa ka yi shekaru da yawa kana mulki a wannan ƙasa; saboda haka ina farin ciki in kāre kaina. Da sauƙi za ka iya tabbatar cewa, bai fi kwana goma sha biyu da suka wuce ne na tafi Urushalima, domin yin sujada ba. Masu zargina ba su same ni ina gardama da kowa a haikali, ko kuma ina tā da hankalin jama’a a majami’u ko kuwa wani wuri dabam a cikin birni ba. Ba kuwa za su iya tabbatar maka ƙarar da suke yi yanzu a kaina ba. Amma na yarda cewa ina bauta wa Allah na kakanninmu a matsayin mai bin Hanyar da suke kira ɗarika. Na gaskata dukan abin da ya amince da Doka da yake kuma a rubuce cikin Annabawa, ina kuma da irin bege ɗaya ga Allah yadda mutanen nan suke da shi, cewa akwai tashin matattu masu adalci da masu mugunta duka. Saboda haka, ina ƙoƙari kullum in kasance da lamiri mai tsabta a gaban Allah da mutane. “Bayan ’yan shekaru da dama da ba na nan, sai na dawo Urushalima don in kawo wa mutanena kyautai saboda matalauta in kuma yi sadaka. Ni tsarkake ne sa’ad da suka same ni cikin filin haikalin ina yin haka. Babu taro tare da ni, ba kuwa ina tā da hankali ba. Amma akwai waɗansu Yahudawa daga lardin Asiya, waɗanda ya kamata suna a nan a gabanka su kawo ƙara in suna da wani a kaina. Ko kuwa waɗannan da suke a nan su faɗi laifin da suka same ni da shi sa’ad da na tsaya a gaban Majalisa, sai ko wannan abu ɗaya kaɗai da na ɗaga murya na faɗi yayinda nake tsaye a gabansu cewa, ‘A game da tashin matattu ake mini shari’a a gabanku yau.’ ” Sai Felis, wanda yake da cikakken sani game da Hanyar, ya ɗaga sauraron ƙarar. Ya ce, “In Lisiyas shugaban ƙungiyar soja ya iso, zan yanke muku shari’a.” Ya yi wa jarumin umarni yă tsare Bulus amma yă ba shi ’yanci yă kuma bar abokansa su lura da bukatunsa. Bayan ’yan kwanaki da dama sai Felis ya zo da matarsa Durusilla, mutuniyar Yahuda. Sai ya aika a zo da Bulus ya kuma saurare shi da yake magana game da bangaskiya cikin Kiristi Yesu. Da Bulus ya ci gaba jawabi a kan adalci, kamunkai da kuma hukunci mai zuwa, sai Felis ya tsorata ya ce, “Yanzu kam, ya isa haka! Kana iya tafi. In na sami zarafi, zan kira ka.” A wani fanni yana sa rai cewa Bulus zai ba shi toshiyar baki, saboda haka ya yi ta aika a kira masa Bulus yă yi magana da shi. Da shekaru biyu suka wuce, sai Forsiyus Festus, ya gāji Felis, amma domin Felis ya so yă biya wa Yahudawa bukata, sai ya bar Bulus a kurkuku. Kwana uku bayan isowa a lardin, sai Festus ya haura daga Kaisariya zuwa Urushalima, inda manyan firistoci da shugabannin Yahudawa suka bayyana a gabansa suka kuma gabatar da ƙararsu a kan Bulus. Suka roƙi Festus a gaggauce a matsayin alfarma gare su, da yă sa a mai da Bulus Urushalima, gama sun ’yan kwanto su kashe shi a hanya. Festus ya amsa ya ce, “Bulus yana tsare a Kaisariya, ni da kaina kuma zan je can ba da daɗewa ba. Ku sa waɗansu daga cikin shugabanninku su tafi tare da ni su kawo ƙararsu a kan mutumin a can, in ya aikata wani laifi.” Bayan ya yi kwanaki takwas ko goma tare da su, sai ya gangara zuwa Kaisariya, kashegari kuma ya kira a yi zaman kotu ya kuma umarta a kawo Bulus a gabansa. Da Bulus ya bayyana, sai Yahudawan da suka gangaro daga Urushalima suka tsaya kewaye shi, suna kawo ƙarar masu tsanani da yawa a kansa, waɗanda ba su iya tabbatarwa ba. Sa’an nan Bulus ya kāre kansa ya ce, “Ban aikata wani laifi game da dokokin Yahudawa ko game da haikali ko kuma game da Kaisar ba.” Festus, da yake yana so yă yi wa Yahudawa alfarma, sai ya ce wa Bulus, “Ka yarda ka je Urushalima a yi maka shari’a a can a gabana a kan waɗannan zarge?” Bulus ya amsa ya ce, “Yanzu ina tsaye a gaban kotun Kaisar, inda ya kamata a yi mini shari’a. Ban yi wani laifi ga Yahudawa ba, kai da kanka ma ka san da haka sarai. In kuwa ina da wani laifin da ya isa kisa, ban ƙi in mutu ba. Amma in ƙarar da waɗannan Yahudawa suka kawo a kaina ba gaskiya ba ne, ba wanda yake da iko ya ba da ni a gare su. Na ɗaukaka ƙara zuwa gaban Kaisar!” Bayan Festus ya yi shawara da majalisarsa sai ya ce, “Ka ɗaukaka ƙara zuwa gaban Kaisar. To, ga Kaisar kuwa za ka tafi!” Bayan ’yan kwanaki sai Sarki Agiriffa da Bernis suka iso Kaisariya don su yi wa Festus gaisuwar bangirma. Da yake za su yi kwanaki da dama a can, sai Festus ya tattauna batun Bulus da sarki. Ya ce, “Akwai mutumin da Felis ya bari a daure. Sa’ad da na je Urushalima, manyan firistoci da dattawan Yahudawa suka kawo ƙara game da shi suka kuma nema a hukunta shi. “Na gaya musu cewa ba al’adar Romawa ba ce a hukunta mutum kafin ya fuskanci masu ƙararsa ya kuma sami damar kāre kansa game da ƙararsu. Da suka zo nan tare da ni, ban yi wani jinkiri ba, na kira zaman kotu kashegari kuma na umarta a kawo mutumin. Sa’ad da masu zarginsa suka tashi tsaye don su yi magana, ba su zarge shi da wani laifin da na yi tsammani ba. A maimako haka, sai suka kawo waɗansu ’yan maganganu game da addininsu da ba su yarda da shi ba da kuma game da wani Yesu da ya mutu wanda Bulus ya ce yana da rai. Na rasa yadda zan bincike irin abubuwan nan; saboda haka na yi tambaya ko zai yarda ya tafi Urushalima a yi masa shari’a a can game da waɗannan zargi. Da Bulus ya ɗaukaka ƙara zuwa gaban Babban Sarki sai na umarta a tsare shi har kafin in aika shi zuwa ga Kaisar.” Sai Agiriffa ya ce wa Festus, “Ni ma zan so in saurari mutumin da kaina.” Sai ya amsa ya ce, “Za ka kuwa ji shi gobe.” Kashegari Agiriffa da Bernis suka yi shiga irin ta sarauta suka shiga ɗakin jama’a tare da manyan sojoji da manyan mutanen birni. Da umarnin Festus, sai aka shigo da Bulus. Sai Festus ya ce, “Sarki Agiriffa, da kuma dukan waɗanda suke tare da mu, kun ga wannan mutum! Dukan jama’ar Yahudawa sun kawo mini kararsa a Urushalima da kuma a nan Kaisariya, suna kururuwa suna cewa bai kamata a bar shi da rai ba. Ban same shi da wani laifin da ya isa kisa ba, amma saboda ya ɗaukaka ƙararsa zuwa gaban Babban Sarki sai na yanke shawara in aika da shi Roma. Ba ni da wata tabbatacciyar maganar da zan rubuta wa Mai Girma game da shi. Saboda haka na kawo shi a gabanku duka, musamman a gabanka, Sarki Agiriffa, saboda a sakamakon wannan bincike zan iya samun abin da zan rubuta. Don a ganina wauta ce a aika da ɗan kurkuku ba tare da an nuna zargin da ake yi a kansa ba.” Sai Agiriffa ya ce wa Bulus, “An ba ka izini ka yi magana.” Saboda haka Bulus ya yi alama da hannunsa ya fara kāriyarsa. Ya ce, “Sarki Agiriffa, na yi sa’a da na tsaya a gabanka yau yayinda nake kāriyata game da dukan zargin Yahudawa, musamman ma domin ka saba sosai da dukan al’adun Yahudawa da kuma maganganunsu. Saboda haka ina roƙonka ka saurare ni da haƙuri. “Yahudawa duk sun san yadda na yi rayuwa tun ina yaro, daga farkon rayuwata a ƙasarmu da kuma a Urushalima. Sun san ni tun da daɗewa za su kuwa shaida, in suna so, cewa bisa ga ɗarikar addininmu mafi tsanani, na yi rayuwar Bafarisiye ne. Yanzu kuwa saboda begena cikin abin da Allah ya yi wa kakanninmu alkawari ne, ake mini shari’a yau. Wannan shi ne alkawarin da kabilanmu goma sha biyu suke bege su ga cikawarsa, yayinda suke bauta wa Allah da himma dare da rana. Ya Sarki, saboda wannan bege ne fa Yahudawa suke zargena. Don me wani a cikinku zai yi shakka cewa Allah yana tā da matattu? “Ni ma a dā na tabbata cewa ya kamata in yi duk abin da zan iya yi domin in yi gāba da sunan Yesu Banazare. Abin da na yi ke nan a Urushalima. Da izinin manyan firistoci na sa tsarkaka da yawa a kurkuku, sa’ad da kuma ake kashe su, nakan ka da ƙuri’ata gāba da su. Sau da dama nakan bi majami’a-majami’a, in sa a yi musu hukunci. Na kuma yi ƙoƙarin tilasta su su yi saɓo. Don kuma tsananin fushi da su, sai da na fafare su har waɗansu garuruwa na ƙetaren iyaka, ina tsananta musu. “A cikin irin tafiye-tafiyen nan ne ina kan hanya zuwa Damaskus tare da izini daga manyan firistoci. Da tsakar rana, ya sarki, sa’ad da nake kan hanya, sai na ga wani haske daga sama, fiye da hasken rana, yana haskakawa kewaye da ni da abokan tafiyata. Dukanmu muka fāɗi ƙasa, na kuwa ji wata murya tana ce mini da harshen Arameyik, ‘Shawulu, Shawulu, don me kake tsananta mini? Yana da wuya ka shuri tsinken tsokanar dabba.’ “Sai na yi tambaya na ce, ‘Wane ne kai, ya Ubangiji?’ “Ubangiji ya ce, ‘Ni ne Yesu wanda kake tsananta wa. Yanzu ka tashi, ka tsaya da ƙafafunka. Na bayyana a gare ka don in naɗa ka bawa da kuma mai shaidar abin da ka gani game da ni da kuma abin da zan nuna maka. Zan tsirar da kai daga mutanenka da kuma daga Al’ummai. Ina aikan ka zuwa gare su domin ka buɗe idanunsu su kuwa juyo daga duhu zuwa haske, daga mulkin Shaiɗan kuma zuwa wurin Allah, domin su sami gafarar zunubai da kuma matsayi a cikin waɗanda aka tsarkake ta wurin bangaskiya a cikina.’ “Saboda haka fa, Sarki Agiriffa, ban yi rashin biyayya ga wahayin nan daga sama ba. Da farko ga waɗanda suke a Damaskus, sa’an nan ga waɗanda suke a Urushalima da kuma cikin dukan Yahudiya, da kuma ga Al’ummai su ma, na yi wa’azi don su tuba su juyo ga Allah su kuma tabbatar da tubansu ta wurin ayyukansu. Shi ya sa Yahudawa suka kama ni a filin haikali suka kuma yi ƙoƙarin kashe ni. Amma na sami taimakon Allah har yă zuwa yau. Yanzu ga ni a tsaye a nan, ina shaida ga babba da yaro. Ba na faɗin kome fiye da abin da annabawa da Musa suka ce zai faru, cewa Kiristi zai sha wahala, kuma a matsayin wanda yake na fari da zai tashi daga matattu, zai yi shelar haske ga mutanensa da kuma Al’ummai.” A nan ne fa Festus ya tsai da kāriyar Bulus. Ya yi ihu ya ce, “Bulus! Kai dai ruɗaɗɗe ne, yawan karatunka yana juya maka kai.” Bulus ya amsa ya ce, “Ba na hauka, ya mafifici Festus. Abin da nake faɗi gaskiya ne da kuma mai kyau. Sarki ya san waɗannan abubuwa, ina kuma iya yin magana da shi a sake. Na tabbata cewa ba ɗaya daga cikin waɗannan da ya kuɓuce saninsa, domin ba a ɓoye aka yi shi ba. Sarki Agiriffa ka gaskata da annabawa? Na san ka gaskata.” Sai Agiriffa ya ce wa Bulus, “Kana tsammani cewa a cikin ɗan ƙanƙanin lokaci kana so ka mai da ni Kirista?” Bulus ya amsa ya ce, “Ko a ɗan lokaci, ko a lokaci mai yawa, ina addu’a ga Allah cewa, ba kai kaɗai ba amma duk waɗanda suke saurare ni a yau su zama abin da nake, sai dai ban da sarƙoƙin nan.” Sai sarki ya tashi, haka kuma gwamna da Bernis da kuma waɗanda suke zaune tare da su. Suka bar ɗakin, kuma yayinda suke magana da juna, sai suka ce, “Wannan mutum ba ya yin kome da ya isa kisa ko dauri.” Sai Agiriffa ya ce wa Festus, “Da ba don wannan mutum ya ɗaukaka ƙara zuwa gaban Kaisar ba da an sake shi.” Sa’ad da aka yanke shawara cewa za mu tashi a jirgin ruwa zuwa Italiya, sai aka danƙa Bulus da waɗansu ’yan kurkuku a hannun wani jarumin mai suna Juliyos, wanda yake na Bataliyar Babban Sarki. Muka shiga jirgin ruwa daga Andiramitiyum wanda yake shirin tashi zuwa tasoshin da suke bakin tekun lardin Asiya, sai muka kama tafiya. Aristarkus, mutumin Makidoniya daga Tessalonika, yana tare da mu. Kashegari muka sauka a Sidon; Juliyos kuwa, cikin alheri ga Bulus, ya bar shi yă je wajen abokansa domin su biya masa bukatunsa. Daga can kuma muka sāke kama tafiya muka zaga ta bayan tsibirin Saifurus saboda iska tana gāba da mu. Sa’ad da muka ƙetare tekun da yake sassan gaɓar Silisiya da Famfiliya sai muka sauka a Mira ta Lisiya. A can jarumin ya sami wani jirgin ruwan Alekzandariyan da za shi Italiya sai ya sa mu a ciki. Tafiyar ta ɗauki kwanaki da yawa muna yi kaɗan-kaɗan da ƙyar muka iso kusa da gaɓar Kinidus. Da iskar ta hana mu ci gaba, sai muka bi ta bayan tsibirin Kirit ɗaura da Salmone. Muka ci gaba a gefen gaɓar da ƙyar har muka iso wani wurin da ake kira Kyakkyawan Mafaka, kusa da garin Laseya. An riga an ɓata lokaci da yawa, tafiya kuwa ta riga ta zama da hatsari domin a lokacin Azumi ya riga ta wuce. Saboda haka Bulus ya gargaɗe su, ya ce, “Mutane, ina gani tafiyarmu za tă zama da masifa ta kuma kawo babbar hasara ga jirgin ruwan da kaya, da kuma ga rayukanmu ma.” Amma jarumin, a maimakon ya saurari abin da Bulus ya ce, sai ya bi shawarar matuƙi da kuma mai jirgin ruwan. Da yake tashar jirgin ruwan ba tă dace a ci damina a can ba, yawanci suka ba yanke shawara cewa mu ci gaba da tafiya, da bege za mu kai Funis mu ci damina a can. Wannan tashar jirgin ruwa ne a Kirit, tana fuskantar kudu maso yamma da kuma arewa maso yamma. Da iska ta fara busowa daga kudu a hankali, sai suka yi tsammani sun sami abin da suke nema; saboda haka suka janye ƙugiyar jirgin ruwa suka bi ta gefen tsibirin Kirit. Ba a jima ba, sai ga wata guguwar iska mai ƙarfin da ake kira “’Yar arewa maso gabas,” ta buga daga tsibirin. Iskar ta ci ƙarfin jirgin ruwan har ya kāsa fuskantar iskar; saboda haka muka sallamar mata tă yi ta tura mu. Da muka bi ta bayan wani ɗan tsibirin da ake kira Kauda, da ƙyar muka jawo ɗan ƙaramin jirgin kusa da jirgin. Da mutanen suka jawo shi cikin babban jirgin ruwan, sai suka sa igiyoyi ta ƙarƙashin jirgin ruwan kanta don su ɗaɗɗaura shi. Don gudun kada a fyaɗa mu da yashin gaɓar Sirtis, sai suka saukar da ƙugiyar jirgin ruwan, suka bari aka yi ta tura jirgin haka. Haka muka yi ta shan bugun guguwar hadarin nan kashegari suka fara jajjefar da kayan da jirgin yake ɗauke da su a cikin teku. A rana ta uku, da hannuwansu suka jefar da kayan aikin jirgin ruwan a cikin teku. Da dai aka yi kwana da kwanaki ba a ga rana ko taurari ba guguwar iska kuma ta ci gaba da bugowa, a ƙarshe muka fid da zuciya za mu tsira. Bayan mutanen sun daɗe ba su ci abinci ba, Bulus ya miƙe tsaye a gabansu ya ce, “Mutane, da kun ji shawarata na kada ku tashi daga Kirit, da ba ku fāɗa wannan masifa da hasara ba. Amma yanzu ina ƙarfafa ku ku yi ƙarfin hali, domin ba ɗayanku da zai rasa ransa; jirgin ruwan ne kaɗai zai hallaka. Jiya da dare wani mala’ikan Allahn da nake nasa nake kuma bauta wa ya tsaya kusa da ni ya ce, ‘Kada ka ji tsoro, Bulus. Lalle za ka tsaya a gaban Kaisar a yi maka shari’a; Allah kuma cikin alherinsa ya ba ka dukan rayukan mutanen da suke tafiya tare da kai.’ Saboda haka ku yi ƙarfin hali, ku jama’a, gama gaskata Allah a kan cewa yadda aka faɗa mini ɗin nan, haka zai faru. Duk da haka, dole a fyaɗa mu a wani tsibiri.” A dare na goma sha huɗu iska dai tana ta korarmu a Tekun Adiriyatik, wajen tsakar dare sai masu tuƙin jirgin suka zaci sun yi kusa da ƙasa. Sai suka gwada zurfin ruwan suka ga ya kai ƙafa ɗari da ashirin. Bayan ɗan lokaci kaɗan suka sāke gwadawa suka ga zurfin ya kai ƙafa tasa’in. Don gudun kada a fyaɗa mu a kan duwatsu, sai suka saki ƙugiyoyin jirgin guda huɗu daga bayan jirgin suka yi fata gari ya waye. Cikin ƙoƙarin tserewa daga jirgin, sai masu tuƙin jirgin suka saukar da ɗan ƙaramin jirgin ruwan cikin tekun, suka yi kamar za su saki waɗansu ƙugiyoyi daga sashen gaba na babban jirgin ne. Sai Bulus ya ce wa jarumin da kuma sojojin, “In mutanen nan ba su tsaya a cikin jirgin nan ba, ba za ku tsira ba.” Sai sojojin suka yayyanke igiyoyin da suke riƙe da ɗan ƙaramin jirgin, suka bar shi ya bi ruwa. Kafin gari ya waye Bulus ya roƙe su duka su ci abinci. Ya ce, “Kwana goma sha huɗu ke nan, kuna zama cikin zulumi kun kuma kasance ba abinci, ba ku ci kome ba. Ina roƙonku yanzu ku ci abinci. Kuna bukatarsa don ku rayu. Ba ɗayanku da zai rasa ko gashin kansa guda ɗaya.” Bayan da ya faɗi haka, sai ya ɗauki burodi ya yi godiya ga Allah a gabansu duka. Sa’an nan ya gutsuttsura ya fara ci. Dukansu kuwa suka sami ƙarfafawa, suka kuma ci abinci. Dukanmu a jirgin kuwa mutane 276 ne. Sa’ad da suka ci iyakar abin da suke so, sai suka rage nauyin jirgin ta wurin zubar da hatsin a cikin tekun. Da gari ya waye, ba su gane ƙasar da suke ba, amma suka ga wani lungu da gaci mai yashi, sai suka yanke shawara su kai jirgin can in za su iya. Da suka yanke ƙugiyoyin, sai suka bar su a cikin teku a lokaci guda kuma suka ɓalle maɗaurin abin juya jirgin. Sai suka tā da filafilan gaban jirgin daidai yadda iska za tă tura shi gaba, sa’an nan suka nufi gaci. Amma jirgin ruwan ya shiga yashi ya kafe. Kan jirgin ya shiga cikin yashin ya kāsa motsi, sai jirgin ya fara farfashewa ta baya saboda haukan raƙuman ruwa. Sojojin suka yi niyya su kakkashe ’yan kurkukun don hana waninsu yă yi iyo yă tsere. Amma jarumin ya so yă ceci ran Bulus, sai ya hana su aiwatar da niyyarsu. Ya kuma yi umarni duk waɗanda suka iya ruwa su fara fāɗawa zuwa gaci. Sauran kuma su bi katakai zuwa can ko kuma a kan tarkacen jirgin ruwan. Ta haka kowa ya kai bakin teku lafiya. Bayan da muka kai bakin tekun lafiya, sai muka tarar cewa sunan tsibirin Malta ne. Mutanen tsibirin kuwa suka nuna mana babban alheri. Suka hura wuta suka marabce mu duka saboda ana ruwan sama da kuma sanyi. Bulus ya tattara tarin itace, yayinda kuma yake sa itacen a wuta, sai maciji ya ɓullo saboda zafi, ya dāfe a hannunsa. Da mutanen tsibirin suka ga macijin yana lilo a hannunsa, sai suka ce wa juna “Lalle, wannan mutum mai kisankai ne; gama ko da yake ya tsira daga teku, Adalci bai bar shi ya rayu ba.” Amma Bulus ya karkaɗe macijin a cikin wuta, bai kuwa ji wani ciwo ba. Mutanen kuma suka yi zato zai kumbura ko kuma nan da nan zai fāɗi matacce, amma da aka daɗe ba su ga wani abu ya faru da shi ba, sai suka sāke ra’ayi suka ce shi wani allah ne. Akwai wani filin nan kusa wanda yake na Fubiliyus, babban shugaban tsibirin. Shi ne ya karɓe mu a gidansa da alheri ya kuma ciyar da mu har kwana uku. Mahaifinsa kuwa yana kwanciya a gado yana fama da zazzaɓi da atuni. Bulus ya shiga ciki don yă gan shi, bayan ya yi masa addu’a, sai ya ɗibiya masa hannuwa ya warkar da shi. Sa’ad da wannan ya faru, sauran marasa lafiya a tsibirin suka zo aka kuma warkar da su. Suka girmama mu ta kowane hali da muka shirya za mu tashi, sai suka ba mu abubuwan da muke bukata. Bayan wata uku sai muka tashi a wani jirgin ruwan da ya ci damina a tsibirin. Jirgin ruwa kuwa na Alekzandariya ne yana da siffar tagwayen allolin Kasto da Follus. Muka isa Sirakus a can muka yi kwana uku. Daga can muka tashi muka isa Regiyum. Kashegari iskar kudu ta taso, kashegari kuma muka kai Futeyoli. A can muka tarar da waɗansu ’yan’uwa waɗanda suka gayyaci mu mu yi mako ɗaya da su. Da haka dai muka kai Roma. ’Yan’uwan da suke can sun sami labari cewa muna zuwa, sai suka tashi tun daga Kasuwar Affiyus da Masauƙi Uku don su tarye mu. Da ganin mutanen nan sai Bulus ya gode wa Allah ya kuma sami ƙarfafawa. Da muka isa Roma, sai aka yarda wa Bulus yă zauna shi kaɗai, tare da sojan da zai yi gadinsa. Bayan kwana uku sai ya kira taron shugabannin Yahudawa. Da suka taru, Bulus ya ce musu, “’Yan’uwana, ko da yake ban yi wa mutanenmu wani laifi ba ko kuma wani abu game da al’adun kakanninmu, aka kama ni a Urushalima aka kuma ba da ni ga Romawa. Suka tuhume ni suka kuma so su sake ni, domin ba a same ni da wani laifin da ya cancanci kisa ba. Amma da Yahudawa suka ƙi, sai ya zama mini dole in ɗaukaka ƙara zuwa gaban Kaisar ba don ina da wani zargin da zan kawo game da mutanena ba. Saboda wannan ne na nemi in gan ku in kuma yi magana da ku. Saboda begen Isra’ila ne, nake a daure da wannan sarƙa.” Suka amsa cewa, “Ba mu sami wani wasiƙa daga Yahudiya game da kai ba, kuma ba kowa daga cikin ’yan’uwan da suka zo daga can ya kawo wani labari ko ya faɗi wani mummuna abu game da kai. Amma muna so mu ji ra’ayinka, gama mun san cewa mutane ko’ina suna muguwar magana a kan wannan ɗarikar.” Suka shirya su sadu da Bulus wata rana, suka ma zo da yawa fiye da dā a wurin da Bulus yake zama. Daga safe har zuwa yamma ya yi ta yin musu bayani, ya kuma shaida musu mulkin Allah yana ƙoƙarin rinjayarsu game da Yesu daga Dokar Musa da kuma daga Annabawa. Waɗansu suka rinjayu da abin da ya faɗa, amma waɗansu suka ba su gaskata ba. Suka kāsa yarda da juna suka fara watsewa bayan Bulus ya yi wannan magana guda cewa, “Ruhu Mai Tsarki ya faɗa wa kakannin-kakanninku gaskiya sa’ad da ya ce ta bakin annabi Ishaya cewa, “ ‘Je ka wurin mutanen nan ka ce, “Za ku yi ta ji amma ba za ku fahimta ba; za ku yi ta dubawa, amma ba za ku gani ba.” Gama zuciyar mutanen nan ta yi tauri; da ƙyar suke ji da kunnuwansu, sun kuma rufe idanunsu. In ba haka ba za su iya gani da idanunsu, su ji da kunnuwansu, su fahimta a zukatansu, su kuma juyo, in kuwa warkar da su.’ “Saboda haka na so ku san cewa an aika da ceton Allah ga Al’ummai, za su kuwa saurara!” Shekaru biyu cif Bulus ya zauna a can a gidansa na haya yana marabtar duk wanda ya je wurinsa. Ya yi wa’azin mulkin Allah yana kuma koyarwa game da Ubangiji Yesu Kiristi, gabagadi ba tare da wani abu ya hana shi ba. Bulus, bawan Kiristi Yesu, kirayaye don yă zama manzo, keɓaɓɓe kuma domin bisharar Allah. Bisharar da Allah ya yi alkawari tuntuni ta bakin annabawansa a cikin Nassosi Masu Tsarki game da Ɗansa. Wanda bisa ga mutuntakarsa, zuriyar Dawuda ne. Wanda bisa ga Ruhun tsarki, an shaida shi da iko cewa shi Ɗan Allah ne ta wurin tashinsa daga matattu. Wannan bishara kuwa game da Yesu Kiristi Ubangijinmu ne. Ta wurinsa da kuma saboda sunansa, muka sami alheri muka kuma zama manzanni don mu kira mutane daga cikin dukan Al’ummai zuwa ga biyayyar da take zuwa daga bangaskiya. Ku ma kuna cikin waɗanda aka kira ku zama na Yesu Kiristi. Wannan wasiƙa ce zuwa ga dukanku da kuke a Roma waɗanda Allah yake ƙauna, waɗanda kuma ya kira domin su zama tsarkaka. Alheri da salama daga Allah Ubanmu da kuma daga Ubangiji Yesu Kiristi, su kasance tare da ku. Da farko, ina gode wa Allahna ta wurin Yesu Kiristi saboda ku duka, gama ana ba da labarin bangaskiyarku a ko’ina a duniya. Allah, wanda nake bauta wa da dukan zuciyata cikin wa’azin bisharar Ɗansa, shi ne shaidata a kan yadda kullum ina tunawa da ku cikin addu’o’ina a kowane lokaci; ina kuma addu’a cewa a ƙarshe in Allah ya yarda hanya za tă buɗe mini in zo wurinku. Ina marmarin ganinku don in ba ku wata baiwar ruhaniya, don ku yi ƙarfi wato, don ni da ku mu ƙarfafa juna ta wurin bangaskiyarmu. Ina so ku sani ’yan’uwa cewa na yi shirin zuwa wurinku sau da dama (amma aka hana ni yin haka sai yanzu). Na so in zo domin in sami mutane wa Kiristi a cikinku, kamar yadda na yi a cikin sauran Al’ummai. Ina da hakki ga Hellenawa da waɗanda ba Hellenawa ba, ga masu hikima da kuma marasa azanci. Shi ya sa na yi himma sosai in yi muku wa’azin bishara ku ma da kuke a Roma. Ba na jin kunyar bishara, gama ita ikon Allah ne domin ceton kowa da ya gaskata, da farko ga Yahudawa, sa’an nan ga Al’ummai. Gama a cikin bishara an bayyana adalci daga Allah wanda yake ta wurin bangaskiya daga farko zuwa ƙarshe, kamar yadda yake a rubuce cewa, “Mai adalci zai rayu ta wurin bangaskiya.” Ana bayyana fushin Allah daga sama a kan dukan rashin sanin Allah da kuma muguntar mutanen da suke danne gaskiya ta wurin muguntarsu, gama abin da ana iya sani game da Allah a bayyane yake a gare su, domin Allah ya bayyana musu shi. Gama tun halittar duniya halayen Allah marar ganuwa, madawwamin ikonsa da kuma allahntakarsa, ana iya ganinsu sarai, ana fahimtarsu ta wurin abubuwan da Allah ya halitta, domin kada mutane su sami wata hujja. Gama ko da yake sun san Allah, ba su ɗaukaka shi a matsayin Allah ko su gode masa ba, sai dai tunaninsu ya zama banza, zukatansu masu wauta kuma suka duhunta. Ko da yake sun ɗauka su masu hikima ne, sai suka zama wawaye, suka kuma yi musayar ɗaukakar Allah marar mutuwa da siffofin da aka ƙera su yi kama da mutum mai mutuwa da tsuntsaye da dabbobi da kuma halittu masu ja da ciki. Saboda haka Allah ya yashe su ga mugayen sha’awace-sha’awacen zukatansu ga fasikanci don a ƙasƙantar da jikunansu ga yin abin kunya. Sun sauya gaskiyar Allah da ƙarya, suka kuma yi wa abubuwan da aka halitta sujada suna bauta musu a maimakon Mahalicci, wanda ake yabo har abada. Amin. Saboda wannan, Allah ya yashe su ga sha’awace-sha’awacensu masu banƙyama. Har matansu suka sauya daga haɗuwar mace da miji wadda ita ce daidai bisa ga halitta zuwa haɗuwa da ’yan’uwansu mata wadda ba daidai ba. Haka ma maza suka bar al’adar kwana da mata suka tunzura cikin sha’awar kwana da juna, abin da ba daidai ba bisa ga halitta. Maza suka aikata rashin kunya da waɗansu maza, suka jawo wa kansu sakamako daidai da bauɗewarsu. Da yake ba su yi tunani cewa ya dace su riƙe sanin Allah da suke da shi ba, sai ya yashe su ga tunanin banza da wofi, su aikata abin da bai kamata a yi ba. Sun cika da kowace irin ƙeta, mugunta, kwaɗayi, da tunanin banza da wofi. Suka kuma cika da kishi, kisankai, faɗa, ruɗu, da kuma riƙo a zuci. Su masu gulma ne, da masu ɓata suna, masu ƙin Allah, masu rashin kunya, masu girman kai, masu rigima; sukan ƙaga hanyoyin yin mugunta; suna rashin biyayya ga iyayensu; su marasa hankali ne, marasa bangaskiya, marasa ƙauna, marasa tausayi. Ko da yake sun san dokar adalcin Allah cewa masu aikata irin waɗannan abubuwa sun cancanci mutuwa, duk da haka ba cin gaba da aikata waɗannan abubuwa kaɗai suke yi ba, har ma suna goyon bayan masu yinsu. Saboda haka, kai da kake ba wa wani laifi, ba ka da wata hujja, gama a duk lokacin da kake ba wa wani laifi, kana hukunta kanka ne, domin kai da kake ba wa wani laifi kai ma kana aikata waɗannan abubuwa. Yanzu mun san cewa hukuncin Allah a kan masu aikata waɗannan abubuwa daidai ne. Saboda haka sa’ad da kai mutum kurum, kana ba su laifi, duk da haka kana aikata abubuwan nan, kana tsammani za ka tsere wa hukuncin Allah ne? Ko kuma kana rena wadatar alherinsa, haƙurinsa, da kuma jimrewarsa ne ba tare da sanin cewa alherin Allah yana kai ka ga tuba ba ne? Amma saboda taurinkanka da zuciyarka marar tuba, kana tara wa kanka fushi a ranar fushin Allah, sa’ad da za a bayyana hukuncinsa mai adalci. Allah, “Zai sāka wa kowane mutum gwargwadon aikin da ya yi.” Ga waɗanda ta wurin naciya suna yin nagarta suna neman ɗaukaka, girma da rashin mutuwa, su za a ba su rai madawwami. Amma ga waɗanda suke sonkai waɗanda suke ƙin gaskiya suke kuma bin mugunta, akwai fushi da haushi dominsu. Akwai wahala da baƙin ciki ga duk mutumin da yake aikata mugunta, da farko Yahudawa, sa’an nan Al’ummai, amma akwai ɗaukaka, girma da salama ga duk mutumin da yake aikata alheri, da farko Yahudawa, sa’an nan Al’ummai. Gama Allah ba ya nuna bambanci. Duk waɗanda suka yi zunubi a rashi sanin doka, a rashin doka za su hallaka, waɗanda kuma suka yi zunubi ƙarƙashin doka, a ƙarƙashin doka za a hukunta su. Gama ba masu jin dokar ne suke da adalci a gaban Allah ba, amma waɗanda suke yin biyayya da dokar, su za a ce da su masu adalci. Tabbatacce, sa’ad da Al’ummai, waɗanda ba su da dokar, suka aikata abubuwan da dokar take bukata, abubuwan sun zama doka ke nan gare su, ko da yake ba su da dokar. To, da yake sun nuna cewa abubuwan da dokar take bukata suna a rubuce a zukatansu, lamirinsu yana kuma ba da shaida, tunaninsu kuwa yanzu yana zarginsu ko kuma yana kāre su. Wannan zai faru a ranar da Allah ta wurin Yesu Kiristi zai shari’anta ɓoyayyun abubuwan da mutane suka yi, yadda bisharata ta furta. To, kai, da kake kiran kanka mutumin Yahuda; in kana dogara ga doka kana kuma taƙama da dangantakarka da Allah; in ka san nufinsa ka kuma amince da abin da yake mafifici domin an koyar da kai bisa ga doka; in ka tabbata cewa kai jagora ne ga makafi, haske ga waɗanda suke cikin duhu, mai koyar da masu wauta, malamin jarirai, domin a cikin dokar ce akwai sani da gaskiya to, kai mai koya wa waɗansu, ba kanka kake koya wa ba? Kai da kake wa’azi kada a yi sata, kana sata? Kai da kake cewa wa mutane kada su yi zina, kana yin zina? Kai da kake ƙyamar gumaka, kana wa haikali fashi? Kai da kake taƙama da doka, kana nuna rashin bangirma ga Allah ta wurin karya dokar? Kamar yadda yake a rubuce, “Ana saɓon sunan Allah a cikin Al’ummai saboda ku.” Kaciya tana da amfani in kana kiyaye dokar, amma in kana karya dokar, ka zama kamar ba a yi maka kaciya ba. In marasa kaciya suna kiyaye dokar, ashe, ba za a ɗauke su kamar an yi musu kaciya ba? Wanda ba shi da kaciya ta jiki duk da haka yana biyayya da dokar zai iya hukunta ka, kai da kake karya dokar, ko da yake kana da rubutaccen tsarin dokar an kuma yi maka kaciya. Mutum ba mutumin Yahuda ba ne in shi mutumin Yahuda ne kawai a jiki, haka kuma kaciya ba a waje ko a jiki kawai ba. A’a, mutum mutumin Yahuda ne in shi mutumin Yahuda ne a zuci; kuma kaciya ita ce kaciya ta zuci, ta wurin Ruhu, ba ta wurin rubutaccen doka ba. Irin wannan mutum yana samun yabo daga Allah ne, ba ɗan adam ba. To, mece ce ribar zama mutumin Yahuda, ko kuwa mene ne amfanin kaciya? Akwai riba ƙwarai ta kowace hanya! Da farko dai, su ne aka danƙa wa kalmomin nan na Allah. Amma a ce waɗansu ba su da bangaskiya fa? Rashin bangaskiyarsu nan zai shafe amincin Allah? Ko kaɗan! Bari Allah yă zama mai gaskiya, kowane mutum kuma yă zama maƙaryaci. Kamar yadda yake a rubuce cewa, “Gama a tabbatar kana da gaskiya, sa’ad da ka yi magana, ka kuma yi nasara sa’ad da ka yi shari’a.” Amma in rashin adalcinmu ya bayyana adalcin Allah a fili, me za mu ce ke nan? Za mu ce Allah ya yi rashin adalci ke nan da ya saukar da fushinsa a kanmu? (Ina magana kamar yadda mutum zai yi ne.) Sam, ko kusa! Da a ce haka ne, ta yaya Allah zai shari’anta duniya? Wani zai iya ce, “In a dalilin ƙaryata, gaskiyar Allah ta ƙara bayyana, har aka ƙara ɗaukaka shi, to, ta yaya zan zama mai zunubi, in ƙaryata tana kawo ɗaukaka ga Allah?” In haka ne, “Ba sai mu yi ta yin mugunta don yă zama hanyar samun nagarta ba”? Kamar yadda masu baƙar magana game da mu suna cewa wai haka muke faɗa. Tabbatacce za a hukunta irin waɗannan da hukuncin da ya dace da su. To, me za mu ce ke nan? Mun fi su ke nan? Ina, ko kaɗan! Mun riga mun zartar cewa da Yahudawa da Al’ummai duk suna a ƙarƙarshin zunubi. Kamar yadda yake a rubuce cewa, “Babu wani mai adalci, babu ko ɗaya; babu wani mai fahimta, babu wani mai neman Allah. Duk sun kauce gaba ɗaya, sun zama marasa amfani; babu wani mai aikata nagarta, babu ko ɗaya.” “Maƙogwaronsu kamar buɗaɗɗun kaburbura ne, harsunansu suna yin ƙarya.” “Dafin mugun maciji yana a leɓunansu.” “Bakunansu sun cike da la’ana da ɗacin rai.” “Ƙafafunsu suna saurin kai su zuwa ga zub da jini; hallaka da baƙin ciki suna ko’ina a hanyoyinsu, ba su kuma san hanyar salama ba.” “Babu tsoron Allah a idanunsu.” Yanzu mun san cewa dukan abin da doka ta ce, tana magana ne ga waɗanda suke ƙarƙarshin doka, saboda a rufe kowane baki; dukan duniya kuma ta ba da lissafin kanta a gaban Allah. Saboda haka babu wanda Allah zai ce da shi mai adalci ta wurin kiyaye doka kawai; a maimako, ta wurin doka ne muke sane da zunubi. Amma yanzu an bayyana wani adalci daga Allah, wannan adalcin bai danganta ga doka ba, Doka da Annabawa suna ba da shaida game da wannan adalci. Wannan adalcin Allah yana zuwa ta wurin bangaskiya a cikin Yesu Kiristi ga dukan waɗanda suka ba da gaskiya ne. Ba bambanci, gama duka sun yi zunubi suka kuma kāsa ga ɗaukakar Allah, an kuma kuɓutar da su kyauta ta wurin alherinsa bisa ga aikin fansar da ya zo ta wurin Yesu Kiristi. Allah ya miƙa Yesu Kiristi a matsayin hadayar kafara, ta wurin bangaskiya cikin jininsa. Ya yi haka domin yă nuna adalcinsa, domin a cikin haƙurinsa bai hukunta zunuban da aka aikata a dā ba ya yi haka domin yă nuna adalcinsa a wannan lokaci, saboda yă zama mai adalci da mai kuɓutar da waɗanda suke ba da gaskiya a cikin Yesu. To, me za mu yi taƙama a kai? Babu wani abin da zamu yi taƙama a kai. A kan wace ƙa’ida ce za mu yi taƙama? Ta hanyar bin doka ne? A’a, sai dai ta wurin bangaskiya. Gama mun tsaya a kan cewa ta wurin bangaskiya ne ake kuɓutar da mutum, ba ta wurin kiyaye doka ba. Allah ɗin, Allahn Yahudawa ne kaɗai? Shi ba Allahn Al’ummai ba ne? I, shi Allahn Al’ummai ne ma, da yake Allah ɗaya ne kaɗai, shi kuma zai kuɓutar da masu kaciya bisa ga bangaskiya da kuma marasa kaciya ta wurin wannan bangaskiya ɗin. To, za mu soke dokar saboda wannan bangaskiyar ne? Ko kaɗan! A maimako, sai ma tabbatar da ita muke yi. To, me za mu ce Ibrahim kakan kakanninmu ya gani game da wannan batu? In fa da gaske ne Ibrahim ya sami kuɓuta ta wurin ayyuka, yana da abin da zai yin taƙama da shi ke nan, amma ba a gaban Allah ba. Me Nassin ya ce? “Ibrahim ya gaskata Allah, aka kuma lissafta wannan adalci ne a gare shi.” To, sa’ad da mutum ya yi aiki, ba a lissafta ladan aikinsa a matsayin kyauta, sai dai a matsayin hakkinsa. Amma fa, game da mutumin da ba ya aiki sai dai dogara ga Allah wanda yake kuɓutar da masu mugunta, akan lissafta bangaskiyarsa a matsayin adalci ne. Dawuda ya faɗi haka sa’ad da ya yi magana game da albarkar da aka yi wa mutumin da Allah ya lissafta adalci a gare shi, ba don yă yi ayyuka ba. “Masu albarka ne waɗanda aka gafarta laifofinsu, waɗanda aka kuma rufe zunubansu. Mai albarka ne mutumin da Ubangiji ba zai taɓa lissafta zunubansa ba.” Shin, wannan albarkar a kan masu kaciya ne kawai, ko kuwa har da marasa kaciya ma? Mun sha faɗi cewa an lissafta bangaskiyar Ibrahim adalci ne a gare shi. A kan wane hali ne aka lissafta masa? Bayan da aka yi masa kaciya ne, ko kuwa kafin kaciyar? Ba bayan an yi masa kaciya ba ne, amma kafin a yi masa kaciya! Ya kuma karɓi alamar kaciya, hatimin adalcin da yake da shi ta wurin bangaskiya tun yana marar kaciya. Saboda haka fa, ya zama mahaifin dukan waɗanda suka gaskata domin su ma a lasafta su masu adalci ne, ba tare da an yi musu kaciya ba. Ya kuma zama mahaifin masu kaciya waɗanda ba kaciya kaɗai suke da ita ba amma har ma suna bin gurbin bangaskiyar da mahaifinmu Ibrahim yake da ita kafin aka yi masa kaciya. Ba ta wurin doka ce Ibrahim da zuriyarsa suka sami alkawarin cewa zai zama magājin duniya ba, amma sai dai ta wurin adalcin da yake zuwa ta wurin bangaskiya. Gama da a ce masu kiyaye doka ne magāda, ai, da bangaskiya ba ta da amfani, alkawarin kuma ya zama banza, domin doka tana jawo fushi ne. Kuma inda babu doka babu keta umarni ke nan. Saboda haka, alkawari yakan zo ta wurin bangaskiya ne, domin yă zama ta wurin alheri, don a tabbatar wa dukan zuriyar Ibrahim ba kawai ga waɗanda suke na doka ba amma har ma ga waɗanda suke na bangaskiyar Ibrahim. Shi ne kuwa mahaifinmu duka. Kamar yadda yake a rubuce cewa, “Na mai da kai uban al’ummai masu yawa.” Shi ubanmu ne a gaban Allah, wanda a cikinsa ya gaskata, Allahn da yake ba da rai ga matattu, yake kuma kiran abubuwan da ba su kasance ba su zama kamar sun kasance. Saɓanin dukan bege, Ibrahim cikin bege ya gaskata, haka kuwa ya zama uban al’ummai masu yawa, kamar yadda aka riga aka faɗa masa cewa, “Haka zuriyarka za tă zama.” Ba tare da ya bar bangaskiyarsa ta yi rauni ba, ya fuskanci gaskiyan nan mai cewa jikinsa mai tsufa matacce ne, da yake yana da shekara wajen ɗari, mahaifar Saratu kuma matacciya ce. Duk da haka bai yi shakka ta wurin rashin bangaskiya game da alkawarin Allah ba, sai ma ya ƙara ƙarfafa ga bangaskiyarsa, ya kuma ɗaukaka Allah, yana kuma da cikakken tabbaci cewa Allah yana da iko yă cika abin da ya yi alkawari. Shi ya sa, “aka lissafta adalci a gare shi.” Kalmomin nan, “aka lissafta a gare shi” ba a rubuta su saboda shi kaɗai ba ne, amma saboda mu ma, mu da Allah zai lissafta adalci, mu da muka ba da gaskiya gare shi da ya tashe Yesu Ubangijinmu daga matattu. An miƙa shi ga mutuwa saboda zunubanmu, aka kuma tashe shi zuwa rai saboda Allah zai same mu marasa laifi. Saboda haka, da yake an same mu marasa laifi ta wurin bangaskiya, muna da salama tare da Allah ta wurin Ubangijinmu Yesu Kiristi, ta wurinsa ne muka sami shiga wannan alherin da muke tsaye yanzu, ta wurin bangaskiya. Muna kuma farin ciki a begen ɗaukakar Allah. Ba haka kawai ba, amma muna kuma da farin ciki cikin shan wuyanmu, gama mun san cewa shan wuyan nan takan haifi jimiri; jimiri kuma yakan kawo hali mai kyau; hali mai kyau kuma yakan sa bege. Bege kuwa ba ya ba mu kunya, domin Allah ya zuba ƙaunarsa a zukatanmu ta wurin Ruhu Mai Tsarkin da ya ba mu. Kun ga, a daidai lokaci, yayinda muke marasa ƙarfi, Kiristi ya mutu saboda waɗanda ba su san Allah ba. Da ƙyar wani yă mutu saboda mai adalci, ko da yake saboda mutumin kirki wani zai iya ƙarfin hali yă mutu. Amma Allah ya nuna mana ƙaunarsa a wannan. Tun muna masu zunubi tukuna, Kiristi ya mutu dominmu. Da yake yanzu mun sami zama marasa laifi ta wurin jininsa, ashe kuwa za a cece mu daga fushin Allah ta wurinsa! Gama in kuwa, sa’ad da muke abokan gāban Allah, aka sulhunta mu da shi ta wurin mutuwar Ɗansa, ashe, da yake an sulhunta mu, za mu sami ceto ta wurin ransa! Ba ma haka yake kawai ba, har muna farin ciki da Allah ta wurin Ubangijinmu Yesu Kiristi, wanda ta wurinsa yanzu muka sami sulhu. Saboda haka, kamar yadda zunubi ya shigo duniya ta wurin mutum ɗaya, mutuwa kuma ta wurin zunubi, ta haka kuwa mutuwa ta shafi dukan mutane, domin dukan mutane sun yi zunubi. Gama kafin a ba da doka, zunubi yana nan a duniya. Amma ba a lissafin zunubi inda babu doka. Duk da haka, mutuwa ta yi mulki tun Adamu har yă zuwa Musa, ta yi mulki har ma a kan waɗanda ba su yi zunubi ta wurin taka umarni kamar yadda Adamu ya yi ba. A wata hanya dai Adamu shi ne kwatancin wani mutumin nan mai zuwa. Amma kyautan nan dabam take da laifin nan. Gama in mutane da yawa sun mutu saboda laifin mutum ɗayan nan, to, ai, alherin Allah da kuma kyautan nan mai zuwa ta wurin alherin mutum ɗayan nan, Yesu Kiristi, ya shafi mutane da yawa! Kyautar Allah kuwa ba kamar sakamakon da ya bi zunubin mutum gudan nan ba ne, Hukuncin ya bi zunubin mutum gudan nan, ya kuma kawo hallaka, amma kyautar ta bi laifofin masu yawa ta kuma sa Allah ya gan mu a matsayin marasa laifi. Gama in, ta wurin laifin mutum ɗaya, mutuwa ta yi mulki ta wurin mutum ɗayan nan, ashe, waɗanda suka sami kyautar alherin Allah a yalwace da kuma kyautar adalci za su yi mulki a wannan rayuwa ta wurin mutum ɗayan nan, Yesu Kiristi. Saboda haka, kamar yadda sakamakon laifin mutum guda ya jawo hallaka ga dukan mutane, haka ma sakamakon aikin adalci guda ya sa Allah ya same mu marasa laifi, wannan kuwa kawo rai ga dukan mutane. Gama kamar yadda ta wurin rashin biyayyar mutum guda, mutane masu yawa suka zama masu zunubi, haka kuma ta wurin biyayyar mutum guda, mutane da yawa za su zama masu adalci. An ba da dokar don mu ga yadda laifi yake da girma. Amma da zunubi ya ƙaru, sai alheri ya ƙaru sosai, domin, kamar yadda zunubi ya yi mulki cikin mutuwa, haka ma alheri yă yi mulki ta wurin adalci yă kuwa kawo rai madawwami ta wurin Yesu Kiristi Ubangijinmu. Me za mu ce ke nan? Za mu ci gaba da yin zunubi domin alheri yă haɓaka? Sam, ko kaɗan! Mun mutu ga zunubi; ta yaya za mu ci gaba da rayuwa a cikinsa kuma? Ko ba ku sani ba cewa dukanmu da aka yi wa baftisma a cikin Kiristi Yesu an yi mana baftismar ne zuwa cikin mutuwarsa? Saboda haka, an binne mu da shi ke nan, ta wurin baftisma cikin mutuwarsa, domin kamar yadda aka tā da Kiristi daga matattu ta wurin ɗaukakar Uba, haka mu ma mu yi zaman sabuwar rayuwa. In kuwa mun zama ɗaya tare da shi haka a cikin mutuwarsa, tabbatacce mu ma za mu zama ɗaya tare da shi cikin tashinsa daga matattu. Gama mun san cewa an gicciye halayenmu na dā tare da shi domin a kawar da jikin nan mai zunubi don kada mu ƙara zama bayi ga zunubi domin duk wanda ya mutu an ’yantar da shi daga zunubi ke nan. To, in mun mutu tare da Kiristi, mun gaskata cewa za mu rayu tare da shi kuma. Gama mun san cewa da yake an tā da Kiristi daga matattu, ba zai sāke mutuwa ba; mutuwa ba ta da sauran iko a kansa. Mutuwar da ya yi, ya mutu ne sau ɗaya tak, saboda yă shafe zunubi, amma rayuwar da yake yi, yana yi ne cikin tarayya da Allah. Haka ku ma, ku ɗauke kanku matattu ne ga ikon zunubi amma rayayyu cikin tarayya da Allah cikin Kiristi Yesu. Saboda haka kada ku bar zunubi yă mallaki jikin nan naku mai mutuwa yă sa ku zama masu biyayya ga mugayen sha’awace-sha’awacensa. Kada ku miƙa gaɓoɓin jikinku ga zunubi a matsayin kayan aikin mugunta, sai dai ku miƙa kanku ga Allah, a matsayin waɗanda aka fitar da su daga mutuwa zuwa rai; ku kuma miƙa gaɓoɓin jikinku gare shi a matsayin kayan aikin adalci. Gama zunubi ba zai zama maigidanku ba, domin ba kwa ƙarƙashin doka, sai dai ƙarƙashin alheri. Me za mu ce ke nan? Za mu ci gaba yin zunubi domin ba ma ƙarƙashin doka sai dai ƙarƙashin alheri? Sam, ko kaɗan! Ba ku sani ba cewa sa’ad da kuka miƙa kanku ga wani don ku yi masa biyayya a matsayin bayi, ko ku bayi ne ga zunubi, wanda yake kai ga mutuwa, ko kuwa ga biyayya, wadda take kai ga adalci, ashe, ba kun zama bayi ga wannan da kuke yi wa biyayya ba ke nan? Amma godiya ga Allah don ko da yake a dā ku bayi ne ga ikon zunubi, da dukan zuciyarku kun yi biyayya ga irin koyarwar da aka danƙa muku. An ’yanta ku daga zunubi, kun kuma zama bayi ga aikin adalci. Ina magana ne kamar mutane saboda kun raunana a jikinku. Kamar yadda kuka saba miƙa gaɓoɓin jikinku a bautar abubuwan ƙazanta da mugun aiki a kan mugun aiki, saboda haka yanzu sai ku miƙa su bayi ga aikin adalci mai kai ga zaman tsarki. Sa’ad da kuke bayin zunubi, ba ruwanku da aikin adalci. Wace riba ce kuka samu a lokacin, daga abubuwan nan da yanzu suka zama muku abin kunya? Ƙarshen irin abubuwan nan dai, mutuwa ne! Amma a yanzu da aka ’yantar da ku daga zunubi kuka kuma zama bayi ga Allah, ribar da kuka samu tana kai ga zaman tsarki, ƙarshenta kuwa rai madawwami ne. Gama sakamakon zunubi mutuwa ne, amma kyautar Allah rai madawwami ne a cikin Kiristi Yesu Ubangijinmu. Ba ku sani ba, ’yan’uwa, ina magana ne fa da mutanen da suka san doka, cewa dokar tana da iko a kan mutum muddin yana a raye ne kawai. Misali, bisa ga doka mace mai aure tana daure ga mijinta muddin mijin yana da rai, amma in mijinta ya mutu, an sake ta ke nan daga dokar aure. Saboda haka fa, in ta auri wani yayinda mijinta yana raye, za a ce da ita mazinaciya. Amma in mijinta ya mutu, an sake ta ke nan daga wannan doka, ita kuwa ba mazinaciya ba ce, ko da yake ta auri wani. Saboda haka ’yan’uwana, ku ma kun mutu ga dokar ta wurin jikin Kiristi, domin ku zama na wani, gare shi wanda aka tashe shi daga matattu, don mu ba da amfani ga Allah. Gama sa’ad da halin mutuntaka yake mulkinmu, sha’awace-sha’awacen zunubi waɗanda dokar ta zuga sun yi ta aiki a jikunanmu, don mu ba da amfani wa mutuwa. Amma yanzu, ta wurin mutuwa ga abin da dā ya daure mu, an sake mu daga dokar saboda mu yi hidima a sabuwar hanyar Ruhu, ba a tsohuwar hanyar rubutaccen ƙa’ida ba. Me za mu ce ke nan? Dokar zunubi ce? Sam, ko kaɗan! Tabbatacce ai, da ban san mene ne zunubi ba in ba ta wurin doka ba. Gama da ban san mene ne ƙyashi yake ba tabbatacce in ba don doka ta ce, “Kada ka yi ƙyashi ba.” Amma zunubi, da ya sami dama ta wurin umarnin nan, ya haifar a cikina kowane halin ƙyashi iri-iri. Gama in babu doka, zunubi matacce ne. Dā kam ina da rai sa’ad da ban san doka ba; amma da umarni ya zo, sai zunubi ya zaburo da rai na kuma mutu. Na gane cewa wannan umarnin da aka nufa ya kawo rai, a gaskiya ya jawo mutuwa ce. Gama zunubi, da ya sami dama ta wurin umarni, sai ya ruɗe ni, kuma ta wurin umarnin kuwa ya kashe ni. Saboda haka fa, dokar tana da tsarki, umarnin kuma yana da tsarki, su duka suna da adalci da kuma kyau. Abin nan da yana mai kyau, zai kawo mini mutuwa? Ko kaɗan! Amma domin zunubi ya bayyana kansa a matsayin zunubi, sai ya haifar da mutuwa a cikina ta wurin abin da yake mai kyau, domin ta wurin umarnin nan zunubi ya fito da matuƙar muninsa. Mun san cewa doka aba ce ta ruhu; amma ni ba na ruhu ba ne, an sayar da ni a matsayin bawa ga zunubi. Ban gane abin da nake yi ba. Don abin da nakan so yi, ba shi nakan yi ba, sai dai abin da nake ƙi, shi nake yi. In kuma na yi abin da ba na son yi, na yarda da cewa dokar aba ce mai kyau. Kamar dai yadda yake, ba ni kaina nake yinsa ba, sai dai zunubin da yake zaune a cikina ne. Gama na san cewa babu wani abin kirkin da yake zaune a cikina, wato, a mutuntakata. Gama sha’awar yin abu mai kyau kam ina da ita, sai dai ikon yin ne fa babu. Gama abin da nake yi ba shi ne abu mai kyau da nake so in yi ba; a’a, mugun da ba na so in yi, shi ne nake ci gaba da yi. To, in na yi abin da ba na so in yi, ba ni ba ne nake yinsa, sai dai zunubin nan da yake zaune a cikina. Saboda haka na gane wannan ƙa’ida ce take aiki a cikina. Sa’ad da nake so in yi abu mai kyau, sai in ga cewa mugun nan ne nake yi. Gama a ciki-cikina ina farin cikin da dokar Allah; amma ina ganin wata doka tana aiki a gaɓoɓin jikina, tana yaƙi da dokar hankalina, tana kuma sa in zama ɗaurarren dokar zunubin da take aiki a gaɓoɓin jikina. Kaitona! Wane ne zai cece ni daga wannan jiki mai mutuwa? Godiya ga Allah ta wurin Yesu Kiristi Ubangijinmu! Saboda haka fa, ni kaina a cikin hankalina, ni bawa ne ga dokar Allah, amma a mutuntaka, ni bawa ne ga dokar zunubi. Saboda haka, yanzu babu hukunci don waɗanda suke cikin Kiristi Yesu, gama ta wurin Kiristi Yesu dokar Ruhu mai ba da rai ta ’yantar da ni daga Dokar Musa. Gama abin da dokar ba tă iya yi saboda kāsawar mutuntaka ba, Allah ya yi shi sa’ad da ya aiko da Ɗansa a kamannin mutum mai zunubi, don yă zama hadaya ta zunubi. Ta haka, ya hukunta zunubi a cikin mutum mai zunubi. Ya yi haka domin yă cika bukatun adalcin doka a cikinmu, mu da ba ma rayuwa bisa ga mutuntaka, sai dai bisa ga Ruhu. Waɗanda suke rayuwa bisa ga mutuntaka sun kafa hankulansu a kan sha’awace-shawa’acen jiki; amma waɗanda suke rayuwa bisa ga Ruhu sun kafa hankulansu a kan abubuwan da Ruhu yake so. Ƙwallafa rai ga al’amuran halin mutuntaka ƙarshensa mutuwa ne, ƙwallafa rai ga al’amuran Ruhu kuwa rai ne da salama; hankalin mai zunubi na gāba da Allah. Ba ya biyayya da dokar Allah, ba kuwa zai iya yin haka ba. Waɗanda mutuntaka yake mulkinsu ba za su iya su gamshi Allah ba. Ku kam, ana mulkinku ba ta wurin mutuntaka ba, sai dai ta wurin Ruhu, in Ruhun Allah yana zaune a cikinku. In kuma wani ba shi da Ruhun Kiristi, shi ba na Kiristi ba ne. Amma in Kiristi yana a cikinku, jikinku matacce ne saboda zunubi, duk da haka ruhunku yana a raye saboda adalci. In kuwa Ruhu wannan da ya tā da Yesu daga matattu yana zama a cikinku, shi wanda ya tā da Kiristi daga matattu zai ba da rai ga jikunanku masu mutuwa ta wurin Ruhunsa, wanda yake zama a cikinku. Saboda haka ’yan’uwa, muna da hakki, amma ba na wanda za mu yi rayuwar mutuntaka da yake so ba. Gama in kuna rayuwa bisa ga mutuntaka, za ku mutu; amma in ta wurin Ruhu kuka kashe ayyukan jikin nan, za ku rayu. Domin waɗanda Ruhun Allah yake bi da su ne ’ya’yan Allah. Gama ba ku karɓi ruhun da ya mai da ku bayi da za ku sāke jin tsoro ba ne, sai dai kun karɓi Ruhun zaman ɗa. Ta wurinsa kuwa muke kira, “ Abba, Uba.” Ruhu kansa yana ba da shaida tare da ruhunmu cewa mu ’ya’yan Allah ne. In kuwa mu ’ya’ya ne, to, mu magāda ne, magādan Allah da kuma abokan gādo tare da Kiristi, in kuwa muna tarayya a cikin shan wuyarsa to, za mu yi tarayya a cikin ɗaukakarsa. A ganina, wuyar da muke sha a wannan lokaci ba su isa a kwatanta da ɗaukakar da za a bayyana a cikinmu ba. Halitta tana jira da marmari ta ƙosa ta ga bayyanuwar ’ya’yan Allah. Gama an sa halitta a cikin wulaƙanci, ba da son ta ba, sai dai ta wurin nufin wannan da ya mai da ita haka, da bege cewa za a ’yantar da halitta kanta daga bautarta ga ruɓewa a kuma kawo ta cikin ’yancin ɗaukakar ’ya’yan Allah. Mun san cewa dukan halitta tana nishi sai ka ce mace mai naƙuda har yă zuwa wannan lokaci. Ba haka kaɗai ba ma, mu kanmu da muke da nunan fari na Ruhu, muna nishi a ciki-cikinmu yayinda muke jira da marmari a maishe mu ’ya’yan riƙo na Allah, fansar jikunanmu. Gama a wannan begen ne muka sami ceto. Amma begen da ake gani ba bege ba ne sam. Wa yake begen abin da ya riga ya samu? Amma in muna begen abin da ba mu riga mun samu tukuna ba, mukan jira da haƙuri. Haka nan ma, Ruhu yana taimakonmu cikin rashin ƙarfinmu. Ba mu san abin da ya kamata mu roƙa cikin addu’a ba, amma Ruhu kansa yana roƙo a madadinmu da nishe-nishen da kalmomi ba sa iya bayyanawa. Shi kuma wanda yake binciken zukatanmu ya san halin Ruhu, domin Ruhu yana roƙo a madadin tsarkaka bisa ga nufin Allah. Mun kuma san cewa a cikin dukan abubuwa Allah yana aikata alheri ga waɗanda suke ƙaunarsa, yana waɗanda aka kira bisa ga nufinsa. Gama waɗanda Allah ya rigyasani ya kuma ƙaddara su dace da kamannin Ɗansa, don yă zama ɗan fari cikin ’yan’uwa masu yawa. Waɗanda kuwa ya ƙaddara, su ne ya kira; waɗanda ya kira kuwa, su ne ya kuɓutar; waɗanda ya kuɓutar kuwa, su ne ya ɗaukaka. Me za mu ce ke nan game da wannan abu? In Allah yana goyon bayanmu, wa kuwa zai iya gāba da mu? Shi da bai hana Ɗansa ba, sai ma ya ba da shi saboda mu duka, ashe, ba zai kuma ba mu, tare da shi, dukan abubuwa cikin alherinsa ba? Wa zai kawo wani zargi a kan waɗanda Allah ya zaɓa? Allah ne mai kuɓutarwa. Wa zai yi hukunci? Yesu Kiristi ne, wanda ya mutu, fiye da haka ma, shi da aka tā da zuwa rai, yana zaune a hannun dama na Allah yana kuma yin roƙo a madadinmu. Wane ne zai raba mu da ƙaunar Kiristi? Masifa ce ko wahala ko tsanani ko yunwa ko tsiraici ko hatsari ko takobi? Kamar yadda yake a rubuce cewa, “Saboda kai ne muke fuskantar mutuwa dukan yini; an ɗauke mu kamar tumakin da za a yanka.” A’a, cikin dukan waɗannan abubuwa mun ma fi masu nasara ta wurin shi wanda ya ƙaunace mu. Gama na tabbata cewa ko mutuwa ko rai, ko mala’iku ko aljanu, ko abubuwa na yanzu ko abubuwa masu zuwa nan gaba, ko ikoki, ko tsayi ko zurfi, ko wani abu dabam cikin dukan halitta da zai iya raba mu da ƙaunar Allah wadda take cikin Kiristi Yesu Ubangijinmu. Ina faɗin gaskiya a cikin Kiristi ba ƙarya nake yi ba, lamirina ya tabbatar da wannan a cikin Ruhu Mai Tsarki. Ina da baƙin ciki mai yawa da kuma rashin kwanciyar rai marar ƙarewa a zuciyata. Gama da so na ne, sai a la’anta ni a kuma raba ni da Kiristi saboda ’yan’uwana, waɗannan na kabilata, mutanen Isra’ila. Su ne Allah ya mai da su ’ya’yansa, ya bayyana musu ɗaukakarsa, ya ba su alkawarinsa da Dokarsa, ya nuna musu hanyar sujada ta gaske, ya kuma ba su sauran alkawura. Kakannin-kakannin nan kuma nasu ne, Kiristi kuma, ta wurin zamansa mutum, na kabilarsu ne. Yabo ya tabbata ga Allah har abada, shi da yake bisa kome! Amin. Ba cewa maganar Allah ta kāsa ba ne. Gama ba duk waɗanda suke zuriyar Isra’ila ne suke Isra’ila na gaske ba. Ba kuwa don su zuriyarsa ne dukansu suka zama ’ya’yan Ibrahim ba. A maimako, “Ta wurin Ishaku ne za a lissafta zuriyarka.” Ana iya cewa zaman zuriyar Ibrahim, ba shi ne zama ’ya’yan Allah ba, a’a, zuriya ta alkawarin nan su ne ake lasaftawa zuriyar Ibrahim. Ga yadda aka yi alkawarin nan, “A ƙayyadadden lokaci zan dawo, Saratu kuma za tă haifi ɗa.” Ba ma haka kaɗai ba, ’ya’yan Rifkatu suna da mahaifi guda ne, wato, mahaifinmu Ishaku. Duk da haka, tun ba a haifi tagwayen nan ba, balle su yi wani abu mai kyau ko marar kyau don nufin Allah bisa ga zaɓensa ya tabbata, ba ga aikin lada ba, sai dai ga kiransa, ba ta wurin ayyuka ba sai dai ta wurin shi wanda ya kira, aka faɗa mata cewa, “Babban zai bauta wa ƙaramin.” Kamar yadda yake a rubuce cewa, “Yaƙub ne na so, amma Isuwa ne na ƙi.” Me za mu ce ke nan? Allah marar adalci ne? Sam, ko kaɗan! Gama ya ce wa Musa, “Zan nuna jinƙai ga wanda zan nuna jinƙai, zan kuma ji tausayin wanda zan ji tausayi.” Saboda haka, bai danganta ga sha’awar mutum ko ƙoƙarinsa ba, sai dai ga jinƙan Allah. Gama Nassi ya ce wa Fir’auna, “Na ɗaga ka saboda wannan manufa, saboda in nuna ikona a cikinka domin kuma a shaida sunana a duniya duka.” Saboda haka Allah yana nuna jinƙai ga wanda yake so, yana kuma taurara zuciyar wanda yake so. Waninku zai iya ce mini, “To, don me har yanzu Allah yake ganin laifinmu? Gama wa zai iya tsayayya da nufinsa?” Amma wane ne kai, ya mutum, da za ka mayar wa Allah magana? “Ashe, abin da aka gina zai iya ce wa wanda ya gina shi, ‘Don me ka gina ni haka?’ ” Ashe, mai ginin tukwane ba shi da iko yin amfani da yumɓu guda yă gina tukunya domin ayyuka masu daraja da kuma waɗansu don ayyuka marasa daraja? Haka ma aikin Allah yake. Ya so yă nuna fushinsa yă kuma sanar da ikonsa, ya yi haka cikin haƙuri ƙwarai ga waɗanda suka cancanci fushinsa, waɗanda aka shirya domin hallaka? Haka kuma ya so yă sanar da wadatar ɗaukakarsa ga waɗanda suka cancanci jinƙansa, waɗanda ya shirya tun kafin lokaci don ɗaukaka har da mu ma, mu da ya kira, ba daga cikin Yahudawa kaɗai ba amma har ma daga cikin Al’ummai? Kamar yadda ya faɗa a Hosiya. “Zan kira su ‘mutanena,’ su da ba mutanena ba; zan kuma kira ta ‘ƙaunatacciyata,’ ita da ba ƙaunatacciyata ba,” kuma, “Zai zama cewa a daidai inda aka ce musu, ‘Ku ba mutanena ba,’ za a ce da su, ‘’ya’yan Allah mai rai.’ ” Ishaya ya ɗaga murya game da Isra’ila ya ce, “Ko da yake yawan Isra’ilawa yana kama da yashi a bakin teku, ragowa ce kaɗai za su sami ceto. Gama Ubangiji zai zartar da hukuncinsa a bisan duniya da sauri kuma ba da ɓata lokaci ba.” Yana nan kamar yadda Ishaya ya riga ya faɗa. “Da ba don Ubangiji Maɗaukaki ya bar mana zuriya ba, da mun zama kamar Sodom, da mun kuma zama kamar Gomorra.” Me za mu ce ke nan? Ai, Al’ummai da ba su nemi adalci ba, sun same shi, adalcin da yake ta wurin bangaskiya; amma Isra’ila da suka yi ƙwazo wajen bin Dokar adalci, ba su same shi ba. Don me? Domin sun yi ƙwazo wajen binta ba ta wurin bangaskiya ba sai dai ta wurin ayyuka. Sun yi tuntuɓe a kan “dutsen sa tuntuɓe.” Kamar yadda yake a rubuce, “Ga shi, na sa dutse a Sihiyona da yake sa mutane yin tuntuɓe da kuma dutsen da yake sa su fāɗi wanda kuwa ya dogara gare shi ba zai taɓa shan kunya ba.” ’Yan’uwa, abin da zuciyata take so da kuma addu’ata ga Allah saboda Isra’ilawa shi ne su sami ceto. Gama na shaida su a kan suna da kishi bin Allah, sai dai kishinsu ba a bisa sani ba. Da yake ba su san adalcin da yake fitowa daga Allah ba suka kuma nemi su kafa nasu, sai suka ƙi miƙa kai ga adalcin Allah. Kiristi shi ne ƙarshen doka domin a sami adalci wa kowane mai bangaskiya. Musa ya bayyana adalcin da yake ga Doka cewa, “Mutumin da ya aikata waɗannan abubuwa zai rayu ta wurinsu.” Amma adalcin da yake ga bangaskiya yana cewa, “Kada ka faɗa a zuciyarka, ‘Wa zai hau sama?’ ” (wato, don yă sauko da Kiristi), “ko kuwa ‘Wa zai gangara can zurfin ƙasa?’ ” (wato, don yă hauro da Kiristi daga matattu). Amma mene ne aka ce? “Maganar tana kusa da kai; tana cikin bakinka da kuma cikin zuciyarka,” wato, maganar bangaskiyan nan da muke shela. Cewa in ka furta da bakinka, “Yesu Ubangiji ne,” ka kuma gaskata a zuciyarka cewa Allah ya tā da shi daga matattu, za ka sami ceto. Gama da zuciyarka ce kakan gaskata a kuma kuɓutar da kai, da bakinka ne kuma kake furta a kuma cece ka. Kamar yadda Nassi ya ce, “Duk wanda ya gaskata da shi ba zai taɓa shan kunya ba.” Gama ba bambanci tsakanin mutumin Yahuda da mutumin Al’ummai, Ubangijin nan ɗaya shi ne Ubangijin kowa yana kuma ba da albarka a yalwace ga duk masu kira gare shi, gama, “Duk wanda ya kira bisa sunan Ubangiji zai sami ceto.” To, ta yaya za su kira ga wanda ba su gaskata ba? Ta yaya kuma za su gaskata wanda ba su taɓa ji ba? Ta yaya kuma za su ji ba tare da wani ya yi musu wa’azi ba? Kuma ta yaya za su yi wa’azi in ba an aike su ba? Kamar yadda yake a rubuce cewa, “Isowar masu kawo labari mai daɗi abu mai kyau ne ƙwarai!” Amma ba dukan Isra’ilawa ne suka karɓi labari mai daɗin nan ba. Gama Ishaya ya ce, “Ubangiji, wa ya gaskata saƙonmu?” Saboda haka, bangaskiya takan zo ne ta wurin jin saƙo, akan ji saƙon kuma ta wurin maganar Kiristi. Amma ina tambaya, “Ba su ji ba ne? Tabbatacce sun ji. “Muryarsu ta tafi ko’ina a cikin duniya, kalmominsu kuma har iyakar duniya.” Har wa yau, ina da tambaya. Shin, Isra’ila ba su fahimta ba ne? Da farko, Musa ya ce, “Zan sa ku yi kishin waɗanda ba al’umma ba; zan sa ku yi fushin al’ummar da ba ta da fahimta.” Ishaya kuma ya fito gabagadi ya ce, “Waɗanda ba su neme ni ba, su suka same ni; Na bayyana kaina ga waɗanda ba su ma taɓa neman sanina ba.” Amma game da Isra’ila ya ce, “Dukan yini na miƙa hannuwana ga mutane marasa biyayya da masu taurinkai.” To, ina da tambaya. Allah ya ƙi mutanensa ne? Sam, ko kaɗan! Ni mutumin Isra’ila ne kaina, zuriyar Ibrahim kuwa, daga kabilar Benyamin. Allah bai ƙi mutanensa da ya rigya sani ba. Ba ku san abin da Nassi ya faɗa game da Iliya ba, yadda ya kawo kuka ga Allah a kan Isra’ila ya ce, “Ya Ubangiji, sun karkashe annabawanka suka kuma rurrushe bagadanka; ni kaɗai na ragu, suna kuma neman raina”? Wace amsa ce Allah ya ba shi? “Na keɓe wa kaina dubu bakwai waɗanda ba su yi wa Ba’al sujada ba.” Haka ma, a wannan zamani akwai ragowar da aka zaɓa ta wurin alheri. In kuwa na alheri ne, ba sauran cewa ya dogara ga ayyuka ke nan. In ba haka ba, ashe, alheri ba alheri ba ne kuma. To, sai me? Abin da Isra’ila suka nema da himma ba su samu ba, amma zaɓaɓɓun suka samu. Sauran suka taurare, kamar yadda yake a rubuce cewa, “Allah ya ba su ruhun ruɗewa, idanu don su kāsa gani, da kuma kunnuwa don su kāsa ji, har yă zuwa yau.” Dawuda kuma ya ce, “Bari teburin cin abincinsu yă zama musu tarko, sanadin fāɗuwa da dutsen sa tuntuɓe da kuma ramuwa a kansu. Bari idanunsu su duhunta don kada su iya gani, bayansu kuma yă tanƙware har abada.” Har yanzu ina da tambaya. Sun yi tuntuɓe har ya kai ga fāɗuwar da ba za su iya tashi ba ne? Sam, ko kaɗan! A maimako, saboda laifinsu ne ceto ya zo ga Al’ummai don a sa mutanen Isra’ila su ji kishi. Amma in laifinsu yana nufin albarka ga duniya, hasararsu kuma albarka ga Al’ummai, ina misalin yalwar da albarkunsu za su kawo! Ina magana da ku ne fa Al’ummai. Tun da yake ni manzo ne ga Al’ummai, ina taƙama da aikin nan nawa, da fata zan rura kabilata a ta kowace hanya su ji kishi har ma yă sa in ceci waɗansunsu. Gama in ƙinsu da aka yi ya zama sulhu ga duniya, me karɓarsu za tă zama in ba rai daga matattu ba? In sashen da aka miƙa a matsayin nunan fari tsattsarka ne, to, sauran ma tsattsarka ne; in saiwar tsattsarka ce, to, sauran rassan ma tsattsarka ne. In an sassare waɗansu rassa, kai kuwa da kake kai zaitun jeji, aka ɗauke ka aka kuma yi muku aure, a yanzu kuwa kana shan ni’imar saiwar zaitun ɗin nan tare da sauran rassan, kada ka yi taƙama cewa ka fi waɗancan rassan da aka sassare. In kuwa ka yi haka, to, ka yi la’akari da wannan. Ba kai ne kake taimakon saiwar ba, saiwar ce take taimakonka. To, kana iya cewa, “An sassare rassan ne don a ɗaura aure da ni.” Haka yake. Amma an sassare su ne saboda rashin bangaskiya, kai kuma kana tsaye ta wurin bangaskiya. Kada ka yi taƙama, sai dai ka ji tsoro. Gama in har Allah bai bar rassan nan na asali ba, kai ma ba zai bar ka ba. Ka lura fa da alheri da kuma tsananin Allah, tsanani ga waɗanda suka fāɗi, amma alheri a gare ka, da fata za ka ci gaba cikin alherinsa. In ba haka ba, kai ma za a sare ka. In kuwa ba su nace cikin rashin bangaskiya ba, za a sāke ɗaura aure da su, domin Allah yana iya sāke haɗa su. Kai ma da aka saro daga zaitun ɗin da asalinsa yake na jeji, aka ɗaura aure da kai a jikin zaitun ɗin na gida, saɓanin yadda aka saba, balle waɗannan rassa na asali, da za a ɗaura aure da su a jikin zaitun ɗin nan nasu na asali? Ba na so ku kasance cikin rashin sani game da wannan asirin ’yan’uwa, domin kada ku ɗaga kai. Isra’ila sun ɗanɗana sashe na taurarewa har sai da shigowar Al’ummai masu yawa ya cika. Ta haka kuwa za a ceci dukan Isra’ila, kamar yadda yake a rubuce cewa, “Mai ceto zai zo daga Sihiyona; zai kawar da rashin bin Allah daga Yaƙub. Wannan kuwa shi ne alkawarina da su sa’ad da na ɗauke musu zunubansu.” Game da zancen nan na bishara kuwa, su abokan gāba ne saboda ku; amma game da zaɓen kuwa, su ƙaunatattunsa ne, albarkacin kakannin kakanninsu, gama kyautar Allah da kiransa ba a sokewa. Kamar yadda a dā can ku da kuke marasa biyayya ga Allah kuka sami jinƙai yanzu ta dalilin rashin biyayyarsu, haka su ma suka zama marasa biyayya a yanzu domin su ma su sami jinƙai ta dalilin jinƙan da Allah ya yi muku. Gama Allah ya daure dukan mutane ga rashin biyayya don yă nuna jinƙai ga kowa. Kai, zurfin yalwar hikima da kuma sanin Allah yana nan a yalwace! Hukunce-hukuncensa kuma su fi gaban bincike, hanyoyinsa kuwa sun wuce gaban ganewa! “Wa ya taɓa sanin zuciyar Ubangiji? Ko kuwa yă ba shi shawara?” “Wa ya taɓa ba wa Allah wani abu, da Allah zai sāka masa?” Gama daga gare shi, ta wurinsa, da kuma saboda shi ne dukan abubuwa suka kasance. Ɗaukaka ta tabbata a gare shi har abada! Amin. Saboda haka, ina roƙonku, ’yan’uwa, saboda yawan jinƙan Allah, ku miƙa jikunanku hadaya wadda take mai rai, mai tsarki abin karɓa kuma ga Allah, wannan ita ce hanyar hidimarku ta ruhaniya. Kada ku ci gaba da yin abin da duniya take yi, sai dai ku bar halinku ya sāke, ta wurin sabunta hankalinku ɗungum, don ku tabbatar da abin da Allah yake so yake, abu mai kyau, mai daɗi da kuma cikakke. Gama ta wurin alherin nan da aka yi mini ne ina ce wa kowannenku. Kada yă ɗauki kansa fiye da yadda ya kamata, a maimakon haka bari yă auna kansa cikin natsuwa, gwargwadon baiwar bangaskiyar da Allah yi masa. Kamar dai yadda kowannenmu yake da jiki ɗaya da gaɓoɓi da yawa, gaɓoɓin nan kuwa ba aiki iri ɗaya suke yi ba, haka ma a cikin Kiristi mu da muke da yawa mun zama jiki ɗaya, kuma kowace gaɓar ɗan’uwan sauran ne. Muna da baye-baye dabam-dabam, gwargwadon alherin da aka yi mana. In baiwar mutum ta yin annabci ce, sai yă yi amfani da ita gwargwadon bangaskiyarsa. In ta hidima ce; sai yă yi hidima. In kuma ta koyarwa ce, sai yă koyar; in ta ƙarfafawa ce, sai yă ƙarfafa; in kuma ta ba da taimako ce don biyan bukatun waɗansu, sai yă yi haka hannu sake; in ta shugabanci ce, sai yă yi shugabanci da himma; in ta nuna jinƙai ce, sai yă yi haka da fara’a. Dole ƙauna tă zama ta gaskiya. Ku ƙi duk abin da yake mugu; ku manne wa abin da yake nagari. Ku ba da kanku ga juna cikin ƙauna irin ta ’yan’uwa. Kowa yă yi ƙoƙari wajen girmama wani fiye da kansa. Kada ku zama marasa himma, sai dai masu himma a ruhaniyarku, kuna bauta wa Ubangiji. Ku yi farin ciki cikin bege, haƙuri cikin shan wuya, aminci cikin addu’a. Ku taimaki mutanen Allah masu bukata. Ku zama masu karɓan baƙi. Ku sa wa masu tsananta muku albarka; ku sa albarka kada fa ku la’anta. Ku yi murna da masu murna, ku yi kuka da masu kuka. Ku yi zaman lafiya da juna. Kada ku nuna girman kai, sai ma ku riƙa cuɗanya da talakawa. Kada ku zama masu ɗaga kai. Idan kowa ya yi muku mugunta, kada ku sāka masa da mugunta. Ku lura don ku aikata abin da kowa zai iya gani cewa daidai ne. Ku yi iya ƙoƙarinku, in zai yiwu, ku yi zaman lafiya da kowa. Kada ku yi ramuwa, abokaina, sai dai ku bar wa Allah. Gama a rubuce yake cewa, “Ramuwa tawa ce; zan kuwa sāka,” in ji Ubangiji. A maimakon haka, “In abokin gābanka yana jin yunwa, ka ciyar da shi; in yana jin ƙishirwa, ka ba shi ruwan sha. Ta yin haka, za ka tara garwashin wuta a kansa.” Kada ku bar mugunta ta sha kanku, sai dai ku sha kan mugunta ta wurin aikata nagarta. Dole kowa yă yi biyayya ga masu mulki, gama babu wani iko sai ko in Allah ya yarda. Duk hukumomin da muke su, naɗin Allah ne. Saboda haka, duk wanda ya yi tawaye ga hukuma yana yin tawaye da abin da Allah ya naɗa ne, waɗanda kuwa suke aikata haka, za su jawo wa kansu hukunci. Gama masu mulki ba abin tsoro ba ne ga waɗanda suke yin abin da yake daidai, sai dai ga waɗanda suke aikata laifi. Kana so ka rabu da jin tsoron wanda yake mulki? To, sai ka aikata abin da yake daidai, zai kuwa yabe ka. Gama shi bawan Allah ne don kyautata rayuwarka. Amma in ka aikata mugunta, to, sai ka ji tsoro, don ba a banza ne shugaba yake ɗaukan takobinsa ba. Shi fa bawan Allah ne, ta wurinsa ne fushin Allah yakan hukunta masu laifi. Saboda haka, dole a yi biyayya ga hukumomi, ba don gudun horo kawai ba amma don lamirinku. Shi ne ma ya sa kuke biyan haraji, gama hukumomin nan bayin Allah ne, waɗanda suke ba da dukan lokacinsu don aikin shugabanci. Ku ba wa kowa hakkinsa. In kuna da bashin haraji, sai ku biya; in kuɗin shiga ne, ku biya kuɗin shiga; in ladabi ne, ku yi ladabi; in kuma girmamawa ne, ku ba da girma. Kada hakkin kowa yă zauna a kanku, sai dai na ƙaunar juna, don mai ƙaunar maƙwabcinsa ya cika Doka ke nan. Umarnan nan, “Kada ka yi zina.” “Kada ka yi kisankai.” “Kada ka yi sata.” “Kada kuma ka yi ƙyashi.” Da dai duk sauran umarnai an ƙunshe su ne a wannan kalma “Ka ƙaunaci maƙwabcinka kamar kanka.” Ƙauna ba ta cutar da maƙwabci. Saboda haka ƙauna cika Doka ce. Ku yi wannan domin kun san irin zamanin da kuke ciki. Lokaci ya yi da za ku farka daga barcinku, don cetonmu ya yi kusa yanzu fiye da lokacin da muka fara ba da gaskiya. Dare fa ya kusan ƙarewa; gari kuma yana gab da wayewa. Saboda haka bari mu kawar da ayyukan duhu mu kuma yafa kayan yaƙi na haske. Bari mu tafiyar da al’amuranmu yadda ya dace a yi da rana, ba a cikin shashanci da buguwa ba, ba cikin fasikanci da rashin kunya ba, ba kuma cikin faɗa da kishi ba. A maimakon haka, ku ɗauki halin Ubangiji Yesu Kiristi, kada kuma ku yi tunani game da yadda za ku gamsar da sha’awace-sha’awacen mutuntaka. Ku karɓi wanda bangaskiyarsa ba tă yi ƙarfi ba, amma fa kada ku hukunta shi a kan abubuwan da ake da shakka a kai ba. Bangaskiyar mutum ta yarda masa yă ci kome, amma wanda bangaskiyarsa ba tă yi ƙarfi ba, yakan ci kayan lambu ne kawai. Mutumin da yake cin kowane irin abinci, kada yă rena wanda ba ya cin, wanda kuma ba ya cin kowane irin abinci, kada yă ga laifin mutumin da yake ci, domin Allah ya riga ya karɓe shi. Kai wane ne har da za ka ga laifin bawan wani? Ko bawan yă yi aiki mai kyau, ko yă kāsa, ai, wannan ruwan maigidansa ne. Za a ma tsai da shi, domin Ubangiji yana da ikon tsai da shi. Wani yakan ɗauki wata rana da daraja fiye da sauran ranaku; wani kuma yana ganin dukan ranakun ɗaya ne. Ya kamata kowa yă kasance da tabbaci a cikin zuciyarsa. Wannan mai ɗaukan rana ɗaya da muhimmanci fiye da sauran, yana yin haka ne ga Ubangiji. Wannan mai cin nama, yana yin haka ne ga Ubangiji, gama yakan yi godiya ga Allah; wannan da ba ya ci kuwa, yana yin haka ne ga Ubangiji yana kuwa yin godiya ga Allah. Gama ba waninmu da yake rayuwa wa kansa kaɗai, kuma ba waninmu da kan mutu don kansa kaɗai. In muna rayuwa, muna rayuwa ne ga Ubangiji; in kuma muna mutuwa, muna mutuwa ne ga Ubangiji. Saboda haka, ko muna a raye ko muna a mace, mu na Ubangiji ne. Saboda wannan ne Kiristi ya mutu, ya kuma sāke rayuwa domin yă zama Ubangiji na matattu da na masu rai. Kai kuwa, don me kake ganin laifin ɗan’uwanka? Ko kuma don me kake rena ɗan’uwanka? Gama duk za mu tsaya a gaban kujerar shari’ar Allah. A rubuce yake cewa, “ ‘Muddin ina raye,’ in ji Ubangiji, ‘kowace gwiwa za tă durƙusa a gabana; kowane harshe kuma zai furta wa Allah.’ ” Don haka kowannenmu zai ba da lissafin kansa ga Allah. Saboda haka bari mu daina ba wa juna laifi. A maimakon, sai kowa yă yi niyya ba zai sa dutsen tuntuɓe ko abin sa fāɗuwa a hanyar ɗan’uwansa ba. A matsayina na mai bin Ubangiji Yesu na tabbata ƙwarai cewa babu abincin da yake marar tsabta don kansa. Amma in wani ya ɗauka wani abu marar tsabta ne, to, a gare shi marar tsabta ne. In kana ɓata wa ɗan’uwanka zuciya saboda abincin da kake ci, ba halin ƙauna kake nunawa ba ke nan. Kada abincin da kake ci yă zama hanyar lalatar da ɗan’uwanka wanda Kiristi ya mutu dominsa. Kada ka bar abin da ka ɗauka a matsayi kyakkyawa yă zama abin zargi ga waɗansu. Gama mulkin Allah ba batun ci da sha ba ne, sai dai na adalci, salama, da kuma farin ciki cikin Ruhu Mai Tsarki, duk kuwa wanda yake bauta wa Kiristi a haka yana faranta wa Allah rai ne, yardajje kuma ga mutane. Saboda haka sai mu yi iya ƙoƙari mu aikata abin da zai kawo salama da kuma ingantawa ga juna. Kada ku lalatar da aikin Allah saboda abinci. Dukan abinci mai tsabta ne, sai dai ba daidai ba ne mutum yă ci abin da zai sa wani yă yi tuntuɓe. Ya fi kyau kada ka ci nama ko ka sha ruwan inabi ko kuma ka yi wani abin da zai sa ɗan’uwanka yă fāɗi. Bari duk ra’ayin da kake da shi game da wannan sha’ani yă kasance tsakaninka da Allah. Mai albarka ne wanda zuciyarsa ba tă ba shi laifi game da abin da shi da kansa ya ɗauka cewa daidai ne ba. Amma wanda yake da shakka yakan jawo wa kansa hukunci ne in ya ci, domin yana ci ne ba bisa ga bangaskiya ba; kuma duk abin da bai zo daga bangaskiya ba zunubi ne. Mu da muke da ƙarfi ya kamata mu yi haƙuri da kāsawar marasa ƙarfi ba kawai mu gamshi kanmu ba. Ya kamata kowannenmu yă faranta wa maƙwabcinsa rai don kyautata zamansa domin kuma yă gina shi. Gama ko Kiristi ma bai gamshi kansa ba, amma kamar yadda yake a rubuce cewa, “Zage-zagen da waɗansu suka yi maka, duk sun fāɗo a kaina.” Gama duk abin da aka rubuta a dā an rubuta ne domin yă koya mana, don ta wurin jimrewa da kuma ƙarfafawar Nassosi mu kasance da bege. Bari Allah mai ba da haƙuri da kuma ƙarfafawa yă ba ku ruhun haɗinkai da juna yayinda kuke bin Kiristi Yesu, don da zuciya ɗaya da kuma baki ɗaya kuke ɗaukaka Allah da kuma Uban Ubangijinmu Yesu Kiristi. Ta haka sai ku karɓi juna kamar yadda Kiristi ya karɓe ku, don a yabi Allah. Ina dai gaya muku cewa Kiristi ya zama bawan Yahudawa a madadin gaskiyar Allah, don yă tabbatar da alkawaran da aka yi wa kakannin kakanninmu domin Al’ummai su ɗaukaka Allah saboda jinƙansa, kamar yadda yake a rubuce, “Saboda haka zan yabe ka a cikin Al’ummai; zan rera waƙoƙi ga sunanka.” Ya kuma ce, “Ku yi farin ciki, ya Al’ummai, tare da mutanensa.” Da kuma, “Ku yabi Ubangiji, dukanku Al’ummai, ku kuma rera masa yabo, dukanku mutanen duniya.” Kuma Ishaya ya ce, “Tushen Yesse zai tsiro, wanda zai taso yă yi mulkin al’ummai; al’ummai za su sa bege a gare shi.” Bari Allah na bege yă cika ku da matuƙar farin ciki da salama yayinda kuke dogara gare shi, domin ku yalwata cikin bege ta wurin ikon Ruhu Mai Tsarki. Ni kaina na tabbata, ’yan’uwana, cewa ku kanku kuna cike da kirki, cikakku cikin sani da kuma ƙwararru don yin wa juna gargaɗi. Na rubuta muku gabagadi a kan waɗansu batuttuwa, don in sāke tuna muku su, saboda alherin da Allah ya ba ni in zama mai hidimar Kiristi Yesu ga Al’ummai da aikin firist na yin shelar bisharar Allah, don Al’ummai su zama hadaya mai karɓuwa ga Allah, tsattsarka ta wurin Ruhu Mai Tsarki. Saboda haka ina taƙama cikin Kiristi Yesu a cikin hidimata ga Allah. Ba zan yi karambani in faɗi kome ba sai dai abin da Kiristi ya aikata ta wurina a jagorantar da Al’ummai su yi biyayya ga Allah ta wurin abin da na faɗa da kuma aikata ta wurin ikon alamu da ayyukan banmamaki, da kuma ikon Ruhun Allah. Ta haka daga Urushalima har yă zuwa kewayen Illirikum, na yi wa’azin bisharar Kiristi. Labudda, burina shi ne in yi wa’azin bishara inda ba a san Kiristi ba, don kada yă zama ina gini ne a kan tushen da wani ya kafa. Sai dai kamar yadda yake a rubuce, “Waɗanda ba a faɗa musu labarinsa ba za su gani, waɗanda kuma ba su ji ba za su fahimta.” Wannan ne ya sa sau da yawa aka hana ni zuwa wurinku. Amma yanzu da babu sauran wurin da ya rage mini in yi aiki a waɗannan yankuna, da yake kuma shekaru masu yawa ina da marmari in gan ku, ina shirin yin haka in na tafi Sifen. Ina fata in ziyarce ku yayinda nake wucewa don ku raka ni can, bayan na ji daɗin zama tare da ku na ɗan lokaci. Yanzu kam, ina hanyata zuwa Urushalima don in kai gudummawa ga tsarkaka a can. Gama Makidoniya da Akayya sun ji daɗin yin gudummawa domin matalautan da suke cikin tsarkakan da suke a Urushalima. Sun kuwa ji daɗin yin haka, gama ya zama kamar bashi ne a gare su. Da yake Al’ummai sun sami rabo cikin albarkun ruhaniyar Yahudawa, ya zama musu kamar bashi su ma su taimaki Yahudawa da albarkunsu na kayan duniya. Saboda haka in na kammala wannan aiki na kuma tabbata cewa sun karɓi wannan amfani, zan tafi Sifen in kuma ziyarce ku a hanyata. Na san cewa sa’ad da na zo wurinku, zan zo ne cikin yalwar albarkar Kiristi. Ina roƙonku ’yan’uwa, saboda Ubangijinmu Yesu Kiristi da kuma saboda ƙaunar Ruhu, ku haɗa kai tare da ni cikin famata ta wurin yin addu’a ga Allah saboda ni. Ku yi addu’a don in kuɓuta daga hannun marasa bi a Yahudiya don kuma gudummawar da nake kaiwa Urushalima ta zama abar karɓa ga tsarkaka a can, don da yardar Allah, in iso wurinku da farin ciki in kuma wartsake tare da ku. Allah na salama yă kasance tare da ku duka. Amin. Ina gabatar muku da ’yar’uwarmu Fibi, baranyar ikkilisiya a Kenkireya. Ina roƙonku ku karɓe ta a cikin Ubangiji yadda ya dace a karɓi tsarkaka a kuma ba ta kowane irin taimakon da take bukata daga wurinku, gama ta zama mai taimako ƙwarai ga mutane masu yawa, haɗe da ni ma. Ku gai da Firiskila da Akwila, abokan aikina cikin Kiristi Yesu. Sun yi kasai da ransu saboda ni. Ba ni kaɗai nake musu godiya ba amma har ma da dukan ikkilisiyoyin Al’ummai. Ku kuma gai da ikkilisiyar da take haɗuwa a gidansu. Ku gai da ƙaunataccen abokina Efenetus, wanda ya zama na farko a karɓar Kiristi a lardin Asiya. Ku gai da Maryamu wadda ta yi muku aiki tuƙuru. Ku gai da Anduronikus da Yuniyas, dangina waɗanda aka daure a kurkuku tare da ni. Su fitattu ne sosai a cikin manzanni, sun riga ni zama masu bin Kiristi. Ku gai da Amfiliyatus, ƙaunataccena a cikin Ubangiji. Ku gai da Urbanus, abokin aikinmu cikin Kiristi, da kuma ƙaunataccen abokina Sitakis. Ku gai da Afelles wanda amincinsa cikin Kiristi tabbatacce ne. Ku gai da iyalin gidan Aristobulus. Ku gai da ɗan’uwana, Hirodiyon. Ku gai da iyalin gidan Narkissus da suke cikin Ubangiji. Ku gai da Tiryifena da Tiryifosa, matan nan da suke aiki tuƙuru cikin Ubangiji. Ku gai da ƙaunatacciyata Fersis, wata matan da ta yi aiki tuƙuru cikin Ubangiji. Ku gai da Rufus zaɓaɓɓe cikin Ubangiji, da kuma mahaifiyarsa, wadda ta zama kamar mahaifiya a gare ni. Ku gai da Asinkiritus, Filegon, Hermes, Faturobas, Hermas da kuma ’yan’uwan da suke tare da su. Ku gai da Filologus, Yuliya, Nereyus da ’yar’uwarsa, da kuma Olimfas da dukan tsarkakan da suke tare da su. Ku gaggai da juna da sumba mai tsarki. Dukan ikkilisiyoyin Kiristi suna gaishe ku. Ina roƙonku, ’yan’uwa, ku yi hankali fa da masu raba tsakani, saɓanin koyarwar da kuka koya, suna sa tuntuɓe. Ku yi nesa da su. Gama irin waɗannan mutane ba sa bautar Ubangijinmu Kiristi, sai dai cikinsu. Ta wurin yaudara da kuma daɗin baki, suna ruɗin marasa wayo. Kowa ya riga ya ji game da biyayyarku, don haka ina cike da farin ciki game da ku; amma ina so ku zama masu hikima game da abin da yake nagari, ku kuma zama marasa laifi ga abin da yake mugu. Allah na salama zai tattake Shaiɗan ba da daɗewa ba yă kuma sa shi a ƙarƙashin sawunku. Alherin Ubangijinmu Yesu kuma yă kasance tare da ku. Timoti, abokin aikina, yana gai da ku, haka ma Lusiyus, Yason, da Sosifater, dangina. Ni, Tertiyus, wanda ya rubuta wannan wasiƙa, ina gai da ku cikin Ubangiji. Gayus, mai masauƙina, mai kuma saukar da dukan ’yan Ikkilisiya, yana gaishe ku. Erastus, mai bi da ayyukan jama’ar gari, da kuma ɗan’uwanmu Kwartus, suna gaishe ku. Ɗaukaka ta tabbata ga mai ikon ƙarfafa ku bisa ga bisharata, bisa ga wa’azin Yesu Kiristi, wadda ta gare ta ne aka bayyana asirin nan da yake ɓoye tun fil azal, amma yanzu kuwa aka bayyana, aka kuma sanar ta wurin rubuce-rubucen annabawa bisa ga umarnin Allah madawwami, domin dukan al’ummai su gaskata su kuma yi masa biyayya ɗaukaka ta tabbata har abada ga Allah, wanda shi ne kaɗai mai hikima ta wurin Yesu Kiristi! Amin. Bulus, wanda aka kira domin yă zama manzon Kiristi Yesu, bisa ga nufin Allah, da kuma ɗan’uwanmu Sostenes, Zuwa ga ikkilisiyar Allah da take a Korint, da waɗanda aka tsarkake cikin Kiristi Yesu, aka kuma kira domin su zama masu tsarki, tare da dukan waɗanda suke ko’ina da suke kiran sunan Ubangijinmu Yesu Kiristi, Ubangijinsu da kuma namu. Alheri da salama daga Allah Ubanmu, da Ubangiji Yesu Kiristi, su kasance tare da ku. Ina gode wa Allah kullum dominku, saboda alherinsa da aka ba ku a cikin Kiristi Yesu. Gama a cikinsa kuka sami wadata ta kowace hanya, a cikin dukan maganarku, da kuma cikin dukan saninku gama shaidarmu game da Kiristi ta tabbata a cikinku. Saboda haka, ba ku rasa kowace baiwa ta ruhaniya ba, yayinda kuke jira da marmari, saboda bayyanuwar Ubangijinmu Yesu Kiristi. Zai ƙarfafa ku har zuwa ƙarshe, domin ku zama marasa aibi a ranar Ubangijinmu Yesu Kiristi. Allah, wanda ya kira ku zuwa ga zumunci tare da Ɗansa Yesu Kiristi Ubangijinmu, shi mai aminci ne. Ina roƙonku ’yan’uwa, a cikin sunan Ubangijinmu Yesu Kiristi, dukanku ku yarda da juna, domin kada a sami tsattsaguwa a cikinku, domin kuma ku zama ɗaya, cikakku a cikin halinku da tunaninku. ’Yan’uwana, waɗansu daga iyalin gidan Kulos sun gaya mini cewa, akwai faɗa a cikinku. Abin da nake nufi shi ne, ɗaya daga cikinku na cewa, “Ni ina bin Bulus,” wani na cewa, “Ni ina bin Afollos,” wani kuma, “Ni ina bin Kefas,” har wa yau wani kuma, “Ni ina bin Kiristi.” Kiristi a rabe ne? Bulus ne aka gicciye dominku? An yi muku baftisma a cikin sunan Bulus ne? Ina godiya domin ban yi wa wani baftisma a cikinku ba, sai dai Kirisbus da Gayus kaɗai. Don haka, ba wanda na iya cewa an yi muku baftisma a cikin sunana. (I, na kuma yi wa iyalin gidan Istifanas baftisma, ban da wannan, ban tuna da wani da na yi masa baftisma ba.) Gama Kiristi bai aike ni yin baftisma ba, sai dai wa’azin bishara ba da kalmomin hikimar mutum ba, domin kada gicciyen Kiristi ya rasa ikonsa. Gama saƙon gicciye wauta ne ga waɗanda suke hallaka, amma a gare mu, mu da ake ceto, ikon Allah ne. Gama a rubuce yake cewa, “Zan rushe hikimar mai hikima, basirar mai azanci kuma zan rikita shi.” Ina mai hikima? Ina mai zurfin bincike? Ina masana na wannan zamani? Ashe, Allah bai wofinta hikimar duniya ba? Gama tun da a cikin hikimar Allah, duniya a cikin hikimarta ba tă san shi ba, Allah ya ji daɗin ceton waɗanda suka ba da gaskiya ta wurin wautar wa’azin bishara. Yahudawa suna so su ga alama, Hellenawa kuma suna neman hikima, amma mu, muna wa’azin Kiristi wanda aka gicciye ne, wanda ya zama dutsen tuntuɓe ga Yahudawa, wauta kuma ga Al’ummai, amma ga su waɗanda Allah ya kira, Yahudawa da Hellenawa, Kiristi ikon Allah ne, da kuma hikimar Allah. Gama wautar Allah ta fi hikimar mutum, kuma rashin ƙarfin Allah ya fi ƙarfin mutum. ’Yan’uwa, ku tuna yadda kuke sa’ad da aka kira ku. Babu masu hikima da yawa a cikinku, bisa ga ganin mutum; babu masu iko da yawa, babu masu martaba da yawa bisa ga haihuwa. Amma Allah ya zaɓi abubuwa masu wautata duniya, don yă kunyata masu hikima. Allah ya zaɓi abubuwa marasa ƙarfi na duniya, domin ya ba wa masu ƙarfi kunya. Ya zaɓi abubuwa marasa martaba na wannan duniya da kuma abubuwan da aka rena da abubuwan da ba a ɗauka a bakin kome ba, domin a wofinta abubuwan da ake ganinsu da daraja, domin kada wani ya yi taƙama a gabansa. Saboda Allah ne kuke cikin Kiristi Yesu, shi wanda ya zama hikima a gare mu daga Allah. Kiristi shi ne adalcinmu, da tsarkinmu, da kuma fansarmu. Saboda haka, kamar yadda yake a rubuce cewa, “Duk wanda yake taƙama, ya yi taƙama a cikin Ubangiji.” Da na zo wurinku ’yan’uwa, ban zo da iya magana ko wani mafificin hikima yayinda na yi muku shelar shaida game da Allah ba. Don na ƙudura a raina sa’ad da nake tare da ku cewa ba zan mai da hankali ga kome ba sai dai Yesu Kiristi wanda aka gicciye. Na zo wurinku cikin rashin ƙarfi da tsoro, da rawan jiki ƙwarai. Saƙona da wa’azina ba su zo cikin hikima da kalmomin lallashi ba, sai dai da nuna ikon Ruhu, domin kada bangaskiyarku ta dogara a kan hikimar mutane, sai dai a kan ikon Allah. Duk da haka, muna sanar da saƙon hikima cikin waɗanda suka balaga, amma ba hikima irin ta wannan zamani ba ne, ko kuwa irin ta masu mulkin zamanin nan, waɗanda za su shuɗe ba. A’a, muna magana ne a kan asirin hikimar Allah, hikimar da tun dā, take a ɓoye, wadda Allah ya ƙaddara domin ɗaukakarmu, tun kafin farkon zamanai. Ba ko ɗaya daga cikin masu mulkin wannan zamani da ya fahimce ta, gama da a ce sun fahimce ta, da ba su gicciye Ubangiji mai ɗaukaka ba. Duk da haka, kamar yadda yake a rubuce cewa, “Ba idon da ya taɓa gani, ba kunnen da ya taɓa ji, ba kuma zuciyar da ta taɓa tunanin abin da Allah ya shirya wa masu ƙaunarsa.” Amma Allah ya bayyana mana shi ta wurin Ruhunsa. Ruhu yana bincika dukan abubuwa, har ma da abubuwa masu zurfi na Allah. Wane ne a cikin mutane ya san tunanin mutum, in ba ruhun mutumin da yake cikinsa ba? Haka kuma ba wanda ya san tunanin Allah, sai dai Ruhun Allah. Ba mu karɓi ruhun duniya ba, sai dai Ruhun da yake daga Allah, domin mu fahimci abin da Allah ya ba mu hannu sake. Wannan shi ne abin da muke sanarwa, ba da kalmomin da muka koya ta wurin hikimar mutum ba, amma da kalmomin da Ruhu yake koyarwa, muna faɗin gaskiya ta ruhaniya da kalmomin ruhaniya. Mutumin da ba shi da Ruhu, ba ya yarda da abubuwan da suka fita daga Ruhun Allah, domin wauta ce a gare shi. Ba kuwa zai fahimce su ba, domin ta Ruhu ne ake fahimtarsu. Mutumin ruhaniya yakan gwada dukan abubuwa, amma shi kansa ba ya ƙarƙashin shari’ar mutum. “Wa ya taɓa sanin hankalin Ubangiji, har da zai koya masa?” Amma muna da tunani iri na Kiristi ne. ’Yan’uwa, ban iya yi muku magana kamar masu ruhaniya ba, sai dai kamar masu halin mutuntaka, jarirai cikin bin Kiristi kawai. Na ba ku madara ba abinci mai tauri ba, domin ba ku balaga ba a lokacin. Kai, har yanzu ma, ba ku balaga ba. Har yanzu kuna rayuwa bisa ga halin mutuntaka. Da yake akwai kishi da faɗace-faɗace a cikinku, ba rayuwa irin ta halin mutuntaka ke nan kuke yi ba? Kuma ba rayuwa irin ta mutane ce kawai kuke yi ba? Gama sa’ad da wani ya ce, “Ni na Bulus ne,” wani kuma ya ce, “Ni na Afollos ne,” ba rayuwa irin ta mutane ke nan kuke yi ba? Shin, wane ne Afollos? Wane ne kuma Bulus? Ai, bayi ne kawai waɗanda ta wurinsu kuka gaskata, kamar yadda Ubangiji ya ba kowannensu aikinsa. Ni na shuka iri, Afollos kuma ya yi banruwa, amma Allah ne ya sa irin ya yi girma. Don haka, da wanda ya yi shuki, da wanda ya yi banruwa, ba a bakin kome suke ba, sai dai Allah kaɗai, mai sa abubuwa su yi girma. Mutumin da ya yi shuki, da mutumin da ya yi banruwa nufinsu ɗaya ne, kuma kowannensu zai sami lada gwargwadon aikinsa. Gama mu abokan aiki ne na Allah; ku kuwa gonar ce ta Allah, ginin Allah kuma. Ta wurin alherin da Allah ya ba ni, na kafa tushen gini kamar ƙwararren magini, wani kuma dabam yana gini a kai. Amma kowa yă lura da yadda yake gini. Gama babu wanda zai iya kafa wani tushen gini dabam da wanda aka riga aka kafa, wanda yake Yesu Kiristi. In wani ya yi gini a kan tushen ginin nan da zinariya, azurfa, duwatsu masu daraja, itace, ciyawa ko kara, aikin zai bayyana kansa, domin za a nuna shi a sarari a Ranar. Wuta ce za tă bayyana aikin, wutar kuwa za tă gwada ingancin aikin kowa. In abin da kowane mutum ya gina ya tsaya, zai sami lada. In ya ƙone, zai yi hasara, amma zai sami ceto, sai dai kamar wanda ya bi ta tsakiyar wuta ne. Ashe, ba ku sani ba cewa ku kanku haikalin Allah ne, Ruhun Allah kuma yana zaune a cikinku? Duk wanda ya ɓata haikalin Allah, Allah zai ɓata shi, don haikalin Allah mai tsarki ne, ku ne kuwa haikalin nan. Kada ku ruɗi kanku. In waninku yana tsammani cewa yana da hikima, yadda duniya ta ɗauki hikima, to, sai ya mai da kansa “wawa” don yă zama mai hikima. Gama hikimar duniyan nan, wauta ce a gaban Allah, kamar yadda yake a rubuce cewa, “Yakan kama masu hikima a cikin makircinsu”; kuma a rubuce yake cewa, “Ubangiji ya san dukan tunanin masu hikima banza ne.” Saboda haka, kada wani yă yi taƙama da mutum! Gama kome naku ne, ko Bulus ko Afollos ko Kefas ko duniya ko rai ko mutuwa ko abubuwa na yanzu ko na nan gaba, ai, duka naku ne, ku kuwa na Kiristi ne, Kiristi kuma na Allah ne. Saboda haka, ya kamata mutane su ɗauke mu a matsayin bayin Kiristi, da kuma a matsayin waɗanda aka ba su amanar asirin abubuwan Allah. Yanzu fa, ana bukatar waɗanda aka ba su riƙon amana, dole su zama masu aminci. Ƙaramin abu ne a gare ni a ce ku ne za ku gwada ni, ko kuwa a gwada ni a wata kotun mutane, ai, ko ni kaina ba na yanka wa kaina hukunci. Lamirina bai ba ni laifi ba, sai dai wannan bai mai da ni marar laifi ba. Ubangiji ne mai hukunta ni. Saboda haka, kada ku shari’anta kome tun lokaci bai yi ba. Ku jira sai Ubangiji ya zo. Zai bayyana abin da yake a ɓoye a cikin duhu a sarari, zai kuma tone nufin zukatan mutane. A lokacin ne fa kowa zai karɓi yabo daga wurin Allah daidai gwargwado. To, fa ’yan’uwa, ga zancen waɗannan abubuwa, na misalta su ne ga kaina, da kuma Afollos saboda ku, don ku yi koyi da mu a kan abin da ake nufi da cewa, “Kada ku zarce abin da yake a rubuce.” Ta haka, ba za ku yi taƙama da wani mutum fiye da wani ba. Wa ya ce ka fi sauran mutane? Me kuma kake da shi, wanda ba karɓa ka yi ba? In kuma karɓa ka yi, me ya sa kake taƙama kamar ba karɓa ba ne ka yi? Kun riga kun sami duk abin da kuke nema! Kun riga kun yi arziki! Kun zama sarakuna, kun kuma zama haka ɗin ba tare da mu ba! Da a ce kun riga kun zama sarakuna mana da sai mu zama sarakuna tare da ku! Gama a ganina fa, Allah ya baje mu manzanni a ƙarshen jerin gwanon, a matsayin mutanen da aka hukunta ga mutuwa a filin wasanni. Mun zama abin kallo ga dukan duniya, ga mala’iku da kuma mutane. Mun zama masu wauta saboda Kiristi, ku kuwa kuna da hikima sosai a cikin Kiristi! Ba mu da ƙarfi, amma ku kuna da ƙarfi! Ana girmama ku, mu kuwa ana ƙasƙantar da mu! Har yă zuwa wannan sa’a, yunwa da ƙishirwa muke ciki, muna sanye da tsummoki, ana wulaƙanta mu, ba mu kuma da gida. Muna aiki da gaske da hannuwanmu. In aka la’anta mu, mukan sa albarka. In aka tsananta mana, mukan jimre; in aka ɓata mana suna, mukan mayar da alheri. Har yă zuwa wannan lokaci, mu ne kamar jujin duniya, abin ƙyamar kowa. Ba don in kunyata ku ba ne na rubuta wannan, sai dai don in gargaɗe ku a kan cewa ku ’ya’yana ne, ƙaunatattu. Ko da kuna da iyayen riƙo dubu goma cikin Kiristi, ba ku da ubanni da yawa, gama a cikin Kiristi Yesu, na zama mahaifi a gare ku, ta wurin bishara. Saboda haka, ina roƙonku ku yi koyi da ni. Saboda wannan dalili ina aika muku Timoti, ɗana, wanda nake ƙauna, mai aminci kuma a cikin Ubangiji. Zai tunashe ku game da yadda za ku bi Kiristi Yesu da kuma yadda ya yi daidai da yadda nake koyarwa a ko’ina, a kowace ikkilisiya. Waɗansunku suna tsammani ba zan zo wurinku ba har suna ɗagankai. Amma in Ubangiji ya yarda zan zo wurinku ba da daɗewa ba. Sa’an nan zan bincike ko masu wannan yawan ɗagan kan nan suna da wani iko. Gama mulkin Allah ba cika baki ba ne, sai dai ga iko. Wanne kuka fi so in na zo? Kuna so in tsananta muku ko in zama mai hankali da kuma sauƙinkai? Ana ba da labari cewa ana lalata a cikinku, irin da ba a ma samu a cikin masu bautar gumaka. Har mutum yana kwana da matar mahaifinsa. Har ya zama muku abin taƙama! Ashe, bai kamata ku cika da baƙin ciki ku kuma daina zumunci da mutumin da yake aikata wannan ba? Ko da yake ba na nan tare da ku cikin jiki, ina tare da ku a cikin ruhu. Na riga na yanke wa wanda ya aikata wannan hukunci, kamar dai ina tare da ku. Saboda haka sa’ad da kun taru ikon Ubangijinmu Yesu kuma yana nan, ni ma ina tare da ku. Ku miƙa irin wannan mutum ga Shaiɗan, don a hallaka halin nan na mutuntaka, ruhunsa kuma yă sami ceto a ranar da Ubangiji zai dawo. Ku daina taƙama. Ba ku san cewa ɗan ƙanƙanin yisti ne yakan sa dukan curin burodi yă kumbura ba? Ku kawar da tsohon yisti don ku zama kamar sabon curi da aka yi babu yisti yadda dai kuke. Gama an miƙa Kiristi Ɗan Ragon Bikin Ƙetarewarmu. Saboda haka, sai mu kiyaye Bikin ba da burodi mai tsohon yisti ba, ba kuma da yisti na ƙeta da mugunta ba, sai dai da burodi marar yisti na sahihanci da na gaskiya. Na rubuta muku cikin wasiƙata, kada ku yi haɗa kai da masu aikin lalata. Ko kusa, ba na nufin fasikai marasa bi, ko makwaɗaita da mazambata, ko matsafa, don in haka ne, sai yă zama dole ku fita daga duniya. Yanzu dai ina rubuta muku cewa kada ku haɗa kai da duk mai kiran kansa ɗan’uwa, amma yana fasikanci, ko kwaɗayi, ko bautar gumaka, ko ɓata suna, ko mashayi, ko mazambaci. Kada ku ko ci abinci da irin wannan mutum. Me zai kai yin hukunci ga waɗanda ba ’yan ikkilisiya ba. Ai, waɗanda suke ’yan ikkilisiya ne za ku hukunta. Allah zai hukunta waɗanda ba namu ba. “Ku yi waje da irin mugun mutumin nan daga cikinku.” In wani a cikinku yana da damuwa da wani, don me zai kai ƙara a gaban marasa bi, maimakon yă kai ƙara a gaban tsarkaka? Ba ku san cewa tsarkaka ne za su yi wa duniya shari’a ba? In kuwa za ku yi wa duniya shari’a, ai, kun isa ku yi shari’a a kan ƙananan damuwoyi ke nan. Ba ku san cewa za mu yi wa mala’iku shari’a ba? Balle al’amuran da suka shafi duniyan nan! Saboda haka, in kuna da damuwa game da irin waɗannan al’amura, sai ku naɗa alƙalai ko cikin waɗanda ba kome ba ne a ikkilisiya! Na faɗi haka ne don ku ji kunya. Ashe, ba za a iya samun wani a cikinku mai hikima wanda zai iya sasanta tsakanin masu bi ba? Me zai sa ɗan’uwa yă kai ƙarar ɗan’uwa, a gaban marasa bi? Ƙarar junanku ma da kuke yi, ai, kāsawa ce a gare ku. Ba gara ku haƙura a cuce ku ba? Ku kuma haƙura ko an zambace ku? Amma ga shi ku da kanku kuna cuta, kuna kuma zamba, har ma ga ’yan’uwanku ne kuke yi wannan. Ba ku sani ba cewa mugaye ba za su gāji mulkin Allah ba? Kada fa a ruɗe ku. Ba masu fasikanci ko masu bautar gumaka ko masu zina ko karuwan maza, ko ’yan daudu, ko ɓarayi ko masu kwaɗayi ko mashaya ko masu ɓata suna ko masu zamba da za su gāji mulkin Allah. Haka waɗansu a cikinku ma suke a dā. Amma an wanke ku, an tsarkake ku, aka kuma sa kuka zama marasa laifi cikin sunan Ubangijinmu Yesu Kiristi da kuma ta wurin Ruhun Allahnmu. “Ina da dama in yi kome,” sai dai ba kome ba ne yake da amfani. “Ina da dama in yi kome” sai dai ba abin da zai mallake ni. “An yi abinci domin ciki ne, ciki kuma domin abinci.” Amma Allah zai hallaka su duka. Ba a yi jiki saboda fasikanci ba, sai dai domin Ubangiji, Ubangiji kuma domin jiki. Ta wurin ikonsa, Allah ya tashe Ubangiji daga matattu, haka zai tashe mu mu ma. Ba ku sani ba cewa jikunanku gaɓoɓin Kiristi ne kansa? Zai kyautu in ɗauki gaɓoɓin Kiristi in haɗa da jikin karuwa? Sam! Ba ku san cewa shi wanda ya haɗa jikinsa da karuwa sun zama ɗaya a cikin jiki ke nan ba? Gama an ce, “Biyun za su zama jiki ɗaya.” Wanda kuwa ya haɗa jikinsa da Ubangiji ya zama ɗaya da shi ke nan a ruhu. Ku guji fasikanci. Duk sauran zunubai da mutum yakan aikata suna waje da jikinsa, amma mai yin fasikanci, yana ɗaukar alhalin jikinsa ne. Ba ku san cewa jikin nan naku haikalin Ruhu Mai Tsarki ba ne wanda yake cikinku yake kuma daga Allah? Ku ba na kanku ba ne; saye ku fa aka yi da tsada, saboda haka, sai ku girmama Allah da jikinku. To, game da zancen da kuka rubuto. Yana da kyau mutum yă zauna ba aure. Amma da yake fasikanci ya yi yawa, ya kamata kowane mutum yă kasance da matarsa, kowace mace kuma da mijinta. Ya kamata miji yă cika hakkinsa na aure ga matarsa. Haka kuma matar ta yi ga mijinta. Jikin matar ba nata ne kaɗai ba, amma na mijinta ne ma. Haka ma jikin mijin, ba na shi ne kaɗai ba, amma na matarsa ne ma. Kada ku ƙi kwana da juna sai ko kun yarda a junanku kuma na ɗan lokaci, don ku himmantu ga addu’a. Sa’an nan ku sāke haɗuwa don kada Shaiɗan yă jarrabce ku saboda rashin ƙamewarku. Wannan fa shawara ce nake ba ku, ba umarni ba. Da ma a ce dukan maza kamar ni suke mana. Sai dai kowa da irin baiwar da Allah ya yi masa; wani yana da wannan baiwa, wani kuwa wancan. To, ga marasa aure da gwauraye kuwa ina cewa yana da kyau su zauna haka ba aure, yadda nake. Sai dai in ba za su iya ƙame kansu ba, to, su yi aure, don yă fi kyau a yi aure, da sha’awa ta sha kan mutum. Ga waɗanda suke da aure kuwa ina ba da wannan umarni (ba ni ba, amma Ubangiji) cewa kada mace ta rabu da mijinta. In kuwa ta rabu da shi, sai ta kasance ba aure, ko kuma ta sāke shiryawa da mijinta. Kada miji kuma yă saki matarsa. Ga sauran kuwa (ni ne fa na ce ba Ubangiji ba), in wani ɗan’uwa yana da mata wadda ba mai bi ba ce, kuma tana so ta zauna tare da shi, kada yă sake ta. In kuma mace tana da miji wanda ba mai bi ba ne, kuma yana so yă zauna tare da ita, kada tă kashe auren. Don miji marar ba da gaskiya an tsarkake shi ta wurin matarsa. Mace marar ba da gaskiya kuma an tsarkake ta ta wurin mijinta. In ba haka ba ’ya’yanku ba za su zama da tsarki ba, amma kamar yadda yake, su masu tsarki ne. Amma in marar bi ɗin ya raba auren, a ƙyale shi. A irin wannan hali, babu tilas a kan wani, ko wata mai bi. Allah ya kira mu ga zaman lafiya ne. Ke mace, kin sani ne, ko ke ce za ki ceci mijinki? Kai miji, ka sani ne, ko kai ne za ka ceci matarka? Duk da haka, sai kowa yă kasance a rayuwar da Ubangiji ya sa shi da kuma wanda Allah ya kira shi. Umarnin da na kafa a dukan ikkilisiyoyi ke nan. In an riga an yi wa mutum kaciya sa’ad da aka kira shi, to, kada yă zama marar kaciya. In an kira mutum sa’ad da yake marar kaciya, to, kada a yi masa kaciya. Kaciya ba wani abu ba ne, rashin kaciya kuma ba wani abu ba ne. Kiyaye umarnin Allah shi ne muhimmin abu. Ya kamata kowa yă kasance a matsayin da yake ciki sa’ad da Allah ya kira shi. Kai bawa ne sa’ad da aka kira ka? Kada wannan yă dame ka, sai dai in kana iya samun ’yanci, sai ka yi amfani da wannan dama. Gama wanda yake bawa sa’ad da Ubangiji ya kira shi, ’yantacce ne na Ubangiji; haka ma, wanda yake ’yantacce sa’ad da aka kira shi, bawa ne na Kiristi. Da tsada fa aka saye ku, kada ku zama bayin mutane. ’Yan’uwa, a duk matsayin da mutum yake sa’ad da aka kira shi, sai yă kasance haka a sabuwar dangantakarsa da Allah. To, game da budurwai. Ba ni da wani umarni daga Ubangiji, sai dai na yanke hukunci a matsayi wanda yake amintacce ta wurin jinƙan Ubangiji. Saboda ƙuncin rayuwar da ake ciki, ina gani ya fi kyau ku kasance yadda kuke. In kuna da aure, kada ku nemi kashe auren. In ba ku da aure, kada ku nemi yin aure. Amma idan ka riga ka yi aure, to, ba laifi, ba zunubi ba ne, kuma idan yarinya ta yi aure, ba tă yi laifi ba. Sai dai waɗanda suka yi aure za su fuskanci damuwoyi masu yawa a cikin rayuwa, ni kuwa ina so in fisshe su daga wannan. ’Yan’uwa, abin da nake nufi shi ne, lokaci ya rage kaɗan. Daga yanzu, waɗanda suke da mata ya kamata su yi rayuwa kamar ba su da su; waɗanda suke kuka kuma kamar ba kuka suke yi ba, waɗanda suke farin ciki kuwa kamar ba farin ciki suke yi ba. Waɗanda suka sayi abu su yi kamar ba nasu ba ne; masu amfani da kayan duniya kuwa, kada su duƙufa a cikinsu. Gama duniyan nan a yadda take mai shuɗewa ce. Zan so ku ’yantu daga damuwa. Mutum marar aure ya damu ne da al’amuran Ubangiji, yadda zai gamshi Ubangiji. Amma mutumin da yake da aure yakan damu ne da al’amuran wannan duniya, yadda zai gamshi matarsa hankalinsa a rabe yake. Mace marar aure ko kuwa budurwa ta damu ne da al’amuran Ubangiji. Nufinta shi ne ta ba da kanta ga Ubangiji cikin jiki da ruhu. Amma mace da take da aure ta damu ne da al’amuran wannan duniya, yadda za tă gamshi mijinta. Na faɗa haka don amfaninku ne, ba don in ƙuntata muku ba. Sai dai don ku yi rayuwa a hanyar da ta dace da nufin ku himmantu ga bautar Ubangiji ba da raba hankali ba. In mutum ya ga cewa ba ya nuna halin da ya kamata ga budurwar da ya yi alkawarin aure da ita, in kuma shekarunta suna wucewa, shi kuma ya ga ya kamata yă yi aure, to, sai yă yi. Ba zunubi ba ne. Ya kamata su yi aure. Amma mutumin da ya riga ya yanke shawara a ransa, wanda kuma ba lalle ba ne amma yana iya shan kan nufinsa, kuma ya riga ya zartar a zuciyarsa ba zai auri budurwar ba, wannan mutum ma ya yi abin da ya dace. Don haka, wanda ya auri budurwar ya yi daidai, amma wanda bai aure ta ba ya ma fi. Mace tana haɗe da mijinta muddin yana da rai. Amma in mijinta ya mutu, tana da ’yanci ta auri wanda take so. Amma fa, sai mai bin Ubangiji. A nawa ra’ayi, za tă fi jin daɗi in ta zauna haka, a ganina kuwa ina ba ku shawara ce daga Ruhun Allah da na ce haka. To, game da abincin da aka miƙa hadaya ga gumaka kuwa. Mun san cewa dukanmu muna da ilimi. Ilimi yakan kawo girman kai, amma ƙauna takan gina. Mutumin da yake tsammani ya san abu, sanin da yake da shi bai isa ba. Amma mutumin da yake ƙaunar Allah, Allah yana sane da shi. To, game da cin abincin da aka miƙa hadaya ga gumaka kuwa, mun san cewa “Gunki ba kome ba ne a duniya”, kuma “Babu wani Allah sai dai ɗaya.” Gama ko da akwai abubuwan da ake ce da su alloli, a sama ko a ƙasa (don kuwa akwai “alloli” da “iyayengiji” da yawa), duk da haka a gare mu dai akwai Allah ɗaya kaɗai, Uba, wanda dukan abubuwa suke daga gare shi, wanda kuma saboda shi ne muke rayuwa, kuma akwai Ubangiji ɗaya, Yesu Kiristi, wanda ta wurinsa ne aka yi dukan abu, ta wurinsa ne kuma muke rayuwa. Amma ba kowa ne ya san wannan ba. Har yanzu, waɗansu mutane sun saba da tunani cewa gumaka ainihi ne, saboda haka sa’ad da suka ci irin abincin nan, sukan ɗauka cewa kamar an miƙa wa ga gunki ne, kuma da yake lamirinsu ba ƙarfi, yakan ƙazantu. Gaskiya ne cewa ba ma samun yardar Allah ta wurin abin da muke ci. Ba ma rasa wani abu idan ba mu ci ba, kuma ba ma ƙaru da wani abu in muka ci. Sai dai ku yi hankali, kada yin amfani da ’yancinku yă zama abin sa tuntuɓe ga marasa ƙarfi. Gama in wani wanda lamirinsa ba shi da ƙarfi ya gan ka, kai da kake da wannan sani, kana ci a haikalin gumaka, ashe, ba zai sami ƙarfin halin cin abin da aka miƙa wa gumaka ba? Saboda haka ta wurin sanin nan naka sai ka sa wannan ɗan’uwa marar ƙarfi wanda Kiristi ya mutu dominsa yă hallaka. Sa’ad da ka rushe lamiri mai bi marar ƙarfi, ka yi wa Kiristi zunubi ke nan. Saboda haka, in abin da nake ci zai sa ɗan’uwana yă yi zunubi, ba zan ƙara cin nama ba, don kada in sa shi yă yi tuntuɓe. Ba ni da ’yanci ne? Ni ba manzo ba ne? Ni ban gan Yesu Ubangijinmu ba ne? Ba ku ne sakamakon aikina cikin Ubangiji ba? Ko da waɗansu ba su ɗauke ni a matsayin manzo ba, tabbatacce, ni manzo ne a gare ku! Gama ku ne hatimin manzancina a gaban Ubangiji. Wannan ita ce kāriyata ga waɗanda suke tuhumata game da manzancina. Ba mu da ’yancin ci da sha ne? Ba mu da ’yancin tafiya tare da matar da muka aura mai bi kamar sauran manzanni da ’yan’uwan Ubangiji da kuma Kefas suke yi? Ko ni da Barnabas ne kawai ba mu da ’yanci a ɗauke mana aikin ci da kai? Wa yake ciyar da kansa yayinda yake aikin soja? Wa yake shukar gonar inabi, da ba ya cin amfaninta? Wa yake kiwon garke, da ba ya sha madararsa? Ina faɗin wannan bisa ga ra’ayin mutum kawai ne? Ashe, Doka ma ba tă faɗa haka ba? Gama yana a rubuce a cikin Dokar Musa cewa, “Kada ka sa wa saniya takunkumi sa’ad da yake sussukar hatsi.” Kuna tsammani a kan shanu ne Allah ya damu sa’ad da ya ce haka? Babu shakka, ya yi maganan nan saboda mu ne. Ko ba haka ba? I, an rubuta wannan saboda mu ne, domin sa’ad da mai noma yake noma, mai sussuka kuma yana sussuka, suna wannan ne da bege za su sami rabonsu daga girbin. In muka shuka iri na ruhaniya a cikinku, ashe, bai kamata mu yi girbin abin biyan bukatarmu daga gare ku ba? In waɗansu suna samun wannan taimako daga gare ku, ashe, mu ba mu fi cancanta mu samu ba? Amma ba mu yi amfani da wannan ’yancin ba. A maimakon haka, mun jure da kome, domin kada mu hana bisharar Kiristi yaɗuwa. Ashe, ba ku san cewa waɗanda suke hidima a haikali suna samun abincinsu daga haikali ba ne, waɗanda kuma suke hidima a bagade suna samun rabo a hadayar da suka miƙa ba ne? Haka ma Ubangiji ya umarta cewa ya kamata waɗanda suke wa’azin bishara, su sami abin biyan bukatarsu daga bisharar. Amma ban yi amfani da ko ɗaya daga cikin waɗannan ’yancin ba. Ba kuma ina rubuta muku wannan da fata za ku yi mini waɗannan abubuwa ba ne. Gwamma in mutu, da wani yă hana ni wannan abin taƙama. Duk da haka, sa’ad da ina wa’azin bishara, ba na taƙama, domin tilas ne a gare ni in yi wa’azi. Kaitona, in ban yi wa’azin bishara ba! In na yi wa’azi da yardar rai, ina da lada; in ba da yardar rai ba, ina dai cika amana da aka danƙa mini ne. To, mene ne ladana? Ladana kaɗai shi ne, in yi wa’azin bishara, in kuma yi shi a kyauta, yadda ba zan yi amfani da ’yancina cikin wa’azin ba. Ko da yake ina da ’yanci ba na kuma ƙarƙashin kowa, na mai da kaina bawa ga kowa, domin in rinjayi mutane da yawa. Ga Yahudawa na zama kamar mutumin Yahuda, domin in rinjayi Yahudawa. Ga waɗanda suke ƙarƙashin doka kuma, na zama kamar wanda yake ƙarƙashin Dokar (ko da yake ni kaina ba na ƙarƙashin Doka), domin in rinjayi waɗanda suke ƙarƙashin Doka. Ga waɗanda ba su da Dokar kuwa, na zama kamar wanda ba shi da Dokar (ko da yake ba ni da ’yanci daga dokar Allah, amma ina ƙarƙashin dokar Kiristi), domin in rinjayi waɗanda ba su da dokar. Ga waɗanda ba su da ƙarfi, na zama marar ƙarfi, domin in rinjayi waɗanda ba su da ƙarfi. Na zama dukan abu ga dukan mutane, domin ko ta yaya in zai yiwu, in ceci waɗansu. Ina yin dukan waɗannan ne saboda bishara, domin in sami rabo a cikin albarkarta. Ba ku sani ba cewa a gasar gudu, dukan masu gudu sukan yi gudu, amma guda ne kaɗai yakan sami lada? To, sai ku yi gudu yadda za ku sami lada. Duk ’yan wasan gasa sukan hori kansu sosai. Sukan yi haka domin su sami rawanin da ba zai daɗe ba. Amma mu muna yi ne domin mu sami rawanin da zai dawwama. To, ni fa ba gudu nake yi kamar mai gudu ba wurin zuwa ba. Dambena kuma ba naushin iska nake yi ba. A’a, ina horon jikina in mai da shi bawana, saboda bayan na yi wa waɗansu wa’azi, ni kaina kada in kāsa cancantar samun lada. Ba na so ku kasance da rashin sani, ’yan’uwa, cewa dukan kakannin-kakanninmu sun yi tafiya a ƙarƙashin girgije, dukansu kuma suka bi ta tsakiyar teku. An yi wa dukansu baftisma ga bin Musa a cikin girgije da kuma cikin teku. Dukansu sun ci abincin ruhaniya guda suka kuma sha ruwan ruhaniyan nan guda; gama sun sha daga dutsen ruhaniya nan, wanda ya yi tafiya tare da su, wannan dutsen kuwa Kiristi ne. Duk da haka, Allah bai ji daɗin yawancinsu ba; gawawwakinsu kuwa suka bazu ko’ina a cikin hamada. To, waɗannan abubuwa misalai ne a gare mu, kada mu yi marmarin mugayen abubuwa, kamar yadda suka yi. Kada ku zama masu bautar gumaka, yadda waɗansunsu suka zama; kamar yadda yake a rubuce cewa, “Mutanen suka zauna don su ci su kuma sha, suka kuma tashi suka shiga rawa ta rashin kunya.” Kada fa mu yi fasikanci yadda waɗansunsu suka yi, har a rana guda mutane dubu ashirin da uku a cikinsu suka mutu. Kada mu gwada Kiristi yadda waɗansunsu suka yi, har macizai suka kakkashe su. Kada kuma ku yi gunaguni yadda waɗansunsu suka yi, har mala’ika mai hallakarwa ya hallaka su. Waɗannnan abubuwa sun same su ne, domin su zama abubuwan koyi, aka kuma rubuta su domin a gargaɗe mu, mu da ƙarshen zamani ya zo mana. Saboda haka in kana tsammani kana tsaye ne, to, ka yi hankali kada ka fāɗi! Ba jarrabar da ta taɓa samunku, wadda ba a saba yi wa mutum ba. Allah mai aminci ne; ba zai bari a jarrabce ku fiye da ƙarfinku ba. Amma in aka jarrabce ku, zai nuna muku mafita, domin ku iya cin nasara. Saboda haka abokaina ƙaunatattu, ku guje wa bautar gumaka. Ina magana da ku a kan ku mutane ne fa masu azanci; ku duba da kanku ku ga abin da nake faɗa. Kwaf nan na godiya da muke yin godiya da shi, ashe ba tarayya ce a cikin jinin Kiristi ba? Wannan burodi kuma da muke karya mu ci, ashe, ba tarayya ne a cikin jikin Kiristi ba? Da yake burodin nan ɗaya ne, ashe kuwa, mu da muke da yawa jiki ɗaya ne, gama dukanmu muna ci daga burodi nan guda. Ku dubi mutanen Isra’ila mana. Ashe, waɗanda suke cin hadayu, ba ɗaya suke da juna cikin cin hadayun da aka miƙa a bagade ba? To, me kuke tsammani nake nufi a nan? Hadayar da aka miƙa wa gunki ce wani abu, ko kuma gunkin ne wani abu? A’a, ina nufin akan miƙa hadayun da masu bautar gumaka suka wa aljanu ne, ba Allah ba. Ba na so ku zama ɗaya da aljanu. Ba zai yiwu ku sha daga kwaf na Ubangiji ku kuma sha daga kwaf na aljanu ba, ba ya yiwuwa ku ci a teburin Ubangiji, ku kuma ci a teburin aljanu. Ashe, so muke mu tsokani Ubangiji ya yi kishi? Mun fi shi ƙarfi ne? “Ana da dama a yi kome” sai dai ba kome ba ne yake da amfani. “Ana da dama a yi kome” sai dai ba kome ba ne mai ginawa. Kada wani yă kula da kansa kawai, sai dai yă kula da waɗansu kuma. Ku ci kowane abin da ake sayarwa a kasuwar nama ba sai kun tambaya ba don kada lamiri yă damu da inda abin ya fito, gama “Duniya da duk abin da yake cikinta na Ubangiji ne.” In wani marar bi ya gayyace ku cin abinci kuka kuwa yarda ku je, sai ku ci ko mene ne da aka sa a gabanku, ba tare da tambaya don kada lamiri yă damu da inda abin ya fito. Sai dai in wani ya ce muku, “Ai, wannan an miƙa ne wa gunki,” to, kada ku ci, saboda duban mutuncin wannan da ya gaya muku, don kuma lamiri yă kasance babu laifi ina nufin lamirin wancan mutum ne fa, ba naku ba. Don me lamirin wani zai shari’anta ’yancina? In na ci abinci da godiya, don me za a zarge ni a kan abin da na ci da godiya ga Allah? Saboda haka, duk abin da kuke yi, ko ci ko sha, ku yi shi duka saboda ɗaukakar Allah. Kada ku sa wani yă yi tuntuɓe, ko mutumin Yahuda ne, ko mutumin Al’ummai ko kuma ikkilisiyar Allah kamar dai yadda nake ƙoƙarin faranta wa kowa rai, ta kowace hanya. Gama ba don kaina kaɗai nake yi ba, sai dai don amfanin mutane da yawa, don su sami ceto. Ku bi gurbina, kamar yadda ni nake bin gurbin Kiristi. Ina yabonku saboda kuna tunawa da ni a cikin kowane abu, kuna kuma riƙe da koyarwar, yadda na ba ku. To, ina so ku gane cewa shugaban kowane namiji Kiristi ne, shugaban mace namiji ne, shugaban Kiristi kuma Allah ne. Kowane namijin da ya yi addu’a ko annabci da kansa a rufe ya jawo kunya wa kansa. Duk macen da ta yi addu’a ko annabci da kanta a buɗe kuwa ta rena kanta, ya zama kamar an aske kanta ke nan. In mace ba ta so tă rufe kanta, to, sai tă aske gashinta; in kuwa abin kunya ne mace tă yanke ko tă aske gashinta, to, sai tă rufe kanta. Namiji kuwa bai kamata ya rufe kansa ba, da yake shi kamannin Allah ne, da kuma darajar Allah, amma mace dai, darajar namiji ne. Gama namiji bai fito daga mace ba, sai dai mace ce ta fito daga namiji. Ba a kuma halicci namiji don mace ba, sai dai mace don namiji. Don haka, saboda wannan, da kuma saboda mala’iku, dole mace ta ɗaura wani abu a kanta. Duk da haka a cikin Ubangiji, mace ba a rabe take da namiji ba, namiji kuma ba a rabe yake da mace ba. Kamar yadda mace ta fito daga namiji, haka kuma aka haifi namiji ta wurin mace. Sai dai kowane abu daga Allah yake. Ku kanku duba mana. Ya yi kyau mace tă yi addu’a ga Allah da kanta a buɗe? Kai, yadda halitta take ma, ai, ta koya muku cewa in namiji yana da dogon gashi, abin kunya ne a gare shi, amma in mace tana da dogon gashi, ai, daraja ce a gare ta. Gama an ba ta dogon gashi saboda rufe kanta ne. In akwai mai gardama da wannan, to, mu dai ba mu da wata al’ada, haka ma ikkilisiyoyin Allah. Game da umarnan nan dai, ban yaba muku ba, domin taruwarku ba ta kirki ba ce, ɓarna ce. Da farko dai, na ji cewa sa’ad da kuka taru a matsayin ikkilisiya, akwai tsattsaguwa a tsakaninku, har na fara yarda da zancen. Ba shakka dole a sami bambanci a tsakaninku don a nuna wa Allah ya amince da shi a cikinku. Sa’ad da kuka taru, ba Cimar Ubangiji kuke ci ba, gama yayinda kuke ci, kowa yakan ci gaba ba tare da jiran wani ba. Wani yă zauna da yunwa, wani kuma yă bugu. Kai, ba ku da gidajen da za ku ci ku sha ne? Ko dai kun rena ikkilisiyar Allah ne, kuna kuma wulaƙanta waɗanda ba su da kome? Me zan ce muku? In yabe ku ne game da wannan? A’a, ko kaɗan! Gama abin da na karɓa daga wurin Ubangiji shi ne nake ba ku. Ubangiji Yesu, a daren da aka bashe shi, ya ɗauki burodi, bayan ya yi godiya, sai ya kakkarya ya ce, “Wannan jikina ne, wanda yake dominku, ku yi wannan don tunawa da ni.” Haka kuma bayan cimar, ya ɗauki kwaf, yana cewa, “Wannan kwaf ne sabon alkawari a jinina; ku yi wannan, a duk sa’ad da kuke sha, don tunawa da ni.” Gama a duk sa’ad da kuke cin wannan burodi, kuke kuma sha daga wannan kwaf, kuna shelar mutuwar Ubangiji ne har yă dawo. Saboda haka, duk wanda ya ci burodin ko ya sha daga kwaf na Ubangiji da rashin cancanta, ya yi laifin wulaƙanta jiki da jinin Ubangiji ke nan. Dole kowa yă bincike kansa kafin yă ci burodin yă kuma sha daga kwaf ɗin. Gama duk wanda ya ci ya kuma sha ba tare da fahimtar jikin Ubangiji ba, ya ci ya kuma sha wa kansa hukunci ne. Shi ya sa da yawa a cikinku ba su da ƙarfi, suna kuma da rashin lafiya, waɗansunku kuma sun riga sun yi barci. Amma in da za mu auna kanmu sosai, da ba za mu shiga irin hukuncin nan ba. Duk da haka sa’ad da Ubangiji ya hukunta mu, ana yin mana horo ne don kada a ƙarshe a hallaka mu tare da duniya. Saboda haka ’yan’uwana, sa’ad da kuka taru don ci, ku jira juna. In wani yana jin yunwa, sai yă ci abinci a gida, saboda in kuka taru kada yă jawo hukunci. Sa’ad da na zo kuma zan ba da ƙarin umarnai. To, game da baye-baye na ruhaniya, ’yan’uwa, ba na so ku kasance da rashin sani. Kun san cewa sa’ad da kuke masu bautar gumaka, ya zama, an shawo kanku, aka kuma ɓad da ku ga bin gumaka marasa magana. Saboda haka, ina gaya muku cewa ba wani mai magana da ikon Ruhun Allah da zai ce, “Yesu la’ananne ne,” haka kuma ba wanda zai ce, “Yesu Ubangiji ne,” sai wanda Ruhu Mai Tsarki yake bi da shi. Akwai baye-baye iri dabam-dabam, amma Ruhu ɗaya ne. Akwai hidimomi iri-iri, amma Ubangiji ɗaya ne. Akwai aiki iri-iri, amma duk Allah ɗaya ne yake aikata su a cikin dukan mutane. An ba wa kowane mutum bayyanuwar Ruhu don amfanin kowa. Ga wani, an ba shi saƙon hikima ta wurin Ruhu, ga wani baiwar saƙon sani ta wurin wannan Ruhu guda. Ga wani bangaskiya ta wurin wannan Ruhu, ga wani kuma baiwar warkarwa ta wurin wannan Ruhu guda. Ga wani yin ayyukan banmamaki, ga wani annabci, ga wani baiwar rarrabe ruhohi, ga wani baiwar magana da harsuna dabam-dabam, ga wani har wa yau iya fassarar harsuna. Duk waɗannan aiki ne na wannan Ruhu guda, yana kuma ba da su ga kowane mutum, yadda yake so. Jiki guda ne, ko da yake an yi shi da gaɓoɓi da yawa; gaɓoɓin kuma ko da yake da yawa suke, jiki ɗaya ne. Haka yake da Kiristi. Dukanmu an yi mana baftisma ta wurin Ruhu guda zuwa ga jiki guda, ko Yahudawa ko Hellenawa, bawa ko ’yantacce, an kuma ba wa dukanmu wannan Ruhu guda mu sha. To, ba a yi jiki da gaɓa ɗaya kawai ba, amma da gaɓoɓi da yawa. Da ƙafa za tă ce, “Saboda ni ba hannu ba ce, ni ba gaɓar jiki ba ce.” Wannan ba zai hana ta zama gaɓar jikin ba. Da kunne zai ce, “Saboda ni ba ido ba ne, ni ba gaɓar jiki ba ne.” Wannan ba zai hana shi zama gaɓar jikin ba. Da a ce dukan jiki ido ne, da me za a ji? Da kuma a ce dukan jiki kunne ne, da me za a sansana? Tabbatacce, Allah ya shirya gaɓoɓin jiki, kowannensu, kamar yadda yake so su zama. Da a ce dukan jiki gaɓa ɗaya ne, da ina sauran jikin? Yadda yake dai, akwai gaɓoɓi da yawa, amma jiki ɗaya. Ba dama ido ya ce wa hannu, “Ba na bukatarka ba!” Kai kuma ba zai ce wa ƙafafu, “Ba na bukatarku ba!” A maimakon haka, gaɓoɓin jiki da ake gani kamar ba su da ƙarfi, su ne masu muhimmanci. Kuma gaɓoɓin da muke tsammani ba su da martaba sosai, su ne mukan fi ba su girma. Sa’an nan gaɓoɓi marasa kyan gani, mun fi mai da hankali a kansu, gaɓoɓi masu kyan gani kuwa, ba su bukatar yawan girmamawa. Allah ya harhaɗa jikunanmu yadda gaɓoɓin da ake gani kamar ba su da muhimmanci suna da amfani, don kada rarrabuwa ta kasance a jiki, sai dai gaɓoɓin jiki su kula da juna. In wata gaɓa tana a damuwa, duk sai su damu tare. In kuma an ɗaukaka wata gaɓa, sai duk su yi farin ciki tare. To, ku jikin Kiristi ne, kowannenku kuwa gaɓarsa ne. A cikin ikkilisiya, da farko dai Allah ya zaɓa waɗansu ya naɗa su su zama manzanni, na biyu annabawa, na uku malamai, sa’an nan masu yin ayyukan banmamaki, sai masu baiwar warkarwa, da masu taimakon waɗansu, da masu baiwar gudanarwa, sa’an nan kuma masu magana da harsuna iri-iri. Shin, duka ne manzanni? Duka ne annabawa? Duka ne malamai? Duka ne suke da baiwar yin ayyukan banmamaki? Duka ne suke da baiwar warkarwa? Duka ne suke magana da harsuna? Duka ne suke iya fassara? Sai dai ku yi marmarin neman baye-baye mafi girma. Yanzu kuwa zan nuna muku mafificiyar hanya. In ina iya yin magana da harsunan mutane, da na mala’iku, amma ba ni da ƙauna, na zama kamar kuge mai yawan ƙara, ko kuma ƙararrawa mai amo kawai. In ina da baiwar annabci, ina kuma iya fahimtar dukan asirai da dukan ilimi, in kuma ina da bangaskiyar da zan iya kawar da manyan duwatsu, amma ba ni da ƙauna, ni ba kome ba ne. In na ba wa matalauta dukan abin da nake da shi, na kuma miƙa jikina a ƙone, amma ba ni da ƙauna, ban yi riban kome ba. Ƙauna tana da haƙuri, ƙauna tana da kirki. Ba ta kishi, ba ta burga, ba ta da girman kai. Ba ta rashin ladabi, ba ta sonkai, ba ta da saurin fushi, ba ta riƙe mutum a zuciya. Ƙauna ba ta jin daɗin mugunta, sai dai ta ji daɗin gaskiya. Tana kāriya kullum, tana amincewa kullum, tana bege kullum, tana jimrewa kullum. Ƙauna ba ta ƙarewa. Amma in akwai annabci zai shuɗe, harsuna su ɓace, ilimi kuma zai ƙare. Gama saninmu ba cikakke ba ne, annabcinmu kuma ba cikakke ba ne. Sai dai sa’ad da cikakken ya zo, sai wanda ba cikakke yă shuɗe. Sa’ad da nake yaro, na yi magana kamar yaro, na yi tunani kamar yaro, na yanke shawara kamar yaro. Da na isa mutum kuwa, sai na bar halin yarantakata. Yanzu kam muna ganin abubuwa kamar a madubi sai dai ba sosai ba, amma a ranan nan za mu gani fuska da fuska. Yanzu kam sanina ba cikakke ba ne, amma a ranan nan zan kasance da cikakken sani, kamar dai yadda Allah ya san ni a yanzu. Yanzu kam abubuwan nan uku sun tabbata, bangaskiya, bege, da kuma ƙauna. Sai dai mafi girma a cikinsu ita ce ƙauna. Ku bi halin ƙauna kuna kuma marmarin neman baye-bayen ruhaniya, musamman baiwar annabci. Gama duk wanda yake magana da wani harshe ba da mutane yake magana ba, sai dai da Allah. Tabbatacce, ba wanda yake fahimtarsa; yana faɗin asirai ta wurin ruhu ne. Amma duk wanda yake annabci, yana magana ne da mutane domin yă gina su, yă ƙarfafa su, yă kuma yi musu ta’aziyya. Wanda yake magana da wani harshe kuwa, kansa yake gina, amma mai annabci, ikkilisiya ce yake gina. Zan so kowannenku yă yi magana da harsuna, sai dai zan fi so ku yi annabci. Wanda yake annabci ya fi wanda yake magana da harsuna, sai dai in ya fassara don ikkilisiya ta ginu. To, ’yan’uwa, a ce na zo wurinku ina kuma yin magana da waɗansu harsuna, amfanin me zan yi muku in ban zo muku da wani bayani ko sani ko annabci, ko kuma kalmar koyarwa ba? Abubuwan nan marasa rai ma da sukan yi ƙara, kamar su algaita ko molo, in muryarsu ba tă fita sosai ba, yaya wani zai san abin da ake busawa ko kaɗawa? Haka ma in ba a busa ƙaho sosai ba, wa zai yi shirin yaƙi? Haka yake sa’ad da kuka yi magana da waɗansu harsunan da ba a fahimta. In babu wanda zai san abin da kuke faɗi, za ka dai yi wa iska magana ne kawai. Ba shakka akwai harsuna iri-iri a duniya, duk da haka kowane a cikinsu yana da ma’ana. To, in ban gane ma’anar abin da wani yake faɗi ba, ni baƙo ne ga mai maganar, shi kuma baƙo ne a gare ni. Haka yake a gare ku. Da yake kuna marmarin samun baye-bayen ruhaniya, sai ku ba da ƙarfinku ga yin amfani da waɗanda za su gina ikkilisiya. Saboda haka, duk wanda yake magana da harshe, sai yă yi addu’a a yi masa baiwar fassara. Gama in na yi addu’a da wani harshe, ruhuna ne yake addu’a, amma tunanina bai amfana kome ba. To, me zan yi? Akwai lokutan da zan yi addu’a da ruhuna; akwai kuma lokutan da zan yi addu’a da hankalina. Wani lokaci ya kamata in yi waƙa da ruhuna, a wani lokacin kuma in yi waƙa da hankalina. A cewa waɗansu baƙi suna cikin sujadarku, sa’ad da kuke yabon Allah da ruhunku, yaya waɗanda suke tare ku za su fahimta, har su ce, “Amin,” da yake ba su san abin da kuke faɗi ba? Ko da yake kuna ba da godiya da kyau, amma wancan mutumin da yake tare da ku bai ginu ba. Na gode wa Allah, domin ina magana da harsuna fiye da ku duka. Amma a cikin ikkilisiya zan gwammace in yi magana da kalmomi biyar da za a fahimta don in koyar da waɗansu da a ce in yi magana da kalmomi guda dubu goma a wani harshe. ’Yan’uwa, ku daina tunani kamar yara. Wajen mugunta ku zama jarirai, sai dai wajen tunaninku, ku zama manya. A cikin Doka yana a rubuce cewa, “Ta wurin mutane masu baƙin harsuna da kuma ta leɓunan baƙi zan yi magana da waɗannan mutane, amma duk da haka, ba za su saurare ni ba,” in ji Ubangiji. Harsuna fa alama ce ba ga masu bi ba, sai dai ga marasa bi. Annabci kuwa ga masu bi ne ba ga marasa bi ba. Saboda haka, in dukan ikkilisiya ta taru, kowa kuma yana magana da waɗansu harsuna, sai waɗansu jahilai ko waɗansu marasa bi suka shigo, ashe, ba za su ce kuna hauka ba? Amma in wani marar bi, ko jahili ya shigo sa’ad da kowa yana annabci, sai maganar kowa ta ratsa shi, za su shawo kansa yă gane cewa shi mai zunubi ne saboda abin da kowa yake faɗi, asirin zuciyarsa kuma su bayyana a fili. Don haka, zai fāɗi a ƙasa yă yi wa Allah sujada yana cewa, “Lalle, Allah yana cikinku!” Me za mu ce ke nan ’yan’uwa? Sa’ad da kuka taru, wani yakan yi waƙa, wani koyarwa, wani wahayi, wani yin magana da wani harshe, wani kuma fassara. Dole ne a yi duka don gina ikkilisiya. In kuwa waɗansu za su yi magana a wani harshe, to, kada su fi mutum biyu ko uku, kuma a yi bi da bi, wani kuma yă fassara. In babu mai fassara, sai mai magana yă yi shiru a cikin ikkilisiya, yă yi wa kansa magana da kuma Allah. Annabawa biyu ko uku za su iya yin magana, sauran kuma sai su auna a hankali abin da aka faɗa. In kuma wahayi ya zo wa wani da yake zaune, sai mai magana na farko yă yi shiru. Dukanku kuna iya yin annabci bi da bi, domin kowa yă sami koyarwa da ƙarfafawa. Ruhohin annabawa kuwa suna ƙarƙashin sarrafawar annabawa. Gama Allah, ba Allah mai sa rikicewa ba ne, sai dai mai salama. Kamar yadda yake a dukan ikkilisiyoyi na tsarkaka. Ya kamata mata su zauna shiru a cikin ikkilisiyoyi. Ba su da izinin yin magana, sai dai su yi biyayya yadda Doka ta faɗi. In suna so su yi tambaya game da wani abu, ya kamata su tambayi mazansu a gida, domin abin kunya ne mace tă yi magana a cikin ikkilisiya. Shin, a kanku ne maganar Allah ta fara? Ko kuma a gare ku ne kaɗai ta iso? In wani yana tsammani shi annabi ne, ko yana da baiwar ruhaniya, bari yă gane cewa abin da nake rubuta muku umarnin Ubangiji ne. In ya ƙi kula da wannan, shi ma sai a ƙi kula da shi. Saboda haka ’yan’uwana, ku yi marmarin yin annabci, kada kuma ku hana magana da harsuna. Sai dai a yi kome daidai da kuma cikin tsari. To, ’yan’uwa, ina so in tuna muku da bisharar da na yi muku wa’azinta, wadda kuka karɓa, wadda kuma kuka yanke shawara ku tsaya a kai. Ta wurin wannan bisharar ce kuka sami ceto, muddin kuna riƙe da wa’azin da na yi muku kam-kam. In ba haka ba, kun gaskata a banza ke nan. Gama abu farko mafi muhimmancin da na karɓo shi ne na ba ku cewa Kiristi ya mutu domin zunubanmu bisa ga Nassi, cewa an binne shi an kuma tashe shi a rana ta uku bisa ga Nassi, cewa ya bayyana ga Bitrus, sa’an nan ga Sha Biyun. Bayan haka, ya bayyana ga fiye da ɗari biyar daga cikin ’yan’uwa a lokaci guda. Yawancinsu kuwa suna nan da rai, ko da yake waɗansu sun riga sun yi barci. Sa’an nan ya bayyana ga Yaƙub, sa’an nan ga dukan manzannin, a ƙarshe duka, ya bayyana a gare ni, kamar wanda an haifa a lokacin da bai kamata ba. Gama ni ne mafi ƙanƙanta a cikin manzanni, ban kuma isa a kira ni manzo ba, domin na tsananta wa ikkilisiyar Allah. Amma bisa ga alherin Allah, na zama abin da nake, alherinsa zuwa gare ni kuwa bai zama a banza ba. A’a, na yi aiki fiye da dukansu, duk da haka, ba ni ba ne, sai dai alherin Allah da yake tare da ni ne. To, ko ni ne, ko su ne, wannan shi ne abin da muke wa’azi, shi ne kuma abin da kuka gaskata. Amma in ana wa’azi cewa Kiristi ya tashi daga matattu, yaya waɗansu a cikinku suke cewa babu tashin matattu? In babu tashin matattu, to, ba a tā da Kiristi ma ba ke nan. In ba a tashe Kiristi ba kuwa, ai, wa’azinmu, da bangaskiyarku banza ne. Sai ma ya zama mun zama masu ba da shaidar ƙarya game da Allah ke nan, domin mun shaida game da Allah cewa ya tashe Kiristi daga matattu. Bai tashe Kiristi ba ke nan, in lalle ba a tā da matattu. Gama in ba a tā da matattu ba, to, Kiristi ma ba a tashe shi ba ke nan. In kuwa ba a tashe Kiristi ba, bangaskiyarku a banza take, ya zama har yanzu kuna cikin zunubanku ke nan. Ashe, waɗanda suka yi barci a cikin Kiristi ma sun hallaka ke nan. In a wannan rayuwar ce kaɗai muke da bege cikin Kiristi, mun zama abin tausayi fiye da dukan mutane. Amma tabbatacce, an tā da Kiristi daga matattu, nunan fari kuwa cikin waɗanda suka yi barci. Da yake mutuwa ta zo ta wurin mutum, haka tashin matattu ma ya zo ta wurin mutum. Kamar yadda duka suka mutu cikin Adamu, haka duka za su rayu cikin Kiristi. Sai dai kowa da lokacinsa. Kiristi ne nunan fari; sa’an nan sa’ad da ya dawo; za a tā da waɗanda suke nasa. Sa’an nan sai ƙarshen ta zo, sa’ad da zai miƙa wa Allah Uba mulki, bayan ya hallaka dukan sarauta, mulki da iko. Gama dole yă yi mulki har sai ya sa dukan abokan gābansa a ƙarƙashin ƙafafunsa. Abokin gāba na ƙarshen da za a hallaka kuwa, shi ne mutuwa. Gama ya “sa kome a ƙarƙashin ƙafafunsa.” To, da aka ce an sa “kome” a ƙarƙashinsa, a fili yake cewa ba a haɗa da Allah a ciki ba, shi wannan da ya sa kome a ƙarƙashin Kiristi. Sa’ad da ya yi haka, sa’an nan Ɗan kansa yă koma a ƙarƙashin shi wanda ya sa kome a ƙarƙashinsa, domin Allah yă zama kome da kome. To, in babu tashin matattu, mene ne waɗanda ake musu baftisma saboda matattu za su yi? In ba a tā da matattu sam, me ya sa ake yin wa mutane baftisma saboda su? Mu ma don me muke sa kanmu cikin hatsari a kowace sa’a? Ina fuskantar mutuwa kowace rana. I, kamar yadda yake tabbatacce cewa ina taƙama da ku cikin Kiristi Yesu Ubangijinmu. In na yi kokawa da mugayen namomin jeji a Afisa bisa ga ra’ayin mutane ne kawai, mece ce ribata, in har ba a tā da matattu? Ai, “Sai mu ci mu sha, da yake gobe za mu mutu.” Kada fa a ruɗe ku, “Ajiyar mugayen abokai yana ɓata hali mai kyau.” Ku koma cikin hankalinku yadda ya kamata, ku kuma daina yin zunubi, gama akwai waɗansu da ba su san Allah ba, na faɗi wannan ne don ku kunyata. Amma wani yana iya tambaya yă ce, “Ta yaya ake tā da matattun? Da wane irin jiki za su tashi?” Kai, marar azanci! Abin da kuka shuka ba zai tsira ba sai ya mutu. Sa’ad da kuke shuki, ba tsiron da zai yi girma ba ne kuka shuka, ƙwayar ce kawai, ko ta alkama ko kuma na wani irin dabam. Amma Allah yakan ba ƙwayar jiki yadda ya yi niyya, kuma ga kowane irin ƙwaya yakan ba ta irin jikinta. Ba dukan nama ne iri ɗaya ba. Mutane da irin nasu, dabbobi da irin nasu, tsuntsaye da irin nasu, kifaye kuma da irin nasu. Akwai jikuna iri na samaniya, akwai kuma jikuna iri na duniya; sai dai darajar jikunan samaniya dabam take, darajar jikunan duniya kuma dabam take. Rana tana da wata irin daraja, wata yana da wata darajar dabam, taurari kuma suna da tasu dabam. Wani tauraro kuwa yakan bambanta da wani a wajen daraja. Haka ne tashin matattu zai kasance. Abin da aka shuka yakan ruɓe, abin da aka tā da shi kuma ba ya ruɓewa; akan shuka shi cikin ƙasƙanci, a kuma tā da shi cikin ɗaukaka, akan shuka shi da rashin ƙarfi, a kuma tā da shi da ƙarfi; akan shuka shi da jiki na mutuntaka, a kuma tā da shi da jikin ruhaniya. In akwai jiki na mutuntaka, to, lalle akwai jikin ruhaniya ma. Haka yake a rubuce cewa, “Adamu, mutumin farko ya zama mai rai”; Adamu na ƙarshe kuwa ruhu ne mai ba da rai. Ba jikin ruhaniya ne ya zo da farko ba, na mutuntakan ne, daga baya kuma sai na ruhaniya. Mutumin farko daga turɓaya ce ya fito, mutum na biyu kuwa daga sama ne ya fito. Kamar yadda mutumin turɓaya yake, haka ma waɗanda suke na turɓaya. Kuma kamar yadda mutumin sama yake, haka ma waɗanda suke na sama. Kamar dai yadda muka ɗauki siffar mutumin turɓaya, haka kuma za mu ɗauki siffar mutumin sama. Ina sanar da ku, ’yan’uwa, cewa nama da jini ba za su gāji mulkin Allah ba, haka ma ruɓa ba zai gāji rashin ruɓa ba. Ku saurara, in gaya muku wani asiri. Ba dukanmu ne za mu yi barci ba, sai dai duk za a sauya kamanninmu farat ɗaya, cikin ƙyaftawar ido, da busan ƙaho na ƙarshe. Gama za a busa ƙaho, za a tā da matattu da jiki irin da ba ya ruɓewa, za a kuma sauya kamanninmu. Gama dole mai ruɓa yă maye wa mai ruɓan nan, marar mutuwa kuma yă maye wa mai mutuwan nan. Sa’ad da mai ruɓan nan ya maye marar ruɓan nan, mai mutuwa kuma ya maye marar mutuwan nan, sa’an nan ne karin maganar da yake a rubuce zai zama gaskiya cewa, “An haɗiye mutuwa cikin nasara.” “Ya ke mutuwa, ina nasararki? Ya ke mutuwa, ina dafinki?” Zunubi ne yake ba wa mutuwa dafi, Doka kuma take ba wa zunubi iko. Amma godiya ga Allah! Shi ne ya ba mu nasara ta wurin Ubangijinmu Yesu Kiristi. Saboda haka, ƙaunatattu ’yan’uwana, ku tsaya da daram. Kada wani abu yă jijjiga ku. Ku ba da kanku kullum ga aikin Ubangiji, domin kun san cewa famar da kuke yi saboda Ubangiji ba a banza take ba. To, game da tara kuɗi domin taimakon mutanen Allah, ku yi abin da na gaya wa ikkilisiyoyin Galatiyawa. A ranar farko ta kowace mako, ya kamata kowannenku yă keɓe ’yan kuɗi bisa ga abin da yake samu, yă ajiye, ba sai na zo kafin a tara taimakon ba. In kuwa na iso sai in ba da wasiƙun gabatarwa ga mutanen da kuka amince da su, in kuma aike su da taimakonku zuwa Urushalima. In kuma ya dace in tafi, to, sai su tafi tare da ni. Bayan na zazzaga Makidoniya, zan zo wurinku, domin zan ratsa ta Makidoniya. Wataƙila zan ɗan jima a wajenku, ko ma in ci damina a can, domin ku yi mini rakiya a tafiyata, duk inda za ni. Ba na so in gan ku yanzu in wuce kawai, ina fata zan yi ’yan kwanaki tare da ku, in Ubangiji ya yarda. Sai dai zan kasance a Afisa har lokacin Fentekos, domin an buɗe mini wata hanya mai fāɗi don aiki mai amfani, ko da yake akwai mutane da yawa masu gāba da ni. In Timoti ya zo, ku tabbata ya sami sakewa a cikinku, domin aikin Ubangiji yake yi kamar yadda nake yi. Kada fa wani yă ƙi karɓansa. Ku sallame shi lafiya, domin yă koma wurina. Ina duban hanyarsa tare da ’yan’uwa. Batun ɗan’uwanmu Afollos kuwa, na roƙe shi sosai yă zo wurinku tare da ’yan’uwa. Bai so zuwa yanzu ba, amma zai zo in ya sami zarafi. Ku zauna a faɗake; ku dāge cikin bangaskiya; ku zauna da ƙarfafawa; ku yi ƙarfi. Ku yi kome da ƙauna. Kun san cewa iyalin gidan Istifanas ne suka fara tuba a Akayya. Sun kuma ba da kansu ga yi wa tsarkaka hidima. Ina roƙonku ’yan’uwa, ku ba da kanku ga irin waɗannan, ga kuma kowa da ya haɗa hannu a aikin, yana kuma faman a cikinsa. Na yi farin ciki da isowar Istifanas, Fortunatus da Akaikus, domin sun biya bukatar da ba ku iya biya ba. Gama sun wartsake ruhuna da kuma naku. Ya kamata ku girmama irin waɗannan mutane. Ikkilisiyoyin da suke a lardin Asiya suna gaisuwa. Akwila da Firiskila suna gaishe ku sosai cikin Ubangiji, haka ma ikkilisiyar da takan taru a gidansu. Dukan ’yan’uwa a nan suna gaisuwa. Ku gai da juna da sumba mai tsarki. Ni, Bulus nake rubuta wannan gaisuwa da hannuna. Duk wanda ba ya ƙaunar Ubangiji, la’ana ta zauna a kansa. Zo, ya Ubangiji! Alherin Ubangiji Yesu yă kasance tare da ku. Ina gaishe ku duka, gaisuwar ƙaunata cikin Kiristi Yesu. Amin. Bulus, manzon Kiristi Yesu ta wurin nufin Allah, da kuma daga Timoti ɗan’uwanmu, Zuwa ga ikkilisiyar Allah da take a Korint, tare da dukan tsarkaka a ko’ina a Akayya. Alheri da salama daga Allah Ubanmu da kuma Ubangiji Yesu Kiristi, su kasance tare da ku. Yabo ya tabbata ga Allah, da Uban Ubangijinmu Yesu Kiristi, Uba mai tausayi, da kuma Allah na dukan ta’aziyya, wanda yakan yi mana ta’aziyya a cikin dukan wahalolinmu, domin mu kuma mu iya ta’azantar da waɗanda suke cikin kowace irin wahala, da ta’aziyyar da mu kanmu muka samu daga Allah. Gama kamar yadda wahalar Kiristi ta cika har tana zuba a cikin rayuwarmu, haka nan kuma ta wurin Kiristi ta’aziyyarmu ta cika har tana zuba. In muna shan wahala, ai, muna shanta domin ta’aziyyarku, da cetonku ne, in mun sami ta’aziyya, ai, mun same ta domin ta’aziyyarku ce, wadda take sa ku jure wa irin wahalan nan, da muke sha. Begen da muke da shi dominku kuwa, tabbatacce ne, domin mun san cewa kamar yadda kuke tarayya da mu a cikin wahalolinmu, haka kuma kuke tarayya da mu a cikin ta’aziyyarmu. ’Yan’uwa, ba ma so ku zama da rashin sani, a kan wahalolin da muka sha a lardin Asiya. Mun sha wahaloli sosai, har abin ya fi ƙarfinmu, ya sa muka fid da tsammanin rayuwa. Ba shakka, a zuciyarmu mun ji kamar hukuncin kisa ne aka yi mana. Wannan kuwa ya faru ne domin kada mu dogara da kanmu, sai dai ga Allah, wanda yake tā da matattu. Shi ya cece mu daga irin wannan hatsari na mutuwa, zai kuwa cece mu. A kansa muka kafa bege cewa zai ci gaba da cetonmu, yayinda kuke taimakonmu ta wurin addu’o’inku. Mutane da yawa kuwa za su yi godiya ta dalilinmu, saboda albarkar da aka yi mana, ta amsa addu’o’i masu yawa. Wannan shi ne taƙamarmu. Lamirinmu yana ba da shaida cewa mun yi zamanmu a duniya, musamman a dangantakarmu da ku cikin tsarki, tsakani da Allah. Mun yi haka ta wurin bishewar alherin Allah, ba bisa ga hikimar duniya ba. Gama ba mu rubuta muku abin da ba za ku iya karatu ko ku kāsa fahimta ba. Ina kuma fata cewa, kamar yadda kuka ɗan fahimce mu, za ku kai ga cikakkiyar fahimta cewa za ku iya yin taƙama da mu, kamar yadda mu ma za mu yi taƙama da ku a ranar da Ubangiji Yesu zai dawo. Saboda na amince da haka, shi ya sa na so zuwa wurinku da fari, domin ku sami albarka riɓi biyu. Na yi shiri in ziyarce ku a kan hanyata zuwa Makidoniya, in kuma sāke dawo wurinku a kan hanyata daga Makidoniya, sa’an nan ku yi mini rakiya a hanyata zuwa Yahudiya. Kuna gani na yi wannan shirin ba da sanin abin da nake yi ba ne? Ko kuwa, kuna gani na yi shirin nan da halin mutuntaka ne, don in ce, “I” in koma in ce, “A’a”? Kamar dai yadda ba shakka Allah yake mai aminci, haka ma maganar da muka yi muku, ba “I” da kuma “A’a” ba ce. Gama Ɗan Allah, Yesu Kiristi, wanda ni da Sila da Timoti muka yi muku wa’azinsa, ai, ba “I” da “A’a” ba ne, amma a cikin Kiristi, “I” ne kullum. Domin dukan alkawaran Allah cikarsu a gare shi suke, ta wurinsa ne kuma muke faɗar “Amin”, domin a ɗaukaka Allah. Allah ne fa yake sa mu da ku mu tsaya daram cikin Kiristi. Shi ne ya shafe mu, ya buga mana hatiminsa a kan mu nasa ne, ya kuma sa mana Ruhunsa a cikin zukatanmu, domin yă tabbatar da abin da yake zuwa nan gaba. Labudda, Allah shi ne shaidata cewa don kada in ƙara muku wahala ne ya sa ban koma Korint ba. Ba nuna muku iko a kan bangaskiyarku muke yi ba, sai dai muna aiki tare da ku ne saboda farin cikinku, domin bisa ga bangaskiya ce kuke tsaye da ƙarfi. Saboda haka na yanke shawara ba zan sāke kawo muku ziyara ta ɓacin rai ba. Gama in na sa ku baƙin ciki, wa ya rage yă faranta mini zuciya, in ba ku waɗanda na sa baƙin cikin ba? Na rubuta yadda na yi ne saboda sa’ad da na iso kada waɗanda ya kamata su faranta mini rai, su sa ni baƙin ciki. Na amince da ku duka a kan farin cikina naku ne ku duka. Gama na rubuta muku ne cikin baƙin ciki mai yawa da ɓacin zuciya har ma da hawaye mai yawa, ba don in sa ku baƙin ciki ba ne, a’a, sai dai domin in nuna muku zurfin ƙaunar da nake yi muku. In wani ya jawo baƙin ciki, ba ni kaɗai ya jawo wa ba, amma a wani fanni, sai in ce dukanku ne ya jawo wa, ba na faɗa haka don in matsa muku lamba ba ne. Irin wannan mutum, horon da yawancin mutane suka yi masa ya isa haka. Yanzu fa, a maimako, gara ku yafe masa, ku kuma ta’azantar da shi, don kada baƙin ciki mai yawa yă sha kansa. Saboda haka, ina roƙonku, ku sāke nuna masa ƙaunarku. Abin da ya sa na rubuta muku shi ne don in ga ko za ku jimre da gwajin nan, kuna kuma yin biyayya ta kowace hanya. In kuka gafarta wa wani, ni ma na gafarta masa. Abin da na gafarta kuwa, in har ma da abin gafartawa, saboda ku ne na gafarta masa, albarkacin Kiristi, don kada Shaiɗan yă rinjaye mu. Da yake muna sane da dabarunsa. To, sa’ad da na tafi Toruwas don in yi wa’azin bisharar Kiristi, ko da yake na tarar cewa Ubangiji ya buɗe mini ƙofa, duk da haka, ban sami salama a zuciyata ba domin ban sami ɗan’uwana Titus a can ba. Sai na yi bankwana da su na wuce zuwa Makidoniya. Amma godiya ga Allah, wanda kullum yake bi da mu da nasara cikin Kiristi, kuma ta wurinmu, yana baza ƙanshin nan na sanin Kiristi a ko’ina. Don kuwa, a wurin Allah mu ƙanshin Kiristi ne cikin waɗanda ake ceto, da kuma waɗanda suke hanyar hallaka. Ga wani, mu warin mutuwa ne, amma ga wani kuwa, mu ƙanshin rai ne. Wa ya isa yă yi irin wannan aikin? Ba ma tallar maganar Allah don riba yadda waɗansu mutane da yawa suke yi. A maimakon haka, muna magana cikin Kiristi a gaban Allah da gaskiya, kamar mutanen da aka aika daga Allah. Yabon kanmu ne kuma muka fara yi? Ko kuwa muna bukatar wasiƙun yabo ne zuwa gare ku, ko daga gare ku, kamar yadda waɗansu suke yi? Ai, ku kanku ku ne wasiƙarmu, wadda aka rubuta a zukatanku, domin kowa yă santa, yă kuma karanta ta. Kun nuna cewa ku wasiƙa ce daga Kiristi, sakamakon hidimarmu, ba wadda aka rubuta da inki ba, sai dai da Ruhun Allah mai rai. Ba kuma a kan allunan dutse ba, sai dai a kan allunan zukatan mutane. Amincewa kamar wannan shi ne namu ta wurin Kiristi a gaban Allah. Ba mu da wani abin da za mu nuna cewa da iyawarmu ne muke aikin nan. Iyawarmu daga wurin Allah ne. Shi ya sa muka gwaninta a matsayinmu na masu hidimar sabon alkawari ba ta rubutacciyar Dokar ba, amma ta Ruhu; don Dokar, kisa take yi, Ruhu kuwa yana ba da rai. To, in hidimar da ta kawo mutuwa, wadda an rubuta a kan allon dutse, ta zo da ɗaukaka har Isra’ilawa suka kāsa duban fuskar Musa saboda tsananin haskenta, ko da yake mai shuɗewa ce, ashe, hidimar Ruhu ba za tă fi wannan ɗaukaka ba? In hidimar da take jawo wa mutane hukunci tana da ɗaukaka haka, to, lalle, hidimar da take kawo adalci za tă fi ta ɗaukaka nesa! Gama abin da dā take da ɗaukaka, ba ta da ɗaukaka a yanzu, in aka kwatantata da mafificiyar ɗaukaka ta yanzu. In kuma aba mai shuɗewa ta zo da ɗaukaka, ashe, abin da yake dawwammame, lalle ne yă kasance da ɗaukakar da ta fi haka nesa! Da yake muna da bege irin wannan, to, muna da ƙarfin zuciya sosai ke nan. Mu ba kamar Musa ba ne, wanda ya rufe fuskarsa da lulluɓi, don kada Isra’ilawa su ga ƙarewar ɗaukakan nan mai shuɗewa. Amma aka sa hankulansu suka dushe, gama har yă zuwa yau akwai lulluɓin nan a duk sa’ad da ake karatun tsohon alkawari. Ba a kawar da shi ba, sai a cikin Kiristi ne kaɗai ake kawar da shi. Har yă zuwa yau, duk sa’ad da ake karatun littattafan Musa, lulluɓin nan yakan rufe zukatansu. Amma duk sa’ad da wani ya juyo ga Ubangiji, akan kawar da lulluɓin. Ubangiji fa, shi ne Ruhu, kuma duk inda Ruhun Ubangiji yake, a nan ’yanci yake. Mu da ba mu da lulluɓi a fuskokinmu duk muna nuna ɗaukakar Ubangiji, ana sauya mu mu ɗauki kamanninsa cikin ɗaukaka mai hauhawa. Ubangiji wanda yake ruhu kuwa shi ne mai zartar da haka. Saboda haka, da yake ta wurin jinƙan Allah ne muke da wannan hidima, ba za mu fid da zuciya ba. Ba ruwanmu da ɓoye-ɓoye na munafuncin da suke abubuwan kunya. Ba ruwanmu da ruɗu, ko yin ƙarya da kalmar Allah. Sai dai muna faɗin gaskiya a fili. Ta haka ne kowa zai yi shaidar gaskiyarmu a gaban Allah cikin zuciyarsa. Ko da bishararmu a rufe take, tana a rufe ne ga waɗanda suke hallaka. Allahn zamanin nan ya makanta hankulan marasa ba da gaskiya, yadda har ba za su iya ganin hasken bishara ta ɗaukakar Kiristi ba, wanda yake kamannin Allah. Gama ba wa’azin kanmu muke yi ba, sai dai na Yesu Kiristi, a kan shi ne Ubangiji, mu kuma bayinku saboda Yesu. Domin shi Allah wanda ya ce, “Bari haske yă haskaka daga duhu,” ya sa haskensa ya haskaka a cikin zukatanmu, don yă ba mu hasken sanin ɗaukakar Allah a fuskar Kiristi. Amma muna da wannan dukiya a cikin tulunan yumɓu, don a nuna wannan mafificin ikon nan daga Allah ne, ba daga gare mu ba. A matse muke a kowane gefe, sai dai ba a gurgunta mu ba. An rikitar da mu, amma ba mu fid da zuciya ba. An tsananta mana, amma ba a yashe mu ba, an fyaɗe mu da ƙasa, amma ba a hallaka mu ba. Kullum muna ɗauke da mutuwar Yesu a jikinmu, domin ran Yesu yă bayyana a jikinmu. Muddin muna a raye, kullum zaman mutuwa muke yi saboda Yesu, don a bayyana ran Yesu ta wurin jikin nan namu mai mutuwa. Ta haka, mutuwa tana aiki a cikinmu, ku kuwa rai a cikinku. A rubuce yake cewa, “Na gaskata; saboda haka na yi magana.” Da wannan ruhun bangaskiya ne mu ma muka gaskata, saboda haka muke magana. Domin mun san cewa shi da ya tā da Ubangiji Yesu daga matattu, zai tashe mu mu ma tare da Kiristi, yă kuma miƙa mu a gabansa tare da ku. Duk wannan fa don amfaninku ne, domin alherin nan da yake bazuwa zuwa ga mutane masu yawa, yă zama dalilin godiya mai yawa ga ɗaukakar Allah. Saboda haka, ba mu fid da zuciya ba. Ko da yake a waje, jikinmu mai mutuwa yana lalacewa, amma can ciki, ana sabunta mu kowace rana. Don wannan ’yar wahalar tamu mai saurin wucewa, ita take tanadar mana madawwamiyar ɗaukaka mai yawa, fiye da kwatanci. Domin ba abubuwan da ido yake gani ne muke dubawa ba, sai dai marasa ganuwa. Gama abubuwan da ake gani masu saurin wucewa ne, marasa ganuwa kuwa, madawwama ne. Yanzu mun san cewa in an hallaka tentin duniyan nan da muke ciki, muna da wani gini daga Allah, madawwamin gida a sama, wanda ba da hannuwan mutum ne suka gina shi ba. Kafin nan muna nishi, da marmari a yi mana sutura da gidanmu na sama, don sa’ad da aka yi mana sutura, ba za a same mu tsirara ba. Sa’ad da muke zaune a cikin jikin nan na duniya, nishi muke domin matsuwar da muke sha, ba domin muna so mu rabu da jikinmu na wannan duniya ba ne, sai dai don so muke yi a suturta mu da na Sama, domin mai rai ya shafe mai mutuwa. Allah ne ya yi mu domin wannan, ya kuma ba mu Ruhu a matsayin abin ajiya, yana kuma tabbatar da abin da zai zo nan gaba. Saboda haka, kullum muna da tabbaci mun kuma san cewa, muddin muna a duniya cikin jikin nan, ana raba mu da Ubangiji. Rayuwa bangaskiya muke, ba ta ganin ido ba. Ina cewa muna da tabbaci, za mu fi so mu rabu da jikin nan, mu kuma kasance a sama tare da Ubangiji. Saboda haka, niyyarmu ita ce, mu gamshe shi, ko muna a duniya cikin jikin nan, ko ba mu nan. Gama dole dukanmu mu bayyana a gaban kujerar shari’ar Kiristi, domin kowannenmu yă karɓi ladan aikin da ya yi a wannan jiki, ko mai kyau ne ko marar kyau. To, da yake mun san ko mene tsoron Ubangiji yake, muna ƙoƙari mu rinjaye mutane. Yadda muke kuwa, yana sane a sarari ga Allah, ina kuma fata yana nan a sarari a lamirinku. Ba ƙoƙari muke mu yabe kanmu a gare ku ba ne, sai dai muna ba ku damar yin taƙama da mu ne, don ku sami amsar da za ku ba wa waɗanda suke taƙama da abin da ake gani ne, a maimakon abin da yake cikin zuciya. In hankalinmu a taɓe yake, ai, saboda Allah ne, in kuwa cikin hankalinmu muke, ai, saboda ku ne. Ƙaunar Kiristi a gare mu, ita take mallakarmu, saboda haka mun tabbata, da yake wani ya mutu saboda dukan mutane, ashe kuwa, mutuwarsu ce dukansu. Ya kuwa mutu ne saboda dukan mutane, domin kada waɗanda suke rayuwa kada su yi zaman ganin dama a nan gaba, sai dai su yi zaman wannan da ya mutu saboda su, aka kuma tashe shi saboda su. Saboda haka, daga yanzu zuwa nan gaba, ba mu ƙara ɗaukan wani mutum bisa ga ganin duniya ba. Ko da yake a dā, mun ɗauki Kiristi haka, amma yanzu mun daina yin haka. Saboda haka, duk wanda yake cikin Kiristi, sabuwar halitta ce, tsohon al’amari ya shuɗe, sabon ya zo! Duk wannan kuwa daga Allah ne, wanda ya sulhunta mu da kansa ta wurin Kiristi, ya kuma ba mu hidimar sulhu, wato, Allah ya sulhunta duniya zuwa kansa ta wurin Kiristi, ba ya lissafta zunuban mutane a kansu. Ya kuma danƙa mana saƙon sulhu. Saboda haka, mu jakadu ne na Kiristi, sai ka ce Allah kansa yake magana ta wurinmu. Muna roƙonku a madadin Kiristi. Ku sulhuntu da Allah. Shi da bai san zunubi ba, Allah ya mai da shi kamar hadayar zunubi saboda mu, domin mu sami adalcin Allah ta wurinsa. A matsayinmu na abokan aikin Allah, muna roƙonku kada ku karɓi alherin Allah a banza. Gama ya ce, “A lokacin samun alherina, na ji ka, a ranar samun ceto kuma, na taimake ka.” Ina gaya muku, yanzu ne lokacin samun alherin Allah, yanzu ne ranar samun ceto. Ba ma sa abin tuntuɓe wa kowa, domin kada hidimarmu ta zama abin zargi. A maimakon haka, duk abin da muke yi, muna yin shi ne don mu nuna cewa mu masu hidimar Allah ne. Muna yin haka cikin jimrewa, da shan wahala, da shan wuya, har da shan masifu. Da shan dūka, da shan dauri, da yawan hargitsi, da yawan fama, da rashin barci, da kuma yunwa. Da cikin tsarki, da fahimta, da haƙuri, da kirki, da cikin Ruhu Mai Tsarki, da cikin ƙauna mai gaskiya, da cikin magana mai gaskiya, da kuma cikin ikon Allah. Muna riƙe da makaman adalci dama da hagu, ta wurin ɗaukaka da ƙasƙanci, da cikin ɓata suna, da kuma cikin yabo. Cikin faɗin gaskiya, an ɗauke mu masu ƙarya, mu sanannu ne, duk da haka an ɗauke mu kamar ba a san mu ba, muna mutuwa, duk da haka a raye muke, an ba mu horo, duk da haka ba a kashe mu ba, cikin baƙin ciki, duk da haka kullum cikin murna muke. Cikin matalauta, duk da haka muna azurtar da mutane da yawa. Ba mu da kome, alhali kuwa kome namu ne. Ya ku Korintiyawa, mun yi muku magana a sake, muka kuma saki zuciya da ku ƙwarai. Ba mu ƙi nuna muku ƙaunarmu ba, sai dai ku kuka ƙi nuna mana. A wannan zance kam, ina magana da ku kamar ’ya’yana, ku ma ku saki zuciya da mu. Kada ku haɗa kai da marasa bi. Gama me ya haɗa adalci da mugunta? Ko kuwa me ya haɗa haske da duhu? Wace daidaituwa ce tsakanin Kiristi da Iblis? Me ya haɗa mai bi da marar bi? Wane alkawari ne tsakanin haikalin Allah da na gumaka? Gama mu haikalin Allah mai rai ne. Kamar yadda Allah ya ce, “Zan zauna tare da su, in yi tafiya a cikinsu, zan zama Allahnsu, su kuma za su zama mutanena.” Saboda haka, “Sai ku fito daga cikinsu, ku keɓe kanku, in ji Ubangiji. Kada ku taɓa wani abu marar tsabta, zan kuma karɓe ku.” Kuma, “Zan zama Uba a gare ku, ku kuma za ku zama ’ya’yana, maza da mata, in ji Ubangiji Maɗaukaki.” Da yake muna da waɗannan alkawura, ya ku ƙaunatattu, sai mu tsarkake kanmu daga kowane abu da yake ƙazantar da jiki, da ruhu, mu zama da cikakken tsarki, saboda bangirma ga Allah. Ku saki zuciya da mu. Ba mu yi wa kowa laifi ba, ba mu ɓata kowa ba, ba mu cuci kowa ba. Ba na faɗin wannan don in sa muku laifi. Na riga na gaya muku yadda muke ƙaunarku ƙwarai cikin zukatanmu, har babu abin da zai iya raba ku da ƙaunarmu, ko a mutuwa ko a rayuwa. Na amince da ku gaya, ina kuma taƙama da ku ƙwarai. Na ƙarfafa sosai. Duk da wahalce wahalcenmu dai ina farin ciki ƙwarai da gaske. Gama sa’ad da muka zo Makidoniya, jikin nan namu bai sami hutu ba, sai ma aka matsa mana a ta kowane gefe, a waje ga rikici, a zukatanmu kuma ga tsoro. Amma Allah, wanda yakan yi wa masu ɓacin rai ta’aziyya ya yi mana ta’aziyya da zuwan Titus, ba ma don zuwansa kaɗai ba, har ma a game da ƙarfafa zuciyan nan da ya samu a wurinku. Ya gaya mana yadda kuke so ku gan ni sosai, da kuma yadda kuka yi baƙin ciki game da abin da ya faru, da niyyar da kuka yi na goyon bayana. Wannan ne ya sa na ji daɗi ƙwarai. Ko da na ɓata muku rai ta wurin wasiƙata, ba na baƙin ciki da haka. Ko da yake dā kam na yi baƙin ciki, don na lura wasiƙata ta ɓata muku rai, amma na ɗan lokaci ne kawai. Duk da haka, yanzu ina farin ciki, ba don na sa ku baƙin ciki ba, sai dai domin baƙin cikinku ya kai ku ga tuba. Gama kun yi baƙin ciki kamar yadda Allah ya so, saboda haka, ba ku yi hasarar kome a sanadinmu ba. Baƙin ciki irin na tsoron Allah yana kai ga tuban da yake kawo ceto, ba ya kuma kawo baƙin ciki, amma baƙin ciki irin na duniya yakan kawo mutuwa. Ku dubi abin da wannan baƙin ciki irin na tsoron Allah ya kawo muku mana, ya sa ku marmarin aikatawa, da nuna cewa kun yi kuskure, ya sa kuka yi fushi, kuka kuma ji tsoro, ya sa kuka sa zuciya, kuka kuma sa aniya, ya sa kuna a shirye ku ga an yi horon da ya dace. Game da wannan sha’ani kam, lalle ta kowace hanya kun nuna cewa ba ku da laifi. To, ko da yake na rubuta muku, ba musamman a kan wanda ya yi laifin ba ne, ba kuwa a kan wanda aka cutar ba, sai dai domin a bayyana muku a gaban Allah tsananin kula da kuke yi mana. Ta wurin wannan duka, muka sami ƙarfafawa. Ban da ƙarfafawar da muka samu, mun ji daɗi ƙwarai saboda yadda muka ga farin cikin Titus, domin ruhunsa ya sami wartsakewa daga gare ku duka. Na yi taƙama da ku a wurinsa, ba ku kuwa ba ni kunya ba. Kamar dai yadda dukan abin da muka gaya muku gaskiya ne, haka ma taƙamarmu a kanku a gaban Titus ya zama gaskiya. Ƙaunar da yake yi muku ya ƙaru ƙwarai, duk sa’ad da yake tunawa da biyayyarku duka, da kuma irin yawan bangirman da kuka nuna masa lokacin da kuka karɓe shi. Ina farin ciki ne don na amince da ku ƙwarai da gaske. To, ’yan’uwa, muna so ku san abin da alherin Allah ya ba wa ikkilisiyoyin Makidoniya. Gama sun sha wuya sosai saboda tsananin wahalar da suka shiga, har yawan farin cikinsu ya kai su ga yin alheri ta bayarwa ga waɗansu, ko da yake suna cikin tsananin talauci. Gama ina shaida cewa sun bayar daidai gwargwadon iyawarsu, har ma fiye da ƙarfinsu. Su kansu, sun roƙe mu sosai don su sami damar yin bayarwa a wannan hidima ga tsarkaka. Ba su yi yadda muka za tă ba, sai ma suka fara ba da kansu ga Ubangiji, sa’an nan sai suka ba da kansu gare mu bisa ga nufin Allah. Ganin haka sai muka roƙi Titus, da yake shi ne ya riga ya tsiro da wannan aikin alheri a cikinku, sai yă ƙarasa shi. To, da yake kun fiffita a kowane abu cikin bangaskiya, cikin magana, cikin sani, cikin dukan ƙwazo, da kuma cikin ƙaunarku dominmu, sai ku fiffita a wannan aikin alheri ma. Ba umarni nake ba ku ba, sai dai ina so in gwada gaskiyar ƙaunarku ne, ta wurin kwatanta ta da aniyar waɗansu. Gama kun san alherin Ubangijinmu Yesu Kiristi cewa ko da yake shi mawadaci ne, duk da haka, ya zama matalauci saboda ku, domin ta wurin talaucinsa, ku zama mawadata. Ga shawarata a kan abin da ya fi muku kyau a wannan al’amari. Bara ku kuka fara bayarwa, kuka kuma zama na farko wajen niyyar yin haka. Yanzu sai ku ƙarasa aikin da irin niyyar da kuka fara, ku yi haka gwargwadon ƙarfinku. Gama in da niyyar bayarwa, za a karɓi bayarwa bisa ga abin da mutum yake da shi, ba bisa ga abin da ba shi da shi ba. Ba nufi nake yi a sawwaƙe wa waɗansu, ku kuwa a jibga muku nauyin ba. Amma ya yi kyau dai a raba daidai wa daida, sai ku taimake su a yanzu da yalwarku saboda rashinsu. Wata rana su ma su taimake ku da yalwarsu saboda rashinku, don a daidaita al’amari, kamar yadda yake a rubuce cewa, “Wanda ya tara da yawa, bai tara fiye da bukatarsa ba, wanda kuma ya tara kaɗan, bai kāsa masa ba.” Ina gode wa Allah, wanda ya sa a zuciyar Titus, irin kula da nake da shi dominku. Ba kawai ya yarda yă je wurinku kamar yadda muka roƙe shi yă yi ba, amma ya so yă zo kamar yadda ya riga ya yi niyya. Ga shi mun aiko ɗan’uwanmu nan tare da shi, wanda ikkilisiyoyi duka suna yabo saboda hidimarsa ga bishara. Ba kuwa haka kaɗai ba, har ma ikkilisiyoyi sun zaɓe shi yă riƙa tafiya tare da mu kan wannan aikin alheri da muke yi saboda ɗaukakar Ubangiji, da kuma nuna kyakkyawar niyyarmu. Muna gudu kada wani yă zarge mu, a kan yadda muke gudanar da wannan kyautar da aka bayar hannu sake. Gama muna iya ƙoƙari mu yi abin da yake daidai, ba a gaban Ubangiji kaɗai ba, amma a gaban mutane ma. Ban da wannan kuma, mun aiko da ɗan’uwanmu tare da su, wanda ya sha tabbatar mana da ƙwazonsa ta hanyoyi iri-iri, musamman yanzu, domin ya amince da ku da gaske. Game da Titus kuma, shi abokin tarayyata ne, da kuma abokin aikina a cikinku; game da ’yan’uwanmu kuwa, su wakilai ne na ikkilisiyoyi, kuma su masu ɗaukaka Kiristi ne. Saboda haka, ku nuna wa waɗannan mutane shaidar ƙaunarku, da kuma dalilin taƙamarmu da ku, domin ikkilisiyoyi su gani. Babu wata bukata in rubuta muku game da hidiman nan ga tsarkaka. Gama na san aniyarku na yin taimako, ina kuma taƙama a kan wannan ga Makidoniyawa, ina faɗin musu cewa tun bara, ku da kuke a Akayya a shirye kuke ku bayar. Ƙoƙarinku kuwa ya zuga yawancinsu ga aiki. Amma ina aika ’yan’uwan nan don kada taƙamar da muke yi da ku, a kan wannan al’amari ta zama a banza, sai dai domin yă zama kuna nan a shirye, kamar yadda na faɗa za ku kasance. Gama in waɗansu mutanen Makidoniya sun zo tare da ni, suka tarar ba a shirye kuke ba, kunya ta ishe mu, balle fa ku, saboda amincewa da muke yi da ku. Saboda haka, na ga ya dace in roƙi ’yan’uwan nan su ziyarce ku kafin lokacin, su kuma gama shirye-shirye saboda bayarwa ta yardar ran da kuka yi alkawari. Ta haka bayarwar za tă zama a shirye, ta yardar rai ba ta dole ba. Ku tuna fa, duk wanda ya yi shuki kaɗan zai girbe kaɗan, kuma duk wanda ya yi shuki da yawa, zai girbe a yalwace. Ya kamata kowa yă bayar bisa ga abin da ya yi shawara a zuciyarsa, ba tare da jin nauyi ko don dole ba, gama Allah yana son mai bayarwa da daɗin rai. Allah kuwa yana da iko yă ba ku fiye da bukatarku, domin kullum ku wadata da kome ta kowace hanya, kuna ta bayarwa hannu sake, kowane irin kyakkyawan aiki. Kamar yadda yake a rubuce cewa, “Ya ba gajiyayyu hannu sake, ayyukansa na alheri madawwama ne.” To, shi da yake ba mai shuka iri, yake kuma ba da abinci a ci, shi ne zai ba ku irin shukawa, yă riɓanya shi, yă kuma albarkaci ayyukanku na alheri da yawa. Za a wadatar da ku ta kowace hanya, domin ku riƙa bayarwa hannu sake a kowane lokaci. Ta wurinmu kuma bayarwarku hannu sake za tă zama sanadin godiya ga Allah. Wannan hidimar da kuke yi, ba bukatun mutanen Allah kaɗai take biya ba, amma tana cike da hanyoyin nuna godiya masu yawa ga Allah. Aikin nan naku na alheri tabbatar bangaskiyarku ne, za a kuwa ɗaukaka Allah saboda kun bayyana yarda, cewa kun yi na’am da bisharar Kiristi, saboda kuma gudummawa da kuka yi musu da saura duka, hannu sake. A cikin addu’arsu dominku kuwa, zukatansu za su koma gare ku, saboda mafificin alherin da Allah ya ba ku. Godiya ga Allah, saboda kyautarsa da ta wuce misali! Ni Bulus da kaina, ina roƙonku albarkacin tawali’u da sanyin hali na Kiristi, ni da ake yi wa kirari “marar tsanani” a cikinku, amma “mai matsawa” sa’ad da nake rabe da ku! Ina roƙonku cewa sa’ad da na zo kada ku tilasta ni in matsa muku, gama na tabbata zan iya tsaya wa waɗanda suka ce abin da muke yi sha’anin duniya ne. Ko da yake muna cikin duniya, ba ma yaƙi kamar yadda duniya take yi. Makaman da muke yaƙi da su, ba makamai na duniya ba ne. Sai dai na ikon Allah ne, masu rushe wuraren mafaka masu ƙarfi. Muna ka da masu gardama da kowane tunanin ɗaga kai da yake kafa kansa gāba da sanin Allah, muna kuma jan hankalin kowa ga bautar Kiristi. A shirye muke mu hori kowane rashin biyayya, sa’ad da biyayyarku ta cika. Kuna duban abubuwa bisa-bisa ne kawai. In wani ya ganin cewa shi na Kiristi ne, ya kamata yă sāke lura cewa kamar yadda yake na Kiristi, haka mu ma muke. Ko da zan yi gadara fiye da kima a game da izinin nan namu, wanda Ubangiji ya bayar saboda inganta ku, ba don rushe ku ba, ba ni da abin jin kunya a ciki. Ba na so yă zama kamar ina ƙoƙari in tsorata ku ne da wasiƙuna. Gama waɗansu suna cewa, “Wasiƙunsa suna da nauyi da kuma ƙarfi, amma kuwa in ka gan shi, ba shi da wani kwarjini, maganarsa kuma ba kome ba ce.” Ya kamata irin waɗannan mutane su gane cewa abin da muke faɗa a cikin wasiƙunmu sa’ad da ba ma nan tare da ku, shi muke aikatawa sa’ad da muke nan. Ba za mu yi ƙarfin halin lissafta kanmu, ko mu kwatanta kanmu da waɗansu masu yabon kansu ba. Sa’ad da suke gwada kansu da kansu, da kuma kwatanta kansu da kansu, ba su da hikima. Amma mu kam, ba za mu yi taƙama mu zarce iyakarmu ba, sai dai za mu yi taƙama cikin filin da Allah ya ƙayyade mana, filin kuwa ya kai har zuwa wurinku. Ba mu wuce gona da iri a taƙamarmu ba, kamar yadda zai zama, da a ce ba mu zo wurinku ba, gama mun kai har wurinku da bisharar Kiristi. Fahariyarmu ba fiye da yadda ya kamata take ba, ba tă kuma shafi aikin waɗansu ba. Sai dai muna sa zuciya bangaskiyarku ta riƙa ƙaruwa, ta haka kuma fagen aikinmu a cikinku yă riƙa ƙaruwa ƙwarai da gaske. Saboda mu iya yin wa’azin bishara a yankunan da suke gaba da ku. Gama ba ma so mu yi taƙama game da aikin da aka riga aka yi a sashen wani. Amma, “Duk mai yin taƙama, sai ya yi taƙama da Ubangiji.” Ai, ba mai yabon kansa ake amincewa da shi ba, sai dai wanda Ubangiji ya yaba wa. Ina fata za ku yi haƙuri da ’yar wautata. Amma, ai, kun riga kun yi haƙuri. Ina kishinku da kishi irin na Allah. Na yi muku alkawarin aure ga miji ɗaya, Kiristi, domin in miƙa ku a gare shi kamar budurwa zalla. Sai dai ina tsoro kada yă zama, kamar yadda maciji ya yaudari Hawwa’u da makircinsa, ku ma a bauɗar da hankalinku daga sahihiyar biyayya amintacciya ga Kiristi. Gama in wani ya zo wurinku yana wa’azin wani Yesu dabam da wanda muka yi wa’azinsa, ko kuma in kun karɓi wani ruhu dabam da wanda kuka karɓa, ko wata bishara dabam da wadda kuka karɓa, ya nuna kun yarda da su ke nan cikin sauƙinkai. Amma a ganina waɗancan da kuke ce da su “manyan manzanni” ba su fi ni da wani abu ba. Mai yiwuwa ni ba horarre ba ne a magana, amma ina da sani. Mun kuwa bayyana muku wannan a sarari, ta kowace hanya. Laifi ke nan ne na yi da na ƙasƙantar da kaina, don a ɗaga ku zuwa babban matsayi ta wurin yin muku wa’azin bisharar Allah kyauta? Na yi wa waɗansu ikkilisiyoyi ƙwace ta wurin karɓar taimako daga wurinsu, domin in yi muku hidima. Sa’ad da nake tare da ku kuma nake zaman rashi, ban nawaita wa kowa ba, gama ’yan’uwan da suka zo daga Makidoniya sun biya bukata. Na kiyaye kaina daga nawaita muku ta kowace hanya, zan kuma ci gaba da yin haka. Ba shakka, kamar yadda gaskiyar Kiristi take a cikina, babu wani a yankunan Akayya da zai iya hana yin taƙaman nan tawa. Don me? Don ba na ƙaunar ku ne? Allah dai ya sani ina ƙaunarku! Zan kuma ci gaba da yin abin da nake yi, domin in toshe kafar mutanen nan da suke fariya, suna nema mu daidaita da su. Gama irin waɗannan mutane manzannin ƙarya ne, ma’aikata ne masu ruɗi, sun ɓad da kamanni kamar su manzannin Kiristi ne. Ba abin mamaki ba ne, gama Shaiɗan kansa ma yana ɓad da kamanni kamar shi mala’ikan haske ne. Don haka, ba abin mamaki ba ne, in bayin Shaiɗan sun ɓad da kamanni kamar su bayin adalci ne. A ƙarshe, za a sāka musu gwargwadon ayyukansu. Ina sāke faɗa, kada wani yă ɗauka ni wawa ne. Amma in kun ɗauke ni haka, to, sai ku karɓe ni kamar yadda kuke karɓan wawa, domin in ɗan in yi taƙama. A wannan taƙamata ba na magana yadda Ubangiji zai yi ba ne, sai dai magana ce irin ta wawa. Da yake mutane da yawa suna taƙama irin ta duniya, ni ma haka zan yi. Ku kam kuna da wayo sosai, har kuna jimre wa wawaye da murna! Gaskiyar ita ce, kuna haƙuri da duk wanda ya sa ku bauta ko ya cuce ku ko ya more ku ko ya nuna muku isa ko kuma ya mare ku a fuska. Ina jin kunya in ce mun nuna kāsawa da ba mu yi waɗannan abubuwan ba! Abin da wani yake da ƙarfin hali yin taƙama a kai, shi ne ni ma nake ƙarfin hali yin taƙama a kai. Ina magana kamar wawa ne. In su Ibraniyawa ne, ni ma haka. In su Isra’ilawa ne, ni ma haka. In su zuriyar Ibrahim ne, ni ma haka. In su bayin Kiristi ne, ni na fi su ma, ina magana kamar ruɗaɗɗe ne fa! Ai, na fi su shan fama ƙwarai da gaske, da shan dauri, na sha dūka marar iyaka, na sha hatsarin mutuwa iri-iri. Sau biyar Yahudawa suka yi mini bulala arba’in ɗaya babu. Sau uku aka bulale ni da bulalar ƙarfe, sau ɗaya aka jajjefe ni da duwatsu, sau uku jirgin ruwa ya ragargaje ina ciki, na kwana na kuma yini ruwan teku yana tafiya da ni. Na yi tafiye-tafiye da yawa, na sha hatsari a koguna, na sha hatsarin ’yan fashi, na sha hatsari a hannun kabilarmu, na sha hatsari a hannun al’ummai, na sha hatsari a birane, na sha hatsari a jeji, na sha hatsari a teku, na kuma sha hatsarin ’yan’uwa na ƙarya. Na yi fama, na shan wuya, ga kuma rashin barci sau da yawa. Na san abin da ake nufin da jin yunwa da ƙishirwa, sau da yawa kuwa na kasance da rashin abinci, na sha sanyi da zaman tsirara. Ban da waɗannan abubuwa, kowace rana ina ɗauke da nauyin kula da dukan ikkilisiyoyi. Wane ne ya rasa ƙarfi, da ban ji shi a jikina ba? Wane ne ya fāɗi cikin zunubi, da ban ji zafin wannan ba? In ma lalle ne in yi taƙama, to, sai in yi taƙama da abubuwan da suka nuna rashin ƙarfina. Allah Uban Ubangiji Yesu Kiristi, wanda yabo ta tabbata a gare shi har abada, ya san cewa ba ƙarya nake yi ba. A Damaskus, gwamnan da yake ƙarƙashin Sarki Aretas, ya sa tsare ƙofofin birnin Damaskus, don yă kama ni. Amma aka saukar da ni cikin kwando ta tagar katanga, na kuɓuce masa. Dole in ci gaba da yin taƙama. Ko da yake ba za tă amfane ni ba, zan yi magana a kan ru’uyoyi da wahayoyi waɗanda na karɓa daga Ubangiji. Na san wani a cikin Kiristi wanda shekaru goma sha huɗu da suka wuce an ɗauke zuwa sama ta uku. Ko a cikin jiki ne, ko kuwa ba a cikin jiki ba, ni dai ban sani ba, Allah ne ya sani. Na kuma san cewa wannan mutum, ko a cikin jiki ne, ko kuma ba a cikin jiki ba, ni dai ban sani ba, amma Allah ne ya sani, an ɗauke shi ne zuwa aljanna. Ya ji waɗansu abubuwa waɗanda ba zai iya faɗarsu da kalmomi ba, abubuwan da ba a ba wa mutum damar faɗi. Zan yi taƙama game da mutum irin wannan, sai dai ni ba zan yi taƙama da kaina ba, sai dai a kan rashin ƙarfina. Ko da zan so yin gadara ma, ba zan zama wawa ba, gama gaskiya zan faɗa. Amma na bar zancen haka, don kada wani ya ɗauke ni fiye da yadda yake ganina, ko yadda yake jin maganata. Don kada in cika da girman kai saboda waɗannan mafifitan manyan wahayoyi, sai aka sa mini wata ƙaya a jikina wadda ta zama ɗan saƙon Shaiɗan, don ta wahalshe ni. Sau uku na roƙi Ubangiji yă raba ni da wannan abu. Amma ya ce mini, “Alherina ya ishe ka, domin a cikin rashin ƙarfi ne ake ganin cikar ikona.” Saboda haka, zan ƙara yin taƙama da farin ciki game da rashin ƙarfina, domin ikon Yesu Kiristi yă zauna tare da ni. Shi ya sa nake murna cikin rashin ƙarfi, da zagi, da shan wahaloli, da tsanantawa, da matsaloli, saboda Kiristi. Don a sa’ad da nake marar ƙarfi a nan ne nake da ƙarfi. Na yi wauta kam, amma ku ne kuke tilasta mini, ku ne kuwa ya kamata ku yaba mini, domin ba inda na kāsa waɗannan mafiffitan manzanni, ko da yake ni ba kome ba ne. Abubuwan da suke tabbatar da manzo, alamu, abubuwa da kuma ayyukan banmamaki, an aikata su a cikinku da matuƙar nacewa. Ta yaya ne darajarku ba tă kai ta sauran ikkilisiyoyi ba, ko kuwa don dai ban nawaita muku ba ne? Ku gafarta mini wannan laifi! Yanzu a shirye nake in ziyarce ku sau na uku, ba zan kuma nawaita muku ba, don ba kayanku nake so ba, ku nake so. Gama ba yara ne da ɗaukar nauyin iyayensu ba, sai dai iyaye ne da ɗaukar nauyin yaran. Don haka ina farin ciki in kashe dukan abin da nake da shi a kanku, har in ba da kaina ma dominku. In na ƙaunace ku fiye da haka, za ku rage ƙaunarku gare ni ne? To, shi ke nan, ban nawaita muku ba. Ashe, sai ku ce dabara na yi muku, na shawo kanku ta hanyar yaudara! Na cuce ku ne ta wurin wani daga cikin waɗanda na aiko a gare ku? Na roƙi Titus ya zo wurinku. Na kuma aiki ɗan’uwanmu tare da shi. Ko Titus ya cuce ku ne? Ba ruhu ɗaya yake bi da mu ba? Ba kuma hanya guda muka bi ba? Ko tun dā can, kuna tsammani muna kāre kanmu a gare ku ne? A gaban Allah muke magana, kamar waɗanda suke cikin Kiristi. Ƙaunatattuna, kome da muke yi, muna yi ne don inganta ku ne. Gama ina tsoro, in na zo, in tarar da ku dabam da yadda nake so, ku ma ku tarar da ni dabam da yadda kuke so. Ina tsoro kada yă zama akwai faɗa, da kishi, da fushi mai zafi, da tsattsaguwa, da ɓata suna, da gulma, da girman kai, da hargitsi. Ina tsoro kada sa’ad da na sāke zuwa, Allahna zai ƙasƙantar da ni a gabanku, kuma in yi baƙin ciki saboda waɗanda suka yi zunubi a dā, ba su kuma tuba daga aikin ƙazanta, da na fasikanci, da kuma lalata da suka sa kansu a ciki ba. Wannan za tă zama ziyarata ta uku a wurinku ke nan. “Dole a tabbatar da kowace magana ta bakin shaidu biyu ko uku.” Na riga na yi muku gargaɗi sa’ad da nake tare da ku a zuwana na biyu. Yanzu da ba na nan tare da ku, ina maimaita irin gargaɗin nan domin in na zo ba wanda zai kuɓuce wa horon nan, da yake kuna neman tabbaci cewa Kiristi yana magana ta wurina ne. To, ai, shi ba rarrauna ba ne a gare ku, amma ƙaƙƙarfa ne a cikinku. Ko da yake tabbatacce an gicciye shi cikin rashin ƙarfi, duk da haka, yana rayuwa bisa ga ikon Allah. Haka mu ma marasa ƙarfi ne a cikinsa, amma ta wurin ikon Allah za mu rayu tare da shi don mu yi muku hidima. Ku gwada kanku ku gani ko kuna cikin bangaskiya; ku auna kanku. Ashe, ba ku san cewa Kiristi Yesu yana cikinku ba? Sai ko in kun fāɗi gwajin. Ina fata za ku gane cewa ba mu fāɗi gwajin ba. Muna addu’a ga Allah kada ku aikata wani laifi. Ba don mutane su gani cewa mun ci gwajin ba ne, a’a, sai dai don ku yi abin da yake daidai, ko da yake zai zama kamar mun fāɗi gwajin ne. Kai, ba dama mu saɓa wa gaskiya, sai dai mu bi bayan gaskiyar. Murna muke sa’ad da ba mu da ƙarfi, ku kuwa kuna da ƙarfi. Addu’armu ita ce, ku zama cikakku. Shi ya sa nake rubuta waɗannan abubuwa, sa’ad da ba na nan tare da ku, domin sa’ad da na zo, kada yă zama mini tilas in yi muku tsanani a game da nuna ikon nan da Ubangiji ya ba ni saboda ingantawa, ba saboda rushewa ba. A ƙarshe ’yan’uwa, sai wata rana. Ku yi ƙoƙari ku zama cikakku. Ku saurari roƙona, ku zama da tunani ɗaya, ku yi zaman salama. Allah na ƙauna da salama kuwa zai kasance tare da ku. Ku gaggai da juna da sumba mai tsarki. Dukan tsarkaka suna gaishe ku. Alherin Ubangiji Yesu Kiristi, da ƙaunar Allah, da zumuntar Ruhu Mai Tsarki su kasance tare da ku duka. Bulus manzo, aikakke ba daga wurin mutum ba, ba kuma ta wurin mutane ba, amma ta wurin Yesu Kiristi da kuma Allah Uba, wanda ya tā da Yesu daga matattu. Dukan ’yan’uwan kuma da suke tare da ni a nan, Suna gai da ikkilisiyoyi a Galatiya. Alheri da salama daga Allah Ubanmu da Ubangiji Yesu Kiristi, su kasance tare da ku. Shi wanda ya ba da kansa saboda zunubanmu don yă cece mu daga wannan mugun zamani na yanzu, bisa ga nufin Allah wanda yake kuma Ubanmu, a gare shi ɗaukaka ta tabbata har abada abadin. Amin. Ina mamaki yadda kuka yi saurin yashe wanda ya kira ku ta wurin alherin Kiristi, kuna juyewa ga wata bishara dabam wadda a gaskiya ba bishara ba ce ko kaɗan. Tabbatacce waɗansu mutane suna birkitar da ku, suna kuma ƙoƙari su karkatar da bisharar Kiristi. Amma ko mu, ko mala’ika daga sama ya yi wa’azin wata bishara dabam da wadda muka yi muku, bari yă zama la’ananne har abada! Kamar yadda muka riga muka faɗa, haka yanzu ma ina ƙara cewa in wani yana muku wa’azin wata bishara dabam da wadda kuka karɓa, bari yă zama la’ananne har abada! Za a ce, ina ƙoƙarin neman amincewar mutane ne, ko amincewa ta Allah? Ko kuwa ina ƙoƙarin faranta wa mutane zuciya ne? Da a ce har yanzu ina ƙoƙarin faranta wa mutane zuciya ne, ai, da ban zama bawan Kiristi ba. Ina so ku sani ’yan’uwa, cewa bisharar da nake wa’azi, ba mutum ne ya ƙago ta ba. Ban karɓe ta daga wurin wani mutum ba, ba a kuma koya mini ita ba, a maimako, na karɓe ta, ta wurin wahayi daga Yesu Kiristi ne. Kun dai ji labarin rayuwata ta dā a cikin Yahudanci, yadda na tsananta wa ikkilisiyar Allah ƙwarai, na kuma yi ƙoƙarin hallaka ta. Na ci gaba a cikin Yahudanci fiye da yawancin Yahudawan da suke tsarana, na kuma yi ƙwazo ƙwarai ga bin al’adun kakannina. Amma sa’ad da Allah, wanda ya keɓe ni daga mahaifa ya kira ni ta wurin alherinsa, ya kuma gamshe shi yă bayyana Ɗansa a cikina, domin in yi wa’azinsa cikin Al’ummai. Ban nemi shawarar wani mutum ba. Ban kuma tafi Urushalima domin in ga waɗanda suka riga ni zaman manzanni ba, sai dai na hanzarta na tafi ƙasar Arabiya, daga baya sai na koma Damaskus. Bayan shekara uku, sai na haura zuwa Urushalima domin in sadu da Bitrus, na kuwa zauna tare da shi kwana goma sha biyar. Ban ga wani a ciki sauran manzanni ba, sai dai Yaƙub ɗan’uwan Ubangiji. Ina tabbatar muku a gaban Allah cewa abin da nake rubuta muku ba ƙarya ba ne. Daga baya sai na tafi Suriya da Silisiya. Ikkilisiyoyin da suke cikin Kiristi da suke a Yahudiya ba su san ni ba tukuna. Sun dai sami labari ne kawai cewa, “Mutumin da dā yake tsananta mana yanzu yana wa’azin bangaskiyar da dā ya yi ƙoƙari yă hallaka.” Sai suka yabi Allah saboda ni. Bayan shekara goma sha huɗu sai na sāke haurawa zuwa Urushalima, a wannan lokaci na tafi tare da Barnabas. Na kuma ɗauki Titus muka tafi tare. Na tafi ne bisa ga wani wahayi. Da na kai can, sai na bayyana musu bisharar da nake wa’azi a cikin Al’ummai. Na yi haka a keɓance a gaban waɗanda suke shugabanni, don tsoro kada gudun da nake yi, ko kuwa na riga na yi, yă zama a banza. Amma ko Titus ma da yake tare da ni, ba a ce dole sai ya yi kaciya ba, ko da yake shi mutumin Al’ummai ne. Wannan zancen kaciya ya taso domin waɗansu ’yan’uwan ƙarya sun shiga cikinmu domin su yi leƙe a kan ’yancin da muke da shi a cikin Kiristi Yesu, su kuma mai da mu bayi. Ba mu kuwa ba su zarafi ba ko kaɗan, don gaskiyar bishara ta ci gaba da kasance tare da ku. Game da waɗanda aka ɗauka a dā a kan su wani abu ne, ko wane ne su, duk ɗaya ne a wurina; gama Allah ba ya nuna bambanci, ina dai gaya muku waɗannan da suke wani abu ne a dā, ba su ƙara mini kome ba. A maimakon haka, sun ga cewa an danƙa mini hakkin wa’azin bishara ga Al’ummai, kamar yadda aka danƙa wa Bitrus ga Yahudawa. Gama Allah wanda ya yi aiki a cikin hidimar Bitrus a matsayin manzo ga Yahudawa, haka ma ya yi aiki a cikin hidimata a matsayin manzo ga Al’ummai. Yaƙub, Bitrus da Yohanna waɗanda suke fitattun ginshiƙai, sun karɓe ni da Barnabas da hannu biyu biyu sa’ad da suka gane alherin da aka ba ni. Suka kuma yarda cewa ya kamata mu tafi wajen Al’ummai, su kuwa su tafi wajen Yahudawa. Abin da dai suka roƙa shi ne ya kamata mu riƙa tuna da matalauta, abin nan da nake marmarin yi. Sa’ad da Bitrus ya zo Antiyok, na tsawata masa ido da ido don laifinsa a fili yake. Kafin waɗansu mutane su zo daga wurin Yaƙub, yakan ci abinci tare da Al’ummai. Amma da suka iso, sai ya fara janyewa, ya kuma ware kansa daga wajen Al’ummai domin yana tsoron waɗanda suke ƙungiyar masu kaciya. Sauran Yahudawa suka haɗa kai da shi a munafuncinsa har Barnabas ma ya bauɗe. Da na ga cewa ba sa yin daidai da gaskiyar bishara, sai na ce wa Bitrus a gabansu duka, “Kai mutumin Yahuda ne, duk da haka kana rayuwa kamar Ba’al’umme ba kamar mutumin Yahuda ba. To, yaya aka yi, kana tilasta Al’ummai su bi al’adun Yahudawa? “Mu da muke Yahudawa ta wurin haihuwa ba Al’ummai masu zunubi ba, mun san cewa mutum ba ya samun kuɓuta ta wurin kiyaye Doka, sai dai ta wurin bangaskiya cikin Kiristi Yesu. Saboda haka, mu ma, muka sa bangaskiyarmu cikin Kiristi Yesu don mu sami kuɓuta ta wurin bangaskiya cikin Kiristi ba ta wurin kiyaye Doka ba, domin ba wanda zai kuɓuta ta wurin bin Doka. “In kuwa ya zama muna so mu sami zaman marasa laifi a gaban Allah ta wurin dogara ga Kiristi, sa’an nan an same mu mu kanmu ma masu zunubi ne, ashe, ko wannan zai nuna Kiristi yana ƙarfafa zunubi ke nan? A’a, ko kusa! In na sāke gina abin da na rushe, na zama mai karyar Doka ke nan. “Gama ta wurin Doka na mutu ga Doka saboda in rayu ga Allah. An gicciye ni tare da Kiristi. Yanzu ba ni ne nake raye ba, Kiristi ne yake raye a cikina. Rayuwar da nake yi a jiki, ina rayuwa ce ta wurin bangaskiya cikin Ɗan Allah, wanda ya ƙaunace ni ya kuma ba da kansa domina. Ba na ajiyar alherin Allah a gefe, gama da a ce ana samun adalci ta wurin Doka, ai, da Kiristi ya mutu a banza ke nan!” Ya ku Galatiyawa marasa azanci! Wa ya ruɗe ku? A idanunku aka bayyana Yesu Kiristi gicciyeyye a sarari. Zan so in san abu guda tak daga gare ku. Kun karɓi Ruhu ta wurin kiyaye Doka ne, ko kuwa ta wurin gaskata abin da kuka ji? Ashe, rashin azancinku har ya kai ga haka? Bayan kun fara da Ruhu, a yanzu kuma da halin mutuntaka za ku ƙarasa? Ashe, wahaloli dabam-dabam da kuka sha sun zama a banza ke nan? Haka zai yiwu kuwa? Allah ya ba ku Ruhunsa yana kuma aikata ayyukan banmamaki a cikinku saboda kuna kiyaye Doka ne, ko kuwa domin kuna gaskatawa abin da kuka ji ne? Ku dubi Ibrahim mana, “Ya gaskata Allah, aka kuwa lissafta wannan adalci ne a gare shi.” Ku sani fa, waɗannan waɗanda suka gaskata, ’ya’yan Ibrahim ne. Nassi ya hanga cewa Allah zai kuɓutar da Al’ummai ta wurin bangaskiya, ya kuwa sanar wa Ibrahim wannan bisharar tun kafin lokaci yă yi cewa, “Dukan al’ummai za su sami albarka ta wurinka.” Saboda haka waɗanda suke da bangaskiya sun sami albarka tare da Ibrahim, mutumin bangaskiya. Dukan waɗanda suka dogara ga kiyaye Doka la’anannu ne, gama a rubuce yake cewa, “La’ananne ne duk wanda bai ci gaba da yi dukan abubuwan da aka rubuta a Littafin Doka ba.” A fili yake ba wanda zai kuɓuta a gaban Allah ta wurin Doka, domin “Mai adalci zai rayu ta wurin bangaskiya.” Doka ba tă dangana ga bangaskiya ba; a maimakon haka, “Mutumin da ya aikata waɗannan abubuwa zai rayu ta wurinsu.” Kiristi ya fanshe mu daga la’anar Doka ta wurin zama la’ana saboda mu, gama a rubuce yake cewa, “La’ananne ne duk wanda aka rataye a kan itace.” Ya fanshe mu domin albarkar da aka yi wa Ibrahim yă zo ga Al’ummai, ta wurin Kiristi Yesu, domin ta wurin bangaskiya mu karɓi alkawarin Ruhu. ’Yan’uwa, bari in yi muku misali da rayuwarmu ta yau da kullum. Kamar dai yadda ba mai kawarwa ko yă ƙara wani abu cikin alkawarin da mutane suka kafa, haka yake a wannan batu. Alkawaran nan fa ga Ibrahim ne aka faɗa da kuma wani zuriyarsa. Nassi bai ce, “da zuriyoyi ba” wanda ya nuna kamar mutane da yawa, amma “ga zuriyarka,” wanda yake nufin mutum ɗaya, wanda shi ne Kiristi. Abin da nake nufi shi ne, Dokar da aka shigar ita bayan shekaru 430, ba tă kawar da alkawarin da Allah ya yi tun dā ba. Gama da a ce gādon yă dangana a kan doka ne, ai, da ba zai dangana a kan alkawari ba; amma Allah cikin alherinsa ya ba wa Ibrahim gādon ta wurin alkawari. To, don me aka kawo Doka? An yi ƙari da Doka ne don fitowa da laifi fili har kafin na zuriyan nan ya zo, wanda aka yi wa alkawarin, an ba da doka ta wurin mala’iku ne, aka kuma danƙa ta a hannun matsakanci. Kuma akan bukaci wani a tsakani ne idan da mutum biyu ake zance, Allah kuwa ɗaya ne. To, Dokar ce tana gāba da alkawaran Allah ke nan? Sam, ko kaɗan! Gama da a ce an ba da Dokar da tana iya ba da rai, tabbatacce, da sai a sami adalci ta wurin Doka. Amma Nassi ya kulle kome a ƙarƙashin ikon zunubi, domin abin da aka yi alkawarin nan, da ake bayar ta wurin bangaskiya a cikin Yesu Kiristi, a ba da shi ga waɗanda suka gaskata. Kafin bangaskiyan nan tă zo, mun kasance a daure a kurkuku a ƙarƙashin Doka, a kulle sai da bangaskiyar da za tă zo ta bayyana. Ta haka aka sa Dokar ta zama jagorarmu zuwa ga Kiristi don mu sami kuɓuta ta wurin bangaskiya. Yanzu da bangaskiya ta zo, ba sauran zamanmu a ƙarƙashin Doka. Dukanku ’ya’yan Allah ne ta wurin bangaskiya cikin Kiristi Yesu. Gama dukanku da aka yi muku baftisma cikin Kiristi, kuna sanye da Kiristi ke nan. Babu bambanci tsakanin mutumin Yahuda da mutumin Al’ummai, bawa da ’yantacce, namiji da ta mace, gama dukanku ɗaya ne cikin Kiristi Yesu. In kuwa ku na Kiristi ne, to, ku zuriyar Ibrahim ne, magāda kuma bisa ga alkawarin nan. Abin da nake nufi shi ne, muddin magāji yana ɗan yaro ne tukuna, babu bambanci tsakaninsa da bawa, ko da yake shi ne da mallakar kome. Yana ƙarƙashin iyayen goyonsa da masu riƙon amana har yă zuwa cikar lokacin da mahaifinsa ya sa. Haka yake, sa’ad da muke ’yan yara, mun kasance cikin bauta a ƙarƙashin ƙa’idodin duniya. Amma da lokacin da aka tsara ya yi sosai, sai Allah ya aiki Ɗansa, haifaffe daga mace, haifaffe a ƙarƙashin Doka, domin yă fanshi waɗanda suke a ƙarƙashin doka, saboda mu sami cikakken matsayin zaman ’ya’ya. Da yake ku ’ya’ya ne, sai Allah ya aiko da Ruhun Ɗansa a cikin zukatanmu, Ruhun da yake kira, “ Abba, Uba.” Saboda haka kai ba bawa ba ne kuma, kai ɗa ne; da yake kuwa kai ɗa ne, Allah ya mai da kai magāji. Dā da ba ku san Allah ba, ku bayi ne ga waɗanda a ainihi ba alloli ba ne. Amma yanzu da kuka san Allah, ko kuma a ce Allah ya san ku, yaya kuke sāke komawa ga ƙa’idodin duniya marasa ƙarfi, abin tausayi kuma? Kuna so ku sāke komawa ga bautarsu ne? Kuna kiyaye ranaku da watanni da lokuta da shekaru na musamman! Kai, kun ba ni tsoro, don ya zama kamar duk wahalar da na yi a kanku banza ne! Ina roƙonku ’yan’uwa, ku zama kamar ni, gama na zama kamar ku. Ba ku yi mini wani laifi ba. Kun san rashin lafiyar da na yi, shi ne ya yi mini hanyar da na kawo muku bishara da farko. Ko da yake ciwona gwaji ne gare ku, ba ku yi mini reni ko ƙyama ba. A maimakon haka, kuka karɓe ni sai ka ce mala’ikan Allah, kuma sai ka ce Kiristi Yesu kansa. Me ya faru da dukan farin cikinku? Na tabbata, a lokacin, da mai yiwuwa ne da kun ciccire idanunku kun ba ni. Yanzu na zama abokin gābanku don na faɗa muku gaskiya ke nan? Waɗancan mutane suna neman su rinjaye ku da ƙwazo, amma ba da kyakkyawar aniya ba. Abin da suke so shi ne su raba ku da mu, saboda ƙwazonku yă koma gare su. Yana da kyau ku kasance da irin wannan niyya idan da nufi mai kyau ne, ku kuma kasance a haka koyaushe ba sai ina tare da ku ba. Ya ku ’ya’yana ƙaunatattu, ina sāke shan wahalar naƙudarku, har sai Kiristi ya kahu a cikinku. Da ma a ce ina tare da ku yanzu in canja muryata mana! Gama na damu ƙwarai saboda ku! Ku gaya mini, ku da kuke so ku zauna a ƙarƙashin Doka, ba ku san abin da Doka ta ce ba ne? Gama a rubuce yake cewa Ibrahim yana da ’ya’ya biyu maza, ɗaya ta wurin mace ’yar aikin gidansa, ɗaya kuma ta wurin ainihin matarsa. Ɗansa na wajen mace ’yar aikin gidansa ya zo bisa ga ƙa’idar jiki ne; amma ɗansa na wajen ainihin matarsa ya zo a sakamakon alkawarin ne. Za a iya ɗaukan waɗannan al’amura a matsayin misali, domin matan nan suna misalta alkawura biyu ne. Alkawari ɗaya daga Dutsen Sinai ne yana kuma haihuwar ’ya’yan da za su zama bayi. Hagar ke nan. Hagar tana a matsayin Dutsen Sinai a Arabiya tana kuma kwatancin birnin Urushalima na yanzu, gama ita baiwa ce tare da ’ya’yanta. Amma Urushalimar da take sama ’yantacciya ce, ita ce kuma mahaifiyarmu. Gama a rubuce yake cewa, “Ki yi farin ciki, ya ke bakararriya, wadda ba ta haihuwa ki ɓarke da murna, ki kuma tā da murya, ke da ba kya naƙuda; domin da yawa ne ’ya’yan macen da aka yashe, fiye da na mai miji.” To, ku ’yan’uwa, ku ’ya’yan alkawari ne kamar Ishaku. A wancan lokaci, wannan ɗa wanda aka haifa ta wurin ƙa’idar jiki ya tsananta wa wanda aka haifa ta ikon Ruhu. Haka ma yake har yanzu. Amma me Nassi ya ce? Nassi ya ce, “Kori macen nan ’yar aikin gida da ɗanta don ɗan mace ’yar aikin gida ba zai taɓa raba gādo tare da ɗa na ainihin matarka ba.” Saboda haka, ’yan’uwa, mu ba ’ya’yan mace ’yar aikin gida ba ne, amma na ainihin matan gidan ne. Saboda ’yanci ne Kiristi ya ’yantar da mu. Sai ku tsaya daram, kada ku yarda ku sāke komawa ƙarƙashin nauyin bauta. Ku lura da kalmomina! Ni Bulus ina gaya muku cewa in kuka yarda aka yi muku kaciya, wannan ya nuna Kiristi ba shi da amfani a gare ku ba ko kaɗan. Haka kuma ina ƙara sanar wa kowane mutumin da ya yarda aka yi masa kaciya cewa dole yă kiyaye dukan Doka. Ku da kuke ƙoƙarin kuɓuta ta wurin Doka an raba ku da Kiristi ke nan; kuka kuma fāɗi daga alheri. Amma ta wurin bangaskiya muna marmarin jira adalcin da muke bege ta wurin Ruhu. Gama a cikin Kiristi Yesu, kaciya ko rashin kaciya ba su da wani amfani. Abin da kawai yake da amfani shi ne, bangaskiyar da take bayyana kanta ta wurin ƙauna. Kun yi tsere mai kyau a dā. Wa ya shige gabanku ya hana ku bin gaskiya? Wannan rarrashin da ake muku ba daga wanda ya kira ku ba ne. “Ɗan yisti kaɗan ne yake gama dukan curin burodi.” Ina da tabbaci cikin Ubangiji cewa ba za ku bi wani ra’ayi dabam ba. Wannan da yake rikita ku za a hukunta shi, ko shi wane ne. ’Yan’uwa, da a ce har yanzu ina wa’azin kaciya ne, to, me ya sa ake tsananta mini har yanzu? In haka ne, ashe, an kawar da abin da yake sa tuntuɓe game da gicciye ke nan. Da ma a ce masu tā da hankalinku ɗin nan su yanke gabansu gaba ɗaya mana! Ku ’yan’uwana, an kira ku ga zama ’yantattu. Amma kada ku yi amfani da ’yancinku don aikata ayyukan mutuntaka a maimakon haka, ku yi hidimar juna da ƙauna. Dukan doka an taƙaita a cikin umarni ɗaya ne cewa, “Ka ƙaunaci maƙwabcinka kamar kanka.” In kun ci gaba da cizo, kuna kuma cin naman juna, ku yi hankali in ba haka ba za ku hallaka juna. Saboda haka ina ce muku, ku yi rayuwa ta wurin Ruhu, ba za ku kuwa gamsar da sha’awace-sha’awacen mutuntaka ba. Gama mutuntaka yana son abin da Ruhu yake ƙi, Ruhu kuma yana son abin da mutuntaka yake ƙi. Waɗannan biyu kuwa gāba suke da juna, har ku kāsa yin abin da kuke so. Amma in Ruhu ne yake bishe ku, ba ku a ƙarƙashin Doka ke nan. Ayyukan mutuntaka kuwa a fili suke. Wato, fasikanci, ƙazanta da kuma lalata; bautar gumaka da sihiri; ƙiyayya, faɗa, kishi, fushi mai zafi, sonkai, tsattsaguwa, hamayya, da ƙyashi; buguwa, shashanci, da ire-irensu. Na gargaɗe ku, yadda na yi a dā, cewa masu irin wannan rayuwa ba za su gāji mulkin Allah ba. Amma amfanin da Ruhu yake bayar shi ne ƙauna, farin ciki, salama, haƙuri, kirki, nagarta, aminci, sauƙinkai, da kuma kamunkai. Ai, ba ruwan Doka da waɗannan abubuwa. Waɗanda suke na Kiristi Yesu, sun gicciye mutuntaka tare da abubuwan da mutum yake marmari da kuma sha’awace-sha’awacensa. Da yake muna rayuwa ta Ruhu ne, bari mu ci gaba da al’amuranmu ta wurin Ruhu. Kada mu zama masu girman kai, muna tsokana muna kuma jin kishin juna. ’Yan’uwa, in an kama wani yana cikin yin zunubi, ku da kuke masu ruhaniya ya kamata ku komo da shi a kan hanya a hankali. Amma ku lura da kanku, domin kada maimakon dawowa da ɗan’uwanku, ku ma ku fāɗi cikin jarraba. Ku ɗauki nawayar juna, a haka kuwa za ku cika dokar Kiristi. In wani yana tsammani shi wani abu ne alhali kuwa shi ba kome ba, ruɗin kansa yake yi. Kowa yă auna ayyukansa. A sa’an nan ne zai iya yin taƙama da kansa, ba tare da kwatanta kansa da wani ba, gama kowa zai ɗauki kayansa. Duk haka, wanda aka koya wa maganar Kiristi, bari yă raba abubuwan nan na alheri tare da wanda ya koyar da shi. Kada a ruɗe ku. Ba a yi wa Allah ba’a. Mutum yakan girbe abin da ya shuka ne. Wanda ya yi shuki don yă gamshi mutuntakarsa, daga wannan mutuntaka zai girbi hallaka. Wanda ya yi shuki domin yă gamshi Ruhu, daga Ruhu zai girbi rai madawwami. Kada mu gaji da yin nagarta, gama a daidai lokaci za mu girbe amfani, in ba mu fid da zuciya ba. Saboda haka, in da hali, bari mu aikata nagarta ga dukan mutane, musamman ga waɗanda suke na iyalin masu bi. Ku dubi irin manya-manyan harufan da na yi amfani da su yayinda nake rubuta muku da hannuna! Waɗanda suke son nuna bajinta a fili suna ƙoƙari su tilasta muku ku yi kaciya ne. Dalilin kaɗai da suke yin haka shi ne don gudu kada a tsananta musu saboda gicciyen Kiristi ne. Kai, su masu kaciya ma ba su kiyaye Doka ba, duk da haka suna so a yi muku kaciya don su yi taƙama kan an yi muku kaciya. Kada in taɓa yin taƙama ga kome sai dai a cikin gicciyen Ubangijinmu Yesu Kiristi, wanda ta wurinsa aka gicciye duniya a gare ni, aka kuma gicciye ni ga duniya. Kaciya ko rashin kaciya ba wani abu ba ne; abin da yake da amfani shi ne sabuwar halitta. Salama da jinƙai su tabbata ga dukan waɗanda suke bin wannan ƙa’ida, har ma ga Isra’ila na Allah. A ƙarshe, kada kowa yă ƙara damuna, gama ina ɗauke da raunuka masu nuna ni bawan Ubangiji Yesu ne. ’Yan’uwa! Alherin Ubangijinmu Yesu Kiristi yă kasance tare da ruhunku. Amin. Bulus, wanda Allah ya zaɓa don yă zama manzon Kiristi Yesu, Zuwa ga tsarkaka da suke a Afisa, da kuma suke amintattu cikin Kiristi Yesu. Alheri da salama daga Allah Ubanmu da Ubangiji Yesu Kiristi, su kasance tare da ku. Yabo ya tabbata ga Allah Uban Ubangijinmu Yesu Kiristi, wanda ya kawo mana kowace albarka ta ruhaniya daga sama. Gama ya zaɓe mu a cikin Kiristi tun dā can, kafin ma a halicci duniya don mu zama masu tsarki da kuma marasa aibi a gabansa. A cikin ƙauna, ya ƙaddara mu zama ’ya’yansa na riƙo ta wurin Kiristi Yesu, bisa ga nufinsa na alheri. Ya yi haka don mu yabi Allah saboda alherin da ya yi mana saboda mu na ƙaunataccen Ɗansa ne. A cikinsa muka sami fansa ta wurin jininsa, wato, yafewar zunubanmu. Kiristi ya yi wannan saboda yawan alherin Allah wanda ya ba mu babu iyaka tare da dukan hikima da fahimta. Allah ya yi abin da ya nufa, ya kuma sanar mana shirin asirin da ya riga ya shirya yă cika ta wurin Kiristi. Nufinsa ke nan, idan lokaci ya cika, yă harhaɗa dukan abubuwa a ƙarƙashin ikon Kiristi, wato, dukan abubuwan da suke sama da abubuwan da suke ƙasa. A cikinsa ne kuma aka zaɓe mu mu sami gādo daga Allah, an kuwa ƙaddara mu ga haka bisa ga nufin wannan da yake zartar da dukan abubuwa yadda ya yi nufi yă yi. Manufar Allah ita ce cewa mu da muka fara sa bege a cikin Kiristi, mu yi zaman yabon ɗaukakar Allah. An kuma haɗa ku a cikin Kiristi lokacin da kuka ji saƙon nan na gaskiya, wanda yake labari mai daɗi na cetonku. Da kuka ba da gaskiya, sai aka yi muku alamar shaida a cikinsa da Ruhu Mai Tsarki. Ruhu Mai Tsarkin nan shi ne tabbacin da Allah ya yi na cewa zai ba mu kome da ya yi alkawari, har ya sa muka sani nan gaba Allah zai ceci waɗanda suke nasa. Wannan kuwa domin yabon ɗaukakarsa ne. Saboda haka, tun lokacin da na ji labarin bangaskiyarku cikin Ubangiji Yesu da kuma ƙaunar da kuke yi wa dukan mutanen Allah, ban fasa yin godiya saboda ku ba, ina tuna da ku cikin addu’o’ina. Ina ta roƙo cewa Allah na Ubangijinmu Yesu Kiristi, Uba Maɗaukaki, yă ba ku Ruhun hikima da na ganewa, domin ku san shi da kyau. Ina kuma addu’a cewa zuciyarku tă waye don ku gane ko mene ne sa zuciyan nan da ya kira ku a kansa, ku kuma san darajar dukiyan nan wadda take ta mutanen Allah, wato, albarkunsa. Ina addu’a ku san girman ikon Allah wanda ya wuce misali, wanda yake namu. Ikon da yake aiki a cikinmu, ɗaya ne da ikon nan da ya tā da Kiristi daga matattu, ya kuma sa ya zauna a hannun damansa a cikin mulkin samaniya. Yanzu yana mulki a kan dukan masu sarauta, da masu iko, da masu ƙarfi, da kuma masu mulki. Yana mulkin kome a wannan duniya, zai kuma yi mulkin duniya mai zuwa. Allah ya sa kome a ƙarƙashin ikonsa, ya kuma ba shi iko a kan kome don amfanin ikkilisiya. Kuma ikkilisiya ce jikinsa; ta kuma cika da Kiristi, wanda ya cika kome ta kowace hanya. Ku kam, a dā ku matattu ne saboda laifofinku da kuma zunubanku. Kun yi rayuwa kamar yadda sauran mutanen duniya suke yi, cike da zunubi, kuna biyayya ga sarki masu ikon sarari sama, wato, ruhun nan da yanzu yake aiki a cikin masu ƙin biyayya ga Allah. Dukanmu a dā mun yi irin rayuwan nan a cikinsu, muna bin kwaɗayi da sha’awace-sha’awacen jikunanmu da tunaninmu. Kamar sauran mutane, mun cancanci fushin Allah. Amma saboda yawan ƙaunar da yake mana, Allah, wanda yake mai yawan jinƙai, ya ba mu rai sa’ad da ya tashe Kiristi daga matattu. Ta wurin alherin Allah ne aka cece ku. Allah ya tashe mu tare da Kiristi, ya kuma ba mu wurin zama tare da shi a cikin mulkin samaniya. Allah ya yi haka domin a tsararraki masu zuwa yă nuna yalwar alherinsa da ya wuce misali, an bayyana alheransa da ya yi mana ta wurin Kiristi Yesu. Allah ya cece ku ta wurin alheri sa’ad da kuka ba da gaskiya. Wannan kuwa ba yinku ba ne, kyauta ce daga Allah. Ba kuwa saboda aikin lada ba, don kada wani yă ɗaga kai. Ai, mu aikinsa ne, an sāke halittarmu a cikin Kiristi Yesu musamman domin mu yi kyawawan ayyuka, waɗanda Allah ya tanadar mana tun da fari, mu yi. Saboda haka, ku tuna dā ku Al’ummai ne bisa ga haihuwa, waɗanda kuma ake kira masu “kaciya” sukan kira ku “marasa kaciya” (ga shi kuwa, kaciyar nan ta jiki ce, wadda ake yi da hannu). Ku kuma tuna a lokacin ba ku san Kiristi ba. A ware kuke daga mutanen Isra’ila, ba ku kuma da dangantaka da alkawaran da Allah ya yi da su. Kun yi zama a duniyan nan babu bege kuma babu Allah. Amma yanzu a cikin Kiristi Yesu, ku da dā kuke can da nesa an kawo ku kusa ta wurin jinin Kiristi. Gama shi kansa shi ne salamarmu, shi ne ya kawo ƙungiyoyi biyu suka zama ɗaya, ya kuma rushe katangan nan ta ƙiyayya wadda ta raba mu. Kiristi ya ba da jikinsa don yă kawar da doka da dukan umarnanta da kuma ƙa’idodinta. Ya yi haka domin yă halicci sabuwar zuriya daga zuriyoyin nan biyu. Ta haka kuma ya kawo salama tsakaninsu. A kan gicciye, Kiristi ya kawar da ƙiyayyar da take tsakaninmu da juna. Ya kuma kawo sulhu tsakaninmu da Allah. Ya zo ya yi muku wa’azin salama; ku da kuke nesa da shi, ya kuma yi wa waɗanda suke kusa. Gama ta wurinsa dukanmu za mu iya zuwa gun Uba ta wurin Ruhu guda. Don haka, yanzu ku ba baƙi ba ne, ku kuma ba bare ba ne. Ku ’yan ƙasa ne tare da mutanen Allah, iyalin gidan Allah kuma. Ku gini ne wanda manzanni da annabawa suke tushensa, Kiristi kuma shi ne dutse mafi muhimmanci na ginin. Ta wurinsa ne dukan ginin yake a haɗe, shi ne kuma yake sa ginin yă yi girma, yă zama haikali mai tsarki domin Ubangiji. Ku ma sashe ne na wannan ginin da Kiristi ya yi inda Allah yake zaune ta wurin Ruhunsa. Saboda haka, ni Bulus, na zama ɗan kurkuku na Kiristi Yesu saboda ku Al’ummai. Na tabbata kun ji labarin hidimar alheri na musamman da Allah ya ba ni dominku. Wannan wasiƙa za tă faɗa muku kaɗan game da yadda Allah ya bayyana mini shirinsa na asiri. A yayinda kuke karanta wannan, za ku gane abin da na sani game da wannan shirin Kiristi. Ba a sanar da wannan asiri wa wani a sauran zamanai ba, amma a yanzu an bayyana shi ta wurin Ruhu Mai Tsarki ga manzanninsa da annabawansa. Asirin nan kuwa shi ne cewa ta wurin bishara, Al’ummai sun zama waɗanda za su yi gādo tare da Isra’ila, sun zama gaɓoɓin jiki ɗaya, abokan tarayya kuma ga alkawaran nan a cikin Kiristi Yesu. Na zama bawan wannan bishara ta wurin baiwar alherin Allah da aka yi mini ta wurin ikonsa da yake aiki a cikina. Ko da yake ni ba kome ba ne a cikin dukan mutanen Ubangiji, aka ba ni wannan baiwa mai daraja don in faɗa wa Al’ummai cewa saboda Kiristi akwai albarkun da suka wuce gaban misali. An zaɓe ni in bayyana wa dukan mutane shirin asirin nan wanda Allah, mahaliccin kome, ya ɓoye shekara da shekaru. Nufinsa shi ne, yanzu, ta wurin ikkilisiya, a sanar da hikima iri dabam-dabam na Allah ga masu mulki, da masu iko a samaniya. Wannan shi ne madawwamin shirinsa, kuma an aikata shi ta wurin Kiristi Yesu Ubangijinmu. A cikinsa, kuma ta wurin bangaskiya a cikinsa ne muke da ƙarfin halin zuwa kusa da Allah gabagadi. Don haka, ina roƙonku kada ku fid da zuciya saboda abin da ake yi mini a nan. Ai, saboda ku ne nake shan wahalolin nan, wannan kuwa ɗaukakarku ce. Saboda wannan ne nake a durƙushe a gaban Uba, wanda ya ba wa kowane iyali a sama da ƙasa suna. Ina addu’a cewa daga yalwar ɗaukakarsa zai ƙarfafa ku da iko daga ciki ta wurin Ruhunsa. Ina addu’a domin Kiristi yă zauna a cikin zukatanku ta wurin bangaskiya. Ina kuma addu’a saboda ku da kuka kahu sosai cikin ƙauna, don ku sami iko, tare da dukan tsarkaka, ku fahimci fāɗi, tsawo, da kuma zurfin ƙaunar Kiristi take. Ku kuma san wannan ƙauna wadda ta fi gaban sani, domin a cika ku da dukan cikar Allah. Bari ɗaukaka ta tabbata a gare shi shi wanda yake da ikon yin aiki a cikinmu, yana kuma aikata abubuwa fiye da dukan abin da muke roƙo, ko muke tunani. Bari ɗaukaka ta tabbata a gare shi a cikin ikkilisiya da kuma a cikin Kiristi Yesu, har yă zuwa dukan zamanai, har abada abadin! Amin. A matsayina na ɗan kurkuku saboda Ubangiji, ina roƙonku ku yi rayuwar da ta dace da kiran da aka yi muku. Kullum ku kasance masu sauƙinkai da kuma hankali; ku zama masu haƙuri, kuna jimrewa da juna cikin ƙauna. Ku yi ƙoƙari sosai ku kiyaye zaman ɗayan nan da Ruhu ya ba ku, ku yi haka ta wurin zaman lafiya da juna. Dukanku jiki ɗaya ne, kuna kuma da Ruhu guda. An ba ku bege guda sa’ad da aka kira ku. Ubangiji ɗaya, bangaskiya ɗaya, baftisma kuma ɗaya, Allah ɗaya Uban duka, wanda yake a bisa duka, ta wurin duka, a cikin duka kuma. Amma ga kowannenmu an ba da alheri bisa ga yadda Kiristi ya rarraba. Shi ya sa aka ce, “Sa’ad da ya hau sama, ya bi da kamammu kamar tawagarsa ya kuma ba da baye-baye ga mutane.” (Me ake nufin da “ya hau,” in ba cewa dā ya sauka can ƙarƙashin ƙasa ba? Shi wannan da ya sauka ɗin, shi ne kuma ya hau zuwa can sama, kai, gaba da sammai, don mulkinsa yă cika duniya gaba ɗaya.) Saboda haka Kiristi kansa ya ba wa waɗansu baiwa su zama manzanni, waɗansu su zama annabawa, waɗansu su zama masu wa’azi, waɗansu kuma su zama fastoci, da kuma malamai. Ya yi haka don yă shirya mutanensa saboda ayyukan hidima, don a gina jikin Kiristi. Wannan zai ci gaba har sai mun zama ɗaya a cikin bangaskiya da kuma ta wurin fahimtarmu na Ɗan Allah. Sa’an nan za mu zama balagaggu, kamar yadda Kiristi yake, mu kuma zama gaba ɗaya cikakku kamar sa. An yi wannan kuwa don kada mu koma zama kamar yara, muna ta canja zukatanmu game da abin da muka gaskata don kawai wani ya faɗa mana wani abu dabam, ko domin wani ya yi wayo ya ruɗe mu, ya sa ƙarya ta zama kamar gaskiya. Ya kamata kullum ƙauna tă sa mu faɗa gaskiya. Ta haka za mu yi girma a kowace hanya, mu kuma zama kamar Kiristi, wanda yake kan dukan jiki. Shi ne ya haɗe jiki duka, ya kuma sa dukan gaɓoɓin jiki suna aiki daidai, yayinda kowace gaɓa take aikinta cikin ƙauna. To, ina dai faɗa muku, ina kuma nace faɗa muku a cikin Ubangiji, cewa kada ku ci gaba da yin rayuwa kamar yadda Al’ummai suke yi, masu banzan tunani. Suna a cikin duhu a fahimtarsu, kuma a rabe suke daga ran Allah saboda jahilcin da yake cikinsu ta dalilin taurarewar zukatansu. Ba sa damu da wani abu ko mai kyau ko marar kyau. Rayukansu sun cika da kowace irin ƙazanta da haɗama. Amma ba abin da aka koya muku ke nan ba sa’ad da kuka zo ga sanin Kiristi. Da yake kun ji duka game da shi, kuka kuma koyi gaskiyar da take cikin Yesu, sai ku tuɓe tsohon mutumin nan naku da kuma rayuwarku ta dā, wadda take lalacewa saboda sha’awace-sha’awacen da suke ruɗe ku. A maimakon haka, bari Ruhu yă sabunta tunaninku da kuma halayenku. Ku sanya sabon halin nan da aka halitta bisa ga kamannin Allah, halin nan kuwa, yă bayyana cikin adalci, da zaman tsarki. Saboda haka dole kowannenku yă bar yin ƙarya, yă kuma riƙa faɗa wa maƙwabcinsa gaskiya, gama dukanmu gaɓoɓi jiki ɗaya ne. “Cikin fushinku kada ku yi zunubi.” Kada ku bar rana ta fāɗi kuna fushi, kada kuma ku ba wa Iblis dama. Duk wanda yake sata, sai yă daina sata, dole kuma yă yi aiki, yă yi wani abu mai amfani da hannuwansa, don yă sami abin da zai iya raba da masu bukata. Kada wata ƙazamar magana ta fita daga bakunanku, sai dai abin da yake da amfani don gina waɗansu bisa ga bukatunsu. Ta haka maganarku za tă zama da amfani ga masu jinta. Kada kuma ku ɓata wa Ruhu Mai Tsarki na Allah rai, wanda da shi aka hatimce ku da shi don ranar fansa. Ku rabu da kowane irin ɗacin rai, haushi da hasala, faɗa da ɓata suna, ku rabu da kowace irin ƙeta. Ku yi alheri, ku kuma ji tausayin juna, kuna gafarta wa juna, kamar yadda a cikin Kiristi, Allah ya gafarta muku. Ku zama masu koyi da Allah, kamar ƙaunatattun ’ya’ya, ku kuma yi rayuwar ƙauna, kamar yadda Kiristi ya ƙaunace mu, har ya ba da kansa dominmu a matsayin sadaka mai ƙanshi da kuma hadaya ga Allah. Kada a ma ambaci fasikanci, da kowane irin aikin lalata, ko kwaɗayi a tsakaninku, domin bai dace da mutane masu tsarki na Allah ba. Haka ma bai kamata a sami datti, ƙazamar magana, ko zancen banza a cikinku ba, domin ba su dace ba, a maimakon haka sai ku yi ta yin godiya. Ku dai tabbata, ba wani mai fasikanci, ko mai aikin lalata, ko mai kwaɗayin (wanda shi da mai bautar gumaka ɗaya ne), da yake da gādo a mulkin Kiristi da na Allah. Kada wani yă ruɗe ku da kalmomin wofi, gama saboda waɗannan abubuwa ne fushin Allah yake zuwa a kan marasa biyayya. Saboda haka kada ku haɗa kai da su. Gama a dā zukatanku sun cika da duhu, amma yanzu ku haske ne a cikin Ubangiji. Ku yi rayuwa kamar ’ya’yan haske (domin amfanin haske ya ƙunshi nagarta, adalci, da kuma gaskiya) ku nemi abin da zai gamshi Ubangiji. Ku yi nesa da ayyukan duhun da mutane suke yi, a maimakon haka, ku tona su. Gama abin kunya ne a ma faɗi abubuwan da marasa biyayya suke yi a ɓoye. Duk abin da aka kawo a gaban haske ana iya ganinsa, kuma duk abin da aka haskaka yakan zama haske. Shi ya sa aka ce, “Ka farka, ya kai mai barci, ka tashi daga matattu, Kiristi kuwa zai haskaka ka.” Sai ku yi hankali sosai da yadda kuke rayuwa, kada ku zama kamar marasa hikima, sai dai kamar masu hikima. Ku kuma yi matuƙar amfani da kowane zarafi, don kwanakin nan mugaye ne. Saboda haka kada ku zama wawaye, sai dai ku fahimci ko mene ne nufin Ubangiji. Kada ku bugu da ruwan inabi, wanda yake kai ga lalaci. A maimako haka, ku cika da Ruhu. Ku yi zance da juna cikin zabura, da waƙoƙi, da kuma waƙoƙin ruhaniya. Ku rera, ku kuma yi kiɗe-kiɗe a zuciyarku ga Ubangiji. Kullum ku dinga yin amfani da sunan Ubangijinmu Yesu Kiristi, kuna gode wa Allah Uba a kome. Ku yi biyayya da juna saboda bangirmar da kuke nuna wa Kiristi. Matan aure, ku yi biyayya ga mazanku, kamar ga Ubangiji ne kuke yi. Gama miji shi ne kan mace, yadda Kiristi yake kai da kuma Mai Ceton ikkilisiya, wadda take jikinsa. To, kamar yadda ikkilisiya take biyayya ga Kiristi, haka ma ya kamata mata su yi biyayya ga mazansu cikin kome. Maza, ku ƙaunaci matanku, kamar yadda Kiristi ya ƙaunaci ikkilisiya, ya kuma ba da kansa dominta. Ya mai da ikkilisiya ta zama mai tsarki ta wurin ikon maganarsa, ya kuma tsabtacce ta ta wurin wanke ta da ruwa. Kiristi ya yi haka don yă miƙa wa kansa ikkilisiya mai ɗaukaka da kuma mai tsarki, marar aibi, marar tabo, da kuma marar lahani. Don haka, dole maza su ƙaunaci matansu kamar yadda suke ƙaunar jikunansu. Wanda yake ƙaunar matarsa, yana ƙaunar kansa ne. Gama ba wanda ya taɓa ƙin jikinsa, sai dai yă ciyar da shi, yă kuma kula da shi, kamar yadda Kiristi yake yi wa ikkilisiya, gama mu gaɓoɓin jikinsa ne. “Saboda haka mutum yakan bar mahaifinsa da mahaifiyarsa, yă manne wa matarsa, su biyun su zama jiki ɗaya.” Wannan babban asiri ne, amma na ɗauke shi a matsayin kwatanci ne na Kiristi da ikkilisiya. Duk da haka, dole kowannenku yă ƙaunaci matarsa kamar yadda yake ƙaunar kansa, kuma dole matar tă yi biyayya ga mijinta. Ku ’ya’ya, ku yi biyayya ga iyayenku, gama ku na Ubangiji, abin da ya dace ku yi ke nan. Doka ta farko wadda aka haɗa da alkawari ita ce, “Ka girmama mahaifinka da mahaifiyarka, don ka zauna lafiya, ka kuma yi tsawon rai a duniya.” Ku kuma iyaye, kada ku tsokane ’ya’yanku. Ku yi musu reno mai kyau. Ku koyar da su, ku kuma gargaɗe su game da Ubangiji. Ku bayi, ku yi biyayya ga iyayengijinku na duniya. Ku nuna musu halin bangirma, kuna kuma yin musu biyayya cikin dukan abu, da zuciya ɗaya kamar ga Kiristi kuke yi. Ku yi aiki sosai, ba don kawai ku gamshe su sa’ad da suke kallonku ba. Da yake ku bayin Kiristi ne, ku aikata nufin Allah da dukan zuciyarku. Ku yi aikinku da kyakkyawar niyya, sai ka ce ga Ubangiji kuke yi, ba mutane ba. Gama kun san cewa Ubangiji zai ba da lada ga kowa gwargwadon kowane aiki nagarin da ya yi, ko shi bawa ne, ko ’yantacce. Ku kuma masu bayi, dole ku bi da bayinku da kyau. Ku daina ba su tsoro. Ku tuna, ku da su, Maigida ɗaya kuke da shi a sama, kuma ba ya nuna bambanci. A ƙarshe, bari ƙarfin ikon Ubangiji yă ba ku ƙarfi. Ku yafa dukan kayan yaƙin da Allah yake bayarwa, don ku iya kāre kanku daga dabarun Shaiɗan. Gama ba da mutane da suke nama da jini ne muke yaƙi ba. Muna yaƙi ne da ikoki, da hukumomi, da masu mulkin duhu, da kuma a ikokin da suke cikin a sararin sama. Saboda haka sai ku yafa dukan kayan yaƙi na Allah, domin sa’ad da ranar mugun nan ta zo, ku iya yin tsayin daka, bayan kuma kuka gama kome, ku dāge. Saboda haka fa ku dāge, ku sa gaskiya tă zama ɗamararku, adalci yă zama sulkenku, shirin kai bisharar salama yă zama kamar takalmi a ƙafafunku. Ban da waɗannan kuma, ku ɗauki garkuwar bangaskiya, wadda za ku iya kashe dukan kibiyoyin wutar Mugun nan da ita. Ku kuma ɗauki hular kwano na ceto, da takobin Ruhu, wato, Maganar Allah. A koyaushe ku kasance kuna addu’a da roƙo ta wurin ikon Ruhu ba fasawa. A kan wannan manufa ku zauna a faɗake da matuƙar naci, kuna yin wa dukan mutanen Ubangiji addu’a. Ku kuma yi addu’a domina, don duk sa’ad da na buɗe bakina, in sami kalmomi babu tsoro, don in sanar da asirin bishara, wadda nake jakadanta cikin sarƙoƙi. Ku yi addu’a don in iya yin shelarta babu tsoro, yadda ya kamata in yi. Tikikus, ƙaunataccen ɗan’uwa da kuma amintaccen bawa cikin Ubangiji, zai faɗa muku kome, domin ku ma ku san yadda nake, da kuma abin da nake yi. Na aike shi gare ku musamman don wannan, domin ku san yadda muke, yă kuma ƙarfafa ku. ’Yan’uwa, salama tare da ƙauna da kuma bangaskiya daga Allah Uba da Ubangiji Yesu Kiristi su kasance tare da ku. Alheri yă tabbata ga dukan masu ƙaunar Ubangiji Yesu Kiristi da ƙauna marar ƙarewa. Bulus da Timoti, bayin Kiristi Yesu, Zuwa ga dukan tsarkaka cikin Kiristi Yesu a Filibbi, tare da masu kula da Ikkilisiya da kuma masu hidima. Alheri da salama daga Allah Ubanmu da kuma Ubangiji Yesu Kiristi, su kasance tare ku. Ina gode wa Allahna a kowane lokacin da na tuna da ku. A cikin dukan addu’o’ina dominku duka, nakan yi addu’a da farin ciki kullum saboda tarayyarku a cikin bishara daga ranar farko har yă zuwa yanzu, da tabbacin cewa wanda ya fara kyakkyawan aikin nan a cikinku, zai kai shi ga kammalawa har yă zuwa ranar Kiristi Yesu. Daidai ne in yi wannan tunani game da dukanku, da yake kuna a zuciyata; domin ko ina daure cikin sarƙoƙi ko ina kāre bishara ina kuma tabbatar da ita, dukanku kuna tarayya cikin alherin Allah tare da ni. Allah shi ne shaidata, ya san yadda nake ƙaunarku duka da ƙaunar Kiristi Yesu. Addu’ata ita ce ƙaunarku tă yi ta cin gaba da ƙaruwa cikin sani da kuma zurfin ganewa, don ku iya rarrabe abin da yake mafi kyau, ku kuma zama da tsarki, marasa aibi har yă zuwa ranar Kiristi, cikakku da sakamakon aikin adalci da yake zuwa ta wurin Yesu Kiristi, zuwa ga ɗaukakar Allah da kuma yabonsa. To, ina so ku sani ’yan’uwa, cewa abin da ya faru da ni ya sa cin gaban bishara. Ta haka, ya zama sananne ga dukan masu gadin fada da kuma ga kowa cewa an daure ni da sarƙoƙi saboda Kiristi. Saboda sarƙoƙina, yawancin ’yan’uwa cikin Ubangiji sun sami ƙarfafawa su yi maganar Allah gabagadi da kuma babu tsoro. Gaskiya ce cewa waɗansu suna yin wa’azin Kiristi saboda kishi da neman faɗa, amma waɗansu da nufi mai kyau suke yi. Na biye suna yin haka cikin ƙauna, da sanin cewa an sa ni a nan ne domin kāriyar bishara. Na farin dai suna wa’azin Kiristi da sonkai ne, ba da zuciya ɗaya ba, a sonsu, su wahalar da ni a cikin sarƙoƙi. Me kuma? Ta ko yaya dai, ko da gangan, ko da gaske, ana shelar Kiristi. Domin wannan kuwa ina farin ciki. I, zan kuwa ci gaba da farin ciki, gama na san cewa ta wurin addu’o’inku da kuma taimako daga Ruhun Yesu Kiristi, abin da ya same ni zai zama sanadin kuɓutata. Ina saurara da marmari da kuma bege cewa ba zan taɓa shan kunya ba, sai dai zan sami issashen ƙarfin hali yanzu kamar kullum, za a ɗaukaka Kiristi a jikina, ko ta wurin rayuwa ko kuma ta wurin mutuwa. Gama a gare ni, rai Kiristi ne, mutuwa kuma riba ce. In zan ci gaba da rayuwa a cikin jiki, wannan zai zama aiki mai amfani a gare ni. Duk da haka me zan zaɓa? Ban sani ba! Na rasa wanda zan zaɓa cikin biyun nan. Ina sha’awa in yi ƙaura in zauna tare da Kiristi, wannan kuwa ya fi kyau nesa ba kusa ba; amma ya fi muku muhimmanci in rayu cikin jiki. Na tabbata haka ne, na kuwa san zan wanzu in zauna tare da ku duka, domin ku ci gaba, bangaskiyarku tana sa ku farin ciki, domin ta wurin kasancewata tare da ku, farin cikinku cikin Kiristi Yesu zai cika sosai ta dalilina. Kome ya faru, ku yi zaman da ya cancanci bisharar Kiristi. Ta haka, ko na zo na gan ku, ko ban zo ba, in ji labari cewa kun tsaya da ƙarfi a cikin ruhu ɗaya, kuna fama kamar mutum ɗaya saboda bangaskiyar bishara ba tare da kun ji tsoron waɗanda suke gāba da ku ta kowace hanya ba. Wannan alama ce a gare su cewa za a hallaka su, amma a gare ku za a cece ku, wannan tabbacin kuwa daga wurin Allah ne. Gama an ba ku zarafi a madadin Kiristi cewa ba gaskatawa da shi kaɗai ba kuka yi ba, har ma ku sha wahala dominsa, da yake kuna shan faman da kuka gan na sha, kuna kuma jin cewa har yanzu ina sha. In kuna da wata ƙarfafawa daga tarayya da Kiristi, in da wata ta’aziyya daga ƙaunarsa, in da wani zumunci da Ruhu, in da juyayi da tausayi, to, sai ku sa farin cikina yă zama cikakke ta wurin kasance da hali ɗaya, kuna ƙauna ɗaya, kuna zama ɗaya cikin ruhu da kuma manufa. Kada ku yi kome da sonkai ko girman kai, sai dai cikin tawali’u, ku ɗauki waɗansu sun fi ku. Bai kamata kowannenku yă kula da sha’anin kansa kawai ba, sai dai yă kula da sha’anin waɗansu ma. A cikin dangantakarku da juna, ya kamata halayenku su zama kamar na Kiristi Yesu. Wanda, ko da yake cikin ainihin surar Allah yake, bai mai da daidaitakansa nan da Allah wani abin riƙewa kam-kam ba, amma ya mai da kansa ba kome ba, yana ɗaukan ainihin surar bawa, aka yi shi cikin siffar mutum. Aka kuma same shi a kamannin mutum, ya ƙasƙantar da kansa ya kuma zama mai biyayya wadda ta kai shi har mutuwa, mutuwar ma ta gicciye! Saboda haka Allah ya ɗaukaka shi zuwa mafificin wuri ya kuma ba shi sunan da ya fi dukan sunaye, don a sunan Yesu kowace gwiwa za tă durƙusa, a sama da a ƙasa da kuma a ƙarƙashin ƙasa, kowane harshe kuma yă furta cewa Yesu Kiristi Ubangiji ne, don ɗaukakar Allah Uba. Saboda haka, ya abokaina ƙaunatattu, kamar yadda kullum kuke biyayya ba kawai sa’ad da ina nan ba, amma yanzu da ba na nan tare da ku, ku ci gaba da yin ayyukan cetonku da tsoro da kuma rawan jiki, gama Allah ne yake aiki a cikinku, don ku nufa ku kuma aikata bisa ga nufinsa mai kyau. Ku yi kome ba tare da gunaguni ko gardama ba, don ku zama marasa abin zargi, sahihai ’ya’yan Allah, waɗanda ba su da laifi, a zamanin mutane karkatattu, kangararru, waɗanda kuke haskakawa a cikinsu kamar fitilu a duniya kuna kuwa cin gaba da riƙe maganar rai domin in yi taƙama a ranar Kiristi cewa ban yi gudu ko fama a banza ba. Amma ko da ana tsiyaye jinina kamar hadaya ta sha a kan hadaya da kuma hidimar da take fitowa daga bangaskiyarku, ina murna ina kuma farin ciki da ku duka. Haka ma ya kamata ku yi murna ku kuma yi farin ciki tare da ni. Ina sa rai a cikin Ubangiji Yesu cewa zan aika da Timoti zuwa gare ku ba da daɗewa ba, don ni ma in ji daɗi sa’ad da na ji labarinku. Ba ni da wani kamar sa, wanda yake da ainihin sha’awa a zaman lafiyarku. Gama kowa yana lura da al’amuran kansa ne kawai, ba na Kiristi Yesu ba. Amma, ai, kun san darajar Timoti yadda muka yi bautar bishara tare, kamar ɗa da mahaifinsa. Saboda haka, ina sa rai, in aike shi da zarar na ga yadda abubuwa suke a nan. Ni kuma ina da tabbaci a cikin Ubangiji cewa zan zo ba da daɗewa ba. Amma ina gani ya dace in aika da Afaforiditus, ɗan’uwana, abokin aikina da kuma abokin famana, wanda kuma yake ɗan saƙonku, wanda kuka aika domin yă biya mini bukatuna. Gama yana marmarin ganinku duka ya kuma damu domin kun ji cewa ya yi rashin lafiya. Ba shakka ya yi rashin lafiya, har ya kusa mutuwa. Amma Allah ya nuna masa jinƙai, ba shi kaɗai ba amma har da ni ma, don yă rage mini baƙin ciki kan baƙin ciki. Saboda haka na yi niyya ƙwarai in aike shi wurinku, don sa’ad da kuka sāke ganinsa za ku yi murna, ni kuma in rage damuwa. Ku marabce shi cikin Ubangiji da farin ciki mai yawa, ku kuma girmama mutane irinsa, domin ya kusa yă mutu saboda aikin Kiristi, ya yi kasai da ransa don yă cikasa taimakon da ba ku iya yi mini ba. A ƙarshe, ’yan’uwana, ku yi farin ciki a cikin Ubangiji! Ba abin damuwa ba ne a gare ni in sāke rubuta muku irin waɗannan abubuwa, domin lafiyarku ne. Ku yi hankali da waɗancan karnuka, waɗancan mutane masu aikata mugunta, waɗancan masu yankan jiki. Gama mu ne masu kaciya, mu da muke yi sujada ta wurin Ruhun Allah, mu da muke taƙama a cikin Kiristi Yesu, mu da ba mu dogara da ayyukan da ake gani ba, ko da yake ni kaina ina da dalilan dogara da haka. In kuwa akwai wani wanda yake tsammani yana da dalilan dogara ga jiki, ni fa na fi shi, an yi mini kaciya a rana ta takwas, asalina Isra’ila ne, na kabilar Benyamin, mutumin Ibraniyawa ɗan Ibraniyawa; bisa ga doka kuwa ni Bafarisiye ne; wajen himma kuwa, ni mai tsananta wa ikkilisiya ne, wajen aikin adalci bisa ga hanyar doka, ni marar laifi ne. Amma abin da dā ya zama mini riba yanzu, na ɗauka hasara ce saboda Kiristi. Me kuma ya fi, na ɗauki dukan abubuwa hasara ne in aka kwatanta da mafificiyar girman sanin Kiristi Yesu Ubangijina, wanda saboda shi ne na yi hasarar kome. Na mai da su kayan wofi, domin in sami Kiristi a kuma same ni a cikinsa, ba da wani adalcin kaina wanda yake zuwa daga bin doka ba, sai dai adalcin da yake samuwa ta wurin bangaskiya a cikin Kiristi, adalcin da yake fitowa daga Allah da kuma yake zuwa ta wurin bangaskiya. Ina so in san Kiristi da ikon tashinsa daga matattu da kuma zumuncin tarayya cikin shan wahalarsa, in kuma zama kamar sa a cikin mutuwarsa, yadda kuma ko ta yaya, in kai ga tashin nan daga matattu. Ba cewa na riga na sami dukan wannan ba ne, ko kuma an riga an mai da ni cikakke ba, sai dai ina nacewa don in kai ga samun abin da Kiristi Yesu ya riƙe ni saboda shi. ’Yan’uwa, ban ɗauki kaina a kan cewa na riga na sami abin ba. Sai dai abu guda nake yi. Ina mantawa da abin da yake baya, ina kuma nacewa zuwa ga samun abin da yake gaba, ina nacewa gaba zuwa ga manufar, don in sami ladar da Allah ya yi mini na kiran nan zuwa sama a cikin Kiristi Yesu. Dukanmu da muka balaga ya kamata mu yi wannan irin ganin abubuwa. In kuwa saboda wani dalili tunaninku ya yi dabam, Allah zai bayyana muku wannan ma. Sai dai a duk inda muka kai, mu ci gaba da haka. Ku haɗa kai da waɗansu cikin bin gurbina, ku kuma lura da waɗanda suke rayuwa bisa ga ƙa’idar da muka ba ku. Gama kamar yadda na sha gaya muku yanzu kuma ina sāke gaya muku har ma da hawaye, waɗansu da yawa suna rayuwa kamar abokan gāban gicciyen Kiristi. Ƙaddararsu hallaka ce, allahnsu cikinsu ne, rashin kunyarsu shi ne abin fahariyarsu. Hankalinsu yana kan kayan duniya. Amma mu ’yan mulkin sama ne. Muna kuma jira zuwan Mai Ceto daga can, Ubangiji Yesu Kiristi, shi ne mai ikon kawo dukan abubuwa ƙarƙashin mulkinsa. Ta wurin ikon nan nasa zai sāke jikin nan namu na ƙasƙanci, yă mai da shi kamar jikin nan nasa na ɗaukaka. Saboda haka ’yan’uwana, ku da nake ƙauna, nake kuma marmarin ganinku, ku da kuke farin cikina da kuma rawanina, ku dāge ga Ubangiji, ya ku ƙaunatattuna! Ina roƙon Yuwodiya ina kuma roƙon Sintike, su yi zaman lafiya da juna saboda su na Ubangiji ne. I, ina kuma roƙonka, abokin famata, ka taimaki matan nan waɗanda suka yi fama aikin bishara tare da ni, haka ma Kilemen da kuma sauran abokan aikina, waɗanda sunayensu suna cikin littafin rai. Ku yi farin ciki a cikin Ubangiji kullum. Ina sāke gaya muku ku yi farin ciki! Bari kowa yă kasance da sauƙinkai. Ubangiji ya yi kusan zuwa. Kada ku damu game da kome sai dai a cikin abu duka, ku gabatar da roƙe-roƙenku ga Allah ta wurin addu’a da roƙo, tare da godiya. Salamar Allah, wadda ta wuce dukan fahimta, za tă tsai da zukatanku da tunaninku cikin Kiristi Yesu. A ƙarshe, ’yan’uwa, duk abin da yake na gaskiya, duk abin da yake na girmamawa, duk abin da yake daidai, duk abin da yake da tsarki, duk abin da yake kyakkyawa, duk abin da yake na sha’awa, in ma wani abu mafifici ne, ko ya cancanci yabo, ku yi tunani a kan irin abubuwan nan. Duk abin da kuka koya ko kuka karɓa ko kuka ji daga wurina, ko kuka gani a cikina, ku yi aiki da shi. Allah na salama kuma zai kasance tare da ku. Na yi farin ciki sosai ga Ubangiji don yanzu kun sāke nuna kun kula da ni. Ko da yake dā ma kun kula da ni sai dai ba ku sami dama ku nuna mini ba. Ba na faɗin haka domin ina cikin bukata, gama na koya yadda zan gamsu a cikin kowane hali. Na san mene ne zaman rashi, na kuma san mene ne zaman samu. Zan iya zama cikin kowane hali, ko cikin ƙoshi ko cikin yunwa, ko cikin yalwa ko kuma cikin fatara. Ina iya yin kome ta wurin wannan wanda yake ba ni ƙarfi. Duk da haka kun kyauta da kuka yi tarayya da ni cikin wahalolina. Ban da haka, kamar yadda ku Filibbiyawa kuka sani, a farkon kwanakin da kuka ji bishara, sa’ad da na tashi daga Makidoniya, babu wata ikkilisiyar da tă yi tarayya da ni a fannin bayarwa da karɓa, sai ku kaɗai; gama ko sa’ad da nake a Tessalonika ma, kun aiko mini da taimako sau da sau sa’ad da nake cikin bukata. Ba cewa ina neman kyauta ba ne, sai dai ina neman abin da za a ƙara a kan ribarku. An biya ni duka, biyan da ya wuce misali. Bukatata ta biya, da yake na karɓi kyautarku da kuka aiko ta hannun Afaforiditus. Baiwa mai ƙanshi, hadaya abar karɓa, mai faranta wa Allah rai. Allahna kuma zai biya dukan bukatunku bisa ga ɗaukakar wadatarsa cikin Kiristi Yesu. Ɗaukaka ta tabbata ga Allahnmu da Ubanmu har abada abadin. Amin. Ku gai da dukan tsarkaka cikin Kiristi Yesu. ’Yan’uwan da suke tare da ni suna gaishe ku. Dukan tsarkaka suna gaishe ku, musamman waɗanda suke na gidan Kaisar. Alherin Ubangiji Yesu Kiristi yă kasance da ruhunku. Amin. Bulus, wanda Allah ya zaɓa don yă zama manzon Kiristi Yesu, da kuma daga Timoti ɗan’uwanmu, Zuwa ga tsarkaka da kuma amintattun ’yan’uwa cikin Kiristi da suke a Kolossi. Alheri da salama daga Allah Ubanmu, su kasance tare da ku. Kullum muna gode wa Allah, Uban Ubangijinmu Yesu Kiristi, sa’ad da muke addu’a dominku. Gama mun ji labarin bangaskiyarku a cikin Yesu Kiristi da kuma ƙaunar da kuke yi saboda dukan tsarkaka. Kuna yin haka ne kuwa domin abin da kuke bege yana a ajiye a sama. Kun riga kun ji game da wannan bege sa’ad da kuka gaskata saƙon nan na gaskiya wanda shi ne bisharar da ta zo muku. Ko’ina a duniya wannan bishara tana yi ta haihuwa tana kuma girma, kamar yadda take yi a cikinku tun daga ranar da kuka ji ta kuka kuma fahimci alherin Allah cikin dukan gaskiyarta. Kun koyi wannan gaskiya daga wurin Efafaras, ƙaunataccen abokin hidimarmu, wanda yake amintacce mai hidimar Kiristi a madadinmu, wanda kuma ya faɗa mana ƙaunar da kuke yi cikin Ruhu. Shi ya sa tun daga ranar da muka sami labarin, ba mu fasa yin addu’a dominku ba. Kullum muna roƙon Allah yă sa ku san kome da yake so ku yi, domin ku sami hikima ta Ruhu, ku kuma sami ganewar kome duka. Ta haka za ku yi rayuwa wadda ta dace da Ubangiji, ku kuma gamshe shi a ta kowace hanya, kuna yin aiki mai kyau ta kowace hanya, kuna kuma yin girma cikin sanin Allah. Allah yă ƙarfafa ku da dukan iko bisa ga ɗaukakar ƙarfinsa domin ku kasance da jimrewa sosai da kuma haƙuri, cikin farin ciki kuna gode wa Uba, wanda ya sa kuka cancanci ku sami rabo a gādon tsarkaka a cikin mulkin haske. Gama ya riga ya cece mu daga mulkin duhu ya kuma kawo mu cikin mulkin Ɗan da yake ƙauna, wanda ta wurinsa muka sami fansa da kuma gafarar zunubai. Kiristi shi ne surar da ake gani na Allah wanda ba a iya gani, ɗan fari a kan dukan halitta. Ta wurinsa aka halicci dukan abu, abubuwan da suke cikin sama da abubuwan da suke a duniya, waɗanda ake gani, da waɗanda ba a gani, ko kursiyoyi ko ikoki ko masu mulki ko hukumomi; an halicci dukan abu ta wurinsa da kuma dominsa ne. Ya kasance kafin dukan abu, kuma a cikinsa ne dukan abubuwa suke a harhaɗe. Shi ne kuma kan ikkilisiya, wadda take jikinsa. Shi ne mafari da kuma na farko da ya tashi daga matattu, domin a cikin kowane abu yă zama mafifici. Gama Allah ya ji daɗi yă sa dukan cikarsa ta kasance a cikin Kiristi, ta wurin Kiristi ne ya komar da kome zuwa ga kansa. Ya kawo salama ga abubuwan da suke ƙasa da abubuwan da suke sama, ta wurin jinin Kiristi da ya zubar a kan gicciye. A dā kuna a ware da Allah, kuka kuma zama abokan gāba a cikin tunaninku saboda mugun halinku. Amma Ɗansa ya zama mutum ya kuma mutu. Saboda haka Allah ya yi sulhu da ku, yanzu kuwa ya bar ku ku tsaya a gabansa da tsarki, marasa aibi, da kuma marasa abin zargi. Sai ku ci gaba cikin bangaskiyarku, kuna tsaye a kafe kuma tsayayyu, ba tare da gusawa daga begen da kuka ji daga bishara ba. Wannan ita ce bisharar da kuka ji wadda aka yi shelarta ga kowace halittar da take ƙarƙashin sama, wadda kuma ni Bulus, na zama mai hidimarta. Yanzu, ina farin ciki saboda wuyar da nake sha dominku, don ta wurin wuyan nan zan cika abin da ya rage na wuyar da Kiristi ya sha saboda jikinsa, wato, ikkilisiya. Na zama mai hidimar ikkilisiya bisa ga aikin nan da Allah ya ba ni amana saboda ku, domin in sanar da maganar Allah sosai. Wannan magana da nake gaya muku asiri ne da yake a ɓoye tun zamanai masu yawa, wanda yanzu aka bayyana ga tsarkaka. Su ne Allah ya so yă sanar da yadda irin yalwar ɗaukakar asirin nan take a cikin al’ummai, asirin nan kuwa shi ne Kiristi a cikinku, begen ɗaukakar da za a bayyana. Saboda haka ko’ina muka tafi, muna shela, muna gargaɗi, muna kuma koyar da kowa da dukan hikima, don mu miƙa kowa cikakke a cikin Kiristi. Don haka ne ina fama, ina kuma ƙoƙari da duk ƙarfin nan da Kiristi ya ba ni. Ina so ku san irin famar da nake yi saboda ku da kuma waɗanda suke a Lawodiseya, da kuma saboda dukan waɗanda ba su taɓa ganina ido da ido ba. Manufata ita ce a ƙarfafa su su kuma zama ɗaya a cikin ƙauna. Ina so su kasance da cikakken ƙarfin hali domin suna da cikakken fahimtar asirin Allah, wato, Kiristi kansa, a cikinsa ne aka ɓoye dukkan dukiya ta hikima da ta sani. Ina faɗa muku wannan ne don kada wani yă ruɗe ku da daɗin baki. Gama ko da yake ba na nan tare da ku a cikin jiki, ina tunaninku kullum, ina kuma farin ciki da gani kuna rayuwa yadda ya kamata, kuna kuma dāgewarku a kan bangaskiyarku a cikin Kiristi. To, da yake kun karɓi Kiristi Yesu a matsayin Ubangiji, sai ku ci gaba da rayuwa a cikinsa, ku tsaya daram ku kuma ginu a cikinsa, ku sami ƙarfafawa a cikin bangaskiya kamar yadda aka koya muku, kuna kuma cike da godiya. Ku lura kada wani yă ruɗe ku da ilimin banza da wofi. Wannan koyarwa ta mutane ce kawai. Ta fito daga ikokin wannan duniya ne ba daga Kiristi ba. Gama a cikin Kiristi cikin jiki dukkan cikar Allahntaka take tabbata, an kuma mai da ku cikakku a cikin Kiristi, wanda yake shi ne kai a kan kowane iko da kuma hukuma. A cikinsa ne kuma aka yi muku kaciya, ba kuwa yin mutum ba, amma wadda Kiristi ya yi muku, ta wurin tuɓe halinku na mutuntaka. Da yake an binne ku tare da shi cikin baftisma haka kuma aka tashe ku tare da shi ta wurin bangaskiyarku a cikin ikon Allah, wanda ya tashe shi daga matattu. Kun zama matattu saboda ku masu zunubi ne kuma saboda halin zunubanku aka ware. Sa’an nan Allah ya sa kuka rayu tare da Kiristi. Ya gafarta mana dukan zunubanmu. Ya soke rubutacciyar doka tare da ƙa’idodinta, wadda take gāba da mu, take kuma hamayya da mu; ya kuma kawar da ta, ya kafe ta a kan gicciye. Bayan ya ƙwace makaman ikoki da hukumomi, ya kunyata su a sarari, ya ci nasara a bisansu ta wurin gicciye. Saboda haka kada ku bar wani yă shari’anta ku a kan abin da kuke ci ko sha, ko bisa ga abin da ya shafi wani bikin addini, ko Bikin Sabon Wata ko na ranar Asabbaci. Waɗannan su ne hoton abubuwan da za su zo; amma Kiristi ne ainihinsu. Kada ku yarda wani yă ɓata ku, cewa shi wani abu ne don yă ga wahayi. Irin mutumin nan yakan nuna ƙasƙancin kai na ƙarya, yă kuma ce yana yi wa mala’iku sujada. Irin mutumin nan yana kumbura kansa ba dalili, sai son zuciya irin na halin mutuntaka. Ya yanke dangantaka da Kiristi wanda yake kai, wanda ta gare shi ne dukan jiki yake a haɗe, yake tsaye ta wurin taimakon gaɓoɓi da jijiyoyi, yana kuma girma kamar yadda Allah yake sa yă yi girma. Kun mutu tare da Kiristi. Yanzu ƙa’idodin wannan duniya ba su da iko a kanku. Don me kuke zama har yanzu kamar ku nasu ne? Kuna biyayya da umarnansu cewa, “Kada ka kama! Kada ka ɗanɗana! Kada ka taɓa”? Irin waɗannan dokoki suna magana a kan abubuwan da ba sa daɗewa. Su ayyukan mutane ne, sun kuma fito daga koyarwar mutane. Yin biyayya da irin waɗannan ƙa’idodi za su yi kamar su ne abu mafi kyau da za a yi. Sukan yi kamar suna sa a ƙaunaci Allah sosai a kuma kasance da sauƙinkai a kuma kasance da kamunkai. Amma ba su da wani iko a kan sha’awace-sha’awacenmu. Da yake an tashe ku tare da Kiristi, sai ku sa zukatanku a kan abubuwan da suke sama, inda Kiristi yake zaune a hannun dama na Allah. Ku sa hankulanku a kan abubuwan sama, ba kan abubuwan duniya ba. Gama kun mutu, ranku yanzu kuwa yana ɓoye tare da Kiristi a cikin Allah. Sa’ad da Kiristi, wanda shi ne ranku, ya bayyana, ku ma za ku bayyana tare da shi cikin ɗaukaka. Saboda haka, sai ku fid da duk wani abin da yake kawo sha’awa a zukatanku, fasikanci, ƙazanta, sha’awa, muguwar sha’awa, da kuma kwaɗayi wanda shi ma bautar gumaka ne. Gama fushin Allah zai sauko a kan masu aikata waɗannan. Dā kun yi waɗannan abubuwa, sa’ad da rayuwar tana cikin duniya mai wannan hali. Amma yanzu dole ku raba kanku da dukan ire-iren abubuwan nan. Ku daina fushi, ku daina ƙiyayya da ƙeta. Ku bar ɓatan suna da kuma ƙazamar magana daga leɓunanku. Kada ku yi wa juna ƙarya, da yake kun tuɓe tsohon halinku tare da ayyukansa kun ɗauki sabon halin nan da ake sabuntawa ga sani, bisa ga kamannin Mahaliccinsa. A wannan sabuwar rayuwa babu bambanci ko kai mutumin Al’ummai ne ko mutumin Yahuda, mai kaciya ne ko marar kaciya, baƙo, baƙauye, bawa ne ko ’yantacce, gama Kiristi shi ne kome, kuma yana cikin kome. Da yake Allah ya mai da ku zaɓaɓɓu, tsarkaka, ƙaunatattu, sai ku dinga jin tausayin juna, kuna yin alheri, kuna nuna tawali’u da sauƙinkai da jimrewa. Ku riƙa yin haƙuri da juna kuna kuma gafarta wa juna duk wani laifin da wani ya yi muku. Ku gafarta kamar yadda Ubangiji ya gafarce ku. Fiye da waɗannan duka, ku yi ƙaunar juna, gama ƙauna ce take haɗa kome gaba ɗaya. Ku bar salamar Kiristi tă yi mulki a zukatanku, da yake a matsayin gaɓoɓin jiki ɗaya an kira ku ga salama. Ku zama masu godiya. Ku bar maganar Kiristi ta zauna a cikinku a yalwace yayinda kuke koya, kuna kuma yi wa juna gargaɗi da dukan hikima, da kuma yayinda kuke waƙoƙin zabura, waƙoƙi da waƙoƙin ruhaniya tare da godiya a zukatanku ga Allah. Kuma ko mene ne kuke yi, ko cikin magana ko cikin ayyuka, ku yi shi duka a cikin sunan Ubangiji Yesu, kuna yin godiya ga Allah Uba ta wurinsa. Mata, ku yi biyayya ga mazanku, yadda ya dace cikin Ubangiji. Maza, ku ƙaunaci matanku kada ku nuna musu hali marar tausayi. ’Ya’ya, ku yi biyayya ga iyayenku cikin kome, gama wannan yakan gamshi Ubangiji. Ubanni, kada ku matsa wa yaranku lamba, don kada su fid da zuciya. Bayi, ku yi biyayya ga iyayengijinku na duniya cikin kome; kada ku yi aikin ganin ido kamar masu neman yabon mutane, sai dai ku yi aiki tsakaninku da Allah, kamar masu tsoron Ubangiji. Kome kuke yi, ku yi shi da dukan zuciyarku, sai ka ce ga Ubangiji kuke yi, ba ga mutum ba. Kun san cewa zai ba ku gādo a matsayin ladanku. Ubangiji Kiristi ne fa kuke bauta wa. Duk wanda ya yi laifi, za a sāka masa don laifinsa, babu sonkai. Masu bayi, ku riƙe bayinku da kyau da kuma daidai, domin kun san cewa ku ma kuna da Ubangiji a sama. Ku nace da yin addu’a, kuna zaman tsaro da kuma godiya. Ku kuma yi mana addu’a, mu ma, don Allah yă buɗe ƙofa saboda saƙonmu, don mu iya yin shelar asirin Kiristi, wanda saboda shi nake cikin sarƙoƙi. Ku yi addu’a yadda zan yi shelarsa, yadda ya kamata. Ku zama masu hikima a yadda kuke ma’amala da waɗanda suke ba masu bi ba; ku kuma yi amfani da kowane zarafi. Bari maganarku kullum ta zama da ladabi da kuma daɗin ji, domin ku san amsar da ta dace ku ba wa kowa. Tikikus shi ne ƙaunataccen ɗan’uwan nan, wanda ya yi aiki da aminci a hidimar Ubangiji tare da mu, zai kuwa faɗa muku dukan labari game da ni. Ina aikansa shi a gare ku musamman domin ku san yadda muke, yă kuma ƙarfafa muku zuciya. Yana zuwa tare da Onesimus, ƙaunatacce da kuma amintaccen mai bin nan, wanda yake ɗaya daga cikinku. Za su gaya muku dukan abin da yake faruwa a nan. Aristarkus yana a kurkuku tare da ni. Yana gaishe ku, haka ma Markus, wanda kakansa ɗaya ne da Barnabas. (Shi ne na riga na yi magana a kansa, na ce muku in ya zo, ku karɓe shi hannu biyu-biyu.) Yesu, wannan da muke kira Yustus, shi ma yana gaisuwa. Waɗannan ne kaɗai Yahudawa masu bi a cikin abokan aikina saboda mulkin Allah. Sun kuma zama da taimako a gare ni. Efafaras naku, mai hidimar Kiristi Yesu, yana gaisuwa. Kullum yana addu’a dominku sosai, don ku san cikakken abin da Allah yake so ku yi don kuma ku yi shi cikakke. Na tabbatar muku, cewa yana aiki ƙwarai dominku da kuma domin waɗanda suke a Lawodiseya da Hiyerafolis. Luka ƙaunataccen likitan nan, da kuma Demas suna gaishe ku. Ku miƙa gaisuwata ga ’yan’uwan da suke a Lawodiseya, musamman ga Nimfa da kuma ikkilisiyar da take taru a gidanta. Bayan an karanta muku wannan wasiƙa, ku tabbata an karanta ta kuma a ikkilisiyar Lawodiseyawa; ku ma ku karanta wasiƙar da ta zo daga Lawodiseya. Ku faɗa wa Arkiffus yă tabbata ya ƙarasa aikin da ya karɓa cikin Ubangiji. Ni Bulus ne nake rubuta muku wannan gaisuwa da hannuna. Ku tuna da sarƙoƙina. Alherin Allah yă kasance tare da ku. Bulus, Sila da Timoti, Zuwa ga ikkilisiyar Tessalonikawa ta Allah Uba da Ubangiji Yesu Kiristi. Alheri da salama su kasance tare da ku. Kullum muna gode wa Allah dominku duka, muna ambatonku cikin addu’o’inmu. Muna tunawa da aikinku ba fasawa a gaban Allah da Ubanmu ta wurin bangaskiya, da famar da kuke yi domin ƙauna, da kuma begenku marar gushewa ga Ubangijinmu Yesu Kiristi. Gama mun sani, ’yan’uwa, ƙaunatattu na Allah, cewa ya zaɓe ku, domin bishararmu ba tă zo gare ku da kalmomi kawai ba, amma da iko, da Ruhu Mai Tsarki, da kuma cikakken tabbaci. Kun san irin rayuwar da muka yi a cikinku don amfaninku. Har kuka zama masu koyi da mu da kuma Ubangiji; duk da tsananin wahala, kuka karɓi saƙon nan da farin ciki wanda Ruhu Mai Tsarki ya bayar. Ta haka kuwa kuka zama gurbi ga dukan masu bi a Makidoniya da Akayya. Saƙon Ubangiji ya fito daga gare ku ne ba a Makidoniya da Akayya kaɗai ba bangaskiyarku ga Allah ta zama sananne ko’ina. Saboda haka ba ma bukata mu faɗa wani abu a kai, gama su kansu su suke ba da labari irin karɓar da kuka yi mana. Suna faɗin yadda kuka juyo ga Allah daga gumaka don ku bauta wa Allah rayayye da kuma na gaskiya, ku kuma jira dawowar Ɗansa daga sama, wanda ya tasa daga matattu, Yesu, wanda ya cece mu daga fushi mai zuwa. Kun sani, ’yan’uwa, cewa ziyararmu a gare ku ba tă zama a banza ba. Mun riga mun sha wahala, aka kuma zage mu a Filibbi, kamar yadda kuka sani, amma da taimakon Allahnmu muka yi ƙarfin hali muka sanar muku bishararsa duk da matsananciyar gāba. Gama roƙon da muke yi bai fito daga kuskure ko munafunci ba, ba kuwa ƙoƙari muke yi mu yaudare ku ba. A maimako haka, muna magana ne kamar mutanen da Allah ya amince yă danƙa musu amanar wannan bishara. Ba ma ƙoƙari mu gamshi mutane sai dai Allah, mai auna zukatanmu. Kun san ba ma taɓa yin daɗin baki ko mu yi ƙoƙarin kasance da halin kwaɗayin da muke ɓoyewa, Allah shi ne shaidarmu. Ba ma neman yabo daga wurin mutane, ko a gare ku, ko ga waɗansu. A matsayinmu na manzannin Kiristi da mun so, da mun nawaita muku, amma muka kasance masu sauƙinkai a cikinku, kamar yadda mahaifiya take lura da ƙananan ’ya’yanta. Muka ƙaunace ku ƙwarai har muka ji daɗin bayyana muku, ba bisharar Allah kaɗai ba amma har rayukanmu ma, domin kun zama ƙaunatattu a gare mu. Ba shakka kuna iya tunawa, ’yan’uwa, famarmu da kuma wahalarmu; mun yi aiki dare da rana don kada mu zama nauyi wa wani yayinda muke muku wa’azin bisharar Allah. Ku shaidu ne, haka ma Allah, na yadda muka yi zaman tsarki, adalci da kuma marar aibi a cikinku, ku da kuka ba da gaskiya. Gama kun san cewa mun bi da kowannenku yadda mahaifi yakan yi da ’ya’yansa, muna ƙarfafa ku, muna ta’azantar da ku, muna kuma gargaɗe ku ku yi rayuwar da za tă cancanci Allah, wanda ya kira ku zuwa mulkinsa da kuma ɗaukakarsa. Muna kuma gode wa Allah ba fasawa domin, sa’ad da kuka karɓi maganar Allah, wadda kuka ji daga gare mu, kun karɓe ta ba kamar maganar mutane ba, sai dai kamar yadda take, maganar Allah wadda take aiki a cikinku ku da kuka ba da gaskiya. Gama ku, ’yan’uwa, kun zama masu koyi da ikkilisiyoyin Allah a Yahudiya waɗanda suke cikin Kiristi Yesu. Kun sha wahala a hannun mutanen ƙasarku kamar yadda ikkilisiyoyin nan ma suka sha a hannun Yahudawa, waɗanda suka kashe Ubangiji Yesu da annabawa suka kuma kore mu. Ba sa yin aikin da Allah yake so, masu gāba ne kuwa da dukan mutane suna ƙoƙarin hana mu yin magana ga Al’ummai don kada su sami ceto. Ta haka kullum suke ƙara tara tsibin zunubansu. Fushin Allah ya aukar musu a ƙarshe. Amma, ’yan’uwa, sa’ad da aka raba mu da ku na ɗan lokaci (a jiki, ba a tunani ba), daga cikin marmarinmu mai tsanani mun yi duk abin da muke iya yi mu gan ku. Gama mun so mu zo wurinku, tabbatacce ni, Bulus, na yi ƙoƙari sau da sau, amma Shaiɗan ya hana mu. Gama mene ne begenmu, farin cikinmu, ko kuma rawanin da zai zama mana abin ɗaukaka a gaban Ubangijinmu Yesu sa’ad da ya dawo? Ba ku ba ne? Tabbatacce, ku ne ɗaukakarmu da kuma farin cikinmu. Saboda haka da muka kāsa daurewa, sai muka ga ya fi kyau a bar mu a Atens mu kaɗai. Muka aiki Timoti, wanda yake ɗan’uwanmu da kuma abokin aikin Allah a cikin yaɗa bisharar Kiristi, don yă gina ku yă kuma ƙarfafa ku cikin bangaskiyarku, don kada kowa yă raunana ta wurin waɗannan gwaje-gwajen. Kun sani sarai cewa an ƙaddara mu don waɗannan. Gaskiyar ita ce, sa’ad da muke tare da ku, mun sha gaya muku cewa za a tsananta mana. Haka kuwa ya faru, kamar dai yadda kuka sani. Saboda wannan, sa’ad da ban iya jimrewa ba, sai na aika domin in sami labarin bangaskiyarku, da fata kada yă zama mai jarraban nan ya riga ya jarrabce ku, ƙoƙarinmu kuma yă zama banza. Amma ga shi yanzu Timoti ya dawo mana daga wurinku ya kuma kawo labari mai daɗi game da bangaskiyarku da kuma ƙaunarku. Ya faɗa mana yadda kullum kuke da tunani mai kyau a kanmu, yadda kuke marmari ku gan mu, kamar dai yadda mu ma muke marmari mu gan ku. Saboda haka ’yan’uwa, cikin dukan damuwarmu da tsananinmu an ƙarfafa mu game da ku saboda bangaskiyarku. Gama yanzu tabbatacce muna da rai, da yake kuna nan tsaye daram a cikin Ubangiji. Wace irin godiya ce za mu yi wa Allah saboda ku a kan dukan farin cikin da muke da shi a gaban Allahnmu ta dalilinku? Dare da rana muna addu’a da himma domin mu sāke ganinku, mu kuma ba ku abin da kuka rasa a bangaskiyarku. Yanzu bari Allahnmu da Ubanmu kansa da kuma Ubangijinmu Yesu yă shirya mana hanya mu zo wurinku. Ubangiji yă sa ƙaunarku ta ƙaru ta kuma yalwata ga juna da kuma ga kowa, kamar yadda tamu take muku. Bari yă ƙarfafa zukatanku har ku zama marasa aibi da kuma tsarkaka a gaban Allahnmu da Ubanmu sa’ad da Ubangijimmu Yesu ya dawo tare da dukan tsarkakansa. A ƙarshe, ’yan’uwa, mun umarce ku yadda za ku yi rayuwa domin ku gamshi Allah, kamar yadda kuke yi. Yanzu muna roƙonku muna kuma gargaɗe ku a cikin Ubangiji Yesu ku yi haka sau da sau. Gama kun san umarnan da muka ba ku ta wurin ikon Ubangiji Yesu. Nufin Allah ne a tsarkake ku, cewa ku guje wa fasikanci; don kowannenku yă koya yadda zai ƙame kansa a hanyar da take mai tsarki, mai mutunci kuma, ba cikin muguwar sha’awa kamar ta marasa bangaskiya, waɗanda ba su san Allah ba; cikin wannan al’amari kuwa kada wani yă yi wa ɗan’uwansa laifi ko yă cuce shi. Ubangiji zai hukunta mutane saboda dukan irin waɗannan zunubai, kamar yadda muka riga muka gaya muku, muka kuma yi muku gargaɗi. Gama Allah bai kira mu ga zaman marasa tsarki ba, sai dai ga zaman tsarki. Saboda haka, duk wanda ya ƙi wannan umarni ba mutum ne ya ƙi ba sai ko Allah, wanda ya ba ku Ruhunsa Mai Tsarki. Yanzu kuwa game da ƙaunar ’yan’uwa, ba ma bukata mu rubuta muku, gama ku kanku Allah ya riga ya koya muku ku ƙaunaci juna. Gaskiyar kuwa ita ce, kuna ƙaunar dukan ’yan’uwa ko’ina a Makidoniya. Duk da haka muna ƙara gargaɗe ku, ’yan’uwa, ku yi haka sau da sau. Ku mai da wannan burinku na yi natsattsiyar rayuwa, kuna mai da hankali ga sha’anin da yake gabanku, kuna kuma yin aiki da hannuwanku, kamar dai yadda muka gaya muku, don rayuwanku ta kullum ta zama da mutunci ga waɗanda suke na waje don kuma kada ku dogara a kan kowa. ’Yan’uwa, ba ma so ku kasance cikin jahilci game da waɗanda suka yi barci, ko kuwa ku yi baƙin ciki kamar sauran mutanen da ba su da bege. Mun gaskata cewa Yesu ya mutu ya tashi kuma daga matattu, ta haka muka gaskata cewa Allah zai kawo waɗanda suka yi barci a cikinsa tare da Yesu. Bisa ga maganar Ubangiji kansa, muna gaya muku cewa mu da muke raye har yanzu, waɗanda aka bari har dawowar Ubangiji, tabbatacce ba za mu riga waɗanda suka yi barci tashi ba. Gama Ubangiji kansa zai sauko daga sama, da umarni mai ƙarfi, da muryar babban mala’ika da kuma busar ƙahon Allah, waɗanda suka mutu kuwa cikin Kiristi za su tashi da farko. Bayan haka, mu da muke da rai da aka bari, za a ɗauke mu tare da su a cikin gizagizai don mu sadu da Ubangiji a sararin sama. Ta haka za mu kasance tare da Ubangiji har abada. Saboda haka ku ƙarfafa juna da waɗannan kalmomi. To, ’yan’uwa, game da lokuta da ranaku, ba ma bukata mu rubuta muku, gama kun sani sarai cewa ranar Ubangiji za tă zo kamar ɓarawo da dare. Yayinda mutane suke cewa, “Akwai salama da zaman lafiya,” hallaka za tă auko musu farat ɗaya, kamar yadda naƙuda take kama mace mai ciki, ba za su kuwa tsira ba. Amma ku, ’yan’uwa, ba kwa cikin duhu da wannan rana za tă zo muku ba zato kamar ɓarawo. Dukanku ’ya’yan haske ne da kuma ’ya’yan rana. Mu ba mutanen dare ko na duhu ba ne. Saboda haka fa, kada mu zama kamar saura, waɗanda suke barci, sai dai mu zama masu tsaro da masu kamunkai. Gama masu barci, da dad dare suke barci, masu sha su bugu kuwa, da dad dare suke buguwa. Amma da yake mu na rana ne, bari mu zama masu kamunkai, sanye da bangaskiya da ƙauna kamar sulke, begen cetonmu kuma kamar hular kwano. Gama Allah bai naɗa mu don mu sha fushi ba, sai dai mu sami ceto ta wurin Ubangijinmu Yesu Kiristi. Ya mutu saboda mu domin, ko muna a faɗake ko muna barci, mu kasance tare da shi. Saboda haka ku ƙarfafa juna ku kuma gina juna, kamar dai yadda kuke yi. To, muna roƙonku, ’yan’uwa, ku girmama waɗanda suke aiki sosai a cikinku, waɗanda suke bisanku cikin Ubangiji da kuma waɗanda suke yin muku gargaɗi. Ku riƙe su da mutunci sosai cikin ƙauna saboda aikinsu. Ku yi zaman lafiya da juna. Muna kuma gargaɗe ku, ’yan’uwa, ku gargaɗe waɗanda suke zaman banza, ku ƙarfafa masu raunanar zuciya, ku taimaki marasa ƙarfi, ku yi haƙuri da kowa. Ku tabbata cewa kada kowa yă rama mugunta da mugunta, sai dai kullum ku yi ƙoƙarin yin wa juna alheri da kuma dukan mutane. Ku riƙa farin ciki kullum; ku ci gaba da yin addu’a; ku yi godiya cikin kowane hali, gama wannan shi ne nufin Allah dominku cikin Kiristi Yesu. Kada ku danne aikin Ruhu. Kada ku rena annabci, amma ku gwada kome, ku riƙe abin da yake mai kyau, ku ƙi kowace mugunta. Bari Allah da kansa, Allah na salama, yă tsarkake ku sarai. Bari dukan ruhunku, ranku, da kuma jikinku su zama marar aibi a dawowar Ubangijinmu Yesu Kiristi. Wannan wanda ya kira ku mai aminci ne zai kuwa aikata. ’Yan’uwa, ku yi mana addu’a. Ku gaggai da dukan ’yan’uwa da sumba mai tsarki. Na gama ku da Ubangiji ku sa a karanta wannan wasiƙa ga dukan ’yan’uwa. Alherin Ubangijinmu Yesu Kiristi yă kasance tare da ku. Bulus, da Sila, da Timoti, Zuwa ga ikkilisiya ta Tessalonikawa ta Allah Ubanmu da Ubangiji Yesu Kiristi. Alheri da salama daga Allah Uba da kuma Ubangiji Yesu Kiristi, su kasance tare da ku. Dole kullum mu gode wa Allah saboda ku, ’yan’uwa, haka kuwa ya dace, domin bangaskiyarku tana girma gaba-gaba, ƙaunar da kowannenku yake yi wa juna kuwa tana ƙaruwa. Saboda haka, a cikin ikkilisiyoyin Allah muna taƙama game da daurewarku da kuma bangaskiyarku cikin dukan tsanani da gwaje-gwajen da kuke sha. Dukan wannan yana tabbatar cewa hukuncin Allah daidai ne, saboda haka kuma za a lissafta ku a kan kun cancanci mulkin Allah, wanda dominsa ne kuke shan wahala. Allah mai adalci ne, Zai sāka wa masu ba ku wahala da wahala yă kuma sauƙaƙa muku ku da kuke wahala, har ma da mu. Wannan zai faru sa’ad da aka bayyana Ubangiji Yesu daga sama cikin wuta mai ci tare da mala’ikunsa masu iko. Zai hukunta waɗanda ba su san Allah ba da kuma waɗanda ba su yi biyayya da bisharar Ubangijinmu Yesu ba. Za a hukunta su da madawwamiyar hallaka a kuma kau da su daga gaban Ubangiji da kuma daga ɗaukakar ikonsa a ranar da zai dawo don a ɗaukaka shi a cikin mutanensa masu tsarki, yă kuma zama abin banmamaki ga dukan waɗanda suka gaskata. Wannan ya haɗa har da ku, domin kun gaskata shaidar da muka yi muku. Sane da wannan, kullum muna addu’a saboda ku, don Allahnmu yă sa ku cancanci kiransa, ta wurin ikonsa kuma yă cika kowace manufarku mai kyau da kuma kowane aikin da bangaskiyarku ta iza. Muna wannan addu’a don sunan Ubangijinmu Yesu yă sami ɗaukaka a cikinku, ku kuma a cikinsa, bisa ga alherin Allahnmu da na Ubangiji Yesu Kiristi. Game da dawowar Ubangijinmu Yesu Kiristi da game da tattara mu gare shi, muna roƙonku, ’yan’uwa, kada ku yi saurin jijjiguwa ko kuwa hankalinku yă tashi ta wurin wani annabci, rahoto ko wasiƙar da an ce daga wurinmu ne, cewa ranar Ubangiji ta riga ta zo. Kada ku bar wani yă ruɗe ku ko ta yaya, gama wannan rana ba za tă zo ba sai an yi tawayen nan an kuma bayyana mutumin tawayen nan, mutumin da aka ƙaddara ga hallaka. Zai yi gāba yă kuma ɗaukaka kansa a bisa kome da ya shafe sunan Allah, ko kuma ake yi wa sujada, domin yă kafa kansa a haikalin Allah, yana shelar kansa a kan shi Allah ne. Ba ku tuna ba cewa sa’ad da nake tare da ku nakan gaya muku waɗannan abubuwa? Yanzu kuwa kun san abin da yake hana shi, wannan yana faruwa ne don a bayyana shi a daidai lokaci. Gama ikon asirin tawaye ya riga ya fara aiki; sai dai wannan da yake hana shi zai ci gaba da yin haka sai an kau da shi. Sa’an nan za a bayyana mai tawayen, Ubangiji Yesu kuwa zai hamɓare shi da numfashin bakinsa yă kuma hallaka shi da darajar dawowarsa. Zuwan mai tawayen nan zai zama ta wurin aikin Shaiɗan da aka bayyana cikin kowane irin ayyukan banmamaki, alamu da abubuwan banmamaki na ƙarya, da kuma cikin kowace irin muguntar da take ruɗin waɗanda suke hallaka. Sun hallaka ne domin sun ƙi su ƙaunaci gaskiya don su sami ceto. Saboda haka Allah zai aiko musu da babban ruɗu don su gaskata ƙarya don kuma a hukunta dukan waɗanda ba su gaskata gaskiyar ba sai dai suke jin daɗin mugunta. Amma dole kullum mu gode wa Allah dominku, ’yan’uwa waɗanda Ubangiji ya ƙaunace, domin daga farko Allah ya zaɓe ku don a cece ku ta wurin aikin tsarkakewar Ruhu da kuma ta wurin gaskatawa da gaskiya. Ya kira ku ga wannan ta wurin bishararmu, don ku sami rabo a cikin ɗaukakar Ubangijinmu Yesu Kiristi. Saboda haka fa, ’yan’uwa, sai ku tsaya daram ku riƙe koyarwar da muka miƙa muku, ko ta wurin maganar baki ko kuma ta wurin wasiƙa. Ubangijinmu Yesu Kiristi kansa da kuma Allah Ubanmu, wanda ya ƙaunace mu kuma ta wurin alherinsa yă ba mu madawwamiyar ƙarfafawa da kyakkyawar bege, yă ƙarfafa zukatanku yă kuma gina ku cikin kowane aikin nagari da kuma magana. A ƙarshe, ’yan’uwa, ku yi mana addu’a domin saƙon Ubangiji yă yi saurin bazuwa a kuma girmama shi, kamar yadda yake a wurinku. Ku kuma yi addu’a yadda za a cece mu daga mugayen mutane masu mugunta, gama ba kowa ba ne yake da bangaskiya. Ubangiji mai aminci ne, zai ƙarfafa ku, yă kuma tsare ku daga mugun nan. Muna da tabbaci cikin Ubangiji cewa kuna bin umarnai da muka yi muku, za ku kuma ci gaba da yin abubuwan da muka umarta. Bari Ubangiji yă bi da zukatanku ga ƙaunan nan ta Allah da kuma jimirin nan na Kiristi. A cikin sunan Ubangiji Yesu Kiristi, muna muku umarni, ’yan’uwa, da ku kiyaye kanku daga kowane ɗan’uwa mai zaman banza da ba ya rayuwa bisa ga koyarwar da kuka karɓa daga wurinmu. Gama ku kanku kun san yadda ya kamata ku bi gurbinmu. Ba mu yi zaman banza sa’ad da muke tare da ku ba, ba mu kuwa ci abincin kowa ba tare da ba mu biya ba. A maimakon haka, mun yi aiki dare da rana, muna fama muna wahala kuma don kada mu nawaita wa waninku. Mun yi wannan, ba don ba mu da ’yancin karɓar irin taimakon nan ba ne, sai dai domin mu zama gurbin da za ku bi. Ko ma a sa’ad da muke tare da ku, mun ba ku wannan umarni cewa, “In mutum ya ƙi yin aiki, kada a ba shi abinci.” Mun ji cewa waɗansunku suna zaman banza. Ba sa aikin kome; sai shisshigi kurum. Irin waɗannan mutane muna ba da umarni muna kuma gargaɗe su cikin Ubangiji Yesu Kiristi su natsu su kuma nemi abincin da suke ci. Game da ku kuma ’yan’uwa, kada ku gaji da yin abin da yake daidai. In wani bai yi biyayya da umarninmu a wannan wasiƙa ba, sai fa ku lura da shi. Kada ku haɗa kai da shi, don yă ji kunya. Duk da haka kada ku mai da shi abokin gāba, sai dai ku gargaɗe shi a matsayin ɗan’uwa. Yanzu, bari Ubangiji mai salama kansa yă ba ku salama a kowane lokaci da kuma a ta kowace hanya. Ubangiji yă kasance tare da ku duka. Ni, Bulus, nake rubuta wannan gaisuwa da hannuna, wannan ce shaida a kowace wasiƙata, haka nake rubutu. Alherin Ubangijinmu Yesu Kiristi yă kasance tare da ku duka. Bulus, manzon Kiristi Yesu ta wurin umarnin Allah Mai Cetonmu da kuma na Yesu Kiristi begenmu, Zuwa ga Timoti ɗana na gaske cikin bangaskiya. Alheri, jinƙai da kuma salama daga Allah Uba da Kiristi Yesu Ubangijinmu, su kasance tare da kai. Kamar yadda na gargaɗe ka sa’ad da zan je Makidoniya, ka zauna can Afisa domin ka umarci waɗansu mutane kada su koyar da ƙa’idodin ƙarya nan gaba ko su ba da kansu ga tatsuniyoyi da ƙididdigar asali marar iyaka. Waɗannan suna kawo faɗa a maimakon aikin Allah wanda yake ta wurin bangaskiya. Maƙasudin wannan umarnin dai ƙauna ce, wadda take zuwa daga zuciya mai tsabta da lamiri mai kyau da kuma sahihiyar bangaskiya. Waɗansu sun bauɗe daga waɗannan al’amura, suka koma ga maganganu marasa ma’ana. So suke su zama malaman doka, ba tare da fahimtar abin da suke faɗa ba, balle abubuwan da suke ta nacewa a kai. Mun san cewa doka tana da kyau in an yi amfani da ita yadda ya kamata. Mun kuma san cewa an yi doka ba domin masu adalci ba sai dai masu tawaye, da marasa biyayya, da marasa bin Allah, da masu zunubi, da marasa tsarkaka, da masu saɓon Allah, da masu kashe iyaye maza da mata, da masu kisankai, da masu zina da kuma da maza masu kwana da maza, ko mata masu kwana da mata, da masu cinikin bayi da masu ƙarya da kuma masu shaidar ƙarya, da kuma duk wani abin da ya saɓa wa sahihiyar koyarwa, da take bisa ga bishara mai ɗaukaka ta Allah mai albarka, wadda ya danƙa mini. Na gode wa Kiristi Yesu Ubangijinmu, wanda ya ba ni ƙarfi, saboda ya amince da ni, har ya sa ni aikinsa. Ko da yake a dā ni mai saɓo da mai tsanantawa da kuma mai rikici ne, aka nuna mini jinƙai saboda na yi haka cikin jahilci ne da kuma rashin bangaskiya. An zubo mini alherin Ubangijinmu a yalwace, tare da bangaskiya da ƙaunar da take cikin Kiristi Yesu. Ga wata magana tabbatacciya wadda ta cancanci cikakkiyar karɓa. Kiristi Yesu ya zo duniya domin ceton masu zunubi, wanda nake mafi muni a cikinsu. Amma saboda wannan dalilin ne aka nuna mini jinƙai domin ta wurina, mafi zunubi duka, Kiristi Yesu yă iya bayyana matuƙar haƙurinsa a matsayin misali ga waɗanda za su gaskata shi su kuma sami rai madawwami. Bari girma da ɗaukaka su tabbata har abada abadin ga Sarki madawwami, wanda ba ya mutuwa, wanda ba a ganinsa, wanda kuma shi ne kaɗai Allah! Amin. Timoti, ɗana, na ba ka wannan umarni bisa ga annabce-annabcen da aka yi a dā game da kai, domin ta wurin binsu ka iya yin yaƙi mai kyau, kana riƙe da bangaskiya da kuma lamiri mai kyau. Gama waɗansu mutane, saboda ƙin kasa kunne ga lamirinsu, suka lalatar da bangaskiyarsu. Cikinsu kuwa akwai Himenayus da Alekzanda, waɗanda na miƙa ga Shaiɗan don su horo su bar yin saɓo. Da farko dai, ina gargaɗe ku cewa a yi roƙe-roƙe, ana addu’o’i, ana yin addu’a a madadin waɗansu da kuma a yi godiya saboda kowane mutum da sarakuna da dukan masu mulki, domin mu zauna lafiya, rai kuma kwance, muna bin Allah sosai a cikin natsuwa. Wannan yana da kyau, yakan kuma gamshi Allah Mai Cetonmu, wanda yake so dukan mutane su sami ceto su kuma zo ga sanin gaskiya. Gama Allah ɗaya ne, matsakanci kuma ɗaya tsakanin Allah da mutane, shi ne kuwa Kiristi Yesu, wanda ya ba da kansa fansa domin dukan mutane, shaidar da aka bayar a daidai lokaci. Don haka ne aka sa ni mai wa’azi, da manzo kuma, gaskiya nake faɗa, ba ƙarya ba, na kuma zama malami mai koya wa al’ummai al’amarin bangaskiya da kuma na gaskiya. Ina so maza a ko’ina su ɗaga hannuwansu masu tsarki cikin addu’a, ba tare da fushi ko faɗa ba. Ina kuma so mata su lura su yi wa kansu adon da ya cancanta, da rigunan da suka dace, ba da adon kitso ko sa kayan zinariya ko lu’ulu’u ko kuma tufafi masu tsada ba, sai dai su yi ayyuka masu kyan da suka dace da matan da suke masu bauta wa Allah. Ya kamata mace ta riƙa koyo cikin natsuwa da cikakkiyar biyayya. Ban ba mace izini ta koyar ko tă yi mulki a kan namiji ba; sai dai ta zauna shiru. Gama Adamu ne aka fara halitta, sa’an nan Hawwa’u. Ba kuma Adamu ne aka yaudara ba; macen ce aka yaudara ta kuma zama mai zunubi. Amma mata Za tă sami ceto za su sami ceto ta wurin haihuwa, in suka ci gaba cikin bangaskiya, ƙauna da kuma tsarki tare da halin sanin ya kamata. Ga wata tabbatacciyar magana. In wani ya sa zuciyarsa a kan zama mai kula da ikkilisiya, yana marmarin yin aiki mai daraja ne. To, dole mai kula da Ikkilisiya yă kasance marar abin zargi, mijin mace guda, mai sauƙinkai, mai kamunkai, wanda ake girmama, mai karɓan baƙi, mai iya koyarwa, ba mai buguwa ba, ba mai rikici ba sai dai mai hankali, ba mai yawan faɗa ba, ba kuma mai yawan son kuɗi ba. Dole yă iya tafiyar da iyalinsa da kyau, yă kuma tabbata cewa ’ya’yansa suna yin masa biyayya da ladabin da ya dace. (In mutum bai san yadda zai tafiyar da iyalinsa ba, yaya zai iya kula da ikkilisiyar Allah?) Kada yă zama sabon tuba, in ba haka zai zama mai girman kai yă kuma fāɗa cikin irin hukuncin da ya fāɗo wa Iblis. Dole kuma yă kasance da shaida mai kyau ga waɗanda suke na waje, don kada yă zama abin kunya yă kuma fāɗa cikin tarkon Iblis. Haka masu hidima a cikin ikkilisiya; su ma, su zama maza da sun cancanci girmamawa, masu gaskiya, ba masu yawan shan ruwan inabi ba, ba masu kwaɗayin ƙazamar riba ba. Dole su riƙe asirin bangaskiya su kuma kasance da lamiri mai tsabta. Dole a fara gwada su tukuna; sa’an nan in ba a sami wani abin zargi game da su ba, sai su shiga aikin masu hidima. A haka kuma, dole matansu su zama matan da suka cancanci girmamawa, ba masu gulma ba, sai dai masu sauƙinkai da kuma masu aminci a cikin kome. Dole mai hidimar ikkilisiya yă zama mijin mace guda dole kuma yă iya tafiyar da ’ya’yansa da kuma iyalinsa da kyau. Waɗanda suke hidima da kyau suna samar wa kansu kyakkyawan suna da kuma cikakken tabbatarwa a cikin bangaskiyarsu cikin Kiristi Yesu. Ko da yake ina sa zuciya zo wurinka nan ba da daɗewa ba, ina rubuta muka waɗannan umarnai domin, in na yi jinkiri, za ka san yadda ya kamata mutane su tafiyar da halayensu a cikin jama’ar Allah, wadda take ikkilisiyar Allah rayayye, ginshiƙi da kuma tushen gaskiya. Ba shakka, asirin addini da girma yake. Ya bayyana cikin jiki, Ruhu ya nuna shi adali ne, mala’iku suka gan shi, aka yi wa’azinsa cikin al’ummai, aka gaskata shi a duniya, aka ɗauke shi sama cikin ɗaukaka. Ruhu a sarari ya faɗa cewa a kwanakin ƙarshe waɗansu za su watsar da bangaskiya su bi ruhohi masu ruɗu da kuma abubuwan da aljanu suke koyarwa. Irin koyarwan nan tana zuwa ne daga waɗansu munafukai maƙaryata, waɗanda aka yi wa lamirinsu kaca-kaca. Suna hana mutane yin aure suna kuma umarce su kada su ci waɗansu irin abinci, waɗanda Allah ya halitta don waɗanda suka gaskata suka kuma san gaskiya, su karɓa da godiya. Gama duk abin da Allah ya halitta yana da kyau, kada kuma a ƙi kome in dai an karɓe shi da godiya, domin an tsarkake shi ta wurin maganar Allah da kuma addu’a. In ka nuna wa ’yan’uwa waɗannan abubuwa, za ka zama mai hidima mai kyau na Kiristi Yesu, wanda aka goya cikin gaskiyar bangaskiya da kuma koyarwa mai kyau wadda ka bi. Ka kiyaye kanka daga tatsuniyoyi na rashin tsoron Allah da labaru banza na tsofaffin mata; a maimako, ka hori kanka ga zama mai tsoron Allah. Gama horon jiki yana da amfani, amma tsoron Allah yana da amfani ga kowane abu, yana da albarka ga rai na yanzu da kuma rai mai zuwa. Wannan magana tabbatacciya ce wadda ta cancanci cikakkiyar karɓa. Saboda wannan kuwa muke wahala da kuma fama, domin mun sa begenmu ga Allah mai rai, wanda yake Mai Ceton dukan mutane, musamman na waɗanda suka ba da gaskiya. Ka umarta ka kuma koyar da waɗannan abubuwa. Kada ka bar wani yă rena ka domin kai matashi ne, sai dai ka zama gurbi ga masu bi cikin magana, cikin rayuwa, cikin ƙauna, cikin bangaskiya da kuma cikin zaman tsarki. Kafin in zo, ka ci gaba da karanta wa mutane Nassi, da yin wa’azi, da kuma koyarwa. Kada ka yi sakaci da baiwarka, wadda aka ba ka ta wurin saƙon annabci sa’ad da ƙungiyar dattawa suka ɗibiya hannuwa a kanka. Ka yi ƙwazo cikin waɗannan batuttuwa; ka ba da kanka gaba ɗaya gare su, don kowa yă ga ci gabanka. Ka kula da rayuwarka da kuma koyarwarka da kyau. Ka daure a cikinsu, domin in ka yi, za ka ceci kanka da kuma masu sauraronka. Kada ka tsawata wa dattijo, sai dai ka gargaɗe shi a matsayinka. Ka ɗauki samari a matsayin ’yan’uwanka, tsofaffin mata kuwa sai ka ce uwaye, ’yan mata kuma a matsayin ’yan’uwa da matuƙar tsarki. Ka girmama gwauraye waɗanda suke cikin bukata ta ainihi. Amma in gwauruwa tana da ’ya’ya ko jikoki, to, sai su fara koyon yin ayyukan addininsu ga danginsu, ta haka za su sāka wa iyayensu da kakanninsu, gama wannan yakan gamshi Allah. Gwauruwa wadda ba ta da kowa da zai taimake ta, za tă sa zuciyarta ga Allah, tana roƙo da addu’o’i dare da rana gare shi don taimako. Amma gwauruwar da take zaman jin daɗi, matacciya ce tun tana da rai. Ka umarce su game da waɗannan abubuwa, don su kasance marasa abin zargi. In wani bai kula da danginsa ba, musamman iyalinsa na kurkusa, ya mūsunta bangaskiya ke nan, ya kuma fi marar ba da gaskiya muni. Kada a lasafta gwauruwa cikin jerin gwauraye sai ta wuce shekara sittin, ta kuma yi zaman aminci ga mijinta, aka kuma santa sosai saboda ayyuka masu kyau, kamar renon ’ya’ya, da karɓan baƙi, tana yi wa tsarkaka hidima, tana taimakon waɗanda suke cikin wahala tana kuma ba da kanta ga yin kowane aikin mai kyau. Game da gwauraye masu ƙuruciya kuwa, kada ka sa su cikin wannan lissafi. Gama sa’ad da sha’awar jikinsu ta kāsa daurewa game da wa’adin da suka yi da Kiristi, sai su so yin aure. Ta haka suna jawo wa kansu hukunci, saboda sun karya alkawarinsu na farko. Ban da haka, sukan koyi zaman banza, suna zirga-zirga gida-gida. Ba kawai sun zama masu zaman banza ba, har ma sun zama masu gulma da masu shisshigi, suna faɗin abubuwan da bai kamata su faɗa ba. Saboda haka ina ba wa gwauraye masu ƙuruciya shawara su yi aure, su sami ’ya’ya, su lura da gidajensu kada kuwa su ba abokin gāba zarafin ɓata suna. Waɗansu dai sun riga sun bauɗe sun bi Shaiɗan. In mace mai bi tana da gwauraye a iyalinta, ya kamata tă taimake su, kada tă bar wa ikkilisiya wannan nauyi, domin ikkilisiya ta sami zarafin taimakon gwaurayen da suke da bukata ta ainihi. Dattawan da suka bi da al’amuran ikkilisiya da kyau sun cancanci girmamawa ninki biyu, musamman waɗanda aikinsu wa’azi ne da kuma koyarwa. Gama Nassi ya ce, “Kada ka sa wa bijimi takunkumi yayinda yake sussukar hatsi,” da kuma, “Ma’aikaci ya cancanci hakkinsa.” Kada ka saurari ƙara game da dattijo sai da shaidu biyu ko uku. Amman waɗannan dattawa waɗanda suke yin zunubi kuwa sai ka kwaɓe su a gaban jama’a, don saura su ji tsoro. Na gama ka da Allah, da Kiristi Yesu, da kuma zaɓaɓɓun mala’iku, ka kiyaye waɗannan abubuwa ƙwarai da gaske, kada ka nuna bambanci. Kada ka yi garajen ɗibiya hannuwa, kada kuma ka yi tarayya a cikin zunuban waɗansu. Ka kiyaye kanka da tsarki. Ka daina shan ruwa kaɗai, yi amfani da ruwan inabi kaɗan saboda cikinka da kuma yawan rashin lafiyarka. Zunuban waɗansu mutane a fili suke, suna shan gabansu zuwa hukunci; zunuban waɗansu kuwa sukan bi su a baya. Haka ma ayyuka nagari a fili suke, ko ba ma a fili suke ba, ba a iya ɓoye su. Duk waɗanda suke ƙarƙashin bauta, ya kamata su ɗauki iyayengijinsu a kan sun cancanci girmamawa matuƙa, don kada a ɓata sunan Allah da kuma koyarwarmu. Waɗanda suke da iyayengiji masu bi, to, kada su yi musu reni domin su ’yan’uwa ne. A maimako, sai ma su fi bauta musu, saboda waɗanda suke cin moriyar hidimarsu masu bi ne, ƙaunatattu ne kuma a gare su. Waɗannan su ne abubuwan da za ka koya musu ka kuma gargaɗe su. In wani yana koyarwar ƙarya bai kuma yarda da sahihiyar koyarwar Ubangijinmu Yesu Kiristi da kuma koyarwa ta tsoron Allah ba, yana cike da girman kai bai kuma san kome ba. Yana da mugun halin son gardama da muhawwara game da kalmomin da suke kawo kishi, rikici, maganar ƙeta, da mugayen zace-zace da yawan tankiya tsakanin mutane masu mugun hali, waɗanda aka raba su da gaskiya, suke kuma tsammani cewa bin Allah wata hanya ce ta samun kuɗi. Amma bin Allah da gamsuwa riba ce mai yawa. Gama ba mu zo duniya da kome ba, ba kuwa za mu fita daga cikinta da kome ba. In dai muna da abinci da sutura, ai, sai mu gamsu da su. Mutanen da suke son yin arziki sukan fāɗi cikin jarraba, su fāɗa a tarko, suna mugayen sha’awace-sha’awace iri-iri na wauta da cutarwa, irin waɗanda suke dulmuyar da mutane, su kai ga lalacewa da hallaka. Gama son kuɗi shi ne tushen kowane irin mugun abu. Waɗansu mutane, don tsananin son kuɗi, sun bauɗe daga bangaskiya suka kuma jawo wa kansu da baƙin ciki iri-iri. Amma kai, mutumin Allah, ka guji duk wannan, ka kuma nemi adalci, tsoron Allah, bangaskiya, ƙauna, jimrewa da kuma hankali. Ka yi fama, kyakkyawar fama ta bangaskiya. Ka riƙi rai madawwamin nan, wanda aka kira saboda shi, sa’ad da ka yi kyakkyawar shaida a gaban shaidu masu yawa. Na umarce ka, a gaban Allah mai ba da rai ga kome, da kuma Kiristi Yesu wanda yayinda yake ba da shaida a gaban Buntus Bilatus ya yi kyakkyawar shaida, ka kiyaye wannan umarni ba tare da wani aibi ko abin zargi ba har yă bayyanuwar Ubangijinmu Yesu Kiristi, wanda Allah zai kawo a daidai lokaci, Allah, mai albarka wanda yake kaɗai Mai Mulki, Sarkin sarakuna da Ubangijin iyayengiji, wanda shi kaɗai ne marar mutuwa wanda kuma yake zaune cikin hasken da ba ya kusatuwa, wanda babu wanda ya taɓa gani ko zai iya gani. A gare shi girma da iko su tabbata har abada. Amin. Ka umarci waɗanda suke da arziki a wannan duniya kada su ɗaga kai ko su sa begensu a kan dukiyar da ba ta da tabbaci, sai dai su sa begensu ga Allah, wanda yake ba mu kome a yalwace don jin daɗinmu. Ka umarce su su yi nagarta, su wadatu cikin ayyuka nagari, su kuma zama masu bayarwa hannu sake da kuma masu niyyar yin taimako. Ta haka za su ajiye wa kansu dukiya a matsayin tushen mai ƙarfi don tsara mai zuwa, don su riƙi rai wanda yake na tabbatacce. Timoti, ka lura da abin da aka danƙa maka amana. Ka yi nesa da masu maganganun rashin tsoron Allah da kuma yawan mūsu da ake ƙarya, ake ce da shi ilimi, wanda waɗansu suka furta kuma ta yin haka suka bauɗe daga bangaskiya. Alheri yă kasance tare da ku. Bulus, manzon Kiristi Yesu ta wurin nufin Allah, bisa ga alkawarin rai wanda yake cikin Kiristi Yesu, Zuwa ga Timoti, ƙaunataccen ɗana. Alheri, jinƙai da salama daga Allah Uba da kuma Kiristi Yesu Ubangijinmu, su kasance tare da kai. Na gode wa Allah wanda nake bauta wa, kamar yadda kakanni-kakannina suka yi da lamiri mai tsabta, yadda kullum dare da rana ina tuna da ku a cikin addu’o’ina. Sa’ad da na tuna da hawayenka, nakan yi marmarin ganinka, don in cika da farin ciki. An tunashe ni da sahihiyar bangaskiyarka, wadda a farko ta kasance a cikin kakarka Loyis da kuma mahaifiyarka Yunis yanzu kuwa na tabbata tana cikinka. Saboda haka, ina so in faɗakar da kai, ka lura baiwan nan ta Allah, wadda take tare da kai ta wurin ɗibiya maka hannuwana. Gama Allah bai ba mu ruhun tsoro ba, sai dai ruhun iko, na ƙauna da kuma na kamunkai. Saboda haka kada ka ji kunyar ba da shaida game da Ubangijinmu, ko kuwa ka ji kunyata, ni da nake ɗan sarƙa saboda shi. Sai dai ka haɗa kai tare da ni cikin shan wahala saboda bishara ta wurin ikon Allah, wanda ya cece mu ya kuma kira mu ga rayuwar tsarki ba saboda wani abin da muka yi ba sai dai saboda nufinsa da kuma alherinsa. An ba mu wannan alheri cikin Kiristi Yesu tun fil azal, amma yanzu an bayyana ta ta wurin bayyanuwar Mai Cetonmu, Kiristi Yesu, wanda ya hallaka mutuwa ya kuma kawo rai da rashin mutuwa a sarari ta wurin bishara. A wannan bishara ce, aka naɗa ni mai shela da manzo da kuma malami. Shi ya sa nake shan wahalar da nake sha. Duk da haka ba na jin kunya, domin na san wanda na gaskata da shi, na kuma tabbata cewa yana iya kiyaye abin da na danƙa masa amana don wancan rana. Abin da ka ji daga gare ni, ka kiyaye shi kamar tsarin sahihiyar koyarwa, cikin bangaskiya da ƙauna cikin Kiristi Yesu. Ka kiyaye kyakkyawar ajiyan nan da aka danƙa maka amana, ka lura da ita da taimakon Ruhu Mai Tsarki wanda yake raye a cikinmu. Ka san cewa kowa a lardin Asiya ya juya mini baya, har da Figelus da Hermogenes. Bari Ubangiji yă yi wa iyalin Onesiforus jinƙai, domin sau da dama yakan wartsakar da ni, bai kuma ji kunyar sarƙoƙina ba. A maimakon haka ma, sa’ad da yake a Roma, ya neme ni ido a rufe sai da ya same ni. Bari Ubangiji yă sa yă sami jinƙai daga Ubangiji a wancan ranar! Ka sani sarai yadda ya taimake ni a hanyoyi dabam-dabam a Afisa. Kai kuma, ɗana, ka yi ƙarfi cikin alherin da yake cikin Kiristi Yesu. Abubuwan da ka ji na faɗa a gaban shaidu masu yawa kuwa ka danƙa wa amintattun mutane waɗanda su ma za su iya koya wa waɗansu. Ka jure wa shan wahala tare da mu kamar soja mai kyau na Kiristi Yesu. Ba wanda yake aikin soja da zai sa kansa a sha’anin mutumin da ba ya aikin soja, domin yakan so yă gamshi wanda ya ɗauke shi soja. Haka ma, in wani ya yi gasa a matsayi shi ɗan wasa ne, ba ya sami rawanin nasara, sai in ya yi gasar bisa ga dokoki. Manomi mai aiki sosai ya kamata yă zama na fari wajen samun rabon amfanin gona. Ka yi tunani a kan abin da nake faɗi, gama Ubangiji zai ba ka ganewa cikin dukan wannan. Ka tuna da Yesu Kiristi, wanda aka tā da shi daga matattu, zuriyar Dawuda, wanda shi ne bisharata, wadda nake shan wahala har ga daurin sarƙa kamar mai laifi. Amma Maganar Allah ba a daure take ba. Saboda haka nake jure kome saboda zaɓaɓɓu, domin su ma su sami ceton da yake cikin Kiristi Yesu, tare da madawwamiyar ɗaukaka. Ga wata magana tabbatacciya, “In muka mutu tare da shi, za mu rayu tare da shi; in muka jimre, za mu yi mulki tare da shi. In muka yi mūsunsa, shi ma zai yi mūsunmu; in ba mu da aminci, shi dai mai aminci ne, domin shi ba zai iya mūsun kansa ba.” Ka riƙa tuna masu da haka, ka kuma gama su da Allah, kada su yi jayayya a kan maganganu, don ba ta da wani amfani, sai ɓad da masu ji kawai take yi. Ka yi iyakacin ƙoƙarinka ka gabatar da kanka a gaban Allah a matsayin wanda aka amince da shi, ma’aikaci wanda ba shi da dalilin jin kunya wanda kuma yake fassara kalmar gaskiya daidai. Ka yi nesa da maganganun banza na rashin tsoron Allah, gama waɗanda suka mai da hankali ga yin waɗannan za su ƙara zama marasa tsoron Allah. Koyarwarsu za tă bazu kamar ruɓaɓɓen gyambo. A cikinsu akwai Himenayus da Filetus, waɗanda suka bauɗe daga gaskiya. Suna cewa tashin matattu ya riga ya faru, suna kuma ɓata bangaskiyar waɗansu. Duk da haka, ƙaƙƙarfan tushen nan na Allah yana nan daram, an hatimce shi da wannan rubutu, “Ubangiji ya san waɗanda suke nasa,” da kuma, “Duk wanda ya bayyana yarda ga sunan Ubangiji, to, dole yă yi nesa da aikata mugunta.” A babban gida akwai kayayyakin da ba na zinariya da na azurfa kaɗai ba, amma har da na katako da na yumɓu ma; waɗansu domin hidima mai daraja waɗansu kuwa domin hidima marar daraja. In mutum ya tsabtacce kansa daga na farkon zai zama kayan aikin hidima mai daraja, mai amfani ga Maigida, kuma shiryayye domin yin kowane aiki mai kyau. Ka yi nesa da mugayen sha’awace-sha’awace na ƙuruciya, ka kuma bi adalci, bangaskiya, ƙauna da kuma salama, tare da waɗanda suke kira ga Ubangiji daga zuciya mai tsabta. Kada wani abu yă haɗa ka da gardandamin banza da wofi, domin ka san yadda suke jawo faɗa. Bai kamata bawan Ubangiji yă zama mai neman faɗa ba; a maimako, dole yă nuna alheri ga kowa, mai iya koyarwa, mai haƙuri kuma. Waɗanda suke gāba da shi kuwa dole yă yi musu gargaɗi cikin hankali, da fata Allah zai sa su tuba su kai ga sanin gaskiya, su kuma dawo cikin hankulansu su kuɓuta daga tarkon Iblis, wanda ya sa suka zama kamammu don su aikata nufinsa. Amma fa ka san wannan, za a yi lokutan shan wahala a kwanakin ƙarshe. Mutane za su zama masu son kansu, masu son kuɗi, masu taƙama, masu girman kai, masu zage-zage, marasa biyayya ga iyayensu, marasa godiya, marasa tsarki, marasa ƙauna, marasa gafartawa, masu ɓata sunayen waɗansu, marasa kamunkai, masu ƙeta, marasa ƙaunar nagarta, masu cin amana, marasa hankali, waɗanda sun cika da ɗaga kai, masu son jin daɗi a maimakon ƙaunar Allah suna riƙe da siffofin ibada, amma suna mūsun ikonta. Kada wani abu yă haɗa ka da su. Irin su ne suke saɗaɗawa su shiga gidaje suna rinjayar mata marasa ƙarfin hali, waɗanda zunubai suka sha kansu, mugayen sha’awace-sha’awace kuma sun ɗauke hankulansu, kullum suna koyo amma ba sa taɓa iya yarda da gaskiya. Kamar dai yadda Yannes da Yamberes suka tayar wa Musa, haka waɗannan mutane ma suke tayar wa gaskiya, mutane masu ɓataccen hankali, waɗanda, in ana zancen bangaskiya ne, to, fa ba sa ciki. Sai dai ba za su yi nisa ba, don rashin hankalinsu zai bayyana ga kowa, kamar na mutanen nan biyu. Kai kam, ka san kome game da koyarwata, da halina, da niyyata, bangaskiya, haƙuri, ƙauna, jimiri, tsanani, shan wahala, irin abubuwan da suka faru da ni a Antiyok, Ikoniyum da kuma Listira, tsananin da na jure. Duk da haka Ubangiji ya cece ni daga dukansu. Labudda, duk masu niyyar zaman tsarkaka, suna na Kiristi Yesu, za su sha tsanani. Mugayen mutane da masu ruɗi kuwa, ƙara muni za su riƙa yi, suna yaudara, ana kuma yaudararsu. Amma kai kam, ka ci gaba da abin da ka koya ka kuma tabbatar, gama ka san waɗanda ka koye su daga gare su, da kuma yadda tun kana ɗan jinjiri ka san Nassosi masu tsarki, waɗanda suke iya sa ka zama mai hikima zuwa ceto ta wurin bangaskiya cikin Kiristi Yesu. Dukan Nassi numfashin Allah ne yana kuma da amfani don koyarwa, tsawatarwa, gyara da kuma horarwa cikin adalci, domin mutumin Allah yă zama shiryayye sosai saboda kowane kyakkyawan aiki. A gaban Allah da kuma Kiristi Yesu, wanda zai yi wa masu rai da matattu shari’a, saboda kuma bayyanuwarsa da mulkinsa, ina ba ka umarni. Ka yi wa’azin Maganar Allah, ka zama a shirye a kullum, ko da zarafi, ko babu zarafi, ka yi gyara, ka kwaɓe, ka kuma ƙarfafa, da matuƙar haƙuri da koyarwa cikin natsuwa. Gama lokaci yana zuwa da mutane ba za su jure da sahihiyar koyarwa ba. A maimako, don cimma burinsu, za su taro wa kansu malamai masu yawa, domin su faɗi abin da kunnuwansu masu ƙaiƙayi suke so su ji. Za su juye kunnuwansu daga gaskiya zuwa ga jin tatsuniyoyi. Amma kai, ka natsu cikin kowane hali, ka jure shan wahala, ka yi aikin mai bishara, ka cika dukan ayyukan hidimarka. Gama an riga an tsiyaye ni kamar hadaya ta sha, kuma lokacin tashina ya yi. Na yi fama mai kyau, na gama tseren, na riƙe bangaskiya. Yanzu kuwa an ajiye mini rawanin adalci, wanda Ubangiji, Alƙali mai adalci zai ba ni a ranan nan ba kuwa ni kaɗai ba, amma ga duk waɗanda suka yi marmarin bayyanuwarsa. Ka yi iyakacin ƙoƙarinka ka zo wurina da sauri, gama Demas, saboda ƙaunar wannan duniya, ya yashe ni ya tafi Tessalonika. Kirssens ya tafi Galatiya, Titus kuwa ya tafi Dalmatiya. Luka ne kaɗai yake tare da ni. Ka nemi Markus ku zo tare, domin yana da amfani a gare ni cikin hidimata. Na aiki Tikikus zuwa Afisa. Sa’ad da za ka dawo, ka zo mini da alkyabbar da na bari a wurin Karbus a Toruwas, da kuma naɗaɗɗun littattafaina, tun ba ma fatun nan masu rubutu ba. Alekzanda maƙerin ƙarafan nan ya yi mini mugunta ƙwarai. Ubangiji zai sāka masa saboda abin da ya yi. Kai ma sai ka lura da shi, domin ya yi gāba sosai da saƙonmu. A lokacin da na kāre kaina da farko, ba wanda ya goyi bayana, sai ma kowa ya yashe ni. Ina fata ba za a lasafta wannan laifi a kansu ba. Amma Ubangiji ya tsaya tare da ni, ya kuma ba ni ƙarfi, don ta wurina a yi cikakkiyar shelar saƙon har Al’ummai duka su ji. Aka kuma cece ni daga bakin zaki. Ubangiji zai cece ni daga kowane mugun hari yă kuma kai ni mulkinsa na sama lafiya. A gare shi ɗaukaka ta tabbata har abada abadin. Amin. Ka gai da Firiskila da Akwila da iyalin Onesiforus. Erastus ya dakata a Korint, na kuma bar Turofimus cikin rashin lafiya a Miletus. Ka yi iyakacin ƙoƙarinka ka iso nan kafin damina. Yubulus yana gaishe ka, haka ma Fuden, Lainus, Kalaudiya da kuma dukan ’yan’uwa. Ubangiji yă zama tare da ruhunka. Alheri yă zama tare da ku. Bulus, bawan Allah da kuma manzon Yesu Kiristi saboda bangaskiyar zaɓaɓɓu na Allah da kuma sanin gaskiya wadda take kaiwa ga rayuwa ta tsoron Allah duk wannan kuwa saboda begen nan ne ga rai madawwami da Allah ya yi alkawari tun fil azal, shi wanda ƙarya ba ta a gare shi, da lokacin da Allah ya zaɓa ya cika sai ya bayyana maganarsa a sarari ta wurin wa’azin da aka danƙa mini amana ta wurin umarnin Allah Mai Cetonmu, Zuwa ga Titus, ɗana na gaske a tarayyarmu cikin bangaskiya. Alheri da salama daga Allah Uba da kuma Kiristi Yesu Mai Cetonmu, su kasance tare da kai. Dalilin da ya sa na bar ka a Kirit shi ne don ka daidaita abubuwan da suka rage da ba a kammala ba, ka kuma naɗa dattawa a kowane gari, yadda na umarce ka. Dole dattijo yă kasance marar aibi, mijin mace guda, mutumin da ’ya’yansa masu bi ne, waɗanda kuma ba a san su da lalata ko rashin biyayya ba. Da yake an danƙa wa mai kula da ikkilisiya riƙon amana saboda Allah, dole yă zama marar aibi ba mai girman kai ba, ba mai saurin fushi ba, ba mai buguwa ba, ba mai rikici ba, ba kuma mai son ƙazamar riba ba. A maimakon haka dole yă zama mai karɓan baƙi, mai son abu nagari, mai kamunkai, mai adalci, mai tsarki da kuma natsattse. Dole yă riƙe tabbataccen saƙon nan kam-kam yadda aka koyar, don yă iya ƙarfafa waɗansu da sahihiyar koyarwa yă kuma ƙaryata waɗanda suke gāba da shi. Gama akwai ’yan tawaye da yawa, masu surutun banza da masu ruɗi, musamman ƙungiyar masu kaciya. Dole a hana su yin magana, domin suna kawo rushewar iyalai ta wurin koyar da abubuwan da bai kamata su koyar ba don neman ƙazamar riba. Wani daga cikin annabawansu ma ya ce, “Kiretawa a kullum maƙaryata ne, mugayen dabbobi, ragwaye haɗamammu.” Wannan shaida gaskiya ce. Saboda haka, sai ka tsawata musu sosai, don su zama sahihai a wajen bangaskiya, ba za su kuma mai da hankalinsu ga tatsuniyoyin Yahudawa ko ga umarnan waɗanda suke ƙin gaskiya ba. Ga tsarkaka kuwa, kome mai tsarki ne, amma ga waɗanda suke marasa tsarki da kuma marasa ba da gaskiya, ba abin da yake da tsarki. Gaskiya dai, hankulansu da lamirinsu duk marasa tsarki ne. Sun ɗauka cewa sun san Allah, amma ta wurin ayyukansu suna mūsunsa. Sun zama abin ƙyama, marasa biyayya, ba su ma isa su yi aiki nagari ba. Dole ka koyar da abin da yake bisa sahihiyar koyarwa. Ka koya wa tsofaffin maza su kasance masu sauƙinkai, waɗanda suka cancanci girmamawa, masu kamunkai, sahihai wajen bangaskiya, da ƙauna da kuma jimiri. Haka ma, ka koya wa tsofaffin mata su zama masu bangirma cikin rayuwarsu, ba masu ɓata suna ko masu jarrabar shan giya ba, sai dai su zama masu koyar da abin da yake nagari. Sa’an nan za su iya su koya wa mata masu ƙuruciya su ƙaunaci mazansu da ’ya’yansu, su kasance da kamunkai da kuma tsarki, masu aiki a gida, masu kirki da kuma masu biyayya ga mazansu, don kada wani yă rena maganar Allah. Haka kuma, ka ƙarfafa samari su zama masu kamunkai. Cikin kowane abu ka zama musu misali mai kyau ta wurin aikata abin da yake nagari. A cikin koyarwarka ka nuna mutunci da ƙwazo da kuma sahihanci cikin maganar da ba za a iya kushewa ba, domin masu gāba da kai su ji kunya, su kuma rasa wani mugun abin da za su faɗa game da mu. Ka koya wa bayi su yi wa iyayengijinsu biyayya cikin kowane abu, su yi ƙoƙari su gamshe su, kada su mayar musu da magana, kada kuma su yi musu sata, sai dai su nuna za a iya amince da su sosai, don ta kowace hanya su sa koyarwa game da Allah Mai Cetonmu ta zama abin ɗaukan hankali. Gama alherin Allah mai kawo ceto ya bayyana ga dukan mutane. Yana koya mana mu ce, “A’a” ga rashin tsoron Allah da kuma sha’awace-sha’awacen duniya, mu kuma yi rayuwa ta kamunkai, ta adalci da kuma ta tsoron Allah a cikin wannan zamani, yayinda muke sauraron begenmu mai albarka bayyanuwar ɗaukakar Allahnmu mai girma da kuma Mai Cetonmu, Yesu Kiristi, wanda ya ba da kansa dominmu don yă fanshe mu daga dukan mugunta yă kuma tsarkake wa kansa mutanen da suke nasa, waɗanda suke marmarin yin abin da yake nagari. Waɗannan kam, su ne abubuwan da ya kamata ka koyar, ka ƙarfafa ka kuma tsawata da dukan iko. Kada ka yarda wani yă rena ka. Ka tuna wa mutane su zama masu biyayya ga masu mulki da kuma hukumomi, su zama masu biyayya suna kuma a shirye su yi kowane abin da yake mai kyau, kada su zama masu ɓata sunan kowa, su zama masu salama da kulawa, su kuma zama masu matuƙar tawali’u ga dukan mutane. A wani lokaci can baya mu ma wawaye ne, marasa biyayya, aka ruɗe mu, sha’awace-sha’awace da kwaɗayi iri-iri suka daure mu, muka yi zaman ƙiyayya da kishi, aka ƙi mu, mu kuma muka ƙi juna. Amma da alheri da kuma ƙaunar Allah Mai Cetonmu suka bayyana, sai ya cece mu, ba saboda abubuwan adalcin da muka aikata ba, sai dai saboda jinƙansa. Ya cece mu ta wurin wankan nan na sāke haihuwa da kuma sabuntawan nan ta Ruhu Mai Tsarki, wanda ya zubo mana a yalwace ta wurin Yesu Kiristi Mai Cetonmu, wannan fa domin an kuɓutar da mu ne ta wurin alherinsa, don mu zama magāda masu begen ga rai madawwami. Wannan magana tabbatacciya ce, ina kuma so ka nanata waɗannan abubuwa ƙwarai, domin waɗanda suka dogara ga Allah su himmantu ga aiki mai kyau. Waɗannan abubuwa suna da kyau sosai suna kuma da amfani ga kowane mutum. Amma ka guji jayayyar banza da ƙididdigar asali da gardandami da faɗace-faɗace game da Doka, gama ba su da riba kuma aikin banza ne. Ka gargaɗe mutumin da yake kawo tsattsaguwa sau ɗaya, ka kuma gargaɗe shi sau na biyu. Bayan haka, kada wani abu yă haɗa ka da shi. Ka dai san cewa irin mutumin nan ya taurare kuma mai zunubi ne; ya yanke wa kansa hukunci. Da zarar na aika Artemas ko Tikikus zuwa wurinka, sai ka yi iyakacin ƙoƙarinka ka zo wurina a Nikofolis, domin na yanke shawara in ci damina a can. Ka yi iyakacin ƙoƙarinka ka taimaki Zenas lauyan nan da Afollos a hanyarsu ka kuma tabbata ba su rasa kome ba. Dole mutanenmu su koyi ba da kansu ga aikata abin da yake nagari, domin su iya biyan bukatunsu na yau da kullum kada kuma su yi rayuwar marar amfani. Dukan waɗanda suke tare da ni suna gaishe ka. Ka gaggai mini da masoyanmu, masu bangaskiya. Alheri yă kasance tare da ku duka. Bulus, ɗan kurkuku saboda Kiristi Yesu, da kuma Timoti ɗan’uwanmu, Zuwa ga Filemon ƙaunataccen abokinmu da kuma abokin aikinmu, zuwa kuma ga Affiya ’yar’uwarmu, zuwa kuma ga Arkiffus abokin famarmu, da zuwa kuma ga ikkilisiyar da take taruwa a gidanka. Alheri da salama daga Allah Ubanmu da kuma Ubangiji Yesu Kiristi, su kasance tare da ku. Kullum nakan gode wa Allahna sa’ad da nake tuna da kai cikin addu’o’ina, domin ina jin labari bangaskiyarka cikin Ubangiji Yesu da kuma ƙaunarka da kake yi saboda dukan tsarkaka. Ina addu’a ka zama mai ƙwazo cikin shaida bangaskiyarka, domin ka sami cikakken fahimta ta kowane abin da yake nagarin da muke da shi cikin Kiristi. Ƙaunarka ta sa ni farin ciki ƙwarai ta kuma ƙarfafa ni, domin kai, ɗan’uwa, ka wartsake zukatan tsarkaka. Saboda haka, ko da yake cikin Kiristi ina iya yin ƙarfin hali in umarce ka ka yi abin da ya kamata, duk da haka ina roƙonka saboda ƙauna, na fi so in roƙe ka, ni Bulus tsoho, a yanzu kuma ga ni ɗan sarƙa saboda Kiristi Yesu. Ina roƙonka saboda ɗana Onesimus, wanda ya zama ɗana yayinda nake cikin sarƙoƙi. Dā kam, ba shi da amfani a gare ka, amma yanzu ya zama da amfani a gare ka da kuma gare ni. Ina aike shi yă koma gare ka, shi da yake zuciyata. Na so in riƙe shi a wurina a madadinka domin yă taimake ni yayinda nake cikin sarƙoƙi saboda bishara. Sai dai ban so in yi kome ban da yardarka ba, domin kowane alherin da za ka yi, yă fito daga zuciyarka, ba na tilas ba. Wataƙila abin da ya sa aka raba ka da shi na ɗan lokaci ƙanƙani shi ne don ka same shi da amfani ba kamar bawa kuma ba, sai dai fiye da bawa, a matsayin ƙaunataccen ɗan’uwa. Shi ƙaunatacce ne sosai a gare ni amma a gare ka ya ma fi zama ƙaunatacce, kamar mutum da kuma kamar ɗan’uwa a cikin Ubangiji. Saboda haka in ka ɗauke ni a kan ni abokin tarayya ne, sai ka marabce shi kamar yadda za ka marabce ni. In ya yi maka wani laifi ko kuma yana riƙe maka wani bashi, sai ka mai da shi a kaina. Ni, Bulus, nake rubuta wannan da hannuna. Zan biya ka, kada ma a yi zancen ranka da kake riƙe mini bashi. Ina fata, ɗan’uwa, zan sami amfani daga gare ka cikin Ubangiji; ka wartsake zuciyata cikin Kiristi. Da tabbacin biyayyarka, ina rubuta maka, da sanin za ka yi fiye da abin da na ce. Abu guda ya rage, ka shirya mini masauƙi, domin ina bege za a mayar da ni gare ku albarkacin addu’o’inku. Efafaras, abokin tarayyata a kurkuku cikin Kiristi Yesu, yana gaishe ka. Haka kuma Markus, Aristarkus, Demas da kuma Luka, abokan aikina. Alherin Ubangiji Yesu Kiristi yă kasance da ruhunku. A dā Allah ya yi wa kakanni-kakanninmu magana ta bakin annabawa a lokuta dabam-dabam da kuma a hanyoyi iri-iri, amma a waɗannan kwanaki a ƙarshe ya yi magana da mu ta wurin Ɗansa, wanda ya naɗa magājin dukan abubuwa, wanda kuma ta wurinsa ya halicci duniya. Ɗan shi ne hasken ɗaukakar Allah, shi ne kuma ainihin kamanninsa, yana riƙe da dukan abubuwa ta wurin kalmarsa mai iko. Bayan ya yi tsarkakewa don zunubai, sai ya zauna a hannun daman Maɗaukaki a sama. Ta haka yake da fifiko a kan mala’iku kamar yadda sunan da ya gāda ya fi nasu fifiko. Gama ga wane daga cikin mala’ikun Allah ya taɓa cewa, “Kai Ɗana ne; yau na zama Uba a gare ka”? Ko kuwa, “Zan zama Ubansa, shi kuma zai zama Ɗana”? Haka kuma, sa’ad da Allah ya kawo ɗan farinsa a duniya ya ce, “Bari dukan mala’ikun Allah su yi masa sujada.” Da yake magana game da mala’iku kuwa ya ce, “Ya mai da mala’ikunsa iska, bayinsa kuma harsunan wuta.” Amma game da Ɗan ya ce, “Kursiyinka, ya Allah, zai kasance har abada abadin, adalci kuma zai zama sandan mulkinka. Ka ƙaunaci abin da yake daidai, ka kuma ƙi mugunta; saboda haka Allah, Allahnka, ya ɗora ka a bisan abokan zamanka, ta wurin shafan da ya yi maka da man farin ciki.” Ya kuma ce, “Tun da farko, ya Ubangiji, ka kafa tushen duniya, sammai kuma aikin hannuwanka ne. Su za su hallaka, amma kai kana nan; dukansu za su tsufa kamar riga. Za ka naɗe su kamar mayafi, kamar riga za su sauya. Amma kai ba za ka canja ba, shekarunka kuma ba za su taɓa ƙarewa ba.” Ga wane daga cikin mala’iku Allah ya taɓa cewa, “Zauna a hannun damana, sai na sa abokan gābanka su zama matashin sawunka”? Ashe, dukan mala’iku ba ruhohi masu hidima ba ne da aka aika don su yi wa waɗanda za su gāji ceto hidima? Dole mu ƙara mai da hankali sosai ga abubuwan da muka ji, don kada mu kauce. Gama in saƙon da aka faɗi ta bakin mala’iku ya zama tabbatacce, kuma kowane ƙeta umarni da rashin biyayya suka karɓi sakamakonsu da ya dace, yaya za mu tsira in muka ƙyale irin wannan babban ceto? Wannan ceto, wanda Ubangiji ne ya fara sanar, aka kuma tabbatar mana ta bakin waɗanda suka ji shi. Allah shi ma ya shaida ta wurin alamu, abubuwan banmamaki da mu’ujizai iri-iri, da kuma baye-bayen Ruhu Mai Tsarki da aka rarraba bisa ga nufinsa. Ba ga mala’iku ba ne ya sa su yi mulkin duniya mai zuwa, wanda muke magana a kai ba. Amma akwai wani wurin da wani ya shaida cewa, “Mene ne mutum, da kake tuna da shi, ɗan mutum da kake kula da shi? Ka sa shi ƙasa kaɗan da darajar mala’iku; ka naɗa shi da ɗaukaka da girma, ka kuma sa kome a ƙarƙashin ƙafafunsa.” Ta wurin sa kome a ƙarƙashinsa, Allah bai bar wani abu da bai sa a ƙarƙashinsa ba. Duk da haka a yanzu ba mu ga kowane abu a ƙarƙashinsa ba. Sai dai muna ganin Yesu, wanda aka mai da shi ƙasa kaɗan da darajar mala’iku, yanzu kuwa an naɗa shi da ɗaukaka da girma domin yă sha wahalar mutuwa, domin ta wurin alherin Allah yă ɗanɗana mutuwa saboda kowa. Ta wurin kawo ’ya’ya masu yawa zuwa ga ɗaukaka, ya dace cewa Allah, wanda dominsa da kuma ta wurinsa ne kome yake kasancewa, ya sa tushen cetonsu yă zama cikakke ta wurin shan wahala. Da shi wanda yake tsarkake mutane da kuma su waɗanda ake tsarkakewa duk ’yan iyali ɗaya ne. Saboda haka Yesu ba ya kunyan kiransu ’yan’uwansa. Ya ce, “Zan sanar da sunanka ga ’yan’uwana; a gaban jama’a zan rera yabonka.” Har wa yau ya ce, “Zan dogara gare shi.” Ya kuma ce, “Ga ni, da ’ya’yan da Allah ya ba ni.” Da yake ’ya’yan suna da nama da jini, shi ma sai ya ɗauki kamanninsu na mutum domin ta wurin mutuwarsa yă hallaka wanda yake riƙe da ikon mutuwa, wato, Iblis ya kuma ’yantar da waɗanda dukan rayuwarsu tsoron mutuwa ya riƙe su cikin bauta. Gama tabbatacce ba mala’iku ne ya taimaka ba, sai dai zuriyar Ibrahim. Saboda wannan dole a mai da shi kamar ’yan’uwansa ta kowace hanya, domin yă zama babban firist mai aminci da mai jinƙai cikin hidima ga Allah, yă kuma miƙa hadayar sulhu saboda zunuban mutane. Domin shi kansa ya sha wahala sa’ad da aka gwada shi, yana iya taimakon waɗanda ake yi wa gwaji. Saboda haka, ’yan’uwa tsarkaka, waɗanda suke da rabo a kiran nan na sama, ku kafa tunaninku a kan Yesu, manzo da kuma babban firist wanda muke shaidawa. Ya yi aminci ga wanda ya naɗa shi, kamar yadda Musa ya yi aminci ga dukan gidan Allah. An ga Yesu ya cancanci girma fiye da Musa, kamar yadda mai ginin gida ya fi gidan daraja. Gama kowane gida yana da wanda ya gina shi, amma maginin dukan abu Allah ne. Musa ya yi aminci a matsayin bawa cikin dukan gidan Allah, yana ba da shaida a kan abubuwan da za a faɗa nan gaba. Amma Kiristi mai aminci ne kamar ɗa a gidan Allah. Mu kuwa gidansa ne, in muka tsaya gabanmu gadi da kuma begen da muke taƙama a kai. Kamar dai yadda Ruhu Mai Tsarki ya ce, “Yau, in kuka ji muryarsa, kada ku taurare zukatanku, yadda kuka yi a tawayen nan, a lokacin gwaji a hamada, inda kakanninku suka gwada ni, suka kuma gwada ni, ko da yake a cikin shekaru arba’in sun ga abin da na yi. Shi ya sa na yi fushi da wancan zamani, na kuma ce, ‘Kullum zukatansu a karkace suke, ba su kuma san hanyoyina ba.’ Saboda haka na yi rantsuwa a cikin fushina, ‘Ba za su taɓa shiga hutuna ba.’ ” Ku lura fa, ’yan’uwa, cewa kada waninku yă kasance da zuciya mai zunubi marar bangaskiya da takan juye daga bin Allah mai rai. Sai dai ku ƙarfafa juna kullum, muddin akwai lokacin da ana ce da shi Yau, don kada waninku yă zama mai taurin zuciya ta wurin ruɗun zunubi. Mu masu tarayya ne da Kiristi idan mun riƙe bangaskiyarmu da ƙarfi daga farko har zuwa ƙarshe. Kamar yadda aka faɗa cewa, “Yau, in kuka ji muryarsa, kada ku taurare zukatanku kamar yadda kuka yi a tawayen nan.” Su wane ne suka ji suka kuma yi tawaye? Ba su ne duk waɗanda Musa ya bi da su daga Masar ba? Da su wane ne kuwa ya yi fushi har shekaru arba’in? Ba da waɗanda suka yi zunubi, waɗanda suka mutu a hamada ba? Kuma ga su wane ne Allah ya rantse cewa ba za su taɓa shiga hutunsa ba, in ba ga marasa biyayyan nan ba? Saboda haka mun ga cewa ba su iya shiga ba, saboda rashin bangaskiyarsu ne. Saboda haka, da yake alkawarin shiga hutunsa yana nan har yanzu, sai mu yi hankali kada waninku yă kāsa shiga. Gama mu ma mun ji an yi mana wa’azin bishara, kamar yadda su ma suka ji; sai dai saƙon da suka ji ba tă amfane su ba, domin waɗanda suka ji ba su karɓe shi da bangaskiya ba. Mu kam da muka gaskata mu ne muka shiga wannan hutu, kamar yadda Allah ya ce, “Saboda haka na yi rantsuwa cikin fushina, ‘Ba za su taɓa shiga hutuna ba.’ ” Allah ya faɗa haka ko da yake ya riga ya kammala aikinsa tun halittar duniya. Gama a wani wuri ya yi magana a kan rana ta bakwai cikin waɗannan kalmomi, “A rana ta bakwai kuwa Allah ya huta daga dukan aikinsa.” Haka kuma a nassin nan ya ce, “Ba za su taɓa shiga hutuna ba.” Har yanzu dai da sauran dama domin waɗansu su shiga, su kuwa waɗanda aka fara yi wa albishirin nan sun kāsa shiga saboda rashin biyayya. Saboda haka Allah ya sāke sa wata rana, yana kiranta Yau, bayan wani dogon lokaci Allah ya yi magana ta bakin Dawuda, yadda aka riga aka faɗa, “Yau, in kuka ji muryarsa, kada ku taurare zukatanku.” Gama da a ce Yoshuwa ya ba su hutu, da Allah bai yi magana daga baya a kan wata rana dabam ba. Har yanzu, akwai wani hutun Asabbacin da ya rage domin mutanen Allah; gama duk wanda ya shiga hutun Allah, shi ma yakan huta daga nasa aiki, kamar yadda Allah ya huta daga nasa. Saboda haka, bari mu yi iyakacin ƙoƙarinmu mu shiga wannan hutu, don kada wani yă kāsa ta wurin bin gurbinsu na rashin biyayya. Maganar Allah tana da rai, tana kuma da ƙarfin aiki. Ta fi kowane takobi mai baki biyu kaifi. Maganarsa takan ratsa har ciki-ciki, tana raba rai da ruhu, gaɓoɓi da kuma ɓargon ƙashi; har sai ta tone ainihi wane ne muke. Babu wani abu cikin dukan halittar da yake ɓoye daga fuskar Allah. Kowane abu a buɗe yake yana kuma a shimfiɗe a idanun wanda dole mu ba da lissafi a gare shi. Saboda haka, da yake muna da babban firist mai girma wanda ya ratsa sama, Yesu Ɗan Allah, bari mu riƙe bangaskiyan nan wadda muke shaidawa da ƙarfi. Gama babban firist da muke da shi ba marar juyayin kāsawarmu ba ne, amma muna da wanda aka gwada ta kowace hanya, kamar dai yadda akan yi mana, duk da haka bai yi zunubi ba. Saboda haka sai mu matso kusa da kursiyin alheri da ƙarfi zuciya, don mu sami jinƙai mu kuma sami alherin da zai taimake mu a lokacin bukata. Akan zaɓi kowane babban firist daga cikin mutane ne, akan kuma naɗa shi domin yă wakilce su a kan al’amuran Allah, domin yă miƙa kyautai da hadayu saboda zunubai. Da yake babban firist ɗin mai kāsawa ne, yana iya bin da jahilai da kuma waɗanda suka kauce hanya, a hankali. Shi ya sa dole yă miƙa hadayu domin zunubansa, da kuma domin zunuban mutane. Ba wanda yakan kai kansa a wannan matsayi mai girma; sai ko Allah ya kira shi, kamar yadda aka yi wa Haruna. Haka ma Kiristi bai kai kansa neman ɗaukaka na zama babban firist ba. Allah ne dai ya ce masa, “Kai Ɗana ne; yau na zama Uba a gare ka.” Ya kuma ya ce a wani wuri, “Kai firist ne na har abada, bisa ga tsarin Melkizedek.” A lokacin da Yesu ya yi rayuwa a duniya, ya yi addu’o’i da roƙe-roƙe tare da kuka mai zafi da kuma hawaye ga wannan wanda yake da ikon cetonsa daga mutuwa, aka kuwa ji shi saboda tsananin bangirman da ya yi. Ko da yake shi ɗa ne, ya yi biyayya ta wurin shan wahala kuma da aka mai da shi cikakke, sai ya zama hanyar samun madawwamin ceto ga dukan waɗanda suke masa biyayya. Allah kuwa ya naɗa shi yă zama babban firist, bisa ga tsarin Melkizedek. Muna da abubuwa masu yawa da za mu faɗa game da wannan batu, sai dai yana da wuya a bayyana, da yake ba ku da saurin ganewa. Gaskiya, a yanzu ya kamata a ce kun zama malamai, sai ga shi kuna bukatar wani yă sāke koya muku abubuwa masu sauƙi game da abin da Allah ya faɗa. Kuna bukatar madara, ba abinci mai kauri ba! Duk wanda yake rayuwa a kan madara, shi kamar jariri ne har yanzu, kuma bai san ainihi mene ne ya dace ba. Amma abinci mai kauri na balagaggu ne, waɗanda suka hori kansu don su bambanta tsakanin nagarta da mugunta. Dole mu yi ƙoƙarin zama balagaggu mu kuma fara tunani game da abubuwan da suka fi koyarwan nan mai sauƙi game da Kiristi. Bai kamata mu ci gaba da magana game da me ya sa dole mu juye daga ayyukan da suke kawo mutuwa da kuma me ya sa za mu kasance da bangaskiya a cikin Allah ba. Kuma bai kamata mu ci gaba da koyar da umarnai game da baftisma, ɗibiya hannuwa, tashin matattu, da kuma madawwamin hukunci ba. Da yardar Allah, za mu ci gaba ga ƙarin ganewa. Waɗanda suka taɓa samun haske, waɗanda suka ɗanɗana kyauta ta sama, waɗanda suka sami rabo cikin Ruhu Mai Tsarki, waɗanda suka ɗanɗana daɗin maganar Allah da kuma ikokin zamani mai zuwa, ba ya yiwuwa a sāke kawo su ga tuba in suka kauce, domin suna sāke gicciye Ɗan Allah ke nan suna kuma kunyata shi a gaban jama’a. Ƙasar da take shan ruwan sama da yake fāɗi a kanta kullum da kuma take ba da hatsin da yake da amfani ga waɗanda ake noma dominsu, takan sami albarkar Allah. Amma ƙasar da take ba da ƙaya da sarƙaƙƙiya ba ta da amfani tana kuma cikin hatsarin la’ana. A ƙarshe za a ƙone ta. Abokaina, ko da yake muna irin maganan nan, mun tabbata kuna yi abubuwan nan masu kyau da waɗanda suka sami ceto suke yi. Allah ba marar adalci ba ne. Ba zai manta da aikinku da kuma ƙaunar da kuka nuna masa wajen taimakon mutanensa da kuma ci gaba da taimakonsu da kuke yi ba. Muna so kowannenku yă nuna ƙwazon nan har zuwa ƙarshe, domin ku tabbatar da begenku. Ba ma so ku zama masu ƙyuya, sai dai ku yi koyi da waɗanda ta wurin bangaskiya da haƙuri suka gāji abin da aka yi alkawari. Babu wanda ya fi Allah, saboda haka sa’ad da ya yi alkawari ga Ibrahim, sai ya rantse da sunansa, cewa, “Tabbatacce zan albarkace ka in kuma ba ka zuriya mai yawa.” Haka kuwa bayan Ibrahim ya jira da haƙuri, sai ya karɓi abin da aka yi alkawari. In mutane za su yi rantsuwa sukan yi haka da wanda ya fi su ne, rantsuwar kuwa takan tabbatar da abin da aka faɗa ta kuma kawo ƙarshen dukan gardama. Saboda haka da Allah ya so yă bayyana nufinsa marar canjawa a sarari ga magādan abin da aka yi alkawari, sai ya tabbatar da shi da rantsuwa. Allah ba ya karya! Haka ma alkawuransa da rantsuwarsa abubuwa biyu ne da ba a iya canjawa. Mun gudu zuwa wurin Allah domin kāriya. Ya kamata alkawuransa su ƙarfafawa sosai mu riƙe begen nan da yake gabanmu. Muna da wannan bege kamar anka na rai, kafaffe da kuma tabbatacce. Yana shiga tsattsarkan wuri na can ciki a bayan labule, inda Yesu, wanda ya sha gabanmu, ya shiga a madadinmu. Ya zama babban firist na har abada, bisa ga tsarin Melkizedek. Wannan Melkizedek sarkin Salem ne da kuma firist na Allah Mafi Ɗaukaka. Shi ne ya sadu da Ibrahim ya albarkace shi sa’ad da Ibrahim ya dawowa daga cin nasara a bisa sarakuna, Ibrahim kuwa ya ba shi kashi ɗaya bisa goma na kome. Ma’anar sunan Melkizedek ita ce, “sarkin adalci.” Amma da yake Salem yana nufin “salama,” shi kuma “Sarkin salama” ne. Ba shi da mahaifi ko mahaifiya, ba shi da asali, ba shi da farko ko ƙarshe, shi dai kamar Ɗan Allah ne kuma firist ne har abada. Ku dubi irin girman da Melkizedek mana. Ko kakanmu Ibrahim ma ya ba shi kashi ɗaya bisa goma na ganima! Yanzu doka ta umarci zuriyar Lawi waɗanda suka zama firistoci su karɓi kashi ɗaya bisa goma daga wurin mutane, wato, ’yan’uwansu, ko da yake ’yan’uwansu zuriyar Ibrahim ne. Ko da yake Melkizedek ba daga zuriyar Lawi ba ne, duk da haka Ibrahim ya ba shi kashi ɗaya bisa goma na abin da yake da shi, Melkizedek kuwa ya sa masa albarka, shi da aka yi wa alkawura. Kowa ya sani cewa na gaba shi yake sa wa na baya albarka. Firistoci ake ba wa kashi ɗaya bisa goma na abin da mutane suke samu. Amma dukan firistoci sukan mutu, sai dai Melkizedek, kuma nassi ya ce yana da rai. Ana ma iya cewa zuriyar Lawi, mai karɓar kashi ɗaya bisa goma daga mutane, ya ba da kashi ɗaya bisa goma ta wurin Ibrahim, wannan ya kasance haka domin an haifi Lawi daga baya a iyalin Ibrahim wanda ya ba wa Melkizedek kashi ɗaya bisa goma. Ko da yake Dokar Musa ta ce dole firistoci su kasance zuriyar Lawi, waɗannan firistoci ba su iya sa wani yă zama cikakke ba. Saboda akwai bukata wani firist kamar Melkizedek ya zo, a maimakon wani daga iyalin Haruna. Gama in aka canja yadda ake zaɓan firist, dole a canja Dokar ita ma. Mutumin da muke wannan zance a kai, ai, shi na wata kabila ce dabam, wadda ba wani daga kabilar da ya taɓa yin hidima a bagade. Kowa ya san cewa Ubangijinmu ya fito ne daga zuriyar Yahuda ne, kuma Musa bai taɓa ce firistoci za su fito daga wannan kabila ba. Canjin nan a Dokar Allah ya ƙara fitowa fili da wani firist dabam wanda yake kamar Melkizedek ya bayyana. Ya zama firist ne ba saboda ya cika wata ƙa’ida ta zama zuriyar Lawi ba, sai dai bisa ga ikon ran da ba a iya hallakawa. Gama nassi ya ce, “Kai firist ne na har abada, bisa ga tsarin Melkizedek.” Ta haka aka kawar da ƙa’ida marar ƙarfi da kuma marar amfani (gama doka ba tă mai da wani abu cikakke ba), yanzu kuwa bege mafi kyau ya ɗauki matsayinta. Ta haka kuma muka matso kusa da Allah. Ba kuwa da rashin rantsuwa aka yi haka ba. Waɗansu sun zama firistocin ba tare da wata rantsuwa ba, shi wannan ya zama firist ta wurin rantsuwar da Allah ya yi da ya ce masa, “Ubangiji ya rantse, ba kuwa zai canja zuciyarsa ba, ‘Kai firist ne na har abada.’ ” Saboda wannan rantsuwa, Yesu ya zama tabbacin alkawari mafi kyau. To, akwai waɗannan firistoci da yawa, da yake mutuwa ta hana su cin gaba da aikin zaman firist; amma Yesu ba zai mutu ba, don haka zai zama firist har abada. Saboda haka ya iya ba da ceto gaba ɗaya ga masu zuwa wurin Allah ta wurinsa, gama kullum a raye yake saboda yă yi roƙo dominsu. Irin wannan babban firist ne muke bukata, shi mai tsarki ne, marar aibi, mai tsabta, ba kamar mu masu zunubi ba sam. An ɗaukaka shi fiye da kome a sama. Ba ya bukata yă yi ta miƙa hadayu kowace rana saboda zunubansa, sa’an nan saboda zunuban mutane kamar sauran firistoci. Ya miƙa hadaya sau ɗaya tak, sa’ad da ya miƙa kansa. Gama doka takan naɗa babban firist a cikin mutane masu kāsawa; amma rantsuwar da ta zo bayan dokar, ta naɗa Ɗan, wanda aka mai da shi cikakke har abada. Abin da muke magana a nan shi ne, muna da irin wannan babban firist, wanda ya zauna a hannun dama na kursiyin Maɗaukaki a sama, wanda yake hidima a cikin wuri mai tsarki, tabanakul na gaskiya wanda Ubangiji ne ya kafa, ba mutum ba. Da yake dole kowane babban firist da aka naɗa yă miƙa baye-baye da hadayu, haka ma wannan ya bukaci yă kasance da abin da zai miƙa. Da a ce yana a duniya ne, da bai zama firist ba, domin a nan akwai mutanen da doka ta naɗa don su miƙa baye-baye. Suna hidima a cikin tsattsarkan wuri wanda yake hoto da kuma siffar abin da yake cikin sama. Shi ya sa aka gargaɗi Musa sa’ad da yana dab da gina tabanakul cewa, “Ka lura fa, ka yi kome daidai bisa ga zānen da aka nuna maka a kan dutsen.” Amma hidimar da Yesu ya karɓa tana da fifiko a kan tasu, kamar yadda alkawarin da shi ne yake matsakanci ya fi na dā fifiko nesa, an kuma kafa shi a kan alkawura mafi kyau. Gama da a ce alkawari na fari ba shi da wani laifi, da ba sai an sāke neman wani ba. Amma Allah ya sami mutane da laifi ya ce, “Ina gaya muku lokaci yana zuwa, sa’ad da zan yi sabon alkawari da gidan Isra’ila da kuma gidan Yahuda. Ba zai zama kamar irin alkawarin da na yi da kakanni-kakanninsu sa’ad da na kama hannunsu don in fitar da su daga Masar ba, domin ba su yi aminci da alkawarina ba, sai na juya musu baya, in ji Ubangiji. Wannan shi ne alkawarin da zan yi da gidan Isra’ila, bayan lokacin nan, in ji Ubangiji. Zan sa dokokina a cikin zukatansu, in kuma rubuta su a kan zukatansu. Zan zama Allahnsu, su kuwa za su zama mutanena. Mutum ba zai ƙara koya wa maƙwabcinsa ba, balle mutum yă ce wa ɗan’uwansa, ‘Ka san Ubangiji,’ domin dukansu za su san ni, daga ƙaraminsu zuwa babba. Gama zan gafarta muguntarsu ba zan kuma ƙara tuna da zunubansu ba.” Ta wurin kira wannan alkawari “sabo,” ya mai da na farin tsoho ke nan; abin da yake tsoho yana kuma daɗa tsufa, zai shuɗe nan ba da daɗewa ba. Alkawarin farko ya ƙunshi ƙa’idodi don sujada da kuma tsattsarkan wuri a duniya. An kafa tabanakul. A cikin ɗakinsa na farko akwai wurin ajiye fitila, tebur da kuma keɓaɓɓen burodi; an kira wannan Wuri Mai Tsarki. Sa’an nan akwai labule, kuma a bayan labulen akwai ɗaki na biyu da ake kira Wuri Mafi Tsarki, wanda yake da bagaden zinariya na turare da kuma akwatin alkawarin da aka dalaye da zinariya. A cikin akwatin alkawarin akwai tulun zinariya mai Manna a ciki, sandan Haruna wanda ya yi toho, da kuma allunan dutsen alkawari. A bisa akwatin alkawarin kuwa akwai kerubobi na Ɗaukaka, waɗanda suka inuwantar da murfin kafara da fikafikansu. Sai dai ba za mu tattauna waɗannan abubuwa dalla-dalla a yanzu ba. Sa’ad da aka shirya kome haka, sai firistoci suka shiga kullum cikin ɗaki na waje don su yi hidimarsu. Amma babban firist ne kaɗai yakan shiga ɗaki na ciki-ciki, sau ɗaya tak a shekara, kuma sai da jini, wanda yakan miƙa domin zunubansa da kuma domin zunuban da mutane suka yi a cikin rashin sani. Ta haka Ruhu Mai Tsarki ya nuna cewa ba a riga an bayyana hanyar shiga Wuri Mafi Tsarki ba tukuna, muddin tabanakul na fari yana nan tsaye. Wannan ma yana da ma’ana wa mutane a yau. Ya nuna cewa ba za mu iya wanke lamirinmu ta wurin miƙa baye-baye da hadayu ba. Waɗannan ƙa’idodi sun shafi sha’anin abinci da abin sha ne kawai da kuma ƙa’idodi tsarkake kanmu. Dokoki game da abubuwa na waje da ake amfani da su za su kasance ne sai lokacin ya yi da za a kawo abu mafi kyau. Sa’ad da Kiristi ya zo a matsayin babban firist na kyawawan abubuwan da suka riga suka kasance a nan, ya bi ta cikin tabanakul mafi girma da kuma mafi cikakke wanda ba mutum ne ya yi ba, wato, ba na wannan halitta ba. Bai shiga ta wurin jinin awaki da na maruƙa ba; amma ya shiga Wuri Mafi Tsarki sau ɗaya tak ta wurin jininsa, bayan ya samo madawwamiyar fansa. In har akan yayyafa jinin awaki da na bijimai da kuma tokar karsanar a kan waɗanda suke marasa tsabta bisa ga al’ada, a tsarkake su yadda za su zama masu tsabta a waje, balle jinin Kiristi, wanda ta wurin Ruhu madawwami ya miƙa kansa marar aibi ga Allah, ai, zai tsabtacce lamirinmu daga ayyukan da suke kai ga mutuwa, don mu bauta wa Allah mai rai! Saboda haka Kiristi shi ne matsakancin sabon alkawari, don waɗanda aka kira su sami madawwamin gādon da aka yi alkawari, yanzu da ya mutu a matsayin mai fansa don yă ’yantar da su daga zunuban da aka aikata a ƙarƙashin alkawari na farko. Sa’ad da wani ya yi alkawari game da gādonsa, dole a tabbatar da mutuwar wanda ya yi ta, domin alkawarin gādo yana aiki ne kawai bayan mai yinsa ya mutu, ba ya taɓa aiki yayinda mai yinsa yana da rai. Shi ya sa alkawari na farko bai fara aiki ba sai da aka zub da jini. Sa’ad da Musa ya sanar wa dukan mutane kowane umarni na doka, sai ya ɗauki jinin maruƙa tare da ruwa, jan ulu da kuma rassan hizzob, ya yayyafa a kan naɗaɗɗen littafin da kuma a kan dukan mutanen. Ya ce, “Wannan shi ne jinin alkawarin da Allah ya umarce ku ku kiyaye.” Ta haka ya yayyafa jinin a kan tabanakul da kuma a kan dukan kayayyakin da ake amfani da su don yin hidima. Tabbatacce, doka ta bukaci a tsabtacce kusa kowane abu da jini, kuma in ba tare da zub da jini ba babu gafara. Waɗannan abubuwa hotuna ne kawai na abin da yake a sama, dole kuma a tsarkake su ta wurin waɗannan ƙa’idodi. Amma dole a tsarkake ainihin abubuwa na sama da wani abu mafi kyau. Gama Kiristi bai shiga wani wuri tsattsarka da mutum ya yi ba, wanda yake hoto ne kawai na gaskataccen, a’a sama kanta ya shiga, domin yă bayyana a gaban zatin Allah a yanzu saboda mu. Bai kuwa shiga sama domin yă yi ta miƙa kansa a kai a kai, yadda babban firist yake shiga Wuri Mafi Tsarki kowace shekara da jinin da ba nasa ba. Da a ce haka ne, ai, da Kiristi ya sha wahala sau da yawa tun halittar duniya. Amma yanzu ya bayyana sau ɗaya tak a ƙarshen zamanai domin yă kawar da zunubi ta wurin miƙa kansa hadaya. Kamar dai yadda aka ƙaddara wa mutum yă mutu sau ɗaya, bayan haka kuma sai shari’a, haka aka miƙa Kiristi hadaya sau ɗaya domin yă ɗauke zunuban mutane masu yawa; zai kuma bayyana sau na biyu, ba don yă ɗauki zunubi ba, sai dai don yă kawo ceto ga waɗanda suke jiransa. Dokar, inuwa ce kawai ta kyawawan abubuwa masu zuwa, wannan inuwar ba ita ce ainihin abubuwan ba ne. Saboda haka ba za tă taɓa mai da masu matsowa kusa don yin sujada cikakku ta wurin irin hadayun da ake maimaitawa ba fasawa shekara-shekara ba. Da a ce za tă iya, da ba su daina miƙa hadayu ba? Ai, da an riga an tsabtacce masu yin sujada sau ɗaya tak, da kuma ba za su ƙara damuwa da zunubansu ba. Amma waɗancan hadayu abin tunawa da zunubai ne na kowace shekara, domin ba zai taɓa yiwuwa jinin bijimai da na awaki yă kawar da zunubai ba. Saboda haka, sa’ad da Kiristi ya shigo duniya ya ce, “Hadaya da sadaka kam ba ka so, sai dai ka tanadar mini jiki; hadayun ƙonawa da kuma hadayun zunubi ba ka ji daɗin. Sai na ce, ‘Ga ni nan, a rubuce yake cikin naɗaɗɗen littafi na zo in aikata nufinka, ya Allah.’ ” Da farko ya ce, “Hadayu da sadakoki, hadayun ƙonawa da hadayun zunubi ba ka so, ba ka kuwa jin daɗinsu” (ko da yake doka ta bukaci a yi su). Sa’an nan ya ce, “Ga ni nan, na zo in aikata nufinka.” Ya kawar da na farkon domin yă kafa na biyun. Kuma bisa ga wannan nufi, aka mai da mu masu tsarki ta wurin miƙa hadayar jikin Yesu Kiristi sau ɗaya tak. Kowace rana kowane firist yakan tsaya yin hidimar ibadarsa; sau da sau yakan miƙa hadayu iri ɗaya, waɗanda ba za su taɓa kawar da zunubai ba. Amma da Kiristi ya miƙa hadaya ɗaya ta dukan lokaci saboda zunubai, sai ya zauna a hannun dama na Allah. Tun daga lokacin nan yana jira a mai da abokan gābansa matashin ƙafafunsa, gama ta wurin hadayan nan guda ɗaya ya kammala har abada waɗanda ake tsarkake. Ruhu Mai Tsarki ma ya yi mana shaida game da wannan. Da farko ya ce, “Wannan shi ne alkawarin da zan yi da su bayan wannan lokaci, in ji Ubangiji. Zan sa dokokina a cikin zukatansu, in kuma rubuta su a kan zukatansu.” Sai ya ƙara da cewa, “Zunubansu da kurakuransu ba zan ƙara tunawa da su ba.” In an gafarta zunubai, babu sauran bukatar miƙa hadaya. Saboda haka, ’yan’uwa, da yake muna da wannan tabbaci na shiga Wuri Mafi Tsarki ta wurin jinin Yesu, ta wurin sabuwa, rayayyiyar hanya kuma wadda aka buɗe mana ta labulen nan, wato, jikinsa, da yake kuma muna da babban firist mai mulkin gidan Allah, bari mu matso kusa da Allah da zuciya mai gaskiya da kuma cikakken tabbaci mai zuwa ta wurin bangaskiya. Bari mu bar zukatan da tsabta, lamirinmu babu mugunta, da kuma jikunanmu a wanke da ruwa. Bari mu tsaya da ƙarfi a kan ga begen da muka ce namu ne, gama shi da ya yi alkawarin, mai aminci ne. Bari kuma mu yi tunani a kan yadda za mu gargaɗe juna ga ƙauna da kuma ayyuka nagari. Kada mu daina taruwa kamar yadda waɗansu suka saba, sai dai mu ƙarfafa juna, tun ba ma da kuka ga Ranan nan tana kusatowa ba. Ba wata hadayar da za a yi don mutanen da suka yanke shawara su yi ci gaba da yin zunubi da gangan bayan sun sami sanin gaskiya. A maimakon haka za su kasance da babban fargabar hukunci da kuma ta ƙunar wuta wadda za tă cinye abokan gāban Allah. Duk wanda ya ƙi ya kiyaye dokar Musa akan kashe shi ba tausayi, a kan shaidar mutum biyu ko uku. Wane irin hukunci mai tsanani ne kuke tsammani zai dace da mutumin da ya nuna rashin bangirma ga Ɗan Allah, wanda ya yi banza da jinin nan na alkawarin da ya tsarkake shi, wanda kuma ya zargi Ruhun alheri? Gama mun san shi, wannan wanda ya ce, “Ramuwa tawa ce; zan rama,” da kuma, “Ubangiji zai yi wa mutanensa hukunci.” Abu mai matuƙar bantsoro ne a fāɗa cikin hannuwan Allah mai rai. Ku tuna da kwanakin nan da suka wuce bayan kun sami haske, sa’ad da kuka tsaya daram a tsananin shan wahala. Wani lokaci a fili an tsananta muku aka kuma zage ku aka kuma tsananta muku; a wani lokaci kuma kuka tsaya tare da waɗanda aka yi musu haka. Kuka ji tausayin waɗanda suke cikin kurkuku, da farin ciki kuma kuka yarda ku rabu da dukiyar da aka ƙwace muku, domin ku kanku kun san cewa kuna da madawwamiyar dukiya mafi kyau. Saboda haka kada ku yar da tabbacinku; za a sāka muku a yalwace. Kuna bukata ku jimre don sa’ad da kuka aikata nufin Allah, za ku karɓi abin da ya yi alkawari. Gama, “A cikin ɗan lokaci kaɗan, mai zuwan nan zai zo ba kuwa zai yi jinkiri ba. Amma, “Mai adalcina zai rayu ta wurin bangaskiya. In kuwa ya ja da baya, ba zan ji daɗinsa ba.” Amma mu ba na waɗanda suke ja da baya, su kuma hallaka ba ne, amma na waɗanda suka gaskata, suka kuma sami ceto ne. Bangaskiya ita ce kasance tabbacin abin da muke bege a kai da kuma tabbatar da abin da ba mu gani ba. Abin da aka yabi kakanni na dā a kai ke nan. Ta wurin bangaskiya ne muka fahimci cewa an halicci duniya bisa ga umarnin Allah, saboda an halicce abin da ake gani daga abin da ba a gani. Ta wurin bangaskiya Habila ya miƙa wa Allah hadayar da ta fi wadda Kayinu ya miƙa. Ta wurin bangaskiya aka yabe shi cewa shi mai adalci ne, sa’ad da Allah ya yi magana mai kyau game da bayarwarsa. Ta wurin bangaskiya kuma har yanzu yana magana, ko da yake ya riga ya mutu. Ta wurin bangaskiya ne aka ɗauki Enok daga wannan rayuwa, ta haka bai ɗanɗana mutuwa ba; ba a kuwa same shi ba, domin Allah ya ɗauke shi. Gama kafin a ɗauke shi, an yabe shi a kan ya gamshi Allah. In ba tare da bangaskiya ba kuwa, ba ya yiwuwa a gamshi Allah, domin duk mai zuwa wurin Allah dole yă gaskata cewa yana nan, kuma shi ne yakan sāka wa waɗanda suke nemansa da gaske. Ta wurin bangaskiya Nuhu, sa’ad da aka yi masa gargaɗi a kan abubuwan da ba a gani ba tukuna, a cikin tsoro mai tsarki ya sassaƙa jirgi don ceton iyalinsa. Ta wurin bangaskiyarsa ya hukunta duniya ya kuma zama magājin adalcin da ake samu ta wurin bangaskiya. Ta wurin bangaskiya ne Ibrahim, sa’ad da aka kira shi ya fita zuwa wata ƙasar da zai karɓi gādo daga baya, ya kuwa yi biyayya ya tafi, ko da yake bai san inda za shi ba. Ta wurin bangaskiya ya yi zama a ƙasar da aka yi masa alkawari kamar baƙo a baƙuwar ƙasa; ya zauna a tentuna, haka ma Ishaku da Yaƙub, waɗanda su ma magādan alkawarin nan ne tare da shi. Gama yana zuba ido ga birnin nan mai tushe, wanda mai zānen gininsa da kuma mai gininsa Allah ne. Ta wurin bangaskiya Ibrahim, ko da yake shekarunsa sun wuce, Saratu kanta kuma bakararriya ce ya iya zama mahaifi domin ya amince cewa shi wanda ya yi alkawarin mai aminci ne. Saboda haka, daga mutum ɗaya, wanda dā shi ma da matacce kusan ɗaya ne, zuriya masu yawa suka fito kamar taurari a sararin sama da kuma kamar yashin da ba a iya ƙirgawa a bakin teku. Duk mutanen nan suna cikin bangaskiya sa’ad da suka mutu. Ba su kuwa karɓi abubuwan da aka yi alkawari ba; sun dai hango su suka kuma marabce su daga nesa. Suka kuma amince cewa su baƙi ne, bare kuma a duniya. Mutane masu faɗin irin abubuwan nan sun nuna cewa suna neman ƙasar da take tasu. Da a ce suna tunanin ƙasar da suka bari a baya, da sun riga sun sami damar komawa. A maimako, suna marmarin wata ƙasa mafi kyau, ta sama. Saboda haka Allah ba ya kunya a kira shi Allahnsu, domin ya riga ya shirya musu birni. Ta wurin bangaskiya Ibrahim, sa’ad da Allah ya gwada shi, sai ya miƙa Ishaku hadaya. Shi da ya karɓi alkawaran ya yi shirin miƙa makaɗaicin ɗansa, ko da yake Allah ya ce masa, “Ta wurin Ishaku ne za a lissafta zuriyarka.” Ibrahim ya yi tunani cewa Allah yana iya tā da matattu, a misalce kuwa, ya sāke karɓan Ishaku daga matattu. Ta wurin bangaskiya ne Ishaku ya albarkaci Yaƙub da Isuwa game da nan gabansu. Ta wurin bangaskiya ne Yaƙub, sa’ad da yake bakin mutuwa, ya albarkaci kowane ɗan Yusuf, ya kuma yi sujada yayinda yake jingine a kan sandansa. Ta wurin bangaskiya ne Yusuf, sa’ad da kwanakinsa suka yi kusan ƙarewa, ya yi magana game da fitowar Isra’ilawa daga Masar ya kuma ba da umarni game da ƙasusuwansa. Ta wurin bangaskiya ne iyayen Musa suka ɓoye shi har wata uku bayan haihuwarsa, domin sun ga cewa shi ba kamar sauran yara ba ne, ba su kuwa ji tsoron umarnin sarki ba. Ta wurin bangaskiya ne Musa, sa’ad da ya yi girma, ya ƙi a kira shi ɗan diyar Fir’auna. Ya zaɓa yă sha wahala tare da mutanen Allah, maimakon yă ji daɗin sha’awace-sha’awacen zunubi na ɗan lokaci. Ya ɗauki wulaƙancin da yake sha saboda Kiristi ya fi dukiyar Masar daraja, domin ya sa ido ga ladansa. Ta wurin bangaskiya ya bar Masar, ba tare da jin tsoron fushin sarki ba; ya kuwa jure domin ya ga wannan wanda ba a iya gani. Ta wurin bangaskiya ya kiyaye Bikin Ƙetarewa ya kuma yayyafa jini, domin kada mai hallakar ’ya’yan fari yă taɓa ’ya’yan fari na Isra’ila. Ta wurin bangaskiya ne mutane suka bi ta cikin Jan Teku, sai ka ce a kan busasshiyar ƙasa; amma da Masarawa suka yi ƙoƙari su yi haka, sai aka nutsar da su. Ta wurin bangaskiya ne katangar Yeriko ta rushe, bayan mutane suka yi ta kewaye ta har kwana bakwai. Ta wurin bangaskiya ne ba a kashe Rahab karuwan nan, ta tare da marasa biyayya ba don ta marabci ’yan leƙan asiri. Me kuma zan faɗa? Ba ni da lokacin da zan ba da labari a kan Gideyon, Barak, Samson, Yefta, Dawuda, Sama’ila, da kuma annabawa, waɗanda ta wurin bangaskiya ne suka ci nasara a kan mulkoki, suka aikata adalci, suka kuma sami abin da aka yi alkawari; waɗanda suka rurrufe bakunan zakoki, suka kashe harshen wuta, suka kuma tsere wa kaifin takobi; waɗanda aka mai da rashin ƙarfinsu ya zama ƙarfi; waɗanda suka yi jaruntaka wajen yaƙi suka kuma fatattaki mayaƙan waɗansu ƙasashe. Mata suka karɓi ƙaunatattunsu da aka sāke tasar daga matattu. Aka azabtar da yawancin mutanen nan, amma suka ƙi a sake su, domin sun tabbata za su sami lada mafi kyau sa’ad da aka tā da matattu. Waɗansu suka sha ba’a da bulala, har da dauri da sarƙa, da kuma jefa su cikin kurkuku. Aka jajjefe su da duwatsu; aka raba su biyu da zarto; aka kashe su da takobi. Suka yi ta yawo saye da fatun tumaki da na awaki, suka yi zaman rashi, suka sha tsanani da kuma wulaƙanci duniya ba tă ma cancanci su zauna a cikinta ba. Suka yi ta yawo a cikin hamada da a kan duwatsu, da cikin kogwanni da kuma cikin ramummuka. Waɗannan duka an yabe su saboda bangaskiyarsu, duk da haka babu waninsu da ya sami abin da aka yi alkawari. Allah ya shirya mana wani abu mafi kyau. Kuma bai so su kai ga maƙasudin bangaskiyarsu ba sai tare da mu. Saboda haka, da yake muna kewaye da irin wannan taron shaidu mai girma, sai mu yar da duk abin da yake hana mu da kuma zunubin da yake saurin daure mu, mu kuma yi tseren da aka sa a gabanmu da nacewa. Bari mu kafa idanunmu a kan Yesu, tushe da kuma kammalar bangaskiyarmu, wanda ya jure kunyar gicciye da aka yi masa, domin ya san cewa daga baya zai yi farin ciki ya yi haka. Yanzu kuma yana zaune a hannun dama na kursiyin Allah. Ku lura da wannan wanda ya jure da irin hamayyan nan daga masu zunubi, don kada ku gaji, har ku fid da zuciya. Cikin famanku da zunubi, ba ku yi tsayayya har ga zub da jininku ba tukuna. Kun kuma manta da kalmar ƙarfafawan nan da tana ce da ku ’ya’ya, “Ɗana kada ka rena horon Ubangiji, kada kuma ka fid da zuciya sa’ad da ya kwaɓe ka, domin Ubangiji yakan hori waɗanda yake ƙauna, yakan kuma hori duk wanda yakan karɓa a matsayin ɗa.” Ku jimre shan wahala a matsayin horo; Allah yana yi da ku kamar ’ya’ya. Gama wane ɗa ne mahaifinsa ba ya horonsa? In ba a hore ku ba (kowa kuwa yakan sami horo), to, ku shegu ne ba ’ya’yan gida ba. Ban da haka ma, dukanmu mun kasance da ubannin jiki waɗanda suka hore mu muka kuma yi musu ladabi. Ashe, bai kamata mu yi wa Uban ruhohinmu biyayya mu kuwa rayu ba! Ubanninmu sun hore mu na ɗan lokaci yadda suka ga ya fi kyau; amma Allah yakan hore mu don amfaninmu, domin mu sami rabo cikin tsarkinsa. Babu horon da yake da daɗi a lokacin da ake yinsa, sai dai zafi. Amma daga baya waɗanda suka horu ta haka sukan sami kwanciyar rai wadda aikin adalci yake bayarwa. Saboda haka, sai ku ƙarfafa raunanan hannuwanku da gwiwoyinku marasa ƙarfi! “Ku shirya hanyoyi marasa gargaɗa saboda ƙafafunku,” don kada guragu su daɗa gurguntawa, sai dai su warke. Ku yi iyakacin ƙoƙari ku yi zaman lafiya da kowa, ku kuma zama masu tsarki; gama in ban da tsarki ba babu wanda zai ga Ubangiji. Ku lura fa kada wani yă kāsa samun alherin Allah, kada kuma wani tushen ɗacin rai yă tsira har yă kawo rikici, yă kuma ƙazantar da mutane da yawa. Ku lura kada wani yă zama mai fasikanci, ko marar tsoron Allah kamar Isuwa, wanda saboda ƙwaryar abinci ɗaya tak ya sayar da gādonsa na ɗan fari. Daga baya, kamar yadda kuka sani, sa’ad da ya nemi yă gāji wannan albarka, aka ƙi shi. Bai sami zarafin tuba ba, ko da yake ya nemi albarkan nan da hawaye. Ba ku zo ga Dutsen Sinai wanda ana iya taɓawa ba, ko ga wuta mai ci sosai, ko ga duhu baƙi ƙirin, ko ko busar ƙaho, ko ga irin wata murya mai magana da kalmomin da masu jinta suka yi roƙo kada su ƙara ji, domin ba su iya jimrewa da abin da aka umarta cewa, “Ko da ma dabba ce ta taɓa dutsen, dole a jajjefe ta da duwatsu.” Ganin wannan abu da matuƙar bantsoro yake, har Musa ya ce, “Ina rawar jiki don tsoro.” Sai dai kun zo ne ga Dutsen Sihiyona, ga Urushalima ta sama, birnin Allah mai rai. Kun zo ga dubu dubban mala’ikun da suke cikin taron farin ciki, kun zo ga ikkilisiyar ɗan fari, waɗanda sunayensu suna a rubuce a sama. Kun zo ga Allah, alƙalin dukan mutane, kun kuma zo ga ruhohin mutane masu adalci da aka mai da su cikakku. Kun zo ga Yesu, mai yin sulhu na sabon alkawari, da kuma ga jinin da aka yayyafa wanda yake magana mafi kyau fiye da jinin Habila. Ku lura fa kada ku ƙi wanda yake magana. Gama in su ba su tsira sa’ad da suka ƙi wanda ya gargaɗe su a wannan duniya ba, to, ƙaƙa mu za mu tsira, in mun ƙi jin wannan da yake yi mana gargaɗi daga Sama? A lokacin nan muryarsa ta jijjiga duniya, amma yanzu ya yi alkawari cewa, “Har wa yau sau ɗaya tak zan ƙara jijjiga ba duniya kaɗai ba, amma har ma da sammai.” Wannan magana “sau ɗayan nan” sun nuna, kawar da abin da za a iya jijjigawa, wato, ƙirƙiro abubuwa, saboda abubuwan da ba a iya jijjigawa, su kasance. Saboda haka, da yake muna karɓar mulkin da ba ya jijjiguwa, sai mu yi godiya, ta haka kuwa mu yi wa Allah sujada yadda ya kamata, tare da bangirma da kuma tsoro, gama “Allahnmu wuta ne mai cinyewa.” Ku ci gaba da ƙaunar juna kamar ’yan’uwa. Kada ku manta da yin alheri ga baƙi, gama ta yin haka ne waɗansu suka yi wa mala’iku hidima, ba da saninsu ba. Ku riƙa tunawa da waɗanda suke a kurkuku kamar tare kuke a kurkuku, da kuma waɗanda ake gwada musu azaba, kamar ku ake yi wa. Aure yă zama abin girmamawa ga kowa, a kuma kiyaye gadon aure da tsabta, gama Allah zai hukunta masu zina da kuma dukan masu fasikanci. Ku kiyaye kanku daga yawan son kuɗi, ku kuma gamsu da abin da kuke da shi, gama Allah ya ce, “Ba zan taɓa bar ka ba; ba zan taɓa yashe ka ba.” Saboda haka muna iya fitowa gabagadi, mu ce, “Ubangiji ne mai taimakona; ba zan ji tsoro ba. Me mutum zai iya yi mini?” Ku tuna da shugabanninku, waɗanda suka faɗa muku maganar Allah. Ku dubi irin rayuwar da suka yi ku kuma yi koyi da bangaskiyarsu. Yesu Kiristi ba ya sākewa, shi ne a jiya, shi ne a yau, shi ne kuma har abada. Kada a ɗauke muku hankali da sababbin koyarwa dabam-dabam. Yana da kyau zukatanmu su ƙarfafa ta wurin alheri, ba ta wurin abinci waɗanda ba su da amfani ga waɗanda suke cinsu. Muna da bagade inda firistocin da suka yi hidima a tabanakul ba su da izini su ci. Babban firist yakan ɗauki jinin dabbobi yă shiga cikin Wuri Mafi Tsarki a matsayin hadaya ta zunubi, amma jikunan dabbobin akan ƙone su a bayan sansani. Haka ma Yesu ya sha wahala a bayan gari don yă tsarkake mutane ta wurin jininsa. Saboda haka, sai mu fita mu je wajensa a bayan sansani, muna ɗaukar kunyar da ya sha. Gama a nan ba mu da dawwammamen birni, sai dai muna zuba ido a kan birnin nan mai zuwa. Saboda haka, ta wurin Yesu, bari mu ci gaba da miƙa hadaya ta yabo ga Allah, yabon leɓuna da yake shaidar sunansa. Kada kuma ku manta yin aikin nagari da kuma taimakon waɗansu, gama da irin waɗannan hadayu ne Allah yake jin daɗi. Ku yi wa shugabanninku biyayya ku kuma miƙa kanku ga ikonsu. Suna lura da ku kuma za su ba da lissafi a gaban Allah. Saboda haka kada ku sa su yi fushi saboda aikinsu, ku sa su yi farin ciki. In ba haka ba za su iya taimakonku ba ko kaɗan. Ku yi mana addu’a. Mun tabbata cewa muna da lamiri mai kyau, kuma muna da marmari mu yi rayuwa ta bangirma a ta kowace hanya. Ni musamman, ina roƙonku ku yi addu’a, don a komo da ni a gare ku ba da daɗewa ba. Bari Allah na salama, wanda ta wurin jinin madawwamin alkawari ya tā da Ubangijinmu Yesu daga matattu, wannan Makiyayin tumaki mai girma, yă kintsa ku da kowane abu mai kyau domin aikata nufinsa, bari kuma yă aikata abin da zai gamshe shi cikinmu, ta wurin Yesu Kiristi, a gare shi ɗaukaka ta tabbata har abada. Amin. ’Yan’uwa, ina roƙonku ku yi haƙuri da wannan gargaɗi, don ba wata doguwar wasiƙa ce na rubuta muku ba. Ina so ku san cewa an saki ɗan’uwanmu Timoti. In ya iso da wuri, zan zo tare da shi in gan ku. Ku gai da dukan shugabanninku da kuma dukan mutanen Allah. Waɗanda suke Italiya suna gaishe ku. Alheri yă kasance da ku duka. Yaƙub, bawan Allah da kuma na Ubangiji Yesu Kiristi, Zuwa ga kabilan nan goma sha biyu, da suke warwartse a cikin al’ummai. Gaisuwa mai yawa. Ku ɗauki wannan da farin ciki mai tsabta, ’yan’uwana, duk sa’ad da gwaje-gwaje na kowane iri suka zo muku, domin kun san cewa gwajin bangaskiyarku yakan haifi daurewa. Dole daurewa ta kammala aikinta don ku zama balagaggu da kuma cikakku, ba ku kuma rasa kome ba. In waninku ya rasa hikima, ya kamata yă roƙi Allah, mai bayarwa hannu sake ga kowa ba tare da gori ba, za a kuwa ba shi. Amma sa’ad da ya roƙa, dole yă gaskata, ba tare da shakka ba, domin shi mai shakka, yana kama da raƙumar ruwan tekun da iska take kori tana kuma ɓuɓɓugowa. Kada irin wannan mutum yă yi tsammani zai sami wani abu daga Ubangiji; shi mai zuciya biyu ne, marar tsai da zuciyarsa wuri ɗaya a cikin duk abin da yake yi. Bari ɗan’uwan da yake cikin halin ƙasƙanci yă yi taƙama a matsayinsa na ɗaukaka. Amma wanda yake mai arziki, ya kamata yă yi taƙama a matsayinsa na ƙasƙanci, gama ba zai daɗe ba kamar furen jeji. Gama in rana ta fito ta yi zafi mai tsanani sai ta sa tsiro yă yanƙwane tsiro; furensa yă kakkaɓe, kyansa kuma yă lalace. Haka ma mai arziki zai shuɗe yayinda yake cikin harkarsa. Mai albarka ne mutumin da yake daurewa cikin gwaji, gama bayan ya yi nasara da gwajin, zai sami rawanin rai wanda Allah ya yi alkawari ga waɗanda suke ƙaunarsa. Sa’ad da aka jarrabci mutum, kada yă ce, “Allah ne yake jarrabtarsa.” Gama ba ya yiwuwa a jarrabci Allah da mugunta, shi kuma ba ya jarrabtar kowa; amma akan jarrabce kowane mutum sa’ad da muguwar sha’awarsa ta janye shi ta kuma rinjaye shi. Sa’an nan, bayan da sha’awar ta yi ciki, takan haifi zunubi; zunubi kuwa, sa’ad da ya balaga yakan haifi mutuwa. Kada a ruɗe ku, ’yan’uwana ƙaunatattu. Kowane abu mai kyau da kuma kowace cikakkiyar kyauta daga sama suke, sun sauko ne daga wurin Uban haskoki, wanda ba sauyawa ko wata alamar sākewa a gare shi faufau. Ya zaɓa yă haife mu ta wurin kalmar gaskiya, domin mu zama ’ya’yan fari na dukan abin da ya halitta. ’Yan’uwana ƙaunatattu, ku lura da wannan. Ya kamata kowa yă kasance mai saurin saurara, ba mai saurin magana ba, ba kuma mai saurin fushi ba, gama fushin mutum ba ya kawo rayuwar adalcin da Allah yake so. Saboda haka, ku rabu da ƙazamin hali da kuma kowace irin mugunta ku kuma yi na’am da maganar da aka shuka a cikinku da tawali’u, wadda za tă iya cetonku. Kada ku zama masu ji kawai, ku ruɗi kanku. A maimakon haka ku zama masu yin abin da ta ce. Duk wanda yake ji magana ne kawai, bai kuwa aikata abin da ta ce ba, yana kama da mutumin da ya kalli fuskarsa a madubi bayan ya kalli kansa, sa’ad da ya tashi daga wurin, nan da nan sai yă manta da kamanninsa. Amma duk mai duba cikakkiyar ƙa’idan nan ta ’yanci, ya kuma nace a kanta, ya zama ba mai ji ne kawai yă mance ba, sai dai mai yi ne yă zartar, to wannan shi za a yi wa albarka a cikin abin da yake yi. In wani ya ɗauki kansa mai addini ne duk da haka bai ƙame harshensa ba, ruɗin kansa yake yi addininsa kuwa banza ne. Addinin da Allah Ubanmu ya yarda da shi a matsayin mai tsabta da kuma marar aibi shi ne, a kula da marayu da gwauraye cikin damuwoyinsu, a kuma kiyaye kai daga lalacin da duniya take sa wa. ’Yan’uwana, a matsayinmu cikin Ubangiji Yesu Kiristi maɗaukaki, kada ku nuna bambanci. A ce wani ya shigo cikin taronku saye da zoben zinariya da riguna masu tsada, wani matalauci kuma saye da tsummoki shi ma ya shigo, in kuka mai da hankali na musamman ga mutumin da yake da riguna masu tsadan nan kuka kuma ce, “Ga wurin zama mai kyau dominka,” amma kuka ce wa matalaucin nan, “Kai tsaya daga can,” ko kuwa, “Ka zauna a ƙasa kusa da ƙafafuna,” ashe, ba ku nuna bambanci a tsakaninku ke nan ba, kuka kuma zama alƙalai masu mugayen tunani? Ku saurara, ’yan’uwana ƙaunatattu. Ashe, Allah bai zaɓi waɗanda suke matalauta a idon duniya don su zama masu wadata cikin bangaskiya, su kuma gāji mulkin da ya yi wa masu ƙaunarsa alkawari ba? Ga shi kun wulaƙanta matalauta. Ashe, ba masu arziki ne suke cutarku ba? Ba su ba ne suke jan ku zuwa kotu? Ba su ba ne suke ɓata sunan nan mai martaba wanda aka san ku da shi ba? In fa kun kiyaye dokan nan ta mulki wadda take cikin Nassi mai cewa, “Ƙaunaci maƙwabcinka kamar kanka,” kun yi daidai. Amma in kuka nuna bambanci, kun yi zunubi ke nan shari’a kuma ta same ku da laifi a matsayin masu karya doka. Gama duk wanda ya kiyaye dukan doka amma ya yi tuntuɓe a kan abu ɗaya kaɗai, ya zama mai laifin karya dukansu ke nan. Gama shi da ya ce, “Kada ka yi zina,” shi ne kuma ya ce, “Kada ka yi kisankai.” In kuwa ba ka zina amma kana kisankai, ka zama mai karya doka ke nan. Ku yi magana ku kuma yi aiki kamar waɗanda za a yi musu shari’a bisa ga doka mai ba da ’yanci, gama za a yi wa duk wanda bai nuna jinƙai ba hukunci babu jinƙai. Jinƙai yakan yi nasara a kan hukunci! Wanda amfani ne, ’yan’uwana, a ce wani yă ce yana da bangaskiya, amma ba shi da ayyuka? Anya, wannan bangaskiya za tă iya cetonsa kuwa? A ce wani ɗan’uwa ko ’yar’uwa ba shi da riguna ko abincin yini, sai waninku yă ce masa, “Sauka lafiya, Allah ya ba da ci da sha da kuma sutura,” amma bai yi wani abu game da bukatunsa na jiki ba, ina amfani? Haka ma bangaskiya ita kaɗai, in ba tare da ayyuka ba, matacciya ce. Amma wani zai ce, “Kai kana da bangaskiya; ni kuma ina da ayyuka.” Ka nuna mini bangaskiyarka ba tare da ayyuka ba, ni kuma zan nuna maka bangaskiyata ta wurin abin da nake yi. Ka gaskata cewa Allah ɗaya ne. To, da kyau! Ai, ko aljanu ma sun gaskata wannan, har da rawan jiki. Kai wawa, kana son tabbaci cewa bangaskiya marar ayyuka banza ce? Ashe, ba a mai da kakanmu Ibrahim mai adalci saboda abin da ya yi ba ne sa’ad da ya miƙa ɗansa Ishaku a bisa bagade? Ai, ka gani cewa bangaskiyarsa da ayyukansa sun yi aiki tare, bangaskiyarsa kuma ta zama cikakkiya ta wurin abin da ya yi. Aka kuma cika nassin nan da ya ce, “Ibrahim ya gaskata Allah, aka kuma lissafta wannan adalci ne gare shi,” aka kuma ce da shi abokin Allah. Kun ga cewa ashe mutum zai sami kuɓuta ta wurin abin da ya yi ne ba ta wurin bangaskiya kaɗai ba. Ta haka kuma ashe, Rahab karuwan nan ba a ɗauke ta mai adalci ce saboda abin da ta yi ba ne sa’ad da ta ba wa ’yan leƙen asirin nan masauƙi ta kuma sallame su suka tafi ta wata hanya dabam? Kamar yadda jikin da babu ruhu matacce ne, haka ma bangaskiyar da babu ayyuka matacciya ce. Kada yawancinku su so ɗaukan kansu a matsayin malamai, ’yan’uwana, domin kun san cewa mu da muke koyarwa za a yi mana shari’a mafi tsanani. Dukanmu mukan yi tuntuɓe a hanyoyi dabam-dabam. In wani bai taɓa yin kuskure a cikin maganarsa ba, shi cikakke ne, yana kuma iya ƙame dukan jikinsa. Sa’ad da muka sa linzamai a bakunan dawakai don mu sa su yi mana biyayya, mukan iya bin da dabbar gaba ɗaya. Ko kuwa misali, mu dubi jiragen ruwa, mana. Ko da yake suna da girma ƙwarai kuma iska mai ƙarfi ce take tura su, ana tuƙa su da ɗan ƙaramin sandan ƙarfe ne zuwa duk inda mai tuƙin jirgin yake so. Haka ma harshe yake, ga shi ɗan ƙanƙanin gaɓar jiki ne, amma sai manyan fariya. Ku dubi yadda ɗan ƙaramin ƙyastu yake ƙuna wa babban jeji wuta mana. Harshe ma wuta ne! A cikin duk gaɓoɓinmu, harshe shi ne tushen kowace irin mugunta, mai ɓata mutum gaba ɗaya, mai zuga zuciyar mutum ta tafasa, shi kuwa jahannama ce take zuga shi. Kowace irin dabba, tsuntsu, masu ja da ciki da kuma halittun da suke cikin teku an sarrafa su kuma mutum ne ya sarrafa, amma ba mutumin da zai iya ya sarrafa harshe. Mugu ne marar hutu, cike da dafi mai kisa. Da harshe mukan yabi Ubangijinmu da kuma Ubanmu, da shi kuma muke la’antar mutane, waɗanda aka halitta a kamannin Allah. Daga wannan baki guda yabo da la’ana suke fitowa. ’Yan’uwana, wannan bai kamata yă zama haka ba. Ruwa mai kyau da kuma ruwan gishiri zai iya fito daga maɓulɓula ɗaya? ’Yan’uwana, itacen ɓaure yana iya haifar ’ya’yan zaitun, ko kuma itacen inabi yă haifi ’ya’yan ɓaure? Haka ma, maɓulɓular ruwan gishiri ba zai iya ba da ruwa mai kyau ba. Wane ne mai hikima da fahimta a cikinku? Bari yă nuna ta ta wurin rayuwarsa mai kyau, ta wurin ayyukan da aka yi cikin tawali’un da suke fitowa daga hikima. Amma in kuna cike da mugun kishi da kuma sonkai a cikin zukatanku, kada ku yi taƙama game da wannan, ko ku danne gaskiya. Irin wannan “hikima” ba daga sama ta sauko ba, ta duniya ce, ta rashin ruhaniya, ta Iblis kuma. Gama inda akwai kishi da sonkai, a can za a tarar da hargitsi da kowane irin mugun aiki. Amma hikimar da ta zo daga sama da fari tana da tsabta gaba ɗaya; sa’an nan mai ƙaunar salama ce, mai sanin ya kamata, mai biyayya, cike da jinƙai da aiki mai kyau, marar nuna bambanci, sahihiya kuma. Masu salama da suke shuki cikin salama sukan girbe adalci. Me yake jawo faɗace-faɗace da gardandami a tsakaninku? Ashe, ba sha’awace-sha’awacenku da suke yaƙi a zukatanku ba ne? Kukan nemi abu ku rasa, sai ku yi kisa da ƙyashi. In kuka rasa abin da kuke nema sai ku shiga yin gardama da faɗa. Kukan rasa ne, domin ba ku roƙi Allah ba. Sa’ad da kuka roƙa, ba kwa samu, don kun roƙa da mugun nufi, don ku kashe abin da kuka samu a kan sha’awace-sha’awacenku. Ku mazinata, ba ku san cewa abokantaka da duniya gāba ce da Allah ba? Duk wanda ya zaɓa yă zama abokin duniya ya zama abokin gāban Allah ke nan. Ko kuna tsammani a banza ne Nassi ya ce ruhun da ya sa yă zauna a cikinmu yana kishi sosai? Amma yakan ba mu alheri a yalwace. Shi ya sa Nassi ya ce, “Allah yana gāba da masu girman kai amma yakan ba da alheri ga masu tawali’u.” Saboda haka, ku miƙa kanku ga Allah. Ku yi tsayayya da Iblis, zai kuwa guje ku. Ku matso kusa da Allah shi kuwa zai matso kusa da ku. Ku wanke hannuwanku, ku masu zunubi, ku kuma tsarkake zukatanku, ku masu zuciya biyu. Ku yi baƙin ciki, ku yi makoki ku kuma yi kuka. Ku mai da dariyarku ta zama makoki, farin cikinku kuma yă zama ɓacin zuciya. Ku ƙasƙantar da kanku a gaban Ubangiji, zai kuwa ɗaukaka ku. ’Yan’uwa, kada ku ɓata wa juna suna. Duk wanda ya zargi ɗan’uwansa ko ya ɗora masa laifi, yana gāba da doka ne yana kuma yin mata shari’a ke nan. In kuwa ka ɗora wa shari’a laifi, kai ba mai binta ba ne, mai ɗora mata laifi ne. Akwai Mai ba da doka da kuma Alƙali guda ɗaya tak, shi ne yake da ikon ceto da kuma hallakarwa. Amma kai, wane ne da za ka hukunta maƙwabcinka? Yanzu fa sai ku saurara, ku da kuke cewa, “Yau ko gobe za mu je wannan ko wancan birni, mu yi shekara a can, mu yi kasuwanci, mu ci riba.” Alhali kuwa ba ku ma san abin da zai faru gobe ba. Wane iri ne ranku? Ku kamar hazo ne da yake bayyana na ɗan lokaci sa’an nan yă ɓace. A maimakon haka, ya kamata ku ce, “In Ubangiji ya yarda, muna kuma a raye, za mu yi wannan ko wancan.” Ga shi, kuna fariya da taƙama. Duk irin wannan taƙama mugun abu ne. Saboda haka, duk wanda ya san abu mai kyan da ya kamata yă yi, bai kuwa yi ba, ya yi zunubi ke nan. Yanzu fa sai ku saurara, ku masu arziki, ku yi kuka da ihu, saboda azabar da take zuwa a kanku. Arzikinku ya ruɓa, asu kuma sun cinye tufafinku. Zinariyarku da azurfarku sun yi tsatsa. Tsatsarsu kuwa za tă zama shaida a kanku, ta kuma ci namar jikinku kamar wuta. Kun ɓoye dukiya a kwanakin ƙarshe. Ga shi! Zaluncin da kuka yi na hakkin ma’aikatan gonakinku yana ta ƙara. Kukan masu girbi ya kai kunnuwan Ubangiji Maɗaukaki. Kun yi rayuwar jin daɗi a duniya kuna ci kuna sha na ganin dama. Kun ciyar da kanku kun yi ƙiba don ranar yanka. Kun hukunta kun kuma kashe mutane marasa laifi, waɗanda ba su yi gāba da ku ba. Saboda haka ’yan’uwa, sai ku yi haƙuri har dawowar Ubangiji. Ku dubi yadda manomi yakan jira gona ta ba da amfaninta mai kyau, da kuma yadda yake haƙurin jiran ruwan sama na damina da na kaka. Haka ku ma, ku yi haƙuri, ku tsaya da ƙarfi, gama dawowar Ubangiji ya yi kusa. ’Yan’uwa, kada ku yi gunaguni da juna, don kada a hukunta ku. Alƙalin yana tsaye a bakin ƙofa! ’Yan’uwa, ku ɗauki annabawa da suka yi magana a cikin sunan Ubangiji, a matsayin gurbi na haƙuri a cikin shan wahala. Kamar yadda kuka sani, mukan ce da waɗanda suka jure, masu albarka ne. Kun ji daurewar Ayuba, kuka kuma ga abin da Ubangiji ya yi a ƙarshe. Ubangiji yana cike da tausayi da jinƙai. ’Yan’uwana, fiye da kome, kada ku yi rantsuwa ko da sama, ko da ƙasa ko da wani abu dabam. Bari “I” naku yă zama “I”. “A’a” naku kuma yă zama “A’a”, don kada a hukunta ku. Akwai waninku da yake shan wahala? Ya kamata yă yi addu’a. Akwai wani mai murna? Sai yă rera waƙoƙin yabo. Akwai waninku da yake ciwo? Ya kamata yă kira dattawan ikkilisiya su yi masa addu’a, su kuma shafa masa mai cikin sunan Ubangiji. Addu’ar da aka yi cikin bangaskiya, za tă warkar da marar lafiya, Ubangiji zai tashe shi. In ya yi zunubi kuwa za a gafarta masa. Saboda haka, ku furta wa juna zunubanku, ku yi addu’a saboda juna, domin ku sami warkarwa. Addu’ar mai adalci tana da iko da kuma amfani. Iliya mutum ne kamar mu. Ya yi addu’a da gaske don kada a yi ruwan sama, ba a kuma yi ruwan sama a ƙasar ba har shekaru uku da rabi. Ya sāke yin addu’a, sai sammai suka ba da ruwan sama, ƙasa kuma ta ba da amfaninta. ’Yan’uwana, in waninku ya kauce daga gaskiya, wani kuma ya komo da shi, sai yă tuna da wannan. Duk wanda ya komo da mai zunubi daga kaucewarsa, zai cece shi daga mutuwa, yă kuma rufe zunubai masu ɗumbun yawa. Bitrus, manzon Yesu Kiristi, Zuwa ga zaɓaɓɓu na Allah, baƙi a duniya, da suke a warwatse ko’ina a Fontus, Galatiya, Kaffadokiya, Asiya da kuma Bitiniya, waɗanda aka zaɓa bisa ga rigyasanin Allah Uba, ta wurin aikin tsarkakewar Ruhu, don biyayya ga Yesu Kiristi, su kuma sami yayyafan jininsa. Alheri da salama su zama naku a yalwace. Yabo ya tabbata ga Allah Uban Ubangijinmu Yesu Kiristi! Cikin jinƙansa mai girma ya ba mu sabuwar haihuwa cikin bege mai rai ta wurin tashin Yesu Kiristi daga matattu, da kuma cikin gādon da ba zai taɓa lalacewa, ɓacewa ko koɗewa ba, ajiyayye a sama dominku, ku waɗanda ta wurin bangaskiya ake kiyayewa ta wurin ikon Allah har yă zuwa ceton da yake a shirye da za a bayyana a ƙarshen lokaci. A kan wannan kuke cike da farin ciki ƙwarai, ko da yake yanzu na ɗan lokaci kuna fuskantar baƙin ciki daga gwaje-gwaje iri-iri. Wannan kuwa domin a tabbatar da sahihancin bangaskiyarku ne, wadda ta fi zinariya daraja nesa, ita zinariya kuwa, ko da yake mai ƙarewa ce, akan gwada ta da wuta, domin bangaskiyan nan taku ta jawo muku yabo da girma da ɗaukaka a bayyanar Yesu Kiristi. Ko da yake ba ku taɓa ganinsa ba, kuna ƙaunarsa; kuma ko da yake ba kwa ganinsa yanzu, kun gaskata shi, kun kuma cika da farin ciki ƙwarai, wanda ya fi gaban faɗi, gama kuna samun sakamakon bangaskiyarku, ceton rayukanku ke nan. Game da ceton nan, annabawa, waɗanda suka yi maganar alherin da za tă zo gare ku, sun yi bincike mai zurfi, a natse, suna ƙoƙari su san lokaci da kuma yanayin da Ruhun Kiristi da yake cikinsu yana nunawa sa’ad da ya yi faɗi a kan wahalolin Kiristi da kuma ɗaukaka da za tă bi. Aka bayyana musu cewa ba kansu ne suke bauta wa ba sai ku, sa’ad da suka yi maganar abubuwan da aka faɗa muku ta wurin waɗanda suka yi muku wa’azin bishara, ta wurin Ruhu Mai Tsarki wanda aka aika daga sama. Ko mala’iku ma suna marmari su ga waɗannan abubuwa. Saboda haka, ku shirya kanku don aiki; ku zama masu kamunkai; ku kafa begenku duka a kan alherin da za a ba ku sa’ad da aka bayyana Yesu Kiristi. Kamar ’ya’ya masu biyayya, kada ku bi mugayen sha’awace-sha’awacen da dā kuke da su sa’ad da kuke rayuwa a cikin jahilci. Amma kamar yadda wanda ya kira ku yake mai tsarki, haka ku ma sai ku kasance masu tsarki cikin dukan abubuwan da kuke yi; gama a rubuce yake cewa, “Ku zama masu tsarki, domin ni mai tsarki ne.” Tun da yake kuna kira ga Uba wanda yake yin wa kowane mutum shari’a bisa ga ayyukansa ba bambanci, sai ku yi rayuwarku a nan kamar baƙi cikin tsoro mai bangirma. Gama kun san cewa ba da abubuwa masu lalacewa kamar azurfa ko zinariya ce aka fanshe ku daga rayuwar banza da kuka karɓa daga kakanni-kakanninku ba, sai dai an fanshe ku da jini mai daraja na Kiristi, ɗan rago marar aibi ko lahani. An zaɓe shi kafin halittar duniya, amma an bayyana shi a zamanin ƙarshe saboda ku. Ta gare shi ne kuka gaskata da Allah, wanda ya tā da shi daga matattu, aka kuma ɗaukaka shi, ta haka bari bangaskiyarku da begenku su kasance ga Allah. Yanzu da kuka tsarkake kanku ta wurin yin biyayya ga gaskiyan nan, don ku kasance da ƙauna mai gaskiya wa ’yan’uwanku, sai ku ƙaunaci juna ƙwarai, daga zuciya. Gama an sāke haihuwarku, ba da iri da yake lalacewa ba, sai dai marar lalacewa, ta wurin rayayyiya da kuma madawwamiyar maganar Allah. Gama, “Dukan mutane kamar ciyawa suke, darajarsu kuma kamar furannin jeji ne; ciyawa takan yanƙwane furannin kuma su kakkaɓe, amma maganar Ubangiji tana nan har abada.” Wannan kuwa ita ce kalmar da aka yi muku wa’azi. Saboda haka, ku rabu da kowace ƙeta da dukan ruɗu, munafunci, kishi, da kuma kowace irin ɓata suna. Kamar sababbin jarirai, ku yi marmarin madara zalla ta ruhaniya, domin ta wurinta za ku yi girma cikin cetonku, yanzu da kuka ɗanɗana alherin Ubangiji. Da kuka zo gare shi, rayayyen Dutse, da mutane suka ƙi amma Allah ya zaɓa, kuma mai daraja a gare shi ku ma, a matsayinku na duwatsu masu rai, ana gina ku ga zama gidan ruhaniya don ku zama tsattsarkar ƙungiyar firistoci, kuna miƙa hadayun ruhaniya, abin karɓa ga Allah ta wurin Yesu Kiristi. Gama a cikin Nassi an ce, “Ga shi, na kafa dutse a Sihiyona, zaɓaɓɓen dutse na kusurwar gini mai daraja, wanda kuma ya dogara gare shi ba zai taɓa kunyata ba.” A gare ku da kuka gaskata, wannan dutse mai daraja ne. Amma ga waɗanda ba su gaskata ba, “Dutsen da magina suka ƙi ya zama dutsen kusurwar gini, kuma, “Dutse ne da yake sa mutane tuntuɓe kuma fā ne da yake sa su fāɗi.” Sun yi tuntuɓe domin sun ƙi su yi biyayya da saƙon, wanda kuma yake abin da aka ƙaddara musu. Amma ku zaɓaɓɓu ne, ƙungiyar firistocin babban Sarki, al’umma mai tsarki, jama’a mallakar Allah, domin ku shaida yabon shi wanda ya kira ku daga cikin duhu zuwa haskensa mai banmamaki. Dā ku ba mutane ba ne, amma yanzu ku mutanen Allah ne; Dā ba ku karɓi jinƙai ba, amma yanzu kun karɓi jinƙai. Abokaina ƙaunatattu, ina roƙonku, a matsayin bare da kuma baƙi a duniya, ku rabu da sha’awace-sha’awacen zunubin da suke yaƙi da ranku. Ku yi irin rayuwa mai kyau a cikin masu bautar gumaka, yadda ko da sun zarge ku da yin laifi, za su iya ganin ayyukanku nagari, su ɗaukaka Allah a ranar da zai ziyarce mu. Saboda Ubangiji, ku yi biyayya ga kowace hukumar da aka kafa cikin mutane, ko ga sarki, a matsayi wanda ya fi iko, ko ga gwamnoni, waɗanda ya aika domin su hukunta masu laifi su kuma yabi masu aikata abin da yake daidai. Gama nufin Allah ne cewa ta wurin yin nagarta za ku toshe jahilcin marasa azanci. Ku yi rayuwa kamar mutanen da aka ’yantar, sai dai kada ku yi amfani da ’yancinku a matsayin hujjar aikata mugunta; ku yi rayuwa kamar bayin Allah. Ku nuna ladabin da ya dace ga kowa. Ku ƙaunaci ’yan’uwantakar masu bi, ku ji tsoron Allah, ku girmama sarki. Bayi, ku yi biyayya ga iyayengijinku da matuƙar ladabi, ba kawai ga waɗanda suke da kirki da masu sauƙinkai ba, amma har ga masu zafin rai ma. Gama abin yabo ne in mutum ya yi haƙuri cikin zafin wahalar rashin adalci saboda yana sane da Allah. Amma ina abin taƙama in kuka sha duka saboda kun yi laifi kuka kuma jimre? Sai dai in kuka sha wahala saboda yin nagari kuka kuma jimre, abin yabo ne a gaban Allah. Ga wannan ne aka kira ku, domin Kiristi ya sha wahala dominku, ya bar muku gurbin da ya kamata ku bi. “Bai taɓa yin laifi ba sam, ba a kuma sami ƙarya a bakinsa ba.” Sa’ad da suka zazzage shi, bai rama ba; sa’ad da ya sha wahala, bai yi barazana ba. A maimakon haka, ya miƙa kansa ga wanda yake shari’ar adalci. Shi kansa ya ɗauki zunubanmu a jikinsa a kan itace, domin mu mutu ga zunubai mu kuma rayu ga adalci; ta wurin raunukansa ne kuka sami warkarwa. Gama dā kuna kama da tumakin da suka ɓace, amma yanzu kun dawo ga Makiyayi da kuma Mai lura da rayukanku. Haka ma, ku matan aure, ku yi biyayya ga mazanku, domin in waɗansunsu ba su gaskata maganar ba, wataƙila a shawo kansu ba tare da magana ba sa’ad da suka ga rayuwarku mai tsabta da kuma na ladabi. Kyanku bai kamata yă zama na adon jiki ba, kamar kitso da sa kayan ado na zinariya da kuma sa kaya masu tsada. Maimakon haka, kyanku ya kamata yă zama ainihi na halinku na ciki, kyan da ba ya koɗewa na tawali’u da kuma na natsattsen ruhu, wanda yake mai daraja a gaban Allah. Gama haka matan masu tsarki na dā waɗanda suka sa begensu ga Allah suka yi wa kansu ado. Sun yi wa mazansu biyayya, kamar Saratu, wadda ta yi biyayya ga Ibrahim, har ta kira shi maigidanta. Ku ’ya’yanta ne mata in kun aikata abin da yake daidai, ba ku kuma ba tsoro dama ba. Mazan aure, ku ma, ku yi zaman sanin ya kamata yayinda kuke zama da matanku, ku girmama su a matsayin abokan zama marasa ƙarfi da kuma a matsayin magādan kyautar rai na alheri tare da ku, don kada wani abu yă hana addu’o’inku. A ƙarshe, dukanku ku zauna lafiya da juna; ku zama masu juyayi, kuna ƙaunar juna kamar ’yan’uwa, ku zama masu tausayi da kuma tawali’u. Kada ku rama mugunta da mugunta ko zagi da zagi, sai dai ku sa albarka, gama ga wannan ne aka kira ku, ku kuma gāji albarka. Gama, “Duk wanda yake so yă ji daɗin rayuwa, yă kuma ga kwanaki masu kyau dole yă ƙame harshensa daga mugunta leɓunansa kuma daga maganar yaudara. Dole yă juye daga mugunta, ya aikata nagarta; dole yă nemi salama yă kuma bi ta. Gama idanun Ubangiji suna a kan masu adalci kunnuwansa kuma suna jin addu’arsu, amma fuskar Ubangiji tana gāba da masu mugunta.” Wa zai yi muku lahani in kun himmantu ga yin nagarta? Amma ko da za ku sha wahala saboda abin da yake daidai, ku masu albarka ne. “Kada ku ji tsoron abin da suke tsoro; kada kuma ku firgita.” Sai dai a cikin zukatanku ku keɓe Kiristi a matsayin Ubangiji. A kullum, ku kasance a shirye ku ba da amsa ga duk wanda yake neman ku ba da dalilin wannan begen da kuke da shi. Amma ku yi wannan cikin tawali’u da ladabi, tare da lamiri mai kyau, saboda waɗanda suke maganganun banza a kan kyawawan ayyukanku cikin Kiristi su ji kunya da irin ɓata suna da suke yi. Ya fi kyau, in nufin Allah ne, a sha wahala don yin nagarta fiye da yin mugunta. Gama Kiristi ya mutu domin zunubi sau ɗaya tak, mai adalci saboda marasa adalci, don yă kawo ku ga Allah. An kashe shi a cikin jiki, amma an rayar da shi a Ruhu, ta wurin wanda kuma ya tafi ya yi wa ruhohin da suke a kurkuku wa’azi waɗanda dā ba su yi biyayya ba sa’ad da Allah ya jira da haƙuri a kwanaki Nuhu yayinda ake sassaƙa jirgi. A cikinsa mutane kima ne kawai, su takwas, aka kuɓutar ta ruwa, ruwan nan kuwa kwatancin baftisma ne da yanzu ya cece ku ku ma, ba kawar da dauda daga jiki ba, sai dai yin alkawari na lamiri mai kyau ga Allah. Ya cece ku ta wurin tashin Yesu Kiristi daga matattu, wanda ya tafi sama, yana kuma a hannun dama na Allah, mala’iku, mulkoki da kuma masu iko suna masa biyayya. Saboda haka, da yake Kiristi ya sha wahala a jikinsa, sai ku ma ku yi wa kanku ɗamara da irin wannan hali, gama wanda ya sha wahala a jikinsa ya gama da zunubi ke nan. Ta haka, ba ya sauran rayuwarsa a kan mugayen sha’awace-sha’awacen jiki, sai dai nufin Allah. Gama kun ɓata lokaci sosai a dā kuna yin abubuwan da masu bauta gumaka suka zaɓa su yi, kuna rayuwa cikin lalata, sha’awace-sha’awace, buguwa, shashanci, shaye-shaye da kuma bautar gumaka masu banƙyama. Sun yi mamaki da ba kwa haɗa kai da su a yanzu, da ba kwa kutsa kai tare da su cikin irin rayuwar banzan nan, har suna zaginku. Amma dole su ba da lissafi gare shi wanda yake a shirye yă shari’anta masu rai da matattu. Dalilin ke nan da ya sa aka yi wa’azin bishara har ga waɗanda yanzu suke mutattu, don ko da yake an hukunta su a matsayin mutane a batun jiki, amma su rayu ga Allah a batun ruhu. Ƙarshen abubuwa duka ya yi kusa. Saboda haka ku kasance masu tunani mai kyau da masu kamunkai don ku iya yin addu’a. Fiye da kome, ku ƙaunaci juna sosai, domin ƙauna tana rufe zunubai masu ɗumbun yawa. Ku riƙa karɓar juna ba da gunaguni ba. Kowa yă yi amfani da kowace baiwar da ya samu don kyautata wa waɗansu, cikin aminci yana aikata alherin Allah a hanyoyi dabam-dabam. In wani ya yi magana, ya kamata yă yi ta a matsayin wanda yake magana ainihin kalmomin Allah. In wani yana yin hidima, ya kamata yă yi ta da ƙarfin da Allah ya tanadar, domin a cikin kome a yabi Allah ta wurin Yesu Kiristi. A gare shi ɗaukaka da iko sun tabbata har abada abadin. Amin. Abokaina ƙaunatattu, kada ku yi mamakin gwaji mai tsananin da kuke sha, sai ka ce wani baƙon abu ne yake faruwa da ku. Sai dai ku yi murna cewa kuna tarayya cikin shan wahalolin Kiristi, domin ku kai ga farin ciki mai yawa sa’ad da aka bayyana ɗaukakarsa. In an zage ku saboda sunan Kiristi, ku masu albarka ne, gama Ruhun ɗaukaka da kuma na Allah yana bisanku. In kuna shan wahala, kada yă zama don ku masu kisankai ne ko ɓarayi ko masu wani irin laifi ko kuma masu shisshigi. Amma fa, in kuka sha wahala a matsayin ku Kirista ne, kada ku ji kunya, sai dai ku yabi Allah cewa kuna amsa wannan suna. Gama lokaci ya yi da za a fara yi wa iyalin Allah shari’a; in kuwa ya fara da mu, to, me zai faru da waɗanda ba sa biyayya da bisharar Allah? Kuma, “In da ƙyar masu adalci su kuɓuta, me zai faru da marasa tsoron Allah da kuma masu zunubi?” Saboda haka, waɗanda suke shan wahala bisa ga nufin Allah ya kamata su danƙa kansu ga Mahaliccinsu mai aminci, su kuma ci gaba da aikata abin da yake daidai. Zuwa ga dattawan da suke cikinku, ina roƙo a matsayin ɗan’uwanku dattijo, mashaidin shan wahalar Kiristi wanda kuma shi ma zai sami rabo cikin ɗaukakar da za a bayyana. Ku zama makiyayan garken Allah da yake a ƙarƙashin kulawarku, kuna hidima kamar masu kula, ba kan dole ba, sai dai da yardar rai, yadda Allah yake so ku zama; ban da kwaɗayin kuɗi, sai dai marmarin yin hidima; ban da nuna iko a kan waɗanda aka danƙa muku amana, sai dai ku zama gurbi ga garken. Sa’ad da kuwa Babban Makiyayin ya bayyana, za ku karɓi rawanin ɗaukaka marar koɗewa. Samari, ku ma, ku yi biyayya ga waɗanda suka girme ku. Dukanku, ku yafa sauƙinkai ga juna, domin, “Allah yana gāba da mai girman kai, amma yakan yi alheri ga mai sauƙinkai.” Saboda haka, ku ƙasƙantar da kanku a ƙarƙashin hannun Allah mai ƙarfi, don yă ɗaukaka ku a lokacin da ya ga dama. Ku danƙa masa dukan damuwarku, domin shi ne yake lura da ku. Ku zama masu kamunkai, ku kuma zauna a faɗake. Abokin gābanku, Iblis yana kewayewa kamar zaki mai ruri, yana neman wanda zai cinye. Ku yi tsayayya da shi, kuna tsayawa daram cikin bangaskiya, domin kun san cewa ’yan’uwanku ko’ina a duniya suna shan irin wahalolin nan. Allah mai dukan alheri, wanda ya kira ku ga madawwamiyar ɗaukaka cikin Kiristi, bayan kun sha wahala na ɗan lokaci, shi da kansa zai raya ku, yă kuma sa ku yi ƙarfi, ku kahu, ku kuma tsaya daram. Gare shi bari iko yă tabbata har abada abadin. Amin. Da taimakon Sila, wanda na ɗauka a matsayin ɗan’uwa mai aminci, na rubuta muku a taƙaice, ina ƙarfafa ku ina kuma shaida muku cewa wannan shi ne alherin Allah na gaske. Ku tsaya daram a cikinsa. Ita wadda take a Babilon, zaɓaɓɓiya tare da ku, tana gaishe ku, haka ma ɗana Markus. Ku gai da juna da sumbar ƙauna. Salama gare ku duka da kuke cikin Kiristi. Siman Bitrus, bawa da kuma manzon Yesu Kiristi, Zuwa ga waɗanda ta wurin adalcin Allahnmu da Mai Cetonmu Yesu Kiristi sun sami bangaskiya mai daraja irin tamu. Alheri da salama su zama naku a yalwace ta wurin sanin Allah da Yesu Ubangijinmu. Ikonsa na Allahntaka ya ba mu kome da muke bukata don rayuwa da kuma tsoron Allah ta wurin sanin wanda ya kira mu ta wurin ɗaukakarsa da nagartarsa. Ta wurin waɗannan ya ba mu alkawaransa masu girma da kuma masu daraja, domin ta wurinsu ku iya yin tarayya cikin Allahntakarsa, ku kuma kuɓuta daga lalatar da take cikin duniya wadda mugayen sha’awace-sha’awace suke jawowa. Saboda haka, ku yi iyakar ƙoƙari ku ƙara wa bangaskiyarku nagarta; ga nagarta kuwa, ku ƙara mata sani; ga sani kuma ku ƙara masa kamunkai; ga kamunkai kuma ku ƙara da daurewa; ga daurewa kuwa ku ƙara da tsoron Allah; ga tsoron Allah kuma ku ƙara da nuna alheri ga ’yan’uwa; ga nuna alheri ga ’yan’uwa kuma ku ƙara da ƙauna. Domin in kuna ƙaruwa a waɗannan halaye, za su kāre ku daga rashin tasiri da rayuwa na rashin amfani cikin saninku na Ubangijinmu Yesu Kiristi. Amma in wani ba shi da su, ba shi da hangen nesa ke nan kuma makaho ne, ya kuma manta cewa an tsarkake shi daga zunubansa na dā. Saboda haka ’yan’uwana, ku ƙara aniya wajen tabbatar da kiranku da zaɓenku da aka yi. Gama in kuka yi waɗannan abubuwa, ba za ku taɓa fāɗuwa ba, za ku sami kyakkyawar marabta cikin madawwamin mulkin Ubangijinmu da Mai Cetonmu Yesu Kiristi. Saboda haka kullum zan tuna muku da waɗannan, ko da yake kun sansu kun kuma kahu ƙwarai cikin gaskiyar da kuke da ita yanzu. A ganina ya dace in tunashe ku muddin ina raye cikin tentin wannan jiki, domin na sani na kusa in ajiye shi a gefe, yadda Ubangijinmu Yesu Kiristi ya nuna mini a sarari. Zan kuwa yi iyakacin ƙoƙari in ga cewa bayan rabuwata kullum za ku iya tuna da waɗannan abubuwa. Ba mu bi tatsuniyoyin da aka ƙaga da wayo sa’ad da muka gaya muku game da ikon Ubangijinmu Yesu Kiristi da zuwansa ba, sai dai mu shaidu ne na ɗaukakarsa mai girma da muka gani da ido. Gama ya sami girma da ɗaukaka daga Allah Uba sa’ad da murya ta zo masa daga Mafificiyar Ɗaukaka cewa, “Wannan Ɗana ne, wanda nake ƙauna; da shi nake jin daɗi ƙwarai.” Mu kanmu mun ji wannan muryar da ta zo daga sama sa’ad da muke tare da shi a kan dutse mai tsarki. Muna kuwa da maganar annabawa da aka ƙara tabbatar mana, zai fi kyau in kuka lura da ita, kamar hasken da yake haskakawa a wuri mai duhu, har yă zuwa wayewar gari da kuma haskakawar tauraron asubahi a zukatanku. Gaba da kome dai, dole ku gane cewa babu annabcin Nassin da ya fito daga fassarar annabi da kansa. Gama annabci bai taɓa samo tushensa daga nufin mutum ba, sai dai mutane sun yi magana daga Allah yayinda Ruhu Mai Tsarki ya bishe su. Amma a dā akwai annabawan ƙarya a cikin mutane, kamar yadda za a sami malaman ƙarya a cikinku. A ɓoye za su shigar da karkataccen koyarwa mai hallaka, har ma su yi mūsun Ubangiji mai iko duka wanda ya saye su suna kawo wa kansu hallaka farat ɗaya. Da yawa za su bi hanyoyinsu na rashin kunya su kuma sa a rena hanyar gaskiya. Cikin kwaɗayinsu waɗannan malaman ƙarya za su cuce ku da tatsuniyoyin da suka ƙaga. Hukuncinsu yana a rataye a kansu tun da daɗewa, hallakarsu kuma ba ta barci. Gama in har Allah bai ƙyale mala’iku sa’ad da suka yi zunubi ba, amma ya tura su cikin lahira, domin a tsare su don hukunci; in har bai ƙyale duniya ta dā ba sa’ad da ya kawo ambaliya a kan mutanenta marasa tsoron Allah, amma ya kiyaye Nuhu, mai wa’azin adalci, da kuma waɗansu bakwai; in har ya hukunta biranen Sodom da Gomorra ta wurin ƙone su suka zama toka, ya kuma maishe su misali na abin da zai faru da marasa tsoron Allah; in kuwa har ya ceci Lot, mai adalci, wanda ya damu ainun da ƙazamar rayuwar mutane marasa bin doka; (adon kuwa abin da adalin nan ya yi, ya kuma gani, sa’ad da yake a cikinsu, sai kowace rana yakan ji ciwon aikinsu na kangara a zuciyarsa mai adalci) in haka ne, to, Ubangiji ya san yadda zai ceci mutane masu tsoron Allah daga gwaje-gwaje, yă kuma tsare marasa adalci don ranar hukunci, har yă zuwa ranar shari’a. Wannan gaskiya ce musamman ga waɗanda suke bin sha’awace-sha’awacen lalaci na mutuntaka, suna kuma rena masu mulki. Da ƙarfin hali da kuma girman kai, waɗannan mutane ba sa tsoro kawo zargin ɓata sunan talikan sama; duk da haka ko mala’iku ma da suka fi su ƙarfi suka kuma fi su iko, ba sa kawo irin wannan zargi na ɓata suna game da waɗannan talikai a gaban Ubangiji. Amma waɗannan mutane suna yin saɓo a kan abubuwan da ba su fahimta ba. Suna kama da dabbobi marasa hankali, halittun da suke bin abin da jikinsu ya faɗa musu kawai, waɗanda aka haifa don a kama a hallaka, kuma kamar dabbobi su ma za su hallaka. Za a yi musu sakamako da muguntar da suka yi. A ra’ayinsu jin daɗi shi ne a yi annashuwa da rana tsaka. Su ƙazamai ne marasa kunya, suna cike da jin daɗin sha’awace-sha’awacensu yayinda suke cin biki tare da ku. Idanunsu sun cike da zina, ba sa ƙoshi da yin zunubi; suna jarrabtar waɗanda ba tsayayyu ba; gwanaye ne a kan kwaɗayi, la’anannun iri! Sun bar miƙaƙƙiyar hanya suka bauɗe suna bin hanyar Bala’am ɗan Beyor, wanda ya yi ƙaunar hakkin mugunta. Amma an tsawata masa saboda laifinsa ta wurin jaki, dabbar da ba ta magana, wadda ta yi magana da muryar mutum ta kuma kwaɓi haukan annabin. Waɗannan mutane maɓulɓulai ne babu ruwa da kuma hazon da guguwar iska take kora. An shirya matsanancin duhu dominsu. Gama suna surutai banza na girman kai, ta wurin son bin fasikanci na mutuntaka, sukan jan hankulan mutanen da suke kuɓucewa daga waɗancan masu zama cikin kuskure. Suna yin musu alkawarin ’yanci, yayinda su kansu bayi ne ga aikin lalata gama mutum bawa ne ga duk abin da ya mallake shi. In har sun kuɓuta daga lalacin duniya ta wurin sanin Ubangijinmu da kuma Mai Cetonmu Yesu Kiristi sai suka sāke koma a cikin lalacin, har ya rinjaye su, za su fi muni a ƙarshe fiye da farko. Zai fi musu kyau da ba su taɓa sanin hanyar adalci ba, fiye da a ce sun sani sa’an nan su juya bayansu ga umarni mai tsarkin nan da aka ba su. A kansu karin maganan nan gaskiya ce, “Kare ya koma kan amansa,” da kuma, “Alade da aka yi wa wanka, ya koma birgimarsa cikin laka.” Abokaina ƙaunatattu, wannan ita ce wasiƙata ta biyu gare ku. Na rubuta su biyun su zama abin tuni don su faɗakar da ku ga tunani mai kyau. Ina so ku tuna da kalmomin da annabawa masu tsarki na dā suka faɗa da kuma umarnin da Ubangijinmu da Mai Cetonmu ya bayar ta wurin manzanninku. Da farko dai, dole ku fahimci wannan cewa a kwanakin ƙarshe masu ba’a za su zo suna ba’a, suna bin mugayen sha’awace-sha’awacensu. Za su ce, “Ina wannan ‘dawowar’ da ya yi alkawari ne? Tun mutuwar kakanninmu, kome yana tafiya kamar yadda yake tun farkon halitta.” Amma da gangan suke manta cewa tun dā can ta wurin maganar Allah sammai suka kasance aka kuma yi ƙasa daga ruwa ta wurin ruwa kuma. Ta wurin waɗannan ruwan ne aka nutsar, aka kuma hallakar da duniya ta wancan lokaci. Ta wurin wannan magana ce aka ajiye sammai da ƙasa na yanzu domin wuta, an ajiye su kuma don ranar hukunci da hallaka ta mutane marasa tsoron Allah. Amma kada ku manta da wannan abu guda ɗaya, abokaina ƙaunatattu. Ga Ubangiji kwana ɗaya kamar shekaru dubu ne, shekaru dubu kuma kamar kwana ɗaya ne. Ubangiji ba mai jinkiri ba ne wajen cika alkawarinsa, yadda waɗansunku suka fahimci jinkiri. Yana haƙuri da ku, ba ya so wani yă hallaka, sai dai kowa yă kai ga tuba. Amma ranar Ubangiji za tă zo kamar ɓarawo. Sammai za su ɓace da ruri, abubuwan da suke cikinsu za su ƙone, ƙasa kuma da dukan abin da yake cikinta za su tonu. Da yake za a hallaka dukan abubuwa ta haka, waɗanne irin mutane ne ya kamata ku zama? Ya kamata ku yi rayuwar tsarki da ta tsoron Allah, yayinda kuke zuba ido ga zuwan ranar Allah kuna gaggauta zuwanta. Wannan rana za tă kawo wa sammai hallaka ta ƙunan wuta, abubuwa kuma za su narke don zafi. Amma bisa ga alkawarinsa muna zuba ido ga sabuwar sama da kuma sabuwar ƙasa, inda adalci zai yi zama. Saboda haka, abokaina ƙaunatattu, da yake kuna zuba ido ga wannan, sai ku yi matuƙar ƙoƙari don a same ku ba tabo, sai dai zaman salama da shi. Ku yi zaman sanin cewa haƙurin Ubangijinmu yana nufin ceto ne, kamar yadda ƙaunataccen ɗan’uwanmu Bulus ma ya rubuta muku da hikimar da Allah ya ba shi. Haka yake rubutu cikin dukan wasiƙunsa, yana magana a cikinsu a kan waɗannan al’amura. Wasiƙunsa sun ƙunshi waɗansu abubuwa masu wuyar fahimta, waɗanda jahilai da kuma waɗanda ba tsayayyu ba ne suke murɗe ma’anarsu, kamar yadda suke yi da sauran Nassosi, ta haka suke jawo wa kansu hallaka. Saboda haka, abokaina ƙaunatattu, da yake kun riga kun san wannan, sai ku zauna a faɗake don kada a ɗauke hankalinku ta wurin kuskuren marasa bin dokan nan har ku fāɗi daga matsayinku. Sai dai ku yi girma cikin alheri da sanin Ubangijinmu da Mai Cetonmu Yesu Kiristi. A gare shi ɗaukaka ta tabbata yanzu da har abada! Amin. Wannan da ya kasance tun farko, wanda muka ji, wanda muka gani da idanunmu, wanda muka duba, hannuwanmu kuma suka taɓa, wannan ne muke shela game da Kalman rai. Wannan Rai ya bayyana, muka kuwa gan shi, muka kuma shaida shi, muna kuwa yin muku shelar wannan rai madawwami, wanda dā yake tare da Uba, ya kuma bayyana a gare mu. Muna yin muku shelar abin da muka gani, muka kuma ji ne, domin ku ma ku yi zumunci tare da mu. Zumuncinmu kuwa yana tare da Uba da kuma Ɗansa, Yesu Kiristi. Muna rubuta wannan domin farin cikinmu yă zama cikakke. Wannan shi ne saƙon da muka ji daga wurinsa, muna kuma sanar da ku cewa Allah haske ne; a cikinsa kuwa babu duhu ko kaɗan. In muka ce muna zumunci da shi amma muna tafiya cikin duhu, ƙarya muke yi, kuma ba ma rayuwa bisa ga gaskiya. Amma in muna tafiya cikin haske, yadda yake cikin haske, muna da zumunci da juna ke nan, kuma jinin Yesu, Ɗansa, yana tsarkake mu daga dukan zunubi. In muka ce ba mu da zunubi, muna ruɗin kanmu ne, gaskiya kuwa ba ta cikinmu. In muka furta zunubanmu, shi mai aminci ne, mai adalci kuma, zai gafarta mana zunubanmu, yă kuma tsarkake mu daga dukan rashin adalci. In muka ce ba mu yi zunubi ba, mun mai da shi maƙaryaci ke nan, maganarsa kuwa ba ta da wuri a cikinmu. ’Ya’yana ƙaunatattu, ina rubuta muku wannan ne don kada ku yi zunubi. Amma in wani ya yi zunubi, muna da wani wanda yake magana da Uba don taimakonmu, wato, Yesu Kiristi, Mai Adalci. Shi ne hadayar kafara saboda zunubanmu, kuma ba don namu kaɗai ba amma har ma da zunuban duniya duka. Ta haka za mu tabbata cewa mun san shi in muna yin biyayya da umarnansa. Mutumin da ya ce, “Na san shi,” amma ba ya yin abin da ya umarta, maƙaryaci ne, gaskiya kuwa ba ta cikinsa. Amma in wani ya yi biyayya da maganarsa, ƙaunar Allah ta zama cikakkiya ke nan a cikinsa. Ta haka muka san cewa muna cikinsa. Duk wanda ya ce yana rayuwa a cikinsa dole yă yi tafiya kamar yadda Yesu ya yi. Abokaina ƙaunatattu, ba sabon umarni nake rubuta muku ba, a’a, daɗaɗɗen umarnin nan ne, wanda kuke da shi tun farko. Wannan tsohon umarni shi ne saƙon da kuka riga kuka ji. Duk da haka ina rubuta muku sabon umarni; ana ganin gaskiyar umarnin a cikinsa da kuma cikinku, gama duhu yana shuɗewa, haske na gaskiya kuwa yana haskakawa. Duk wanda ya ce yana cikin haske yana kuma ƙin ɗan’uwansa, ashe a duhu yake har yanzu. Duk wanda yake ƙaunar ɗan’uwansa, a cikin hasken yake rayuwa ke nan, kuma babu wani abin da yake cikinsa da zai sa yă yi tuntuɓe. Amma duk wanda yake ƙin ɗan’uwansa, cikin duhu yake, yana kuma tafiya cikin duhu ke nan; bai ma san inda za shi ba, domin duhun ya makanta shi. Ina rubuta muku, ’ya’yana ƙaunatattu, domin an gafarta muku zunubanku saboda sunansa. Ina rubuta muku, ubanni, domin kun san shi wanda yake tun farko. Ina rubuta muku, samari, domin kun ci nasara a kan mugun nan. Ina rubuta muku, ’ya’yana ƙaunatattu, domin kun san Uba. Ina rubuta muku, ubanni, domin kun san shi wanda yake tun farko. Ina rubuta muku, samari, domin kuna da ƙarfi, maganar Allah kuwa tana zaune a cikinku, kun kuma ci nasara a kan mugun nan. Kada ku ƙaunaci duniya, ko wani abin da yake cikinta. In wani yana ƙaunar duniya, ƙaunar Uba ba ta cikinsa. Gama duk abin da yake na duniya, kamar sha’awace-sha’awacen mutuntaka, sha’awar idanunsa, da kuma taƙama da abin da yake da shi, yake kuma yi, ba daga wurin Uba suke fitowa ba sai dai daga duniya. Duniya da sha’awace-sha’awacenta suna shuɗewa, amma mutumin da yake aikata nufin Allah, zai rayu har abada. ’Ya’yana ƙaunatattu, waɗannan su ne kwanakin ƙarshe; kuma kamar yadda kuka ji cewa magabcin Kiristi yana zuwa, ko yanzu ma abokan gāban Kiristi da yawa sun zo. Ta haka muka san cewa kwanakin ƙarshe sun iso. Waɗannan masu gāba da Kiristi suna cikinmu a dā, amma sun bar mu, don tun dā ma su ba namu ba ne. Ai, da su namu ne, da har yanzu suna tare da mu. Amma sun bar mu, wannan ya nuna a fili cewa su ba namu ba ne. Amma ku kam, kuna da shafewa daga wurin Mai Tsarkin nan, kuma dukanku kun san gaskiya. Ina rubuta muku ba domin ba ku san gaskiya ba ne, a’a, sai dai domin kun santa, kun kuma san cewa babu yadda ƙarya za tă fito daga gaskiya. Wane ne maƙaryaci? Ai, shi ne mutumin da yake mūsun cewa Yesu shi ne Kiristi. Irin wannan mutum shi ne magabcin Kiristi, ya yi mūsun Uban da kuma Ɗan. Ba wanda yake mūsun Ɗan, sa’an nan yă ce yana da Uban; duk wanda ya yarda da Ɗan, yana da Uban a cikinsa ke nan. Ku lura fa cewa abin da kuka ji daga farko, bari yă ci gaba da kasance a cikinku. In kuwa ya ci gaba da zama a cikinku, za ku kasance a cikin Ɗan, da kuma a cikin Uban. Wannan shi ne abin da ya yi mana alkawari, wato, rai madawwami. Ina rubuta muku waɗannan abubuwa ne game da waɗanda suke ƙoƙari su sa ku kauce. Game da ku kuwa, shafan nan da kuka karɓa daga gare shi tana nan a cikinku, ba kwa kuma bukata wani yă koyar da ku. Amma kamar yadda shafan nan tasa tana koya muku kome, ita kuwa gaskiya ce ba ƙarya ba, yadda dai ta koya muku, to, sai ku zauna a cikinsa. Yanzu fa, ya ku ’ya’yana ƙaunatattu, sai ku ci gaba a cikinsa, domin sa’ad da ya bayyana, mu iya tsaya gabagadi babu kunya a dawowarsa. In kun san cewa shi mai adalci ne, to, kun dai san cewa duk mai aikata abin da yake daidai haifaffensa ne. Dubi irin ƙaunar da Uba ya ƙaunace mu da ita mana, har ana ce da mu ’ya’yan Allah! Haka kuwa muke! Dalilin da ya sa duniya ba tă san mu ba shi ne, don ba tă san shi ba. Abokaina ƙaunatattu, yanzu, mu ’ya’yan Allah ne, kuma abin da za mu zama nan gaba ba a riga an bayyana ba. Sai dai mun san cewa sa’ad da Kiristi ya bayyana, za mu zama kamar sa, domin za mu gan shi kamar yadda yake. Duk mai wannan bege a cikinsa yakan tsarkake kansa, kamar yadda shi Kiristi yake da tsabta. Duk mai yin zunubi yana karya doka ne; tabbatacce, zunubi, karya doka ne. Sai dai kun san cewa Kiristi ya bayyana ne domin yă ɗauke zunubanmu. A cikinsa kuwa babu zunubi. Ba mai rayuwa a cikinsa da yake cin gaba da yin zunubi. Kowa da yake aikata zunubi, bai taɓa ganinsa ba, bai ma san shi ba. ’Ya’yana ƙaunatattu, kada ku yarda wani yă ruɗe ku. Duk mai yin abin da yake daidai mai adalci ne, yadda Kiristi yake mai adalci. Duk mai aikata abin da yake zunubi shi na Iblis ne, domin Iblis mai aikata zunubi ne tun farko. Dalilin da ya sa Ɗan Allah ya bayyana kuwa shi ne don yă rushe aikin Iblis. Babu haifaffe na Allah da zai ci gaba da yin zunubi, domin iri na Allah yana a cikinsa; ba zai iya ci gaba da yin zunubi ba, domin haifaffe ne na Allah. Ta haka muka san waɗanda suke ’ya’yan Allah da kuma waɗanda suke ’ya’yan Iblis. Duk wanda ba ya yin abin da yake daidai, ba ɗan Allah ba ne; haka ma wanda ba ya ƙaunar ɗan’uwansa. Wannan shi ne saƙon da kuka ji tun farko. Ya kamata mu ƙaunaci juna. Kada ku zama kamar Kayinu, wanda ya zama na mugun nan, ya kuma kashe ɗan’uwansa. Me ya sa ya kashe shi? Domin ayyukansa mugaye ne, na ɗan’uwansa kuma na adalci ne. Kada ku yi mamaki ’yan’uwana, in duniya ta ƙi ku. Mun san cewa mun riga mun ratsa daga mutuwa zuwa rai, domin muna ƙaunar ’yan’uwanmu. Duk wanda ba ya ƙauna matacce ne har yanzu. Duk mai ƙin ɗan’uwansa mai kisankai ne, kun kuma san cewa ba mai kisankan da yake da rai madawwami a cikinsa. Yadda muka san ƙauna ke nan, wato, Yesu Kiristi ya ba da ransa dominmu. Ya kamata mu ma mu ba da rayukanmu domin ’yan’uwanmu. In wani yana da arziki, ya kuma ga ɗan’uwansa cikin rashi, bai kuwa taimake shi ba, anya, ƙaunar Allah tana a cikinsa kuwa? ’Ya’yana ƙaunatattu, kada mu yi ƙauna da fatar baki kawai, sai dai mu nuna ta ta wurin aikatawa da kuma gaskiya. Ta haka muka san cewa mu na gaskiya ne, kuma za mu iya tsaya a gaban Allah ba tare da rawar jiki ba. Idan zuciyarmu ta nuna mana muna da laifi, mun san cewa Allah ya fi zuciyarmu, ya kuma san dukan kome. Abokaina ƙaunatattu, in zukatanmu ba su ba mu laifi ba, muna da ƙarfin halin tsayawa a gaban Allah ke nan. Muna kuma samun dukan abin da muka roƙa daga gare shi, domin muna biyayya da umarnansa, muna kuma yin abin da ya gamshe shi. Umarninsa kuwa shi ne, mu gaskata da sunan Ɗansa, Yesu Kiristi, mu kuma ƙaunaci juna kamar yadda ya umarce mu. Waɗanda suke biyayya da umarnansa kuwa suna rayuwa a cikinsa, shi kuma a cikinsu. Ta haka muka san cewa yana raye a cikinmu. Mun san haka ta wurin Ruhun da ya ba mu. Abokaina ƙaunatattu, ba kowane ruhu za ku gaskata ba, sai dai ku gwada ruhohi don ku ga ko daga Allah ne, domin annabawan ƙarya da yawa sun fito duniya. Ga yadda za ku gane Ruhun Allah, duk ruhun da ya yarda cewa Yesu Kiristi ya zo cikin jiki, to, daga Allah yake. Amma duk ruhun da bai yarda da Yesu ba, ba daga Allah ba ne, ruhun magabcin Kiristi ne, wanda kuka ji yana zuwa, har ma ya riga ya shigo duniya. Ku, ’ya’yana ƙaunatattu, ku daga Allah ne, kun kuma yi nasara a kan magabtan Kiristi, domin wanda yake a cikinku ya fi wanda yake a duniya girma. Su daga duniya ne saboda haka suke magana yadda duniya take ganin abubuwa, duniya kuwa tana sauraronsu. Mu daga Allah ne, kuma duk wanda ya san Allah yakan saurare mu. Amma duk wanda ba daga Allah ba, ba ya sauraronmu. Ta haka ne muke gane Ruhun gaskiya, da kuma ruhun ƙarya. Abokaina ƙaunatattu, mu ƙaunaci juna, domin ƙauna tana zuwa daga Allah ne. Duk mai ƙauna, haifaffe ne na Allah, ya kuma san Allah. Duk wanda ba ya ƙauna, bai san Allah ba, domin Allah ƙauna ne. Ga yadda Allah ya nuna ƙaunarsa a cikinmu, Allah ya aiki makaɗaici Ɗansa zuwa duniya domin mu rayu ta wurinsa. Wannan ita ce ƙauna, wato, ba mu ne muka ƙaunaci Allah ba, sai dai shi ne ya ƙaunace mu, ya kuma aiko Ɗansa yă zama hadaya ta kafara saboda zunubanmu. Abokaina ƙaunatattu, da yake Allah ya ƙaunace mu haka, ya kamata mu ma mu ƙaunaci juna. Ba wanda ya taɓa ganin Allah; amma in muna ƙaunar juna, Allah yana raye a cikinmu, ƙaunarsa kuwa ta zama cikakkiya a cikinmu ke nan. Mun san cewa muna rayuwa a cikinsa shi kuma a cikinmu, domin ya ba mu Ruhunsa. Mun gani, mun kuma shaida cewa Uba ya aiko Ɗansa domin yă zama Mai Ceton duniya. Duk wanda ya yarda cewa Yesu Ɗan Allah ne, Allah yana raye a cikinsa, shi kuma a cikin Allah. Ta haka muka sani, muke kuma dogara ga ƙaunar da Allah yake mana. Allah ƙauna ne. Duk wanda yake rayuwa cikin ƙauna, yana rayuwa a cikin Allah ne, Allah kuma a cikinsa. Ta haka, ƙauna ta zama cikakkiya a cikinmu domin mu kasance masu ƙarfin hali a ranar shari’a, domin a wannan duniya muna kama da shi. Babu tsoro cikin ƙauna. Cikakkiyar ƙauna dai takan kawar da tsoro, domin hukunci ne yake kawo tsoro. Mai jin tsoro ba cikakke ba ne a cikin ƙauna. Muna ƙauna, domin ya ƙaunace mu da farko. Duk wanda ya ce, “Ina ƙaunar Allah,” amma yana ƙin ɗan’uwansa, maƙaryaci ne. Gama duk wanda ba ya ƙaunar ɗan’uwansa da yake gani, ba zai iya ƙaunar Allah wanda ba ya gani ba. Ya kuma ba mu wannan umarni cewa duk wanda yake ƙaunar Allah, dole yă ƙaunaci ɗan’uwansa. Kowa ya gaskata cewa Yesu shi ne Kiristi, shi haifaffe na Allah ne, kuma duk mai ƙaunar mahaifi kuwa, yakan ƙaunaci ɗansa ma. Ga yadda muka san cewa muna ƙaunar ’ya’yan Allah. Muna yin haka ta wurin ƙaunar Allah da kuma aikata umarnansa. Ƙaunar Allah ita ce, a yi biyayya da umarnansa. Umarnansa kuwa ba masu nauyi ba ne; domin duk haifaffe na Allah yana cin nasara a kan duniya. Bangaskiyarmu kuwa ita ce ta ba mu wannan nasara a kan duniya. Wa ya cin nasara a kan duniya? Sai wanda ya gaskata cewa Yesu Ɗan Allah ne. Ga wanda ya zo ta wurin ruwa da jini, wato, Yesu Kiristi. Bai zo ta wurin ruwa kaɗai ba, sai dai ta wurin ruwa da kuma jini. Ruhu ne kuwa yake ba da shaida, gama Ruhu shi ne gaskiya. Akwai shaidu uku, wato, Ruhu, da ruwa, da kuma jini; waɗannan uku kuwa manufarsu ɗaya ce. Tun da yake mukan yarda da shaida mutane, ai, shaidar Allah ta fi ƙarfi. Wannan ita ce shaidar Allah, wato, ya shaidi Ɗansa. Duk wanda ya gaskata da Ɗan Allah, yana da shaidan nan a zuciyarsa. Duk wanda bai gaskata da Allah ba kuwa ya mai da shi maƙaryaci, domin bai gaskata shaidar da Allah ya bayar game da Ɗansa ba. Wannan kuwa ita ce shaidar; cewa Allah ya ba mu rai madawwami, wannan rai kuwa yana cikin Ɗansa. Duk wanda yake da Ɗan, yana da rai; wanda kuwa ba shi da Ɗan Allah, ba shi da rai. Ina rubuta waɗannan abubuwa gare ku, ku da kuka gaskata sunan Ɗan Allah domin ku san kuna da rai madawwami. Wannan shi ne ƙarfin halin da muke da shi sa’ad da muke zuwa a gaban Allah, gama mun san cewa kome muka roƙa bisa ga nufinsa, yakan saurare mu. In kuwa muka san cewa yana sauraranmu, ko mene ne muka roƙa, mun sani, mun riga mun sami abin da muka roƙa daga gare shi ke nan. Kowa ya ga ɗan’uwansa yana yin zunubin da bai kai ga mutuwa ba, sai yă yi masa addu’a. Ta dalilin mai addu’an nan kuwa, Allah zai ba da rai ga mai yin zunubin da bai kai ga mutuwa ba. Akwai zunubin da yakan kai ga mutuwa. Ban ce a yi addu’a domin wannan ba. Duk rashin adalci, zunubi ne, amma akwai waɗansu zunuban da ba sa kai ga mutuwa. Mun san cewa kowane haifaffe na Allah ba ya cin gaba da yin zunubi; kasancewarsa haifaffe na Allah ita takan kāre shi, mugun kuwa ba zai iya cuce shi ba. Mun san cewa mu ’ya’yan Allah ne, duniya duka kuwa tana hannun Mugun. Mun san cewa Ɗan Allah ya zo duniya, ya kuma ba mu ganewa domin mu san shi wanda yake na gaskiya. Mu kuwa muna cikinsa, shi da yake Allah na gaskiya wato, cikin Ɗansa Yesu Kiristi. Shi ne Allah na gaskiya da kuma rai na har abada. ’Ya’yana ƙaunatattu, ku yi nesa da gumaka. Dattijon nan, Zuwa ga uwargida zaɓaɓɓiya da kuma ’ya’yanta, waɗanda nake ƙauna ƙwarai da gaske kuma ba ni kaɗai ba, amma har da dukan waɗanda suka san gaskiya. Muna ƙaunarku saboda gaskiyan nan, wadda take cikinmu za tă kuma kasance tare da mu har abada. Alheri, jinƙai da kuma salama daga Allah Uba da kuma Yesu Kiristi, Ɗan Uba, su kasance tare da mu cikin gaskiya da ƙauna. Na yi farin ciki ƙwarai, da na sami waɗansu ’ya’yanki suna tafiya cikin gaskiya, kamar yadda Uba ya umarce mu. Yanzu kuma, uwargida ƙaunatacciya, ba sabon umarni nake rubuta miki ba sai dai wanda muke da shi tun farko. Ina roƙo cewa mu ƙaunaci juna. Ƙauna, ita ce mu yi biyayya ga umarnansa. Kamar yadda kuka ji tun da fari, umarninsa shi ne ku yi zaman ƙauna. Masu ruɗi da yawa, waɗanda ba su yarda da zuwan Yesu Kiristi cikin jiki ba, sun riga sun fito a duniya. Duk irin mutumin nan mai ruɗi ne kuma magabcin Kiristi. Ku lura don kada ku yi hasarar aikin da kuka yi, sai dai ku sami cikakken lada. Duk mutumin da bai tsaya a kan koyarwar Kiristi ba, amma ya yi ƙari a kanta, mutumin nan ba shi da Allah. Amma wanda ya tsaya a kan koyarwar Kiristi, yana da Uban da kuma Ɗan. Duk wanda ya zo wurinku bai kuma kawo koyarwan nan ba, kada ku karɓe shi a gidanku ko ku marabce shi. Duk wanda ya karɓe shi yana tarayya da mugun aikinsa ke nan. Ina da abubuwa da dama da zan rubuta muku, sai dai ba na so in yi amfani da takarda da inki in rubuta. A maimako, ina fata in ziyarce ku in kuma yi magana da ku fuska da fuska, domin farin cikinmu yă zama cikakke. ’Ya’yan ’yar’uwarki wadda Allah ya keɓe, suna gaishe ku. Dattijon nan, Zuwa ga ƙaunataccen abokina Gayus, wanda nake ƙauna ƙwarai da gaske. Abokina ƙaunatacce, ina addu’a ka sami zaman lafiya don kome yă yi maka daidai, kamar yadda ruhunka yake zaune lafiya. Na yi farin ciki ƙwarai sa’ad da waɗansu ’yan’uwa suka zo suka yi zance game da yadda kake da aminci ga gaskiyan nan da kuma yadda kake cin gaba cikin gaskiyan nan. Ba abin da ya fi sa ni farin ciki fiye da in ji cewa ’ya’yana suna cikin gaskiyan nan. Abokina ƙaunatacce, kana da aminci cikin abin da kake yi wa ’yan’uwa, ko da yake su baƙi ne a gare ka. Sun faɗa wa ikkilisiya game da ƙaunarka. Za ka kyauta in ka sallame su a hanyar da ta cancanci Allah. Saboda Sunan nan ne suka fito, ba sa karɓan wani taimako daga waɗanda ba masu bi ba. Saboda haka ya kamata mu nuna halin karɓan baƙi ga irin mutanen nan domin mu yi aiki tare saboda gaskiyan nan. Na rubuta wa ikkilisiya, amma Diyotirefes, wanda yake son zama na farko, ya ƙi yă yi hulɗa da mu. Saboda haka in na zo, zan tone abin da yake yi, yana surutu game da mu, yana ɓaɓɓata mu. Wannan ma bai ishe shi ba, har yana ƙin marabtar ’yan’uwa. Yana hana waɗanda suke so yin haka, yana ma korinsu daga ikkilisiya. Abokina ƙaunatacce, kada ka yi koyi da abin da yake mugu sai dai abin da yake nagari. Duk mai yin abin da yake nagari daga Allah yake. Duk mai yin abin da yake mugu bai taɓa sanin Allah ba. Demetiriyus yana da shaida mai kyau daga wurin kowa, har gaskiya kanta ma ta shaide shi. Mu ma muna ba da shaida mai kyau a kansa, ka kuma san cewa shaidarmu gaskiya ce. Ina da abubuwa da dama da zan rubuta maka, sai dai ba na so in yi amfani da alƙalami da inki in rubuta su. Ina fata in gan ka nan ba da daɗewa ba, za mu kuwa yi magana fuska da fuska. Salama gare ka. Abokai a nan suna gaishe ka. Ka gai da abokai a can da sunansu. Yahuda, bawan Yesu Kiristi, ɗan’uwan Yaƙub, Zuwa ga waɗanda aka kira, waɗanda Allah Uba yake ƙauna, waɗanda kuma Yesu Kiristi ya kiyaye. Jinƙai, salama da kuma ƙauna, su kasance tare da ku a yalwace. Abokaina ƙaunatattu, ko da yake na yi marmari ƙwarai in rubuta muku game da ceton nan namu, sai na ga ya dace in rubuta, in gargaɗe ku ku tsaya da ƙarfi cikin bangaskiya wadda aka danƙa wa mutane masu tsarki na Allah sau ɗaya tak. Na faɗa haka ne domin waɗansu mutanen da aka rubuta hukuncinsu tun dā sun shiga cikinku a ɓoye. Su fa marasa tsoron Allah ne. Su ne waɗanda suka mai da alherin Allahnmu ya zama dalilin yin fasikanci, suna kuma mūsun Yesu Kiristi wanda shi ne Makaɗaici Mai Iko Duka da kuma Ubangijinmu. Ko da yake kun riga kun san duk wannan, ina so in tuna muku cewa Ubangiji ya ceci mutanensa daga Masar, duk da haka daga baya ya hallaka waɗanda ba su ba da gaskiya ba. Haka ma mala’ikun da ba su riƙe matsayinsu na iko ba, waɗanda suka bar ainihin mazauninsu, su ne ya tsare a duhu daure da dawwammamun sarƙoƙi don hukunci ta babbar Ranan nan. Haka ma Sodom da Gomorra da garuruwan da suke kewaye da su, waɗanda su ma suka ba da kansu ga fasikanci da muguwar sha’awar jiki, sun zama misalin waɗanda suke shan hukuncin madawwamiyar wuta. Haka yake da masu mafarke-mafarken nan, gama sun ƙazantar da jikunansu, suka ƙi bin masu mulki, suna ɓata sunan talikan sararin sama. Kai, ko Mika’ilu babban shugaban mala’iku ma, sa’ad da yake mūsu da Iblis game da gawar Musa, bai yi garajen ɗora masa laifi da baƙar magana ba, sai dai ya ce, “Ubangiji yă tsawata maka!” Duk da haka mutanen nan suna maganar banza a kan kome da ba su gane ba; kuma abubuwan da suka fahimta bisa ga jiki, kamar dabbobi marasa hankali, waɗannan abubuwa ne suke hallaka su. Kaitonsu! Gama sun kama hanyar Kayinu; sun ruga a guje garin neman riba cikin kuskure kamar Bala’am; aka kuma hallaka su cikin tawayen Kora. Waɗannan mutane sun zama kamar ƙazanta a taronku na soyayya, suna ta ciye-ciye a cikinku, ba kunya ba tsoro. Su masu kiwo ne da suke ciyar da kansu kawai. Su kamar hadari ne da babu ruwa da iska take kori. Su kamar itatuwa ne, marasa ’ya’ya da rani, waɗanda aka tumɓuke, ko kamar itatuwan da aka tumɓuke suka kuma mutu ƙurmus. Su kamar raƙuman ruwan teku ne masu hauka, suna taƙama da tumbatsan kumfar kunyarsu. Su kamar taurari ne masu yawo barkatai, waɗanda aka ajiye mugun duhu saboda su har abada. Enok ma, wanda yake na bakwai daga Adamu, ya yi annabci game da waɗannan mutane cewa, “Duba, Ubangiji yana zuwa da dubu dubban tsarkakansa don yă yi wa kowa shari’a, yă kuma hukunta duk marasa tsoron Allah game da dukan ayyukansu na rashin tsoron Allah da suka aikata ta hanyar rashin tsoron Allah, da kuma dukan baƙaƙen kalmomin da masu zunubi marasa tsoron Allah suka faɗa game da shi.” Waɗannan mutane dai, gunaguni gare su, kullum ganin laifin waɗansu suke yi. Muguwar sha’awa ce kaɗai tunaninsu. Sun cika da banzar magana ta yabon kansu. Suna ruɗin mutane da zaƙin baki don samun ribar kansu. Amma ku abokaina ƙaunatattu, ku tuna da abin da manzannin Ubangijinmu Yesu Kiristi suka faɗa a dā. Sun ce muku, “A kwanakin ƙarshe za a kasance da masu ba’a waɗanda za su bi sha’awace-sha’awacensu na rashin tsoron Allah.” Waɗannan mutanen ne, suke kawo rabe-rabe, masu bin abin da jiki yake so, marasa Ruhu. Amma ku, abokaina ƙaunatattu, ku gina kanku cikin bangaskiyarku mafi tsarki, ku kuma yi addu’a cikin Ruhu Mai Tsarki. Ku zauna cikin ƙaunar Allah yayinda kuke jira jinƙan Ubangijinmu Yesu Kiristi don yă kawo ku ga rai madawwami. Ku ji tausayin waɗanda suke shakka; ku cece waɗansu ta wurin fizge su daga wuta. Ga waɗansu kuma ku ji tausayinsu, amma tare da tsoro, har ma ku yi ƙyamar tufafin da suka ɓata da ayyukansu na jiki. To, yabo yă tabbata a gare shi, shi wanda yake da iko yă tsare ku daga fāɗuwa, yă kuma miƙa ku marasa laifi a gaban ɗaukakarsa da matuƙar farin ciki. Gare shi kuma, shi da yake kaɗai Allah Mai Cetonmu, ta wurin Yesu Kiristi Ubangijinmu, bari ɗaukaka, daraja, iko da mulki, su tabbata a gare shi, tun farkon zamanai, yanzu, da har abada abadin! Amin. Wahayin Yesu Kiristi, wanda Allah ya ba shi yă nuna wa bayinsa abin da lalle zai faru nan ba da daɗewa ba. Ya bayyana shi ta wurin aiko da mala’ikansa zuwa ga bawansa Yohanna, wanda ya shaida dukan abin da ya gani, wato, maganar Allah da kuma shaidar Yesu Kiristi. Mai albarka ne wanda yake karanta waɗannan kalmomin annabci, masu albarka ne kuma waɗanda suke jinsu, suke kuma sa abin da aka rubuta a ciki a zuciya, domin lokaci ya yi kusa. Daga Yohanna, Zuwa ga ikkilisiyoyi bakwai da suke a lardin Asiya. Alheri da salama gare ku daga shi wanda yake a yanzu, wanda yake a dā, da kuma wanda zai zo, da kuma daga ruhohi bakwai da suke a gaban kursiyinsa, da kuma daga Yesu Kiristi, wanda yake amintaccen shaida, ɗan farin daga tashin matattu, da kuma mai mulkin sarakunan duniya. Gare shi wanda yake ƙaunarmu wanda kuma ya ’yantar da mu daga zunubanmu ta wurin jininsa, ya kuma mai da mu masarauta da firistoci don mu yi wa Allahnsa da Ubansa hidima, a gare shi ɗaukaka da iko sun tabbata har abada abadin! Amin. “Duba, yana zuwa cikin gizagizai, kowane ido kuwa zai gan shi, har da waɗanda suka soke shi”; dukan mutanen duniya kuwa “za su yi makoki dominsa.” Bari yă zama haka nan! Amin. “Ni ne Alfa da kuma Omega,” in ji Ubangiji Allah, “wanda yake a yanzu, wanda yake a dā, da kuma wanda zai zo, Maɗaukaki.” Ni, Yohanna, ɗan’uwanku da kuma abokin tarayyarku cikin wahala da mulki, da kuma haƙurin jimrewa da suke namu cikin Yesu, ina can tsibirin Fatmos saboda maganar Allah da kuma saboda shaidar Yesu. A Ranar Ubangiji ina cikin Ruhu, sai na ji a bayana wata babbar murya kamar ƙaho, wadda ta ce, “Rubuta a cikin naɗaɗɗen littafi abin da ka gani ka kuma aika ta zuwa ga ikkilisiyoyi bakwai, zuwa Afisa, Simirna, Fergamum, Tiyatira, Sardis, Filadelfiya, da kuma Lawodiseya.” Sai na juya don in ga muryar da take magana da ni. Da na juya kuwa sai na ga alkukan fitilu bakwai na zinariya. A tsakiyar alkukan kuwa akwai wani “kama da ɗan mutum,” saye da rigar da ya kai har ƙafafunsa da kuma ɗamarar zinariya daure a ƙirjinsa. Kansa da kuma gashin fari ne fat kamar ulu, fari kamar dusar ƙanƙara, idanunsa kuwa kamar harshen wuta. Sawunsa sun yi kamar tagullar da take haske cikin matoya, muryarsa kuma ta yi kamar muryar ruwaye masu gudu. A hannunsa na dama ya riƙe taurari bakwai, daga bakinsa kuwa takobi mai kaifi biyu ya fito. Fuskarsa ta yi kamar rana mai haskakawa da dukan haskenta. Sa’ad da na gan shi, sai na fāɗi a gabansa sai ka ce matacce. Sai ya ɗibiya hannunsa na dama a kaina ya ce, “Kada ka ji tsoro. Ni ne Farko da kuma Ƙarshe. Ni ne Rayayye, dā na mutu, ga shi kuwa ina a raye har abada abadin! Ina kuma riƙe da mabuɗan mutuwa da na Hades. “Saboda haka, ka rubuta abin da ka gani, abin da yake yanzu, da abin da zai faru nan gaba. Asirin taurari bakwai da ka gani a hannuna na dama da kuma na alkukan fitilu bakwai na zinariya shi ne, Taurarin bakwai ɗin nan, mala’ikun ikkilisiyoyi bakwai ne; alkukan fitilu bakwai ɗin nan kuma ikkilisiyoyi bakwai ne. “Zuwa ga mala’ikan ikkilisiya a Afisa, ka rubuta, Waɗannan su ne kalmomi na wannan wanda yake riƙe da taurari bakwai a hannunsa na dama yana kuma tafiya a tsakanin alkukan fitilu bakwai na zinariya. Na san ayyukanka, faman aikinka da daurewarka. Na san cewa ba ka iya haƙuri da mugayen mutane, ka gwada waɗanda suke cewa su manzanni ne, alhali kuwa ba haka ba ne, ka kuwa tarar cewa su na ƙarya ne. Kai kam ka daure ka kuma jimre da wahala saboda sunana, ba ka kuwa gaji ba. Duk da haka ina riƙe da wannan game da kai. Ka watsar da ƙaunarka ta farko. Ka tuna da matsayinka a dā kafin ka fāɗi! Ka tuba ka kuma yi ayyukan da ka yi da fari. In ba ka tuba ba, zan zo wajenka in ɗauke wurin ajiye fitilanka daga inda yake. Sai dai kana da wannan abu mai kyau. Ka ƙi ayyukan Nikolaitawa da ni ma nake ƙi. Duk mai kunnen ji, yă ji abin da Ruhu yake faɗa wa ikkilisiyoyi. Duk wanda ya ci nasara, zan ba shi ikon ci daga itacen rai, da yake cikin aljannar Allah. “Zuwa ga mala’ikan ikkilisiya a Simirna, ka rubuta, Waɗannan su ne kalmomin wannan da yake na Farko da na Ƙarshe, wanda ya mutu ya kuma sāke tashi da rai. Na san wahalarka da kuma talaucinka, duk da haka kai mai arziki ne! Na san ɓata suna da waɗannan suke yi maka waɗannan da suke cewa su Yahudawa ne alhali kuwa ba haka ba ne, su dai majami’ar Shaiɗan ne. Kada ka ji tsoron wahalar da kake gab da sha. Ina gaya maka, Iblis zai sa waɗansunku a kurkuku don yă gwada ku. Za ku sha tsanani na kwana goma. Ka yi aminci ko da za a kashe ka, ni kuwa zan ba ka rawanin rai. Duk mai kunnen ji, yă ji abin da Ruhu yake faɗa wa ikkilisiyoyi. Duk wanda ya ci nasara mutuwa ta biyu ba za tă cuce shi ba ko kaɗan. “Zuwa ga mala’ikan ikkilisiya a Fergamum, ka rubuta, Waɗannan su ne kalmomin wannan wanda yake da takobi mai kaifi biyu. Na san inda kake da zama, inda Shaiɗan yana da gadon sarautarsa. Duk da haka ka riƙe sunana da gaske. Ba ka yi mūsun bangaskiyarka gare ni ba, har ma a kwanakin Antifas, amintaccen mashaidina, wanda aka kashe a birninku, inda Shaiɗan yake zama. Duk da haka, ina da abubuwa kima game da kai. Kana da mutane a can waɗanda suke riƙe da koyarwar Bala’am, wanda ya koya wa Balak yă ja hankalin Isra’ilawa su yi zunubi ta wurin cin abincin da aka miƙa wa gumaka hadaya, su kuma yi fasikanci. Haka ma kana da waɗanda suke riƙe da koyarwar Nikolaitawa. Saboda haka ka tuba! In ba haka ba, zan zo wajenka ba da daɗewa ba in yaƙe su da takobin bakina. Duk mai kunnen ji, yă ji abin da Ruhu yake faɗa wa ikkilisiyoyi. Duk wanda ya ci nasara zan ba shi kaɗan daga cikin ɓoyayyiyar Manna. Zan kuma ba shi farin dutse tare da sabon suna a rubuce a bisansa, sananne kawai ga mai karɓan dutsen. “Zuwa ga mala’ikan ikkilisiya a Tiyatira, ka rubuta, Waɗannan su ne kalmomin Ɗan Allah, wanda idanunsa suna kama da harshen wuta wanda kuma ƙafafunsa suna kama da tagullar da aka goge. Na san ayyukanka, ƙaunarka da bangaskiyarka, hidimarka da daurewarka, kuma cewa kana yin abubuwa a yanzu fiye da abin da ka yi da farko. Duk da haka, ina da wannan game da kai. Kana haƙuri da matan nan Yezebel, wadda take kira kanta annabiya. Ta wurin koyarwarta tana ɓad da bayina ga yin fasikanci suka kuma ci abincin da aka miƙa wa gumaka. Na ba ta lokaci tă tuba daga fasikancinta, amma ba ta da niyya. Don haka zan jefa ta a kan gadon wahala, zan kuma sa waɗanda suke zina da ita, su sha azaba ƙwarai, sai dai in sun tuba daga hanyoyinta. Zan kashe ’ya’yanta. Sa’an nan dukan ikkilisiyoyi za su san cewa ni ne mai bincika zukata da tunani, zan kuwa sāka wa kowannenku gwargwadon ayyukansa. Yanzu, ina ce wa sauranku da kuke a Tiyatira, ku da ba ku riƙe da koyarwarta ba kuma ba ku koyi abin da suke kira zurfafan asiran Shaiɗan, ‘Ba zan ƙara muku wani nauyi ba. Sai dai ku riƙe abin da kuke da shi har sai na zo.’ Gare shi wanda ya ci nasara ya kuma aikata nufina har ƙarshe, zan ba shi iko a kan al’ummai. ‘Zai yi mulki a kansu da sandar sarauta ta ƙarfe, zai farfashe su, kamar tukwanen yumɓu’ kamar yadda na karɓi iko daga Ubana. Zan kuma ba shi tauraron asubahi. Duk mai kunnen ji, yă ji abin da Ruhu yake faɗa wa ikkilisiyoyi. “Zuwa ga mala’ikan ikkilisiya a Sardis, ka rubuta, Waɗannan su ne kalmomi, na wanda yake riƙe da ruhohi bakwai na Allah da kuma taurari bakwai. Na san ayyukanka; ana ganinka kamar rayayye, amma kai matacce ne. Ka farka! Ka ƙarfafa abin da ya rage wanda kuma yake bakin mutuwa, don ban ga ayyukanka cikakke ne ba a gaban Allahna. Saboda haka, ka tuna fa, abin da ka karɓa ka kuma ji; ka yi biyayya da shi, ka kuma tuba. Amma in ba ka farka ba, zan zo kamar ɓarawo, ba kuwa za ka san lokacin da zan zo maka ba. Duk da haka kana da mutane kima cikin Sardis waɗanda ba su ɓata tufafinsu ba. Za su yi tafiya tare da ni, saye da fararen tufafi, don sun cancanta. Wanda ya ci nasara, kamar su, za a sanya masa fararen tufafi. Ba zan taɓa share sunansa daga cikin littafin rai ba, sai dai zan shaida sunansa a gaban Ubana da mala’ikunsa. Duk mai kunnen ji, yă ji abin da Ruhu yake faɗa wa ikkilisiyoyi. “Zuwa ga mala’ikan ikkilisiya a Filadelfiya, ka rubuta, Waɗannan su ne kalmomi, na wanda yake mai tsarki da kuma gaskiya, wanda yake riƙe da mabuɗin Dawuda. Abin da ya buɗe ba mai rufewa, abin da kuma ya rufe ba mai buɗewa. Na san ayyukanka. Duba, na sa a gabanka buɗaɗɗen ƙofa wadda ba mai iya rufewa. Na san cewa kana da ɗan ƙarfi, duk da haka ka kiyaye maganata ba ka kuwa yi mūsun sunana ba. Zan sa waɗanda suke na majami’ar Shaiɗan, waɗanda suke cewa su Yahudawa ne alhali kuwa ba haka ba ne, sai dai maƙaryata, zan sa su zo su fāɗi a ƙasa a gabanka su kuma shaida cewa na ƙaunace ka. Da yake ka kiyaye umarnina ta wurin jimrewa, ni ma zan tsare ka daga lokacin nan na gwaji wanda zai zo bisan dukan duniya don a gwada waɗanda suke zama a duniya. Ina zuwa ba da daɗewa ba. Ka riƙe abin da kake da shi, don kada wani ya karɓe rawaninka. Duk wanda ya ci nasara zan mai da shi ginshiƙi a haikalin Allahna. Ba kuwa zai sāke barin wurin ba. Zan rubuta a kansa sunan Allahna da kuma sunan birnin Allahna, sabuwar Urushalima, wadda take saukowa daga sama daga Allahna; ni kuma zan rubuta a kansa sabon sunana. Duk mai kunnen ji, yă ji abin da Ruhu yake faɗa wa ikkilisiyoyi. “Zuwa ga mala’ikan ikkilisiya a Lawodiseya, ka rubuta, Waɗannan su ne kalmomina Amin, amintaccen mashaidi mai gaskiya, da kuma mai mulkin halittar Allah. Na san ayyukanka, ba ka da sanyi ba ka kuma da zafi. Na so da kai ɗaya ne daga ciki, ko sanyi, ko zafi! Amma domin kana tsaka-tsaka ba zafi ba, ba kuma sanyi ba, ina dab da tofar da kai daga bakina. Ka ce, ‘Ina da arziki; na sami dukiya ba na kuma bukatar kome.’ Amma ba ka gane ba cewa kai matsiyaci ne, abin tausayi, matalauci, makaho kana kuma tsirara. Na shawarce ka ka sayi zinariyar da aka tace cikin wuta daga gare ni, don ka yi arziki; da fararen tufafi ka sa, don ka rufe kunyar tsirancinka; da kuma maganin ido ka sa a idanunka, don ka gani. Waɗanda nake ƙauna su nake tsawata wa, nake kuma horo. Saboda haka ka yi himma ka tuba. Ga ni! Ina tsaye a bakin ƙofa, ina ƙwanƙwasawa. Duk wanda ya ji muryata ya kuma buɗe ƙofar, zan shiga in kuma ci tare da shi, shi kuma tare da ni. Duk wanda ya ci nasara, zan ba shi ikon zama tare da ni a kursiyina, kamar yadda na ci nasara, kuma ina zaune tare da Ubana a kursiyinsa. Duk mai kunnen ji, yă ji abin da Ruhu yake faɗa wa ikkilisiyoyi.” Bayan wannan sai na duba, a can kuma a gabana ga ƙofa a buɗe a sama. Sai muryar da na ji da fari da take magana da ni mai kama da busar ƙaho ta ce, “Hauro nan, zan kuma nuna maka abin da lalle zai faru bayan wannan.” Nan da nan sai ga ni cikin Ruhu, a can a gabana kuwa ga kursiyi a cikin sama da wani zaune a kansa. Wannan mai zama a can kuwa yana da kamannin dutsen yasfa da karneliya. Bakan gizo, mai kama da zumurrudu, ya kewaye kursiyin. Kewaye da kursiyin kuwa akwai waɗansu kursiyoyi ashirin da huɗu, zaune a kansu kuwa dattawa ashirin da huɗu ne. Suna saye da fararen tufafi suna kuma da rawanin zinariya a kawunansu. Daga kursiyin hasken walƙiya yana ta fitowa, da ƙararraki da kuma tsawa. A gaban kursiyin, fitilu bakwai suna ci. Waɗannan ne ruhohi bakwai na Allah. Haka kuma a gaban kursiyin akwai wani abu mai kama da tekun gilashi, yana ƙyalli kamar madubi. A tsakiya kuwa, kewaye da kursiyin, akwai halittu huɗu masu rai, cike kuma suna da idanu gaba da baya. Halitta ta fari tana kama da zaki, ta biyun kuwa tana kama da bijimi, ta ukun kuma tana da fuska kamar ta mutum, ta huɗun kuma tana kama da gaggafa mai tashi sama. Kowace a cikin halittu huɗu masu rai ɗin nan tana da fikafikai guda shida, tana kuma cike da idanu a ko’ina, har ma ƙarƙashin fikafikanta. Dare da rana ba sa fasa cewa, “ ‘Mai Tsarki, Mai Tsarki, Mai Tsarki shi ne Ubangiji Allah Maɗaukaki,’ wanda yake a dā, wanda yake a yanzu, wanda kuma yake nan gaba.” Duk lokacin da halittu masu ran nan suka rera ɗaukaka, girma da kuma godiya ga wannan wanda yake zaune a kan kursiyin da kuma wanda yake mai rai har abada abadin, sai dattawa ashirin da huɗun nan su fāɗi a ƙasa a gaban wannan wanda yake zaune a kursiyin, su yi sujada wa wannan wanda yake da rai har abada abadin. Sukan ajiye rawaninsu a gaban kursiyin suna cewa, “Ya Ubangijinmu da Allahnmu, ka cancanci ɗaukaka da girma da iko, domin ka halicci dukan abubuwa, kuma ta wurin nufinka aka halicce su suka kuma kasance.” Sa’an nan na ga a hannun damar wannan wanda yake zaune a kursiyin naɗaɗɗen littafi da rubutu a ciki da wajensa an kuma hatimce shi da hatimai bakwai. Na kuma ga wani babban mala’ika yana shela da babbar murya cewa, “Wa ya cancanta yă ɓalle hatiman nan yă kuma buɗe naɗaɗɗen littafin?” Amma ba wani a sama ko a ƙasa ko a ƙarƙashin ƙasan da ya iya buɗe naɗaɗɗen littafin ko ma yă duba cikinsa. Na yi ta kuka domin ba a iya samun wanda ya cancanta yă buɗe naɗaɗɗen littafin ko yă duba cikinsa ba. Sai ɗaya daga cikin dattawan ya ce mini, “Kada ka yi kuka! Duba, Zakin kabilar Yahuda, da kuma Tushen Dawuda ya ci nasara. Ya iya buɗe naɗaɗɗen littafin da hatimansa bakwai.” Sa’an nan na ga Ɗan Rago, yana kamar an yanka, tsaye a tsakiyar kursiyin, halittu huɗun nan masu rai da kuma dattawan an sun kewaye shi. Yana da ƙahoni bakwai da idanu bakwai, waɗanda suke ruhohi bakwai na Allah da aka aika cikin dukan duniya. Ya zo ya karɓi naɗaɗɗen littafin daga hannun dama na wannan wanda yake zaune a kursiyin. Bayan ya karɓa, sai halittu huɗun nan masu rai da kuma dattawan nan ashirin da huɗu suka fāɗi ƙasa a gaban Ɗan Ragon. Kowannensu yana da garaya kuma suna riƙe da kaskon zinariya cike da turare, waɗanda suke addu’o’in tsarkaka. Suka rera sabuwar waƙa, “Ka cancanci ka karɓi naɗaɗɗen littafin ka kuma buɗe hatimansa, domin an kashe ka, da jininka kuma ka sayi mutane wa Allah, daga kowace kabila da harshe da mutane da kuma al’umma. Ka mai da su masarauta da kuma firistoci, don su yi wa Allahnmu hidima, kuma za su yi mulki a duniya.” Sai na duba na kuma ji muryar mala’iku masu yawa, yawansu kuwa ya kai dubu dubbai, da kuma dubu goma sau dubu goma. Suka kewaye kursiyin da halittu huɗun nan masu rai da kuma dattawan nan. Da babbar murya suka rera, “Macancanci ne Ɗan Ragon nan da aka kashe, don yă sami iko da wadata da hikima da ƙarfi da girma da ɗaukaka da kuma yabo!” Sa’an nan na ji kowace halitta a sama da ƙasa da ƙarƙashin ƙasa da kuma bisan teku, da kome da yake cikinsu yana rerawa, “Gare shi mai zama a kan kursiyin da kuma ga Ɗan Ragon yabo da girma da ɗaukaka da iko, sun tabbata har abada abadin!” Sai halittu huɗun nan masu rai suka ce, “Amin”, dattawan kuma suka fāɗi suka yi sujada. Na kalli yayinda Ɗan Ragon ya buɗe hatimin farko na hatimai bakwai ɗin nan. Sai na ji ɗaya daga cikin halittu huɗun nan masu rai ya yi magana da murya mai kama da tsawa ya ce, “Zo!” Na duba, can kuwa a gabana ga wani farin doki! Mai hawansa yana riƙe da baka, aka kuma ba shi rawani, ya yi sukuwa ya fito kamar mai nasara da ya kutsa don nasara. Sa’ad da Ɗan Ragon ya buɗe hatimi na biyun, sai na ji halitta mai rai na biyu ya ce, “Zo!” Sai wani doki ya fito, ja wur. Aka ba wa mai hawansa iko yă ɗauke salama daga duniya yă kuma sa mutane su kashe juna. Aka ba shi babban takobi. Sa’ad da Ɗan Ragon ya buɗe hatimi na uku, sai na ji halitta mai rai na uku ya ce, “Zo!” Na duba, can a gabana kuwa ga wani baƙin doki! Mai hawansa yana riƙe da abubuwan awo guda biyu a hannunsa. Sai na ji wani abu mai ƙara kamar wata murya a tsakiyar halittu huɗun nan masu rai tana cewa, “Kwatan alkama don albashin aikin yini, da kuma kwata uku na sha’ir don albashin yini guda, kada kuwa ka ɓata man da ruwan inabi!” Sa’ad da Ɗan Ragon ya buɗe hatimi na huɗu, sai na ji muryar halitta mai rai na huɗu ya ce, “Zo!” Na duba, can a gabana kuwa ga ƙodaɗɗen doki! An ba wa mai hawansa suna Mutuwa, Hades kuwa yana biye da shi. Aka ba su iko a kan kashi ɗaya bisa huɗu na duniya don su yi kisa da takobi, yunwa da annoba, har ma da namomin jeji na duniya. Sa’ad da ya buɗe hatimi na biyar, sai na ga a ƙarƙashin bagaden rayukan waɗanda aka kashe saboda maganar Allah da kuma shaidar da suka yi. Suka yi kira da babbar murya suka ce, “Ya Ubangiji Mai Iko Duka, Mai Tsarki da kuma Mai Gaskiya, sai yaushe za ka shari’anta mazaunan duniya ka kuma ɗauki mana fansar jininmu?” Sai aka ba wa kowannensu farin riga, aka kuma faɗa musu su ɗan jira kaɗan sai an cika adadin abokansu masu hidima da kuma ’yan’uwansu waɗanda za a kashe kamar yadda su ma aka kashe su. Ina kallo yayinda ya buɗe hatimi na shida. Sai aka yi babban girgizar ƙasa. Rana ta zama baƙa kamar gwado na gashin akuya, wata kuma gaba ɗaya ya zama ja wur kamar jini, taurarin sararin sama suka fāffāɗi a ƙasa, kamar yadda ɗanyun ’ya’yan ɓaure suke fāɗuwa daga itacen ɓaure sa’ad da iska mai ƙarfi ta jijjiga shi. Sararin sama kuwa ya janye kamar naɗaɗɗen littafi, ya yi ta naɗewa, aka kuma kawar da kowane dutse da kowane tsibiri daga wurinsa. Sa’an nan sarakunan duniya, hakimai, jarumawa, masu arziki, masu ƙarfi, da kowane bawa da kuma kowane ’yantacce ya ɓoye a cikin koguna da kuma cikin duwatsun tsaunuka. Suka kira duwatsu da tsaunuka suna cewa, “Ku fāɗi a kanmu ku kuma ɓoye mu daga fuskar wannan mai zama a kan kursiyi da kuma daga fushin Ɗan Ragon nan! Gama babbar ranar fushinsu ta zo, wa kuwa zai iya tsayawa?” Bayan wannan, na ga mala’iku huɗu, a tsaye a kusurwoyi huɗu na duniya, suna tsare iskoki huɗu na duniya, domin su hana wani iska hurawa a bisan ƙasa ko a bisan teku ko a bisa wani itace. Sai na ga wani mala’ika yana zuwa daga gabas, yana da hatimin Allah mai rai. Ya yi kira da babbar murya wa mala’ikun nan huɗu da aka ba su iko su cuci ƙasa da teku ya ce, “Kada ku cuci ƙasa ko teku ko kuma itatuwa sai bayan mun sa hatimi a goshin dukan bayin Allahnmu.” Sai na ji yawan waɗanda aka sa musu hatimi. Su 144,000 daga dukan kabilan Isra’ila. Daga kabilar Yahuda mutum 12,000 ne aka sa musu hatimin, daga kabilar Ruben mutum 12,000, daga kabilar Gad mutum 12,000, daga kabilar Asher mutum 12,000, daga kabilar Naftali mutum 12,000, daga kabilar Manasse mutum 12,000, daga kabilar Simeyon mutum 12,000, daga kabilar Lawi mutum 12,000, daga kabilar Issakar mutum 12,000, daga kabilar Zebulun mutum 12,000, daga kabilar Yusuf mutum 12,000, daga kabilar Benyamin mutum 12,000. Bayan wannan sai na duba, can a gabana kuwa ga wani taro mai girma, wanda ba mai iya ƙirgawa, daga kowace al’umma, kabila, mutane da kuma harshe, suna tsaye a gaban kursiyin da kuma gaban Ɗan Ragon nan. Suna saye da fararen tufafi suna kuma riƙe da rassan dabino a hannuwansu. Suka tā da murya da ƙarfi suna cewa, “Ceto na Allahnmu ne, wanda yake zaune a bisan kursiyi, da kuma na Ɗan Ragon.” Dukan mala’iku suna tsaye kewaye da kursiyin da kuma kewaye da dattawan tare da halittu huɗun nan masu rai. Suka fāɗi da fuskokinsu ƙasa a gaban kursiyin suka kuma yi wa Allah sujada, suna cewa, “Amin! Yabo da ɗaukaka, da hikima da godiya da girma da iko da ƙarfi sun tabbata ga Allahnmu har abada abadin. Amin!” Sai ɗaya daga cikin dattawan ya tambaye ni ya ce, “Waɗannan da suke saye da fararen tufafi su wane ne, daga ina kuma suka fito?” Na amsa na ce, “Ranka yă daɗe, kai ka sani.” Sai ya ce, “Waɗannan su ne waɗanda suka fito daga matsananciyar wahala; sun wanke tufafinsu suka kuma mai da su farare da jinin Ɗan Ragon nan. Saboda haka, “suna a gaban kursiyin Allah suna masa hidima dare da rana a cikin haikalinsa; kuma wannan mai zaune a kursiyin zai shimfiɗa tentinsa a bisansu. ‘Ba za su sāke jin yunwa ba; ba za su kuma sāke jin ƙishirwa ba. Rana ba za tă buga su ba,’ ko kuma kowane irin zafin ƙuna. Gama Ɗan Ragon da yake a tsakiyar kursiyin zai zama makiyayinsu; ‘zai bi da su zuwa ga maɓulɓular ruwan rai.’ ‘Allah kuwa zai share dukan hawaye daga idanunsu.’ ” Sa’ad da ya buɗe hatimi na bakwai, sai aka yi shiru a sama na kusan rabin sa’a. Sai na ga mala’iku bakwai da suke tsayawa a gaban Allah, a gare su kuwa aka ba da ƙahoni bakwai. Wani mala’ika, da yake da kaskon zinariyar da ake zuba turare, ya zo ya tsaya kusa da bagaden. Aka ba shi turare da yawa don yă miƙa tare da addu’o’in dukan tsarkaka a bisa bagaden zinariya a gaban kursiyin. Hayaƙin turaren tare da addu’o’in tsarkaka, suka hau zuwa gaban Allah daga hannun mala’ikan. Sai mala’ikan ya ɗauki kaskon, ya cika shi da wuta daga bagaden, ya kuma wurga shi bisan duniya; sai aka yi ta yin tsawa, ƙararraki, walƙiya, da kuma girgizar ƙasa. Sai mala’iku bakwai ɗin nan da suke da ƙahoni bakwai suka shirya don su busa su. Mala’ika na fari ya busa ƙahonsa, sai ga ƙanƙara da wuta haɗe da jini, aka kuma wurga su bisan duniya. Kashi ɗaya bisa uku na duniya ya ƙone, kashi ɗaya bisa uku na itatuwa suka ƙone, dukan ɗanyar ciyawa kuma ta ƙone. Mala’ika na biyu ya busa ƙahonsa, sai ga wani abu kamar babban dutse mai cin wuta, aka jefa cikin teku. Kashi ɗaya bisa uku na teku ya zama jini, kashi ɗaya bisa uku na halittu masu rai da suke cikin tekun suka mutu, kashi ɗaya bisa uku kuma na jiragen ruwa kuma suka hallaka. Mala’ika na uku ya busa ƙahonsa, sai wani babban tauraro mai cin wuta kamar toci, ya fāɗi daga sararin sama, a kan kashi ɗaya bisa uku na koguna da kuma a bisa maɓulɓulan ruwa sunan tauraron kuwa Maɗaci. Kashi ɗaya bisa uku na ruwaye ya zama mai ɗaci, mutane da yawa kuma suka mutu saboda shan ruwan, don ɗacinsa. Mala’ika na huɗu ya busa ƙahonsa, sai aka bugi kashi ɗaya bisa uku na rana, kashi ɗaya bisa uku na wata, da kashi ɗaya bisa uku na taurari, har kashi ɗaya bisa uku nasu ya duhunta. Kashi ɗaya bisa uku na yini ya kasance babu haske, haka ma kashi ɗaya bisan uku na dare. Yayinda nake kallo, sai na ji gaggafar da take tashi sama a tsakiyar sararin sama ta yi kira da babbar murya ta ce, “Kaito! Kaito! Kaiton mazaunan duniya, in an yi busan sauran ƙahonin da mala’ikun nan uku suke shirin busawa!” Mala’ika na biyar ya busa ƙahonsa, sai na ga tauraron da ya fāɗo duniya daga sararin sama. Aka ba wa tauraron mabuɗin ramin Abis. Da ya buɗe Abis ɗin, sai hayaƙi ya taso daga cikin kamar hayaƙin matoya mai girma. Hayaƙin nan daga Abis ya duhunta rana da sararin sama. Daga cikin hayaƙin kuwa fāri suka fito zuwa cikin duniya aka kuma ba su iko irin na kunaman duniya. Aka faɗa musu kada su yi wa ciyawa na duniya lahani ko wani tsiro ko itace, sai dai su yi wa mutanen da ba su da hatimin Allah a goshinsu kaɗai lahani. Ba a ba su iko su kashe su ba, sai dai su ba su azaba na watanni biyar. Azabar da suka sha kuwa ya yi kamar ta harbin kunama sa’ad da ta harbi mutum. Cikin waɗannan kwanakin mutane za su nemi mutuwa, amma ba za su samu ba; za su yi marmarin mutuwa, amma mutuwa za tă ɓace musu. Kamannin fārin nan kuwa yana kama da dawakan da aka shirya don yaƙi. A kawunansu kuwa da wani abu da ya yi kamar rawanin zinariya, fuskokinsu kuma sun yi kamar fuskokin mutane. Gashin kansu ya yi kamar gashin kan mata, haƙoransu kuma sun yi kamar haƙoran zakoki. Suna da sulkuna kamar sulkunan ƙarfe, ƙarar fikafikansu kuma ta yi kamar motsin dawakai da kekunan yaƙi masu yawa da suke rugawa zuwa yaƙi. Suna da wutsiyoyi da ƙari kamar kunamai, kuma a wutsiyoyinsu suna da iko su ba wa mutane azaba na wata biyar. Suna da sarkin da yake mulki a bisansu wanda yake mala’ikan Abis, wanda sunansa a harshen Yahudawa shi ne Abaddon, da harshen Hellenawa kuwa shi ne, Afolliyon. Bala’i na fari ya wuce, sauran bala’i biyu suna nan zuwa. Mala’ika na shida ya busa ƙahonsa, sai na ji murya tana fitowa daga ƙahonin bagaden zinariya da suke a gaban Allah. Ta ce wa mala’ika na shida da yake da ƙahon, “Ka saki mala’iku huɗun nan da suke a daure a babban kogin Yuferites.” Mala’iku huɗun nan kuwa da aka shirya musamman don wannan sa’a da kuma don wannan rana da wata da kuma shekara aka sake su domin su kashe kashi ɗaya bisa uku na ’yan Adam. Yawan rundunan masu hawan dawakan nan mutum miliyon ɗari biyu ne. Na ji adadinsu. Dawakai da masu hawansu da na gani cikin wahayina sun yi kamar. Sulkunansu ja wur ne, baƙin shuɗi, da kuma rawaya kamar farar wuta. Kawunan dawakan sun yi kamar kawunan zakoki, daga bakunansu kuwa wuta, hayaƙi, da farar wuta suna fitowa. Aka kashe kashi ɗaya bisa uku na ’yan Adam da annobai uku na wuta, hayaƙi da farar wuta da suka fito daga bakunansu. Ƙarfin dawakan nan kuwa yana a bakunansu da wutsiyoyinsu; gama wutsiyoyinsu suna kama da macizai masu kawuna, da wutsiyoyin ne kuma suke yi wa mutane rauni. Sauran ’yan Adam da ba a kashe ta wajen waɗannan annobai ba kuwa har wa yau ba su tuba daga aikin hannuwansu ba; ba su daina bauta wa aljanu, da gumakan zinariya, azurfa, tagulla, dutse da na itace, gumakan da ba sa iya gani ko ji ko tafiya ba. Ba su kuma tuba daga kisankansu, sihirinsu, fasikancinsu ko kuma daga sace-sacensu ba. Sai na ga wani babban mala’ika yana saukowa daga sama. An lulluɓe shi da girgije, bakan gizo kuma yana kansa; fuskarsa tana kama da rana, ƙafafunsa kuma suna kama da ginshiƙan wuta. Yana riƙe da ɗan ƙaramin naɗaɗɗen littafi, wanda yake a buɗe a hannunsa. Ya kafa ƙafarsa ta dama a kan teku ƙafarsa ta hagu kuma a kan ƙasa, ya kuma yi ihu da ƙarfi kamar rurin zaki. Da ya yi ihun, sai muryoyin tsawan nan bakwai suka yi magana. Sa’ad da tsawan nan bakwai kuwa suka yi magana, ina dab da rubutawa; amma na ji wata murya daga sama ta ce, “Rufe abin da tsawan nan bakwai suka faɗa kada ka rubuta.” Sai mala’ikan da na gani na tsaye a teku da ƙasa ya ɗaga hannunsa na dama sama. Ya kuma yi rantsuwa da wannan wanda yake raye har abada abadin, wanda ya halicci sammai da dukan abin da yake cikinsu, duniya da dukan abin da yake cikinta, da kuma teku da dukan abin da yake cikinsa, ya kuma ce, “Babu sauran jinkiri! Amma a ranakun da mala’ika na bakwai na dab da busa ƙahonsa, za a cika asirin Allah, kamar yadda ya sanar wa bayinsa annabawa.” Sai muryar da na ji daga sama ta sāke magana da ni ta ce, “Tafi, ka karɓi naɗaɗɗen littafin da yake a buɗe a hannun mala’ikan da yake tsaye bisa teku da ƙasa.” Sai na je wajen mala’ikan na ce masa yă ba ni ƙaramin naɗaɗɗen littafin. Ya ce mini, “Karɓa ka ci. Zai sa cikinka yă yi tsami, amma ‘a bakinka zai zama da zaƙi kamar zuma.’ ” Na karɓi ƙaramin naɗaɗɗen littafin daga hannun mala’ikan na kuma ci. Ya yi zaƙi kamar zuma a bakina, amma sa’ad da na cinye, cikina ya yi tsami. Sa’an nan aka ce mini, “Dole ne ka sāke yin annabci game da mutane masu yawa, al’ummai, harsuna da kuma sarakuna.” Aka ba ni ƙara kamar sandan awo aka kuma ce mini, “Tafi ka auna haikalin Allah da bagaden, ka kuma ƙirga waɗanda suke sujada a can. Sai dai kada ka haɗa da harabar waje; kada ka auna ta, domin an ba da ita ga Al’ummai. Za su tattaka birni mai tsarki har watanni 42. Zan kuma ba wa shaiduna nan biyu iko, za su kuwa yi annabci na kwanaki 1,260, saye da gwadon makoki.” Waɗannan su ne itatuwan zaitun biyu da kuma alkukai biyu da suke tsaye a gaban Ubangijin duniya. Duk wanda ya yi ƙoƙari yin musu lahani, wuta za tă fito daga bakunansu ta cinye abokan gābansu. Haka ne duk mai niyyar yin musu lahani zai mutu. Waɗannan mutane suna da iko su kulle sararin sama don kada a yi ruwan sama a lokacin da suke annabci; suna kuma da iko su juye ruwaye su zama jini su kuma bugi duniya da kowace irin annoba a duk lokacin da suke so. To, da suka gama shaidarsu, dabbar da takan fito daga Abis za tă kai musu hari, tă kuwa sha ƙarfinsu tă kuma kashe su. Gawawwakinsu za su kasance a kwance a titin babban birni, wanda a misalce ake kira Sodom da Masar, inda kuma aka gicciye Ubangijinsu. Kwana uku da rabi mutane daga kowace jama’a, kabila, harshe da kuma al’umma za su yi ta kallon gawawwakinsu su kuma ƙi binne su. Mazaunan duniya za su ƙyaface su kuma yi biki ta wurin aika kyautai wa juna, domin waɗannan annabawan nan biyu ne suka azabtar da mazaunan duniya. Amma bayan kwana uku da rabi ɗin numfashin rai daga Allah ya shige su, suka kuwa tashi tsaye, tsoro kuma ya kama waɗanda suka gan su. Sai suka ji wata babbar murya daga sama tana ce musu, “Ku hauro nan.” Suka kuwa haura zuwa sama cikin girgije, yayinda abokan gābansu suna kallo. A wannan sa’a aka yi wata babbar girgizar ƙasa kashi ɗaya bisa goma kuma na birnin ya rushe. Aka kashe mutane dubu bakwai a girgizar ƙasar, waɗanda suka tsira kuwa suka ji tsoro suka ɗaukaka Allah na sama. Kaito na biyu ya wuce; kaito na uku yana zuwa ba da daɗewa ba. Mala’ika na bakwai ya busa ƙahonsa, sai aka ji muryoyi masu ƙarfi a sama da suka ce, “Mulkin duniya ya zama mulkin Ubangijinmu da na Kiristinsa, zai kuwa yi mulki har abada abadin.” Sai dattawan nan ashirin da huɗu da suke zaune a kursiyoyinsu a gaban Allah, suka fāɗi da fuskokinsu a ƙasa suka kuma yi wa Allah sujada, suna cewa, “Muna maka godiya ya Ubangiji Allah, Maɗaukaki, wanda yake a yanzu, shi ne kuma a dā, domin ka karɓi ikonka mai girma ka kuma fara mulki. Al’ummai suka yi fushi; fushinka kuwa ya zo. Lokaci ya yi don a shari’anta matattu, da kuma don sākawa wa bayinka annabawa da tsarkakanka da kuma su waɗanda suke girmama sunanka, ƙarami da babba, don kuma hallakar da waɗanda suka hallaka duniya.” Sa’an nan aka buɗe haikalin Allah da yake a sama, kuma a cikin haikalinsa aka ga akwatin alkawarinsa. Sai kuwa ga walƙiya, ƙararraki, tsawa, girgizar ƙasa, da kuma ƙanƙara masu girma. Babbar alama mai banmamaki ta bayyana a sama, mace tana lulluɓe da rana, da kuma wata a ƙarƙashin sawunta, akwai kuma rawani mai taurari goma sha biyu a kanta. Tana da ciki ta kuma yi kuka mai zafi yayinda take gab da haihuwa. Sai wata alama ta bayyana a sama, wani babban jan maciji mai kawuna bakwai da ƙahoni goma da rawani bakwai a kan kawunansa. Wutsiyarsa ta share kashi ɗaya bisa uku na taurari daga sararin sama ta kuma zubar da su ƙasa. Ƙaton jan macijin ya tsaya a gaban macen wadda take gab da haihuwa, don yă cinye ɗanta nan take bayan an haife shi. Ta haifi ɗa, namiji, wanda zai yi mulkin dukan al’ummai da sandar ƙarfe. Aka fyauce ɗanta zuwa wurin Allah da kuma kursiyinsa. Sai macen ta gudu zuwa hamada zuwa inda Allah ya shirya dominta, inda za a lura da ita har kwana 1,260. Aka kuwa yi yaƙi a sama. Mika’ilu da mala’ikunsa yaƙi macijin, maciji da mala’ikunsa su ma suka mai da martani. Amma macijin nan ba shi da isashen ƙarfi, har suka rasa matsayinsu a sama. Aka jefar da ƙaton jan macijin ƙasa, tsohon maciji nan da ake kira Iblis, ko Shaiɗan, wanda ya ɓad da dukan duniya. Aka jefar da shi ƙasa, tare da mala’ikunsa a duniya. Sa’an nan na ji babbar murya daga sama tana cewa, “Yanzu ceto da iko da mulkin Allahnmu, da kuma ikon Kiristinsa. Gama mai zargin ’yan’uwanmu, wanda yake zarginsu a gaban Allahnmu dare da rana, an jefar da shi ƙasa. Sun ci nasara a kansa ta wurin jinin Ɗan Ragon da ta wurin kalmar shaidarsu; ba su ƙaunaci rayukansu sosai har da za su ja da baya daga mutuwa. Saboda haka ku yi farin ciki, ku sammai, da ku da kuke zaune a cikinsu! Amma kaiton duniya da kuma teku, gama Iblis ya sauko gare ku! Ya cika da fushi, domin ya san cewa lokacinsa ya rage kaɗan.” Sa’ad da macijin ya ga an jefar da shi a duniya, sai ya fafari macen nan da ta haifi ɗa namiji. Sai aka ba wa macen fikafikai biyu na babban gaggafa, don ta tashi sama zuwa inda aka shirya mata a hamada, inda za a lura da ita na ɗan lokaci, lokuta da rabin lokaci, inda macijin ba zai iya kaiwa ba. Sa’an nan daga bakinsa macijin ya kwarara ruwa kamar kogi, don ruwan ya cimma matan yă kuma kwashe ta tare da ambaliya. Amma ƙasa ta taimaki macen ta wurin buɗe bakinta ta kuma shanye ruwan kogin da macijin ya kwarara daga bakinsa. Sai macijin ya yi fushi da macen ya kuma koma wajen sauran zuriyarta don yă yaƙe su waɗannan waɗanda suke biyayya da umarnan Allah suke kuma riƙe da shaidar Yesu. Macijin kuwa ya tsaya a bakin teku. Sai na ga wata dabba tana fitowa daga teku. Tana da ƙahoni goma da kawuna bakwai, da kuma rawani goma a ƙahoninta, a kowane kai kuwa akwai sunan saɓo. Dabbar da na gani ta yi kamar damisa, amma tana da ƙafafu kamar na beyar, bakinta kuma ya yi kamar na zaki. Macijin nan ya ba wa dabbar ƙarfinsa da gadon sarautarsa da kuma ikonsa mai girma. Ɗaya daga cikin kawunan dabbar ya yi kamar yana da raunin da zai iya kashe shi, amma raunin nan da zai iya kashe shi ya riga ya warke. Dukan duniya ta yi mamaki ta kuma bi dabbar. Mutane suka yi wa macijin sujada domin ya ba wa dabbar ikonsa, suka yi wa dabbar sujada, suka kuma yi tambaya cewa, “Wane ne yake kama da dabban nan? Wa zai iya yaƙe ta?” Aka ba wa dabbar baki don ta faɗi kalmomin girman kai da na saɓo ta kuma yi amfani da ikonta har watanni arba’in da biyu. Ta buɗe bakinta don tă yi wa Allah saɓo, ta kuma ɓata sunansa da kuma mazauninsa da na waɗanda suke zama a sama. Aka ba ta iko tă yaƙi tsarkaka tă kuma ci nasara a kansu. Aka kuma ba ta iko bisa kowace kabila, jama’a, harshe da kuma al’umma. Dukan mazaunan duniya za su yi wa dabbar sujada, dukan waɗanda ba a rubuta sunayensu a cikin littafin ran da yake na Ɗan Ragon da aka yanka tun kafin halittar duniya ba. Duk mai kunne ji, bari yă ji. Duk wanda aka ƙaddara ga bauta, ga bauta zai tafi. Duk wanda aka ƙaddara za a kashe da takobi, da takobin za a kashe shi. Wannan yana bukata haƙuri da aminci a gefen tsarkaka. Sai na ga wata dabba tana fitowa daga ƙasa. Tana da ƙahoni biyu kamar ɗan rago, amma ta yi magana kamar maciji. Ta mori dukan ikon dabban nan ta fari a madadinta, ta sa duniya da mazaunanta su yi wa dabba ta farin nan sujada, wadda aka warkar mata da raunin nan da zai iya kashe ta. Ta kuma yi manyan ayyuka da kuma alamu masu banmamaki, har ta sa wuta ta sauko daga sama zuwa ƙasa a gaban idon mutane. Saboda alamun nan da aka ba ta iko tă yi a madadin dabban nan ta fari, sai ta ruɗi mazaunan duniya. Ta umarce su su kafa siffa don girmama dabbar da aka ji mata rauni da takobi duk da haka ta rayu. Aka ba ta iko tă ba da numfashi ga siffar dabban nan ta fari, don tă yi magana tă kuma sa a kashe duk waɗanda suka ƙi yi wa siffar sujada. Ta kuma tilasta wa kowa, manya da yara, mawadata da matalauta, ’yantattu da bayi, don a yi musu alama a hannun dama ko a goshi, don kada kowa yă saya ko yă sayar, sai dai yana da alamar, wadda take sunan dabbar ko kuma lambar sunanta. Wannan yana bukata hikima. Duk mai hankali, sai yă lissafta lambar dabbar, gama lamban nan ta mutum ne. Lambarta kuwa ita ce 666. Sai na duba, can a gabana kuwa ga Ɗan Rago, tsaye a kan Dutsen Sihiyona, tare da shi akwai kuma mutane 144,000 waɗanda suke da sunansa da sunan Ubansa a rubuce a goshinsu. Sai na ji ƙara daga sama kamar motsin ruwaye masu gudu, kamar kuma tsawa. Ƙarar da na ji ta yi kamar ta masu garaya da suke kiɗin garayarsu. Suka kuwa rera sabuwar waƙa a gaban kursiyin da kuma a gaban halittu huɗun nan masu rai, da kuma a gaban dattawa. Ba wanda ya iya koyon waƙar sai mutanen nan 144,000 da aka fansa daga duniya. Waɗannan su ne waɗanda ba su ƙazantar da kansu da mata ba, gama sun kiyaye kansu da tsarki. Suna bin Ɗan Ragon duk inda ya tafi. Su ne aka saya daga cikin mutane aka kuwa miƙa su kamar ’ya’yan fari ga Allah da kuma Ɗan Ragon. Ba a sami ƙarya a bakunansu ba; su kuma marasa aibi ne. Sai na ga wani mala’ika yana tashi sama a tsakiyar sararin sama, yana kuma da madawwamiyar bishara wadda zai yi shela ga waɗanda suke zama a duniya, ga kowace al’umma, kabila, harshe, da kuma jama’a. Ya ce da babbar murya, “Ku ji tsoron Allah ku kuma ɗaukaka shi, domin sa’ar hukuncinsa ya yi. Ku yi wa wannan da ya halicci sammai, ƙasa, teku, da maɓulɓulan ruwa sujada.” Mala’ika na biyu ya biyo yana cewa, “Ta fāɗi! Babilon Mai Girma ta fāɗi, wadda ta sa dukan al’ummai suka sha ruwan inabin hauka na zinanta.” Mala’ika na uku ya biyo su ya ce da babbar murya, “Duk wanda ya yi wa dabban nan da siffarta sujada ya kuma sami alamarta a goshi ko a hannu, shi ma zai sha ruwan inabin fushin Allah, wanda aka zuba da duk ƙarfinsa a kwaf fushinsa. Za a ba shi azaba da farar wuta mai ci a gaban tsarkakan mala’iku da na Ɗan Ragon. Hayaƙin azabarsu kuwa zai dinga tashi har abada abadin. Kuma babu hutu dare ko rana wa waɗanda suke wa dabbar da siffarta sujada, ko kuwa ga duk wanda ya sami alamar sunanta.” Wannan yana bukata haƙuri, a gefen tsarkakan da suke biyayya da umarnan Allah suka kuma kasance da aminci ga Yesu. Sai na ji murya daga sama ta ce, “Rubuta, Masu albarka ne matattun da suka mutu cikin Ubangiji daga yanzu zuwa gaba.” “I, za su huta daga faman aikinsu, gama ayyukansu za su bi su,” in ji Ruhu. Na duba, can gabana kuwa ga farin girgije, zaune kuma a kan girgijen kuwa ga wani da ya yi kamar “ɗan mutum” tare da rawanin zinariya a kansa da kuma lauje mai kaifi a hannunsa. Sai wani mala’ika ya fito daga haikali ya kuma yi kira da babbar murya ga wannan mai zaune a kan girgijen ya ce, “Ɗauki laujenka ka yi girbi, domin lokacin girbi ya yi, gama amfanin da yake duniya ya nuna.” Sai wannan mai zaune a girgijen ya wurga laujensa a duniya, sai aka kuwa girbe duniya. Wani mala’ika kuma ya fito daga haikali a sama, shi ma yana da lauje mai kaifi. Har yanzu, wani mala’ika mai lura da wuta, ya fito daga bagaden ya yi kira da babbar murya ga wannan wanda yake da lauje mai kaifi ya ce, “Ɗauki laujenka mai kaifi ka tattara kawunan ’ya’yan inabi daga kuringar inabin duniya, domin ’ya’yan inabin sun nuna.” Mala’ikan ya wurga laujensa a duniya, ya tattara ’ya’yan inabin, ya kuma zuba su cikin babbar wurin matsewar inabin fushin Allah. Aka tattake su a wurin matsin inabi a bayan gari, jini kuwa ya yi ta gudana daga wurin matsin inabi tsayinsa ya kai kamar tsawon linzami a bakin doki, nisansa kuma ya kai wajen kilomita 300. Na ga wata babbar alama mai banmamaki a sama, mala’iku bakwai da annobai bakwai na ƙarshe, na ƙarshe, domin da su ne fushin Allah ya cika. Sai na ga abin da ya yi kamar tekun gilashi gauraye da wuta kuma tsaye kusa da teku, waɗanda suka ci nasara bisan dabbar da siffarta da bisan lambar sunanta. Suna riƙe da garayu waɗanda Allah ya ba su suka rera waƙar Musa bawan Allah da kuma waƙar Ɗan Ragon suna cewa, “Ayyukanka suna da girma da kuma banmamaki, ya Ubangiji Maɗaukaki. Al’amuranka suna da aminci da kuma gaskiya, ya Sarkin zamanai. Wane ne ba zai ji tsoronka, yă kuma kawo ɗaukaka ga sunanka ba, ya Ubangiji? Gama kai kaɗai ne mai tsarki. Dukan al’ummai za su zo su yi sujada a gabanka, gama an bayyana ayyukan adalcinka.” Bayan wannan sai na duba, a cikin sama kuwa sai ga haikali, wato, tabanakul na Shaida, a buɗe. Daga cikin haikalin mala’iku bakwai tare da annobai bakwai suka fito. Suna saye da tufafin lilin masu tsabta masu walƙiya, suna kuma saye da ɗamarar zinariya a ƙirjinsu. Sai ɗaya daga cikin halittu huɗun nan masu rai, ya ba wa mala’iku bakwai nan kwanonin zinariya bakwai cike da fushin Allah, wanda yake raye har abada abadin. Aka kuma cika haikalin da hayaƙi daga ɗaukakar Allah da kuma daga ikonsa, kuma ba wanda ya iya shiga haikalin sai da aka cika annobai bakwai nan na mala’iku bakwai. Sai na ji wata babbar murya daga haikalin tana ce wa mala’iku bakwai nan, “Ku tafi ku zuba kwanoni bakwai nan na fushin Allah a kan duniya.” Mala’ika na fari ya je ya juye kwanonsa a bisan ƙasa, sai munanan gyambuna masu zafi suka fito a jikin mutanen da suke da alamar dabbar suka kuma yi wa siffarta sujada. Mala’ika na biyu ya juye kwanonsa a bisan teku, sai tekun ya zama jini kamar na mataccen mutum, kuma kowane abu mai rai da yake cikin tekun ya mutu. Mala’ika na uku ya juye kwanonsa a bisan koguna da maɓulɓulan ruwa, sai suka zama jini. Sa’an nan na ji mala’ikan da yake lura da ruwaye ya ce, “Kai mai adalci ne cikin waɗannan hukuntai, kai da kake yanzu, kake kuma a dā, Mai Tsarki, saboda yadda ka yi hukuncin nan; gama sun zub da jinin tsarkakanka da kuma annabawanka, ka kuwa ba su jini su sha, yadda ya dace da su.” Na kuma ji bagaden ya amsa, “I, Ubangiji Allah, Maɗaukaki, hukuntanka daidai yake na adalci ne kuma.” Mala’ika na huɗu ya juye kwanonsa a bisan rana, sai aka ba wa rana iko ta ƙona mutane da wuta. Aka ƙone su da zafin wuta mai tsanani suka kuwa la’anci sunan Allah wanda yake da iko a kan waɗannan annoban, amma suka ƙi su tuba su kuma ɗaukaka shi. Mala’ika na biyar ya juye kwanonsa a bisan gadon sarautar dabbar, mulkinta kuwa ya zama duhu. Mutane suka yi ta cizon bakinsu saboda azaba suka kuma la’anci Allah na sama saboda zafinsu, da kuma saboda gyambunansu, amma suka ƙi su tuba daga abin da suka riga suka yi. Mala’ika na shida ya juye kwanonsa a bisan babban kogin Yuferites, sai ruwansa ya shanye don a shirya hanya saboda sarakuna daga Gabas. Sa’an nan na ga mugayen ruhohi guda uku da suka yi kamar kwaɗi; suka fito daga bakin macijin nan, da kuma daga bakin dabbar, da kuma daga bakin annabin ƙaryan nan. Su ruhohin aljanu ne da suke aikata abubuwan banmamaki, sukan je wurin sarakunan dukan duniya, don su tattara su don yaƙi a babbar ranar Allah Maɗaukaki. “Ga shi, ina zuwa kamar ɓarawo! Mai albarka ne wanda yake zama a faɗake yana kuma saye da tufafinsa, don kada yă yi tafiya tsirara a kuma kunyata shi.” Sa’an nan aka tattara sarakuna zuwa wurin da a Ibraniyanci ake kira Armageddon. Mala’ika na bakwai ya juye kwanonsa cikin iska, daga haikalin kuwa sai aka ji wata babbar murya daga kursiyin, tana cewa, “An gama!” Sai ga walƙiya, ƙararraki, tsawa da kuma matsananciyar girgizar ƙasa. Ba a taɓa yin irin wannan girgizar ƙasar ba, tun kasancewar mutum a duniya, girgizar ƙasar kuwa gawurtacciya ce. Babban birnin ya rabu kashi uku, biranen al’ummai kuma suka rurrushe. Allah ya tuna da Babilon Mai Girma ya kuma ba ta kwaf cike da ruwan inabin fushinsa. Kowane tsibiri ya gudu ba a kuwa ƙara ganin duwatsu ba. Daga sararin sama manyan ƙanƙara masu nauyin gaske suka fāɗo a kan mutane. Suka kuma la’anci Allah saboda annobar ƙanƙarar, domin annobar ta yi muni ƙwarai. Ɗaya daga cikin mala’iku bakwai masu ɗauke da kwanoni bakwai nan, ya zo ya ce mini, “Zo, zan nuna maka hukuncin babbar karuwan nan da take zaune a bisan ruwaye masu yawa. Da ita ce sarakunan duniya suka yi zina mazaunan duniya kuma suka bugu da ruwan inabin zinace zinacenta.” Sa’an nan mala’ikan ya ɗauke ni cikin Ruhu zuwa hamada. A can na ga mace zaune a kan wata jan dabbar da aka rufe da sunayen saɓo tana kuma da kawuna bakwai da ƙahoni goma. Macen tana saye da tufafi masu ruwan ja da shunayya, tana ƙyalli da zinariya, duwatsu masu daraja da kuma lu’ulu’ai. Tana riƙe da kwaf na zinariya a hannunta, cike da abubuwa masu banƙyama da kuma ƙazantar zinace zinacenta. Sunan da aka rubuta a goshinta asiri ne, Babilon mai girma mahaifiyar karuwai da kuma na abubuwa masu banƙyama na duniya. Na ga cewa macen ta bugu da jinin tsarkaka, jinin waɗanda suka shaida Yesu. Da na gan ta, sai na yi mamaki ƙwarai. Sa’an nan mala’ikan ya ce mini, “Don me kake mamaki? Zan bayyana maka asirin macen nan da dabbar da take hawa, wadda take da kawuna bakwai da ƙahoni goma. Dabbar da ka gani, a dā ta taɓa kasancewa, a yanzu, ba ta, za tă kuma fito daga Abis zuwa ga hallakarta. Mazaunan duniya waɗanda ba a rubuta sunayensu a littafin rai tun kafin halittar duniya ba za su yi mamaki sa’ad da suka ga dabbar, domin a dā ta taɓa kasancewa, yanzu kuwa ba ta, duk da haka za tă dawo. “Wannan yana bukata hankali da kuma hikima. Kawuna bakwai nan tuddai bakwai ne da macen take zama a kai. Sarakuna bakwai ne kuma. Biyar sun fāɗi, ɗaya yana nan, ɗayan kuma bai zo ba tukuna; amma sa’ad da ya zo, zai kasance na ɗan lokaci. Dabbar da a dā ta taɓa kasancewa, amma yanzu ba ta, ita ce sarki na takwas. Ita ɗaya ce cikin bakwai ɗin, kuma tana tafiya zuwa ga hallakarta. “Ƙahonin nan goma da ka gani sarakuna goma ne da ba su riga sun karɓi mulki ba, amma waɗanda na sa’a guda za su karɓi iko a matsayin sarakuna tare da dabbar. Suna da manufa guda za su kuma ba wa dabbar ikonsu da kuma sarautarsu. Za su yi yaƙi da Ɗan Ragon, sai dai Ɗan Ragon zai ci nasara a bisansu domin shi ne Ubangijin iyayengiji, Sarkin sarakuna, tare da shi kuwa kirayayunsa, zaɓaɓɓunsa da kuma amintattu masu binsa za su kasance.” Sa’an nan mala’ikan ya ce mini, “Ruwayen da ka gani, inda karuwan take zama, jama’a ce, taro masu yawa, al’ummai da kuma harsuna. Dabbar da kuma ƙahoni goma da ka gani za su ƙi jinin karuwar. Za su kai ta ga hallaka su kuma bar ta tsirara; za su ci namanta su kuma ƙone ta da wuta. Gama Allah ya sa a zukatansu su cika nufinsa ta wurin yarda su ba wa dabbar ikonsu tă yi mulki, sai lokacin da kalmomin Allah sun cika. Macen da ka gani ita ce babban birnin da yake mulki a bisan sarakunan duniya.” Bayan wannan sai na ga wani mala’ika yana saukowa daga sama. Yana da iko mai girma, aka haskaka duniya da darajarsa. Ya yi kira da babbar murya ya ce, “Ta fāɗi! Babilon Mai Girma ta fāɗi. Ta zama gidan aljanu da kuma wurin zaman kowace irin mugun ruhu, wurin zaman kowane irin tsuntsu marar tsabta da mai banƙyama. Gama dukan al’ummai sun sha ruwan inabin haukan zinace zinacenta. Sarakunan duniya sun yi zina tare da ita, attajiran duniya kuma sun arzuta da almubazzarancinta.” Sai na ji wata murya daga sama ta ce, “Ku fita daga cikinta, mutanena, don kada zunubanta su shafe ku, don kada wata annobarta ta same ku; gama zunubanta sun yi tsororuwa sun kai sama. Allah kuma ya tuna da laifofinta. Ku sāka mata kamar yadda ta sāka muku; ku sāka mata sau biyu na abin da ta yi. Ku dama mata sau biyu na abin da yake cikin kwaf nata. Ku ba ta isashen azaba da baƙin ciki kamar daraja da kuma jin daɗin da ta ba wa kanta. A zuciyarta takan yi taƙama, ta ce, ‘Ina zama kamar sarauniya; ni ba gwauruwa ba ce, kuma ba zan taɓa yin makoki ba.’ Saboda haka a rana ɗaya annobarta za su cim mata, mutuwa, makoki da kuma yunwa. Wuta zai cinye ta, gama Ubangiji Allah mai girma ne, wanda yake shari’anta ta. “Sa’ad da sarakunan duniya da suka yi zina da ita suka kuma yi tarayya cikin jin daɗinta suka ga hayaƙin ƙunarta, za su yi kuka da makoki saboda ita. Don tsoron ganin azabarta za su tsaya daga nesa, su yi kuka suna cewa, “ ‘Kaito! Kaito, ya birni mai girma. Ya ke Babilon, birni mai iko! Cikin sa’a guda hallakarki ta zo!’ “Attajiran duniya za su yi kuka su kuma yi makoki a kanta, domin ba wanda yake ƙara sayen kayayyakinsu kayayyakin zinariya, azurfa, duwatsu masu daraja da lu’ulu’ai; lallausan lilin, tufa masu ruwan shunayya, siliki da jan tufa; da kowane irin katakai masu ƙanshi da kayayyaki na kowane iri da aka yi da hauren giwa, katakai masu tsada, tagulla, baƙin ƙarfe da dutse mai sheƙi; kayayyakin sinnamon da kayan yaji, na turaren wuta, mur da turare, na ruwan inabi da man zaitun, na gari mai laushi da alkama; shanu da tumaki; dawakai da kekunan doki, da jikuna da kuma rayukan mutane. “Za su ce, ‘Amfanin da kike marmari ya kuɓuce. Dukan arzikinki da darajarki sun ɓace, ba kuwa za a ƙara samunsu ba.’ Attajiran da suka sayar da waɗannan kayayyaki suka kuma sami arzikinsu daga gare ta za su tsaya daga nesa, cike da tsoron ganin azabarta. Za su yi kuka da makoki su ce, “ ‘Kaito! Kaito, ya birni mai girma, saye da lallausan lilin, shunayya da kuma ja, mai walƙiya da zinariya, duwatsu masu daraja da kuma lu’ulu’ai! Cikin sa’a guda irin wannan dukiya mai yawa ta hallaka!’ “Duk matuƙan jirgin ruwa, da dukan waɗanda suke tafiya a jirgin ruwa, ma’aikatanta, da duk masu samun abin zama gari daga teku za su tsaya daga nesa. Sa’ad da suka ga hayaƙin ƙunarta, za su yi ihu su ce, ‘An taɓa samun birni kamar wannan babban birnin kuwa?’ Za su zuba ƙura a kawunansu, da kuka da makoki za su yi ta kururuwa, “ ‘Kaito! Kaito, ya birni mai girma, inda dukan waɗanda suke da jiragen ruwa a teku suka arzuta da ɗumbun dukiyarsa! Cikin sa’a ɗaya ta hallaka!’ “Ki yi murna a kanta, ya sama! Ku yi murna, ku tsarkaka! Ku yi murna, ku manzanni da annabawa! Allah ya hukunta shi saboda abin da ya yi muku.” Sa’an nan wani mala’ika mai ƙarfi ya ɗauki dutse kamar girman babban dutsen niƙa ya jefa cikin teku ya ce, “Da wannan irin giggitawa za a jefar da birnin Babilon mai girma ƙasa, ba za a ƙara ganin ta ba. Ba za a ƙara jin ƙarar kiɗin masu garaya da muryar mawaƙa, da na masu bushe-bushe, da na masu busan ƙaho a cikinki ba. Ba za a ƙara samun ma’aikaci na kowace irin sana’a a cikinki kuma ba. Ba za a ƙara jin ƙarar dutsen niƙa a cikinki kuma ba. Hasken fitila ba zai ƙara haskakawa a cikinki ba. Ba za a ƙara jin muryar ango da amarya a cikinki ba. Attajiranki, dā su ne manyan mutanen duniya. Ta wurin sihirinki, dukan ƙasashe sun kauce. A cikinta aka sami jinin annabawa, da na tsarkaka, da kuma na dukan waɗanda aka kashe a duniya.” Bayan wannan sai na ji abin da ya yi kamar ƙasaitaccen taron mutane a sama, suna cewa, “Halleluya! Ceto da ɗaukaka da iko sun tabbata ga Allahnmu, gama hukuncinsa daidai ne, mai adalci kuma. Ya hukunta babbar karuwan nan wadda ta ɓata duniya da zinace zinacenta. Ya rama jinin bayinsa a kanta.” Suka sāke tā da murya suka ce, “Halleluya! Hayaƙin yake fitowa daga wurinta ya yi ta tashi sama har abada abadin.” Dattawan nan ashirin da huɗu da halittu huɗun nan masu rai suka fāɗi suka yi wa Allah sujada, wannan da yake zaune a kursiyi. Suka tā da murya suka ce, “Amin, Halleluya!” Sa’an nan wata murya ta fito daga kursiyin, tana cewa, “Ku yabi Allahnmu, dukanku da kuke bayinsa, ku da kuke tsoronsa, babba da yaro!” Sai na ji wani abu mai ƙara kamar ƙasaitaccen taron mutane, kamar rurin ruwaye masu gudu da kuma kamar bugun tsawa mai ƙarfi, suna tā da murya suna cewa, “Halleluya! Gama Ubangiji Allahnmu Maɗaukaki ne yake mulki. Bari mu yi farin ciki mu kuma yi murna mu kuma ɗaukaka shi! Domin lokacin auren Ɗan Ragon ya yi, amaryarsa kuwa ta shirya kanta. Aka ba ta lallausan lilin, mai haske da tsabta ta sanya.” (Lallausan lilin yana misalta ayyukan adalci na tsarkaka.) Sai mala’ikan ya ce mini, “Rubuta, ‘Masu albarka ne waɗanda aka gayyace su zuwa bikin auren Ɗan Ragon!’ ” Sai ya ƙara da cewa, “Waɗannan su ne kalmomin Allah da gaske.” Da wannan sai na fāɗi a gabansa, don in yi masa sujada. Amma ya ce mini, “Kada ka yi haka! Ni ma abokin bauta ne da kai da kuma ’yan’uwanka waɗanda suke riƙe da shaidar Yesu. Ka yi wa Allah sujada! Domin shaidar Yesu ita ce ruhun annabci.” Sai na ga sama a buɗe can kuwa a gabana ga farin doki, sunan mahayinsa Mai Aminci da Mai Gaskiya ne. Da adalci yake shari’a yake kuma yaƙi. Idanunsa sun yi kamar harshen wuta, a kansa kuwa akwai rawani masu yawa. Yana da suna rubuce a kansa da babu wanda ya sani sai dai shi. Yana saye da rigar da aka tsoma a jini, sunansa kuwa Kalman Allah ne. Mayaƙan sama suna biye da shi, suna hawan fararen dawakai, saye da fararen tufafi masu tsabta na lallausan lilin. Daga bakinsa takobi mai kaifi ya fito. Da shi zai karkashe al’ummai. “Zai yi mulkinsu da sandan sarautar ƙarfe.” Yana tattake wurin matsin ruwan inabi na fushin Allah Maɗaukaki. A rigarsa da kuma a cinyarsa akwai wannan suna a rubuce, Sarkin sarakuna da Ubangijin iyayengiji. Na kuma ga wani mala’ika tsaye a cikin rana, wanda ya yi kira da babbar murya ga dukan tsuntsaye da suke tashi sama a tsakiyar sararin sama cewa, “Ku zo, ku taru don babban bikin nan na Allah, don ku ci naman sarakuna, jarumawa, da kuma manyan mutane, na dawakai da mahayansu, da kuma naman dukan mutane, ’yantacce da bawa, babba da yaro.” Sa’an nan na ga dabbar da sarakunan duniya da mayaƙansu sun taru don su yi yaƙi da wannan wanda yake kan farin dokin da kuma mayaƙansa. Amma aka kama dabbar tare da annabin ƙaryan nan wanda ya aikata alamu masu banmamaki a madadinta. Da waɗannan alamun ne ya ruɗe waɗanda suka sami alamar dabbar suka kuma bauta wa siffarta. Aka jefa dukansu biyu da rai cikin tafkin wuta ta da farar wuta mai ci. Sauran kuma aka kashe su da takobin da ya fito daga bakin wannan wanda yake kan dokin. Dukan tsuntsaye kuwa suka ci namansu iyakar iyawarsu. Na kuma ga wani mala’ika yana saukowa daga sama, yana da mabuɗin Abis yana kuma riƙe da ƙaton sarƙa a hannunsa. Ya kama macijin, wannan tsohon maciji, wanda yake shi ne Iblis, ko kuwa Shaiɗan, aka kuma ɗaura shi har shekara dubu. Ya jefa shi cikin Abis, ya kuma kulle ya sa hatimi a kansa, don a hana kada yă ƙara ruɗin al’ummai, sai shekarun nan dubu sun cika. Bayan wannan, dole a sake shi na ɗan lokaci. Na ga kursiyoyi inda waɗanda aka ba su ikon shari’a suke zama a kai. Sai na ga rayukan waɗanda aka yanke kawunansu saboda shaidarsu don Yesu saboda kuma maganar Allah. Ba su yi wa dabban nan ko siffarta sujada ba, ba su kuma sami alamarta a goshinsu ko a hannuwansu ba. Suka sāke rayuwa daga matattu, suka yi mulki tare da Kiristi shekaru dubu. (Sauran matattu ba su sāke rayuwa ba, sai da shekaru dubun nan suka cika.) Wannan fa shi ne tashin matattu na farko. Masu albarka da kuma tsarki ne waɗanda suke da rabo a tashin matattu na farko. Mutuwa ta biyu ba ta da iko a kansu, sai dai za su zama firistocin Allah da kuma na Kiristi za su kuma yi mulki tare da shi na shekaru dubu. Sa’ad da shekaru dubun nan suka cika, za a saki Shaiɗan daga kurkukun da yake, zai kuma fito don yă ruɗi al’ummai da suke a kursuyoyi huɗu na duniya, Gog da Magog, yă tattara su don yaƙi. Yawansu kuwa ya yi kamar yashi a bakin teku. Suka mamaye duk fāɗin duniya suka kuma kewaye sansanin mutanen Allah, birnin da yake ƙauna. Amma wuta ta fito daga sama ta cinye su. Aka jefa Iblis da ya ruɗe su cikin tafkin farar wuta, inda aka jefa dabban nan da annabin ƙaryan nan. Za a ba su azaba dare da rana har abada abadin. Sa’an nan na ga babban farin kursiyi da kuma wannan da yake zama a kansa. Duniya da sararin sama kuwa suka ɓace daga gabansa, babu wuri kuwa dominsu. Sai na ga matattu, babba da yaro tsaye a gaban kursiyin, aka kuma buɗe littattafai. Aka buɗe wani littafi, wanda yake shi ne littafin rai. Aka yi wa matattu shari’a bisa ga abin da suka aikata yadda yake a rubuce a cikin littattafai. Teku ya ba da matattu da suke cikinsa, mutuwa da Hades kuma suka ba da matattu da suke cikinsu, aka kuma yi wa kowane mutum shari’a bisa ga abin da ya aikata. Sa’an nan aka jefar da mutuwa da kuma Hades cikin tafkin wuta. Tafkin wutar nan kuwa shi ne mutuwa ta biyu. Duk wanda ba a sami sunansa a rubuce a cikin littafin rai ba, an jefar da shi cikin tafkin wutar nan. Sa’an nan na ga sabon sama da sabuwar duniya, gama sama na farko da duniya ta farko sun shuɗe, babu kuma wani teku. Na ga Birni Mai Tsarki, sabuwar Urushalima tana saukowa daga sama, daga Allah, a shirye kamar amaryar da aka yi mata ado mai kyau saboda mijinta. Na kuma ji wata babbar murya daga kursiyin tana cewa, “Yanzu mazaunin Allah yana tare da mutane, zai kuma zauna tare da su. Za su zama mutanensa, Allah kansa kuwa zai kasance tare da su yă kuma zama Allahnsu. Zai share dukan hawaye daga idanunsu. Ba sauran mutuwa ko makoki ko kuka ko azaba, gama tsofaffin al’amura sun shuɗe.” Wannan da yake zaune a kursiyin ya ce. “Ina yin kome sabo!” Sai ya ce, “Rubuta wannan, domin waɗannan kalmomi amintattu ne gaskiya ne kuma.” Ya ce mini, “An gama. Ni ne Alfa da kuma Omega, na Farko da kuma na Ƙarshe. Duk mai jin ƙishirwa zan ba shi abin sha kyauta daga maɓulɓular ruwan rai. Duk wanda ya ci nasara zai gāji dukan wannan, zan kuma zama Allahnsa, shi kuma zai zama ɗana. Amma matsorata, da marasa bangaskiya, masu ƙazanta, masu kisankai, masu fasikanci, masu sihiri, masu bautar gumaka da dukan maƙaryata, wurinsu zai kasance a cikin tafkin wutar da yake farar wuta mai ci. Wannan fa ita ce mutuwa ta biyu.” Ɗaya daga cikin mala’ikun nan bakwai masu kwanonin nan bakwai cike da annoban nan bakwai na ƙarshe, ya zo ya ce mini “Zo, zan nuna maka amaryar, matar Ɗan Ragon.” Ya kuwa ɗauke ni cikin Ruhu zuwa wani babban dutse mai tsayi, ya kuma nuna mini Birni Mai Tsarki, Urushalima, tana saukowa daga sama, daga Allah. Ya haskaka da ɗaukakar Allah, haskensa kuwa ya yi kamar lu’ulu’u mai daraja sosai, kamar yasfa, yana ƙyalƙyali kamar madubi. Yana da babbar katanga mai tsayi, mai ƙofofi goma sha biyu, da kuma mala’iku goma sha biyu a ƙofofin. A bisa ƙofofin an rubuta sunayen kabilu goma sha biyu na Isra’ila. Akwai ƙofofi uku a gabas, uku a arewa, uku a kudu, uku kuma a yamma. An gina katangar birnin a kan tushen gini goma sha biyu, a kansu kuwa akwai sunayen manzannin sha biyu na Ɗan Ragon. Mala’ikan da ya yi magana da ni yana da sandan awo na zinariya don awon birnin, ƙofofinsa, da kuma katangarsa. Birnin murabba’i ne, tsayinsa daidai ne da fāɗinsa. Ya auna birnin da sandarsa ya kuwa sami mil 1,400 (wajen kilomita 2,200) tsawonsa, fāɗinsa da kuma tsayinsa daidai suke. Ya auna katangarsa ya kuma sami ƙaurinta kamun 144, bisa ga ma’aunin mutum, wanda mala’ikan ya yi amfani da shi. An yi katangar da yasfa, birnin kuma da zinariya zalla, yana kuma ƙyalli kamar madubi. Tushen ginin katangar birnin kuwa an yi masa adon da kowane irin dutse mai daraja. Tushe na farko an yi shi yasfa, na biyu saffaya, na uku agat, na huɗu zumurrudu, na biyar onis, na shida yakutu, na bakwai kirisolit, na takwas beril, na tara tofaz, na goma kirisofuras, na goma sha ɗaya yasin, na goma sha biyu kuma ametis. Ƙofofi goma sha biyun nan lu’ulu’ai goma sha biyu ne, kowace ƙofa an yi ta da lu’ulu’u guda. Babban titin birnin kuwa an yi shi da zinariya zalla, yana kuma ƙyalli kamar madubi. Ban ga haikali a cikin birnin ba, domin Ubangiji Allah Maɗaukaki da kuma Ɗan Ragon ne haikalin birnin. Birnin ba ya bukatar rana ko wata su haskaka shi, gama ɗaukakar Allah tana ba shi haske, Ɗan Ragon kuwa shi ne fitilar birnin. Al’ummai za su yi tafiya cikin hasken birnin, sarakunan duniya kuma za su kawo darajarsu cikin birnin. Ba za a taɓa rufe ƙofofin birnin da rana ba, gama ba za a yi dare a can ba. Za a kawo ɗaukaka da girmar al’ummai a cikin birnin. Babu wani abu marar tsarkin da zai taɓa shiga cikin birnin, babu kuma wani mai aikata abin kunya ko ruɗi da zai shiga, sai dai waɗanda aka rubuta sunayensu a cikin littafin rai na Ɗan Ragon. Sai mala’ikan ya nuna mini kogin ruwan rai, mai ƙyalli kamar madubi, yana gangarawa daga kursiyin Allah da na Ɗan Ragon, yana bin tsakiyar babban titi na birnin. A kowane gefen kogin akwai itacen rai mai ba da ’ya’ya goma sha biyu, yana ba da ’ya’yansa kowane wata. Ganyayen itacen kuwa saboda warkar da al’ummai ne. Ba za a ƙara samun la’ana ba. Kursiyin Allah da na Ɗan Ragon zai kasance a cikin birnin, bayinsa kuma za su yi masa hidima. Za su ga fuskarsa, sunansa kuma zai kasance a goshinsu. Ba za a ƙara yin dare ba. Ba za su bukaci hasken fitila ko hasken rana ba, domin Ubangiji Allah zai haskaka su. Za su kuwa yi mulki har abada abadin. Mala’ikan ya ce mini, “Waɗannan kalmomi amintattu ne gaskiya ne kuma. Ubangiji, Allahn ruhohin annabawa, ya aiki mala’ikansa, don yă nuna wa bayinsa abubuwan da za su faru nan ba da daɗewa ba.” “Ga shi! Ina zuwa da wuri! Mai albarka ne wanda yake kiyaye kalmomin annabcin da suke cikin wannan littafi.” Ni, Yohanna, na ji, na kuma ga abubuwan nan. Kuma sa’ad da na ji, na kuma gan su, sai na fāɗi a ƙasa a gaban mala’ikan da yake nuna mini su, don in yi sujada. Amma ya ce mini, “Kada ka yi haka! Ni abokin bautarku ne, kai da ’yan’uwanka annabawa, da kuma waɗanda suke kiyaye kalmomin wannan littafi. Allah za ka yi wa sujada!” Sa’an nan ya gaya mini cewa, “Kada ka rufe kalmomin annabcin littafin nan, domin lokaci ya yi kusa. Duk mai yin laifi yă ci gaba da yin laifi; duk mai aikata ƙazanta yă ci gaba da aikata ƙazanta. Duk mai aikata abin da yake daidai, yă ci gaba da aikata abin da yake daidai. Kuma duk wanda yake mai tsarki, yă ci gaba da yin abin da yake da tsarki.” “Ga shi, ina zuwa da wuri! Ladan da zan bayar yana tare da ni, kuma zan ba wa kowa gwargwadon abin da ya yi. Ni ne Alfa da kuma Omega, na Fari da kuma na Baya, Farko da kuma Ƙarshe. “Masu albarka ne waɗanda suka wanke tufafinsu, don su sami izinin ci daga itacen rai su kuma shiga birnin ta ƙofofi. Waɗanda suke waje kuwa karnuka ne, masu sihiri, masu fasikanci, masu kisankai, masu bautar gumaka, da duk wanda yake ƙaunar ƙarya yake kuma aikata ta. “Ni, Yesu, na aiko mala’ikana ya ba ka wannan shaida saboda ikkilisiyoyi. Ni ne Tushe da kuma Zuriyar Dawuda, da kuma Tauraron Asubahi mai haske.” Ruhu da kuma amarya suna cewa, “Zo!” Duk wanda ya ji kuwa, yă ce, “Zo!” Duk mai jin ƙishirwa, yă zo; duk mai bukata kuma, yă ɗibi ruwan rai kyauta. Ina yin wa duk wanda ya ji kalmomin annabcin wannan littafi gargaɗi. Duk wanda ya ƙara wani abu a kansu, Allah zai ƙara masa annoban da aka bayyana a littafin nan. Duk wanda kuma ya yi ragi a kalmomi daga littafin annabcin nan, Allah zai ɗauke rabonsa na itacen rai da kuma na birnin nan mai tsarki, waɗanda aka bayyana a littafin nan. Shi da ya shaida waɗannan abubuwa ya ce, “I, ina zuwa da wuri.” Amin. Zo, Ubangiji Yesu! Alherin Ubangiji Yesu yă kasance tare da mutanen Allah. Amin.